MAFARI CHAPTER 9 BY UMMU AZAMM
Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan an sallami mama daga asibiti sun dawo gida , idan banda lelen ta babu abunda falmata take rabon ta da makarantar ta ma yau kusan sati guda kenan ,+
Domin duk yadda hajja ta so falmata ta tafi makarantar ta bar mata kulawar mama ta ƙiya ,
gani take daga ta matsa daga kusa da ita ciwon nata zai iya tashi .

A zaune suke a falo hajja tana kishingiɗe tana hutawa bayan ta gama ƴan kananun aiyukan ta na safe ,
Mama tana kalmashe bisa cinyar falmata , wacce take bin duk gaɓoɓin maman tana tausa mata su sannu a hankali , jikin ta sanye da ruwan hodan kayan sanyi na yara mata me adon ƴan ƙula-ƙulai farare , ƙafafun ta a ƙunshe cikin fararen safar ƙafa .
Biyamuradi ya shigo falon , a shirye yake tsaf cikin kakin sa na soji , fitowar sa kenan daga sashin sa da yake sabon gidan da ya saya musu wanda ya fi wanda suka fara zaman haya a cikin sa girma da tsari , domin wannan sashi uku ne da shi ƴan madaidaita , sashin da su falmata suke da sashin baƙi wanda ba’a amfani da shi sai kuma sashin biyamuradi da idan ya zo garin yake sauƙa a cikin sa a wasu lokuta , musamman a lokacin da ya tarar da rashin lafiyar mama , wasu lokutan kuwa a hotel yake zaman sa .
Mama tana jin sallamar sa ta miƙe daga jikin falmata wacce take ƙoƙarin riƙe ta ,
Mama ki tafi a hankali kin ga ba wani ƙwarin jiki kika samu sosai ba ,
Bata kula ba
Ta taka da ɗan gudun ta , da sassarfa shima ya ƙaraso ya chafe ta sama ya cillata ,
Yana juyi da ita kafin ya sauke ta zuwa ƙirjin sa yana dariya ,
Bonjour papa , ina kwana papa .
tace daidai lokacin da take kai hannu tana ƙoƙarin cire hular kan sa ,
Taya ta cire hular yayi ya ɗora mata bisa kan ta da aka mata manyan kitson kalba suka zubo har kan kafaɗun ta ,
Bonjour mon cher ,” yaya kin ka tashi ?
Lafiya papa
tace da shi daidai lokacin da take ƙoƙarin sauƙa daga ƙirjin sa ,
Ya sauƙe ta yana riƙe da hannun ta suka ƙarasa cikin falon , ya samu mazauni kan ɗaya daga cikin kujerun wajen yana gaisawa da hajja wacce ta miƙe zaune daga kishingiɗar da tayi ,
Kamar yadda ta saba , yanayin ta babu walwala idan har yana waje ta gaida shi , tana riƙo hannun mama wacce take ƙoƙarin ajiye mata hular baban ta a kai ,
Bata iya hana ta ba sai da ta ɗaura mata hular akan hular da take rufe akan ta wacce take mahaɗin doguwar rigar jikin ta ruwan madara me ɗan nawi saboda tashi da aka yi da ɗan sanyi garin sakamakon ruwan sama da aka kwana yi daren jiya .
Shafa fuskar ta mama tayi , kamar yadda yake al’adar su ita da mamar ta .
Maama kin yi chau dayawa ,
Papa ka ga maama na tayi chau , donne-nous des photos ,
ta ƙarasa zancen tana hayewa kan kujerar da falmata take ta zagaya ta bayan ta gami da sarƙafa hannuwan ta biyu ta wuyan falmatan ta cusa fuskar ta gefen wuyan ta .,
Biyamuradi wanda ya fara yiwa hajja bayani game da shirye-shiryen da yake na tafiyar su US , ya juyo da duban sa kan su idanun sa suka sauƙa kan fuskar falmata wacce haƙoranta ke buɗe tana murmushin da yake bayyana farin cikin ta da ganin walwalar mama ya assasa mata ,
Kamar maganaɗisu ya riƙe shi , ya kasa janye idanun sa daga kan ƴar fuskar ta da komen ta yake ɗan madaidaici idan aka cire manyan idanun ta ,
Ba tare da ya iya ɗauke ido daga kallon ta ba ya zaro wayar sa daga aljihu , ya juyo baki ɗayan sa ya saita cemara ya haska musu hotuna wajen kala shidda ,
STORY CONTINUES BELOW
Da gudu mama ta sake sauƙowa ta dawo wajen baban ta , tana cewa zata ga hoto ?
Ta ɗare cinyar sa ,
Batare da ya sake mata wayar ba ya nuna mata hotunan , da sauri ta sanya hannu tana sake tura huton gaba , fuskar wata ƴar baby me kyau kamar ta ya cika fuskar wayar , ƴar yarinya ce da bata wuce shekaru biyu ba tana tsaye a hoton ,
A hankali mama ta ɗago kan ta tana duban fuskar sa
Papa bebe waye ?
Zare wayar yayi daga hannun ta ba tare da ya bata amsa ba, daidai lokacin da hajja ta ke cewa ,
Wannan yarinyar da surutu kike kamar aku , duk kin bi kin tsare shi da surutu kin hana shi ya yi magana , bayan kuma yayi shirin tafiya aiki , ni zo nan ki zauna na miki tafiyar tsutsa a ƙafar ki .
Sauƙa tayi daga jikin sa , maimakon ta tafi wajen hajja , sai ta nufi mamar ta , tana zuwa ta zauna a gefen ta gami da kwantar da kai a jikin ta tayi shiru ,
Boyayyar ajiyar zuciya Biyamuradi yayi , cikin ran sa yana hamdala da hajja ta katse masa tambayoyin mama , domin Alƙawari ya ɗaukarwa kan sa ba zai taɓa yiwa ƴaƴan sa ƙarya ba , akan duk wata tambaya da suka masa , sai dai ko ya sakaya amsar idan kaifin hankalin su bai kai su fahimce ta ba , amma a yanzu bai shirya amsa ba ga tambayar da mama tayi ma sa .
Cigaba da yiwa hajja bayani yayi , inda yake sanar da ita , yana son ranar litinin ya zo su je ayiwa falmata da mama passport , zai fara nema musu visa
Idan Allah ya yadda daga sun samu visa shi da su zasu tafi US , da ba zai wuce tsawon nan da wata ɗaya da ƴan kwanaki ba nan gaba ,
Ba shi da masaniya akan tsawon lokacin da zasu iya yi a chan ,saboda harka ce ta neman lafiya , bai san yadda lamura zasu kasance ba , amma dai visa ta tsawon watanni shidda zai samar musu .3
Ya ɗora da neman hajja ta masa bayanin duk wasu abubuwan da zata iya buƙata bayan kayan abinci da sauran abubuwan buƙata na rayuwar yau da kullum wanda zai iya kai ta watanni shidda ko fiye da haka ,2
Da farko addu’o’in samun nasara akan abunda zasu nema tare da addu’ar nemawa mama samun waraka tayi ta jerowa , tana jin yadda tausayin su duk ukun ke kama ta ,
Babban soja , ni ba sai an min tanadin kome ba , saboda ka ga nima wajen shekaru biyu ake nema rabona da ƴan uwa da dangi , dan haka idan har tafiyar ta tashi , bayan kun tafi a washegari nima zan ɗau hanya zuwa nigeria nima naje na sada zuminci na ga ƴan uwa da dangi , shekaru sun fara jaa , mutuwar nan ta yanzu kar ta gifta tsakani ba’a nemi gafarar ƴan uwa ba , idan ya so bayan dawowar ku ko kuwa ma kafin ku dawo sai a sanar min nayi dawowa ta , ai ka ga nima na ribaci lokaci ko kuwa ?
Babu shakka hakane hajja , to babu kome idan har tafiya ta kama lokaci yayi sai ki tafi zouwa gida kafin dawowar mu , Allah ya saka da Alheri , ki min duk wasu bayanai na abubuwan da kike buƙata da zaki yiwa mutanen gida tsaraba don Allah .!
Toh madallah Babban soja , amma dayake nima a wajen nawa akwai ƴan kuɗaɗe irin waɗanda kake min kyautar su ai ba ma sai na maka lissafin kayan tsaraba ba , idan tafiya ta zo ni da kaina zani nayo ƴar tsaraba ta ,
A ah hajja , don Allah kar ki ce hakka , irin Alherin da kika mouna a rayuwa ba zamou iya biyan ki ba sai dai Allah shi saka da Alheri , ƙwarai ƙwarai ina miki godiya , ki min lissafi abun da kike buƙata duk zan sa a kawo kome ranar da zaki tafi sai direban da ya kai ki wancen karon ya sake kai ki nagode !
Ni ce da godiya Babban soja ni ce da godiya , Allah dai ya ƙara buɗi , ya ba wa mama lafiya ,
Ameen ameen hajja ya amsa yana miƙewa ,
Sashin da suke ya mayar da duban sa , mama har tayi bacci fuskar nan a chakuɗe alamun fushi take ,
Bai yi mamaki ba saboda sanin ta da yayi da saurin bacci ,
STORY CONTINUES BELOW
A hankali ya taka zuwa gaban falmata wacce tayi shiru , tana ɗan shafar kan mama da yake bisa cinyar ta ,
Fatima ni zan tafi bakin aiki zouwa le lundi zan dawo mu tai à muku passeport , ki kula da mama kar tayi wassa dayawa idan ta ji sauƙi sosai sai ta cigaba da zouwa école .
Toh Allah ya kiyaye hanya ,!
Ta amsa masa ,
Ɗan jim yayi a tsaye yana ƙure mata kallo da buɗaɗɗun idanun sa , hular ta shi ta karɓi yar zagayayyar fuskar ta me ɗan haske kaɗan , ji yake kamar ya bar mata hular a kan ta yayi ta kallon ta a haka ,
Jin yayi shiru kuma ta san da tsayuwar sa a wajen ya sa ta ɗan dago kan ta , tana sake haɗe fuska ,
Gyaran murya yayi ganin yadda tayi kicin-kicin kamar zata fashe masa da kuka .
Fatima donne moi mon chapeau! ( miƙe min hula ta )
Ya furta hakan yana sake rage amon muryar sa ,
Falmata wacce tsayuwar sa akan ta da idanun sa da take ji suna mata yawo a jiki tamkar suna mintsinin ta ya sa ta diririce ta gaza fahimtar me yake cewa , ba wai dan bata jin yaren da yake yi ba ,
Mama bacci take .
ta ce da shi tana fatan ya bar kan ta
A hankali ya sunkuyo har tana iya jiyo hucin humfashin sa a fuskar ta ya kai hannun sa guda ya zare hular sa dake kan ta , ya mayar kan sa .
Na tafi
Yace da ita yana juyawa ya bar wajen .
Wani irin yanayi ta ji a jikin ta uwa wacce aka zubawa ruwan sanyi , har ga Allah ta mance da hular sa da take kafe a kan ta ,
Runtse idanun ta tayi da ƙarfi tana jin yadda zuciyar ta ke bugu .2
Hajja wacce duk abunda ya faru akan idanun ta tana iya hango su daga inda take .
auho ! aikin banza ihu bayan hari , da kike wani runtse ido kina wani kawar da kai ya ƙadangariyar gobara , ai wallahi ni dai na daina saki a hanya kan sha’anin auren ki , tsakani na da ke ido ,!1
Ace wai tsawon shekaru fiye da biyar kin kasa zama cikakkiyar matar gida , ke kenan ɗaurewa miji fuska kina muzurai , zauna nan yarinya za’a yi bake lokacin da Babban soja ya gaji da halin ki ya sillo auren sa babu ni a masu yi miki dannar ƙirji , ko muƙamuƙi ba zan danna miki ba .6
Cikin rashin kulawa da zantukan hajja wanda falmata ta riga ta saba da jin makamantan su , tace
Hajja ta me kika ce ?
Abunda wancan yace , shi nace1
Ta amsa mata tana shirin miƙewa daga inda take tana cigaba da mita ,
Ƙatuwar mace kamar ki ace wai har yau tana da miji amma bata san amfanin sa ba sai rainon ƴa ,?
Ai ni ina kamar ki nayi aure na na biyu ma ,
Ki ka ce me hajja ta ban ji da kyau ba ??4
Na ce gidan ku !1
Ta amsa mata tana ƙarasa barin wajen
Murmushi falmata tayi domin ta san ta ƙular da hajja ,
Cikin ran ta tana juya maganganun hajja ,
Ban da abun hajja shi mutumin da kullum.take kumfar baki akan a kula da shi ɗin , shi ya taɓa nuna wata alama ne na kasancewar ta matar sa ? Tsawon shekarun auren su a tun bata san me takamaimai kalmar auratayya ke nufi ba ,
har ta zo ta san me ake nufi da aure ta hanyar malamar da take koyar da ita wacce a farkon fara ɗaukar darasi a wajen ta take yawan yi mata bayani akan auratayya a addinance da yadda mace zata kula da kan ta da mijin ta ta fuskar auratayya ba tare da kunyar kome ba cikin rashin sanin ta hajja ce ta yiwa malamar bayanin ƙarancin ilmi da wayon falmata ta kuma roƙi da ta dunga mata darasi na musamman akan auratayya ,
STORY CONTINUES BELOW
A hankali yau da gobe ta fahimci manene aure , matsayin miji a gun matar sa da matsayin mata a wajen mijin ta ,
Ta shiga ruɗani na sosai da har kawo yau bata fita daga cikin sa ba , ” yaushe yakaka da Baban mama suka yi aure ?? Ita ba ta san lokacin ba kawai jin yakaka tayi da cikin mama .3
Akwai tsoro me tafe da son bada kariya tare da kyautata zato ga ƴar uwar ta yakaka , haɗi da son tsaftace mama shi yasa a duk lokacin da tunanin hanyar da aka bi aka samar da mama ya taso mata , take yaƙar tunanin da ƙarfi da yaji , bata son wani abu da zai aibata yakaka ya raɓi tunanin ta ,
Kewa tare da ƙaunar ƴar uwar ta bai ragu ba ko kaɗan a cikin ran ta sai ma zurfafa da yake sake yi yayi mata ƙaton miƙi a cikin rai .
Rashin son suyi zaman auratayya irin na sauran ma’aurata da Biyamuradi ya nuna tsawon shekarun bai taɓa damun ta ba ,
Hasalima ta fi son hakan .
Zaman mama take , tana rayuwa ne a ƙarƙashin sa kaɗai domin mama , za kuma ta cigaba da tsayawa ɗauke da auren sa a kan ta har abada muddin tana tare da mama .
****
Daga niamey kai tsaye maraɗi ya wuce , bayan isar shi faɗa ya kai gaisuwa , kai tsaye ɓangaren sa ya nufa ba tare da ya shiga cikin gidan su wajen hajiya umma ba , yasan yanzu tana tare da jama’a masu neman taimako da ƴan barandar ta , sai zuwa yammaci zai shiga wajen ta zuwa lokacin ƙafa ta ragu a sashin nata ..
Tattaki yayi zuwa sashin sa da yake bigire guda na gidan , bayun da suke kai kawo a fada su na ta kai gaisuwa bayan waɗanda ke take masa baya tun daga ƙofar fada .
A bakin sashin sa suka jaa tunga saboda a tsarin sa bayi maza basa shiga ɓangaren gidan sa da matan sa ke ciki .
Yana sanya ƙafar sa a cikin gidan ya ji wani yanayi marar daɗi na lullubar sa , hakan kuwa yana da nasaba da rashin daɗin zama a gidan da yake ji har kullum ya kuma rasa dalili .
Taku ya fara yi da nufin isa sashin gimbiyar ta shi maimouna .
Sai dai ƴan hannuwan da ya ji sun riƙe masa ƙafafun sa su suka sanya shi ya maida ganin sa ƙasa ,!
Yumna
Ya furta yana ƴar dariya tare da kai hannu ya ɗauki ƴar yarinyar da take ta yi masa dariya , ya ɗaga ta sama ya cilla ta tana ɓangala masa dariya .
Rungume ta yayi a jikin sa lokacin da yake maida duban sa kan mamar ta wacce take ƙarasowa wajen fuskar ta ɗauke da murmushi , a shirye take tsaf , ba wata shahararriyar kwalliyar fuska tayi ba illa jikin ta da yake kiruf a rufe da babban mayafi tun daga wuyan ta da ya sha ado da tufafi irin na alfarma ,wanda ya amshi zubi da tsarin jikin ta na samɓaleliyar mace me zubin matan fulanin usul .
Janye idanun ta tayi daga cikin nasa kamar koyaushe da bata iya jurar ganin cikin idanun sa duk kuwa da tsawon shekarun da suka shafe a matsayin ma’aurata ,
Barka da zouwa Baban Yumna , da fatan ka isso lafiya ?
Lafiya mun same ku lafiya ? Yaya Yumna ?
Ga ta tana lafiya ,
Ɗan shiru suka yi kafin ya katse shirun da tambayar ta
Ina kuke da noufin zouwa da hantsi hakka ??
A ɗan ruɗe tace , zamu shiga fada gaishe da hajiya umma ,
STORY CONTINUES BELOW
Baza ku fita yanzou ba umma na tare da jama’a da wannan lokacin bani son idanun jama’a bisa ga kan ɗiya ta , ko dai ki bar ta ki tahi ke ɗai , ko kuwa ki bari da sanyin la’asar kun tahi tare .
Ko kusa baza ta so ƴar ta ta gifta ta kurkusa da shigifar gimbiya moumuna ba bare har ta taka ƙafafun ta cikin wani al’amari da ya gifta a tsakanin su me girma , wanda ya tarwatsa takaitatcen zaman daɗin da suka fara gudanarwa a tsakanin su , daga nan aka yi walƙiya kowa ya shaida kowa , yayin da daga lokacin ta fara bin irin takun gimbiya moumuna da nazari , nan ta fahimci dayawa daga cikin boƴaƴƴun fuskokin ta masu cike da abubuwan al’ajabi tare da sarƙaƙiya da baki yayi kaɗan wajen furta su ga wani har sai idan wannnan mutumin ya ga kome a idanun sa .
Hakan ya sa ta rufe kome ta haɗiye a cikin ta , ta kuma killace kan ta da ɗiyar ta daga gimbiya moumuna da ƴan barandar ta doumin ita ɗin ai gubba ce ga rayukan alhalin masarautar maraɗi !
Da sauri ta miƙa hannu tana ƙoƙarin amsar ƴar ta daga gare shi
Mun hakure zouwa yammaci kamar yadda ka faɗi mouna Biyamuradi .
Janye yumna yayi ya hana ta ɗaukar ta , a hankali ya kamo hannun tare da sarƙafe ƴan yatsun sa a cikin nata hannun yana jin yadda taushin hannun ke tado masa da yanayin da yake ta dannewa tsawon satika , ” muryar sa tafe da amo marar ƙarfi yace
Mu tai ki ciyar da ni abounci na taho tare da yunwa me tsanani .
Ƙoƙarin zare hannun ta take tana satar kallon sashin gimbiya maimouna ,
Cikin sa’a idanun ta ya sauƙa akan gnala shugabar bayin sashin gimbiya moumuna ta na abunda yake goge gilashin falon gimbiyar ta ciki a zahiri , wanda tashin farko siyama ta fassara abunda take da ɗaukar rahoto
Toh Biyamuradi , amm…
Shitt
yace mata lokacin da yake jan hannun ta zouwa sashin sa kai tsaye da yumna saɓe kan kafaɗar sa ta dama tana ƙoƙarin ɗauke hular kan sa ,
Suka fara taku tare da masaniyar yau wajen ta ya kamata ya kwana a tsarin ƙwanakin girki .
Gimbiya moumuna wacce tun isar sa fada ta samou labarin zuwan sa , inda bata yi ƙasa a guiwa ba ta tashi shirin tarɓar sa ,
Ta tashi hankulan bayun ta da aikin gyara gida wasu kuma na haɗa mata ruwan wanka tare da fidda mata kayan da zata sanya a jikin ta ,
Zuwa shigowar sa gidan ta fito daga wanka ta fara shiri , yana dosar gidan saƙo ya iso mata , hakan ya sa ta miƙe daga gaban mudubi ta ƙarasa gaban babban window na ɗakin ta dake sama ta raba labulen biyu daga inda take ta hangi kome da ya wakana tsakanin sa da siyama .
Wani irin tuƙuƙi take ji yana taso mata daga cikin rai har tana jin ɗacin sa a maƙogoro .
Meyasa ne wankin hula ya kai ta ɗare har tsakiyar sa ?? Lamarin da suka yi hasashen yiwuwar sa a watanni zuwa
Shekara bayan zuwan ta masarautar maraɗi , sai ga shi shekaru har sun fara ƙoƙarin haurawa kirgen yatsu biyar ?? Wacce iriyar mummunar rashin sa’a ne gare su haka ?? Wanne sirri ne da yake boye cikin duhu da ya zamto shamaƙin da ya shiga tsakanin ta da cikar burin ta ?? Menene shi da ya wuce tasirin ƙarfin su ??
Tattare labulen tayi ta cukuikuye shi a tafin hannun ta tana jin kamar tayi girgiza ta fasa bango ta dira a sashin yarima youssouf ta kaddamar da manufar ta ..
Ranki ya daɗe kƴakya…..
Bata bari gnala ta ƙarasa kalmomin ta ba wacce ta shigo ta durƙusa daga bayan ta ,
STORY CONTINUES BELOW
Da hannu ta dakatar da ita ,
Ayi gaugawar shiryawa Biyamuradi abincin sa a aika da shi shiyar sa .,
Ke zaki miƙa abincin da kan ki daga nan kin kawo mi ni labari na lamarin da ya auku gaba gare ki .
Allah ya huci ran gimbiya ƴar sarkin nahiyar mu maigirma oumarnin ki shine abun bi .!
da shigar su sashin nasa da yake me matuƙar girma , da tsari tare da wadatar tsaftar da ta haifar da kyakkyawan yanayi a wajen ,
Ya zauna bisa ɗaya daga cikin kujerun falon nasa , yana sauƙe yumna kan kafafun sa ,
siyama wacce ta saɓule mayafin ta ta ajiye a gefe ta sunkuya tare da yin gurfano a gaban sa , cikin nutsuwa ta kai hannuwan ta tana kunce masa igiyar takalmin sa tare da zare masa shi a hankali ,
Ɗan kiɗan da wayar sa ta yi dake nuna alamun shigowar saƙo ya sa shi zaro wayar daga aljihun sa ,
Lokacin da take ƙoƙarin karɓe hular sa dake hannun yumna ta ƙi bada hular ,
Ki bar mata hular mana , kin ka sani ko ɗiya tayi gadon baban ta ?
Da murmushi bisa fuskar ta ta wuce sama domin ajiye masa takalman sa , ta zo ta fara yi masa shirin girki .
Saƙon gimbiya maimouna ne mai ɗauke da tsararrun kalamai na barka da zuwa ƙarshe take sanar da shi ta bada saƙo a kawo masa ,
Fita yayi daga wajen adana saƙon yana shirin ajiye wayar hoton da ya ɗauke su ɗazu ya bayyana a fuskar wayar,
Ƴan yatsun sa ya sa ya jawo hoton ya cika wayar ya na nutsar da idanun sa kan fuskar ta me ɗan haske kaɗan da take ɗauke da wani sirri me tasirin da ya zarce a ƙira shi kyau ,
fatar ta suɓul-suɓul babu wasu ƙurarraji bare tabbuna manyan idanun ta da yankan su yake a tsaye da ƙwayar baƙi na cikin su me girma ne sosai , suna da ɗaukar hankali ta yadda ko yaya ta juya su sai mutum ya gan su , har kullum yana dogon tunani akan son sanin me ya makanta su ??
A hankali yayi ƙasa da hoton zuwa kan bakin ta da haƙoranta suke a buɗe tana dariya ,
Tsintar kan sa yayi da murmusawa, ya kai babban ɗan yatsan sa yana shafar fuskar wayar daidai zagayen ɗan bakin nata ,
lokacin da ya tuno da yadda take haɗe fuska ta tsuke bakin , duk idan ta ji motsin sa a waje , ta takura kan ta ta gaza walwala ,,
Kiyi haƙuri fatima ni ma ba zaɓi na bane irin rayuwar da muke gudanarwa a tsakanin mu a matsayin ki ta iyalina ,girman laifi na ya sa na gaza yin wani yunƙuri , ni ɗin me laifi ne a gare ki da duk ranar da gaskiya ta bayyana wataƙila baza ki yafe min ba , hakan ya sa na jinkirta miki har zouwa lokacin da kome zai bayyana agare ki , da na tabbatar ranar ta na zouwa , lokacin kike da zaɓi na zama da ni ko bari na bisa ra’ayin kan ki ,
Kiyi haƙuri Fatima zahra ina jin kunyar ki .
Ƙwanƙwasa ƙofar da aka yi ya sa shi kai duban sa ga ƙofar tare da mayar da wayar sa cikin aljihu
Daidai da ƙarasowar siyama wajen wacce kalaman sa na ƙarshe suka sauƙa cikin kunnuwan ta ,
Suka yi sanadiyyar harɗewar takun kafafun ta tare da sa zuciyar ta yin tsalle .
Wacece fatima ? Wanne matsayi ne gare ta da har Biyamuradi ke neman afouwar ta ? Shin laifin me ya aikata mata ?
Ruɗanin da ta afkawa ya hana ta tsinkayar kalaman da yake mata sai da ya ɗan ɗaga muryar sa da ƙarfi .
Siyama ki buɗe kofar nan saƙon maimounatu ne ya iso ,
Ba tare da ta amsa ba ta taka tana nufar ƙofar , cikin ran ta damuwa goma da ishirin ta san sarai saƙon ko na menene, abunda maimounatu ta saba yi mata ne a koyaushe , shine yau ma ta maimaita .
STORY CONTINUES BELOW
Tana buɗe ƙofar tayi arba da gnala tare da wasu bayu biyu hannuwan su riƙe da manyan farantai da aka rufe su da tumaƙasa irin na alfarma ,
Ajiye faranta suka yi tare da yin gurfano a gaban ta ,
Ranki ya daɗe barka da fitowa ! saƙo ne daga gimbiya tace a shigar da kaɓaki ga maigirma yarima .
Fuskar ta a ɗaure ta ce
Ki je sashi na yanzu yanzu ki ƙira min Rakiya ku zo tare !
Da sauri Gnala ta miƙe
Ba ke ba .
Tace da kaushin murya
Ciki sauri ta koma ta tsugunna
Ke tashi ki je ki taho da Rakiya
Tana nuni da ɗayar baiwar .
Cikin ƙasa da mintuna uku sai ga su tare da wata yarinyar mace da zata iya zuwa sa’a ga siyamar ,
Ranki ya daɗe uwargijiya ta .
Rakiya ki ɗauko waɗannan farantan ki biyo ni da su ,
Ta furta haka tana juyawa ciki Rakiya ta bita ɗauke da faranti guda , kafin ta dawo ta ɗau sauran da ɗai ɗaya ta shiga da su ,
Tana gama shigarwa ta fito gami da jan ƙofar , tana iya jiyo lokacin da uwargiyar ta ta murza ɗan mukulli ,
Kallon kallo suka yi tsakanin ta da gnala , kafin ta ratsa ta tsakanin su tana wucewa kan ta a ɗage bakin ta ɗauke da ɗan siririn murmushi ta fara rere waƙar da ta zo kan harshen ta a dai-dai lokacin
Aiki yayi kyau , tunda gida ya gyaru tsaf-tsaf ?
Allah kawo ran albashi mui fatantamawaaa .
Na ku nawa ne ? nawa kuka ɗauka a wata ɗaƴa ?
In an bincika in an bibbiku da ɗai ɗai , har ma’aikatan zaria har ku na fi kowa , ɗan ɗan ɗaraɗanɗan ………
Da kallo suka bi ta tsaurin idanun Rakiya ba sabon abu bane a wajen su duk kuwa da cewa su sun fita daɗewa a gidan domin ita sabuwar ƴar aiki ce da ubbo ta kawo wa siyama tun daga jahar kanon nigeria .
Bata da kunya , bata kuma da tsoro ko kaɗan fallalliya ce ta ƙin ƙarawa .1
****
Fuskar ta babu walwala ta zuzzuba masa duk abincin da yake wajen akan wani ɗan faranti me ɗaukar ido , ta tanadar masa duk wasu abubuwan da ta san zai buƙata a wajen cin abincin ta mike tana barin wajen bata bi ta kan yumna ba wacce ta ɗau murfin wani ɗan kwano tana miƙa mata tare da yi mata gwarancin ta na yara , ta wuce ta tana nufar sama ,….
Ta ƙasan ido ya bita da kallo , ganin fushin ta a duk lokacin da maimounatu tayi masa aike ya haka ba sabon abu bane a wajen sa , siyama tana da zafin kishi shi da kan sa ya san haka , saɓanin maimounatu wacce tarin hikimar ta tare da wayo ya sa bata saurin bayyana kishin ta a fili har a fahimta ,
Shi da kan sa yana mamakin yadda ake maimouna take sanin zuwan sa maraɗi tun kafin ya iso gida ,Ko da kuwa bai sanar da kowa zuwan nasa ba , ya haka da yayi zuwan bazata , zai zo ya tarar tayo shirin tarɓar sa na musamman kamar daman ya sanar da ita zuwan sa , hakan ya sha faruwa ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba maimouna tana iya sanin duk wani motsin sa a cikin maraɗi , wanda shi ya ɗau hakan a matsayin tsantsar kulawa , to ina laifin wanda ya kula da lamarin ka ??4
STORY CONTINUES BELOW
Cigaba yayi da cin abincin sa cikin nutsuwa , yana jin yadda hoton fuskar falmata ke yawo a ran sa har ya hana shi jin daɗin cin abincin so yake ya sake kallon ta, dan haka ya sake ɗaukar wayar sa ya buɗo hoton , yana sake kallo lokaci lokaci yana cin abincin sa tare da sanyawa yumna a nata bakin .
Abuja
Yau garin an tashi da hadari bakikkirin kafin zuwa hantsi ruwa ya fara sauƙa kamar da bakin ƙwarya ,
Yakaka ita kaɗai ce a gidan ƙwal , saboda samira bata kwana a gidan ba tun jiya da yamma suka fita tare da Alhaji Gali .
Gaba ɗaya bata jin ɗaɗin yanayin da ta ke ciki , gidan yayi shiru dayawa duk da dai ba shi da girma sosai , zaman shirun ya sa tunaninnika yi mata dirar mikiya ,
cikin kwanakin nan tunanin falmata da mama ya matsanta mata , ko dan karatun da ya ɗan tsagaita mata ne ? Amma koyaushe cikin tunanin su take ,
Yaya suke ? , ta san duk sun girma Falmata yanzu shekaru ishirin ne da ita babu ƴan watanni yayin da mama ta haura shekaru biyar ,
Tana begen ganin su duk da cewa samy baby tana tabbatar mata da lafiyar su , a cewar ta suns waya da Rahima wacce take sanar da ita halin da suke ciki , har ma ta ce yaya doctor ya sa su a makarantu , sai dai duk da haka tana son jin ko da muryar su ne amma anty samy ta hana a cewar ta ji daga garesu zai iys kawo tsaiko ga harkar karatun ta , zata yi rauni ta gaza maida hankali ga karatun ta , da jin hakan ya sa ta haƙurewa jin su ,3
Ta bari har sai bayan kammaluwar karatun ta da samy baby ta mata alƙawarin zasu tafi maidugurin tare kamar yadda ta ɗauko ta ƙafa-da-ƙafa , ta je ta taya ta wanke kan ta a wajen falmata , yaya doctor , rahima da ma baba , ƙarshe kuma ta rungumi ƴar ta da ƙanwar ta su dawo tare nan .!
Duk da cewa a farkon zaman su da samy baby ta kasa sakin jiki da ita ganin irin yAudarar da tayi mata ta rabo ta da maiduguri da ƴar uwar ta , sai ta kasance cikin ɗari-ɗari da ita tana tunanin ko zata yi yunƙurin cutar da ita sai dai abunda ya sa ta saki jiki bai wuce yadda lokaci yayi ta tafiya ba tare da ta ga wani sauyi na gallazawa , tilastawa ko ɓatanci daga samy baby ba ,sai ma hidima da take yi da ita tare da kyautata mata fiye da zaton ta ,
Tsawon shekaru biyar da suka yi tare samy baby ke ɗauke da nawin duk wasu buƙatun ta na yau da kullum , cin ta shan ta suturar ta kuɗin magani da na karatun ta duk ta dalilin samy baby ta same su kuma masu kyau masu inganci da suka taimaka mata ƙwarai ta fannin yin rayuwa me cike da inganci da isasshiyar lafiya tare da nasarar kammala karatun ta ,
Dan haka a sannu sannu samy baby ta mantar da ita girman laifi tare da yaudarar da tayi mata , a ƙarshe ta sake shirya mata sabuwar ƙaryar cewa suna waya da rahima , falmata da mama suna lafiya , wanda a zahiri ba gaskiya bane , hasalima rabon ta da shiga maiduguri ita ma ya doshi shekaru huɗu , kuma bata tare da number rahima , ba ta ma sake biyawa ta kan rayuwar bayin Allah biyun da ta raba su da garkuwar su ba ,
Ta tsara haka ne saboda yakaka ta sau jiki ta zauna tare da ita , yadda gaba zata cimma manufar ta hankali kwance ba tare da yakaka ta sake tayar mata da bori ba !
Sai dai kamar yadda suka alƙawarta lokaci ya zo da zasu maiduguri , idan ya so bayan dawowar su sai ta shiga jami’a kamar yadda samy baby ta sake ƙwaɗaita mata a cewar ta jami’a shine mataki na gaba da ya dace da yakaka , duk a ƙoƙarin ta na son janye ta zuwa kan turba irin ta ta , da take ganin fa a yanzu lokaci yayi .
Ƙofar da ake bugu da ɗan ƙarfi ya sanya ta firgita ta dawo daga nisan tunanin da ta tafi .
Duban agogo tayi ta ga ƙarfe goma sha biyu na rana ,
STORY CONTINUES BELOW
Fitowa tayi da nufin zuwa ta buɗe ƙofar da take hasashen dawowar samy baby .
Har lokacin ana yayyafi yif-yif da alamun yau yinin na marka-marka ne .
Da ɗan gudun ta ta ƙarasa bakin ƙofar ta zare sakatar ƙofar ba tare da ta waiwaya ba ta juya da gudun kar ruwan sama ya taɓa ta tana cewa
Sannu da zuwa anty samy .
Sai da ta tsallaka kan Balcony tukun ta juyo ,
A tsorace ta kai duban ta ga mutumin da yake tsaye a maimakon samy baby ,
Saurayi ne dogo wankan tarwaɗa yana tsaye ya zura hannun sa cikin wondon jikin sa , idanun sa sakaye cikin wani kwafcecen baƙin gilashi da kallo ɗaya za’a masa a fahimci rangwamen mutumcin dake tare da shi .
Juyawa tayi da sauri ta tura ƙofar falon ta shiga sabods tunowa da tayi da riga da wondon da suke jikin ta na bacci da duk da cewa basu kama ta ba ko kaɗan amma kaya ne masu tsantsi.
Kai tsaye ta shiga ɗakin ta ta fara bincikar hijabin ta ,
Sai dai hannun da ta ji ya sauƙa a ƙafaɗar ta ya sa hantar cikin ta kaɗawa ,
Da sauri ta jaa baya har tana gwaruwa da jikin wardrobe ,
Idanun ta ya shiga cikin na saurayin da ta bari a waje ,
Anty samira bata nan
ta furta haka , muryar ta na karkawa , lokacin da take ƙoƙarin zira hijabin da ta samu nasarar ɗauka ,
Riƙe hajibin yayi da hannun sa ɗaya , yayi amfani da ɗayan hannun sa wajen zare gilashin idanun sa , mitsitsin jajayen idanun sa da suka sake shigewa ciki-ciki suka bayyana , yana bin ta da wani shu’umin kallo
Da muryar sa irin ta mashaya , yace
Wa yake ta samira tsahuwar guzuma ?
Ga kamar ki gorgeous , ya ƙarasa zancen yana kai hannu zai taɓa kumatun ta ,
Da ƙarfi ta make hannun sa gami da saurin zura hijabin ta ,
Ni ba ƴar iska ba ce kar ka sake taɓa ni , ka fita min daga ɗaki ,
Ɗan baya ya jaa yana yarfe hannun sa da ta buge bakin sa a ɗan buɗe alamun mamaki ,
Baby har da duka ??
Bata kula shi ba ta haura ta kan gadon ta ta dira tana nufar ƙofa , sai dai taku biyu kawai tayi ta ji ya kamo ta ta baya ya haɗa bayan ta da ƙirjin sa ya ɗaga ta ciɗak , ya shiga juyi da ita ,
To tunda wasan tsale tsalle kike so bari na miki hajijiyar ƙauna .2
ya furta haka yana ɓaɓɓaka dariya .
Tun ƙarfin ta ta fara ihu tana wutsil-wutsil da kafafu tare da ƙoƙarin son ɓanɓare hannun sa da ya zagaye cikin ta da shi ,
A guje samy baby da tun a tsakar gida ta fara jiyo ihun yakaka ta ƙaraso cikin ɗakin .
Kai kamal meye haka ? kayi hauka ne ?? Dallah sauƙe ta .
Ba tare da ya sauƙe ta ba ya ce
Ke dallah kauce ki ɗan sakayo mana ƙofa zamu buga ƙwallo ne ni da wannan me zafin kan da tayi gigin duka na .6
Ƙarasowa tayi ta jaa hannun sa ,
Kamal kar muyi haka da kai dan Allah ka sauƙe ta , ƙanwa ta ce fa , yaushe muka fara ƴar haka da kai mutumina ??
A hankali ya sassauta rikon da yayi mata kafin ya sake ta tana jin ya ajiye ta ta fita a guje , ƙafafun ta ko takalmi babu ,
Kallon baka kyauta ba samy baby ta wurga masa kafin ta ja ƙaramin tsaki ,
Kai dai kamal anyi tantiri ɗan iska , to bari na faɗa maka wannan haja ce me matuƙar tsada ba irin taku ba ce domin kuwa sabuwa ce fil , ba’a riga an shiga kasuwa da ita an daka mata wawa ba ,
Ba ta wasa bace na san a ɗan abunda ya shiga tsakanin ku a yanzu kaɗai ,laushin fatar ta da ka taɓa ya isa sanar da kai irin maɗuɗan da zasu taho ta hanyar ta muddin ta shiga kasuwa .
Ƙafar sa ɗaya dake sanye da wani ƙwamemen takalmi sau ciki ya ɗaga yana tokare ta da jikin gadon yakaka .
Ni kuma kin san maƙudan da kike faɗa ba matsala ta bane , ko ruwan su kike so nayi miki kin san zan iya , muddin zan mayar ƙwaɗayi na akan wannan nunanniyar gwandar , nawa kike sa mata kuɗi ??
Two Million Naira
Ta furta cikin gatsali
Bani account number da zan zira miki su ,
A ɗan jirkice ta dube shi cikin ran ta tana son ƙure shi , domin kuwa duk da sanin da tayi wa kamal na shahararran ɗan masu hali da iyayen sa suka gama gurɓata tarbiyyar sa , ya zama tamkar ɗan taure wajen bibiyar mata , manya da ƙanana kyakkyawa da mummuna shi baya zaɓe kawai dai idan ran shi ya biya ya samu ya maida mugun yawu shikenan kuma bai ƙara bi ta kan mace , bata zaton wasan sa da kuɗi ya kai ya haka .
A ɗage ta karanto masa account number da suna , cikin abunda bai gaza mintuna biyu ba sai ga wayar ta dake cikin jaka ta ɗau ƙara ,
Jikin ta na mazari ta fiddo wayar ta duba ,
Alert ne na adadin kuɗin da ta buƙata cif .
Ɗan wara ido tayi da sigar mamaki , sai kuma ta kaɗa idon cikin yanayi na shanye mamakin ta irin na gogaggun matan bariki .
Babu shakka ka ɗau haja me girma , kuma na san baza ka yi wadarai da ita ba , yaushe kake buƙatar ta ?
Haɗe fuska yayi kafin ya watsa hannu
Ka duba wannan da wata maganar iska ? Irin waɗannan kuɗaɗen da na cire har sai kin min iyaka da ita ? Ai yadda ta sani haɗiyar mugun yawu dole daren yau na fanshe kuɗi na , daman ga gari ya ɗau sanyi yanayi ne na shiga daga ciki da sauri .
Ta saki Wata dariyar da take bayyana farin cikin ta akan kuɗaɗen da ta samu da dama tana tsakiya da buƙatar su ,
Alhaji kamalu , to baka da damuwa , yanzu ka tafi , sai ka aika mun address ɗin da kake son na kai maka ita ni da hannun na zan miƙa maka ita anjima da dare ,
Kasan na faɗa maka sabuwa ce bata harkar nan to sai na maka yaƙin shawo maka kan ta ,
Ɗaga kafaɗa yayi cikin nuna halin ko oho ,
Ni dai ki tabbatar kin mata Wankan irin yadda ya kamata
Ya ƙarasa zancen yana kashe mata ido ,
Alhaji kamalu , kar ka ji kome .daren yau na kai ne a sama .
Yakaka wacce take zaune dirshan a cikin ruwan sama ta jikin bangon ɗakin ta ta baya ,
Ta kai hannuwan ta duk biyu ta toshe bakin ta a ƙoƙarin ta na hana kukan da take fitowa sarari kar su samy baby su ji , kamar yadda duk zantukan su ya ratsa kunnuwan ta .
Ashe daman anty samy yaudarar take akan kome , ashe burin ta ta tsundumata cikin irin rayuwar da tunda ta fahimci girman saɓon da ake aikatawa ta hanyar zina take yi mata addu’ar Allah ya sa ita ma ta tuba ta daina ,
Manufar ta ashe ta mayar da ita ga aikata zunubin da tayiwa ubangijinta Alƙawarin ta daina baza ta sake ba !
Ƙuka take da hawaye wani na korar wani , tana jin yadda tsoro ke mamaye ran ta , tsoron kowa da kome , tsoron sake yin zina ta hanyar tirsasawa ,2
Takurewa tayi ta sanya fuskar ta tsakanin ƙafafun ta , sanyin ruwan da ya ɗan sake dawowa da ƙarfin yana ratsa ta ta hanyar jiƙa kayan jikin ta .Fiye da awa ɗaya Samy baby ta kwashe tana shirya Yakaka , wacce ta sha fama da kanta kafin ta iya tsayar da hawayenta batare da bari Samy baby ta fahimci cewa ta san manufar ta ba ,+
Wacce ta shagaltu wajen shirya ta tana jaan ta da hirararrakin da suka shafi jin daɗin duniya , wankan da kansa so tayi ta wanke ta sai dan ganin ba fuska ya sanya ta tsayawa daga bakin ƙofar banɗakin tana sake jaddada mata ta fa yi wankan nan siral ta fita , domin inda zasu tafi waje ne na manyan ƴan gayu kar ta sake tayi abinda zata jawa kan ta raini ,
Daga cikin banɗakin nan ta ci kukan ta a ƙarshe ta tattara duk wani tunani nata da Allah ya mata baiwar sa ,ta matse ƙwaƙwalwar ta, ta haɗa kai da bango akan tunanin hanyar da zata bi ta samarwa da kan ta mafita .

Ƙarfe baƙwai na dare suka fita a motar Samy baby dukkanin su sun ɗau kwalliyya ta gani a faɗa ,
Duk da fuskar Yakaka a tamke take da bayyanannen ɓacin rai hakan bai hana kyaun da tayi ratsowa ba , dai-dai tana karya kan motar ta fito kan titi sosai Samy baby ta dubi sashin Yakaka a kaikaice ,
Yanzu ke Yaks meye haka ? Dan asara akan na hana ki saka wannan uban barigizan hijabin naki shine kike wannan ƙuncin ? Mts!
Ji wannan ƙatuwar jakar da kika ɗauko kamar wata wanzamiya na faɗa miki bata dace da ƙwalliyar nan ba , ƙwalliyar nan taki ba ta babbar jaka bace ta ƴar ƙaramar jakar hannu ce amma kin ƙi ji , ai daman ɗan ƙauye sai ya shekara hamsin a birni yake barin ƙauyenci da gidadanci , ke kika sani sautun mahaukaciya !
Ta danna motar da gudun gaske suka cilla kan titi cikin manyan unguwannin abuja da ko sau ɗaya Yakaka bata taɓa kai ƙafar ta bigiren ba tun zuwan ta garin .
Bata cewa samy ƙala ba illa sake rungume jakar ta da tayi wanda a ciki ta saka hijabinta da niƙab ɗin ta , ƙwaƙwalwar ta a hargitse take da sabon tsoron da yake mamayar ta ,
Ƙofar wani tafakeken gida samy baby ta tsaya tare da zaro wayar ta ta latsa lamba , bugu ɗaya ya ɗauka
Gamu mun iso tace tare da sauƙe wayar daga kunnen ta ,
ba’a yi mintuna uku ba sai maigadi ya buɗe musu ƙofar gidan , samy baby ta danna kan motar a hankali
shigar su gidan yazo dai-dai da ƙaruwar firgici a fuskar yakaka , saboda girman gidan da ya wuce hankalin ta ga fitulu da suke a watse birjik a harabar gidan haske ya wadata tamkar tsakar rana ,
Gefen wasu tsirarun motoci da basu wuce guda shida ba samy baby ta ajiye motar ta ,
Muje Yaks ,
A tsorace ta fito tana bin gidan da kallo , ba tare da samy baby ta kula ta ba tayi gaba , cikin jaan ƙafafu ta bita a baya maƙale da jakar ta , suka dumfari katafaren ginin da yake tsaye a gaban su ,
Babu yalwar mutane a babban ɗakin hutawar da suka shiga , mata da mazan da suke harkokin su a wajen babu wanda ya kula su ,
Samy baby ta jagorance su suka zauna , basu jima da zama ba aka murɗo ɗaya daga cikin ƙofofin da suke ta cikin falon aka shigo ,
Kamal ne ya shigo yana ɗan gama hanya ya ƙaraso tare da sakin jiki ya faɗa kan kujerar kusa da yakaka , rigijib !
a tsorace ta miƙe tana raba ido .
Idanun sa da suka yi nawi saboda kayan mayen da ya ɗibga ya ɗaga ya watsa mata wani kallon ƙasƙanci ,
Ke wai ji mana , ya kike wani safurewa haka kina wani ƙoƙarin waskewa , ? Kamar baki da sanin cewa na biya kuɗin ki , zo nan na fara morar kuɗi na dallah1
Ya miƙa hannu ya fisgota ta koma da ƙarfi ta zauna ,
Ganin sa ya mayar kan Samy baby
Yane to yawa kike fa, Zaman me kike ? Ko kina neman me tayi ne ? Nan duk suna da chicks ɗin su dan haka ki ƙara gaba ,..
STORY CONTINUES BELOW
Ke kuma zo muje ki fara tausa min gaɓɓai da waɗannan tausasan hannuwan naki tuɓus-tuɓus , wayyo laushi!
Ya fisgi hannun Yakaka suka miƙe tsaye ,
Fuskar samy baby ta kalla , idanunsu suka gauraya cikin na juna ,
Ga mamakin samy baby ba kamar yadda ta zaci zata ga hawaye a idanun yakaka ba , saɓanin ta idanun ta a bushe suke ƙyamas ,ɗauke da wani irin yanayi wanda yayi tasiri ƙwarai wajen rage mata kuzarin tashi ta bar gurin kamar yadda aka mata umarni ,
Kallon da yakaka take mata kallo ne me kaifi da yake ɗauke da fasasarori da dama ,wanda ta gaza ɗaukar masa fassara guda ,2
tana ganin lokacin da ta fisge hannun ta daga cikin na kamal ɗin ta nufi ƙofar da ta ga ya nufa da ita , ba tare da ta sake waiwayowa gare ta ba ,
A sanyaye ta miƙe cikin ran ta tana harhaɗa kalmomin da zata yi amfani da su wajen kalmaso kan yakaka ta rarrashe ta kamar yadda ta saba yi mata a duk lokacin da tayi mata wani gagarumin laifi ,1
gefe guda tana tunanin ware wani kaso me ɗan tsoka daga cikin kuɗin da kamal ɗin ya bata ta danƙa mata su duk domin su taimaka wajen shawo kan ta cikin sauki.
Da wannan tunanin ta faɗa motar ta bar gidan tana duban agogon hannun ta da yake nuna ƙarfe tara saura ƴan mintoci , sama ta haskaka da hadarin da yake haɗuwa da ke nuni da koyaushe cikin dare ruwa zai iya sauƙa .
Kar ka kuskura ka sake taɓani ,
Ta ce da shi lokacin da take samun wajen zama bisa kan kujerar gaban tafkeken gadon ɗakin na alfarma .
Wata dariya ya kwashe da ita yayi sufa ya faɗa gadon rubda ciki .
Kai yarinyar nan salon ki na burge ni , wat….
Zan sha BURKUTU ,
Ya tsinkayi muryar ta ta katse masa kalaman sa , waigowa yayi yana daga kwance ya dube ta , fuskar sa na bayyana mamaki yace :
Burkutu ?
Eh
tace da shi tana tsattsare shi da idanun ta ,
Ni bana shan giyar gargajiya ,”blue moon ,” ita ce giyar da nafi ƙauna , yanzu ma ita na sha ƴar kaɗan , kin san tana da ƙarfi shegiyar giya ce , ko za ki iya sha na zubo miki kaɗan ki taɓa irin ta ?
Kawo min
ta ce da shi a taikaice .
Miƙewa yayi ya fita
Yana fita ta miƙe tsaye ta shiga kai kawo a ɗakin tana yarfe hannu , da tayi zaton zata iya , a zaton ta tana da ƙarfin zuciya , ya kome yake shirin kufce mata ? Me zai faru da ita idan har shirin ta bai tafi dai-dai ba , ??
Jin motsin taɓa ƙofar ya sa tayi saurin komawa ta zauna ,
Ya shigo hannun sa ɗaya riƙe da kwalbar giyar blue moon ɗaya kuma kofin gilashi da ya zubo ƴar ƙanƙara a ciki ,
Zuba giyar yayi ƴar madaidaiciya ya miƙa mata ,
Idanun ta na duba ƙasa ta ce da shi ka fara sha ,
Jim yayi riƙe da kofin sai kuma ya kai bakin sa ya ɗan kurɓa ,
Ya Sake miƙa mata ,
Ka cika min taf
Tace da shi ba tare da ta bari sun haɗa ido ba ,
Keeeee hahaha , wannan fa blue moon ce ba’a mata haɗama yanzu nan za ki ji ki warwas kin gaza motsi, ba ta wasa bace wannan , ke kin san kuɗin ta kuwa ? Yafi jarin baban ki .
STORY CONTINUES BELOW
Bana shan wannan , warin ta bai min daɗi ba ka kawo min wata idan akwai , nafi son wacce zata ƙara min kuzari ,
Ɓata rai yayi ! ya tsaya kallon ta sai kuma ya kwashe da wata dariyar sakarci ,
Tunda ta ƙara kuzari kike nema bari na kawo miki Amstel kina shanta yau ji za kiyi kamar an miki allurar da ake yiwa dawakai ,
Ya ƙarasa zancen yana kafa kai ya sha fiye da rabin wacce ya zuba a kofin ya ajiye sauran ya fita yana gama hanya tare da jaan wani siririn fito irin na wanda duniya ta yiwa daɗi .
Yana fita ta miƙe tare da murɗa ƙofar ta fito , ɗan yawatawa tayi da idanun ta cikin daƙiƙoƙi ta fahimci ɗaukewar ƙafar da ya ƙaru a wajen domin mutum ɗaya ta hango a zaune ya tasa kwalaban giya a gaban sa ,
Da sassarfar da take harɗe kafafun ta ta taka tana nufar ƙofar ficewa daga wajen bakin ta ɗauke da addu’o’i iri-iri ,
Siit ji mana , ?
Numfashin ta ya nemi siƙewa da jin muryar wani yana dakatar da ita , bata juya ba sai ma ƙaimi da ta ƙara ba tare da ta bari ta ƙarasa jikin ƙofar ba ta miƙe hannuwan ta duk biyu ta tura ƙofar , ta jefa ƙafar ta waje .
Tana jin sa yana sake sanar da ita ba fa nan kamal ɗin yake ba ,
Ba ta saurare shi ba , ta kara da saurin da yafi kusa da gudu tana keta farfajiyar gidan ta nufi ƙofar da suka shigo gidan ,
Ƴar ƙaramar kofar da take maƙale da babbar ƙofar gidan ta nufa kai tsaye ta tura ta , cikin sa’a ƙofar ta buɗu da gudun gaske ta ƙarasa ficewa daga gidan ,1
Tsawa tare da rugugin hadari da ya karaɗe sararin sama bai toshe mata kunne daga barin jin tashin muryar kamal ba , hakan ya sa a diririce ta tura ƙaramar ƙofar gidan da yake daura da ita ta faɗa ,
Ga babbar sa’ar ta babu kowa a harabar ɗan madaidaicin gidan me tsari , dan haka cikin sauri ta cire hijabin ta daga cikin jakar ta ta zira akan kayan ta , ta sake zaro niƙabin ta ta fara ƙoƙarin ɗaurawa ,
Gurnanin da ta ji daga gefen ta kaɗan shi yasa zuciyar ta dokawa da ƙarfi , tare da taimakon hasken ƙwan lantarkin ta waiga da sauri idanun ta suka shiga cikin na wani ƙosasshen kare da yake kwance daga gefe kusa da ita ,
Ɓurɓushin tsoron daga ƙasan ran ta ya fara toroƙo kafin baki ɗayan jikin ta ya ɗauki rawa ,
Cikin abunda yake gaza da minti guda ta juya da gudun gaske ta fita a gidan tana banko ƙofar , karen kuwa bai jinkirta ba ya rufa mata baya da ƙaƙƙarfan haushin sa , suka zuba ƴar tsare akan titin da yake shal babu kowa saboda dare da ya fara yi ƙarfe goma saura , haɗi da garin da yake gangame da hadari .
Gudu take tamkar wacce aka ɗaurawa tayoyi a ƙafa , bata san gabas ba bare yamma , karen wanda haushin sa ya jawo ƴan uwan sa karnai na bakin titi suka zama su uku , su ma bin ta suke da iyakar gudun su .
Ruwan saman da ya tsinke kamar da bakin ƙwarya shi ya sake gigita yakaka , har numfashin ta na barazanar ɗaukewa duhu na fara mamaye ganin ta .
Hakan shi ya hana ta fahimci karnukan sun koma baya sun daina bin ta tunda ruwan saman ya fara sauƙa .
Duk da cewa dare ne kuma titin babu kowa , amma shi ka’idar tukin sa ne haka baya cika gudu , sannu-sannu yake tuƙin sa cikin nutsuwa ƙira’ar Sheik Sudais cikin Suratul Al-Araf tana tashi ta cikin sifiƙun motar , fitowar sa kenan daga asibiti inda ya yini yana wasu muhimman aiyuka ( shigar da bayanai akan marasa lafiyan da yake ɗauke da alhakin duba su ) saboda hutu da yake son rubutawa na sati shidda ya je gida ya gaida iyayen sa , sannan yayi amfani da damar wajen sasantan tsakanin iyayen sa ,1
STORY CONTINUES BELOW
lokaci yayi da yakamata ace an kawo ƙarshen koma menene ya jawo rabuwar ta su tsawon waɗannan shekarun , ga su suna zaune babu abokan rayuwa wanda hakan ko kusa ba martabar su bane , duba da cewa shekarun su sun fara jaa ,
À son ransa a maida auren iyayen nasu kafin bikin Rahima wanda za’a yi a farkon sabuwar shekara me kamawa nan da watanni bakwai masu zuwa ,
Bai yi aune ba ta ɓullo daga kwanar gaban sa da gudun gaske , da ba domin a hankali yake tafiyar ba da babu abunda zai hana ya yi ciki da ita da mota.
Da ƙarfin gaske ya jaa burki ganin yadda ta bugu da jikin motar ta sa , ruwan saman bai hana shi ɓalle murfin motar ya fito ba , ya zagayo da sauri ta sashin da take dai-dai lokacin da ta miƙe tsaye daga faɗuwar da tayi ,
Da gudun ta tayi bayan sa ta ɓuya bayan ta riƙe jikin rigar sa ƙam da dukkanin hannuwan ta biyu , jikin ta ko’ina rawa yake .
Tsai yayi yana jin yadda wani nisasshen yanayi a wani shuɗaɗɗen lokaci makamancin wannan yana bijiro masa ,
KARE , KARNUKA su na bina dan Allah ka taimaka min , zasu kashe ni .
Muryar ta tayi amsa kuwwa a kunnuwan sa ta tafi ta tado ƴar uwar ta da take binne cikin ran sa me ɗauke da salo da kalmomi iri ɗaya da suka fito a jere cikin yanayi me kama sak da wannan , dan haka sai ya jiyo baki ɗayan sa yana fuskantar ta bayan ya fizge jikin sa ,
Hasken walkiya da na fitilun gefen hanya sun gaza wajen fiddo masa da ainahin kamannin fuskar ta da take rufe da niƙabi illa idanun ta da suka jirkita da zallar tsoro , da ya gaza jurar kallon su .
A hankali ya janye ganin sa daga kan ta ya dubi gefen titi inda ta ɓullo , ko alamun karnai babu , dan haka ya juya da sassarfa yana nufar ƙofar motar sa , cikin ran sa yana aiyanawa wannan wani sabon salo ne na matan banza .
Ki koma gida dare yayi .
Yace da ita .
Halin ruɗanin da take ciki bai isa jirkita mata tunanin da zai sa ta gaza gane shi ba , zuban ruwan sama akan kamilallar fuskar sa ba zai taimaka ba wajen hana ta shaida kamannin sa duk kuwa da rabuwa da yin tozali da tayi da shi na tsawon wasu shekaru , shi ɗin ne dai mutumin da Allah yake kawo mata shi a duk lokacin da take tsaka da neman agaji me girma a cikin rayuwarta ,
Wani irin yanayi ta tsinci kan ta a ciki me nawi , da ya sanya ta sauƙe ganin ta ƙasa ,
A hankali ya tada motar sa ya gifta ta tana me cigaba da tsayuwa a wajen ruwan sama na sauƙa kan ta cikin yanayi na rashin madafa ,
Tsaki yayi a karo na biyu lokacin da yake sake kai ganin sa jikin ɗan madubin saman motar sa yana hango ta , cikin nutsuwa ya murɗa kan motar sa ya taka ta yayi baya tare da dawowa inda ya bar ta ,
Shigo na kai ki gida .
yace ga ita ba tare da ya dubi sashin da take tsaye ba .
A hankali ta buɗe gidan baya na motar ta shiga ta rufe ƙofar tare da takurewa da jikin murfin motar tayi ƙasa da idanunta , wata irin kunya da nawin sa take ji ., girman laifin ta ninƙaya yake cikin tunanin ta yana ƙara girmama a idanun ta , zuciyar ta na raɗa mata ai ita ɗin bata cancanta da sake samun wani taimako kome ƙanƙantar sa daga gare sa ba .
ko motsi ta gaza yi , gani take cikin duk wani motsi da zata yi zai iya gane ta , zai fahimci ko ita wacece , da zuwa yanzu ta tabbatar bai shaida ta ba .
me zai faru idan ya gane ta ? Wataƙila ya wurgata kan titi .
Tana son tace wani abu ko da kalmomi biyu ne ,
ina Falmata ? A wanne hali take ciki ?
A sama ta tsinkayi muryar sa ,
Wacce unguwa kike
STORY CONTINUES BELOW
Muryar ta a dushe ƙasan maƙoshin ta ta sanar da shi ,
Babu wanda ya sake magana a tsakanin su har zuwa lokacin da suka kawo unguwar , ƙofar gidan malama maryam ta nemi ya dakata zata sauƙa , baice ƙala ba ya tsayar da motar ,
Na-nagode
ta furta tana barin motar kai tsaye ta isa jikin ƙofar gidan malama maryam ta shiga ƙwanƙwasawa sannu kan hankali .
Jaan motar sa yayi yana barin unguwar lokacin da zuciyar sa ke nace masa wajen son bijiro masa da tunanin waccen tana haɗa su da yanayin wannan , amma bai bari tunanin yayi tasiri ba ya kunna karatun Al’qur’ani yana cigaba da saurara .
bai son tuno wani abu da ya shafe ta , ita ɗin ai bata cancanta da kutsowa cikin tunanin sa ba ko kaɗan .
A hankali ta zame ta zauna a jikin ƙofar bayan shuɗewar ƙugin tayoyin motar sa bisa kan kwalta, ruwan saman na cigaba da sauƙa a jikin ta , kukan da take riƙewa tun shigarta motar ta saki da ƙarfi , kukan ha’incin da samy baby ta yi mata , kukan nadamar kuskuren da ta aikata a rayuwar ta, babu abunda take so a dai-dai lokacin irin ta buɗi ido ta ga falmata da mama a tare da ita , ta haƙiƙance sune kaɗai jinin ta a duniya sune baza su taɓa cutar da ita ba ,
Takurewa tayi a wajen tana karkarwar sanyin iskar ɗaukewar ruwan sama da yake busa ta .
Washegari
Samy baby tana tsakiyar baccin ta na tofon gira misalin ƙarfe goma na safe ta tsinkayo bugun ƙofar gidan ta tamkar a tsakiyar kan ta ,
Mummunan tsaki ta jaa , bayan ta miƙe tana haɗa maballan gaban rigar baccin ta , kan ta ko ɗan kwali babu ta fito , dai-dai lokacin da aka kaiwa ƙofar wani mugun bugu tamkar za’a ɓalla ta ,
Kai wai wanne ɗan^ yake ƙoƙarin ɓalla min kofa , tamkar na ci bashin sa ban biya ba ?
Ta furta hakan a tsawace tana ƙoƙarin zare sakatar ƙofar , bata gama zarewa ba ta ji anyi ciki da ita da ƙofar , tayi baya taga-taga ƙiris ya rage ta faɗi ,
A fusace ta ɗago kan ta hannun ta dafe da goshin ta , da ƙofar ta buga
Kutumelesi ,….
Kar ki yadda ki zage ni tsohuwar ƴar damfara , kuɗaɗena na zo ki mayar min da su account , saboda ƙaramar ƴar iskar da kuka haɗa baki kuka damfare ni tun daren jiya ta gudu , dan haka ko naira ɗaya ban yadda a samu giɓin su ba a cikin kuɗina ki dawo min da su yanzu-yanzu .
Wani irin fargaba ne ya dirarwa Samy baby , me Kamal yake cewa ? Yakaka ta gudu ?
Da kƴar ta tattaro guntuwar nutsuwar ta ,
Ta juƴa ta fara taku tana cigaba da murza goshin ta ,
Kamal ka shigo muyi magana a ciki , zancen ba na tsaye bane ,
Ke duba Samira ba inda zan shiga kawai kuɗaɗen nan zaki dawo min da su domin ko hannun ta bata yadda na taɓa ba tayi tafiyar ta tun jiya , bayan wahalar neman ta da ta saka ni cikin ruwan sama ƴar^ ke daman kin san yarinyar nan wata gara ce irin haka har zaki karɓi kuɗina akan ta ? Yi sauri dallah ki dawo min da su , da akwai inda zan tafi daga nan bani da lokacin ɓatawa .
Kallon ba yadda zan yi Samy baby take bin Kamal da shi , ta fahimci a bugen sa yake tatil kamar koyaushe , idan har ta nemi yin gardama kan zancen kuɗin nan kome zai iya faruwa da ita ,
Bani account number
Ta ce masa tana shigewa ɗaki ɗauko wayar ta , daga ƙasan ran ta take jin mummunan ɓacin rai na taso mata akan abunda Yakaka tayi mata , ashe rashin mutumcin Yaks har ya kai haka ? Ta gudu ta jawo mata irin wannan babbar asara ? Allah ya so bata riga ta kacan-chala kuɗin nan ba da yanzu yaya zata yi da tijarar Kamal ? Tabɗi dole ne ta ɗau mataki akan Yaks , ta nuna mata kuskuren ta saboda gaba kar ta sake gwada mata irin wannan mugun wasan .
STORY CONTINUES BELOW
Cikin mintoci biyar Samy baby ta ɗibga asarar Naira miliyan biyun da suke mallakinta daga jiya zuwa yau , har gumi ne ke tsattsafo mata , lokacin da ta koma falo ta zauna bayan tafiyar Kamal da bai bar gidan ba sai da miliyan ɗin sa biyu ta koma account ɗin sa .
Ina Yakaka ta kwana ? Shine tambayar da Samy baby take yiwa kanta ,
Zumbur ! ta miƙe tsaye lokacin da ta ayyana inda Yakaka ta kwana , gidan Malama Maryam .
Ɗan siririn mayafinta da yake ajiye a falon shi ta ɗauka ta yafa akan rigar baccin jikin ta , ta fito a fusace bayan ta rufe ƙofar gidan da makulli ta zagaya layin bayan su kai tsaye ta doshi gidan malama Maryam da tunda take sau ɗaya ta taɓa taka gidan , Sai fa yau da zata kuma zuwa .
Ko sallama bata yi ba ta danna kai cikin gidan , ilai kuwa tana shiga falon ta tadda Yakaka tana zaune ta jingina da jikin ɗaya daga cikin kujerun falon da farantin cin abinci a gaban ta wanda bata kai ga sa hannun cikin sa ba .
Da shigowar ta Yakaka ta miƙe da alamun firgici a fuskar ta wacce ta ɗan kumbura kaɗan tayi jaa ,
Anty Samy ..
Da hannu ta dakatar da ita , ki min shiru Yaks , ashe baki da mutumci haka daman? Ƙyat ! tayi Kwafa ki wuce mu tafi gida inason yin magana da ke .
Malama Maryam wacce tashin muryar Samy baby ya sanyata fitowa daga cikin ɗakin ta , ta ƙaraso wajen tana bin Samy baby da kallon nazari
Yayar Yakaka lafiya dai ko ? Anan Yakaka ta kwana tun jiya cikin dare take ta kuka taƙi sanar da mu abunda ya sameta , dan Allah idan laifi tayi miki kiyi haƙuri ki yafe mata
Wani kallon banza Samy baby ta jefawa Malama Maryam saboda ta fara fahimtar duk wani taurin kai da take hango alamun Yakaka zata gwada mata har da taimakon koyarwar Malama Maryam wacce ta lura duk wasu sabbin ɗabi’un Yakaka daga gurin ta ta kwafe .
Ki wuce mu tafi
Ta sake maimaitawa tana mayar da duban ta kan Yakakar
Da wani irin yanayi cikin muryar Yakaka , wanda yake fallasa halin baƙin cikin da zuciyar ta ke ciki , tace
Bazan bi ki ba Anty Samira ni daga nan Maiduguri zan koma wajen Falmata da ƴa ta , bazan taɓa yadda nayi yadda kike so nayi ba . BAZAN SAKE YIN ZINA BA
Kif-kifta ido Samy baby tayi tamkar bata ji da kyau ba ,ta karkata kai tare da ɗage shi sama ta ce :
Kika ce me Yaks ?
Bata jira ta amsa mata ba ta ɗora da cewa .
Maiduguri ?? Sai ta kwashe da wata gajerar dariya ,
Wa kika sani a Maidugurin ? Waye naki a can wa kike da shi a duniya ?
Da sauri Yakaka ta amsa mata har muryar ta na sarƙewa
Ƙanwata Falmata da ƴata Mama !
Hahaha !
Yaks kenan ai Falmata da ƴar jaririyar da kika gudu kika bari duk sun riga sun mutu , au ashe ban faɗa miki ba ko ? Sorry lokacin kina tsaka da jarabawa ne kin san fa ke mayyar karatu ce …
Kukan kurar da Yakaka tayi ta tura samy baby ta faɗa kan kujerar bayan ta , ta hau ɗare-ɗare kan ta , tare da maƙure mata wuya shi ya hana samy baby cigaba da zancen da ta shiryo shi a yanzu ,
Me na miki Anty Samira ? Me na miki ? Ƙarya kike min koyaushe Ƙarya kike min baki taɓa faɗa min gaskiya ba Ƙarya kike Falmata na bata mutu ba , Ƙarya kike yi bata mutu ba , ki faɗa min gaskiya me kike shiryawa game da rayuwata ? Me na miki ?
Da taimakon Malama Maryam suka ɗaga Yakaka daga kan Samy baby wacce duk Yakaka ta yakushewa wuya , gabaɗaya ta birkice musu kamar me tashin Aljanu , ihu kawai take tana cewa1
STORY CONTINUES BELOW
Falmata bata mutu ba ƙarya ne ,
Addu’o’i Malama Maryam take tofa mata tana riƙe da ita ,
Bata cikin hankalinta ta ɗago kan ta hawaye wani na korar wani a fuskar ta ,
Ummi , ki kaini Maiduguri yanzu-yanzu dan Allah , ki kaini naga Falmata
Zan kai ki Yakaka ki nutsu ki daina wannan ihun babu kyau , kiyi innalillahi wa inna ilahi raji’oon , kiyi addu’a ki bar kukan nan haka .
Gƴaɗa kai take ba domin tana fahimtar kalmomin Malama Maryam ba , bakin ta ya gaza furta kalma guda illa karkarwa da laɓɓan ta ke yi , zuciyar ta ke wani irin bugu da tsananin tsoron da yake barazanar tarwatsa mata zuciya , kalmar Mutuwa ga Falmata tayi mata tsauri da girma ta yadda zuciyar ta gaza ɗauka , tunanin ta ya guntule cikin rashin sanin takamaimai a halin da take ciki , ƙiyayyar samy baby sabuwa fil take yaɗo cikin ran ta .
Da baya-da-baya Samy baby ta ƙarasa barin falon tana jin yadda tsoron halin da ta ga Yakaka a ciki na cika mata zuciya ,
Niamey Niger
Cikin makonni uku da ƴan kwanaki visa Falmata da Mama ta fito , Biyamuradi Youssouf bai jinkirta ba wajen fara shirye-shiryen tafiyar su , bayan ya ɗauki hutun sa na kwanaki talatin a wajen aikin sa , tare da gudurtawa cikin ran sa idan kwanakin sun gaza wajen yin abunda ya kai su , zai dawo ya rubuta takardar neman iznin hutu batare da biyansa albashi ba ya koma .
Cikin satin zuwan sa Maradi sau biyu , bayani sosai ya tsarawa Maimartaba tare da hajiya Umma kan cewa aiki ne zai kai shi zouwa ƙasar Amurka ,
Babu shakku cikin ran su suka masa addu’o’in samun nasara kan abunda za shi nema , tare da fatan dawowa lafiya .
Bangaren matan sa ma bai samu matsala da Siyama ba , wacce take da tsananin yarda ga mijinta , dan haka ta hau shirya masa ƴan kayan cimaka da zai iya yin guzurin su zuwa ƙasar da za shi , zuciyar ta cike taf da kewar sa da ta fara tundaga yanzu , lokaci-lokaci tana sharar ƙwalla rabuwa da masoyi duk da cewa ba sabon abu bane shafe kwanaki masu yawa irin haka basu tare , amma haka kawai taji wannan tafiyar tasa ta tsaya mata a zuci ko domin ƙasar zai bari bakiɗaya zuwa wata nahiyar ?
Ga Gimbiya Maimounatou kuwa sam bata gamsu ba da zancen barin sa ƙasar , hasalima batun tafiyar sa ya kawo mata tsaiko ne kan wani Al’amari da take ɗorarwa akan sa , sai take ganin tamkar da gayya ya tsiri tafiyar ,hakan ba kome bane face salo ne na kauda-bara da ya sha faruwa a duk lokacin da take kan gaɓa na son cimma ƙudirin ta , sai dai baza ta fasa ba , ba kuma zata gaza ba wajen cigaba da bibiyar kome a sannu har sai haƙar ta ta cimma ruwa .1
Dan haka babu ƙarsashi a tare da ita suka yi bankwana bayan ta haɗa masa ƴan nata kayan cimakan da basu cika yawa ba saboda zuciyar ta da take shaƙare da takaici , duk da cewa tayi iyakar ƙoƙari kamar yadda ta saba ta boye abunda ke binne ƙarƙashin ran ta .1
Daga Tafeeda kaɗai ya so samun tangarɗa wanda yake da sani sosai akan harkar aikin su , ya kuma titsiye Biyamuradin da tambayoyi akan aikin da yace zai kai shi US , sai dai ga mamakin sa hanya-hanya da zamiya iri-iri Biyamuradi ya dunga yi masa da ya hana shi sanin takamaimai gaskiyar lamari game da tafiyar ta shi ,
karshe dai ya fahimci babu shakka akwai abu me girma da Aminin sa ke ɓoye ma sa wanda kuma lalle wannan abun ya shafi rayuwar sa ta kurkusa , sai ya ɗiga ayar tambayar . Cikin ran sa ya ƙudurci bin diddigin kome .2
Duk wani shirin tafiyar su ya kammala , kamar yadda Biyamuradi ya Alƙwarta ga Hajja , ya ƙira direban da zai kai ta ana washegarin ranar tafiyar su , ya sanar da shi gobe da safe ya zo su kama hanyar Nigeria da Hajja .
STORY CONTINUES BELOW
Jakar matafiya karama da Babba Ya kawo musu ,
Ya miƙa Babbar ga Hajja , yana cewa
Hajja ga wannan jakar ki shirya suturun ki ciki , wannan ƙaramar kouma na Fatima ne , kayan ta kaɗan zata ɗauka ba wasou masou yawa ba kawai aboubouwa masu muhimmanci da zata iya bouƙata su zata zouba a ciki, ita kouwa Mama ba sai an ɗauka mata wasu suturu ba , kaya biyu kawai sun isar mata idan munka kai can duk za’a saya wasu suturu sabouda yanayin mu da nasou ba ɗaya bane .
Au Babban soja wai da ni har mun shirya kayan a cikin manyan akwatuna ? Fiye da rabin kayan nasu ma ai mun loda su a akwatuna har huɗu , ashe tafiyar ba ta guzurin kaya bace ikon Allah .
Ɗan murmushi yayi , a ah hajja a ajiye waɗannan suturu a gida zamu sayi wasu a can .
To ai babu kome , huta-roro ( waken gizo ya ƙi ‘Ya’ya ) wannan babu neman masu dakon kaya a tashar jirgin sama , oh duniya kullum cigaba ake watau ita turai ba’a zuwa da kayayyaki dayawa ? Dayake ma can gidan kaya ne , kamfaninnika ne da su na suturu sai ka zaɓa ka darje , kuma fa irin atamfofin nan namu arhar bulus ne da su a can ko Babban soja ?
Cikin gundura da hirar hajja , yace
hajja ai can basou sanya tufafi hakka irin namou , su suturun su duk kananun kaya ne sai kouma kayan sanyi ,
Firfito da idanu tayi bayan ta rafka tagumi fuskar ta cike da alhini ta ɗora da :
Ƙananun kaya ni hauw’u ? Da kai da Falmatar watau duk ƙananun kaya za ku dunga sawa ? O’o ana bariki a turai , to ita dai Mama ku dunga suturtata da kyau saboda yanayin lafiyar ta daman ba kumari ta cika ba . Kai tir da rayuwa da ba ta Musulunci ba1
Sai kuma ta ɗan saki murmushi tunowa da tayi da wani abu ,
Kuma ka ga ƙananan kayan zasu amshi jikin ku Babban soja , musamman ma ita Falmata , ƴar riga da wondon nan na zamani ka daure ka saya mata ɗanɗasa-ɗanɗasa ba ƙaramin haska ta zasu yi ba .2
Ɗan zunkuɗawa yayi akan kujerar jin an taɓo masa inda yake masa ƙaiƙayi ,
Hajja ina Fatima tare da mama sun ka tafi tun shigowata ban ji motsin su ba ,
Nan suka shiga gidan su Zainaba ta je ayi mata kitso da kunshin tafiya . Ai tana gaf da shigowa ma .
Ƙunshi kuma hajja ?
Tafiyar mu ai ta neman lafiya ce hajja ba’a buƙatar duk irin wannan shirye-shiryen ,
Ta gefen ido hajja ta dube shi , Babban soja ai shi ƙunshi ado ne ga ɗiya mace …
Sallamar Falmata ita ta hana ta ƙarasa zancen ,
Da gudu mama ta saki hannun Falmata da take yiwa jagora ta nufi Baban ta
Papa bienvenue , ta ƙarasa shigewa jikin sa da ya buɗe mata hannunwan sa , ta kwantar da kan ta a ƙirjin sa , ya shafi kan ta yana sauƙe idanun sa akan Falmata da take ƙarasowa wajen jikin ta sanye da dogon hijabin ta har ƙwauri ta zauna daga ƙasa a gefe ,
Sashin da take hasashen yana wajen ta fuskan ta cikin nutsuwa ta gaishe shi fuskar ta kadaran-kadahan .
Ya amsa yana bin fuskar ta da kallo da kitson da aka mata ya sake fiddo ƙyallin fatar ta tare da bayyana hasken goshin ta ,
STORY CONTINUES BELOW
Hajja wacce bata zama a tsakanin su ta yunƙura ta miƙe riƙe da jakankunan a hannu ta nufi ɗaki , tana ƙiran mama wacce tayi biris da ita taƙi amsawa sai ma sake lafewa da tayi a jikin baban ta .
Fatima ya shiri ? Kin kammala kou ?
Eh mun kammala tace
To madallah gobe insha Allah zamou tafi ku zama cikin shiri kin ji kou ?
Toh ta amsa tana gyaɗa kai !
Shiru ne ya ɗan gitta tsakani , kafin mama ta ɗago kan ta daga jikin Baban ta ,
Papa , an mana kitso ni da Mamaa na ka gani yayi chau ?
Ta janye hular kan ta , manyan kitson chuku da aka mata suka bayyana , duk da kitson manya-manya ne amma sun yi kyaun zane kasantuwar ta me yalwar gashi sai ya ƙarawa kyaun kitson armashi .
Shafa kan nata yayi yana murmushi yace ,
wow c’est très beau ,
Da dariya ta bar jikin sa ta nufi Falmata tana zuwa ta fara kici-kicin buɗe mata kai ,
Mamaa ke ma ki nunawa papa kitson ki , yafi nawa ma chau ko papa ?
A hankali ya gyaɗa mata kai yana jingina bayan sa da jikin kujerar ba tare da ya janye ganin sa daga kan su ba ,
Ture hannun ta Falmata tayi ta ɗan ɗaga sauti ,
Ki bari mama ba na hana ki buɗe min kai ba ?
Ba tare da ta sauke hannuwan ta daga kan falmata ba tace
Ai papa ne zai gani .
Tsawa tayi mata lokacin da take son ta sauƙe mata hijabin a tilas ,
Firgita tayi ta ja baya ta rakuɓe tana ƙwalan-ƙwalan da ido tare da raba kallon ta tsakanin mamar ta da baban ta ,
A hankali wasu siraran ƙwalla suka silalo daga gurbin idanun ta ganin an mata abunda ba’a saba yi mata ba ba kuma tare da an rarrashe ta ba ,
Cikin ran ta taji shirun da tayi tare da sanin manufar sa , dagulewar zuciyar ta ya zo dai-dai da zubar hawayen Mama ,
Hannu ta ɗaga ta fara lalubar inda take jin tashin shisshiƙar kukan ta , ta jawo ta jikin ta tare da ɗaura ta akan cinyoyin ta ,
Kwantar da kan ta tayi da ƙarfi a jikin mamar ta gami da fashewa da kukan da tayi tanadin sa ,
Kamar ruwan maɗaci haka take jin ɗacin sautin kukan ta daga cikin zuciyar ta, dan haka ta fara aikin lallashin ta ,
Hannu ta kai ta zame hajibin nata , ƙananan kitson da aka mata yir-yir suka bayyana
Ta karya murya cikin kuikoyon muryar mama tace :
Papa ka ga kitso na yayi chau ??
A hankali ta ɗago kan ta daga jikin ta idanun ta jage-jage da hawayen rikici , ta washe ƴan haƙoran ta lokacin da take kama dogon jelar kitson shade ,'( me hawa biyu ) da aka tufke shi ya sauƙa kan dokin wuyan ta , ta waiga tana duban Baban ta wanda duk abunda suke yana bin su da ido ,
STORY CONTINUES BELOW
ransa cike taf da ƙauna tare da shauƙin soyayyar dake tsakanin uwa da ɗiyar ta .
Muryar ta kamar ba ita ke kuka yanzu ba tace ,
Papa ka ga kitson mamaa na yayi chau ko ?
Yunƙurawa yayi ya matso sosai gaban kujerar da yake kai ,
Yana ƴar dariyar yadda fuskar falmata take a ɗaure tana wani takurewa yace ,
Ai tayi nissa daga can bani ganin kitson nata , ta matso nan kussa na gani kou ? Ya ƙarasa zancen yana karya wuya .
Eh Mamaa ki zo ya gani ,
Ta jawo hannun Falmata , gudun rikici ya sa Falmata ta biye mata ta taso ta biyo ta , gaf da ƙafafun sa Mama ta zaunar da ita ,
Idanun sa ya sauƙe akan kitson da suke yir-yir kamar inji ne ya jera , ƙwarai kyaun kitson ya birge shi .
Basu yi aune ba ta jaa hannun Baban ta ta ɗora akan Falmata ,
Papa ka ga ni ?
Ta ce tana washe masa haƙoranta .
Kasa janye hannun nasa yayi daga kan ta , saboda wani irin yanayi da yake ji yana zagaya illahirin jikin sa ,
Tundaga kan yatsar kafar ta taji tashin tsikar jikin ta , da wani yanayi da ya tsinka gudun jinin jikin ta , irin yadda bata taɓa ji ba a rayuwar ta , bakiɗayan jikin ta babu kuzari ,
Ganin shirun su ya tsawaita ya sa Mama ta raba ganin ta a tsakanin su , kafin ta ɗan turo baki ,
Papaa , baka ce kitson mama yayi kyau ba ??
Cikin dai-daita nutsuwar sa ya janye hannun sa daga kan ta ya janyo Mama Zuwa jikin sa ,
Kitson Maman Mama yayi kyau sossai
très belle .
Batare da ta ƙara daƙiƙa guda ba ta miƙe , tana nufar hanyar ɗakin hajja , zuciyar ta na cigaba da tsananta bugu , cikin kowanne takun ƙafafunta take jin idanun sa na yi mata rakiya .
9:30pm
Falmata ta sake muskuɗawa tana rufe bakin ta daga gajerar hamma da take yi akai-akai saboda bacci da ya fara cin ƙarfin ta ,
Ita bata kaiwa dare sosai take yin bacci a yawancin lokuta ƙarfe takwas da rabi na dare sun yi bacci ita da Mama , shiyasa yau da hajja ta buƙaci son suyi magana ta zo kuma ta tadda ta tana shafa’i da wutiri , bayan ta idar kuma ta ɗora da addu’o’i , duk sai zaman jiran ya gundure ta bacci yake kawo mata samame ,
Falmata , Falmata . Ko kin yi baccin ne ?
Na’am hajja idona biyu .
To taso ki zo nan kusa da ni magana nake so muyi ,
a hankali ta taso ta taho inda take jin tashin muryar hajja ta zauna daga gefen ta bisa dardumar sallah .
Fatima ki nutsu da kyau ki saurareni , da kunnen basira , kin ga wannan tafiyar da za kuyi ke da Mijinki tamkar wata babbar dama ce Allah ya baki da za kiyi ƙoƙari ki dai-daita zaman ku ke da shi , ki ƙarbo martabar ki ta ɗiya mace , cikakkiyar matar aure , ke yanzu ba yarinya ƙanƙanuwa bace ba , da za’a zauna ana yi miki bayani dalla-dallah baƙi da fari akan aure , shekaru biyar ana cikin na shida da yin auren ku , lokaci yayi da yakamata ku kawo ƙarshen wannan zaman kai da ƙafar da kuke yi a tsakanin ku , ku haɗa kai ku rungumi junan ku cikin inuwa da alfarma irin ta aure ,
STORY CONTINUES BELOW
Ke kece mace bance ba ki bada kan ki ba , amma ki yunƙura kiyi hoɓɓasa cikin dabarun ki na ɗiya mace da Allah yayi miki baiwa da su , ki karkato da hankalin mijinki kan ki , tunda jajayen sawun ki , da sauran damar ki , kina kuma tare da makaman yaƙin da zasu taya ki karɓo kambun ki tun kafin damar ki ta kufce miki , futsanci , jin kai , halin ko inkula da miji ba naki bane , yanzu anwuce wannan zamanin , zamani ne muke ciki na tarairayar miji a gatata shi ta yadda za’a masa riƙon tsauri da kufcewa zata masa wahala , kin dai ji na faɗa miki .
turai zaku je , kiyi ƙoƙari ki sau jiki , ki shige masa , ƴan kananun kayan nan da yace ana saka su a can ki sa ya kawo miki su dayawa kullum ki dunga yi masa ado da su , daman ga ki da kyakkyawan jiki…..
Ƙananun kaya fa kika ce hajja ?
Falmata ta katse ta tana yamutsa fuska .
Eh su nace to meye ba mijinki bane ? Wani ma yayi rawa bare ɗan makaɗi ? Cewa nake kowa a garin su yake sawa ? To ke meye laifin ki idan kin yiwa mijinki ado da su ? Ji min rashin wayo .
Ta mula kafin ta cigaba da cewa :
Ƴar rangwaɗa da kisisina irin ta mata dunga yi masa , ki raba kan ki da ƙwalafacin Mama ki fara tunanin hanyoyin da za ki bi ki faranta ran mijinki saboda kin ga dai dai-dai gawargado shi yana nuna miki kulawa ke kece kike ƙin bada haɗin kai , to ki sake zane tun dundumin ki da danshi , shi mijin mace huɗu ne .
Ga ƴan magunguna nan na karɓo miki su musamman a wajen uwar zainaba , ta tabbatar min da ingancin su su ma zasu taimaka miki ƙwarai da aniya .
Anya hajja idanun nawa kuwa magungunan nan zasu min aiki ? Amma dai ba na sawa a ido bane kin san fa a asibiti sun hana ni zuba magani a ido ,2
Mts’ ana raba ki da kiwon awaki kina kyalla ta haihu , wanne maganin ido kuma ?? Wannan maganin gyara tsakanin ku ne ke da mijinki , idan kika daure da shan su suma zasu taka rawar gani wajen karkato miki da hankalin sa .
Ni zan dunga sha ko shi ? Nifa bangane bafa hajja .1
Yo ina kuwa zaki gane ana nuna miki gabas kina bauɗewa yamma , kina girma kina sake shiga daji ., maganin mata ne .
Maganin mata ?
Ta maimaita da sigar tambayar
Eh
hajja ta amsa tana dangwara mata kullin maganin a hannu ,
Karɓi ki sa a cikin akwatin tafiyar taku , da madarar ruwa ko ta gari ake shan su ,
Taɓe baki falmata tayi ,
Tana ciro Envelop daga hijabin ta ,
Hajja ga hotunan Mama din an karɓo ɗazu Baban ta ya bata ta kawo min,
Karɓar envelop ɗin tayi ta zaro ƴan madai-daitan hotunan Mama da aka ɗauketa kwanaki uku da suka wuce da zummar hajja zata tafi da su Maiduguri ta kaiwa mutanen gida su ganta domin rabon su da ganin hoton ta tun tana ƴar shekaru biyu ,
Kai ɗanɗashi hotuna kuwa sun yi kyau kamar a ƙirata ta amsa tar-tar da su , ƴar wayayyar fuskar nan ta fito , ai kin ga hakan yafi a tafi musu da hoton ta su ganta ko dan yadda Rahima da Alhaji suke begen ganin ta .
Murmushi tayi , jin daɗin Hajja ta yabi ‘yarta
Hajja kar ki manta dan Allah da saƙon gaisuwata , ga Baba , Yaya dakta , Rahima , kai kowa da kowa dai hajja , ki miƙa musu gaisuwata tare da fatan alkhairi .
STORY CONTINUES BELOW
Insha Allah kuwa duk zasu ji Falmata , kin dai ji duk abubuwan da na faɗa miki ko ?
Eh duk naji Hajja ,
To ki dai yi amfani da cewa ta , idan Allah ya yarda za ki ga amfanin sa .
To Hajja .
Ƴar dariya Hajja tayi, to Allah shi sa idan kun dawo nayi farin ganin gamdakatar da sabon ango ko kuwa sabuwar ƙawa .
Falmata ta yunƙura ta miƙe tsaye , tana cewa
Aina kenan Hajja ? Ko daga can za’a kawo miki ɗan turawa ? kai kai kai Hajja baki da dama .2
Saƙare Hajja tayi bakinta buɗe , sai kuma ta gallawa Falmata harara .1
Kinci gidan ku da sauyawa zancena launi , ƴar nema ai nasan sarai kina fahimta ta da gangan kike bauɗewa , oho ni dai na faɗa miki kowa rai yayiwa daɗi ai bayan me shi ne .2
tana ƴar dariya ta ƙarasa barin ɗakin , kalaman Hajja na kutsawa cikin tunaninta tana ɗora su a mizanin nazari .
Washegari
Da farar safiya direban da zai kai Hajja Nigeria ya iso , daman da shirin ta tsaf , dan haka babu wani jinkiri aka fito da kayanta aka sanya su cikin mota ,
Tare da rakiyar Biyamuradi , Falmata da Mama suka ƙaraso jikin motar sallamar bankwana suka yi , Hajja ta shige mota direba ya tada motar suka miƙa hanya Mama tana ɗaga mata hannu .
Allah ya kiyaye hanya Hajja ta
Falmata ta furta a sarari tana jin yadda kewar ta ke fara kamata , “sabo tirken wawa ‘,
Muje cikki Fatima kafin zouwar le chauffeur mu tahi I’aéroport .
Hannun ta cikin na Mama wacce take ta zuba surutu suka juya zuwa cikin gida ,
kai tsaye ɗaki ta shige ta zauna a bakin gado , tunaninnika suka yi mata dirar mikiya , kewar ahalinta na kassara duk wani karsashi nata , shekaru biyar ɗin basu zo mata da sauƙi ba , ba kuma sun rageta da kome ba wajen jin ƙauna tare da muradin sake ganin wani jinin ta a duniya bayan Mama ,
duk kuwa da cewa ita ɗin ta kasance daga cikin jajirtattun mutane masu yaƙi da damuwar su, tare da danneta su binne ƙarƙashin ran su , su yunƙura wajen gina rayuwar su a yadda ta zo musu ,
ba domin ƙarfin zuciyarta ba da tuni damuwar halin da ta tsinci kanta ciki sun kaita ƙasa .
A hankali irin nata akwai hangen wani ƙalubale da take yi wanda take hasashen zai iya ɓullowa cikin rayuwar su ita da Mama ,
daga dangin Biyamuradi , wanda har kawo yau da Mama tayi shekaru a duniya da yake dai-dai da shekarun auren su babu wani dangi nasa ɗaya da ya taɓa zuwa wajen su , ya gan su .
Shi kaɗai suka sani , duk kuwa da yana ikirarin cewa yana da iyaye da danginsa makusanta , to ina suke ? Meyasa basu taɓa zuwa inda suke ba ko su su ziyarce su ? Shin menene aboye wanda su basu kai ga sani ba ? Tsakanin ƙarya da gaskiya wa ake yiwa wasan ƴar ɓoye a tsakanin su da dangin sa ? Tabbas akwai lauje cikin naɗi .1
Sai dai koma menene a shirye take tsaf da taryar sa , zata yi kome domin ta bada kariya ga Mama , ƙuɗirinta bazai taɓa sauyawa ba muddin tana numfashi ita zata cigaba da kasancewa garkuwa ga Mama .
Ya jima yana tsaye daga dokin ƙofar yana duban ta , a tsawon zaman su da shi da ita koyaushe yanayi ɗaya yake hangowa a fuskar ta idan bata san da wanzuwar sa ba a guri , “damuwa” tana da damuwa wanda yake danganta damuwar ta ta da kansa .
STORY CONTINUES BELOW
Yana sane da cewa shi da ƴar sa sunyi kutse tare da yin karan-tsaye cikin rayuwar ta , ba kuma tare da suna amfanar mata da kome ba .
Anya yana yi mata Adalci ??
Gyaran murya yayi da ya sa tayi firgit!
Tana gyara zaman hijabin kanta ,
Fatima tasso le chauffeur ya zou .
Jakar kayan su uku babbar ƴan kayan cimaka ne a cikin su da sauran ƙananan tarkacen matafiya , ƙananan biyun suturun su ne a ciki .
A shirye suke tsaf , Falmata tana sanye da doguwar riga ruwan sararin samaniya me ɗan nawi ta ɗaura mayafin rigar akan ta ( tayi ɗankwali da shi ) da ɗan madaidaicin hijabin ta , takalman kafafun ta marasa tudu sun shiga da hijabin ta kalar ruwan hoda me haske ( baby pink )
Mama anshirya ta cikin ƴar riga iya guiwar ta da dogon wondo kanta rufe da hular saƙa me nawi mahaɗin safar ƙafar ta dake sanye da rufaffun takalman yara .
Biyamuradi ya riƙo hannunta da shima yake shirye cikin shigar kwat da wando ( suit ) ruwan ƙasa , ita kuma ta riƙe ƴan ƴatsun Falmata , sun sanyata a tsakiyar su suka fito farfajiyar gidan , Biyamuradi ya kulle ƙofofin gidan bayan ya kashe duk wasu na’urori masu amfani da lantarki .
tazarar ba wata me yawa bace tsakanin su da farfajiyar tashin jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa ( Diori Hamani International Airport )
Dan haka cikin ƙanƙanin lokaci suka isa , bayan Bayan bin duk wasu tsare-taren da ya kamata matafiya masu tsallakawa ƙasashen ƙetere suyi tare da zaman jiran dai-daituwar jirgi da ya ɗauke su tsawon awanni uku da rabi ,
Biyamuradi Youssouf tare da Falmata da Mama suka bi sawun takwarorin su masu tafiya zuwa United States of America , a sawu na farko suka taka matakala , kafaɗar sa ta dama ɗauke da Mama wacce ta sarƙafo hannayen ta a jikin wuyan sa , ɗaya hannun nasa ya zare daga cikin na Falmata da tunda suka shigo airport ɗin yake kaffa-kaffa da ita yana riƙe da hannun ta , duk kuwa da yadda take yawan mutsu-mutsu da hannun tana son zamewa amma ya ƙi kulawa bare ya bata dama , ya maida hannun sa bisa ƙugunta tare da matso da ita jikin sa , a hankali yace da ita ,
Fatima ki kulla da kyau ki saurari takun ƙafa ta bissa matakala muke ,
ba tare da ta amsa ba ta gyaɗa kanta , tana jin yadda tsikar jikin ta ke miƙewa .
Cikin jerun kujerun first class suka yi mazauni akan kujerun su masu ɗauke da numbobin su da suke fuskantar juna , sai ɗan teburi a tsakanin su , bayan zaman su ya yunƙura tare da ɗaurawa Falmata seatbelt ɗin ta ya koma ya zauna tare da ɗaurawa Mama nata , bai tsimaya ba ya ɗaura nasa .
A hankali ya kai hannun sa ya kamo hannun Falmata da yake kan teburin gaban su , ya damƙe hannunta guda cikin nasa dai-dai lokacin da zazzaƙar muryar shugabar masu dauke da alhakin kula da walwalar mutanen cikin jirgin “Chief flight Attendant ,” ta karaɗe cikin jirgin ɗauke da sanarwa da take cewa :
“Ladies and gentlemen, this is Rose jackson and I’m your chief flight attendant. On behalf of Captain Mike Abraham and the entire crew, welcome Turkish Airlines flight non-stop service from Niamey Niger Republic to Washington DC United States of America.
Our flight time will be of 9hours and 11minutes. We will be flying at an altitude of feet/meters 5612 miles .
At this time, make sure your seat backs and tray tables are in their full upright position and that your seat belt is correctly fastened. Also, your portable electronic devices must be set to ‘airplane’ mode until an announcement is made upon arrival. Thank you.”
STORY CONTINUES BELOW
Ta sake maimaitawa cikin yaren faransanci .
( Mesdames et messieurs, voici Rose Jackson et moi, votre agent de bord. Au nom du capitaine Mike Abraham et de l’ensemble de l’équipage, accueillez le vol sans escale de Turkish Airlines entre Niamey Niger Republic et Washington DC, États-Unis d’Amérique.
Notre temps de vol sera de 9 heures et 11 minutes. Nous volerons à une altitude de 5612 milles.
À ce stade, assurez-vous que vos dossiers de siège et vos plateaux sont dans leur position verticale maximale et que votre ceinture de sécurité est correctement bouclée. De plus, vos appareils électroniques portables doivent être en mode “avion” jusqu’à ce qu’une annonce soit faite à l’arrivée. Je vous remercie.”)
Girgizan da jirgin ya ɗauka shi yasa ba shiri Falmata ta sake ɗora ɗayan hannun ta akan na Youssouf tana ƙanƙame sa hannayen su suka cure guri guda , kamar yadda zuciyoyin kowannen su ke ƙoƙarin jawo kusanci a tsakani .3
Idanun sa a kafe kan fuskar ta dake bayyana tsoro ɓaro-ɓaro .
Cikin ikon Allah jirgin ya samu dai-daituwa a sararin subahana ya shilla da gudun gaske cikin tafiyar gaibu bisa iska a tsakanin sama da ƙasa .
Nigeria
Tafiyar kwana ɗaya da yini biyu ta sada Hajja da birnin Maiduguri , da la’asar sakaliya motar da ta kawota ta dakata a ƙofar gidan Prof .
Kai tsaye ta sauƙa ta shiga gidan , tarɓa ta musamman ita da direban suka samu daga sabbin ƴan aikin gidan guda biyu tare da Rahima da daman duk ansan da zuwan su .
Bayan magarib ta nemi iznin zuwa gaishe da prof da zuwan su a ɗazu suka tadda shi tare da baƙi , hakan ya sa basu samu ganin sa ba sai yanzu .
Bayan doguwar gaisuwa tare da godiyar da akayi musayar su tsakanin Prof da Hajja , taƙaitatciyar hira suka yi wanda duk rabin ta akan Al’amuran da suka shafi taɓarɓarewar tsaro ne tsakanin Niger ɗin da Nigeria da har kawo yau Ƴan tawayen Boko Haram basu saduda sun bar yin kisan mimmiƙe tare da ɓarnannaki tsakanin ƙanana da ma manyan garuruwan Niger da Nigeria ba .
Sannan kuma har kawo yau gwamanatin ƙasar Nigeria ta gagara kawo ƙarshen hare-haren ƴan kungiyar duk kuwa da cewa cikin ƙasar tushe da MAFARIN kafuwar ƙungiyar da ta jefa Dubunnan rayukan Al’umma cikin HARGITSIN RAYUWA yake .
Shin yaushe ne kome zai kawo ƙarshe ? Yaushe ne abubuwa zasu koma dai-dai ? Yaushe ne za’a ƙira ƙungiyar Boko Haram da shuɗaɗɗan lamari da ya zama tarihi ? Allah Shine Mafi sani .
Hajja ta miƙe ta ƙarasa gaban Prof tana miƙa masa envelop ɗin dake ɗauke da hoton Mama ,
Alhaji ga hoton Amaryar taka ta Niger ka ga yadda ta girma duk da ƙarancin lafiyar ta amma ta miƙe .
STORY CONTINUES BELOW
Miƙa hannu yayi ya karɓa yana dariya , dai-dai da shigowar Doctor Hamza wanda ya dawo daga Masallaci .
To toh Masha Allah , Babu kome ai kowacce cuta Allah yayi maganinta , sai dai idan har sanin ɗan Adam bai kai ga gano maganin ba .
Ƙwarai maganar ka dutse Alhaji .
Cewar Hajja .
ya zaro hoton yana gyara zaman gilashin idanun sa , bayan sun haɗa baki wajen amsa sallamar Doctor Hamza ,
ka ga Babban Likita , Likita bokan turai , ƙarshen ƙwaƙƙwafi da bincike sai likita , lalle tafiyata bana me sa’a ce tunda naci karo da kai , shekaru fiye da biyar rabona da na ganka .
Murmushi yayi yana zama daga gefen ƙafafun Prof .
Hajja sannun ki da zuwa , da fatan kin samu isowa lafiya ?
Lafiya ƙalau Likita ,yaya bayan rabuwa ? Ya iyalin naka ?
Duk kowa lafiya hajja .
To Alhamdulillah .
Masha Allah wannan Amarya tawa ai tafi kama da ƴaƴan nasara , ga dukkanin Alamu tana da wayo .
Prof ya furta haka yana mayar da hotunan cikin envelop ɗin .
Wayo kuwa na sosai Alhaji ai Mama sai godiyar Allah ba shakka tana da kaifin ƙwaƙwalwa da saurin ɗaukar abu
Allah shi rayata , ya bata lafiya , yayi Albarka cikin rayuwarta ita da sauran yaran musulmai baki ɗaya !
Ameen Ameen Alhaji
Hajja ta amsa tana sanya hannuwanta biyu ta karɓi envelop ɗin da yake maida mata , ta miƙe tana yi musu bankwana tare da barin falon ta koma cikin gida .
Baba , wacce yarinya ce hajja ta kawo maka hoton ta ?
Doctor Hamza ya tambayi Prof .
Ya buɗe baki da zummar bashi amsa shigowar ɗaya daga cikin dattijan unguwar da suke cin abincin dare tare da Prof ya katse musu hirar .
Abuja
Yakaka ce a zaune kan hannun kujerar falon Malama Maryam gabanta kuwa babbar jakar kaya ce da take shaƙare taf da kaya , daga gefen ƙafafunta ma wata ƴar matsakaiciyar jakar ce .
tana shirye tsaf cikin dogon hijabinta da yake har kusa da idon sawun ta , fuskar ta fayau babu ko kwalli , ramar da tayi ta fito sosai akan fuskar ta da idanunta da suka ɗan zurma ciki .
daga gefe a cikin falon Lubna ce a zaune tayi jugum tana kallon Yakaka wacce idanun ta ke kallon ƙasa , tayi shiru tamkar ba sune masu yin dararraki ba muddin suna waje guda .
Malama Maryam ce ta fito itama shirye take , ta kai dubanta ga Yakaka tana jin yadda tausayin ta ke sake narkar da ranta tabbas Yakaka tana buƙatar majiɓanci cikin Rayuwar ta .
Yakaka tashi mu tafi , lubna taya ta ɗauko kayan ku kai cikin mota Abban ku yana jiran mu , kar mu rasa motar farko ko ta biyu , saboda mu samu isa da wuri tafiya daga Abuja zuwa Maiduguri da tazara gara muyi sammako .
Jikin Lubna babu kuzari ta miƙe tana gyara zaman hijabin jikinta ta sunkuya ta ɗau ƙaramar jakar tare da kama gefen babbar ta taya Yakaka riƙewa ,
STORY CONTINUES BELOW
Sun zo tsakar gida Lubna ta jaa ta tsaya da hakan ya sa Yakaka waigowa .
idanunta cike taf da ƙwalla tace
Sahiba irin rabuwar da zamuyi kenan babu bankwana ? Shekaru biyar ba kwana biyar bane Sahiba ban so ba zaki tafi tare da maɗaukakiyar damuwa .
ɗan guntun murmushi Yakaka tayi ,
Sahiba kin san har abada kina cikin mutanen da bazan iya mantawa da su ba cikin rayuwata , cikin kowanne irin hali na tsinci kaina , nima zanyi kewar ki Lubna , ta ƙarasa zancen siririyar ƙwallar da bata shirya zubowar ta ba na sauƙa bisa ƙuncin ta .
Idan kika tafi a yanzu waye zata maye min gurbin ki ? Waye zata zama babbar ƙawata a bikina ? Da ke muka tsara kome Yakaka .
Idan Allah ya yarda zan dawo Lubna , zan halarci bikin ki na ɗau Alƙawari , amma dole na tafi a yau shekaru biyar Falmata tayi cikin rashina ,
Hon ɗin da aka matsa da ƙarfi shi yasa suka fara taku cikin hanzari ba tare da sun sake musayar wata kalma ba a tsakanin su .
Ƙarfe takwas da rabi na safe motar da su Yakaka tare da Malama Maryam suka shiga domin tafiya Maiduguri ta ɗau hanya ɗoɗar .
Tafiya ce me nisa ta tsawon fiye da awanni takwas tsakanin Babban birnin tarayya Abuja da Birnin Maiduguri dan haka a saboda yawan tsaye-tsaye akan hanya daga jami’an kula da hanya da suke gudanar da bincike , ya sa dare ya fara shiga har ƙarfe shida na yammaci ta gota , wanda hakan kuma ya sa dole su yada zango a garin Damaturu saboda lokacin dokar hana zirga-zirgan motoci ya shiga ( curfew) ala tilas suka kwana a tasha ,
Washegari da hantsi ƙarfe tara suka shiga garin Maiduguri , a idanun Yakaka babu wani sauyi da garin ya samu tsawon shekaru biyar ɗin ko kuwa dan hankalinta bashi kan duban yanayin garin ne ? Baki ɗaya ta ƙagauta ta ɗora idanunta akan ƙanwarta da ƴar ta .
Tsawon lokacin rabuwar ta da garin bai sa ta manta da sunan unguwar da ta bar Falmata ba , dan haka bayan sauƙar su a tasha kai tsaye ta shaidawa direban taxi da ya ɗaukesu da kayan su unguwar da zai kai su .
tafiyar mintoci 15 kachal ta sada su da unguwar , layi bayan layi ta kwatantawa direban har zuwa gaban gidan da a koyaushe yake yawan samun gyaran da yake sake fiddo kyaun tsarin ginin dai-dai da na zamani .
Bayan sun sauƙe kayan su a gefen hanya daga jikin katangar gidan Yakaka tace ga Malama Maryam
Ummi bari na shiga na nema mana iznin shiga da kayan mu .
To Yakaka .
taku ta fara yi tana jin yadda zuciyarta ke bugu da fargabar da ta rasa takamaimai dalilin samuwarta daga ƙasan ran ta ,
ta kawo kusa da ƙofar gidan aka buɗo Babbar ƙofar ya danno hancin motar sa yana ƙoƙarin fitowa … !!!!Doctor hamza ba tare da ya dubi sashin da Yakaka take tsaye ba yayi wucewar sa yana waya da ɗaya daga cikin abokan aikin sa na nan Asibitin Maiduguri wanda ya masa ƙiran gaugawa sakamakon neman sa da ake a asibitin jahar saboda wani aiki na gaugawa da za’a yiwa wata mata da take halin buƙatar taimako ,+
Kan ta a ƙasa tana satar kallon gefen fuskar sa , zuciyar ta cike taf da addu’o’i iri-iri , ta wuce ta ƙarasa wajen maigadi wanda ya tattara dukkanin hankalin sa akan ta ,

Sama-sama ya amsa gaisuwar ta ya ɗora da tambayar ta wajen wa ta zo ?
Wajen Rahima na zo .
tace da shi tana fatan kar ya hana ta shiga gidan saboda wannan maigadin baƙon fuska ne ba wanda ta sani a da ba ne
Kallon tsanaki yayi mata bai hango wani alamun rashin gaskiya a tattare da ita ba ,
Ki shiga tana ciki .
Yace yana komawa kan ɗan bencin sa na zama .
Hamdala tayi bayan ta yi masa godiya ta taka tana nufar cikin gidan da bai zamto baƙo ba a gareta , tsarin sa bai sauya ba illa zuciyar ta da take cike da taraddadin hasashen da irin fuskar da Mutanen gidan zasu ƙarbe ta da hakan ya hana ta kuzarin isa cikin gidan cikin ƙanƙanin lokaci
Da duk takun ta guda kunnuwan ta suke sake kusanto mata tashin muryar ta suke,
da bata riga ta manta amonta ba ko dan ita ɗin tana daga cikin mutanen da suka gwada mata ƙauna a duniyar ta ne ?
Hajja dan dai kince kin manta fuskar maman ta ne amma idanunta sak na mamar ta ne , sosai tana ɗibar yanayi da mamarta sai dai ko kamannin Baban ta yafi ƙarfi ,
ai babyn nan ƙarshe ce a kyau wallahi kamar naje Niger na kwato ta nake ji , Allah sarki baby na Allah dai ya baki lafiya , yasa a dace wajen neman maganin nan , Allah kuma ya jiƙan Mamar ki me kirkin nan .
Da murmushi hajja ta amsa da Amin Amin Rahimatu
A hankali ta sauƙe idanun ta a bayan Rahima lokacin da ta ƙaraso ƙofar falon , wacce ta juya baya tana ƙoƙarin saƙala tangamemen hoton Mama cikin jerin hotunan da suke killace a jikin bangon inda aka tanadi sashi na musamman domin ajiyar hotuna ,
Ɗaya daga cikin hotunan da hajja ta zo da su ne da ta kai aka wanke mata shi zuwa Babban takardan hoto aka yi mata gidan sanya hoto na musamman tare da sanya shi a cikin gilashi .
Ganin ta ta mika kan hoton , fuskar da ta gani jikin hoton ya sauya bugun zuciyar ta nan take , a hankali take wara idanun ta tamkar wacce ta warke daga makanta , kamar yadda take jin zuciyar ta tana buɗewa da wani irin yanayi ƙaƙƙarfa , ƙofofin gashin jikinta baki ɗaya suka buɗe suna tsattsafo da gumi ,
Taku ta fara yi tana ƙara kusantar hoton da zuciya da tunaninta baki ɗaya suka tafi ga fuskar dake jikin sa.
Haƙiƙa bata taɓa ganin ta ba amma kusancin dake tsakanin uwa , mahaifiya da abunda ta haifa daga cikin jikinta ya wuce wasa ya kuma wuce hankalin duk wani me tunani ƙauna ce me rassa da take yaɗo a dunƙule da babu me iya ganin zurfn ta bare a iya hasaso iyakar ta ,
Bayan Rahima ta zo daf ta tsaya tana sake nutsar da idanun ta akan fuskar mama wacce tayi ƴar kyakkyawar dariya a hoton.
Hajja wacce ta miƙe tsaye daga gefe tayi sororo tana bin Yakaka da ido kafin tace
Ke , Ke , Ke baiwar Allah lafiya kike kuwa ? Zaki shigo mana gida haka sangam-sangam babu sallama bare neman izni ? Kin kuma zo kin yi tsaye ƙere-re uwa wacce ta haɗiyi taɓarya ince ko baki da lafiya ne ?3
STORY CONTINUES BELOW
Rahima wacce bata ji tsayuwar Yakaka kusa da ita ba , saboda raggon taku marar sauti da Yakaka tayi a yayin isowa wajen , ta ɗan waiga sashin hajja lokacin da take gama sarƙafe hoton a inda ya dace tare da janye hannun ta daga jikin hoton ta waigo tana cewa
Hajja da wa kike magana ne ?
Fuskar ta ce ta kusan haɗuwa da ta Yakaka da ya sa ta ɗan jaa baya
Bismillahi waye ha…
Kalmomin ta ta haɗiye muƙut , maƙwallon maƙogoron ta ya motsa kamar yadda idanun ta suka firfito da mabayyanin firgici baro-baro a cikin su ,
Shekarun da suka raba haɗuwar fuskokin su basu yi yawan da zasu sa su mance da kamannin juna ba .
Ya-Ya-Yakaka ke-ke kece ??
Rahima ta furta muryar ta tana makyarkyata kamar yadda kwakwalwarta take hautsinewa da kokonto ,
Yakaka wacce zuciyar ta ta zaƙu da son samun tabbaci akan gudan jinin ta , ba tare da ta janye idanun ta daga kan hoton ba ta lalubo hannuwan Rahima ta damƙo su da ƙarfi ,
Rahima, Rahima ni ce ,
Ta zarce da tambayar ta
wannan ,? wannan Mama ce ? Ƴa ta Mama ?
Rahima wacce tunanin ta ya gama dunƙuluwa waje guda , ta fisge hannuwan ta da matuƙar ƙarfi bata tsaya ba ta taka da gudun gaske tana nufar ƙofa , kafin ta ƙarasa ficewa ta ɗaga murya tana sanar da Hajja .
Hajja ki gudu wallahi Fatalwar Maman Mama ce wannan .11
Turus hajja tayi tana bin bayan Rahima da kallo , kafin ta sake waigo Yakaka wacce bata bi ta kan kalaman Rahima ba tamkar ma dai bata kai ga fahimtar me kalaman Rahima ke nufi ba .
Ta saka hannu ta ɗago Hoton ta ciro shi daga mazaunin sa , tare da riƙe shi da hannuwan ta duk biyu , tamkar ta riƙe yar jaririyar ta .
Kai tsaye ta nufo Hajja da hoton , fuskar ta da wani irin yanayi na chakuɗuwar tsantsar farinciki da kuma fargaba tace
Wannan ƴata ce ko ? Mama ce ko ?
Kafin ta ƙaraso hajja ta juya da ƴar sassarfa tana ɗingisa kafafun ta da basu cika lafiya ba ,2
Un-un-un ƴar nan , ni kuwa ina zan sani ?
Mutum dai baya ƙin ta Mutane wai ance da ɓarawo ya gudu , Bi Rahima can dai kin tambaye ta Dan Allah .1
Garam !
Hajja ta rufo ƙofar ɗakin ta .1
Saƙare tayi a tsaye tana son harhaɗa tunanin ta domin ta kai ga fahimtar meyasa ta ga kamar ana gudun ta ? Ashe girman laifin ta har ya kai ya sa ta zama abun gudu a wajen mutane ?
Falmata ina Falmata ? Ta san idan kowa zai guje ta a duniya a zare Falmata a cikin su , Falmata baza ta taɓa gudun ta ba , ina take ?3
Ta juyo da nufin fitowa ta nufi sashin Baba , sai ga Rahima tare da wani mutum wanda bata kai ga sanin sa ba .
Mallam Kabir ga ta nan , ta nuno Yakaka wacce take tsaye ƙiƙam rungume da hoto .
Dan Allah kana ganin ta ?
Ina ganin ta mana Hajiya Rahima , ai wannan Mutum ce , ba Fatalwa ba , hala an samu akasi ne wajen jin wani labari akan ta ?
Ke baiwar Allah wacece ke ? Daga ina kike ? Me kuma kika zo yi nan?
Zuwa lokacin Yakaka ta fara hasaso abunda yake faruwa , dan haka fuskar ta na bayyana sabon alhini ta matso tana cewa .
Rahima ni ce Yakaka , ba Fatalwa ba ce ni , ban mutu ba , waye yace na Mutu ???? Ina Falmata ?2
STORY CONTINUES BELOW
Ba tare da Rahima ta ce ƙala ba , bata kuma yadda ta ƙarasa kusa da Yakaka ba ta sake juyawa da ɗan gudu ta nufi sashin Baba , da daman daga can ɗin take shine ma ya haɗo ta da Mallam kabir ɗin da ta zo ta same su tare suna ganawa ,
Tana cikin yiwa Baba bayanin dawowar Yakaka ƴar gudun hijira wanda suke da tabbacin mutuwar ta a wajen haihuwa shekaru kusan shidda da suka wuce ,
Sai ga Mallam kabir tare da Yakaka wacce take biye da shi .
Da ido Baba ya bisu bayan ya amsa sallamar su , har suka ƙaraso cikin falon inda Yakaka ta nemi waje daga can gefe guda ta durƙusa bisa guiwowin ta ,
Mallam kabir bai zauna ba yayi bankwana da prof tare da juyawa kan takun sa ya bar wajen .
Prof bai yiwa kamannin Yakaka sani na sosai ba amma tabbas ya shaida fuskar ta , saboda ya taɓa ganin ta a farkon zuwan ta gidan sa , sannan a ɗan taƙaitatcen zaman da tayi a gidan tana zuwa gaishe shi lokaci-lokaci .
Babu alamun firgici a tare da shi yake amsa gaisuwar Yakaka , wacce kan ta ke a sunkuye .5
Cikin nutsuwa irin ta manyan mutane da suke da tarin ilmi ya soma da tambayar Yakaka daga ina take ? Me kuma ya faru da ita tsawon shekarun da tayi bata nan ? Bai shigo mata da batun labarin mutuwar ta da yake tabbatacen Al’amari ba a wajen su a tsawon shekarun da tayi bata nan .
Tambayoyin sa suka fargar da Yakaka tare da tuno mata da Malama Maryam da ta baro can a layi fiye da mintoci ishirin ,
Wacce ta san zata taya ta fuskantar mutanen ta da tarin laifukan da suke kan ta ,
Tare muke da baƙuwa Baba , a min iznin na shigo da ita .
Je ki shigo da ita babu kome .
Bata jima ba suka dawo da tare da Malama Maryam wacce har ta fara shiga halin damuwa ganin lokaci ya ɗan jaa batare da ta ga dawowar Yakaka ba .
Cikin nutsuwa da kamalar da Allah ya hore mata Malama Maryam ta gaishe da prof , sannan ta gabatar da kan ta a matsayin Malamar Yakaka wacce ta ɗau darasi a wajen ta tsawon shekaru biyar da ɗoriyar watanni , a garin Abuja , daga haka ta tsagaita .
A hankali muryar Yakaka ta fara tashi tiryan-tiryan take bada labari tun daga irin Gadar zaren da Samy baby ta haɗa mata har kawo ranar barin ta Maiduguri da ta sanyata ta tsallake ta bar Jaririyar ta a ranar da ta haife ta , da zummar zata kai ta Abuja wajen mahaifn ƴar ta suyi aure ta dawo ta ɗau yar da ƙanwar ta .
Wacece ita Matar da kika bi ? Menene dangantar ku da ita ?
Tambayar Prof ta katse Yakaka .
Shiru Yakaka tayi na ɗan wani lokaci , tunowa da tayi da irin rufin asirin da Doctor Hamza ya yi mata a farkon kawo ta gidan ya bayyana ta a matsayin ƴar gudun hijirar da mijinta ya mutu ya bar ta da ciki ,
Ƙaramin tunani irin nata tare da mummunar ƙaddara suka sa ta sanya ƙafafu ta hamɓarar da irin tarin rufin asirin da Allah ya yi mata a tun wancen lokacin da hakan ya jawo a yau ita da kanta zata tona binnannen sirrin nata .
Domin a yanzu ta ɗau alƙawarin baza ta sake yin ƙarya ba , dan haka idanun ta na tara ƙwallar nadama da irin laifin da ta aikata ta koma baya , kan haƙiƙanin gaskiya ta ɗorar da labarin ta tun daga farkon shigowar su birnin Maiduguri zaman su a sansanin su, da zaman da suka yi a gidan Madam saly , shigowar Biyamuradi rayuwar ta wanda ta ambace shi da “sojan wata ƙasa ,” har zuwa zaman ta a Abuja tare da dawowar ta a yau bata boye duk wasu gaskiyar da yakamata ta bayyana su ba ga mutumin da shine na farko da suka samu mafaka mai cike da karamci da tarin ƙauna a ƙarƙashin sa ,
Shiru ne ya gifta na tsawon wasu mintoci , da hakan ya bada dama ga malama Maryam ta ɗora da sake bada kyakkyawar shaida ga Yakaka , yadda ta jajirce wajen neman ilmi haɗi da yadda ta cije tare da taimakon Allah ta hayewa faɗawa ga rayuwar karuwanci kamar yadda ita samy baby ta so da ta aikata .
STORY CONTINUES BELOW
Mamakin mazajen guda biyu shi yafi kome yin tasiri a tunanin Prof, da har ta kai shi ga gaza cewa wani abu .
A zahiri yau ta bayyana a gareshi cewa daga Ɗan sa Hamza har shi wancen mutumin da ya zo har nan gurin sa ya ƙarbi auren ƴa a wajen sa duk ƙarya suka wanzu tsawon lokaci suna gindaya masa akan rayuwar marayun yaran su biyu .
Wanda a zahiri ƙaryar ta su ta cutar matuƙa gaya , ba su kuma kyauta ba .
Ƙaryar da Hamza yayi ita ta tokare ta hana shi yayi yunƙurin nemo yarinyar ya dawo da ita ta zauna ƙarƙashin kulawar sa kamar yadda a tun ranar da ya karɓe su ya alƙawartawa kan sa , wanda hakan ba wani abu ne me wahala ba kasantuwar sa babban Mutum , amma sai hamza yayi masa ƙarya cewa ta mutu har ma yayi jana’izar ta a asibiti , wanda a zahiri tun lokacin shi Hamza yana da masaniyar guduwa tayi , ko me yasa yayi hakan oho !
Sai kuma shi wancen mutumin Niger da ya riga ya san irin mummunan ta’asar da ya aikata na lalata tarbiyar yarinyar nan , amma kuma shine ya sake dawowa ya rufe shi a baibai tare da karɓe ɗiyar sa domin sake samun garaɓasa har aka ƙara masa da ƙanwar ta a matsayin mata duk a tafarkin ƙarya ??
Wannan wane irin son zuciya ne ? Meyasa ne gaskiya tayi ƙaranci ? Shin ƴan gudun hijara ba ‘ya’ya bane ba ? Ba mutane ne masu ƴanci da galihu irin na sauran Al’umma ba ? Da rayuwar su zata zam ba a bakin kome ba ? Za kuma a dunga yin walagigi da su cikin rashin kulawa da tozartawa , a maishe su ba a bakin kome ba , shin zaɓin su ne rabuwa da iyayen su , dangin su , garuruwan su ? Ko kuwa ƙaddara makamanciyar wannan bata iya faɗawa kan kowa ne ?1
Idan har ya tabbatar da duk labaran da suka bayyana a gare shi gaskiya ne , babu shakka zai yi tsayuwar daka cikin rayuwar ƴan gudun hijirar nan guda biyu , zai zama katanga tsakanin su da duk masu shirin tozarta su a sannu kuma zai ɗau hukuncin da ya dace akan Hamza da ɗan mutan Niger .
Muryar Malama Maryam ita ta sanya shi nisawa , ya maida ganin sa kan ta .
Baba ayiwa Yakaka hakuri a yafe mata babu shakka tayi laifi tare da zallar wauta amma domin Allah a ɗau hakan a matsayin kaddara a cigaba da godewa Allah da ya sa har ta dawo gida lafiya ba tare da wani mummunan lamari ya auku gareta ba ,
Babu kome baiwar Allah mun gode ƙwarai Allah ya saka miki da Alheri kan yadda kika kula da ita , kema Allah ya duba miki naki iyali , Allah ya ƙara mana yawaitar irin ku cikin Al’umma masu taimako domin Allah .2
Cikin jin daɗi Malama Maryam ta amsa da Ameen .
Ƴar boyayyar Ajiyar zuciya Yakaka ta sauƙe ganin yadda Alamu ke bayyanuwa yadda take zaton tsanantar lamarin nata duk bai kai haka ba ,
A hankali ta ɗora idanun ta kan Rahima wacce ita ma kallon ta take , suka haɗa ido kafin Rahimar tayi mata guntun murmushi marar sauti .
A yanzu hankalin ta ya kwanta ta kuma amince Yakaka ce da gaske ba Fatalwa ba .
Ita ma ta mayar mata da martanin Murmushin , ƙaunar junan su tamkar a jinin su take , duk da tarin abubuwan ƙi da Rahima ta san yakaka ta aikata su a yanzu , hakan bai sa ta ji kamar ta tsane ta ba .
Kalaman Prof ya sa Yakaka sake nutsuwa ta mayar da hankalin ta kan shi ,
Bisa ga doron kuskuren da kika riga kika aikata su Abubuwa biyu zuwa uku sun faru ,
Na farko labarin mutuwar ki , a gare mu tuntuni kin mutu tundaga ranar da kika gudu kika bar ‘yar ki .
Na biyu shine zuwan da mutumin da ya ƙira kan sa mijin ki uban abunda kika haifa yayi ,
Na ukun su shine tafiyar sa da yayi da ‘yar sa tare da auren ƙanwar ki a lokaci guda da ni da kaina nayi waliccin auren a nan falon nan na bada auren ƙanwar ki Fatima ga mijin ta uban ‘yar ki na kuma ɗanka masa ita suka tafi tare ƙasar su niger tare da rikiyar Hajja me wurya .
STORY CONTINUES BELOW
Da ace Yakaka ta taɓa sanin yadda ciwon Ajali yake da babu shakka zata iya cewa shine ya dirar mata a lokacin saboda wani irin abu me kaifi da ta ji ya taso mata daga ƙasan mara ya zo ƙirjin ta ya tokare ta ,3
Muryar ta a shiɗe ta wufto kalaman da suke kan harshen ta ta watso su ga Prof idanun ta tsaye ƙem a kan fuskar sa
Falmata ce tayi aure da Baban Mama ?
Da sake tabbatarwa Prof ya amsa mata da
Haka kalamaina ke nufi.
Abunda take jin ne ya watsu a cikin jikinta ya barbazu tamkar an watsa mata wuta kafin ya sake dunƙulewa a maƙogoran ta ya tsaya ,
Yaa Allah , Yaa Allah , Allah na tuba kar laifin da na aikata ya shafi Falmata , Allah ka dawo min da Falmata , Allah ka…
Mul-mulan hawayen da suka fara ƙwaranyowa daga idanun ta tare da fashewar ƙullutun da yake wuyan ta shi ya hana ta cigaba da magana illa kukan da ta fashe da shi marar ƙarfin sauti ,
Kuka ne irin na mutumin da ya ke a halin ɗimuwa tare da nadama kuka ne irin na ba yadda zan yi , kukan neman taimako ,
Baki ɗayan su irin kukan da take ya taɓa zukatan su ,
Musamman Malama Maryam da Rahima ,
A bangaren Prof duk da cewa ya ji tausayin ta amma ya bar ta da hakan a matsayin sakamakon laifin da ta aikata .2
A hankali Rahima ta ƙarasa inda take ta sanya hannu ta dafa ta ,
Kiyi hakuri Yakaka tashi mu shiga cikin gida , ki bar kuka hakan ,
Miƙewa tayi ta fara taku ba tare da ta cewa kowa kome ba ta wuce ,
Malama Maryam ta rissina ta yiwa Prof sallama tare da shaida masa gobe da sassafe zata kama hanyar komawa gida
Godiya ya sake yi mata , suka rabu suna bin juna da kalaman fatan alheri .
Bayan fitar su bai jinkirta ba ya ɗau wayar sa ya nemo lambobin wayar Doctor Hamza ,
Fitowar sa kenan daga ICU inda ya jonawa marar lafiyar da aka ƙira shi domin ita wasu na’urai ya kuma sake duba ta sosai kasancewar ya ƙware sosai wajen gano tare da bada taimako akan cutar da take damun ta na dajin bakin mahaifa ,
Mutanen da suke ƴan uwa ga marar lafiyar suka taso caa su kusan rai shidda suna tambayar sa yanayin jikin nata ,
Nan dai ya kwantar musu da hankali tare da sanar musu da insha Allah zasu yi bakin ƙoƙarin su, su kuma su taya su da addu’a ya ratsa su ya wuce ,
Ya ji lokacin da ɗaya daga cikin su tace tunda mun ji yanayin da take ciki sai Maman Bulama ta koma gida ta yi girki ta kawo kuma ta haɗo wasu kayan da za’a iya buƙata ,4
Maa ki mata bayani yadda zata gane sosai dan ke ce kika iya maganar su ta kurame ,7
Da hannu suka yafito wata mata wacce take zaune a ƙasa daga gefe .
Da sauri ta taso ta ɗan russuna daga gefe ,
Maa tayi mata bayani da hannu cikin maganar kurame ,
Cikin sauri take gyaɗa kai alamun tana fahimta,
Naira ɗari biyu ta zaro daga jaka ta miƙa mata , ta sanya hanu biyu ta karɓa ,
Ta mata alamar cewa kuɗin mota ne
Ita ma ta gyaɗa kai kan cewa ta gane
Har ta juya ta sake dawowa ,
Tayi musu alamar tambaya tana nuna ɗakin da marar lafiyar ke ciki . Fuskar ta na bayyana Alhini .11
Amsa maa ta bata da hannu .
STORY CONTINUES BELOW
Ta juya ta kama hanyar barin asibitin ,
Doctor hamza wanda ya gama amsa wayar prof da yake sanar da shi kan lalle ya zo yana son ganin sa daga zarar ya kammala abunda yake a asibitin ,
Ya mayar da wayar sa aljihu tare da juyawa da zummar komawa cikin ofishin abokin aikin sa da shi yayi ƙiran sa domin suyi sallama ya kuma gama yi masa bayani akan irin matakin da yakamata a ɗaura marar lafiya akai zuwa gwaje-gwajen da ya dace ayi mata
Ƙiris ya rage ya ci karo da matar da ta taho tana ta sauri ,
sannu Hajiya ,
Yace yana kaucewa yin karon su , a fisge ya dubi fuskar ta lokacin da take gota shi ba tare da ta amsa ban hakurin da yayi mata ba
Cak ! Ya tsaya , lokacin da kamannin ta suka yi masa yanayi da na wata da ya sani waye ?
khaalty Rahima .6
Juyowa yayi da sauri da son sake ganin fuskar ta sosai , sai dai ta riga tayi nisa sai tashin hijabin ta ya ke iya gani wanda ya cika da iska saboda saurin da take zabgawa .6
*****
Daga bakin ƙofar falon Yakaka ta zame ta zauna , tana wani irin kuka ciki-ciki , a halin da take jin zuciyar ta a ciki babu abunda take fata irin kome da ta ji ace a mafarki ne , bacci take yi ta yi wannan mummunan mafarkin , ta gwammaci ace ta buɗi ido ta ga kan ta a gidan samy baby , kai ta amince kome ya faru da ita , da dai dawowar ta Maiduguri ta tarar da wannan mummunan labarin da ya kassara duk wani guntun ɗoki da mararin sake ganin wani nata a duniya ,3
Aure , wai Aure da Falmata da mutumin da ya yaudare ta ya cutar da ita , ya lalata mata rayuwa tare da bar mata taɓon da har abada ba zai gogu ba , ?6
To wai ma ina ya tafi mata da ƙanwar ta ? Kamar ta ji prof yace ya tafi da ita Ina ya kai ta ? Mutumin da ya saba yin manyan ƙarya da yaudara irin haka kome ma zai iya yi , ina suke ? Kai zata iya barin kome ya wuce ya zama ba kome ba amma banda zaman Falmata tare da wannan mayaudarin domin shi ɗin ai guba ne, dafin sa kuma ya fi na maja-ciki in yai sara .
Ɗaga sautin kukan ta tayi tunowa da ta yi da miskinancin ƙanwar ta , Wanne irin hali ta kasance a ciki lokacin da labarin mutuwar da aka ce tayi ya riske ta ? Wataƙila tundaga lokacin bata sake farin-ciki ba , yaya rayuwa ta kasance mata bayan bata nan ? Wanne irin zama take da wannan macucin mayaudarin ?
ƙwarai ta gaza a wajen bada kariya ga Falmata maimakon haka ma ta zama sila na faɗawar ta a hatsari , ƙwarai hatsari mana aure da mutumin da ba’a kai ga sanin asalin sa na haƙiƙa ba ,
A hankali Hajja ta murɗa makulli ta fito daga ɗakin da ta shige ” jin tashin muryoyin su Rahima da Malama Maryam da suke faman rarrashin Yakaka , da sautin kukan ta ya karaɗe falon
Oh ni Hauwa’u naga ta kaina ! yanzu ke ‘yar nan me ya miki zafi haka a duniyar nan da zaki zo ki faɗi a nan shakwaɓ , kina rusa ihu ya Amaryar da Angon ta ya mutu daren buɗan kai ?
Ganin babu wanda ya kula ta ya sa ta samu waje ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon , ta cigaba da cewa ,
Rahimatu , ince ko dai an fitar da Fatalwar ? Kar sai mutum yana ƙailula ya farka ya gan ta daf da kan sa .1
Hajja dagaske Yayar Falmata ce ta dawo , Mamar Mama ashe bata mutu ba Hajja ki taya mu Murna ,
A kaikace ta dube su tana daga inda take zaune , ta gyaɗa kai .
STORY CONTINUES BELOW
Toh , ah lalle kun kaima Barka , ‘Yar nan sannu da bayyana , kuma tsawon lokacin nan da kika shafe bakya nan dandi kike ko kuwa Da’awa ? oh duniya me abun mamaki .3
Malama Maryam da take zaton Hajja ƴar uwa ce ga su Yakaka jin abunda Hajja tace ya sa tayi saurin amsawa a ƙoƙarin ta na son ganin ta wanke Yakaka tace ,
Hajiya , Yakaka yarinyar kirki ce tsawon shekarun nan ta yi su ne wajen neman ilmi , bata aikata wasu munanan aiyuka ba .
Ah to babu laifi ilmi ai abun so ne abun nema , shiyasa ma wani mawaƙi ya ƙira jahili da dattijon biri mai ɗan kwale .1
Ita kuwa Falmata ,uwarɗakina duk biyu ta haɗa ga neman ilmi ga bautar ubangiji ,bautar aure , ta zama gizako katafila a gidan Babban soja , Fatima uwar Mama mata a gidan Babban Mutum ,Allah dai ya dawo mana da ku lafiya uwarɗakina .
Chak!
Yakaka ta tsayar da kukan ta , ta miƙe cikin rashin kuzari ta dawo gaban Hajja ta zauna ,
Dan Allah ki bani labarin Falmata tare da Mama , ki faɗa min a wanne hali suke ciki ? Waye yake kula da Falmata a halin Larurar ta ? Kince Falmata ta shiga makaranta ? Ta koyi karatun addini ?
Ta ƙasan ido hajja take duban Yakaka ,
Falmata da Mama suna nan sumul-luwai ƙalau , ƙarƙashin kulawar jigon da ya tallafi rayuwar su , sai girma suke yi suna bunƙasa , karatu arabi da boko kullum cikin yin sa suke , yanzu haka ma yau kwanakin su shidda da tafiya ƙasar Amurka can turai ince ko kina jin sunan ƙasar ?1
Hawayen dake fuskar ta basu bushe ba ta kamar yadda bata janye rinannun idanun ta daga kan fuskar Hajja ba , tace
Falmata bata kasance ba cikin damuwa ? Bata shan wahalar kome , babu me zaluntar ta ko cin zarafin ta ?
Buɗe baki Hajja tayi da sigar mamaki
Ah kinji min kiɗifi ? To wa kuwa zai zalince ta tana tare da mijinta adali gamjigo , wacce damuwa zata kasance a ciki bayan yana kyautayin ta tare da kyautatawa , ke ‘yar nan raba mu da mugun fata ,
Ɗan karyar da kai Yakaka tayi fuskar ta ta ɗan washe kaɗan daga damuwar da take bayyane ,
Falmata ta girma sosai ko Hajja ?
Ɗan tsinken tsintsiyar da hajja ta ɗauka a ƙasa ta kai bakin ta tana saƙace hakori ,
Idan kika ce girma ma ai kin ɓata bakin ki , ta cika tayi fam , ɓul-ɓul da ita kamar kazar gidan gona , ta fiki kome-da-kome , ‘yar nan hutun gidan miji fa aka ce miki ?11
Ƴar ajiyar zuciya Yakaka ta sauƙe tana Miƙewa tsaye , kaso biyar cikin ɗari na daga halin da ta tsinci kan ta ciki ya sauƙa ,duk da cewa baƙin-cikin da yayi mata tsaye a rai yana nan bai gusa ba amma jin lafiyar su ya rage mata matsananciyar damuwar da ta tsincin kan ta a ciki dalilin rashin ganin su ,
Rahima ki ba mu masauƙi ni da Ummi .
Ta furta hakan tana ɗora ganin ta ga Rahima ,
To Yakaka Bismillah ku shigo .
Da kallo Hajja ta bi su tana nazari , duk da cewa ta ji daɗin dawowar Yakaka cikin ran ta , amma bata so zuwan nata a dai-dai wannan lokacin ba domin ko kusa Allah ya sani baza ta so rabuwar Falmata da Youssouf ba wanda ita Hajja ta riga ta san ko wanene Youssouf Abdul-azizou Baskore ,
STORY CONTINUES BELOW
ta san matsayin sa na Yarima ɗan sarki da kasancewar sa Babban soja. Ta san abubuwa masu ɗan yawa akan sa wanda tsawon lokaci ta ɗauka tana bincike a kan sa sannu-sannu batare da shi kan sa ya sani ba , ta kuma cigaba da taya shi boye ko shi wanene agare su ita da Falmata duk da cewa ita ta sani , abunda take da yaƙini akan sa shine rana na nan zuwa da zai bayyana kan sa da kan sa .2
A ganin ta Youssouf yafi dacewa da Falmata , sannan muddin aka raba auren su a wannan gaɓar an cutar da Falmata cuta kuwa me tarin yawa duba da yadda ta rungumi Mama ba tare da ta taɓa cin moriyar auren ba ko na lokaci guda tsawon shekun tayi ta yi su ne wajen kula da Mama da hidimar ta da jinyar ta ,
duk kuwa da miskinancin ta , karon farko yakama ta samu tubarrakin da ke cikin aure sannan kuma Yakaka ta kauda kai ta haƙurewa Falmata Youssouf su cigaba da zaman auren su idan ya so ita ta nemi wani mijin ta aura ,2
Wannan dalilin ya sa Hajja ta ƙudurci niyyar toshe duk wata hanya da Yakaka zata iya bi ta iya raunata auren Falmata duk kuwa da cewa bata hango alamun hakan daga gareta ba domin ko Youssouf ɗin bata ji ta gwada ambatar sa ba , amma ko ma dai menene dole ta bada kariya ga auren Yarima Youssouf da Musaƙa Falmata.2
Washington DC
Sauƙar tsakar dare jirgin su ya yi a Harabar tashi da sauƙar jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa dake Washington DC, ( Ronald Reagan Washington National Airport )
Muryar chief flight attendant da ta zagaya cikin jirgin shi ya tada Falmata daga baccin da ya ɗan dauke ta ,
Good evening Ladies and gentlemen we have landed at DCA airport in Washington DC, where the local time is 2 :30 and the temperature is 6°. We hope you have enjoyed your flight with Turkish Airlines this evening and wish you a very safe journey to your final destination .
Bonsoir Mesdames et Messieurs, nous avons atterri à l’aéroport DCA de Washington DC, où l’heure locale est de 2h30 et la température de 6 °. Nous espérons que vous avez apprécié votre vol avec Turkish Airlines ce soir et nous vous souhaitons un voyage très sûr jusqu’à votre destination finale .
matsanancin sanyin da ya ratsa ƙasusuwan Falmata lokacin da suke tako matakalar jirgin a yayin fitowa da bata taɓa jin makamancin sa ba , shi ya sa ta sake shigewa cikin jikin youssouf da yake ɗauke da Mama bisa kafaɗar sa wacce take baccin ta naɗe cikin nannauyan bargo .
Sake kusantata da jikin sa yayi , yana gyara kwanciyar Mama , ya ce
il fait extrêmement froid ( yanayin da akwai tsananin sanyi )
Bayan sun bi duk tsare-tsaren da yake dole a yi su a airport yayin da aka shiga ƙasar Amurka a farko, kama daga kan yin hoton yatsu zuwa hoton fuska da sauran su , zuwa lokacin da jakankunan su suka zo hannun su
Youssouf ya ɗau Babbar jakar kayan su ba domin ya so ba ya danƙawa Falmata Ƙananun jakankunan guda biyu a hannun ta da basu wani cika nawi ba, ƴar tafiya kaɗan suka yi suka samu wajen zama a cikin airport ɗin,
Cikin sauri ya buɗe jakar kayan sa bayan ya ɗora mama a kan ƙafafun sa wacce ta farka tana ta kalle-kallen baƙon gurin da haske ya wadata shi tamkar tsakar rana.
Babbar rigar sanyin sa ya zaro daga ciki jakar shi doguwa ce har ƙauri mai buɗaɗɗan gaba da turawan ƙasar Amurka ke ƙiran ta ( tribal oversized Cardigan sweater )
STORY CONTINUES BELOW
Fatima sa rigar sanyi , kadda hunturu shi yi miki lahani ,
Ya furta hakan lokacin da ya zagaya mata rigar da jikin ta ya taya ta sawa , hijabin kan ta ya gyara mata , ya zarce da riko hannuwanta biyu da suka ɗau sanyi , ya haɗa tafukan su waje ɗaya , bayan ya kusanci jikin ta sosai ,6
Tsananin sanyin ya yi mata yawa da ya sa take jin sa har cikin cikin ta , jikin ta sai karkarwar yake , idanun ta da basu cika lafiya ba suka fara tara ruwan hawaye ,
Lura da hakan da youssouf yayi ya sanya shi rankwafo da kan sa saitin kunnuwan ta ,
Fatima na biɗo miki , café kafin zouwan notre prochain vol ? ( kafin zuwan jirgin mu na gaba ? )
Muryar ta na ɗan karkarwa tace
Har yanzu zamu sake tafiya wani waje ? Akwai sanyi dayawa anan , bana son sanyi ina da cutar wahalar numfashi .
Je sais Fatima que vous allez passer à notre destination finale d’ici 1 heure , ( Na sani Fatima zamu tafi zuwa matsayar mu nan da awa guda )
Shiru tayi ta sunkui da kai .
Hannun sa ya kai ya ƙarasa jawo ta jikin sa , ya haɗa su ita da Mama wacce ita ma sanyin wajen ya fara damun ta duk kuwa da lodin kayan sanyin da suke naɗe da jikin ta ya rungume su ,2
Cusa fuskar ta da sanyin yake shiga ta ƙofofin hancin ta tayi a jikin sa , ɗumin jikin sa ya sa ta ji sauƙin sanyin tare da yin lamo bata ko ƙwaƙƙwaran motsi .
Zaman mintoci Arba’in da biyar suka yi , lokacin da sanarwa ta karaɗe illahirin wajen ,
Would all passengers traveling to Rochester, on flight FR3522 please have your Passport ready for boarding flight FR3522 now boarding at gate 21, Your flight is ready to Leave.
Fatima , tashi mou tafi , notre vol est prêt à partir ( jirgin mu ya fara shirin tashi ) .
*****
Tafiyar awa guda da mintuna ishirin a sararin sama ya sada su da birnin Rochester dake babban garin New York ɗin Amurka da sanyin Asubahi ,
Bai zauna ba sai da ya yi waya a Hajiya umma ya sanar da ita sauƙar sa lafiya , tayi masa fatan alheri , suka ajiye waya bayan ya biɗi da ta isar da sakon sauƙar sa lafiya da gaisuwa ga Maimartaba .
Yayi Niyyar ƙiran matan sa sai kuma ya fasa , da nufin sai sun cimma masauƙin su sannan .
Basu sha wani wahalan zaman jira ba suka sadu da Mr Brian ƙarƙashin hukumar asibitin Mayo da Biyamuradi ya riga ya tura musu duk wasu bayanai da ya kamata su sani game da hanyar tafiyar su tun daga Niger har zuwa saduwar su da Asibitin Mayo ,
Cikin mutuntawa bayan gaisuwar barka da zuwa Mr Brian yayi musu jagora zuwa wajen motar sa da zai ja su kai tsaye zuwa Asibitin su ,
A gajiye liƙis Falmata tayi mazauni a bayan motar hannun ta cikin na Youssouf , bayan ta zauna , ta kwantar da Mama a jikin ta da ita ma tayi laushi tuɓus , bakin nan tsit sai narai-narai da ido take, duk walwalar ta tayi ƙasa .
Awanni uku na gudun mota suka sada su da Mayo Clinic , asibitin da yayi suna a faɗin ƙasar Amurka da ma duniya baki ɗaya wajen ƙwararrun likitocin da suka shafi manyan gagararrun cututtuka haɗi da ingantattun kayan aiki irin na zamani .
Doctor Williams Robert Shine ƙwararren likitan cutukan da suka shafi jini na yara da hukumar asibitin ta danƙa masa alhakin kula da lafiyar Safiyyah Youssouf Baskore .
Dan haka kai tsaye ofishin sa Mr Brian ya dangana da su , babu jinkiri suka samu iznin ganawa da shi da daman ya san da zuwan su .
Bayan sun yi taƙaitatciyar gaisuwa da harshen turancin Amurka cikin sakin fuska Doctor Williams ya nemi da su maƙala ( pilot in-ear / Ambasador, ) ƴar na’urar da ake maƙalawa a kunne domin amfani da ita wajen fassara yare kai tsaye zuwa kunnen me sauraro cikin harshen da ya fi fahimta .
STORY CONTINUES BELOW
Tarin tambayoyi ne daki-daki ya dunga jero su game da matakan lafiyar Mama , Youssouf na amsa masa , lokaci zuwa lokaci yana auna Mama da na’urorin auna marasa lafiya ,
Da hakan ya ɗauke su fiye da awanni biyu , har sai da Mama ta fara ƴan ƙananun rikici na gajiya , tana ture hannun Doctor Williams daga jikin ta fuskar ta a kwaɓe .
Bayan ya tattara bayanan cikin na’ura mai ƙwaƙwalwa dake gaban sa kan teburi ,
Ya musu iznin tafiya masauƙin su su huta zuwa gobe da zai sake ganin su ,
Wanda ya kawo su shi ya yi musu jagora zuwa masauƙin nasu da bashi da nisa sosai da cikin asibitin tafiyar mintoci basu wuce goma ba a mota , a tafiyar ƙafa zai kai mintoci ishirin da ɗoriya ,
Tun gabannin zuwan su da kwanaki biyar youssouf ya samu nasarar kama hayar ɗan madai-daicin gida na tsawon watanni huɗu a Lofts Apartment, dake 1st St SW.
Bakin wata ƴar ƙaramar ƙofa ya dakata da su , bayan youssouf ya sauƙe musu jakankunan su da ke bayan motar , Mr Brian ya miƙe masa ƴan mukullin gidan tare da shaida masa daga yanzu shi aikin sa ya ƙare idan suna buƙatar wani taimako akwai ma’aika na musamman da zasu zo waɗanda aikin su ne kulawa da su da lura da masauƙin su .
Bayan tafiyar Mr Brian , Youssouf ya kama hannu Falmata da Mama suka ƙarasa gaban ƴar ƙaramat ƙofar gidan tare da sanya ɗan makulli ya buɗe .
Sai da ya zaunar da su a cikin falo
sannan ya fita ya shigo musu da kayan su cikin sauri-sauri saboda tsananin sanyin da ke akwai duk kuwa da cewa rana ta take tsaka misalin sha biyu na rana agogon can .
Ɗan madai-daicin falon ya bi da kallo wanda yake tsare tsaf babu wasu tarkace illa kujeru da ƴan tebura sai Tv da kayan kallo daga gefe , tare da kan Tarho ajiye bisa ɗan teburi , ko’ina a share a goge tamkar da ɗai ba’a taɓa rayuwa a gidan ba .
Idanun sa ne suka sauƙa akan Fireplace ( ɗan wajen da ake tanada domin hura wutar ɗumama ɗaki ) da sauri ya ƙarasa wajen cikin zuciyar sa yana hamdala , ya harhaɗa ƴan kututturan itatuwan ( ironwood ) da ya tarar a wajen da basu cika yawa ba , ya ɗau poker tare da cinna wuta a jikin itatuwan ,
Hannun ta ya riƙo ya kawo ta gaban wutar ya ajiye ta ya ɗau mama ya ɗora bisa cinyar sa , suka yi shiru suna ƴan kara hannuwan su ɗumin wutar na ratsa su , suna jin yadda jijiyoyin jikin su ke warwarewa , jinin jikin su na gudana .
Fatima muyi sallah sai na fita ga wajen gari na biɗɗo mana kayan cimaka da amfanin gida ,
To ,
Ta amsa tana miƙewa riƙe da hannun Mama
Hannun ta ya riƙo suka shiga ɗaya daga cikin ɗakunan biyu da suke manne da juna , ɗan madaidaicin gado ne a ɗakin na kwanciyar mutum biyu da yake shimfiɗe da rigar katifa sai matasan kai biyu, gefe kwabar kaya ce ,
ɗan ƙaramin agogo bisa teburin gefen gado shine abu na ƙarshe da yake girke cikin ɗakin
Gaba kaɗan daga fuskar gadon banɗaki ne wanda ake iya hango kome dake cikin sa ( mai murfin gilashi ) da a turance ake kiran sa da ( Framless Glass shower Door )
Tare suka shiga banɗakin ya gwada mata wajen alwala .
Bi yayi ya dudduba tsarin gidan da bashi da girma sai tsaruwa ɗan cas da shi kamar a ɗauke , bayan ɗakuna biyun da suke falon akwai kitchen da ke ɗauke da ƴan abubuwan buƙata da ya zama dole a kitchen , cikin kitchen ɗin anyi killatatcen guri domin cin abinci ,
Sai ƙaramin laundry dake ɗauke da na’urar wanke kaya .
Daga haka babu kome a gidan sai fa shinfiɗaɗɗen Hardwood floor ruwan zuma da ya malale ko wanne lungu da saƙo na gidan .
STORY CONTINUES BELOW
Ɗaya ɗakin ya shiga wanda ya tarar da shi ya ɗara wancen a girma haka ma kayan ciki sun fi na wancen girma sannan a cikin sa akwai ɗan ƙaramin fireplace da babu a ɗayan ɗakin ,
Cikin sauri ya shiga banɗaki domin yin uzurin sa , abunda ya ba shi mamaki tare da yi masa daɗi a lokaci guda bai wuce ganin Falmata da ta gama ɗaura Alwala tar a gaban shi ba tamkar suna banɗakin tare , nan ya fahimci banɗakin ɗaya ne me ƙofa biyu a tsakanin ɗakuna biyu da ake ƙiran irin sa da ( jack and jill bathroom ) sai dai wannan akwai gilashi a tsakanin su ,
Ya ji ɗaɗin ganin banɗakin a haka ba dan kome ba sai dan sake samun kusanci da ita a matsayin ta na mai laruri a kuma baƙon guri da bata kai ga haddace tsarin sa ba bare ta iya yin gaban kan ta a yayin mu’amalar cikin gida .
***
Baban Mama .
Ta ƙira sunan sa cikin sanyin Muryar ta lokacin da ta gama sallolin ta tana son fitowa daga ɗakin ta gaza gano ƙofar , ga sanyi da take ji yana daɗa ruɗa ta , gami da sasuƙaƙƙar yunwar da ta fara gallabar ƴan hanjin ta ,
Da sauri ya taso, kasantuwar daman hankalin sa na gare ta , ya fito zuwa ɗakin riƙe da Mama wacce take sanya ƴan ƙafafun ta a duk inda ya ajiye nasa ,
Yana tura ƙofar cikin rashin sani tana tsaye a wajen ƙofar ta ɗan daki fuskar ta ,
Ashih
Ta furta tana murza goshin ta ,
Da sauri ya saki hannun Mama ya ƙarasa gami da tallafo ta jikin sa ya riƙo ƙugun ta ya ɗora tafin sa akan goshin ta yana murzawa a hankali
Je suis désolé Fatima, ban san kina kussa ba , akwai zafi ? T’ai-je blessé ?
A hankali ta zame jikin ta ,1
Ban ji ciwo ba , ka kaini wajen wuta na ji ɗumi nan akwai sanyi ,2
Bai zauna a gaban Fireplace ɗin ba , yana tsaye akan ƙafar sa ya zura hannayen sa biyu cikin aljihun sweater dake jikin sa ya ce
Fatima zani dubo wajen gari ku zauna nan kadda ki tashi , bani jinkirtawa zan dawo , me kuke so daga abinci ?
Papa abinci j’ai faim aussi ,2
Mama ta furta haka tana shirin fashewa da kuka ,
Mama kai ni wajen jakar kayan mu akwai Tourte à la viande,( meat pie ) samosa , sai mu ci mu sha ruwa ko ?
Eh mama , papa ka kawo jakkar mu ,
Bayan ya miƙo mata jakar kayan ta , ta ciro ƙunshin meat pie da samosa, da suke nade cikin takarda ,
Ƴar ajiyar zuciya yayi yana juyawa kan ƙafafun sa ,
Taku biyu yayi ya ji ta ƙira sunan sa ,
Baban Mama , ka tsaya ka ci abinci .
Kallon ta yayi ya ga ita ma bata kai ga fara cin abincin ba , sai Mama ta danƙawa meat pie babba ɗaya ,
Ku ci abinci Fatima idan na dawo zan ci rabo na ,
Bata amsa ba ya juya domin ya ƙagauta da ya tafi sanin da yayi idan yammaci tayi sanyin na iya ƙaruwa ,
STORY CONTINUES BELOW
Baban mama
Ta sake ƙiran sa
Fatima
ya ce yana juyowa gami da ɗora idanun sa kan fuskar ta ,
Sunkui da kai tayi , da zata iya hana shi fita zata yi ya bar su su kaɗai .
Ka dawo da wuri ,
Shiru tayi tana jiran amsar sa .
Da shi kuma ya ji kalmar ta ɗarsu a ran sa da wani irin yanayi da ya sanya shi murmusawa yana cigaba da kallon fuskar ta daga inda yake tsaye ,
Saboda-saboda nan baƙon waje ne ba mu san kowa ba , kar ka daɗe ko Mama zata nemi wani abu.
je serai bientôt de retour Fatima.
Yace yana ƙarasa barin falon ya fita gami da rufo musu ƙofar .
Shiru tayi ta kasa cin wani abincin kirki duk kuwa da yunwar da take ji , tana jin kan ta a nesa sosai da ƙasar ta ta haihuwa kewar Nahiyar ta Al’ummar ta , Yaren ta ƴan Ƙasar ta na taso mata , yanayin tsananin sanyin Nahiyar nan sam bai mata daɗi ba , yayi yawa . Ta gwammaci rana irin na Nahiyar ta ,( Africa ) ” Tabbas kowa ya bar gida ?
Zaman jiran awowi uku da lokaci ya kai gefen la’asar ,nisan sa ya kai na kwanaki uku a wajen Falmata ,
Ta sauya salon tagumi ya fi iri takwas , Mama kuwa baccin ta take hankali kwance bisa jikin mamar ta ,1
Ƙarar buɗe ƙofa ya sanya ta ɗago kai gami da maida hankalin ta kachokam kan ƙofar da fatan jin tashin muryar sa ,
Sallamar sa ya sa fara’ar da bata da masaniya daga inda ta ɓullo bayyana kan fuskar ta ,1
ya shigo da kayayyaki niƙi-niƙi a hannun sa , bakin sa na amsa gaisuwar barka da dawowa da take jera masa ,
Fita yayi tare da sake shigowa da wasu kayan a jakankunan takarda , bayan ya sallami me taxi da ya kawo shi ya rufe ƙofar tare da ƙarasowa kan kujera ya zauna daga gefen ta.
Ɗaya daga cikin jakar kayan ya jawo , ya ciro safar hannu sun kai saiti takwas , haka ma na ƙafa ,a jiye su a gefe ya cigaba da zaro manya-manyan rigunan sanyi sun kai guda shida na mata masu launika daban-daban ƙaurara masu inganci
Fatima sauya wannan chandail ɗin da wannan Le pull ta fi nawi ,
Ta sauya rigar jikin ta da wata lallusar rigar sanyin da aka yi ta da fatar dabbar cikin ƙanƙara ( Bear ) me ɗauke da launin fari da baƙi , da ta kawo mata iya guiwar ta , zame hijabin kan ta yayi ya ɗora mata hular sanyi da take mahaɗin rigar , ya zarce da riƙo hannayen ta ya zira mata safar hannu ,
Sauƙa yayi bisa guiwowin sa bayan ya kamo tafukan ƙafar ta ya fara ƙoƙarin saka mata safa ,
Cikin sanyin murya ta ce
Baban Mama zan iya sakawa , tare da kai hannun ta ta sauƙe akan na shi hannun da yake sanyi ƙalau saboda yawon da yayi a waje .
Muryar shi a ƙasa ya ce .
Zan saka miki Fatima hakkin ki ne na kula da ke .
STORY CONTINUES BELOW
A hankali ta ɗauke hannun ta , ya ɗago ƙafar ta ya ɗora bisa cinyar sa cikin sannu kan hankali ya sanya mata safar ,
Nagode ta furta
A wani irin yanayi na jin tsantsar kusanci da shi ta tsinci kan ta da bata taɓa jin irin sa ba , wani shauƙi me daɗi ya fara ɗibar ta .
vous êtes belle ( kin yi kyau )
Ta tsinci muryar sa
Ɗan murmusawa tayi duk da bata ganin sa ta ji tashin muryar sa ya maida mata da martanin murmushin ta ,
Bayan tarin suturun da ya sayo musu da fiye da rabin su suke masu nawi ( kayan sanyi ) takalma da sauran suturu , da bargunan rufuwa .
ya sayo kayan abinci da fiye da rabin su na cikin gongoni ,da kwalaye ne irin wanda yake hasashen zasu iya ci musamman ma Falmata ( shi ai ya saba fita ƙasashen ƙetere ya saba da irin cimakar su) Mama kuwa ya sayo mata kunun yara dai-dai shekarun ta da yake tsammanin zata so shi kasancewar ta ma’abociyar shan kunu .
Sai turarurruka da sabulai da sauran ƙananun abubuwan buƙatu na gida , sai kuma itacen wutar ɗumama ɗaki da ya ƙaro musu ,2
Shi ya ajiye kome a muhallan da suka dace da hakan ya ɗauke shi har lokacin da duhun dare ya fara shigowa da yake hasashen magariba ta kawo jiki , ya duba lokacin sallah ta yanar gizo ( online prayer timetable ) ya ga cewa lokacin sallah yayi .
Bayan sun idar da sallar magarib da kan sa ya shiga kitchen domin samar musu da abunda za su ci ,
Elbow macaroni ya tafasa musu , tare da ƴar miyar da ya soya ta sama-sama bayan ya haɗa kifin gongoni da zallar tsokar nama na gongoni a ciki , nan take kitchen ɗin ya ɗau ƙamshin girkin maza .2
Shi ya zuba musu a plate guda me ɗan girma suka ci tare baki ɗayan su .
Bayan sun sallaci isha’ zaman shiru ne ya ratsa tsakanin su , saboda rashin sabo da yin hira da juna ,
Miƙewa yayi ya ɗauki mama wacce ta sake komawa baccin gajiya ,
Fatima tasso ku tai ku kwanta ke ma kiyi bacci dare ya yi da akwai gajiya ga jikkin mou .
Babu musu ta miƙe ya kama hannun ta zuwa ɗakin da yake mafi girma , bayan ya zaunar ta bakin gado ya kwantar da mama daga tsakiyar gadon ya miƙe tare da ƙarasawa gaban fireplace ya kunna musu wuta
Ɗaya daga cikin bargon da ya kawo ya ɗauka ya rufa musu ,
Ki yi mouku du’a Fatima bonne nuit et fait de beaux rêves ,
gyaɗa kai tayi
Kan sofa ɗaya jal da take ɗakin ya koma ya kwanta tare da rufuwa da bargo bakin sa ɗauke da addu’o’in neman tsari daga abun cutarwar da daren ke ɗauke da shi .
****
Iskar da take kaɗawa da ƙarfi tare da sauƙar dusar ƙanƙara suka sa birnin na Rochester ɗaukar matsanancin sanyin da ya sa baƙi ire-iren su Falmata gaza samun nutsuwar bacci saboda tun baccin farko da ya ɗan ɗauke ta da bai kai ko’ina ba ta farka saboda matsanancin sanyin da yake ratsa ɓargon jikin ta ,8
STORY CONTINUES BELOW
Motsi ta sake yi a hankali gudun tada Mama wacce ga alama ita sanyin bai dame ta har sosai ba ko kuwa dan ta nitse ne cikin kayayyakin sanyi da bargo ?
sake tattakewa tayi a cikin bargon tana jin yadda ƙofofin hancin ta ke toshewa .
Biyamuradi da duk motsin da take yi a kunnen sa , ya buɗe kan sa daga cikin bargon sa , tare da miƙewa ya zauna ,
Ta hasken ƙwan fitilar gefen gado da bata cika haske ba ya hango yadda ta cure tana rawar sanyi ,
Kumama ce , bata son sanyi
ya kitsima haka cikin ran sa ,2
Miƙewa yayi ɗauke da bargon sa ya ƙaraso bakin gadon
Falmata wacce tayi lamo tana saurarar takun ƙafar sa cikin ran ta tana kitsimawa ,
Ashe shima ya kasa bacci ,? Haba me ake da wannan irin sanyi kamar cikin firiji ?
Zuciyarta ta buga ɗas
Lokacin ta ji hawowar sa kan gadon , bata yi aune ba ta ji kwanciyar sa ta bayan ta , hannuwan sa ya kai ya zagaye ta da su , ya zarce da sake matso da mama jikin Falmata ,2
ya yi amfani da hannun sa guda wajen sake rufa musu bargo .
Lamo tayi tana shaƙar ƙamshin turaren jikin sa , bata ce kome ba kamar yadda shi ma bai ce ƙala ba ,
Sannu kan hankali ɗumin numfashin su ya gauraya tare da taimakon ɗumin jikin su da yake ratsowa ta cikin suturun jikin su, tsanani sanyin da suke ji ya ragu , bacci mai daɗi da nutsuwa ya yi awon gaba da su baki ɗaya .2
Washegari
Tara na safe ta yi musu a ofishin Dr Williams inda bayan gaisuwa Suka makala pilot-in-ear a kunnuwan su
Da bayani game da irin matakin cutar Mama ya fara , yana cigaba da bayani kan magungunan da zasu ɗora ta akai wanda zai iya taimakawa wajen rage tasirin cutar da tsananin ta duk cikin harshen turanci
Falmata da ta ƙosa ta ji maganin da zai warkar mata da Mama ta katse Dr Williams da tambayar sa cikin harshen farasanci
Dr la drépanocytose peut-elle être guérie? ( shin cutar amosani jini tana warkewa ? )
Kai tsaye ya amsa mata da cewa cutar amosanin jini a halin yanzu ba’a kai ga gano maganin ta da za’a sha a warke ba a duniya sai dai hanya guda da ake yin amfani da ita wajen samun warakar cutar , hanyar ita ce dashen Ɓargo ,
Ana yin dashen Ɓargo/dashen ƙwayoyin jini ga masu ɗauke da cutar amosanin jini daga kan masu shekaru bakwai zuwa sama ,
ana amfani ne da ɓargon dake jikin ɗan uwa/ƴar uwa na jini ga marar lafiyan wanda jinin su ya zo ɗaya .
Duk da ba’a da tabbaci na samun waraka baki ɗaya ga mai ɗauke da wannan cutar bayan an masa dashen ɓargo amma fiye da kashi hamsin na waɗanda aka yiwa aikin an samu nasara sun samu waraka daga cutar baki ɗaya,
Sai dai akwai yiwuwar hatsari a yayin aikin da bayan yin sa , zai iya kawo hauhawar wasu cututtukan da yake tsakanin Rayuwa da Mutuwa da kashi hamsin cikin ɗari .
Bayan ɗan uwa ko ƴar uwa shin mahaifiya zata iya bada kwayoyin jinin/Ɓargon ta ga ƴar ta ??
Baza ta iya ba , sai dai idan an rasa ɗan uwa ko ƴar uwar da suka haurawa shekarun balaga , ana amfani da ƙwayoyin jinin cibiya na ɗan da ke cikin mahaifiyar sa da ya kasance ɗan uwa ne ga shi marar lafiya da jinin su ya zo ɗaya .
A hankali Falmata ta zare Ambassador dake kunnuwan ta , hawayen idanun ta na sauƙa bisa kan hular Mama da take cinyar ta ,
Ashe cutar Mama Babba ce daga cikin manyan cutuka , ? Tausayi me tsanani ya taso mata yana kassara gaɓɓan jikin ta . Rungumeta tayi tsam a jikin ta , tana shafar bayan ta .
Mama bata da ɗan uwan da zai iya sadauƙar da jini da ɓargon sa a gare ta , a halin yanzu
Bani da damar sadauƙar miki da jini ko ɓargo na Mama .
Amma ina da damar zama uwar jaririn da zai sadauƙar miki da jinin sa Mama tun kafin ya zo duniya ..Doctor Hamza tare da wasu abokan aikin su, da wasun su ke a zaune wasu na tsaye daga cikin ofishin shugaban su kuma tsohon malamin wasu daga cikin su a zamanin karatu , Professor Talba Garkiɗa,
A zahiri a nutse yake ya bada hankalin sa da ƙululun idanun sa bisa kan Prof wanda ya dilmiye sosai cikin yin bayanai game da cutar da take damun matar dake cikin mawuyacin hali a ICU da jagorancin duba ta ke a hannun mutane huɗu daga cikin su .
Sai dai a baɗini cikin hankalin sa sam babu nutsuwa , babu jin daɗi bare kwanciyar hankali a tun jiya da ya amsa ƙiran prof .

Nisawa yayi yana sake jin yadda zuciyar sa ke ƙara ƙuntata , wai shikenan domin Ubangiji Allah yayi umarni ‘ya’ya su bi iyayen su sai kuma su iyayen suyi amfani da wannan dama wajen cusgunawa ‘ya’yan su ?
Ah cusgunawa mana , idan ba dai Baba ya so sanya shi a tsaka me wuya tare da damal-mala masa ginin tsarin rayuwar da ya riga ya tsarawa kan sa ba wanne dalili ne zai sa shi ya ɓaɓ-ɓako masa da maganar ƙarin aure ?? Wai fa ƙarin aure ? Shi lamarin ma har kawo yanzu mamaki yake bashi , yana tantamar anya ma kunnuwan sa sun ji zancen a dai-dai ?3
Idan ya tuno da yadda kalaman suka fito daki-daki tare da sake jaddadawa akan babu shakka umarni yake ba shi har ma kuma ya riga ya sama masa matar , sai ya ji wani mololon baƙin ciki ya tokare shi , shi fa ba yaro bane yanzu.
Shi kenan haka zai yi rayuwar sa tare da mata har biyu da ba zaɓin sa ba a matsayin matan sa ? Safiyya da kan ta ba zaɓin sa ba ce , aure ne mai kama da na dole aka liƙa masa shi kuma ya sa hannu dole ya amsa daɗi da ƙarawa lokacin yana a tsakiya da jin takaicin ɗiya mace , domin haka yasa shi gaza musantawa .
Yanzu kuma da yake ɗan lallabawa da Safiyyan da daɗi ba daɗi suna zaman su tana faran ta masa dai-dai gwargwado shine kuma za’a sake bijiro masa da wani auren ? To a dalili da me ? Shi a tsarin rayuwar sa babu saki ba kuma gurbin mata biyu .4
Mace ɗaya tal ta ishe shi ,shiyasa ma ya bada kai yana lallabawa da wacce ta zama ƙaddarar sa , rabon sa duk kuwa da cewa ba zaɓin sa bace .
to yayi yaya da mata biyu ? Jera su zai yi yana kallo ? Ko kuwa a wuya zai rataya su yana yawo da su suna reto ? Ɗan tsaki ya saki a hankali .2
Lokacin da ya fahimci professor Garkiɗa ya kammala jawabin sa ba tare da shi ya fahimci kome ba , alhalin kuma musamman yayi tattaki ya zo domin ya saurari koyarwar duk da cewa kusan abunda ya riga ya sani ne zai sake sanar da su , to amma shi ai maye ne akan neman ilmi kome ƙanƙantar sa , hakan ya sa shi yin zarra a cikin abokan aikin sa masu matsayin karatu irin nasa ,
Ai ga irin ta nan tun kafin a je ko’ina ya fara sururucewa akan tunanin rayuwa da mata biyu , anya kuwa zai iya ?1
Miƙewa yayi yana jin takaicin rashin saurarar koyarwar da prof yayi musu .
Bayan fitowar su daga ofishin suka tsaya shi da abokin aikin sa suna tattaunawa .
Mata biyu ne suka doso wajen hannuwan su riƙe da kayayyaki , kondunan zuba abinci da wasu tarkace ,
Karaf idanun sa suka sauka akan matar rannan ,
Tun a ɗan nesa yake nacewa kallon kamannin ta da ke kamanceceniya sosai da na Khaalty Rahima , ba su da wata maraba , sai tsabar tsufa da wani irin duhu da wannan tayi marar kyaun gani,
tabbas ko da khaalty Rahima na raye bai ci ba ace tayi wannan tsufan, dududu shekaru biyar zuwa shidda ta ba shi ,
Bai farga ba suka gota shi , da sauri ya bi bayan su ba tare da yayi sallama da Abokin sa ba
Yana son sanin wacece ita , ?
Sallama ya dunga rangaɗa musu har baki biyu babu wacce ta juyo a tsakanin su sai da yayi ta uku ,
Ɗayar kakkaurar matar baƙa gajera ta juyo ,
” Au nan ne ? Da mu ne ? Ca nake a iska nake ji ,
STORY CONTINUES BELOW
“Sannu Mama Da abokiyar tafiyar ki na ke son yin magana ,
ya furta haka yana nuna bayan ta da ta ɗan yi gaba batare da ta tsaya ba tana cigaba da tafiyar ta , takawa yayi ya bita ganin tana shirin shan wata kwana .
“Hajiya sannu ,
” sannu Hajiya ,”
Shiru ya ji tayi ,
Dan haka ya ɗaga taku ya sha gaban ta ,
Da sauri ta ɗago kan ta , ta kai duban ta kan shi ,
Kallon-kallo suka yi , jakar kayan da yake hannun ta ya sulluɓe ƙasa ,
Lokacin da ta wara idanun ta dake nuni ƙarara da halin ruɗanin da zuciyar ta ke ciki ,
Motsa baki tayi da sautin ya gagara fitowa , sai kuma tayi saurin kauda kai .
,”Khaalty Rahima ??
Yace da wani irin maɗaukakin sauti , da ya zarce da wata ƴar dariya da ke nuna tsantsar farin-cikin da ya kawo masa ,
Hannuwan sa biyu duk ya kai ya kamo nata hannuwan dake cikin hijabi ya riƙe ,
” Malam lafiya kuwa ?
Matar da take abokiyar tafiyar ta ta furta haka lokacin da take ƙarasowa tana bin su da kallon mamaki da manyan idanun ta .
Bai kula ta ba ya jijjiga hannun ta dake cikin nasa ,
,”Khaalty Rahima tahadah ‘iilaya rja’a ,
Ya furta hakan yana sake kallon ta da ta sunkui da kai tayi ƙiƙam kamar bata jin sa , bai yi aune ba ta warce hannun da ƙarfi , ta sunkuya tana tattara kayan hannun ta .
Durƙuso yayi yana taya ta kwashewa ,tare da leƙa fuskar ta yana son sake ganin ta .
“Khaalty Rahima”
ya sake ƙira da wata irin murya , fuskar sa na nuna tsantsar damuwar da ta maye gurbin farin cikin sa .
“Yau ga ikon Allah Malam kurma ce fa kake ta faman yi mata magana , ‘1
Tare suka miƙe da ita , da wani yanayi na firgici ya juya yana kallon matar .
“Kurma ?
“Eh kurma ce mana , hala ka san ta a wani waje ? Mamar Bulama da yawan gidajen masu kuɗi take , Ai manyan gidaje ɗaya-ɗaya ne a cikin garin nan da bata yi aiki ba , har gidan inn-in wannan mashahurin attajirin mai tashen kuɗi na bala’i da masifa , bani sunan sa ma ? Ga shi da suna mema sunan na sa ??,’3
,” kika ce kurma ce ? Mamar Bulama ? Wacece ita ? Ba gaskiya bane wannan ƙanwar Mama ta ce .
Juyowa yayi , sai dai ko alamar ta bai gani ba a wajen ,
” ina take ?,”
“,Tayi tafiyar ta , ai kaga halin ta na miskilancin da yake sa ake tisa ƙeyar ta a kore ta daga gidajen da tayi aiki , miskilanci da faɗin rai na tsiya , to Allah na tuba kana talaka faƙiri mai neman na sawa a bakin salati ina kai ina faɗin rai ? Wa kuma zaka gwadawa ya ɗauka? Gidaje daban-daban huɗu muka yi aiki tare , biyu akan halin ta aka ƙore ta biyu akan wannan ifiritun ɗaya-ɗayan ɗan nata Bulama haba me ake da batsal-tsalewa irin ta Bulama ya ɗan yayen biri ? .1
Bai ƙarasa sauraron matar da take tsakiyar yi masa bayani har bakin ta na kumfa ba yayi wucewar sa ya bi sawun ta ,
Cikin ran sa yana faɗin
“,haba me ake da ɗan banzan surutu marar ma’ana ?
Duba ta yayi har ɗakin da ya san marar lafiyar da suke zuwa wajen ta na ciki amma bai gan ta ba.
Bai kuma tambayi matan da ya tarar a ɗakin ba da ko alamu basu da nasaba ta jini da ita , dan haka sai ya koma.
kichiɓus suka yi da matar da ya baro a waje ,
STORY CONTINUES BELOW
,” ka same ta….
Da hannu ya dakatar da ita , alamar tayi masa shiru ya wuce cikin ran sa yana bawa kansa tabbaci babu shakka Khaalty Rahima ce , ita ya gani
Ƙanwar mamar sa ce da kusan tare suka tashi , tunda ya buɗi ido ya gan ta a gaban iyayen sa kafin daga baya kaddarar da bai san ta mecece ba ta gifta tsakani ta raba su .
Sai dai koma menene yana ganin yazo ƙarshe , zai bi kuma duk hanyar da ta dace domin dai-daita rayuwar iyayen nasa daga walagigi .
Kai tsaye wajen motar sa ya nufa zuciyar sa cike da tunanin hanyoyin da zai bi domin gano haƙiƙanin rayuwar da Khaalty Rahima take tsawon shekarun nan, shin ita ce ko kuwa ba ita bace ?
Khaalty Rahima bata da wata larura da ta shafi ji ko gani , ance wannan kurma ce ??1
Tada motar sa yayi , zuciyar sa maƙare da wasi-wasi , wajen Amne yake da burin zuwa a yau ɗin to amma yadda yake jin zuciyar sa a yanzu bai son kome illa ya kaɗaice .1
Yana isa gida kai tsaye sashin su Rahima ya nufa saboda yunwa da yake ji tana ƙwaƙular ƴan hanjin sa ,
Da sallama ya shiga falon , idanun sa suka sauƙa akan ta da ta juya baya tsaye a gaban hoton ƴar yarinyar da bai kai ga rarrabewa ɗiyar wacece a tsakanin Hafsa da Zainab ba ?
Zama ya yi akan kujera tare da yin baya da kan sa ya jingina da kujerar
“Rahima idan akwai abinci ki kawo min , idan kuma babu ki dafa min Noddles yanzu ina jin yunwa sosai ki haɗo min da tea .’
Numfashin ta ne yayi sassarfa lokacin da sautin muryar sa ya sauƙa a kunnuwan ta,
shikenan addu’ar ta bata karɓu ba , domin kuwa tunda Rahima ta tabbatar mata da cewa hutu ya zo zai ya koma garin Abuja inda ya koma aiki da zama baki ɗaya tare da matar sa ,
take addu’ar Allah ya raba ganawa a tsakanin su har ya gama hutun sa ya koma .
To sai dai addu’ar ta ta a iya ranakun jiya da shekaranjiya tasirin ta ya tsaya , domin ga shi yau ko azahar bata yi ba Alƙadarin ta ya karye ,
Ita kunyar sa take ji , kunya mai tsanani kuwa , kunyar abunda ta aikata , me zata ce masa ? Da wanne ido zata dube shi , anya duniya da gaskiya ita tana da tsaurin idon sake kallon sa ?1
“Rahima baki ji na ?
Satar kallon inda yake Yakaka tayi ta gan shi har yanzu yana yadda yake kan shi a kwance bisa kujerar ya miƙe ƙafafun sa .
Ba tare da ta juyo ba ta kama hanya da ƴar sassarfa da nufin barin wajen tsawar da ya daka mata ya sa ta dakatawa tana jin yadda zuciyar ta ke tsananta bugu .
“Rahima yaushe kika zama haka , marar ɗa’a ? Ni nake yi miki magana kina tafiyar ki ? Zo nan .
Juyowa tayi a hankali , ta tsugunna a wajen da take , muryar ta tana sarƙewa tace
“Ba-ba Rahima bace ni ce Yaya Dakta .
Tamkar a ire-iren shuɗaɗɗun mafarkan sa da ya saba yi a shekarun baya ya ji sautin muryar ta , dan haka ya buɗe idanun sa da suke lumshe a hankali .
“Rahima zo nan nace “
Ya sake maimaitawa cike da burin son kawar da mummunan tunanin da ya bijiro masa da sautin ta a yau .
Ni ce Yaya dakta ta sake maimaitawa tana kif-kifta ido daga inda take .
A wani irin yanayi ya yunkuro kamar an tunkuɗo shi , ya zauna da kyau lokacin da yake ɗora idanun sa akan ta , da ta sunkui da kai ta ƙi kallon sa illa bakin hijabin ta da take wasa da shi a hannun ta ,
STORY CONTINUES BELOW
Ita ce ? Me ya dawo da ita ? Me ta zo yi nan ?
“Ke ce wa ?
Ya furta hakan da wata buɗaɗɗiyar murya me amo da ya sa Yakaka yin rau-rau da idanun ta da suka kawo ƙwalla ,
Shiru tayi ,
“Ke ce wa nace ? Me kika zo yi gidan nan ?
,”Ni ce Yakaka .”1
Ta bashi amsa cikin sanyin murya ba domin tana da yaƙinin bai gane ta ba , sai domin yunƙurin ta na ganin ta wanke kan ta .
Miƙewa tsaye yayi yana jin yadda wani irin bacin rai da ya sauƙo masa tun daga tsakar ka yana neman rufe masa idanu ,
“Tashi ki bar gidan nan ,” ko kuwa na sa maigadi ya fita da ke , nan da kike gani “,
ya buga ƙafar sa guda a dandaryar falon cikin yi mata nuni ,
” Ba gidan Karuwai bane , ba kuma gidan giya bane , tashi nace ,”
Ya kwatsa mata tsawa
Tsawar da yayi mata bata razana ta ba , bata kuma huda zuciyar ta ba irin kalmar karuwa da gidan giya da danganta ta da su ,
A hankali ta ɗago kan ta , idanun ta suna zubar ƙwalla tace ,
“,Yaya Dakta kayi hakuri dan Allah na san nayi kuskure amma wallahi ba karuwanci naje ina yi ba makarant….
,”Shut up,
“Ki tashi ki fita nace ,
ya furta hakan yana kusanto ta da takun ƙafar sa ,
,” Big Bro ,
Ya tsinkayi muryar Rahima daga bayan sa ,
Ƙarasowa tayi tana raba ganin ta a tsakanin su biyun , da sauri ta ƙarasa wajen Yakaka wacce zuwa lokacin kuka take haiƙan , ta ɗago ta tsaye
“Big Bro , Mamar Mama ce fa Yakaka , bata mutu ba , kai ma kayi zaton Fatalwa ce kamar yadda ta tsorata ni da farko ko ? ,
“Rahima ki min shiru ,
yace yana nuna ta da allin ɗan yatsan sa , goshin sa a tattare da mabayyanin ɓacin rai .
,”ke ki tattara ki bar gidan nan yanzu-yanzu , kar ki ƙara minti goma idan ba haka ba kuma zan sa a fitar da ke ,”
Da sassarfa ya bar falon ,
Babu shakka kunya tayi ƙaranci a zamanin da muke ciki , idan banda tsagoron rashin kunya ita wannan yarinyar har tana da ƙarfin guiwar dawowa cikin gidan da ta gudu ta bari ?? Shin da wata alaƙa ta jini ne a tsakanin su bayan taimakon da yayi mata da ta saka masa da tarin butulci ,?
Da har kuma yanzu zata ɗebo ƙafafu ta zo gidan su to a matsayin wa take ? Kuma gurin wa ta zo ?
Har ta gama barikin ne ta gaji ta dawo ? Zaton ta nan matattarar karuwai ne ? Ko kuwa har auren nasu da uban ƴar ta ta ya ƙare ne ?
Dole ta bar gidan kamar yadda tayi a baya, tayi nesa da shi da dangin sa domin mumini ai baya sanya hannun sa a ramin Macijiya sau biyu .
Ba zai taɓa saurarar ta ba , ita ɗin zantukan bakin ta ai duk ƙarya ne , da yaudara , kirkin baka ne da ita tare da ladabin banza .
Runtse idon sa yayi yana tura ƙofar sashin sa da ƙarfi , ɓacin ran ganin ta yana sake hauhawa a ran sa hatta yunwar da yake ji tayi ƙaura .
,”Rahima dole na tafi tunda Yaya Dakta ne da kan sa ya kore ni kin manta shi ne ya fara kawo mu ? Dalilin sa muka zo gidan ku Rahima bani da ikon cigaba da zama ,”
Yakaka ta furta hakan tana shiƙar kuka lokacin da take jawo jakankunan kayan ta ,
Kukan ta daga ƙasan ran ta yake , kukan tausayin rayuwar ta tare da nadama , ina zata je ? Tun zamantowar su ‘yan gudun hijira nan gidan ne kaɗai mafakar da suka tsaya cikin ta ba tare da ƙalubale ya cisgesu ba har sai da ita da ta sanya kafafun ta da kan ta ta bar mafakarta ,
STORY CONTINUES BELOW
Tayi zaton kome zai zo mata da sauƙi zaton ta zai yi saurin yafe mata , tayi tunanin zai tare ta da yawan ƙaunar nan tare da tausayin da ta san yana gwada mata can baya , har ma tana sanya ran cigaba da samun kulawar sa kamar farkon fari ,1
Ashe dama ta riga ta kufce mata , ta riga ta ɗibga kashi a inuwar da ta huta ,
ashe ita ɗin yanzu wulaƙantattace a wajen sa ? Ashe yanzu ita abun kƴamata ce da bata wuce a kore ta ba ? Babu shakka ba’a ɓari a kwashe du , hangen hadarin nesa kuma ya sanya ta damal-malewa cikin kashi .
Ɗauki take nema , so take ta samu wanda zai dube ta ya fahimce ta ba tare da ya aibata ta da laifin da ta riga ta aikata ba , ba tare da wani hukunci yayi tsalle kan ta ba sakamakon abunda ta aikata da bai wuce Kaddarar da zata iya hawa kan kowanne ɗan Adam ba .
Malama Maryam ita ce ɗaya jal wacce ta sani da tashin farko bayan sanin laifin da ta aikata ta tausasa mata , a yanzu kuma bata nan , tayi komawar ta garin su tun kwanaki biyu da suka wuce .
Shin Mutane ba za su mata uzuri ba ? Ashe haka halli ‘yan adam yake ?? Da wanne zata ji ? Ita kenan haka guguwar Rayuwa zata cigaba da walagigi da ita ? Yanzu ina zata ?
“Kar ki tafi Yakaka tsaya ina zuwa .
Rahima ta katse ta bata tsaya jiran amsar ta ba ta fita da ɗan gudun ta ,
bata tsaya ba , ta cigaba da jan baccon ta da yafi ƙarfin kinkimar ta , tana yi tana rera kuka da murya mai ban tausayi .
” Yakaka , Yakaka ki tsaya , kar ki tafi nace ki zo Baba yana ƙiran ki .’
Kanta a ƙasa tana sharar ƙwalla ta shiga falon Prof , da ta tadda shi kamar koyaushe a zaune , muddin zai miƙe tsaye sai da sanda mai ƙarƙo .
Muryar ta tana rawa ta gaida shi , ya amsa yana nazarin ta ,
,” Me ya faru zaki bar gida ‘yata ,? meye dalili ?
Muryar ta na rawa tace
“Yaya dakta ne yace na tafi .
Ya gane wanda take nufi dan haka ya ɗan yi jim cikin ransa yana sake ganin dai-dai kan ƙudirin sa .
“Ki koma ciki , nan gidana ne ba na wasu ba , dan haka babu wanda yake da damar korar ki , kin ji ko ?
‘,To Baba , nagode ,”
“, Madallah ku koma ciki ,’
Bayan tafiyar su ya ɗau wayar sa tare da ƙiran Doctor Hamza wanda tunda ya shiga sashin nasa ya gaza aikata kome illa kai-kawo da yake yi , zuciyar sa na cigaba da tafasa ,
Bayan ajiye wayar sa , sashin Prof ya tasamma , inda ya tarar da shi yana tsimayen sa , bai saurari gaisuwar da yake yi masa ba , ya fara da tambayar sa fuskar sa na nuna ɓacin rai
“Me yarinyar nan tayi maka zaka kore ta ?
Da sauri ya ɗago kan sa yana duban Baba , a zaton sa yau ta zo , sannan Baba bai ma san da zuwan ta ba , ashe ba haka bane .
Shin ƙarar sa ta kawo ? Babu shakka babu kome a bariki sai darussan da ke koyar da tsaurin ido tare da rashin kunya ,2
Shiru yayi , ganin yayi shiru ya sa Prof sake jefa masa wata tambayar
“Ko kuwa ta aikata wani abu da ba dai-dai bane ? Ko tana kan aikatawa da ta cancanci kora ?
Shiru Doctor Hamza ya sake yi , kai tsaye ba zai ce ga abunda ya hana shi ya ce kome ba , Bazai ce ga dalilin da yasa ya gaza bayyana laifin ta da yake sirri ne a gurin sa wanda yake tunanin a iya tsakanin su biyu yake, da kuma can inda tayi rayuwar bariki ,
STORY CONTINUES BELOW
sai dai hankalin sa yafi tafiya akan ya rufawa ƙaryar sa da yayi a baya asiri ne, sanin da yayi Ƙarya wata mummunar ɗabi’a ce da iyayen su suka wanzu suna hanin su da aikatawa ,
“Idan baka da wani dalili ,kar ka sake korar ta , ita ɗiya mace rauni ne da ita a koyaushe , a kuma ko’ina tana buƙatar matallafi ne cikin rayuwar ta , ‘
” Wanda daga zarar ta rasa mai tallafar ta zata iya faɗawa kowacce irin mummunar rayuwa , yan gudun hijira su ma mutane ne kamar kowa walaƙanta su abune marar kyau , ka kiyaye .
“Zan kiyaye Baba ,
***
Yakaka tana komawa cikin gida bayan Rahima ta kama mata kayanta sun mayar su ɗakin da cikin sa suka zauna ita da Falmata tun farkon zuwan su gidan , muryar ta a ɗan dishe ta ce
” Rahima yaya Dakta fa yunwa yake ji , da farko da ya shigo yace ki masa girki ,
Zama Rahima tayi a bakin gado tana ɗan riƙe kanta ,
“Yakaka wallahi kaina ciwo yake ba kaɗan ba , yau nasha yawo a School ( makaranta ) taimaka ki ɗan dafa masa ko ƴar indomie ce .
Bata ƙarasa zancen ba yakaka ta nufi ƙofa , tana amsawa da “To yanzu zan yi ,”
Bayanta Rahima ta bi da kallo cikin ranta tausayi ne me tarin yawa , Yakaka mai kirki ce kaddarar Rayuwa ce ta faɗa mata ta dalilin raunin Ilmi da wayewar ta .1
Ita da aka ce ta dafa indomie sai ga ta ta zage damtse wajen girka lafiyayyar jalloup ɗin Spaghetti da ta sha niƙaƙƙen nama da kayan ɗanɗano , cikin sauri da azama take aikin dan haka bata ɗau ɗogon lokaci ba ta kammala , ta tafasa shayi ( tea ) da ya buƙata ta adana su a mazubi me kyau ta ɗora bisa ɗan faranti ,
Zuwa tayi ta samu Rahima tana bacci , bata son tashin ta domin kar ta ƙara mata ciwon kai .
Dan haka ta fita daga ɗakin ta koma kitchen tayi tsumu a tsaye hankalin ta ya rabu kashi biyu , tunanin Dakta da yace yana jin yunwa da kuma tsoro da take ji na kai masa abincin ,
Tayi tsayuwar kusan mintuna uku ta gaza ɗaukar abincin kafin daga baya ta gyara zaman hijabin ta ta ɗau tiren tare da nufar sashin nasa da ba baƙo bane a wajen ta ,
Cikin sanɗa take tafiya lokacin da ta shiga sashin nasa a yunƙurin ta na son ta shigar masa da abincin ta fita ba tare da ya san ita ta kawo masa ba ,
Ta zo dai-dai ƙofar tayi tiris ganin ƙofar shiga falon nasa a rufe , ajiye tiren tayi , tana tunanin yadda zata yi ?
Wata dabara ce ta faɗo mata , dan haka ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya kafin ta kai hannu ta ƙwanƙwasa ƙofar da ɗan ƙarfi , tayi wuf ta juya da saurin ta ,
garam !
ta ji tayi karo da mutum .
Da sauri ta ɗago kanta ganin fuskar sa a murtuƙe yana jifanta da mummunan kallo ya sa ta haɗiyar yawun tsoro ,
“, Un- um daman Yaya Dakta abincin ne , Un Rahim..
,”Wuce ki bar nan bana so na sake ganin fuskar ki .
Yace da maɗaukakin sauti ,
Sum-sum ta ratsa ta gefen sa da yayi banga-banga yaƙi matsawa tamkar mai shirin jibgar ta ta bar wajen har tana haɗawa da ɗan gudun ta bayan matsanancin bugu da zuciyar ta ke yi .
Sanin darajar abinci ya sa shi ɗaukar abincin da ta kawo masa ya shigar da shi falon nasa ya zauna tare da ajiye ledar da ya sayo abinda zai ɗan ci ,
Dafadukar shinkafa ce irin wacce aka cika mata ƙaƙale da launi ruwan ɗorawa shar , da ya taka takanas zuwa shahararren gurin sayar da abinci da ake ji da shi a garin ya sayo .1
STORY CONTINUES BELOW
Loma ɗaya-biyu yayi yaji abincin bai masa yadda yake so ba , sam shinkafar ma bata dahu sosai ba a bakin sa , shi yafi son yaji abinci ya dahu sosai ko shinkafar ce yaji ta suɓut-suɓut tuɓus-ɓus daɗin tauna , ba irin wannan dahuwar ƴan gayun ba, da yake hasashen rabin shinkafar sai dai ta ƙarasa dahuwa a cikin sa .
Rufe abincin yayi ya ɗan ture gefe , yayi jugum a zaune , yana tunanin matan zamanin gaba kamar nan da shekara hamsin anya za’a iya cin girkin su ? Ko Amne da take ba tsohuwa tukuf ba salon girkinta ya banbanta dana yaran mata irin su Hafsa, zainab ,Rahima a bar batun Safiyya wannan ba abunda tafi ƙwarewa akai irin Kwaɗon ganyen salad da take cin sa kamar me .1
Ɗan satar kallon girkin da Yakaka ta kawo yayi ta wutsiyar idon sa , tsaki yayi tunowa da yayi duk kanwar dai ja ce da girkin su Rahima da na wannan da ya raina dahuwar tasa .
kasa jure yunwar da take sasuƙar sa yayi dan haka cikin yanayin, ya na iya ? Ya ɗauko tiren abincin zuwa kan teburin gaban shi ,
Sai dai Yana ɗora ido akan abincin ya haɗiye yawu , da sauri ya ɗau chokali yayi bismillah ,gami da kai lomar farko bakin sa ,
Bai saurara ba cikin nutsuwa ya dinga aikawa hanjinsa haƙƙin sa har sai da yaji cikin sa ya samu dai-dai da buƙatar sa sannan ya sarara , a fili yace
“, Alhamdulillah wannan ko wacce irin pasta ce haka Rahima ta dafa ? Wataƙila ta zallar Alkama ce ba surki .12
***
Bayan Yakaka ta idar da sallah tayi addu’o’in da ta saba yi duk bayan sallar ta ,
Ta waiga ga Rahima wacce ta farka daga bacci
“Rahima yaya ciwon kan naki ? Kin ji sauƙi ko ?
” Ya ɗan sake ni Yakaka thanks ,
“Yakaka yawan ibadar ki na burgeni ga yawan addu’o’i da kike yi kin fa kusa mintoci ishirin kina addu’a , Yakaka me kike roƙa haka mai yawa ? Ko dai har da shi ake yiwa addu’ar ,
Ta ƙarasa zancen tana ƴar dariya tare da kashe idonta ɗaya na ɗabi’a .
Ɗan zaro ido Yakaka tayi sai kuma tayi murmushi ,
“Rahima , Bawa baza’a tambaye shi me yake nema a wajen Ubangijin sa ba , Duk abunda nake roƙa bai wuce neman gafara da samun Rahamar Ubangiji ba gare ni da iyayena da ‘yan uwa na ,
Jim tayi kafin ta cigaba da cewa ,
,”Ummin mu , Rashin sanin a wanne hali mamana take tsakanin Rayuwa da mutuwa yana matuƙar tayar min da hankali Rahima , kullum roƙon Allah nake ya ƙaddara haɗuwar fuskokin mu , idan kuma ita ma ta rasu kamar Baban mu , ina tsawaita musu addu’ar samun gafara a wajen Allah .
Hawayen da ya tsatsafo a idonta ta goge cikin ranta ciwo take ji na rashin iyayen ta .
Cikin tausayawa Rahima tace ,
“kiyi Haƙuri Yakaka , babu shakka abune mai ciwo naka ya ɓata har gara ma ace mutuwa yayi kaga gawar sa aka yi jana’iza aka binne , kowa ma jiran mutuwa yake ,
” Muma akwai Auntie na takwarata ce sunanta aka sa min , ita ma ɓata tayi tun ma kafin a haife ni ,
“Amne tana bani labari lokacin tana da ciki na , Khaalty Rahima ta bar gida tana yarinyar ta yadda Amne ke bani labari bata ma kai mu shekaru a yanzu ba ,
STORY CONTINUES BELOW
” tundaga lokacin Rayuwar gidan mu bata sake zama dai-dai ba , duk da bansan Ƙhaalty Rahima ba amma labarin kirkin ta da yadda Amne ke ƙaunar ta yasa nima ina sonta sosai , ina kuma so ta dawo wataƙila rayuwar gidanmu ma ta dawo mai daɗi , “
Cike da jimami da tausayi Yakaka tace ,
” Allah sarki Khaalty Rahima Allah ya bayyana ki daga yau zan dunga saka ta cikin addu’o’i na .
” Nagode Yakaka , duk ranar da muka je gidan Amne tare zan sa ta nuna miki hoton Khaalty Rahima .
Cikin zumuɗi Yakaka tace
” yaushe zamu je Rahima ? Ina so naje na gaishe da Amne .
“Weekend ( ƙarshen sati ) insha Allah .1
” Allah ya kaimu ,
Rochester New York City2
Tafe Biyamuradi Youssouf yake akan titin 3rd Ave, jikin sa sanye da kayan sanyi daga ƙafa zuwa kansa da ya ɗora hular da take da laɓɓa biyu da suka rufe masa kunnuwa elmer fudd da aka fi ƙiranta da Trapper hat .
Hannun sa ɗaya riƙe da ‘yar jakar takarda da ya sayo ( Hot chocolate ) mai dauke da tambari tare da sunan kamfanin chocolate and Vines a jiki , domin su ɗumama cikin su ɗumin hot chocolate ya ratsa musu gaɓɓai kafin su fita zuwa cikin asibiti nan da awa ɗaya mai zuwa ,
Cikin kwanaki biyar da suka biyo bayan zuwan su ƙasar Amurka zuwa ganawar su da likita da duk wasu bayanai da suka samu game da Cutar dake tare da Mama .
Daga Biyamuradi Youssouf har Falmata sun rasa karsashi da nishaɗin su , musamman Falmata wacce tundaga wannan ranar take cikin damuwa da tunanin hanyar da zata iya bi domin ganin ta samar da abunda zai zama sanadi na samun warakar cutar Mama da sanyin ƙasar tare da sauyin ruwa suka haɗu suka sa ta ɗan fara kukan ciwo ,1
Sai dai kasancewar nan Amurka ba kamar ƙasashen Africa da basu cigaba bane ta fuskar kula da lafiyar ɗan Adam .
Cikin ƙanƙanin lokaci a rana ɗaya aka bata magunguna tare da duk wani taimakon da ya dace a ƙarshe likitan ya gargaɗe su akan kiyayeta daga wannan sanyin mai tsanani , dan haka ciwon bai tsananta ba ya lafa .
Kwanaki biyu Biyamuradi yayi yana tsara abunda ya dace na daga sabon kuɗirin sa , da tunda ya samu gamsassun bayanai daga bakin likitan Mama ,
Ya dangana da nema mata lafiya a yanzu domin babu damar yi mata dashen ɓargo ko juyen jini da zai iya bata waraka , dole zasu cigaba da haƙuri tare da kula da ita , tana shan magungunan ta har zuwa wasu shekaru nan gaba da za’a samu wani cikin ‘yan’uwan ta da zai isa sadauƙar mata da ɓargon sa .
Tun a washegarin ranar ya koma asibiti ɗauke da sabon ƙudirin sa bayan dogon nazari tare da kai komo a ƙarshe zuciyar sa ta amince ya haƙiƙance cewa zai kai Falmata ga Manyan likitocin ido dake Mayo clinic su duba ta , idan tana da rabon gani shi zai yi iyakar ƙoƙarin sa wajen biyan kuɗaɗen da za’a buƙata domin yi mata aiki zuwa kan magunguna domin samun warakar ta .
Babu shakka Falmata ta cancanci duk wata kulawar sa duba da yadda take nuna ƙauna ta haƙiƙa ga gudan jinin sa da yake da tabbacin ko mahaifiyar Mama baza ta so ta sama da son da Falmata take yi mata ba ,1
Sannan akwai wani abu da shi yake ji game da Fatima da ya kasa fasaltawa a zuciyar sa sai dai yana yawan sakawa a ransa cewa saboda irin kulawar da take yiwa ‘yarsa ne.2
STORY CONTINUES BELOW
Bayan haka Halin mutum yana zama tsani wajen samarwa da mutum Alkairi ko akasin sa ,
halayen Fatima mafi yawansu masu kyau ne , ƙwari yake yabawa da Yakanah tare da Nagartar dake gare ta .
****
Yau ne Alƙawarin sa da Sabon likitan da zai Fara duba Falmata wacce bata kai ga sanin ƙudirin sa ba , domin bai kai ga sanar da ita ba .
Kasancewar ƙarfe uku na yamma shine lokacin da zasu ga likitan hakan ya sa shi fita sayo musu hot chocolate Su sha kafin fitar su domin zai taimaka wajen rage musu jin matsanancin sanyi .
Da Sallama ya tura ‘yar ƙofar ya shiga inda ya tarar da su a zaune yadda ya fita ya bar su , da ɗan gudu Mama ta taho gurin sa
“,Bienvenue Papa, que m’as-tu apporté? (sannu da zouwa Papa me ka kawo min ?)
Rungumar ta yayi suka ƙarasa kan doguwar kujerar da Falmata ke zaune fuskar ta ɗauke da siririn murmushi ,
“, Sannu da dawowa Baban Mama ,
“Sannu da hutawa Maman Mama , yace da sigar zolaya yana kallon fuskar ta
Hot Chocolate ɗin ya ciro musu gami da sanya ‘yan chokula ya sakawa Falmata nata a hannu,
Ya ɗauki Mama ya ɗora a cinyar sa ya shiga bata a baki tana kurɓa a hankali
Shiru ne ya biyo baya ,
ɗumin shayin da aka yi shi da garin koko ( cocoa ) da damammiyar Madara mai zafi yana ratsa sassan jikin su daɗin sa kuma yana basu nishaɗi , da yasa Falmata bata farga da tayi shan haɗama ba sai da ta ji ‘yar robar hannun ta sakayau , ta kai chokalin baki , taji bata ɗebo kome ba .
Biyamuradi Youssouf wanda duk idanun sa ke kan ta ya ga irin shan da tayiwa chakulan ɗin, ya kai hannu a hankali ya zare robar daga hannun ta tare da musanya mata da nashi wanda bai kai ga fara sha ba ,
“, Fatima bois ça aussi ( ki sha wannan ma )
” Baban Mama na ƙoshi fa , nagode .
Ta furta hakan tana jin kunya na taso mata ,
Murmushi mai sauti yayi , ganin yadda gefen bakin ta ya ɓaci ,
ya kai hannun sa kusa da fuskar ta , hannun sa na sauƙa a jikinta ta jaa baya da sauri tare da ajiye robar hannun ta ,
“Dakata Fatima , repérer zan ɗagga miki daga fuskar ki ,
Babban ɗan yatsan sa ya kai gami da goge mata gefen bakinta inda hot chocolate ɗin ya sauƙa bata sani ba .
Kanta a ƙasa tace
“Nagode .
bai amsa ba illa ɗibar chakulan ɗin da yayi ya kai bakin ta ,
” amshi lait au chocolat chaud ,
buɗe bakin ta tayi cike da kunya ta karɓa ,
“zan iya sha da kaina .
tace masa muryarta can ƙasa ,
yayi kamar bai ji ta ba , tare da cigaba da bata a lokaci guda shima yana sha , bata sha dayawa ba tace da shi ta ƙoshi ,
STORY CONTINUES BELOW
cikin nishaɗi ya shanye sauran , yana ƙurewa fuskar ta kallo da take sumul babu ɗigon ƙwalliya ,
Bayan sun gama , yace mata
“Fatima zamou fita zouwa hospitalisé ku shirya yanzou ,
” Baban Mama zamu sake ganin wani likita daban ko ? Wannan bai ƙware ba sosai ya zai ce cutar Mama bata warkewa bace ? akwai ciwon da bashi da magani ne ?
da wani irin yanayi yake dubanta yadda take maganar cike da son samun warakar Mama ya taɓa ransa , ita bata da wani sauran buri ne a rayuwa da ya wuce lafiya tare da walwalar Mama ? Bata yiwa kanta wani shiri ko tanadi ? Bata da wani buri ne na gina tata rayuwar ?
” Doctorat gasskiya ya faɗi Fatima , cutar Mama batta maganin waraka a yanzou sai fa kou ɗaya bissa hanyoyin da ya faɗi da kouma babu dama a yanzou , ba bissa lafiyar Mama zamou tafi hospitalisé ba ,
Shiru tayi ranta babu daɗi , yaya zai ce babu hanyar samun warakar Mama , shi baya irin tunanin da ita take yi ne ? Meyasa bazai yi wani yunƙuri ba domin taimakawa gurin samar da yadda zasu yi su tsaretar da Mama daga wannan ciwon me azabtarwa , ?
So take tace masa akwai hanya mana , sai dai tana cike da tsoro , da jin nawi tare da zargin ko matsayin da take da shi a wajen sa bai kai wannan matakin ba , mafi girman lamarin ya tambayeta ƙarin bayani , to tace da shi me ? Ko a mafarki bata jin ta san amsar da zata iya ba shi .
Cikin sanyin jiki ta tashi , da gudu mama ta sauƙa daga jikin Baban ta ta zo ta kama hannun Falmata , sannu kan hankali tayi mata jagora zuwa ɗaki ,
Ajiyar zuciya ya sauƙe bayan shigewar su ɗaki , bai ji daɗin sanyin da jikinta yayi ba kan amsar da ya bata ,
Mayo clinic
Doctor Omer Berat ɗan asalin ƙasar turkiyya ( Turkey ) da aiki ya kawo shi Amurka , shine ƙwararren likitan ido da zai duba lafiyar Idon Falmata ,
Bayan sun shiga wajen sa tare da taimakon na’urar fassara yare suka gaisa ,
Babu ɓata lokaci ya nemi da ya fara zantawa da marar lafiyar sa ,
A hankali Youssouf ya kamo hannun Falmata da take zaune a kujerar da take fuskantar ta shi yace ,
“Fatima ki saurara da kyau likita ke son yin magana da ke kan lafiyar ki .
” Lafiya ta ko ta Mama ?
“Lafiyar idon ki Fatima .
Ya amsa yana sake tabbatar mata ,
Mayar da hankali tayi ga likitan lokacin da ta ji ya ƙira sunan ta ,
Ta amsa , tana mamaki daman ita ya kawo asibitin a yau ?
Tambayoyi ne sosai Likitan yake yi mata da mafi yawan su Falmata bata da takamai-mai amsar su domin tambayoyin sun shafi asalin dalilin sumuwar rashin lafiyar idon nata da ita bata sani ba , amsar da ta bashi a ƙarshe ita ce
” Je ne sais pas, je viens de vivre dans la cécité , mes parents sont morts sans me dire à quel point j’étais aveugle . ( nima ban sani ba kawai na tsinci kaina cikin rayuwar makanta kuma iyayena sun mutu ba tare da sun bani labarin yadda makanta ta ta samo asali ba . )
Biyamuradi Youssouf da amsar ta ta taɓa masa zuciya , ya sake runtse hannun ta cikin nashi , yana jin yadda tausayin ta ya kawo masa .
STORY CONTINUES BELOW
bayan ɗan guntun rubutun da likitan yayi ya umarci Falmata da ta zo kan ɗan wani gado da yake daga gefe a ofishin ya duba idanun nata ,
Har bakin gadon Biyamuradi ya kama hannun ta , ya kaita tare da kama mata ta hau gadon ta kwanta ,
Doctor Omer ya haska ƙwarar idanun nata da penlight , ya ɗora da tambayar ta ko ta ga haske ? Tace ita bata ganin kome ,
Cigaba yayi da haska idon yana dubawa , a ƙarshe ya kunna slit-lamp ya dallare mata ido da haske ,
Wani irin kaifi ta ji ya soki idanun ta da ya sata kifta idanun da sauri tare da kai hannu biyu ta riƙe kanta da ya sara mata ,
“washh kaina .
” Sannu ‘, ita ce kalmar da Youssouf ya furta da sauri yana riƙo hannuwan nata ya sauƙe daga kan ta ,
Bata amsa ba illa riƙe hannun sa da tayi saboda yadda har yanzu take ji ba dai-dai ba a ƙwarar idanun ta .
Bayan likita ya gama dube-dube a ainashin cikin ƙwarar idanun ta ,
Biyamuradi Youssouf ya kamata suka dawo wajen zaman su suna fuskantar likitan da yake rubuce-rubucen sa cikin kwamfiyuta ,
Turo ƙofar ofishin akayi wata mace ta shigo , babu ɓata lokaci ta jagoranci su Youssouf zuwa wani sashi na daban inda aka yiwa Falmata hoton ƙwarar ido aka tura ga sakamakon ga Likitan ta ta kwamfiyuta kamar yadda ya turo musu da bayanan irin hoton da yake so su yi mata ta kwamfiyuta .
Kafin isowar su hoto tare da bayanan da duk suka dace sun riga sun iso masa , dan haka bayan ya kammala binciken sa , ya zunkuɗa yana mai gyara zaman gilashin idon sa , ya shiga yi musu bayani dalla-dallah cikin turancin sa yayin da su kuma pilot-in-ear yake fassara musu cikin faransanci ,
Iritis shine ciwon da ya haddasawa Falmata matsalar idanu da har ya kai ga ta rasa ganinta , shi iritis wata cuta ce da take samun ƙwayar baƙi/brown na tsakiyar idon ɗan adam , da take kumbura ƙwayar idon , sa ciwon ƙwayar idon da disashe gani ,gaza ɗaukar haske da sauran matsaltsalu da dama ,
wanda ake iya samun sa ta hanyoyin da suka haɗa da ƙwayoyin cutar maɗamfari ( infection ) , jin ciwo kai tsaye ga cikin ido , kamar bugu zuwa ƙwarar ido na daga kowanne irin abu , da kuma cutar da take kama ƙwayoyin halitta na jini tana kashe su.
Bayan dogon bayanin da likitan yayi musu ya ɗora musu da bayani kan matakin da cutar ta kai ga idon na Falmata wanda rashin samun maganungunan da suka kamata a kuma lokacin da ya dace , ya kai ga ta rasa ganin ta na tsawon wasu shekaru sakamakon mutuwa da wasu daga cikin jijiyoyin ƙwarar idon suka yi .
kai tsaye bazai yuwu ba ganin ta ya dawo kamar na sauran mutane masu lafiya , duk da cewa akwai yuwuwar kaso ɗaya bisa uku na ganin nata ya dawo tare da taimakon magunguna da allurai zuwa kan aiki na musamman da za’a iya yi mata a idon idan har magunguna da alluran basu taimaka yadda yakamata ba , wanda zai ɗora ta akai da zarar ya kammala binciken sa a yau .1
Cigaba yayi da yi musu bayani har zuwa lokacin da ya tabbatar sun samu gamsuwa sun kuma fahimci duk bayanan da yayi musu ,
da kan shi ya jaa jinin Falmata ya fita da shi zuwa ɗakin gwaji saboda ya auna ya san irin magunguna da alluran da suka dace yayi mata bisa ga mataki na farko .
Basu bar asibitin ba sai da aka mata allurai biyu ta babbar jijiyar hannun ta tare da yi mata ɗaya a jijiyar da take daf da idonta na dama ,
Ba ƙaramar juriya ta nuna ba wajen tsayuwa da tayi cikin nutsuwa aka huda mata jikinta babu zilliya bare ihu da hatta shida kansa likitan sai da ta burge shi sanin da yayi allurar gefen idon tana da zafi ,
Ya dube ta bayan ya ƙare mata allurar gefen idon ,
” sorry It’ll hurt but just for a few minutes .
STORY CONTINUES BELOW
Gyaɗa kai tayi tana jin yadda idanun nata suka yi nawi ga wani irin yanayi marar daɗi da take ji a idon ,
” Baban Mama , ta ƙira sunan sa tana lalubar hannun sa ,
Da sauri ya riƙo ta
” Na’am Fatima , sannu kina jin ciwou ? comment vous sentez-vous en général ? ( How are you feeling overall ? )
” Idona yayi jini ne ?
“bai yi jini ba Fatima , sannu .
****
Misalin ƙarfe tara na dare suka bar asibitin bayan sun ci abinci sama-sama daga kitchen ɗin cikin asibiti .
Suka yi bankwana da likita omer bisa ga yarjejeniyar sake dawowa asibitin nan da kwanaki huɗu masu zuwa , bayan ya haɗasu da mugunguna ɗore da dokoki da sharuɗɗan da ya gindaya musu .
Baki ɗayan su sun gaji Mama tayi bacci a jikin Babanta , Falmata kuwa tsukun da idanunta ke yi yana damunta wanda yake ta zubar hawaye , gaba ɗaya bata jin daɗin kome ,
damuwarta ta tayar da Hankalin Youssouf da yake amfani da kalmomin rarrashi iri-iri yana jera mata sannu , har suka dawo gida , kai tsaye ya zarce da mama ɗakin baccin su ya kwantar da ita ya lulluɓa mata bargo tare da kunna hutar ɗumama daki ya fito falo inda ya tarar da Falmata ta rufe fuskarta da hannu biyu , ta jingina kanta da jikin kujerar da take
A sanyaye ya ƙaraso wajen fuskar sa na nuna damuwa ƙarara ,
Zama yayi a kusa da ita jikin sa na gogar nata , ya kai hannu a hankali ya sauke hannun ta daga fuskar ,
Hawayen da idanun ke yi ya goge da hankicif ɗin da ya zaro a aljihunsa ,
“Fatima yaya ne ? Ciwo ne har yanzou ? Kou zamou koma ga doctorat ?
” Baban Mama idanuna ciwo suke kamar zasu fita , idona bai taɓa ciwo haka ba , bazan warke ba kar kayi asarar kuɗi dayawa , lafiyar Mama yafi samun lafiyar idona muhimmanci kuma ..1
” Shittt , yace yana kai hannun sa kan ɗan bakin ta .
” Fatima baki ji abounda Doctorat ya faɗi ba ? Zaki warke ko ba du ba , waye ya faɗi miki zata zam asara doumun nayi jinyar ki daga jakka ta ?
” kiyi ta addu’a Allah shi sa a cimma nasara bissa ga neman lafiyar ki kin ji kou ?
Shiru tayi , ita ganin zancen likitan take soki-burutsu tayaya idanun ta zasu fara gani ? Bayan a iya sanin ta bata taɓa ganin hasken duniya ba .1
Muryar sa ta katse tunaninta “
Kou baki so watarana ki ga fuskar mijinki ? Kou baki so watarana ki ga fuskar ɗiyar ki Mama tare da ‘ɗiyan da zaki haifa nan gaba ?
Jin ya sosa mata inda ke yi mata ƙaiƙayi sai ta ɗago kanta , ‘
” inaso , amma nafi son na samu ɗa domin ya sadauƙar da ɓargon sa ga Mama , ta warke kamar yadda likita ya faɗa ,
Sai yayi shiru yana kallon ta da taimakon hasken da bai cika yawa ba da ya hasko daga jikin ƙwan fitilan dake ajiye saman teburin gaban su ,
zancen ta ya zo masa a bazata , ya ratsa ƙwaƙwalwar sa a jirkitatcen yanayi da ya kasa tantancewa .
Ita ma shiru tayi cike da fargabar kasassaɓar da tayi , kada dai tayi masa laifi ? Ko dai zantukanta basu dace ba ? Tayi masa tsaurin ido ko ?
STORY CONTINUES BELOW
Sauƙar hannun sa cikin nata ya katse mata tunanin zucin da take yi ,
“Fatima mu tafi muyi sallar isha’i kiyi kwana (bacci ) dare yayi ,”
A sanyaye ta amsa da “To,
Har suka kwanta bacci babu wanda ya kuma magana kowanne a tsakanin su yana tunani,
Wayar sa ce tayi ƙara alamar shigowar ƙira , da azama ya ɗauka ganin wacce ke ƙiransa ya sanya shi miƙewa a hankali ya nufi ƙofar ɗakin , ya zo fita ya juya gami da kai kallon sa kanta da tayi lamo cikin bargo kamar mai bacci ,
ajiyar zuciya ya sauƙe ransa cike da tunaninnika barkatai ya fita gami da jaa musu ƙofar ,
Falmata wacce duk motsinsa a kunnen ta , ta miƙe zaune gami da yaye bargon , cikin ranta sam babu daɗi gani take kamar ta ɓata masa rai da maganganun ta tunda gashi daga lokacin bai sake cewa da ita kome ba , ko fushi yayi ?
Tashin muryar sa da yake magana kamar a gabanta “kasantuwar ta mai buɗaɗɗen kunne ” ya sa ta saurarawa zagayayyar fuskarta na bayyana wani yanayi irin na wanda aka shammata lokacin da taji yana cewa ,
“bonjour ma princesse comment allez-vous aujourd’hui mon amour? ( Alo gimbiyata yaya kike yau masoyiya ? )
Cigaba yayi da cewa
“Je vais très bien et tu me manques aussi , ( ina lafiya lau nima nayi ƙewar ki )
Ƴar dariyar nishaɗi yayi , kana ya cigaba da cewa ,
” wannan kalma ke kin ka faɗe ta , ni kouwa gurina ba haka ne ba , duk wani bigeren da babu ke cikin sa wajena daɗin sa ragagge ne , babu kome anan sai matsanancin sanyi tafe da tarin nawi da wahalwalu bisa kaina ,
Murmushi yayi mai sauti ,
” a gida nake Yarima , ga gurin aikina kuma Mai muƙamin Major , nan kuwa ai ban wucce matsayin bawa dake hidima ga wassu rayukan ba ,
Gicciyewa yayi ya kishingiɗa yana me cigaba da sauraron ta ,
” ba domin yanayi da bashi yiwuwa na taho da ke ba, kin sani ban iya tafiya ga nissan duniya batare da ke gefena ba maimounatu ke ai sashi ce daga jikina ,
Falmata da take sauraran sa , sai ta koma ta kwanta tare da lulluɓuwa ta cure jikinta guri ɗaya ga barin sauraran zantukan sa , zuciyarta ke wani irin bugu da yake tafe da zallar tashin hankali ,
Sunan wacce aka ƙira da Maimounatu tare da irin Kalmomi masu daraja da aka mallaka mata , sun gaftare tare da ruguza duk wani ɗan guntun tunanin banza da ta fara yi ,”Ah to na banza mana , tunda ‘yar kulawar da yake bata ya sa ta hasashen hawa wani matsayi da bata kai shi ba a wajen sa ashe ita ɗin ba kome bace face tarin nawi da wahalhalu .
Hawaye masu ɗumi suka gangaro daga idanunta suna ɗiga bisa hular sanyin kan Mama .
Maiduguri Nigeria
Tun ranar da Doctor Hamza ya gargaɗi Yakaka akan kada ya sake ganin fuskarta bata sake bari sun haɗu ba ,
Ko muryar sa ta ji yayi Sallama da shi bai cika shigowa ma sashin nasu ba , da sauri zata nemi gurin ɓuya , duk cewa tun daga ranar duk lokacin da ya buƙaci abinci daga Rahima ita take girka masa , sai ita kuma Rahima ta kai masa .
Yau Asabar ya shigo gidan da safe misalin ƙarfe tara shirye yake tsaf cikin shirin sa na zuwa ɗaurin auren ƙanin Abokin sa .
STORY CONTINUES BELOW
Yana yin Sallama , Yakaka da take goge Falon bayan ta gama sharewa tayi saurin ajiye moper ( mofi ) ta tsallaka da ɗan gudu ta shige ɗaki ta rufo ƙofar ,
Hajja da take zaune a gefe tana karin kumallo ta harari bayanta ta wutsiyar ido kafin ta taɓe baki ,
” Ni hauwa’u naga abunda yafi ƙarfi na , ke kenan kullum a tsalle-tsalle da guje-guje ? Uwa wata tunkiyar da take rawar turke ? Allah ya kyauta .3
Washe baki tayi tana dariya ,lokacin da Doctor Hamza ya shigo
” a ah kaga manya ɗiban farko , Babban likita ,
Fuskar sa ɗauke da murmushi suka gaisa , ba tare da ya zauna ba yace
“Hajja ina Rahima ?
” Yanzu ta hau sama , a ƙira ta ne ?
” a ah yi zaman ki Hajja idan dai ta fito ace ta min girki kafin dawowata ta kai min ɗakina .
” To babu laifi zan faɗa mata .
” Nagode Hajja .
Ya juyawa da nufin fita idanun sa suka sauƙa kan Hoton Mama da tun ranar da ya fara ganin hoton yake son tambayar Rahima ‘yar waye ? Ƙwarai hoton yarinyar yake fusgar hankalin sa ,
Dan haka ya dawo da baya yana tambayar Hajja ,
” Hajja wannan ‘yar waye haka aka samu kyakkyawa ?
Da dariya Hajja ta amsa masa
” ‘yar wajen Fatima ce , Mama sunan ta ai sun ma yi tafiya ne can Amurka ita da iyayen nata .
“Fatima ?
Ya maimaita ,
” wacce Fatima Hajja ?
” Ƙanwar wannan yarinyar Yakaka take ko wa ?
‘okay ,
Ya amsa yana barin wajen ba domin ya gane wacce ake nufi ba kai tsaye sai dan ƙiran sunan Yakaka da Hajja tayi .
ƙarfe biyu na rana suka shirya tafiya gidan Amne su Uku Rahima , Yakaka da kuma Hajja da itama tace zata je .
Shatar shatar adai-daita Rahima ta ɗaukar musu wanda ya tokare daga bakin hanya yaƙi gangarawa kwarin unguwar a cewar sa gargadar cikin unguwar zai ɓata masa mashin , dan haka dolen su suka sauƙa Rahima tana ta mitar wahalar tafiyar da zasu yi a ƙafa kafin isar su gidan .
Da wani tasowar sabon yanayi a zuciyar Yakaka take bin unguwar da kallo , unguwar da ta zama tushe na hargitswar rayuwar ta da bata tsinci kome a ciki ba illa wahalhalu da tarin abubuwan ƙi , unguwar da suka sha gwagwarmaya a cikin ta ita da ƙanwar ta da ƙawarta Yagana ko ina yagana take a halin yanzu ? Wataƙila ita rayuwa tayi mata kyau , tayi aure ta fara ginin rayuwar ‘ya’yan ta .2
tunaninta ya katse lokacin da Rahima ke cewa su gangara ,
Tana bin layin tana tuno da haɗuwar su da Doctor Hamza a bakin layin ana ruwan sama ,taimakon da yayi mata a ranar da ba domin shi ba da ta faɗa babbar kwatar taji mummunan ciwo ko ma ta rasa ranta ,
“Allah sarki yaya dakta ,
Ta furta hakan daga ƙasan ranta lokacin da suke miƙawa cikin layin .
STORY CONTINUES BELOW
Daga nesa ta fara jiyo hargowar sa muryar sa a sama yana rantse-rantse , domin ta tabbatar da shi ɗin ne ? Tayi saurin ɗaga idonta ta ɗora a kan sa shi da wata matar da kallo guda tayi mata ta gane yanayinta na matan banza ,
Da sauri ta ɗauke kai tana ɗan jawo hijabinta gaba kaɗan , zuciyarta cike da fatan Allah ya rufe masa ido ya wuce bai ganta ba bare ya gane ta.
cikin rashin sa’a hasken da take da shi ya riga ya ɗau hankalinsa kasancewar sa kawali idanun sa koyaushe akan wankakkiyar mace yake babu ruwansa da matsayinta na matar aure ko akasinta .1
Sun ƙaraso gaf da juna ya jaa ya tsaya , kafin ya ɗau salatin da Hajja ta ƙarasar masa ,
Sauri yayi ya zagaya ta sashin ta ya dogare , yana kallon fuskar ta da taƙi yadda su haɗa ido ,
Dariya ya kwashe da ita yana tafa hannuwan sa alamun mamaki yace ,
“Ahayye nanaye ke duniya mai abun mamaki ? Yanzu duniya da gaskiya Yaks kƴa ga Ɗanliti ki ɗauke ido ki kawar da kai ? Lalle Yaks kin zama kaza ci ki goge bakin ki , Ko da yake ai kome kika yi ba mamaki tunda baki da shayin kowa .1
Yakaka ta saci kallon Hajja wacce tayi saƙare tana bin Ɗanliti da kallon banza ,
” Ɗan-Ɗan liti ya kake ?
” Ras nake Yaks .
Yayi fari da ido kafin ya ɗora da
“Ke kuma fa ? Ya na ganki haka da Bargo yaro-yaro kina yawo kadda dai kice min kin yi ƙarkon kifi , ? Kin fito daga ruwa kin faɗa wuta ? Yo ai kuwa da kin ɗibga asara a duniyar nan Yaks ace dai wai mace hamshaƙiya kamar ke kina yawo a ƙuɗunɗune cikin hirami yake ko hijabi ko jallabiya ? Bani sunan sa ɗaya .3
” Ubanka yake nace Ubanka yake shashasha , wofin wofiyo banzan banza , yau ga ɗa ya zama lalatatce bayan an kashe ragon suna , to Allah ya shirye ka , ke un-un Yakaka wuce muje .7
Hajja ta furta hakan tana huci tare da yiwa ɗanliti daƙuwa da hannuwanta duk biyu , ta ƙarasa zancen da fusgar hannun Yakaka ,
Buɗe baki Ɗanliti yayi da mamaki ,
,” Ke tsohuwa , ki kiyayeni ki kiyayen nace da zaki zo ki shiga cikin maganata dake nake ? Nace da ke nake ? Yo Allah na tuba ke a zamanin ki waye ya san irin tsiyar da kika shuka ta rawar banjo da kiɗan gurmi daga ke sai ɗan kanfai ? Ko da yake wannan baƙin naki uwa shuni ba wani tasiri kika yi ba ko a wajen su garbati mai kalangu . ,3
“,Na rantse kin ci darajar yaks domin ni na falle tsohuwa da marin da zai sa ta ga star abune mai sauƙi a wajena , gaba ki kiyaye kin ji na gaya miki .
tsaki Hajja tayi suna barin wajen ,
” Allah ya shirya ka zindiƙi .
Shima ya rama Hararar da tayi masa ,
” waye yake ta taki tsohuwar guzuma , Yaks Ki samu lokaci ki leƙo mu akwai labarai da hanyoyin arziki masu tarin yawa , af na manta na faɗa miki uwarɗakin fa bata da lafiya…
Bai ƙarasa zance ba yayi shiru ganin sunyi nisa ,
” ji min tsohuwar nan zata yaɓan magana wai nine zindiƙi ? Tsohon ki ne dai zindiƙi aikin banza .
3
****
Da sallama suka shiga gidan Amne , tana zaune kan barandar ta tana ƙunsa lalle a ƙafafunta da basa rabuwa da ƙunshi ,
Tayi mamakin ganin su saboda Rahima bata sanar da ita zuwan nasu ba ,
ta tare su da fara’a tana yiwa baƙi barka da zuwa , idanunta da hankalinta baki ɗaya akan yakaka .
Bayan sun gaisa ta dubi Rahima ,
” aina kika sake samo min mai kama da Rahima ta ? Da ace shekaru basu jaa dayawa ba zan iya cewa Rahima ta ce wannan ,
” dariya Rahima tayi , Amne baki gane ta ba ko ? Yakaka ce fa , ‘yar gudun hijarar da suka zauna a gidan mu shekarun baya da akayi zaton ta rasu wajen haihuwa ?
duk da ba wani jimawa tayi da yaran ba amma sunan su ya tsaya a ƙwaƙwalwar ta ,
” Yakaka ke ce ?
” ni ce Amne ,
” Alhamdulillah ashe Yakaka kina raye ? Ina kika tsaya tsawon lokacin nan ? Ina ƙanwar ki tare da ‘yar ki ?
hannun ta ta ɗora akan na Amne da ta miƙo mata su , fuskar ta ɗauke da murmushin jin daɗin zallar ƙaunar da ta hango a idanun Amne ta matso kusa da ita ,
“Falmata su na America wai .
Hajja tace ,
” Wai ne ma ? ai ya wuce wai .,
Amne bata tsananta tambayoyi ba ga Yakakar domin ta bata damar sakewa ,
Lallen da Amne take sawa ta karɓa , tare da cewa
” kawo na sa miki Amne .
tana murmushi ta miƙa mata ‘yar robar da lallen ke ciki , ta shiga sanya mata sannu kan hankali ,
da sauri Rahima tace
“Daman kin iya lalle ne Yakaka ?
tana murmushi tace ,
” ko ban iya ba zan koya a ƙafar Amne .
Hajja da Amne suka cigaba da hirar su ,
zuwa lokacin da Rahima tace ,
” Yauwa Amne ki nunawa Yakaka Hoton Khaalty Rahima da kike cewa suna kama Yakaka tana son ganin ta…
“eh Amne ina son ganin Khaalty Rahima , Yakaka ta furta hakan cike da ɗoki ..