KUCHAKAR KISHIYA COMPLETE BY AYSHERTH MOHAMMED SANI(PREETY XAYEESHERTH)
*KUCHAKAR KISHIYA*
*STORY AND WRITEN BY AYSHERTH MOHAMMED SANI(PREETY XAYEESHERTH)*
*PAGE* 1
————————————————————————
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM INA ROKAN ALLAH YASA NA KAMMALA LITTAFINNAN LAFIYA KAMAR YARDA NAFARA KUMA YASA YA ANNFANAR DA MUTANE KAMAR YADDA NA TSARA*
Amman ne yashigo tare da sallamarsa
Kayan takaici abin da yasaba gani amman har yanzu baya juran ganin hakan.
Hamlat ce kwance akan kujera tana ta zabga uban barci ga daki kacha kacha kamar anyi dambe da alamu ma dakin yafi wata ba agyarashi ba.
Ran Amaan yayi matukar baci hakan yasa ya dibo ruwan sanyi yamakawa hamlat afuska.
Afusace ta farka tare da fadin kan ubancen wani dan iskan ne ya watsamin ru…….
Ganin Amaan tsaye agabanta ne yasa takasa karasawa .
Sai da taja dogon numfashi sannan tace”toh uban yan tsurfa andawo kenan nikuma banda sukuni”
.
Shikuma Amaan tsaye yake agabanta tsabar bacin rai ko magana ma yakasa kawai kallonta yake.
Sai da takara da cewa dallah malam ka matsamin akai ko?
Amaan yayi murmushi sannan yace”kingama?
Ina ke bakisan darajar kanki ba bare na mijinki?.
Da duk kan alamu tunda nabar gidannan ba agyarashi ba kusan wata kennan fa.
Kuma wai da sunan mijin ki yadawo daga tafiya ko ajikinki.
Sai rashin mutuncin dakika tanada kika fara zubamin.
Yana maganganun nan hamlat na hararasa tare buga kafa akasa.
Bata bari ya kammal abinda zai fada ba tace”dakata dan matsiyata nifa ba bai warka bace karka kuskura kanemi batamin rai .
Bawai dankaga ina dan ragama yanzu ba to wallahi zan dawo yafi nadama domin bana daukar raini kai kafi kowa sani”.
Amaan yace”wai ina mijinki kike fadamin maganganun nan toh wallahi daga yau inzakiyi rashin kunyarki ta tsaya akaina batare da kin hada da iyayena ba”.
Hamlat taja dogon tsaki tare da fadin”su iyayen naka suwaye ai bansan su ba bare nasan da zamansu domin kasan bana harka d matsiyata kaima dai lalurace tasa nake zaune dakai domin kasan inba haka ba da tuni na dade ba barinka.”.
Tana kaiwa karshe tayi tsaki tare da bangaje shi tukun tashiga daki.
Amaan binta yake kawai da kallo bamusan me yke aiyanawa azuciyarsa ba .
Yafi minti talatin yana tsaye ba abinda yake illa tunani .
Daga karshe kuma yace”Allah yakyauta”.
Alokacin yafara gyaran falon nan yafi awa sannan falon yafara kyan gani kuma duk da hka ba bai gyaruba yadai rage neh
Page 2
Amaan yana gama gyaran falon nan yashiga dakinsa domin yin wanka Allah yatai makesa yagyara dakin kafin yayi tafiya kuma daman hamlat bata cika shiga ba hakan yasa dakin bai baci ba sai yar kura da dakin yayi.
Hakan yasa yayi wanka sannan yafito yashirya cikin kananun kaya domin bai damu da manyan kaya ba.
Yana gama shiryama yanufi inda motarsa take ko ta kan hamlat bai yi ba domin yasan ynzu zata iya bata masa rai fiye da haka.
Yana shiga motarnan ba inda yanufa sai *layin zana* gudu yake amota kai kace wani gari zai je.
Abin da yabani mamaki shine naga yayi paking akusa da wani gida wanda bai da mara ba dana laka domin inba kasan garin birni bne inka gidannnan kace na karkarah neh.
Yana paking naga yafito kawai yatsaya ajikin motarsa sai kallon wata yarinya yake wace da alamu batafi shekara 15 amman duk da hka alamu sun nuna yarinta shakaf natare da ita domin kuwa wasan kassa take da uniform din skul ajikinta.
Amaan sai murmushi yake yana kallonta har ya manta ma da damuwar dake ransa kawai kallon yarinyar nan yake.
Ita kuwa batama san yanayi ba sai wasan ta take .
Tana cikin wasa sai taga wata me tallen doya .
Aikuwa karaf tafaracewa”musu gari da tallen doya”.
Tanayi tana murguda baki.
Aikuwa aguje me doyarnan tabi yarinyar .
Ita kuwa yarinya me xatayi banda gudu menaci ban baka ba.
Duk abinnan da ake Amaan yana kallonsu
Sai murmushi yake tare da karajin sonta azuciyarsa.
Tana zuwa kwofar gidansu ta turo kofar galan galan din tare da yima me doya gwalo.
Shiko Amaan me zai yi banda dariya .
Haka me doya ta hakura ta tafi abinta.
Shima Amaan duk da bai gaji da kallonta ba amman haka ya hakura yashiga mota yanata kwasan dariya tare dafadin”inaga watarana yar nan sai ta kumburamin ciki dan dariya”.
Sannan yacigaba da driven dinsa.
Akullum indai Amaan nagari sai yazo layin zana inya tashi daga aiki dai dai da lokacin dayasan yarinyarnan nadawowa daga skul .
Aduk ranar da bai gantaba toh sai yayi zazzabi.
Domin tazama masa kamar mahadin rayuwrsa.
Daga nan ba inda Amaan yanufa sai family house dinsu inda suke zaune duka harda iyayensa.
Yana shiga ba inda yafara nufa sai Falon Alhaji .
Yana shiga kuwa yatarar da hajiya ma tana falon suka gesa cikin sakin fuska .
Sannan Alhaji yace “ya hanya .
Amaan ya amsa da”lafiyau”.
Sannam hajiya tace”ya hamlat dafatan dai kuna lafiya”.
Amaan yace”tana nan lafiya”.
Bayan sun dan gaggaisa ne yanufi shashin babansa.
Yana shiga kuwa yatarar da ummansa sai washe baki take.
Ita da baba .
Sai da suka gesa sannan suka tambayi lafiyar dan nasu.
Ananne umma take cewa”amaan nasan kana hakuri amman kakara akan nada”.
Shidai Amaan kawai murmushi yake domin yana matukar gudun abin da zai batawa iyayensa rai.
Dole nema yasa sukasan halinda suke ciki shida hamlat.
Sai da suka masa nisiha meshiga jiki sannan umma tazuba masa abinci yaci.
Sai da yayi dak sannan yanufi hanyar gida.
Yana isa gida kuwa yatarar da hamlat har takara birkita falon .
Tana ganinsa tafara toh karamin munafika anje ankai ni kotu neh ko?.
Toh wallahi kasani kayi kadan domin ko ina zaka nafi karfinka.
Shidai amaan kawai murmushi yake domin hankalinsa ma baya wajenta shi tunanin little babynsa yake.
Hamlat data fahimci hankalinsa baya wajenta ai tuni ta matsa garesa tare da rike masa kwalar riga.
Tace”ni zaka mayar mahaukaciya?.
Page 3
Amaan yakasa magana domin abin hamlat din yafara basa tsoro da har ace zata iya chukume shi.
Hamlat tace”wai ba magana nakema bane dan gidan matsiyata?.
Alokacin idon Amaan yayi jajir sannan yacika da hawaye sana diyar kiran iyayan da sunan matsiyata da hamlat tayi.
Gaba daya rikice jikinsa har rawa yake
Da sauri yadaga hannu domin marin hamlat.
Har yakai fuskarta itakuwa duk tsiwarta sai da tayi shiru ta rufe ido domin tsorata.
Shiko Amaaan yana kai hannu ya tsaya domin yayi tunani me mahimmaci arayuwarsa hakan yasa kawai ya zuciya yafasa
Yasauke hannun.
Ita kuwa hamlat tana nan ta kame domin jiran jin saukan mari take sai ko taji shiru ai tuni ta bude ido tare da galla ma Amaan harara.
Sannan ta huce ta bar falon.
Amaan yana tsaye amman ba abinda yake illa hawaye dayake zirarowa daga idanunsa.
Ahaka har hawayen nan yakame sannan shima yashiga daki ya dauro alola yayi sallah sannan yadauko QUR’ANI domin yakaranta ko zai ji dadi aransa.
Ita kuwa hamlat tana shiga sharar dakinta tadauko waya domin kiran kawarta me sata ahanyar yan bori
Takira kuwa aka dauka.
Hamlat tace”hello sweet maama ya banganki bane ?
Kinsan fa dan matsiyatn yadawo gari kuma bakimin lectures ba shiyasa ma yasa tarba me dan mutunci”.
Maama ta sheke da dariya sannan tace”oh Aminiya ai yaci ace namiki free kinfara karawa da naki”.
Hamlat tace”tab nidai gaskiya kizo ko bakya bukatar abin neh?
Maaama tayi saurin cewa”nina isa?
Ai dolema nagarzayo miki da kayan aiki”.
Hamlat tace”,dax my sweet maama sai kinzo”.
Maaama tsce”ok byeee.
Washe gari
Da sassafe Amaan yashirya domin tafiya office yayinda ita hamlat ko tashi ma daga barcin batayi ba.
Amaaan yana kammala shirinsa yanufi shashin hamlat tunda yanufi shashin yakejin wani irin mugun wari me wagiza cika.
Yana tafiya yana toshe hannci azuciyarsa kuwa cewa yake kazamiyar bnza sai shegen iyayi ba abin da aka iya .
Sannam yana mamakin yanda take rayuwa cikin kazantar nan.
Bai ma ga kome ba sai daya shiga bedroom dinta kasa hadiye yahu yayi.
Dakyar ya iya cewa”ke hamlat tashi kishiyar d huri yau muna da meeting karfe 9″.
Hamlat batace kome ba sai harara data gilla masa alamar taji din
Shikuwa daman kaman akan kaya yake fit yafita adakin .
Yana fita kuwa yafara zabga amai.
Sai da yalafa sannan yasamu damar fita.
Ba inda yanufa sai layin zana .
Isar sa keda wuya yahango Ahalaam tafito daga gida ita da babanta zataje school Aikuwa sai rigama take masa akan sai yasiya mata chocolate.
Baba yace”haba auta kinsa fa yau banda kudi kuma gashi ke bazaki yarda ki taka akafa ba sai a mota kuma sauran chanjin kennan”.
Tuni Ahalaam tafara buri tare da cewa”to ma nina fasa zuwa skul din kai kaje kawai”.
Duk abin nan da ake idon Amaan nakansu.
Sai murmushi yake wanda shi kansa bai san dalilin hakan ba.
Ahalam tace”laaa baba kaga wani mutum achan yanata min dariya”.
Baba yace”to kirabu dashi inaga ba dake yake ba mutafi karki sa amiki duka”.
Ahalam tace”tab yssssn sai nima narama tunda yamin dariya.
Shiko Amaan bai san ma tagansa ba domin yatafi duniyar tunaninta.
Akullum in Ahalam zata tafi skul sai ta bata lokaci ko da kuwa awajen tsokana neh sai sunfi 30minit awaje.
Da gudu Ahalam takarasa wajen da Amaan yake .
Tana zuwa….
Page 4
Ahalam nazuwa takama kunnen Amaan
Tana fadin”wato kai bakajin magana ko?
Ance katafi makaranta kazo kana tsokanata harda dariya ko?.
Tsabar abin yabawa Amaan mamaki kasa magana yayi sai wata dariya data kara kubuce masa.
Ahalam ta zabga ihu tare da cewa”baba kaga mutumin nan ko?.
Baba kam ma yakasa motsi domin abin ahalam mamaki yake basa.
Amaan yadaure yace”haba yan mata sakemin kunnan mana da zafi fah”.
Ananne Ahalam ta shekye da dariya tare da fadin”ashe dai kaji zafi daga yau ka kuma min dariya ai .
Ko zaka kuma ne?
Amaan yayi murmushi tare da cewa”Aa ai naji zafi”.
Baba yazo da saury tare da cewa”ahalam munyi letti kizo ga abin hawa munsamu”.
Ahalam ta gallama Amaaan harara sannan tame gwalo tare da bin baba.
Baba yajuyo yna bawa Amaan hakury Amaaan yace”bKome ai”.
Sai da Amaaan yAdau lokaci yana tunanin Ahalam yana dariya sannan yanufi hanyar office dinsa.
Ahalam kuwa tana zuwa skul taga anfara tare letti ai tuni tayi kalar marasa lafiya.
Tana tafiya da kyar .
Tana isa wAjen itama tayi nildown .
AnAta duka uncle Salim yazo kanta kenan tafara kuka tare dacewa”sir nifa banda lafiya”.
Tafara mirgine mirgeni akasa.
Duk ta sakar me jiki da shagwabarta.
Tuni uncle salim yace”oya to tashi kitafi aji ai dama bakizo bA’.
Dasaury Ahalam ta mike ta mantamA da karyar rashin lafiyarta.
Tana tashi tana yan wajen gwalo.
Sannan ta zura da gudu.
Yan wajen sai haushi suke suna un uni.
Wasu kowa sunce sai sunma Ahalam duka.
Amaaan yana isa office ba jimawa suka shiga meeting sai da sukafara meeting sunkai minti 30 tunkunnna hamlat ta isa ta na wani shekan kamshi .
Jikinta tatas sai kamshi dake tashi kamar ba itace ke rayuwa cikin kazanta ba .
Ta gyara jikinta Amman gida akazance .
Tana tafiya tana yamutsa fuskar kamar tana kyamar kowa bayan kuma itace abin kymar.
Haka tashiga dakin meeting dinnan cikin tafiyar kasaita tare da nuna isa .
Ba wanda ta kula sai wajen zamanta data nufa.
Amaaan ko kallon inda take baiyi ba dan takaici.
Suko sauran ma aikata sai gesheta suke ita ko tana musu kallon raini.
Amaaan yacigaba da jawabinsa.
Kowa nasaurara aman bnda hamlat domin ita charting dinta ma takeyi.
Amaaan yakalle ta ya girgiza kai sannan yacigaba da jawabinsa.
Ahaka taro ya watse.
Kowa yakoma kan aikinsa.
Ahalam sun fito break suna zaune ita da kawarta hanan .
Ahalam batada wata kawa banda hanan domin tsokanarta tayi yawa jininsune yazo daya da hannan ma yasa suke shiri.
Hanan tana matukar son Ahalam duk da wani lokaci ahalam na hulakanta ta amman bAta dai na son kawarta ta ba.
Sannan kuma hanan yar masu kudice amman hakan bai sa ta guji ahalam ba.
Suna zaune suna cin kayan break dinsu.
Sai ga…
Page 5
Sai ga amrah nan tazo tana fadin”toh yar matsiyata wato ke skul dinma sai kinnuna halin talakawan ko?.
Ke kuma hanan kina yar babban gida amman kina bin yar me kwosai gidan laka?.
Alokacin ahalam ta razana ta miki zumbur Tare da chukumo amrah tana fadin”ke wai ni sa ar wasan kice?.
Wato ke yar masu kudi ko.
Idon Amrah yaciko tayi zuru zuru.
Ahalam takara dacewa”toh inaga ma kudin uban naki nasata neh kum wlh inkika kara cemin matsiyaciya sai naci miki mutunci.
Hanan tayani mulakada banza.
Aiko hanan da ahalam suka hadu suka dunga xabgawa amrah duka tun tana kuka har tayi shiru sai nishi.
Duk sun kumbura mata fuska anfasa baki.
Students sun hadu sai murna suke yau amrah ta hadu da wadda tafita masifa.
Sai ga wata malama nan dakyar tasamu tarabasu sannan tasasu nildown .
Aka kira uncle salim domin musu hukunci dan kuwa yafi kowa iya duka amakarantar dan hka ma in dalibai sukayi laifi shike dukan su amman sabida bala”i na ahalam shi gudun laifinta yake dan yasan tsagwarar rigima gareta .
Yana zuwa yaga ahalam aikuwa sai da gabansa yafadi ganinta da yayi awajen.
Yace”ahalam yadai lafiya dai ko?
Keda baki lafiya meyakawo ki nan?.
Aituni ahalam ta shagwabe sannan tace”uhumm ba wannan yarinyar bace take zagina.
Shine fa nafasa mata baki”.
Amrah tace”,kut ni zakima shari?.
Uncle salim yama amrah tsawa me girgiza mutum dukansu sai da suka razana.
Sannan yace”nasan halinki sarai amrah bakyajin magana kece baki da gaskiya domin nasan ahalam batada lafiya barata taba shiga harkar ki ba .
Dan haka maza kitashi kibar wajen nan’.
Amrah ta tashi tana tafiya dakyar.
Shiko uncle salim yace”pls sister kidai na dukan mutune haka kinga fa watarana inbana nan sai an rama musu abin da kike musu”.
Ahalam tace”kuttt wallahi inta karamin sai na fasa mata hanci”.
Hanan dai tanajin su tayi shiru tna ganin ikon Allah dan tasan uncle da ahalam sai Allah.
Uncle salim yace”to naji nidai tashi kikoma aji kinga tun dazu akakoma”.
Ahalam tace”wallahi bazani ajinba gida zanje abuna inci kwosai”.
Uncle salim dakyar yashawo hankalin ahalam sannan ta yarda sai antashi.
Lokacin tashi yayi daidai da lokacin tashi daga office din Amaan da hamlat.
Ahalam tana tafi tana tsokanar mutane.
Dreban su hanan yazo amman taki yarda tabisu domin tafiso tana tafiya tana tsokanar mutane.
Aiko tana cikin tafiya taga wasu mutane na fada.
Da alama ma mata da mijine.
Mijin yana cewa”ke baki da hankali ko akan titinma sai kin nuna halinki .
Kafin matar takara magana yafara dukanta.
Ahalam tana hangosu tazura da gudu tana zuwa tadau katon dutse ta dane bayan mijin tana buga masa dutsen aiko kuwa tuni ta fasa masa goshi.
Tana fadin mugu kawai saketa.
Yanajin zafi kuwa yasake matar itakuma ahalam ta dirka abayansa.
Matar tana dagowa taga jini agoshin mijinta tafara kuka tana ke miye hka wayace kifasa masa goshi tafara goge masa jinin.
Ita kuwa ahalam sai dariya take tana cewa”wayace kadaketa aigashi narama mata”.
matar ta biyo ahalam dagudu.
Aikuwa ahalam kafa menaci banbaka tana gudun amman tana cew”wawiya kawai ta tsaya wani garde nadukanta narama mata amman tanajin haushi.
Har matar tagaji da gudun ta tsaya amman ahalam bata tsaya ba .
Ahalam tajuyo tana mata gwalo aiko sai gashi karaf tabige me mangoro.
Me mangoro akasa mangoro ma akasa.
Page 6 & 7
*ASALIN LABARIN*
*SHIN AMAAN DA HAMLAT SU WAYE*?
*SANNAN KUMA WACECE AHLAM*?
*SHIN AMAAN DA HAMLAT SU WAYE*?
Amaan dane ga mallam sani tare da mahai fiyarsa baba nafi.
Su biyune kadai awajen iyayensu daga Amaan sai kanwarsa Amrin
Asalin sunan Amaan Ahamed ita kuwa Amrin Amina.
Baban Amaan shine babba a familynsu daga shi sai kaninsa
Alhaji sulaiman
Asalinsu yan garin kanone Amman kasuwanci yadawo dasu garin jos.
Alhaji sulaiman me arzikine na gaske domin kuwa ya ninka yayansa adukiya.
Yanada kampani dayawa wa inda yasa ake lura masa dasu .
Sanadiyar hakan shiyake daukan dawainiyar yayan yayansa .
Alhaji sulaiman shine mahaifin Hamlat wadda asalin sunnanta halima itace ya daya tak awajensa.
Tare da mahaifiyarta hajiya salma.
Alhaji sulaiman yana matukar son Amaan sabida kyawawan halayensa.
Akan hakan yabasa kamfani guda.
Itakuwa hajiya salma sam bata kaunar Amaan sabida tana ganin Alhaji sulaiman yafi nunawa Amaan so akan hamlat.
Tare Amaan da Hamlat suka taso duk da ya girmeta amman kome nasu tare alhaji yke musu.
Karatuma tare sukayi har suka gama.
Kwatakwata Amaan bayason hamlat sabida halinta na nunawa talakawa suba mutane bane sannan ga nuna isa ga kowa.
Amman ita ahakan tadaurawa kanta son sa duk da bata nuna masa hAkan.
Tasamu hajiya salma tasanar mata ita kuwa hajiya salma taji dadin hakan domin atunaninta hanyar da zasu ceto dukiyar Alhaji daga hannun Amaan kenan.
Da aka sanarwa da Alhaji yaji dadi sose dan hka yaje yasanarwa da yayansa shima yanuna amincewarsa duk da kuwa yana jiyewa dan sa mugun hali irin na hamlat.
Da aka sanar da Amaan ya girgiza sose Amman dan biyayya haka ya hakura akasa biki batare da bata lokaci ba.
Alhaji sulaiman shi yadau nauyin kome domin acewarsa shine uban ango .
Ankashe nera kamar ba asan zafinta ba.
Bayan aure Amaan yaso adaukan musu yar aiki sabida yasan tsabar kazantar hamlat amman taki.
Wai ita adole me kishi tana matukar kishin Amaan amman bata taba nuna mai soyayya ba koda kuwa ta minti daya sai zagi da cin mutunci.
Ahaka Amaan yake juran zama da hamlat sai dai inshi yaso yagyara gidan ko kuma yakira Amrin ta gyara.
Kuma ita intazo ta tsiya suke ravuwa da hamlat domin Amrin bata barin takwana anamata abu
take ramawa.
Hamlat bata taba neman Amaan sai bukatar ta tashi tukunnah.
Koda Amaan yayi niyar wulakantata inya tuna da maihinsa da nata sai yafasa.
Wannan shine takaitacen tarihin Amaan da hamlat.
*WACECE AHLAM*?
Ahlam ya’ce ga mAllam Rabi”u da baba maryam.
Asalin sunan Ahlam Aisha wadda akamata lakabi da Ahlam.
Mallam Rabi”u talakane fitik dan haka inkaje gidansu ma kazata awata karkara kake domin kuwa gidan lakane sannan kuma dan karami.
Baba kuwa suyan kosai take kwofar gidansu
Asalinsu yan niger ne cirani yakawo mallam jos hakan yasa yatawo da matarsa.
Mallam nakoyar da manyan mutane addini tahaka ne yakesamu damar biyawa Ahlam makaranta da bukatunta.
Ita kuw baba intayi suyanta tasamu riba anan take musu cefanan abin da zasuci.
Ahlam takasance ya me rikice da shagwaba ga tsokanar mutane.
Mutane dayawa suna sonta domin tana gwarjini awajen mutane ko ina taje anasonta.
Duk ranar ba ba school kuma ba madarasa sai ankawo karar fin sau goma.
Inko aka hanata fita tata kuka kenan ko kuma tazauna ta ta tsokanar baba.
Da mallam.
Intaso tata jama baba kumatu tana cewa”babata yar kyakkyawa me kumatun cincin”.
Tun baba na dariya har sai tagaji tacewa”ahlam taje wasa”.
Kadan daga cikin tarihin Ahlam kennam.
Page 8 & 9
Ahlam na ganin haka ta dauki katon mangoro acikin mangororin dasuka zuba sannan ta kara zurawa da gudu.
Sai mutanen wajen ne suka taimakawa me mangoron nan yatashi sannan aka kwashe .
Shiko me mangaro baya ma ta sauran mangoron sai ta wanda tadauka dominn kuwa duk aciki shine babba kuma me kyau.
Yaso yabita amman ina ahlam tafi karfinsa domin acikin minti daya har yadai nah hangota.
Ahlam kuwa kafa me naci ban baki ba .
Amaaan ya iso kofar gidansu ahlam kawai jira yake yaga da me yau tadawo.
Aiko sai gashi ta yanko kwana da shegen guda hanu rake da mangoro.
Amaan yakasa magana bai san lokacin daya sake baki ba yana kallon ikon Allah.
Tana zuwa taje wajen da ake sai da ruwa tace su sanmata ta wanke mangoro.
Aikuwa dayike sun san halin ahlam yar rikice ce haka suka bata batare da bin layiba.
Tana wankewa ta watsama me ruwan nasauran hannunta.
Shiko kawai dariya yake domin yasan halin ta .
Tasamu waje tazauna tana ta shan mangoronta.
Sai ga wani yaron makwotansu nan.
Yace”ahlam dan sammin”.
Ahlam tace”tab sai inka yarda zaka rakani mu tsinko danyen mangoro”.
Aliyu yace”bayan inmunje guduwa kike kibarni”.
Ahlam tace”toh ysssn yau bazan gudu ba ”
Aliyu yace”toh sammin nasha tukun muje kumama yau gidan baba kadan bala’i zamu kinsan natasunfi girma.
Ahlam tace”ehmana ai nata kaman wannan suke kasan danye yafi dadi barin ma inmukasa gishiri .
Aliyu yace”eh mana yawo na tsinkewa yana nidai bani nafara shan wannan”.
Ahlam tasa hakory ta gutsiro masa dan kadan duk yabaci da yawo sannan tace”gashi.
Aliyu yace”haba dan wannan me zanyi dashi nikam”.
Ahlam tace”kambala’iiiiiiiiii !
Lallaima wato ka raina ko?
Toh shikenan bara nashan ye kayana
Ai Aliyu najin hakan yakarba da sauri domin yasan zata iya hanasama gaba daya”.
Shiko Amaan yanan anbarsa da sakakken baki sai dayaga yadda take fincikar mangoronma yadauko waya yanata mata hoto.
Ita kuwa shan abunta take batama san yana wajenba.
Ahlam tashanye tana neman ruwan wanke hannu sai ga wata yarinya da ruwa akanta tana tafiya.
Ahlam tace”ke yar nan me majina zoki sammin ruwa na wanke hanuna”.
Yarinyar ta galla mata harara sannan tace”bazan bayar ba din”.
Ahlam tace”kuttt”
Sannan tacire hijabinta tadaura akugu .
Ta chikumo yarinyar ruwan yazuba sannan tafara dukanta tana ina ke baki da kunya ko?
Kina yar karama dake har kin iya rashin kunya to yau sai nakoya miki kunya awajennan.
Yarinya sai ihu take
Anrasa me kwatarta ahannun ahlam kowa tsoro yake ji kar tadawo kansa.
Sai da Amaan yaga abin yakici yaki karewa yaje yarabasu.
Dakyar suka rabu
Yana rabasu sai ga baba nan ta fito aliyu yaje ya fada mata
Ahlam tana ganin Amaan tasa dariya sannan ta galla masa harara da gwalo.
Tana cewa”nadai dana”.
Baba nazuwa tace”ohh ni ahlam wai bazaki girma bane”.
Ahlam tuni tashagwabe harda kakulo kuka tana”uhumm baba rashin kunya fa tamin kuma na girme ta “.
Baba tace”eh lallai kam tunda ke bakya ma nagaba dake ba”.
Baba tajata dasu shige gida.
Tajuyo taga amaan ta daga masa gira.
Amaan yamata murmushi sannan shima yahau motarsa yanufi gida.
Yana cikin tuki daya tuna hamlat zaije yatarar agida har ransa ya jagule.
Yana isa yatarar maamah kawar hamlat na gidan yayi sallamAh basu kulashi ba hakan yasa yahuce shashinsa
Yana tafiya maamah tace”ah lallai kin sakema mutumin nan ko geshemu fa bai yi ba.
Hamlat taja numfashi tace”oh indai wannnan ai karki damu bari kitafi dama da haushinsa nadawo daga office domin duk meeting dinnan daya shirya akai na ne.
Kuma yau zan basa mamaki.
Maaamah tayi guda sannan sukayi shewa .
Maaamah takara dacewa”shiyasa nake jidake yau banaso ayi barci agidannan”.
Hamlat tace”aiko baki fada bama dan yau natanadi buhun rashin mutunci.
Maaamah tadubi agogo tace kinga kar dare yamin anan bara natafi”.
Hamlat tace”toh ina zuwa bara nJe nadauko miki abin”.
Tana tafiya maamah ta gallama mata harara sannan tace ballagaza kawai.
Tana ganin hamlat tadawo tafara cewa”kawa ta gari kenan tana murmushun gulmah.”.
Hamlat tace”hmm gashi bayawq dubu darine kya fara rage abubuwa kafin naciro wasu”
Maamah ta washe baki sannan tace”bakome ai sai munyi waya”.
Hamlat tace”owk byeee.
Maaamah natafiya hamlat tanufi shashin Amaaan.
Tana zuwa ta bankada kofa.
Page 10 & 11
Yana zuwa yadaga hannu domin marintA har hamlat ta rufe ido tsabar tsoro.
Amaan yaji jiri yafara dibansa kan ya ankara yafadi kasa.
Karar fadiwarsa ce ta sa hamlat bude ido.
Tana ganin amaan akasa ko numfashi babu ai tuni ta firgita tafara fadin”Amaaan Amaaan Ammaaan ‘.
Kakara girgizShi sannan ta kuma cewa”Dan Allah karka mutu katashi wallahi inasonka inka mutu nima mutuwa zanyi pls katashi mana Amaaan dinah”.
Dataga Amaaan bai da niyar motsi tuni ta tashi tana kuka takira me gadi.
Shikanshi maigadi sai da yaji mamakin ganin Hamlat tadamu akan Amaaan .
Dasaury maigadi yataimaka mata akasa Amaan amota.
Ba inda suka huce sai asibiti.
Da hike daman nan Amaan yake zuwa aituni aka karbesu akabashi gado.
Bayan hamlat ta dan samu kanta ne takira momynta ta fada mata.
Momy tace”dafatan dai ba abinda kika masa kinsan halin dadynku akan wannan yaron nidama bakikaisaa asibityn ba dakinbarsa yakarasa”.
Hamlat tace”haba momy nifa wallahi inason Amaaan”.
Momy taja tsaki sannan tace”toh maiya ai sai kitasonshi
Gamunan zuwa”.
Hamlat takashe wayar tana nishi.
Momy taje wajen dady kamar mutuniyar aziki tasanar dashi .
Aiko afusace dady yatashi yaji sahibinsa ba lafiya.
Sai da momy tadanyi guntun tsaki.
Dady yace”kidaukomin key din mota bari nama yayanah magana mutafi”.
Dady yaje yasanarda baban Amaan da mama duk suka fito domin tafiya asibiti.
Dady tuki yake dagudu sose sai da baban Amaam yace”haba kayi ahankali mana kadaina sa damuwa aranka insha Allah jikin dasauki”.
Shidai dady kawai jinsa yke Aman zuciyarsa bugawa take.
Suna isa suka nufi inda Amaan yake amman anhana shiga domin har yanzu bai farfado ba.
Doctor yakira dady domin yamasa bayani annan ne yake fada masa cewa”Alhaji yakamata kuna lurah da danku sose domin da alama damuwa tamasa yawa sannan kuma zuciyarsa tana daf da bugawa dan haka aguji bacin ransa”.
Dady yafirgita sose hakan yasa zufa tafara keto masa sannan yace”yanzu ba yadda za ayi dashi”.
Likita yace”eh to akwai maganin da inya jury sha insha Allah za”asamu nasara”.
Dady yaji dadin jin hakan ahaka sukayi sallama da likita.
Hamlat kuwa tunda taji ance ya farfado tayi tafiyarta tabar asibitin.
Washe gari
Ahlam tana gida yau ba makaranta.
Baba na suyan kwosai awaje ita tazauna agun baba tayitayi da ita takoma gida taki domin tasan sai taja mata magana.
AhakA tazauna sai ga wani me ruwa nan yazo siyan kwosai.
Ahlam tace”dannan na nawa za”abaka?.
Baba tayi karaf tace”ke baki da kunya ko”.
Ahlam tace”uhymmm baba ai nabar tukunyar agida ko naje na dauko?.
Baba ta kalla mata harara sannan tace”mallam na nawa kakeso?.
Yace”na hamsin.
Baba tace”to kadan yi hakuri bari yakarasa”.
Ahlam takalli kafarsa tace”haba kawu mai ruwa baka wanka ne?.
Mai ruwa yace”,eh “.
Ahlam takara cewa”Allah sarki jibi yarda kake wari kuma gashi har kafarka tafashe “.
Mai ruwa dai sai kauda kai yake.
Ahlam takuma cewa”tunda mamanka batasonka batama wanka to kazo gidanmu babata zatama kaga ni sai nashafa ma mai ko?.
Page 12 & 13
shidai dan mai ruwa yayi zugum kawai kallon ahlam yake.
Mama tayi sauri tasamasa kwosansa ai kuwa bai fi minti daya ba yabace awajen.
Ahlam tace”baba yssn mai ruwan nan kazami nr wari fa yake shiyasa nace yazo kimasa wanka nikuma nashafa masa mai ga kafarsa duk faso kamar kafar saurayin *khadija Ahmad(princess deejerh)*”.
Baba tace”kai kaiiiiii ahlam nikam bansan yazan yi dake ba yanzu inba dan Allah yasa mai ruwan dan kirki bane ai da wani ne datuni yayi gudunbala dake”.
Ahlam tasheke da dariya sannan tace”aikuwa danasa uncle salim yamasa dukan tsiya”.
Baba tace”hmm Allah yakyauta dai”.
Ahlam tace”Ameen yar babata kyakkyawa mai fuskar cinçin”..
Baba tayi murmushi sannan tace”wato kedai ko kinbatama mutum rai sai kinsashi dariya ko”?.
Ahlam tasa dariya
Ahaka yau suka gama suya duk wanda yazo sai ta tsokaneshi wasu ko dariyama take basu.
Yawancin kostoman baba kawai dansuga ahlam da shirmenta suke zuwa siyan kwosai domin kuwa ahlam tanasa mutane nishadi fiye da yadda ake zato.
Amaaan na farfadowa ba wadda yatuna sai Ahlam hakan yasa shi wani dogon murmushi wanda yasa bai kula da mutanan dake kansa ba.
Sai abokinsa arfan yace”yadai yallabe daga farfadowa sai murmushi?”.
Sai alokacin Amaan yafahimci ma inda yake da wa inda suke tare.
Dady yace”yadai son fatan lafiya?
Amaan yakara murmushi sannan yaace”lafiyalau dady ina kwanan ku”.
Dukansu suka amsa cikin farinciki.
Bayan nan Amaan yatashi yayi wanka yayi sallah sannan yasha tea.
Bayan ya hutane arfan yake cewa”wai ya akayine ciwon nan ya riskeka lokaci guda?.
Sai ga hamlat tashigo adai dai sanda arfan ke tambayar nan.
Kowa yabada hankalinsa ga Amaaan.
Page 14
Amaaan yace”arfan alokaci daya kawai naji jiri yadibeni kuma gashi ba hamlat akusa so bansan lokacin ma dana subuce ba”.
Sai da hamlat tayi wata doguwar ajiyar zuciya sannan ta kakulo murmushin gulma tace”wallahi kuma na hanasa zama shikAdai sAbida irin haka amman yaki”.
Sai alokacin Amaan yasan hamlat tashigo yadago yakalleta suka hada ido aikuwa ta galla masa harara.
Amaan yayi murmushi azuciyarsa kuwa cewa yake”Allah karabani da sharri irin na hamlat”.
Ana cikin haka sai ga doctor yashigo tare da takardar sallamah.
Bayan anyi sallamar ne akanufi gidan su Amaan harda su dady .
Suna shiga dady yace”subhanallah ya gidan naku haka?.
Hamlat tafara burin kunya tana fadin umm dady dama da nake zuwa asibitin nan ne bana samun lokAcin gyara gidan”.
Dady yace”toh dai Allah yakyauta sai yanzu adage agyara ga Amrin nan ta tayaki’.
Amrin kuwa azuciyarta cewa take”aiko dady bakasan hamlat kuchaka bace acikin gida”.
Hamlat ta kalli amrin kamar tasan metake kunsawa azuciya ta galla mata harara.
Ashe amrin na ankare da hike bata barin ta kwana ai tuna tarama harda murguda baki ma .
Su dady da mama d momy suka koma gida daman shi baba tun dazu yatafi .
Amrin ce tafara gyaran gidan tagma gyara dakin amaan dahike shiba me dati bane sose tazo falo kenan tna gyarawa.
Hamlat tace”ke mara kunya jeki fara gyaramin nawa dakin”.
Amrin tace”,kuttt a lallaima kincika fitsararriya ai ni dana shiga dakinki gwara nashiga kurkuku sabida yafishi tsabta bana *KUCHAKAI* irinki bane”.
Hamlat tace”wacece *KUCHAKAR*?
Amrin tace”yoo ina wata bayan ke”.
Hamlat tace”kinsan halina sarai so zan daga miki kafa sabida kigamamin aikin gidannan sai indawo kanki domin ynzu da yayanki nake”.
Amriin tayi dariya iya son ranta harda rike ciki sannan tace”ai Wallahi yayana yafi karfinki zakisha mamaki nan gaba kusa “.
Hamlat tayi tsaki sannan tace”nidai amin aiki tana fada tana tafiya”.
Amrin tace”ai dan dady da dan uwa nke ba danke ba so matsamin anan”.
Abangaran ahlam kuwa yau moday zata tafi skul mallam nata fama da ita taki saury ita wai yau bazataje da huri ba saboda tasan dutyn uncle salim ne
Baba tace”in ma unko ne ba unclai ba koma dai mekikece masa dole kitafi eheee gwara ma kisani.
Ahlam tafara birgima akasan gida tana “ysssn inbaku barni na zo sai anjima ba innayi kudi nafasa siya muku gida da mota uncle kawai zan siyama”.
Page 15
Baba tace”ke ko ai da mun huta da rigimarki ahlam dan inaga ba mai iya jure halinki inko ansameshi to na musamman neh”.
Ahlam ta kurma ihu sannan tace”mallam baba kaganta ko?.
Baba yace”naganta mamana kiyi hakuri bazamu siya mata chocolate ba”.
Ahlam tace”yAuwa babAna kai kam zan siyama mota itakuma baba mai fuskar cincin ysin bazan siyamata ba uncle dakai kawai zan siyama”.
Baba tace”kwadai ji dashi”.
MAllam baba yace”yauwa yar albarka tashi muje insiya miki chocolate din sai in anjiyeki askul ko”
Ahlam tace”yes my sweet dad “sannab ta kalli baba tace kekuma biscuit mom ce wallahi”.
BabA da mallam baba sai da sukayi dariya iya son ransu.
Har ahlam tafara jin haushi tace”to ma nafasa”.
Mallam yace”a”a muje yar albarka”.
Ahlam tayi murmushi sannan takama kumatun baba tace”bAbata mai kumAtun cincin na yafe miki kuma harda ke zan siyawa gida’.
Ta shgwabe fuska sannan tace”kimin addu”ah babata”.
*daman wannan dabi”ar ahlam ce tasaba tun tana karama kullum inzata fita sai iyayenta sun mata addu’ah sAnnan ita kwata-kwata bata da rikwo arayuwarta kana bata mata rai intayi masifarta alokacin to anjima ma zata kulaka*
Baba ma tayi murmushi sannan tace”toh mamanah yar albarka Allah yakiyaye hanya yatsaremin ke yasa kuma kiyi abinda kikaje yi haka kuma arage tsokanar nan dai”.
Ahlam ta tashi ta zura da gudu sai da taji bakin kwofa tace”Ameeen mai fuskar cincin dina”.
Baba tayi murmushi mallam ma yabita suka tafi.
Suna fita kuwa Allah yasa suka samu mota batare da bata lokaci ba.
Karfe 7:30 dai-dai suka isa aiko da ahlam taga batayi latti ba sai murna take yau zasu tare masu latti ita da uncle.
Sai da baba yashigar da ita sannan yabata naira 20 tayi break tamasa godiya sose sannan tashiga ciki.
Tana shiga ta hango uncle salim da gudu takarasa gunsa tana cewa”oyo yo uncle”.
Uncle yace”welcome sweetyn”
Ahlam tace”good morning uncle”.
Ashagwabe take magana
Shima uncle yashagwabe domin shagwabar ahlam kashe masa jiki take
Yace”morning sweetyn”.
Ahlam tace”uhumm uncle kaga yau banyi latti ba ko?.
Yace”yes my sweetyn ya akayi hakan ne kokin fara samun sauki ne?.
Ahlam tayi dariya sannan tace”yasin kasan dama lafiyata lau yau su babane suka hanani zama agun kwosai”
Uncle yace”aiko sun min dai-dai domin ina bukatar ganin sweetyn akusa”.
Ahlam tashagwabe snnan tace”aiko yau ni zanyi dukan latti”.
Uncle ya rike hannun ahlam yace”yes sweetyn muje” .
Page 16
Suna zuwa uncle yabawa ahlam kujerar zamansa.
Yace”,get a site sweetyn”.
Ahlam tayi murmushi tace”owk uncle”.
Uncle yaduba agogon hannunsa sannan yace”yes sweetyn yanzu 80:00 kuma kinsan yau ba assembly andan daga musu kafa amman yanzu zamu fara tare letti”.
Ahlam sai murmushi take abin nema yasamu
Sai ga su amrah nan sun iso uncle yace”yauwa akan wa innan zamu fara kisamu kishiga ajiko kinga har mallami yashiga ajinku”.
Ahlam tashagwabe tace”uhumm su amrah ne ba ni baza adakan munsu ba inkuma kadake su kuka Zanyi”.
Tana fada amrah na isowa.
Aikuwa tuni uncle yace”toh sweetyn tashi kushiga aji to”.
Ahlam tasauka da dariyarta tace”owk uncle “.
Uncle yamata murmushi.
Har takusa shiga aji tajuyo tace”uncle”.
Yadago kai .
Tadaga masa hannu sannan tamasa alamon kiss da hannu.
Bakaramin dadi uncle yaji ba duk da shiyasaba mata hakan amman yau baiyi ba shine ita tayi.
Sai yaga kaman tafi kowama iyawa tuni yatafi duniyar tunani.
Itakuwa tana masa tashiga aji da gudu amrah kawai tsayawa tayi tana kallonta.
Tana shiga aji dagudu tabige kafar zainab .
Aiko zainab ba bayaba wajen bala”i .
Tamanta ma da malami a ajin tuni ta tashi tarikewa ahlam riga.
Ahlam tace”mallama yadai?
Zainab tace”kut kitaka ni kina cemin yadai”.
Ahlam tace”ayya sorry wallahi bansani bane”.
Ahlam nada hakuri in ba”atabota ba amman f in aka tabota anashan mamaki.
Zainab tace”naki hakurin yau sai nagyara miki zama a ajinnnan dan kinga sauran na tsoronki to wallahi ninafi karfinki”.
Ahlam tace”owk haka kikace lallai yau kinaso adumama miki jiki agida.”.
Kafin zainab ta ankara har ahlam tayi tadaga tayi hulli da ita gefe sannan tabita tacigaba da dukanta da hike ajin da na girma malamin ma bai gani ba sai da amrah tamai magana.
Yna zuwa dayaga ahlam ce azuciyarsa yace”wannan ya’ dai bansan yazanyi da ita ba dan tafi karfina”.
Ahlam kuwa duka take kakkaautawa tun zAinab nazaginta har tafaracewa”dan Allah kiyi hakuri”.
Da mallam yaga abin bayi ahlam zata iya la anta yar mutane ai tuni yasa amrah takira uncle salim domin kallon yayan ahlam suke masa.
Uncle salim nazuwa yace”laaaa sweetyn kin manta promise din mune kika kara fada”.
Ahlam na nishi tace’umm har hakury fa nabata taki ji”
Uncle yace”owk to daga yanzu dai”.
Ahlam ta duma mata dundu sannan tace”da wani dagon bakinta kaman rabin faskare”.
Sannan ta dagata.
Uncle salim yace”nasan laifinkine zainab gba kya kuma “.
Yan aji sai dariya suke zainab kuwa takumbura zata fashe kmar pampers
Page 17
Ahlam tayi gaba abinta tazauna agurin zamanta.
Amrah ma tabita suka zauna tare abin su.
Uncle salim kuwa yafita yatafi office dinsa.
Malam yacigaba da karutu tsit kakejin aji kowa yayi shiru.
Abangaren su Amaaan kuwa.
Amrin takammala gyara gidannan tsab kaman bashiba.
Ita kanta matar gidan sai kallo take tana wani fadi kamar ita ta gyara.
Amrin taje dakin Amaaan tace”bloodly br mai zan dafa neh?.
Amaaan yayi murmushi sannan yace”ayya bloodly sis ni banason cin kome’.
Amrin ta tabe baki tace”uhum wallahi sai kaci wani abu inba haka ba nafadawa dady”.
Amaaan yarike baki sannan yace”toh aunty bombolas zata hadani da dadyna”.
Amrin tayi dariya sannan tace”toh mezakaci yanzu”.
Amaaan yashagwabe fuska sannan yace”uhumm kawai kadamamin custard inaga ya isa”.
Amrin tayi murmushi tace”as u wish bloodly bara naje nadamama”.
Amaan yace”,okey”.
Amrin nafita tashiga kichen batare da bata lokaci ba kuwa ta dama masa tasa madara sose domin tasan bloodly dinta bayason sugar sabida haka batasa masa ba.
Tana zuwa tace”oya bloodly tashi inbaka”.
Amaan yayi murmushi yace”randa kikayi aure zanyi rashi bloodly”.
Amrin taji tausayi Amaan sose domin ita kadai tasan wahalar dayake sha agun hamlat.
Idonta yaciciko amman haka ta dage tayi murmushi sannan tace”ai dole kasamanmin aunty kafin nabarka’.
Amaan yayi murmushi azuciyarsa kuwa Ahlam ce tazo masa
Amrin tace”umm kaga tashi kasha “.
Amaan yatashi yana murmushi .
Amrin nabasa suna yar hirarsu ta yan uwa.
Sai dariya suke ita kuwa hamlat tanajin su duk zuciyarta ta jagule sai faman mita take.
Ai tuni tanufa kofar dakiin amaaan
Tabankade kofar tashiga.
Amaan da Amrin suka dago suna kallon ikon Allah.
Tafi minti biyu rike da kwankwsso suna kallon juna.
Amrin taga abin nata bana wasa bane tacigaba da basa custard dinsa.
Alokacin hamlat takuma tunzura tace”wai wannan irin rashin hankali ne zakazo kucikamin gida sannan kuma ina jiranki ki kawomin abincina shiru.
Dasaury amrin tamike tare da cewa”wai ke wace irin dabbace?
Sannan kuma ance miki ni yar aikin kice?.
Hamlat tace”kutt alallai yar matsiyata ansamu waje”.
Amrin tace”hmm wallahi ni tausayima kike bani domin halinki zai kaiki ga halak amman bakome kicigaba”.
Sai alokacin Amaaan yayi magana yace”amrin kinga daukomin key din chan mufita”.
Amrin tace”ok bloodly”.
Hamlat tayi wata kara.
Page 18
Sai da Amaan ya firgita tare da Amrin afirgice suka mike.
Hamlat takama kugu tare da fadin”wallau ba inda zakuje ku barni agidannan ai ba me gadi bace nj”.
Amrin tayi dogon tsaki sannan tabangaje hamlat taja hannun Amaaan suka fita.
Agurin hamlat ta tsaya tanata zabga uban masifa.
Suko suna fita Amrin tace”ina zamu bloodly?.
Sai da Amaaan yayi murmushi sannan yace”layin zana”.
Amrin tace”bloodly?
Me ya hadamu da layin zana kuma?
Amaaan yakara murmushi sannan yace”kedai muje kyaganema idonki”.
Amrin ce me tuka motar sai sakye-sakye take azuciyarta ko ina dasu oho.
Sunzo daidai wani gida me kama dana laka gashi kuntu sai kuwa Amaan yace”tsaya anan bloodly”.
Amrin da mamakinta tanemi waje tayi paking.
Adai-dai lokacin sai ga ahlam ta bullo da uniform ajikin ta tana dan tsalle-tsalle .
Amaan yabada hankalinsa ga ahlam hakan yasa itama Amrin ta bada nata.
Aikuwa ahlam nadan tsalle-tsallenta sai ta hango me rake.
Tanufi gunsa tace”,me rake abani naa biyar”.
Me rake yace”babu na biyar yar nan”.
Ahlam tace”kut gashi ina gani fa”.
Me rake yamata shiru .
Aikuwa tuni tafara waka.
Tana cewa” *me rake, inba rake, mutuwa tazo, ta tafi dakai*”.
Dahike me raken tsohune ai tuni ya firgita yace”haba yar nan aai akwai rake kyauta ma zan baki ba sai kin ban biyar ba amman fa karki kara cewa mutuwa tazo ta tafi dani”.
Ahlam tayi dariya sannan tace”to baba me jiran duniya bani intafi zanje islamiya”.
Sai da merake yasamo lukyekyen ciki dan dari biyu
yace”gashi toh”.
Ahlam nakarba tazura da gudu tana cewa”wallahi sai kamutu baba ai kowa ma zai mutu hhhhh wallahi zaka mutu “.
Aituni baba me rake yasoma kuka shi adole bayason mutuwa.
Hawaye nabin hawaye.
Ahlam data juyo taga yana kuka sai yabata tausayi.
Tazo tashare masa hawaye tace”sory baba bazaka mutu ba to daman fa wasaa nakema”.
Me rake yayi murmushi .
Ahlam tace”to kasamin albarka”
Me rake yace”Allah yamiki albarka yar nan”.
Ahlam tayi murmushi sannan tace”amin tacigaba d tafiyarta”.
Amrin sai dariya take haka kawai sai taji yarinyar tashige mata rai.
Amaan yace”amrin wallahi inason yar nan fiye da yadda nakeson kaai nah”.
Amrin tace”nima inasonta wallahi yayana”.
Suna cikin maganar nab ahlam har tazo zata shige gida kawai sai ta hango su amaaan na lekyenta.
Ta tawo da gudu
Page 19
ta tawo da gudu,tana zuwa wajen sai tace “lah wato yau har matar ka ka tawo yawo ko?,
amaan yayi murmushi yace”a,a kanwatace.”
amrin tace”ina hini ”
ahlam tayi murmushi tace”oh sory ban geshe ku ba to ina hininku”,
amrin tace”lafiyalau yakike? ya gida?,
ahlam ta galla mata harara tace”uhumm ni fa yayanki na gesar ba ke yar sa ido”,
amaaan dai yanata kallon ikon allah,
amrin tayi murmushi tace”ayya auntyna sorry”,
ahlam ta washe baki tace”wayyo nidaman aunty wayyo allah nah yau ancemin aunty”,
ai tuni tafara tsalle tana murna tana cewa yeeeeeh wallahi tace min aunty,
amrin da amaan sai dariya suke ta mata,
sai amaan yace”haba auntynta kidai na tsalle mana kar amiki dariya fa”,
ahlam ta murguda baki sannan tace”ni karka kara kulani ai kai bakacemin aunty ba”,
amaan yayi murmushi sannan yace”toh aunty ahlam”,
ahlam tace”yauwa dan kanina allah yamuku albarka”,
amaan da amrin sukace”amin suna dariya”,
ahlam tace”byeee zan shiga gida kanne nah”,
tana tafiya tana juyowa sunawa juna bye,bye alamu dai sun nuna dukansu bason rabuwa har tazo shiga gida ta kara juyowa saura kadan ta fadi,
amaaan yaji hakan har ransa sai yaji kaman yaje yadauke,ta,
tana shigewa gida amrin tace”wooow yayana wallahi tayi sose ga kuruciya da barkwanci i love her ho,”,
amaan yayi murmushi yace”ayya kanwata to kitayani da addu,a ko zan samu wannan kakkyawar gimbiyar”,
amrin tace”amin”,
alokacin suka dauki hanyar gida,
ahlam nashiga gida tayi sallama kafin baba ta amsa har tafara ihu tana cewa”wayyo babata wallahi yau ancemin aunty”
baba tafa wasu masu halin nakine suke cemiki aunty?,
amrin ta kyalkyale da dariya tace”wallahi wasu manya ne fa hhh nikam ai naji dadi nah nima yanzu nazama babba,uhun ta shagwabe tace”ina ke da baba ma zakuna cemin aunty ko?
baba tace”ke dai bakya gajiya da shirme”,
ahlam tafara buga kafa tana bury tana cewa”wallahi ni inbaki cemin aunty ba baranci abincin gidannan ba “,
baba tace-“yahkuri yar auta tah”,
ahlam tace”uhummm ni wallahi ba yar autarki bace sai kincemin aunty ko nafadaki da uncle salim dina”,
baba tace”yo ba sai ki fadan ba tunda shi ubananeh”,
ahlam tafara ihu tana wayyo,uncle salim dina har da kukanta,
baba tace”oh ni yasu naga takai nah wai mekikeso neh?
ahlam ta shagwabe tace”ni kicemin aunty”,.
baba tace”
Page 20
baba tace”toh aunty ahlam”,
da ahlam tayi wata kara sai da baba ta firgita tazatama cin naka ne yacije tah,
sai tayi ahlam nacewa yeeeeessss my momy me kumatun cincin ,
ta kara da wani ihun tana cewa”kai gaskiya nagirma mah daga yau nadai na wasa dasu amira awaje,
baba ta kalle ta taba baki tace”kyaji dashi dai”,
ahlam tace”yauwa mumy babata daga yau kina cemin aunty kinji ko?,
nikuma zan daina cemiki baba sai mumybaba shima baba inaceme dadybaba”,
baba tace”eh to naji zokici abinci”,
ahlam ta shagwabe tace”uuumm ni wallahi banajin yunwa fah”,
baba ta girgiza kai domin tasan halin yar ta ta sarai daman bason cin abinci,gareta ba ,sannan tace”haba aunty ahlam dina zo inbaki abaki”,
wayaga bakin ahlam ta washe shi kaman taga bankararriyar kaza dan murna tace”mumybaba wallahi zanci tunda dai kincemin aunty”,
baba na fara bata tayi loma uku tace”ita fa ta koshi islamiya xata tafi”,
ahaka dai baba ta ta,fama da ita dakyar tasamu tayi loma goma tukun ta tafi makaranta,
abangaren amaaan kuwa suna komawa gida suka tarar da bakin ciki mara misaltuwa,
gaba daya hamlat ta wargitsa gidan kamqn ba mutane aciki tafasa kayan fasawa ta bata na bata kuma tayi ficewarta,
suna shiga gidan ba abinda amaaan yake cewa” sai”inalillahi wa inna illaihir raji,un ,amrin kinga abinda mahaukaciyar matar nan tayi ko?,
gaskiya nafara gajiya yana fada yana hawaye,
amrin tazaunar dashi sannan itama tazauna tace”haba my bloodly karka karaya nasqn kayi dauriya sose amman ka kara akan nada”,
amaaan yace”hmmm amrin bazaki gane bane wallahi,
amrin tace”bloodly niko inada wata shawara , kaga dai baban ba yarda zaiyi da inkace xaka kara aure ba to mezai hana ka fadawa dady”,
amaaan yace”wallahi nima hakan nke shirin yi amman nakasa fada masa abinma dayasa bandamu sose ba dan naga ahlam din yarinyace dasauranta amman insha allah ynzu kam zan masa magana ko na huta da masifar matar nan
yana gama fada ko rufe baki bai yi ba yaji an bankado kofa,
Page 21
hamlat ce tana ta huci kamar wata sabuwar mota,
takaraso inda suke tace”wato nice masifaffiyar ko,zaka rabu dani ka huta ko?,toh wlh kayi kadan dan talakawa”,
amrin tace”hamlat bafa tsoronki mukeji ba dan kinga ana miki kawai ci toh wallahi kisani yayana zai kara aure kuma baki isa ki hana ba duk haukar dazakiyi kije kiyi kinga zaki iya ne,maganar talauci kuma dakike ai allahn daya baku kudi bawai yafi sonku bane ya,gwada imanin kowa ne dan hakan mind ur langauge yar masu dukiya”,
hamlat ta sume atsaye batasan sanda hawa yafara zubo mata ba,
ta yanke jiki tafadi asanyaye tace”yaya amaan dan allah kayi hakuri,wallahi,inasonka kayi hakuri muyi zama lafiya, nama alkawari daga yau zan chanja halina,.
amaaan da amrin suma sunyi wata sabuwar suman tsaye domin tunda amaan yake amrin bata cemasa yaya ba kuma bai taba ganin,tana kuka akan wani,abu daya shafesa ba,
amrin ta kada baki tace”ai lokaci yakure yan mata sai dai akiyaye gaba”,
afirgice hamlat ta mikye tana”wallahi baku isa ba kunyi kadan ma natsaya baku hakury”,
ta shakye da dariya tana daga baya kenan wai,anyi sadaka da bazawara,
hamlat takara firgita fuuuu tayi dakinta tana”wallahi baku isa da hamlat kuke zance”,
tana shiga dakin tadauko wayarta ajaka tashiga kiran maaamah,
maaaamah tadau waya tana ya akayine aminiya,
hamlat tace”ba lafiya wallahi,maaamah kizo ina bukatarki yanzu da matsala wallahi”,
maaamah tace”bakome aminiyar da alama dai yau wannan banza talakan,yataboki ,karki damu ina hanya,
Page 22
amaaan yace”to fa antabo me jiran kadan kinga ni kam muje insanar da dady domin,nasan inta riga fada toh da matsala”,
amrin tace”owk hakane fa muje”,
suka nufi hanyar gida,
hamlat taji ana buga kwofa dahike tasan kawartace dasaurin ta tafito aiko taga falo wayam azuciyarta tace”lallai mah gayannan wato tafiyarsu ma sukayi”,
tayi kwafa taje ta bude kwofar,
maaamah naganinta tace”kut yanaga har kin rame wai meke faruwa neh haka?,
hamlat tace”hmm muje muzauna tukun, dai”,
maamah tace”owk “,
hamlat tace”kiga dan rainin hankalin nan wai aure yakeson yi fah ko,ince zai ma yi”,
maamah ta tashi afirgice tace”kanbala’iiiiii aiki wallahi bai isa ba yamasan ko mu suwaye kuwa?,
hamlat tace”hmm ni duk ba wannan ba kifadamin mafita”,
maamah tace”kinsan gidan su yarinyar neh? toh ma wai yar wani hamshakin ce da zasu kara damu”,
hamlat tace”wallahi bansan yar waye ba?
maamah tace”owk yakamata musan yar waye amman kafin,nan zamuje gun wani hatsabibin boka wanda asanda mukaje zai mana aiki”,
hamlat takama bqki sannan tace”boka fa kikace?,
kinsan duk abuna banason shirka ko?,
maaamah tace”toh shikennan zauna amiki kishiyar ninayi gaba sai munzo shan biki da suna dama gashi ke ba haihuwa kike ba”,
tuni hamlat ta fara kuka tana rukwo maaamah”dan allah kitsaya ni muje ma ko gun waye wallahi zani indai za afasa auren nan”,
maamah tayi murmushi tace”ko kefa aminiyar”,
azuciyarta kuwa cewa take”banza ballagaza kuchakar da batasan metake ba sai na hallakar dake insha allah tunda dai ke son duniya kikasa agaba ai abinda nake nema kenan muzama daya”,
hamlat ta taba maaamah tace”baran dauko gyale da jaka mutafi “,
maaamah tayi murmushi tace”toh kiyi sauri muyi muje dai kam”,
amaan da amrin suna shiga gida sukayi shashin mumy na ganinsu tafara harare2 suko suka gesheta suka nufi dakin dady,
suna zuwa suka sami dady azaune yana karanta jarida dahike yau weekend ne ,
dady naganinsu yafara murmushi
atake suka durkusa suka geshesa ya amsa cike da farinciki,
dady yace”son meke tafe dakune tare da yar auta tah”,
amaan yafara murmushi yana sosa kyeya ,
dady yace”toh fa ke yar auta fadamin”,
amrin tayi murmushi tana wasa da yan yatsunta tace”uhymm,dady yayane yakeson yakara aure”,
dady yace”masha allah amman gaskiya naji dadin wannan maganar son allah yama albarka ,yar waye kuma a ina suke,?,
amaan yace”babanta ba kowA bane alayin zana ma suke da zama”,
dady yace”owk to nasan dai baku fadawa babban yaya ba ,amman karku damu zan masa magana sai muje gidansu yarinyar ayi bincike,
Page 23
suna tashi dady yanufi shashin babbqn yaya,
yana zuwa ya durkusa yageshe da yayansa,
sannan yace”yaya dama akwai maganar danake so muyi dakai neh,”,
baba yace”toh ina sauraron ka”,
dady yace”dama so nake amaan yakara aure domin ya auro zabinsa tunda dai na hamlat umarni yabi”,
baba yace”toh nidai gaskiya banga amfanin kara aurensa ba tunda dai bawani girma yayi ba”,
dady yace”aa yaya ayanzu kam wa inda basu kai shi bama suna auren fin biyu bare shi”,
baba yace”toh ai danka neh kuyi duk abindq yakamata,amman da sharadi daya”,
dady yace”toh allah yasa bai fi karfinmu ba”,
baba yace”banaso amusguna wa yata koda nq minti daya,neh”,
dady yayi murmushi yace”yaya ai indai dan hamlat ne karka samu damuwa insha allah kome zai tafi daidai,yanzu dai zanje indau liman muje gidansu yarinyar”,
baba yace”toh allah bada sa,a”,
dady yace”amin “,
dady nafita waje yaga amaan yakirasa yace”kaje ka kira min mallam liman sai kazo ka kaimu gidansu yarinyar”,
amaan jiki na rawa yaje yakirq liman suka nufi layin zana,
suna zuwa dady daya ga gidan sai da yayi mamaki amman kuma daya tuni halin amaan sai yayi murmushi,
sun fito kenan sukaci karo da ahlam zata tafi,islamiya tsaf-tsaf ,
ahlam naganin amaan tace”kanina bara ka gesheni bane yau?,
kuma mekazo mana agida?,
dady na bayansu suna ginin ikon allah allah,
amaan yace”sorry aunty ahlam babanki wa ince suke nema shine sukace inkirashi”,
bai gama rufe baki ba sai ga baba yafito yana”ahlam karfi kiyi letti kayi sauri ki tafi ga hadari”,
da baba yaganta tsaye da,amman yace”au yauma tsokanar kika tsaya yi kenan?
amaaan yayi murmushi yace”aa baba cewa nayi ta kiramin kai”,
ahlam,tace”_baba kaga,shine kanina fa na rannan “,
baba yace”to uwar yan son girma naganshi bamu waje muyi magana”,
ahlam ta tafi tana dan wasanta datazo dai-dai wajensu dady dq liman ta tsuguna ta geshesu ,
suka amsa cikin fara,a sannan tacigaba da tafiyarta dady sai binta yake dq kallo domin yar tashiga ransa,
amaan yageshe da baba sannan yamasa iso ga bakinsa,
dady yafadawa baba abinda ke tafe dasu,
baba yayi,shiru sannan yace”to agskiya dai niba kowa bane kuma banda kome sai gidannan dakuka ganshi shima dai ajogale yake dan haka da kunji kunsama wa danku dai-dai ku dan nikam kunfi karfina”,
liman yayi murmushi sannan yace”haba bawan allah ka tuna fq da talakan da me kudin duk allah ne yayimu to dan haka ba wani zancen banbanci kuma mu ahaka mukeson yar taka”,
baba yace”toh nikam ma ai ayanzu banga abinsu,agun ahlam ba domin yarinyace danya shakaf dan nasan kungqma abinda tagqmq yi anan”,
dady yace”bakome mu munaso ahakan indai zaka bqmu zamu cigaba da rainonta har ta mallaki hankalinta”,
baba yace”toh shikenan alhaji gaskiya naji dadi kuma nagode amman zamuyi shawara da mai dakina dai”,
dady yace”bakome mukeda godiya suka rabu cikin nishadi”,
Page 24
bayan baba yashiga gidane yasanar da baba abinda bakinsa suke bukata,
baba tayi shiru domin ko kadan batason abinda zai rabasu da ahlam,
baba yace”nafisa nasan me kike tunani domin ba abu me wasa bane rabuwar mu da ahlam toh amman,in hakan ne alkairy ya muka iya,”,
baba taja dogon,numfashi tace”toh allah yazabq mana mafi alkairi”,
baba yace”amin kinga yanzu sai insanar da yaya ko inzasu kara zuwa sai suyi magana dasu”-,
baba tace”hakan ma yayi”,
suna cikin,maganar,sai,ga ahlam tashigo da gudu ,
baba yace”lafiya ?,
ahlam tace”uhumm yau anbamu hutu neh fa kuma ninazo ta daya”,
baba tace”wow,masha allah yar albarka sannu”,
ahlam tace”baba kasan me nakeso ka siyomin?,
baba yace”aa yata”,
ahlam tace”yar bebi nakeso”,
baba yace”laa ahakan kikeso anace miki aunty kina wasa da yar bebi ke kam dai bazaki girma ba ahlam “,
ahlam tace”uhumm nifa babbace kuma manya ma nawasa ai “,
baba yace”toh shikenan”,
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
hamlat da maama suka nufi wajen boka ,
suka sanar dashi,abinda ke tafe dasu aiko boka yasanar dasu cewa wannan yar tafi karfinsu,kuma yar talakawace sose,amman ba abinda suka isa su mata sai,dai,subita hanyar muzguna musu”,
maamah tace,”bakome sun gode kuma sunada hanyoyi,kala-kala “,
suna fita maamah tace”kinga talakawane inmukaje muka wulakantasu zasu ce,sun fasa”,
hamlat tace”yauwa dama ninafison hakan”,
maamah tace”amman kifara nemomana adress din gidansu tukun”,
hqmlat tace”wannan ba kome bane”,
ahaka suka rabu,
washe gari,
da safe amaan natashi bayan yayi wanka ko break bai yi domin dama basaba masa akayi ba inba amrjn ce tazo ba ,yanufi gidansu ahlam,
ashe hamlat na biye dashi,abaya,
yana zuwa dai-dai kwofar gidan yayi paking aiko sai ga ahlam tafito,zata tafi,skul, yana ganinta yace”morning auntynah”,
ahlam tayi murmushi sannan tace”morning kaninah”,
saj ga baba yafito yana ahlam,muyi sauri karki makara fa,
amaan ya durkusa yageshe da baba sannan yace”baba kabari kawai zan kai ta”,
baba yace “toh shikenan allah yayi maka albarka”,
ahlam aka shiga gaban mota aka harde kafa,
sunfara tafiya kowa dai yayi shiru ,
amaan yace”aunty ahlam kina sona?,
ahlam tayi sauri ta rufe,fuska,
sannan tace”tab kai fa kanina ne sai dai yayanka”,
amaan ya kyalkyale da dariya sannan yace”toh kinason yayan nawa?,
ahlam tace”eh mana indai kamar ku daya,
amaan yace”toh shikenan aunty matar yayanah,yanzu kullum zanna zuwa inkaiki skul kuma indauko ki”,
ahlam,tace”toh kanina nagode ka geshemin da yayanka”,
amaan yayi murmushi sannan yabude mata kwofa tafito,
karaf a idon,uncle salim,
ai tuni,zuciyarsa tafara bugawa,
Page 25
dasauri uncle salim ya kawar da idonsa akansu,
ahlam tace”kaninah byeed”,
amaan yace”aunty byee take care of ur self auntynahr”
ahlam tayi murmushi jindadi sannan tazura da gudu,
alokacin amaan ya hango uncle salim dasauri yakarasa wajensa,
yace”hello abokina”,
uncle salim yayi mutuwar tsaye yace”amaan !
anya ba mafarki nake ba anya kuma kai neh?,
amaan yayi murmushi,
duk da haka dai uncle salim bai yarda ba sai da yakara murza idonsa,
amaan yace”salim dama zamu gamu aduniyar nan?,
uncle salim yace”ai yanzu kam nayarda amaan din na neh ,
daga rabuwar skul ka manta dani ko?,
amaan yace”hmm salim baraka gane bane wallahi bayan munbar makaranta narasa wayata gaba daya kome nawa,yatafi nabi duk yadda zan sameka ammam ba dama”,
uncle salim yace”oh kaga yadda ka kara kyau kuwa gaskiya kanacin kudinka”,
amaan yace”hm salim kenan yanzu dai ga numberta zantafi office ne inka kira ni mayi magana”,
salim yace”ok dama nima inada ajin farko sai kaji ni”
amaan yashiga mota ,
uncle salim kuma yanufi aji,
salim abokin amaan ne sose lokacin suna jami”ah duk inda kaga amaan zakaga salim gama skul ne yarabasu kasancewar ba wanda yasan gidan kowa,
“,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
hamlat nazuwa tasanar da maamah cewa”ta gano gidansu yarinyar fa,amman gaskiya amaan ka chuce ni karasa wadda zaka kawu min akishiya sai yar gidan matsiyata kuma yarinya shakaf”,
maamah tace”karki damu kawata aiko kinga munsamu hanyace me sauki dazamu wulakanta su”
hamlat tace”hmm har fa zuwa yayi wai zai kai ta skul amman gaskiya na yarda dan talaka bai iya samun waje ba amman ba kome zamu nemi taimakon mumy mah”,
maamah tace”yauwa kira manq mumyn”,
hamlat nakiran mumy tafara kuka,
aituni mumy ta rikice sannan tace”kardai kicemin dan matsiyatan nan ne yabata miki rai”,
hamlat tace”uhum mumy au…..bata karasa ba kuka yakubuce mata,
mumy tayi wani ihu tana fadin”karkicemun aure zai yi”
hamlat,tace”eh”,
mumy tace”kutttt, kanbala,iiiiiii aiko wallahi daga shi,har mahaifin nasa basu isa ba sunyi kadan,
yau ba zaman lafiya agidannan ba yar da ta isa tayi kishi dake agidan ubanki kuma a aurota da kudin ubanki babusu wallahi,
yata kibar kuka yanzu aka fara zancen indai dani hajiya salma suke zasu shq mamamki,
antabq wasu ma munji zafi bare mu,
hmmm dai na kukq hamlat “,
hamlat tayi murmushi sannan tace”yauwa mumy nah wallahi har naji dadi kuma infada miki ma yar matsiyata wai yakeso wallahi ko ruwa aka baki agida,su yarinyar baraki iya sha ba,,,
{niko nace ke hamlat har kya fadama wasu kazanta aduniyar nan hmm}
mumy tayi dariyar mugunta sannan tace”aiko sai sunyi dana sanin haduwarsu da shi ma bare ma aurensa”,
hamlat tace”daz my mumy”,
mumy tace”kinga sai anjima yanzu zan bude fagen bala,iii da masifa agidannan”,
Page 26
mumy na gama magana da ahlam tayi waje ,
inda ta tadda dady,afalo alamar dai yanzu tashigo ko kulasa batayi ba tayi,waje inda ta,nufi bangarensu amrin,
tana zuwa ko sallama babu,
baba da mama kawai ganinta suka agabansu kaman anjefo ta da hike hakan ba sabo bane agaresu ko damuwa basu yi ba,
mama ce tace”sannu hajiya”,
mumy ta galla mata harara sannan tace”aiki kikaga inayi da zakimin sannu?,
wato,ku kuna nan kuna hutunku dan son zuciya kunsa danku yakara aure,wai ma dukiyar da kuke kwashewan bai isa haka bane?,
iyeee?,
wato sai kun gama kwashe kome,ko ?,
baba yace”ke salma kinsan dai dagani har mata ta ba sa,o,inki bane ko?,
ba wai kinga muna miki kawaici akan duk abinda kike mana yasa zaki samu damar ci mana mutunci ba,kuma maganar dukiya dakike ta dan uwana ce dan haka nafi ki mulki da ita”,
mumy,tace”ohhh matsiyata ansamu waje,har ansamu bakin magana”,
mama tace”kiyi hakuri kibar mana daki,kuma aure ne insha allah sai dan mu yayi domin samun kwanciyar hankalinsa data mu”,
mumy tayi wata kara sannan tace”wallahi baku isa ba indai kudi na aiki dan ku bai isa yakarawa yata,kishiya ba gwara ya mutu kowa ya huta”,
baba yace”ta allah ba taki ba salma bakisa ki kashe mana da ba in kwanan sa bai kare ba dan haka barmin daki kije chan ki karata”,
mumy tayi wata dariyar mugunta tace”toh me tawakkali,mu zuba mugani”,
sannan ta fita tana cigaba da dariyar mugunta,
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
hamlat sungama kintsa muguntarsu ita da maamah ,
sannan ta nufi office,
tana zuwa ta tarar da amaan nasauri zai fita,
ta kallesa ta gallah masa harara sannan tace”to za,aje gun matsiyata yan uwan matsiyata kenan”,
amaan ya kalleta yayi murmushi yace”hakane fa yar masu dukiya kuma uwar gida agun matsiyaci angon matsiyata,”,
ya kalleta ya kara da murmushi sannan yaci gaba da tafiyarsa,
agurin hamlat ta kame domin tunda take arayuwarta,amaan bai taba fada mata magana irin haka ba duk tsiya tasan yana hakuri da ita, domin kome zata mesa sai dai ya kalleta ya mata murmushi kawai yayi gaba amman wai yau har amaan yafara mai da martani,,,,
azuciyar ta tace”kut lallai matsiyatan nan sun gama da amaan amman bakome zasu sha mamaki,
tashiga office dinta.
amaaan kuwa yatafi yana farin ciki domin zai je yadauko masoyiyarsa amakaranta
Page 27
amaan nazuwa ya tarar da ahlam sun fito kenan ta tsaya tana tsokanar zainab,
zainab ce tace”ahlam wallahi kifita aharkata ni bazanyi fada dake ba kiyi hakuri”,
ahlam tashekye da dariya sannan tace”ashe dai ni din boss ce”,
bata gama rufe baki,ba har amaan yakaraso yana”a’a nidai aunty tah jarumace ba boss,ba”,
ahlam tayi murmushi sannan tace”a’a fa kanina basawa sunfi jarume karfi”,
zainab suna tsaye suna kallon ikon allah,
wai da gaske kanin ahlam ne wannan babban kuma kyakkyawa?,
amaan yace”toh auntynah yanzu dai karki kara fada da kawarki ku shirya kunji”.
ahlam ta shagwabe fuska sannan tace”uhumm bayan itace take hantara tah wai mune talakawa”,
amaan yarike baki sannan yace”ah toh ke kuma karki kara kinji ko?’
zainab tace”nida man mumyna tamin fada nadai na so nake ma tazama kawatah”‘,
amaan yace”yauwa daga yau kun zama kawaye ba fada”,
ahlam tayi murmushi ,
zainab tace”kin yafemin ko”,
ahlam tace”eh”,
amaan yace”toh shikenan dai yanzu bara mutafi kema kije ga kannanki cen anzo daukan ku”,
ahlam da amaan suka nufi mota har amaan yashiga mota yazauna ya lura ahlam fa bata shigo,ba,
ya fito yace”haba auntyna ya baki shiga ba?
ahlam tayi kaman zatayi kuka tace”uhum bayan naga masu kudi bude ma auntynansu kwofa suke nikuma kaki budemin”,
amaan yayi murmushi yace”afwan ranki shidade na bude”,
ahlam tace”yauwa kanina allah yama albarka
amaan ya kalleta azuciyarsa yace”masha allah”,
afili,kuma yace”amin aunty”,
ahlam ta rufe fuskarta dasauri
amaan yace……
Page 28
WASHE GARI
Kamar yadda su Amaan basu da Aiki haka ma Ahlam basu da skul sai islamiyar yammah.
Dassafe Maamah tuni fo gidan Hamlat Inda Ko tashi daga barci,Amaan bai yi ba.
Tana zuwa,kamar munafuka ta shiga dakin Hamlat da hike kwofar abude take tun sallar asuba.
Hamlat naganin Maamah Ta fara kuka.
Maamah tace”haba kawata miye na kuka mufa mata ne munada hanyoyi da ban-da ban,dan haka share hawayenki kimin bayani”.
Hamlat ta share hawayen ta sannan tazauna tama Maamah bayanin duk abinda yafaru tsakanin ta da Amaan jiya.
Maamah tayi murmushi mugunta azuciyar ta tace”ai kadan ma kika fara gani”.
afili kuma tace”aikin banza ni nazata ma cewa yayi zai sake ki,kar kiji kome yanzu akafara ,tunda dai kinsa moma gidan su yarinyar ai kome ya huce”.
Hamlat tayi”murmushin dole tace”yauwa kawata shiyasa nake alfahari dake”.
Maamah tace”umm yanzu dai naga alama ko,wanka ma baki yi ba je kiyi wanka kafin wancen matsiyacin ya fita sai muje muyi aika-aika”.
Hamlat tace”nikam ba sai nayi wani wanka ba shekaran jiya fa nayi zan shafa turare kawai”.
Maamah ta rike baki tace”haba dan ALLAH karki bani kunya mana tashi kiyi wanka aganmu zam-zam ba raini”.
Hamlat bata so ba haka ta tashi tashiga wanka.
tana shiga wanka Maamah tafara mata bincike tadau abin dauka ta bar na bari domin,ita kanta kyamar Hamlat take dan dai tanason abin hannunta neh yasa take tare da ita.
Hamlat batafi minti biyar ba ta fito duk wanda yaganta yasan jika-jika tayi.
Maamah tace”nashige yanzu har kin gama wankan”.
Hamlat tace”hmm kema sanin kanki ne banason wahala arayuwata agidama dan mumy nake wanka wallahi yanzu ko sai naga daman yi”.
Maamah tace”ah kam naga alama turare na aiki,yanzu dai ba wannan ba jeki sa kaya mutafi”.
Hamlat tashirya cikin hanzari aka mulka turare ajiki waje yayi kyau amman ciki tsami.
suna fita suka ga ba motar Amaan awaje Hamlat tayi,tsaki,tace”yanzu haka yatafi gun wa innan matsiyatan,iyayen nasa ne.
Maamah tace”umm ba nan ba muyi abinda ke gabanmu”.
suka nufi gidan su Ahlam da Maaamah taga Hamlat ta tsaya kusa da wani dan gajeren gida,ai tuni ta tun tsire da dariya tana cewa”kar kice min nan ne gidan su kishiyar tamu”.
Hamlat tayi tsaki sannan tace”yo ehmana ai dai-dai su yanemo kamar yadda suke”.
Maamah ta bude baki zatayi magana sai ko hango Amaan ai tuni ta kame kam.
Hamlat ma zatayi magana sai taga inda Maamah take kallo sai da tayi suman tsaye.
Page 29
Amaaan ne tsaye shida Ahlam,wajen suyan,kwosen baba,
Hamlat tace”kambuuuuuu lallai ma wato har yazama bawan su”.
Maamah ta yi dariya iya son ranta sai da ta lura ran Hamlat yafara baci sannan,tace”yoo,bawa na nawa kuma.”.
Hamlat tace”Maamah ki,bari banason,wulakacin,yanzu,dai miye mafita?.
Maamah,ta numfasa,sannan tace”zabi biyu garemu ko,mu bari,Amaan, ya tafi ku koma mu afka musu,yanzu
amman,fa kinsan,inyana nan da matsala”.
Hamlat ta kalli wayar hannunta sannan tace”yanzu karfe,tara da da minti hamsin neh kuma duk nasan karfe goma zai bar wajen nan dan haka mu jira yata,fi kawai”.
Maamah tace”owk”.
aiko suna dan tsayawa jim,kadan Amaan yanufi motar sa Ahlam,ta bisa tana masa bye bye.
Anan ma Hamlat ta kara kulla kamar taje wajen.
*niko,nace tunda ke ba masa kike ba ai sai ki bar masu niya su masa*
Amaan na tafiya sai da sukaga yayi,nisa,
tuni su,Hamlat suka tawo,tana huci kamar zaki yaga nama.
Suna zuwa wajen Baba tace”sannun ku da zuwa na nawa kuke so?.
Hamlat ta gallawa Baba harara sannan tace”kinga mun miki kama da matsiyata irinku ne?.
Maamah tace”ke ko baba me zamuyi da kayan kazantar nan naku ai sai irinku”.
Ahlam tace”kut wai ku suwa ye ne zaku,zo har kwofar gidan mu kuna fada mana magana”.
Hamlat ta dafa kafa dar Ahlam,tace”yo ke yarnan,ai,bamu fara takan ki ba ta kan,uwarki,muka fara tukun nah”.
Ahlam,tayi,murmushi,sannan,tace”hmm kisa,ni,cewa yarinya itace wadda,batasan me take ba,da,kuma sanin,darajar nagaba da,ita”.
Maamah tace”ke yar matsiya kimana shiru”.
Ahlam ta bude baki,kenan zatayi,magana sai,Baba tace”A’a Ahlam,kiyi shiru”.
Hamlat,tace”ai dole kice tayi,shiru tunda kun,riga kun mallake,min miji kun da bai,bayeshi da tsafe-tsafe,”.
Ahlam tace”ku ya isa fa kubar wajennan ku wallahi ba tsoronku nake ji ba”.
Hamlat ta dago,abin suyan kwasen sama sannan tasake shi.
Ahlam tayi wata kara……
Page 30
Ahlam tayi wata kara tana fadin”wayyo ALLAH kafata,wayyo babatah”.
gaba daya baba ta birkice takasa magana tana rikwo yarta.
Hamlat da,Maamah kuwa me zasuyi banda dariya suna”ai wannan kadan ma kuka gani,indai dani kuku”.
Baba ta fara ihu tana fadin”DAN ALLAH jama’ah ku taimaka mana”.
Dasu Hamlat su ka ga anfara nufuwo wajen ai da sauri sukabar gun.
Duk matasan layin suka nufo wajen inda wani mutumi yataimaki Baba yadau Ahlam yakai ta wani kemis da ke kusa dasu.
Ahlam duk tabi ta fita ahaiyacinta ta ma rasa a ina take tun tana ihu har tayi shiru sai hawaye dake kwaranya daga idaniyan ta.
Dakyar likitan yadan yi dara ya wanke mata kafar domin,abin ya chabe da yawa.
kafin agama wankewa har Baba ya iso.
Haka Baba yadau Ahlam suka koma gida Baba dai ta kasa magana domin ji take kamar abin ajikinta yake.
Suna zuwa gida Baba ya kwantar da Ahlam a yar katifarsu, tukun yadawo kan Baba da takasa magana sai zubar hawaye yace”Haba kedai na kukan nan mana ya isa haka, yanzu ki fada min me yafaru,neh ya akayi haka”.
Baba ta numfasa sannan tace”wasu mata ne suka zo,su biyu suna ta fada mana bakyakyen maganganu tun ina kawar da kai har Ahlam ta fusata tafara magana,
suna ta magana akan miji abinda yafi dauremin kai kenan domin ban gane mesuke nufi ba, ban kai ga tambaya,sumin bayani ba kawai naji,Ahlam dita na ihu suka kuma suka yi tafiyarsu”.
Baba ya numfasa yana fadin”INNALILLAHI-WA”INNA-ILLAIHIR-RAJI’UN
wannan wace irin musiba ce me shirin afka mana da duk kan alamu matar Amaan ce”.
Baba ta rike baki tana fadin”dama yana da mata neh.?.
Baba yayi murmushi,yana”eh yana da mata nazabi boye miki ne domin gudun halinku na mata”.
Baba tace”subhanallah gaskiya da matsala domin yariyar nan idonta abude yake zata iya kome”.
Baba yayi numfasa yace”kinga irin halin naku kenan , ita dama tayi hakan ne dan mutsorata muce A,a kuma mu ba kana nun mutane bane ai munsa me muke”.
Baba tacr”Hakane to yanzu dai fatan mu Allah ya bata lafiya”.
Bba yace”yauwa koke fa ALLAH dai ya miki,Albarka”.
Baba tayi murmushi tace”AMEEN AMEEN”.
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
Abangaren Hamlat kuwa gidan iyayenta ta huce domin tasan Amaan ma yana chan.
tana zuwa ta nufi,shashin mumy sai murmushi take.
Mumy na ganinta tace”ya akayine daughter naga kina murna muda muke cikin matsala”.
Hamlat ta shekye da,dariya sannan tace”yoo,ai munga da yar matsiyatan “.
Mumy tayi shewar data fi ta Hamlat sannan tace”yoo yar nan bani nasha mana”.
Hamlat ta kwashe duk,abinda suka gani da wanda sukayi,ta fadawa Mumy.
Bakaramin dadi,Mumy taji ba hakan,yasa sai shewa suke ita da yar ta ba mai wa wani,fada abin nema yasamu.
Amaan,ya fito,daga bangaren Dady kenan yazo,zai geshe da Mumy yaji shewa hakan bai hanasa shiga ba domin yasan,inya tafi ma kansa yajawa wata sabuwar masifar.
yana shiga suka kara kwashewa da dariya.
Hamlat tayi masa wani irin kallo,sannan tace”ango kashe kamshi “,
Page 31
Amaan ko kallon Hamlat bai yi ba yace”mumy ina kwana?.
mumy ta masa wani mummunan kallo tana”na kwana agida na ko baka ga alamun hakan bane?.
Amaan yayi shiru domin in bawai Dady na wajen ba yasan daman bakar magana ce zata hada sa da Mumy.
Ya juya kenan zai fita mumy tace”dan matsiya ta ansamu waje to wallahi baki isa ka dauko ko yar waye ka hada ta da diyata ba bare yar matsiya ta irin ka, kaje chan suna jiranka dan nasan iyanzu sun shiga halin dana sani”.
Amaan najin Mumy ta fada haka gabansa ya fadi domin yasan da wata kullalliya.
da sauri ya fita adakin su ko su Mumy suka cigaba da shewar su dan su aganin su sunyi nasara akan matsiyata.
Amaan na fita ya nufi gidan su Ahlam tuki yake cikin hanzari domin ya riga yagama tsorata,da su,Mumy.
Tunda yake bai taba shiga cikin gidan ba amman yau,afusace ya shige ciki.
Aiko yana shiga ya hango Baba da Baaba sun zubawa Ahlam ido kallon ta kawai suke.
Yana zuwa ya durkusa gaban su baba yana kuka cewa yake”Baba dan ALLAH karku,ce zaku rabani da Ahlam wallahi inason ta bazan iya rayuwa ba ita ba”.
Baba yayi murmushi ya rikwo Amaan na fadin”kar ka damu ai insha ALLAH Ahlam matar kace, baka ji ance matar mutum kabarinsa ba?
to karka damu inda rai da rabo zaka auri Ahlam.
sai alokacin Amaan yaji sanyi aransa .
yace”toh Baaba ya jikin nata”.
Baaba tayi murmushi tace”jiki da sauki yanzu ta samu barci ne”.
Amaan yace”wani asibiti kuka kai ta?.
Baba yace”oh ban da abinka ina zuwa wani asibiti ai kemis din dake anguwar,nan ma ya wadatar”.
Amaan yace”subhanallah kemis!
ai Baba gaskiya ku tashi mu tafi asibiti domin ba awasa da maganar kuna”.
Baba zai yi magana Amaan ya katse sa da cewa”DAN ALLAH Baba”.
Haka suka tashi ba da niya ba aka nufi asibitin *OLA* Dake cikin garin jos.
Suna zuwa aka bawa Ahlam gado domin acewar likitan bakaramin kwonewa tayi ba amman ga dukkan alamu tana da kyan jiki zai iya warkewa da wuri indai ka,kiyaye shi yarda yakamata.
Sai da Amaan ya gama biyan kudin kome sannan yacewa su Baba bara yaje yadawo su Baba sai godiya suke.
Amaan na fita ya nufi gidan Dady amman bai je bangarensa ba ya nufi bangaren babansa.
yana zuwa ya geshesu sannan yasansar dasu duk abinda yafaru .
basuyi mamakin jin hakan ba domin su kansu basu sha agun uwar ta ba bare shi mijin yarta.
Alokacin Amrin ta tashi ta daura abinci da shike taliyace bata bata lokaci ba ta kammala.
suka fita ita da Amaaan .
Suna fita kenan sai ga Hamlat sun fito ita Mumy.
Hamlat tana hango basket din kayan abinci .
ta wage ido sannan tace”……..
Page32
Tace”kambuuuuuuu!
lallai ma ina zaku haka da kayan basket?.
Amrin tayi murmushi tana”yoo banda abinki miye na da mun kai zira zamu kai asibiti”.
Hamlat tayi wata dariyar mugunta tana”ai wallahi baku isa ba kafa ta kafarku”.
Sai alokacin Amaan yayi magana
yace”kinga Amrin zo muta fi karmu bata lokaci gashi yamma tafara yi”.
Amrin tazo zata shiga har ta bude kwofa Hamlat ta bangaje ta tana cewa”ai wallahi kunyi kadan “.
ta shige tazauna abinta.
Amaan yace”ohh ikon ALLAH Amrin shiga baya muje”.
Amrin har zata yi magana Amaan ya mata alama da tayi shiru .
aiko ko magana batayi ba tashiga baya ta zauna.
suka fara tafiya.
Hamlat tafara habaici tana zage zage har da fadin”tun dai mutane matsiya,ta ne dole abi umarnin mu tunda dai azikin mu ake ci”.
Amaaan yayi murmushi
ita kuwa Amrin sai bugawa zuciyarta take tsabar bakin ciki tqyi shiru ne kawai dan Amaan ya nuna bai son tashin hankali.
Tace”kambuuuuuuu!
lallai ma ina zaku haka da kayan basket?.
Amrin tayi murmushi tana”yoo banda abinki miye na da mun kai zira zamu kai asibiti”.
Hamlat tayi wata dariyar mugunta tana”ai wallahi baku isa ba kafa ta kafarku”.
Sai alokacin Amaan yayi magana
yace”kinga Amrin zo muta fi karmu bata lokaci gashi yamma tafara yi”.
Amrin tazo zata shiga har ta bude kwofa Hamlat ta bangaje ta tana cewa”ai wallahi kunyi kadan “.
ta shige tazauna abinta.
Amaan yace”ohh ikon ALLAH Amrin shiga baya muje”.
Amrin har zata yi magana Amaan ya mata alama da tayi shiru .
aiko ko magana batayi ba tashiga baya ta zauna.
suka fara tafiya.
Hamlat tafara habaici tana zage zage har da fadin”tun dai mutane matsiya,ta ne dole abi umarnin mu tunda dai azikin mu ake ci”.
Amaaan yayi murmushi
ita kuwa Amrin sai bugawa zuciyarta take tsabar bakin ciki tqyi shiru ne kawai dan Amaan ya nuna bai son tashin hankali.
Page33
Sun isa dai-dai asibitin OLA dake cikin garin JOS suna zuwa Amaan ya bude mota ya fito Amrin ma ta bi yoshi abaya.
Da har Hamlat ta fuske tana jiransu sai kawai wata zuciyar tace ta dai shiga taga ko su waye.
Amaan nashiga yasamu Ahlam ta farka sai kuka take yayi saurin karasawa yanq”ayya Ahlam di ta kidai na kuka mana ai kin kusa warkewa “.
Ahlam ko kallon sa bata yi ba bare kulasa.
Amriin ta shigo ita sai da ta geda su baba sannan ta karasa wajen su Ahlam.
Tana zuwa tace”ya jiki auntynah?.
Ahlam ta kakulo murmushin dole tama Amrin.
Amaan yace”Amriin zuba mata a………
bai karasa ba Hamlat ta ban kado kwofa.
Dukan su sai da suka razana domin shi kan shi Amaan ya manta ma da ita suka zo.
Tana shigowa ta nufin inda ta hango Amaaan Ta karewa Ahlam kallo sannan tace”Oh anyi asararrun matsiyata dai wato bara dai arabu dashi ba ko?.
Amaan yace”wai miye haka ne Hamlat ke baki da hankali ne?.
Hamlat tace”ai dole kayi tunanin banda hankali tunda anbaka kasha”.
Su baba dai sun tsaya kallon ikon Allah.
Amaan yace”tunda abinda yakowo ki kenan to ki fita ya isa haka inba kinaso na batq miki rai ba”.
Hamlat tayi murmushi sannan tace”Yoo ai ko baka fada bq bazan iya zama cikin kazantar nan ba” .
Ta fice abinta.
Amaan yacewa su baba”Dan Allah kuyi hakuri zan dau mataki”.
Baba yayi murmushi yace”bakome Amaan ai banga laifinta ba kishi ne yaja hakan nidai fatana kana hakuri kar kadau hukunci cikin zafin rai”.
Amaaan yama baba godiya sannan ya tashi suka koma gida shida Amriin Ita kuwa Hamlat daman tayi gaba.
Hamlat ba inda tq nufa sai gidansu ta sanarwa da mumy duk abin da ta gani da kuma abin da yafaru su ka kintsa sabon makircin da aikata wa iyayen Ahlam bayan sun gama Hamlat takoma gida cikin farin ciki domin ita aganinta insuka aiwatar da abinda suka shirya sun gama da su Ahlam.
Kullum sai Amaan yaje yaduba Ahlam a asibiti sau biyu arana safe dq dare hakan yasa Amaan da Ahlam suka kara shakuwa wanda inhar bai zo ba Ahlam kan iya shiga damuwa domin sun shaku .
Hamlat na ankare da hakan domin kullum sai ta bincika ko ansallame su.
Satinsu biyu aka sallamesu domin kuwa kafar Ahlam tq warke sose har ta fara takawa sai sauran tabo shima da dukkan alamu zai bace.
Da Hamlat taji labarin ansallamesu ba karamin dadi taji ba domin kuwa yau zasu kawo karshen soyayyar Amaan da Ahlam.
Page34
Amaaan ne ya dauko su amota domin ko mawa gida .
Suna isa su ka ga wani abu me firgitarwa wanda yasa kaf acikinsu ba wanda ya iya magana sai babba ne yayi dauriyar cewa” *Innalillahi-wa’inna-illaihir-raji’un*”.
Baba kuwa da Ahlam ba abinda suke sai kuka.
Bama su kadai ba ni kai na wannan abu ya rikita ni domin kuwa anrushe gidan su Ahlam ko alamar gini ma babu inba wai wanda yama wajen kyakkyawan sani ba bazai ce da da gida agun ba.
Amaaan yayi shiru kawai yana kallon ikon Allah .
Baba ne yakara dauriyar cewa”haba kuyi dan gana ga Allah mana domin kuwa da abinda yatare mana”.
Amaan yace”baba kuyi hakuri domin kuwa nasan wannan aikin Hamlat ne babu shakka domin ya tuna lokacin dana ji tana waya cewa”take sun rushe kuwa?.
Adai dai lokacin nashiga gida kuma ni wallahi ban kawo tunanin hakan ba.
Baba yace”ba kome Amaan ai nasan ba yinka bane”.
Baba tace”to yanzu ina kake so mu zauna muyi rayuwa ba mu da kome ba mu da kowa akusa” .
Amaan yace”indai wannan ne karku damu dama ina da niyar chanja muku gida nafiso ne agama kafin na muku magana toh kuma angama kuna asibity shiyasa nabar maganar “.
Baba yace”ba ayi haka ba dannan kabari kawai ai wahalar sai tama yawa kuma kaga dama rikici ake akan ka” .
Amaan yace”indai wannan ne karka sa mu damuwa baba ko me zai da wo dai dai”.
Baba yace”aa kadai sauke mu kawai”.
Baba tace”haba mai gida yanzu ina kake tunanin zamu je daga nan ka bari kawai tunda Allah yakawo shi ya taimaka mana”.
Baba yace”toh shikenan Allah ya mana jagora”.
Baba da Amaan su ka ce amin banda Ahlam wadda har yanzu kuka take.
Baba tace”haba Ahlam dina kidai na kuka mana kinga yanzu munyi sabon gida”.
Amaan naji zafin kukanta har cikin ransa yadaure ne dai kawai dan kar ace yayi rashin kunya”.
Da kyar akasamu Ahlam tayi shiru sannan su ka dau hanya.
Ba inda suka nufa sai filin sukuwa inda anan Amaaan yatsaya
Abangaren su Hamlat kuwa sun hadu ita da mumy da maama sun sake kida sai rawa suke ba me wa wani fada acikin su adole suna murna sun samu nasara domin aganinsu tunda suka rusa gidansu Ahlam sun riga sun gama raza na su.
Koda Daddy yashigo ma basu fasa abinda suke ba shiko da hike yasan halinsu girgiza kai kawai.
Amaaan ya yi paking dai-dai wani kata faren gida wanda ni kai na yaban sha’awa domin dan dai-dai na mata daya ne.
Suna shiga……
Page 35
Tana haba yayanah ba ka ganni bane?.
Amaan yayi murmushi yace”Naganki mana kanwata lafiya dai ko.”
Hamlat tayi wani murmushin kissa da kisisina tana shafa jikinsa tare da cewa”uhumm bakome yayana daman ina ma barka da dawowa neh.”
Amaan yayi murmushi sannan yacire hannunta ajikinsa yace”owk nagode sai da safe ko?.
Bai jira me za ta ce ba yayi tafiyarsa yana murmushin mugunta.
Ita kuwa ta kame kam ta rasa abin cewa.
Tafi minti goma atsaye sannan ta shige bangarenta tana kuka batare da bata lokaci ba ta dau waya ta kira mumy ta sanar da ita abinda yafaru Su ka kara kintsi wani Abun da ba mu san menene ba ji nayi kawai Hamlat na dariyar mugunta tana”Shiyasa nake kara sonki uwa ta gari.”
Da haka sukayi sallama
WASHE GARI
Da sassafe Hamlat ta tashi ko sallah ba ta yi ba domin ba sa ba yi kullum tayi ba inbawai Amaan ya tashe ta ba kuma shima din da kyar take yi ba don son ranta ba.
Ba inda ta nufa sai dakin girki ta ciro wayar ta sannan ta bude data domin shiga whatsApp group din da take na girke girke mesuna *ZAINAB SPECIAL KITCHEN* bata taba magana aciki ba domin ita aganinta bata da damuwarsu sai yau tayi sallama tayi sa’a kuwa Aunty *Shaxee* na online ta amsa mata Bayan ta amsa ne ta sanar da ita cewa girki takeso tayi kuma bata iya ba adan koya mata me sauki.
Anan ne Shaxee ta mata bayanin yadda zatayi saukakkakiyar jallop din taliya.
Aiko tana koya ma ta ko godiya babu ta sauka ta daura tukunya akan gass sannan ta soya mangyada ko soyuwa bai yi ba ta zuba wata katuwar albasa da kayan miya tukun ta dibo su karas da koren wake ta raba su bibbiyu suma ta zuba,ta dibo ruwa ta maka akai ko zafi bai fara ba ta dauko taliya leda daya ta juyo,sannan tasa magi guda ashirin.
Sai murna take adole yau tayi girki hakan yasa ta daura ruwan zafi adaya bangaren.
Taliyar bata kai minti goma ba aka sauke akasa a flas din abinci sannan aka juyo ruwan da ko ta fasa bai yi ba aflas din tea.
Da sauri ta koma daki tayi kwaskwarima ta feshe jiki da turare sannan tadawo ta jera abincin akan dinning table tukun ta nufi bangaren Amaan domin ta sanar dashi yazo suci abinci .
Sai wani tafiyar kasai ta take kamar wadda kashi ya taru mata aciki.
Tana zuwa….
Page 36
Tana zuwa ta Domin ta sanar da Amaan tagama hada musu abincin karyawa.
Da ta je kwofar dakin sai ta kasa budewa domin ita kanta kunya take abinka da basa ban ba.
Tafi minti biyar atsaye sai chan da ta ji motsinsa kawai ta daure ta bude kwofar dai-dai da isowar Amaan kwofar kenan.
Dukansu su ka tsaya kallon juna domin kuwa Amaan yasan inba neman masifa ba ba abinda yake kawota bangarensa.
Amaan ne yadaure yace”Lafiya kuwa Hamlat.”
Ta gyada kai alamar eh sannan tadaure tace”Dama na ma na abinci karyawa ne nazo na fada ma.”
Amaan yayi murmushi sannan yace”Kinnsan dai ni bana karyawa sai karfe TARA kuma yanzu bakwai da rabi ne.”
Hamlat ta shagwabe fuska tana”Haba yayana pls na yau fa kadai.”
Ba da son ran Amaan ba yace”To muje.”
Suna tafiya Hamlat na kisisina kamar baza ta tafi shiko Amaan azuciyarsa cewa yake”Koma miye dai na fi karfin ku da ikon Allah.”
Suna zuwa ta bude flas din taliyar shikan shi kamshin in mutum yaji sai cikinsa ya burga haka Amaan yadaure duk da ya fara jin Amai kafin ma yaci .
Ita kuwa oganniyar sai murmushi take tana ta zuba jagwalgwalon ta aflet ta gama zuba mai kafin ta miki masa ta dibo Ruwan tea a cup ta zabga uban suga da madara ta mika masa tare da taliyan.
Tuni Amaan yaji numfashin ya fara daukewa yaso yadaure Amman ina ai cikinsa ya fara gurnani da gudu yatashi ya nufi bayan gida.
Page 37
Yana zuwa sai Amai tun abinda yaci jiya shine yake dawowa .
Hamlat ta biyoshi ta tsaya abayansa Hannu rike da k’ugu tana fadin”lallai ma rainin wayon yayi yawa tsabar bakason cin abincin da nayi shine za ka tsiri amai?
Shi dai Amaan bai kulata ba ya na ta k’ak’a tun amansa .
Ta ci gaba da cewa”lallai ma gaskiya da sa ke.”
Da k’yar Amaan yasamu amannan ya tsaya ya kurkure bakinsa ya juya kenan zai fita yaga Hamlat ta tare hanya .
Araunane yace”Hamlat dan matsa banajin dadin jiki nah.”
Ta kallesa ta galla masa harara tare da tsake sannan tayi gaba.
Da k’yar Amaan yake tafiya Amman wannan bawair Allahn ko tausayinsa ba ta yi sai ma bala”i da ta ke ta faman surfawa haka yadau jakarsa ya barmata gidan .
Da ya je motar ma da k’yar yake tukin haka yadaure har ya isa office dinsa anan ne ya kira likitansa domin yazo ya dubasa.
Hamlat kuwa tunda yafita ta kira mumy da maama tasanar musu abinda yafaru anan ne maama take sanar da ita cewa”ai Amaan yabawa su Ahlam gida.”
Hamlat tace”lallai matsiyatan nan basu daddara ba ko?
Hmmmm
Anan suka yi sak’e sak’ensu Kafin ta shirya ta nufi office yadda dai aka saba waje tsaf ciki tsami.
Bayan an idar da sallar azahar Amaan yasamu karfin jikinsa sose ya nufi gidan su Ahlam.
Yana bud’e k’ofar gidan Ahlam ya gani zaune tana ta karatun ta yanzu tunda tayi ciwon nan ba magana ta cika son yi ba ko tsokanarta bakamar da ba.
Tana hangoshi tayi murmushi ta tashi kenan zata zura da gudu ai tuni ta tuna fa tana da ciwo hakan yasa ta fara jan kafar.
Amaan yace”Ke Ahlam miye haka tsaya mutafi tare.”
Batasan lokacin da ta tsinci kanta da tsayawa da sai ji tayi anriko hannunta ana cewa”Muje mana.”
Ta bude baki kenan za ta yi magana…..
Page 38
Taji Amaan yace”Kanwa Tah? Ahlam ta dago ta kalleshi Alamar bai fada dai-dai ba hakan yashi yin murmushi sannan yace”Auh sorry Aunty Ahlam ya jikin?
Ahlam ta washe baki tare da cewa da sauki.
Sun karasa shiga falo suna shiga Ahlam ta fisge hannunta ta nufi inda baba ta ke ta zauna kan cinyarta.
Amaan yayi murmshi yana”lallai ma wato guduna kike zaki sani.”
Baba tace”Hmm ai Wannan sai ahankali dama ta gun tsokana ne ta fi kauri.”
Amaan yayi murmushi yace”Ina hini baba?
Baba ta amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsa mutanen gidan.
Bayan sun gama gesawa ne Amaan ke tambayar shin ko su na da wani abun bukata.
Annan ne Baba takara masa godiya tare da fadin suna da kome ai .
Bai tambayi baba ba domin kuwa yasan Baba baya nan yabude masa shagon sai da atampopi a sabuwar kasu da ke yan tifa.
Dan haka yatashi domin tafiya yayiwa Baba sallama har ya kusa fita yaji Ahlam tace”kanina!
Sai kuma tayi shiru,
Ya juyo tare da murmushin sa yace”kanwa Tah zo ma na.”
Ita ma da murmushin ta takarsa wajen sa.
Amaan yace”yane Aunty? Yana kallon idon ta.
Ahlam tace”Dama fa naji sauki ne kuma banje skul nakarbo takardar gama aji uku na ba.”
Amaan yaji dadi domin ya kara tabbatar da cewa Ahlam yar kirkice me son karatu.
Yace”toh shikenan ki ba ri zanje da kai na karbo miki da ga nan sai ma muyi maganar cigaban ki.”
Ahlam taji dadi sosai hakan ya sa ta ma sa godiya sannan ta ko ma cikin gida.
Washe gari da safe kuwa Amaan ya shirya ya nufi gidansu bayan sun gesa da Daddy ne yake sanar masa cewa”ai sunyi zama da Baban Ahlam yace kawai duk sanda suke da bukatar ayi bikin ba matsala.”
Amaan yaji dadin hakan matuka yanason ya Ma Dady magana Amman yakasa Dady ya fahimci akwai magana abakinsa hakan yasa yace”Ina ga asa bikin nan da wata ko?
Dasauri Amaan yadago yana murmushi alamar eh.
Dady yace”toh shikenan bakome Allah yama Albarka .”
Amaan yace”Ameen.”
Sannan yatashi ya nufi bangaren babansa.
Yana zuwa yasanar da Baba abin da ake ciki .
Baba ma yasa masa albarka sannan Dady yakara kiransa akan anjima zasu gidansu Ahlam din.
Abangaren su Hamlat kuwa sunshirya tsaf ita da kawarta maama tare da wawiyar mahaifiyarta domin zuwa su gidansu Ahlam sukara ci musu mutunci.
Mumy ce taje tasamu Dady akan bara takai Hamlat asibiti domin ciwon ta na kwokarin tashi.
Dady yace”Adawo lafiya inda shima yanufi gun motarsa.”
Basu san Amaan nacikin motar Dadynba shiko ya hangosu domin bai sanma Hamlat bata gun aiki ba azuciyarsa cewa yake”Allah yakyauta da mata irin wannan.”
Maganar Dady ce dawo dashi yace”Amaan muje mufara dauko mallam sai muje gidan nasu.”
Amaan yace”toh.”
Sun zuwa suka tarar da malam ya fito su kawai yake jira hakan yasa basu bata lokacinsu ba Suna isa gidan Amaan ya hango motar Ahlam achan gefe inda suko su Dady ko lura basu yi ba,tuni gaban Amaan ya fara faduwa addu”ah kawai yake azuciya har suka shiga gidan sannan yayi hamdala tunda bai ga su mumy ba.
Suna shiga Amaan yaje yakira Baba .
Suko su maama sai yanzu suka fito amota domin sun tsaya kitsa irin wulakanci da zasu musu.
Mumy ce gaba suna binta abaya.
Baba yafito suna gesawa da su Dady sukaji anwani bankado kofa idonta rufe da masifa tashigo tana”Ina matsiyatan marasa zuciyan suke ?
Duk kansu kowa ya kame banda Baba wanda yatafi duniyar tunani ko wacece wannan.
Hamlat da Maama ma kamewa su kayi ganin Dady Da Amaan na wajen.
Mumy ta ci gaba da cewa”wai bazaku fito bane talakawan banza da wofi.”
Ta ga dai shirun yayi yawa tana bude ido ta cii karo da Dady tuni ta fara rawar murya domin tasan yau ta kawo karshe hakurin Dady.
Tana”ba fa ba fa nan mu mu ka zo ba maama meyasa zakusa muzo nan nibance muzo ba ba fa.”
Dady yace”ku fita agidannan inba kwaso ranku ya baci .”
Yana fada tare da nuna musu kofa.
Dasauri mumy ta fita inda Hamlat da maama suka bi bayan tah.
Dadyne yabawa Baba hakuri.
Baba yace”Bakome ai mata sai hakuri haka suke.”
Anan dai Dady yama Baba bayanin yadda su ke son auren anan kuwa akasa karshen watan satin ban nan .
Suka yi sallama da su Baba sannan suka nufo hanyar gida.
Mumy kuwa tana nan tarasa ina zata sa kanta domin ita bawai ma ganin Dadyn bane ya fi damunta kar ace maganar aure su ka je yi.
Dady na shigowa yanufi bangarenta .
Tana ganinsa ta mike tana”…
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 39
——————————————————————————————
~AuntyNah AuntyNah banji zafin mutuwarki ba sai yau danazo gida naga yaranki hmm Allah ya jikanki AuntyNah Dukanmu muna kewarki~
_Wannan shafin sadaukarwa ne agareka Amsard dina Yayana Abin Alfahari nah_
Tana, “Haba Alhaji ya za ka min haka wai harda kai za’a hada baki domin a wulakan tah yar ka?
Dady ya mata alamu da hannu yana fadin ,”Da ka ta!
Yanzu duk abinda ki ka je kika aika ta bai yi ba sai kinzo gida ma kinyi wani?, toh wallahi ya isheki na gaji da irin wannan mummunan halin , gashi har kin fa ra ko ya wa yar ki Ko ince har ma ta ko ya.”
Mumy tayi rau da ido domin tunda take Dady bai taba fita mata agiya ba irin na yau.
Dady ya kara da ce wa, “Kuma wallahi indai kikayi sanadiyar fasuwan auren nan to abakin naki auren.”
Ya na gama fada ya yi ficewarsa abinsa mumy kuwa ta zube agefen gado azuciyar ta ce wa ta ke, “Ah lallai akwai aiki agaba na har abin ya kai ga anamin bara za na da aure na hmmm zan bari ayi auren nan amman wallahi yar matsiyata sai kin gwanmace kidi da karatu.”
Bayan ta gama tunanin ta ne ta kira Hamlat awaya ta sanar da ita kome sannan yanzu zasu fara shirin biki.
Hamlat ba ta so hakan ba amman ya ta iya duk jarabar mahaifiyarta ma ta kasa bare ita kuma ita awa.”
Washe gari
Da sassafe mumy ta nufi bangaren Dady bayan ta geshe sa ne ta neman Afwan akan abinda tayi jiya .
Shiko Dady yaji dadin hakan inda ita kuwa azuciyarta ba haka bane.
Mumy tace, “Tou yaushe akasa bikin?,kasan mu mata akwai mu shirye-shirye gwara afada tun huri.”
Dady ya gyara zama yana, “Haka ne fa toh ance dai karshen watan nan inaga asabar din da za to akarshen watan nan shine ranar d’aurin auren.”
Mumy tayi murmushin dole tare da fadin, “Toh Allah ya kai mu.”
Dady ya Amsa da, “Ameen.”
Mumy na barin falon Dady ta kira Hamlat awaya bayan ta gama bayyana mata yadda suka yi da dadyne take cewa, “ki barni dasu wallahi Allah yakai mu ayi Auren da kafar ta zata fita wallahi.”
Hamlat tace, “Hmm mumy ki barni da ita wallahi indai wannan mitsitsiyar yarinyar ce ai kaman nagama da ita.”
Mumy tace, “Hmm ina nan ina kara mana wani babban shiri.”
Ahaka hirar tasu ta kare ba abin arziki sai yadda za ashuka tsiya ake tsarawa.
Amaan ya fito zai tafi office , Hamlat nazaune afalo ,ya kalleta yakau da kai alamar bai ma ganta ba.
Har yaje kwofar fita , Hamlat tace , “……..
Urs preety xayeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 40
——————————————————————————————
Life without you will be like going to sleep and never having sweet dreams~❤❤❤
Haba ango ba magana? ai dai yaci ka tsaya mu gesa .
Amaan ya juyo da murmushin nasa wanda bai kai zuci ba yace, “Au uwargida ai ban lura kina wajen ba.”
Wannan kalma sai da ta taba zuciyar Hamlat Amman ta daure domin ba tason nuna masa tsarinsu ya baci tace, “Hmm Ango kenan To Ina kwana?”
Amaan yace”lafiyalau fatan kin tashi lafiya?”
Tace, “lafiyalau, ya kanwar tawa?”
Amaan yace ,”Wace kanwa kuma? Daman kina da Kanwa ne? ko Amrin kike nufi?”
Hamlat tayi murmushin dole tare da fadin, “Wace kanwa kuma nake da ita bayan Amarya ?”
Amaan yace, “Oh ai sai kice min Ahlam dinah toh tana lafiya kuma tana geshe ki.”
Hamlat ta kasa magana tsabar takaici sai Hmm.
Amaan yace, “Toh nikam natafi sai nadawo uwar gida.”
Hamlat ta so yin magana sai kuma ta tuna da abinda mumy ta fada mata awaya ai ko tuni tace, “Adawo lafiya.”
Amaan ya ji mamakin jin hakan kawai cewa ya yi, “Ameen.” sannan ya fita office.
Yana fita kuwa ita ma ta tashi ta nufi gidan su Maamah sai ta je sun gama tseguminsu sannan ta nufi office itama.
Amaan kuwa yana zuwa yakirawo uncle Salim awaya yazo ya sa me shi a office .
Ba bata lokaci uncle Salim yazo .
Yana zuwa bayan sun gesa Amaan yake sanar masa cewa ,”biki fa ya karato ya kamata mufara shirye-shirye.”
Uncle Salim yace, “Haba dai Har abun ya matso kusa haka?”
Amaan ya ce, “kwarai ma kuwa karshen watan nan.”
Salim yace, “Ah dole musan abin yi .”
Da ganan suka tattauna yadda abin zai kasance .
Sun dade sose suna hira sannan suka rabu akan Anjima zasu hadu suje gidan su Ahlam tare.
***************
Misalin karfe hudu da minti arba”in Amaan ya bar office yaje domin su hadu da Salim.
Suna haduwa Salim yace, “Kaga kamata yayi muje shagon babanta yanzu musanar masa tsarinmu.”
Amaan yace ,”To shikenan muje.”
Suna zuwa gun Baba suka gesa cikin girmamq juna bayan nan ne Salim yake sanar da Baba ce wa, “Suna so in anyi auren Ahlam ta tafi kano karatu sai ta karasa zata dawo kafin ta kara girma.”
Ba karamin Dadi Baba Yaji ba Domin yana so Ahlam tayi karatu.
Baba yace, “Masha Allah ai hakan ma yayi.”
Ahaka suka rabu cikin girmama juna.
Suna barin gun Baba Suka Nufi filin sukuwa gidan su Ahlam.
Suna isa suka shiga ciki Baba ce zau ne atsakar gida tana yanka *latas*.
Da sallamarsu suka shiga ta amsa cikin fara’ah.
Ba ta musu iso ga su shiga cikin daki bayan sun shiga ne suka gesa Anan ne Baba take cewa, “Oh Ahlam fa yau narasa meke damunta taki walwala sai zaman daki tun safe.”
Salim yace, “To anya kuwa lafiya?
Baba tace, “Toh wayasan mata bara nakiro muku ita ko ku ta fada muku.”
Baba ta tashi ta nufi dakin Ahlam ta sa me ta akwance tace, ” to Ahlam kinyi baki kizo ana jira.”
Ahlam tace, “umm Baba tah ni fa bana son fita.”
Baba tace, “Kiyi hakuri kinji auta tah.”
Dakyar Baba ta shawo hankalin Ahlam ta taso Ta nufi falo Baba kuma ta nufi kichin.
Tana zuwa….
Urs preety xayeesherth.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 41
——————————————————————————————
~Your love warms my heart like the glow of a candle light in a midsummer night’s dream.~
“`WANNAN SHAFIN NAKUNE KU KADAI YAN GRP DINA KUCHKAR KISHIYA FANS MY AMBEBY ZAINAB ADAMU MATAR KAWU MY SISTER MY WALIDA MY MOMIN YASMIN MY HAFSAT MY MMN SHAHEEDA MY HUSAINA KAI KUNA DA YAWA FA DUKANKU INA JIN DADIN COMMENTS DINKU KUMA INA ALFAHARI DAKU AMATSAYIN MASOYANA GA PAGE DINNAN KUYI YADDA KUKESO DASHI SAI WA INNDA KUKA ZABA ZASU KARANTA🥰🥰 XaYeesherth luvs u oll❤❤“`
Ta ga Uncle Salim ne da Amaan
Ta washe baki sai kuma ta tuna da wani abu tuni ta bata rai.
Uncle salim yace, “Haba yar kanwata ya yau ku murmushin ma babu.”
Ahlam ta turbune baki kamar za ta yi kuka tace, “Uhum bayan Wannan kanin nawa ne yaki zuwa ya duba ni yau fa kusan kwana uku?”
Amaan da Uncle Salim suka yi murmushi .
Amaan ya durkusa kasa ya kama kunnensa sannan yace, “Afwan ranki yadade.”
Ahlam ta washe baki tace, “Uhum to ba ka ce min Aunty ba.”
Amaan yace, “Au to aunty nah.”
Tace, “Toh tashi kazauna.”
Shiko Salim gaba daya hankalinsa ma yatafi wata duniyar azuciyarsa cewa ya ke, “Dama ni ne da Ahlam mana da na nuna mata cikakkiyar soyayya amman abota tafi kome dole nabarwa Amininah.”
Sai da Amaan yatabo sa tukun hankalinsa yadawo jikinsa.
Amaan yace, “ya dai mutumi nah?”
Salim yace, “bakome naga ai kuna ta soyayya neh.”
Ahlam tace, “Uncle ya maganar sakamakon jarabawar mu neh .”
Salim yace, “Ai sai dai mugodewa Allah tunda duk kun haye sai sarai da cigaba.”
Amaan yace, “kunga hirar nan taku baza ta kare ba gashi ana kiran sallah, Ahlam bamu buta muyi alwala.”
Ahlam ta tashi taje tadauko musu buta ta basu .
Suka fita tsakar gida sukayi alwalarsu bayan sun idar ne Amaan ya kira Ahlam ta karba sannan suka yi sallama .
Har yaje kwofa zai fita tace , “saura gobe ma karka zo sai nasaka tsallen kwado yasin.”
Uncle Salim ya kyal-kyale da dariya yana cewa, “Ahlam wato dai har yanzu halin na nan ko?”
Amaan yace, “Ai sai ma wanda yakaru kuma fa innazo ba bari na take na tafi ba yau ma dan ta ganka neh.”
Ahlam ta galla musu harar sannan tace, “Eh din Nayi.”
Ta musu gwalo sannan ta shiga gida da gudu.
Suka fita suna ta dariya Salim yace, “Wallahi yarinyar nan na birgeni kullum kara girma take amman intama wani abu kamar yarinya in taso kuwa tafi babbar ma hankali da basira.”
Amaan ya numfasa sannan yace, “Salim bazan bo ye ma ba wallahi ina matukar kaunar Ahlam fiye da yadda ake tsammani tun tanq yar karama inaga ma batafi shekaru hudu ba lokacin tafara zuwa makaranta nake zuwa kwofar gidansu domin kawai inganta Kuma ahakan ban taba bari taganni ba sai da ta fara girmab nan domin tsoro nake ji kar ta ce bata so na ko kuma iyayenta su hanani, haka kuma duk randa bangan ta ba kuwa wallahi bana iya barci, shiyasa yanzu inna tuna wai zan aure ta sai abin ya ban mamaki.”
Salim ya ce, “Tab Ah lallai kai neh *Majnon* wannan irin soyayya haka akalla fa kun fi shekara goma kuna tare.”
Da wannan hira suka rabu Amaan ya huce gida shima uncle yayi gidan su.
Urs preety xayeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 42
——————————————————————————————
~Everything in your life is a reflection of a choice you have made. If you want a different result, make a different choice.~❤
“`MATAR KAWU ZAINAB ADAMU SAKO DAGA HAMLAT KIN KUSA KAI TA MAKURA FA WATO KE YAR ZUMUNI HARDA ANKO KO? TO AYI AUREN MUGANI🤪 “`
Bayan Baba ya dawo gida ne yake sanar da Baba yadda su ka yi da su Amaan Baba taji dadi sose tace, “Ai kaga ta kara girma ma kan lokacin hakan zai fi.”
Baba yace, “wallahi kuwa ai ni naji dadin shawarar nan ko ayanzu nakara sanin cewa yaron nan nada hankali.”
Tace, “Sai dai kawai muce Allah yasaka da Alkairi”.
Baba yace”Ameeen summa Ameen.”
********Washe gari*********
Yau ya rage saura kwana uku biki.
Da sassafe Amaan yatashi dOmin yanzu sun fara hidimar biki duk da wani programs zasu yi ba da yahuce daya zuwa biyu, Yana tashi yaje yayi wanka sannan yashirya cikin manyan kaya da kagansa kasan yana cikin farin ciki ba kaMar kwanakin baya ba.
Su uwar gayya Hamlat ko tashi daga barci ba ayi ba.
Shiko Amaan yana fita ba inda ya nufa sai gidan su,yaje ya samin Amrin domin zasuje tadau Ahlam akai ta wajen gyaran jiki da sauransu.
Amrin taji dadi sose domin zata ganin masoyiyarta barin ma tanaso taga Ahlam ta dau wanka domin tasan anan kyanta zai kara baiyana.
Tace masa, “Yaya Ango ai ba matsala tunda ma ta iya karatun hausa ai zama zamuyi tayi karatu sose domin sanin ita wacece.”
Amaan yace, “Ah lallai Amrin ni kike fadawa hakan ma ko?”
Amrin ta kyalkyale da dariya sannan tace, “Yo ai wannan kaza miyar matar ta ka ce sai antashi tsaye anuna mata cewa ita ba kome ba ce.”
Amaan yayi murmushi yace, “kidai na fadan haka Amrin.”
Amrin tace, “Umm nidai bara nadauko hijabi na muje kar lokaci ya kure,domin gun aunty Aisha nakeso muje.”
Amaan yace, “yauwa yar kanwata maza ki zo mu tafi yakarasa maganar yana fita.”
Amrin tayi sauri tasako hijabinta har kasa sannan ta fito.
Suna cikin tafiya Amman yakirowo Salim awaya akan cewar,”Su hadu abakin titin yan TIFA.”
ai kowa ba jimawa sai ga Salim nan,Amrin ta bude kwofa zata dawo baya yace, “Aa wallahi ba matsala ki zauna abinki.”
Amaan yace, “Aa dai da kabari “.
Yace, “Aa kabari kawai.” yashige baya ya zauna.
Bayan ya shiga ne suka gesa da Amrin.
Yace, “Amaan daman muna da kanwa haka baka taba fada min ba.”
Amaan yace, “Hmm ai gashi yau ka gan ta ma.”
Suna ta hira har suka isa gidan su Ahlam .
Amrin ce ta fara shiga da sallamar ta inda Ahlam ta tawo da gudu tana, “Oyoyo Amman fa ni na yi fushi dake.”
Amrin tace, “Umm Auntyna kinsan fa ina skul ne ai da tuni nazo.”
Ahlam tace, “kinci sa,ah kince min Aunty da bazan yarda ba.”
Amaan da Salim suka shigo da sallamar su
Ahlam ta musu iso ga su shiga daki.
Ahlam kam ta manta dasu ma sai zuba takewa Amrin ita ko tana ta dariya .
Baba ce tazo suka gesa sannan tace, “Toh uwar yan surutu ko ruwa ma ba abasu ba?”
Salim yace, “Aa Baba karki damu wallahi daga gIda muke.”
Amaan ya ma Baba bayani akan zasu gurin gyaran jiki dA Ahlam .
Baba tace, “Ai ba kome Adawo lafiya.”
, “Toh Babata Tashi ki shirya zaku fita anguwa .” cewar Baba.
Ahlam ta tashi tashiga daki batare da bata lokaci ba ta fito tana, “Aunty Baba tah kimin Dan sululu na kafin nadawo.”
Dukan su sai da sukayi dariya.
Baba tace, “kunga halin nata ko? kai da kam Amaan kana da aiki agaba.”
Dukansu suka kara dariya sannan suka fitA.
Ahlam tashige gaba abinta Amrin da Salim abaya.
Ba inda suka nufa sai gidan Aunty Aisha, suna isa kuwa Aunty Aisha ta karbesu da karamci da hike damqn me son mutanece ga bar kwanci.
Bayan sun gama zaiyana mata abinda yakawo su Amaan ya ce, “su zasu tafi sai yamma zasu zo su daukeso.”
Bayan sun tafi ne Aunty Aisha tace,”……….
Urs preety xayeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
NASIHA
*Yake Yar uwa musulma;*
_1.Ki kiyaye daga yin surutu da yawan magana,Allah madaukakin sarki yace;_
_”Babu wani alheri acikin masu yawa daga ganawarsu,face wanda yayi umarni da wata sadaka ko kuwa gyara tsakanin mutane.”_
*Kuma ki sanu cewar akwai mala’iku masu rubutawa kuma su dididge duk abinda kike fada.*
_”Alokacin da masu haduwa (mala’iku) biyu suke haduwa daga dama,kuma daga hagu akwai mazauni,baya lafazi da wata maganq face a like da shi akwai mai tsoron halartacce.”_
*Kiyi kokari wajen magana takaitacciya mai ma’ana*
*PAGE* 43
——————————————————————————————
_wayyoo yan grp dina kuchakar kishiya fans kuna nishadantar dani da cmmts dinku ina jin dadi wallahi akullum koda banda niyar cmmts inna tuna ku sai inji karfin gwiwa much luv sisters_🥰🥰🥰❤❤❤❤
_wannan shafin sadaukarwa ne agareki sister LAYUZA KABIR ina tayaki murnar kammala book din ki YAN ARABIC Allah yakara basira_
************
Tace,”Toh Hajiya Ahlam Amarya kafin in fara miki gyaran jiki ya ka ma ta muyi wata muhimmiyar magana ki saurare domin naga kinfi kauri ta wajen abin wasa,ki sani cewa Aure zakiyi yanzu kuma ba ke kadai bace kina da abokiyar zama dole sai kin dage da AZKAR safe,rana,da kuma dare sannan ki san yadda zakina tattalin mijinki, karki yarda ki kasance me kazantar kullum cikin tsafta da kuma kamshin ya kasance jikinki nayi dakin ki na yi haka kuma shima mijinki nayi, kullum karki kasance cikin yin shiga daya inya fita da safe ya barki da kananun kaya to fa kafin ya dawo ki tattabatar kinsa masa doguwar riga ko ko atamfa dai inko da safe atamfa ce ajikin ki to kafin yadawo kinci kananun kayanki, yawancin maza suna, son mace me gashi dan haka ko baki da dashi inkika dage da gyarawa kina masa ado dashi zai ji dadi,haka kuma fannin abinci da drinks yakamata ki koyesu kala kala, sannan kullum ki kasance kina wanka da ruwan lalle basai kin kashe kudin ki awasu abubuwan ba ke da kanki zaki iya gyara jikinki kina shan kunnun wanken suya,gyada,aya,alkama,shinka far tuwa koda sau daya ne arana,Ki kasance me kissa da kisisina awajen mijinki karki yarda da wani cewa kina da abokiyar zama alokacin mantawa da ita zakiyi sannan kuma da ma naga alamun ki na da shagwaba tanan fannin bamu da matsala.”
Ahlam da Amrin su nutsu kawai sauraren Aunty Aisha suke.
Aunty Aisha ta kara da cewa, “Fatan dai kin fahimta.”
Ahlam tace, “eh jiki asanyaye.”
Aunty Aisha tace, “Yauwa haka akeso Amman fa kisaki jiki dani domin ni yayarku ce dukanku kuma ma zan baki wani hausa novel da zAi tai makeki duk akan abubuwan dana fada miki da wanda ban ma fada ba.”
Ahlam tace, “Toh nagode Auntynmu.”
Amrin tace, “Aunty adai rage kar ahauka tamin yayanqh.”
Aunty tace, “Ai sai dai kuyi hakuri kawai domin yayanki sai yaji chanji na mussamman.”
Dukansu suka sa dariya sannan Aunty Ta tashi tana, “Kunga lokaci na kurewa bara muyi mu fara.”
Batare da bata lokaci ba Aunty ta fara dilke Ahlam suna yi tana kara mata wasu bayanin .
Abangaren Amaan da Salim kuwa ba inda suka huce sai wajen telen da yakaiwa dinkunan Ahlam suka karbo .
Dagq nan kuma suka huce kasuwa anan ne suke hira Salim yace, “Amaan gaskiya nima fa yanzu auren nan zanyi dan nasamo mata.”
Amaan yace, “Haba ai wallahi ko dana ji dadi tun tuni anata fama dakai.”
Salim yace, “Ba kowa bace illa kanwar mu Amrin.”
Amaam yayi murmushi yace, “seriouse?”
Salim yace, “Eh mana ko baza abanin bane?”
Amaan yace, “wane ni ai wallahi naji dadin lamarin nan yau mq zan sanar da dady.”
Salim yace, “woo amman gaskiya nagode wallahi .”
Da wannqn hirar suka gama siyayyarsu.
Ahlam kuwa tanan ta fito asak amarya “ko ayau adaura.” cewar Amrin.
Aunty tace”ai ba zama ki gane ta sai mun dau wankan dina.”
Ahlam dai tayi shiru baki ya mutu duk rawar kannan da surutu babu .
Da kyar Aunty tasa tadan saki jikinta aiko ta fara zuba.
Misalin karfe 5 dai dai su Amaan suka dawo daukan dai-dai da fitowa Ahlam daga wanka.
Tana jin su afolo tuni tafara sa kaya kamar wadda suke ganinta.
Auntyce tazo ta bata wasu kayan tace, “tasa .”
Bayan ta gama sawa ne ta fito falo tana fitowa kamshinta yakarade dakin Amaan kawai zuba mata ido yayi azuciyarsa yana cewa, “Aminci da karamci su kara tabbata agun sarauniyar kyawawa.”
Salim ne yace ” Dalla mallam kwanq nawa ne wai anan dinma sai kq nuna halinka.”
Amaan yaji kunya sose domin ya manta ma a inda yke murmushi kawai yayi.
Aunty tace, “Ango kenan.”
Amman yayi murmushi sannan yatashi yna fadin, “Toh Aisha sai anjima mun gode sose sai kuma in mun dawo gobe.”
Aunty tace, “Bakome ai Allah ya kai mu.”
Aunty ta rakasu har wajen get tace, “Ahlam karfa ki manta ki karanta littafin nan.”
Ahlam tace, “Insha Allah Aunty.”
Amrin tace, “umm nima dai asamin nakaranta.”
Aunty tace, “Anki din kema ki fito da miji.”
Dukansu sukayi dariya sannan sukayi sallqma.
_Urs Preety Xayeesherth_
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 44
——————————————————————————————
_Ina kuke yan team 🅰 dangin uwar gida Hamlat fatan kun karbo ankon ku domin gobe fa akwai💃💃ba daku nke ba yan team 🅱 dangin amarya Ahlam abamu waje🤪_
*Yake Yar uwa musulma;*
_1.Ki kiyaye daga yin surutu da yawan magana,Allah madaukakin sarki yace;_
_”Babu wani alheri acikin masu yawa daga ganawarsu,face wanda yayi umarni da wata sadaka ko kuwa gyara tsakanin mutane.”_
*Kuma ki sanu cewar akwai mala’iku masu rubutawa kuma su dididge duk abinda kike fada.*
_”Alokacin da masu haduwa (mala’iku) biyu suke haduwa daga dama,kuma daga hagu akwai mazauni,baya lafazi da wata maganq face a like da shi akwai mai tsoron halartacce.”_
*Kiyi kokari wajen magana takaitacciya mai ma’ana*
Anan ne fa Salim ya fara nema wa zuciyarsa wajen zama agun Amrin Shiko Amaan sai tsokanarsa yake yana, “wato ma ko kunya ko? yanzu dai ka fara girmama ni nazama siriki.”
Ko kulasa bai yi ba yana ta wa Amrin magana .
Ita kuwa Ahlam sai dariya take Amaan najin dadi.
Ahlam suka fara saukewa agida sannan suka je suka sauke Amrin.
WASHE GARI
Da sassafe Hamlat ta tashi Maamah ta zo ta dauke to adole suma an bazana gyaran jiki anje LALLE,WANKE KAI,DAKUMA DILKA.
Amaaan da ya tashi bai ganta ba baiyi mamaki ba domin yasa ba dama da hakan ba yau tafara ba hasali ma bata taba tambayarsa fita anguwa bA.
Ashiryensa ya fito inka gansa kace yau ne daurin Auren, Yana fita suka hadu da salim domin sun riga sun gama magana tun jiya basu nufi ko ina ba sai gidan su Amaan domin daukan Amrin ashirye suka sameta hakan yasa basu bata lokaci ba suku nufi gidan su Ahlam,
Ahlam na nan da kawaye ancika gida adole anfara sha anin biki barin ma su Amrah uwar gaiya.
Amrin ce tashiga domin kiran Ahlam su Amaan sun tsaya awaje sabida gidan acike yake da baki.
Ahlam da Amrah ne suka biyo bayan Amrin,
Suna fitowa Amaan yace, “Toh matata ta fito mallam sai akoma baya ko.”
Salim yayi murmushi yanq, “kai ma ai kasan nafison bayan domin anan sahibata take.”
Aiko Ahlam na zuwa ta shige gaba abinta su Amrah da Amrin tare da Salim ne abaya.
Suna tafiya anata wasa da dariya musamman ma uncle Salim da yake ta tsokanar Ahlam Da Amrah Har suka isa gidan Aunty Aisha.
Suna zuwa batare da bata lokaci ba Aka fara gyara Amarya Aisha takirawo me jan lalle domin ta wa Ahlam kafa da tafin hannu har ma da bayan hannun domin ita tace batason bakin lalle.
Da sauri sauri suke abin domin sukoma da huri kar azo sa lalle.
Su Amaan kuwa gida suka koma domin Daddy da Baba suna nemansa.
Bayan sun gesa ba Dadyne yake sanar masa cewa, “Ga Akwatunan nan nasa anmin order daga DUBAI Guda sabin fitowa ne me seti TAKWAS ka duba ko kayan sunyi.”
Amaan yayi murmushi sannan yace, “Ah Dady ai nasan kome ma yayi ba abinda zance sai dai godiya Allah yasaka da Alkairi.”
Salim ma ya taya Amaan godiya sannan Dady yace, “bakome ai son kome namq naka ne yanzu dai anjima za akai kafin sa lallen danaji su khadija na fada anayi daman dan basu zo bane ba akai tun huri ba Amman tunda sunzo nace su shirya bara su karasa sai akai kayan.”
Amaan yace, “Toh shikenan Dady.”
Shidai Baba ba abinda yakewa Amaan sai nasiha akan yq rike matan shi da Amana kar ya nuna musu banbanci.
Ba tare da bacin lokaci ba duk su Aunty khadeeja sun shirya da hike yar itace babbar yar abokin Dady wanda suka zama dangi guda.
Alokacin suka nufi gidansu Ahlam batare da sannin yau za akawo kaya ba.
Gaba daya yan gidan sunyi mamakin irin kayan da ake shigowa dashi domin kaf acikin su ba wanda yataba ganin irin wannan akwanti GOLDEN me adon gyali gyali kaman huta kuma gashi har guda takwas da jaka zuwa unguwa sannan da karama ta rikewa ahannun,
Ga kayan sa lalle bokiti biyu ta burma hudu.
Gaba daya yan gidan su rasa ina zasu sa kansu dan farin ciki mussaman baba da ta rasa me zata basu Khadeeja ce tace mata, “karki damu wallahi mu kam akwoshe muke daga gida yanzu zamu koma domin aiki ya mana yawa.”
Har bakin kwofa Baba da yayarta suka rakosu suna godiya sai da suka shga mota sannan suka koma.
Ahlam ana nan ansha kyau ko ayau adaura ga LECTURES da Aunty Aisha ke kara mata .
Suna cikin hira Ahlam tace ,”Aunty Aisha Dan Allah ki tambayi Dadynson Hanan yabarki yau muje gidan mu ki kwana kinga ni ban cika kwalliya ba ban iya ba wallahi.”
Aunty Aisha tayi murmushi tace, “Ah yaushe zan bar mijina shi kadai na dai miki Alkawari zan zo da huri kuma har dina ma sai munje.”
Ahlam tace,’ yauwA har naji dadi wallahi.”
Ahaka suka ta hirarsu har aka kammala har akama Amrin da Amrah ma lalle, misalin karfe 4 su Amaan suka zo suka daukesu.
Ita kuwa uwargida ana chan ana hauka.
Aranar da kyar Ahlam suka rabu da Amaan domin yanzu ta fara sanin me ne ne so.
Washe gari🤪🤪
Urs preety xayeeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 45
——————————————————————————————
_Ayiri riii Ayiri riiii banda hanci dana muku guda💃💃💃_
*WAKA TAFARKO*
💃💃💃 _RANAR MUKE JIRA YAU GASHI TAZO_💃💃💃 _NIMA DA TAMBURA NAH GANI NAZO🥁🥁🥁 AHLAM MUKE YI WA ITA DA AMAAN MUYO RAWA 💃💃💃DA MURNAH🥰🥰🥰ANYI AURE_
*WAKA TA BIYO*
_BIKI YAYI BIKI ASHE DA DANGI MUKA KURI🥰🥰🥰MATAN GARIN MU BA ANUNA MASU KOME💃💃💃💃AHLAM DIN MU DADY YA SAI MATA KOME_🥰🥰🥰
_My Abeby Ranar muke jira yau gashi taxo muma da ankunnamu gamu munzo👩🦰👩🦰👩🦰, Ahlam muke jira itada Amaan_
_Mu sanya Anko, muyi rawa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻_
_Kai nifa harna hango👀👀 Ahlam dinmu a high table_
_Up Up Preety waiting 2d next page_
*EHEEM MY PANS KUMA INA JIRAN NAKU WAKOKIN*🤪
Hausawa suka ce Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya .
Yau Asabar 28 ga watan september wanda yakance ranar auren AMAAN DA AHLAM.
Tun asuba tsakinnin gidaje biyun nan yakaure da hayaniya wanda ko ina mutane sun cika sai aiki ake yi banda Hamlat da uwarta wanda tun jiya da daddre ta tawo gida acewar ta , “Ba ayi ba ita ba gwanda tadawo gidan uban tah.”
Suna daki suna ta kintse kintsen tsiyarsu .
Abangaren Amaan kuwa farinciki yake kaman an masa kyauta Aljannah yayin da Ahlam taga abin bana wasa bane tun da akasa lalle jiya da daddare da kyar ta iya barci yau ko tunda ta tashi sallah ta ga anata ciku ciku abin bana wasa bane ai sai tasa kuka,kuka take ba mai tsagaitawa ba.
Tun asuba take abu daya sai karfe 7 da Aunty Aisha tazo ta fara shawo kan ta tayi wanka sannan ta sa daya daga cikin kayan da Aka kawo a akwati Atamface me kyau da tsada kana gani kasan taci kudinta kala uku ne ajiki daga blue,maron sai kuma fari hakan yasa aka dauko mata bluen takalmi da gyale sai karamar jakar hannu .
Ahlam tayi matukar kyau duk wanda ya ganta yasan Amaryace basai an fada ba .
Tana gama shiryata suka cigaba da hirarsu .
Abangaren Amaan ma yashirya yaci farar babbar riga da dizain din blue hula blue takalmi blue agogo da glass fari,suna tare da Salim da sauran abokansa anata hidima .
Misalin karfe 9:00
Aka cika akwofar gidansu Ahlam domin daurin Aure.
Alokacin daukacin mutane suka shaida daurin Auren Ahmed Mohammed Sani(Amaan)
Tare da Aisha Mohammed Rabi”u(Ahlam)….
Abisa sadaki duba dari(1000).
Wa ya ga Amaan sai washe baki ake ana gesawa da mutane .
Yayin da ita kuwa Ahlam taji wannan lamari da tayi wata kara bata kara motsi ba.
Alokacin Amrah ma ta kurma wani ihu wanda duk yan gidan sai da suka raza nah tana cewa, “,Ahlam Dan Allah karki mutu,wayyo Allah na shiga uku.’
Gaba daya yan gidan azagaye Ahlam Aunty Aisha tana ta faman motsa ta Amaan ba nasara.
*To Fah Ana wata ga wata,murna ta koma ciki*
_Urs preety xayeesherth_
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 46
——————————————————————————————
_gaskiya ina fushi da masoyana kuma masoyan book dinnan basai na fada ba kunsan abinda kukayi_
Banda yan daurin Aure da basu san dawar da ake ciki ba.
Aunty Aisha ce ta kirawo Amaan awaya sannan ta dauki Ahlam suka je dakin da ba kowa .
Anan Amaan ya shigo yasame su gaba daya ya birkice suka fara mata Addu”o”i sun kusa Awa daya Ahaka sannan ta farka .
Tana farkawa kuwa Amaan ya miki godiyarsa ga Allah alokacin Aunty Tace , “Yauwa sannu Ahlam tashi kiyi wanka ko?’
Ahlam ta kalli Amaan tace, “Dan Allah karka rabani da gidanmu wallahi inason Baba tah.”
Amaan yayi murmushi yana, “karki damu ai kina tare da babarki yanzu tashi kiyi wanka,ni barin je ana jira na awaje.”
Alokacin Ahlam tayi wanka takara sa wani kayan Aunty ta gyara ta kamar ba ita ba.
Doguwar rigace fara sol me jibin kayan sarauta ko ina ston ne da bit sai kyalli take kome fari ga tashin kamshi.
Sai da tagama kintsawa tsab sannan ta fito yan gidan sunji dadin ganinta haka ai tuni kowa yakomq sabgarsa.
Abangaren Amaan kuwa suna chan Anata hotuna da hira da abokai salim kuwa ana chan an nanikewa Amrin.
Misalin karfe biyar aka zo daukan Ahlam domin zasuje ayi shirin tafiya dina.
Baba ta kasa zuwa wajen yar tata bare ta mata nasiha , Baba ne yayi dauriyar mata nasiha me ratsa jiki wanda gaba daya ya tafi da Hankalin Ahlam..
Haka Aka rike ta domin sata amota ai tuni ta bincike ta je wajen Baba tana, “Babata kizo kisamin Albarka banaso na rabu dake wallahi inasonki ni na fasa auren ki fada musu wallahi nafasa, nace miki na sake shi,na sake shi fa.”
Ta zube akasa tana kuka.
Baba ma sai kuka take takasa magana yan gurun kowa jiki yayi sanyi sai Baba ne yazo yadauketa chak yasata amota.
Ahlam tayi kuka ba iyaka wanda duk wanda ya gantq sai ya tausaya mata .
Gidan su Dady aka huce da ita.
Suna zuwa mama ta rungumeta tana, “Haba yata kidai na kuka ai dani da Mamanki duk daya ne kinji.”
Mama ce ta rarrashi Ahlam har tayi shiru.
Su Hamlat da Mumy kuwa suna daka anata abinda aka saba basu ma san ankawo Ahlam ba sai suka ji Anata guda.
Ai tuni suka leko da suka abin ke faruwa Hamlat tayi wani tsaki tana, “Ashe kuchakar yarinyar nan aka kawo.”
Mumy da Maamah suka hada baki tare da fadin, “kayan takaicI.”
Suka koma ciki abinsu.
Mangariba nayi duk suka yi sallah Aunty Aisha da Amrin nata dibewa Ahlam kewa har ta sake jikinta .
Amaan ya kira Amrin yabata kayan da Ahlam zata sa anjima su Amrah da zainab kuwa anata faman rawar kai kawayen Amarya.
Sai da akayi sallar isha sanan Aunty tafarawa Ahlam kwalliya.
Andau lokaci awajen yin kwalliyar nan domin ta nutsuwa ake bayan sun gamq ne Ahlam tasa kayanta pitch din doguwar riga wadda tayi ado da golden tare da dankwalinta golden takalmin ta golden da pitch karamar jakar ta ma pitch kayan ya mata dai dai kaman ajikinta aka dinka ga sarka da dankunnenta tare dq warwaraye golden da ka gani kasan Ahlam taci kudi ba karamin kyau tayi ba mara misaltuwa.
Amaan ma yashirya cikin shaddar sa pitch me dizen din golden hula ma hka tare da takalmi ya fito sak ango.
Yayin da Ahlam ta fito shima Amaan ya fito sun hadu dukan su sai dai ace masha Allah.
Ga kawaye da Abokai dasukaci ankon golden din kaya .
Gaskiya abin nasu yakayatu bazan iya ceWa kome sai dai MASHA ALLAH
Urs preety xayeesher
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*WANNAN SHAFIN NAKUNE YAYANA DA KAWUNA HASSAN ATK,HUSAINI ATK KUYI YADDA KUKE SO DASHI INA YINKU KAMAR YADDA KUKE YINA IRIN TOTALLYN NAN*🥰
*Khaleesat haiydar agaskiya inajin dadin cmmts dinku*🥰
*PAGE* 47
——————————————————————————————
Ahlam tazo zata shiga motar da Amaan yake Hamlat tayi fit tashige abinta.
Amaan yace, “Haba Hamlat ga motoci da yawa ki zabi wata mana.”
Hamlat takalleshi sama da kasa sanan tace, “Toh awannan naga damar zuwa ko za ahanani ne?”
Amaan yakalle ta yana, “Allah ya kyauta dai,ya ma Ahlam alama da ta shiga bayan ya shiga.”
Haka akayi tafiyar nan kuwa Amaan atsakiya Ahlam da Hamlat agefensa .
Ba abinda Hamlat keyi sai habaici acikin motar nan har suka isa.
Suna isa akace ango da Amarya tare da kwayaye su shigo .
kamar yadda ango yajeru da matan nasa haka ma abokai suka jeru da kawayen Ahlam mussamman uncle salim wanda yake tare da asalin masoyiyarsa Amrin.
Hamlat taki matsawa haka suka shiga tare Amman fa hakan natq ba karamin burge mutane yayi ba,Ita atunanin ta tabata su batasan kara tsarim nasu tayi ba.
Batare da batq lokaciba aka fara dina yayin su ma su *zainab Adam, Amebeby,walida ,mmn shaheeda,maman sadik,maman yesmin,husaina*,Suka fara sambadan abinci ha kakkautawa sai da sukayi hani,an sannan suka shiga fili domin takewa Ahlam alokacin nikuma *Preety xayeesherth tare dasu maman fatima zahra da salma tare da sauran zugata muka shigewa uwargida domin nuna bajintarmu*
Ahlam taki yin rawa kwata-kwata haka ma Amaan sai uwargida da take ta famqn haukar rawanta wanda kowa na gurin ita yake kallo.
Dina tayi dadi sose mussaman inda akazo yanka cake sai dA Amaan yadaga Ahlam sama sannan tabashi ba abinda kakeji sai tafi tare da likin farare da ake kamar ruwa.
Sai misalin karfe 12 dare aka tashi daga dina anci anshq anyi hotuna kamar baza arabu ba.
Aunty Aisha tana ta kaf kaf da Ahlam .
Urs preety xayeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*BANDA LAFIYA WLH DAN ALLAH KU TAYANI DA ADDU”AH YAN UWA WLH WNNAN TYPE DIN MA DKYAR NAKARASA SHI DAGA ASIBITY NAKE ZAKU IYA JINA SHIRU AMIN AFWAN BANDA LAFIYA NE🙏🙏*
*PAGE* 50
——————————————————————————————
Da sassafe Ahlam da Nisher suka shirya tsaf domin tafiya skul dukanninsu cikin uniform me kalan blue da fari riga da sket ne sai karamin hijabi yamusu kyau sose kaman ajikinsu aka dinka.
Amaan ma yafito cikin shirinsa dan haka ba inda suka nufa sai makarantar ASIYANDA dake cikin garin kano.
Amaan ne ke tuki yayinda Ahlam take gaba Nisher ko na baya.
Amaan ya ce, “Nisher ga amana nan nabaki karki bari maza su kulata domin nasan Ahlam dina dai ba kulasu za tai ba.”
Nisher ta ce, “kai yayah Amaan ba ma me kulata ai ba hade da maza muke ba iyaka mata ne kowa da bangarensu.”
Amaan ya ce, “Yauwa toh yar kanwata banda kula kawayen banza dai.”
Nisher ta ce, “Insha Allah br.”
Ahlam ta ce, “Yayan Ahlam choculate.”ta fada tana nuna masa shagon shopping.
Amaan yayi murmushi ya ce, “Daman nasani toh nasa miki ajakarki keda Nisher shiyasa nasiyo katon naba aunty ta ajiye muku.”
Ahlam ta ce, “wooo Yayan Ahlam nagode.”
Amaan ya ce, “Bayan godiyar kuma sai wace kalmar?”
Ahlam tayi saurin rufe fuskarta da hannu.
Nisher ta ce,”uhum fa ina nan naga kaman anmata dani.”
Da sauri Amaan ya ce, “Mu mun isa ma.”
Dai dai da ciga get din skul din kenan.
Amaan yasamu waje yayi paking din motar sannan yabudewa uwar sarauta Ahlam kofa.
Ita kuwa Nisher tuni ta fita dama.
Ba inda suka nufa sai ofishin shugaban makaranta da hike Dadyn Nisher ya gama kome tun kan suzo basu dau lokaci ba aka kai Ahlam ajinsu Nisher Anan sukayi sallama da Amaan domin yau zai koma jos.
Ahlam taji dadin makarantar sose daga ita sai Nisher agun zamansu basa kula kowa.
Banda malamai da nisher ba wanda yasan Ahlam matar aurece tunda tashiga skul dinnan takara kama kanta domin kullum sai Amaan ya mata nasiha mai ratsa jiki hakan yasa batama laifi bare ace za adaketa duk da cewa tasan ma ba dukkanta za ayi amatsayinta na matar aure ba amman tana kiyayewa.
Akullum suna dawowa daga skul suke hucewa islamiya ba su lokaci sai dare ko ranar weekend .
Soyayya kuwa tsakanin Ahlam da Amaan karuwa ta ke akullum sai sunyi waya kusan sau biyar na safe da ban na rana da ban haka ma nadare bayan sun gama waya sai kuma akoma chart.
Ahlam dai ankara girma anzama babbar yarinya kullum da glass a ido ga kwalliya bata taba yarda tazauna batayi koda simple makeup bane.
***************
Abangaren Hamlat kuwa tana nan ta ma manta da sunan waj an mata kishiya cigaba da wulakantA Amaan sai wanda ya karu shiko baya damuwa domin inda sabo yasaba iyakaci yakira Ahlam dinsa awaya ta faranta masa.
******************
Anyi exams din first term dan haka Ahlam ta nami izinin zuwa gida gun babarta Amaaan sam yaki yarda ya ce mata ai shi yana zuwa dubasu kuma itama suna waya dan haka yace mata karta damu Shi zai zo ya ganta.
Ahlam farinciki har zuci dan haka tunda sassafe suka tashi itq da nisher Da faty me aiki sai girke girke ake ita ko Aunty Sai binsu da kallo take tana oh andai ki fadamin wa nene zai zo gashi an bade min gida da kamshi kuma nasan ba sammin za ai ba.
Nisher ta ce, “Ai ko Aunty ki ma maida yawunki domin kamshin ma kin kusa dai na ji.”
Aunty ta ce, “Ahlam yata ai ke dai nasan bazakimin haka ba ko?”
Ahlam tace, “Hm Aunty bari dai naje nashirya in bakon ya rage ma sammiki.”
Faty da Nisher duk suka sa dariya Aunty ta ce, “Ai duk zanyi maganinku bari mijina yadawo fita ma zamuyi.”
Su dai dariyarsu suke.
Ahlam tagama shiri tSaf cikin bakar doguwar rigar tq tayi rolin din gyalen ba karamin kyau tayi ba gashi taci glashi kaman a idonta aka dasa shi .
Ta fito kenan tayi ana kwankwasa kwofa ai da gudu ta karasa .
Tana budewaaaaa…..
Urs preety Xayeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*ALHMDLH NAFARA SAMUN SAUKI GDY NKE MASU KIRA DA MASU MSG*
*PAGE* 51
——————————————————————————————
*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NEH AGAREKI SARATU TA GRP DINA KUCHAKAR KISHIYA FANS KIYI YADDA KIKESO DASH😍I*
Taga Amaan sai murmushi yake sakar mata batasan lokacin data rungumeshi ba sun fi minti biyar suna shakar numfashin juna sai da Nisher da faty suka zo Nisher tayi gyaran murya alama dai basu ji ta ba sai da ta tabo Ahlam .
Amaan yaji kunya ita ko Ahlam sai dariya take tana fadin, “Yaushe kuka zo haka ai ni na manta daku ma agidan.”
Nisher tace, “Ah lallai ma bara yatafi ysn zaki sha mamaki.”
Amaan dai yna tsaye yana kallon ikon Allah.
Ahlam tace, “Umm kyaji dashi nikam kinbarmin miji atsaye.” taja hannun Amaan suka shige Nisher da Faty kuwa sai dariya suke suka bita abaya.
Ba inda suka nufa sai daining table ta ajiye mijinta sannan tafara zuba masa abinci .
Amaan tsabar farin ciki yakasa magana yadda yaga ana tarerayarsa.
Suko su Nisher sun koma dakin mumy suna ta hira da Mumy kafin Amaan ya gama cin abinci su fito su gesa.
Tana zuba masa tace, “Toh Yayan Ahlam inbaka ko zakaci da kanka?”
Amaan ya shagwabe fuska sannan yace, “Aa nidai Auntyn Amaan tabani abaki.”
Ahlam tayi murmushi sannan tace, “Toh bude bakin.”
Ahaka su ka ci abincin nan cike da soyayya da nishadi duk wanda yagansu yasan suna cikin shaukin so.
Bayan Ahlam tagama ba Amaan abinci taje ta sanar da su Mumy da Nisher .
Mumy ta fito da fara”arta tana Ah kucemin angon ne yazo shine akaki fadamin.
Amaan yanata murmushi suka gesa sannan nisher da faty ma suka geshesa daga nan kuwa aka bude fagen hira.
Amaan yaji dadin zuwansa kano sose domin yadauke masa damuwar da Ahlam ke dasa masa agida.
Sunsha luv sose domin duk su nisher basu waje suka yi misalin karfe 5 Amaan yayi shirin komawa jos domin tafiyar dare zai yi .
Ahlam batasan lokacin data fara kuka ba bataso su rabu ko kadan Da kyar ya rarrasheta sannan yabata choculate da turaren da yakawo mata sukayi sallama.
Dare ranar Ahlam takasa barci sai kiran Amaan take burinta kawai ace ya isa gida lafiya aiko sai kusan karfe 2 nadare ya isa sai lokacin tayi Hamdala sannan tasamu damar yin barci harda munshari.
*KUNGA MACE TA GARI KENAN ME DAMUWA DA MIJI BA IRIN WACER KUCHAKAR BA*
washe gari
Da safe Amaan ya fito kenan yatarar da Hamlat nashirin zuwa dAkinsa.
Hamlat tace, “kai ji mana……
Urs Preety xayeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*SADAUKARWA GA DUK MASOYANA WA INDA NASANI DA WA INDA BANSANI BA*🥰🥰
*PAGE* 52
——————————————————————————————
Amaan tsaya yayi kawai yana kallon ikon Allah .
Ita ko takara da cewa, “Ina kaje jiya bakaje office ba?”
Amaan abin yabasa mamaki yama kasa magana .
Tace, “Wai ba dakai nake magana bane?”
Sai alokacin Amaan yadaure ya ce , “Daman kin aike ni ne ko ya?”
ta cE, “ban aike ka ba amman kana aiki a karkashin ubana.”
Amaan yayi murmushi sannan ya ce, “yadda kike takama ubanki ne nima ubana neh.”
Hamlat tayi wata dariyar mugunta sannan tace, “Yoo ai abin ajini yake.”
Tana fada tayi gaba abinta.
Shiko Amaan abin ya matukar ba ta masa rai haka ya juya ya fita abinsa.
Ba Wadda ta fado ransa sai Ahlam dama yau basu sallama ba.
*YAKASANCE KULLUM IN AHLAM ZATA TAFI SKUL AMMAN KUMA ZAIJE GUN AIKI SAI SUNYI WAYA TA MASA ADDU”O”I SHIMA YA MATA SANNAN SUYI SALLAMA*
Yau ma kamar kullum yana shiga mota ya kirasa awaya ta daga da murmushin ta tana, “Sahib Gud morning da har yanzu zan kira naji lafiya?”
Amaan yayi murmushi sannan ya ce, “sahibty sorry ban shirya da huri bane.”
Ta ce, “Bakome ya gajiya.”
Ya ce, “ALHAMDULILLAH.”
Ahlam ta ce, ” *Umm toh sannu Allah ya kiyaye Hanya ya karemin mijina daga sharrin mutum da* *aljan,Allah yabaka sa’a aduk abin da zakayi na alkairy fatana kullum kasamu halal domin gina mana rayuwa* *ingantacciya fatan sa”ah ta kullum tana gareka,Karka manta da alkawari nah banda kallon mata kuma banda kula mata banda murmushi ga duk wata ya mace kasan kanwarka nada kishi* .”
*Amaan yayi wani dogon numfashi sannan ya ce, “Akullum bazan gaji da godewa Allah da yaban mata me ilimi,hankali tare da biyayya ba nasan cewa nazabawa ya ya na uwa ta gari kuma yar uwa aguna ta gari kullum ina kara sa miki Albarka tare da fatan Alkairy akome naki*.”
Ahlam ta ce, “Umm adawo lafiya luv yhu sahib.”
Amaan ya ce, “Allah yasa Luv yhu more sahibty ki kulamin da kanki.”
Ahlam ta ce, “Umm Amin same to u byeeeeeee miss u.”
Ba ason ransu suka rabu da wayar ba kamar kullum .
Ba inda Amaan ya nufa sai office Ahlam ma ta nufi skul.
*KULLUM MGNRKU NAKARA YAWAN PAGE TOH NIMA KU KARA YAWAN CMMTS HAR SAI KUN GAJIDA KARATU*🥰🥰🥰
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 53
——————————————————————————————
*HMM ALLAH YARABAMU DA MUGUN HALI IRIN NA HAMLAT*
Ahlam da Nisher sun dawo daga skul sun gaji dan haka suka kara yin wanka sannan su ka yi sallah su ka ci abinci.
Daddare misalin karfe ta kwas bayan sun yi sallar isha Ahlam ta shiga duniyar yaranar gizo inda ta tarar da ana program din ME AUREN YA KUNSA? awani group me suna *TSARABAR MA AURATA* wanda Aunty Aisha take gabatarwa taji Dadin program dan haka ta bada hankalinta agun inda ta hadu da zainab adamu tare real shaxee suke bata shawarwar domin Aunty Aisha ta gabatar da ita akan cewa kanwar ta ce kuma ta na da aure.
Tana jin dadin group din nan sose har Amaan ya hau suka cigaba da soyayyar me ban sha’awa domin yanzu kullum Ahlam kara kilewa take,Amaan kuwa har yafara kosawa matarsa ta dawo garesa ko dan ya huta da halin jarababbiyar nan.
Ayanzu Ahlam da Nisher suna sss3 amadarsa kuma aji biyar dan haka ta kowani fanni shirin zana jarabawa ake .
Kullum suna cikin karatu dan hakq ma yanzu Ahlam bata samu wata damar yin chart domin ga karatu madarasa ga na skul abin ya musu yawa.
Amaan kuwa sai dauki yake matarsa takusa dawowa kullum su ka yi waya sai ya tambaye ta saura kwana nawa ne su fara exams ita ko Ahlam ta ta masa dariya tana wai miyasa ya damu neh.
*******************
Abangaren su uncle salim da Amrin kuwa dankon so karuwa yake domin yanzu ma ansa biki dai dai da gama exams din su Ahlam .
Hakan yasa Ahlam ma ta biyewa Amaan sai daukin dawowa take domin asha biki.
Safiyar yau asabar Amaan bai da lafiya yatashi da zazzafi sose dan haka ya kirawo Hamlat domin ta taimaka masa.
Hamlat na zuwa ta kallesa ta na, “kalau neh wai ka kira ni ina barci na katashi?”
Dakyar Amaan ya iya cewa, “ki taimaka min wallahi banda lafiya ne ko Doctor ki kirawo.”
Hamlat ta zabga wani uban tsaki sannan ta ce, “Aikin banza mutum sai lalacin tsiya ai da ka kirawo kuchakar matsiyaciyar matar ka ta taimaka maka.”
Amaan sai rawar sanyi yake ba damar magana .
Ta kara da ce wa , “kasani zan kira doctor amman wallahi ba abin da zan taimaka maka dashi ka mutu mah mana.”
Ta juya zata fita abinta .
Ya daure yace, “Ham…. Hamlat ki ki taimaka mi ru ru ruwa.”
Ta yi tsaki tana, ” ka mutu mana wallahi ba abin zan baka godema zan kira doctorn.”
Ta fita abinta.
Urs Preety xayeesherth.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 54
——————————————————————————————
*MASU NEMAN NO DINA GASHI 08103080717 banda flashing😍*
*SADAUKARWA GAREKA SON ABUBAKAR SALE ALQURAMEY TARE YAN GRP DIN KHALEESARTH HAIYDAR*
Tana fita ta kira doctor , “Hello kazo wannan abokin naka wai bai da lafiya.”
Bata jira taji me zai ce ba ta katse wayartq sannan ta nufi bangarenta ko ajikin .
Azuciyar ta tana, “Kai Gaskiya Hamlat baki kyauta ba mijinki neh fa ya kamata ki taimakesa.”
Wata zuciyar ta ce, “Ke dallah yi harkan gabanki me zai sa ki damu akan mutum da bayason ki.”
Ta ci gaba da game dintq awaya.
Ba jimawa sai ga doctor Yazo yana zuwa ya shiga domin shima inda sabo yasaba da halin hamlat dan haka kai tsaye ya huce dakin Amaan .
Ya matukar firgita yadda yaga Amaan ko magana ba ya iyawa tuni ya fara masa allure sannan yasamu ya fAra barci.
Doctor ya kirawo Amrin domin kuwa family doctornsu ne yasan kowa.
Da sauri Amrin ta kirawo uncle salim suka taho bata fadawa kowa ba sabida gudun tashin hankalin iyayen nasu domin Amaan bai cika karamin ciwo ba.
Batare da bata lokaci ba suka iso doctor ya musu bayanin kome tare da maganin da za abasa inyatashi sannan ya musu sallamah .
Tuni Amrin ta fara gyara dakin sannan ta nufi kichin domin dafa masa ruwan tea.
Salim na tare da Amaan yana lura dashi har ya farka sannan yataimaka masa yayi wanka, yasa masa kaya marasa nauyi sannan yakara kwanciya bayan wasu yan mintuna sai ga Amrin ta dawo tare tea a cup .
Salim ne yakara taimakawa Amaan ya zauna yasha tean sannan yasha magani Sannan yakara komawa barci .
Duk abinda akeyi Hamlat bata sani ba illa ma kunnq kida datayi tana ta tikan rawar ta.
******************
Ahlam tana ta tsimayin kira agun sahib dinta Amman taji shiru tun tana kawaici har ta fara nuna damuwarta akai ta kira ba adauka ba ta dunga kira ba adauka ba da hike wayar a silent take ba me ji .
Gaba daya hankalin Ahlam yatashi tq kasa zaune ta kasa tsaye ko abinci ma yau ta ka sa ci har su Aunty da Nisher sun fuskanci akwai damuwa.
Aunty ta kira ta tana tambayar ta takasa magana sai da aunty ta lallabe ta ta ce, “Aunty Yaya Amaan …. Ta kasa maganq sai kuka .
Dakyar aunty ta kara rarrashinta tukun ta ce, “yaki daukan kira na kuma bai kiran ba .” ta cigaba da kuka.
Aunty ta ce, “Haba Ahlam ki masa uzuri mana watakila wani aiki ne ya rike sa bari muga nan da rana ko ba zai kira ba ko? karki damu nasan yana busyne.”
Da haka aunty ta lallaba Ahlam har ta samu nutsuwa.
Ai ko tunda tasamu nutsuwa tadau wayarta tana ta tura masa text messege ko gajiya batayi sai kalame take zuba masa.
Amaan ya farka kenan ya ce, “Amrin Ahlam kar tayi kuka ku bani wayata.”
Salim ya ce, “Kai oga ka bari kasamu nutsuwa dai ko?”
Ko kallonsa Amaan bai yi ba ya amshi wayarsa aiko yafara karo da massege kusan 20 missed calls 50
*WAYYO AHLAM*🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣
Urs preety xayeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*MY DIJA INA TAYAKI MURNAR FARA SABON NOVEL DINKI ME SUNA GIDAN AURE NAH ALLAH YASA AGAMA LAHIYA I PRAY FOR MORE SHARHI TO UR NVL😍*
*PAGE* 56
——————————————————————————————
*Sarauniyar Sharhis my walida ina Alfahari dake tare da gimbiyar Sharhis My Ambeby ko da banyi niya type ba inna tuna kuna jira na fa sai naji karfin gwaiwar fara wa i really luv yhu hoo😍*
Haka soyayya ta cigaba da bunkasa tsakanin zukatan masoyan nan guda biyu wa inda kusan kullum suna tare awaya duk da basa ganin junansu hakan bai hanasu yin abinda ya kamata.
Biki sai karatowa yake yayinda jarabarwa su Ahlam sai kara raguwa take.
Yau ya kasance ranar exam din karshe askul da kuma islamiyyah.
Kamar yadda suka saba kullum kan ta tafi exam sai Amaan ya mata Addu”ah haka yakasance yau ma yq mata doguwar Addu”ah tare da fatan Sa’a.
Ba da son ransu suka rabu awayar ba sai dan kowa yaje ya ai watar da abinda ke gabansa.
Ahlam na dawowa aka fara shirya kayan komawa gida sai dauki take banda nisher waddq duk ta damu domin ta riga ta gama sabo da Ahlam da kyar Ahlam ta nuna mata ai basu rabuba ta dan kwantar mata da hankali sannan itama ta fara himmar shiri domin da ita za a bikin.
Amaan ko ya bazama kasuwa sai siye siye yake wa Ahlam.
Hamlat na gida Hankali yafara tashi domin da ashirmenta ta manta ma tana da wata kishiya sai yau da taga Daddy ya turo mutane ana gyara bangaren Ahlqm ai tuni karamar haukar Hamlat ta motsa, Dan haka tuni ta kira uwar ta suka cigaba da muguyen shirye-shiryensu har maama tazo da wasu maganin mata wai adole Hamlat tasha domin ita zata zamana amaryar ba wata kuchaka ba.
Tuni mumy ta samu Dady akan cewar sai an sauyawa Hamlat kayan Daki.
Ba musu dady ya amsa domin baya neman rigima hakan yasa akayi odar kaya daga dubai aranar ya biyo jirgin yamma aka kawo wa hamlat.
Ba abinda Hamlat take sai washe baki.
Ita ko Amrin ta na nan anata faman shirye-shirye Aunty Aisha da kanwar ta Maryam kawar Amrin din sune agaba dan ko kayan su Ahlam ma Aunty Aisha ce ta tsara kome.
Washe gari
Da sassafe Su Ahlam,Nisher,Aunty Da Dady suka dauko hanyar jos domin yau ne sa lalle kumA Daddyne waliyin Amrin so anq bukatarsa da Huri.
Hamlat kuwa antashi da gyaran gida ko gidan biki ma bata nufa ba kuma ita ba aiki take ba ta tsaya yima masu jeren iyayi tun suna kawaici har sun fara bata rai domin tsurfarta tayi yawa ahakq dai har aka gama jeren.
Amaam kuwa yana tashi ya nufi gida domin bai da burin da ya huce yaga sahibtynsa yau dan haka yayi shigar dq ta fiso wata manyan kaya ya sa glass da agogonsa yayi matukar kyau sose kamar shine angon goben.
Su Ahlam sun iso Amaan na tsaye ya zuba ido yaga fitowar Ahlam Auntyce tafara fitowa sannan daddy sai ga Nisher daga karshe.
Amaan dai yadaure yanata gesawa da mutane ammqn sai leke leke yake ta ina zai ga sahibtynsa amman ba alamarsa daga karshe dai ya ce, “Nisher wai Ahlam din fa?”
Nisher , “Tayi shiru sannan ta ce umm ai bata da lafiya mun barta agida.”
Amaan ya ce ,”what?”
kan kace me har yafara zufa.
Nisher ta huce Abinta ta barsa.
Ga zufa ga jiri Amaan ya fara rikicewa har yakusa kaiwa kasa yaji anriko sa.
Urs preety xayyeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*Yah hassan atk ysn nagaji kajo muyi type dinnan yau*🤨
*PAGE* 57
——————————————————————————————
*UMMU ABDALLAH TA GRP DINA K$K FANS WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE AGAREKI KIYI YADDA KIKESO DASHI*😍
Ahlam ta ce, “haba dai sahib dina kai fa gwarzo neh karka bada maza.”
Amaan yayi murmushi sannan ya ce, “Umm sahibty bakisan yadda kike azuciyata bane aduk sanda naji kewarki zuciyata radadi take narasa gane meke min dadi aduniyar nan.”
Ahlam tayi murmushi , “Ummm naga alamun hakan da ido na amman yanzu dai zo mushiga ciki, Kaga ina su inje inga mumynah me anjima.”
Suka shiga suna yar hirarsu kadam kadan Amrin na ganin Ahlam ta tawo da gudu tana murmushi ta rungume ta tare da fadin , “Oyoyoooo er uwata .”
Gaba daya gida ya kaure da surutai ta ko ina shiko Amaan idonshi nakan Ahlam ya kasa saukesa azuciyarsa ba abinda yake fadin sai, “Masha Allah na godewa Allah da ya mallaka min wannan diyar amatsayin abokiyar rayuwa.”
Ahlam anzama babbar yarinya koda mumyn Hamlat tazo ta ganta sai da ta tsorata tuni ta kira Hamlat awaya tana fadin, “Hamlat dole mutashi tsaye bakiga yadda yarinyar nan ta kara girma fa kwarjini ba hmm sai kinganta kawai kizo ynzu ina jiranki.”
Tuni Hamlat ta harzuka ta bar masu aiki suka cigaba da gyaran gidan ba wanka haka ta nufo gida..
Aiko tana zuwa ta tarar da Amaan da Ahlam suna zaune afarandar su mamah .
Basu san ma tazo ba sunata hirarsu sai shekewa da dariya suke Amaan yace, “Oh lallai yanzu Matata angirma rigima ta ragu andai na cewa sai nace Aunty.”
Karaf Hamlat tace, “Eh tunda yan matsiyata sun hadu atare ai dole amallake juna gaba gaba mq uwarka zaka fara ce mata.”
Ahlam ta kalle ta sama da kasa sannan ta ce, “yoo ai dan hakin da ka raina shike tsole maka ido amman ki san cewa rashin mutunci ga mijinki ba abin alkairy bane zai iya kaiki ga halaka yan matsiyanta da kike gani sunfi wasu masu dukiyar wadatar zuci tare da sanin darajar dan Adam .”
taja hannun Amaan da ya tsaya kawai yana kallon ikon Allah tace, “Sahib hakuri zakayi da jahilcin wasu masu kudin muje ka kai ni gun babata nikam.”
Amaan ya bita kaman rakumi da akala ita ko uwar mata ta tsaya kaman dutse awajen.
Ba inda suka Nufa sai gidan Su Ahlam da gudu ta shige tana,” Babata me kumatun cincin ina kike neh?”
Baba ta fito tana fadin ,”oh Angirma ba afasa halin ba.”
Amaan da Ahlam sukayi dariya atare .
Baba ma yafito yana dariya.
Ahlam ko zama vatayi ba tanufi dakinta tana za bincike agidan Amaan ne ya tsaya suka gesa sannan suka fara hira dasu baba da baaba sai da baaba ta kwallawa Ahlam kira sannan tazo.
Suka fara shan hira halin nan dai na nan na surutu sai labarin su nisher ake ba wa su baba .
Amaan ya tafi akan sai dare zai dawo ya dauki Ahlam.
Aiko taji dadin hakan domin ta kara bude sabon fagen hira.
Urs preety xayeesherth.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
_WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE AGAREKI MY KISHIYAS FATIMA ZAHRAH TARE DA DOTE MEENARLUV KUYI YADDA KUKESO DASHI INAYINKU IRIN TOTALLYN NAN😍_
*PAGE* 59
——————————————————————————————
Misalin karfe 8 Amaan da salim suka zo daukan Ahlam.
Ahlam tuni ta murza ido zatayi kuka tare da kebe baki.
Da kyar Baaba ta shawo kanta tukun ta tashi suka tafI da nufin gobe su baban zasu zo biki ai.
Suna shiga mota Salim yasa Ahlam agaba da tsokana.
Tuni Ahlam ta ware ta fara zuba.
Amaan dai sai murmushi kawai yake domin zuciyarsa fal take da farinciki.
Suna isa gida Salim ya nufi gun amaryarsa ita ko Ahlam ta makye amotar masoyinta.
Amaan yace , “Sahibty?”
Ahlam tayi wani war da ido sannan tace , “Sahib .”
Sai da Amaan yaji jikinsa ba laka gaba daya ta kashe masa jiki.
ya kara da cewa, “Duk da cewa gobe zamu tare Amman inaso tun yau nabaki Amanar kai nah, Ahlam Dan Allah karki nunamin hali irin na Hamlat nabaki Amanar kai na karki wulakanta ni karki tozartani.”
Ahlam, “Ta Juyo gareshi tare da rikwo hannuwansa guda biyu sannan ta sun kuyar da kanta kasa tare da fadin, “Yayanah Ai aganina nice amana agareka duk yadda ka tafiyar dani da haka zan taso kuma ina maka alkawarin cewa insha Allah baraka yi kuka dani ba azamantakewar har abada.”
Ba karamin jindadi Amaan yayi da jin wannan kalman daga bakin masoyiyarsa lallai yasan yasamawa ya’yansa uwa ta gari.
Sunyi hira sose har sai da salim yazo tafiya Amrin ta rakosa sannan tace, “Toh Masoya Aunty Ahlam sai aje mama nakira ankawo kayanmu ki gwada kar sai gobe asamu matsala.”
Tuni Ahlam ta fito tana, “Byee Bye Sahib inlaw na kira ma hadu awtsp.”
Takarasa maganar tana tafiya.
Salim da Amrin suka shekye da dariya .
Amaan ya bata rai yana fadin, “Ina kun koran min ita kunji dadii.”
Amrin tace, “Ayyah bldly wlh da gaske nake mama na kiranmu kaga nima natafi.”
Tabar Salim Da Amaan.
Amaan yace, “wlh kaa kiyayeni ko gobe nafasa baka kanwata.”
Salim yace, “Wane ni Ayi hakuri ai Amrin ta zama jinin jikinah kaga tafiyatq mah.”
Amaan ya juya yana dariya ya shige bangaransa na gidan.
**********************
Hamlat ta koma gida shiru Bataji shigowar Amaan ba ta zauna tayi shiru kamar abin tausayi haka ta kwana afalo.
WASHE GARI
Yau take ranar daurin Auren salim da Amrin tare da tarewar Ahlam agidan Amaan gaba daya gida yaciki dangi da abokan arziki anata shige da fice .
Yan daurin Aure sun halara tun kan lokaci ya cikA.
Su Aunty Aisha,Aunty Ambeby Aunty Walida,Sister,Ummu Abdallah,Hussaina,Aisha Humaira my Kishiyas fatima zahrah,zainab Adamu, Duk sun hallara musamman aunty Aisha da Ambeby suna gefen Amare sai lectures suke musu.
Ambeby ta fara da cewa bara na fara dake domin kece me babban matsala wanda inkin ssn yadda zaki bi ba wata matsla bace zai zama bakome ba da farko dai karki taba ma er uwar zamanki rashin kunya karki taba shiga harkarta inba ita tashiga taki ba dags gesuwa shikenan yawadatar .sannan abu mafi mahimmanci kinunawa mijinki so da kauna karki taba nuna masa wata damuwa akan abokiyar zamanki, nuna masa kullum ke cikin farinciki kike gyra dakinki fese shi da turare ta ko ina shi ma mjinki kulllum kan ya fita ki feshe shi da turare ,karki bare ya fita batare da kin fadamasa kalaman da ko ina yaje yana tunawa ba ki masa Addu”o”i kullum kan ya fita ,sannan in yafita yabarki da kananun kaya toh kan yadawo ki tabbatar kinsa wani launin irinsu atamfa ,gyaran jikin da na mijinki karki sawa kanki kunya zagewa zakiyi ki gyarashi kema ki gyara kanki,girki kuwa kullum kina masa kala kala mussaman abubuwan da kikasan yafi so,nunawa danginsa so kaman naki ,aganina inkika rike wannan kin gama da kome.”
Anan sauran ma suka daura akan na ambeby Amrin da Ahlam sun sha nasihohi wanda dukansu sai da suka fara kuka.
Adai-dai wannan lokacin dumbin jama”ah suka sheda daurin Auren Amrin da Salim.
wayaga Salim sai washe baki yake yau yazama ango Amaan ma yasha kyau sai murmushi ake ana gesawa da mutane.
Misalin karfe 4:00 aka tafi kamu domin anaso akai kowace amarya gidanta kan 8 nadare .
Anje gurin kamu anjagije Anci ansha kowa yaje amman banda hamlat domin ita yanzu ne tafara sanin asalin zafin kishi takasa moruwa tana gida shiru .
Angama kamu lafiya daga nan aka huce da kowace amarya gidanta .
Amaan yana tare da matarsa dan Haka tare aka kaisu Nisher da Ahlam sunyi kukan rabuwa sose shiko Amaan ko ajikinsa so yake ma baki suyi su basu waje.
Hamlat tunda tsji shigowarsu ta rufe kanta adaki taki fitowa munafukar kawarta kuwa maama bata zo shiyads kadaicin ya mata yawa.
Kowa ya watse daga Amrin sai Salim haka ms abangaren Amaan daga shi sai Ahlam.
Amaan yace, ”
Urs preety xayeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
_Wannan shafin nakine my eyman marubuciyar wata rayuwa ina tayaki murnar dawowa gida😍_
*Amin afwa a page din baya nayi mistake maimakon nasa 58 sai nasa 59 to gashi na cigaba ahakan kawai*
*PAGE* 60
——————————————————————————————
Toh Auntynah Atashi ayi sallah ko mu godewa ubangijinmu da ya nuna mana wannan rana me cike da alfabarka.”
Ahlam tabatace kome ba jiki asanyaye ta tashi ta nufi toilet ta dauro alwala sannan Amaan ma yaje yayi suka gabatar da sallar isha sannan suka kara raka”ah biyu na godewa ga Allah.
aranar Amaan ya nunawa Ahlam soyayya iyakq soyayya wadda ake kira da masoyan asali Dan haka cikin farinciki suka kasance.
Washe gari da sassafe Hamlat ta tawo rikye da kugu tana bugawa su Ahlam daki .
Amaan yana jin hakan yasan itace dan haka yaki sauraronta.
Ahlam tace, “Yaya buga kwofa fa ake.”
ya ce, “eh ai naji barta nasan Hamlat ce kuma ba abinda tazo nrma sai masifa.”
Ahlam tayi rau da fuska sannan ta kara tausasa harshenta tace, “please ka bude mata bamu san ko wata matsala take dashi ba.”
Ahlam ta matukar ba Amaan tausayi hakan yashi yatashi ya bude kwofar.
Yna budewa Hamlat ta bangaje shi ta shige tare da fadin, “wato ma sai anbaka izini zaka bude ko, tun yanzu ka Zama mijin tace nan gqba kuma sai dai mijin kan tace.”
Amaan ya ce, “waike yaushe zakiyi hankali neh.”
Tace, “dakata mallam bara nagama da yar matsiyatan chan kan nadawo gareka ta nuna Ahlam da hannu sannan tace wallahi wallahi ki kiyayeni inkinga kin zauna agidannan to sai bayan raina domin nan gidan ubanane ba gidan ki ba.”
ka bakin Ahlam kuwa ta ce, “Ayyah Aunty ai kya bari mugesa ko? ina kwana ai ni ban ma san kin shigo ba.”
Tsabar takaici Hamlat ta rasa me ma zatace tuni ta fita adakin tare da tsaki.
Amaan kuwa tuni yakoma ga matarsa tare da murmushin sa yana fadin, “yar Albarka gaskiya kin kyauta kin nuna min cewa kece babbar ita kuma yarinya.”
Ahlam tayi murmushi sannan tace, “umm kaga tashi muje mu daura breakfast.
Amaan yatashi sukaje kichin suna hirarsu suna girki aiko sai ga Hamlat ta dawo.
,”Hmmm lallai ma agida ake fitsarancin nan ?”
Ahlam ta Dago tare da fadin, “Ayyah aunty kina cewa gidan mijinmu dai ki inaga hakan zai fi.”
Hamlat data wani tunzura ta fisge wukar da take hannu Ahlam ai ko tuni jini ya fara fitowa ahannun Ahlam .
Amaan ya rikice Ga Ahlam ta fara kuka.
Ta yanka ta sose jini saj zuba yake.
Juyowan da Amaan zaiyi ya waskawa Hamlat mari..
Hamlat ta….
Urs preety xayeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*Sadaukarwa ga duk masoyana wa inda nasani da wa inda bansani ba mussaman sarauniyar sharhi walida tare da gimbiyar sharhi Ambeby ina yinku irin overn nan😍*
*PAGE* 62
——————————————————————————————
Tace, “Toh fah anbar tuwon dawa agida yanzu an samu na semo sai rawar kai ake.”
Duk acikinsu ba wanda yadago ya kalleta bare ma ya kullata.
Data ga haka ta nufi hanyar fita.
Amaan yace, “Ina zaki da safiyar nan?”
Tajuyo sannan tace, “Gun uwata wadda tafi kowa sona domin ta ban abinci nacI.”
Tana kara fada tayi ficewarta abinta.
Amaan ya kalli Ahlam ya girgiza kai kawai.
Ahlam ta rikwo hannunsa tare da fadin, “Haba nasan fa sahib dina gwarzon na mijine da ma ka iya hakuri da ita bare yanzu,please ka cire damuwar nan aranka.”
Amaan yace, “Hmm Sahibty bazaki gane bane wllahi kullum halin hamlat fa kara gaba yake ba baya na rasa ya zanyi da ita ta gyara wannan muguwar dabi”ar da Mumy ke koya mata ta gane gaskiya.”
Ahlam tace, “Hmm indai wannan Kama cire aranka domin ta kusa gano gaskiya indai tanasonka toh zata fara nuna kishi akanka daga nan kuma zataga ba abinda yakamata da tayi illa tama biyayya,shiyasa wani lokacin ma sai naga alamun zuwanta nake kara ma wasu abubuwan ba wai dan taji haushi bane sai dan taji kishi tayi tunanin yi maka abinda yafi hakaN.
Amaan yace, “Wooo er karama me kwakwalwar manya anya kuwa bana nemi su Auntynan naki ba daki bane labari Aunty Aisha,Aunty Ambeby,Aunty Walida dama sauransu domin nasan wannan duk darasun sune.”
Ahlam ta galla masa harara tare da fadin, “Auntinane ni kadai bara kamin kwace ba eheee.”
Amaan yace, “umm shine wato harda harara ta ko zan kamaki ne.”
Ahlam ta tashi tana masa gwalo sannan ta shige daki da gudu tana dariya.
Amaan yataso yabita yana zaki sani inna kamaki yau ko zakamin indiancin yan rugarku.
*********************
Hamlat nazuwa bata bari dady yaganta ba ta nufi dakin Mumy ta zaiyanewA Mumy kome aiko mumy tafara surfa bala”i tana, “Ni Wallahi hamlat har kin fara bani kunya,bazakiyi kasa kasa da er matsiyantan nan ba iyee? ai wlh da kin kwara mata ruwan zafinnan ma ba iyaka yanka kadai ba maza maza kije ki kira maamah kuje gidan tare da kuma dukan tsiya bana son raini fa.”
Hamlat tace, “mumy ba wani zancen duka yamzu fa ni burina kawai ta bar min gida .”
Mumy tace, “ok ga wata shawara in bata yi aiki ba ma gwada na dukan kawo kunnnenki kiji.”
Hamlat tace, “Wooo mumyna shiyasa nke kara sonki wallahi kin iya kissa da kisisi na Amman kinsan miye ba yau ba sai randa kwananshi adakinta ma yakare abin zai fi sugar.”
Mumy tace, “Yoo ai bakome hakan ma dabarace.”
sai misalin karfe 6 takoma gida inda tA tarar da Ahlam da Amaan suna wasAn buya.
Amaan ido rufe ya fito yana , “sahibty wallahi nagaji ki fito fa inkikasa na fadi kukq zanyi wallau.”
Ahlam tana ta dariya abinta.
Sai ga hamlat ta banko kwofa.
Amaan yace, “yess ysn sai nakamaki.”
Juyowan da zaiyi ya chafko Hamlat….
*Urs preety xayeesheerth*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*BANCE KOME BA DOMIN NIMA SAI DA NAYI 😭*
*PAGE* 64
——————————————————————————————
Ahlam tace, “umm nidai ba ruwana.”
Anan suka manta da zancen Hamlat suka fara hirarsu.
Wunin ranar zubur Hamlat ta kasa fitowa waje kwata-kwata.
Yau Ahlam da Amaan sun cika sati chif dan haka yau zai fara zuwa office kuma in ya dawo kwanan hamlat neh.
Amaan ya shirya zai tafi office Ahlam sai shagwaba take ita fa bataso yatafi yabarta da kyar yasamu ta hakuri ya tafi harda kukanta.
Hamlat na kallonsu tana cizan yatsa.
Amaan na fita tadau waya ta kirawo mamah .
Aiko ba ayi minti talatin ba sai ga maamah ta iso .
Tana isowo Hamlat tace su shiga bangaren Ahlam.
Ahlam na ganinsu gabantA yafadi mussaman ma irin kallon da taga Maamah take yi mata hakan yakarasa mata tsoronsu ba abinda yafado mata arai sai lokacin da suka kwonata da mangyada.
Hamlat ta ce, “Ahlam wai bakiga nakawo miki bakuwa bane?”
Ahlam ta daure tadanyi murmushi sannan ta ce, “sannanku da zuwa aunty bara nakawo muku ruwa.”
Hamlat ta ce, “A a ba ruwa mu ka Zo sha kinsan ba shi muka saba sha ba ruwa sai irinku.”
Maamah kawai kallewa dakin kallo take azuciyarta tana, “Hmm Insha Allah ina dap da shigowa gidannan nima na mori arziki tare da samun gwarzon miji.”
Hamlat ta ce, “Kawata tunanin me kike neh yakamata fa mu fara ai watar da aiki.”
Maamah tuni ta mike ta nufi Ahlam tana,” ke yar matsiyata kin samu guri ko , sai yadda kika yi da mijin kawata toh wallahi ina fada miki tun huri ki fita a idonmu inba haka ba zaki sha mamaki.”
Ahlam sai baya baya take Hamlat na bayanta Maama na gaba .
Ahlam ta ce, “Innalillahi-wa’inna-illaihir-raji’un Dan Allah kuyi hakur…….
Bata karasa ba taji mari tassssss hamlat ma ta kara mata taaasssssss.
Gaba daya Ahlam ta gigice ta ko ina dukanta suke.
Hamlat nadukanta tana fadin”wai har er nan zata nama gwalo kuma na fada magana ta mayar min hmm yau maga bakin maganar da harshen gwalo.”
Tun tana iya basu hakuri har ta daina sai numfashi kawai da take, Daga karshe ta daina numfashin.
Hamlat ta ce, “Ke Maamah ta mutu fa”.
Maamah ta kara tabata taga dai ba alamun motsi.
Maamah tace kinga wallahi kuwa ta mutu toh nidai ba ruwqna sai natafi sai anjima.
Hamlat ta fara kuka tana fadin, “Maamah Dan Allah ki tsaya karki tafi ki barni.”
Ko kallonta batayi ba tayi ficewarta da sauri.
Hamlat ta rasa me zatayi kawai sai kuka take.
Chan dai kawai ta dau waya ta kira Amaan awaya da dai har bazai dauka ba sai ya dauka.
Yna dauka tafara cewa, “Ahlam ta mutu wallahi bani na kashetq ba maamah ce kazo ka gani.”
Amaan bai gama jin me take fada ba kawai yq katse ya hawo mota sai gida tuki kawai yake hankalinsa baya jikinsa.
Yana shiga ko ta kan Hamlat bai yi ba yadau Ahlam yana kuka ya nufi mota.
Cewa, “yake Ahlam dan Allah karki tafi ki barni inkika barni bazan iya rayuwa ba.”
Ahaka har yakai asibiti.
suna isa likitoci suka karbeta .
Sai cewa, “yake wallahi bata mutu ba karku bare ta mutu inta mutu sai nqkashe kowa aduniyar nan.”sai yasa kuka kawai
😰😰wannan page din ni kaina ya girgiza ni ba kai kadai ba Amaan.
URs preety xayyesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*Remain 5 pages to finish insha Allah*💃
*PAGE* 65
——————————————————————————————
*WANNAN SHAFIN NAKINE AMARYA KHADEEJAERTH AHMED MUHAMMAD DEBERSH MARUBUCIYAR BADON SHI BA ALLAH YASANYA ALKAIRY YASA ZA AYI ASA”A TARE ZURI”AH DIYYIBA😍*
Dakyar likitan yasa Amaan yadan nutsu sannnan likitan yakirawo dadyn da hike likitan familynsu ne.
Ba jimawa sai ga dady,baba,dasu mama harda ma mumy.
Ita ko Hamlat tana gida ba abinda take sai kuka tayi nadamar rayuwarta gaba daya ta rasa meke mata dadi.
Da kyar likita yasamu ceto rayuwar Ahlam amman duk da haka bata farfado ba.
Dadyne yake tambayar Amaan , “wai meya faru ne.”
Amaan yace, “Dady wallahi nima bansani ba kawai hamlat ce ta kirani ta fadamin amman ga dukkan alamu dukanta tayi.”
Mumy najin hakan gabanta yafadi ras aiko suka hada ido da Dady.
Mama da baba dai basa cewa kome sai Allah yakyauta.
Hamlat ce tashigo cikin asibitin tana kuka.”Amaan da Ahlqm dan ALLAH kuya femin wallahi mumyce tace mu ma ma ta duka ba kasheta mukuje yi ba.”
Ta durkusa gabansa tana kuka mumy kuwa ta kasa sukuni.
Dady yajuyo ya kalli mumy rai abace yace, “Burinki yacika kin bata yarki da duk mugayan halayanki har ma tanaso ta fiki ke baki barni ba,baki bar yan uwa na ba
Naga alama kinaso hakuri na yagaza ko toh wallahi kibarmin gida nasake ki saki daya.”
Yana fada ya ficewarsa a asibityn baba nakiransa ko juyowa bai ba.
Mumy kuwa tuni itama ta zube tana, “Dan Allah ku yafemin wallahi sharrin zuciyane daga yau nabar mugun hali ku basa hakuri dan Allah.”
Mamace ta dagota tare da fadin,”karki damu yanzu afusace yake shiyasa kije gidan insha Allah zamu zo mu dauke ke.”
Mumy tace,”toh nagode Amman dan Allah kuzo.”ta tafi tana dan kukanta.
Hamlat ma haka mama da baba suka nuna mata cewa ai bakome amman duk da haka ta kasa sakewa jikinta na dar-dar.
Sai chan anjima dady yadawo inda yayi dai-dai da farfadowar Ahlam.
Hamlat sai kuka take tana Ahlam ta yafe mata.
Ahlam tace, “Aunty ki daina kuka ai ba wanda ya huce kuskure da tsautsayi kaddara tace dole sai hakan ya faru Allah ya yafe mana duka.”
Gaba daya yan gurin Ahlam kara shiga ransu sai albarka suke sa mata.
Ba jimawa aka sallamesu tare da magunguna hamlat sai rawar kai take wa Ahlam shidai Amaan bayaso kawai kawaici yake dan da iyayensa agun.
Gidan Dady suka huce duka wanda kuwa baba ne ya bukaci hakan.
Salim ma sunji dan haka suka tawo tare da amarya Amrin.
Suna zuwa gida hamlat ce me hadawa Ahlam ruwan wanka harda taimaka matA taje toilet.
Kowa abin yabasa mamaki mussaman Amrin da Amaan suda suka fi sanin rashin mutuncin Hamlat.
Aha suka kasance har safiyar ranar.
Washe gari da safe.
Baba ya hada kowa da kowa a falo yayinda ya nemi da dady yadawo da Mumy domin bai ga amfanin hakan ba halinta dai inda sabo ansaba bare yanzu da tanuna alamum nadama.
Sannan yakoma ga Amaan,Hamlat,tare da Ahlam.
Yace, “banda abince wa gareka da yahuce kanunawa matanka adalci kar ka yadda ka fifita wata awajen watq nuna musu cewa duk kaunarsu kake,Hamlat kece Babba kamata yayi ki rike girman ki kinga abaya kinbarwa Ahlam girman ke kindau kankantar wamda bai kamata ba agareki yanzu inaso ki jajirce ki fito amatsayinki ta babba agidan miji tare da masa ladabi da biyayyah,kinga ita Ahlam banda abinda zance mata sai dai Allah yayi albarka sannan in muku fatam alkairy duka,domin tana da duk abin bukata ga mata ta gari sai sai dai ince ta kara,nadawo gareka Amaan kasani cewa yanzu matanka tarbiyarsu tana hannunka duk yadda ka tafi da su haka zasu tashi fan za akiyaye.”
Bakaramin jin Dadi dady yayi game da maganar baba dan haka anjima mama da shi zasu je sudawo da mumy.
Hamlat ba abinda take sai kuka domin tasan ada tayi kucha kanci.
Hamlat tace, “Nagode sose ba sai yanzu nakara sanin cewa ni ce *KUCHAKAR KISHIYA* Ba Ahlam ba.”
MAma tace, “aa ya’ta karki kara kiran kanki da wannan mummunan sunan domin ada ne kike haka amman ayanzu ke kamar kowace.”
Tuni Hamlat ta rumgume mama tana mama nagode da ace ke nasamu amatsayin uwa tun farko da banyi kukan yau ba.
Baba yayi murmushi yace, “toh dai isa kome ma ya huce yanZu.”
Ana gama tattaunawa dady da kanshi yamaida su Amaan gida .
Sannan yazo yadau mama domin adauko mumy.
Suna zuwa gidansu mumy iyayenta suka dunga basu hakuri itama ta kara basu tare da alkawarin ta chanja hali sannan suka nufo gida.
Su Amaan kuwa baki yakasa rufuwa sai washewa yakw wai yau shine da mata biyu kuma cikin farinciki.
Ahlam taki hutu suna zuwa tashiga kichin ai tuni Hamlat ta biyota tana nima gaskiya sai kin koyamin girki.
Ahlam tayi murmushi tace, “yoo ai aunty sai ma kinfini iyawa domin kinsam tsohon hannu yafi sabO.”
Hamlat tace, “Ummm nice me tsohon hannun ko zaki sani.”
Aha sulayi girkinnan cike da zolayar juna Amaan najinsu sai murmushi yake.
Bayan sun gama abincin rana sunci Ahlam ta nufi bangaren hamlat ta gyarasa tsaf sannan tace to aunty aje ayi wanka kinsan fa yau oga adakin ki yake.”
Hamlat tace, “umm anya kuwa nifa kunya nke ji gaskiya kawai nabar miki shi yakara sati.”
Ahlam ta rike baki tarw da fadin rufamun asiri ai sai yau oga yakaini kotu wlh bawani shima so yke yazo fa.”
Hamlat tace, “haba dai?”
Ahlam ta girgiZa kai.
Hamlat tace, “bara nayi bani hanya kiga har ta shiga tace karki fita fa ki jira na fito kimin kwalliya.”
Ahlam tayi murmushi ta jirata ta fito sannam ta dauko mata sabuwar abaya tasa ta mata daurin chakwai tare da simple make up dinta .
Hamlat ita kanta tasan tayi kyau sose kawai godiya tkewa Ahlam.
Ahlam tace, “yauwa toh aunty zauna yqnzu oga zai iso bara na fada masa munshirya.”
Hamlat kawai murmushi tke domin ko ran aurensu batayi farinciki irin na yau ba.
Ahlam na fita taje ta durkusa gaban Amaan tana, “Kayi hakuri bansan ko na aikata abinda bai kamata ba agunka amman aguna dai dai-dai ne yau zaka koma dakN Auntyna Na fada matq kuma ta shirya kawai kai take jira.”
Amaan yayi shiru yarasa mema zai cewa Ahlam .
kaji yaya plsss dan ni zakayi .
Amaan yace, “shikenan naji kuma nagode Allah yamiki albarka sahibty er aljannah.”
Ahlam tayi murmushi ta riko hannuna tashi muje.
Amaan yatashi suna zuwa kwofar daki tasake shi ta kwankwasa sannan ta juyo da gudu domin tafiya dakinta hawaye ne fal a idonta kuma bataso Amaan yagani bare yadamu.
Dn Haka tana shiga ta fada kan gado tana kuka.
Shiko Amaan yashiga da sallamarsa…
*Preety xayeesherth*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 66,67&68
——————————————————————————————
*SADAUKARWA GA DUK MASOYAN HAMLAT*
Amaan yayi mamakin ganin Hamlat awannan yanayi hakan yasa kawai ya tsaya yana kallon ta,bai san cewa Hamlat kyakkyawa bace sai yau.
Hamlat tayi murmushi tare da kara sowa garesa da murmushinta ta ce, “Ayyah yayanah nasan dole zakaji wani iri yanayin da baka saba gani na ashi ba amman inaso kasancewa da , da yanzu ba daya bane.”
Ta durkusa agabansa tare da riko hannunsa ta ci gaba da ce wa, “Dan Allah kayafemin ina me maka alkawarin cewa bazan taba komawa Hamlat din da ba yanzu A Amina ta nake Insha Allah baraka kara kuka dani ba ko na second daya.”
Ta matukar ba Amaan tausayi mussaman da yaga hawayen da take zubarwa har yaji yamanta da rayuwarsu ada.
Hakan yasa yadago ta tare da share mata hawa ya rungumeta yana fadin, “Ai koda ace ke ba matata bace ke jininace bazan taba kinki ba Hamlat.”
Ahaka suka kasance asabuwar rayuwa adaren ranar.
Ahlam tasha kukanta har ta gaji hakan yasa ta tashi ta dauro alwala tayi sallah sannan ta karanta Alqur’ani agurin barci yadauke.
Da asuba kuwa Amaan yazo ya kwankwsa mata kwofa ta tashi tayi sallah bayan ta idar bata koma barci ba ta gyara dakinta tsaf sannan ta nufi kichin.
Breakfast taje hada musu soyayyar doya tare da miyar kwai sannan ta musu farfesun kifi.
Tana gamawa ta shirya su tsaf akan dainin aiko ta gama shiryawa kenan sai kasu sun fito da murmushinsu.
Ahlam ta kasa hada ido da Amaan kawai murmushin dole take tace, “morning sahib and Auntyna.”
Hamlat tace, “morning sister.”
Amaan ya ce, “wai me gimbiyar ta shirya mana ne naji gidan duk ya dume da kamshi.”
Ahlam tayi murmushi tare da fadin, “Umm kuzo muyi karya nidai inason nasha tea.”
Tuni Amaan da Hamlat suka zo na.
Hamlat tace, “toh sister tunda ke kika girka ai kya bari ni yi saving din kinga anraba ladan.”
Ahlam tace, “As u wish Auntynah.”
Haka suka kasance cikin farinciki da begen juna hakan ya hana Amaan fita ko kwofar gida bare yaje office hamlat kuwa tadau hutun wata guda daman domin ta zauna Ahlam ta koya mata girki da gyaran jiki.
Ya kasance akullum yana cikin farin ciki da iyalansa har in yana office kullum burinsa kawai yadawo yatarar da gimbiyarsa Ahlam, Duk da cewa Hamlat ma tafara shiga ransa Amaan ba kamar Sahibtynsa ba.
Yau yakasance ranar asabar Amaan bai je aiki ba kuma adakin Ahlam yake hakan yasa Hamlat ta nemi alfarmar fita.
Amaan ko ya yarje mata domin kuwa intana gidan baya iya bajewa sahibtynsa asalin so da kaunar da yake mata domin gudun kar ta shiga damuwa.
Ba inda Hamlat ta nufa sai gidan su Maamah tana zuwa bata karasa shiga ba taji Mumyn Maamah na cewa, “Wai niko kwana biyu ina Hamlat neh.”
Ai tuni hamlat ta tsaya chak.
Maamah tace, “Mumy ina zaki ga wannan matsiyaciyar ta nan ta kusa kisa,ai ni wallahi kawai ina daga mata kafa ne amman sai na auri Amaan domin tun randa nafara ganinsa nakamu da sonsa fatana kawai boko jum yadawo daga nema min maganin da yaje na aure abi nah.”
Mumyn Maama tace, “Subhannallah wannan lamarin abun kunyan tare da shirka ba agidannan ba wallahi.”
Hamlat ta rasa ta cewa sai yanzu abubuwa suke dawo mata daman ashe Maamah bason tsakani da Allah take mata ba?.
Ba ma bari tagama jin me suke fada ba tashige dakin tare da cewa, “Nagode da hallacin da kikamin Maamah kuma wallahi indai Amaan ne yafi karfinki sanin kanki neh.”
Mamah tace, “mtswww aikin banza to se me?”
Hamlat ta yi murmushi sannan ta cewa mumy”mumy nagode da irin nasihar da kikemin da kuma nagyara hali Allah ya saka da Alkairi.”
Tayi ficewar tah.
Bakaramin mamaki Hamlat taji bq hakan nr ma yasa ta kira mumy ta fada matA.
Mumy tace, “hmm Hamlat kenan ai gwada kema kingane da huri niko ina tare da makiyata kuma er uwata taji kusan shekara talatin da wani abu tana sani yin mummunan aiki ai kawai sai dai muce Allah ya yafe mana.”
Hamlat tace, “Amin kam”.
Suna gama wayar kuwa tayi gida.
Rayuwa ta cigaba da dadi agidan Amaan domin kuwa dukansu sunq bawa junansu kulawa yanzu har kwatance ake dasu domin hadin kansu tare da zaman lafiyansu.
Har yakasance duk inda zasu tare suke zuwa sai kuma an nemawa Ahlam admission a universty of jos tana digirin ta afannin computer science Hamlat kuma ta cigaba da zuwa gun aikinta.
Yau yakasance ranar monday kuma Amaan yanq dakin Ahlam tunda ya bugawa Hamlat daki da asuba bai koma ba dan hakq bai sani bsma ko ta tashi.
Har sungama shiri bata fito ba hakan yaSa Amaan yakara bugawa yaji shiru da karshe dai sai keyn gunsa yadauko yq bude dakin .
Hamlat kwance zazzabi ya riketa rawar sanyi kawai take.
Tuni Amaan ya kira doctor ba jimawa yazo.
Ya ma Hamlat gwaje gwaje alamu suka nuna cewa tana dauke da ciki wata biyu.
Ai ba wanda yakai Ahlam murna kin tafiya skul tayi ita zata kula da unborn babynsu .
Amaan ma yayi farinciki sose amman azuciya ynq fatan ganin jininsama daga bangaren Ahlam.
Hamlat kawai murmushi take.
Daga ranar kuwa kullum Hamlat sai sunyi fada Da Ahlam akan aikin gida .
Hamlat tace ai sai tayi , Ita ko Ahlam tq ce wallahi bazaki wahalar mana da baby ba kije ki hutA.
Amman duk da hakA Hamlat ba yarda sai tayi aikinnan bata bari ma Ahlam tazo ta tarar da aiki domin tasan farincikin Ahlam shine na Amaan shiyasa kullum koda bata jin dadin jikinta ta gwammace ta ta aiki dan kawai tasa mijintq farinciki.
Akullum in suna zaune ana hira sai Ahlam tace, “Auntynah karfa kizo kina min rowar babynmu domin aguna zai na huni sai barci da shan nono zai na kawoshi gunki.”
Hamlat tayi murmushi sannan tace, “Ai babyn ma naki ne Ahlam bansan ran zan rani da ko yar da zan hafe ba.”
Amaan ko yakance kullum dai maganar ku kenan.
Watan haihuwar Hamlat yakama kullum karatun Alqur’ani take tare da addu”o”in samu rahama .
Inko ana hira bata da abin fadan da yahuce yayana ka yafemin kanwata kema ki yafe min domin bansan ko zan tashi .
Tun Amaan da Ahlam suna maida abin wasa har sai yafara basu haushi.
Amaan yace, “indai ba so kike ki tarwaatsa mana farin ciki ba kidai na kawo mana zancen kina ganin zaki barmu.”
Hamlat tayi murmushi sannan tace, “nabari insha Allah yayanah.”
Ahlam tace, “yauwa auntyna me kumatun cincin.”
Dukamsu sai da suka yi dariya mussaman hamlat.
yau hamlat ta tashi da ciwon nakuda Amaan taki fadawa kowa agidan har Amaan yatafi office Ahlam ma ta tafi skul.
Har ta dafa ruwan zafi.
nakuda tazo gadan dagan aiko ba bata lokaci ta haihu alokacin haka ta daure ta yankewa dan ta cibiya ta masa wanka da ruwan da ta dafa sannan ita ma tama kanta.
Ta kwanta tana hutuwa kennan ciwo yadawo mata sabo Jini yabarke.
Da kyar tasamu damar janyo waya ta kira Amaan awaya.
Tama kasa magana duk jikinta ya mutu cewa take, “Kazo gida zan mutu kazo yaYa.”
Da sauri Amaan ya katse wayar ya tawo gida .
Yana zuwa yatarar da yaro sai kuka yake ita ko Hamlat asume.
Da sauri yakira me gadi yarike masa yaron ita kuma yasa ta amota suna zuwa aka karbeta emergency.
Amaan ya kira gida yasanar musu duk sun hallara a asibitn Ahlam ma ta iso.
Hamlat na farfadowa ta sa akira mata Ahlam da Amaan da gudun su suka shiga .
Suna Zuwa Hamlat tace, “Sister,Yayanah kuyi hakuri nasan bazan rayu ba amman ina so kafin nabar duniya kace kana so na ban taba jin wannan kalmar ta ka gareni ba.”
Amaan na kuKa Ahlam na kuka
Amaan, “Ina sonki Hamlat wallahi ina sonki dan Allah karki tafi ki barmu wallahi duk muna sonki.”
Hamlat ta rikye hannunsa da na Ahl am tace, “Umm yayana na gode amman ina neman alfarmar karshe kasawa yarona sunanka domin inaso yayo hali irin naka indai yayi nasan bazai taba shan wahala ba arayuwarsa ke kuma Sister ga danki nan nasan zaki rike shi kaman danki na cikinki,ina Alfahari daku Amine na kuma yan uwa na duka ina sonku.”
Amaan yakasa magana Ahlam ce tadaure tace , “Dan Allah Aunty kibar fadan haka karki barmu plssssss.”
Hamlat ba abinda yake futuwa daga bakinta sai kalmar shahada.
Atake Allah yadau Abinsa.
*INNALILLAHI-WA”INNA-ILLAIHIR-RAJI”UN*
Abinda Amaan yake firtawa kenan.
Ita ko Ahlam itama atake ta suma awajen.
Gaba daya dangi sun shigo sai kuka kawai ake.
Urs preety xayeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
*PAGE* 69,70
——————————————————————————————
Amaan yaga Matukar tashin hankali awannan ranar domin ita kanta Ahlam sai dare aka samu kanta.
Tunda ta farka kuwa ta kankame Little Amaan ahannunta taki ba kowa ko sallah zatayi sai da ta goyasa.
Akullum Ahlam na cikin kuka Amaan ne yake dauriya har ya mata nasiha akan cewa yanzu ba abinda Hamlat ke bukata agun mu illa Addu’ah .
Yau Hamlat tacika kwana uku da rasuwa dan haka duk mutane sun tafi Ahlam da Amaan ma sun koma gida.
Ba karamar kulawa little Amaan yake samu ba awajen Ahlam baya fin mintuna sai anbasa madarasa da kuma ruwan dume tare da gulukos.
Yau Hamlat ta cika kwana bakwai da rasuwa kuma sunan little Amaan ba ayi taron suna ba anma anyi sadakawa mutane sose Dadyne ya radawa little Amaan suna.
Ahlam dai ta fara sakewa Amman ta kasa sabo da rashin hamlat kwata-kwata.
Little Amaan sai girma yake duk wanda yagansa kaman yaga Hamlat domin kamansu daya sak.
Yaron yakasance me gwarjini a idon mutane gashi ko yaushe cikin murmushi yake hakan yake karasa shi shiga zukatan mutane da dama.
Soyayya ta kara karfafa atsakanin Amaan da Ahlam.
Litte Amaan nada shekara biyu Ahlam tasamu ciki,duk da cewa tana shan wahalar cikin amman hakan bai hanata dawainiya da Little Amaan ba kullum burinta taga die heart dinta kusa da ita sunnan da take kiransa dashi kenan hakan yasa kowa ma yake ce masa die heart.
Ahlam ta haifi yarta mace wacce taci sunan Hamlat Wato Amina Amman Da Hamlat dinta ake kiranta.
Dady da mumy kuwa suna nunawa takwarar yar su so sose mara misaltuwa domin acewarsu ita hamlat dinsu ce.
************
Bayan shekara biyar
Muka kara lekawa gidan Amaan .
Ahlam ta kammala karatun ta har tayi bautar kasa amman bata aiki ita tace kula da ya’yanta zatayi hakan kuwa Yama Amaan dadi.
Little Amaan na primary one hamlat kuwa na nusery 1.
Hamlat ce ta tawo da gudu tana,” Ammi nah kinga Yaya Ko ?”
Ahlam tace, “Me ya faru neh die heart ya kasa kanwarka kuka.”
die heart ya ce, “Umm Ammi wai fa take cewa me kumatun cincin shine nikuma nace ita kumatun alale ne da ita.”
Ahlam ta kalli Amaan,Amaan ya kalle ta aiko sai sukq sa dariya dukansu.
Amaan yace, “yan Albarka sunyi Halin Ammin su kunga kuzo na kai ku skul karku yi letti.”
*ALHAMDULLILAH ALHAMDULLILAH NAGODEWA ALLAH DAYA BANI DAMAR KAMMALA WANNAN LITTAFI LAFIYA ALLAH YASA ANDAU DARASIN DAKE CIKI NA ALKAIRI WANDA NAYI BA DAIDAI BA ALLAH KA YAFEMIN DUK WANDA NABATAWA RAI SANADIN WANNAN LITTAFI YA YAFEMIN DOMIN DAN ADAM AJIZI NE*