KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 8 BY ayshay bee

KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 8 BY ayshay bee

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sallama Fati ta fara musu, Umar ne ya amsa ya na kallon Aliyu. A tare su ka gaishe su dukkan su biyun, faran faran Umar ya amsa sabanin Aliyu da ke ta faman danna wayan shi kasa kasa ya amsa gaisuwan nashi.

Wani kallo Umar ya mai ba shiri ya sa wayan cikin aljihu sannan ya mike ya rufe motan.

  “Sannun Ku fa, mun same Ku lfy?” Ciki ciki ya fada kaman an sa shi dole fati ya ke kallo kuma itan ce ta amsa mishi ga me da tmbyn shi aiki shi ma ya tmby karatun su.

Zahrau dai kanta na kasa kaman wurin Fatin aka zo ta rakota.

“Zahrau” Umar ya kirata, nisan da tayi a duniyan tunani ne ya sa ba ta ji kiran ba sai da Fati ta tabo ta. Firgigit, ta dago tana kallon fatin, nuna ma ta Umar ta yi “yana magana”

“Haka kike irin wannan tunanin ke da baki da lfy Zahrau, so kike ki jawo wa kanki wani matsala ko?” Umar ke maganan yana kallon Abokin shi da yayi shiru yana sauraren shi.

Murmushi ta yi sannan ta amsa “Yaya Umar ba fa tunani na ke ba banji ka ba ne” shima murmushin yayi sannan ya ce ma ta “to shknn tunda kince hakan, Kaman yanda kika sani wurin ki mu ka zo musamman dan mu baki hakuri, ko shakka bbu kowa ya San an dauki hakkin ki ba kadan ba. Maganar gsky shi aure ba abun wasa bane abinda ya ke sunnar mazon Allah (SAW) sannan kuma har iyaye su ka shigo ciki to wlh matukar kuna son ganin cigaba a rayuwanku sai kun ajiye makaman yakin Ku kun rungumi kaddarar Ku da hannu biyu, Nasan Aliyu ke da laifi Zahra sai dai ke ma kin matukar ba da gudunmowa akan laifinnasa. Dukkanku mu nan mun San gskyn zance kenan so is better you face your reality” Kaman ko yaushe Zahrau kan ta na kasa Aliyu ko lumshe idon shi yayi yana sauraran Amininsa.

Alama Umar ya ma Fati su ka je gefe su ka bar su su biyu a wurin.

  Sun kai minti biyar a tsaye ba Wanda ya iya ma wani magana hasali ma kowa da wurin da ya ke kallo. Sake sake Aliyu ke ta faman yi a zuciyan shi yana kuncewa, har ga Allah bai san ran shi bai son abinda ya ke shirin aikatawa amma ya ya iya this his only option, ya riga yayi Na’am akan rungumar auren Zahrau ko dan samun Albarkar iyayen shi ba wai dan akwai ko digon son ta a zuciyan shi ba, gani ya ke an zubar mai da class in shi ne dan yafi karfin ya so wannan mitsitsiyar yarinyar amma ya zai yi this is his only solution.

A hankali yayi gyaran murya sannan ya juyo yana kallon ta tabbas ya San ba za ta yi magana ba don da alamun ta fishi miskilancin ma “Zahrau” a hankali ya kira sunan na ta ta yanda za ta jiyo.

Dan dago ta yi ta kalle shi sannan ta sadda kanta kasa, ita ma a hankalin ta amsa da” Na’am “

  “Ki dago ki kalle ni za mu yi magana”

Sarai ta San shi da saurin zuciya hakan ne ya ke ja mata duka a wurin shi tun tana karama tsoron kar ya mata wani abu gaban mutane ne ya sa ta yi saurin dago da kanta tana kallon shi.

“Ba ki ga text INA ba ranar?” Shiru ta yi dan ba ta San me zata ce mishi.

Harara ya bi ta da shi sannan ya ce “sarai kin San hali na kar ki kaini bango, please ki yi hakuri ki bani amsa kafin a samu matsala” for the first time a rayuwan ta taji ya ambaci hakuri sai dai burin ta bai wuce ta daina ganin shi ba right now, jikin ta ko har rawa ya ke tsabagen tsoro da ke daman ita gwana Ce.

Sanin saurin zuciyan zai iya kai shi ya baro ya sa ya bata hakuri su rabu lfy already daman a wuya ya ke coz he hate what he is doing right now.

“Ban ban San kai ba ne” dariya ta bashi yanda ta yi maganan a tsorace amma kuma bai bar dariyan ya fito ba ya tsare gida “calm down magana kawai za muyi. firstly, kiyi hakuri da duk abinda na miki a baya kina kai ni bango ne and kinsan ban San raini shiyasa, maganganun da na fada miki kuma su ma cikin fushi ne haushi na nake hucewa akan ki so am sorry pls. Kaman yanda ki ka Sani both of us ba son auren nan muke ba but at least let us give it a chance ba mu San abinda Allah ya boye ba” a firgice ta dago tana kallon shi ko kadan ba ta taba expecting maganan zai iya fitowa daga bakin uncle Aliy ba.

Sarai ya gane abinda ta ke nufi hakan ya sa ya dan dara sannan ya ce “expect the unexpected life is always changing same goes to situations” shiru ta yi tana Satan kallon shi sai dai wannan karon ba mamakin abinda ya fada ta ke ba illa mamakin yanda ya ke gani duk abinda ya zaba shi za a yi, there is no doubt he is selfish. Ya gama ma ta wulakancin da ya ga dama yanzu kuma ya dawo yana tunanin su shirya lfy kalau, if he is okay with it ita an fada mishi she is.okay ko kuma shi kadai ke da feelings? Ba ta gaa tunani ba ta ji yana fadin “Maganan kenan daman dare nayi ba ra mu tafi, we will talk later”

Gaba daya daren tunanin halin Aliyu ta ke yi, shin in ma ta amince wani irin zama za suyi he is so selfish, infact she is not ready to accept him ma.

Haka dai ta cigaba da bin shi duk yanda ya so duk bayan kwana biyu za aiko mata da text yana tmbyn lafiyan ta da karatun ta iya ka ta mai reply da lfyn ta kalau ta gode shknn.

2 months later

  Zaune ta ke gaban Yaya deedat yana mata bayani “am so sorry sister ban fada miki ba amma industrial attachment inki Abuja na nema miki har sun yi approving”

  A firgice ta juyo tana kallon shi “Yaya Deedat ina zan zauna a Abuja”

  “Gidan mijinki” ya bata amsa hakan ya sa ta yi kasa da kanta tana cigaba da sauraron shi “Zahrau its high time you face reality, Nasan Ya Aliyu ya miki laifi but tunda yanzu ya nuna yana son ya goge laifin shi pls give him a chance aure ba abin wasa bane Zahra. Just get to know your husband he is so nice kuma lada ma zaki samu”

“Tohm shknn” ta amsa ba wai dan ta so sai Dan ba za ta iya mishi musu ba

“Shknn in kinje Abujan zai kai ki asibitin”

Zaune ta ke a falon mami tana karanta littafi a watt pad, Sallaman da taji a bakin kofan dakin ne yayi nasarar janye hankalin ta daga gun littafin. Ido hudu su kayi dashi saurin dauke idanun ta tayi “INA wuni” ta fada kanta a kasa “lafiya kalau Mami na cike ne” ya bukata

  “Tana kitchen” ta bashi amsa sannan ta cigaba da abinda ta ke.

  Hanyar kitchen in ya nufa, ya dade suna magana da mami sannan ya dawo falon “Ki zo Mami na kiran ki” ya fada yana kallon ta, ba yanda ta iya mikewa tayi ta bishi zuwa dakin mamin.

  Dukkan su biyun a kujeran da ke dakin mamin su ka zauna, kallon ta bi su dashi dukkan su sannan ta mai da kallon ta gun Zahrau “ke kunyi da Aliyu za ki bi shi ne?” Mami ta tmby tana kallon ta, shima Aliyun kallo ya bita dashi yana jiran mai za ta fada, daga inda ta ke tana iya hango shi da ke kujerun na kallon juna, harara ya fara aika ma ta hakan ya sa tayi saurin canja zuciyan ta kan abinda ta yi niyyan fada daga farko tunda shi gani ya ke takaman shi ke yi mai komai “Aa Mami yau ma Yaya Deedat ya ke fada Abuja ya cika min IT letter na” ko kallon shi bata yi balle ta lura da irin kallon banzan da ya ke aika ma ta.

“Kai kasa shi ko Aliyu?” A duniya in akwai Wanda Aliyu ba zai iya wa karya ba to mahaifiyar sa ce”eh mami nine” ya bata amsa hade da sunkuyar da kai.

  “Toh ban amince ba” A firgice ya dago yana kallon ta “Mami me ya sa?”

  “Saboda ban yarda da kai ba Aliyu, ba za kaje ka hallakar min da Yarinya ba a gida ma ka illatata balle kuma ka kai ta inda daga kai sai ita”

Ajiyar zuciya ya saki “Sannan ya ce mami please wlh kuskure ne kuma ma ki tmby ta na bata hakuri”

  Girgiza kai tayi sannan ta ce “ka ma bar zancen nan, Abbah ma ba zai yarda ba shi kanshi ya sauke sharadin da ya daura ma ka yace raba Ku zai yi”

  “Innalillahi mami Dan Allah ki bashi hakuri” muryar shi na rawa ya ke maganar “wlh mami Abbah baki zai min in har ya rabu mu, kuyi hakuri mami wlh zanyi abinda kuke so”

  Kallo Zahrau ta bishi da shi ganin yanda ya rude sai yanzu ta fahimci dalilin da yasa ya ke ta bin ta sau da kafa ashe bacin ran iyayen shi ya ke gudu.

  Sallamar da Abbah yayi ne ya katsewa Aliyu abinda ya ke shirin fada. Kallon su yayi daya bayan daya sannan ya amsa gaisuwan da Zahrau ta ke mai, Aliyu ne ya gaishe shi maimakon ya amsa harara ya bishi dashi sannan ya ce “Daman INA Neman ka”

   Sunkuyar da kai yayi yana sauraran abinda Abbah zai ce  “bani takardan Zahrau” wani irin faduwan gaba yaji “Abbah Dan Allah…”

  “Dakata Malam” Abbah ya katse shi a zuciye da hannu “ban son wani magana, INA nina hada auren to na fasa tun farko ban San halayen ka bane that’s why bincike ya ke da kyau” A fusace Abbahn ke magana, Aliyu zai iya rantse wa bai taba ganin bacin ran shi ba irin na yau ba har ko lokacin case in farida.

  Zahrau dai kan ta na kasa ba zata iya cancance wani irin hali ta ke ciki ba farin ciki ko akasin shi ita dai yanzu shirye ta ke ta amshi duk abinda ya kutso cikin rayuwan ta.

  Mami ma kallon su kawai ta ke amma ko kyar ba ta ji tausayin Aliyun ba ya kamata ace shi dansu ya rufa musu asiri amma maimakon haka sai ya nemi tozarta su.

  Kasa ya durkusa gaban Abbah yana bashi hakuri amma ba ko kallon shi bai yi ba illa takardan da ya ke Neman ya bashi.Kiran Sallahn da aka yi ne ya katse musu draman da su ke yi, masallaci su ka nufa mami da Zahrau ma sallahn su ka tafi yi.

Zaune ta ke akan sallaya tana azkar bayan ta idar da Sallah a dakin da ya za ma nata yanzu a side in mami.

Sallaman da akayi a bakin kofar ne ya sa ta dagowa dan ganin wa ke magana…

Uncle Aliy ne, “wa’alaika Salam” ta amsa but still tana zaune akan sallayar “Ba za ki bani wurin zama ba” ya fada yana ma ta murmushin da ya zama bako a gare ta hakan ya sa ta jin abun banbarakwai. “Bismillah” ta fada tana nuna mishi kujeran dake dakin.

Kujeran da ke kusa da ita ya zauna yana fuskantan ta. “Zahrau Dan Allah taimakon ki nake nema” ya fada yana kallon ta alamun amsan ta ya ke jira, tana mamakin yanda Aliyu ke iya komai ya ga ya samu abinda ya sa a rai. Daga mishi kai tayi alamun tana jin shi.

