KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 3 BY ayshay bee
Www.bankinhausanovels.com.ng
6:06 pm
5:30 na yammaci ake tashin su amma sai shida su ka isa gida a sanadiyar fadan da suka tsaye. Kaman yanda suka saba gudu suke ta shatatawa sai ka rantse gudun tseran rai su ke.
Flowers in da ke kofan gidan ya sa ya ke son zama a wurin kasancewar shi mutum mai son iska. Kaman kullum da yamma yake zaman zaka ganshi da abokanan shi kala kala suna hira sai dai yau shi da Umar ne kadai.
Abokan takan su da Umar in ya fara ne time in lokacin da suke JSS1, suna labari ne sai Umar ya ke ce shi ma dan Zaria ne, “ta wani area?” Aliyu ya tmby, “Gaskiya layout but kwanan muka yi relocating” Gano wa da suka yi su yan unguwa daya ne ya sa suka fara shiri sosai. Wasa wasa har iyayen su suka San juna, presently kam tare suke a ke kai su in zasu koma haka dawo wa har ma da visiting tare ake zuwa musu, duk inda kaga daya ko shakka bbu dayan ma na nan. Zuwan yanzu sun wuce abokanai sai dai mu kira su aminai ko ma yan’uwa.
Umar in ne ya fara hango su suna tahowa “Ga fa mutanen ka sun Faso” ya fada yana kallon irin gudun da suke, shi kam ko kadan ba sa bata mai rai, yaran kawai abubuwan su dariya da nishadi suke sa mai.
“Mtsww” tsaki Aliyu ya ja hade da fadin “yara sai kace dabbobi, ba su taba komai cikin natsuwa”
“Aliy kenan they are just a kids ai zasu dena”
Su na ganin shi a bakin gate su ka daina gudun hade da Shiga taitayin su, a daddare su ka gaida su “little angels, are you back?” Umar ya tambaye su.
Dukkan su bin shi suka yi kawai da kallo ba wai Dan sun fahimci abinda yake nufi ba. “Can’t I have an answer?” Ya daga musu gira.
Da za a ba Ummiy wuka to ba abinda zai hana ta caka mishi Dan ita a ganin ta ya ma fi Uncle Aliy iyayi don shi bai musu turancin saboda ya San basu iya ba.
“Me kuka tsaya yi a hanya?” Kaman daga sama suka ji tambayan Aliyun
Dukkansu shiru suka yi suna kallon shi ba wacce ta iya bashi amsa.
“Ba magana nake muku ba dukkanku kun wani bini da wasu munanan idanuwanku na mujiya, ni sa’an Ku ne?”
Da sauri suka sadda kan nasu kasa “maza Ku Shiga ciki Ku cire kazaman kayan da ke jikin Ku Ku dawo yanzun nan”
Da sauri su ka nufi gate in Shiga, yanda suke rige rigen fara wuce ne ya ba Umar dariya “Aliy wlh ba ka da kyau ji yanda su ke reacting kaman sunga mala’ikan mutuwa”
Ba su dauki cikakkun mintuna goma ba su ka dawo kiran da yake musu, daidai lokacin Napep ya sauke Anty Zainab, mantawa su ka ma yi da Aliyu na wurin su ka ruga wurinta suna “Oyoyo ga Antyn kano”
Ita ma cikin Murna ta bude musu hannunta su ka karasa ta rungume su duka Ukkun “Oyoyo yan kannena, I miss you”
Sai da ta sake su Umar ya gaishe ta yana fadin “Anty kin mana zuwan bazata” Murmushi ta yi sannan tace “Abinka da yan Jami’a”
Sai a sannan Aliyu ya dago kanshi cike da girmama wa yace “Ina wuni Anty zee, kin sha hanya” hararan shi tayi “Ba zan amsa ba wato kai jin kai sai kowa ya gama magana za ka yi ko?”
“Anty ba fa haka bane, kinga ai zanyi distracting insu kema kuma zaki rasa wa zaki ma responding”
Girgiza kai tayi tace “Allah ya shiryeka Aliy, mu karasa ciki ko”
“Assalamu Alaikum” aka fada daya sa dukkan su juyawa Dan ganin me magana.
Dan matashin saurayi ne kusan sa’an Aliyun da yarinya mace karama, Ummiy na ganin ta ta ruga zata Shiga gida, wani tsawa Aliyu ya daka mata.
Dolen ta ta tsaya, da kagansu ukun kasan ba su da gaskiya.
“Nan ne gidan?” Saurayin ya tambayi yarinyar da suke tare
“Ehm Yaya ga su nan ma” ta fada tana nuna su Zahrau.
Hannu ya ba su Aliyu su ka gaisa sannan ya fara mishi bayanin abinda ya kawo su. “Daman nazo Dan Allah ya kamata ka sawa kannen nan naka ido dalili kuwa shi ne suna takura wa yara yan’uwansu in an tashi Islamiyya sai su jasu fili su musu taron dangi, kaga yarinyan nan ita da yar’uwarta da sauran kawayen su na kusa damu sun musu ba sau daya ba ba sau biyu ba shine dai aka turo ni kila in aka musu fada a gida zasu daina.”
Ba Wanda ya mishi magana har ya kai aya. Anty Zainab bin su tayi da kallo game da fadin “daga dawo wa na ba za Ku Sani magana ba daman Aliyu shine daidai da Ku” shiga ciki tayi niyya Zahrau ta rike gyalenta kaman za tayi kuka tana rokon ta da idanu kar ta tafi Dan tasan mai cecen su yau sai Allah.
“Bakomai, Nagode, Dan Allah ka bada hakuri zamu dau mataki” Aliyu ya fada ma yaron
“Bakomai, ni ke da godiya”
Dukkansu ukun ya kamo sai zare idanu su ke suna kiran Anty zainab ta cece su “A dai yi sassauci Soja”
“Ke dai Anty je ki kawai”
Frog jump ya sa suyi kowacce round Talatin, duk sun jigata gashi ba daman tsaya wa Hutu ko kuma suyi cucuwa Dan kar ya ke kallon su.
Duk round in da suka yi in za su koma sai Umar ya ce musu “Sannu fah” hakan na kara kona musu rai ganin cewa shi bai taba bada hakuri in ana zaluntar su (a cewarsu) ba kuma zai sa hannu ba haka kuma ba zai tura ba sai dai zai yi duk abinda ya San tsokana ce dan ya kara bata musu rai.
Sai da aka kira Sallahn magreeba sannan ya kyale su duk sunyi sanyi, da kyar su ka iya karasa wa cikin gida wurin mami sai hakki su ke.
Sai Bayan Sallah Isha’i ya koma gida, sassan Mami ya nufa ya same ta ita da Ammah da Anty Zainab suna hira. Gaishe su ya fara yi suka amsa
“Daman jiranka nake ka dawo ka fada min in yarana ma sun zama sojoji ne?”
“Mami me ya faru?”
“Au bama kasani ba frog jump in da kasa su fa”
“Mami yaran naki ne terrorist ne Allah, Anty Zainab bata fada miki me suke yi ba”
“Naji ta fada amma hukuncin ka ya musu tsauri, duka duka nawa suke?”
“Shknn Mami, za a rage”
Ko da ya nemi su kawo mishi spellings in da ya basu da kyar kowaccen su ta iya kawo biyar biyar a sakamakon wahalan da su ka sha a wurin shi yammacin ranar.
Ranar ko da zai koma makaranta yanda kasan an musu albishir da Aljanna haka suka dinga ji.
They are free again, rashin ji sai abinda yayi gaba karatu ko ko oho baya gabansu, anyi fadan a gida har an gaji, kullum cikin kawo karar su ake, yau sun tsokani wannan gobe sun bugi wancan sai ya zamo Allah Allah Aliyun ya dawo ake a gidan dan shi kadai ke iya musu.3 Years Later+
December, 2008
Zaune ya ke a filin da ke tsakar gidan su yana shan shayi kasantuwar lokaci ne na hunturu, Su uku ne da Umar da wani abokin shi Salim, Tare su ke karatu a NDA Kaduna.
“Oh Aliy wai ina little angels ne, tun da muka dawo ban gansu ba” Umar ya tambaya
“Mtswww” tsaki ya ja sannan yace “banda kai wa ke Neman sakarkarun yaran nan”
“That means shima sakaran ne kenan” Salim ya fada yana dariya.
Dai dai nan ko Ummiy ta turo kofa ta shigo cikin gidan sun tashi daga islamiyya, simi simi ta gaishe su “INA yan’uwanki yau kuma” Umar ya tmby
“Suna baya”
“Kun daina tafiya tare ne”
“Aa haushi su ka ban na taho na barsu” ta fada tana ya mutsa fuska ta na kuma kar kada jiki alamun fada
Dariya abin ya ba wa Salim “Kai Amma ko baki kyauta” ya fada yana mata murmushi. “Ya sunanki” ya bukata
“Ummiy” ta bashi amsa tana cigaba da karkadan jikinta game da citson baki
“Real name fa” ya CE
To fah an zo wurin… Sororo tayi tana kallon shi, Umar ne ya cemata “Asalin sunan ki yake nufi”
“Ohh Amina” ta fada tana zaro idanu irin daman tun can shige mata yayi.
Daga Salim in har Umar sai da suka dara ganin draman nata.
“Ke jeki dakina ki dauko min system yana caji kuma sauran ki min shirme, na San halinku” Aliy ne ya fada yana hararan ta.
Da sauri da sauri ta nufi dakin, sai da ta isa sannan abin da yace ta dauko ya fado mata, ita har ga Allah ba ta San abinda yace ta dauko ba amma ta fada gaban shi wannan abokan nashi masu iyayin tsiya su raina mata wayau.
Newspaper ta hango kan kujera, ta lura yana dan son karanta jarida da yamma kila shi yake nufi daman taji ana kiran shi wani suna da turanci ba mamaki wannan ne.
Da zumudin ta ta dauka ta isa wurin shi. Gashi ta fada tana mika mai, binta yayi da kallo sannan yace “miye wannan”
“Abinda kace na dauko ma”
Rike baki yayi yana kallon ta ya rasa abinda zai ce, Salim da Umar kam me zasu yi inba dariya ba
“Me nace ki dauko”
“Sy sy sy” ta kasa fada
“System?” Umar ya karasa mata
“Yauwa shi” ta fada
Galla mata harara Aliyu yayi “ajiye kije ki kama kunnen ki, zaki Sani”
Kaman daga sama sai ga Zahrau da Maijidda sun shigo suna haki.
“Yauwa kuma Ku zo nan” Aliy ya kwalla musu kira
Tuni jikin su ya dau rawa ganin Ummiy na punishment a gaban su.
“Ku fa ya sunayenku”
A tare su ka amsa “Maijidda, Zahrau”
“Nice name Hauwa’u da Fatima koh”
Daga mishi kai su kayi “amma dai ku kusan miye system ai” Umar ya fada yana musu murmushi
“Maijidda ja daki na ki dauko min system yana chaji” Aliyu ya katse su.
Da sauri ita ma ta tafi dakin tana dube dube ko za taga abinda za a iya cewa system amma bata ga alama ba.
Can wani tunani ya fado mata Baffah ya taba aiken ta dauko wani Abu mai kama da sunan ta tambayi hamza yace mata maclean ne, da sauri tashiga toilet ta dauko mai close-up.2
Wannan karan Salim da Umar tare suka kyal kyace da dariya hadda rike ciki.
Wani kallo ya bita dashi sannan yace “ajiye kiyi joining yar’uwar ki”
Kan Zharau ya koma “Sauran ke, je ki dauko min System ina a daki yana caji”
Itan ma jikin ta na kyarma ta nufi dakin, a hankali ta fara binciken ko ina na dakin amma ba ta ga abinda take nema, tunowan da tayi yace a caji ya sata murmushi, Dan tsale tayi tana fadin woo ni yau zan tsira a gun Uncle Aliy.
