KWASAR GANIMA CHAPTER 6 BY FAUZIYYAH D. SULAIMAN

KWASAR GANIMA CHAPTER 6 BY FAUZIYYAH D. SULAIMAN

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wayo Ya Tarar Da Wayo

SUka hadu a hanya su ka tafa gami da yi wa juna kirari “Wayo ya tadda wayo!” da ya ke haka ake kiran su. Audu Wayo yace, “Yaya aboki na? Kwana biyu ba mu hadu ba; ko dai ka hadu da mai wayo ta yimaka wayo?”
Ilu Wayo ya ce, “Haba dai! Sai dai kai a yi maka wayo; ai ni yanzu wani labarin zan ba ka ma.”
“To ai ni ma da nawa labarin, amma fara ba ni naka na sha.”
Su ka samu gindin wata bishiya su ka zauna. Ilu Wayo ya zaro rake guda biyu daga aljihun sa, ya miKa masa daya, ya fara shan dayan. Sai da ya gaftara ya sha sannan ya fara ba da labarin nasa kamar haka.
Ka na ji? Bayan rabuwar mu da kai na yi wata budurwa mai suna Abuwa. Yarinya ce mai kyau sai dai akwai wayo. Ni kuwa na yi mata lamfo kamar dolo, tana ta wanka ta. Rannan watan Maulidi ya kama aka fara

