UMM ADIYYAH CHAPTER 32 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 32 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 



MUN TSAYA 

Kamar daga sama ta ji muryarsa kusa da ita, sai lokacin ta fahimci a cikin riKonsa take. Matsawa ta yi daga jikin motar, zuwa lokacin Mai-gadin ya ga inda Mai-gidansu ya fito da hanzari, ya nufi motar, don ya san ba lafiya. Wani jijiya ne ya motsa gefen kan Zaid, ya cije haKoransa cikin tsananin tashin
hankali, amma bai furta komai ba. “Ruben, shiga ciki ka kira min Charles.” Mai-gadin ya damki hularsa ta uniform a hannu, da gudu ya shiga kiran shugaban
tsaro na kamfanin. Hannunsa ya sa ya zagaye Umm Adiyya, ya riKeta a jikinsa sosai. “Komai zai daidaita, it’s going to be alright. Mu je ciki ki zauna kafin a duba kin ji? Akwai abinda aka dauka?” Sai lokacin abin ma ya zo mata, da ta duba budadden motarta ko an cire wasu ababen.

ZAMU TASHI 

Lokacin da ta zo sa hannu za ta bude murfin motar, ba ta taba tsammanin ganin sa
a bude ba, ta tabbata garin saurin a rufe Kofar ne mai shi ya manta shi a dan bude kadan bai rufu kirif ba. Daidai lokacin sai ga Charles da Ruben sun iso wurin. LeKa motar da za ta yi ne, ta ga komai a yadda ta bar shi, don ita ba ta da tarkace ma a motar bare ta yi tunanin za su cire wani abu, su C.D Player da komai ba a taba ba. Sai a lokacin gabanta ya fadii, har ta ji cikinta ya Kulle. Sai lokacin abin ya zo mata kanta.
“(Lapton) dina.” Da sauri ta bude Kofar baya, kasancewar yau ta fito da komfutar da take amfani da ita na ofis, ba ta dauki nata ba, a motar ta bari.
Zaid ne ya taa ta, “Bari na duba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Abin mamaki, komfutar tana inda ta bar ta, sai dai zif din jakar a bude rabin hanya. Mr. Charles ina so ka bude duka footage din yau, daga safe har zuwa yanzu.” Bai saurari me zai ce ba, ya rataya jakar komfutar a kafadfarsa, sannan ya rufe Kofar
motar, ya kulle da mukulli. Riko Umm Adiyya ya yi zuwa motarsa, ya bude mata ta zauna tukun, ya bude robar ruwa, ya ba ta tasha. “Kina jin dama-dama yanzu?” Kai ta dan gyada masa, tunda take ba ta taba cin karo da barawo ko dan fashi ba, amma yau ganin an kuskureta, ba Karamin tada mata
hankali hakan ya yi ba. Zaid ya koma Dangaren direba ya tada motar, hannunsa na kan na Umm Adiyya yana ba ta baki, har suka isa gida, a hanya dai ta ji yana magana da wani, ba tantama dan Sanda ne mutumin. Wannan ne ya Kara birkita ta. Ba sai ka sauko ba, na san ka tashi ka bar ayyuka zan shiga ciki.” Kallon da yayi mata ya kusa ya kada mata ciki, tamkar yadda ya faru dazu da ta fuskanci an bude mata mota bayan ba ta nan. Dole ta hakura, ya rakata har cikin dakinta kamar Karamar baby. Sai da ya kunna mata ruwan wanka, ya kunna A.C din dakin, duk da a damina ake wurin akwai zafi,
sannan dadin Karawa ga halin da take ciki. Ya sauka, ya sa Innayo ta kawo mata abinci, sannan ya ce, “Ki kwanta ki huta, ki zauna kuma kusa da wayarki, idan kin ga lambar da ba ki sani ba, kar ki dauka, na yi
magana da ASP zai yi arranging security a nan gida da gidan Abba.” “Gidan Abba?” Kar ki damu, ba abinda zai faru Inshaa-Allah,” Ya fada hade da sumbatarta a hankali, ya shafa gefen fuskarta, sannan ya fita ya bar ta, za tayi masa magana ne akan komfutarta da ya manta bai ba ta bane, ta ga ya fice da ita, har da gyara zaman hannun a kafadarsa, wannan yana nufin yana sane da jakar kenan. Hasbunallahu Wa ni’mal Wakeel.” Umm Adiyya ta furta a hankali. Tabbas suna cikin matsala gagaruma tsundum!
Ta idar da sallar la’asar kenan, wayarta ta shiga Kara, sai da ta ga sunan da ke kai, ta tuna da cewa tana da baki, shaf! Ta manta saboda tsabar tashin hankalli. “Hello sorry ina sallah.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ni ma dai na ce. Na yi ta kira ai, gamu nan mun shigo layin, ko za ki Kara fada masa address din, ni kam na mance.” “To shi kenan, ba shi wayar.” Tana rufe baki, ta ji wani azababben suka ya ziyarce ta, har sai da ta durkushe Kasa. Ya dauki sakanni kafin ta samu sukunin magana, haka dai har ta gama kwatanta
masu gidan, ashe ma suna kusa da wurin, rashin sani ne, wanda ya fi dare duhu. Don haka nan da nan suka iso. Yaron Mai-gadinsu, Rabilu wanda yake masu share-sharen waje da babban falo ne, ya Karaso da su Takiyya ciki, ba Karamin farin-ciki suka yi da ganin juna ba, nan falon Yaya Zaid ta masu masauki.
“Hajiya kin san ku mata kwatancen ku sai a hankali, ashe tuntuni muna ta wuce ma Kofar gidan.”
Umm Adiyya ta cije, ta yi dariya, “Ka san dama Madam din taka sai a hankali, ba ta gane wurare, bare kwatance, ka ce mata gabas, sai ta yi yamma.”
“Yo komin gane wurina kam, ai ya halasta na bata a Abuja.” Suna dariya cikin raha, aka gaisa ta gabatar masu da wurin sallah da abinci. “Shi ma ya kusa dawowa, wani abu ne ya taso, ya Kara ma fitar. Ko za ka jira shi Uncle Ahmad?” “A’a zan dai shiga gari na yi sabgogina, da dare sai na zo mu gaisa da shi In shaa Allah.” Takiyya ce ta kula da gumin da Umm Adiyya take yi, duk da sanyin iyakwandishon dake falon, ga shi lokaci zuwa lokaci tana cije leBe. “Friend, lafiya kuwa na ga kamar ba kya jin dad?”
Murmushi ta yi ta ce, “Lafiya Kalau, kawai ciki na ke dan murda min. Amma idan na sha ruwa zai daina.”
Ta fada hade da daukar robar ruwa a hannunta, tana budewa. TaKiyya ta kalli Mai
gidanta ta ce, “Tsaya dai kar ka tafi, ni fa ina ga ba ta da lafiya ne tun shigowarmu take dauriya. Bari mu nemi Yaya Zaid din dai.” Nan ne ta karbi lambar wayar Zaid a wayar Umm Adiyya, don zuwa lokacin dauriyarta ya ma soma Karewa, hawaye ke bin fuskarta. Abu kamar wasa ciwo gadan-gadan! Ba shiri Takiyya ta shiga ta samu Innayo, “Zamu kai ta asibiti, ba ta da lafiya.” Dama Umm Adiyyan da hijabinta a jikinta, don haka takalma kawai Innayo ta bayar nata, sannan Takiyya ta gyara nata Www.bankinhausanovels.com.ng mayafin. Ba su ma tsaya jiran isowar Zaid ba. Ahmad ya kai su asibitin da ta fada masu tana zuwa, wanda yake kusa da unguwar nasu. Tunda Zaid ya samu wayar TaKiyya hankalinsa ya yi Kololuwar tashi, nan take ya kira Maami ya fada mata, abinda ake ciki, akan su hadu a can asibiti.

**********?

Karar fankar falon karban bakin ne yake aiki, sai maganganun da yake ji daga can nesa na akwatin Talabijin da ke manne a saman bangon falon. Lokaci zuwa lokaci yana jin takun wucewar ma’aikatan jinyar, yayin da za su je bayar da allura ko magani wa marasa lafiya. Yatsunsa ya sa ya shafo cikin idanunsa wadanda barci suka Kauracewa, ba yadda
Maami ba ta yi da shi ba akan ya je gida, amma baya tsammanin zai samu natsuwa koda yana gidan ne. Duk da kasancewarsa a nan ba zai cirewa Umm Adiyyarsa
ciwon da take ciki ba, daga zuwanta asibitin, zuwa yanzu an ba ta maganin rage zafin ciwo, an kuma sa mata Karin ruwa. Su Takiyya ma dazu suka wuce gida da Maami. Aunty A’isha ce akan Umm Adiyyan, har yanzu dai ba su fadi me ya janyo mata ciwon ba, amma sun dai masu bayanin akan barazanar ficewar cikin jikinta, wanda a yanzu ya kai watanni hudu.
Baya son ya tuno halin da zai shiga, in suka rasa wannan cikin, amma haka nan baya ma ko kwatanton abinda zai fuskanta, muddin wani abu ya samu Adiyyarsa. Lokacin da ya ganta kwance magashiyyan akan gadon asibitin, ya zaci zuciyarsa ce ta tsaya, saboda yadda komai ya masa dif! Bai taba ganinta cikin mawuyacin halin da take ciki ba.
Nan take ya ji ashe duk yadda hankalinsa ya tashi game da matsalolin wurin aiki, baiyi kwatankwacin abinda yake fuskanta a lokacin ba, na bugun zuciya. Fatansa daya. Allah ya ba su lafiya baki aya.
Ya san tana tare da gajiya sosai, sannan ga yadda hankalinta yake tashe kan abubuwan da suke faruwa, amma Allah kadai ne masanin abinda ya haddasa mata
wannan ciwon. Yanzu dai Likitocin sun ce za su Www.bankinhausanovels.com.ng riKeta su kula da ita akan hutun zama wuri guda,
idan an ci sa’a komai ya daidaita, shi kenan sai ta koma gida.

*********

BABI NA ASHIRIN DA HUDU

“Ta farka.” Muryar Aunty A’isha ce ta zaburar da shi, a hanzarce ya mike ya bi bayanta zuwa dakin da Umm Adiyya ke kwance. Gaba daya wuni guda kacal! Amma har ta fada, riko hannunta mai daurin ruwa cikin nasa guda ya yi, yayin da ya sa daya hannun ya shafi gefen fuskarta. “Twinkle, yaya ki ke ji yanzu?”
“Da sauki, Alhamdulillah.” Ta fada a raunane, sai da ya ji abu ya matse masa zuciya. “Ya-Salam, kin ba mu tsoro. Tun yaushe ne ba ki da lafiya?” Jiya ne fa kawai na dan fara jin ciwo, sai kuma last week na ji suka dai haka sau daya.” “Shi ne ba ki fada min ba?”
Juya idanunta ta yi kadan, “Ka yi hakuri, ya wuce ai. Yanzu kam da sauKi, ina su Takiyya?”
“Ta je gida da Maami, ki yi shiru, ki huta sosai, Allah Ya ba ki lafiya.”” “Ameen, ba ka je gida ba? Ta fada tana kallon farar rigarsa ta suit, wacce har
lokacin ita ce a jikin sa, ya cire kwat din ya nade hannun rigar zuwa gwiwan hannu, ba tantama, saboda alwala. “Eh, ina na ga ta zuwa wani wuri, bayan ga gidana a nan. Uhm? Sleep well, ina nan
a kusa da ke, ba inda zan je.” Kanta ya shafa, lokacin da ta Kara lumshe idanunta. Ta budesu a hankali. “Bari na yi sallolina tukun, sai na yi barcin.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“To ina zuwa.” A hankali ya ajiye hannunta, sannan ya bulla Kofar cikin dakin wanda bandaki ne. Dawowa ya yi dakin ya ce, “Za ki iya tashi?” Kai ta gyada masa, don haka ya sa hannu ya zare mata  din da ke manne a hannunta, ya rataye shi. Sannan ya taimaka mata, ta sauko daga kan gadon. Ji yake yi tafiyar ma tamkar ya yi mata da kansa, saboda duk hanzarin ta, yau ta koma tafiya kamar mai koyo, saboda ciwo.
Sai da ya yi mata alwala da kansa, sannan suka fito daga bandakin. Aunty A’ isha dai shigowa ta yi ta ganta a zaune kan sallaya tana sallah. Murmushi ta yi ganin yadda Zaid ya kasa, ya tsare, yana bin duk wani motsi na matar ta sa. Ba tantama kallo daya za kai masa ka san yadda ya damu Kwarai da ita. Hakan ya cika mata zuciya da dadii. “Zaid, ai da ka je gida kai ma ka samu hutu, sha biyu fa yanzu, ga aiki gobe, kar rashin hutun yai maka illa.” “Ba komai Aunty A’isha, bari na barku ku kwanta.” Ya san ya takura ta ne, idan banda haka ba, abinda zai matsarsa daga gangan Twinkle dinsa.
Sai da ya ga ta sha farfesu, sannan ya bar dakin hade da masu sai da safe. Koda ya je gidan ma, baccinsa kadan ne, don ana Asuba ya shirya ya Kara fitowa. Nan ya tarar da Abba ma a gate, shi ma ana sallar ya yiwo asibiti, sai dai sam ba yadda ya yi fatan samun Twinkle dinsa ya sameta ba. Tana cikin mawuyacin hali sosai. “Ai tun fitarka, a nan jiya kuma dai sai ta birkice, ciwo ya Ki ci ya Ki kicinyewa. Yanzu dai Likitan ya iso, ya ce za su Kara yin hoto, don a ga menene.” Aunty A’ isha ta shiga masa bayani. Salati kawai yake yi a zuciyarsa, shi dai fatansa daya kar wani abu ya samu Umm Adiyyarsa. Likita na zuwa ya hau gwaje-gwajensa, nan ne yake shaida masu cikin fa ya lalace, dole a cire mata shi muddin ana so ta samu lafiya, don ko an bar shi, sai
dai ta yi ta shan wahala.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *