KUDIRI
CHAPTER 8
Rayuwar duniya juyi-juyi, wai kwado ya fada ruwan zafi. A daren jiya idan wani y ace da shi zai shiga wannan hali a yanzu zai musanta. Ko sau daya ma bai kawo hakan ba a rayuwar sa ta aure. +
Hakika wannan ziyara da Mariya ta kai ma sa it ace ta haddasa ma sa fitinar da ya ke cikin ta. Ya shiga jin haushin kan sa.
Me ya sa ma bai fafare ta ba sannan ya kulle masaukin na sa bayan hakan? Me yasa bai gaya ma ta kalaman da su ka dace da it aba, wadanda za su hana ta mancewa da shi a tsawon rayuwar ta?
Ya nisa, a yayin da yake ta yawo a harabar gidan sa. Cikin dakin sa ya yi ma sa zafi, gami da kuma halin da Asiya ke ciki a lokacin. Ya san kuka ta ke yi amma ya fi ta bacin rai.
Asiya ba ta yarda da shi ba, hakan ke kona ma sa rai. Ko kafin auren sa ma bai yi abin da kalamanta ke zargin ya aikata ba. shi da yak e ganin ko da a ce a gaban ta ya aikata wani laifi za ta kawar da kanta, sannan ta ki amincewa da laifin?
Ya sake nisawa. Ba laifin ta bane, ban a Mariya b ace. Laifin sa ne, da ya mayar da rauywar sa abar sadaukarwa gare su, hakan y aba su damar juya shi son ran su. Daya ta Haifa ta gudu, dayar kuma ta aure shi amma ga yadda take zargin sa. 2
Amma zai ba su mamaki dukan su. Zai gwada mu su cewa shi ba kanwar lasa ba ne. Musamman ma Mariya, wadda ke neman raba ma sa aure sannan ta bata ma sa suna tare da lika ma sa babban tabo.
Ya tuno da abin da Asiya ta fitar daga jakar sa. Bireziya ce da kamfai a dunkule hade da kwalin kwaroron roba. Wannan ba bu ko shakka zai ruruta wutar zargi a tsakanin su, kuma babu mai haddasa hakan sai shaidaniya Mariya.
Shi fa da kan say a gama hada kayan sa. Zuwa kawai ya yi ya fitar da su a lokacin tafiyar ta su. Kuma a wurin da ya ajiye jakankunan a nan ya tarar da su.
Karo na fiye da kirgen say a yi nadamar barin Mariya ita kadai a cikin masaukin sa. Bai zaton za ta taba aikata hakan ba, musamman ga ‘yar uwar ta. Ko tausayin halin da take ciki ma ba ta ji ba.
Karar motar da ta tsaya a gaban get din sa ta ja hankalin sa. A sanin motar, ya san ta Hadi ce. Ya duba agogon hannun sa, karfe hudu da rabi na asuba.
Jikin sa ya ba shi, cewa ba bu lafiya. Don duk da cewa Hadi ya sake da shi ainun, ba zai yiwu ya zo gidan sa a wannan lokacin ba, alhalin ma a daren nan a ka kawo ma sa sabuwar amarya.
Bayan ya latsa ham, maigadi ya bude da sauri. Zama da likita, wanda ke fita a lokutan da ya yi bamban da na sauran mutane sun sa shi sabo da budewa da rufe kofar a kowane lokaci.
Hadi ya shigar da motar sa, amma bai fita ba har sai da Yusuf ya shigar da karnukan gidan sa cikin dakin su. Su kuwa sai haushi suke yi kamar za su daga motar ta sa.
“Me kake yi a nan?” Hadi ya nufo wurin da Yusuf din yake, bayan ya fito daga motar ta sa.
Ba tambayar da ya yi tsammani ba ne daga wajen Hadi. Don kuwa a duk ziyarar Hadi gidan sai ya yi ma sa mitar karnukan sa. Amma a ganin sa, kasancewar sa a harabar gidan sa a wannan lokaci ne zai sa Hadi yi ma sa wannan tambayar.
“Ina fata dai komai lafiya. Don ban yi tsammanin ka a yanzu ba.”
Bai tuna ko sun yi maganar zuwa aiki cikin dare ba, ko ma yin wa ta tafiya. Balle ma tun da ya zama CMD ba ya cika shiga hidimar tiyata sosai don ayyuka sun ma sa yawa.
“Na kira wayoyin ka kamar sau talatin ko ma fiye, amma ba ka dauka ba. Seriously, ba ka kai tsada har hakan ba.”
Yusuf ya kalle shi sosai, a yayin da ya ke la’akari da cewar ya bar wayar sa guda cikin dakin sa, kusa da gadon sa, wurin da jakar sa ke zaune. Daya wayar kuma ta na wata duniyar daban, a hannun Mariya.
STORY CONTINUES BELOW
“Waya ta ta na daki. Kai me ka ke yi a nan? Ba dai zuwa ka yi musamman don ka fada min ka yi min missed calls ba.”
Ya san Hadi aminin sa ne, amma ba zai so ya san abin da ya ke ciki a cikin gidan sa ba. Balle ma cikin sa’a, Ummah ba ta dawo daga Dagauda ba sai washegari.
Hadi ya kalle shi sama zuwa kasa, sannan ya shige falon gidan, kan sa tsaye. Yusuf ya bi bayan sa. Ba wai shigar Hadin ba ne, yanayin fuskar sa ce ya sa Yusuf shiga damuwa.
Bacin rai ne karara, wanda saboda yanayin saukin kan Hadi, bai cika nunawa ba sai idan da kwakkwarar dalili. Hakan ya daga ma sa hankali fiye da wanda ya ke ciki.
“Hadi tell me, wai me ke faruwa ne?”
Hadi ya dan kalle shi, “Da ta fada min, zuciya ta ba ta amince ba. na yi ta fatan Allah Ya sa kuskure a ka samu, ba kai din ba ne.”
Yusuf ya ji gaban sa ya buga, zuciyar sa ta nutse cikin karin bacin rai. Wai me? Wato ashe Asiya ba za ta iya rufe sirri ya tsaya tsakanin su biyu ba, sai ta tona wa wani? Ya san Hadi aminin sa ne.
Amma duk da haka, akwai sirrin da ke rufuwa tsakanin ma’aurata. Musammam wannan sigar, ta zargin cin amana.
“Me ta ce da kai?”
“Me za ta fada da wuce wanda na gani da ido na?” Hadi ya tuhume shi, tare da nade hannayen sa saman kirjin sa. “Don me za ka bar ta ta sha wahala ita kadai?”
Yanzu kam kan sa kullewa ya yi, “Wahala? Wahalar me?”
Hadi bai ba da amsa kai tsaye ba. ya nufi kofar dakin Asiya ya shiga bugawa. Ya nemi ta bude kofar don ya samo Yusuf din. Ya dan kalle shi, sannan amsar ta fito, “She’s in pain. Ina tsammanin ta na labour ne.
Lokacin da ta yi wa Muhibbat waya, ta ce min b aka cikin dakin, ba ta kuma san wurin da ka ke ba. Shi ya sa na nemi layukan ka ko Allah zai san a same ka. Shirun da na ji ne ya sa ni zuwa da kaina, don ta na bukatar taimako, ka fi kowa sani.”
Matar sa ta na nakuda? Duk wata kafa ta jikin Yusuf sai da ta bude. Ya yi watsi da komai, zai je ga matar sa, wacce ke bukatar sa a lokacin. “Me ya sa ba ka fada min ba tuntuni?” 2
Hankalin sa ya kara tashi. Bai san halin da ta ke ciki ba. Wane irin ciwo da zafi ta ke ciki, sannan ita kadai. Wayyo!! Ya saka hannun sa ya taba kofar dakin, a kulle ya ke ga-gam. Ya koma ta dakin say a shiga dakin ta ta wancan kofar da suke amfani da ita.
Irin yanayin da ya gan ta ya kara saka shi kaduwa da razana. Ta na durkushe ne jikin gadon ta, gurnanin zafi ne kadai sautin da ke fita daga bakin ta.
Ya matsa dab da ita, ya na kiran sunan ta, amma ba ta ko daga kai ta kalle shi ba. jikin ta ya dauki zafi, zufa ya jika ta sharkaf!
Tsananin tausayi da kauna suka addabi zuciyar sa. Hankalin say a kara ta shi. Asiya ta samu kan ta a tsakanin rayuwa ko mutuwa. Ya na son ta haifo mu su babyn su, amma kuma tausayin da take bas hi ya na neman tsaga zuciyar sa.
“Ki na iya ji na my dear?” 4
Ta gyada ma sa kai alamar eh. Sannan ya ci gaba da cewa, “Ina gay a kamata mu je asibiti…”
Komai ya na iya faruwa. Haihuwar farko ce, don haka akwai hatsarin gaske. Ta na bukatar kulawa ta gaggawa. Har ya fara yunkurin daga ta ya ji ta damki hannun sa caraf, da karfin gaske. Sai mirgina kan ta take yi tare da nishi. Ta shiga salati, hawaye na zubowa ta gefen idanun ta.
Anya, zai iya kuwa? Shi ba likitan mata ba ne, amma ya na kishin wani namiji ya kalli matar sa wajen haihuwar ta. Sai dai zuciyar sa tana neman tsagewa gida biyu. Ya na ganin ba zai iya ba. Abu ne mai sauki mutum ya tsaga wasu. Amma wadan da ya ke so kuma daban ne.
STORY CONTINUES BELOW
“Me ke faruwa ne Dan auta?”
Muryar Hadi ya ji ta kwararo ta jikin kofar dakin. Wata zuciyar ta raya ma sa kan ya bude ma sa kofar don kuwa shi ne gynaecologist, wato kwararren likitan mata. Amma yadda ta rike shi ya kasa yin hakan. Sannan jikin ta rawa ya ke yi kamar wacce ke jin sanyi.
Karshe dai bayan ya lura ciwon na ta ya dan lafa, sai ya bude kofar wa Hadi, ya nemi ya taya shi gyara bandakin ta. Ya ba shi tawul manyan manya guda biyar ya shimfida su cikin bahon wanka. Shi kuwa ya tsaya a jikin ta, ya na rike da ita.
“Ka tabbata ba za mu je asibiti ba?” Hadi ya nuna tababar sa game da shirin Yusuf na karbar haihuwar matar sa a gida. 2
“Ciwon na zuwa a kai a kai. Ina ga ta yi kusa. Ba na kuma son na saka ta a mota, kafin mu isa komai ya na iya faruwa.”
Kowane murdar ciwon ta har cikin kahon zuciyar sa yake ji. Ya sha jin Hadi ya je karbar haihuwar da ta samu matsala. Ya kan mata suna juyi kan gadon nakudar haihuwa, amma ganin wacce ya ke so cikin wannan hali ya sosa zuciyar sa matuka. Da a ce a na karbar ciwon, da ya yi. A dole ya rika yi ma ta addu’a, ba bu abin da zai yi fiye da hakan.
Tsoro daya ya kama shi. Kar fa dalilin halin da ta shiga kafin nakudar ta ya yi sanadin jinin jikin ta yah aura fiye da kima. Hadi ya koma motar say a debo mu su safunan hannu da wani akwati mai dauke da kayan aikin haihuwa na gaggawa.
“Muna bukatar ruwan zafi, sannan zan ajiye allurer tsayar da jini a gefe na.”
Ya na magana ne a yayin da yake tsaye ta kan ta. Shi kuma mijin ta shi ya ke ta kasa. Tare suke jin ciwon, shi da ita. Ya rika karfafa ma ta gwiwa ta hanyar saka ta ta rika salatin Annabi da hailala, sannan kuma ta rika nishin sosai. Hadi ya fice neman Larai, don ta saka mu su ruwan zafi.
Asiya ta ba da nishin farko, na biyu, sannan na ukun ta tattare duka karfin ta ta turo sambalelen yaro, wanda ya sauka a hannun mahaifin sa. Ko da fitar sa, ya cara kuka lafiyayye. Ba tare da wahala ba mabiya ta fado.
Idanun Yusuf suka cika da kwalla, wanda ya gagara tsayar wa. Allahu Akbar! Komai na duniya ba ya da daraja ko kima face dadin rike dan sa a hannun sa. Zuciyar sa bulbular dadi ta rika yi. 4
Ya yanke cibi da almakashin da ya samu cikin kayan aikin da Hadi ya bashi a daidai lokacin da Larai da Hadin su ka koma bandakin cikin murna da zumudi. Ya kalli Asiya, wadda ke kwance cikin mutuwar jiki, ta na kallon su shi da jaririn su.
Ya dan daga ma ta shi, ya ce, “Duba ki gani Asiya, kyautar da Allah Ya ba mu, wanda ba bu wanda ya isa ya yi ma na sai Shi.”
Idanun ta suka wanzar da sabbin hawaye. Sun yi hulu-hulu don nuna irin kuka da wahalar da ta sha. Amma bai hana shi ganin tsabar so da kauna cikin su ba. Ya sha tunanin yadda komai zai kasance a lokacin haihuwar ta, kuma ya faru ne sak daidai.
“Masha Allah, amarya, na taya ki murna. Allah Ya raya cikin musulunci bisa Imani ingantacce.”
Ta dan yi murmushi da kyar, ta ce, “Na gode kwarai da gaske, da ka zo cikin gaggawa. Allah Ya saka da alherin Sa,Ya kuma b aka naka rabon mai albarka nan ba da jimawa ba.”
“Amin!!” Ya furta da babbar murya.
“Shh, ka na razana baby da muryar ka.”
Hadi ya harare shi, “Ba laifin ka ba ne. With time, dan boko ya ga mota. Ni ma nawa lokacin ya na zuwa da izinin Allah.”
“In sha Allah.” Yusuf ya furta cikin murmushi.
Daga nan Larai ta shiga kimtsa yaro, ita kuma Asiya mijin ta ya tsaya duba ta ko ta samu kari ko kuma babu.
Ganin cewa babu, sai ya mata allura. Hadi ya dage kan a bari ta huta kafin ta yi wanka. Ya na yunkurin mikewa don ya fitar da ita daga bahon da take kwance ne ya ji ta sake damkar hannun sa, fuskar ta a murtuke, ta shiga sabon nishi. Nan take jiki na sabuwar rawa ya sake taba kan cikin ta. Ilay! Ya ji da tauri, alamar akwai wani guda a cikin ta ke nan. 8
A tsawon goyon cikin Asiya, sau daya ta je a ka yi hoton cikin ta don a tabbatar da lafiyar abin da ke ciki, amma sakamako ya nuna bai nuna ‘yan biyu ba ne. Cikin ikon Allah kuma ba ta samu matsalolin daukar cikin fiye da wanda a ke tsammanin za ta samu ba. A kan samu hakan dama. Wani cikin tagwayen bay a nuna kan sa gaba daya. 1
Don haka ganin jaririn su na biyu ya wanzar ma sa da farin ciki fiye da tunanin sa. Bayan kamar sa’a guda, y agama kimtsa matar sa, wacce ta yi wanka ta samu kwanciya. Ya umurci Larai da ta dafa mata abin da zata ci, da na sha don ta samu karfin jiki, sannan ruwan nono ya fara gudana.
Kafin wayewar gari, ya sanar wa Umma, wadda ta sanar wa Dada. Ko daga ta wayar ne ma yana iya jin farin cikin su, sun kidime wajen murna da hamdala ga Allah. Shi ma godiyar ya ke ta yi, kusan kowane bayan dakika biyar.
Ya tsaya a gefen gadon su ya kura musu idanu. Gari ya waye tangaran a lokacin. Shi da Hadi sun duba lafiyar yaran sun samu ba matsala. Zuwa washe gari za a yi mu su rigakafin BCG.
Daya daga cikin su ya motsa. Yusuf ya kai hannu ya dan shafa shi, hawaye cike da idanun sa. Ma su magana sun ce dare daya Allah kan yi bature. A daren jiya Ya juya ma sa al’amuran sa gaba daya, bayan ya yanke kauna ga samun sukuni na tsawon lokaci.
Ya yi murmushi, dadi ya mamaye zuciyar sa. Ya gagara kawar da idanun sa a kan su. Tashi daya ya zama baban tagwaye. Ba zai iya kwatanta yadda ya ke ji ba a lokacin.
Oh! Allah Mai kyauta da kari. Allah Ya cika mu su burin su, shi da Ummarsa. Fata ya ke yi, kan cewa wannan ya zama silar shiryawar sa da matar sa.
* * *
Asiya ta na kwance kan gadon ta a dakin ta, komai yi ma ta shi a ke yi. Sai abin da ta ke so za ta ci, ba a bari ta motsa komai in ban da shayarwa.
Nan ma musamman a ka kai ma ta Nas daga asibiti, don kula da su. Sannan ga Umma nan, ga Larai, Sara…kowannen su da dawainiyar da yake yi a kan su duka.
Ta kalli wajen da suke kwance, farin ciki ya cike zuciyar ta ganin cewar burin samun tagwaye ga mijin ta ya samu cika. 1
Ta nisa, a lokacin da zuciyar ta ta koma tunanin sa. A kwanaki biyu bayan haihuwar ta ba saka shi kan idon ta na awa biyu ba. ya na yawan fita aiki, amma da zarar ya dawo gida, to sai ya shiga ya ga lafiyar ta da yara, bayan ya je wajen Umma.
Akasarin ziyarar sa ya kan yi ne da dare. Ko da sassafe. Ita kuwa ba ta yarda su hada idanu, sai ta kwanta kamar barci ta ke yi har sai ya fice daga dakin. Ba ta san dalili ba, amma ba ta son fuskantar shi. A kalla ba a lokacin ba.
Ta gagara mancewa da abin da ta gani cikin jakar sa, da kuma manufar hakan. Duk da cewa bai sake dago maganar ba, hasali ma ita din ma sai idan ‘yan zuwa barka sun waste ne take tuna komai, bai sa ta kara sakewa da shi ba. Ba ta san abin da ya rike cikin ran sa ba. Ba ta jin a shirye ta ke don fuskantar hakan.
Jariri daya ya motsa, ta dan jijjiga shi ya koma barci. Ta saka hannu ta dauke shi ta na kallon sa kirr. A wannan lokaci ne kanta ya shiga halin rudani game da al’amuran ta.
Tilas ne a kan ta, kan cewa komai za ta aiwatar daga lokacin ya kasance ta saka tagwayen ta a farko kafin komai. Ba za ta yi kuskuren da Maree ta yi da Amatullah ba.
Sannan ba za ta yarda yaranta su tashi ba tare da mahaifi ba, kamar ita. Don yadda suka taso da Baban su, shi da babun su duk daya ne. 2
Ta nisa. Hakan na nufin dole ta zage dates, ta kwato mijin ta, in ya so taga abin da rayuwa ta tanadar mu su.
Sallama ta ji na Yusuf, cikin sassanyar murya, fuskar sa dauke da fara’a. Bayan ta amsa sallamar ne ya kalle ta, idanun sa cike da so da kauna, “Yau dai na yi sa’ar samun ki ido biyu.” Jin ta yi shiru, ya dora da, “Shawara kike yi da dan naki?” 2
Abin ya dan ba ta dariya, amma sai ba ta yi ba. ya karasa wajen da ta ke zaune, wato bakin gado, ya zauna dab da su. Shigar da ya yi, da kuma kwarjinin sa suka zuke numfashin ta tashi guda. Yaudarar kan ta take yi, idan ta ce baya shafar ta kamar yadda yayi a baya, kafin ‘yar rigimar su.
“Ya ya ku ka yini?” ya ci gaba da tambayar ta.
Sama-sama ta amsa ma sa, “Lafiya.” Kan ta a sunkuye.
Ji ta yi ya zuki numfashi ya fitar sosai ta bakin sa, sannan ya yi abin da ba ta taba tunanin zai yi ba…..Ya durkusa a kan gwiwowin sa duka biyu a gaban ta, idanun sa da rauni, muryar sa dauke da nadama. Nan take zuciyar ta ta shiga zogi da tsananin rudani.
“Asiya, na rantse da Mahallicin mu, babu abin da ya taba shiga tsakanina da Mariya ‘yar uwar ki. Wallahi, ban taba kallon ta ta wannan sigar ba. Ban taba cin amanar auren mu ba. Amma duk da haka, na amince, na karbi hukuncin da ki ka yi min, wanda ya kasance mai tsauri matuka. Na yi hakan ne, don ki samu sanyi cikin ranki, tare fatan cewa idan har hakan ya samu, za ki huce har ma ki saurare ni.” 6
Ya ja tafin hannun ta ya rungume cikin na sa, ya kara sauke muryar sa, “Asiya, ki tausaya wa rayuwa ta, kar ki jefa ni cikin ukuba bayan kin dandana min dadi tun farko. 2
Tun faruwar wannan abu, gidan nan ya zama tamkar daji a gare ni; babu haske, babu tsaro. Kin kaurace wa yi min murmushi balle dariya. Na bar ganin kauna cikin kwayar idanun ki. Don haka na ke neman gafarar ki. Please ki yafe min, ki bar azabtar da zuciyata haka nan.” 7
Asiya ta fadi kasa tare da baje hannayen ta, ta rungumi mijin ta cikin kuka mai ratsa zuciya, “Na shiga uku, na saka mijina kuka tare da cusa ma sa bakin ciki.” 6
Shi ma ya kara rungumar ta ga-gam, sai ajiyar zuciya kawai yake yi. Ta ci gaba da cewa, “Ka yafe min mijina, ko zan yi dace da rahamar Allah. Idan na tarar da Ubangiji na cikin wannan hali, kaicona!”
Da gaske ta ke jin ta shige su. Zuciyar ta ta matukar sosuwa, ganin yadda ya saukar da kan sa, ya amsa laifin da bai aikata ba, don kawai su yi sulhu.
Yadda Yusuf ya rufa ma ta asiri, ita da ‘yar uwar ta da iyayen ta bai dace a ce ya shiga kunci ta hanyar su ba. Ta taba jin an ce mutum ya fi bata rai wa wanda ya fi son shi. Ma’ana dai, kishin sa ne ya rufe idanun ta, har ya kai su ga halin da ta jefa su ciki.
Ba taba soyayya ba sai a kan sa. Don haka ba ta san yadda za ta shawo zuciyar ta a kan kishin da ta taso gare ta ba a kan sa. Garin neman bayani, ta soki zuciyar sa, ta so tarwatsa ginin rayuwar da suka fara shimfidawa.
Yusuf ya ja daga jikinta, sannan ya shiga share hawayen ta da hannun sa. “Ki bar kuka my dear, domin har ga Allah, na yafe mi ki duniya da lahira. Ban karaya ba, daga rahamar Allah. Kamar yadda Ya mallaka min ke cikin ta, Ya kuma bani tagwaye. Hakika, na yi alkawarin rike ku tsakani na da Shi duk wuya duk rintsi.”
Hawaye ya ci gaba da zuba daga idanun ta. Ya y aba za ta yi kuka ba? ta na ji da gani ta saka kafa ta na neman fatali da farin cikin ta, hanyar aljannar ta? Ta tausaya wa kan ta, da ma shi gaba daya. Dole ta gyara, tun ba ta shiga bone ba.
Ya ci gaba da share hawayen ta, “Kukan ki masifa ce gareni, ki daure ki tsagaita haka don Allah.”
Ta kai na ta hannun ita ma, ta na goge fuskar ta sa cikin tsananin jimami da nadama, “Na bar kukan. Ka yafe min, ba zan sake yarda shakka ta shiga tsakanin mu ba. Wata kila na makara da furtawa, amma so nake na kara jadadda cewa na yarda da kai, dari bisa dari.”
Ya dan sumbace ta, gaba daya jijiyoyin jikin ta suka mace, ya saki murmushi, “No, ba ki makara ba. So na ke na ji wadannan kalamai daga gare ki. Sun fi min komai a duniya.”
Ya ja ta a hankali ya sake rungume ta. Iska mai ni’ima, wadda suka dade ba su ji irin ta ba ta gewaye su. Karar bugun zuciyar sa take ji, wadda ta yi daidai da yadda tata zuciyar ke yi. Ta lumshe idanun ta, ta ji ajiyar zuciya.
Wannan mutum, wanda ya dandana ma ta farin ciki ya na rike da ita a lokacin da ta kawo ma sa bacin rai ta dalilin da baya da tushe. Mariya ce ‘yar uwar ta, amma ba ta taba haddasa ma ta komai ba sai bakin ciki.
Ta yi nadamar wautar ta, da yarintar ta. Don me ta bari har Mariya ta ci galaba a kan ta? Me yasa, duk da sanin halayen ta, ta bar ta tayi tasiri a kan ta?
STORY CONTINUES BELOW
Kishi. Kishi ne ya toshe mata basira. Da kuma tsautsayi. Don tun farko ba hakan ta so wannan magana ta kai ba, amma ta wuce tsammanin ta.
In Allah Ya yarda, ta yi na farko ta yi na karshe ke nan. Maree ta bar samun karbuwa ke nan daga gare ta. Sun yi wannan dai ya wuce mu su. Sai ko idan wa ta kurar daban ta taso. 2
Sun dade a haka, suna jin iskar nan mai ni’ima ta na ratsa su tare da watsa mu su dadi. Can, Yusuf ya yi ajiyar zuciya, sannan ya daga ta, suka mike tare a hankali.
Bayan ya zaunar da ita a kan gado, wurin da tun farko ya same ta, sai ya zauna shi ma a gefen ta tare da rike hannun ta cikin na sa. Kallon da yak e ma ta na kauna ya watsa ma ta kunya a jikin ta. Kunya ce ta kaunar sa, ba wai ta fada ba.
“So, Maman twins, wane sunaye ki ke ganin sun dace a saka mu su?”
Ta zaro idanu, “Ba ka yi mu su huduba ba dama?”
Ya yi murmushi, “Ban yi ba, don ban samu natsuwa da kwanciyar hankalin da za su bamu damar shawartar juna ba. ina son jin ra’ayin ki dangane da sunayen da ki ke so.”
Ta ji wani kulliti ya makale ma ta a wuya, ta na kokarin mayar da kwallar da suke neman gudana cikin idanun ta. Yusuf mutum ne nagari, wanda samun irin sa sai an tona. A tarihin gidan su, wanda suka sha jin a na fada,
Baban su bai taba tambayar Dada shawarar sunaye a lokacin da ta haife su ba, ko lokacin na yayyen su. Kawai saka wa yake yi wando ya ga dama.
Sun lura da cewar sunayen su kaf matan gidan su, sun zo daya da kanne, yayye ko gwaggonin mahaifin su ne. cikin su babu dangin Dada ko daya. Asiya ce kadai ba ta da takwara don sunayen sun kare. A madadin ya saka ma ta sunan mahaifiyar Dada wato Hafsa ne ya saka Asiyar.
“Kin yi shiru ba ki ce komai ba.”
Ta hadiye yawu da kyar, “Sunayen da na ke matukar sha’awa, su ne Harun da Yahya.”
Ya daga girar sa daya, ya na kokarin danne dariyar da take son kwace ma sa. Ya yi mata kyau, don ba ta san ya iya daga girar guda daya kadai ba.
“Harun? Yahya? Seriously? Na ga kamar tsoffin suna ne?”
Ta yi murmushi ita ma, “Na san tsoffin sunaye ne. Amma kuma suna a kan saka ne don neman tabarrakin ta, tare da fatan Allah Ya sa yaro ya dauki halayen mai shi. Harun da Yahya sunayen annabawan da na fi bas u muhimmanci ne bayan Annabin rahama Muhammad (SAW). Sannan Harun sunan mahaifin ka ne.”
Ya dan tsuke fuskar sa, “Ba ki taba jin sunan Annabi Yusuf ba ne?”
Ta fashe da dariya har da nema kwarewa. Shi kuwa ya kara shan mur, “Seriously, idan ba ki san tarihin sunan ba sai na mi ki bayani.”
“Ai ban isa in ce ban san tarihin Annabi Yusuf ba. Ba ni ba, duk musulmai da ahlul kitabi sun san jarumta, kwarjini, rikon amana da kuma kyaun surar sa. Shi ne Annabin da bayan Manzon mu, ba a yi mai kyaun sa ba duk fadin duniyar nan.”
Ya dan yi murmushi, “Ke ba kya son daya daga cikin ‘ya’yanmu su dauki wadannan baiwar halayen?”
Ta dan yi dariya mai aika sako, wanda ta lura da yadda ya kalle ta, wannan sako ya samu shiga, ta ce, “Ina so mana. Na kuma san sun yi babban arziki da suka same ka a matsayin mahaifi.”
Ya dan lakaci hancin ta, “Ke din ma ba baya ba ce. Trust me, ki yarda da ni, za ki kasance uwa tagari.”
Hakan ya kara ma ta dadi marar misaltuwa. Jin hakan daga mijin ta ya nuna kaunar sa gare ta, da kuma yarda. Ta kalli yaran da ke kwance, sannan ta ce, “Ka taya ni da addu’ar Allah Ya nufe ni da yi mu su tarbiyya kamar yadda ya dace.”
STORY CONTINUES BELOW
“Allah Ya mana jagora. Actually, kafin ki haihu, na ji ana cewa ba sai an jira an yi huduba wa yara kafin a sanar mu su sunayen su ba. Tun suna ciki a ke fadin suna, a ce idan mace ce ga suna, idan namiji ne ga sunan sa, don ko da a ce bas u fito duniya da rai ba, za su samu sunan da za su tashi da shi ranar Qiyama. Amma a nan gaba za mu aiwatar da wannan tsarin, idan wasu ‘yan biyun suka sake zuwa” Ya kashe ma ta idanu ya na dariya.
Ta san zolaya ce, amma duk da hakan sai da ta ji ras! “Tabdijan! Ban fa mance da zafin ciwon wadannan ba fa.”
Ya saki dariya tare da daga ma ta gira, “Za ki manta. Bari su kai watanni hudu nan gaba, tsaf za ki manta. Da haka iyayen mu suka tara mu ai.”
Ta bata fuskar ta, “Lallai ba ka da tausayi ashe. Kai fa likita ne, tausayi ne ya kamata ya zama tambarin ka.”
Ya kyalkyale da dariya, “Mata da dama da ke zuwa asibitin mu shekara shekara suke haihuwa yawanci. Ki tambayi Hadi ki ji. Shi ya ke cewa a yanzu da tattalin arzikin kasa ta ruguje, babu sana’ar da ta fi ci irin haihuwa.”
“Da yake ba haihuwar ku ke yi ba a jikin ku dole ku ce hakan.”
Ya yi dariya, “Come on, its just a simple joke, kawai barkwanci ya ke yi. Amma ko mu mun san ba abu ne mai sauki ba. kawai yayi la’akari ne da yawan zaman da maza ke yi a gidajen su babu wata sana’a. kin ga kuwa dole mata su haihu duk shekara.”
Ta wulkita idanun ta, “To ni da wata haihuwar sai nan da shekaru biyar ma su lafiya.”
Ya dan tsuke fuskar sa, “Kar ki yi fatan hakan ‘yan Amin su amsa.”
“Hmmm, ni fan a san me nake ji.”
Ya girgiza kan sa cikim murmushi, “Ke dai ki ce Allah Ya kawo ma su albarka kawai.”
Jikin ta ya mutu jin kalaman sa. A gaskiya ta sha azabar nakuda, wanda ta ke jin ba za ta iya mancewa ba har abada. Don haka a sake kawo batun wa ta haihuwar nan kusa ma bai ta so ba. “To na ji. Allah Ya kawo ma su albarka.”
“Nan da shekara daya.”
Ta harare shi, “Ka kera injin da zai yi maka hakan ai.”
Ya fashe da dariya, “Ba bu in ji. Ke din dai za ki yi, don na fada mi ki za ki manta da komai. Ya dan kara sauke muryar sa, tare da dukawa dab da ita, “A lokacin za ki dawo ki na rook na, kan ki na son a yi wa wadannan kanne.”
Ta ja numfashi na ajiyar zuci, sannan ta tokare shi da hannun ta kadan don kar ya karasa hada jikin sa da na ta, “Likita ka kama kan ka fa. Ka fa san ba mu kadai ba ne cikin dakin.” 2
“Kar ki damu, Yusuf da Harun ba za su fahimci cewar Daddynsu ya na kaunar Mummynsu ne.”
Dadi ya cika fal, jin kiran ta Mummy da ya yi. Da gaske ne fa, ta zama uwa ba a mafarki ba. ita ma Allah Ya dandana ma ta dadin da Ya jiyar da ‘yar uwar ta. “Alhamdulllah! Na ji sunayen su; Yusuf wa Harun, Allah Ya raya mana su bisa tafarkin musulunci.”
Ya y murmushi mai fadi, “Amin.”
Sannan daya bayan daya, ya karbe su ya na mu su huduba. Ta gagara kawar da kan ta, hawaye tab a cikin idanun ta. A lokacin da ya kamala, ya kalle ta cikin kauna da kulawa, “Me ya same ki kuma my dear?”
Ta nisa tare da girgiza kan ta, “Ba wani abu ba ne. kawai na tuno ne da ranar da ka yi wa Amatullah huduba.”
Ya ja hannun ta cikin nuna kulawar sa, ya ce, “Why? Me ya sa ki ke wa kan ki haka? Me ya sa za ki kawo abin da zai sosa mi ki zuciya ki dora wa kan ki? Musamman a yanzu da Allah Ya mi ki babban baiwa, yawan wannan tunani tamkar juya baya ne ga hakan.”
Ta sunkuyar da kan ta, kwallar sun a zuba, “Na kasa daure wa zuciya na ne. A duk lokacin da na kalli Yusuf da Harun, san a ji zuciya ta ta sosu ba da son raina ba. Amatullah bangaren jikin ce, wacce ba zan taba mancewa ba.”
Hakika, ba za ta mance da dimbin farin cikin da ta samu ta dalilin Ama ba. Ko da dai ba ita ta haife ta ba, Allah ne Ya mallaka ma ta ita a matsayin diyar ta. Don haka zama babu ita tamkar wa ta azaba ce ta nan duniya.
Ya nisa, “Duk kusancin ki da Amatullah ba ki kai Mariya ba, na sha fada mi ki wannan. Allah ne Ya zaba ma ta ita a matsayin mahaifiya, Ya kuma fi mu sanin dalilin kasancewar su tare a yanzu. Addu’a za mu ci gaba da yi ma ta, cewa a duk wurin da take, Allah Y aba ta koshin lafiya. Ba zamu iya abin da ya fi hakan ba. Yawan tunani kuma ba zai tsinana ma na komai ba.”
“Na sani, amma da ciwo ne. Kamar an saka gizago ne an sassaka zuciya ta cikin kirjina, sannan an bade yaji.” Ta kai hannun ta daya ta share hawayen ta, “Ko sau daya ban saka ta a idanu na ba tun tafiyar ta. Idan na tuna hakan ba karamin radadi na kan ji ba.”
Yusuf ya dan ja ta zuwa jikin sa don ya ba ta kwarin gwiwar shanye zafin da take ji. Bai ce komai ba, rike ta hakan da yayi ma tamkar kalamai dubu ne. dumin jikin sa da karar bugun zuciyar sa suka kara wa tata sauri.
Kamar tsafi ta fara jin sukuni ya na mamaye ta. Ta na kewar Ama, ta na begen son ganin ta, amma kamar yadda mijin ta ya fada ne, ba suda yadda za su yi.
“Kin san babu abin da za ki neme shi a duniyar nan da b azan mi ki shi ba, matsawon ina da ikon yi miki. Kuma ni ma ina kewar Amatullah, zan kuma so a ce ta dawo gare mu. Amma na hakura ne don fawwala wa Allah komai. Shi ya mallaka ma na ita tun farko, sannan Ya mayar wa mahaifiyar ta. Idan Ya ga dama, zai sake ba mu ita. Amma ba zai kyautu mu hana kanmu sukuni don hukuncin da ya fi karfin mu ba.”
Ya dan ja daga jikin ta kadan, suna kallon juna, numfashin su ya cakude, “Mu bar rayuwa kan abin da ya wuce, komai dadin sa. Babu ruwan mu da abin da ya wuce. Mu rayu a kan yanzu, cikin ni’ima da baiwar Ubangijin mu. Kar kuma mu kai kan mu zuwa gobe tun Allah bai kai mu ba.”
Ta sake birne kan ta cikin kirjin sa, tana jin dadin natsuwar da ta ke kara samu. Karfi yake kara ba ta, na yin juriya ga rashin Ama. Bai kamata ta rufe idanu kan rahamar Allah ba, wanda Ya karbe daya, Ya kuma mallaka ma ta biyu a lokaci guda.
Shin da Amatullah mutuwa ta yi, ba zata ci gaba da rayuwa ba? ba za ta hakura ba? wadan da ‘ya’yan su ke mutuwa ba sa ci gaba ne da rayuwa?
Sanin cewar Amatullah ta na nan da rai ne ke kara saka ta cikin damuwa. Gwara ma a ce mutuwar ta yi, ta san cewar ta bar duniyar ne gaba daya.
Amma a ce ta na hannun Maree, wadda ba ta san rikon da za ta yi ma ta da tarbiyya ba. sannan ma tun farko ta guje ma ta, ke kara saka ma ta tashin hankali da ban tsoro.
Yusuf ya fi ta gaskiya. Lokaci ya yi da za ta hakura da Amatullah kwata-kwata, ba don rashin kaunar ta ba. Sai don yarda da kaddara da karbar hukuncin Allah. Addu’a ta fi bukata, wadda ta san, ba ta faduwa kasa banza.
Ya Allah, Ya sa duk wurin da Amatullah ta ke, ta samu natsuwa da kwanciyar hankali, ta samu kulawa da tarbiyya ingantattu. Allah Ya so haduwar su wata rana, idan suna da tsawon rai.
Ta nisa, a lokacin da fuskar Ama da murmushinta suka bayyana cikin idanun ta. Ita ma ta yi murmushi. Duk yin Maree ba za ta iya kankare ko janye wadannan lokuta da Amatullah ta yi tare da su ba. Ba kuma za ta taba mayar da hannun agogo baya don hakan ba. Farin cikin da suka samu ba za ta iya raba su da shi ba.Ranar suna an yi taron walimar suna. Kusan kowa ya halarci wannan taro. Maza a waje, mata ta ciki. A nan ne aka yi wa’azi kan ladubban aure da zamantakewar sa, daukar ciki da goyon sa, sannan hakkokin iyaye da ‘ya’ya a kan kowannen su. +
An ci, an sha, sannan an rarraba abin tsaraba kamar littafan addini, zannuwa wa mata da kuma turmin shadda wa maza. Akwai CD da a ka tsara, kan tarihin annabawan da a ka saka sunayen su wa yaran nan.
Cikin CDn, an nuna Harun, sannan a ka zayyana tarihin Annabi Haruna wanda ya yi rayuwa tare da dan uwansa Annabi Musa, sannan a ka nuna Harun karami da yadda a ke shirya shi, a ke ba shi abinci, a na mai ma sa fatan ya taimaka wa dan uwan sa kamar yadda wancan Harun din ya yi.
Haka ma Annabi Yusuf.
Daga bisani a ka yi intabiyu da mahaifan yara da kakkanin su. Yusuf ya ba da tarihin kan sa da kuma yadda su ka hadu da matar sa Asiya. Ita ma Asiyar haka. Gaba daya kuma suka yi mu su addu’a da fatan alheri a rayuwar su. Kowane bako sai da a ka ba shi wannan CD don tunawa da su.
Hakan ya burge Muhibbat, wacce ta halarci sunan tun da sassafe. Ta rika shiga da fita, jikin ta na kamshi na musamman, yanayin fuskar ta na nuna hasken amarci. Dole ne ai, idan a ka yi la’akari da cewa kwanakin ta bakwai ne kacal a gidan miji.
“Mama Minde, ummin Aslam da Nurain. Jego fa ya karbe ki.”
Asiya ta yi dariya, ta na sanye cikin leshi ne mai tsadar gaske mai ruwan hoda da ratsin fari. Ga daham nan a makale a wuyan ta. “Ke fa Muhi ba ki da dama. Har yanzu ba za ki sassauta min ba?”
“Me na yi ma tukunna? Hmmm Allah Ya sa mu a danshin ku ke dai.”
Asiya ta kara dariya, “Cewa nake za kid an ci amarci tukunna kafin ‘ya’ya su zo?”
Ta harari Asiya, “An ce mi ki kowa irin ki ne? Ai ki jira ki gani.”
“Muhi, babu ko kunya?”
“Kunyar wa zan ji? Ke dai Allah Ya gyara rimi, cediya ta bar fushi.” 2
Hankalin Asiya ya tsaya sosai kan Muhibbat, ba bu barkwanci, “Me ya faru Muhi?”
Tabbas akwai matsala in a ka yi la’akari da yanayin muryar Muhibbat da fuskar ta, duk da dai murmushi ta ke kokarin yi,
“Ba bu. Ba abin da zai gagare ni bane.”
“Ki kara min bayani, don ban gane ba.”
Muhibbat ta yi murmushi mai fadi, sannan ta ce, “Ki shiga hankalin ki, kin fa san ni ce yaya babba.”
Muhibbat na kokarin kawar da maganar ne. amma Asiya ta san akwai matsala, wand aba zata yi saurin fada ma ta ba. ta fahimci hakan, ba wai fushi ta yi ba. kawai dai hankalin ta bai kwanta ba ne saboda Suhaima.
“Allah Ya kyauta Muhi. Amma na jiye mi ki tsoron Suhaima ne.”
Muhibbat ta dan yi dariya marar armashi, “Sai ka ce ni ba mace ba ce Minde? Ai na yi likimo ne na zuba ma ta idanu naga takun ta. Ba ta da wayo, don kwanakina uku a gidan ta fara sake makaman yakin ta. Ni kuwa ina kallon iya gudun ruwan ta ne kafin na saki boma-bomai na.” 5
Dariya Asiya ta ke yi har da kyarkyata. Ta dade ba ta ji dariya irin na lokacin ba. “Ki ce ta tako kulli ba ta sani ba.”
Muhibbat ta wulkita idanun ta, ta ce, “Ai Minde, rufin asirin mai loma kawai kar a yi walkiya. Amma an yi walkiya na gan ta. Sati na daya ne, amma na riga na raina wa hankalin ta wayo. Ke dai a je zuwa kawai, wata rana za ki sha labari.”
Asiya ta yi murmushi, “Allah Ya kara kare min ke Muhi na, ta Dokta Hadi komai dozin.” 2
“Ke Minde, ashe kin yi baki ne haka?”
STORY CONTINUES BELOW
“Kya ji da shi dai. Na san dadi ya cika ki yanzu amma kina basarwar gulma.”
Har cikin zuciyar ta, Asiya ta na jin dadin ganin yadda Muhibbat ta samu farin ciki a yanzu. Don kuwa sunan Hadi kadai idan a ka ambata sai an ga idanun ta sun canja. Ba wuya a gane soyayya ta buga ta.
“Mu tafi ko?”
Muryar Hadi ta katse ko ma me ye Muhibbat ke shirin furtawa. Idanun sa kan Muhibbat din ce, wani kyallin so da kauna ke haska su.
Muhibbat ta kalli agogon bango, “Karfe bakwai da kwata ne fa. Kai da ka min alkawarin zan kai goma kafin?” Muryar ta cike da lankwasa da kwarkwasa.
Ya dan gyara tsayuwar sa a kofar dakin Asiya, “To ai gani na yi duk daya ne ai.”
Ta gigiza kan ta, “A’a, ba duk daya ba ne. Ni kam ma da naga mutanen Dagauda sun cike gidan nan fal, cewa nake z aka bar ni sai zuwa gobe ka dawo?”
Idanun Hadu su ka gwalo kamar za su fado. Asiya ta dan shige bandaki don ta basu wuri. Don ta ga Muhibbat da gaske ta ke yi. Ta na iya jin muryar sa cikin magiya, ya na rokon ta da su koma gida don bai kyautu a ce ta na amarya kuma ta kwana a wani waje ba.
“Kai ka san wannan.” Muryar Muhibbat ta zo da kaushi. “Don na gaji da kwana zaune a gefen matar ka, wacce ciwon ta baya tashi sai dare yayi. Gwara ka bar ni nan na kwana cikin dangina, in ya so ka koma wajen ta kamar yadda ka saba.”
Hadi ya kara sauke muryar sa, “Ki yi hakuri Muhibbat. Wallahi Suhaima ta na da lalura ce.”
“To shi ne ai n ace ni ka bar ni nan zan kwana.”
“Ke dai akwai ki da zolaya. Zan jira ki a falo, ki fito yanzu.”
“Ba zai yiwu ba. Don ban aure ka na takura wa kaina ba. Ina nan, babu wurin da zan je.”
“Haba ke kuwa? So ki ke jama’a su san abin da muke ciki?”
“Ai gwara su sani, don ko na koman ma duk daya ne. Ni ba kowa ba ce gare ka.”
“Subhanallahi! Ke ba kowa ba ce zan aure ki?”
“Ni dai ba zan koma ba.”
Kamar Asiya ta tumtsire da dariya, amma ta daure. Ba so ta ke yi su ji tana iya jin su ba.
“To yanzu yaya ki ke son a yi?”
Daga nan ta dauke hankalin ta daga gare su, don su suka san yadda za su sasanta kan su. Ba ta san rayuwar kishi ba, don Dada ita kadai ce wajen mahaifin su, sannan ita din ma ita kadai ce.
Don haka ba za ta san yadda Muhibbat ke ji ko kakarin tunanin yadda za ta bullo wa al’amuran ta ba. Ta san dai ba fata take yi ba, ba ta kaunar hada miji da wata mace a fadin duniyar nan. 2
Muhibbat ta buga ma ta kofar, “To fito, jin gulmar ta kare.”
Asiya ta bude kofar, ta ga Muhibbat ta na rataya jaka, “Ba laifin ki ba ne. Don na baku wuri ne za ki ce ina gulma?”
Muhibbat ba ta amsa ba. Turare kawai take bulbulawa a jikin ta. Asiya ta kale ta sosai, “Ba kya da niyyar yin wanka ne na tsawon sati daya?”
Muhibbat ta yi malalacin murmushi, “Hmm, ai yau kam duk maitar Suhaima sai dai ta hakura. Don yau kwana sai Fariah Suites.” 6
Da wannan ta fita wajen da mijin ta ke jiran ta. Asiya dai ta yi ma ta rakiya ne lokacin da ta je sallamar su umma da sauran jama’a, sannan zuwa gaban gida. Ko da ganin ta Hadi ya yi sauri ya bude kofar motar. Ita kuwa sai takun yanga ta ke yi, ta na juyi.
“Mu je ko?” Hadi ya kara nu na zumudin sa.
Yusuf ya zolaye shi, “Easy Ango. Sai ka ce ba motar za ta shiga ba? ko ce ma ka a ka yi za sace ta ne.”
STORY CONTINUES BELOW
Hadi ya harare shi, “Kai fa dan sa ido ne Yusufa.”
Yusuf ya ce, “Ba laifin ka ba ne. guguwar angwanci ke dibar ka.”
“To ai gwara ni, guguwar ba ta debe ni da yaw aba tun da har na kawo ta gidan ka. Kai har yau ina kake barin Asiya ta je?”
“Haka ne. b aka samu Muhibbat ta tare gidan ka ba, dole ka yi min baki.”
Hadi ya tayar da motar sa, Muhibbat ta kame a gidan gaba, sannan ya ja suna daga mu su hannu. Asiya ta karkada kan ta, ta na murmushi.
Sara ta taba fada ma ta cewar matsalar Hadi ba wai rashin kulawa daga gare shi bane. Munafurcin Suhaima ne ke kawo ma sa nisanta da duk wa ta mace. Idan muhibbat ta samu yadda take so a yau, to lallai Suhaima sai dai ta sake sabon lale.
Bayan Asiya ta koma dakin ta ne ta tarar da Larai tare da Aslam da Nurain. A lokacin ta ke kokarin yi mu su wankan dare. Ita din ma ta na bukatar yin wankan don ta samu hutu mai tsawo.
Ta na matukar bukatar hakan. Sai dai so bas hi ne samu ba. domin a lokacin wayar ta ta dau karar shigar sako.
“Ina jiran ki a dakin mu.”
Ta mike ta nufi dakin, kasalar ba ta bar ta ba. ta san ba wani abin za ta iya yi ma sa ba, amma dai wajibi ne ta amsa kiran sa. Balle ma ba hakura zai yi ba misali, in a ce ma ta ki zuwa din. Don haka ta shiga dakin na su a hankali, tare da ce wa Larai ta na zuwa.
Ta wuce setin akwatuna biyu ne ma su shida sabbi. Seti guda na ta ne da mijin ta ya hada mata, sai kace kayan lefe.
Daya setin kuma na cike ne da kayan jariran ta tun daga haihuwa har zuwa girman su. Hadi da Sadi ma sun yin a su akwatuna bi-biyu na zannuwan goyo da kayan yaran. Komai dai tubarkallah.
Ta yi sallama shi kuma ya amsa. Ya na kwance ne a kan gado, daga shi sai dogon wando. Nan take jinin jikin ta ya dau dumi, zai fara tafasa. Ya tafi da rabin imanin ta. 6
Ta lura albom ya ke kallo a gaban sa. Gefen sa kuma wasu albom din ne har uku daban. Ya kalle ta sosai, idanun san a kyalli. Ta hadiye yawu da kyar. Ita kadai ta san abin da kallon sa ke haddasa ma ta. 4
Ya dan buga katifar ta gefen sa, alamar ta zauna a wajen. Ta yi yadda ya bukata cikin rangwada da made. “Hotunan ki na ke kallo ina kewar ki. Shi ne naga mai zai hana kawai na kira ki don na kale ki a zahiri?”
Ta rausaya kan ta cikin jin dadi, “Ba ka da dama. Yaushe na bar gaban ka? Ko fa minti ashirin ban yi ba.”
Ya ja hannun ta ya sumbata, bai bar kallon kwayar idanun ta ba, “Wa ya ce da ke ina son rabuwa da ke ko da na minti biyar ne? a yau kowa ya samu hankalin ki, face ni, bawan Allah.”
Ba ta yi aune ba aune ba ta ji ya ja ta zuwa jikin sa ya rungume ta. A yanzu kam ta tabbata jinin ta ya fara tafarfasa. Duk da cewa jikin ta da riga, tana iya jin wucewar wuta daga na sa jikin zuwa na ta.
“Ka fa san ba biyan bukata dai daga gare ni.”
Ya kara sauke muryar sa zuwa rada, “Bukata ta ki debe min kadaici na wasu lokuta. Ba kusanci ba.”
Sun dade a hakan, kafin ta ce da shi, “Ba za mu kalli hotunan ba ne?”
“Wannan din ya fi kallon.”
Jikin ta zogi ya ke yi na dadi. Tun bayan sulhun su bayan haihuwar ta ba su sake kasancewa kusa da juna haka ba. Lokuta da dama a baya Yusuf kan rike ta hakan na tsawon lokaci su yi ta hira zuwa sulusin dare. Ta yi kewar hakan ita ma.
“Ban fa yi wanka ba.”
Bai sake ta ba, “Hakan ya fi. You still smell nice.”
Ta dan ja daga jikin sa, “Ka dai daure ka ban minti ashirin. Na yi alkawarin zan dawo mu yi kallon tare.”
Za ta tashi ya rike hannun ta caraf, idanun san a nuna rashin jin dadin hakan. “Zan yi kewar ki bayan kin tafi. Don haka kar ki saka ni jira da yawa.”
Tare da alkawarin ba za ta dade ba, Asiya ta koma dakin ta, wurin da tarar Larai ta gama yi wa yaran wanka. Dakin sai kamshin mai da hodar su yake yi. Da kuma wani irin kaurin da ba za ta iya fayyacewa ba. 2
“Har kin kammala? Na dawowa don na taya ki, don na san Nurain ya fi rigimar kin wanka a kan dan uwan sa.”
Larai ta ce, “Ai ni ma saura kadan na neme ki. Sai kuma Allah Ya turo min Yayar ki ta taimaka min.” 2
Ba ta kawo komai a ran ta ba. Ta tambaya, “Au, wacce a cikin su? Yaya Asabe ko Indo?” don su kadai ne suka samu halarta walimar sunan.
Amsar da ta fito daga bakin Larai ya firgita ta. “A’a, wacce ta zo da wasu mutane ta karbi Amatullah wata rana.”
“Maree?” Idanun ta tamkar su fado kasa don mamaki. “Yaushe Maree ta shigo nan gidan kuma?” 2
Tambaya ce ta ke yi wa kan ta fiye da Larai. Zuciyar ta bugawa take da sauri. Ba ta dade da rakiyar Muhibbat ba, ba ta kuma dade a wajen Yusuf ba da har za ta shigo ba ta lura ba.
“Ai ki na shiga wajen Likita ta shigo. Ta samu Nurain yana ‘yar rigimar sa da ya kan yi. Shine ta ce na ba ta shi in ya so na dauki Aslam na kula da shi.”
Mamaki bai bar ta ba har a lokacin. Me ya kai Maree har dakin ta? Ita har ta na da karfin halin zuwa wurin da ta ke, bayan abin da ta haddasa tsakanin da Yusuf? Har ta na da hantar nuna fuskar ta gare su?
“To yanzu ina Mariyar ta ke?” ta tambaya ta na kallon gefen ta. Wata kila Allah Ya nufa za ta ga Amatullah a daren yau din nan. Don idan har Maree ta shigo, ba mamaki da Amatullah ta je.
Za ta so ta kalli kwayar idon ta, don ta ga da wace karyar za ta fidda kan ta. Ta sha yi ma ta karairayi ta na bari suna wucewa.
Amma wannan karon kam ta yi alwashin daukar mataki a kan ta. Kawai don ta shiga har ta dauki dan ta ba shi zai sa ta samu sassauci daga wajen ta ba.
“A nan na bar ta zaune da yaro a hannun ta, na je kawo ma ta abinci da ruwan sha bayan ta ce min ta na jin kishirwa da yunwa. Ko da na dawo ban same ta ba. na dauka ko ta koma wajen su Hajiya Umma ne.”
Asiya ba ta tsaya sauraron karashen shirmmen Larai ba. Zuciyar ta cikin bakin ta, ta nufi sashen Umma. Ta tarar kowa na nan, amma ba su san Mariya ta je ba, ba su gan ta ba balle Nurain.
Wani irin kugi cikin ta ya yi, kan ta ya na neman tsagewa gida biyu. Cikin tsananin tsoron da ba ta taba jin sa ba ta shiga zaagawa harabar gidan, ta na alla-alla ta hadu da Maree.
Maigadi ya shaida mata wasu matan unguwar dai sun shiga don gaisuwa, amma bai ga fitar kowacce daga cikin su ba.
A wannan lokaci ne Yusuf ya fito ya iske ta, ta na kokarin zuwa ta same shi cikin taraddadi. Hayaniyar su ce a harabar ta ja hankalin sa. Jallabiya ya saka a jikin sa, idanun sa suna nuna damuwa.
“Me ke faruwa?”
“Maree….Maree.”
Idanun sa sun nuna tartsatsin wuta na haushi, amma ya kwantar da muryar sa, ganin yadda magana ke neman ya gagare ta, “Wace Mariyar? Me ya faru da ita?”
“Maree ce ta shigo ta karbi Nurain a hannun Larai. Shi ne ba a ga wurin da suke ba.”