NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Salmanu ya ga Adamu na gyara wajen kwanciya zai kwanta, ya ce masa, “Ni fa ban gane maka ba”. Adamu ya dago cikin rashin hayyaci ya dubeshi,
“To hayatu, ina fatan ba wani daga hankalin zaka yi min ba…” “Haba sai na sake daga maka wani hankalin ban da wanda kake ciki?” Adamu ya dan yi nishi, “Hnm!” Sannan ya mayar da kai ya kwanta. Salmanu yace, “Allah sarki, yanzu kiyayyar Husna ta shafi Salma kenan? Dalilin kin Husna ka zabi ka kauracewa Salma ma?”. Adamu yayi shiru bai tanka ba, amma fuskarsa tana nuna alamun rauni. Sun jima cikin shiru dukkansu, sannan babu zato babu tsanunani suka ji Adamu na shasshekar kuka. Tanimu da Salmanu suka dubi juna, cikin su babu wanda ya tanka. Sai da Adamu yayi abinsa ya ishe shi sannan ya dago ya dubi Salmanu, “Wai wa yace maka ba na son Husna ne?

ZAMU TASHI 

Salma ce bata son ta, ina tsoron zuwa gidan ta yi min umarnin in sake ta”. Dukkansu babu wanda tausayin Adamu bai dake shi ba, Tanimu ma da ba shi da saurin hawaye yau sai da ya ji shi, a yau ne kuma ya Kara gasKata cewa sihiri ne ke dawainiya da Adamu, in aka yi la’akari da yawan kukansa da sauye sauyen maganarsa. Ko jiya ya ci layar ba ya son Husna, amma ga shi yau yana kuka yana fadin shi yana sonta kuma ya Ki zuwa gidan ne don kar a yi masa umarnin ya sake ta. _ _ Duk kaifin basirar Salmanu yau ya rasa abinda zai cewa Adamu, ya kuma kasa gane ta inda zai ‘murde wannan jumurdar, wadda zata tserar da rayuwar Adamu ta kuma Www.bankinhausanovels.com.ng tserar da Aurensa da  masoyiyarsa. Bai iya komai ba sai bugun kafadar Adamu cikin sigar rarrashi, Oh, na fahimce ka, kwanta zuwa safiya zan yi tunani”. . Adamu bai yi wata-wata ba ya kwanta. ; .

*********

A ranar da Adamu ya fice, gidan babu wanda bai yi kwanan tashin hankali ba, duk da Husna ba ta san hakiKanin abinda ke akwai ba, ranta ya raya mata gaskiya lafiya ba zata samar da abinda Adamu yayi ba. Sai dai ba ta‘yi wan yunkuri ba ko da na neman ba’asi ne a wajen Salma sai ta cigaba da kafa goshinta a Kasa tana kai wa Ubangiji kukanta cikin tsananin rauni. Ta bar Salma da zirga-zirga a tsakar gida zuwa falo, bayan a tsorace ta silala ta rufo musu gidan da Adamu ya bar musu.a bude
Har safiya babu Adamu, da sassafe ta yi waya gida ta sanar da Sa’a, tare da sanar mata abinda ya_ fari A gigice Sa’a tace“To yi shiru kar a yi gaggawar sanar da Alhaji”. , : Cikin damuwa Salma tace a  “Saboda me Anti?” Muryar Sa’a babu dadi tace “Jiya ya kama ni ina binne layun nan masu Karin kunama a gindin turmi, ban taba ganin bacin ransa ba irin na jiyan nan, har yake ce min in dai wannan ce dabi’ata to yana min bushara da zamowa makamashin wutar jahannama?
Salma ta toshe baki tana toshe Karar da tsoronta ya haifo,Mun shiga uku! Yanzu ba’a binne layun ba? Kina nufin in Adamu ya sami dama zai iya shiga dakin waccan tsinanniyar ya kwana? Na _ shiga uku…”
Sa’a tace“Ke kar ki yi min shirme don Allah, ke ba ki kula da hatsarin da na shiga bane?”. A raunane Salma tace “Na fi ki shiga hatsari Anti, in har Adamu ya karbi waccan matar a matsayin matarsa, to ni zai iya mayar da ni‘ fiye da kare a KasKanci, wallahi ‘yar duniya ce Anti. Sa’a ta ce, “Ai kece da abin haushi, ba ki ko yi min jajen nawa mijin ya kama ni da abinda bai kamata ba saboda ke har ma yana tunkuda ni wuta, kuma ki hau tuhuma ta..Salma ta yi ajiyar zuciya tace “Yi haKuri Anti, hankalina ne a tashe, kin ji ta can ta tashi taci uwar kwalliya ta hau keken dinki tana ta faman cika min kunne ta ga fa Adamu jiya, kuma ta san fitarsa a hargitse amma ta tashi tana nuna ko a jikinta…” Shegiya tsinanniya ba!”
In ji Sa’a, sannan ta dora da cewa, “Na samu na tone layun na canja musu matsuguni bayan alhajin ya kauce dole mu jira mu ga kuma abinda zai faru”.Www.bankinhausanovels.com.ng Salma ta yi ajiyar zuciya, To yanzu menene mafita da fitar da Adamu yayi har yau bai dawo ba?”Sa’a ta dan jima cikin shiru sannan taceKi jira dawowarsa kar ki sake Alhaji ya ji a bakinki, sannan idan ya dawo kar ke ki yi masa maganar ya saki matarsa don kar a zo bayar da bayani sunanmu ya fito ni da ke bare har Alhaji ya kafa mana hujjar mu muka yi asiri muka kore ta sabo da binnin da ya ga ina yi, ki jira tasu ta hado su ko. kuma kunamun da za’a zuba mata a daki mu samu daya ta harbi shegiya ta margaya kowa ya huta”Salma.ba don ranta ya so ba ta karbi wannan shawarar, don ita dai ba ta da wani kwanciyar  hankali wanda ya wuce ta bude ido ta ga dakin –
’Husna yana rushe, musamman kitchen din can da
« aka nuna mata iyakarta a kansa, ko yaushe ta fito ta kalle shi sai ta ji tana neman hadiye zuciya ta mutu. – . A haka suka wuni har dare ya shigo, Husna na tsananta Karfin hali yadda babu wanda ya fahimci cikin damuwar da take, alhalin can cikin zuciyarta kamar ana shirin gobara. Duk da abin na damunta ta ji kamatar adana sirrin gidanta, ba ta kira bokanta ba, kuma bata kira Abokin Adamu Salmanu ba, ta yarda a ranta wannan wahalar da take sha tana cikin jarrabar ubangiji: da idan ta jure ta kadaita Allah za’a rubuta mata lada. A haka suka kwanta bacci suka sake wayar gari babu. Adamu. Da hantsi salma ta gama zuwa wuya da yadda Husna ke watsar da lamarin, tana ta sabgarta da shige da ficenta cikin kwalliya da hidimar girki, sai ta bi ta har kitchen dinta ta sameta, cikin kumbura fuska tace, — “Wai ke Malamia me kika yi wa Adamu kika firgita shi, na san Kinsan ya dawo yanayin arba da ke _ hankalinsa a tashe ya‘ fice daga gidan nan gashi har yau babu labarinsa, kin sani kuma kina cigaba da harkoki.. Babu wani jirikiri Husna ta sami amsar bata, “Kai haba! In ke baki firgita shi ya zabura ya . arce ba, ai ko a mafarki ba za’a nuna gani na ya firgitashiba”, Salma ta fahimci inda ta dosa, abinda kuma ya Kara Kular da ita kenan, ta shiga fadin maganganu, To mu dai ba ki shigo mana gida da Kafar dama ba gaskiya..Husna ta dan daga mata hannu, ~ “Don Allah in dai ba ki ga na yi miki kama da karya ba ki ja sawayenki ki Bace min da gani, na iya haushi ba wai ban iya ba, amma ina yi da abokan burmi nane ba irinsu ‘yan kwikuyo ba, kin gane? Ni ina da aikin yi da kuma sabgar da ta fi haushinki muhimmanci, ki je an ji da Kafar hagu na shigo, ke – ce baki da Karfin jini tunda Kafar damanki ta kasa Boye ta haguna ”.
********
“An sake kwana guda kafin Salmanu ya sa bakin roKon Adamu ya waiwayi gida, yayi wannan dabarar ne ta dakatar da shi inda ya dinga matsa _ masa yana shan maganin nan yana wanka, sannan suka taru shi da Tanimu suka sauke kur’ani duk bisa shawarar Salmanu shi da ko izu biyar bai yi ba. . Ranar da yamma ya ce masa,“Yakamata ka je gida Adamu, kar iyalinka su, fara zargin wani abu ya faru da kai”Yanzu Adamu ya fara sakin ransa, ya ce
“In na je ban san me zan cewa kowa ba”.Salmanu yace, Wai kai menene faidar zuwanka makkan nan’ ne? ji nake nan na zaunar da kai na dinga karanta maka yadda zaka kai wa Allah kukan shaidanun da
ke hawa kanka”Idon Adamu a KanKance yana duban Salmanu ya ce masa, “Kar ka yi sabo Salmanu, wai ana yi wa Allah dole ne? na roKa, har abinda yafi haka ma na roKa amma dole na jira wa’adi”.Www.bankinhausanovels.com.ng
“Eh haka ne, amma kai ma ka dinga Karfafawa kanka gwiwa, haba kana namiji kana wai tsoron zuwa ka fuskanci matan da suke a KarKashinka? Ka je ka yi jan ido ga duk wadda ta kawo maka wargi, ka aiwatar da ra’ayinka kar ka aiwatar da ra’ayin ko waccensu, ka tafi da addu’a,muna nan muna maka fatan alkahiri ni da Tanimu, ko Tanimu?”. Tanimu ya kada kai da sauri. Adamu ya ji wani guntun Kwarin gwiwa wanda ya bashi damar shiryawa ya tashi ya doshi gidansa bayan sallar isha. Husna na tsakar gida tana alwala yayi sallama ya shiga gidan, Salma kuma na kitchen. Sai da Husna ta ji ina ma Kasa ta dare ta shige ciki saboda tsoro da razana, ba ta san yadda Adamu  gai karbe ta ba, ba ta son mummunar karba a gaban Salma. ~ . Bakinta na rawa ta amsa sallamar Adamu, sannan ta zarce da yi masa sannu da zuwa Adamu ya tsaya saroro kamar wani dutse yana kallonta, ya kasa namijin KoKarin amsa sallamarta saboda shakkun kar Salma ta jiyo shi ta ji damuwa a ranta, ko kuma ta nuna masa a fuska.  Husna ta kawar da kai kwalla na ciko mata a ido, wai ita da Adamu ne suka zama haka? Da kyar ta daure ta Karasa alwalar ta tashi ta wuce dakinta daidai lokacin da Salma ta fito daga kicin da kawarta tana ambaton sunan Adamu. A sace ya dauke kai daga kallon Husna tana Bacewa a dakinta zuwa kallon Salma mai kakacin kiran sunansa, ya bayyanar da fara’ar babu gaira babu dalili ba don har can cikin zuciyarsa yana fara’ar don murnar ganin Salma ba. Wadda zai wa irin wannan murnar ga ta can ta Kule daki bata sami ko arzikin ya amsa mata sallama da sannu da zuwa ba, bare ta sami na kyautar murmushi. “Ka bar ni cikin tashin hankali Adamu, ina ka shiga?”Salma ke masa wannan tambayar lokacin da ta doshi dakinta shi kuma zaro-zaro ya bi ta a baya ba tare da ya tanka ba, kuma da alama ba zai tanka din ba. Yana ta waiwayen dakin Husna kamar yadda take make a windo tana hangensa, sai da ya shige dakin Salma sannan ta saki labile ta fara kuka. Wanne irin shiri ne ba su zauna sun yi wa gidan aurensu ita da Adamu ba? Shi ne aka sami azzaluman da suka barbadar da shirin a iska, suka bar su da hangen juna daga nesa babu ko alakoron murmushi.
Salma na ta faman hidima da shi da sunan , kwantar masa da zuciya da mantar da shi Husna, tabbas ta ci nasara ya mantu a fuska, amma kacokam din Www.bankinhausanovels.com.ng zuciyarsa na can ga Husna da tausayinta tare da jinjinawa girman rashin adalcin da yayi mata, ya kuma shafa dalili ya rasa.. Aka dauke wuta ya fita ya siyo mai ya tashi Inji, Salma na lekensa ta windo da murnar zai bar injin a muhallinsa wanda yake dab da windon uwar dakin Husna, yadda zai ambula mata hayaki da Kara, tun tuni a nan Injin yake, kuma da yake tunda Adamu ya tafi ba su tashi Injin ba. Amma sai gashi Adamu ya canjawa Injin wajen zama, wajen da ya dawo da shi ma ya fi maKotaka da nata dakin. Ta saki labile haushi na turnike mata Kirji, wannan dalilin ya sa da ya shigo ta kasa hadiyewa sai da ta takalo maganar Husna. Ba ka shiga dakin amaryar kun gaisa ba ai”. Ba tare da ya dube ta ba ya amsa mata, “Ina jin ta yi bacci, na ji shiru”. Zagi Salma ta so ta ji Adamu ya kurma wa Husna, don haka da ya fadi wadannan kalmomin masu kama da yabo ta ji ita ya zage ta, ta cije ta ce, “Wato su amare idan suna bacci ba a ’ tashinsu?” Yayi dan nishi bai ce komai ba.
Ta yi fuska ta ce, “Ai na zaci ma dakinta zaka sauka, tunda daga nan har sati ita ce da kai”. Ya dan tsura mata ido tamkar yana canki-cankin da gaske ta ke ko da wasa? Da ya ga ‘ fuskarta a daure kawai sai ya doshi doguwar kujera ya hau kwanciya yana cewa,
“Idan kin ji bacci ki kashe Injin nan ni na kwanta”.
Sai ta rasa me zata ce masa face bin sa da kallo har zuwa lokacin da ya runtse ido da alamun fara bacci.
Don ganin Kwakwaf da Kurilla, sai ita ta Ki shigewa dakin, ta yi shimfida da bargo a tsakiyar falon ta kashe injin sannan ta kwanta tamkar tana zaton zai tashi cikin dare ya tafi dakin amarya.
Daga Adamu har Husna babu wanda ya runtsa bacci a ranar nan, Husna na kuka a zahiri da badini yayin da Adamu ke na zuci zalla cikin baccin Karya, tabbas ba don Salma na gadin nasa ba da tuni ya Balle ya kai kansa dakin Husna. Karfe uku saura ya ji motsin bude Kofar dakin Husna, gabansa yayi mummunan yankewa ya fadi, a tsammaninsa Husna gida zata bude ta gudu tunda ya wulakantar da lamarinta. Sai gashi zaune tunkurkur cikin fargaba yana kasa kunne. Amma sai ya jiyo  Husna bandaki ta dosa, can jimawa kuma ta fito ya ji ta a tsakar gida tana alwala.  Bai bawa zuciyarsa damar wani zabi ba bare ta zaba masa abinda zai cutar da shi, kawai sai ya gan shi a hanyar yin abinda ya zaba wato tashi kai tsayae ya fice ya doshi wajen Husna da ke alwala. Tunda ya tashi zaune Salma ta farka, don haka a idonta ya fice, inda ita kuma ta yi saurin dira windo ta fara hangensa kai tsaye ya doshi wajen Husna da ke alwala, sai zuciyar Salma ta fara dara tana shirin tatarwatsewaAdamu yayi tsaye kan Husna yana ta kallonta wasu irin abubuwa da bai san ko meye ba suna ta faman zagaye kansa a guje.
Husna neman rasa hayyaci take, tun daga fitowarsa har tsayawar da yayi a kanta zuciyarta ta tsaya da aiki, wanke fuska kawai take tana Karawa har ba zata iya tantance Kafa nawa ta yi ba.
‘Adamu da yake mallake da nasa hankalin sai ya mika hannu ya karbi butar hannunta, murya Kasa-Kasa kuma a tausashe ya ce mata, Kawo na zuba miki ruwan yi alwalarki a nutse”.Ta sakar masa butar cikin rauni da hawaye, ya _ dinga zuba mata ruwa ita kuma ta daure ta mallaki_—hayyacinta ta cika alwalar duk da tana yi tana kuka kamar yadda ta fahimci shi ma Adamu kukan yake. Bayan ta gama sai suka yi duru-duru, ita tana ~ jin kewar ta tafi ta barshi, shi kuma ba ya jin komai sai kaunarta da Ke Kara ninninka kanta a zuciyarsa, ya ji ba zai taba fanshewa ba in bai kai mata matsayin bawan da zata dinga takawa tana wucewaba, in ana yi wa so bauta fiye da haka shi in yayi yana jin bai biya yadda yake jin na Husna a Kirjinsa ba. °WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Babu wani zabi dole su rabun, don haka Husna ta mike a hankali da sarKakKiyar muryarta tace
“Na gode Adamu bai iya daurewa ba sai da ya amayar,
“Ina sonki Husna, ban taba son wani abu a duniya sama da ke ba, in na yi miki abinda ya sosa ranki ki Kaddara ba ni na zaba ba zaba min aka yi, in ni zan zaba faranta miki zan ta yi har bayan mutuwata… ki yafe min, kar kar ki biye ta aibuna ki Kwace min son da kika bani… ki ba ni dama zan je in nemo maganin ciwon da ya dami zuciyata har yake ba ni damar saba miki…”Bai iya direwa ba kuka ya hana shi, Husna ma sai toshe baki ta yi saboda sautin kukan da ya yunKuro mata, da sauri ta toshi dakinta ta rufo Kofa. – Adamu ya tsaya ya gama hucin kukansa da tashin hankalinsa sannan ya je Kofar dakin Husna ya ajiye mata butarta, ya doshi bandaki shi ma domin daura tasa Alwalar, sai sannan Salma ta zo ransa, yaji wani jarabar tsoro ya cika shi. Bayan yayi alwala ya koma dakin Salma sai ya same ta zaune ta sa ruwan sanyi a gaba tana ta faman daddaka, jin zuciyarta take tana kamawa da wuta, lallai in bata kai mata dauki da ruwan sanyi ba yanzun nan zata janyo ranta ta shaKe mata shi ta bar duniyar ita da son Adamun da burikanta. Da ya same ta zaune tana ta faman daddakar ruwa tamkar ‘Yar giyar da aka batowa rai, sai ya fi nutsuwar cewa bata fahimci abinda yayi ba, bai

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *