RAI BIYU CHAPTER 3

RAI BIYU




CHAPTER 3




Cikin tashin hankali na kwantar da Habiba da ta faɗo kaina, na nufi Inna da ke baya-baya tana nuna Baba da yatsa. Ina riƙata sai ta cafki hannayena jikinta na karkarwa. +

“Gawa suka kawo mana Nawwara, sun kasheshi, miya musu? Basu yarda zamu biya kuɗin ba? Ko dan sun maida mu talakawa? Saboda ba mu da galihu? Akan ƴan kunnen zinari da wayoyi suka ɗauki rai? Miyasa za su kawo mana shi? Saboda muma mu taru mu mutu ko? Sun maida mu mahaukata…” 1

Daga kalaman da take na fahimcin ƙoƙarin fita hayyacinta take. Riƙata na yi na zaunar, Sakina da Jamila da ke kuka na tura su ɗaki. Sai kuma na dawo tsakar gidan na yi tsaye ina kallon Baba, kana na kalli Habiba da ke sume, sai kuma Inna da ke zaune tana kallona, neman kukana na yi na rasa ashe akwai ranar da zaka buƙaci kukan ya ƙi zuwa maka, idona gaba ɗaya na ƙafe kamar hawaye be taɓa taruwa a ciki ba, yawun bakina na bushe kaina kuma yayi mugun nauyi kamar an ɗora min dala.

Ban damu da rashin mayafi da babu a jikina ba da kuma takalmi na fita da gudu zuwa babban gida. Gudu na ke amman gani nake kamar ƙara maida ni baya ake, tsakaninmu da su babu nisa amman yau sai ya koma min kamar gari da gari.

“Keeeeeeee”

Na ji an kirani sai dai hakan be sani tsayawa ba, har sai da na ji an harba bindigar mahalba. A firgice na juyo ina ɗaga hannuna sama yayinda su kuma suka tunkaroni suna nuna ni da bindigar, ɗaya daga cikinta da dalla min fitila mai tsananin haske da kashe ido.

“Nawwara miya fito da ke cikin daren nan?”

Jin muryar Baban su ƙawata Ruƙaiya yasa na gane cewar ƴan sitirine masu yawo da zarar dare yayi domin kama ɓarayi.

“Babanmu ne aka kawo shi ne zan je na faɗawa Baban Sulaiman, Babban gida zani”

Na faɗa cikin wani irin mugun haƙƙi da sarƙewar murya.

“Tah koma gida zanje na faɗa musu, Ibrahim rakata”

Ya ƙarasa yana kallon ɗaya daga cikin yaransa. Wanda aka kira da Ibrahim ɗin ya saka ni gaba shi ya rakani har ƙofar gida sannan ya koma. Ko da na shiga na samu Inna zaune gaban Baba ta zuba masa bokiti biyu na ruwa sai fifita take masa da ɗankwalinta, atunaninta ko ya yi doguwar suma ne wata ƙila idan ta yi masa haka zai farko. Ƙarasa na yi ƙusa da ita na ɗauki ragowar ruwan da ke bokitin na juyewa Habiba sai gata ta farka a firgice tana haƙi kamar na fitar rai. A nan Inna ta juyo ta kalleni fuskarta a taɓe tana shirin fasa kuka.

“Shi wannan ya mutu kenan?”

Wani irin uhu Habiba ta saka iya ƙarfinta tana shurin ƙafafunta, tana danƙar ƙasar tana watsarwa. Ni kuma na yi zaune a gurin bana kuka kuma bana iya bawa ɗayansu haƙuri daga ita har Inna da ke kuka, ƙaɗan-ƙaɗan juri yake ɗibata ina jin sautin kukansu kamar a cikin bachi. Kan kace kwabo maƙota sun cika gidanmu kamar ba dare ba, masu taya Inna kuka na yi wasu kuma na girgiza kai, shigowar su Baban Sulaiman ne yasa kowa yaja baya, Baba Dahiru ya shiga duba Baba, Baba Sulaiman kuma ya fasa kuka yana faɗin

“Sun kashe min ɗan’uwa ba bisa haƙƙi ba, Wallahi ɗan’uwana be yi sata ba, ya rantse min da Allah be ɗauka ba, sun ɗauki alhakin ɗan’uwana Allah ya isa Allah ya isa”

Yasa taɓar rigarsa ya share hawayensa sai kuma ya faɗin a gurin yana kuka. Har sai dai sauran ƴan’uwansa suka riƙashi, sai ya fisge kansa ya nufi ƙofa yana faɗin.

“Bayan sun karɓi dubu ashirin na beli sai kuma su kawo mana gawa, ba zata saɓuba”

Baba Dahiru yayi saurin riƙeshi.

“Sulaiman ina zaka je cikin dare nan?”

Komawa yayi ya zauna yana rawar ƙafa alamun masifa na tare da shi. Inna A’i ce ta zo ta riƙa Inna ta tasheta daga gaban Gawar Baba ta maidata can gurin ƙofar ɗaki ta zaunar da ita. A nan suka shiga tambayar Sakina yaushe suka kawo shi, kasancewar itace mai wayo saman da Jamila, cikin in’innar kuka ta zayyana musu abunda ta sani. Ni kan ina zaune gurin kamar kayan wanki komai ina ganinsa kamar mafarki, har kuma lokacin babu hawaye a idona balle alamun kukan. Habiba na gefena tana rusar kuka. Can ƙasa-ƙasa na riƙa jiyo muryar Baba Sulaiman yana faɗin.

“Sai da ya faɗa min suna ta dukansa akan sai ya karɓa laifinsa cewar yayi satar, shi kuma ya rantse min da Allah ba zai amsa ba sai dai su kashe shi, amman da naje na samu ƴan sanda nan na ce mu mun yarda yayi satar kuma za mu biya, daker suka yarda zasu ba da belinsa dubu ashiri, da yamman mu ka cika musu kuɗinsu sai kuma su kawo mana gawa? Shiyasa suka ƙi bamu shi, suka ce sai dai su kawo shi da kansu ashe sun san sun kashe shi, kuma suka karɓe kuɗin, Wallahi ba zamu bar wannan maganar ba, ba zamu barta ba”

Faɗa yake cikin kuka kamar ba mace ba, sai yana buga ƙafarsa yake da ƙasa. Magana da shi ta ƙarshe a police station ne ya dawo min a rai.

_“Mahaifinku be yi sata ba Nawwara, kuma be taɓa yi ba, ki gamsar da ƴan’uwanki da wannan”-

A take na ji idona ya cika da ƙwalla, kan kace kwabo sai ga hawaye suna saukowa daga idona kamar ba gobe, ban san lokacin da na kwara wani uban ihu ina kiran sunansa ba.

“Baba! Baba!! Baba!!!”

Mama ladi ta zo da gudu ta rufe min baki, sai na faɗa hannunta ina kallon fuskarta da ke min gizo kamar ta mahaifina…Riƙani ta yi ta tayar ta maida can kusa da Inna ta zaunar tana bani haƙuri da kalaman da za su sanyayamin zuciya.

Kuka muke ta yi ni da Habiba, yayinda Inna ta rafka uban tagumi tana kallon gawar Baba. Baba Dahiru ne yaja janena dake kan igiya ya rufa masa. Haka muka zauna har garin Allah ya waye babu wanda ya runtsa. Su Baba Dahiru ne suka yi alwala suka tafi masallaci yayinda mu muka yi namu sallah a gida, bayan na gama na ɗauko alƙur’ane ina karantawa, izuwa yanzu bana da buƙatar wani kuka bayan wanda na yi jiya ya haddasa min ciwon kai da kumburewar idanu, ina jin yadda maƙota na nesa da na kusa ke ta shigowa suna jajantama Inna, wasu na san gulma ce ta kawo su tun da gari ma be gama wayewa ba amman har labarin ya zaga unguwarmu da ma unguwanin da ke kusa da mu.

Bayan fitowa Masallci sauran ƴan’uwan Babana suka shigo maza da mata cikin har da Yakumbo. masu kuka na yi masu faɗa na yi, Baba Ayuba ne ya bada shawarar a ɗauki gawar Baba aje da ita police station a mayar musu, Baba Sulaiman kuma ya hana wai ba za a tagayar masa da gawar ɗan’uwa ba, idan aka yi haka ɗan’uwansa aka wulaƙanta. Daga ƙarshe suka yanke shawarar zuwa station ɗin ba tare da gawar Baba ba, a ɗakin mu aka saka shi sai aka rufe ɗakin duk muka kwaso muka dawo ɗakin Inna. Noor ya zo kusa da ni ya zauna, Jamila da Sakina kuma suka zauna gurin ƙofa suna ta aikin kuka kamar yadda Habiba ke yi. Ni kuma ɓa noce kaina ƙasa bana kuka kuma bana tunani kaina kamar fanko na ke jinsa, shigowar Jidda da Mahaifiyarta ce ta ɗaga hankalin kowa, saboda kuka da take kamar ita akayi ma mutuwar, sai gida ya ɗauki kuka muryarta muryar Habiba da Inna sai kuma Jamila da Sakina. Yakumbo ce ta katsa musu tsawa tana faɗa kan kuka da suke, musamman Inna da take ganin ita ya kamata ace ta rarrashe mu amman ita take kukan ma. 1

“Mamaci addu’a yake so ba kuka ba, bawan Allah nan fa yana cikin gidan nan amman kuna ta masa kuka, kuka ai ba zai dawo da shi ba, ba zai muku maganin komai ba, amman addu’a zata iya sanyaya muku zuciya kuma ta canja lamarinku, sannan shi kuma Allah ya karɓa yayi masa rahama.
Yanzu ke Hajara ke da ya kamata ace kin bawa yaran nan haƙuri, sai ki zauna kina kukan tare da su, Allah be yi wani dan wani ba, be yi Musa dan ku ba kuma be yi ku dan Musa ba, shi ya hallita abunda yasa masa rai yanzu kuma ya karɓi abunsa, gode masa ma ya kamata ku yi kuma ku yi haƙuri sai kuga Allah ya yi muku wata mafitar”

Ba laifi kalamanta sun yi tasiri gurin Inna da har tasa hannu ta share hawayenta tana ta kokuwar tsayar da kukanta, Habiba kan kunne uwar shegu ta yi sai abunda ya cigaba, kusa da ni Jidda ta dawo ta zauna ta kama hannuna ta riƙe sai hawaye take, ni kan kallonta kawai na ke ina jin kaina kamar babu komai a ciki.

Tun da suka ta fi basu dawo ba sai ƙarfe goma na safe har da ƴan mintuna, mutane da suka je tun hasken alfijir ba gama yayewa ba. Tare da tawagar ƴan sanda suka zo wanda hakan ya haddasa mana dandazo jama’a a ƙofar gida.

Dpo ne ya shiga da kansa ya duba gawar baba tare da wani ƙaramin ɗan sanda mai ɗaukar hoton jikin Baba, bayan ya gama dubawa ne ya dawo gurinmu, a bakin ƙofa ya tsaya yana ba mu haƙuri tare da faɗar za a ɗauki mataki da ya dace.

“Wacan ƴarsa ce?”

Ya tambaya ganin ni kaɗaice na kasa ɗago kai na kalleshi tun da ya soma maganar har ya gama. Inna A’i ta nuna Habiba da Jamila da kuma Sakina

“Eh da wannan da wacan da wacan, su kaɗai Allah ya bashi”

“Allah sarki ku yi haƙuri zamu ɗauki mataki, yanzu haka mun sa an kama ƴan sandan da suka yi wannan aika-aikar kuma za a gabatar da su a gaban kotu In’sha Allahu”

Ya ƙarasa yana ciro duba goma da uku ya miƙawa Jamila da ke kusa da shi, kana ya miƙe tsaye yana mana sallama.

“Mu za mu tafi Allah ya sanyaya zuciyarku”

Na yi zaton ya tafi hakan yasa na ɗago idona da ke cike da hawaye na kalli ƙofa, karaf idona sai cikin nasa, sauke na sa idon yayi ya wuce ƴan sanda na take masa baya. Na yi baƙin cikin haɗa ido da shi domin a yanzu ko mutuwa ban tsana kamar yadda na tsanesa ba, da saninsa aka yi ma mahaifina komai saboda ƴar’uwarsa har suka kashe shi. Bayan fitarsa Baba Sulaiman ya shigo yana mana bayanin yadda abun ya wakana lokacin da suka isa station ɗin.

STORY CONTINUES BELOW


“Ko da muka je dpo baya nan, muka faɗawa ƴan sanda da ke nan, sai suka ce wai matarsa ce ta danka ta zo ta tafi da shi da ɗansa, Ayuba ya ce ai ba shi da ɗa namiji ma, kuma jiya mun zo nan kuka hana mana shi, sai suka ce bayan tafiyar mu matar da ɗansa suka zo suka tafi da shi, a gurin aka riƙa rigima wai su zayi ma ƙazafi, ɗayan su har da barazanar a barshi ya harbe mu, da suka ga abun na mu bana wasa ba ne yasa suka kira dpo, yana zuwa ya rufe su da faɗa, yasa aka tuɓe kayan ƴan sanda da suka yi aikin dare aka shigar da su cell, ya bamu dubu ashirin ɗin sai kuma ya biyo mu nan yana ƙara ba mu haƙuri”

Baba Dahiru yaja tsaki.

“Allah ya waddaran ƙasar nan, ai daga gani da saninsa aka yi komai, kuma babu matakin da zasu ɗauka, Allah dai ya isar ma ɗan’uwanmu kawai”

Ni kaina jikina be bani za a ɗauki wani matakin ba, saboda na san mahaifina ba kowa ba ne a cikin unguwarmu balle kuma a gari. Maƙocin mu ne yayi ma Baba wanka saboda Inna ta kasa duk da kasancewar ta iya raunin zuciya be barta ta iya masa wanka ba, ban tabbatar da mai rai ba a bakin komai ya ke ba sai da aka ɗauko karaga aka saka gawar Baba aka fita da shi waje dan yi masa Sallah.

Allahu akbar shine abunda na iya faɗa a zuciyata, na kwantar da kaina jikin Jidda hawaye na bin fuskata. Baba ya samu mutane sosai daman mutumen mutane ne, kuma wannan abun da ya faru ya ƙarawa mutane ƙaunarsa, har wasu na baranar idan ba a ɗauki mataki ba zasu ƙona station ɗin.

Bayan an kai shi makocinsa suka dawo, mazan unguwa na ta shigowa suna mana gaisuwa, ciki har da Bilal da Babansa.
Mutanen da suke zuwa mana gaisuwa kamar turo su ake, maza da mata ta ko’ina gaisuwa suke zuwa mana suna yi ma Baba addu’ah, maƙota kuma na ta kawo mana abinci, sai kuma gidan Baban gida da suka haɗa kuɗi duka siyo mana buhun shimkafa. Can da yamma Baba Sulaiman ya shigo yana tambayar mu ko ana binsa bashi.

“Sai dai a tambaya guraren da yake zama amman Malam be cika cin bashi ba, shi dai bar shi da zuwa gidan ciyaman neman kuɗi”

“Toh zamu bincika, Alhaji Sani ma ya zo nan yace yana muku gaisuwa”

“Toh muna amsawa, Allah ya bada lada”

Baba Sulaiman ne yayi ta ɗawainiya da mu tun da Baba ya rasu har ranar da aka yi addu’ah ukunsa. A daren ranar sai gidan ya zame nama wayan kamar Baba be taɓa wanzuwa a cikin gidan ba. Ina daga cikin ɗaki na hango Habiba ta ɗauki tabarma ta je ta shimfiɗa gurin da Baba yake zama ta kwanta. Tausayinta ne ya kama ni na unƙura na tashi naje kusa da ita na zauna, sai ta ɗago kai ta kalleni.

“Nawwara”

“Na’am”

Na amsa mata ina danne tausayinta da ke raina.

“Yanzu ya zan yi Baba ya yafe min? Na yi tunanin Baba zai rayu na roƙi gafararsa wata rana”

Hannu na kai na ɗaga kanta na ɗora saman cinyata yayinda fuskarta ke fuskantar ƙofar ɗakin Inna, cikin ƙarfin hali da dauriya na soma mata magana.

“Idan har Allah ya yafe miki, to Baba ma ya yafe miki, amman Habiba kin ga abunda kika aikata be amfana miki komai ba, tun da kuɗin ma be amfana komai ba, da kin yi haƙuri da baki siyar da mutuncinki ba”

“Wallahi Nawwara ban ɗauka Baba zai mutu ba, a tunani zai rayu ne, kuma ni ina ganin kamar bamu da wata mafita sai wannan”

“Da sata kika je kika yi Habiba ko kika yi bara, zai fi wannan abun da kika aikata”

Shiru ta yi tana shesshekar kuka, yayinda ni nake hawaye. Can ƙasa-ƙasa ta soma magana.

“Masu kuɗi suna da kuɗi Nawwara amman basa taimako, babu ruwansu da matsalar mu, idan mun ci babu ruwansu idan ba mu ci ba sai dai mu mutu”

Ajiyar zuciya na sauke cike da gasgata zancen Habiba, haƙiƙa masu abu na da shi amman babu ruwansu da mu, ko ɗan abincin nan a zuba a abawa maƙota basa yi.

Tashi ta yi zaune tana kallona, cikin kuka ta soma magana.

“Nawwara sai da na je gidan Hajiya Murja na faɗa mata halin da muke ciki, har ƙarya na yi mata Inna na ce tace a ara mata kuɗi, ta ce min bata da kuɗi amman dai za ta yi ma mijinta magana. Da na fito sai na haɗu da ɗanta Mustapha a harabar gidan, shi ya kirani ya tambayeni miya kawo ni gidan, na faɗa masa sai ya ce zai bani kuɗin amman na masa alƙawarin duk abunda ya ce zan masa, na ce na yi, muka fita daga gidan gaba ɗaya, ya fiddo kuɗi da yawa a aljihunsa ya ƙirga dubu ashirin, har zai ba ni sai kuma ya fasa, ya ce sai idan na aminta na na bashi abunda ya ke so yanzu, na ce mi yake so, ya ce kawai taɓa jikina zai yi sai ya bani kuɗi shi ba iskanci zai yi da ni ba, har da min ratsuwa”

Ta yi shiru. Can kuma sai ta cigaba.

“Na ƙi yarda na nufo haɓyar gida, har na kawo sai kuma na ga ba mu da wata mafita sai wannan, dole tasa na koma, ko da na koma ya fita, sai nasa mai gadinsa ya kirashi a waya yace ina nemansa, sai yace na same shi gidansu killers, haka na je gidan na same shi shi kaɗai a gidan, sai… Sai… Sai. Ya ya.. Riƙani Wallahi Nawwara cewa kawai yayi zai taɓa jikina ya ba ni kuɗi, amman shi ne ya kira har da abokinsa suka.. Suka.. Suka yi.. Yi iskaci da ni…” 4

Ba shiri na buɗe baki ina kallonta hawaye na bin fuskata.Miyasa ba ki masa ihu ba?” +

“Mi zai sa na yi masa bayan ni na kaina? Idan na masa ihu ba zai ba ni kuɗin ba kuma zai iya dukana ma”

Kwantar da ita na yi jikina, ina kuka kamar yadda ita na take. Har dare ya bara muna zaune ni da ita a gurin muna aikin kuka.
Wannan abu shi ya zame min jiki, a duka lokacin da na keɓe ni kaɗai na kan yi kukana sosai, saboda tausayin rayuwar Inna da Sakina da Jamila, sai kuma Habiba da kullum na ke zullumin idan ciki be shige ta ba.

Yau ce ranar da Baba ya cika sati ɗayda rasuwa, har kuma tsawon lokacin ba mu sake jin wani abu daga gurin ƴan sandan ba, da yamma Baba Sulaiman ya samu Inna a gida yana faɗa mata gobe zasu je su ji halin da ake ciki, ita kan uffan bata iya ce musu ba, Bilal ya sallama a ƙofar gidan mu yana nemana. Cikin rashin kuzari na miƙe tsaye kasancewar Hijabin da na yi sallah da shi yana jikina ne.

Jikine da ƙofa na same shi yana rumgume da hannayensa, fuskarsa ba yabo ba fallasa. Sallama na fara masa kamin na miƙa masa gaisuwa.

“Lafiya Ƙalau Nawancy ya haƙuri?”

Ya tambaya ba tare da ya kalleni ba, har lokacin idonsa na kallon wasu gidajen da ke fuskarta na mu.

“Mun gode Allah”

“Nawancy kawai ina son na ɗan miki wasu tunatarwa ne akan abunda ya faru-”

Na tsaleshi tun kamin ma ya fara.

“Dan Allah Bilal ka karka so ma idan ba kuka na kake son ya dawo sabo ba”

Ya juyo ya kalleni ido cikin ido.

“Na daina Nawancy”

Yaja wani dogon numfashi ya sauke yayinda ni kuma na ke tare ƙwalla da suka cika min ido.

“Am sorry ban zo nan dan saka ki kuka ba, daman na zo ne na faɗa miki aiki da nace miki za a ɗauka a gurin aikinmu an fara”

“Yaushe?”

“Tun lokacin da abubuwan nan suka soma faruwa, kawai ban miki magana ba ne saboda ina ganin kamar be dace ba, gobe ma za a rufe, daman kwana goma ya bada”

“Da gaske? Amman suna ɗauka masu ssce?”

“Yeah sai dai aikinsu goge-goge da kuma mopping sai aikin kai documents ko ɗaukowa, maza kuma shara da buɗe ƙofa”

“Indai zasu ɗauke ni zan iya Bilal, ina ake applying?”

“A can gurin mu zakije ki bada takardun idan sun duba sun ga ka cancanta zasu nemaka ta waya”

“Ƙarfe nawa ake zuwa?”

“Goma”

“Allah ya kaimu zan zo”

Ya ɗaga min, sai ya miƙa min nokia hannunsa.

“Wannan ki saka layinki saboda kira suke ba zuwa ba, ara miki na yi ba kyauta ba”

Na san ya ce haka ne dan kawai na karɓa, duk da nima bana da wata mafitar da da wuce na karɓa ɗin, kasancewar babu waya a hannuna ga shi kuma number Jidda da nake badawa wani lokacin yanzu ta siyar.

“Aro”

Na faɗa yayinda na ke miƙa hannuna na karɓa. Murmushi ya yi

“Yes aro, da kin fara aiki ki siya min sabuwa,ko da yake albashinku mai yawa ba ne”

“Nawa ne?”

“12k”

“Ba laifi Bilal indai zasu biya ƙarshen wata”

“On 25 suke biya, baki da matsala da wannan”

“Allah dai yasa na samu”

“Zaki samu inshallah”

“Na gode”

Na faɗa cike da ƙosawa da kuma son ya tafi, ba kasafai nake son ana ganin ina tsayuwa da shi ba, saboda ƴan sa idon unguwa. Shi kansa ya lura da hakan sai yayi min sallama ya tafi ni kuma na dawo cikin gida.

Bayan Sallah isha’i nake labarwatawa Inna maganar aikin har ma na nuna mata wayar da Bilal ya bani.

“Allah ya bada sa’a”

Kawai tace min ta jingina da gini tana jan carbi, wanda hakan san be min daɗi ba, Habiba ce kawai ta zo ta zauna kusa da ni tana tambayar yadda aikin yake. A cikin dare na ɗauko tsohon layina na saka a wayar da Bilal ya ba ni.

Washe gari ta kama ranar alhamis, ranar na tashi da azumi, daman duk litanin da alhasmis na kan yi azumi wani lokaci, musamman yanzu da ya zama ba komai na ke ci ba idana ban yi azuminba zan wuni da yunwa ne kawai.

Misalin bakwai na safe na ɗumama su Jamila tuwon shinkafar da na yi musu jiya miyar kuka, Inna kuma na dama mata kunu ita da Habiba saboda shi kaɗai suke iya sha ko da rana da dare kuma ruwan tea. Bayaɓ na gama na je yani wanka na shirya ciki wata farar atamfa na saka baƙin Hijabi sai kuma tsofi takalmi waɗanda suka kasance baƙaƙe sannan na sake dawowa ɗakin Inna na same ta har lokacin tana shan kunu.
Jaƙar da muke ajiye kayan karatu na buɗe na ɗauki takarduna na makaranta na buɗe ina duba tare da tunatar da Habiba maganar zuwa makaranta.

“Ya kamata ace kin je makaranta gobe ko kuma monday nan mai zuwa, yau kusan kwana nawa baki je ba, kuma jarabawa kuke fa, gashi rashin zuwanki ya haddasa har su Sakina sun daina zuwa”

Ta turo baki.

“Ni ba zan sake zuwa ba, karanta mo zai tsinana min, ko na yi karatu ba zan wuce babbar makaranta ba, kema da kike da ssce min kika amfana da shi”

Murmushi na yi, nasan tana tunanin babu wanda zai iya ɗaukar ɗawainiyarta ne da har zata yi babbar makarantar gaba da secondry, tun da karatun ya zama sai da kuɗi.

“Na miki alƙawari zan ɗauki nauyin karatun ki, ke dai ki dage ki cigaba da wannan ki kammala sai kije babbar makaranta”

“Ta yaya?”

Ta tambaya tana hararata irin bata yarda ɗin nan ba.

“Wannan aikin idan na samu zan riƙa aje wani abu daga albashina saboda ke Habiba”

“To Hajiya bari har ki samu”

Ta faɗa tana ɗaukar Noor ta ɗora saman ƙafafunta. Ni kuma na yi murmushi na kalli Inna na ce

“Ni zan ta fi Inna”

Fillo ta ɗaga ta ɗauko ɗari biyu ta miƙa min.

“Ki hau Napep, karki manta da nasihar da mahaifinki yake miki akan mutuncinki Nawwara”

“In’sha Allahu”

Na tashi cikin jiki ba ƙwari na fita. Yau kan sai da na yi nisa sosai sannan na samu Napep, kai tsaye na kwatanta masa inda zai kaini wato koko road.
Nesa da Company ya sauke ni na bashi kuɗinsa, sannan na aikawa Bilal please call me kasancewar babu ko na flashing a wayar, sai ga shi ya kirani cikin ƴan mituna, na sanar masa ina kusa da gurin.

“Ki ƙaraso mana gani nan fitowa”

Bayan na amsa masa da okay na doshi company gaba sai dukan uku-uku yake, wata ƙila ko dan ban taɓa zuwa babban kamfani kamar wannan ba oho..

*ONE-ON-ONE LIMITLESS*
_One of the Largest Metal Companies in the world_

A hankali na karanta, ina ƙara faɗaɗa ido ga kallon ƙofar gate ɗin company ma da ta kasancewa ƙatuwa.

‘Anya za su ɗauke ni aiki kuwa’

Na tambayi kaina ina kallon securities da ke bakin gate ɗin sanye da uniform kamar na ƴan police sai dai na su farar rigace sai baƙin wando. A ƴar ƙaramar ƙofar da ke gefen gate ɗin na hango Bilal ya fito sai sauri yake ya doso inda na ke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *