KWASAR GANIMA CHAPTER 2 BY FAUZIYYAH D. SULAIMAN

KWASAR GANIMA CHAPTER 2 BY FAUZIYYAH D. SULAIMAN

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 



MUN TSAYA 

Ana saura kwana daya su fara jarabawar ta isa ofis din shugaban makarantar. Ta Kwankwasa, ya ba ta izinin shiga, ta murda Kofar ta shiga tare da sallama. Ya na ta rubuce-rubuce bisa makeken tebur. Ya gyara tabaran idon sa. Ya na duban ta kallo irin na Kurulla. Ta ce, “Sannu da aiki, Malam.”
Ya yi saurin natsuwa don kada a yi abin kunya. Ya ce, ““Yauwa. Ki na da matsala ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta rausayar da kai cikin yanga da jan hankali, ta ce, “Malam, da man na zo neman taimako ne a kan jarabar da za mu fara gobe. Ina son na haye ne…”
“To-to-to! Na fahimta,” ya katse ta da sauri ya na wangale baki, sannan ya ce, “Wannan maganar ai ba wacce za a yi a ofis ba ce. Ungo nan…” Ya mika mata wani dan kati ya dora da cewa, “Ki je gida na na shaKatawa da daddare ga adireshi nan jikin wannan katin.”
Ta Karba jikin ta babu Kwari. Ya gyara gilas din da ke idon nasa ya na fadin, “Kada ki damu. Kamar kin ci jarabawar nan kin gama ne; tunda ki ka ZO guri na ai magana ta Kare tunda dai ai ni ne shugaban makarantar gaba

ZAMU TASHI 

daya.” Maganar sa ta Karfafa mata gwiwa. Tace, “To Malam, na gode.” Ta fice ta na ta saKe-saKe a zuciyar ta, Ba ta sanar da Zainab ba, don haka ma da daddare ta yaudare ta a kan ta tafi karatu na Kungiya ne. Zainab ta ji dadin hakan, don ta san Kawar ta ba ta son karatu a da. Ta na ganin kamar shawarar da ta ba ta ce ta fara aiki.

*
Ta je gidan nasa kamar yadda ya buKata. Ya yi mata alKawarin cin jarabawar kamar yadda ya fada mata tun da farko. Ya amshi sunan ta da lambar ta ta makaranta. Sannan ya yi mata irin abin da ya saba yi wa masu hali irin nata wadanda su ke ganin sai sun yi karatun boko ko ta halin Kaka ne.

*
Wata guda su ka kammala zana jarabawa. Sam, Talatu ba ta yi karatun komai ba, don ta na da tabbacin ta haye daga majiya mai tushe. Sai dai kullum ta sharbi barcin ta har da saleba, duk da yake Zainab ta na mata fada. Sai ma fada da su ka yi daga Karshe. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan wata uku da zana jarabawar tasu aka kafe masu sakamakon a allon sanarwa. Dalibai su ka yi cincirindo kowa ya na duba sakamakon da ya samu. Da Kwarin gwiwa Talatu ta isa wurin domin dai ta san kawai ta ci ta gama ma. Sai dai ga mamakin ta, sunan ta ya na jerin sunayen wadanda makaranta ta kora saboda rashin tabuka komai da su ka yi. Ran ta ya baci matuKa. Ta ji kamar ta fashe da kuka, sai dai don kada ta tona wa kan ta asiri ya sanya ta danne don dai lamba ce ba suna ba. Ta bar wurin, ta yi kukan taa gefe.
Sai dai ta yi taku biyu kafin ta yi na ukun ta ji muryar wasu dalibai su na hira. “Allah sarki, Ruky! Kin ga ’yan shekarar farko su na duba jarabawar su. Gaskiya bana an yi ragargaza ba kamar shekarar mu ba.”
Wacce aka kira da Ruky din ta ce, “Bari ke dai, Jamila. Ni wadanda su ka yi biyu babu ne su ka fi ba ni tausayi, don na san shegen malamin nan mai idon ’yan iska sai ya lalata wasu kamar yanda ya saba…”
Jamila ta ce, “Bari ke dai! Ni takaicin ma daya ne: shegen ciwon da ya ke
dauke da shi duk wacce ya lalata sai ya goga mata. Uhm! Allah dai ya kyauta.” Su ka wuce su na hirar su.
Talatu ta kuma shiga tashin hankali saboda jin abin da su ka fada, har ta ji gudawa da fitsari sun cika mata mara. Ta yi bandaki da gudu. Ai kuwa ta na fitowa kai-tsaye cikin asibitin da ke jikin makarantar tasu ta nufa don a duba ta ko ta sami guzirin ita ma.

*
“Malama layi ya zo kan ki,” wata murya ta katse mata dogon tunanin da ta shiga. Kasa motsawa ta yi sai ido kawai da ta Kura wa matar. Ganin kamar ba a cikin hayyacin ta ta ke ba ya sanya ma’ aikaciyar jinyar ta kama lallaba ta har aka samu ta shiga dakin dibar jinin, aka debi jinin ta, aka fara gwadawa. Wata gudawar ta kuma matsar ta, ta miKe da hanzari ta shiga bandakin da ta ga marasa lafiya su na shiga. Bayan ta dawo ta Kura wa ’yar madam din nan da ke ba da shawara ido. Www.bankinhausanovels.com.ng
Lokacin da aka yi kiran ta don ba ta sakamakon ta da za ka tsaga jikin ta ba zaka tarar da jini ba saboda tsabar shiga tashin hankali. Sa’ilin da ya fara yi mata bayanin cewa jinin ta ya nuna tana dauke da cutar Kanjamau, sai kawai ta fasa ihu ta dafe kai tana kururuwa ta na fadin: “Na shiga uku ni Talatu! Na yi biyu babu: babu cin jarabawa, ga kuma ciwo alaKaKai da na ja wa kai na. Na cuci kai na! Ashe gaskiya Zainab ke gaya mini, ga shi ita ta ci jarabawar kuma ta na zaune lafiya. Wayyo Allah na! Me zan ce da iyaye na?” Likitocin su ka yo kan ta don lallashi kamar yadda su ka saba, don duk kusan wanda ya fara jin yana da ciwon sai ya yi irin haka.

CAJE HAR LIMAN

TUN safe ya ke kan layin tantance ma’aikatan. Yau kwanan sa uku kenan ya na zuwa, amma ba ya samu saboda yawa da cikowa. Ga shi yau kwanan sa hamsin da daya babu albashi, sai yau aka yi, idan kuma ba a tantance ka ba ba za a ba ka albashi ba. A wannan tsukun matar sa ta haihu, sai bashi ya ci ya yi hidimar suna da sauran buKatun gida. Don haka ko ya amshi kudin kashi bakwai cikin goma na biyan bashi ne. Don haka ya ke ta boyewa, kada wanda ya ke bin sa bashi ya ga ya amsa ya ce sai ya ba shi.
Bai sami damar an tantance shi ba sai shida da mintina na yamma. Ya amso kudin sa ya zuba aljihun gefen rigar sa domin ya fi fadi. Sai dai me, ya na ta raragefe zai wuce sai ya ji an Kwala masa kira: ‘““Malam Kalla!
Ko bai waiwaya ba ya gane muryar mai kiran. Malam Mudi mai kawo masu bashi ne. Ya ja dogon tsaki. Kamar ya zunduma da gudu ya ke ji. Malam Mudi ya ce, “Yaya za ka wuce ba ka neme ni ba, bayan ka san ina nan ina jiran a bai wa kowa ya biya ni kudi na?”
Ya yamutsa fuska, ya na riKe ciki, ya ce, “Ba tafiya zan yi ba; bayan gida zan zagaya. Bari na fito…”
Malam Mudi ya bi shi bakin bandakin, ya tsaya ya na jiran fitowar sa.

*

Malam Kalla ya yi tsaye a bandakin, ya na shirya yadda zai yi. Can sai ya hango wata taga Katuwa. Da sauri ya Karasa, ya cire gilashin, ya dirga, ya fice a guije. Malam Mudi kuwa ya na tsaye, duk wanda ya zo ya ce, “Ai da mutum a ciki.”’ Mutane su ka gaji da jira, don haka aka fara buga Kofar. Amma shiru ka ke ji. Malam Mudi ya yi dariyar mugunta ya na fadin, “Wai so ya ke na gaji da jira na yi zuciya na tafi. Wallahi ko kwana zan yi anan sai ya fito!” Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga Karshe dai aka tura Kofar, sai bandakin wayam. Ran Malam Mudi ya baci, ya tafi ya na ta masifa kamar zai ci babu.
Shi kam Malam Kalla, tun da ya kwasa da gudu bai tsaya ko’ina ba sai a bakin titi, wanda da babur zai hayo sai ya biya murtala biyu. Ya na isa ya ga ana ta dambe wurin shiga mota, ya shiga shi ma ana yi da shi. Amma bai samu wuri ba. Ya dawo baya ya na jiran wata. Can, ya jiyo ana kiran sallar magariba, ya ce gara ya je ya yi sallah domin kafin ya Karasa gida lokaci ya Kure. Ya daura alwala ya shiga masallaci aka fara sallah da shi. Sai dai sa’ilin da mutum ya ke yin ruku’u, wurin miKewa tsaye hannun sa ya kan dan daki cinyar sa. Sa’ilin da nasa hannun ya daki cinyar sa sai ya ji bai ji tudun kudin sa ba. Ya kuma shafawa, ya ji wayam. Nan da nan ya ce, “Assalamu alaikum!” Ya kama cajejikin sa, bai ji komai ba. Ya koma bakin Kofa ya tsaya. Cikin daga murya ya ce, “Kan uban nan! Kudin nan da na samo su da Kyar? To wallahi ku idar, acaje har Liman!”
Wadanda ke sallah kowa ya shiga dar-dar, sun Kosa su idar. Su na zaton ko mahaukaci ne. Ana kammalawa, Liman ya ce, “Bawan Allah, me aka yi maka na ji kana cewa caje har da liman?” “E! Na kuma maimaitawa, a caje har Liman. Haka kawai kusan wata biyu kenan ina fama da jarabar talauci, na samu na amso kudin yanzu ku sace mini…?”
“Ka ga, bawan Allah, ka nutsu. Ka na shigowa aka tada sallah. Ta yaya za a dauke maka kudi? Daga ina ka taho mana nan?” Daga amso kudin ban tsaya a ko’ ina ba sai nan. Sai dai gurin turereniyar mota da na tsaya ban samu bana yo nan.” “To ka ji inda aka sace maka kudin kagurin turereniya!”
Ya yi jim, ya na tunani. Sai kawai ya fashe da kuka, ya na fadin: “Na shiga uku! Da na sani na biya Malam Mudi kudin sa ma!” Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan dai jama’ar Annabi su ka tara masa kudi. Sai ga shi ya samu abin da ya haura albashin nasa ma. Daga nan kuwa ya ce, “Sai gidan Malam Mudi, don watakila hakkin sa ne ya ja mini haka. Don ma Allah ya tarfa wa garina nono!”

GARIN NEMAN GIRA…
INA zaune a tsakar gida na hada uban tagumi. Tunanin inda zan sami kudin da zan yi gyaran daki na kawai na ke yi. Jimmala Facalata a satin nan ta sauya kayan dakin ta, ga shi ni da ita ba ma shiri; duk wanda ya sauya wani abu sai dayan ya yi shi ma ko ta halin Kaka ne kuwa don kada a yi maka gori.
Can sai na jiyo hargowa da ihun yara a Kofar gida. Ai kuwa na mike na runtuma da gudu, don da a ba ka labari gara ka bayar.
Na tokare a jikin Kofar gida, rabin jikin ya na waje yayin da rabi kuma ke cikin soro. Daga inda na ke na hango wani bakule, irin masu tallar magungunan nan wadanda ke yawo da bantai na fata da layu a jikin su, suna ihu da wata irin busa, su na ba da magani.
Daga nan na jiyo ya na fadin, “Mu na ba da maganin ciwon daji! Mu na ba da maganin sanyi! Mu na ba da maganin mallaka, dana sammu, dana…”
“Laa! Shi kenan faduwa ta zo daidai da zama,” na fada a fili. Ina ganin hanyar warwarewar matsala ta ta zo kenan. Na dinga yafuto bakulan nan har dai na aika yara. Da ya iso inda na ke tsaye, na gyara tsayuwa ta na ce, “Malam, da man wata matsala ce da ni. Ka ga ina So miji na ya ba ni kudi na sake kayan daki, ga shi shi din tsumulmula ce da shi.” Ya fashe da dariya, ya ce, “An gama, yarinya! Amshi nan.”
Ya miko mani wata laya da ke sagale a Kugun sa. Ya dora da cewa, “Ki ba da kayan sakawar ki kala biyu da naira dubu uku. Idan ya dawo ki matsa ta a hannun ki na hagu. Duk abin da ki ka ce ki na so sai ya yi maki, na tabbatar maki da izinin Barbushe… Ha! Ha! Ha! Ko da rijiya ki ka ce ya fada kuwa sai ya fada.” Na yi dan jim ina tunani don ba ni da ko kwabo sai kudin adashi, wanda gobe da safe ne dauka kuma. Amma tunda dai a yau maigida na zai iya bani sama da haka ma, idan ya ba ni sai na sanya masu kawai. Don haka na yanke shawarar cewa kawai na daukaa cikin na adashin. Na kawo wa dan ’yar mai ganyen nan, ya Kirga, ya ga sun cika cif. Ya yi murmushi ya na fadin: “Bayan kwana uku zan dawo, sai ki gaya mani yadda
ku ka yi da shi.” Ya sa kai ya yi tafiyar sa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sa’ilin da maigida na ya dawo ina tsakar gida a zaune. Na yi daurin ‘ture ka ga tsiya.’ Ko sannu da zuwa ban yi masa ba balle ya sanya ran zan karbi jakar ledar da ke hannun sa ba. Sai ma bin jakar da na yi da harara don na san ba zai wuce tarkacen mangwaro da su ayaba da lemo ba, don aikin sa kenan; shi ba ya ba da kudi kamar Sabo mijin Facalata, wanda ya ke ba ta kudi masu yawa ta na zuba adashi. Ita sai ta ga dama ta ke girki ma sai kawai ta jiKa masu kwakwi su sha tare da ’ya’ yan ta.
Bayan maigidan nawa ya zauna, na kawo masa abincin sa, ina wani fisgefisge. Ya dube ni ya ce, “Yaya dai? Lafiya ko?” Na yamutsa fuska na ce, “Kalau.” Na wuce cikin daki. Sai da ya kammala cin abincin na fito na zauna ina duban sa. Na matse layar nan a hannu na. Can nace, “Alhaji so na ke ka ba ni dubu hamsin.”
“Dubu hamsin kuma Salame?” ya tambaya da mamaki.
Na kuma matse layar, na kuma shan kunu, na ce, “E! Haka nace.” Ya yi wani murmushi ya ce, “Lallai Salame yau dai raha ki ke ji kenan.”
Na kuma matse layar Kam na ce, “Wane irin raha kuma? Da gaske fa nake. Ko dubu arba’in ko talatin ka ba ni to.” Na rage buri ko kudin ne su ka yi yawa.
Ya ce, “Don Allah ki bar wannan wasan. Ni yanzu idan na sami kudin da ki ke magana ma ai jari zan Kara.” Na kuma hade rai ina fadin, “Kai ta shafa! Ni kam wallahi yau sai ka ba ni kudin nan ko kuma rai ya baci.” Na kuma matse layar har hannu na ya na digar da gumi saboda tsabar matsa. Kai, in taKaice maku labari, tun Alhaji ya na dauka da wasa na ke har ya yarda lallai da gaske na ke yi. Don haka ya koma ya na lallashi na ya na cewa: “Salame, kin san ba ni da wannan halin. Da ina da shi me zai hana in ba ki?”
Ganin ya na lallashi na yarda lallai laya ta fara aiki, don haka na dage wallahi sai ya ba ni, har dai abin ya zame mana rigima. Daga Karshe na ce, “Wallahi in dai ba ka ba ni kudin nan ba sai dai na tafi gidan mu.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Babu wata damuwa a tattare da shi yace, “Sai kin dawo.” Na jawo gyale na a kan Kyaure babu ko dar, don nasan sai ya biyo ni ya ba ni haKuri. Na nufi hanyar soro. Abin mamaki, har na kai Kofar gidan uba na bai biyo ni ba. Duk da haka ban karaya ba, na shiga. Har yamma ina ta matsa laya; kai, har washegari da mahaifi na ya tambaye ni. Nace, “Duka ya yi mani yace na tafi gidan uba na.” Baba na ya ce in zauna tunda dai shi maigidan nawa ne ya ce in zauna. Na share wuri na zauna har tsawon kwanaki babu Alhaji. Daga Karshe na yi cilli da layar nan don dai na tabbar cuta ta aka yi. Ga masu kudin adashi sun dame ni. Daga Karshe ma na ji labarin Alhaji ya daura aure. A ranar na dinga kuka, ina fadin, “Shi kenan, garin neman gira na rasa idanuwa!”

HMMM WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *