KUDIRI CHAPTER 5

KUDIRI




CHAPTER 5




Da nauyin zuciya Asiya ta fita, don ba ta son haduwar ta da Suhaima ko kadan, musamman ma a yanzu da ta kasance ita kadai ce wajen Dokta Hadi. +

Ba wai sun taba sabani ba ne. Kawai kaunar matar ce kawai ba ta yi. Ta san ita din ma ba son ta ta ke yi ba, duk da kokarin nuna hakan da ta ke yi.

Ilay! Ko da kofar gaba ta bude, ba Suhaimar ta gani ba. Muhibbat ta gani. Ta fito cikin sauri ta je ta rungume ta. Zuciyar ta ta yi kaaal don ganin ta. Oh! Yaushe rabon da ganin ta? Tun fa bayan auren ta. 2

“Muhi, ashe zan sake ganin ki?” Kwalla su ka ciko wa Asiya idanu. Ji ta ke tamkar ta ga Dadar ta. Ko ma Mariya. Nan take ta ji raas! Ko dai mariya c eta bayyana a gida?

“Ai ke ba kya da kirki. Ko ki dan waiga gida sau daya?” Ta kalli Yusuf wanda ya gama musabaha da Hadi, ta ce, “Mhmmm, ka samu amarya ka wani makale ta a gefen ka, ka hana ta zuwa kauye… to yau na zo ma ka da tuhuma ce, dole ka amsa.”

Yusuf ya yi murmushi, “Ba dole na ba. A ce ta hannun damar amarya ta zo da kan ta, ai dole ne.”

Duka suka kyalkyale da dariya. Asiya ta kalle shi cikin mamaki. Ashe a wancan ranar sayen bakin nan ya saurare su. Ta yi zaton bai damu da abin da abokan na sa ke yi bane. Ko kuma auren bai dame shi kamar yadda yake nuna ma ta a yanzu ba.

Bayan ta gaida Dokta Hadi, sai ya ce, “To, ta hannun damar amarya, ni zan koma. Tun da na danka ki hannun mutanen gidan nan, na sauke nauyi.”

Ta yi dariya, “Gaskiya, ka fita. Na gode sosai. Sai wata rana.”

Hadi ya kalle sosai, “Sai wata rana kuma? Ta ya ya haka? Ina ‘yar malelen da a ka kwadaita min a biki na?”

Muhibbat ta sake fashewa da dariya, “’Yan Bauchi kauyawa ne. Dan-malele a ke fadi, ba ‘yar malele ba.”

Asiya ta shiga maganar, “Haba, Muhi. Ki na magana kamar wani dan-malelen wani kayan gabas ne.”

Hadi ya ce, “Kyale ta amarya. Na ga alamar ta raina wa mutanen Bauchin ne. Kuma ga shi ‘yar Bauchin ce ita, gaba da baya. Ba ta da wurin da ya wuce nan nan din idan Kanawa koro ta.”

Muhibbat ta ce, “Duk da dai ni ‘yar jihar Bauchin ce, babu abin da zai kawo ni nan, idan ba dole ba.”

Hadi ya ce, “To, tun da dole ne ya saka hakan, an kara zama daya ke nan. Gobe in Allah Ya kai mu, zan dawo na ci dan-malele na ke nan.” 2

“Tab, ai gobe da yamma ko kura ta ba za ka samu ba. Na yi nisa.”

Ya kalli Asiya, “Amarya, ban san mutanen garin ku su na da rowa ba.”

Asiya ta yi dariya, “A’a, ba ma da rowa.” Ba ta san abin da zaata ce masa ba, don ga alama, sun dan yi jayayya ne tun a motar sa.

“To in dai haka ne, ya kamata na ci dan-malele.”

Muhibbat ta girgiza kan ta, tana ‘yar dariya. Ba ta sake cewa komai ba, kawai shigewa ciki ta yi. Asiya ma ta bi bayan ta. Bature direban gidan ya bi bayan su da jibgegen buhun da ta zo da shi.

Nan suka yi sallar maghrib, Yusuf da Hadi kuwa masjid suka koma suka yi na su. Ta san daga can Hadi zai wuce ke nan.

“Ina ki ka samu Dokta Hadi, Muhi?” Asiya ta tambaye ta, bayan sun idar da sallah. Tun ganin su tare ta ke kaikayin yi mata wannan tambayar.

STORY CONTINUES BELOW


“Wannan likitan? A asibitin Sauki. Ni kin san sau daya na zo gidan nan. Gani na yi ba zan iya ganewa ba, kawai sai na wuce can kai tsaye. Ko da isa ta sai ban yi sa’ar likita ba, don sun ce yau ya dauki off. Hmm, na zauna zugum, ina tunanin yadda zan yi, shi ne sai ga wannan likitan. Shi ma ya gane ni. 2

Ya nemi na dan jira shi a ofis din sa, ya gama ganin marasa lafiyar da ke jiran sa. Kin kuwa sanni wajen hira. Ban san lokacin da na fada muna ta hira ba. Ke duk iya yi na wannan ya dama ni ya shanye. Bayan ya gama ne kuma ya kawo ni nan.”

Asiya ta yi murmushi, “Da baki same shi ba, yaya ke nan? Tab! Wa ya ga min Muhi ta bace a Bauchi.”

Muhibbat ta harare ta, “Allah ya sawwake! Ban bata a Kano ba ma, sai a Bauchi? Ke ma kin san na wuce haka. Ba alfahari ba Amma ina ga ko Makka na je ba zan bata ba, balle karamin wuri irin Bauchi.”

“To, mu bar wannan. Yanzu ki zo mu je ki gaida da Ummah. In ya so sai mu dawo, ki yi wanka, sannan ki ci abinci. Yau za mu sha hira.” 2

Hakan su ka yi. Bayan sun yi gaisuwar ne, Muhibbat ta warware ma ta kayan tsarabar da Dada ta hado ma ta su; garin kuka, daddawa, kubaiwa busasshe, jarkar zuma ta ce a baiwa Yusuf, da gallon din soyayyen manshanu, wanda ta ce a ba wa Ummah. Ta kuma dafa ma ta kwadon zogale, ta ce wata kila ba sa samun zogalen a Bauchi. 6

Kwalla suka ciko idanun ta, ta sa hannu ta share da sauri. Ta na kewar mahaifiyar ta, ta na kuma tausaya mata. Ta san ba za ta iya zaman sukuni ba har sai ta turo an gan ta da lafiyar ta. Ga shi ba waya gare ta ba, sai ko idan Muhibbat ta je ne suke gaisawa. Ita ma Muhin wayar ta ta a ka sace har sau biyu, shi ne ta hakura ba ta kara saye ba. Amma tun da ta zo, za ta sayi waya ta aika wa Dadar ta, don su rika hira da junan su a duk lokacin da suka ga dama.

“Ai Dada sai ka ce wata tsohuwa.” In ji Muhibbat, bayan sun zauna ta na kokarin cin abinci. Naman d suka sayo ne hade da couscous, dafa-dukan sa. Ga ruwan sha da lemo ma su sanyi. “Kin ga abubuwan da ta lafto kuwa? Wasu abubuwan ma kin dauka na yi.”

Asiya ta dan yi dariya. “Baba fa, Muhi?” Ta tambaya. Ta gagara daure zuciyar ta. Hakika, a lokacin auren ta ya juya ma ta baya, ya kuma nuna rashin jin dadin sa karara na son ta rike diyar titin da take shirin yi.

Amma duk da haka, ba zata juya ma sa bay aba. Ba ita ta zabe shi a matsayinmahaifi ba, Allah ne Ya zaba ma ta. Don haka ba ta da halin canja shi.

“Ya na nan.” Cikin murmushi dai ta amsa, amma muryar ta ba ta boye sakon ta ba, cewa bay a cikin walwala. Ta fi kowa sanin halin baban su. A yanzu haka bai bar kuntata wa Dada ba kan laifukan su, ita da Maree.

“Muhi, Maree ta bayyana kuwa?” Ta tambaya zuciyar ta cikin bakin ta, Allah sa an same ta. Ta san idan ta bayyana ba mamaki za ta ziyarce ta. Allah kadai Ya bar wa kan Sa sanin abin da zai faru idan hakan ya faru.

Muhibbat ta girgiza kan ta, “Babu dai wani sabon labari, bayan wanda na ji an ce an gan ta a garin Jos.”

Asiya ta zaro ido,”An ga Maree? Yaushe? Ta ina?” Zuciyar ta sai tsalle ta ke yi. Fiye da kullum, ta ji zumudin son ganin ‘yar uwar ta, ko da za ta dubi idanun ta ta fada mata dalilin guduwar da ta yi.

“Wai a Unguwar Gangare. Wata mata mai suna Kande ta ce ta je wajen ta cikin rashin lafiya, har ta yi mata jiyya kwana biyu saboda tausaya ma ta da ta yi. Daga bisani ne kuma Mareen ta dauke ma ta wasu ‘yan kudaden ta da ‘yan kunnen gwal din diyar ta ta bace. Daga nan har yau ba a sake jin duriyar ta ba.”

Wannan labari ya kara bawa Asiya mamaki. Ta ce, “Yaushe ne hakan ya faru? Yaushe ku ka samu labari?” Ya ya a ka yi ba ta ji ba?

Wannan karon Muhibbat ce ta ma ta kallon mamakin, “Kusan sati uku da suka shude. A wajen Dada ni ma na samu labari, ta ce min mijin ki ne ya fada mu su hakan, bayan ‘yan sandan garin nan sun tuntube shi. Tare ma su ka je can Dagaudan lokacin da su ka fada.”

STORY CONTINUES BELOW


Yusuf ne ya fada mu su? Mamaki ya kusan daure harshen ta a lokacin. Me wai? Yusuf ya je Dagauda? Yaushe? Kuma me ya sa bai fada mata ba? Sati uku da suka wuce….ta tuna dai ta na cikin tashin hankalin raba ta da Ama, amma me ya sa bai fada ma ta ba? Shin Maree ba ‘yar uwar ta ba ce?

“Ni ma ba na gari a lokacin da ya je Dagaudan. Har ma Dadar ta ke fada min cewa ya ba da Baba makudan kudi, wai ya gyara zauren gidan da kuma dakin sa. Wallahi kudi ma su yawa, ita ma ba ta san yawan su ba. Ga shi ma har yanzun bai gyara ba.”

Ta gagara cire kaduwar da ta yi a kan cewar Yusuf ya je Dagauda, ya samu labara a kan Maree, amma duk bai fada ma ta ba. Anya? Ta san mijin ta kuwa kamar yadda ta ke tunanin ta sani?

Ta nisa. Ya dai ce za su yi magana. To ko wannan din ya na daya daga cikin abin da zza su tattauna a kai? Za ta jira ta ji, ba za ta yi saurin yanke hukunci ba.

“Ke mu bar wannan…. ya ya gidan aure?” Muhibbat ta canja akalar hirar su, ta na daga ma ta gira tare da murmushi. “Ina labari? Na ga sai wani yawan dariya ki ke yiyi.”

Ta dan yi dariya, “Kai Muhi sharri za ki min?”

“Kin san ban a boye-boye cikin al’amarina. Na lura tun haduwar mu bakin ki ya ki rufuwa, sai yawan dariya kamar tsumma. Mene ne sirrin?” 4

“Ke fa ‘yar sa ido ce.”

Da gaske ne, a ‘yan kwanankin nan ba bu abin da yak e iya bata ma ta rai. A ko yaushe, kuma komai kankantar lamari sai ta ji wani irin farin ciki ya mamaye ta. Komai kara kyau ya ke ma ta, komai kyalkyali ya ke yi da kamshi.

Muhibbat ta mike tsaye, “Ba ki ga ma sa ido ba tukunna, ‘yar rainin hankali. Mike tsaye…” 2

Asiya ba ta ankara ba ta ji Muhibbat ta ja ta sama, sannan ta shiga zagaya ta a hankali, idanun ta kyam a ta kasa-kasan jikin na ta. Ta daure dariyar da ta ke neman kubce mata.

“Kin san ni ‘yar aiken Dada ce, dole na zama jasusi(spy), wato ‘yar liken asiri. Na dai ga kin canja, kin kara kyau. Amma wannan shafaffen cikin na ki ne ban a so. Wai me kike jira?” 2

Bai kamata ba, amma Asiya ta ji ta fada cikin tsananin rudani da jin kunya. Hakan ba zai rasa nasaba da yadda Yusuf ya nemi bukatar su ciyar da alakar su gaba ba. Kallon cikin idanun ta ya yi, y ace, ‘ni, ke…sai mahaliccinmu….

Da kyar ta karkade wannan tunani, ta mayar da hankali kan Muhibbat. Zuciyar ta zogi ta ke ma ta. Idan ta sake Muhibbat din ta gane ta na cikin wannan hali to fa abin ba zai kare ba.

“Kamar yaya? Ban fa gane abin da ki ke nufi ba.”

Muhibbat ta harare ta, “’Yar rainin hankali, to bari na mi ki gwari gwari; yaya aka yi ba ki yi ciki ba har yanzu?” 2

Asiya ta gwalo idanu, “Muhi? Ba Allah ne ke bayar wa ba? Kin san dai ba a ruwa a ke shan sa ba ko?”

“Haka ne. amma kar ki bata lokaci fa. Don yadda naga Ummah ta na yi da Amatullah, zai kyautu ta fara rike nata jikokin, na jini.”

Zuciyar Asiya ta dan sosu kadan. Da gaske ne Ummah na son ganin jikokin ta. Kuma a halin da a ke ciki, babu babbar katangar da ke hana ta kai ga burin ta da ta wuce Asiyar, ita da sharadin ta. Wata kila da ba ta gindaya ba, da hakan bai faru ba.

Ta shiga jin zuciyar ta na tsere, ta kasa zama cikin kirjin ta. Shin da yanzu tana dake da juna biyu ke nan? Da yaya Ummah za ta rika ma ta? A yanzun ma da babu komai jikin ta ba ta rage ta da komai ba ta fagen kauna don kuwa yadda ta ke son ta ko Dada ce albarka. Ai sai dai kuma son ya karu.

Asiya ta yi dariya, “To, na ji. Allah Ya kawo ma su albarka.”

“Amin. Ko ke fa? idan ma ki ka tsaya wasa, kya ga Dada da hayakin sassaken sawun giwa da na arrarabi da duk wata kwamacala. Zan rako ta mu rika danna miki har sai kin fadi kudin farin ki. Ehe!”

STORY CONTINUES BELOW


Asiya ta zauna ta na dariya. Ita ma kan ta ta tuno lokacin da yayar ta Asabe ta dan samu jinkirin samun juna biyu a gidan mijin ta na fari. Ta tuno da yadda Dada ta daga hankalin ta. Musamman ta je har Sara-dugub, kauyen da ta ke aure ta nemi izinin mijin ta dauko ta.

Babu hadin da ba ta narka ma ta ba, kama daga hayakin mayu, zuwa kan na shaidanu da su kaikayi-koma-kan-mashekiya, da ma dai wasu abubuwan da ba ta san sunan sub a, ciki har da ma su kalar kashin bera. Duk kuma wannan a dalilin ta kai watanni takwas ne babu cikin.

Ta tabbata idan ita din ma hakan ya kama, Dada za ta zo ta dauke ta, ta mayar da ita ta rika danna mata wadannan. Yiiii! Ba za ta iya wannan ba gaskiya. Tsikar jikin ta ya shiga tashi. Ba da ita ba, wai gada a hurumi. 2

“Ni kam wai babu wanda zai yi motsi ne cikin samarin ki, ya rage miki wannan bakin naki?”

Muhibbat ta wulkita idanun ta, “Ke ma kin san ni din fa sai a hankali. Babu mai iyawa da ni.”

“Gaskiya ne, mutuniyar. Babu ja, wai jaki ya mutu a jeji. Na fa san ke din sai Ardo!”

Muhibbat ta ja gwauron numfashi. Fuskar ta ta tsuke. Asiya ta gyara zaman ta, “Me ya faru Muhi? Na fadi wani abin da ya bata miki rai ne?”

Muhibbat ta girgiza kan ta, “A’a. kawai. Kin san har fay a fito, ya kai goro gidanmu. Amma mahaifan sa bas a sona. Kan hakan suka ma sa wani auren da wata ‘yar uwar sa kimanin watanni biyu ke nan, amma ya ki amincewa. A yanzu haka ya bar gidan su, wurin da suka ajiye matar ta sa, ya koma gidan wani kawun sa.”

“Subhanallahi!” Asiya ta matsa kusa da ita, ta na mai tsananin tausaya ma ta. Muhibbat ba sa’ar ta ba ce, yawancin sa’anin ta duk suna daki. Ita ce ta yi nauyin aure a cikin su. “Ban san abin da zan ce ba. Na san kun yi nisa….”

Muhibbat ta sake nisawa, “Ni dai nace ma sa mu hakura kawai. Idan ban yi aure ba, ba mutuwa zan yi ba. Sai me idan kowa ya yi aure ya bar ni? Ai ba kowa ba ce Allah Ya kaddara ma ta yin aure a duniyar nan.?”

“Kar k ice haka Muhi. Lokacin ki ne bai yi ba.” Ta dan saka fuskar zolaya, sannan ta ci gaba da cewa, “Wata kila da Sani Kwatambe ne, da tuni kin fafo ma sa ‘ya’ya biyu.”

Muhibbat ta tsakuri kunnuwan ta, “Wai ma, yarinyar nan kin fa raina ni. Ni wata kaza ce da zan fafe ‘ya’ya?”

“Ouch! Zan fa kai ki kara wajen Likita, in fada ma sa abin da kika min.”

“Iye! Su ‘yar gatar likitan ba! To ni in ba karnukan nan zai sako min ba, ba zai hana ki rankwashin ki ba ma, ehe.”

Su ka yi dariya, Muhibbat ta kara da cewa, “Ban san irin abincin da ku ke ba su ba. Karnuka kamar marakin shanu? Ko dai allura a ke dirka mu su?”

Ita ma kan ta Asiya ba ta san irin abincin ba. Ta kan ga Larai na bude na gwangwani ta hada da farar shinkafa wasu lokutan. Ko kuma ta dafa mu su jan nama musamman don a zuba mu su su ci.

“To yanzu me a ke ciki ke nan Muhi?”

A bayyane ne, Asiya ta na tambaya ne game da auren ta. Ta san Muhibbat zai yi wuya ta amsa, amma duk da haka, ya dace ta tambaye ta.

Muhibbat ta kalli Asiya, ta amsa, “Babu.”

“Babu? Me kuka tsara, ke da Adon?”

“Babu.” Ta sake maimaitawa, tare da fadada murmushin ta. “Babu amfanin auren sa, don daga ni har shi, babu wanda zai kasance cikin farin ciki. To don me zamu fara abin da ba zai karko ba?”

“Amma kin tattauna hakan da shi ne?”

Muhibbat ta dan yi dariya, “Me ye abin tattaunawa a nan? Abu a bayyane ya ke, iyayen sa ba sa kauna ta, b azan taba burge su ba. A cewar su, na waye da yawa, ba zai iya juya ni ba….ki ji fa.” Ta tsaya ta na farii da idanun ta, ta na ‘yar dariyar takaici, “Sai ka ce zan canja don burge wasu. Hmmm.”

Ba za mu so ki canja ba Muhi.”

“Ni dai du’a’i nake yi ta yi, kan cewa Allah Ya sa hakan shi ne mafi alkhairi. Wa ya san abin da Ya kare, wanda zai faru idan n adage kan auren sa? Shi ya sa na mayar ma sa da goron sa. Allah Ya hada kowa da rabon sa.”

“Amin.” Kawai Asiya ta iya furtawa. Muhibbat ce ta fara zama a jerin wabin ‘ya’yan da mahaifan ta suka yi ta yi. Daga it ace kuma sai kanin ta Alfa.

Dole ne a ce sun dora burin ganin auren ta kafin sum utu, don kuwa da tsufar su suka haife su. Akwai ma su zargin cewa sun sakalta ta ne sai yadda taga dama ta ke yi, shi ya hana ta auren. Amma kamar yadda su Asiya suka sani, lokaci ne bai yi ba. Kuma abokin zaman ne Allah bai bayyana shi ba.

“Kar ki damu, Allah Ya mi ki tanadin miji, wanda ya fi Ardo. Bari ya fito kawai mu taru mu ma sa rubdugu, mu ji dalilin kin fitowa da yayi har sai da ya wahalar da mu.”

Muhibbat ta dan yi dariya, “Ke ni fa hankalina kwance, bandamu ba. Idan ya fito kawai zai sha shagwaba da soyayya, har sai ya gode Allah.”

Ta gyara zamanta, ta ci gaba da cewa, “Minde, ki kara gode wa Allah da irin baiwar da Ya mi ki. Na san haka na nasaba ne da irin hakurin ki da biyayya ga iyaye.Wallahi, hankalin Dada ya kwanta sosai, mu kanmu na gefen ki hankulan mu a kwance, don ganin mijin da Allah Ya baki daya ne cikin miliyoyi. Don haka ke ma ki kwantar da naki. Zancen Maree kuwa, an sa Malamai addu’a, a na kuma kan yi.”

Ta nisa sosai. Idan ta na son rike Yusuf, wanda kuma hakan ta ke so, tilas ne ta sadaukar da zuciyar ta, ta cire kunya, ta kuma rike Allah, sannan ta mika ma sa kanta ba tare da wata fargaba ba.

Wannan kwakwalwar ta ke fada ma ta, zuciyar ta na kaucewa. Soyayya babban tarko ce, mai sarkakiyar da ke da wahalar warwara. Sai dai a shirye take ta fada duk wani tarko in a dalilin mijin ta ne.

Larai ta leko, “Anti, Maigidan ya dawo daga masallaci.”

Asiya ta duba agogo, karfe takwas da minti biyar. Lokacin da ya saba dawowa ke nan bayan ya idar da sallah a masallaci yayi zikirin sa, idan har ba asibiti ya ke ba.

Ta mike cikin sauri, “Muhi, bari na kai ma sa abinci, yanzu zan dawo.”

Muhibbat ta gwalo idanu, “Ina za ki je?”

Asiya ba ta kalle ta ba. Yanzu su ka yi maganar abincin mijinta fa. Ta ce, “Don Allah ki kyale ni na kai ma sa abinci, kar ya gaji da jira na.”

“Hakan za ki je?”

Asiya ta kalli kanta, “Me ye aibun hakan?” Dazu fa Yusuf sai da ya ma ta kallo na musamman har ta ji dadi a zuciyar ta.

Muhibbat ta dafe kan ta, ta kalli sama, “Oh ni Muhibbat ki ce Likita ya na fama da ke.” Ta harer ta, “Ashe aikina bai yi ba sam, tun da baki dauki huduba ta ba. Ai shiga bandaki za ki yi ki fesa wanka yarinya, ki kuma canja kaya dole. Don haka ba zan bari ki fita ba, shiga bandaki kawai.” 5

Wasa ne, gaske ne, Muhibbat ta tura ta bandaki ta tsare kofar. Har sai da ta yi wanka tukunna ta kyale ta ta fita. A nan kuma ta iske Muhibbat ta zaba ma ta kayan da zata saka, sai da bakin ta ya bude don mamaki.

Na farko dai riga ce da siket na turawa damammu. Siket din iya gwiwa ne. Shakka babu, ma su fallasa sirrin jiki ne, amma ba hakan ne ya dame ta ba, tun da ai doguwar rigar da ta cire ma ta dame ta. Kawai likitan ne zai ga kamar ta na aika ma sa da sakon da ya saba da sharadin ta, kamar ta matsu ne.

“Muhi, kin mance ne ba mu kadai ba ne cikin gidan nan? Idan mahaifiyar sa ta yanke shawarar zuwa sashen mu fa?”

Ta yi nasarar ture wannan, don Muhibbat sai ta ajiye, ta dauki riga da wando, su ma dammamu, “Shi ke nan. Wannan fa?”

Asiya ta girgiza kan ta, “Zai iya yin baki a falo. Kin san…”

Muhibbat ta kara nisawa, “Shi ke nan.” Ta fidda doguwar riga, dinkin gown mai lanin silba da baki. Akwai duwatsu gaba daya, ma sus aka rigar sheki. “Wannan kam, ina ga Likita ya saya ne don ya kalli matar sa cikin nishadi.”

Asiya ta karba ta saka, Muhibbat ta na, “Mashaa Allah, Tabarakallah. Kin sha kyau, sauran kin sumar da shi da kwalliya.”

“Kai Muhi, idan ya suma wa zai ci abincin?”

Ta sake samun harara daga Muhibbat, “Ce mi ki aka yi yunwar ciki ne
kadai mutum zai toshe? Har fan a idanu.”

Asiya bata bari tunanin ya ratsa ta ba, balle ta yi dogon nazari a kai.

Ta yi kwalliya har da ‘yan kunne da sarkar da ya shiga da kayan, ta yi lullubi kafin Muhibbat ta bar ta ta fita. Ta sha kamshi kuwa, sai ka ce ranar a ka daura auren su.A falo ta same shi, ya na zaune gaban talabijin, amma ya na dauke da komfutar sa bisa cinyar sa, ya dannawa.

“Assalamu Alaikum.” Ta yi ma sa sallama.

Ya amsa, “Wa alaikis salam.”

Ya kalle ta a hankali cikin natsuwa daga sama har kasa, sannan fuskar ta. Ta ji idanun sa na shiga jikin ta tamkar askar wanzami. Idanun sa na dauke da abin da zuciyar ta ce kadai ke iya fahimta, amma ba za ta iya fassara shi da harshe ba. 2

Bai taba ganin shigar ta irin wannan ba. Ta yi ma sa kyau gaskiya, kamar ne a ce mutum ya rika kallon hudowar rana daga sararin samaniya. Akwai haske mai watsa launin gwal tare da dimbin alkawarin haskaka wannan rana. Dukkan furanni da ma mai rai ya dogara ne da wannan fitar ranar.

“Na kai abincin ne tebur.” Ta furta, kan ta a sunkuye.

Ya lura da jin kunyar ta. Ba zai iya misalta yadda hakan ke kara burge shi ba game da ita. Taraddadin ta tsima shi ya ke yi.

“To Bismillah.” Ya ce da ita.

Ta koma teburin, har ta zauna idanun sa ba su kau daga kan ta ba. Shi ma ya taso zuwa teburin ya ja kujerar sa da ke kusa da na ta ya zauna. Ya canza kayan jikin sa zuwa doguwar jallabiya mai gajeren hannu. Kamshi biyu ke tashi daga gare shi; na sabulun wankan sa da kuma turare.

“What’s for dinner? Me ye abincin daren yau?”

Ta dan kalle shi, shi kuwa ya tsare ta da idanu. Da gangan ya sauke muryar sa, ya na murmushi a lokacin da yak e ganin tasirin hakan. Ta kasa tabaka komai.

Ta bude kwanukan a matsayin amsar ta. Kamshin ferfesun kaji mai kayan kamshi tare da tafarnuwa ya naushi hancin sa. Taliyar Penne ta dafa tun kafin fitar su da yamma, don haka ta hada da kajin da suka sayo, wanda ta sake gasawa cikin oven cikin gaggawa. Ta kara cika kayan kamshi da albasa da yaji.

Bai san lokacin da cikin say a rika yi ma sa kugi ba. Kafin ta fito yayi zaton a koshe yak e, kawai dai zai dan taba ne. amma a yanzu ji yake kamar zai ci giwa.

“Na san zaa iya neman ka zuwa aiki a ko da yaushe, shi ne na yi maka abinci marar nauyi.” Ta furta cikin murmushi mai garwaye da jin kunya.

Ya yi murmushi. Ya ji dadin kulawar ta. A dan zamantakewar su, ta fara kiyaye abubuwan sa da dama. Bai san ko duk ta na hakan ba ne don Amatullah. Shi ya sa ya ke son su zauna su dan tattauna a kan hakan.

Ita ma ta yi murmushi sannan ta kara sunkuyar da kan ta cikin kunya. Bai san wanne ne ya fi tsima shi ba; abincin da ke gaban sa ne, ko kuma ita. Ta ma fi abincin da ke gaban sa.

“Well, ina jira, ki zuba min da hannayen ki.”

Ta dago ta kalle shi. Bai san ko zai iya jurewa ba, amma idan ta kara yi ma sa wannan kallo to zai mance da yunwar abincin da ke gaban sa ya ja ta zuwa jikin sa. Ko ma me za ta dauke shi sai ta dauka, zai mance da alkawarin da ya dauka ma ta kafin auren su.

Bayan ta zuba a filet, har ya fara ci, ya ce da ita, “Bismillah mana, ina kwarya.”

Ta ce, “Ba na jin yunwa. Na ci abinci da Muhibbat dazu.”

Ya dan bata ransa tare da ajiye cokalin sa, “Ni kadai za ki bari ina ci yanzu? Gaskiya ban ji dadi ba. Ko albarka ki saka min.”

Ya lura da damuwa cike da idanun ta hade da nadama. Abin da ya ke son gani ke nan. Ta dauki wani filet zata saka na ta. Yayi sauri ya dakatar da ita, “Me ye amfanin nawa filet din?” 2

STORY CONTINUES BELOW


Ya saka mu su a tsakiya, ita kuma ta dauki cokali mai yatsu ta fara ci. A lokacin ne ya lura, cewar akwai abin da ke damun ta, ta ke boye shi cikin zuciyar ta. Kokari take yi, ta na ma sa murmushi, amma ya lura da giftawar sa. Zai jira ya ga, ko zagin idanu ne. ko kuma hakikani ne.

Cikin barkwanci ya debe ta zuwa wata hirar, ya ce, “Yanzu dai a raba kowa ya cinye nasa. Ko za a gane mai babbar loma.”

Ta dan yi dariya, ganin da gaske ya ke yi. Ya raba gaban sa da nata, “Kar a yi warwaso. Kuma ban da cin gaban wani.”

Sakewar ta ya saka ma sa sukuni. Idan ta na son fada ma sa wani abin da ta ke shakka ne game da yadda zai ji, wajibi ne ya sassauta yanayin. Ya yi ta bata labarin cin abincin sa da su Hadi a lokacin sun a sakandaren kwana, da ma irin girke-girken su irin na maza.

“Idan mu na girkin shinkafa ne, to kowannen mu da cokalin sa ya ke zama. Sai mu gewaye tukunyar da murhun. kowanne bayan minti goma za a bude tukunyar nan, don a taba a ji ko abincin ya nuna. Nan fa kowa sai ya diba da cokalin sa ya ji da kan sa.”

Cikin dariya ta ce, “To ai wannan kun cinye kafin ku gama girkin.”

“Eh to, an dai ci fiye da rabi kuma ta hakan mu na maganin ma su jiran girkin namu,’yan kwadayi. Lokacin da za su zo bayan mun sauke, kadan za su samu. Mu kuma cinye tare da su.”

“A lokacin har taliya ku ke dafawa?”

“Sosai ma, taliyar murji ‘yar gida. Ba irin wannan da a ke ci na kanti ba. Ina gaya miki, kina cin irin su kamar roba kike ci cikin bakin ki.”

Ta tuntsire da dariya. Sai a lokacin ya lura da abin da ta yi ma sa. Yayi sauri ya ce, “Ba fa santi na ke yi ba.” Sai kuma ya kalli filet din da ke gaban su, babu komai a ciki. Ya sake kallon ta, dariyar dai ta ke yi. 3

“Ni ma ban ce santin ka ke yi ba. Ka na bai labarin taliyar murji….”

Ya ajiye cokalin sa, “Tsokana ta kike?”

Ta dan tsime fuskar ta don ta bar yin dariyar, amma dai ta gagara. Shi ma karshe sai da yayi dariyar. y ace, “Ni fa ina ga ke ce kika cinye abincin nan, ki ka kala min.”

“Na yarda.” Ta furta cikin dariya. “Bari na je nemo waiji na saka a bayana.”

Da wannan ta mike ta tattara kwanukan, ta kai kicin. A bisa al’adar gidan, kwano ba ya kwana da datti. Don haka ta shiga wanke su. Shi ma ya kai sauran kwanukan, ya same ta dab da bakin famfon. Maimakon ya tafi, sai ya tsaya su ka yi wanke-wanken tare. Ta na wankewa yana darwayewa. Ta kifa su a wajen kifawa. 5

Sun gama tsaf, su na goge hannayen su ne, ya ce, “Ban fada mi ki yadda girkin ki ya yi ba.” Ya jefa ma ta kallon da ke nuna halin da zuciyar sa ke ciki. A kalla, hakan yake fata. Don ba zai iya misalta halin da zuciyar ta sa ke ciki ba.

Ba tare da bata lokaci ba, ya ja ta zuwa jikin sa. Ya na jin zukar numfashin da ta yi, wanda ya yi daidai da lokacin da iska ta kaurace wa huhun na sa.

Yanzu ne ya ke fahimta, cewar ya fada kaunar wannan jarumar yarinyar ce, wadda ta bar kauyen su don fuskantar sa. Lokaci guda ta zama duniyar sa, ya shiga kaunar ta ta hakika, ba wai don ya na son zuri’a da it aba ne. Wani irin tsallen da zuciyar sa ta yi, a tsammanin sa ta fice ne ta kan sa.

Ya sauke muryar sa sosai, “Ban kuma fada mi ki yadda kwalliyar da ki ka yi ta yi ba.”

Jikin ta gaba daya rawa ya shiga yi. Shi ma ya dimauce, don bait aba yin hakan da wata ‘ya mace a duniya ba. Tsakanin sa da mata, sai marasa lafiyar da suka kasance lalura. Ya dan jira, kafin ya aiwatar da abin da ya yi niyya. Wata kila ta riga shi komawa hayyacin sa, ta tsayar da shi, ko ma ta ture shi ta yi tafiyar ta.

STORY CONTINUES BELOW


Ba ta motsa ba. Ta na jikin kirjin sa, numfashin sa hade da na ta, idanun sa cikin na ta. A hankali ya duka kadan, ya sumbaci lebban ta, a hankali. Suna da taushin gaske, kamar yadda yayi zato. Ya taba yin sumba, amma ba kamar wannan ba.

Bayan ya dan ja daga fuskar ta, ya na kallon kwayar idanun ta. Na sa dauke da zallar sha’awa, ya ce, “A-ONE.” 2

Tabbas ya na nufin kwalliyar ce da kuma abincin. Amma tunanin sa ya zarce wurin da suke, ya shiga wani wuri daban. Zuciyar sa ta shiga raya ma sa ya aiwatar da tunanin na sa, amma dole ya ture wannan.

Da farko dai, su na kicin ne. Sannan su na da babbar bakuwa, wacce ba ya son ta san halin da suke ciki. Yin wani abu zai fallasa komai. A dole zai hakura.

Komai ya na da lokacin sa. Ya tabbata tun da ya iya hakurin watanni, wannan din ma ba zai kasha shi ba. Amma zai fada ma ta abin da yayi niyya fada tun kafin ya makara.
Numfashin ta ya yanke gaba daya daga huhunta,kafafuwanta suka dawo ruwa.zuciyarta kuwa sai a likacin ta ke jin bugunta mai tsanani.ta shiga wata duniyar daban,ta mance da wanan duniyar.Duniyar da daga ita,sais hi,sai wata igiyar da ke gewaye das u,wadda ke kara kusantar dasu .

Ya dan tallafi fuskar ta da hannun sa, abin da ta gani cikin idon ta, ya tabo ruhin sa. Sai kuma kunya mai tsananin da ta saka ta sunkuyar da kan ta.

Ya sauke muryar sa sosai zuwa ga rada-rada,ya ce, “Asiya a matsayi na na mijin ki, ki na ganin akwai damar da za ki bude min zuciyar ki, na samu mazauni komai kankantar sa?” Ya shiga shafa gefen fuskar ta da bayan yatsun sa biyu a hankali, ya na jin shaukin kauna na kara kama shi kamar wutar lantarki. 4

Ya ci gaba da cewa, “Na san kafin mu yi aure, babu zancen soyayya a tsakanin mu. Amma a hankali son ki ya shiga zuciya ta, ba tare da na yi la’akari ba. Cikin kadaici na ke, zuwan ki ne ya san a zama cikakke. A halin yanzu, kin mamaye zuciya ta, da ke da Amatullah. Kun zama ginshikin rayuwa ta, ta yadda na ke jin idan babu ku, to babu ni.

“Don haka please, Asiya, ki daure ki dan bude min mazauni kankani a cikin zuciyar ki. Idan kuma babu hali, to ki san cewa ba zan tilasta miki ba. Zan kuma ci gaba da rike ki bisa duk sharudan da ki ka shimfida tun farko.” 2

Gaba daya ta sunkuyar da kan ta tare da rufe fuskar ta da hannayen ta.

“Amma kuma idan har ki na ganin za ki bani dama, to zan saurari ishara daga gare ki. A duk lokacin da ki ka shirya hakan. Na yi mi ki alkawari, za ki yi alfahari da ni wajen kiyaye hakokkin ki. Idan kuma Allah Ya ba mu zuri’a zan yi kokarin kasancewa mahaifi nagari. Na san ba abu ne mai sauki ba, amma idan kin bani dama, komai zai zo cikin sauki.”

Ya ja ta daga kicin har zuwa kofar dakin ta, bai bari ta yi nesa da jikin sa ba. Ko da suka tsaya, sai ya sake jan ta sosai zuwa jikin sa. “Ina son ki je ki kwanta a kan rokon da na yi mi ki. Duk abin da ki ka yanke, ni mai karbar sa ne hannu bi-biyu.”

Ya sake sumbatar ta kamar ba gobe. Daga karshe ya janye da ga jikin na ta, ya ce, “Sai da safe, my love.” 8

                 *                *               *

Asiya  a lokacin ta ji tamkar ta na shawagi ne a iska. Sai ya jefa ma ta kallon mai kasha jiki na karshe, sannan ya tafi, kafin ta dawo hayyacin ta. Da kyar ta iya bude kofar dakin ta shiga, ta na jin kafafuwan ta kamar sun manne da wajen da ta ke tsaye. Bayan ta bude ne ta manne da jikin kofar, hannun ta kan kirjin ta. Zuciyar ta na tuna yadda sumbar sa ta kasance. 2

Ta tarar da Muhibbat ta yi barci, ta na rungume da Amatullah. Ta san akwai gajiyar hanya ne a tare da ita. Ta yi wanka ta canja kayan jikin ta zuwa kanana, ta yi kwanciyar ta. Ta rika sandar taku a hankali, gudun kar ta tayar da daya daga cikin su. Kowacce za ta iya ba ta irin ta ta matsalar. 2

STORY CONTINUES BELOW


Ta wuce cikin dakin kayayyakin ta, ta rufe kofar tare da dafe kirjin ta da hannayen ta duka biyu. A yanzu ne kalaman Yusuf ke kara shiga zuciyar ta. Sai yanzu ne ta ke jin ta a sararin samaniya, a kan gajimare. Yusuf ya furta ya na son ta, ya na kuma neman ta so shi…. wayyo ina za ta saka kan ta don dadi?!

Ta na kallon sama, a yayin da dadi ke kara bulbula daga jikin ta. Allah Sarki dadi, in ji barawon zuma. Ashe Yusuf ya na son ta… 2

Ba za ta iya misalta yadda son sa ke wanzuwa cikin zuciyar ta ba. Ba za ta iya bayyanawa ba, don kawai jin sa na ke ya na bulbula kamar yadda a ce ta ke numfashi ne da kuma bugun zuciya. Ita ma ta na son sa, ya mamaye zuciyar ta, ya mamaye ruhin ta. Ya zama duniyar ta gaba daya.

Ya na sona, Yusuf ya na so na, abin da zuciyar ta ta rika buga ma ta ke nan cikin kwanyar ta a kai a kai. Ta rasa in da za ta jefa kan ta don dadi. Ta so fada ma sa yadda ita ma ta ke ji, amma tsabar kaduwar jin a sa sirrin zuciyar a lokacin da ba ta tsammani ba ne ya daure harshen ta.

Ta je ne da niyyar za ta yi ma sa maganar samun Maree da a ka yi, ta tambaye shi dalilin da ya sa bai fada ma ta an ganta a Jos ba, ko da kuwa ta bace ne bayan an gan ta.

Sai kuma ba ta ga dacewar yin hakan ba. Idan ya boye ma ta, to lallai akwai dalilin san a yin hakan. Don haka ta fasa tambayar. Idan ma a kai yake neman su tattauna, zai bayyana ma ta.

Ta koma dakin ta a hankali bayan ta canja zuwa kayan barcin ta na daguwar riga mai silbi. Ta ja matashi ta rungume ta a hankali, ta kwanta ta na fuskantar silin din dakin na POP. 2

Ba ta san yadda zan fara fada ma sa ba, cewar ta na kaunar sa. A da, ta na tsoron nuna alama ne gudun kar ko zuciyar sa da wani abin ne daban. Ta nisa, tare da taba lebban ta. Ta tuno da sumbar sa, sai ta kara jin wani shaukin son sa na sauka a jikin ta kamar ruwan sama a watan Augusta. 1

Ta gagara fada masa komai ne don kunya ba za ta bar ta ba. Dole ta daure ta cire wannan kunyar ta fada masa abin da ke zuciyar ta cikin gaggawa kafin ta makara. Aiki mai kyau ba a yi ma sa jinkiri. Amma dole sai gobe da safe. A yanzu kam zata bar shi ya kwanta, ya huta.

Ita kam, ta san ita da barci sun yi hannun riga. Za ta kwana tunanin mijin ta, da kalaman sa dadada…
                    *                    *                  *

“Amatullah ta zo gaishe ka.” 2

Yusuf ya daga kan sa, ya kalli Asiya daga kan kofin shayin da ya ke kurba kan teburin cin abinci. Ya yi ma ta kallon tsaf, ta na jin idanun sa kamar yadda tartsatsin wutar lantarki a illahirin jikin ta. Zuciyar sa na tsalle cikin kirjin sa. 4

Atamfa ta daura, launin tsanwa da rawaya. Dinkin ya kara kawata ta. Ya lura ta saka sarkar daya taba saka mata da hannun sa a kwanakin baya can. Daurin dankwalin ta ya zauna daram a kan ta tamkar kambum sarauta; sarautar zuciyar sa. Kamshin ta sai tashi ya ke yi, ya na kara tsima shi.

Ya mike tsaye a lokacin da ta mika masa Ama. Ya karbe ta. Ita ma ta sha ado da kamshi, sai neman jijiga shi ta ke yi. Ya kalle su dai-dai, zuciyar sa ta yi faaat. Hakika, duniyar sa ta cika.

“Good morning, dear.” Ya ce da ita. “Kin tashi lafiya?”

Amatullah ta dan yi gwalanton ta, shi kuwa ya saki murmushi, “That’s right, na gane.”

Asiya ta dan yi dariya. Ya kalle ta, ya na jin zuciyar sa na radadin dadi. Ta na yawan yin dariya a kwanan nan. Hakan ba karamin dadi ya ke ma sa ba. 2

“Me ya baki dariya?”

Ta kau da fuska kadan, “Ba komai.”Amma ba ta bar dariya ba.

Shi ma ya yi murmushi, “Ba ki yarda cewa na ganen ba ko?”

STORY CONTINUES BELOW


Ta tsagaita dariyar, idanun ta na kyallin farinciki zalla, “Me ka ganen?”

“Me na gane? Abubuwa da dama. Na gano cewa mata ta ta na da sautin dariya mai dadin gaske.” Ya ja ta zuwa jikin sa ta bangaren damar sa, Amatullah na rike ta gefen hagunsa, “Na gano cewa hakan ya na burgeni.”

Ya ji sautin zukar numfashin ta, amma shi tasa kwanyar ta cike da karar bugun zuciyar sa, balle ya fahimci wani abu. Ya ce da ita, “Ba mu gaisa ba.”

Ta sunkuyar da kai don kunya, amma bayan ta kalle shi cikin idanu, ta ce, “Ina kwana?”

Ya ji wani irin tsima a jikin sa. Dadi ya cike ma sa zuciya. Sautin muryar ta ta rika yi ma sa abubuwa kala kala cikin jikin sa.

Ya ba ta amsa, “Na fada mi ki gaskiya? Ban yi barci ba sam daren jiya. Kwana na yi ina tunanin ki, tare da zullumin amsar da za ki ba ni ta neman bukatu na gare ki.”

Da gaske ya ke yi, bai yi barci ba. Ya kwana ne juye-juye kan gadon sa, halin da tun Abida bai samu kan sa ciki ba. Karshe ya koma teburin karatun sa, ya shiga karance-karance, binciken cututtuka iri-iri cikin takardu da ma komfutar sa. Amma bai gane kan cutar da ta addabe shi ba, ta hana shi sukuni. Wai yaya za a ce abu mai saka zogi da radadi zai watsa dadi jikin mutum? 2

A wani bangare kuma ya rika fatan ganin ta je gare shi a jiyan, ta bayyana ma sa matsayin sa. Bangare guda kuwa ya san ba za ta je ba, ya kuma yi fatan hakan. Ya ba ta damar tunani ne don ta kara jin kaunar sa, ta yi kewar sa.

“Me ya sa za ka ji zullumi?” Ya ji sautin muryar ta ya kutsa cikin kan sa.

“Dole na yi zullumin sanin matsayina wajen ki.”

Ta sake kallon sa, ta na murmushi. Zuciyar sa ta sake yin tsalle, ta hada da dungure da mirgine. Alamar rashin barci ya hango cikin idanun ta? 2

“Ni ma ban ji barci ba.” Ta furta a kunyace, idanun ta a kasa.

Zuciyar sa ta yi shewa, ta na fatan dalilin rashin barcin ta, ya kasance abin da ya hana shi barcin ne jiya da dare. 2

Cikin muryar da ya san zai ratsa zuciyar ta, ya tambaye ta, “Ko me ya hana ki barci?”

Ba ta daga kan ta ba. Ba ta kuma bar jikin na sa ba. Good. Hakan ya yi ma sa dadi.Wata kila za ta amince da tayin soyayyar da ya yi ma ta. Zuciyar sa ta shiga radadin dadi marar misaltuwa.

“Ba ki bani amsa ba.”

Cikin kunya, game da muryar da ke kara tsima shi, ya ji ta ce, “Wani ne, Likita ne mai kyaun suna, mai kyawawan dabi’u da rikon amana. Shi ya mamaye tunani na, ya cike zuciya ta, ta yadda ba bu taku daya da ya rage.

Ya cika min zuciya ta da dimbin kaunar sa. Idanuwa na su na begen ganin sa a ko yaushe. Shi na ke muradi, na ke jin shaukin son sa a rayuwa ta. In babu shi, babu ni. Shi ya zama duniya ta gaba daya. Ina son sa, zuciya ta da rashin ta.” 7

Kasancewar ta na jikin sa ne, ya na iya jin wani abu tamkar tartsatsin wuta ya na fita daga jikin ta, ya na watsuwa a nasa jikin. Dadi ya kama shi marar misali. Zuciyar sa ta shiga shawagi a sama, ya na mai jin dadin kalaman ta. Ko a yau mafarkin sa zai zama gaskiya? 4

“Wannan likitan ya taki sa’a. Da jin yadda ki ke jin sa, sai kamar shi ne autan maza?”

Ta kalle shi kadan, fuska cike da murmushi, “Ai autan mazan ne a wajena.”

Zuciyar sa cike da zumudi, ya tambaye ta, “Shi ba ya da suna ne likintan?”

“Ya na da shi.”

“To ki fada min mana.”

Ta girgiza kan ta, alamar a’a. Sannan ta manne goshin ta da kafadar sa ta dama. Ya san kunya ce ta sa ta haka.

A lokacin Ama ta yi wani gwallaben sauti hade da ihun wasa irin na yara. Ya kalle ta, zuciyar sa babu iyaka wajen farinciki, ya ce, “Amatullah, ki ce wa maman ki ta bar jan ran bawan Allah. Ta fadi sunan likitan nan.” Ta sake wani gwalaben ta, ya ce, “Oh, kin sani ke? To fada min.”

STORY CONTINUES BELOW


Ya kalli Asiya, ita ma ta yi ma sa wani irin kallo. Ya lura a duk lokacin da ta gan shi ya rike Amatullah, ta kan masa wannn irin kallo. Shi ma ya na jin dadin hakan.

“Amatullah ta fada min sunan…saura ke.”

“Tun da ta fada maka, ba sai na furta ba ke nan.” Ta yi yunkurin janyewa daga jikin sa a hankali.

Yayi sauri ya kara rike ta, ya ce, “A’a, waka a bakin mai ita ta fi dadi.”

Fiiit! Fiiit!! Karar ham game da na bude get su ka ja hankulan su zuwa ga kofar shiga. Nan ya hango motar Hadi ta na shigowa harabar gidan. Murmushi ya zo ma sa. Hadi akwai shi da fitna in ya so! 7

Asiya ta sake yunkurin janyewa daga jikin sa, idanun ta cike da rudani. Ya dan rike ta. “Ki bani amsa ta.”

“Ba yanzu ba.”

“Me ya sa?”

Idanun ta cike da roko, ta amsa, “Bako ya zo.”

Da zai ki sake ta, don kuwa ba ya jin kunyar kowa, balle a ce Hadi. Amma ba zai so ta takura ba. Don haka ya kyale ta, ta karbi Ama, ta juya daidai lokacin da Hadi ke sallamar shiga cikin falon.

“Kai wai ni me ye amfanin ajiye manya-manyan karnuka ne? Kai ba Gwamna ba, ba wani shugaban kasa ba.”

Yusuf  bai kula shakiyancin sa ba, ya ce, “Na ajiye su maganin irin ku, ma su zuwa a lokacin da bai dace ba. Me ya kawo ka nan da sassafe?” 5

“Mantuwa na yi.” Hadi ya amsa tare da jan kujerar teburin cin abinci ya zauna.

“Me ka manta?” Yusuf ya tsare shi da ido.

“Ina ruwan ka?” Ya daga muryar sa, “Amarya, ga bako nan ya zo. A kawo ma sa shayi!”

Asiya ta fito, ta lullube jikin ta da hijabi lub. Fuska cike da fara’a ta gaishe shi. Sha’awar ta da na dabi’un ta su ka kara burge Yusuf.

“Me zan kawo maka?” Ta tambaye Hadi.

“Yauwa amarya.” Ya shiga buga yatsun sa kan teburin cikin sautin kida, ya tsaya ya kalli Yusuf, “Me ye wannan mutumin ya ci?”

“Ina ruwan ka?” Ya kalli Asiya, “Kawo ma sa abin da ki ka ga dama. Nan ai ba Otel ba ne da zai ba da Oda.”

“Mayar da wukar! Cewa na ke bakon ka annabin ka ne?” In ji Hadi

“Kai ne bakon?”

Asiya ta shiga tsakani, ta ce, “Akwai lemon tea, ginger tea, coffee, bournvita da madara. Muna da wainar kwai, da kuma sandwich.”

Hadi ya dan yi nazari, “Mmm, a kawo min lemon tea da sandwich, amarya. Ba a dai yi ‘yar malelen nan ba ko?”

Asiya ta fashe da dariya. Shi kan sa Yusuf sai da ya yi murmushi, ya sunkuyar da kai yana kadawa a hankali.

Ta amsa, “A’a, ba a yi ba.”

“Kar dai ta hannun damar ta ki har ta tafi?”

“A’a, sai an jima. Bari na kawo ma ka abincin.”

“Ba ka bata lokaci, Hadi.” Yusuf ya furta, bayan Asiya ta shiga kicin.

“Yusuf ka fi kowa sanin matsala ta.”

“Yes, haka ne. Amma da ganin sarkin fawa, sai miya ta yi zaki?”

Hadi ya gyara zaman sa da kyau, “Eh to, ai shi ya sa jiya na bar ma ka sallahu. Na zo jin matsayi na ne.”

Yusuf ya dan yi shiru. A gaskiya, tun bayan tafiyar Hadi hankalin sa ya tsaya ne kan Asiya. Ya ma mance da maganar Hadi. Sai da ya ga motar sa tukunna ya nuna. 3

“Gaskiya na manta ban yi ba jiya.”

Idanun Hadi kamar za su zubo don mamaki. Sannan takaici, “Haba Dan-auta, me ka yi min haka? Kai da ka san dawar garin? Ka san sarkakiyar da na ke ciki, me ya sa za ka taimake ni ba?”

Ba da niyya ya manta ba. Shi ma ya na neman warware ta sa sarkakiyar ce. Ya ce, “Gani na yi ka yi shigar sauri ne. Za ka iya korar yarinyar nan.”

“A ganin ka ba. Ni ban a jinkirta aikin alheri. Gwara na fara da wuri, idan zan samu karbuwa na ci gaba. In kuma ba hali sai na duba wani wajen. Amma tilas na gwada sa’a ta, ko kuwa?”

“To, yanzu tun da ka zo, sai ka yi da kan ka.”

A lokacin Asiya ta shiga da abinci a kan tire. Ta ajiye filet din burodin sandwich din a gaban sa, ta ajiye kofin shayi mai turiri a gefan sa, “Ga shi.”

“Yauwa, amarya. Na gode, Allah ba da lada. In an bi na wannan mijin na ki ne, mutum ba zai zo gidan nan ba.”

Ta yi murmushi, “A’a na tabbata wasa ya ke maka. Ba ya da rowa sam.”

Hadi ya gutsiri burodi.” Da ya ke mijin ki ne ba! Dole ko kare shi…wow, wannan burodi akwai dadi. Shin ke ce ki ka iya girki, ko duk ‘yan garin ku ne?”

Ta yi murmushi, “Na gode. Duk mace ta iya girki, sai ko rashin samun dama.”

“Haka ne.” ya ajiye burodin kan filet din, ya gyara muryar sa, “Amm, amarya, akwai abin da ke tafe da ni da safen nan. Da fatan in na mika kokon bara ta, ba zan koma da ita wayam ba.”Hannayen ta rike da saman kujera, ta kalli mijin ta, bai ce komai ba, kallon su kawai ya ke yi. Ta ce, “Tooo?! A waje na? Allah Ya ba ni ikon cika ma ka kokon ka.”

Yusuf ya kalle ta, ya ce da ita, “Gwara ki zauna.” +

Ba ta yi dogon tunani ba, ta zauna. Hadi ya ce, “Game da kawar nan taki ce.”

Mamaki ya bayyana a fuskar ta, “Muhi? Me ta yi kuma?”

“Kwantar da hankalin ki. Za ta yin dai.”

Ya ture shayin da burodin sa gefe, ya tsayar da hankalin sa kan Asiya, “Gaskiya, amarya babu boye-boye, ko kwane-kwane; na gani ne ina so. Auren ta kuma na ke son yi, amma fa in an ba ni dama.”

Yusuf ya lura da fuskar Asiya. Tsoro ne zalla, sannan mamaki. Da kyar ta yi magani, “Don Allah zolaya ta ka ke yi?”

Hadi ya tsuke fuskar sa, “Babu wasa a cikin wannan magana. Na fa zo ne na ji in zan samu shiga. Don kuwa na san kamar ta, ba za ta rasa masoya tari guda ba.”

Nan fuskar Asiya ta nuna matukar kaduwa, “Haba kai kuwa? Ya ya ka ke son na kalli Suhaima? Gaskiya, ba zai yiwu ba.”

“Amarya, ki taimaka na samu shiga a wajen ta.” Ya ci gaba da naci. “Da alheri na zo, babu sharri. Na fada mi ki, son ta na ke da aure.”

“Amma ba ku san juna ba. Ya ya za ka fara zancen aure?”

“Aure gamon jini ne. Kuma sau da dama za a so juna, a san komai game da juna, amma a zo ba a yi auren ba. Komai ai nufin Allah ne.”

A lokacin Yusuf ya sa baki, “He is right. Aure nufin Allah ne. Ke dai in babu matsala ta fannin Muhibbat, kawai ki ma sa jagora. Sauran zai ci gaba daga nan.”

Ta dage da a kan kin maganar, “Ku maza ba ku da matsala ta wannan fanni. Amma mu mata mu na da ita. Ya ya Suhaima za ta dauke ni?” 2

“Ai ba wai wannan ne karon da za ta zauna da kishiya ba.” Shi ma ba hakuran zai yi bag a alama.

Yusuf ya ja tafin hannun ta, wanda ya yi sanyi kalau, ya rungume cikin na sa, a yunkurin kara mata kwarin gwiwa, “My dear, me zai hana ki tuntubi Muhibbat da maganar don jin ra’ayin ta. In ta ce ba ta amince ba kin ga sai ya hakura. Idan kuwa ta karbi wannan tayin na sa, sai ya fara ziyartar ta a can gida, a hankali su kuma sai su tsayar da magana. Idan Allah ya sa rabon sa ne, sai ya aure ta. In kuma Allah bai yi ba, shi ke nan.” 2

Asiya ta nisa, ta kalle shi sosai. Idanun ta na bayyana jin dadin kalaman sa, ta ce, “To, bari na je na ji ra’ayin nata.” Ta san Muhibbat za ta ki shi a take kuwa.

Ta mike za ta tafi, Hadi ya ce, “Yauwa amarya. Baki ce Allah Ya bani sa’a ba.”

Ta kalle shi kadan, “Allah Ya ba da sa’a.”

Ya nuna jin dadin sa, “Allah, Amin. Ina sauraron fitowar ki.”

Asiya ta iske Muhibbat tare da Amatullah, su na kwance kan gado. Muhibbat na tsakurin ta, ita kuma ta na kyalkyatar dariya, har da makaki. Dama a ce ita ke da damar yin wannan dariya a wannan lokacin?

Zuciyar ta dauke da nauyin dutsen dala ta nufe su. Ko da Muhibbat ta gan ta, ta ce, “Duba Minde, yadda yarinyar nan ke dariya. Tun dazu abin da mu ke yi ke nan. Da zarar na tsaya, sai ta fara kuka.” Ta ci gaba da yi mata wasa.

Asiya ta nisa. Za ta so a ce ta shiga layin su, amma abu ke gaban ta, wanda ya fi karfin ta. Me ya sa ne maza ba sa da kwakwalwar tunani ne? Kawai abin da zuciyar su ta so shi ke nan sai su aiwatar? Ga shi Hadi ya na neman jefa ta cikin matsala. Da ma yaya, balle sarki ya aiko?

“Dokta Hadi ne yazo…”

Muhibbat ya kalle ta sosai, “Likitan jiyan nan? Me ya faru kuma?”

STORY CONTINUES BELOW


Asiya ta nisa sosai, sannan ta zauna gefen ta, ta kura ma ta idanu, “Muhi, ya zo ne da maganar so da kaunar ki. Kuma cewa ya yi ya na son zai aure ki.”

Muhibbat ta tsaya cik, ta kalli Asiya, sannan ta fashe da dariya, “Haba Minde, ni fa yayar ki ce. Mene ne kuma na zolaya ta?” 2

“Ba zolayar ki na ke yi ba. Yanzu haka ya na falo, ya na jiran amsar ki. Ni ma na dauka wasa ne, sai ya tabbatar min cewa auren ki ya ke da niyyar yi.”

Muhibbat ta sake mayar da hankalin ta kan Amatullah, wacce ta fara dan mitar an kyale ta. Ta ja bulumboti mai ruwa ta manna mata cikin bakin ta.

“Ba ya da mata ne?” Ta tambayi

Ga alama Asiya ba ta yi tsammanin Muhibbat za ta saurari sakon ba ma balle har a ce ta fara nazari a kai. “Sunan matar sa Suhaima. Akwai Kausar, wacce ba su dade da rabuwa ba.”

“Ya’yan sa nawa?”

Jikin ta ya fara sanyi, ta amsa, “Ba ko daya.”

Muhibbat ta kalle ta sosai. Asiya ta ci gaba da cewa, “Ba a taba haihuwa a gidan sa ba.”

Ba sai an fassarawa Asiya yadda tunanin Muhibbat zai kasance ba a wannan lokacin. Ita mai matukar son yara ce. A ce kuma wanda ya ce ya na son ta da aure, bai taba haihuwa ba?

Muhibbat ta nisa, sannan ta ce da Asiya, “Mutum ba zai ki mutum dan uwan sa ba. Amma tun da jiran amsa ya ke yi…” ta sake kallon Asiya, wacce numfashin ta ke rike cikin huhun ta, ta ci gaba da cewa, ki ce na gode da dimbin kauna, na kuma tabbata tsakani da Allah ya min. Amma aure tsakani na da shi, ba zai yiwu ba.”

Asiya ta yi kyakyawar nisawa. Ba wai auren Hadi da Muhibbat din ne ba ta so ba. Abubuwan da ka iya zuwa ya komo ne matsalar. Da Muhibbat ta kutsa kai wajen kishi da Suhaima, gwara ta ja gefe, ta shafa ma kan ta ruwan sanyi. Suhaima irin matan nan ne da suka kasance ma su munafurci ta kasa kasa. Duk wata hulda da ita, ba ta kaunar ta.

“Shi ke nan abin da zan fada?”

Muhibbat ta gyada kan ta, ta ce, “Ki ce da shi na san shi mutum ne mai nagarta, ya kuma mallaki dukkan abin da ‘ya mace mai hankali da tunani ta ke bukata. Amma idan na aure shi, ba zai iya cika min burina ba. Don haka na ke masa fatan alheri, duniya da lahira.” 2

Asiya ta fita, ta isar da sakon Muhibbat. Dokta Hadi ya yi zugum, ya na nazari. Can ya tambayi Asiya, “Mene ne burin nata a rayuwa, wanda ba zan iya cikawa ba?” Ga alama, ta soki jarumtar sa ne, ta jefa kalubale a gare shi. Fatan ta dai kar hakan ya sa shi dagewa sai ya mallake ta, don tabbatar da jarumtar ta saw a duniya.

“Ba ta fada min ba.”

“Amma ke ya kamata a ce kin sani.” Yusuf ya furta.

A bayyane ya ke ba su yi tsammanin wannan amsar daga Muhibbat ba. A ganin Asiya, ba su saba neman mace, ta ki su ba. Duk sun kadu, sun birkice.

Hadi ya ce, “Ba komai.  Zan so jin burin nan na ta, ko Allah zai sa idan ina da rabo, na cika mata su. Idan fa har cikin zuciyar ta, da gaske ta ke yi, kan cewa zan iya kasancewa mai mallakar halayen da mace ke so a miji.”

Yanayin fuskar sa, da sautin muryar sa sun tabo zuciyar ta. Ta tausaya masa don irin matsuwar da ya nuna. Amma fa ta na tsoro, idan an yi aure tsakanin sa da Muhibbat, to lallai su za su zama abin tausayi. Balle maza akwai su da nacin tsiya. Tun da har ya saka ta a zuciyar sa, ba zai cire ba sam, har sai ya aure ta, ko kuma ta yi aure.

Asiya ta nisa, “Zan dai turo ta, ku yi maganar kai da ita. Ko za ku fi samun fahimtar juna.”

Hadi ya yi murmushi, “Kin gama min komai, amarya. Zan mi ki addu’ar Allah kara barin ki da angon nan naki, mai miskilancin tsiya. Da ma ance babban goro sai mogogin karfe.”

STORY CONTINUES BELOW


Yusuf ya harare shi, “Au, ni kuma ka fada yi wa tsiyar ka?”

“Ba tsiya ba ce, gaskiya na fada. Ita ce daidai da kai.”
Yusuf ya girgiza kan sa, “Na kyale ka ne, albarkacin Asiya. Ba don haka ba, da sai ka fita yanzun nan ba shiri.”

“Afwan, aboki na zan fita. Na ga ka saka min idanu ne don na zo na ci burodin gidan ka. To dadin abin ba kai ka bani ba.”

“Ka dai yi sa’a.”

Asiya ta koma wajen Muhibbat, ta same ta ita da Amatullah a kan kafet wannan karon, sun baje kayan wasan Ama su na yin wasa. Aman na zaune cikin kujerar koyon zaman ta, ta na ta jijjiga kacau-kacau, ta na ihun wasa.

Nan take murmushi ya zo fuskar ta. Da Ama za ta yi sati wajen Muhibbat, ba za a ji fitinar ta ba. Don kuwa Muhibbat ta iya biyar da yara.

“Kin gama da mijin na ki, don ina son komawa ne da wuri. Ki zo ki karbi diyar ki, in ba haka ba, za ta sa na sake kwana. Kin ga baby da wayo?” Muhibbat na magana cike da sha’awa.

Asiya ta yi murmushi, “To ga shi na zo karbar ta ai.” Ta zauna dab da su, ta ci gaba da cewa, “Muhi, dokta Hadi ya na jiran ki a falo.”

Muhibbat ta kalle ta, “Dan-a-nace ne ko?” Ta furta cikin murmushi. “Ai maza ba su da dama in su na son abu.”

“Hmm, gaskiya kam. Wannan ya nace. Cewa ya yi wai ya na son sanin burin ki, ko zai iya cika mi ki. Na ce dai zan ce ki je ki same shi, ko za ku samu fahimtar juna.”

Muhibbat ta nisa, “To, bari na je in ji irin na sa salon kuma.”

Ta mike, ta dauki babban mayafi ta rufe jikin ta. Atamfa ta saka, mai launin rawayan bula, garwaye da fari. Ya sha dinki zan-zan, ya kuma karbe ta. Muhibbat na da tsarin halittar mata mai kyau, ta yadda ko mace ce ‘yar uwar ta sai ta kyasa ta, balle namiji. Dole mana Hadi ya rude.

“Sai na dawo. Yanzu ma zan juyo in sha Allah.” In ji Muhibbat.

Asiya kawai dai murmushi ta yi. Ta san sai Allah, wai an saka jaka a rami. Domin irin kwalliyar kawar ta da yadda shigar ta ta karbe ta, malam Dokta Hadi ba zai bari ta kubuce masa ba. A kalla, ba da wuri haka ba. Allah Ya sa su yi nasarar fahimtar juna, kowa ya kama gaban sa.

“Assalamu alaikum.” Yusuf ya furta sallama. Ya same ta da Amatullah su na zaune, ta na mata wasa.

“Hira ku ke ne ku ka bar ni a falo?” Ya zauna shi ma, kamshin say a cika ma ta kwanya, kunya ta kara kamata.

Asiya ta yi murmushi cike da taraddadi, “Mun ba ku fili ne ko za ku samu nasarar zakin baki wa Muhibbat, ita kuma ta ji dadin kwadaku da kasa.”

Yayi ‘yar dariya, “Haka ki ke gani? To ashe dadin bakin namu ya shahara. Kuma in haka ne, tabbas kanwa zata kar tsami, kwarnafi ya kwanta.” Ya kai hannun sa ya dauki na ta, ya kai bayan hannun bakin sa, ya sumbata, idanun sa suna kan nata. Nan take ta ji ta na narkewa, zuciyar ta ta na bugawa. Ya ci gaba da cewa, “Ba ki san abin da ka ke so ne, ka ke ma sa dadin baki ba?”

Ta janye hannunta a hankali, ta ce, “Dadin baki ya na nufin fadar abin da ba haka yake ba, don kawai ya ji dadi.”

Ya yi murmushi, “Idan abin da ka furta ne, to hakan ya ke a gare ka. Ya rage wa wanda a ka fada masa ya yarda da hakan, ko ya ki. Yanzu misali, zan iya cewa Amatullah ta fi kowacce yarinya kyau a duniya, amma sai ki samu akwai yaran da suka tsere ta kyau a duniyar nan da dama. Sai dai gare ni, har cikin zuciya ta kyakyawa ce, don don kuwa ba na jin zan iya kallon wata yarinya, komai kyaunta na ji son ta kamar yadda na ke son Amatullah.

Ya kara sauke muryar sa, “Kamar yadda kyaun ki ke burge ni, ya rufe idanuna daga dukkan sauran matan duniya. Dabi’un ki suka sa ki yin fintinkau wa sauran mata gare ni. Cikin zuciya ta babu wacce na yi wa mazauni, in ba ke ba.” 2

Wani sabon shaukin so ya rika sauka a kanta tamkar yayyafi cikin watan Afirilu. Dadi kan dadi ya rika sauka cikin zuciyar ta, ya cike shi faal. Amma duk da haka, sai  da ta ce, “Dadin baki ne dai duk wannan.” 5

Ya kashe idanun sa tare da jefa ma ta kallo, “Ki na nufin ba na samun nasara?”

“Nasara? Nasarar me?” Ta matse zuciyar ta.

“Nasarar dadada mi ki zuciya, na karkata ta zuwa gare ni.” Ya matsa da fuskar sa dab da nata, “Has it worked so far?” 2

Ta hadiye yawu da kyar, zuciyar ta tamkar ta fashe don dadi. Ta sake shiga rudani. Ta sauke idanun ta, ta amsa da kyar, ta gyada masa kai kawai a kunyace.

Bai matsa ba, ya ci gaba da cewa, “Good. Then, ba za ki damu ba, idan anjima da yamma na dawo, zamu je Yankari?”

“Yankari? Ina jin sunan wajen a wurin kawaye na na makarantar mu a da. Ina ne wajen ya ke?”

“Gaba da nan wurin kadan. Babu nisa sosai.”

Ta dan tsuke fuska, “Kuma har za mu je mu dawo, dare ba zai yi ba? Tafiyar dare fa babu kyau.”

Ya saki siriryar dariya, “Actually, kwana bakwai na ke son mu je mu yi a can.” 3

Zuciyar ta ta buga. Kwana bakwai? Ta ce, “Idan mu ka tafi har tsawon haka, Ummah ba za ta yi kadaici ba?” A tunanin ta, bai dace su tafi su bar Ummah ita kadai ba ma.

Ya amsa, “Don me? Ga Larai a tare da ita. Ga ma Amatullah.”

“Amatullah kuma?” Ta zaro idanun ta.

Ya yi murmushi hade da gyada kan sa, “Eh, Amatullah.Wannan tafiyar daga ni ne, sai ke. Idan ya so bayan mun dawo, zan dauke ki mu je Dagauda, don ki gaida Dada.” 1

Ba ta san wane ne ya fi ruda ta ba. Tafiyar Yankari ita da shi ne, ko kuwa zuwa wajen Dadarta.

“Kin amince?” Muryar sa ta kara sauka kasa-kasa, tamkar ta na lasar fatar jinkin ta.

Ta ji sanyi ya kara ratsawa jikin nata. Ta sake gyada masa kai. Ta ji ya fidda wani irin sautin dariya mai shagaltar da mai sauraro. A yanzu ba gudu ba ja da baya.

Ta riga ta mika masa zuciyar ta da ruhin ta. Ba ta jin za ta rage shi da komai a halin yanzu. Idanun ta ke rokon ta haka, su na neman zama daya da ita, zuciya da ruhi.

Da wannan ya mike,ya na mai farin ciki ya bar ta nan ita ma ta na                  cikin kogin sa.Wani lokacin ma har gani take tamkar mafarki ta ke yi. A ce Yusuf ne ke son ta kamar yadda take son sa.

Abu kamar a mafarki, wanda a da ba ta ta tunanin yin kwatankwacin sa ba, balle har ya zama gaskiya. Hakika, a yau din nan za ta bude sabuwar shafi a rayuwar ta, tare da masoyin ta na asali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *