KUNDIN KADDARATA CHAPTER 1 BY HUGUMA
Falo ne mai matsakaicin girma wanda ke dauke da set din kujeru labulaye carfet wanda dukkansu kalolin ash ne turarre da kuma mai haske,daga bangare daya t.v plasma ce ‘yar matsakaiciya reciever da kuma D.V.D wadanda aka qawata jeransu.
Can daga kowacce kusurwa ta falon flower ce cikin plower vase dake a tsaye masu matsakaicin kudi,sosai falon ya bada sha’awa duk da ba wani uban kudi aka narka masa ba sakamakon yadda komai yake tsare a muhallinsa,bugu da qari kuma yadda ya wadatu da tsafta yake bada qamshin turaren wuta mai sanyi
Mamallakiyar falon ce zaune kan daya daga cikin kujerun falon,matashiya ce wadda ba zata wuce shekara sha takwas ba,fara ce ba irin qal din nan ba,tana da matsakaicin kyau wanda kwalliyar da tayi cikin shadda orange dinkin bubu ya sake fidda kyanta,dan kwalin shaddar na ajjiye gefanta wanda ya zamo sanadiyyar bayyanar kitson dake kanta qananu wadanda aqalla sun doshi guda dari da hamsin,yadda falonta ke qamshi hakama jikinta yake yi.
A hankali ta daga kanta karo na barkatai ta sake aza su kan agogon bangon dake manne saman t.v plasma din dake gabanta maqale jikin bango.
Sauke idanun nata tayi kana ta maida kan dan madaidaicin centre table din dake gabanta,ta miqa hannunta ta dauki wayarta samfurin tecno w3 ta sake lalubo lambar da tun dazun take ta nacin kira,duk da cewa amsa daya ake bata tun dazun cewa lambar da take nema din a kashe take amma hakan bai sanyata ta daina kira ba.
Yanzu ma amsar duka daya ce,bai saba kaiwa war haka bai dawo gida ba,yawancin baya gota qarfe takwas indai ya dade da yawa bai dawo din ba,sau tari idan taga hakan kuma ta tabbatar ba zaya wuce gidan babbar yayarsu ba hajiya yahanasu,saidai yau duk sai taji gidan shiru babu dadi,saboda baki daya ‘yan tayata zaman sun tafi gida saura ita daya.
Sauke ajiyar zuciya tayi tare da lumshe idanunta,ta dan zame kadan ta kwanta saman kujerar tana jin kewa na ratsata,kewar yara take sosai,mutum ce ita mai bala’in son yara,saidai Allah bai azurta ta da samun nata na kanta ba tsahon shekara shida da aurenta,kasancewar tayi aure tun tana da shekara goma sha biyu kacal a duniya.
Tayi zurfi kadan cikin tunanin nata taji ana yunqurin bude qofar gidan da muqulli,ta bude idanunta tana duban agogo,qarfe tara har da mintina arba’in da biyar goma saura kenan,zumbur ta miqe ta janyo dankwalinta ta daura kana ta fito a hankali ziwa tsakar gidan nasu wanda yake da yalwa babu laifi,bayan nata dakin ciki da falo akwai dakuna biyu masu ciki dai dai wanda guda daya mallakin mai gidan ne,dayan kuma ‘yan karikicen da ba’a rasa ba take ajjiyewa ciki,sai kuma bandaki daga bangare daya gefensa rijiya ce,sai kuma yalwataccen kitchen dake kallon dakuna biyu masu ciki dai dai din wanda yayi girman dakunan nasu,fes tsakar gidan shima yake kamar yadda ilahirin gidan yake,sumuntin tamkar ka zuba abinci a qasa kaci saboda wadatar tsafta.
Tana tsayen har ya kammala bude gidan ya turo babur dinsa(lifan)samfurin companion,a tsakar gidan ya masa matsugunni gefe daya lokacin da take qarasowa gareshi tana ambaton “sannu da zuwa” fuskarta qunshe da murmushi wanda lokaci guda ya soma qoqarin gushewa daga fuskarsa sakamakon ganin fuskarsa sam babu annuri lokacin da yake amsa mata da “yauwa sannu da gida,na barki ke daya na tsaya gidan yaaya yahanasu”
“Eh nayi zaton hakan” ta fada tana sanya hannunta ta amshi jaka da ledar hannunsa jikinta a sanyaye tana qara cika da mamakinsa saboda sam ba haka ya sabar mata ba idan ya shigo gidan.
Tana gaba yana biye da ita a baya tare da qare mata kallo,komai na sumayyarsa na burgeshi,har yau baya manta lokacin da ya aureta da qananun shekarunta wanda za’a iya kiranta qwaila,amma a ayanzun sai ka rantse ba sumayyar nan bace wadda ya aureta shekara shida baya da suka wuce.
A falon ta barshi ta dawo tsakar gida tana hada mishi ruwan wanka zuciyarta na sake gaya mata akwai abinda yau ke damun mukhtar dinta,mutumin da ita ke tayashi shigowa da babur dinsa ta hanyar bude masa qofa da rufewa,da ya shigo zai rungume ta yana yaba kwalliyarta,a haka zasu qarasa falo,ko da ruwan wanka wani lokaci tare suke hadawa,bai barin bakinta ya huta idan ya dawo,gwanin tsokana ne da son sanyata dariya.
Falon ta sake dawowa tana tsane ruwan hannunta,yadda ta barshi zaune haka tazo ta tarad da shi,bata ce uffan ba ta qarasa gareshi ta rage masa kayan jikinsa,shima bai tanka ba illa kallo da yake binta da shi har ta kammala ta miqa masa towel,karba yayi ya rataya a wuyansa sannan ya fice.
Kafin ya fito har ta kammala jera abinci zuwa ruwan wanke hannu,dakinsa ya wuce kansa tsaye ya sanya jallabiya kana ya dawo cikin falon.
Dukkaninsu jagula abincin kawai suke da cokulansu,damuwar data lura yana ciki ita ta hana mata sakewa taci abincin,duk da yunwar da take ji saboda bata iya cin abinci sai tare da shi,hakan ya sanya ko da rana ba don albarkacin yaran dake shigo mata ba wanda ta maida tamkar qannenta da ba zata dinga cin abincin rana ba,tana son tambayarsa amma bata son masa katsalandan,saboda shi da kansa yake sanar mata damuwarsa ba tare da ta kai ga tambayarsa ba,kasancewar ya maidata tamkar abokiyar shawara gareshi,sosai zuciyarta tayi ta kasa sukuni.
A hankali ya daga idanunsa ya dora akanta sakamakon tuna a inda yake,sai yaji tausayinta ya kamashi,baiji dadin sanyata a damuwa ba,ga uwa uba yana hasashen nan gaba kadan zata iya shiga damuwar data linka wannan.
Ajjiyr cokalin yayi yana qirqirar murmushi tare da kamo hannayenta ya riqe
“Lafiya qalau kuwa yau kike my sumy?” Cikin raunanniyar murya tana qoqarin maida qwallar data taru a idonta kasancewarta mace marason damuwa,kanta ta langabe cike da rauni
“Kai zan tambaya yaya mukhtar” ta qarashe fada muryarta na rawa,girarsa ya dage
“Me ya faru?” Qoqarin daidaita muryarta tayi
“Ban taba ganinka cikin damuwa yaa mukhtar irin haka ba,me ya faru da kai” kai ya girgiza yana sake qirqirar murmushi yana qoqarin azawa fuskarsa,don baisan ta ina zai fara sanar mata damuwarsa ba,ya tabbatar za tayi nauyi a qirjinta fiye da yadda tayi nauyi a nasa qirjin,bai da buqatar fadawarta damuwa ko kusa,sai gashi yaya yahanasu nason jefasu damuwa duka su biyun,sonta da tausayinta wani bangare ne mai girma a rayuwarsa
“Sumayyaaaaah” ya dan ja sunan nata yana kallonta
“Babu wani abu da yake damu na,gajiya ce kawai,matso maza kici abinci don na tabbata babu abinda kika ci” ya fada yana janyo plate din gabansa tare da zare nata cokalin ya fara juya abincin da iya nasa cokalin da alamu yana nufin ciyar da ita da kansa kamar yadda yake mata wasu lokuta.
Kan ta ta girgiza idanunta cike da qwalla”ya mukhtar kayi haquri amma wlh ban yarda cewa baka da damuwa ba,bazan ci abincin nan ba har sai ka gayamin meke damunka”cokalin ya ajjiye kana ya sauke ajiyar zuciya,baya da nufin fada mata komai amma ya fuskanci idan baiyi wani abu ba zata qi cin abincin ne kuma ta kwana cikin damuwa saboda haka yace da ita
“Naji,zan gaya miki amma ba yanzu ba,kinga dare yayi sai gobe idan Allah ya kaimu,yanzun ki matso kici abinci tukun”
“Kayi alqawari?” Dariya ta bashi saboda yadda quruciyarta ta fito muraran sanda tayi maganar
“Eh nayi” ya fada shima.
Ko da suka zo kwanciya haka ya dinga qoqarin boye damuwarsa,ya dinga qarfin halin aiwatar da duk wani abu da ya saba yi mata su don cire zargi daga zuciyarta da kuma son ganin ta sake,zamu iya cewa barcinsa kadan ne a daren ranar,cikin duhun dakin ya dinga juyi yana sake bitar maganganun da sukayi da yaaya yahanasu a wannin da suka shude dazu,yana cikin wannan tufka da warwarar bacci yayi awon gaba da shi.
Washegarin ranar duk da maganar da sukayi daren jiya na maqale a zuciyarta tana mata yawo wanda ya haddasa mata wata kasala hakanan da mutuwar jiki saboda har wayewar garin damuwar dake fuskar sa bata bace ba,hakan bai mata tasiri ya hanata yin duka wata hidima ta gidan ta ba,wanda ya kama da tsaftace gidan kafin tashin mukhtar daga bacci,shirya abun kari da tanadar masa ruwan wanka.
Yana tsaye bakin gado yana sanya links din hannun rigar shaddarsa,yayin da take gaban madubi tana shirya masa ragowar kudadensa da ya taho da su daga kasuwa da zai fita da su ya kaisu banki,hira suke jefi jefi duk da ba kamar yadda suka saba bane.
Bayan ya kammala ya tako gaban madubin yana gyara zaman hularsa a kanshi,sumayya ta dubeshi cikin zuciyarta tana yaba kyawun da yayi,ya kula da ita saboda haka cikin salon tsokana yace
“Ki fito kawai kice na fiki kyau yarinya,sai wani satar kallona kike” sau tari idan ya fadi haka kunya da dariya yake bata,har ma wani lokacin musu ya dan kaure tsakaninsu,yau din ma dariyar tayi,maimakon ta biye masa auyi musun su na ta fishi kyau da iya kwalliya yadda suka saba sai tace
“Yaa mukhtar,yau ne fa sunan fiddausin” yanayin fuskarsa taga ya dan sauya,bai ce komai ba yana daura agogon hannunsa,har ta fidda rai tayi zaton ba zaya ce komai din ba sai taji yace
“Zaki je dinne?” Murmushi tayi saboda mamaki tambayar ta bata,fiddausi ai kamar diyarsa ce saboda ‘yar yaya yahanasu ce,kuma shi da kansa ya bada kudin ankon sunan harda kudin dinkin ma
“Me zai hana yaa mukhtar,saidai idan kai ka hana” shiru ya sake yi har ya kammala ya dauki jakarsa ya rataya sannan ya sanya hannu cikin aljihun rigarsa ya fiddo da dari biyar ya miqa mata kudin cefane,sannan ya sake fitar da dubu daya daban yace mata kudin mota,ya sake bata wata dubu biyun yace ta baiwa mai jego barka,hannu biyu ta saka ta amsa tana jera godiya kamar yadda ya zame mata al’ada duk qanqantar alkhairin da zaya yi mata,tako masa tayi ta rakoshi har ya fidda babur dinsa waje tayi masa a dawo lafiya.
Tana shirin mayar da qofar gidan ta rufe taga ya juyo
“Idan kika je kada ki dade,ki dawo gida da wuri,kuma bana son ki shiga cikinsu kuyita faman surutu” dan jim tayi saboda bai taba cewa hakan ba idan zata shiga cikinsu sai yau,amma sai ta share ta gyada kai kawai tace
“Insha Allahu”.
Qarfe sha biyu da arba’in ta kammala shirinta tsaf,tayi kyau cikin ankon sunan duk da cewa qaramar atamfa ce ‘yar leda wadda kudinta bai wuce dubu da dari biyar ba,mayafinta takalmi da jakarta har sarqarta duka sun dace da atamfar,yau cikin yaranta ba wanda ya leqo,hakan baya rasa nasaba da ce musu da tayi zata unguwa ne gobe,yaran kusan tarbiyyarta ce,suna da hankali da nutsuwa,tsahon shekara shida suna tare suke debe mata kewa,sanda aka kawota unguwar ita din ma tana qwailarta,yaran basu wuce shekara biyu ba harda masu daya da rabi,ita ta dinga rainonsu,don karbo su take su wuni gurinta,iyayensu sun riqeta tamkar ‘yarsu,don haka sabo da shaquwa ne tsakaninsu sosai.
Gidan maman sadiya ta shiga saboda tahowa da nana yarinyar maman sadiya wadda zata rakata,duk cikin yaran yarinyar tafi shiga ranta,a kitchen ta samu maman sadiyan na dora girkin rana,nana anci kwalliya ana tsaye bakin qofar daki,hatta da takalminta na qafarta,cikin barkwanci suka gaisa da maman sadiya kana tac” ga mutuniyar nan,tun dazun ta addaba sai taje taga kin shirya,ni na hanata”dariya sumayya tayi
“Ai na gama sai tafiya” fatan dawowa lafiya maman sadiyan tayi musu kana suka fice.
Qarfe daya da wasu mintina ta isa gidan,tuni har ya fara cika da jama’a kasancewar haihuwar fari fiddausin tayi,gaisawa ta dinga yi da duk wanda taci karo har ta dangana da dakin mai jegon,’yan uwan mukhatar ne cike da falo zuwa uwar dakan fiddausin,bata gajiya ba sai data bi ta gaida kowa,yayin da kowa ke amsa mata cikin mabanbantan yanayi,wani ya amsa mata ba yabo ba fallasa,wani ya amsa mata cikin shakulaton bangaro,yayin da wani bai amsawa ma sai an tabo shi ance ana gaidaka,duk hakan bai dameta ba saboda shekaru biyu kenan da fara fuskantar irin hakan daga garesu,mutum ce ita mai qaranta zargi qwarai a kan mutum,babu wani abu da suka taba ce mata face sauyin fuska kawai da take gani daga garesu.
Cikin uwar dakan ta cimma fiddausi tare da yaya bara’atu wadda ita ke bin muktar sai mai bi mata fadima sai kubra ‘yar yayan mukhtar,sai babbar ‘yar yaaya yahanasu mansura,jaririyar ta dauka fuskarta qunshe da murmushi tana fadin
“Kai masha Allah,jariri akwai abun sha’awa”
“Hmmm,ku kam ba ruwanku da ita ko?”cewar fadima kafin tace wani abu yaaya bara’atu ta karbe zancen
“Nan da wata goma idan Allah yaso gidan mutari zamu suna,wannan karon kam shima Allah ya kusa kawo masa”
“Allah yasa”inji fadiman.
Hakanan ta samu kanta da fargaba hadi da faduwar gaba,bata fita daga wannan yanayin ba maganar fiddausi ta katse mata zaren tunanin da ta fara qullawa
” au,ciki ne da sumayyan?”tabe baki yaya bara’atu tayi tana fadin
“Hmm,ina fa,yaaya yahanasu ke nema masa auren fa’iza” wata matsananciyar faduwar gaba ta saukar mata,jikinta yayi sanyi qalau,ta dinga jin zuciyarta na bugawa da sauri
“Alla ya sanya alkhairi” fiddausi ta fada tana kwashe rigunan barka na jaririyar daga kan gadonta tana lodawa cikin sif,hakanan take,baka fiya gane alqiblarta kan lamura ba.
A hankali ta zame yarinyar daga cinyarta cikin kasala sakamakon shigowar ‘yan suna cikin dakin,ta budr jakarta ta fito da dubu biyun da mukhtar ya bata ta miqawa fiddausin tana cewa
“Gashi,a siyawa baby turare” karba tayi tana fadin
“An gode”.
Duk yadda zancan ya daketa haka ta dinga dakewa tana yaqe,sam hankalinta ba’a kwance yake ba,qarfe hudu da rabi ta musu sallama don komawa gidan,ba wanda ya damu da tafiyar tata ballantana ya tambaya,sai data miqa nana gida sannan ta bude gidanta ta shigr.
Kan kujerar falonta ta zube tana kiran sunan Allab,tayi a qalla awa guda tana saqa tana warwarewa,tabbas sauyin fuska da ta samu daga garesu yana da nasaba da rashin haihuwarta?,aure kenan mukhtar zai qara?,eh mana,dole mukhtar ya qara aure,’yana da buqatar ganin jininsa kamar yadda danginsa ke da irin wannan buqatar’,abinda zuciyarta ta tunasar da ita kenan,ambaton sunan Allah tayi ta runtse idanunta,babu shakka don so tana son mukhtar,amma bata jin zata yarda ta zama silar batawarsa da yayarsa wadda take tamkar mahaifiya a wajensu,tasan halin yaaya yahanasu sarai,duk abinda ta quduri aniya sai ta aiwatar da shi,hana na nufin bashi da amfani tace zatayi adawa da abinda ta umarceshi.
Cikin mutuwar jiki ta miqe don yin sallar la’asar tana istigfari,saboda lokacin ta da ya kusa qwace mata ba tare da ta yita ba,ko da ta idar ta jima zaune saman abun sallar tana addu’o’i sannan ta samu ta miqe,kitchen ta shiga,ta riga da tasan yau ta makara don haka bata da buqatar dora girki mai wuya saboda bata son mukhtar din ya dawo ya buqaci abinci bata kammala ba.
Tana girkin tana saqe saqe,tana ta faman hada daya da daya,sai yanzu ta tabbatar cewa damuwar jiya da mukhtar ya shigo da ita bata rasa nasaba da wannan zancan kenan?,da gaske ne kenan auren mukhtar zai qara?,sai tasa tafin hannunta ta share qwallar da take zubo mata tana addu’ar neman agajin ubangiji,babu shakka qauna ce ta sanya mukhtar ya kasa gaya mata komai.
Jallope din shinkafa tayi da kayan lambu saboda haka ana kiraye kirayen sallar magariba ta kammala,tuni dama tana da lemonta cikin dan qaramim fridge dinta wanda zobo ne da lemon tsamiya saboda mukhtar na sonsu musamman lemon tsamiya saboda maiqo.
A gurguje tayi wanka ta hada da alwala,bayan ta kammala sallah ta shirya tsaf cikin qananun kaya wanda take siya cikin gumama da ake budewa bayan layinsu,sosai kayan suka yi mata kyau,sai ka rantse babu wani abu dake damun zuciyarta.
Tana cikin yin turaren wuta taji bugun qofa,ta ajjiue kaskon ta zira hijabinta kana taje ta bude,Amrah ce ‘yar maqotansu daya daga cikin yaran gidanta kenan riqe da kwanon samira a hannunta
“Anty yau duk bamu ganki ba,baki dawo daga unguwar da wuri bane?” Yarinyar ta tambaya tana murmushi,murmushin itama sumayya tayi
“Da wuri na dawo amrah,banajin dadi ne sosai yau”
“Allah sarki anty sannu” yarinyar ta fada cikin nuna alhini,sumayyan ta amsa mata tana karbar kwanon da amrahn ke miqo mata
“Gashi,dama mama ce tace na kawo miki dambu ne” murmushi ta sake yi tana cewa
“Ayyah ki cewa mama na gode,ashe bata manta da ni ba,jirani ina zuwa” ta fada tana shiga da kwanon ciki,alewa ta ciro guda biyu cikin jakar alawar ‘yar dari da hamsin da take badawa ana siyo mata saboda yaran
“Ungo ki gaida mama da kyau” hannu biyu tasa ta amsa tana cewa an gode ta juya ta tafi.
Tana shirin maida qofar ta rufe horn din mashin din mukhtar ya dakatar da ita,sai ta zare sakatar gami da bude masa qofar ta raabe daga can bakin qofar tana jiran shigowarsa.
Shi din ma a yau kallo daya yayi mata ya tabbar akwai abinda ya mata kutse cikin farinciki da walwalarta,sosai fuska da jikinta baki daya suka nuna gazawa da kasawarta,gabansa ya fadi saboda wani tunani da ya darsu cikin zuciyarsa,a hankali qirjinsa ya dinga bugawa.
Yarinya ce amma a dabi’unta sam ba zaka kirata haka ba,tana da halin manya da dattako da sanin ya kamata,sai tayi qoqarin cilla duk wata damuwarta gefe guda ta garbeshi yadda suka saba,a yau din ya sake sosai har ma yana tsokanarta,amma ta nan fannin sai ta samu kanta da gaza amsa masa,duk da murmushin yaqen da take ta qoqarin binsa da shi,wani abu ne cunkushe a qirjinta.
Tana ta kai kawon shirya masa abinci yana ta binta da kallo,babu shakka iya kula da miji ba wai mace mai karatun boko kawai ta iya ba,shi ya yadda da wannan,komai na sumayya a nutse yake,ba zaka taba tunanin bata taba shiga aji ba face ajinsa,shi ya koya mata yadda zata yi karatu da rubutu,rainonsa ce shi ya raini abarsa,ko motsi sumayya tayi yasan me yake nufi,hakan ya sanya a yanzu kallon da yake binta da shi karantarta yake,duk wani motsi nata na gaya masa akwai damuwa mai yawa cikin zuciyarta.
Hannunsa ya sanya ya ruqota lokacin da take duqe tana shirin zuba mishi abinci,sai ta dago idonta take idanunsu suka gamu,ko baiyi magana ba tasan meke yawo cikin idanunsa,sai ta narke qwalla ta cika idanunta,janyota yayi ta fada jikinsa ya rungumeta da dukka hannayensa,kuka ne ya qwace mata ba tare data shiryawa hakan ba,baice mata komai ba har sai da tayi mai isarta,ya fuskanci zuciyarta ta soma sanyi sannan yace da ita cikin murya mai sanyi
“Me ya faru my sumy,me ya sameki?” Cikin muryar kuka maganar na kakkatse mata saboda shishshiqar kukan dake kawo wa muryarta caffa
“Yaa mukhtar,yanzu saboda zakayi aure kake boyemin?,me yasa baka gayan ba ya mukhtar saidai na tsincin zancan a waje?” Shiru yayi wuta ta dauke masa lokaci guda,zancan da yake ta faman boye mata kenan,shi kansa cikin awanni kadan maganar ta dagulamasa dukka wata nutsuwa tasa,ina ga sumayyar tasa,ajiyar zuciya ya saki sannan yace
“Sumayya,bana son ki tada hankalinki kan wannan maganar,ni mukhtar a yanzu bana sha’awar qara wani aure,ke daya sumayya kin isheni,kuma babu wanda ya isa ya sani dole tunda ni zan zauna da ita”.
Da sauri ta daga kanta daga qirjinsa tana dubansa tana kada kanta.
“Ko ba jima ko ba dade dole ya mukhtar sai ka qara aure,koda baka da muradi ‘yan uwanka zasu tursasa ka,tunda na kasa samar musu da abinda suke da buqata,na kasa haihuwa…..” Ta qarasa maganar kuka na sake qwace mata.
Da sauri ya sanya hannunshi ya rufe bakinta.
“Subhanallah,sumayya!,ina ilimin addininki ya tafi?,Allah kadai ke bada haihuwa kin sani na sani kowa ma ya sani saidai klwa ya take saninsa,to saboda haka babu wani sake auren da zanyi,mu barwa Allah lamuranshi har zuwa lokacin da yaga damar bamu”.
Ta lura da gaske mukhtar yake ba zaya karbi auren da aka bashi ba,wanda hakan dai dai yake ya debo baqin fenti ya yaba mata a idanun ‘yan uwanshi,a yanzun ma tana rakawa ne kawai da yanayin dangantaka da alaqarsu,ba zata iya tuna yaushe rabon da ta ga wani da ya jibanceshi a gidansu da zummar ziyara ba,kawaici kara da yakanarta ne kawai yasa bata dauki lamarin a bakin komai ba,ta riga ta sani ta kuma yi imani da shi shine dukkan tsanani yana tare da sauqi.
Ji take a jikinta wannan ce kadai dama ta qarshe a gareta da zata dawo da kyakkyawar alaqar da a da can baya take tsakaninsu
” ya mukhtar”ta kira sunansa,bata tsumayi jin amsarsa ba ta dora
“Don Allah da annabinsa kada ka yimin haka,kada kace ba zaka karbi auren nan ba”
“Sumayya,bana so kuma bazan karba ba,bana da buqatar qarin aure a yanzu haka,domin babu abinda na nema na rasa ga mata ta” ya fadi yana dubanta kansa tsaye,rasa me zata ce masa tayi saboda yadda taga ya tunzura kamar ta sokeshi da allura.
Qarar wayarsa ce ta sanyashi mai da idanunsa kan wayar,har ra qaraci ringing dinta ta katse bai daga ba,tana katsewa wani kiran ya sake shigowa,sai da ta kusa katsewa sannan ya daga
“Hello” aka fada daga can bangaren,ko bata ga sunan mai kiran ba tasan yaya yahanasu ce,tana jiyo muryarta tar kasancewar tana jikinsa
“Assalamu alaikum”mukhtar ya fada
” sai yanzu kaga damar daga kiran nawa hamshaqi?”ta fada cikin fada
“A’ah ba haka bane….” Ta katseshi da sauri ta hanyar fadin
“Ba wannan nake so naji daga gareka,munyi maganar yarinyar nan fa’iza,naji shiru baka ce komai ba” ransa ya sake baci fiye da dazu,har yanayin fuskarsa ya sake munana fiye da dazun.
“Yaaya,kiyi haquri,inaga gaskiya gwara kawai abar maganar nan,kada in zama silar bata zumuncinku ke da qawarki,domin a gaskiya bani da sha’awar qara aure a yanzu haka,mata ta babu abinda na nema daga gareta na rasa”.
” iyeeee,ni muntari kake gayawa haka,kai kuwa ka rasa komai daga matarka,shekararku nawa tare,ko dan yatsa ta taba haifa maka?,hala ma haka sumayyan tace ka fadamin kenan?”.
“Babu ruwanta yaya,hasalima bata san da zancan ba banda yanzu,nine kawai bani da ra’ayi”.
” muntari ka bini a hankali,idan nayi maka baki fa sai ya kamaka wallahi kai ka sani,aure kuma babu fashi wallahil azim,mu zuba ni da kai da ita kanta qaramar alhakin sumayyar muga wanda zai kai qasa,banza shashasha kawai solobiyo,yarinyar da a haihuwar tumaki ka haifeta zaka tsaya tana juyaka kana tsoronta”qit ta kashe wayar daga fadin hakan.
Tuni sumayyan tayi nisa a duniyar kuka,so tayi ma ya saketa ta zauna qasa ko ta kwanta ko zata fi jin dadin yin kukanta son ranta amma yaqi sakin nata.
Cikin jarumta ta hadiye kukan nata ta dubeshi
“Ya mukhtar,wallahi kaji nima na rantse qarin aure gareka babu fashi matuqar kana qaunata da gaskiya kamar yadda ka fada,wannan kawai ya isheka ishara ka gane kashin kaji kake shirin sake yabamin bayan wanda na goga a baya,saboda haka ya zama dole ka yiwa yaayaa biyayya tunda mazaunin mahaifiya take a gareka” tana gama fadar haka ta miqe daga jikinsa ta shige dakin gadonta.
Cikin kwanakin gaba daya ta daina yi da shi,ta tsame hannu daga sabgarsa ba wai don haka ta so ba,tayi amanna auren da zaiyi ne kadai zai sama mata salama cikin rayuwar aurenta,ta tabbata ba zasu barta ba ko ba dade ko ba jima tunda bata haihu ba.
Kwanaki uku kenan zaman babu dadi,saidai ta tara yaranta suyita sabgarsu amma na ruwanta da shi.
Ranar cikon ta hudun bayan ya dawo daga kasuwa,ya tadda kayan abincinsa ta jera kamar yadda ta saba,tayi shigewarta uwar dakanta babu ita ba alamarta,toilet ya shiga yayi wanka duka tana jinsa bata ko motsa ba balle ta fito,ya gama ya kintsa cikin jallabiya,bai ko kalli abincin ba ya shiga uwar dakan tata,nan ya cimmata saman gado zaune jingine da fuskar gadon,hannunta dauke da qaramin littafin alma’asuraat,ba taka haue bace ‘yar gado ce,domin gidansu gidan malamai ne akwai ilimin addini tsantsa wanda hakan ya sanya yara matan gidan basa karatun boko sam sam.
Bata dubeshi ba har ya hauro gadon ya sanya hannu ya karbe littafin ya ajjiye gefe guda,ganin tana shirin yi masa bore ya sanyashi saka qarfinsa ya riqeta gam,cikin salo ya soma rarrashinta da neman sulhu daga gareta,cike da tuburewa ta dubeshi
“Karbar auren nan ne kadai zaya samo maka kaina yaa mukhatar,idan ba haka ba zaka iya tafiyarka muci gaba da zama a haka,ya fiye min akan danginka su dinga ganin na mallakeka,kullum ban da kwanciyar hankali ko nutsuwa a cikinsu” ta qarashe maganar zuciyarta na sake yin rauni,dama can a raunane take,dakiya da haquri yasa take iya sabgoginta kamar bata da damuwa,tun asali mutumce mai zurfin ciki,bugu da qaari zamanta da mukhtar babu wani abun tur da yake mata don haka bata iya fadar matsala ko kai qara ba.
Ya kusan kwashe minti talatin cikin nazari da dogon tunani,har ta fara jan abun rufa zata yi kwanciyarta tana tsammanin yana kan batunsa,ya waiwaya cikin sanyin jiki ya dubeta
“Sumayya,ina sonki kin riga da kin sani,babu kuma abinda na nema na rasa daga garekin,ban dauki rashin haibuwarki a wata matsala ba,saboda na riga da na sani cewa bawa bai isa ya tasara kansa *KUNDIN QADDARARSA* ba,tunda kina gani shine buqatarki kuma shine kwanciyar hakalinki na amince”.
Duk da hakan take buqata saboda tasan shine samun salamarta daga hannunsu yaa yahanasu amma sai da wata ‘yar banzar faduwar gaba ta ziyarceta,ta hadiye wani abu sannan tace
” shikenan,amma ya kamata gobe kafin ka dawo gida kaje ka sanar da yaayaa yahanasu amincewarka,so nake ta daina zargi ko jin haushina”kallonta ya waiwaya yayi,saboda a yadda tayi maganar shi zai nuna maka akwai ragiwar zallar quruciya a tattare da ita,bai son zuwan saboda haka ya kada kai yace
“Bazan je ba saidai idan zaki shirya muje tare”.
Ido ta dan zaro don har ga Allah batasan ya hafuwarsu zata kasance da ita ba,amma sai dabara ta fado mata,kasancewar babu wani nisa sosai tsakanin gidansu da gidan yaya yahanasun bazai wuce naira talatin ba kudin mota
” eh zani,amma saidai ka ajjiiyeni a gida,idan ka dawo kazo ka daukeni mu tafi”baice komai ba ya tire bargon ya shige ciki tare da janyota jikinsa,da sauri ta dubeshi
“Abinci fa kaci ne?” Kai ya girgiza mata
“Na qoshi”
“Amma yaa mukhtar bai…….”
“Shshshshsh” yace da ita sai tayi shirun tare da komawa ta lafe ajikinsa,ta sani tunda yace bzaici din ba bazai ci ba,ita kuma bata saba musu da shi ba saboda girman da yake da shi a idanunta.
Cikin dare ta kasa barci,itadai bata san kishi ba tunda bata taba soyayya ba saboda shekarunta sha biyu a sanda aka aurar da ita,tadai auri yaya mukhatar,kuma tanaji a zuciyarta tana sonsa bata so wani abu ya rabeshi,amma tana jin babu dadi duk sanda ta tuna zai kawo wata gidan ta zauna tare da su,ya dinga kulata kamar yadda yake kulata,da tunanin yaqi qare mata sai ta sauko daga saman gadon,ta sadada ta fita ta daura alwala ta kabbara sallah.
Kusan wannan tarbiyyar gidansu ce tun kafin tayi aure,mamarsu tasha gaya musu duk sanda suka kasa barci da kwanciyar banza suyita zaman tunani gwara suyi salla,zasu samu lada kuma daga bisani baccin yazo,a lokacin dariya sumayya take qyalqyalewa da shi saboda tsantsar quruciya,takan ce
“Nikuwa mama mai zai hanani bacci?,bacci fa dadi ne da shi wallahi mama,baki ga da qyar nake iya tashi nayi sallar asuba ba,wataran ma sai kin sanya tsumagiya kin dakeni?” Murmushi kawai uwar takeyi kana tace
“Sumayya kenan quruciya mai dadi ko” sai ta sake yin dariya tace
“Hmmm,mama kenan,nikam babu abinda zai hanani bacci na,ga katifata mai laushi,ga iskar fanka”.
Washegari tare suka tashi,shi ya dinga taimakata da ayyukan gidan kamar yadda suka saba yi wadansu lokuta,sunayi yana tsokanarta saboda ya fuskanci tamkar bata da walwala,hatta sallar jiya a idanunsa tayi kasancewar shima bai samu isasshen bacci ba,sai goma ya fita yana gaya mata ta shirya bayan sallar magariba idan ya dawo zasu fita.
Qarfe shida ta kammala girkinta ta tsaftace gidan,ta hada kan yaranta ta zuba musu abinci cikin kwano daya,sannan ta kwashe na mai gidan ta kai falo ta jera sannan ta shiga wanka tana gaya musu saura ta jiyo su suna fada,duk wanda yayi fada ba ruwanta da shi.
Tsaf ta shirya cikin wami swiss lace mai matsakaicin kudi cikin kayan sallarta yake,sanyawarta daya wannan ne na biyu,mukhtar akwai qoqari da zuciyar yiwa iyali,sosai yayi mata kyau,ya sake fidda zallar quruciyarta,tana cikin fesa turare ta jiyo yaran na yi masa sannu da zuwa,bai shigo yau da babur din nashi ba saboda zasu sake fita.
Ta fito sanda yake raba musu alewa suna karba suna godiya kana suka yi mata sallama suka fice,haka ta koya musu,da ya dawo ko bata fada ba zasuyi mata sai gobe su tafi saidai idan ita ta tsaidasu,idanunsa a kanta ya bude mata hannayensa ta tako a hankali cikin kunya ta shige cike ya kulleta gam cikin qirjinsa yana fadin
” kinyi kyau my sumy ta”siririyar dariya ta saki cike da jin dadin yadda yake yaba kwalliyarta.
Wanka ya shiga yayi a gurguje saboda qaratowar lokacin sallah magariba,y hada da alwalarsa ya fice,bayan ya dawo ya shirya cikin shadda ruwan bula mai turuwa(dark blue)wanda yayi shige da lace din jikinta,dariya ta dinga ganin yadda yake waqar(munyi anko da anko)irin ta yara.
Gidan yaya yahanasu taga sun nufa,bugawa qirjinta ya dinga yi,bata so ta masa magana yaga kamar tana qin ‘yan uwansa,tunda duk tsiya naka naka ne,sai da ya faka babur dinsa qofar gidan sannan yace da ita
“Idan mun gama da nan gidan mama zamuje ki gaidasu” hakan ne ya dan sake sa mata nutsuwa,”to”kawai tace da shi.
Yana gaba tana biye da shi kamar wadda za’a kama,a tsakar gida suka ci karo da yaron yaya yahanasu wanda bazai wuce shekara goma sha uku ba,ya gaida mukhtar ya amsa yana ce masa
“Jeka qofar gida ka kulamin da machine dina kafin na fito”
“To kawu” ya fada yana ajjiye modar hannunsa saman randa ya fice.
Suna shirin shiga rumfarta tana daga labulen dakin
“Au sai yau kaga damar zuwa kenan……shashan yaro ana maka gata kana noqewa” ta fada tana sakin labulen ta juya zuwa ciki.
Bata lura tare suke ba sai da suka shiga ciki suka zauna,sumayya ta gaisheta ta amsa sama sama,ganin idonta sam bai hana yaya yahanasu yin duk maganganunta ba,ita dai kam kanta ta sunkuyar,daga bisani ta miqe ta basu guri jin musu nason barkewa tsakanin mukhtar da yaya yahanasu kan lissafin abinda suke da buqatar ya bada,kama daga kudin aure kudin zance lefe har zuwa sadaki,yace zaya bada kudin aure da na sadaki amma shikam bazaya iya yin wani lefe ba,kasuwa babu ciniki,nan ta barsu batasan yanda suka kaya ba yadai fito yace ta tashi su tafi.
Ko sallamar da take wa yaya yahanasun bata tanka mata ba har suke wuce,suna kan hanya babu wanda yace da dan uwansa komai har suka qarasa gidansu.
Ciki ya shiga suka gaisa da maman nata kasancewar abba malam mahaifinsu kamar yadda suke ce masa baya nan,’yan qannanta duk suna tsakar gida mukhtar ya raba misu biscuite kamar yadda ya saba,ya miqe zai fice yana cewa zai zaga bayansu gun wani abokinsa idan ya dawo zai kirata su wuce tace tom.
Gaisawa sosai sukayi da mamanta ta tambayi lafiyarta da ta gidanta ta amsa mata da komai lafiya.
Shiru ne ya biyo baya,tunanin abinda ya faru dazun gidan yaya yahanasu yayi nasarar wafce tunaninta ba tare da ta shirya ba,haka maman ta tadda ta,ta ajjiye kwanon dambun data je debo mata
“Lafiya dai ko sumayya” murmushin yaqe tayi ta janyo kwanon dambun tana budewa sannan tace
“Mama aure yaya mukhtar zai qara” maganar ta dan taba maman,tsakanin da d’a da mahaifi,tausayinta ta dinga ji yana ratsata,babu shakka abu ne mai wuya zama da kishiya a wannan zamanin,abu ne da har yau yaqi dadi a cikin gidajen aurenmu,ga yarinyar tata gwanar haquri da shegen zurfin ciki ce,amma duk da haka ta sani ba duka aka taru aka zama daya ba,duk abinda zata gaya mata a yanzu shi zai zame mata madubin dubawarta.
Murmushi maman tayi sannan tace
“Babu komai,ai namiji mijin mace hudu ne,Allah ne ya halasta masa,abinda nake son gaya miki kawai shine kada ki soma cewa zaki tada hankalinki ko ki daga hankalin mijinki,ki zauna da ita tsakani da Allah,ki sauke duk wani haqqi nata dake wuyanki,sumayya kada ki sake kice zaki cuceta,idan kika cuceta sumayya ni mahaifiyarki ban yafe miki ba”.
Kai ta gyada” in sha Allahu mama zanyi duk abinda kika ce,da ikon Allah bazan zama mai sabawa maganarki ba”a hankali maman ta dinga hilatarta tana kwantar mata da hankali har ta kusa cinye dambun baki daya.