KWASAR GANIMA CHAPTER 3 BY FAUZIYYAH D. SULAIMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
ILLAR HARSHE
Duk wanda ya sanni to da baki abin magana ya sanni tuni sunan da iyaye na su ka rada mani, wato Saude, ya bata. Hakan ya samo asali ne sakamakon shegen surutu da na ke da shi, duk inda na je sai an san na je — ko gidan biki ko suna ko na mutuwa. Na kan yi Karin gishiri ko in zaKalKale kan abin da baa yi ba sam, ko ban gani ba. In dai na ji labarin abu kuwa sai na yi Karin gishiri wurin ba wani. Sai dai ban farga ga cewa abin da na ke yi ya na da muni ba sai ranar wata Talata da daddare. Abin ya samo asali ne a ranar Litinin da yamma, na dawo daga saro kayan da na ke rabawa bashi a Kasuwar Kofar Wambai, bayan na tsallako titin i.B.B. na fada wata mota da kwandastan ta ke ta kiran “Kurna, Bachirawa, Rijiyar Lemo.” Na fada motar na zauna a kujerar tsakiya, kusa da wata mata, yayin da wanda ya ke kusa da ita ya matsa, na dauko raken da na yo guziri na fara sha, na miKa wa matar da ke kusa da ni,Www.bankinhausanovels.com.ng nace, “Bisimillah.” Matar ta girgiza kai, tace, “Alhamdu lillahi, na gode.” Na yi ’yar dariya na ce, “Wallahi Hajiya ban ga laifin ki ba don kin Ki shan raken nan, domin babu wuya yanzu an maida mutum doya, don ni yanzu haka daga wurin sarin kaya na ke, wanda na ke bayarwa bashi ga
ma’aikata. Wajen mutum shida ne su ka yi mani tayin kaza da soye na Ki ci, don mutane yanzu ba su da gaskiya.” Wallahi Hajiya maganar ki a kan hanya ta ke, don kwanaki wani a bayan layin mu daga amsa gaisuwa aka neme shi aka rasa har yau babu labari,” wani mutum da ke zaune a kujerar baya ya shigo cikin hirar tamu.
Na juya wurin sa ina magana, ina KoKarin kwanto yaro na daga baya. Na ciro mama na sanya masa a baki, sannan na ci gaba da fadin: ““Dan’uwa, ai ni kuwa na ga zahiri, domin wata rana mun hau mota sai wani ya yi wa wani tayin nama. Daga cin yanka daya aka neme su su duka aka rasa. Nan fa mu ka dinga bincike a motar nan amman har rana irin ta yau ba a kuma ganin mutumin ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Kai Hajiya, yanzu a gaban ki aka yi?” wanda ke kusa da ni ya tambaya. Haba bawan Allah, zan maka Karya ne?” na ba shi amsa. Na dora da cewa,
DUK wanda ya san ni, to da Baki Abin Magana ya san ni. Tuni sunan “Idan na fara ba ka irin wannan labarin sai na ba ka guda dari wallahi, kuma duk a gaba na su ka faru.,. Kai, ni fa duk masu kudin garin nan dake yankan kai babu wanda ban sani ba, kuma har inda su ke aikin su na sani, kawai don dai ba ka da gatan da idan ka nuna zaa yarda.” Gaba daya hankalin jama’ar da ke motar ya dawo kai na. Na zage na dinga ba su labarin Kanzon kurege kala-kala har na zo inda zan sauka. Na mai da maman nawa gami da fita, mutumin da ke kusa da ni ya fito shi ma. Na ajiye gyale na a gefe bisa tulin kayan da na sayo, na fara goya dana. Sai da na gama, sannan na dauki gyale na, na yafa, na dora wa dan dako kayan.
Bayan na yi nisa, na ji ana kira na: “Hajiya! Hajiya!” Ko ba da ni ake ba, Saina juya, na ga wacce ake ake kira saboda tsabar saka ido na, sai ma nayi katari da ni ake. Wannan mutumin da ya zauna a kusa da ni ne a cikin mota. Na tsaya gami da tsayar da dan dakon, har ya Karaso inda mu ke. Da ya Karaso, ya ce, “Suna na Sadau. Na ji dazu a mota ki na cewa kina saro wa ma’ aikata kayan bashi…” “Kwarai kuwa!” na katse shi. Na dora da cewa: “Daga atamfa, shadda zuwa leshi da kayan daki… Kai, babu abin da ba na kawowa. Har Gidan Gwamna na ke kai masu kaya.”
Ya yi murmushi, ya ce, “Lallai ki ce abin naki babba ne. Don haka ne ma ya sanya na ga gara in yi miki magana domin ina aiki ne a lokal gammen. To mu na da wacce ke kawo mana kaya, sai ta rasu. Mu na neman wacce za ta kawo mana sai na ga ai ke ya dace ki kawo mana.”
Dadi ya cika ni. Nan fa na saki baki na dinga zuba. Daga Karshe mu ka je na nuna masa gida na, mu ka yanke shawarar gobe da safe zai zo ya tafi da ni ya gabatar a Karamar hukumar tasu. Tun da safe na kammala shiri ina jiran sa. Da ma ba wani sanar da mijin nake inda za ni ba, don haka bai sani ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da mutumin ya iso, ya aiko mini ya zo. Na bar yaro na wurin yayyen sa; jiya ma don ba sa nan ne na tafi da shi kasuwa. Ina fita, na gan shi cikin wata hadaddiyar mota. Na dafe Kirji cike da mamaki, sannan na Karasa na shiga motar, ina fadin: “Ka ce kai ma din bana wasa ba ne!”
Ya yi dariya kawai, sannan mu ka gaisa. Ya tada motar ni kuwa ina ta ba shi labarin jiya na ‘yan yankan kai don na ji ya na son hirar. Shi kuwa sai mamaki ya ke. Ya ce, “Kai, mutane ba su da kirki! Ke kuwa kin sha kallo. Wai ni yaya sunan ki ne ma?”
Na yi dariya na ce, “Suna na Saude, amman an fi kira na da Baki-AbinMagana.” Ya ce, “Lallai kam ai sunan ya dace dake.” Daga nan ban kuma sanin abin da ya faru ba sai dai na farka na gan ni a wani katon zagayayyen gida, Na tashi a firgice ina salati, sai na ji an saki dariya a bayana. Na juya da sauri don na san ba muryar mutum daya ba ce. Manyan alhazai na gani guda uku, sun sha manyan kaya; sai wanda mu ka fito da shi, wanda ko sunan sa ban sani ba. A firgice, na ce, “Malam ina ka kawo ni? Kai da mu ka yi da kai za ka kai ni lokal gammen?” Ya yi dariya, kana ya ce , “Hajiya ai nan ne lokal gammen din. Ke da ki ka ce duk gidajen yankan kan da ke garin nan kin sani, shi ne na kawo ki nan ko kin taba zuwa nan. Sannan ki dubi wadannan mutanen, a cikin su ko akwai wanda ki ka sani, tunda kin ce duk garin nan babu mai yankan kan da ba ki sani ba.” Ina jin haka ciki na ya Kulle. Na shiga tsananin firgici don na gano ina hannun ‘yan yankan kai ne kuma a gidan su. Fitsari ya Kwace mani. Sai na fara kuka da roKo: “Don Allah ku yi haKuri! Wallahi da man Karya na ke; don dai kawai na ba da labari ne, amman ban da Kasuwar Kofar Wambai ban san ko’ina a Kano ba, sai dai unguwar mu da Kauyen mu.” Sai su ka kama yi mani dariya. ‘Daya daga cikin alhazan ya ce, “Kin ga, Hajiya, kwantar da hankalin ki. Ba kan ki za mu Www.bankinhausanovels.com.ng yanka ba, sai dai haKoran ki da za mu kwashe duka; shi ne ladar maganar da ki ka yi. Sai mu sake ki ki ji dadin ba da labari a mota gobe.” Na dora hannu a kai gami da kurma ihu. Na shiga birgima, ina neman gafara, amma a banza. Haka nan ina ji ina gani wasu Kartai su ka fito daga wani daki su ka kama ni, su ka daure tamau. Sannan aka fara bantarar hakora na kamar ana bantarar masara daga jikin kwansan ta. Tun ina ihu ina gane abin da su ke yi har na suma, na gaza sanin abin da su ke fada.
*****
Ban tashi farkawa ba sai a wani asibiti. Bayan na dan dawo hayyaci na ne aka sanar da ni wai a gefen wani titi aka gan ni a sume. Sai a sannan na tuno abin da ya faru. Na kai hannu cikin baki na, sai na ji babu haKori ko Kwaya daya. Na fashe da kuka cike da nadama, ina fadi a rai na: “Lallai baki shi ke yanka wuya! Ni da surutu mara amfani har abada!”
To da wane bakin ma zan yi? na tambayi kai na.
Kwasar Ganima
YAna gadon sa ya na ta sharar barci. Tun da ya ji garin babu lafiya, ana ta rikici a kan zabe, ya ce babu inda zai fita yau ko wurin aikin sa ba zai je ba. Kamar a mafarki, sai ya ji ana kwatsa masa duka. Ya mike da sauri ya na ta soshe-soshe. Bai yi yunKurin Www.bankinhausanovels.com.ng yin masifa ba domin dai ya san mahaifiyar sa ce. Mace ce ma’abociyar masifa. Har ya saba da halin ta ma.