tunatar da ni tun kafin lokacin ya yi. Na dage na dinga tari har na tara kudin kaza guda uku da na kayan miya da na shinkafa. Na tafi kasuwa na sayo na kai gidan su Abuwa. Ina hura hanci. Aka amsa ana murna da zumudi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da yamma ta yi mu ka cika shago da abokai na mu na jira a kawo mana alibidin Maulidi, sai dai har aka yi sallar Isha’i babu abinci babu labarin sa. Sai wajen Karfe goma ta yi kiran waya, ta shagwabe murya ta na fadin: “Don Allah dalin ka yi haKuri, za ka ga abincin kadan. Wallahi baKi aka yi a gidan namu, su ka kwashe abincin ina wanka.” Da sauri na ce mata, “Ai babu komai.” Domin na yi zaton dai ko kaza daya akawo mana. Aka kawo mana abinci. Har lokacin abokan nawa na nan. Sai dai me za mu gani? Kai da Kafa ne guda uku da wuya guda daya. Wani abu ya tsaya mani a wuya na. Abokan nawa su ka dinga yi mani shaKiyanci, amma na dake kawai, na hakura domin na Kudiri aniyar ramawa ni ma. Na ci gaba da zuwa wurin ta. Komai ya wuce, ita tama manta.
Sai watan Kadiriyya ya Kara kamawa. Na hada kaya na kuma kaiwa na ce
mata ta dafa mani baKi zan yi. Sannan na sai mata nata ita ma. Aka dafo mani kuwa. Ta aro samiru a maKotan su har guda hudu, saiti guda kenan irin mai hannun kwana nan ka san ta fi tsada. Mu ka cinye abinci. Washegari, na tafi bakin Kasuwar Kurmi na saida saitin samirar na zuba kudi naa aljihu. Na kira ta a waya nace mata, “Dalin, bugowa na yi na ba ki haKuri, don jiya bayan mun kamalla cin abincin nan na manta kwanukan a waje, sai da safe na duba ban gani ba. Ki yi hakuri.”
Ina jiyo salatin ta, ta na fadin, “Na shiga uku wallahi! A maKota na aro ta.” Su ka fashe da dariya gami da tafawa. Audu Wayo ya ce, “Lallai abokina ashe dai wayon yana nan. Tsaya to, nikajinawa.”
Ka na ji? Wata rana na je gurin budurwa ta Lami. Mu na tsaka da zance a zauren su, na fara jiyo maganganu, mahaifiyar ta ce ta miKa wa baban ta biredi, ta na fadin: “Inji abokin ka.”
Sai na jiyo shi ya ce, “Yaya zan yi da biredi babu shayi? Ga shi ni ba kudin saya ba.”
‘Daya daga cikin Kannen Lami ta ce, “Baba, kawai ka ba da a siyo maka kifin gwangwani.” Da sauri ya ce, “Ga ashirin a sawo mani.” Matar tasa ta ce, “Haba dai! Ai zai kai arba’in yanzu.”
Da Kyar ya ba da, yana mita ya na cewa, “Wallahi tun da kikasaka naba da arba’in din nan kudin cefanen ki kin rasa tunda ke ki ka kawo shawarar.”
Bayan kamar minti goma sai yaron ya dawo da gudu ya ce, “Baba, an ce casa’in ne.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Uban ya luKa wata uwar ashar ya ce, “Ni za a cuta? Abin ashirin din? Ba ni suga na hada da ruwana sha.”
Da alama hadin aka yi, sai dai ba a kuma minti uku ba na ji an yi facali da wani abu, ji ka ke gwaram! ana fadin: “Jarababbiya! Sai dai kin kashe ni za ki ji dadi, dan ruwan sigan sai kin dangwala ba za ki ci gayan ba ke. Wallahi da ki dangwala gwara a zubar kowa ya huta.” Da alama tura gayan biredin ya yi a baki, don Karashen maganar da shaKakKiyar murya na jiyo ta. “Kin rasa biredin ma gaba daya, gwara Kanwar Lamin ta ce, “Baba, saurayin Lami fa ya zo.”
Ban ji abin da su ka kuma fadi ba don an rage sautin muryar. Ita dai Lami duk kunya ta kama ta, kamar ta nutse Kasa don kunya. Can sai ga Kanin nan nata ya shigo zauren, ya ce, “Baba ya ce wai a ina ki ka ajiye kudin cefanen da ya ba ki?”
Da man fa ba shi ne karo na farko da ya ke mini haka ba, don haka na ke zuwa da rana zance, don na san ba ya zama a gida sosai. Ashe yau na yi rashin sa’a!
Lami ta gyara tsayuwa ta ce, “Yana kan kwabet.”
Kanin nata ya juya da sauri. Sai dai ko minti uku ba a rufa ba sai ga Kanin nata tare da baban ta ya taho ya na huci ya na fadin: “Ki ga yarinya mara kirki! Kin san dai kudi na kenan ko? Za ki je ki kashe mani, to da me zaa yi muku girkin yau?”
Tayi shiru cike da kunya don dai ta san Karya kawai ya shirya. Ya dinga bambami.
Rai na ya baci, don dai na san so ya ke na ba shi wani abu, ga shi sai kudin baba ta ne kawai da ta ba ni in saro mata soda a cikin aljihu na. Ba ni da ko kwabo nawa. Haka ina ji ina gani na zaro daya cikin dubu biyu na ba da da zummar idan na koma gida na ce da babar tawa faduwata yi.
Na gaya maka mara mutuncin tsohon nan wai sai ya dage ba zai amsa ba sai da na yi ta magiya ina fadin, “Haba Baba, ai duk daya ne.” Sannan ya amsa ya koma cikin gidan ya na sanya mini albarka. Ya saba yi min haka fa, ba sau daya mu ka yi haka da shi ba,don haka na Kudiri aniyar ramawa a wannan karon, balle da na koma gida baba ta ta rantse sai na biyata kudin ta. Rannan mu na zance sai ga wani yaro ya shigo gidan, hannun sa dauke da babbar leda, ya shige. Ina jin hargowar matan gidan su na fadin, ““Wallahi kudi ne dubu biyu da kayan miya. Waye ya aiko ka?”
Yaron ya ce, “Wai na ce Malam Musa ne abokin maigidan, kudin dashin sa ne na kati da kuma kayan cefanen da ya ba shi sallahu, ya duba inda ya ke zama bai gan shi ba, idan ya zo a ba shi.”
Nan take dabara ta fado mani.
Mu nanan mu na zance har aka gama girki, don haka mu ka yi sallama. Sai dai bayan kamar minti goma na dawo na kuma yin sallama. Budurwar tawa ta fito cike da mamaki ta na tambayar ko lafiya.
Na ce, “Ina fita na hadu da Baba na nan gidan, ya ce wai idan an gama abincin a zubo masa, sannan a ba da saKon kudin nan da aka kawo masa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba ta ji komai ba, ta shiga ta fito da abinci cikin kula ta kawo da kudin, na sanya a aljihu, na tafi ina murna. Yau dai na san akwai rigima a cikin gidan, don na san baban Lami da son kudi kamar ya Kwata. Ilai kuwa, da daddare  ga kiran wayar ta. Na daga da sauri na make murya na ce, “Caji ya kawo.
Audu da Ilu su ka fashe da dariya su na fadin: “Wayo ya tadda wayo!”

Yasin Din Babarbare

WANI Babarbare ne ya je kasuwa tallar da takubban sa masu dama. Da ya taho daga gida, ya jima ya na tunanin ranar da zai kai su kasuwa. Bikin diyar sa zai yi da kudin. Kafin ya sayar da takubban an sha fama, don duk wanda ya taya sai ya ce albarka, har dai aka samu ya sayar da Kyar. Bayan ya sayar, ya ga dacewar ya zauna ya sha ko da furace. Ya isa wurin wata Bafillatana, ya zauna. Ta dama masa fura.
Yana kurbar ludayi daya ya daga kai ya dube ta ya ce, ““Wannan furar taka tayi dadi. Ko kuna sa mata zuma da madara ne?” Tana masa dariya, ta ce, “Kai dai kawai ka she ka yi santi ne.”
Bayan ya gama sha, maimakon ya tashi ya tafi sai ya zauna ya kama hira da Bafillatanar nan har rana ta take. Sai ma ya gyara ya kwanta a nan, amma ya na riKe da aljihun sa da kudin ke ciki gam. Ba dadewa barci ya kwashe shi. Bai farka ba sai bayan la’asar lis. Ya na tashi, ya kama zare ido. Can sai ya tuno da kudin sa. Ya kalli hannun nasa da ya dafe kudin ya ga ya na can gefe don haka ya kai wa aljihun nasa cafka. Ya fara lalubawa, ya ga babu komai. Ya tashi ya dinga dube-dube, amma babu kudi. Ya kalli inda Bafillatanar nan ke zaune, babu ita. Sai ya fashe da kuka. Jama’a su ka taru a kan sa, ana ta tambayar sa abin da ya faru. Ya Ki magana. Sai daga Karshe ya ce: “Ku nuna mini gidan malami mai yasin kawai.”
Babu bata lokaci aka nuna masa gidan malamin.
Yana zuwa, ya Kara fashewa da kuka. Malamin ya dinga lallashin saa kan ya yi shiru ya gaya masa abin da ke damun sa. Da Kyar yayi shiru sannan ya fara magana.
“Kudi su ka kwashe mini. Ina so a yi masu yasin me ci, dukkan su — da wanda ta dauki kudin da wanda ta ga san da ta dauki kudin ba ta tashe ta ba, da wanda ta zauna a kusa da ni da wanda an sai wani abu a wurin ta da kudin, da wanda an wushe ta gaban ta da kudin da…” Www.bankinhausanovels.com.ng

“Haba Babarbare! Ina rawan wanda aka wuce ta gaban sa kuma da wanda aka sayi wani abu a gurin sa?”

Sai ya sake gyara zama, ya ce, “Yauwa, da wanda ta yi magana yanzu ma ta amince da daukan kudin kenan!”

Azal!

A wani yammaci na je gidan su Zaliha zance. Ta rako ni har gurin babur di na. Mun rabu ba don mun gaji da hirar ba sai don hadarin
da ya hadu. Na tada babur din, ina daga mata hannu, na wuce da gudu. Sai dai ina fita bakin layin aka tsuge da ruwa, babur di na ya mutu. Na tsaya na dinga tada shi amma ya Ki tashi. Jin ruwan ya na ta duka na ya sa na ja babur din zuwa KarKashin wata bishiya. Na ciro fulogi na fara gogewa, ihun mace da na jiyo ne ya sanya ni daga kai, sai na hango Indo. Abokiyar aikina ce. Wasu Katti su hudu sun biyo ta babu gyale balle dankwali a kan ta. Wani Katon dutse ya harde ta, ta fadi jabar a Kasa, ta fasa baki.

Daidai lokacin da garadan su ka Karasa kusa da ita, daga can nesa na jiyo Indo ta na fadin: “Me na yi muku?” Kafin su kai ga ba ta amsa wata mota Kirar jif da ta manno da gudu ta tsaya a wurin. Alhaji Yawale, dan takarar gwamna, ya fito daga motar. Cikin kakkausar murya ya ce: “Ku tura ta a mota; yau ajalin tane ya sauka!”
Da Karfi Kartin nan su ka danna ta a mota su ka shige. Na yanke shawarar bin su. Na yi sa’a ina buga babur din ya tashi a wannan lokaci, don haka na bisi a baya. Bayan gari su ka nufa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga nesa na labe na hango su sun shiga wani Katon gida mai kama da kango. Sai da su ka shiga sannan na bi su da Kafa ta, na Boye babur din cikin duhuwa. Katangar ba ta da tsawo sosai, don haka na zagaya ta baya na kama na dan leKa. Sai na hango su sun zagaye Indo, wadda ke kuka.
Can na jiyo Alhaji Yawale na fadin: ““Ya zama dole ki ba mu kwafen kaset din da ki ka dauka ko mu halaka ki ke da dangin ki gaba daya.”
Alokacin na gano inda maganar ta dosa. Wato zuwan da Indo ta ce mini za ta yi hira da Alhaji Yawale ta jiyo wani mugun abu ta dauko, su kuma sun kama ta. Ni da ita duk ’yan jarida ne.
Indo ta na kuka, ta ce, “Ya fadi a hanya. Kada ku kashe ni don Allah!”
‘Dan takarar ya ce, “‘Karya ki ke yi! Ku shigar mini da ita ciki, sannan ku je ku kashe Shehu yanzu, don bana son ya Kara kwana a duniya.”
Jin an ambaci sunan siriki na, wanda shi ma ke takarar gwanna, na ji hankali na ya kuma tashi.
Na dirga da sauri na nufi inda na Boye babur di na, na zaro tsohuwar way ta ta irin ‘raka ni kashi’ din nan, na fara neman wayar budurwar tawa don in sanar da ita su bar gidan. Sai dai wayar tana ta ce mini ba netwok. A haka na ga gittawar motar nan ta dazu. Hankali na ya Kara tashi. Na Kagara in bi su.
Da Kyar babur di na ya tashi, na bisu gidan surikin nawa. A tunani na, ko rahoto na dauko idan sun kashe shi. Na yanke shawarar haurawa ta wanj maKocin kangon gidan. Na kama katangar na haura na dirga. Kasancewar
bola ce da ruwa ya cika ta, na Bata kaya na. Duhun wurin ya sanya ni kunna
tocilan din jikin waya ta na fara haskawa a hankali. Abin da ya ba ni tsoro bai wuce hasko gawar Alhaji Shehu da na yi ba, wato har sun kashe shi sun wurgo kango. Www.bankinhausanovels.com.ng

Na yi duruduru, na rasa abin yi. Can na jiyo jiniyar ‘yan sanda, don haka na yanke shawarar barin wurin. Na kama katanga na haura, sai dai waya ta ta subuce ta fado kangon. Na yi niyyar komawa in dauko, sai na ji alamun shigowa kangon da gudu. Dalleliyar tocilan din da na hango ce ta tabbatar mini da ‘yan sanda ne, don haka na dirga da sauri na bar wurin.

* Ina daga can maboya ta na hango Zaliha da wasu gungun ’yan sanda sun fito daga gidan su Zaliha ta na ta kuka. Ta kara waya a kunnen ta, da alamar wani ta ke nema. Wani dan sanda da na ke tunanin shi ne wanda ya shiga kangon ya fallo da gudu da waya ta a hannun sa wacce Karar ringin din ta ya sa na gane, ya na fadin, “Sir, ga gawar can a kangon can, kuma ga wata waya da na gania gurin tana ringin.”

Wanda aka kira da ‘Sir’ din nan ya amsa da sauri, ya kara kunnen sa bayan ya danna madannin dannawa. Ga mamakin su, sai su ka ji muryar Zaliha ta fito ta na fadin, “Nura ka na ina? Ka zo ka ga wasu sun kashe mini Daddy na!”
‘Dan sandan ya matsa kusa da ita ya ce, “Waye Nuran? Ai ga wayar tasa at tsinta a kangon. Meye hadin ki da shi?”
Cikin kuka ta ce, “Saurayi na ne. Shine wanda zan aura!” Abin da na iya ji kenan, na kwasa da gudu da Kafa ta na nufi gidan mv. Rudewa ta sanya na manta da babur din ma.
Kai-tsaye gidan mu na nufa da gudu inda na ke zaune ni da kaka ta, don ni maraya ne. Ina isa, na tarar har kaka ta ta kulle gidan. Na kama bugawa a kidime. Kaka ta iso ta bude cikin magagin barci a idon ta. Da ace da ne, da tsokanar ta zan fara yi da “Tsohuwa har kin yi bacci?” Sai dai yau na kasa cewakomai sai shige tanayi akidime. Ta bini da kallo cike da mamaki ta na fadin, “Danbaba lafiya na gan ka haka kamar wanda su ka kasa tsere da mutuwa?”
“Ba na jin dadi,” abin da na iya fada kenan. Na shige daki na da sauri. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nasan Kaka ta dan jima nan tsaye kafin ta Kara kulle gidan ta nufi dakin ta da sauri.
Nakasa zama na Kasa tsayuwa, sai sintiri na ke yi. Gaba daya KwaKwalwa ta ta cushe. Da Kyar na iya dofana kafada ta na kwanta. Sai dai ko minti goma ban yi da kwanciya ba na ji ana ta buga gidan mu. Na yi firgigit na tashia tsorace, ina jin wucewar Kaka ta na fadin, “Waye?” Nayi farat na fito don bin umarnin shawarar Kwakwalwa ta don ba naraba daya biyu: “yan sanda ne su ka biyo ni da taimakon kwatancen Zaliha.
Sa’ilin da na kama katangar ya yi daidai da lokacin da Kaka ta isa zauren tana cewa, “Waye ne?”
Daga can waje na ji an ce, “Jami’an tsaro ne. Ki bude. Wasu tambayoyi za mu yi miki.”
Arude, Kaka ta ce, “Jami’an tsaro kuma? Na shiga uku!” Takama Kofar ta bude, jikin ta yanarawa.
Sukabayyana cikin baKaKen kayan su.
Daya daga cikin su ya ce, “Ina Nura?” Ande, tace, “Lafiya dai ko?”
“K wantar da hankalin ki. Wasu tambayoyi zai amsa mana kawai.” Suka nufi daki na. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ni kuwa tuni na dire na fara falla da gudu, ban san inda na dosa ba. Ga Mamakin su sai su ka tarar da dakin nawa babu kowa. Daya daga cikin su ya kalli Kaka ya ce, “Kika ce yana cikin daki!”
Arde, ta ce, “Tabbas, ya shigo ya kwanta kuma babu wani alamun bude
Kofa tun bayan da na kulle balle na ce ko fita ya kuma yi. Abin da mamaki-~ kamar daukarjinnu?”
*Yan sandan su ka futo da sauri su na dube-dube. Can, daya ya karasa wurin da na haura, ya ce, “Oga, kalli nan! Ina jin ta nan ya haura.”
Shugaban nasu ya dalle wurin da tocilan kafin ya ba su umarni cikin gaggawa: “Oya, lets go!”
Su ka bi shi da sauri su ka bar Kaka ta na salallami.
Ni kam gudu na ke iyakar rai na. Can daga baya na na jiyo Karar jiniyar motar ’yan sanda, alamar su na biye da ni. Na san mutane da yawa za su yi mamakin gudun da na ke yi. To, ina gudu ne don na san idan ’yan sandan nan su ka kama ni na kade tunda ga waya ta sun gani a wurin gawar.
Ina tsakar gudun ceton rai na ji Karar jiniya na biye da ni. Nan na Kara wuta ina waigen su.
Allah ya taimake ni na shige wani lungu, na bace musu. Na ci gaba da gudu har sai da na ji numfashi ya na shirin daukewa sannan na sami wata duhuwa na zauna. Na kai minti talatin kafin na dawo hayyaci na. Na fara tuninin yaya zan yi, a ina zan kwana, tunanin aboki na sani ya fado mini. Na mike na nufi gidan sa. Duk da tazarar da ke tsakanin sa da inda na ke, na fi tunanin halin da Kaka za ta shiga da Zaliha. Na kama bugun Kofar Sani. Ya iso ya na tambayar waye. San da ya gan ni ya cika da mamaki. Ya kama tambaya ta abin da ya faru.
Na zauna na sanar da shi komai. Ya dafe kai ya na fadin, “Lallai ka shiga tsaka mai wuya!”
Washegari da safe ya tafi ya bar ni a kan zai je ya gano Kaka da kuma nemo yadda za a yi. Da yamma ya dawo a gigice. Na tambaye shi, “Lafiya?”
Ya ce, “An kashe Indo, an ba da sanarwar neman ka. Kaka ta na cikin tashin hankali.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Na durkushe a nan ina kuka kamar rai na zai fita.
Yaya zan yi yanzu? na tambayi kai na.
Bayan fitar Sani, na yanke shawarar fita na zagaya ko Allah zai sa Zaliha ta yarda dani.
Sa’ilin da na isa gidan su ta gan ni, ihu ta kama yi ta na kiran jama’a, abin da ya sanya ni fita da gudu. Hakan ne ya tabbatar mani da cewa ita ma ta yarda da Kazafin da aka yi mani.
Haka na dinga yawo cike da baKin ciki har yamma ta yi. Na sami gindin wata bishiya da ke bayan gari na zauna ina kuka da tunanin abin da ya dace in yi. Kamar an ce in kalli bayan bishiyar, sai na hango wani abu kamar kyamarar bidiyon Indo da Sani. Na dauka ina duddubawa. Ai kuwa ita ce tabbas. Na dauka cike da zumudi na nufi gidan Sani, na tarar da shi cikin tashin hankalin rashin gani na.
Cike da zumudi ya tambaye ni inda na je. Ban Boye masa ba, na sanar da shi har kyamara din da na tsinto. Washegari da kai na na kai kai na wurin ’yan sanda. Ai kuwa kamar mage ta ga Gera, su ka damKe ni, su na tambaya ta yadda aka yi. Ban ji tsoron sanar da su komai ba. Nan da nan aka tafi aka kamo Alhaji Yawale. Sai dai ya Karyata abin da na ce. Babu bata lokaci, aka shigar da mu kotu, aka fara shari’a. Babu bata lokaci, lauya na ya fito da shaidar kaset, aka sanya, sai ga duk abin da su ka Kulla na kashe Alhaji Shehu. Anan Allah ya kubutar da ni, shi kuma Alhaji Yawale aka yanke masa hukuncin kisa.
Zaliha ta nemi afuwa ta, mu ka yi auren mu, na maye mata gurbin miji da iyaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *