KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 2 BY ayshay bee
Www.bankinhausanovels.com.ng
Asubancin barin Zaria Aliyu yayi coz ba zai iya zama yana ganin abin takaici ba. Fisabillilahi upon all matan duniya a rasa da wacce za a hada shi sai daya daga cikin yaran nan, yaran da basu San mai ke musu ciwo ba kai at all ma shi ba ajin su bane, yaushe su ka girma duka duka ma ko ishashen hankali da ilimi he don’t think su na dashi da har zasu iya mu’amala da mutanen shi. Shi Mutum ne mai hulda da manyan mutane shiyasa tun farko yana mi wayyayar mace wacce ba zata bashi kunya ko kadan ba duk bayan wadannan ma Zahrau ba choice in shi ba ce ko kadan ba ta cikin irin maccen da yake so.1
Shi dai Umar hakuri ya dinga bashi da kuma bashi shawaran yayi biyayya ga iyayen shi sai ya ga alkhairi da bai taba expecting ba.1
••••••••••••
Cirkowa suka yi gaban Zahrau da ke ta rawan dari, zazzabi ne mai zafin gaske ya rufe ta lokaci daya sai sambatu ta ke yi. Ummiy ce ta kalli Zahrau ta girgiza kai “gashi nan ai tun ba a kai ko ina ba, ni ban ga dalilin da yasa za a fara irin tunanin nan ba”
“Zuwa zanyi kawai in kira Mami ta zo ta gane wa idonta abinda ke faruwa in kuma sun shirya rasa ta ne fine” Maijidda ta fada tana share guntun kwallan da ke idonta. Har ta kai baki kofa Nanah ta yi saurin tare ta “Haba Dan Allah wai Ku me ke damun Ku ne, yanzu ke kika je kika fada musu da wanne kike so suji, kar fa ki manta halin da Abbah ya Shiga a dalilin abinda mahaifin Farida ya musu suna kuma ganin su samu solution sai kije ki kara daga musu hankali? Gani zasuyi sunyi failing ta a matsayinta na yar su shi ya sa ba za ta iya musu
biyayya ba. Kuma ita ma kamata yayi Ku kwantar mata da hankali ba Ku dinga daga mata ba wai shi Uncle Aliyn annoba ne ko kuma makiyinta ne. After all yanda zazzabin nan ya rufe ta tausayinta ya kamata kuji ba Ku kara dagula mata lissafi ba” Ummiy ce ta katse ta “Ba gwara Annoban da kika kira ba akan Uncle Aliyn, Nanah kina ganin shi ne kawai Allah kadan ya San iya tarin muguntan da ke cikin shi. Wlh auren nan ba alkhairi a cikin shi ko kadan Dan kawai cutan ta za ayi”
“Subhanallah shin Ummiy ke ke da ikon Allah ne ka kuwa da zaki yi rantsuwan nan”
“Ai juma’ar da zata yi kyau tun daga laraba ake iya gane ta, mu ba zamu yadda muna kallo a kai ta ajalin ta ba”
Maijidda ta fada tana hararan Nanah
“Ehmm tun da kuka haife ta ba” Nanah ta fada cikin fushi dan zuwa yanzu sun fara kai ta bango.
Hayayako mata su kayi tayi banza da su ta Shiga baya debo ruwa a wani roba da towel. A kai tazo tana shasha fa mata ko taji saukin ciwon.
************
Mami na zaune da Ammah suna tattauna hidimomin bikin wayanta ya dau kara. Aliyu ne daman ta San dole yau sai ya neme ta shiyasa ta share batunsa da ya zo da safe shaida masa batun komawarsa Abuja.
“Mami an wuni lfy?” Shiru mami tayi tana nazarin muryar shi daga ji ta San yana cikin damuwa
“Aliyu lafiya naji ka haka?”
“Mami Dan Allah wani Alfarma nake nema a wurin ki”
“Ince wa Abbah ba ka son auren ko?”
Shiru yayi ganin ta dago inda ya dosa, ko da yake daman ya San zata ganen.
Dan Jim tayi kafin ta cigaba da magana “Tun farko shi ya sa raina bai wani dau abin daman na San a kaina komai zai kare. Abinda zan iya ma ka shine kawai in ba ka hakuri ka amshi auren hannu bi biyu in kuma ka ki ai mahaifin ka ne kunfi kusa ka neme shi, Aha banga dalilin da za Ku Sani a tsakiya ba” kashe wayan ta yi ta cigaba da sababinta don tunda su Ummiy su ka dawo su ma suka sata a gaba.
Aiko Maijidda ce tayi Sallama game da sanar mata da rashin lafiyar Zahrau.
Girgiza kai mami tayi hade da ajiyar zuciya “mu je inga jikin na ta” ta fada hade da mikewa.
A can ta iske Ammah kasancewar tunda Aliyu ya kira ta Ammah ta ce bara ta dubo abu a side inta. Sosai su ka matsawa Zahrau ta ci Abinci sannan ta Sha magani, still dai ba su gushe ba sai da su ka mata nasiha kaman yadda su ka saba sannan su ka ja kunnen su akan kar Wanda ya sake ya sanar da Abbah ko Baffah.
*****************
Ganin da gaske ba fa sa auren za ayi kuma rana ma sai kara matsowa yake yasa su Ummiy hakura su fawwala ma Allah komai bayan nasihohin da Nanah ta dunga musu.
Gadan gadan su ka fara shiryawa bikin, sun gayyaci kawayen su na Zaria da kuma Kaduna sai some few daga katsina.
A bangaren su mami ko, Anty Zainab aka ba wa kudi ta hado mata hadadden kayan daki hatta lefe canja mata su ka yi set biyu sannan an mata dinkunan bikin ma kala kala, sosai su ke gyara Amaryar da ita dai kawai bin su take da ido. Kabon Aliyu ba a kashe ba ma ba su bi ta kanshi ba kwata kwata. Abbah kam cewa yayi In daura auren ya sako ta a ranar. Anty Zainab ta labarta mi shi hakan ya sa ya baro duk abinda ya ke a Abujan ya iso Zaria gudun kar su ga kaman bai musu biyayya ne. Umar ne ya tsaya mai kan komai Dan in dai tashi ne ba za ayi koman ba.
3 days to auren
They are not with the idea a yi biki dry hakan ya sa su ka shirya bridal shower sai kuma kamu na kowa da kowa. Hira su ke suna planning yanda bridal shower insu zai kasance su da wasu kawayen su da su ka zo bikin daga wani gari. Adnan ne ya musu hade da sanar musu Ya Umar na neman daya daga cikin su, Ummiy cewa tayi Allah ya kasheta ta he wurin shi Maijidda kan daman wani aikin ta ke shiyasa ko ta Kansu bata bi ba. Nanah ce dai ta tashi da fati kawar Zahrau da su kayi secondary tare kuma presently ma tare su ke a Uni.
Tsaye su ka tadda shi shi kadai yana dadanna waya, Nanah ce ta fara gaishe shi sannan fati, cikin fara’a ya amsa musu. Kallon Nanah yayi yace Nanah Aisha ko, gyada mishi kai tayi coz ba tayi mamakin yanda aka yi ya Santa ba Dan duk zuwan Aliyu Kaduna tare su ke zuwa.
“Daman na neme Ku ne inji ko kawai shirye shiryen da kuke Wanda ya kamata mu Sani”
“Ba wani abu bane Bridal shower ne kawai kuma all girls event nema”
“Ma Sha Allah ko akwai abinda kuke bukata?”
“Aa su Mami sun tanadar mana komai”
Murmushi yayi sannan yace “Still dai akwai hakkin da ya kamata mu sauke, nawa zai ishe Ku”
“Allah muna da komai ka bashi kawai”
“Aa ba fa a haka ko ba haka ba baiwar Allah, ke miye sunanki” ya fada yana kallon Fati
“Fati” ta bashi amsa
“Ashe takwarar Amaryar ta mu ce ma, ke fada min yanda zai ishe Ku tunda ita taki”
“Ina ganin KO nawa ka bada zai yi tunda already muna da komai”
Bandir in N500 guda hudu ya miko ma ta N200,000 kenan, amsa fatin tayi su ka mai godiya. Dai dai nan Aliyu ya zo wuce wa, a tare su ka gaishe shi ya amsa a daddare, he didn’t even spare them a second glance ya ce wa Umar in ka gama ka same ni a gidan can sannan yayi tafiyan shi.
Umar dinne ya kalli Nanah ya ce “Bani numbanki”
Karanta mishi tayi yana sawa sannan yayi dialling numban shi ya fito kan wayanta “Ga numba na in case in Kuna son wani abu sai ki kira ni”
••••••••••••••••••••••
A side in Babban Yaya su ka sa aka musu decorating inda za suyi Bridal shower. Ankon gown da cape top suka yi sai Amaryar da ta sa hadadden dark purple gown ba karamin kyau tayi ba abinka da farar mace.
Nan dai suka yi nishadin su aka yanka cake sannan su kayi ta pictures aka kuma Sha kida hatta Amaryar ta saki jikin ta ganin duk frnds ne a wurin sai ta ga kaman fun time kadai suke having.
Washegari aka yi kamun da sai ka rantse dinner ne, grandeur concept su ka musu decoration a Ras event center. Shiga tayi in light purple and golden, a wurin bridalhub su kayi ordering Asoebin sannan a ka dauko lbvmakeovers. Ba karamin kyau ta haka ma event hall din decoration in gargajiya ne amma ba karamin kyau yayi ba, every where is screaming money.
Sai da Umar ya hada da kiran Babban Yaya sannan Aliyu ya hakura ya fara shirin zuwa wurin kamun.
Brown shadda da aka wa surfanin Golden colour ya sa da Babbar riga sai hular shi da ake kira zanna bukhar sannan ya sa agoga da wani cute glasses da ya ke kara wa idanuwan shi kyau, he looks so handsome sai dai duk a daure ya ke abuwawan nan coz everything is against his idea. Ko da aka ce mishi da amarya zai tafi fir yaki zancen game da nuna wa Abokan nashi shi fa bai son raini.
Ko da aka isa hall din ma entrance in Amarya da Ango daban daban ne. Zaman kusa da ita ma sai da Umar ya ta hada shi da Allah and guess what? They just makes a perfect match, dukkansu farare ne sai dai ta fishi haske sosai. Pictures a ka fara daukan su ta ko ina, jiya ke kaman ya tashi ya hana coz a wurin shi ba karamin ci baya bane a ga hoton shi da yarinyar a matsayin couples. A bangaren Zahrau ma ji take kaman ta yi tsuntsuwa coz she is not comfortable ko kadan ma karfin hali kawai take.
Anyi sha’ani, an ci ansha sannan kuma an Sha kida da nishadi Dan musamman har comedians aka gayyato, shi kanshi MC ma comedian.
Duk wannan abubuwan ba abinda ya hada Ango da Amaryar, daidai da kallo kuwa.11:00 Am
Safiyar Asabar+
Dubban mutane su ka shaida daurin auren Aliyu Abubakar Tafida da amaryarsa Fatima Al-ameen Turaki. Daurin auren ya samu halittar mutane da dama Wanda ya hada da Manyan sojojin Nigeria, Manyan malamai, masu sarauta, yan siyasa dama ma’aikatan gwamnati ta wani bangarorin Nigeria. Both Abbah da Baffah mutane masu hulda da jama’a dayawa shiyasa in kaga dimbin mutane da motoccin da suka samu halattar auren sai kayi tunanin yar wani mai fada aji a kasan nan ne tayi auren.
Gagarumin Reception mazan suka wuce daga wurin daurin auren,
Ba kauyanci ba ni dai nace ba irin cuisines in da babu a wurin nan, Naira ta Sha kuka.
Dole ta sa Aliyu sakin ranshi saboda dimbin mutanen da suka zo taya shi murna su a cewan su kenan shi kanshi Mutum ne mai jama’a sosai.
*************
A can gida ko, ko ta ina ya kicime da mata da kuma yara sai kai kawo su ke a ko ta wani bari na gidan.
Amaren dole ya sa su barin sashen su da ke cikin gidan su ka koma bangaren Babban Yaya. Ita kanta Amaryar tayi mamakin kawayen da ta gani duba da yanda yanayin auren ya zo, ita da kanta ba tayi gayyata ba aikin su Maijidda ne da kuma su fati.
Tana ganin Sha daya yayi gaban ta ya fadi, shakka babu yanzu haka daura auren ake, auren ma nata kuma ba da Abdul rahman ba ba kuma Sulaiman ba A’a da Uncle Aliy mutumin da tun tasowarta ba Wanda ta ke tsoro irin shi, ganin shi kadai fadar mata da gaba yake balle magana ta hada su.
Bayi ta shi ta dauro Alwala hade da gabatar da Sallah raka’a biyu tana rokon Allah neman dukkan abin Alkhairi a rayuwarta. Kawayenta suka sa ta a gaba suna ta tsokanar ta wai tana tsoron auren share su tayi ta cigaba da azkar inta amma abin ka da taron yan bodin sai da su kayi nasarar sa ta kuka, nan kuma sai su ka koma lallashinta gama daman sun Santa da saurin kuka, ai ko sai da ta samu yan’uwan da suka taya ta kukan.
Set in kaya kala biyu aka mata hakan ya sa aka jera daya a nan bangaren shi da ke kusa da na Babban Yaya dayan kuma Abuja a ka kai.
Samun Abbah Aliyu yayi ya sanar dashi suna da wani important aiki da za suyi ranar Monday a Abuja, ko kallon banza Abbah bai mai ba balle ya hana shi sai ma ce mishi da yayi ita ma Zahrau ranar Monday din za a kai ta can Abujan saboda bai ga reason din da zai sa a barta a nan ba bayan an daura auren.
Sarai ya gane Abbah ya dago shi ne ya sa ya mai hakan sai ma yayi dana sanin abinda ya fada wannan shi ne anyi gudun gara an fada gidan zago gashi kuma ba zai iya samun Baffah ba ko ba komai ido ai da kunya.
Cigaba da sha’anin bikin aka yi, Walima na mata kawai Wanda aka yi a cikin gidan, malama ce wacce tayi wa’azin.
Monday
4:00 pm
Ba abinda ya rage na game da shirin kai amarya gidan ta da ke babbar birnin tarayya Abuja.
Ba wasu mutane masu yawa bane, close relations ne kawai mota uku.
Ta sha kuka idanun ta duk sun kumbura, kawayen nata ma sai da aka Samu masu tayata kuka hatta kannen ta shahida, Yusrah da Adnan a bar su a baya ba.
A haka aka kaita wurin iyayen nata domin su sauke nauyin da ke kansu. Daga Mami har Amman dauriyan yi Mata magana su kayi coz su ma ba karamin alhinin rabuwa da ita za su yi ba. Nasiha su ka Mata mai ratsa jiki sai dai jinsu kawai ba wayai ta na fahimtar abinda su ke fadin ba Dan tuni ta yi nisa a duniyar tunanin rayuwar da zata afka.
Bayan an fita da ita wani irin Farin ciki ne hade da annashuwa ya ziyarci zuciyoyin iyayen nata Dan ganin sun sauke nauyin da Allah ya basu. Sun sauke Amanar da Dan’uwansu ya bar musu.
A jere motoci ukun ke tafiya… Umar ne ke tukin second car tare da Nanah, fati sai Anty Rukayya last car in kuma Deedat ke tuki da Yusrah a gefen Shi sai Anties biyu da shahida.
6:30 pm a cikin Abuja ta musu a gidan Aliyun da ke Asokoro Villa. Har an yi magriba da ke lokacin sanyi ne so suna isa Sallahn su ka fara gabatarwa. Ita dai Zahrau dar dar dar kawai ta ke don ta kasa yadda nan ake nufin ta zauna a matsayin gidan auren ta kuma wai da Uncle Aliy. Ya ilahi anya su Abbah sun duba abin nan kuwa.
Gidan ya hadu sai santin Shi suke tayi brain ma da aka sa kayan nata.
Babban gida ne da ka shigo side in mai gadine ta left side sai parking lodge na gaban Shi. Wani small garden ke facing wurin an shuka differents kinds of fruits a wurin an shinfide da grass carpet ta gaban Shi ko flowers ne da sukayi brightening wurin so alluring. Steps uku ne zai sada ka varendar first parlor in Wanda akayi decorating in Black and ash, kujeru, carpets, pots of flowers da frames in pictures. Dayan parlorn in coffe brown da milk, kujerun kadai abin kallo ne balle a kai da Babban television in da ke a jiye a wurin. By the right side corridor ne na 2 bedrooms, daya daga ciki Shi ne na Amarya, in purple and cream aka shirya Mata dakin da ka ganshi kasan kudi yayi kuka sai dayan room in ne dai empty da Alamun gida yayi Shi ne Har zuwa nan gaba. By the left nan ma 2 bedrooms ne nan master bedroom ya ke Wanda ya ke shirya in Royal blue gaba daya, sai dayan room in computers in Shi da bench in books ne a wurin da Alamun dai study room ne. Dinning ne kafin ka kai rooms in da suke left side in Shi ma sai an sauka daga steps tukunna sai kitchen a gefen Shi, kayan kitchen in ba karamin kyau su kayi ba in lemon green and ash ne komai ma masha Allah za a ce.
Sai da suka yi Sallah sannan Aliyun ya zo su ka gagaisa ya sa aka kawo musu Abinci.
Sun dade suna rarrashin ta da yi Mata nasiha Banda Ummiy da ke bata shawaran in ya Mata Wani Abu ta fadawa Abbah kar ta yadda ya wahalar da ita a nan har Maijidda sai da ta bata rashin gaskiya su ka nuna Mata tun da an riga an daura hakuri Shi ya fi komai.
Washegari bayan Azahar su ka shirya komawa Zaria bayan sun Kara yi Mata nasiha, da kuka ta raka su haka duk kawayen nata da suka zo kukan su ke yi sai Anties in nasu ne ke musu fara. Sai da Umar da Deedat su ka sa baki tukunna su ka yi shirun.
Da gudu ta koma cikin gida ganin motansu ya fara tafiya, dakin da aka kira nata ta shiga tana bi da kallo komai na gidan ya Mata in aka cire Shi mai gidan da kanshi, ko Wani irin rayuwa za suyi? Wahala mana za ki ta sha wata zuciyar ta bata amsa.
A hankali ta fara tunano rayuwarta gabadaya, irin wahalan da su ka sha hannun Shi da kuma irin ta ta rayuwar soyayyar…
Asalin labarin…Justice Abubakar Tafida Dan asalin
Unguwar Alkali dake cikin Zaria city ne.
Family insu family sun gaji sarauta da malinta ta ko ina, yana Dan shekara Goma Sha biyu Allah yayi wa mahaifin shi rasuwa mahaifiyar shi daman tun wurin haihuwar shi ta rasu, hakan ya sa rikon shi ya koma wurin Baffahn shi da su ke abokannan wasa da mahaifin shi.+
Ya taso cikin gata da tarbiyya na gari ko kadan bai San maraici ba don ko ya rike shi cikin gaskiya da Amana.
Ya’yan’ Baffahn na shi biyu Ahmad da Al-ameen Turaki. Suna matukar girma ma shi kasancewar ya girme mu su nesa ba kusa ba haka kuma Kansu a hade yake.
Mami yar asalin jahar Gombe ce, sun hadu da Abbah wurin bikin Abokin shi da yaje can Gomben ita kuma yar’uwar Amaryar ce. Kaman wasa magana mai karfi ya Shiga tsakanin su har su kayi aure.
A gaskiya layout ya siya Babban fili yayi gini dayawa a cewar shi shi da kannen shi in sun tashi aure.
Muhammad ne Babban dansu sai Zainab sai Aliyu da ga nan kuma haihuwar ta tsaya musu don basu yi zaton za su kara samun wani ba. Aliyu na da shekara biyu Kannen baban sa suka yi aure su ka tare a gidajen da yayannasu ya tanadar musu. Ammah yar nan cikin Zaria ce, Mummy KO cousin in Mami ce ta gama karatun secondary ta zo mata Hutu a nan su ka hadu da Daddy Al-ameen.
Su gina zuri’a me kyau wurin fahimtar juna da kuma tafarkin Addini. Bayan shekara daya da auren Ammah ta haifi Deedat sai dai mummy shiru kake ji amma da yake ance komai lokaci ne abin bai dame su ba.
Bayan shekara Hudu Mami ta same cikin Hamza, sunyi farin cikin ba kadan saboda ba su yi tsammani za ta kara haihu ba saboda a lokacin Aliyu ya shekara bakwai ma. Bayan 2 years mami ta kara haifo yan biyu Amina (Ummiy) da Hauwa’u (Maijidda) Wanda kuma sai lokacin Mummy ta samu cikin ta na farko. Ba karamin wahala yake bata ba tun yana karamin shi amma sun danganta hakan da haihuwan farko ne shiyasa. Haihuwar yan biyun da one month mummyn ta haifo Fatima (Zahrau) bayan wahalan nakudan da ta gama sha Dan har an yanke shawaran yi mata operation ma Allah yayi ikon shi.
Tana da wata bakwai Mummyn ta tafi Gombe ganin gida, Daddy (Al-ameen Turaki) ya je dauko ta a hanyar su ta dawo wa suka yi hatsari.
Kiran su Abbah aka yi aka sanar musu, a gigice suka isa garin Gombe kasancewar inda suka samu accident in ba nisa da cikin Gari ya sa aka maida su Babban Asibitin Gomben.
Ba karamin rauni su ka ji ga karaya ko ta ina motan nasu ma kaca kaca yayi, wani ikon Allah Ba wani Abu da ya samu Fatima sosai.
Sati daya a na musu treatment ba wani cigaba har a yanke shawaran fitar da su waje sai dai suna nasu Allah na nashi domin a ranar Mummy ta amsa kiran ubangiji, sunji mutuwar ba kadan ba ya girgiza su haka wurin yan uwanta. Jin Mutuwar Mummy ya girgiza Daddy ba kadan ba tunda daga ranar ba su kare gane kan shi ba, Cigaba da shirin fitan su ka yi suka mai da shi Ahmadu Bello University Teaching hospital (Shika).
Awanni Uku bai yi cikakku ba ya bi bayan matar shi. Kulli nafsin za’ikatul maut babu makawa kowa sai ya tafi lokaci kawai ake jira. Tausayin kan Zahrau ya koma ganin tun kafin ta shekara daya a duniya ta zama marainiya ba uwa ba uba, hakan ya sa su ka dauki son duniya su ka daura mata. Yan’uwan mahaifiyarta sun so a basu ita Abbah yaki yadda ganin Mami na shayarwa ya’ya’ har biyu ya sa ya ba wa Ammah ita. Sai dai har yau Zahraun bata San cewa iyayen nata sun rasu ba Dan ita duk a cewar ta Ammah da Baffah ne suka haife ta. Sun dai San akwai Mummy da Daddy da suka rasu ana cewa su dinga musu addu’a.
Shahida, Yusrah da Adnan Ammah ta haifa bayan Deedat. Gaba daya Zuri’an nasu kenan.
August 2005
Zahrau ce zaune kan wani dakali wurin kan kwanar layin gidan su, daga wurin tana iya hango ko mai da ke faruwa a kofan gidan, kayan Islamiyya ne a jikin ta Dan da Alamu an tashe su daga Islamiyyan ne, Yunwa ne ya kora ta tabar yan’uwanta sai dai tsoron abinda take gani a kofan gidan nasu ya hanata komawa.
Tana zaune ta marairai ce kaman tayi kuka sa’anninta suka wucewa da gudu wai suna rige rigen zuwa gida, Turus su kayi ganin ta a zaune.
“Sarkin jin Yunwa gidan kenan” Ummiy ta fada cike da tsiwa, sannan Maijidda ta amshe da fadin “Kai wlh Zahra kallo ya wuce ki in gaya miki bugun tsiya mu ka musu Hadiza sannan muka tsero kar su hada mu da malamai kinsan su shegen tsoro ne dasu” “Hmm duk ba wannan ba” ta katse su “Ku kalli kofar gida Ku gani”
A tare suka maida hankalin nasu kofar gidan abinda su ka gani ba karamin kidima su yayi “Mun Shiga Uku, Uncle Aliy ya dawo Hutu” Maijidda ta fada tana zaro idanu, Ummiy ko wuri ta samu ta zauna tana fadin “ban ga laifin ki da kika zauna ba Zahra ni Babban takaici na ma wancan Abokin nashi mai iyayin tsiya yanzu ya tsare mutum da turanci shi ala dole Dan boko” Hamza ne ya zo wuce Dan shi har yaje gida ya canja kaya wurin Abokin shi ya je amsan abu. “Lafiya har yanzu ba Ku koma gida ba?”
“Ina fa lfy ka na ganin Uncle Aliy na gida” Ummiy ke magana cike da tsiwan da ya hali nata. Dariya ya kwashe dashi hade da fadin “Haba shiyasa na ga ana turo baki, ko ba komai rashin jin Ku zai tafi na kwana biyu” Gwalo ya musu. Hararan shi Ummiy ta yi Maijidda ta ce “Haba Hamza harda kai, shknn” Dan darawa yayi sannan ya ce “Ku ne ba Ku ji gashi ba Ku son karatu shiyasa ba Ku shiri da Yaya Aliyu” Juya mishi kai su kayi su ka yi banza dashi, Zahrau ko yunwan da ta ke ji ne ke kwakular cikin ta, rabon ta da Abinci tun breakfast. Za ta ci suka azzaza be ta taso su tafi wai su kama benci da wuri yanda za su yi rashin Mutunci.
Ganin da gaske su ke ba za su tafi ba yasa Hamza yayi tafiyan shi ya barsu.
Hadari ke haduwa a wurin kafin kace mai ruwa mai karfin gaske ya sauko kasancewar watar August ne.
Da gudu su ka tashi su ka fake a jikin wani gida amma duk da haka sai da suka jike. Tsaye suke a wurin suna rawar dari har aka kira Sallahn magariba sannan ruwan ya tsagaita sai da su ka hango mazan gidan su sun fita masallaci sannan su ka ruga gidan.
Ba su San gudun gara su kayi su ka afka gidan zago don a bakin gate su ka hadu da Aliyun yana sauri kafin a tada Sallah. Kallo ya bi su dashi ganin yanda Uniform insu da jakukunan su su kayi sharkaf da ruwa, harara ya bi su dashi ya jawo Ummiy da Maijidda ya gwara Kansu wuri daya, wani irin gigicewa su kayi amma tsoron da suke mai ya hana su kuka. Koma yayi kan Zahrau ya ja kunnen ta sannan ya rankwashe ta a kai bare baki tayi zata fara kuka, kallon da ya mata ya sa ta yin saurin mai da kukan. “Bari in dawo daga Sallah sai kun fada min inda kuka tsaya Ku ka jika jikinki” ya fada hade da yin saurin karasa wa masallaci. Su kuma a guje su ka karasa cikin gidan.