Cikin hargowa ta na cewa, “Shashasha! Soko! Ka na nan ka na ta sharar bacci ga *ya’yan arzifi can su na ta kwaso wa iyayen su ganima! Ba ka ga abin da Balele ya samar wa mahaifiyar sa ba, har da su firji.” (Ta na nufin kishiyar ta da dan ta) “Maza ka tashi ni ma ka je ka samo mani ko da tibi ce!”
Ya kwantar da murya, ya ce, “Haba Mama! Wacce irin ganima kuma? Kin san dai wannan fadan ba a kan gaskiya ake yin sa ba, fada ne kawai na Kabilanci, kuma malamai su na ta gargadin…”
“Rufe mini baki, soko! Da an maka magana ka kama yi wa mutane wa’azi, to wallahi idan ba ka tashi ka samo mini wani abu ba sai ran ka ya baci. Waccan rigimar ma da aka yi sai da Balele ya kusan cika wa mahaifiyar sa daki da kaya, kai kuwa ko cokali ba ka samo mini ba sai wa’azi. Don haka dole ni ma a wannan karon na samu ladar haihuwa. Tashi ka fita tun ran ka bai baci ba!” Ya mike, jikin sa sanyi Kalau, ran saa Bace, ya fice. Ya san idan bai fita din ba ba za ta daina wannan mitar ba. Amma sai ya yanke shawarar ya zauna a shagon sa da ke Kofar gidan su inda ya ke dinki, sana’ ar da kullum ta ke mita.
Ya na tsakar aiki sai ya ga ta fito lullube da zanin atamfa. Ta galla masa harara, ta ce, “Ai da man tun da na jiyo Karar keke gigar-gigar na san sai kai. Wato ban isa na saka ka yi ba ko? To, wallahi idan ba ka tafi ka debo mani ganimar nan ba sai na tsine maka. Ga yaran da ba su kai ka nan ba su na ta jido kaya!” Ya mike domin kada ta yi masa baki; ya san idan ta tsine masa ba zai yi albarka ba, Www.bankinhausanovels.com.ng
Abdullahi yaro ne natsattse wanda ke bin mahaifiyar sa sau da Kafa, amma ita ba ta gani. Ta na tsaye ta na kallon sa ya nufi bakin titin da ake kwaso ganimar. Sai daga murya ta ke ta na fadin: “Bakin El-Duniya za ka je; anan ake debo kayan kallon!”
Shi dai tafiya kawai ya ke yi. A ran sa ya na shawarar kawai zai wuce wurin wani ubangidan sa ya ba shi aron kudi ya sayo mata talabijin din, alabasshi idan ya so idan ya yi aikin Sallah sai ya biya shi kudin sa. Ya na isa bakin titin sai ga wata mota ta ’yan sandan kwantar da tarzoma sun fararo da gudu sun biyo yara da ke Kone-Konen. Sai shi ma ya juyaa guje saboda ya ga harbin kan mai uwa da wabi su ke yi. A rashin sa’a, wani daga cikin ’yan sandan ya harbe shi a kan sa. Nan take ya fadi, jini ya Balle kamar da bakin Kwarya. Sai da ’yan sandan su ka tafi sa’annan jama’a su ka kawo masa dauki. Da yake dan unguwar ne, kowa ya san shi, aka kwashe shi aka yi gidan su.
Mahaifiyar sa ta na ganin sa sai ta fasa kuka, ta na fadin: “Na shiga uku! Abdullahi kada ka mutu don Allah! Ni ce na ja maka, ka na zaman zaman ka!”
Mahaifin sa da wasu dattawa su ka dauke shi aka yi asibiti. Su na isa, aka ce babu likita, sai dai su tafi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Can din ma da aka je, ma’aikatan su ka ce sai an cake masu wasu makudan kudi za su taba shi. Hankalin Mama ya kuma tashi, domin in dai ba gidan su aka daga ba babu inda za su sami wannan kudin, kafin a samu masu sayen gidan kuma ai ya galabaita. Mahaifin ya bazama ya shiga gari, duk da yake ya san ba zai samo ko da kaso goma daga cikin dari na kudin ba. Mama ta na Www.bankinhausanovels.com.ng rungume da Abdullahi ta na ta kuka tana neman gafarar sa. Ya yi mata wani murmushi, sannan ya yi Kalmar Shahada, ya amsa kiran Allah. Mama ta Kara kidimewa. Abdullahi shi ne kadai namiji a cikin ’ya’yan ta. Da mahaifin sa ya dawo ya ga ya cika, sai ya yi shiru kamar ruwa ya ciwo shi. Can dai ya goge hawaye, ya dubi Mama ya ce, “Kin jawo kin rasa dan ki a kan ganimar banza. Gobe ma sai ki Kara.”
Ta kuma fashewa da kuka, ta na da-na-sani mara amfani.