Jikin socket ta isa ta cire tana wani murmushin jin dadi.
Da karfin guiwa ta karasa ta mika mai. “Ya akayi kika dade” Umar ya tmby
“Ya Umar na tsaya nema ne da kyar ma nagani”
Habawa wani dariya ya saki gami da ba Salim hannu su ka tafa suna rike ciki, har kasa suke kaiwa Dan mugunta.
Bangaren Aliyu ko rechargeable lantern in dake hannun ta ya amsa ya buga mata a kai. “Dalla wuce ki yi abinda kika ga sunayi.2
Shahida ce ta fito dauke da Yusrah tana mata wasa ” Zo nan shahida” Aliyu ya kwalla Mata kira
Karasa tayi sannan ta gaishe su, amsan Yusrah Salim yayi yana Fadin “cutie ya sunan babyn taki”
“Yusy” ta amsa mai
“Oh Yusrah ke fa toh”
“Shahida”
“Seriously Salim ina ga Sunan mutane ya kama ta kayi specializing a kai ba Army ba” Aliyu ya fada yana mishi dariya
“Na sha fada mai ai, da ya ga bakon fuska to burin shi kawai ya San sunan ko yaro ko babba kuwa” Umar ke maganan yana kallon Salim
“Allah kun San da naga Mutum karantar face in shi nake inga zai yi matching da sunan shi to sai in tambaya in ji”
“Shahida je ki daki na ki dauko min System yana caji kinji”
“Tohm” ta fada
Da gudun ta taje dakin sai gata da da jakan mini laptop a hannun ta.
“Yauwa Good girl amshi Yusrah Ku shiga ciki kinji”
“Dukkanku Ku tashi Ku zo”
A hankali su ka matso gaban shi suna turo baki sun kumbura kaman za su fashe, Zahrau kan hawaye ke zuba a idanun ta shabe shabe saboda lantern in da ya buga mata a kai kanta ya fara ciwo.
“Shekarunku nawa” ya bukata
“Goma” Ummiy ta amsa
“Class fa?”
“Primary four”
“Ta ya ake muku promotion, Ku kunya ma ba kuji”
Duk dai shiru su kayi suna kallon shi sai sheshekan kukan Zahrau da ke tashi.
Amma abinda ke kular da Aliyu duk abinda zai musu ba zasu taba iya buden baki su bashi hakuri ba sai dai in ya gaji ya barsu dan kanshi.
“Zaku sani, tunda ba za kuyi karatu ba aiki zan dinga baku shine maganin Ku”
Tun daga ranar ya sa su a gaba, Saharan tsakar gida da wanke wanke kiri kiri zai hana masu aiki yana zaune yana kallo dole suyi, saukin ta ba su da kiwiyar aiki.
Tun a lokacin su ka sa wa ransu tsana ce kawai ya sa Uncle Aliy ke musu haka don ko abincin shi ne aka ba daya daga cikin su ta kai mai ya dinga mita kenan kuma ba zai ci Abincin ba
Anyi bikin Anty zainab da yaya Muhammad (Babban yaya). Kano aka kaita can ta ke karatu daman a can suka hadu da mijin nata.
Yaya Babba kuma Kaduna ya tare da matarsa Anty Rukayya Itan ma yar kadunan ce, yana aiki da NNPC
Su Zahrau yan mata an sha biki har da gayyata aka yi kawaye gasu nan dai barkatai wasu ma sun girme su babu dai na arziki duk tarkace ne.Su Uku suka shiga Kitchen domin taya Ammah abincin rana. Kaman hadin baki yau yan gidan gabadaya ke shirin haduwa, wadan da za su dawo hutu makaranta ranar da wadanda kuma za su zo Hutu.+
Kusan su suka hada abincin dan duk wani yanke yanke, jajjage, kai hata kula da abincin su su kayi da kuma Drinks in gargajiya, zobo, kunun aya da kunun gyada. Ammah kawai guiding in su take. Shekaru goma sha daya ba abin mamaki bane in aka ce duk su su kayi wadannan ayyukan.
A shekarar suka gama primary ba wai dan ya kamata su gaman ba A’a Malaman makarantar ne su kace ba zasu iya da rigimar su ba su ka sallame su “Kilan a secondary sa mai da hankali” a fadan malaman.
Lesson teacher mai tsauri sosai wannan karan Baffah ya nemo su da ma malamin islamiyya saboda ganin karatun nasu na son ya lalace gaba daya, su Kansu sai da su ka kara da sa musu ido musamman ma Mami da Ammah.
Ba laifi suna dan karatun sai dai ba yanda ya kamata ba, da an fara hankali zai gushe wurin wani abin a hakan ba karamin tsauri malaman ke musu ba.
***********************************
Deedat da ke nan Zaria Academy (SS2) driver ya fara dauko wa da safe, sai
Yaya Babba da Anty Rukayya da dansu Khalipha, Anty Zee da Ameeranta ma sun iso wuraren 11. Hamza ne dai sai around 1 ya iso dake a Maiduguri ya ke makaranta El-kenemi yana JSS2, a hakan ma ya iso da wuri. Aliyu kam sai da aka idar da Azhar ya iso abinka da makarantar sojoji.
Duk suna a babban falon gidan suna hira yaushe rabo, little angels kam suna gefe abin su suna wasan su na tafa tafa.
Sallamar Aliyu ce ta katse musu hiran nasu, cikin tafiyan shi na kasaita ya karasa kusa da Deedat ya zauna “Mazan Fama, har ka kimtse kenan” yaya Babba ya fada yana kallon shi, Amsawa yayi sannan ya gaida iyayen shi kannen shi ma suka gaishe shi.
Ameerah da ke hannun Anty zee ya mika ma hannu zai dauka, wani irin kara ta saki da ya sa shi ja baya da sauri yana fadin “Anty Zee kiwiya kika koya mata”
“Wlh Aliyu kullum haka nake fama da ita kaman chingum tunda muka iso ba Wanda ta bari ya dauke ta”
Ammah ce tace “Bakunta take ai zata ware zuwa anjima”
“Ni dai Ammah wlh yunwa nake ji sosai” Aliyu ya fada yana taba cikin shi
“Gashi kuma Abinci ya kare ba” Wannan karan Mami ce tayi magana
Ido ya zaro yana fadin “Mami bari mana”
Dariya duka falon suka dauka Baffah na fadin “Sojanmu ba wasa kenan”
“Ai in Aliyu bai samu Abinci ba har kara sai ya kai mutum” Abbah ya fada yana murmusawa.
Sosa kanshi yayi yana fadin “Ni dai Dan Allah in da Abincin kawai a miko”
“Kwantar da hankali ka mazan fama, Abinci kam sai ka tura” Ammah ta fada sannan ta sa Su Zahrau suka dauko kulolin Abincin.
“Aa Ammah bari ma in dauko da kaina ko kuma shahida ta dauko, wadannan shirmammun sai su ma mutum kazanta” Ya fada yana mikewa
Mami ce ta katse shi da fadin “oh ni Allah Aliyu ka matsa wa Ya’ya’na karshen kazanta ma su suka yi aikin Abincin”
Har yasa kai zai fita falon yayi saurin juyo wa yana fadin “bari mana Mami, zaki sa in fasa ci”
“Ehmm da gaske kake, sai dai ko ka fasa cin”
Anty zee ce ta kara dace wan “kuma ko Abincin nasu yayi dadi”
Kwafa yayi ya fita falon su ka bishi da dariya, “Ina ruwan Soja” cewan Ammah.
Bayan mintuna kalilan ya dawo falon rike da plate, Indomie ne da ya sha kayan hadi sai kamshi ke ta tashi da cup in tea.
Duk bin shi su kayi da kallo suna mamakin hali irin nashi Dan ko kadan ba su yi zaton dagaske yake ba.
“Aliyu da gaske kake daman ba za kaci Abincin ba” Ammah ta tambaya cike da mamaki
“Haba Ammah su kan su ba fa abinda su ka iya balle kuma inci abinda su ka hada” ya fada yana dagune fuska
“Da kyau mu ma ai ba musan Abinda muke ma tunda dukkanmu mu ka ci, kai ka dai ke da hankali” Mami ta fada tana hararan sa
“Aa Mami kawai dai Allah ya gani ni din ba zan iya ci bane”
“To wannan in wa ya maka, nasan dai kannin nawa ba Abinci ya iya ba” Anty zee ta fada tana tsokanan shi
“Hadiza mai aikin Mami na sa ta min”
“Gwara kaci nata kenan akan na Yan’uwanka”
Abbah da Baffah kam ba su bi ta kan lamarin ba hasali ma wani Abu suke tattaunawa, sauran yan falon dai sun cika da mamaki Amman bangaren little angels kam ko a jikinsu yanda bai son su haka suma kawai matsalan su takura musun da yake ya hana su sakat.
Tun daga ranar ya ke taka tsan tsan da Abincin gidan, sai ya tabbatar da Wanda yayi sannan zai ci, Dan a cewarsa Allah ya kyauta ya ci Abincin su Zahrau yafi karfi, in fact ai ba abinda ma su ka iya banda shashanci.
Haka ya cigaba da musu lesson shi ma ba laifi sun dan yi improving amma still ko kadan basu yi satisfying in shi ba. Punishments kala kala ba Wanda ba su sha hannun Aliyu hakan yasa su ka sa wa ransu tsana ce ya sa yake musu la’akari da ko hannun su abu ya shiga to bashi ba abun.
Hantara da kyara ke tsakanin su dai sai ko bakar azabar da su ke sha hannun shi tun suna kananan su.
Lokacin da Babban yaya ya tashi komawa Kaduna nace wa su kayi za su bishi ba don komai saboda su huta da hantarar Uncle Aliy.
Abbah ne ya hana saboda lesson in da su ke yi ganin JSS1 su ke Neman shiga.
Habawa ai rigima suka saki suna rokon a bar su ko kwana biyu su je suyi.
Ganin haka Babban yaya ya roki Alfarmar ya barshi ya tafi da su in yaso zai sama musu lesson teacher a can.
Da kyar Abbahn ya amince da sharadin ana bude school zai dawo dasu.
Baki har kunne su ka hau murna suna hada kayan su, kaya dayawa suka diba yanda kasan Zarian zasu bari gaba daya.
***********************************
5:30 pm daidai na yamma su kayi parking a gidan Babban yaya da ke Kinkinau G.R.A
Wani annashuwa su ke ji yana shigan su basu ba takurar Uncle Aliy.
Anty Rukayya mace mai matukar kirki da fara’a sai nan nan ta ke dasu rainon khalipha ma gaba daya hannun su ya koma ranar.
Washegari ta debe su suka je gidan su dake Yahaya road Unguwan rimi,
Autar su Nanah ce Sa’ar su Ummiy, ta su ko ta zo daya saboda ita ma gwanar wasa ce, haka suka yi ta tsalle tsallen su sai dai da ga alamu kwakwal war naja, Simple magana ma in za tayi sai ta hada da English.
Da ko suka tashi tafiya da Yamma zuwa tayi ta hado akwatin ta, Maman ba ta yi kokarin hana ta ba sanin cewa ta ga yara yan’uwan ta ne.
To fah gidan da da kaman ba mutane a ciki ya zama karamin cinema, Saukin abin ma matar gidan Mutum ce mai son jama’a gashi sun dauke mata kusan duka ayyukan gidan, rashin kiwiyan su ba karamin burgeta yake sai gashi kanwar ta da ta Sani da shegen son jiki da ita suke komai.
Tuni Babban yaya ya samo musu lesson teacher da zai koya musu both Islamiyya da boko, da faarko ba sa mai da hankali amma ganin yanda Nanah ke da hazaka yasa Zahrau da maijidda su kaji suna sha’awar ilimin.
Daman Ummiy ce ogan su don daman in an fara ita ke fara tsokano su sai su biye mata, yanzu ko in tayi tayi share ta suke ganin ba sarki sai Allah dole ya sa ta bada kai bori ya hau.Kaman da wasa dai gashi su kansu jin dadin ilimin su ke ganin su ma sun fara komawa kaman Nanah sun fara sanin abubuwa, yanzu ba za suji kunya ba in an musu turanci za su iya gane though maidawan tukun dai.+
Sosai da sosai su ka sa karatun A gaba sai gashi Ummiyn da ke tunzura su duk ta fisu saurin dauka, tabbas ba ayi karya da aka ce mutum ma ra ji akwai kokari. Yanzu kam Uncle Aliy sai dai ya ma wasu gori ba dai su bah haka suke fadan ma Anty Rukayya ita dai dariya kawai ta ke ta ce musu “shi ma daman ai hakan ya ke so su zama” fir su ka musu don su a ganin su so yake kawai ya ga ya musu tambaya sun kasa ya musu mugunta.
Sun shaku sosai da Nanah da Anty Rukayya har ma khalipha ba karamin saba wa yayi dasu ba, su kan basu ki su dawo Kaduna gaba daya da zama ba don ba karamin dadin hutun su kayi ba.
Some times su kan fita suga gari a biya wurare kala kala ayi shopping sannan cikin unguwa ma suna zuwa masallacin sheikh Ahmad Al-karqawi kallon musabaka da kuma wa’azi hakan ya kara Jan ra’ayin su ga ilimin Addini sosai musamman ganin yanda kananan yara kaman su ke karatun Qur’ani da murya mai sauti ga kuma tajweed abin dai zan ban sha’awa.
Ko da Hutu ya kare Ya Babba ya zo mai dasu da kuka suka rabu da Nanah, Anty Rukayya kanta sai da tayi kewan su balle kuma khalipha da suka shagwaba kaman me, Alkawarin zuwa Kaduna ko wani Hutu suka dauka kaman dai za a barsu.
**********************************
Kwanan su biyu da komawa Zaria Zahrau ta tashi da matsanancin zazzabi sai rawan dari take.
Bayan ta samu ta ci abinci ta sha magani. Su na zaune a falon mami suna kallo gaba dayansu har da hamza da shahida. Amai ta ji tana ji gadan gadan da sauri ta yi yunkurin tashi sai dai me? A bakin kofan falon jiri ya debe ta ta zube a wurin, da sauri su ka nufi kanta, ta yi kokarin tsaida Aman amma hakan bai yiwu ba a wurin ta yi shi gaba daya.
Ummiy ce ta tallafa mata su ka tafi toilet, Hamza maijidda kuma su ka yi yunkurin gyara wurin.
Dai dai lokacin Aliyu ya nufi falon Mami cikin tafiyan shi ta kasaita, a kofan ya cire takalmin shi ya nufi ciki, bai yi aune ba ya jishi cikin Abu mai lami lami, Duba yayi ya ga amai duk ya bata mishi kafa.1
Shahida da ke tsaya a wurin ba karamin tsorata da yanayin shi ta yi ba “wa yayi?” Kawai ya ce mata “Zahrau ce bata da…” Bai tsaya jin abinda zata karasa fada ba ya sa kai cikin falon.
Ita da Ummiy ya gani sun fito cikin toilet, bai tsaya wani tunani ba rai bace ya kwasheta da wani wawan mari ai ko a idon Mami da ta shigo corridor din.
Tsabagen rude wa Zahrau zube tayi a kasa ta ka sa motsi hannun ta na tallabe da wurin kukan ma ta kasa sai ma Ummiy ce idon ta ya ciko da hawaye.
Wani irin Kallo mami ta bishi da shi ta na fadin “sannu kaji yarinyar da bata da lafiya ne za ka ma wannan Marin, sa’arka ce? Ko kuma kashe ta kake so kayi?” Dago Zahrau n tayi fuskar ta har shatin hannuwan shi ya fito, idon nan ya kumbura yayi suntum, abinka da farar mace… Daman ya lafiyar kura.
Shi kam tsaya wa yayi ya kasa gaba balle baya har ga Allah zuciya ce ta debe shi ba wai da gan gan ba, maganar mami ce ta katse shi daga dana sanin da ya ke “ni wuce ka bar min bakin kofan daki, in ba so kake ka karasa min ya’ya’ ba.
Maijidda da Ummiy da suka yi zuru suna shirin kuka ya wulla wa harara sannan ya shigo toilet ya wanko kafan shi. Ko kallon su bai kara yi ba ya fita ya bar side in gaba daya. Halin ko in kula da ya nuna ba karamin haushi ya ba wasu Ummiy ba dan gani suke duk cikin kiyayyan ne.
Marin da yayi mata ya taimaka wurin zafafa zazzabin Wanda har ya kai ta da kwanciya asibiti, akwai Mami ta sa shi a gaba dashi aka yi jinyan gaba daya, duk wani aike daga gida zuwa asibitin a kanshi ya kare gashi ba kusa bane. Saukin shi ma ta boye wa su Abbah abinda ya faru ko da suka tambaya me ya sami fuskanta kawai cewa tayi ta bige ne.1
Satin ta daya sannan aka sallamota, ta warke garas sai da har yanzu akwai tabon hannun shi a fuskanta Dan ma wani cream aka bata tana shafawa.
***********************************
Lesson Gadan gadan Baffah ya sa Aliyu ya dinga musu, musamman suka zauna su kayi meeting akan ko sun iya kar su bashi amsa saboda kiyayyar daya ke musu.
Ai ko sun hada kai Dan taurin kai sosai suka nuna mishi, yayi dukan, punishment in amma duk a banza shi kanshi ba karamin wahala yayi ba akan hakan.
Sosai Ranar ya tsaya yana musu explaining, yanda su ka dage suna kallonshi ya sa yayi tunanin suna ganewa amma me? Duk cikin su ba wacce ta amsa mishi question daya.1
Ba karamin harzuka yayi, ba kallan punishment in da bai basu ba a ranar suna yi suna kuka amma ko kallo basu ishe shi ba, wani abinda ya ke matukar bata mishi rai duk wuyan da zasu sha basu taba bashi hakuri.
Mami ce taji shiru ta fita domin ta duba su, samun su tayi duk sun jigata suna ta haki ba hawaye sai ambaliya yake, kasa cewa komai tayi ta tsaya tana kallon shi, kara hade fuska tayi yana hararan su. “Ehm dole ka daure fuska, wannan wani irin zalunci ne? An fada su ma makarantar sojojin suke ne, yaran ma duka duka nawa suke?” Shiru yayi dan ya San bai da abin cewa.1
Tattara su tayi suka tafi tana fadin “daga yau ma na kashe lesson in inga karshen zalunci”
Washegari da sassafe yayi Sallama falon Baffah, da fara’a ya tarbe shi yana fadin “maraba da Sojanmu mazan fama”
Sai da ya gaida Baffahn sannan ya fara sanar dashi abinda ya kawo shi. “Baffah daman batun yaran nan ne, Allah ya gani nayi iya kokari na amma ba su dauka kuma in na basu punishment mami tayi ta fada”
Girgiza kai Abbahn yayi yana jimamin irin hali nasu Zahrau, sannan ya ce “Shikenan Aliyu hakan ma mun gode zan San yanda zan bullo wa lamarin”
“Baffah ni kam ga shawara, me zai hana a kai su boarding school amma daban daban” ya fada yana Sosa kai
“Shawaranka abun dubawa ne Aliy, zanyi magana da Abbah “
Abbahn ma daya ji shawaran yayi Na’am dashi sai dai Ammah da Mami ne suka so su hana, convincing in su suka yi da alkawarin cire su in suka yi first term basu canja ba.
A bangaren little angels kuwa abin ba karamin kidima su yayi ba sai dai ko shakka babu sun San aikin Uncle Aliy ne domin ko gar da gar ya fada musu.
Allah ya is a ko kwando kwando ya sha.