Kallo ya bita dashi ganin yanda gaba daya jikin ta ke rawa, ko shakka bbu ya sa Zahrau matsoraciya ce sosai musamman ma shi da ya ke kaman dodo a wurinta. Ko ma ta ya za suyi zaman?

Ganin at anytime Abbah zai iya shigowa ya sa ya kauda duk wani tunani ya fara mata magana “ke kadai ce zaki roka min Abbah ya sauko da wuri so pls ki bashi hakuri” a hankali ta juyo ta kalle shi sai kuma ta yi saurin kauda kai “kinji” ya fada yana kallon reaction inta.

A hankali ta fara magana though da kaji muryan ta kasan a tsorace ta ke “kayi hakuri Pls Amma ba zan iya gardama da hukuncin da Abbah ya yanke a kaina amma in har ya tmby ni zan nuna mishi ba komai” tausayi Aliyun ya bata ganin yanda har ya sauko kasa yana Neman tainakon ta kwanan ba shakka yana gudun duk wani Abu da zai hada shi da mahaifan shi ita ma kuma ba zata so ta zamo sila.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dan ja tsaki, shin me ma ya kawo shi gun Zahrau bayan ya San ko da Deedat ya ce abu ba ta tsallake shi balle kuma Abbah.

“Zahrau, Aliyu” Mami ke kwalla masu kira, juyowa su ka yi duka suna kallon ta “Ku fito falo” kawai ta ce musu sannan ta wuce.

Ba hakurin duniyan da Aliyu bai ba Abbah amma INA ko kadan Abban bai sauko ba.

Yau dai duk jarumtar sojan sai da idon shi yayi ja yayi tagumi sai zufa ya ke hadawa. Daga Mami har ita kanta Zahraun da ake son kwato wa yanci ba Wanda bai ba tausayi ba.

Gashi Baffa ba ya nan balle ya sa baki.

“Abbah Dan Allah ka yi hakuri wlh ni bai min komai ba” kaman daga sama su ka ji siririn muryan na ta. Dukkansu kallon mamaki su ka bita dashi She hardly talks balle kuma a irin situation in nan.

“Ka ga ni ko tsakanin Mata da miji ai sai Allah” Mami ke fada wa Abbah bayan ya sallami su.

Wani ajiyar zuciya yayi sannan yace “ya dauki hakkin yarinyar dayawa gata Amana ce gare mu, wlh ba Dan ta sa baki ba sai na raba auren nan”

“Allah ya kyauta” kawai mami ta ce

Zaman musamman Mami tayi da Dan ta, nasiha ta mai sosai game da mai tuni da Zahrau amana ce a gare su. Jikin shi yayi sanyi sosai, kwata kwata ya kan mance da iyayen Zahrau n su rasu, gabadaya yaran gida a zaton su Ammah ta haife ta hadda itan ma haka ta ke gani. Babban Yaya, Anty zee, Aliyu da Deedat kadai su kasan zance.

Wani irin tausayin Yarinyar yaji yana shigan shi, Ga ta Allah ya bata hakuri. Amma shin yaushe Mami su ka shirya fada ma ta ne, ko sun manta yakamata ta dinga ma iyayen ta addu’a. She deserves to know gsky amma ya San me zai yi.

A washegarin ranan ya nemi koma wa Abuja tare da Zahrau n Abbah ya so ya hana shi sai da mami ta bashi baki sannan.

Safiyar ranar da zasu wuce Abujan kuka tayi ta wa Ammah da Deedat, rarrashinta su ka yi ta game da mata nasiha. Ba ta son bin shi Abujan amma ba yanda ta iya hakanan ta saduda.

Shi ke tuki ita kuma tana seat in mai zaman banza. Tunda ta gaishe shi ba ta kara magana ba shima din shirun yayi hankalin shi na kan tukin da ya ke.

Kiran Ahmad Sulaiman ya sa a motan yana bi. Kafin su karasa Kaduna har tayi bacci ba mamaki dadin karatun ne tun da ya kunna ta lumshe ido daman.

Kallo ya bita dashi ganin yanda numfashin ta ke sauka a hankali, wani irin tausayin ta yaji yana ratsa shi. Yasan ba kowace mace za ta iya juriyan da tayi. Bayan duk abinda ya mata ta kareshi gun Abbah duk kawaicin ta da rashin magana. Ba shakka Zahrau ta cancanci a jinjina mata.

Har zai dau hanyan Abuja ya fasa ya yi hanyan gidan Babban Yaya, Sai da yayi parking a kofar gidan sannan ta farka, kallo ta bi gidan shi cikin mamaki. “Mu shiga mana ko in zagayo in bude miki kofa ne?”

Saurin girgiza kai tayi sannan ta bude kofan ta fita, Murmushi yayi ganin yanda ta yi saurin girgiza kai cike da tsoro.

Khalipha da kanen shi na tsakar gida su ka shiga da gudu gaba dayan su su kayi kanta “oyoyo Anty Zahra” daya bayan daya ta daga su banda khalipha da ta ce shi ya girma, baki ya turo yana shi bai yadda ba suna ta mishi dariya “Ina wuni Uncle” Anisa ta fada tana kallon Shi

Hararan ta yayi sannan yace “ba ruwana da dukkan Ku Antynku kadai kuka gani koh”

Hannu khalipha ya hada yana “sorry Uncle Wlh Anty Zahra ce ta ja munyi missing inta sosai” Sauran kannen ma dauka su kayi suna fadin “eh mana Uncle”

Yaran ba dai wayau ba, suna birge shi sosai.

Da gudu Anisa ta yi cikin gidan tana fadin “Mommy Anty Zahra da Uncle sun zo”

Cikin Sauri Nanah ta fito ta rungume Zahrau sannan ta gaida Aliyu.

“Oyoyo Zahra na” Anty Rukayya ma fito wa tayi ta tarbe ta shi dai Aliyu sai kallon su ya ke ba sa ma ta kan shi sunyi kewan ta ba kadan ba.

Falon su ka karasa suna masu farin cikin ganin juna.

Da gudu Maijidderh ta fito daga daki dan daman Sallah ta ke yi “oyoyo Yaruwa” kanta gabadaya tayi tsaban farin ciki saura kadan dukkan su su zube kasa.

“Ah ah miye haka da auren naki ma ba za kiyi hankali ba” Aliyu ke magana cikin bacin rai.

“Sorry, nayi farin cikin ganin ki ne Sister. Ina wuni Uncle”

Hararanta yayi ba tare da ya amsa ba.

Daki Nanah da Maijidderhn su ka kai ta. “Au ni Uncle Aliy ba zai taba canjawa ba” Maijidderh ta fada.

“Kinga laifin shi? Da auren ki kya kama gudu so kike kima Mijinki asara abinda ke cikin nan ko?” Nanah ta fada cike da tsokana.

“Ke wai Wa ya ce miki ina da ciki” dukkan su biyun harara su ka bita dashi “ana ganin ki an gane Hauwa’u” Zahrau ta fada tana kare mata kallo.

Ummiy su ka kira, ji tayi kaman ta yi tsuntsuwa ta ganta a kadunan amma ba hali.

Suna cikin cin Abinci Anisa ta leko dakin “Anty Zahra Uncle ya ce kizo Ku tafi”

“Daga ina kuke wai” Maijidderh ta bukata

“Zaria”

“Abuja za Ku wuce”

Kai kawai Zahrau ta gyade mata game da mikewa.

“Ki bari mu gama cikin Abincin mana” Nanah ta fada.

“No am okay”

“Shknn muje mu raka ki kar Uncle Aliy ya ce mun rike mai mata daman na samu arzikin tsawa da na dade ba a min ba”

Murmushi kawai Zahrau ta mata suka fita.

Karfe hudu dai dai su ka isa Abujan, gidan su ka nufa kai tsaye.

Gidan na nan yanda ya ke sai fenti da aka canja da kuma furnitures.

Kai tsaye dakin ta na da ta nufa daman Aliyun bai shigo gida ba masallacin ya nufa.

Abin mamaki akwatunan ta gani ajiye ta yanda ta barsu haka gado da sauran kayan daki duk suna nan.

Bayi ta shiga ta dauro alwala sannan ta gabatar da Sallan La’asar tana me rokon Allah ya zaba mata dukkan abinda yafi alkhairi a rayuwan ta.

Ko wani irin Zama za ta yi wannan karon? Abinda ke ta fado mata kenan a rai tana tuno irin zaman da tayi da.

Text ya turo mata yana jiran ta a falo zasu je wani wuri.+

Gyalenta kadai ta dauka ta fita falon “Sannu koh ya gajiyan hanya?” Ya fada hankalin shi na kan wayan shi.

“Lafiya kalau, ya naka” ta amsa mai a hankali

“Nima lfy muje ko” ya fada bayan ya dauki keyn Motan.

Bata tmby shi ina za su je ba shi ma bai fada mata. In less than 10 minutes su ka isa gidan Salim daman ta yi suspecting can za su.

“Oyoyo Amaryar mu ta dawo”

“Ina wuni Maman khalipha”

Da gudu khaliphan ya zo ya rungumeta yaron yayi girma sosai haka yar kanwar ta shi ma tayi wayau.

Hira yayi dadi sosai sai karfe goman dare su ka nufi gida. Zahrau kan ba ta ma ki su kwana a nan ba.

A gajiye likis ta shiga cikin gida, saukin ta tayi Sallan isha’i dan haka ruwa kawai ta watsa ta yi haramar bacci.

  Ba ta iya bacci da kaya masu nauyi ba dan haka wani yololuwar half gown ta sa shara shara a na iya ganin komai na jikinta. Gashin kanta ta baza tana tajewa lokacin da taji Sallama a kofan dakin ta.

Kafin ta yi wani kwakaran motsi har ya shigo cikin dakin. Saurin sadda kanta kasa tayi cike da kunya jikin ta sai karkarwa ya ke.

Ganin haka ya sa Aliyu saurin barin dakin yana mai cike da mamakin tsoro irin na Zahrau, abu kadan jikin ta ya dau rawa.

Ribbon ta sa ta kama gashin na ta sannan ta dauko dogon hijab inta har kasa ta bishi falon.

Still dai jikin na ta rawa ya ke, kanta na kasa har ta karasa inda ya ke, dan nesa dashi kadan ta tsaya “Uncle ga ga ni” ta fada cikin siririn muryan ta dake rawa.

Kallon gefen ido ya bita dashi sannan ya ce “Na kira ki ne?” Saurin Jan baya tayi a firgice a sanadiyar yanda yayi maganan.

Zaro idanun shi yayi sannan yace “seriously tsoron ki yayi yawa, ki rage”

Shiru ta yi kawai kanta a kasa “Je ki abinki daman Nazo in duba Amanan Abbah ne” Hankalin shi na kan waya ya ke magana. She wonder me ya ke yi da waya 2/4/7.

“Sai da safe” ta fada ta yanda zai iya jiyo ta bayan ta mike

“Tsaya, kayan da ki ka bar min a nan ba ki so ne?”

Rashin sanin amsan da za ta bashi ya sa ta yin shiru.

A hankali ya ja tsaki “kinsan fa banson ina magana a share ni”

“Ina so” kawai ta fadi sannan ta nufi dakin ta.

….

Kwance ya ke rigingine a dakin shi, bacci ya ke son yi amma ina ko alamu baccin ya ki zuwa sai ma wasu shirmen imaginations da ya fara zuwa mai rai, kaman da wasa surorin Zahrau ya fara fado mishi a rai tun yana kokarin cire a rai har dai ya ga alamun rashin yiwuwan hakan.

Ganin bai da mafitan hana zuciyan shi tunani abinda ya ga dama ya sa shi janyo Qur’an yana karanta a haka har ya fara jin bacci sannan ya samu ya kwanta.

Da safe ko da ya tashi bai bi ta kan ta ba office ya shirye ya wuce daman ba satin za ta fara zuwa IT ba.

Ita ma ko da tashi ba taji alamun duriyan shi ba kitchen ta nufa straight ta samu abinda za ta ci.

Kwana Uku kenan Zahrau ba ta sa Aliyu a idon ta ba. Ko kadan hakan bai dame ta ba sanin cewa daman fushin Abbah da Mami ya sa shi dauko ta ba wai dan wani abu ba. Abinci ma ko kadan ba ta taba tunanin ajiye mishi ba iyaka komai ta ke nema tana samu daman ta taammaci hakan saboda sojan ba wai yana wasa da cikin shi bane.

Shi kanshi ya San Abinda yayi bai kyauta ba sai dai yayi hakan ne ba dan komai ba sai dan ya samu ya cire wa zuciyan shi tunanin Yarinyar. As he claimed Zahrau ba sa’ar shi bace ta mishi karanta yana dai tausayin ta ne kawai amma kuma ita ma ai bata neme shi ba that means ba ta damu dashi ba kenan? Haka kurum yaji bai ji dadin hakan ba.

Dakin ta ya nufa already har ta kashe wuta alamun ta yi bacci. Har zai juya sai kuma ya tsinci hannun shi da kunna Switch in wutan.

Baccin ta ta ke cikin kwanciyar hankali  ka ganta kasan ba ta da matsalan komai a rayuwa. Gashin kanta a baje yake kan pillow ta kunce ribbon in.

Sha’awa ya ji ta bashi, gashin na ta ya bi da kallo yanda ya baje, a rayuwan shi yana matukar son mace mai gashi.

Kishi kuma ya fara ji ganin cewa ya dade rabon da yayi baccin cikin kwanciyar hankali haka.

Saurin kashe wutan yayi ya bar mata dakin gudun kar ya kara dasa wa zuciyan shi wani abun dan kwanan nan Zahrau da ya raina zuciyan na neman bashi Kunya a kanta.

Washegari, da safe bai fita aiki da wuri ba yana wanka yaji kaman motsin mutum na kaiwa da kawo wa. Nan da nan ya gama wanka. Yana cikin shiryawa ya tabbatar da itan ce jin kamshin da ke tashi a gidan.

Cikin Uniform ya shirya bayan ya gama shafe shafen turaruka da mai, sosai Uniform in ke amsan shi da ka ganshi ka ga kaga hadadden Sojan da ya dace da matsayin shi.

  Sanye ta ke da kayan bacin ta Riga da wando ta daura kimonan kayan a saman shi, black veil ta daura a kanta amma still gashin ta ya fito ta baya.

 

Ya dade a tsaye yana kallon yanda ta ke ta faman soya golden yam In da ke gaban ta a gefe daya kuma tana pepper soup in kayan ciki Wanda ya wadatu da kayan kamshi dan kuwa kamshin sai faman tashi ya ke.

Jikin ta ne ya bata ana kallon ta da sauri ta juya, four eyes tayi dashi da sauri ta sadda kanta kasa sannan ta gaishe shi.

“Ba zan amsa ba, wato kin manta da yayanki ko?”

Sanin ya tsani a share shi ya sa tayi saurin girgiza kanta.

“Eh mana, you are not even sure if am well 3 days amma you are here enjoying”

“Am sorry ” ta fada kasa kasa

“Shknn INA jiran breakfast INA ko ba dani aka daura ba?”

“Okay” kawai ta ce sannan ta mai da hankalin ta kan aikin ta.

  Ganin hakan ya sa shi zuwa dinning yana jiran ta, haka kawai ya tsinci kanshi da son cin abincin na ta da ko kallo bai ishe shi ba kafin a hada su aure.

Aikin ta take a zahiri amma cikin zuciyan tunanin sabon halin Uncle Aliy ta ke ko kadan bai yi kama dashi ba shi ne har da Jan ta da wasa gsky abin da mamaki INA ma twins na nan su ga abin alajabin nan.

Allah ya so tayi niyyan yin abinci har rana ne da ba zai ishe su ba dake tana son doyan since from time.

Cikin 15 minutes ta gama komai cikin warmers ta shirya mishi komai sannan ta kai mishi plates hade da flask in tea da sauran kayan.

“Thank you” kawai yace mata sannan ya fara kwasan gara. Gsky ya dade yana missing abinda ya dinga ayyanawa a ran shi kenan har ya gama cin abinci.

“Zan wuce office”

  “Allah ya kiyaye hanya” ta amsa

  “Ba za ki rakani ba?”

  Toh fah har ga ranta ji tayi abin Aliyu na neman ya fi karfin ta. Rakiya kuma.

Ganin still ita ya ke kallo ya sa ta tashi ta bi bayan shi.

“A haka zaki fita akwai fa masu aiki a gidan” wannan karan ran shi hade ya fadi maganan zuwa yanzu saurin canja mood in shi ya far daina ba ta mamaki.

Har ga Allah ba ta ga  laifin shigan ta ba gaba daya jikin ta a rufe yake amma da ya ke ba ta son magana ya sa ta shiga daki ta dauko dogon hijabi ga mamkin ta yana nan Inda ta barshi yana jiranta.

Har bakin Motan ta raka shi sannan ta dawo cikin gidan ta fara tattarewa.

Nan da nan ta gama ta afka duniyar da tafi karfi wato karatun novel.

   Zaune ya ke a office ya yi jigum yana mamakin tunanin Zahrau da ya ke yi ba gaira ba dalili, wani siririn tsaki ya ja yana fadin OMG wannan wani irin rayuwa ce? Shin me ke damuna ne? Karan wayan shi ne ya katse shi daga zancen zuci da ya ke. Text message ne ” an Bayan Sallah da Sati biyu” kallo ya bi text in dashi Sam bai gane inda ya dosa ba, ko me zai sa Umar turo mai text in nan. Tsaki ya ja sannan ya ajiye wayan.

  Shiru yayi kaman ya tuno wani abu kuma yayi saurin dauko wayan ya kira Umar. Bai dauka ba sai mssg in da ya kara turo mai “sorry Frnd ina tare da baba, will call you later.”

Ba shi ya koma gida ba sai bayan Sallan isha’i, meeting ya tsaya har magariba da ya shiga Sallah kuma sai ya jira har bayan isha’i.

Ba ta falon so straight dakin shi ya wuce yayi wanka sannan ya sa jallabiya Mara nauyi har zai kwanta saboda gajiya gashi gobe suna da tafiya wata zuciyan yace ya je ya dubo Zahrau. Ya lura kwata kwata bai gaban yarinyar and bai jin dadin hakan.

Zaune ta ke kan sallaya tana karatun Al-qur’ani cikin suratul Yasin lokacin da yayi sallama. Sai da ta kai aya sannan ta dago ta amsa sallaman nashi. Murmushi ya sakan mata hakan ya sa tayi saurin sadda kai kasa “Ya aiki” ta fada tana wasa da yatsun hannun ta “aiki lfy Malama Fatima ba za a cigaba da karatun ba”

Tab banbarakwai taji fatiman da ya ce mata sau daya ta kan manta sunan ta kenan in ba malamai su ka kirata ba. “Na gama” ta bashi amsa.

  “Shknn tunda kince haka, Abinci na fa?”

  “Ban yi abinci ba” Zaro idanu yayi yana kallon ta “me kika ci da rana?”

“Na sha tea”

“Keh wasa kike da lfyn ki ko?” Saurin girgiza mishi kai tayi.

  “Ko kiwiyan girkin kike” yanzu ma dai kara girgiza kan tayi.

“Ki daina girgiza min kai Fatima. Ni gidana ba a zama da yunwa so zan miki afuwan na yau. Me zaki ci in samo miki?”

“Allah am okay”

  “Ki sameni a mota” kawai yace ya fita dakin.

She have no other choice haka nan ta bishi Motan.Blucabana Restaurant and cafe aka rubuta a inda yayi parking motan “mu je ko”  ya fada hade da daga mata gira, Saurin bude Motan tayi shi ma haka.+

  A jera suke tafiya kan ta a kasa tana ji yana gaisawa da workers in wurin, da alamun he is their Usually Customer.

  Light food ya musu ordering ba tare da ya tmby abinda za ta ci ba, ba ta damuwa coz she goes for everything.

Ita dai kallon wurin kawai ta ke a ranta tana fadin This place is exotic. Ko da aka kawo abincin ba wani cin arziki tayi ba, Sojan na ta ko sosai ya zage ya ci abin shi sai ma fadan rashin cin abinci da ya mata ita dai she is speechless.

Yana driving wayan shi ta fara ringing “kai sai yanzu za ka kira ni?”

  “Sorry friend sabgogi ne su ka min yawa” aka fadi daga daya bangaren.

  Tsaki ya ja “fada min an sa maka rana, what there to be busy akai”

“Bari zan baka lbr”

“Waya ga frnd da mata wai za ta sha caring”

“Na ka matar ma ai sai da na taya ka koh”

“Ban son gori, miye shirye shiryen mu”

“Zan shigo Abuja in two days zamu yi maganan”

“Allah ya kai mu a gaida fiancée”

Ko ba a fada mata ba tasan maganan bikin Nanah da Umar su ke yi Coz dazu Nanahn ta kirata ta fada Mata, she still wonder ya akayi su ka fara soyayya, Nana dai ta ce mata tun daga bikin ta ne.

Bacci ke idonta har hamma ta ke yi lokacin da su ka shiga gida, daki ta nufa direct “Fatima” Ya kira ta, har cikin ranta ta ke jin sunan ba ta San dalilin da yasa ya zabi ya kirata Fatiman ba bayan kowa na gidan su Zahrau ya ke ce mata.  Because he wants to be Special mana wani zuciyan ya fada mata, Saurin kawar da zancen tayi a zuciyan ta ta juyo tana fuskantar shi. “Bacci kike ji ne?” Ya tamabaya yana kallon kwayar idon ta.

Ta tabbatar ba ta jin komai game da Uncle Aliyu sai dai ba za ta iya jure kallon brown eyes In shi ba kai bashi ba ma kowa ne. Gyade mishi kai tayi idanuwan ta a kasa.

“Ba za ki dena ban amsa da kai ba ko”

Banza tayi dashi haka kurum taji ta fara gajiya da bin dokokin shi, is not always about him ai, he is so selfish.

Tsoron ma taji ba taji yau.

Kallo ya bita dashi ganin ba ta da niyyan tankawa, da dane ya San tuni ranshi zai baci amma maimakon haka sai yaji zuciyan nace yana yawan takura mata ne shiyasa ta gaji.

Share zancen yayi ya dauko wata “an tura ni wani aiki a Yola zaki raka ni?”

Ga mamakin shi gani yayi ta girgiza kai baza ta ba “why  2days kawai zanyi” wannan karan gaba daya shiru ta yi.

Zuwa yanzu kan ta kai shi bango amma haka kurum ya ke jin ba zai iya mata komai ba. “Je ki kwanta” ya fada hade da barin wurin gudun kar a samu matsala.

Kashegari, da safe ko ta farka har ta gama abubuwan ta ba ta ji motsin shi hakan ya tabbatar mata da ya tafi Yolan ne.

Sosai ta sake a gidan tana abinda ta ga dama ba tare da wani takura ba, sai ma taji gidan ya fi mata dadi da baya nan har ma ba ta so ya dawo.

~~~

Bai samu dawo wa Cikin Abuja sai ranar lahadi da dare, aiki su kayi sosai a Yola so yan isowa airport taxi ya tara ya nufi gidan shi.

Gaba daya kwana biyun da yayi a Yola da ita ya ke kwana da ita ya ke tashi duk da yaso yakice ta a ranshi amma INA Abu ya faskara haka nan ya yarda ya amince da cewa Zuciya da ruhin shi Zahrau su ke muradi, zuwa yanzu ya cire harkan ta mishi karanta ko kuma makammanci haka illa zallan shauki da idanuwan shi ke hangowa.

Bai Kira ta yana tunanin ko za ta neme shi tunda ya sanar mata da da tafiyan shi sai dai ya sha matukar mamaki domin ko Flashing inta bai gani ba.1

Yanzu ma haka da ya kusa isa gidan tunanin shi daya, wani irin tarba za ta mishi? Shin za ta ji dadin ganin shi? Sai dai ya manta da abu daya wanda ya nuna maka aminci shi ka ke marmari, amma dai muje zuwa.

Sallama yayi a kofan falon ba ta ma ji shi saboda gabadaya ta mai da hankalin ta kan Series film in da take kallo na India sai murmushi take.

Kila bata ganshi ba ya ayyana a ranshi har inda ta ke ya karasa hade da tafa hannu, a firgice ta dago ta kalle shi sai kuma ta ja baya.

Murmushin da ke kwance akan fuskan ta gabadaya ya bace sai dai kuma ba hade rai tayi ba “Sannu da zuwa” ta fada sai dai maimakon ya amsa mata kallo ya bita dashi.

Bakin dogo riga irin mai roba ke jikin ta, gabadaya surorin jikin ta a bayyane ya ke haka gashi kanta kama shi tayi da ribbon ta sake ya kwanto har gadon bayan ta, Saurin Jan katon gyalen ta da ke kan kujera tayi ta rufe jikin ta.

Bai so ta kama shi amma kuma da ke namijin duniya ne sai ya hade rai. “Ke haka ake tarban Wanda ya dawo daga tafiya”

Kala ba ta ce mishi illa ma sadda kanta kasa da tayi ai ta ce mishi Sannu da zuwa ya isa, abinda ta ayyana a zuciyan ta kenan.

Ba karamin kuluwa yayi ganin sharen shi da tayi, abin mamaki kuma duk hassalan da yayi sai yaji ya kasa mata komai.

“Ki shirya gobe zaki fara zuwa Asibitin” yana gama fada ma ta ya nufi dakin shi yana mai matukar mamakin yanda Zahrau ba ta damu dashi ba ko kadan.

Am i not worth loving? Rhetoric question yayi ma kanshi, saurin girgiza kai yayi yana fadin Farida fa bayan ita ma mata dayawa bai basu fuska bane.

Ruwa ya shiga ya watsa, wani irin azzababen yunwa ke dawainiya dashi sai dai kuma bai da appetite in cin abincin.

A tunanin shi Zahrau za ta zo ko abinci ta kawo mai tunda ta San tafiya yayi mai nisa ga mamakin shi ko motsin ta ba alamu haka ya dinga juye juye yana dawainiya da azababben Son ta da ke shigan shi a cikin ko wani second, anya ba hakkin yarinyar nan ba ne ya kama shi? Ya Allah ka kawo min sassauci a cikin wannan lamari, ji yake kaman kirjin zai fashe ne tsabagen nauyin da ya mai, sai ajiyan zuciya ya ke yana kiran sunan Allah a haka baccin Wahala yayi gaba dashi.Karfe  takwas na safe ya gama shiryawa ya fito falo, a nan ya same tana jiran shi. “Ina kwana” ta fada tana danna wayan ta “lfy” kawai yace yana kallon ta ta kasan ido. Wai shi yau tunanin kanwar kanwar bayan shi ke garawa a cikin gidan shi lallai wannan shi ake kira kaddara “shall we” kofan falon ya nufa, mikewa tayi sannan ta juya ta kalli dinning table “uncle akwai abinci”

   “Am okay” ya amsa yana cigaba da tafiya, as he expect bata damu da rashin cin abincin nasa ba duk da ta San shi mutum ne da bai son wasa da ciki, basarwa ma tayi ta bishi wajen.

  Ba Wanda ya ce ma wani kala har su isa Hospital in da za tayi industrial attachment inta, sai da ya tabbatar da komai intact sannan ya wuce barrack insu.

  Ita ko Zahrau a tunanin ta halin shi na asali ya dawo shiyasa ma canjawar shi ba ta Dada ta da kasa ba inda sabo ai yaci ace ta saba.

Kullum da safe shi ke kai ta asibitin in an tashi ya je ya dauko ta su wuce gida, ba wani maganan arzikin da ke shiga tsakanin su banda gaisuwa.

  Ko da wasa ya daina sake ma ta fuska a tunanin shi hakan da yayi zai sa ya dena damuwa da tunanin sai dai kash maimakon abu yayi baya ma gaba ya ci, shin wai ya zai yi da rayuwar shi ne?

Sati daya su ka dauka ba sa wani magana a tsakanin su, iya ka ta mishi girki daga baya ma driver yasa yana kai ta  asibitin.

 

    Jiki da jini, Da wani irin zazzabi da ciwon kai ya tashi safiyar ranan ko falo bai iya fito wa ba. Tara su ka yi zasu hadu da Umar amma har shadaya shiru, Umar in yana ta Kira shi bai daga waya ganin haka yasa shi zuwa gidan ya ga ko lfy.

  Zaune ta ke a kan gadon ta tana kallon wani Korean film descendants of the sun, Sallama da taji ne ya sa ta sako hijabin ta domin ganin waye. Tana ganin shi ta saki murmushi sannan ta gaishe shi, sai da su ka dan gaisa sannan ya tmby abokin shi.  Kallon hanyar dakin shi tayi sannan ta ce “ko za ka duba shi yau gabadaya ban ma ji duriyar shi ba” Kallon mamaki ya mata yana ayyana abu a ranshi sannan ya mike ya tafi dakin.

Kwance ya same shi kan gado ya lullube jikin shi da bargo sai rawan dari ya ke, da sauri ya karasa inda yake bargon kanshi ya dau zafi ballantana jikin shi da yayi kaman wuta.

Bargon yayi kokarin janyewa ba shiru Aliyu yayi saurin kankame jikin shi gaba daya jikin shi rawa ya ke yi idon shi yayi ja, A fili Umar ya nuna tsoron shi saboda ya manta rabon ya ga abokin shi a a haka, shi mutum ne mai dauriyar ciwo so ba karamin jin jiki yake ba.

Da hanzari ya shiga toilet ya debo ruwa da towel, da kyar ya bari ya Dan goga masa ruwa ko za a samu zazzani ya ragu. Abokin su doctor ya kira game da gaya masa halin da Umar in ke ciki sannan ya fita wurin Zahrau.

  A dinning ya same ta tana shirya abinci. “Sannu madam” ya fadi yana kallon ta, Murmushi kawai ta mai game da cigaba da abinda ta ke yi. Kan stairs ya sauko ya karasa dinning ya zauna “zauna INA so muyi magana” ba musu ta zauna tana sauraran shi.

  “Haba haba Zahrau a gsky kin ban mamaki” yayi maganan yana girgiza, ita ko sakin baki tayi tana kallon shi “ban ce frnd bai da laifi but ke fa mace ce yaka mata ace yanzu ba wani sauran matsala tsakanin ku, ba ki tunanin Ma Allah zai tambaye ki? Duba fa ki gani Aliy bai rage ki da ci ko sha ba kina da sutura basu kirguwa ga gida nan kina zaune cikin rufin asiri, kinga ko kenan in za a wa Aliyu adalci ya sauke hakokin shi dayawa Amma ke fa Zahrau? Nayi tunanin ke ce za ki bi hanyoyin da za Ku zauna lfy, Duba fa ki gani tun safe ba kiji duriyar shi ba ai kya duba halin da ya ke ciki ko dan zaman tare” ajiyar zuciya yayi sannan ya ce “anyway, Dan Allah ki canja kika kawo mana Abincin daki bai da lfy ne” Da mamaki ta dago ta kalle shi sai dai bai tsaya sauraron ta ba ya koma dakin.

  Jiki a sanyaye ta tattara warmers in kan tire ta nufi dakin nashi, wannan ne karo na farko da zata fara shiga dakin tunda ta zo gidan, Da siririyar muryata tayi sallama a hankali Umar ya amsa ma ta yana fadin shigo mana Zahrau.

Kan ta na kallon kasa ta shiga ta ajiye tray in sannan ta dago kan ta, Four eyes su kayi dashi coz shi in ma ita ya ke kallo, Jallabiya ke jikin shi kallon ruwan kasa buttons in gaban a bude hakan ya bata daman ganin bakin gashin da ke kwance a kirjin shi kaman bargo saurin dauke idon ta tayi “Sannu Uncle Ya jikin?” Muryar ta na rawa ta masa magana, Gyada mata kai kawai yayi “Allah ya kara sauki”

“Ameen” ya amsa a takaice.

Karan wayan Umar ne ya katse shirun da ya biyo baya cikin dakin, Doctor ne sun dan yi magana kadan sannan ya katse wayan “serve him Bara in shigo da Doctor” gyada mishi kai kawai tayi sannan ta fara kokarin bude warmers in.

Faten dankalin turawa ne da ya sha kayan lambu da kayan ciki kamshi sai tashi ya ke tayi sannan kunun gyada. Tana kokarin zuba dankalin ya dan kalleta “kadan za ki sa” ya fada yana lumshe idanu dan shi kadai ya San radadin da ya ke ji. “Sannu” ta fada gami da mika mai abinci ganin rawan da hannun shi ke yi ya sa ta jawo study table in da ta gani ta daura abincin. Ya fi shan kunun akan dankalin da ke tafi ruwa ruwa “Doctor na jiran ka a falo” Umar ya fada bayan ya shigo dakin. Gyada kai yayi hade da kokarin tashi ba shiri ya koma zaune saboda wani jirin da ya debe shi kanshi ya mai nauyi. Umar ne ya rike shi da kyar su ka karasa falon. Da sauri doctor ya nufe shi yana mishi sannu ya fara aune aune “Captain ma ba zamu asibiti ba kuwa? Your temperature is high” Girgiza kai Aliyun yayi, “shknn tunda ba ka so bara muga yanda za ayi, Bara inje clinic in dawo tunda ba nisa” Gyade mishi kai Umar yayi.

Ba a cika mintuna Ashirin ba ya dawo da abubuwa a hannun shi, drip yayi kokarin sa masa sannan ya dura allurori a ciki bayan nan ya debi jinin sa da niyyan ya masa test in ya koma asibiti, Magunguna ya mishi prescribing sannan ya mishi fatan Samun saukin sannan ya wuce.

Gabadaya magungunan sai da Umar ya nuna wa Zahrau sannan ya bar gidan da niyyan zai dawo anjima kasancewar baccin da Aliyu yayi.

Ba yanda ta iya haka ta dawo falon ta zauna tana Reporting IT NATA. Dai dai karewar drip in ya farka, idanuwan shi a kanta ya fara sauka tana rubutu kallon na ta ya cigaba dayi ba kakkautawa, jikin ta ne ya ba ta ana kallon ta dagowa tayi su jayi ido hudu saurin janye idon tayi ta mishi sannu da jiki, murmushi kawai ya sakan mata hade da lumshe idanu “pls in za ki iya ki cire min INA son nayi wanka” Ya fada ya na nuna hannun shi. Zuwa lab in da tayi kwana biyu ya sa ta iya Jan coka allura ta ja jini, a hankali ta rike hannun nasa, duk Kansu sun ji reaction in haduwan hannayen nasu amma sai su kayi choosing  ignoring, A hankali ta zare plasta in sannan ta cire aluran.

Ba lefi ba kaman dazu ba yanzun ya Dan samu karfi tunda har ya iya takawa zuwa daki.

Ya dauki mintuna dayawa yana shiryawa har Umar ya dawo, wannan karon a dinning ta shirya musu abinci, bayan sun gama ne Umar ya ja shi waje su sha iska da ke zazzabin ya dan sake shi.

Sau Uku Umar ya na mishi magana amma gabadaya hankalin shi bai wurin sai da ya tabo shi sannan ya dago a zabure yana tmbyn shi me ya ce “Tunanin me kake frnd?” Wani irin ajiyan zuciya yayi sannan ya kai hannu kan kirjin shi “Zuciyana na min zafin frnd akwai matsala?”

   “Subhanallah me ya faru?”

   “Zahrau”

   “What about her?”

   ” Frnd na kuma da son ta wlh ban San ya aka yi ba”

   “She is your wife already, ai abu mai sauki ne” Girgiza kai yayi yana kallon Umar in “ba ka fahimceni ba, Yarinyar nan ba ta so na, ba ta damu dani ba kwata kwata in ba zan mata karya ba amma kaman ina ganin kiyayyata a cikin idanun ta, tana zama dani saboda is her only choice” murmushi Umar yayi sannan yace “Haba captain sai dai kace ba soja ba Allah ni ka ban kunya, Mace ce fa kai za ka tafiyar da ita ka koya mata son ka da damuwa da kai balle ma Zahrau ba wata mai rigima bace INA ganin hakan zai zo da sauki”

   “Hakane amma frnd ba ka ganin ta kullace ni ne? Kasan abubuwan da suka faru dai”

   “Ranar irin ta yau tuntuni daman nake guje maka amma ba ka jiba, da ga ganin ta akwai riko ba shakka. Aiki ya zame maka biyu kenan ka fara goge wannan bakin tabon da kake dashi a wurin ta shi ne sannan ka fuskanci dayan”

  

 

     Sun dade suna tattauna yanda za su bullo wa lamarin sannan su ka shiga batun shirye shiryen bikin Umar, sai gab da magriba ya tafi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *