KWASAR GANIMA CHAPTER 1 BY FAUZIYYAH D. SULAIMAN

KWASAR GANIMA CHAPTER 1 BY FAUZIYYAH D. SULAIMAN 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Aljani Ya Yi Ciki

ZAINABU yarinya ce kyakkyawa, sarkin kwalliya, Idan za ta fita ta kan shafe awanni ta na kwalliya, don haka kusan duk fitar da za ta yi sai ta yi saurayi, sai dai daga san da ya yi mata maganar aure a nan gayyar za ta watse. Wannan abu ya na damun iyayen ta da duk wani mai Kaunar ta. An ce mutanen Boye ne. Don haka iyayen su ka tashi tsaye wurin nema mata magani, amma abin ya ci tira.
Ran nan kakar ta ta zo da wani labari na wani mai magani ana kiran sa Malam Sharu Mai Rukiyya. Su ka yi sa’ar samun sa, ya zo har gida. Kallo daya ya yi mata ya ce, “Ai wannan yarinyar ta jima da aljanu a kan ta. Kalli yanda ta ke wani gatsine-gatsine! Ai dole sai an yi mata karatu.” Iyayen nata su ka amince.

WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Malam Sharu ya ce amma dole sai kowa ya fita daga dakin saboda idan su ka fita daga kan ta za su iya komawa kan wani. Da kowa ya fita, sai ya garKame Kofa da zummar sai ya Kona aljanun Kurmus.
Haka din kuwa aka yi, don daga inda jama’a su ke su na jiyo kuwwa da ihun Zainabu, abin da ya tabbatar masu da an fara cire aljanun.
Karatun wata guda aka yi za a yi wa Zainabu. Har iyayen ta sun fara murna domin ganin jikin ya fara sauki. Cikin wata biyu har ta tsaida wanda za ta aura, aka saka rana. Malam Sharu kuma ya koma duk wata ya ke mata karatu. Ana cikin haka, sai cikin Zainabu ya fara kumbura kamar an hura balo.
Hankalin iyayen ya Kara tashi. Aka koma wurin Malam. Ya na duba ta sai ya ce, “Ayya! Ai, tanan su ka koma aljanun? A nan su ke mata saka kuma yanzu. Don haka aiki ya dawo sabo.” Haka aka ci gaba da aiki, amma kullum sai Kara hawa cikin ya ke yi. Hankalin iyayen Zainabu ya na kumatashi.
Kwatsam, ran nan sai ga Halima, wata yayar ta da ke aure a Legas, tazo ganin gida tare da mijin ta, wanda soja ne. Su na ganin halin da Zainabu ke ciki sai ta ba su tausayi. Su ka ce lallai sai an tafi asibiti don a tabbatar da abin da ke damun ta. Da farko, iyayen sun yi gardama domin Malam Mai RuKiyya ya yi gargadin ba a hada masa aikin sa da na Bature, ya ce idan an yi haka aikin zai iya lalacewa. Amma da mijin Halima ya dage, sai aka tafi asibitin Www.bankinhausanovels.com.ng
Gwayjin farko da likita ya yi ya ga yaro dan wata bakwai kwance a cikin mahaifar Zainabu cike da Koshin lafiya. Ko da iyayen ta su ka ji abin da ya faru sai su ka hau ta da duka, su na cewa sai ta fadi wanda ya yi mata. Amma ta kasa cewa komai, sai kuka. A Karshe, Halima ta bada shawarar a koma wurin Malam aji wanda ya yi ciki. Ana isa, aka sanar da Malam abin da ya faru. Sai ya kama fadin: “Subhanallahi! Shi kenan, aljani ya yi ciki! Ai shi ne ya yi mata cikin nan, babu tantama. Ai da man sun aure ta tun tuni.” Ran sojan nan ya baci. Ya ciro bindiga daga aljihun sa ya na fadin: “To kuwa yau zan harbe ka kai da aljanin, kowa ma ya huta.” Idan akwai abin da Malam Sharu ke tsoro a duniya, to bayan bindiga da dan sanda ne. Nan da nan jikin sa ya kama rawa. Ya zube a Kasa ya na fadin: “Don Allah ku yafe mini. Wallahi kwadayi ne ya ja mini…!” Www.bankinhausanovels.com.ng
Su ka kama shi sai caji ofis. Ko da jama’a su ka ji labari sai su ka fara tururuwar zuwa. Ashe ba a kan ta ya fara ba. Ashe a duk lokacin da aka bar su a daki da yarinya sai ya fara lalata da ita sannan sai ya fara karatu. Sai ya ce mata idan ta fada wa wani sai aljanu sun kashe ta ita da iyayen ta. Shi ya sa
yaran ba sa iya fada. Daga Karshe dai sai ga Malam kotu ta yanke masa mummunan hukunci.

Ai Ga Irin Ta Nan!

ya na talla, Shaddoji da atamfofi da kuma lesuka ne. Ya zo daidai Kofar wani gidan Kasa, sai wani yaro wanda da alamun almajiri ne ya tsaida shi ya ce, “Wai a cikin gidan nan an ce ka kawo atamfar a ga irin ta. Ka bada har da leshin za a zaba.” Dadi ya cika dillalin. Ya zauna bisa dakalin Kofar gidan, ya sauke kayan. Ya zabo atamfofi masu kyau kala uku da leshi kala biyu ya ce, “Kai masu su zaba anan. Duk ruwan idon su za su sami wacce za ta yi masu.”
Yaron, wanda bai wuce shekara goma ba, ya amsa ya shiga cikin gidan ya kai wa matan, shi kuma mutumin ya na ta zaman jiran sa. Amma bai fito ba, Har mutumin ya gaji ya aika wani yaron. Da ya shiga, bai jima ba sai ga shi ya dawo, ya ce, “Wai an ce wane bangare ne su ka amshi kayan?” Mamaki ya cika shi, ya mike ya na kumfar baki, ya ce, “Ku ji rainin wayo! Ai wadanda su ka turo shi sun sani. Gidan har Www.bankinhausanovels.com.ng bangare nawa ne da shi?” Yaron ya ce, “Malam, gidan gandu ne; bangare kusan goma ne a ciki.”
Cikin hassala, dillalin ya ce, “Ka ga, ka shiga ka ce su fito da shi ko kuma na shiga da kai nana amshi kaya na. Ai wannan rainin wayone!” Ya na rufe baki, sai wani babban mutum ya fito daga gidan, ya tambaye shi da ya ji yana ta masifa, ya yi masa bayanin abin da ya faru. Da dillali yayi masa bayani, sai ya ce, “Ina zuwa, bari na shiga na ji wane Bangare ne su ka amsa.Bayan kamar minti ashirin, ya dawo ya ce, “Duk gidan sun ce babu wanda ya turo wani yaro.”
“Ka ga Malam, kada ka raina mani hankali. In dai yaron ba aljani ba ne to ya na cikin gidan nan, domin ina zaune a Kofar nan ban ga ta inda zai wuce ba. Don haka a fito da shi.” Mutumin ya kalle shi da mamaki, ya ce, “Lallai kai baKo ne a unguwar nan. Shi ya sanya almajiri ya yi maka wayo, domin dai Kofofin gidan nan guda shida ne, za ka iya fita ta duk inda ka so. Amma zo mu shiga na nunnuna maka su.” Ya na ta zagaya unguwa rike da kaya a hannun sa, wasu kumaa kan sa, Ya tura yaron da ke tsaye ya ce da matan gidan kowacce ta koma dakin ta, za su shigo da wani. Ai kuwa da dillalin ya ga tarin Kofofin da za su kuma bullar da kai wasu layukan, sai ya amince lallai an yi masa wayon. Hankalin sa ya tashi matuKa, ya ji kamar ya yi kuka. Mutumin gidan ya dafa kafadar sa ya ce: “Ka yi haKuri ka yi addu’ar Allah ya yi gaggawar saka maka. Yaron da ya ke ganin ya yi maka wayo tabbas wayon nashi mara wayo ne tunda Allah sai ya saka maka.” Da wannan shawara dillali ya haKura ya bi ta Kofar da su ke tsaye wacce ta kuma sada shi da wani layin. Ya na tafe ya na zancen zuci. Daga can gaban sa sai ya hango dandazon jama’a. Kamar ya wuce, amma Sai ya ga ya dace ya je ya ga abin da ake kallo. Ya na Www.bankinhausanovels.com.ng lekawa me zai gani? Yaron nan ne da ya karbar masa kaya, zaune yarike Kafa ya na ta ihu, da alamar karyewa maya yi. Dillali ya kutsa da sauri ya na salati, ya ce: ““Yaro mai wayo, me ya same ka?”
Yaron na ganin sa sai ya kuma rushewa da kuka ya na cewa, “Don Allah ka yi hakuri, na tuba!” Mutanen da ke wurin su kace, “Ka san shi ne? Dillalin ya labarta masu abin da ya faru. Nan su ka dauki salati.
Wani mutum ya ce, “Haba, gudun da ya ke da mamaki. Mai mota ya na ta yi masa hon amman bai gan shi ba har ya kwashe shi ya watsar a gefe, ya kuma gudu. Ashe shi ma macucin ne! To ai ga irin ta nan, wayon naka bai je ko’ina ba. Allah ya kama ka. Sai dai ‘yan sanda su zo su taimaka maka tunda mun tura su zo. Kai kuwa malam tattara kayan ka, ka wuce. Allah ya rufa maka asiri.” Mai kaya ya hada kayan sa ya wuce ya na godiya gaAllah. Da ’yan sanda su ka zo, su ka tambayi yaron makarantar allon su. Cikin kuka ya ce, “Malamin mu ma nemana ya ke yi domin guduwanayi.” Da Kyar ya yi masu kwatancen makarantar tasu. Sai daga baya aka gano cewa wani mutum ne ya koya masa wannan dabara idan ya sato kayan ya kai masa ya saya a banza ya ba shi kudin.

Biyu Babu

TAyi wuki-wuki a kan bencin da ake bin layin ganin likita. Saizazzare idanu ta ke yi kamar mara gaskiya. A sace ta ke kallon hotunan da su ka yi wa ofishin Kawanya, kamr ka ce firit ta zura da gudu. Ban da lugude babu abin da Kirjin ta ya ke yi. “Ka ga dakta, kada ka yi Karya! Ka gaya mana gaskiya wallahi…”Www.bankinhausanovels.com.ng muryar wata Inyamura da aka biyo ta na shirin fita ta katse mata tunanin ta. Da sauri ta mayar da hankalin ta gaba daya kan su.
Likitan ya kwantar da murya ya ce, “Madam, ki kwantar da hankalin ki. Zan sanar da ke gaskiya, amma ki koma ciki don kina buKatar sirri ne.”
“Ka ga dakta, na gane ma, ka bar wahalar da kan ka. Kawai ina jin positive ne.” Nan ta kuma yin hanyar a gigice. Ya ce, “Madam, ki kwantar da hankalin ki. Don kina da wannan ciwon ba wai ya na nufin kin gama rayuwa kenan ba; kina da damar da za ki yi rayuwa kamar kowa muddin kin bi Ka’idojin da likita ya gindaya miki…” Hey likita, ya isa!” ta katse shi da sauri sannan ta kwasa da sauri, ta na fadin, “Wallahi, I won’t die alone!” Gaba daya likitocin da ke ba da shawara su ka yi kan ta, amma masifa ta ke yi ta na cewa, “Daga zuwa karatu sai a shafa mini masifa? Wallahi sai na saka wa mutum dari ni ma…” Sai ta fashe da kuka mai ban tausayi. Ta zube a nan tana birgima. Likitocin su ka yi kan ta, suna lallashi.
Wannan abu ya kuma karya zuciyar wata ’yar budurwa Talatu da ke kan layi ta na jiran tsammani. Sai ta kama zubar da hawaye duk da yake baa yi mata gwajin an tabbatar ta na da ciwon ba. Abubuwan da su ka faru watanni uku baya su ka fara bijiro mata kamar yanzu su ka faru.

*****

Tafe su ke ita da Zainabu daga cikin makaranta, sun nufi dakunan su na kwana, Talatu ce fara cewa: “Kin san Allah, Zainab? Ba zan yarda wannan damar ta kubce mini ba. Zan yi amfani da duk wata dama da na san ina da ita ~ko ta wacce irin hanya ce kuwa — in tabbatar na tsallake wannan jarabawar, domin ita ce Karshen buri na da kuma dama ta na zama mai arziKi a wannan duniyar.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Zainab ba ta yi mamakin jin kalaman Kawar ta ba domin dai idan da sabo ta saba da jin su, don haka ita ba ta gajiya da abin da ta ke maida mata da martani a duk san da su ke irin wannan hirar. Ta gyara riKon littattafan ta, ta ce, “Ni kam ban dauki duniya da zafi ba don na san boko ba shi ne Karshe arziki na ba. Ina neman zabin Allah. Ke ma kuma ina ba ki shawara kamar yanda na saba, ki miKa lamarin ki gurin…”
“Ha! Ha! Ha!” dariyar Talatu ta Katse mata maganar ta. Sannan ta dora da cewa: “Haba Zainab! Kina ganin zan yarda a ce duk wahalar nan da mu ka sha ta wata shida duk ta tashi a banza? Duk Karshen sati ina zuwa gida cikin fararen kaya har an fara kira na da ‘dokta’… Na riga na yanke wa kai na shawarar zan ci jarabawar nan ko ta wacce hanyane. Kin ga tafiya ta ma ni.” Ta kama sauri ta bar Zainab nan tsaye, ta na kallon ta cike da mamaki baki bude.

****

Ana saura kwana daya su fara jarabawar ta isa ofis din shugaban makarantar. Ta Kwankwasa, ya ba ta izinin shiga, ta murda Kofar ta shiga tare da sallama. Ya na ta rubuce-rubuce bisa makeken tebur. Ya gyara tabaran idon sa. Ya na duban ta kallo irin na Kurulla. Ta ce, “Sannu da aiki, Malam.”
Ya yi saurin natsuwa don kada a yi abin kunya. Ya ce, ““Yauwa. Ki na da matsala ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta rausayar da kai cikin yanga da jan hankali, ta ce, “Malam, da man na zo neman taimako ne a kan jarabar da za mu fara gobe. Ina son na haye ne…”
“To-to-to! Na fahimta,” ya katse ta da sauri ya na wangale baki, sannan ya ce, “Wannan maganar ai ba wacce za a yi a ofis ba ce. Ungo nan…” Ya mika mata wani dan kati ya dora da cewa, “Ki je gida na na shaKatawa da daddare ga adireshi nan jikin wannan katin.”
Ta Karba jikin ta babu Kwari. Ya gyara gilas din da ke idon nasa ya na fadin, “Kada ki damu. Kamar kin ci jarabawar nan kin gama ne; tunda ki ka ZO guri na ai magana ta Kare tunda dai ai ni ne shugaban makarantar gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *