LABARIN RAYUWATA CHAPTER 2 BY Ayeshay bee
Www.bankinhausanovels.com.ng
A hankali Suhaima ke samu sauki, da ke akwai orthopaedic doctor in da ke zuww asibitin yana duba ta. Abin yana zuwa da sauki sosai don har an fara koya mata taka kafan. Qur’ani kuwa tun ranar da su ka fara da Dr Fahad bai yarda an tsaya ba, har ma sunyi nisa. Ganin tana saurin dauka ya sa ya ke dan hada Mata da wasu littatafai gabadaya. Suhaima ko jinta ta ke wani fayau kaman ba ita ba saboda azkar in da ta sa gaba d istigfari. Hakanan kawai ta ke jin ta cikin annashuwa, kaman rayuwar ta ya canja gabadaya, sai yanzun ta gane ba abinda ya kai ka koma wa Allah dadi.
+
A gidan su Rufaida ko tuni su ka fara shiryen shiryen bikin da ya rage sauran wata uku sai dai ba tare da sa hannun ango ko Amaryan ba. Wani zuwan mahaifin Fahad da su ke Kira Abbah Kaduna ne ya ga irin ramar da Rufaida tayi gabadaya ta yi baki ta rame. Ganin hakan ya sa ya Kira ta gefe don Jin ko aiko abinda ke damun ta game da auren amma ta tabbatar mishi bbu, Fahad inma sai da ya tuhume shi ko akwai abinda ya ke mata shi ma dai babun ne. Mahaifin ta Baffah ya samu akan ko su hakura da auren tunda yaran kaman ba su so. Aiko ya ga bacin rai gun Baffah, kaca kaca ya mishi da ke daman shine Yaya, ya tabbatar mishi da ba abinda zai sa a fasa wannan auren. Don Haka Dr Fahad da Sister Rufaida sai hakuri.
“Oh yau dai ya kamata muje mu duba Suhaima gsky” Anty Ke maganan tana typing a system inta, Zaune su ke gabadaya a parlor suna kallo Amma as a workaholic ba ta iya Zama hakanan. Lecturer a Kaduna polytechnic da ke tudun wada, tana koyarwa da Course in SLT wato Science and laboratory technology. Mace mai ilimi sosai da ta San mahimmanci karatun boko Kuma ta daraja shi. Haka yaranta gabadaya ta daura su akai domin ko gabadayan su ba dakiki, da kanta ta ke sparing time ma ta musu lesson. sai dai Kuma Kash! Bata ba Ya’ya’n ta karatun addini kaman yanda ta basu na bokon ba. Ba Wai ba suyi bane gabadaya, Aa suna zuwa islamiyya kullum sai dai ko kadan ba ta damu da ta tmby su abinda aka koya musu koma ta koyar dasu kaman yanda ta ke wa na bokon.
Da murna Anisa ta tashi “Yauwa daman 2 days nayi missing inta so Zan biki”
“Nima zanje” Muhibba ta fada hankalin ta na Kan littafin da take dubawa. Kusan ita ce ta dauka gabadaya halin Antyn a gidan, kullum ka ganta da littafi gaban ta.
Nan fa Kulsoom da twins su ke ihun su ma zasu je har sai da Faroukh ya daka musu tsawa sannan su ka natsu.
Siririn tsaki ya ja “Za ku Wani cika ma mutane kunne”
“Ehm ehm Faroukh ban son zalunci fa”
“Allah Mummy sai ana musu haka ne. Ni wai Mummy wai wannan yarinyar ba zaku nemi iyayen ta bane ko Kuma Zaku huta haba!”
“Amma ai kana ganin kokarin da babanka da Uncle Musty ke yi ko”
“Mummy mutanen tunda fa kuka ji haka ba zasu fito ba, may be bata dasu ne”
“Ni dai yanzu tashi ka shirya da Kai zamu fita” tashin yayi ya nufi hanyan dakin shi yana gunguni “Duk Mimin nan ta jawa mutane”
“Haka kace a kunnen Uncle Musty” Da sauri ya juyo ya daga hannayen shi alaman surrender “Wai mommy ki rufa min asiri kisa aji mu da Uncle”
Mustapha ba ya gari so Maryam da Haydar kawai ta nufi asibitin. A haraban asibitin su ka hadu, da gudu Kulsoom ta je wurin ta daman ita ce mutuniyar ta, a daddafe su ka gaisa kafin su karasa cikin asibitin.
Dr Fahad da Suhaiman ne kawai a daki yana mata bayanin wani hadisin sahihul bukhari. Yana ganin su ya ajiye littafin kafin ya juyo gaida Anty “sannnun ku da zuwa, Anty Ina Kwana” Ya kirata kaman yanda yaji Su Mustapha na kiranta. Da murmushi kwance a fuskan ta ta amsa hadda zolayan shi”Dr naga alamun ka Saba sosai da patient in nan naka, anya za ka sallamo mana ita kuwa?”
“Ai Anty Ina ganin nan da 2 weeks ma za ayi discharging in nata”
“Ah Ma Sha Allah jiki kam yayi sauki Alhmdlh”
Gabadayan su suka gaisa da Suhaima hade da Mata ya jiki bayan Dr ya fita Amma banda Faroukh da ya maida hankalin shi gabadaya Kan wayan shi. Sai daga baya Anty ta lura sannan ta zungure shi “Kai wa Faroukh lafiyan ka, ba ka iya gaida mara lafiya bane” tabe baki yayi kafin ya juya ya watsa mata wani mugun kallo “sannu ya jiki?” “Alhmdlh” kawai ta bashi amsa ba tare da ko Kallon shi tayi ba. Ganin Anty ta cigaba da yin fadan ya sa yayi saurin mikewa zai bar dakin.
“Yauwa Faroukh please dan siyo airtime tunda fita zaka yi” Maryam ta fada.
“Ai ni ba bawan ki bane ba” Bai jira Jin wani comment ba ya rufe kofan dakin “Allah ya shirya” Anty ta fada tana girgiza Kai. sai dai Muhibba ce ta je ta siyo mata credit in.
Ba su wani Jima ba su ka bar asibitin amma sun bar Maryam a nan da ita ba lokacin za ta tafi ba.
Dr Fahad ko Yana barin dakin ya hadu da Rufaida idanuwan ta sun kumbura sun yi ja alamun kuka tayi. “Me ya same ki?” Ya tambaye ta cike da mamaki. Kauda kanta tayi saurin yi sannan ta maida idanuwan ta kasa. “Kai na ke ciwo” kallo daya ya mata ya San ba asalin abinda ke damun ta kenan ba, Ya mata sanin da zai iya gane ta inta yi karya ko Kuma tana kokarin boye wani abu. Shaking Kan shi yayi “Kar ki fada min abinda ba shi bane don kin San zan iya gane ki” wannan karon Kam shiru tayi domin ta San magana daya zata yi ta rushe da kuka. Wayan da ke hannun ta ya bi da kallo da alamun waya ta gama. “Mu ga wayanki” ba musu ta mika mishi, Yana amsa yayi sliding cikin call logs inta. Sunan Fa’iza ya gani karshe “Wani abu ya faru a gida ne?” Girgiza kanta tayi. “Okay Zan wuce gida tunda am now a stranger to you baki iya fada min damuwanki, karfe nawa za ki gama schedules inki na asibitin” “Four” ta bashi amsa.
“Shknn Zan zo in dauke ki” ya fada kafin ya wuce abin shi.
Aiko Yana komawa gida ya tarar da abinda ya sata kukan. Daga kofan falon ya ke jiyo Muryar Dada tana ta wa Aliyu fada cikin natsuwa “Haba Aliyu zagi za ka ja min, ni dai nasan ban baka wannan tarbiyyan ba”
“Ki yi hakuri Dada na bata Miki rai amma ba Zan iya Kallon ana ci Miki fuska ba inyi shiru” girgiza Kai tayi cike da takaici “Allah ko Ali? Amma har kana iya maidawa Mahaifiyar ka magana ko bakomai ai ta ci darajan Abbanku da yayanku ko balle Kuma ta haifeka”
“Toh Dada Kiyi hakuri ba Zan sake ba” badan ranshi yaso ba ya fada bai jira ma amsan ta ba ya tashi ya fita daga Falon kaman zai fashe, ba ta dakatar dashi ba sanin irin zuciyan shi. Ai ko a kofan falon su ka ci karo da Fahad, kallo daya ya Mai ya kauda Kai ya wuce dakin shi. Fahad ko jiki a sanyaye ya karasa Falon.
“Dada sannu da gida”
“Ushe binga am har en yattake? Noi kude?” (Sannu dana har ka dawo? Ya aiki)
“Alhamdulillah, Dada Ummi ta Zo ko?” Idon shi kasa ya ke magana, kana Jin kasan ya shiga wani Irin hali. Tausayi ma ya bawa Dadan sai dai ba sai ta bashi amsa ba yanayin shi kadai ya tabbatar mata da ya riga ya sani.
“Dada Kiyi hakuri Dan Allah, In Sha Allah watarana za ta gane”
“Bakomai Dana Nima ban taba riketa ba. Yanzun ma akan aurenka da Rufaida ne. Ni nace ma ko za a hakura domin zaman lafiya yafi zama dan sarki amma Baffanku ya ki zancen” murmushi ya kakalo Wanda ya tsaya iya labba kawai “Kar ki damu In Sha Allah aurena da Rufaida za ayi shi cikin kwanciyar hankali.”
“Ehm ehm Binga am, kasan bakin uwa kuwa? Kar kazo ka samu matsala daga baya Ina jiye maka tsoro”
“Allah ya San ba biyayya na ki Mata ba Dada Kuma bata da kwakwaron hujja a addinance da za ta hana aurena da Rufaida” shiru Dada tayi don ka tasan gsky Aliyun ke fadi.
Faizah ya kwala wa Kira ta fito “ki same ni a sashen mu” kawai yace kafin yayi wa Dada Sallama ya bar falon.
Tun kafin ya karasa sashen nasu ya ji Karan shigowan text wayan shi ko daya duba Ummi ce: Hamma i’ve warned her so consider the marriage cancelled. Murmushin takaici kawai yayi a ranshi Yana fadin “its not that easy Ummi” don ita acewarta Dada ke sa Baffah yin komai ta mallake shi, unknown to her Baffah mutum ne murdade da in yayi niyyan abu to fa ba Wanda ya Isa ya canja mai.
A hankali ya juyo ya kana Kallon Faizah da tayi five minutes tana jiran ya mata magana. “Meye sa Kika Kira Rufaida Kika fada mata abinda ke faruwa a gida?” Gabadaya jikin ta rawa ya ke sanin ba ya musu wasa har gumin wahala ta fara hadawa “ba magana na ke Miki ba?”
“Yayah ka yi hakuri pls” wani irin harara ya bita dashi “ba abinda na tambayeki ba kenan”
“Kawai kawai fa na kirata ne sai na bata lbr”
“Saboda gaki parrot ko? Ba ki San asibiti ta ke ba tana treating patient in ta je tayi mistake fa rai nawa Kika wahalar? Bayan kinsan halin Faidah da Saurin rudewa” wannan karon gabadaya kasa ta zube tana bashi hakuri ganin yanda ya ke fada sosai. Tsaki ya ja “infact me ya dawo da ke gida?”
“Weekend nazo”
“Weekend tun ran Thursday? Ki hada kayanki you are going back right now maza” da sauri ta bar dakin. Aliyu da ke zaune yana sauraran su ne ya ja dogon tsaki “ba fa ita ta Kar zomon ba” Yana fada ya fuske ya cigaba da danne danne a wayan shi.
“Aliyu ni kake wa magana haka?”
“Yi hakuri ba da Kai nake ba?”
“Da Mahaifiya ta?” Shiru Aliyu yayi kafin ya tashi ya shige cikin dakin shi.
Sai da ya Kai Faizah har cikin KASU sannan ya nufi asibitin dauko Rufaida.
Suhaima ya fara zuwa dubawa ya samu tana ta bacci abun ta. Nan da nan ya ji ran shi yayi sanyi. Lallai fa sauki ya samu, ya dan Jima a dakin Yana Kallon sleepy face inta. Tsintar kanshi yayi da ciro waya ya fara snapping inta. Ya dauka kusan biyar sannan ya bar dakin yayi dialling numban Rufaida. Daman ta gama shiryawa so tana ganin numban shi ta yima Nabeela sallama ta fita haraban asibitin.
Tana fita ta hango shi suna magana da Dr Najib, kawai sai ta wuce wurin motan shi. Ta Kai five minutes tana jira kafin ya taho “Sorry Amarya na barki ko?” Bata tanka shi ba har ya tada motan su ka bar asibitin.
“Ina zamu je?”
“Gida” ta amsa a takaice
“No not there, let go somewhere”
“Ya Fad fa na gaji, I’ve been working since morning”
“Inda Zaki huta Zan Kai ki and I guess tomorrow is ur day off”
Turo baki tayi kaman za ta fashe shi abin ma dariya ya bashi, wato Faidah ba zata taba canjawa ba.
“Pardon me” kawai ya ce ya cigaba da driving.
A crystal garden yayi parking, wani open space su ka nufa, the place scream peace and beautiful!
“You still come here?” Ta fada with some suprise expression.
“Why not? I like it comfort, Bismillah nasan you are hungry”
“I can’t eat here”
“Ni kadai ke Kallon ki”
“Still”
“Come on I’ve feed you with my own hands” sanin ba zai yi giving up ba yasa ta fara cin snacks in.
“Rufaida” ya Kira sounding serious, ganin haka ta Mika mishi attention in ta gabadaya.
“Are you willing to marry me?” Shiru tayi for some seconds tana tunain Mai zata fada mishi, a hankali ta fara magana “is not like I have a choice”
“Ina saurayin ki”
Shiru tayi gabadaya jikin ta yayi sanyi, ba ta San sanda kwalla ya fara cika Mata idanu ba “Ya fad he dumped and betrayed me, he cheats on me” zuwa yanzu Kam kuka ta ke sosai, shi dai Fahad ka Sa ce Mata komai yayi sai kallo da ya ke binta dashi, ya najin kaman ya ja ta jikin shi ya rarrashe ta Amma he can’t, ba da bane. She looks hurt and pale, hanky ya ciro da ga cikin aljihu ya Mika Mata “can you please stop crying for him”
“Ya fad am am hurting inside” ta fada with a stutter.
“I understand but share hawayen ki kiji” yi tayi kaman yanda yace in tana ajiyan zuciya, tsaya yayi har sai da tayi calming kanta sannan ya ce “tell me me ya faru? Spit it”
“He used me, Yayi succeeding ya sa na fara son shi but he ends up betraying me claiming me that Ina resembling Ex in shi da ta yaudara shi and that’s why he choose me ya rama abinda ta mishi. Is it fair? I don’t even know her fa, ba laifina bane and I can believe me he say it to my face” by now she is mercilessly sobbing.
“karki damu maybe daman shi in ba alkhairi bane a gareki don haka ina fatan zaki fawwalawa ALLAH dukkan lamuranki”
“Bakomai ya fad, i feel ease now that i share it out”
“you should have done that since. by the way, meye sa baki kawaye”
“i have some little”
“Ina nufin ƙawar da zaki iya tunƙara kin sanar da ita da mun ki, hakan yana da amfani sosai”
“you have always been my friend since from time”
“still, Kinsan ance ciwon mace na ƴa mace. ina ganin kaman za tafi fahimtar ki fiye dani. you even have trust issue Faidah”
“Ya Fad kawayen nan sai a slow kananun maganganu da gutsiri tsoma bai taba karewa”
“Just one ma ta isa and if you can consider Nabeela, she likes you” dago kanta tayi tana kallon shi cike da mamaki, aiko four eyes su kayi maimakon ya dauke winking ma ya mata, saurin saukar dana ta tayi”
“That aside for now let give an us a chance”
“you mean”
“i mean let make this relationship works, we don’t even have another option” da dariya ya ida zancen nashi making her smile.
“okay”
“you mean YES!” Nodding kanta tayi in affirmative.
“That will be good” shiru yayi yana nazarin abin da zai fada mata, ya kuma zata dauki maganar tashi.
“Ya fad you want to talk”
“waya fada miki?”
“i can read you”
“okay! ehmm faida maganan Ummi nake son miki, kinsan despite all her flaws i still love her ko”
“nasani” kanta a kasa ta bashi amsan.
“so please ina son kiyi hakuri kuma kar ki raina min ita, mahaifiyata ce she deserves my respect”
“bakomai ya fad, Allah ya bani iko”
“Ameen, in har kika min hakan kin gama min komai. NAGODE”
murmushi tayi har sai dai dimples inta ya lotsa.
wannan kenan!
Cike da sha’awa ya Kallon ta har sai da ta Kai karshen Aya.
“Ma Sha Allah Suhaima, you are very brilliant, Allah ya Kara basira, ya sa ki amfana da karatun gabadaya, Ina fatan Zaki yi aiki da abinda muka karanta Kuma kema ki koya ma wani domin ko Manzon Allah SAW Yana ce ‘khairukun man ta’allamal Qur’ana wa’alamahu’ mafificin ku shine Wanda ya San Al-qur’ani Kuma ya sanar dashi”
Unknown to him hawaye kaman famfo ke fitowa daga idon ta sai dai sunkuyar da kanta kasa da tayi Bai bashi daman gane hakan ba. Ba shakka ta taba irin wannan a baya da mutumin da ta ke wa Kallon shakikinta unknown to her shi ne zaman su na karshe.
“Kaman yanda na fada Miki” Dr Fahad ya katse Mata tunanin “Gobe za a sallame ki, Ina Mai baki Shawaran yarda da kaddara a dukkan halin da Zaki tsinci kanki ki gode wa Allah sannan Kuma ki rike addini kar kiyi Wasa dashi” shiru yayi Jin sheshekan kukan ta.
“My God! Don’t tell me you are crying Suhaima”
“Sorry Dr, kana nufin shikenan kenan”
“What? No No no, akwai zumunci Mai karfi tsakanin mu, I will always check on you”
“Are you sure”
“I mean it, I will be leaving for Abuja now”
“Allah ya kiyaye hanya, Thank you for everything Dr, I really appreciate …”
“Shhhh Kar ki fara fa na fada Miki ke kanwata ce ko” murmushi tayi kawai kafin ta sa hanky ta goge sauran kwallan da ya rage a fuskan ta.
“Toh ko kefa, gwara ma ki daina kukan nan Dan ba kyau ya ke Miki ba and I hate it when my sister looks ugly” dariya tayi sosai wannan karon kafin ya Mata sallama ya wuce kamar ba zai bar dakin ba, he knows that dole haduwan su zai ragu da ga rana irin wannan and he will surely miss her, sabo turken Wawa.
A kofan dakin nata ya ci karo da Faroukh da alamun ya Dade a kofan dakin. Hannu ya Mika mishi “You have been here”
“Ehmm nazo Naga Kuna magana so shiyasa na baka space”
“Oh Thank you” ya fada yana wuce wa. Saurin kamo hannuwan shi Faroukh ya yi “Zan so in baka shawara”
“Shawara Kuma?”
“Ehmm, Dr how can you let a stranger have that effect on you, she is just a patient and someone you hardly knows for God sake its better if you stay away. Am warning you”
“Ehmm really? So waye Kai da za ka bani wannan Shawaran Young man? Ka koyi fita daga abinda ba ruwan ka” Bai tsaya Jin Mai zai fada ba yayi tafiyan shi. Murmushi Faroukh yayi kawai hade da girgiza Kai “it seems like they will never understand what he is trying to warn them”
Da karfi ya tura kofan dakin nata, tana zaune a kasa still tana karanta wani littatafai da Mustapha ya kawo Mata domin ta dinga rage kewa. “Sannu da zuwa” ta ce mishi. Tsaki ya ja mai karfi “munafukar Allah ta’ala, nazo ne in Miki gargadi, na ji cewa gobe za a sallame ki so ina mai baki Shawaran tattarawa ki koma inda Kika fito Kar ki sake ki ce zaki zauna cikin family inmu, in ba haka ba ki kiyaye abinda zai biyo baya. Saboda ni dai kinsan bazan taba yarda da ke kaman yanda sauran su ka amince miki ba.” Kala ba ta ce mishi ba har ya gama fadin abinda ke ranshi ya bar dakin. Wani kuka mai karfi ta rushe dashi.
Wata Sabuwa inji Yan caca…