ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 7 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Har yanzu bata iya motsi, ga dai alamu tana da rai ba mutuwa tayi ba, amma idan ka ganta ka zata ta mutu. Alh. Jafar, Alh. Aminu da Mustapha suna zaune a (officc) din manyan likitoci guda biyu suna yi musu tambaya.
Dr. Sha’aibu yace, “Kamar yadda muka tambayeku cewa tsawon awanni nawa aka yi da faruwar wannan al’amari ku kace baku sani ba
Yadda binciken mu ya nuna ta shafe awanni uku cikin wannan yanayi wanda jinkin da rashin samun taimako a lokacin da abin ya faru ya janyo mata illoli da dama, na farko dai a yanzu tana cikin koma zata jima a haka, idan Allah Ya kawo cikin sauki zata iya farkawa ta dawo cikn tunaninta, idan kuma aka samu rashin sa’a zata iya zautuwa gaba daya ko kuma tayi mantuwar abinda ya gabata a baya (losing memory). Illa kuwa ta mutuncinta anyi mata sosai, amma zamu yi iya yinmu don ganin munyi nasara akan aikinmu”
“Lahaula wala Kuwwata illa billah! Ya Allah Ka fitar da yarinyar nan daga cikin wannan masifa da ta same mu”. Ya Karasa fada yana kuka.
Alh. Aminu ne ya dafa kafadas Mustapha ‘ shima idonsa yayi jajir, ya ce.
“Kayi hakuri Mustapha, insha Allah Allah zai yi mana sakayya, duk wanda suka aikata mana haka”
Haka ya dora kansa a cinyar dan uwansa yana kuka, yace Yaya Aminu an cuci rayuwar mu, me ya
yi saura yanzu ga rayuwar Aziza? Ka dai ji irin abin da aka fada”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hawaye na zuba ya dago ya dubi Dr. Shu’aibu, yace
“Doctor don Allah kuyi iya yin ku don ganin kun ceto min rayuwar Aziza na, ban so na rasa ta, ban so kuyi mata komai har sai kunga ta dawo cikin hayyacinta”.
“Alh. Mustapha ka taya mu da addu’a, muma fatanmu da koKarin mu kenan gareta, babbar addu’ar mu shi ne Allah Ya tsayar da yawan firgitar da take yi, domin yin hakan kan janyo abin ya taba KwakKwalwar ta, domin yawan tuna abin da ya faru a gareta ne. Kuma ba lallai bance idan ta farka ta iya tuno abinda ya faru da ita ba”Dr. Salisu ya Kara da cewa, “Wannan matsalar ta samo asali ne da jinkirin kawo ta asibiti, amma abu ne na Allah idan Yaso cikin yardar sa sai kuga komai ya warwarce cikin sauki”.
“Ameen Ya Allah, Doctor .mun_ gode, Allah Ya bata lafiya, Ya kuma tashi kafadunta.
” Don haka mu yanzu zamu je muyi (police report) don su taya mu bincike su wane suka yi mana haka? Kuma dole ne mu tuhumi masu gadin (estate) dinmu”. Cewar Alh. Jafar.
Cikin damuwa Mustapha ya _ dago idanunsa Jajaye, yaCe. Yaya Jafar babu wani hukuma da zamu
~ nema mu saka ta a cikin wannan abin da ya faru damu sirrin zuri’armu ne, idan muka fitar da shi duniya ta ji mun tonawa kanmu asiri, mu bar komai cikin sirri cikin yardar Allah ko ma su waye suka yi mana haka da bakin su za su fada mana, daga nan sai mu hukunta su don wallahi ba zan bar duk wanda ya yi mana haka ba”.
“Gaskiyar Mustapha, hakan ya yi, insha Allah albarkar zumuncin mu sai Allah Ya bayyana ko ma su wayce suka yi wannan rashin imanin”. Alh., Jafar ya fada, daga nan ya ce.Doctor mun gode, ko zamu iya ganinta yanzu?” . Babu laifi ku din. za ku iya ganinta, amma mata saboda koke-koken su ba zamu iya barin su ba”.Mun gode”. Alh. Jafar ya fada, haka suka mike suka ce za suje dakin da take kwance.
Gata nan kwance duk an saka mata na’ura masu taimakawar zuko numfashi, ta jikin na’‘urar kawai ake iya ganin bugun zuciyarta.
Da sauri yaje ya rike hannunta yana hawaye yana cewa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Aziza na, Ammi na me kika yiwa wadanda suka yi miki haka? Ki yi haKuri ki yafe min a matsayina na mahaifin ki ban tsare rayuwar ki ba kamar yadda ya kamata, (please) Ammi na ki yafe min, ban kyauta miki ba, ki yafe min”, Nan kuka ya ci Karfinsa, haka yayi ta kuka kamar yaro dan goye.
Alh. Jafar ne ya ce, “Haba Mustapha, meye haka? Wannan ai sai ya kai ka ga yin sabo, ‘da kaine kake tsare ta ba Allah Mahaliccin mu ba? (Please ka nutsu kasan me kake furtawa”.
Daga kai ya yi alamar yaji, sun jima a haka daga baya su suka fito amma shi ya Ki fitowa, dole suka hakKura suka barshi don likitocin sun ce idan shi ne zai iya zama a gurin tunda ba wani hayaiya zai ba. .
Haka muka zo duka muna hangenta ta cikin glass kwance kamar wata gawa, banda kuka babu abinda muke yi.
Satin ta biyu a haka amma babu wani samun ci gaba jiya iyau, Mustapha duk ya zama abin tausayi domin ko da yaushe shi ne a gurinta, anyi-anyo da shi akan ya bar wani ya zauna a gurinta ya Ki, haka kullum yake wuni a gurin.
Ranar da ta kwan goma sha bakwai ne yana zaune kusa da ita kamar yadda ya saba yana mata karatu yana tofawa, can ya ga tana motsa hannunta hade da girgiza kai, zuwa can sai ta runtse idanunta ta kurma ihu ta ce.
– “Wayyo Allah Abba ka zo ka cece ni zai kashe ni, zai kashe ni Abba, Granny zan mutu kuzo ku cece ni
Da sauri ya mike yaje ya rungumeta yana kuka, yana cewa
“Ammina fada min wane yayi miki haka? Kada min ina kusa da ke, babu abinda zai miki ko waye ki fada min wane ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun daga wannan furucin da tayi cikin firgita bata Kara yin wani kalami ba ta Kara komawa cikin halin da take ciki, da hanzari ya fito zuwa kiran likita, nan suka shiga gurin cikin rudani. Nan dai suka ci gaba da aune-aune, nan suka ce masa tunda har ta fara yin haka cikin yardar Allah komai zai dai daita.
Kowa da yaji haka sai ya fara jin dadin al’amarin, sai-dai ni akwai wani abu da yake min yawo a Cikin zuciya, amma ban samu na furtawa kowa ba na ja bakina nayi shiru, shi ne tun ranar
_ da wannan al’amarin ya faru babu wanda ya yi maganar Hameed, bai kuma tako inda take ba, ba kuma wanda naji yace min gashi ya zo. Don haka na shiga shakku akan hakan sai dai ban
. Samu na tofawa kowa ba gudun kada ace nice babba ni kuma na fito da wani abu.
“Da ‘yammacin ranar ne muna asibiti kusan kullum anan muke kwana mu wuni, muna cikin zaune na ce da Maryam. –
“Wai na tambaye ki mana? Shin Hameed tunda abin nan ya faru ya zo asibitin nan kuwa?”
“Umma yazo mana, ina ganin ke ce. dai baki ganshi ba, yana zuwa bai jimawa sai ya koma, shi kansa baki ga yadda ya shiga rudani ba, haka ya ce ba zai jure ganin Aziza a haka ba shi yasa ba ya son zuwa ya zo ya ganta a wannan mawuyacin halin. Sau biyu muka hadu da shi a gurin nan, da kuka yake barin nan don haka ina tunanin shi yasa ma ya dauke Kafar sa da zuwa nan din”
Ajiyar zuciya nayi na ce, “To babu laifi, na yi zaton tun sanda aka kawo ta bai zo ba”.
“Ummah Aziza da Hameed sai Allah, na yarda da UZURIn da ya bayar don naga irin tashin hankalin da ya shiga, duk zuwan da yake za ki ganshi cikin rashin nutsuwa, domin abin ya _ yi matuKar tadar masa da hankali”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi kenan dai, Allah Ya tashi kafadar ta, sannan Ya tona asirin dukkan azzaluman da suka yi mata haka”.”Ameen”,
Muna rufe bakin mu sai ga Alh. Jafar da Hiameed sun shigo inda muke, suka yi mana sallama muka amsa baki daya. Bayan nan Alh. Jafar ne ya fara gaida ni sannan Hameed shima ya gaida ni, kallon sa nayi na ganshi cikin tashin hakali, na ga duk ya yi baki ya wani rame, duk ga zulumi nan a tare da shi. Haka kawai sai naji tausayin sa ya kama ni, na kuma tabbatar da abin da Maryam ta fada min.
Cikin yanayin damuwa ya ce, “Granny ya mai jiki? Da fatan dai ta soma jin sauki?”
Ya fada cikin wani irin yanayi gwanin ban tausayi
Na ce, “Eh sauki yana dai gurin Allah, © amma dai dazu ta soma magana har tana ce…”
Cikin sauri Hameed ya ce, “Granny me ta ce? Fada min naji ko ta fadi wane ya yi mata hakan”.
“Kwantar da hankalin ka Abdulhamced, bata iya fadin kowa ne sai dai ta kira suna na da Abban ku akan wai mu taimake ta”.Daga haka bata Kara cewa komai ba, kota Kara ce muku wani abu?”
“Gaskiya babu abinda naji ance ta ce tunda ni bana gurin”. “Toh me likitan ya ce game da dawowar tunanin ta? Shin ya fada zai dawo ko ya tafi gaba daya?” Alh. Jafar ya fada yana kallo na.
Maryam ta ce, “Yaya bai dai ce komai ba akan haka, mu dai fatan mu dai Allah Yasa ta warke ras, ba ma fatan ta warke ta kuma tashi da mantuwar tunanin, don yin haka ba Karamin nakasa ta samu ba, domin da ita da — nakashasshiya duk daya ne ko ma yafi”. _
Ya ja ajiyar zuciya, ya ce, “Gaskiya ne”.
Na yi duba ga goshin Hameed da yake _ daure da bandeji, na ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Abdulhameed mene ya faru da kai a goshin ka haka?”
Dora hannun sa ya yi akan goshin ya shiga inda-inda, ya mai da kallon sa ga mahaifin sa, zuwa can ya yi Karfin hali ya ce. Mun fadi ne akan mashin tun ran nan”Nace, “Allah Ya sauwake, don Allah Abdul ku dinga lura sosai”.
“Umma kina ganin yarinyar nan tunaninta zai iya dawowa kuwa? Don gashi har yanzu babu wani abu da ya sauya cikin halin da take ciki”. Cewar Alh. Jafar. “Toh mu dai: gamu nan mun zubawa Sarautar Allah ido, Shi ne mai iko akan komai, domin Ya fimu sanin abinda ya Boye a ciki, bamu da masaniya akan komai. Amma dai abinda likita ya fada dai dazu da ta yi wannan surutan cikin firgita ya ce cikin kowane irin hali zata iya farfadowa tare da tuna dukkan abin daya faru da ita. Sai dai kuma da akwai yiwuwar ta farfado din ta iya manta wani sashe na bangaren tunanin ta, shi yasa mu yanzu muke ta addu’a akan Allah Ya tashi kafadunta. Yacee, “Ameen, Allah Yasa”,Granny ina son ganin Aziza na (plceasc) ku barni na ganta ko na samu nutsuwa, Granny idan da hali ina son a aura min Aziza na a yanzu don na samu damar kula da ita da jinyar ta, ban damu ta dawo cikin tunaninta. ba, matuKar zara Www.bankinhausanovels.com.ng
warke ko da tunaninta bai dawo ba ni zan zauna da ita, ban damu da su wane suka yi mata haka ba, zan so na rayu da ‘yar uwata a haka, ni dai ina sonta, zan kuma dauki dawainiyarta a haka”.
Duk jikin mu ya yi sanyi ni da Maryam, take naji hawaye sun zomin, na ce.
“Abdulhameed kai yaro ne, a matsayin shekarun ka da karatun ka ai ya yi wuri ace kana da aure, kuma ga ta da lalura, shin ya zaka yi da karatun ka?”
“Granny idan za a yarda na auri Aziza a yanzu a cikin wannan halin zan iya hakura da komai har karatun na tsaya na lura da rayuwar ta saboda nasan na girma zan kuma iya kula da ita don haka yanzu na fadawa Daddy haka ne shi yasa muka zo nan tare domin ke kadai ce za ki yarda da haka auraminita”, Umma wannan haka yake, gaskiya ya fada, ki daure ki yarda da hakan”.
“Jafar babu damuwa tun da ZURI’A DAYA muke, babu wani abu da zai gagara a ciki, amma ku dan yi haKuri ka ci gaba da fahimtar Abdulhameed, insha Allahu shi ne zai
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG