MAFARI CHAPTER 5 BY UMMU AZAMM
Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin sati biyu da tarewar su yakaka a gidan madam saly ,sun zama ƴan gari a da’irar ta yadda yakaka ta san ɗakunan manyan kilakai da ƙananun karuwan da suke unguwar saboda aiken ta da madam saly take wurin su , a gefe ɗaya kuma ta zama ƴar ɗakin samy baby , wacce bayan dawowar yakaka gidan madam saly ta gama nazarin yarinyar tsaf , ta gane bata san ma mai kalmar bariki take nufi ba kamar yadda da tayi zaton yakakar ƙaramar karuwa ce , sai ta fahimci ashe yakakan neman abun sawa a bakin salati take tare da wajen da zata sanya haƙarƙarin ta , dan haka sai ta jaa ta a jiki ta maida ta mai gyara mata ɗaki tare da yi mata ƴan kananun aike da aiki , ita kuma tana bata ƴan kuɗaɗe bayan jibgin suturun ta da ta fitar ta bata kwance , tun yakakan tana ɗari-ɗari ganin abun da samy baby tayi mata a farkon haɗuwar su , har dai ta zo ta saki jiki da ita , sosai take kyautatawa samy baby da ta riƙa a matsayin uwarɗakin ta , wacce take samun alheri tare da sakewa a wurin ta , domin a lokuta da dama har ƴar hira samy baby take zama su yi da yaks ,
Aikin gidan madam saly kuwa tuƙuru yakaka take yin sa domin gwanintar da take nunawa ya faranta ran madam saly da take ganin ta a matsayin ginshiƙin su cikin duniya a yanzu , bata da wani lokaci nata na kan ta sai na aikin burkutu wanda ba’a sanya ba ma yi take kamar su wanke dawa , juya ruwan dahuwar burkutun da kuma tace shi wanke kayan madam saly da gyara mata ɗaki , tun safe idan ta kama aiki sai dare karfe sha ɗaya take samun hutu ,” wanda hakan ke matuƙar farantawa madam saly rai har take ganin wautar kan ta da farko, da ta so korar su ashe dai maganar ɗan liti dutse ,
Ga falmata ma sai sam barka domin kuwa har ɗan kumatu tayi ta sake mul-mul , sakamakon cika mata ƙundu da ɗan liti yake da cimar daɗi kullum dare kafin su kwanta bacci , ga kuma labaru masu sanya nishaɗi da yake bata har bacci ya ɗauke ta ,bata zuwa ko’ina daga ɗakin ɗan liti da yake daga wajen filin rawa sai cikin gidan madam saly da take aikin wanke-wanke kofuna tare da farantan aikin burkutu tsawon yini a cikin gidan , bata da wata matsala saboda duk lokacin da yakaka ta ɗan zagaya zata taho bakin fanfon da take zaune din-din a gefen sa ta shafi kan ta koh kuwa fuskar ta , ta kuma tambaye ta bata da wata matsala koh ? Nan zata amsa mata cikin farin ciki da ita bata da wata matsala ,3
Haka zata sake komawa bakin aikin ta tana mai farin cikin sauyin rayuwar da suka samu , musamman farin cikin da take hangowa a fuskar ƙanwar ta wacce ɗan liti ya wadata ta da ƴan kayayyakin gonjo na ƴan matasan yara maza sa’annin ta fes-fes da ita hasken ƴar luwai ɗin fatar ta ruwan zuma yana bayyanuwa,
Ranar da suka kwana huɗu a gidan ɗan liti yayi mata kyautar kayan wanda daga ita har falmata kyautar bata wani faranta musu ba , saboda ƴan rigunan basu da wani girma kayan turawa ne , su kuma sun san kayan nan burguza burguza da falmata ke sanye da su sune rufin asirin su a kasantuwar falmata namiji saboda kayan ya boye ɗan tudun kirjin falmatan wanda suka fara tasowa tare da bunƙasa , 4
Da kƴar yakaka ta shawo kan falmata wacce da farko ta tubure akan shawarar da yakaka ta kawo na falmatan ta dunga sanya riguna biyu bayan ta tamke kirjin ta da ɗankwali ,saboda boye tudun tare da yi mata gargaɗi kada ta yadda ta sauya kaya a gaban ɗanliti duk juyin duniya , ta kan ce
Kiyi hakuri falmata har mu ɗan tara abun da muka tara anan ɗin zuwa lokacin kuma mun san gari sosai idan ya so sai mu koma wani wurin da babu ƴan iska mu raɓa ki koma saka kayan mu na mata , kamar kowacce mace ina nan ina ware miki kayan ki cikin kayan da nake samu ,”2
STORY CONTINUES BELOW
Ranar da ta fara ɗaure kirjin ta yini tayi tana fama da ciwon kirjin , amma da ta kwana biyu sai ta saba ta daina jin ciwon ,1
Bata taɓa yin wanka sai sun tabbatar da ɗan liti ya bar da’irar wajen sannan zata yi wankan a gurguje yakaka ta raka ta ta sauya kaya tare da sake gyara mata ɗaurin kirjin ta wanda ya taimaka ƙwarai wurin boye halittun kirjin ta , sai dai salon takun tafiyar ta tare da tudun bayan ta ke sa samy baby tana yawan tsokanar ta da
“Kachallah me jikin mata ,”
tafiyar ka sai kace ta hamshaƙan mata , koh kuwa tace shege kachallah da kai mace ne da anyi manyan kaya a wurin ka ,”2
Idan yagana tana wurin tayi ta sheƙa dariya ,wacce ita ma a yanzu sha’awar rayuwar su yakakan take , domin kuwa har kuɗi da suturu yakaka ta bata daga cikin wanda samy baby ta bata ,”
Haka kwanaki suka yi ta tafiya har suka samu wata guda da ƴan kwanaki a dafdalar wannan gidan , wanda zuwa lokacin yakaka tayi jazur wannan maɗaukakin hasken fatar ta ta ya sake bayyana dal tamkar fitila haka take a waje , ƴar kyakkyawar ƙaramar budurwa mai sanyi tare da yawan fara’a koyaushe cikin murmushi take , ko magana yakaka take haka zaka ga fuskar ta da yalwatattacen murmushi dasashin ta a waje , wanda hakan yake tasiri matuƙa wurin bayyana ƴan ƙananun kyaun ta wanda hasken da take da shi ya fi jaan hankalin mazan da suka fara ƙaraƙaina akan ta fiye da kyan nata ,”2
Zuwa lokacin samy baby ta fara jaan ɗamarar wanke yakaka daga dauɗar datti gami da ƙazantar ƙauye a cewar ta yakaka haja ce me matuƙar tsada , wacce sayan ta sai alhajin da ya rufu ya tada kai , ” sai ya so zama tamkar gasa a tsakanin ta da madam saly wacce ita ma take bada sumfurin tata kulawar ga yakaka domin ta farga gaba kaɗan yakakan zata zame mata hanyar samun arziki ,dan haka ta fara kokarin janye ta daga wurin samy baby da ta lura tana son kawo mata tsaiko domin kuwa ga alama so take ta fanɗarar da yakaka ta sanar da ita daɗin ƴancin kai kamar yadda ita take da nata ƴancin a hannu domin samy baby ba’a ƙarƙashin kowa take ba cikin magajiyoyin gidan , da karfin ta ta shigo bariki da kuma nawin aljihunta tare da gatan ta domin ba kukan yunwa koh na rashin wurin kwana koh kuwa na neman kuɗin zuwa asibiti zubda ciki ne suka kawo ta bariki ba , ƴar cikin ƙwaryar gari ce da gatan ta da kome iyayen ta ma manyan mutane ne sanannu , uwa uba bata da duhun jahilci domin kwalin digiri ke gare ta ,” sha’awar rayuwar barikin take tare da taimakon matar uban ta wacce take sake ingiza ta , uwa uba shaiɗan da yake tsakiyar kan ta yana buga ganga ,2
Gidan kakaf ba wata tsohuwar kilaki da take shakka , sai ma su da idan jarabar su ta busa sigari koh afa ƙwayoyi suka motsa , kuma suka laluba lalitar su suka ji wayam , su je wurin ta neman ƴan kuɗaɗe sanin da suka yi kaf cikin karuwan gidan ba wacce ta kai ta kama kuɗi , da kuma kyauta domin hannun ta a sake yake bata da rowa ,”
Ranar wata litinin da safe yakaka ta wayi gari da wani irin matsanancin ciwon mara wanda tun kwanaki biyu da suka wuce take jin sa kaɗan kaɗan amma ta daure ,3
Har zuwa yanzu da take kan hanyar ta ta zuwa ɗakin samy baby domin ta gyara mata ɗakin ,bayan ta gama kintsa na madam saly kamar yadda ta saba kafin su duƙufa aikin sana’ar su ,”
A dudduƙe da jaan ƙafa ta ƙarasa cikin ɗakin samy wacce take kwance tana sharar bacci daga ita sai ƴar ficiciyar rigar bacci kan gadon duk a hargitse kayayyakin ta tun daga kan rigar mama da ɗan kafai duk a wurge a kan gadon , tayi ɗai-ɗai da kafafu gashin dokin da yake kan ta ya baje akan filon da tayi matashin kai da shi ,” idan da sabo yakaka ta saba tadda ta a haka kullum .
Tana shiga ɗakin ta zube akan shimfiɗar kafet ɗin ta kwanta gami da dunƙulewa wuri guda tana murƙususu , dunƙulewar da tayi ta haɗe guiwar kafafun ta da kirjin ta sai ya sa taji rangwamen kartawa tare da murɗar da marar ta ke mata har ɗan wani bacci ta fara ji yana figarta saboda rashin bacci da tayi daren jiya a sakamakon ciwon cikin ,” bata ankara ba bacci mai karfi ya fisge ta , ta sake jiki sosai tana baccin ta ,
STORY CONTINUES BELOW
Samy baby ce ta farka bayan da taji baccin ya soma gundurar ta , ta daina jin dadin sa , doguwar hamma ta hangame baki ta jaa babu neman tsari daga shaiɗan babu salati , ta gantsare bayan ta ya bada sautin ƙaƙas , tana zira ƙafar ta ƙasa ta sauke akan yakaka wacce baccin ta yake kai mata karo har tsibirin keemala na ƙasar bankok,”
Da farko ta firgita da ganin mutum kwance a gaban gadon ta sai dai fahimtar wacece a kwance ya sa ta ƙewaye ta gami da nufar kofar banɗakin da take ta cikin ɗakin nata , a ranta tana raya cewa gajiyar aiki da rashin bacci ne suka sa yakaka ta bingire anan ta na bacci , tare da sake aiyana niyyar taimakon yakakan har ta samu karfin tsayuwa da kafafun ta muddin yakakan zata yadda ta bi hanyar da zata ɗora ta ,” yo ina ma zata ƙi ?? Ai duk wanda ruwa ya ci shi idan aka miƙa masa takobi sai ya kama ,”1
A firgice yakaka ta farka lokacin da samy baby take tashin ta , “cikin inda-inda ta fara bata haƙuri bayan ta gaishe ta, tare da faɗa mata cikin ta ne yake ciwo amma yanzu ya lafa ,”ta daina jin ciwon sa sosai , sai dai lema-lemar da take ji ta ƙasan ta ya sa ta gaza miƙewa sai faman muskuɗawa take cikin ran ta tana Allah ya sa dai ba fitsarin kwance tayi ba , toh amma ai ita bata fitsarin kwance tun da ƙuruciyar ta bare yanzu da ta zama ƴar budurwa ,
Tunanin ta ya katse lokacin da samy baby tayi mata umarni bayan ta miƙa mata kuɗi akan ta sayo mata soyayyar indomi da ƙwai tare da shayi haɗin murtuku ya ji sugar sosai ,”1
A sanyaye yakaka ta miƙa hannu biyu ta ƙarba tana mai taraddadin tashi kar samy baby ta ga yadda ta jiƙa mata kafet ,” amma ba yadda ta iya haka ta miƙe tare da nufar bakin kofa
Bin bayan ta da kallo samy baby tayi tana tunanin me ya sanyayar mata da jiki ?ko cikin ke damun ta saboda ta san a wurin aiki da aike yakaka bata da sanya ,” karaf idanun ta suka sauka a bayan yakaka inda shuɗin siket ɗin yadin da take sanya da shi duk ya baci ,”
Ke yaks dawo nan wai ke me yasa kin cika gidadanci ne ?? Yanzu har yau baki yi wayewar da zaki saka pad a jikin ki idan kina menses ba ? Haba mana yaks meyasa kullum ina kai ki kina dawowa , yanzu ba dan na gani na ƙira ki ba da kenan haka zaki fita ?? Ta ƙarasa zancen tana balla mata harara ,”
Ƙasa da kan ta yakaka tayi tana me satar kallon wurin da ta tashi domin ita duk bata wani gane kalmar pad da menses ba , ga zaton ta faɗa samy baby take yi mata akan fitsarin da ta saddaƙar shi tayi a kwance “ɓacin rana”
, sai dai ga mamakin ta wurin da ta tashin ɗan alamun danshin kaɗan ne kuma bai wani fidda kala ba saboda kafet ɗin ruwan kunkumadi ne ita ma da kƴar ta hango danshin toh akan me samy baby take mata faɗa ?? Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji samy baby ta ce ,”
Ki buɗe ƙaramin akwati na ki ɗauki sabon pant da pad ki shiga banɗaki ki gyara jikin ki nan gaba kar ki sake zama babu pad alhalin kin san lokacin yin menses ɗin ki yayi kusa kina jin alamar sa ki tanadi pad idan ma baki da ita ki zo na baki koh kuma ki yi ƙunzugu da tsabatatatcen tsunma kin ji koh ,??
Da sauri yakaka ta gyaɗa kai tana rarraba idanu , domin ita har ga Allah ba wani fahimtar dogon bayanin samy baby tayi ba , koh ta so fahimta ma kalmomin da ta jefo guda uku da turanci sun hana ta gane kan maganar , dan haka kawai sai ta je ta durƙusa a gaban akwatin tayi zugui ,”
Fahimtar da samy baby tayi yakaka fa bata fahimce ta ba ya sa ta tashi ta zo ta buɗe akwatun ta tare da ciro sabon pant fil sai tashin ƙamshi yake ( ku sani mata tsabtace undies tare da wanke shi da kuma goge shi wani babban sirri ne na sanya nishaɗi a gangar jiki tare da bada kariya na musamman daga kamuwa da cututtukan da suke addabar mata daga ƙasan su a zamanin yanzu ,ki kasance kullum cikin wanke tare da goge panties ɗin ki bayan kin shanya su a rana sun yi a ƙalla awanni shidda a rana ) da kuma ledar pad mai guda takwas ta danƙa mata,” ki shiga banɗaki ki gyara jikin ki ,”
STORY CONTINUES BELOW
Da sauri yakaka ta amsa da toh ,
Kin iya amfani da shi koh ?
Gƴaɗa kai ta yi sai kuma ta sake girgiza shi ,”
Samy baby wacce ta fara zowa wuya da gidadanci tare da jahilcin yakaka tace ,”
Buɗe baki zaki yi kiyi magana ba ki dunga gƴaɗa min kai ya kadangaren gobara ba , kin iya amfani da shi koh na gwada miki ??
A sanyaye ta amsa ban iya ba ,”
Karɓa tayi tare da nuna mata yadda ake amfani da shi ta ɗora mata da ,”ki wanke siket ɗin naki a banɗakin zan miko miki wasu kayan ,”
Ƙiris ya rage yakaka ta kurma ihu lokacin da ta ga yadda jikin ta ya ɓaci da jini ,”tashin hankali na shiga uku na lalace fitsarin jini na fara shikenan nima zan mutu na bi su abba wayyo Allah falmata waye zai kula min da ke ,” wannan shine tunanin da yakaka take yi lokacin da take wanke jikin ta da kayan ta , tana yi tana sharar hawaye ,”3
Ido jazur ta fito bayan ta shirya kan ta cikin kayan da samy baby ta miƙa mata na wata koriyar atamfa riga da siket , sun zauna mata ɗas kasancewar ita ma samy baby ƴar madaidaiciya ce tamkar ta ,”
Sumi-sumi ta wuce tana share guntun hawaye ta nufi wurin aiken da aka mata ,’ samy baby ta bi bayan ta da kallo tana me jin tausayin yarinyar na zaunawa cikin ranta , ta fahimci yau ne ta fara tsintar kan ta a yanayi na al’ada saboda tashin hankali da damuwar da ta gani tare da yakakar wanda ba kome ya jawo hakan ba illa jahilcin addini da na boko saboda da tana zuwa makaranta kowacce daga cikin ta boko koh ta islamiyya a shekarun ta da take sha shidda da ƴan watanni ya ci ace ta san me wannan jinin yake nufi saboda ana wayar da kai a makarantu ,” nan take ta ji tana son tayi yunƙuri domin ganin yakaka ta ɗan samu ilmi ko kaɗan ne domin ita kan ta harkar da take son ɗora ta akai idan kana da ilmin boko kafi samun kasuwa wurin manyan wayayyun mutane irin wanda take yi wa yakakar yangen su , domin su basu cika harka da jahila ba ,” zamani ya zo da kome zaka yi domin cigaban kan ka sai kana da ilmin zamani ilmi shine gishirin rayuwa ,”1
Tana tafiya tana rarrakaɓewa ta jikin gini tafiyar kan ta ba yadda ta saba take yin ta ba tana tafe tana mammatse kafafu domin ji da take tamkar ƴar audugar da take jikin ta zata faɗo wacce rashin sanya ta a dai-dai ya sa take jin hakan ,” cikin ranta kuwa kalmomin wasiyyar da zata barwa falmata take haɗawa ,”
Yaks baby , yaks baby , ke yaks ji mana wai yane ina miki magana kina wani ƙara wuta tamkar baki ji na , zo mana magana za muyi ,”
Muryar babasho mai sayar da wiski da su matallah , zuwa kan taba sigari da sauran kwayoyin sanya maye a cikin ɗan shagon da yayi da tsoffin kwanukan rufi da katako ,ta katse mata tunani , babasho yayi masifar maƙalewa yakaka , yana bala’in son ta kamar zai yi hauka ,sai dai samy baby ta kasa ta tsare ta hana ya samu damar koh ɗan zantawa da yaks , duk kuwa da cewa kullum sai ya je rumfar saly baby ya sai burkutu dan kawai ya samu ya ga fuskar yaks ,” samy baby ta kan faɗa mata ,” ta wuce ajin babasho fintinkau , me zata yi da wannan sauran tabar ? Da duka-duka idan aka haɗa jarinsa da shagon nasa ba zai fice dubu goma ba ,?? Ai sama tayi wa yaro nisa tsakanin ta da ire-iren su babasho sai dai ta kira su ta aike su ,”amma ita kalar manya ce kalar hamshaƙan da suka ci suka tada kai da naira ,1
,” kar ki kuskura ki kula shi yaks bashi ma da isasshen hankali idan ya sha ta kai masa karo yana iya shaƙe ki ya kar ki ya kar banza atoh kiyi hankali,”
Ga yakaka kuwa ita ba ma babasho ba da take jin mugun-tsoron sa saboda chukurkuɗaɗɗan gashin sa da ya tara akai baya wani kula da shi duguzum-duguzum ya fenta kan kalar jaa shuɗi da kuma yalo , uwa uba faranta hannunsa zaƙo-zaƙo da suke cike taf da annakiyar dauɗa suna tsorata ta har su sanya ta hasashen yadda zai kafa mata farce a wuya idan ya shaƙo ta kamar yadda samy baby take faɗa mata , ita gaba ɗaya maza ma ƙarƙashin ranta tsoron su take , babu wani ɗa namiji da ta taɓa jin sa cikin ranta idan aka ɗauke dakta hamza wanda shi ma ta ɗauki tunanin sa da yake faɗo mata jifa-jifa a zuwan tana tuna sa ne domin taimakon da yayi a gare su ita da ƙanwar ta , bayan shi babu wani ɗa namiji da yakaka take ɗaga kai ta dube shi iyakar ta da su harkar cinikayyar su ta burkutu su , su zo saya ta je ta kawo musu ta karbi kuɗin ,” bata taɓa buɗe baki tayi tsiwa koh rashin kunya ga kowa ba duk kuwa da yadda suke kai mata wawura tare da maganganun banza da ita bata ma kai ga fahimtar wasu kalmomin su na batsa ba ,”ita dai ba’a raba fuskar ta da tsadadden murmushin ta , dan haka yanzu ma da babasho yake kwala mata kira koh kallo bai isheta ba haka ta cigaba da tafiyar ta ,’ shi kuwa ya bi bayan ta da kallo yana lashe leɓe tare da lanƙwasa ƴan yatsun sa cikin ransa yana fatan Allah ya kai damo ga harawa koh bai ci ba yayi birgima,”,1
STORY CONTINUES BELOW
Karo taji tayi da mutum wanda zurfin da tayi a tunanin ta ya sa bata ga tahowar sa ba ,” da sauri tayi baya ,tare da durƙusawa ta ɗauko masa makullin motar sa da ya faɗi a hannun sa ta sanya bakin gyalen ta ta goge ƙasan jikin ɗan makullin bakin ta ɗauke da kalmar ban hakuri ta miƙa masa mukullin ba tare da ta ɗago kan ta ba ,
Miƙa wankakken hannunsa mai ɗauke da wankakkun fararen farata ƙal yayi ya karbi makullin agogon hannun sa na ta ɗaukar ido ,”hannun ta bi da kallo wanda kyaun sa da gogewar sa a tsafta irin wanda bata taɓa gani ba ya ɗauke hankalin ta , muryar sa ce ta dawo da ita daga shagalal da tayi cikin hausar sa ta bamarɗe yace ,”
“, Ai ni ke da laifin ina gaugawa ban lura da ke ba yi mini afouwa ,”2
Da hanzari ta ɗago kan ta jin muryar sa da ta yi kamar ta san ta , tana ɗagowa yana gifta ta sai tashin mabuwayin ƙamshin sa da ta shaƙa wanda ya sa ta jin tsaftar sa ta burge ta har ta waiwaya tana bin takun sa da kallo ,”
Har ta je ta amso aiken da aka mata tana jin ƙamshin turaren sa cike taf da hancin ta ,” bayan samy baby ta ci indomie da soyayyen ƙwai ta cika cikin ta har ta barwa yakaka sauran ta cinye tas tare da wanke kwanon , ta tashi da niyyar fara gyaran ɗakin , samy baby ta dakatar da ita tare da cewa ta bata hankalin ta ,” nan tayi mata bayanin jinin haila da ta fara da yadda ake wankan sa , ta kuma jaa kunnen ta akan ta kula kar ta yadda wani ɗa namiji ya ɗirka mata ciki kar ma ta kula kowa a yanzu idan lokacin fara harkar ta yayi ita da kan ta zata kaita a bata maganin hana ɗaukar ciki ta yadda zata ji daɗin cin kasuwar ta ba tare da wata fargabar yin ciki ba , nan dai suka ɗauki lokaci samy baby tana mata huɗuba wanda mafi yawan su ba na kirki bane , idan aka cire wankan hailar da ta koya mata a taƙaice babu wani abun kirki cikin sauran shawarwarin da ta bata ,’
Ki lura da kyau da lissafin kwanakin menses ɗin ki domin ta haka ne idan kin fara harka zaki gane lokacin da kike danger ɗin ki dan ki kiyaye harka a waɗannan kwanakin duk da dak zamu je a miki ƴan dabaru amma kau da bara sai ana haɗawa da zamiya ,”kin ga yau ɗaya ga wata kika fara duk inda wata ya kai shidda takwas zuwa goma zaki iya gamawa toh kwanaki bakwai da zasu biyo bayan kwana uku na kammala jinin al’adar ki sune ranaku mafi hatsari gare ki idan kin fara harka domin tabbas kina iya samun ciki idan kika sake kika yi koh da wasa da lawurjen namiji ne ehee ,sai ki kiyaye kin ji koh ?2
Ba tare da yakaka ta fahimci mafi akasarin bayanan samy baby ba ta amsa da “toh” hankalin ta ya fi karkata ga son sanin wacce harka ce zata ɗora ta akai wacce har akwaj hatsarin samun ciki ?? Ita fa tana tsoron zancen ciki kowacce irin harka ce zata iya hakura da ita idan har zata iya yin ciki , toh amma tayaya ma ake samun cikin ?????? ( ta miƙa tambayar ga masu karatu 😂)4
Cikin sanyin jiki ta koma bakin aikin ta inda duk take a takure domin gani take kamar kowa ya san tana fitsarin jini bini-bini ta leƙa ta kalli bayan siket ɗin ta ,kou kuwa ta shiga bayi tayi tsarki , duk a matse take jin kan ta , sai dai tata damuwar ta kau koh kuwa ace ganin damuwa kwance ɓaro-ɓaro akan fuskar falmata ya sa ta daina jin ta ta sai wani sabon tashin hankali tare da damuwar da ta fi ta farko da taji ya mamaye ta , sam bata ƙaunar ganin falmata cikin damuwa
Falmata nah ! faɗa min menene ?? wani ne ya zage ki ? Koh baki da lafiya ne , yunwa kike ji ?? Koh kina son wani abu ne ?? Koh jiya ɗan liti ya miki wani abun da ya ɓata miki rai ne ? Gaya min dan Allah menene
Ɗan guntun murmushin da daga ganin sa na ƙaƙale ne shi falmata ta ɗora a fuskar ta ,”
Yakaka ni babu wanda ya min kome kuma lafiyata ƙalau , bana jin yunwa ,”
Toh meye ne koh kin tuno da su mama ne ??
Da sauri falmata ta gƴaɗa kai tana me rushewa da kukan da tuntuni yake cin ta , sakamakon abun da ya faru da ita a wurin wani mutum wanda ɗan liti ya ɗauke ta jiya ya kai ta a matsayin shine ubanɗakin sa wanda yake bashi kayan daɗin da yake kawo mata tana cika cikin ta da shi ,”
Ita dai bata san ina ɗan litin ya kai ta ba domin a mota suka tafi ,
Duk da cewa ba gani take ba amma ta fahimci gidan da ɗan liti ya kai ta gidan me hali ne , domin maɗaukakin sanyin da ta ji a parlour da suka tadda mutumin har zuwa kan lallausar abun da aka zaunar da ita akai kujera zata kira abun koh gado ?? Ita dai bata taɓa zama a makamancin abu mai taushin sa ba ga wani fitinannen ƙamshi da ya cika wurin , bata ji ta fara tsorata ba sai da ɗan liti ya ɗibo wani abu mai matsanancin sanyi ya cusa mata a baki da ya umarce ta da ta buɗe bakin ta zai bata wani abu wai shi “ice cream” anan ta ji ta tsorata domin kuwa dawo da abun tayi ta tofar da shi saboda bata taɓa shan abu mai tsananin sanyin irin sa ba ,”
Mutumin da suka tara a falon ya buɗe ƙatuwar muryar sa marar daɗin sauti kamar fasasshiyar gangar ya dunga tuntsira dariya ɗan liti yana taya sa harda shewa ,”3
Watau kachallah bai taɓa shan ice cream ba ?? Ai kuwa daɗi ya bar ka , toh liti bashi gasasshiyar kaza ya ci nasan dai koh daga kan dutse ya sauko ya san nama ,
Wata ƙatuwar cinya ɗan liti ya fisgo ya damƙawa falmata a hannun ta bayan ya miƙa mata kwalin lemun ,”five alive” a ɗaya hannun ,
Maza ɗan kachallari ci kaza ka sha lemu yaro ai ka zo gidan arziki duk wasu kayan daɗi da nake kai maka kana ci kana lashe baki “ya tsohon kare nan ne tushen sa kaɗan ne daga cikin ire-iren kayan maƙulashen da suke jibge a gidan nan yaro saki jiki ka ci arziki ka bar shi a inda ka gan shi ,”1
Cikin sanyin jiki falmata ta kai cinyar kazar bakin ta ta gutsuri kaɗan tana taunawa ,” zaƙin kayayyakin ɗanɗano irin na alfarma tare da zaƙin naman kazar suka haɗu suka sa kunnen falmata motsi har bata san lokacin da ta cinye wacce ɗan liti ya bata ba ,
tana tanɗe baki , ɗan liti wanda suke kus-kus da wannan ɗan tsurut ɗin mutumin shi ya lura da ita ya sake fisgo ɗaya cinyar ya ɗangwala mata a hannu ,”
ungo maza cinye har ƙashin ka tauna ka haɗiye , yau ta shiga ranakun tarihi a wurin ka ɗan kachallari ,”1
Miƙewa ɗan liti yayi bayan sun gama kitsa abun da suka kitsa ,”
Ɗan kachallari ni zan ɗan je na dawo nan kusa ka jira…
Koh kafin ya ƙarasa abun da yake nufin cewa falmata ta miƙe zuruf ta dangwarar da sauran naman hannun ta ”,
Ah ah mu tafi tare nima zan bika ,”
Haɗa ido ɗan liti da wannan mutumin suka yi , mutumin ya yiwa ɗan liti alama da ido akan ya tafi kawai zasu yi waya ,”
Saɗaf-saɗaf ɗan liti ya fita ya jaa musu kofar wanda ƙarar rufe kofar ya sa falmata wacce take tsaye tana jiran amsar ɗan liti ta farga da barin ɗan liti wajen ,”
Kuka ta sa tare da fara taku tana nufar hanyar da ta ji motsin rufowar kofar da ɗan liti yayi lokaci ɗaya tana jera kiran sunan ɗan litin ,”
Dariya ta ji mutumin ya kwashe da ita kafin ta ji ya fara tahowa inda take yana cewa haba ɗan kyakkyawan yaro kachalla menene abun kuka yi shiru yanzu ɗan liti zai dawo aiken sa nayi , kafin ya dawo zo muyi wasa ,”kafin ta ankara ta ji ya sure ta sama yana cewa ,” A ɗaga sama anyi wa wada kwace 😂 ,”Tuƙuru ɗan tsamurmurin mutumin nan yake son danne falmata , sai dai lamarin ya faskara domin daga ya samu nasarar cillata kan gadon kafin yayi wani yunƙuri ta zabura ta mike , babu abun da ya fi fusata shi da har ya kai shi ga danna mata cizo a kafaɗa irin ihun da ta buɗe maƙogoro tana yi tun karfin ta , wanda hakan ba karamin tada masa da hankali yayi ba sanin da yayi matar sa tana nan a sashin ta da yake maƙotan nasa , zata iya jin ihun falmata kuma duk irin manyan alfashan da yake aikatawa matar tasa bata kai ga sanin wannan mafi muni daga cikin su ba watau ,”luwaɗi,” baya kuma son ta sani domin yana matuƙar son ta bai haɗa ta da kowacce mace ba cikin rayuwar sa ita take biya masa bukatar sa uwa uba ita ce silar arzikin sa tare da bazar ta yake taka rawa ,” neman yara maza da basu kai ga balaga ba da yake yi a duk daren lahadi wayewar litinin wani sirri ne cikin rayuwar sa ,”+
Dan haka a wannan karon cikin hakin da gajiyar kokawar da yake yi ya haifar masa , gami da tsabar mugunta ya ɗaga falmata a karo na takwas ya maka ta da kan katifar gami da sanya hannun sa ya danne mata baki , ya fara ƙokarin zare mata bujen ta da ɗaya hannun ,”
Bai ankara ba yaji ta gantsara masa wani fitinannen cizo a ɗan yatsan sa babba , wanda hakan ya sa shi sakin wani ihun azaba jin tana yunkurin gutsire mishi ɗan yatsa ,”
Da ɗaya hannun sa yayi amfani wajen kai mata maruka da duka ta ko’ina amma falmata ko gizau taƙi sakin ɗan yatsan da zuwa yanzu take jin gishiri-gishiri a bakin ta da ta tabbatar jinin sa ne ,” ƙara nutsa haƙoran ta tayi da ya sanya shi ba shiri ya daina dukan ta ya koma roko cikin kuka akan ta sakar masa yatsa ,”
Bata sakar masa da yatsan ba sai da ta tabbatar ta jikkata shi ta inda ko ta sake shi jinyar raunin da tayi masa zai fara sannan ta sakar masa yatsan ta miƙe da sauri tana tofar da jinin da ya zuba mata cikin baki,”
Tana sakin sa ya tashi da gudu ya buɗe kofar banɗaki da yake cikin ɗakin ,’
Tana jin tashin muryar sa tare da ihu lokacin da ya buɗe fanfo yana wanke yatsan ,”
Bin bango ta fara yi da lalube tana neman hanyar fita duk kayan jikin ta sun yamutse , tsumman da take ɗaure kirjin ta da shi ya zazzago wanda hakan ya bawa kirjin ta damar tasowa ,
Sai dai duk yadda ta kai ga lalubawa ta gaza gano kofar bare ta buɗe ta sai kewayawa take yi cikin hawayen tausayin kai da take yi ,” makanta mutuwar tsaye ,”
Ido jawur ya fito ya tsaya ta bayan ta yana kallon ta cikin ran sa yana aiyana irin azabar da zai ganawa yaron nan a daren yau ,”
Cigaba yayi da naɗe hannun sa da Bandage yana kallon yadda take ta laluben bango , chak ya tsaya da abun da yake lokacin da idanun sa suka fara bayyana masa ainahin surar ta ta ƴa mace ,’
Sosai ya ƙura mata ido yana kare mata kallo daga sama har ƙasa domin tabbatarwa ,”
Wata chafka yayi mata tare da haɗa ta da bango yana mai ɗaura hannayen sa akan kirjin ta ,
Zabura tayi ta angaje shi baya,
Dan ubanki daman ke mace ce ??
Shine aka kawo min ke a matsayin namiji ??
Kika bani wahala irin wannan har da yi min rauni ? ashe ma ungulu da kan zabo ce ? Me zanyi da macen titi ? Kuma ma ƙwaila ?
Dan uban ki yau zaki yabawa aya zaƙin ta , sai na wassafa ki ta yadda gaba baza ki sake yadda ayi haɗin baki da ke ba , ƴar yarinya da ke amma har kin san ta kan bariki , kin san yadda ake maguɗi ,
Bugun kofar falon da aka Fara yi da karfi shi ya sa shi dakatawa da maganar da yake yi ,tare da yin kasaƙe domin sauraro , ai kuwa ya tsinkayo muryar matar sa tana danna masa kira tare da cigaba da bugun kofar , wani irin zillo yayi cikin taraddadin riskar falmata da zata yi cikin ɗakin sa ,’
STORY CONTINUES BELOW
Diri-diri yayi yana neman abun yi ba tare da ya lura da falmata wacce ta fara kokarin kintsa kanta ta cikin shigar ta na maza ba,
Bugun yana tsananta tare da ƙarin fargabar sa juyowa yayi da nufin chafkar falmata ya tura ta cikin wardrobe Ya kulle domin ya san muddin matar sa tayi ido hudu da budurwa a ɗaƙin sa da daren nan kome zai faɗa mata baza ta yadda ba , bai kuma san wanne irin mataki zata ɗauka akan sa ba , da ya san ba mai sauki bane domin ya san kalar kishin ta na masifa dan haka ya gama yanke shawarar ko ta halin ƙaƙa sai ya rufawa kan sa asiri ko da kuwa zai kashe falmata ne,
Sai dai ga mamakin sa shirye ya ga falmatan tsaf yaro namiji kamar dai yadda ɗan liti ya kawo masa ita , wanda ya tabbatar a kallo ɗaya baza’a taba gane falmata ƴar budurwa bace ,
Wani ɗan sanyin daɗi ya ji cikin ransa ,
Dan haka ya matso kusa da falmatan
Dan uban ki ga mata ta ta zo tana buga min kofa , idan kika yadda kika yi wani abun da ya sa ta gane ke mace ce sai na kashe ki kin ji ko baki ji ba ??
Cikin sauri falmata take gyaɗa kan ta tana gwalalo ido jin kalmar kisa daga bakin sa wanda azabar da ya gana mata a cikin mintuna da suke ƙasa da talatin ya sa ta tabbatar tsaf zai iya sheƙe ta har lahira ,”
Ungo nan ya watso mata kayan sa masu datti da ya ciro su daga loƙo ,
ki riƙe su a matsayin garƙuwar ki da zata fidda ki gidan nan lafiya
Da gudu ya fita ya buɗewa matar sa da take tsaye daga bakin kofa tana ƙuta , tare da mamakin meye yake yi haka a ciki da bai jin bugun kofa kuma ta kira wayar sa bai ɗauka ba , ita ba kome ya kawo ta ba illah ihun da ta tsinkayo daga sashin nasa ,” ta ɗaga hannu da nufin sake buga kofar ,karaf ya buɗo kofar
Yanayin fuskar sa kawai ta duba ta san ba lafiya ba , lafiya kuwa baban sadiq?
ta tambaye shi ,
Subahananlahi ta furta hakan tana mai riko hannun sa da ta gani naɗe da bandage kafin ta ja shi ciki tana tambayar sa cikin tashin hankali akan meye ya same shi , ‘ shi kuwa sai faman yamutsa fuska yake cikin alamun nuna jin zafin ciwon ,”
Kwantar da hankalin ki my dear ɗan ciwo na ji da wuƙa ,ya furta hakan yana me satar kallon kofar ɗakin sa cikin ransa yana zagin falmata akan me ta tsaya yi masa kuma cikin ɗaki ?
Fitowar falmata rungume da kayan da ta naɗe su da kƴar cikin daya daga cikin rigunan nasa , shi ya maida hankalin matar sa kan falmata ,’
Bin falmatar tayi da kallo lokacin da ta ga ta doshi jikin bango gadan-gadan tana shirin cin karo ,”
Kai yaro kai kuma daga ina da daren nan ?
Chak falmata ta tsaya lokacin da ta ji kafar ta ta zunguri garu ,
Juyawa tayi ga mijin ta wanda yayi kicin-kicin da fuska ,
Baban sadiq kana ganin yaron da nake gani koh dai gamo nayi ?
Cikin bagararwa yace wane irin gamo kuma bilkisu ? Yaro ne ya shigo karɓan kayan wanki ,?1
Kayan wanki kuma ? A daren nan ?
Kuma naga kai kake kai kayan ka laundry da kan ka yaushe kuma ka koma bawa masu wanki , ? Tukun ma yaron baya gani ne naga yana bulunbutuwa ?1
Bagarar da sauran tambayoyin ta yayi ya bata amsar tambayar ta ta karshe almajiri ne kuma makaho ,” nuna masa hanyar fita daga falon , ya saki ƴar wata ƙarar da ke bayyana azabar da hannun sa yake yi ,da hakan ya tilasta bilkisu ta bar sauran tambayoyin ta tare da watsar da wasi-wasin da ya fara zuwar mata na ganin yaro a turakar maigidan nata har uwar ɗaki da dare ,’
Ta kama hannun falmata wacce tun da a garin neman hanya ta bige ɗan yatsan ta da kafar kujera ta raƙube ta tsaya daga wajen tana sauraran duk maganganun su ,cikin ranta ta gudurta muddin ta ga matar nan zata zalunce ta , zata fyaɗe mata biri har wutsiya ta faɗa mata gaskiyar zancen , idan ya so shi mijin nata ya kashe ta a gaban matar ta sa kamar yadda ya ce ,”
Ga hanya nan ka miƙe nan kar kayi kwana ,’
Ɗan turus tayi cikin kokonton
Kai yaro !
Chak falmata ta tsaya wacce har ta fara taku cikin sauri tare da hamdalar kubutar da ita da Allah yayi daga hannun wannan azzalumin mutumin da bata kai ga sanin sunan sa ba ,”
STORY CONTINUES BELOW
Waye ya kawo ka ? Ina nufin tare da wa kuka shigo gidan ?
Unn’umm’un tare tare da alhajin muka shigo shi ya kawo ni ,” cikin inda-inda kalaman suke fitowa daga bakin falmata ,’
Shikenan tafi,”
Babu ko waiwaye falmata ta miƙa hanya , bata yi wata tafiya mai nisa ba ta fara tsinkayo tashin muryar ɗan liti da yake hira da wani , yana ta faman sheƙa dariya cikin salon maganar sa ,” wata irin tsanar sa ta taso ta maƙure ta ,” macuci azzalumi ta ambata a ranta ,’
Hangon ta da ɗan liti yayi ya sa shi miƙewa daga inda yake zaune akan bencin mai gadi suna hirar su ta duniya domin zamu ce ta tadda muje mu ,( yaƙin ruwa ya ci sakaina ,) shi ma maigadin tsohon ɗan iska ne wanda duniya ta gama kare masa ba tare da ya farga ba , duk wasu tsiyatakun da ubangidan sa yake yi ya sani , ya kuma san ɗan liti kawalin ubangidan sa ne , dan kuwa duk lokacin da ɗan litin ya shiga da yaron da ya kawo , nan yake zama a wurin sa yayi jiran fitowar yaron ,’
A ah kaga ɗan kachallarin Alhaji har ka fito ? Iyeeh har da kaya haka alhajin ya baka ,?? Inji dai baka yi masa gardama ba ?? Ka saki jiki ka ci tsokokin nama ka kora da ruwan tatattun ƴaƴan itatuwa yadda ya kamata ? Toh albishirin ka ɗan kachallari ? Kafin ka ce goro kawo kayan na riƙe maka ya furta hakan yana mai karɓe kayan hannun falmata ,”
Sati mai zuwa iwar haka kana nan na sake kawo ka ka dangwali arziki kayi buroshi da zuƙa-zuƙan cinyoyin kaza ɗan kachallari fiye da yadda kayi a yau,’
Ni bazan sake zuwa ba , bazan sake bin ka ba , ka maida ni gida ,’ falmata ta furta hakan tana me rushewa da kuka
Wata ƴar iskar dariya ɗan liti ya kwashe da ita da ya sa falmata ƙaro sautin kukan ta wanda yake tabbatarwa da ɗan liti aikin gama ya gama a tunanin sa ,’
Tsawon dare falmata bata yi wani baccin kirki ba daga ta fara baccin zata ji ƙarar marukan da mutumin nan ya dunga yi mata , cikin ranta tana sake tsorata da mutane gaba ɗaya , abun da ta fahimta a ɗan ƙarancin shekarun ta shine mutane basu da kirki mafi yawan su azzalumai ne tana mace bata huta ba ta zama namiji ma bata tsira ba , sai dai cikin ran ta tayi niyyar boyewa yakaka abun da ya faru da ita domin ta huttashe ta shiga damuwa a dalilin ta , tasan daga lokacin da yakaka ta ji abun da ya faru baza ta sake samun nutsuwa ba har sai ta samo hanyar da take ganin ta bada kariya a gare ta , kwatankwacin wacce ta baro su daga sansanin su , a gare ta samun kwanciyar hankali tare da walwalar da take tsinkayowa daga muryar yakaka yafi mata kome , baza ta so tayi wani abu da zai Wargaza mata farinciki ba , hakan ya sa da a halin yanzun yakaka ta takura ta faɗa mata abun da ya sa ta kuka , taƙi bayyana mata haƙiƙanin gaskiya ta danganta kukan ta da tuno da mahaifan su da tayi ,
Kwanaki biyun da suka biyo baya sun yi su ne cikin takura , ita yakaka al’adar da take yi ita ta hana ta sakewa a matsayin ta na sabon shiga , dan haka duk a takure take jin kan ta gani take kamar kowa ya san halin da take ciki duk kuwa da cewa dai-dai gwargawdo samy baby ta wayar mata da kai tare da saya mata sabbin pad da pants,kuma zuwa yau da take kwanaki biyar da fara yi , ya fara jaa baya, ita kuwa falmata fargabar da take danƙare cikin ran ta akan irin matakin da ɗan liti zai ɗauka akan ta ne a lokacin da mutumin da ya kai ta wajen sa ya tabbatar masa da cewa ita mace ce ,
Sai dai a yau da ake kwana biyar da faruwar lamarin ta ɗan samu nutsuwar zuciya ganin har yau bata ji ko ganin wani sauyin da yake nuna mutumin nan ya gayawa ɗan liti wani zance ba, dan haka ta sake suka yi hirar su ita da yakaka da yagana waɗanda suke ɗan zagayowa su taya ta wanke-wanke , walwalar ta ta sauya zuwa taraddadi ne lokacin da ta ji muryar ɗan liti yana dannanawa madam saly kira ,
ahayye nanayee madam saly fito, fito , fito ki ji sabon bayani abun mamaki ciyawa da cin doki ,wai kamar mu a garin nan za’a nunawa barikanci , za’a yi mana ungulu da kan zabo ,? Chafɗijam , inji masu iya magana suka ce bar ganin ƙanƙantar allura karfe ce , yekuwa jama’a ku hallaro ku ji abun al’ajabi ango ya kwana da ƙunzugu ,5
STORY CONTINUES BELOW
Da ɗai-ɗaya hankali mutanen wurin ya fara dawowa kan sa saboda tsabar ƙwarmaton sa hatta masu cinikin madam saly da suke cikin rumfa sai da suka ji yo shi wasu ma har suka tsallako suka zo ganin dal ,”
Liti yaya ne ? Yaya ne ?ya da irin wannan kiran haka ? Ta samu ne ? Ko kuwa ta guntso ne zata fesar , ? Kunne na tarwai ina jin ka bamu mu sha ,” cewar madam saly wacce take ƙarasowa wurin tare da wasu daga cikin ƴan aikin gidan ,”1
To wallahi yaran nan yaks da ƙawar ta tare da munafiki koh munafukar ƙanwar ta zan ce ? Yo abun ne ya sauya , ninke mu baibai suka yi suka buga mana stamp ɗin sakarkaru na gaya miki, “
Wani banzan kallo madam saly take sakar masa kafin ta jaa ɗan guntun tsaki ,
Ban gane ba ? Daman akan waɗannan yaran kake kwalla wa jama’a kira har da yekuwa ? , kai dai Allah wadaran ka dan liti3
Tsiya ta da ke wutar ciki madam saly , toh na rantse da Allah kachalla dai mace ce , macen ma luntsumemiya kuma nunanniya , shine dan iskanci da kuturun munafurci yaran nan suka ce wani wai namiji ne , aradun Allah ma ni ban yadda da su ba idan ba turo su ɗaukar rohoto aka yi ba , atoh ki dai bincika ki kuma san abun da kike ciki kar sai kin baje kafafu ki ji anyi ramm da ke anyi sama da duwaiwan ki atoh , zamanin nan na yanzu ko inuwar ka baka sakankance da ita ba dan zata iya harɗewa ta shige cikin na makiyin ka idan kuka jeru, ji min duniya mai abun mamaki wai ƴan waɗannan ƙuya-ƙuyan yaran sun iya dabo-dabo da rufa-rufa , toh dan uban uban ku yau asirin ku ya tonu ,”3
Duk maganganun da yake suna sauka a kunnuwan falmata wacce take duƙe a bakin fanfo da kuma yakaka wacce ta kawo kai domin shigowa ta karbi burkutu ta kaiwa abokan ciniki , dukkanin su tsam suka yi da jin kalaman ɗan liti , wannan fa shi ake kira an yanka ta tashi , take falmata ta fara yin hawaye , yayin da yakaka ta ɗaure ta cije tare da jaan ƙwanjin kare falmata ,”sai dai ayi wacce za’a yi wai bera ya zubda garin ƙyanwa ,”
Madam saly ce ta juya ga falmata bayan da ta gama jin zantukan ɗan liti ,
Kai kachalla zo nan
Sum-sum falmata ta taso tana laluben hanya ta sashin da taji tashin muryar madam saly
Haiyaratataa ni idan ba makantar taki ma ban yadda da ita ba , ni daman kullum ina shakkar waɗannan idanun naki da suke wural uwa na mujiya da tsakiyar dare ace wai bakya gani ??? Cewar ɗan liti wanda yake jijjiga ya dogare daga gefe ,”1
Kai kachallah meye gaskiyar maganar da ɗan liti yake faɗa akan ka ? Tambayar da madam saly ta jefawa falmata wacce take durƙushe a gaban ta kenan , “
Madam karya yake min ni ban san kome akan abun da yake cewa ba ,”
Wata irin zaburowa ɗan liti yayi ya dako tsalle ya bangaje ƴan matan da suke tsaye daga gaban shi ,ya dire a gaban falmata ,”
Dan ubanki Alhaji basko zai miki karya ne ,? Toh idan kin ce karya ne ɗaga rigar ki aga kirjin ki , nace ɗaga rigar ki mu ga kirjin ki ƴar iska jaririyar ƴar bariki ,’
Toh kai kachalla ai sai ka cire rigar mu ga kirjin naka domin cire zargi cewar madam saly,” sunkuyar da kai falmata tayi tana matsar ƙwalla
Koh kafin su farga ɗan liti yayi charaf ya kaiwa gaban rigar falmata chafka , baiyi wani jinkiri ba ya sa karfin tuwo ya balla baturan da suke jere gaban rigar , yana cewa
Dan uwar ki rigar uban waye ya saya miki ba ni ba ?? Yau sai mun ga karshen karya ,”
Da gudu yakaka ta karaso wurin ganin ana neman tozarta ƙanwar ta ayi mata tsirara cikin taron maza da mata ,”
Ƙoƙarin raba hannun ɗan liti da jikin rigar falmatan ta fara , tana cewa
Ɗan liti ka sake mata riga meye hakan ? Wai ina ruwan ka da harkar mu ,”
Wata dariya ɗan liti ya sake , kin ji koh madam saly nace kin ji koh ? Da bakin ta take ambaton ta a jinsin mata , shegu munafukai , yau me raba ni da ku sai Allah tun da kuka jawo min asara , yana gama faɗin hakan ya ingije yakaka tayi faɗuwar ƴan bori , kafin ta taso , ya sanya dukkanin karfin sa ya jijjiga falmata gami da keta mata riga , ya sanya hannayen sa duk biyu ya cisge tsunman da take ɗaure kirjin da shi ,ya murɗa hannayen ta tare da lanƙwasa su baya ya banƙaro kirjin ta gaba wanda hakan ya bayyana haliltar kirjin ta tsai a tsaye ,”6
STORY CONTINUES BELOW
Wani irin guntun salatin da ba’a ƙarasa shi ba tare da shewa da ihu sune suka cika wajen daga bakunan mata da mazan da ke wajen , cewa suke wallahi chika ce , laaah ,
A toh idan har yanzu ba’a yadda ba sai na ɗaga muku ƙasan shi ma ku gani dan gaba kar a karkace a kuma sharo wata ƙaryar ace mata-maza ce gara a ga ƙarƙashin ,
Nan dai wasu suka fara ihu suna cewa a ɗaga su gani a ɗaga su gani
Da gudu yakaka ta taso tare da yi wa falmata rumfa da jikin ta idanun ta kuwa tuni suka fara zubar ruwa , cewa take menene hakan ?dan Allah kuyi hakuri ku kƴale ta , ƙanwata miskiniya ce makauniya ce , ni ce da laifi , ni nace ta koma shigar maza , kowanne hukunci zaku yi mata ku min a madadin ta ,’ tana faɗin hakan tana warware ɗankwalin kan ta tare da rufawa falmatan da take risgar kuka , cikin tsokar jikin ta take jin idanun jama’ar da suke zagaye da wajen , cikin ran ta tana jin wani irin rauni da bata taɓa jin irin sa ba tabbas an cuce ta an tazorta ta matuƙa an tsaraita ta a gaban jama’a1
Yagana ma matsar ƙwallar tausayin falmata take ,
Madam saly kuwa wani malalacin kallo take bin su da shi ,”
Yanzu daman dan uwar ki yaks ƙarya kuke min ? Toh kuwa yau yau ɗin nan zaku bar min gida ƴan iska maƙaryata , da sauri yakaka ta matso gaban saly ta shiga rokon ta akan ta taimaka kar ta kore su domin basu da kowa ,”
Da ƙyar da jibin goshi larki da hema suka sanya baki wurin taya yakaka bawa madam saly hakuri saboda tausayin yaran da ya tsirga musu , bayan sun ƙora ɗan liti wanda ya zama ziga-zigi yana sake tunzura madam saly ta kori su yakaka , ya dage akan cewa turo su C.I.D aka yi wanda hakan ke ruda madam saly , sanin cewa ita ba mutum bace mai gaskiya , sanna a cewar ta kewaye take da makiya ƴan hassadar ta .1
Ficewa yayi bayan ya tabbatarwa yakaka duk inda kuɗi suke ta nemo ta biya sa kayayyakin da ya sissiyawa falmata domin shi bai yin asara koh ta sisin kobo , kuma kar falmata ta sake taka ko da kofar ɗakin sa ne , idan har kuwa ya gan ta a gaban ɗakin sa babu abun da zai hana ya kirɓe ta ,’
Toh yanzu da ku ka nace kar a kore su akan ku zasu dunga kwana su biyun ? Kun san dai ku ukun ma a matse kuke tamkar kifin gongoni , cewar madam saly
Da sauri yakaka wacce har lokacin rungume take da falmata da take ta faman sauke ajiyar zuci akan kukan da ta sha , tace
Ni zan dunga kwana a kan benci cikin rumfa idan ya so falmata ta kwanta tare da su a ɗakin idan kin yadda ,
Sai da madam saly ta wurga mata harara domin har yanzu tana ɗan jin haushin su
Ƙya ce haka mana dan kun samu na ƙyale ku algungumai , ni dai ku kiyaye ni kar ku bari na sake kama ku da wani laifi domin gaba ko kun fi kuturu naci sai kun bar gidan nan , tun da kin zaɓi kwanan kan benci a cikin shagon toh ke kika sani sautun mahaukaciya , duk abun da ya biyo baya ki kuka da kan ki , kar ki ce ban faɗa miki ba ,
Ba tare da fargabar kome ba yakaka ta amince da zantukan madam saly cikin ran ta tana sa mata albarka ,1
Wanene Alhaji basko ?? Aina kika san shi ? meye haɗin ki da shi ? Kuma ta yaya yasan cewa ke mace ce ??
Su ne tambayoyin da yakaka ta jerowa falmata lokacin da take taya ta shiryawa cikin ɗaya daga cikin kayan da take warewa take ajiyewa falmatan su ,
Ba tare da jinkirin kome ba falmata ta fayyace mata kome ,
Hawaye ne yake sauka bisa kumatun ta , meyasa mutanen duniya suke son zukatan su ?meyasa taimako domin Allah yayi ƙaranci meyasa zalunci ya yawaita , meyasa fasikanci ya zama mahaɗin rayuwar mafi yawan mutane ,??? Meyasa meyasa ? Ji tayi tsanar dukkanin mutanen da suke kewaye da duniyar ta ya kama ta idan aka ɗauke ƙanwar ta ,’
Nan gaba kar ki sake yadda da kowa falmata , idan na ce kowa ina nufin kowa ,! Kin ji ko ?
Ba tare da falmata ta hakiƙance da inda kalaman yakaka suka dosa ba ta amsa mata da toh ,”
STORY CONTINUES BELOW
Daga ranar yakaka ta koma kwanan cikin rumfar da suke sana’ar su ciki , yayin da idan kafafu sun yanke a wurin kamar sha biyun dare sun riga sun gama sana’ar su, zuwa lokacin duk ƴan iskan sun watse wasu sun shige ɗakunan su tare da abokan iskancin su sai ta haɗa teburan da suke gaban kujerun , guda huɗu ta shimfiɗa zanin ta akai tayi matashi da hannunwan ta tare da rufuwa da wani zanin , sai tayi baccin ta ba tare da tsoron duhu da shirun da wajen yayi ba ko kuma tsoron ƴan iskan da ka iya kawo mata farmaƙi , wurin kwanan ta na cikin ɗakin kuwa ta barwa falmata ,
A haka kwanaki suka fara miƙawa har yau da ake kwana na uku da faruwar lamarin falmata ta gagara sakewa dan kuwa tuƙuru ƴan matan gidan suke tsokanar ta , har suna cisge mata ɗan kwali , suna faɗin ta koma shigar maza ta fi yi mata kyau , da hakan ba ƙaramin sanya ta takaici yake ba , sai dai tayi matuƙar koƙari wajen boye damuwar ta domin kar ta jefa yakaka cikin damuwa ita ma , duk wani abun da idon ƴakakar bai gani ba game da tozarcin da ake yi mata bata faɗa mata .
Juyi yake ta yi akan katifar sa kaɗan-kaɗan yana jin wani sabon yanayi da ya fara ziyartar sa a tun lokacin da agogon wayar sa ya nuna masa sha biyun dare cib wanda a lokacin yana kan computer sa yana wani aiki sai dai wannan yanayi da ya fara ji yana taso masa ya sa shi rufe computer tare da wani irin bingirewa akan katifar sa tamkar dai an tunkuɗa shi ,’
daran ranar ya zo dai-dai da cikar sa shekaru talatin cif a lissafin watanni turawa ,
Miƙewa yake so yayi ya fita ya ɗauro alwala , domin ya samu damar raya ƙarshen daren da ibada Kamar yadda yake aikata hakan jifa-jifa , sai dai ga mamakin sa ya kasa tashi , haka yake jin sa kamar an ɗaure shi ko kuma an aza masa wani abu mai nawi an danne shi , yana jin sa a wani yanayi mai cike da fargaba da tsoro zuciyar sa na wani irin bugu , yana jin sa ɗan mitsitsi kuma sakayau tamkar ba shi ba , shi ya san ba bacci yake ba ba kuma a farke yake ba sannan ba mafarki yake yi ba , yana jin sa kawai a wata duniya ta daban , duk yadda ya so yayi addu’a ya kasa ,
Haka ya shafe tsawon awannin karshen daren har zuwa lokacin da alarm ɗin da ya saita a wayar sa ya fara rangwaɗo sautin kiran sallah cikin zazzaƙar muryar balarabe , wanda cikin ikon Allah ya ji cimak wannan nawin da yake ji ya hana shi motsi , babu shi tamkar dai an sauka a kan sa , da gudu ya miƙe tsaye , jikin sa ya jiƙe sharaf da gumi , wannan tsoron da yake ji ya kau , sai dai har yanzu ɗan sauyin da yake ji a jikin sa yana nan , amma cikin ran sa sai ya dangan ta hakan da zamantowar sa cikakken ɗa namiji lafiyayye da ya kai minzalin da ya kamata ya buƙaci mace , duk da cewa shi youssouf ba manemin mata bane , bai taɓa zina ba , bai taɓa kusantar kowacce mace ba duk yadda ya kai ga cuɗanya da matan bariki matan banza , shi mutum ne mai tsantsani ta wannan fannin ,
Da sauri ya ɓude ruwan leda ya juye cikin ɗan bokatin da yake yin amfani da shi wurin yin wanka , ya cika shi taf da ruwa gami da sunkuta ya fito daga tantin sa zuwa ɗan bayan gidan da aka samar masa na wucin gadi wanda yake mallakin sa shi ɗaya ,’
Ruwan na da sanyi sosai dan haka yayi tunanin zai taimaka wurin kawar masa da yanayin da yake ji a jikin sa , sai dai ga mamakin sa daga lokacin da ruwan ya sauka akan fatar jikin sa , ya ji tamkar an ƙara masa masifa ne domin gaba ɗaya tsikar jikin sa tashi tayi da ya sa dukkanin wasu jijiyoyi na jikin sai da suka taurara tare da fitowa baro-baro ,wani irin ƙullewa ya ji marar sa tayi ,
Ba shiri ya sanya tufafin sa gami da ɗauro alwala ya dawo cikin tantin sa , a daddafe ya idar da sallah saboda yadda marar sa take tamkewa tana sakewa ,
Kwanciya rub da ciki yayi bayan ya sanya ɗaya hannun sa ya riƙe marar sa ,tun da yake bai taɓa tsintar kansa cikin wani hali makamancin wannan ba, a hankali ya fara jin ciwon marar yana raguwa , wani ɗan daddaɗan bacci yana fisgar sa a sakamakon lafawa da ciwon yayi tare da daɗin ƴar sassayan iskar asuba da take shigowa ta tsakankanin rumfar tantin sa ,,’
STORY CONTINUES BELOW
Bacci yake yi sosai da bai samu irin sa ba duk tsawon daren jiya , kafin sautin kiran wayar sa ya tashe shi , miƙa hannu yayi ya jawo wayar tare da miƙewa zaune saboda sautin kiran ya bayyana masa girma tare da muhimmancin mai kiran na sa
Allô mama oui meilleur sava,?
Daga chan ta amsa masa sava bien yaro na ya kwanan ka ? Da dama kou ?
Ɗan jim yayi yana son faɗa mata yadda yake jin jikin sa saboda ya saba bayyana mata duk wata damuwar sa , sai dai kuma yanayin da yake jin yayi masa nawin faɗi a kan harshe musamman ma ga mahaifiyar sa *
Daga bangaren ta kuwa zuciyar ta ce ta buga a sakamakon tunowa da mummunan mafarkin da tayi akan sa asubahin daren jiya da ya haddasa mata rashin nutsuwa , da ya sa tun asubah take neman layukan sa domin ta ji lafiyar sa kou ta samu kwanciyar rai amma rashin kyaun hanyoyin sadarwa ya sa sai yanzu da safe ta cimma nasarar samun sa a wayar ,”
Yaro na yi min magana mana hankalina ya tashi ,
Da sauri ya katse ta ,” da dama umma ya ɗaura da tambayar ta ina merama ? Ta amsa masa da lafiya take , “
Cigaba tayi da tambayar sa lamuran da suke gudana daga wurin sa , yana bata cikakkun amsoshin da suka gaza wurin gamsar da ita , zuciyar ta ta gaza nutsuwa duk lokacin da ta tuno da mafarkin da tayi sai ta ji bata son ta daina jin sa a waya , inda da hali so take ya kasance a idanun ta cikin waɗannan kwanakin dan tana jin kamar wani abu marar daɗi zai faru da su,
duk da ta san sau dayawa mafarki bai zama gaskiya a mafi yawan lokuta daga shaiɗan yake , kuma ita bata da ikon kare kan ta ma bare wanin ta , ta san ko da agaban idanun ta yake , bata isa ta bashi kariya ba , illah addu’ar ta da ka iya yin tasiri akan ko ma menene , kuma duk nisan tazarar da ke tsakanin su ta san addu’ar zata isar masa ,
sanin da tayi youssouf ba sosai sosai yake tsayuwa yayi addu’a ba , shi dai mai tsayar da ibadun sa na farillah ne , bayan su sauran lokutan sa ƙorafi yake aiki ya cinye su ,wanda ita kuma hakan bai mata daɗi , ta san duk wata nasar da kariya daga wurin ubangiji ake samun su ,
dan haka a yanzu ma sai ta sake tunasasshe sa game da girman addu’a inda shi kuma ya tabbatar mata da yana yi ,’
Sallama yake shirin yi mata , sai kalaman ta suka katse shi ,”Tu es notre lumière, notre joie, et pour toi nous donnerons le meilleur. En te souhaitant une vie abondante et en bonne santé.Joyeux anniversaire mon fils!,’ Allah shi yi maka Albarka shi kare ka du inda kake yaro na ,
Murmushi ne ya suɓce masa halin da ya wayi gari cikin sa ya sa ya ma mance da yau take ranar zagayowar haihuwar sa kalaman ta na yanxu suka suka tunassashe sa,’amsa ya maida mata cikin tsantsar ƙaunar ta da yake ji cikin ran sa ,” merci mama je t’aime,”
Daga bangaren ta ajiyar zuciya ta sauke bayan kammala wayar su , babu laifi ta ɗan samu nutsuwar zuciya , sai dai ta kuɗurce a ran ta zata ƙara ƙaimi wurin neman kariyar ubangiji akan ta da ƴaƴan ta , daga makiyan su da ta san suna kewaye da su ,
Juyowar da zata yi domin nufin ta shiga ɗaki ta fara sallar walha , idanun ta suka sauka akan hajiya uwa wacce take yi mata wani irin hargitsattsen murmushin da baza ta iya hasashen nufin sa ba , bata san lokacin da ta wanzu a wurin ba domin baya ta bawa kofar shigowa falon nata na ciki ,4
Tsawon zaman su baza ta iya tuna rana ta karshe da hajiya saratu ta tako kafafun ta sashin ta ba , basa shiga sassan juna iyakacin su , su haɗu a bangaren mai martaba idan haɗuwar ta kama dole , ko kuwa wurin gaishe da hajiya uwa ,’
Sannan tayi mamakin ganin ta ita ɗaya kai tsaye har cikin bigiren ta da sai an nemi iznin ta kafin a shigo ,’ a sanin ta tare da tawagar ta hajiya saratun zata iso kuma karƙashin jagorancin shugabar bayi ta bangaren ta ,’
STORY CONTINUES BELOW
Da kallo ta bita lokacin da take yi wa kan ta mazauni akan shimfiɗar alfarma da ta tashi daga kan ta yanzu ,’
Hala uwargidan mai martaba sarauniya tayi mamakin wanzuwa ta gaba gare ta a yau ,? Shi yassa aka gaza wurin taryaa ta kamar yadda ya kamaace ni ,
Fuskar ta babu walwala ta ce ,”
Ban yi mamakin zouwar ki nan ba saratu , shin ƙaƙa za’ai mamakin wanzuwar macce a kowanne bangare cikin gidan amren ta ? Sannun ki da isowa ina miki lale marhaban ,’ zama tayi daga ɗaya bangaren shimfiɗar ,’
Suka yi kallon kallo na tsakiyar ido , kafin saratu ta ce ,’
Yau yariman maraɗi ke cikkace shekarun sa talatin cikkin duniya , kou ba hakka ba ?
Kallon mamaki hajiya safiyya ta bi ta da shi tana jin bugun zuciyar ta na ƙaruwa a hankali mafarkin ta na jiya ke dawo mata da fuskar saratu da ta gani cikin mafarkin ,” janye idanun ta tayi daga kan ta ,”
Ƙaƙa kin ka sani ? Kafin ta rufe baki saratu ta amsa mata cikin wani yanayi mai tattare da ma’anoni ,ƙaƙa uwa zata kasa sanin ranar haihuwan ɗiyan ta ,? ???
Guntun murmushin fatar bakin ta safiyya tayi ,’haka ne kin yi gaskiya ,!
Kiraye ma ni shi na taya shi murna shine abu da ya kawo ni gaba gare ki ,”
Tsam hajiya safiyya tayi tun haihuwar youssouf yau shekaru talatin saratu bata taɓa taya shi murnar zagowar ranar haihuwar sa ba sai yau ,? Sama ta ka zata ce zata taya shi murna ? Wallah banza bata kai zomo kasuwa ,!
Ta bangaren biyamuradi youssouf kuwa tun yana cikin yin waya da umma yake jin kira yana shigowa wayar ,
Yana gama magana da umma ya bi bayan kiran da ya gani daga wata bakuwar lamba daga ƙasar su , sai dai har kiran ya tsinke ba’a ɗaga ba , yana shirin ajiye wayar ɗan guntun sako daga lambar ya shigo wayar sa ,”
Mon frère, je t’aime tellement. Que toutes les meilleures bénédictions te parviennent aujourd’hui et pour toujours. !Bon anniversaire.!
Sakon taya murnar zagayowar haihuwa ne ,duba lambar ya sake yi yaga bai san ta ba dan haka kawai sai ya share , ya fara koƙarin kiran layin maimouna kamar yadda suka saba kullum safe
Neman iznin shigowa aka yi ya bada izni aka shigo , abincin karyawar sa ne , aka shigo masa da shi,
Da hannu yayi nuni da a ajiye masa abincin ,
Allo ma jolie fille
Allô joyeux anniversaire mon amour ,
Ɗan jim yayi yana tunanin ta yaya maimouna ta san yau ranar zagayowar haihuwar sa ,? Shi dai ba shi ya sanar da ita ba , ‘
Princesse wa ya fadi miki wagga batou ?
Cikin dariya ta bashi amsa a iska ta ji , murmushi yayi tare da share batun , suka cigaba da hirar su cikin nutsuwa tare da ƙaunar junan su ,
Wayar su ba mai yankewa da wuri ba ce ,musamman yau da daɗin soyayar ya juyo , dan haka riƙe da wayar ya fita ya wanko bakin sa ya dawo ya zauna cin abincin sa ,
Tashin farko ya kai abincin bakin sa ba tare da bismillah ba , saboda hirar maimouna ta ɗauke hankalin sa , haka har ya cinye abincin tas tana zuba masa zantukan soyayya , sai dai me ? yana gama ci ya ji marar sa ta murɗa , ba shiri suka yi sallama ,’ ga mamakin sa sai kuma ya nemi ciwon ya rasa ,
Dan haka ya tashi yayi shirin sa tsaf cikin kayan sa na soji , ya fito
Ya tarar da duk sauran da ke ƙarƙashin sa ma sun shirya domin a yau zasu ɗan yawata ne cikin daji ta sama ta hanyar jirgi mai saukar ungulu,’helicopter”domin su ga wuraren da ƴan tawayen boko haram suke da mafaka su tabbatar basu tsallaka iyaka sun shiga yankin ƙasar su ba ,’
Suka hau jirgi ya ɗaga da su , sun ga wuraren da boko haram suka yi bigire na dindin-din cikin dazuzzuka tare da matan su da ƴaƴa suna rayuwar su cikin walwala tare da jin daɗi fiye ma da al’ummar cikin gari , abun da ya ɗaure kan youssouf kenan , ƙaƙa ƴan ta’adda irin wannan suka samu bigire cikin ƙasa kamar nigeria ? Shin wake ciyar da su ? Wake kai musu makamai ? Waye ke da alhakin basu magunguna zuwa kaƴan bukatun yau da kullum ?? Tabbas akwai lauje cikin naɗi ,’1
STORY CONTINUES BELOW
Sun samu kimanin awa guda a sama suna shawagi kafin suka sauko , kai tsaye ya wuce cikin tantin sa ya kwanta , gaba ɗaya yau ya gaza gane kan sa wani iri yake jin sa tamkar akwai wanda ke sarrafa shi a gefe , yana ji kamar su biyu suke gudanar da kome , amma kuma shi baya ganin kowa ,”
Haka ya yini babu walwala , sun yi waya sau biyu da umma wacce take sake jaddada masa ya riƙe addu”a tare da yawaita karatun kur’ani sai dai kuma abun da bata sani ba shine yau sam-sam ya gaza yin addu’a a yanzu haka da yake kwance ya gagara tashi yayi sallar azahar alhalin kuma la’asar har ta gota , karfe huɗu ma ta wuce , sannu sannu ya fara jin wannan yanayin da yake ji na safe yana sake tado masa , ” wata irin mahaukaciyar sha’awa yake ji kamar zai fidda wani sashi na jikin sa ya ajiye koh ya huta ,” shi kuwa yau wacce irin masifa ce ta same shi ? Ita ce tambayar da yake yiwa kan sa ,”
Sau biyu sojojin da ke da alhakin kula da lafiyar sa suna leƙowa su duba shi domin sun ji shirun yayi yawa , koh ɗan masallacin da suka tayar suke jam’i cikin sa bai zo yayi sallah tare da su ba a yau baki ɗaya ,
Ga mamakin su duk shigar su a zaune suke tadda shi , sannan kuma yana tabbatar musu da lafiyar sa lau babu abun da ke damun sa , dan haka sai suka kƴale shi ,
Zuwa magariba youssouf ya fara gagara iya riƙe kan sa domin tashin hankalin da yake jin kan sa a ciki ya wuce tunanin sa ya wuce yadda yake ji idan bai sha burkutu ba , wannan karon ji yake yana gab da mutuwa idan bai samu biyan bukatar sa ba ,
Ina zai samu mace a yanzu alhalin yana cikin jeji ? Yaya zai yi ? Dama a cikin gari yake sai ya fita ko’ina ne ya samo wacce zata taya shi ya kauda bala’in da yake ji ,’
miƙewa yayi a dudduƙe ya ɗauki walet ɗin sa tare da ID card ɗin sa , har yayi nufin fita sai kuma ya fasa lokacin da ya kalli jikin sa ya ga yadda ya ke , wani kunya da takaici suka dirar masa , lokaci guda wani duhu ya mamaye masa kwakwalwa da ya sa nan take ya mance da wani batun kunya illah umarni da yaji ana bashi akan ya tafi ,
Yana daga cikin ɗakin ya danna kiran masu kula da shi ta wayar hannun sa , ba tare da jinkiri ba suka zo , yace su kawo masa mukullin mota zak ɗan fita , ” jim suka yi ,toh sai dai basu da ikon musa umarnin sa dan haka suka kawo masa mukullin motar suna jiran su ji yayi musu umarnin su mishi rakiya wani wurin , sai suka ji ya sallame su , ficewa suka yi suka bar shi ,” suka nufi bakin masallaci domin yin shirin sallar isha’i
Suna tafiya shima ya fito ya buɗe motar ya faɗa ,’ ya jaa ta da mugun gudu , ya hau titi tare da nufar cikin garin maiduguri a wannan daren ,’
Gudun da yake ba na hankali bane , bai ko tsoron dare da yadda garin yake haɗe da hadari sai walƙiya ake yi, bai tsagaita ba sai da ya shigo da’irar birnin maiduguri lokacin sha ɗaya da rabi na ɗare har ta gota, cikin garin babu kowa kan titi sai sojoji ƴan uwan sa da suna hango motar ta sa mai ɗauke da fentin launin kakin soja suke buɗe hanyoyin da suka bi suka tottoshe saboda tsaro, shawagi ya fara yi da motar marar sa na cigaba da karta masa har yana ganin duhu-duhu , ya haɗa zufa sai tsuma yake yi, ina zashi ? Shi ba wani sanin kan garin yayi ba guri ɗaya zuwa biyu ya sani , daga barikin garin wurin abokin sa , sai kuma wurin sayar da burkutu ,
karya kan motar yayi ya lokacin da ya ji kamar an umarce shi da ya tafi zuwa wurin sayar da burkutun , a chan zai samu wacce zata iya kula da shi ,
Yana yin fakin ɗin motar ya fito ba tare da ya damu ya rufe murfin ba ya fara taku yana bin hanyar da zai sada shi da cikin gidan hannun sa ɗaya ya riƙe marar sa , da layii ya ƙaraso cikin rumfar , sai dai bakikkirin ya tadda wurin , babu kowa an watse kujerun gurin kansu a tattare suke, wani irin jiri ya ji yana kwasar sa , ya tabbata yau mutuwa zai yi ,
STORY CONTINUES BELOW
Tun shigowar sa yakaka wacce bata daɗe da kwanciya ba, bayan ta tattara cikin shagon ta kintsa kome, sai dai ta gagara bacci saboda tsinkewar da zuciyar ta ke yi wanda ta danganta hakan da tsoron tsawa da walkiyar da ake yi ,
Taji shigowar sa a tun takun sa na farko a cikin shagon , tsumu tayi cikin zanin rufuwar ta , tana sake jin bugun zuciyar ta na ƙaruwa da duk wani motsi da yake ,wanene cikin daren nan ? Koh wani ne yayi mantuwa ? kaƙƙarfan kamshin turaren sa shi ya ziyarci hancin ta , kamshin da ya ɗauki tsawon kwanaki a hancin ta kafin ta daina jin sa a wancen haɗuwar ta su ,’
Kamshin na musamman ne dan haka sai ta zame abun rufuwar daga kan ta dan ta samu damar shaƙar ƙamshin da kyau cikin ran ta kuma tana ƙwaɗayin ganin fuskar sa ,
Da ɗan tazara a tsakanin su domin shi yana tsaye daga bakin kofar ta ciki yana fuskantar inda yakaka ke kwance sai dai bai kai ga fahimtar mutum ba ce saboda babu wadatar haske kuma baki ɗaya bai cikin hayyacin sa ,
Sosai ta buɗe fuskar ta tana ƙare masa kallo ta cikin ɗan hasken da yake shigowa ɗakin da taimakon hasken hadarin da ya gangamo cikin duhun daren , bata gani ainahin kamannin fuskar sa sai dai siffar jikin sa da take gani , gani tayi ya sunkuya yana riƙe da cikin sa
Tsawa aka yi tare da walƙiya da ya haddasa yakaka tsorata har ta miƙe zaune , motsin ta ya sanya shi ɗago kan sa ,walƙiyar da aka sake yi ta hasko masa farar fuskar ta ta zuba masa ido tana kallon sa daga inda take zaune ,’
Wani tsallen farin ciki zuciyar sa tayi, da sassarfa ya fara takawa yana nufar ta tamkar mayunwacin zakin da ya kwan uku ba abinci ,
Baya ta fara yi akan bencin tana matsawa , cikin in’ina tace ,’
Babu ruwa ya ƙare ,mun ruga mun tashi an gama aiki sai gobe da rana ,’
Kalaman ta sun zo dai-dai da ƙarasowar sa gaban ta , baiyi wata wata ba ya miƙa hannu ya ɗago ta daga kan bencin ta hanyar ɗago kafaɗun ta ya tsaida ta akan kafafun ta , ba kuma tare da ya ce da ita ƙala ba ya juya tare da jaan hannun ta da ya riƙe nufin sa ta biyo shi ,’
Waiwayowa yayi jin ta turje tana ƙokarin zame hannun ta da ya riƙe tamau ,
Cikin wata irin dusasshiyar murya da take fitowa daga ƙarƙashin maƙoshin sa yace ,”
Ki taimaka min kar na mutu ko nawa ne zan biya ki ki taimake ni ,”
Daga haka ya juya yana jaan hannun ta , bata yi turjiya ba ta fara bin sa kafafun ta ko takalma babu ,” kalmar taimako da ya ambata tare da wani abu da take ji yana fisgar ta a game da shi ya sa ta bi shi ,’1
Sun zo tsakiyar filin gidan aka fara yayyafi ,’ yakaka ta sake tsayawa saboda gargaɗin da zuciyar ta ke yi mata akan yunƙurin bin mutumin da bata sani ba cikin dare zuwa wurin da bata kai ga sani ba wai shin ina hankalin ta yake ne ??
Juyowa yayi aka saki tsawa da walkiya tare da ƙaruwar ƙarfin ruwan sama , haɗa ido suka yi ta hasken walkiyar suka kalli juna na wasu dakikai ba tare da kowannen su ya samu damar magana ba ,”
Cikin idanun sa ta hango ruɗanin da yake ciki , tare da wani abu da ya taɓa zuciyar ta da bata kai ga fahimtar yanayin sa ba , sai dai koma menene yayi tasiri matuƙa wurin raunana mata zuciya ta yadda ta ji kowanne irin taimako ne zata iya yi masa , zata mishi kome yake so , tana nufin kome ,
A bangaren biyamuradi youssouf kuwa shi ma kallon cikin idanun ta ya taɓa shi , ya hango rauni tare da zallar ƙuruciyar da ke tattare da ita ,sai dai sun gaza tasiri agare shi domin daga lokacin da ya riƙo hannun ta ya fara jin wani irin nutsuwa tare da ɗaukewar ciwon da yake ji ,har da wani danshi danshi yake ji a ƙasan ran sa wanda ya tabbatar masa ita zata iya fidda shi halin da ya ɗauki tsawo awanni ashirin da huɗu cikin sa , yana jin zai iya biyan ta ko nawa ne domin ta yadda da shi ,
Ganin bata ce kome ba ya sa shi ya cigaba da tafiya riƙe da hannun ta sai dai wannan karon tare suke jefa kafafun su a jere tamkar sabbin masoya cikin samun amincewar yakaka da ta hakiƙance zata taimaka masa , “
Bai saki hannun ta ba sai da ya dangana ta da cikin motar sa ba tare da fargaban kome ba yakaka ta shiga ta zauna tana shaƙar ƙamshin turaren sa da ke da matuƙar tasiri agare ta ,”
Da ƙarfi ya fisga motar wanda yayi dai-dai da fara saukar ruwan sama da matuƙar ƙarfi ,
wani ƙaramin Guest house ya nufa wanda yake ganin sa akan hanyar shigowa gari , cikin su babu wanda yake ce da ɗan uwan sa ƙala ba har suka isa , bai wani sha wahala ba wurinnsamar musu da ɗaki zamantowar sa jami’in tsaro ,
Riƙe da hannun yakaka wacce ta zamto tamkar rakumi da akala ya danna kai cikin ɗakin ,’
Daga lokacin da suka sanya ƙafa cikin ɗakin kome ya fara kasancewa nan ne mafarin hargitsin rayuwar su , sun gudanar da kome cikin amincewa tare da tallafin junan su , yakaka bata hana biyamuradi kan ta ba wanda ita da kan ta baza ta iya faɗin dalilin ta na sadauƙar masa da mutuncin ta ba ita dai ta san koma wanene wannan mutumin da ya kasance mutum na farko da ya fara kasancewa da ita a wani bigire kuma cikin wani yanayi irin wannan ,akwai wani al’amari mai girma a tare da shi .’3
A bangaren biyamuradi kuwa tsintar kan sa yayi a wata duniya mai nisa wacce take tare da wani irin daɗi da sanya nishaɗi da bai taɓa jin makamancin sa ba , ji yayi ko da dakika guda baya fatan wani abu ya gifta da zai katse masa jin daɗin sa ,
Yana jin zai iya mallakawa yarinyar nan kome ta buƙata , idan ya ce kome yana nufin kome .”
Ta hasken ranar da ya hasko ɗakin ta tsakanin ɗan yalolon labulen ɗakin yakaka take ƙarewa fuskar biyamuradi kallo , komen sa mai kyau ne babu abun da ya fi ɗaukar hankalin yakaka irin jajayen laɓɓan sa ,” tambayar kan ta take daman maza ma na shafa jambaki ? hannu take niyyar kaiwa fuskar sa ta ga ya buɗe idanun sa a firgice kamar ba wanda ke bacci ba ,”
Da sauri ta jaa baƴa tare da maƙurewa a jikin gadon ,”
Zama yayi yana me ƙarewa ɗakin kallo kafin ya waiwayo kan yakaka tare da wani irin kallo da ta kasa tantance ma’anar sa ya watso mata tambayar da ta shayar da ita mamaki ,”
Wacece ke ??????Ni ni nice yakaka ,”+
Ya ka ka ? Ya maimata sunan kamar me koyon magana ,’
Ina ne nan ? Waye ya kawo ni nan ? Me muke yi anan ??
Wannan karon a tsorace yakaka take kallon sa ,”kar dai mahaukaci na biyo ni yakaka na shiga uku ,” ?1
Tsawar shi ita ta katse mata tunani cikin hargagin su irin na soji yake sake maimaita mata tambayoyin ,”
Fashewa tayi da kuka cikin rikici ta fara cewa ,” ni ka mayar da ni gida nima ban san ina ka kawo ni ba ,!
Tare da tarin wani al’amari da ya shallake tunanin sa ,’ ya maimata tambayar ,’
Na kawo ki ?
Eh ba kai bane jiya ka ɗauko ni cikin dare ka ce zan taimaka maka shine ka kawo ni nan ,”
Kamar a majigi ya ji al’amuran da suka faru gare shi tsawon yinin jiya sun fara komawa baya suna giftawa ta cikin ƙwaƙwalwar sa tare da hotuna ,” har zuwa kan al’amuran da suka gudana tsakanin sa da yarinyar da take gaban sa a yanzu ,”1
Wani irin sufa yayi ya wawuro yakaka wacce ta cika tayi fam ta tsattsare shi da ido ,”
Riƙe ta yayi gam ,!
Yarinya yi gaogawa sanar da ni mafalki muke faɗa mini ba gaske bane ni nayi tarayyah da ɗiyar mutane ta hanyar banza , ki ce mafalki ne, ya ƙarasa zancen yana jijjiga ta .
Gaba ɗaya ya shiga ruɗani ji yake tamkar ya haukace yana son ya gano wace masifa ce ta kunno cikin rayuwar sa daga jiya bayan wacce yake ciki na shan burkutu? Shi bai sha’awar zina hasalima yana ƙyamatar masu yin ta ,” wani tsoro ne ya ziyarce shi da ya sa shi angaje yakaka lokacin da ya tuno da girman laifin sa wurin ubangiji ,” zuwa yanzu ya gama tuno da kome da ya faru da shi ,”
Bai san lokacin da ya fashe da kuka ba da dukkanin karfin sa , kuka yake babu kakkautawa ,”ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige cikin ta ,” zuciyar sa ke sake raɗa masa ya tabbata mutumin banza gafalalle lalatatce , “
Cikin mamaki tare da shakkun samuwar cikakken hankali a gare shi yakaka ta ware ido tana kallon sa tare da nutsuwa cikin shirin ko ta kwana idan ya kawo mata chafka ta daka tsalle zuwa waje ,”
Sai da yayi kukan sa mashi’i cikin ransa kuwa ya rasa takamaimai addu’ar neman tuba da zai yi kowacce ya kamo sai ya ji ta tayi ƙanƙanta wurin rokon Allah akan yafiyar zunubin da ya aikata ,” chak ya tsaya da kukan lokacin da ya tuno da dauɗar da ke tare da shi ,”
A sukwane ya nufi kofar da bai da tantama ta banɗaki ce ,”ba tare da ya kuma kai duban sa ga yakaka ba wacce take ɗosane a gefen gadon tana ƙare masa kallo ,”
Maimaita wankan tsarki yake yana kuka , sai da ya gaji dan kan sa ya sanya tufafin sa gami da fitowa ,”
Karaf suka haɗa ido da yakaka wacce ta zubawa kofar banɗakin ido tamkar mai tsumayin fitowar sa ,”
Kallon ta yayi na ƴan wasu dakikai da idanun sa da suka yi jawur ,” cikin ran sa yana gorantawa kan sa yanzu wannan ƴar ficiciyar yarinyar da bata wuce merama ba ita ya saukewa larurar sa ,’? Shin wai ma meya sa ita yarinyar nan bata yi masa turjiya ba yana tune da shine mutum na farko da ya fara tarayyah da ita , shin ko ita ma abun da ya faru da shi ne a jiyan ita ma ya faru da ita ? Toh amma kuma ai ita ta so taƙi yadda da shi sai dai a ƙurarren lokaci ne , har yanzu yana tuno amsa kuwwar kalmomin ta waɗanda suka gaza tasiri wurin daƙile shi ga aikata abun da yayi niyya a jiya da yanzu kuma kalmomin suka zama tamkar ɗigar ruwan dalma a kunnuwan sa , bai ko son tuno da su ,” ko ma menene ita ma tana da nata laifin a wurin shi na yadda ta gaza yin hoɓɓasa wurin dakile fadawar su ga halaka ,”
Tsaki ya ja tare da auna mata harara , ki tashi na maida ki inda na ɗauko ki ,!
Tafiyar kuramen suka sake yi babu um ba a ah ,” kowannen su yana sauraren taɗin zuciyar sa ,
STORY CONTINUES BELOW
Ga yakaka ita har yanzu bata daina mamakin mutumin da bata kai ga sanin ko da sunan sa ba har zuwa yanzu , bata wani jin nadama koh damuwa akan halin da suka kasance ciki tare idan aka ɗauke ɗan raɗaɗin da take ji a jikin ta,
dalili shine bata kai ga sanin girma tare da darajar budurcin ta ba , rayuwar kaɗaici suka taso a ciki , ko a garin su a ware suke cikin jama’ar gari sannan mahaifiyar su bata yi wani yunƙuri wajen nuna musu girman budurcin su ba , basa makaranta illa mahaifin su da yake koyar da su karatun sallah a gida ,”6
Chan wani saƙo na zuciyar ta kuwa yaba gayu tare da gogewar biyamuradi yousouf take har ma take jin yana matuƙar burge ta , hakan ya sa take yawan satar kallon sa zuciyar ta na tuno mata da mahaukaciyar soyayyar sa da ya gwada mata a daren jiyan tamkar zai cinye ta ,’
Ga biyamuradi youssouf kuwa tunane-tunane barkatai cikin kan sa har ya rasa takamaimai na kamawa , shin yaya iyayen sa zasu ji lokacin da labari ya isar musu na irin lalacewar da yake ace wai bayan shan barasa shi youssouf har neman mata ya fara yi yayi nadama da bai amince an ɗaura musu aure shi da maimouna ya taho da ita ba da duk wannan masifar bata auka masa ba da bai lalata ƴar mutane ba shin yaya shi zai ji lokacin da wani abu makamancin wanda ya aikata ga ƴar yarinyar nan ya faru akan meramar sa ?? Runtse ido yayi yana mai jin nadama na sake lulluɓar sa , yayi nadama kuma yana alƙawartawa kan sa ba zai sake yi ba , burkutun da kan ta a yau yana jin wani irin karfin imani da ya jima bai ji irin sa ba akan barin shan ta, ya bar shan burkutun ma , zai yi nesa da duk wasu manyan zunubai tare da yaddar Allah ,
Yana tsayuwa ya juyo ya dubi yakaka wacce daman shi take kallo , suna haɗa ido ya murtuke fuska ,
Duk wasu kuɗaɗe da suke aljihun sa na niger da nigeria sai da ya tattaro su ya zube su akan cinyar yakaka , ” maida hannun sa yayi kan Steering ya ɗauke kan sa da nuna alamun yana jira ta fitar masa a mota ne ,
A hankali yakaka ta ɗago kai tana kallon sa bayan ta kalli kuɗin da ya zube mata su a jiki , kuɗin na menene ? Wani abu zata sayo masa ? toh amma ai waɗannan kuɗin sun yi yawa a sayan abu a dai unguwar nan tasu , anya anya kuwa mutumin nan kan sa ɗaya , ???3
Ta wutsiyar ido yaga irin kallon shakkun da take yi masa wanda ya fassara shi a kallon rainuwar yawan kuɗin da ya bata , dan haka ba tare da yace ƙala ba ya sunce agogon hannun sa na ɗanyen farin azurfa da aka ƙawata shi da ƙananun duwatsu masu daraja , ya ɗora mata akan kuɗin ,
Idan kin ka saida shi kudi ne me tarin yawa ,” ki gaugawar fita ina da tafiya mai nisa a gaba na ,”
Cikin in-ina yakaka tace
Me zan sayo maka da kuɗin toh ?
Wani kallon baki da hankali biyamuradi youssouf ya wurga mata ,”
Kuɗin biyan ki taimakon da kika min ne , ki fita ni zan tafi ,”
Toh ai wannan kuɗin sun min yawa babu abunda zan yi da su ta furta hakan tana mai sauke masa kudaɗen tare da agogon nasa agefen kujerar ta saka kafafu da nufin ficewa a motar kamar yadda yake buƙata ,”
Wata razananniyar tsawa ya daka mata
Ke bani son sokonci kwashi abun da na baki kiyi tafiyar ki , bana so na sake ganin fuskar ki ,”
cikin ran sa yana jin takaicin yarinta tare da rashin wayewar ta da take nuna masa a fili wanda yake sa shi ƙara ganin laifin sa tare da zubewar ƙimar sa wai ace kamar shi ya haiƙewa ƴar yarinyar da bata ma kai ga sanin kan ta ba a matsayin mace,” wannan abun kunya agare shi dayawa yake ,’
Yadda yayi maganar cikin hargagi yasa ba shiri yakaka ta kwashi duk abunda ya bata ta naɗe cikin zanin rufuwar ta da ta tafi da shi a jikin ta jiya ,” cikin sauri ta sauka daga motar
STORY CONTINUES BELOW
Bata yi taku biyu ba ya jaa motar a zabari ya bar harabar wajen yana mai jin yadda bugun zuciyar sa ya fara sauyawa tare da iya adadin nisan tazarar da yake yi da yarinyar ,”
Jiki a sanyaye yakaka ta juyo cikin gida tana mai jin yadda wani abu mai kama da rashin jin daɗin rabuwar su a wannan lokacin yana mamaye ta bata ƙi ba ya zauna tayi ta kallon sa ita dai yana burge ta ɗan gayu ne bugun farko .
Biyawa ta fara yi ta ɗakin samy baby domin ta ajiye kuɗin da ya bata amma sai ta tadda ɗakin a datse da kwaɗo ga alama samy baby bata kwan a gidan ba ,
Zubawa Kuɗaɗen ido tayi tana kallon su kuɗaɗen suna da yawan da ita bata san adadin su ba , ta san suna buƙatar kuɗi ko domin su jaa jari kamar yadda suke da ƙudirin yi , to amma ina zata boye kuɗin ba tare da wani ya gani ba , samy baby tayi niyyar baiwa ajiya ita kuma ga shi bata nan , tana da tabbacin idan har ta shiga da kudin cikin gidam madam saly ta ƙyalla ido ta gan su , raba ta da su zata yi ,
Hannu ta sa gami da ɗaukar agogon da yake ta ɗaukar ido a hasken ranar hantsi , tsaruwar agogon ya burge ta ko ba’a faɗa mata ba kuma ko da ta kasance bagidajiya ta san wannan agogon mai daraja ne , bare mamallakin agogo da bakin sa ya ce agogon mai kuɗi dayawa ne ,” shin har taimakon da tayi masa ya kai ya bata wannan agogon da dukkanin kuɗaɗen sa ? Watakila shi ɗin mai kirki ne ,1
Ɗaga rigar ta tayi ta soka agogon a bakin zanin ta tare da gyara ɗaurin zanin gam-gam ,
Burum aka shigo ƴar kewayayyiyar rumfar katakon da samy baby tayi a gaban ɗakin nata ,”
A firgice yakaka ta ɗago kan ta tana mai kokarin boye kuɗaɗen hannun ta ,”
Karaf suka haɗa ido da yagana wacce wannan ne zuwan ta na uku ɗakin samy baby neman yakaka wacce aka tabbatar mata da bata kwana a gida ba kuma babu wanda ya san inda take wanda hakan ya tashi hankalin yagana tare da falmata wacce tun da ta farka ta laluba gidan taji babu yakaka take ta surfa kuka babu ƙaƙƙautawa ,”
Kai kawo suke ta yi daga waje zuwa harabar gidan da kewayen sa ɗaki-ɗaki neman yakaka , wayam babu ita babu wanda ya ce ya gan ta ma sai mutum ɗaya ne babasho yace tabbas ya ga fitar yakaka tare da wani mutum a daren jiya ,
Da sauri yagana ta ƙaraso
Yakaka ina kika je ? Daga ina kike ? Aina kika kwana ?? Sune tambayoyin da ta jero mata ,”
Na raka samy baby gidan su ne ! Ina falmata ? Mu ƙarasa ciki ,”
Tare da shakku yagana ta tsare yakaka da ido , domin sarai ta ga kuɗin da yakaka ta boye mata , uwa uba wani fitinannen ƙamshi da take ji yana tasowa daga jikin yakakar
Amma ganin yakakar taƙi nuna mata da kan ta sai ita ma ta bar batun .
Ki taho muje falmata taji muryar ki ko ta daina kukan da take ta faman yi tun farar safiya ,”
Bata ƙarasa rufe baki ba yakaka ta taka da gudu ta nufi cikin gidan ,
Zaune ta tadda falmatan ta haɗa kai da guiwa a inda ta saba aiki bakin fanfo ga tulin wanke-wanken kofuna da faranten sana’ar su a gaban ta ,”gefe guda kuma kwanan da ta saba sayo musu waina ƴar tsala da suke karin safe da ita ne , a rufe ga alama ko sayo wainar bata yi ba , “ta gaza yin aikin sai kuka ,”
Da sauri ta ɗago ta tare da rungume ta cikin jikin ta ,’falmata ki bar kuka gani nan na dawo ,”
Yakaka ina kika je kika kwana ? Meyasa baki faɗa min ba ? Kin sa hankali na ya tashi , yakaka ya zan yi a wurin da bakya nan ? Dan Allah duk inda zaki tafi kike tafiya da ni kin ji ?
Naji falmata kuma bazan sake tafiya na bar ki ba ,” ta furta hakan tana mai bubbuga bayan ta sigar lallashi ,”
Yakaka ƙamshin meye ne haka a jikin ki ? Aina kika samu ƙamshi ko a gidan turare kika kwana ?
STORY CONTINUES BELOW
Eh__Ah ah
Unm falmata muyi wanke-wanken kafin rana tayi sosai kin ga mun yi jinkirin fara aiki ,
Toh ai duk ke kika jawo mana !
Madam saly ma ta zo tayi ta masifa tace wai kin fara yawo ,’
Tsam yakaka tayi da jin cewar madam saly tayi masifa ,” a duniya tana tsoron madam saly , tana matuƙar gujewa bacin ran ta gani take ita ce gatan su ,”
Kafin rana ta take sun kammala aikin su da suka saba yi har sun fara hidimar abokan cinikayyar su kamar yadda suke a kullum ,”da hakan ya kwaci yakaka daga shan masifar madam saly , dan ita faɗan ta akan harkar ta ne ba wai dan rashin kwanan yakakar a gida ba ! Yo me ya shalle ta ?
Babu wanda ya bi ta kan yakaka akan rashin kwanan ta a gida yo bariki ce fa ! ?1
Yagana ce ma ta so matsawa ta ji toh amma ganin yakakar taƙi bada haɗin kai ta gaya mata inda ta kwanan sai ita ma ta haƙura , har lokacin rabuwar su yayi suka kammala aikin su na yinin ranar ,
Yakakar ta rako yagana bakin titi kamar yadda suka saba kullum idan yaganar zata koma sansanin su ,”
Kuɗin da suke dunƙule a hannun ta ta kamo hannun yaganar ta danƙa mata su ,”
Ga shi yagana ki sayi wani abu nima bani aka yi ,”
Da sauri yaganar ta ce wa ya baki ? lokacin da take warware ƴan naira dubu guda biyu da yakakar ta miƙa mata su a dunƙule,
Wanda na taimakawa ne ya bani !
Taimako ? Wane irin taimako waye shi ?
Yagana yanzu ba lokacin hira bane kin ga an kusa rufe hanya kiyi sauri ki tafi sai da safe !
A sanyaye yagana tace
Toh nagode !
Sai gobe ,” ta kaɗa kai tayi tafiyar ta zuciyar ta na shakkun ina yakaka ta samu kuɗi haka masu yawa ? Koma menene ita dai tayi farin ciki da kudin da yakaka ta bata koh banza ta toshe wasu daga cikin tarin matsalolin da suke kewaye da ita na talauci !
Akan hanyar komawar ta gida yakaka take tuhumar kan ta meye yasa ta boyewa kowa abun da ya gudana tsakanin ta da mutumin da ta taimaka ? Oho ita da kan ta bata san dalili ba , abun da ta gane kawai shine tana jin kunyar bada labarin yadda suka kasance tare ,”
Dai-dai ta shawo kwanar layin su ƙamshin balangu Barde mai nama ya daki hancin ta , tun ba yau ba tasha haɗiyar mugun yawu akan ƙamshin balangun da kullum take wuce wajen da tunanin ina ma ina ma Allah zai kawo wani tsautsayin da zai gifta ya sa tukubar balangu barde ta tuntsira ita kuwa ta daka wawaso ,! Saboda ba ƙaramin ran ta biyawa yayi da balangun nan ba ,! Rabon ta da nama shekarun da ƴan yawa ,’ to su da suke ta abinda zasu ci su kori yunwa ina su ina nama ,”kayan wadata “2
Yau da take jin ƙugun ta danƙam da kuɗi , tana shaƙar ƙamshin ta saki hannu ta bishi , har cikin ƴar rumfar barde ,
Cikin nutsuwa ta gaida barde
Ya amsa mata haba-haba irin na ƴan kasuwa ,”
Ta miƙa masa gudar ɗari biyar ɗin da ta ciro daga ƙugunta ,
Na nawa za’a yanka miki Ƴan mata ,?”
Na dukka ! yakaka ta furta hakan tana mai gyara tsayuwa jin kan take a sama ,” naman ɗari biyar ai ba kusa ba ,”
Take barde ya washe baki ya fara yanko naman daga gefe-gefe yana kachal-chala shi akan ƴar takarda neɗe nama ,’
Da sauri yakaka tace a ah ba nan zaka yanka min ba nan nake so wuri mai nama-nama da mai ɗin ,” ta nuno wurin da yafi ko’ina sheƙi a jikin naman yana ta nason mai da yaji ,”2
Au to toh bari a yanko miki nan ɗin,”( kuturu da kuɗin sa ai alkaki sai na ƙasan langa )3
Ƙarbar balangun tayi bayan ya naɗe mata yaji a wata ƴar takadda daban ya haɗa ya sa mata cikin leda ,”
STORY CONTINUES BELOW
A ci daɗi lafiya ƴan mata !
Tun a harabar gidan ta fara ƙwallawa falmata kira wacce take zaune daga gefe a babban filin , inda ɗan asharalle ya baje gangunan sa da shi da yaran sa suna ta bugun ganguna ,” kalmomi ne na batsa ake rera waƙar da su , mata Sun shiga layi kowacce tana nuna ƙwarewar ta a fannin girgiza kwankwaso tare da juya sassan jiki ,’ mazan da suke zagaye da su suna kallon su tare da yin eho har wasu suna faɗawa filin su yi wa budurwar su ko wacce ta birge su liƙi ,”
Ta ko’ina jama’a ne birjik a harabar masu cha-cha da karta nayi masu hira musun ball suna fama ,!
Kamo hannun falmata tayi suka shiga daga ciki sashin madam saly inda babu yawaitar mutane sosai saboda mafi yawa suna filin chasu ,”
A gefe ta zaunar da falmata kan wani ɗan dutse , ita ma ta zauna gami da warware ƙunshin naman ta ɗauko ƙatuwar tsoka bayan ta ɗan ɗangwalo yaji ta nufi bakin falmata da shi , wacce tun da aka buɗe naman ƙamshin sa ya buge ta yawun ta ya tsinke ,”2
Ungo falmata buɗe bakin ki kici nama ,”
Unm unm yakaka waye ya baki wannan naman mai daɗin tsiya ?, cewar falmata a lokacin da take ƙoƙarin haɗiye na bakin ta ,!
Ni na sayo mana falmata ,
Yakaka ta furta hakan tana mai sake nufar bakin falmatan da wani yankan
Chak falmata ta tsaya da taunar wanda yake bakin ta .
Aina kika samu kuɗi yakaka ?
Wanda na taimakawa jiya ne ya bani !
Waye shi , ?
Wani ne baki san shi ba falmata nima kuma ban san shi ba , taimakon sa kawai nayi ya tafi kuma yace ba zai sake dawowa ba , ta furta hakan tana jin wani yanayi marar daɗi yana taso mata kalaman sa na ƙarshe suna mata amsa kuwwa cikin kunnen ta ,” Bana son na sake ganin fuskar ki ,”
Kenan ba zai dawo ba ,
zuciyar ta ta aiyana haka!
Kai amma yana da kirki ! Cewar falmata lokacin da zaƙin naman yake ratsa ta ,”
yakaka bata samu zarafin amsa mata ba saboda zuciyar ta da tayi ƙunci ,” a take ta ji ta daina jin garɗin naman dan haka ta miƙe gami da cewa falmata tana zuwa ,” ta ci naman iya cin ta .
Shagon sayar da kayan masarufi da amfanin yau da kullum ta tafi wanda bashi da nisa sosai da gidan su ,
Ta miƙa dubu ɗaya tace a bata manyan jakar bacco guda biyu , da sabulun wanki guda uku da na wanka sinki ɗaya da kuma omo babbar jaka ,”
ɗan jim tayi tana tunanin bayan su kuma me yakamata ta saya ?
Har zata ƙarbi sauran chanjin ta idanun ta suka sauka akan jerin ƴan mukullaye da suke jikin wani ɗan karfe ,” wani tunani ne ya faɗo mata
A bani ƴan mukulli ƙanana guda biyu ,”
Ta haɗo sayayyar ta ta komo gida kai tsaye ta wuce ɗakin da su falmata ke kwana , ta jawo yagaggen jakar bacco wanda suke tara kayan su a ciki ita da falmata ,
Ta fiddo dukkanin suturun su ,”babu laifi yanzu suna da ƴan kaya ,”
Ta warware sabbin bacco , ta ware kayan falmata ta jera mata su tsaf a ciki bayan ta gyara ninkin ta ɗauki ɗaya daga cikin ƴan mukullin ta kama bakin zif ɗin ta sarƙafa shi ta bame ,”
Ta warware ɗayar bacco ta buɗe ciki ,
Ta fiddo kuɗaɗen ta tare da agogon da ya bata ta saka kuɗin a cikin bacco , ta riƙe agogon a hannun ta , ta tsura masa ido , ” kyakyawar fuskar sa tana mata yawo a zuci , ƙamshin da yake manne da jikin agogon ya mamaye mata hanci , ta ji wani irin nishaɗi tare da shauƙi suna huda ta, ina ma ina ma da ace har yanzu suna tare tana kallon sa tare da shaƙar ƙamshin sa ? , a hankali ta kai agogon hancin ta ta sunsuna gami da rufe idanun ta , shi ma’abocin ƙamshi ne kome da ya dangance shi ƙamshi yake hatta kuɗaɗen da ya bata ƙamshin sa suke ,” a hankali laɓɓan ta suka motsa cikin yaren ta tace,”Bature kam silum ,” ( baturen baƙaƙen fata ,)
STORY CONTINUES BELOW
Motsin da ta ji yana nufo ɗakin ya sa tayi saurin ajiye agogon a gefen kuɗin ta fara jera kayan ta bisan su ,”
******************
Iya adadin nisan da yake yi da yarinyar iya adadin daɗuwar rikicin da yake ji cikin zuciyar sa tare da gangar jikin sa baki ɗaya ji yayi masifar da yake zaton ta ƙare tana sake taso masa ,’1
Addu’o’i ya shiga yi iri-iri idan ya kama wannan ya gama ya kamo wancen ,
Ga mamakin sa kamar sake ƙaruwa lamarin yake domin zuwa yanzu karfi da yaji yake jin ana son sarrafa gangar jikin sa ya juya kan motar ya koma wurin ta , kamar yadda zuciyar sa ta riga tayi tsalla ta koma gare ta , “
Karfin addu’ar da yake yi ita ta duƙushe tasirin ko ma menene , har ya samu ya kawo inda suka yi masauki a bakin dajin ,
Bai kula kowa ba duk kuwa da gaisuwar ban girman da suke yi masa ta hanyar ƙamewa su sara masa ,
Kai tsaye ya shiga bayin sa ya ɗauro alwala , ya dawo cikin tantin sa ya sauke farillar sallar asubha da take kan sa ,
Yana idarwa baiyi ƙasa a guiwa ba ya ɗauko alqur’anin sa ya buɗe murya cikin nutsuwa ya fara tilawa ,
A hankali nutsuwa tare da amincin da suke tare da alqur’ani suka fara ratsa shi tare da yin tasiri ga wannan yanayin da yake tunzura shi ,’
Jingina kan sa yayi da jikin karfen tantin nasa lokacin da yaji wani irin bacci mai nawi yana son fusgar sa ,’
Ƙiran wayar sa shi yasa shi buɗe idon sa daga son yin bacci da yake ,’
Ami Tafeêdah
Shine sunan da ya bayyana à fuskar wayar !
Da rashin kuzari biyamuradi ya amsawa tafeedah sallamar sa, bayan nan suka ɗora da tambayar lafiyar juna ,” ?
Ɗan ouwa da dama kou ? meke damun ka ? lalle cikin yanayin ka akwai damouwa yi gaogawar sanar da ni ?
Shiru youssouf yayi , yasan tafeedah yayi masa farin sani , yana kuma iya karantar kowanne irin yanayi yake ciki ,” to amma baya jin zai iya faɗa masa damuwar sa, toh yace me wai ?? Ya sake dulmiyewa cikin alfasha bayan wanda tafeedan ya san yana aikatawa, ya ƙara da wata ??
Ɗan ouwa bani jin daɗin jiki na ne kawai , ciwon kai na damu na ,!
Babu kome ka ɗaure abokina idan har ka cigaba da ƙaurace mata a hankali ahankali duk wasu yanayi masu wuya da kake shiga idan baka sha ba zaka ji ka daina jin yanayin , sannan ka sake dagewa da addu’a .
Uhum
ita ce kawai kalmar da youssouf ya furta
Da ace tafeedah ya san abun da ya aikata da babu abun da zai hana abotar su ta samu tangarɗa
Nagode ! Cewar youssouf
Daga haka suka ɗan yi hira sama-sama , ganin youssouf ɗin bai tare da nutsuwar sa sosai ya sa suka yi sallama tare da sake ƙara masa ƙarfin guiwar gujewa burkutu !
Yadda youssouf ya ga rana haka ya ga daren yau ,” tsafi gaskiyar mai yin sa ne ,”3
Da ita yake son kasancewa a yanayi irin na daren jiya , rashin samuwar hakan a gareshi ya haifar masa da masifaffan ciwon ciki da amai bayan masifar da yake ji a ruhi da ƙwaƙwalwar sa , ji yake kamar ya zura da gudu yayi ta gudu har ya tadda ta , ko kuwa dai yayi fiffike ya sauka gare ta a cikin daren ,”
Shajaran majaran ya wayi garin a halin jikkata , da ya sanya tilas likitocin da suke abokanan aikin su suka shiga bashi taimakon gaggawa , ƙarin ruwa zuwa magunguna ,”
STORY CONTINUES BELOW
ba laifi lafiyar jikin sa a zahiri ta dai-daita amma shi kaɗai ya san halin da yake ciki a ruhin sa ,
Zuwa azahar ya ɗan ji karfin jikin sa , dan haka yayi wanka ya ɗau shiri , zuciyar sa ta gama samun galaba akan sa tare da taimakon shaiɗanin da yake tare da shi yana bibiyar sa tare da ingiza shi ,
Karfe biyar na yammaci tayi masa dot a ƙofar su yakaka ,’
Kan sa tsaye ya shiga gidan yana mai fatan cin karo da ita kawai su tafi , sai dai kuma inda gizo ke saƙar shine , shi fa bai wani tantance da kamannin yarinyar nan ba ,” alhali kuma ya gama shawartar kan sa akan ya tsaya tare da ita kawai ta dunga biya masa buƙatar sa tun da shi ne mutum na farko da ya fara sanin ta ,” shi kuma zai ɗauki duk wasu hidindimun ta har sai zuwa lokacin da ya fita a masifar da ya faɗa ,’
Da wannan tunanin ya sanya kai cikin rumfar madam saly , ya tadda babu mutane dayawa mafi yawa suna wurin chasun da ya gitta a yayin shigowa ,”
Wuri ya samu daga gefe ya zauna , zuciyar sa na fatan ganin ta kamar yadda yake yawata idanun sa akan ƴan matan da ke kai kawo ta gaban sa , baki ɗaya bai ga fuskar ta ba acikin su ,
Ina take ?
Ya san fara ce tas , bayan haka babu abun da zai ɗorar na daga suffar ta ,’
Yagana ce ta ratso ta cikin rumfar cikin shirin tafiya gida, yakaka biye da ita da nufin yi mata rakiya ta dawo ta ƙarasa aiyukan da take kaiwa har dare tana yin su daga wannan zuwa wancen !
Tana sanyo kai ta ji ƙamshin sa ,’ tabbas wannan ƙamshin “bature kam silum ” ne , a take bugun zuciyar ta ya sauya tare da wata kewar sa mai tsanani da ta taso mata
Ina yake ! Tambayar zuciyar ta
Tun da suka bullo ya gan su , a take zuciyar sa ta shaida ta tabbas ita ce abar kwaɗayin sa ita ya zo nema ,!
Hankalin ta ya rabu biyu ɗaya yana ga hirar da yagana ke yi mata ɗaya yana ga son gano inda yake , dan haka bata samu nasarar ganin sa ba har suka zo giftawa ta gefen sa ,”
Ganin zata wuce shi ya sa shi miƙa hannu ya kamo hannun ta ,”
Da sauri ta juyo domin ganin waye ne ,”duk da cewa an saba yi mata haka ,”
Idanun su suka sarƙe cikin na juna kowannen su ya gaza ɗauke idanun sa , a yayin da suke fassara kallon da suke yiwa juna a zuciyoyin su ,”
Kallon da yakaka ke bin biyamuradi kallo ne na nayi kewar ka , na kuma yi farin cikin sake ganin ka ,
Yayin da take fassara kallon da biyamuradi yake jifan ta da shi a nufin.!
Gani na dawo ki sake taimaka min .,’
Zan taimaka maka ta ƙudurce cikin ran ta ,!
Har yagana tayi ɗan nisa ta waiwaya bata ga yakaka ba dan haka ta dawo da baya
nan ta tadda ta suna kallon juna da wani mutum da bata kai ga sanin sa ba , da ido ta bi hannayen su da yake manne ,!
Dafa kafaɗar yakakan tayi ganin irin shagalar da tayi ,bata san ma ta zo wurin ba
Da sauri yakaka ta zame hannun ta daga cikin na biyamurdi ,” Ina zuwa ,’ tace da shi !
A bakin kofar shigowa ainahin gidan ta dogare
yagana zan koma daga nan kin ga ana jira na !
Da ido yagana take bin ta cikin ranta tana mamakin farin ciki tare da murnar da yakaka take yi wanda kafin fitowar su a ɗazu babu shi,’
A karo na huɗu ta sake tambayar ta
Wai yakaka sai tambayar ki nake kin share ni waye wannan ɗin ko ƴan uwan ku ne ?
STORY CONTINUES BELOW
Bature kam silum ne ,
Ɗan uwan mu ne
Daga haka ta juya da sauri har tana haɗawa da ɗan gudu ta koma ciki ,1
Ta bar yagana da mamakin ta fal cikin rai ,
” bature kam silum’ ta maimata sunan ,!
sashi guda na zuciyar ta yana shakkun ambaton sa da tayi da ɗan uwan ta , kai wannan daga gani ba yaren mu bane !
Da murmushi akan fuskar ta ta ƙaraso gaban sa ,
Ki kimtsa ki taho mu tafi ,kadda ki ɗau lokaci
Ya furta hakan yana mai ɗauke kan sa daga kallon ta ya mayar ga agogon hannun sa ,”
Kalmar kimtsawa tai mata tsauri wurin fahimta , amma da yake tana jin sa cikin zuciyar ta , sai ta kintata ta hasaso abun da yake nufi , dan haka ta shige ciki ,”
Ƙasa-ƙasa ya bi takun kafafu da kallo wanda yake halin sa ne kallon ƙasan ido ,”
nan ya hango dauɗa tare da taron kursashin da yake danƙare ƙasan kafafun ta . Cikin sauri ya ɗauke kan sa !1
A gurguje ta shiga ta ɗibi ruwa tayo wanka , ta dawo ɗakin su larki ta hau shiri ,” falmata wacce take zaune shiru kamar yadda yake al’adar ta ce killace kan ta wurin da babu kowa tayi shiru ,”
Motsin da taji an taɓa musu jakar kayan su , ya sa takai hannu tana kamo jakankunan nasu ,”
Waye anan ?
Yakaka wacce ɗoki ya sa bata ko yi sallama ba bare tayi wa falmatar magana , tace,
Nice fa falmata nah ,”
Aiyo yakaka na , to ai baki min magana bane ! Yau har kin gama aikin ne ?
Ban gama ba falmata ,
Mutumin shekaranjiya ne ya dawo yana so mu je na sake taimaka masa ,”
Zuruf falmata ta miƙe nima zan biki yakaka ,!
Tsam yakaka tayi ta bar ƙoƙarin sanya kayan ta da take yi ,
Ta taso ta zo ta kamo hannuwan falmata ,”
Falmata na kiyi hakuri ki zauna har naje na dawo , kin ga aikin da nake yi masa mai wahala ne baza ki iya ba , kuma yau bazan kwana ba , anjima kaɗan zan dawo kin ji ?
Da kyar ta shawo kan ta ta yadda zata jira ta tare da alƙawarin baza ta kwana ba zata dawo , da haka ta kammala shiryawa cikin wata atamfar cote d’ivoire ruwan zuma mai cizawa da aka yiwa ɗinkin riga da siket , duk cikin ire iren kayan da samy baby tayi mata kyautar su ne da basu sha jiki sosai ba ,” wani turaren da samy baby ta bata lokacin da take menses ta ce ta dunga shafawa a jikin ta ,”shi ta ɗauko ta mutsittsika ,”
Fes tayi kyau ta ɗaura ɗankwalin ta shigen yadda ta ga samy baby na yi , bata sanya gyale ba domin bata da shi kuma ka’idar gidan madam saly ba’a yawo da mayafi .!1
Wannan karon a tsaye ta tarad da shi ya saka hannun sa ɗaya cikin aljihun wandan sa , da alama tsumayen ta yake cikin ƙaguwa ,”
Babu laifi a idon sa tayi kyau , duk da cewa shi ba wannan bane ya dame sa ,
Sai dai tana matsowa kusa da shi ya ji wani ƙamshi marar daɗi a hancin sa yana tashi daga jikin ta , sam ƙamshin bai masa ba ,!
Juyawa yayi ya fara taku ba tare da yace da ita ƙala ba ,”
Zungui-zungui ta bishi a baya ,
Duk yadda yaso ya Daurewa ƙamshin turaren dake tashi a jikin ta ya kasa , sosai yake jin wani yanayi marar daɗi a cikin ƙamshin , shi mutum ne mai tsananin tsafta da ƙyanƙyami sam bai son wani abu da yake da alaƙa da ƙazanta ,”
Dan haka lokacin da suka daidaita akan titi ,ya ɗan juyo da ganin sa kan ta ,”
Ki gwouda mini hanyar les salons !
meye kuma Les salons, ? ita hausar sa gaba ɗaya wahalar fahimta take yi ma ta ,”
STORY CONTINUES BELOW
A takaice ta amsa
ban san wajen ba !
Wani wuri ya samu a gaba kamar super market ya tsaya shaguna birjik a wurin ,
Mayuka tare da sabulai zuwa turaruruka na mata , masu kyau da tsada ya jida ,
Ya koma banagare kayan sawa ,”shi ba wani sanin size ɗin ta ya yi ba dan haka ya ɗauki dogayen riguna baƙaƙe biyu ,
A wurin biyan kuɗin ya tambayi Cashier wurin salons , nan ya masa kwatance na wani shahararren wurin gyaran jiki da yin kwalliya , TaTa saloons da yake kan titin danboa .3
Ya ajiye kayan a kujerar baya ya zo ya tada motar ba tare da yace da ita ƙala ba , ita ma kuma tayi shiru bata magana sai satar kallon sa ,
Tata salon babban wurin gyaran gashi , ƙafa da ƙumba , yin kwalliya da gyaran jiki , zuwa sayar da turarurrukan arabs masu kyau da ƙamshin sanyaya rai ,suna da gyalalluka na yayi masu matuƙar kyau da inganci .
Hajiya ruma mamallakiyar shagon mace ce mai karamci wacce ta san harkar kasuwa dan haka take girmama abokan cinikayyar ta , ( Allah ya ƙara ɗaukaka ƴar ƙanwa ta )1
Sun ci sa’ar tarar da ita da kan ta , inda tayi musu tarɓar girma tare da ruwan gora da lemun gongoni ,”
nan youssouf yace ayi wa yakaka gyaran jiki tun daga salons zuwa pédicure , kai har wanka ma ayi mata ,! . Aka sa masa kuɗi ya biya .
Nan aka shiga da yakaka wani ɗan ɗakin da ya wadata da fitilun haske ,’
Suka fara aikin su , goge nan wanke chan , dirza nan shafa wannan goge wancen , har dai suka samar da yadda suke so a jikin yakaka , duk da cewa su da kan su sun yi mamakin irin dauɗar da take danƙare a kowanne lungu da sakon jikin yakaka ,
,misalin karfe takwas na dare suka fito da ita , tayi kyau ba kaɗan ba , ɗan nude makeup ɗin da suka mata ya sake fiddo da zallar manyan kyaun da take da shi , jikin ta sanye da ɗaya daga cikin dogayen rigunan da ya saya mata ,sun yi mata naɗi da gyalen rigar bayan sun tara mata gashin ta mai rangwamen duhu sai tsanananin laushi da tsawo a tsakiyar kan ta sun kama mata shi da roba ,”
, ita da kan ta jin kanta take kamar ba ita ba kamar an sauya ta , wani irin nishaɗi ne yake huda ta , ƙamshin da yake mamaye da sassan jikin ta yana bata wani irin farin ciki na musamman, tsafta tayi a rayuwa ,” ita kuwa me bature kam silum zai biɗa a wajen ta da baza ta iya masa ba ? ai babu !4
Da ido yake bin ta da kallo lokacin da suka fito , duk da cewa idanuwan sa sun saba ganin kyawawan mata daga bangarori daban daban na duniya , amma kwarai irin nata kyaun ya burge shi ,” daga inda yake yana jin tashin ƙamshin ta ,”
Da hakan ya sa shi sakar mata murmushi da suka haɗo ido , a karo na farko da yakaka ta ga murmushin sa wanda yake ƙarawa fuskar sa haiba , nan take ta washe gajerun hakoran ta da suka sha wanki tana maida masa da martanin dariya , tsintar kan ta tayi da tambayar sa ,”
Nayi kyau ko ?
Murmushin bai gushe ba akan fuskar sa ya haɗa yatsun sa biyu babban da mabiyin sa ya mata alamu da kinyi kyau sosai !
Hannun sa ya miƙa mata ta ɗora nata akai ya ja ta suna mai ficewa a shagon
ma’aikatan shagon suka bisu da kallon sha’awar da suka basu ,”Cikin ran su suna aiyyanawa ma’aurata ne irin sabon auren nan har wata ƴar gaza gani daga cikin su ta tanka ,” perfect couples”2
Kwanakin da suka biyo bayan wannan ranar biyamuradi youssouf da yakaka zama suke irin na masoyan ma’aurata , babu wata rana da ta tsallake musu da basu kwana tare ba .
Yayin da biyamuradi yake fidda kuɗi yana mayar da yakaka irin macen da yake so , ƴar hutu ƴar gayu mai tsafta , tata salons ya zama wurin zuwan su , bai jin ƙyashin kashe mata kuɗi tare da bata farin kuɗin tsurar su domin ta biya wasu buƙatun , har ƴar ƙaramar waya ya saya mata , wanda yake amfani da ita wurin kiran ta idan ya zo ɗaukar ta ,” a yanzu burkutu guzurin ta yakaka take yi masa , har ɗakin da suka mayar na kwanan su a garki Guesthouses ,
STORY CONTINUES BELOW
Yakaka kuwa sau da kafa take bin biyamuradi youssouf cikin dukkanin buƙatun da ya zo mata da shi bata iya kuya masa baya , tana bashin haɗin kai tare da juriyar ɗaukar bukatun nasa ,”
A yanzu aikin gidan madam saly ya ragu a kan ta , saboda yadda biyamuradi da ita kan ta yakakar suke sakarwa madam saly kuɗi , wacce a rana ta biyu da yakaka ta sake bin biyamuradi suka kwana alhalin bata gama mata aiyukan ta ba kusan raba dare tayi tana zagin yakakar tare da shan alwashin a gobe gobe zata kore su ,
Da hakan ya sa falmata kwana tana kuka ita ba kome yafi bata mata rai ba irin kalmar “ƙaramar karuwa sabuwar yar iska ,” da madam saly ta danganta yakakar da shi ba ,”
cikin muryar kuka ta dunga maimaita kalmar
Yakaka na ba ƴar iska bace
Yakaka na ba ƴar iska bace
Ƙasa-ƙasa yadda madam saly bata jiyo ta ,’ tsaf ta gama kintsa musu jakar kayan su tana jiran gari ya waye yakaka ta dawo su kama hanyar su,”
Sai dai abun da ya ɗaure mata kai washegari bayan dawowar yakaka gidan tayi ta kasa kunne ta ji hayaniyar madam saly tana zagin su tare da kora kamar yadda tayi rantsuwa , ” sai taji tsit , sai ma jin madam saly tayi ta zo har cikin ɗakin nasu tana bawa yakaka wani abu tare da shaida mata idan har ta sha shi da madarar ruwa ko nono , ba ƙaramar kyauta saurayin ta zai yi mata ba ƙila ma ya bata “mota ,”
Saurayi kuma yakaka ?
Wanne saurayi ? Tambayar da falmata ta jefawa yakaka kenan , bayan ta cika bakin ta da donut, wacce ita ma yakakar ta toshe mata baki da kayan maƙulashen da biyamuradi ya ciko mata manyan ledoji da su ,lokacin da ta so tada bori akan kwanan da yakaka ta sake yi a waje ,!
Ba saurayi na bane wanda nake taimakawa ne ,”
Wai yakaka wane irin taimako kike yi masa da har yake baki kayan daɗi haka ? ga turare mai ƙamshi da kika ce ya baki har da su mai ,” to kawai mu koma gidan su mana mu dunga yi musu aikin tare koh ba taimakon sa kike da aiki ba ?
Cikin diriricewa yakaka ta ce,”
Ba-ba ba agidan su muke aikin ba a wani waje ne ,falmata kiyi zaman ki anan tun da ni ina zuwa nemo mana , kuma ina samo mana kuɗi , kin ga tunda kuɗaɗen dayawa idan suka taru har ɗaki zamu iya kamawa mu bar gidan nan , mu kama sana’a a hankali a hankali muna neman su maman mu ko ?
Take falmata ta hau murna jin za’a nemo maman su ,” nan dai ta hakura zata dunga zama yakaka ita zata dunga zuwa sabon aikin da ta samu !
Haka kwanaki suka jaa har yau da suke kwanaki goma sha huɗu da fara tarayyar su , zuwa yanzu yakaka tayi nisa cikin makauniyar soyayyar biyamuradi bata ji bata gani wata irin mahaukaciyar soyayyah take masa da bata ƙi ba su tabbata har abada a tare ,6
Ta bangaren biyamuradi kuwa shi tun farko babu batun so atsakanin sa da yarinyar , hasalima ya ɗauke ta ne kawai a matsayin mai bashi maganin cutar da yake ganin ta kama sa a kwanakin nan na jarabar mace , wanda a yanzu kuma yake jin ya fara samun sauƙi domin a ƴan kwanakin nan yanayin da yake ji mai tsanani a duk ranar da bai kusance ta ba ya ragu , dan haka zuwa yanzu ya fara jin zai iya daina harkar gaba ɗaya tunda daman dole ce ta sanya shi farawa ,( a cewar sa )
A yau yayi niyyar sallamar yarinyar da ƴan kuɗaɗe masu tsoka domin yau idan ya koma daji ba zai sake fitowa kwana kusa ba zai maida hankalin sa kachokam kan aiki , giyar da kan ta zai gwada barin ta na kwana biyu ,
Daga wanka ya fito jikin sa ɗaure da towel , kai tsaye ya nufi ƴar wadrobe ɗin da take ɗakin ya fiddo da mai tare da mataji ,( comb ) ya shafa mai tare da taje ƴar sumar sa da bata cika yawa ba , , ya jawo ƴar ƙaramar jakar matafiya da yake sako kayan sa a ciki shiga ɗaya idan zai shigo gari ya fiddo kakin sa na soji ya sanya ya fesa turare tare da ɗaura agogon sa , kayan jikin sa da ya cire wanda yake riga long-sleeved da dogon wando , ya ɗauka ya mayar cikin jakar tare da haɗo ƴan sauran tarkacen sa duk ya zuba a ciki ,
STORY CONTINUES BELOW
Ya samu wuri ya zauna a gefen gadon ya jawo takalman sa mahaɗin kayan sa yana ɗaurawa a kafar sa ,
Duk abun da yake yakaka wacce take shirye tsaf a kishingiɗe a gefen gadon tana bin sa da kallon so da ƙauna haɗi da burge ta da duk wani motsi na sa yake , “
Tunani take ina ma ina ma ace wannan kyakkyawan mutumin da har yau bata kai ga sanin sunan sa ba duk kuwa da kusanci mafi girma da suka samu a tsakanin su , ina ma da zai AURE TA , ?
Da ita kuwa ta gama jin daɗin rayuwa tare da nasarar rayuwa ,1
Ɗago kan sa yayi ya kalle ta , ɗan gajeren murmushi yayi mata
Yaya irin wannan kallo haka ƴan mata ?
Kayi kyau bature kam silum ,” amma ina ta tambayar ka meyasa kai kayan ka ba irin na sauran sojoji ba , baka bani amsa ,”
A takaice ya amsa mata saboda ni ba sojin ƙasar ku bane ,”
To inane ƙasar ku ?
Wani wuri ne mai nisan gaske ! ,”ya amsa mata
Wallet ɗin sa ya ɗauka ya fiddo da dukkanin kuɗaɗen ciki , da suke sabbin ƴan dubu ɗai ɗaya , ” ya tako ya zagayo ta bangaren da yakaka take ,
Kamo hannun ta yayi tare da ɗora mata kuɗin ,”
Ƴan mata ,( kamar yadda yake kiran ta tun haɗuwar su a zahiri ya manta sunan ta bai kuma taɓa damuwa ya sake tambayar ta sunan ta ba toh ina ruwan sa da sunan ta ? Amfanin me sunan zai masa ? )
Ni zan tafi yau kuma bazan dawo nan kusa ba saboda yanayin aiki na , ƙila na dawo cikin sati biyu masu zuwa ƙila sai cikin wani watan watakila kuma …. Sai ya ɗan yi shiru tare da duban fuskar ta ,”
Wacce tunda ya fara bayani idanuwan ta suka cika da ƙwalla , wani irin bugu zuciyar ta take yi ,
Zame hannun ta tayi kuɗin suka sauka akan katifar ,”
“ka bar kuɗin ka bature kam silum ba sai ka biya ni ba , ni dai dan Allah kar kace baza ka dawo yau ba , ka dawo dan Allah ni ko baka bani kuɗi ba zan taimaka maka kamar kullum , akwai wasu sauran kuɗin da kake bani ma ina tara su duk zan dawo maka da su ni dai dan Allah bana so na daina ganin ka , idan bana tare da kai zuciya ta bata min daɗi , na saba da kai .
tun da ta fara magana yake bin fuskar ta da kallo wacce kafin ta kammala ta jiƙe da ruwan hawaye , wani irin tausayin ta ne ya kama shi , tausayi mai tsanani , ya fahimci yarinyar ta faɗa a tarkon son sa , wanda shi kuma sam bai so hakan ba domin kuwa a zahiri bata da gurbi cikin rayuwar sa ko kaɗan , ” shi kuwa ina zai kai ƴar talakawa marar galihu irin wannan yarinyar toh ya kai ta ina ? Masarautar su ? Ai auren ɗan sarki sai ƴar sarki idan kuwa ba ita ba toh sai fa ƴar manyan attajirai ,” kai shi bai taɓa ɗaukar ta da wani matsayi ba ma da ya wuce macen da yake biya ta gusar masa da sha’awar sa , bata da wani banbanci da sauran karuwai !3
Duba ƴan mata ,” ni akan aiki na zo ƙasar ku , batta kasancewa kullum mu zauna tare , ki ɗauki kuɗin ki riƙe a hannun ki zasu miki amfani watarana , ni akan hanya nake ,” ki manta da ni kiyi rayuwar gaba har yanzu ke yarinya ce kin ji kou ? Tashi mu tai na sauke ki gida .
A motar ma share hawaye yakaka take sosai take jin ciwon barin ta da zai yi , yace wai ta manta da shi , anya ? Ita ta san baza ta iya mancewa da shi ba ,” ya samu wani irin gurbi mai girma ya kafa kan sa cikin zuciyar ta ,”
kiran wayar sa shi ya katse shirun su , samun waje yayi ya tsayar da motar a gefen hanya , ” nan ya amsa wayar
Kira ne na gaggawa ake yi masa daga sansanin su na soji !
Da sauri ya buɗe murfin motar da hannu yake yiwa yakaka alama na ta sauƙa masa a mota ,”
Jikin ta a sanyaye ta sauƙa tana gama ficewa a motar ya ja murfin da ƙarfi ya harba motar bisa titi a guje .’
tsumu ta tsaya a gefen hanyar tana sake kallon kuɗin hannun ta ,” kome bai mata daɗi wani irin ɗaci take ji daga ƙasan ran ta yana taso mata ,
Matsawa tayi jikin wata mota da take tsaye a gefe ta jingina jin da tayi tsayuwa na neman gagarar ta ,” kuka take son yi so take ta samu wuri tayi ta kuka ko zata ji saukin abun da take ji a ran ta , da gaske ya tafi bazai dawo ba ? ko wasa yake yi mata ?
Tun kafin ya tsallako titin daga ɗan shagon da ya tsaya ya saya kayan marmari a gefen titin , hasken ta ya dalle masa idanu , amma kasancewar sa mai tsananin kamun kai da nutsuwa babu ruwan sa da harkar mata (irin yadda samarin yanzu suke ) ya sa yayi saurin ɗauke kan sa ,
Har ya ƙaraso jikin motar da take jingine da take mallakin sa ce bai sake kallon inda take ba ,”
Murfin motar ya kama zai buɗe sannan ya juyo ya dube ta ,”
Baiwar Allah zan ɗauke motar daga wurin ,!
Ko gizau bata motsa ba
Ɗan tsaki ya ja marar sauti , wasu matan dai basu da kamun kai dubi wannan yadda ta zo ta dogare a bakin titi duk masu wucewa idon su akan ta .
Ya sake maimaitawa da ɗan karfi ,
Zan ɗauki motar nace baiwar Allah
a hankali ta juyo da fuskar ta inda take jin tashin muryar sa , kamar ta san muryar ,!
Kallon juna suka yi ido cikin ido ,
Tsai yayi yana kallon ƙwarar idon ta , shin ita ce ne ko ba ita bace ? Ƙwarar idanun ta suna tabbatar masa ita ce wacce ya shafe fiye da watanni biyu yana neman ta tsakanin sansanin su da zagayen kasuwa ,wacce a karshe ƙawar ta tace sun gudu sun bar garin ,” sai dai kuma yanayin shigar ta da gogewar da ya hango tare da wannan suna ƙarya ta masa ita ce , wacce ya sani ai ƴar ƙauye ce ƙazama , wannan kuwa ƴar birni ce wayayyiya kuma ƴar gayu ,” kai sai dai kamanni ,1
,” da sauri ya saita kan sa daga ruɗanin da ganin kamar wacce yake bulayin nema ce ya sanya shi ,”
Ya ɗaure fuska gami da maimaita maganar sa ta farko cikin ƙosawa ,”
A hankali ta janye jikin ta daga motar , “
Ta gane shi sarai shine likitan da ya sha taimakon ta tun farkon zuwan ta garin ,”! Sai dai halin da zuciyar ta ke ciki a yanzu babu damar da zata tsaya yin magana da kowa ko da kuwa kalmar gaisuwa ce , domin tana buɗe baki kukan da take yi a zuci ne zai fito fili , dan haka ta ɗauke kan ta ,’ ta matsa bakin titin sosai domin tarar adaidaita ya kai ta gida tayi jinyar gangar jiki da ruhin ta da tun yanzu suka fara kewar bature kam silum ,”1
Tana matsawa a jikin motar ya shiga gami da jan motar sa , a cikin ran sa yana mamakin al’amarin hatta tafiyar su iri ɗaya ya furta hakan a fili yana sake leƙen ta ta jikin madubin motar ,” gefe guda na ran sa ƙaunar yarinyar da har yau bai ko kai ga sanin sunan ta ba yana tasowa , ya so ƙwarai ya nemo ta , domin a ranar da suka bar asibiti ita da ƙanwar ta ba ƙaramin damuwa ya shiga ba , so yayi ya ɗauke su ya kai su gidan sa inda yake zama tare da mahaifin sa da ƙannen sa ya ɗau nawin su ya inganta rayuwar su ita da ƙanwar ta , ya sha wahalar neman su da kwatance su a sansanin su dakyar aka samu wacce ta san su aka ce tare suka zo , tashin farko da ya tambaye ta game da su tace da shi YAKAKA DA FALMATA SUN BAR GARIN .Yakaka tana shiga gida Kai tsaye sashin samy baby ta nufa , ta ci sa’ar samun kofar ɗakin ta a buɗe kai tsaye ta danna kai cikin ɗakin idanun ta a rufe da ruwan hawayen da yake ambaliya ,”4
Zube guiwar ta tayi a ƙasa tare da yin jifa da kuɗaɗen hannun ta suka tarwatse a tsakiyar ɗakin ,hannuwan ta biyu ta sa ta rufe fuskar ta lokacin da take sakin kukan da yake cin ta a zuci .
Sautin kukan da yayi sanadiyyar tashin samy baby a firgice daga baccin tofon girar da take shaƙa ,”
Da sauri ta zo ta kama ta
Yaks meye ya same ki ? Duka aka miki ? Ko meye ?
Kusan ba a hayyacin ta ba ta riƙo hannun samy baby ,
Dan Allah ki ce masa ya dawo kar ya bar ni , idan bana ganin sa mutuwa zan yi , kin ga nan ,”ta ɗora hannun samy baby akan zuciyar ta ,”ciwo take min ina jin wani abu ya tokare ni ,” INA SON SHI WALLAHI INA SON SHI,”4
Kalmar ta ta ƙarshe ita ta sa samy baby kwashewa da dariya bayan fitar ta daga ruɗanin da kukan yakakar ya haifar mata shi da farko ,”
Shashashar banza yanzu ke yaks akan soyayya kike wannan uban kukan ? Kamar wacce aka cewa uwar ta ta mace ? To wai ma tsaya yaushe kika fara soyayya ban sani ba ? Duk kuwa da kashedin da nake yi miki ? Koh daga tafiyar da nayi ta sati biyun ce har kananan ƴan iskan nan da nake raba ki da su suka samu damar hure miki kunne ,ah lalle fa ga ki kuwa kin sauya kin yi lumui lumui kin cika kin yi clean , hala saurayin naki mai ɗan gwaɓi-gwaɓi ne naga ya wanke min ke , ah toh ai babu laifi tun da mai maiƙo ne ,”
shi ya baki wannan kuɗaɗen kenan ? ,” ta furta hakan tana mai bin kuɗaɗen da kallo , ” idanun ta suka sauƙa kan ɗan wani hoton fasfo wanda ga alama daga tsakanin kuɗin ya fito , ta kai hannu gami da ɗaukar hoton ,
Hoton sa ne sanye da kakin sa na soji daga kirjin sa zuwa fuskar sa ,” kallon hoton tayi da kyau tabbas ta san shi abokin saurayin ta nuhu ne ,’bata manta ba nuhu ya bata ɗan takaitatcen tarihin sa a wani yammaci da taje bariki wurin nuhu ta tarad da youssouf ɗin , bayan tafiyar sa take tambayar nuhu yaya ta ga launin uniform ɗin su ya banbanta ? Nan ya shaida mata youssouf sojin niger ne , ya ɗora da bata labarin sa kar ki gan shi haka anan fitattace ne a ƙasar su ɗan sarki ne , yarima ne mai jiran gadon birnin maraɗi ,babbar masarauta ce a niger ,”5
Yaks wanene wannan ?? Ko shine masoyin naki ?
Da sauri yakaka ta ɗago kan ta domin ta ga wanda samy baby take kira da masoyin ta ,
Idon ta ya sauka akan ƙaramin hoton biyamuradi , da sauri ta kaiwa hoton chafka !
Shine wallahi shine , ina son shi dan Allah anty idan kin san shi , ki kai ni wurin sa ,”
Cikin mamaki samy take yi mata kallon kan ki ɗaya ?
Ke yaks wannan ne saurayin ki ? Kar ki min ƙarya , gaya min ta yaya ya zama saurayin ki ?
Yakaka bata boye mata kome ba daga ranar haɗuwar su ta farko da youssouf zuwa yau ,”
Jinjina kai samy bby tayi bayan ta gama jin bayanin yakaka da ta tabbatar ba ƙarya bane ,! Domin ta san goge yaks a ɗan ƙaramin lokaci ta zama fes yadda ta gan ta sai mai kuɗi ,3
Idan kuwa hakane babu shakka tayi farincikin ƙulluwar alaƙar sa da yakaka , daman irin namijin da take mata hange kenan wanda zasu tatsi arziki daga jikin sa !tab , ai batun yace ya rabu da yakaka ma zancen iska ne , wasa tsakanin sa da yakaka yanzu aka fara , zata yi duk yadda zata yi taga mu’amalar sa da yaks ta ɗore , har sai ya gama wanke yaks ya zamar da ita mace mai aji yadda baza ta yi wahala ba wurin samun irin sa ko ma wanda ya fi shi koh da shi ya zo ya bar ta , ! Ai da ruwan ciki akan jaa na rijiya ,’ idan yaks bata wanku ba ina zata samo masu attajirai irin wanda take buri???3
Share hawayen ki yaks idan wannan ne na san shi abokin saurayi na ne , duk inda yake sai na nemo miki shi , kin ji ? Bai isa ba ya wurgar da ke bayan ya morewa ƙuruciyar ki , dole ya zo ya ƙarasa aikin da ya fara ,”
STORY CONTINUES BELOW
Cikin murna yakaka ta fara share hawayen ta , tana jin damuwar zuciyar ta fiye da rabi ta kau , jin cewar samy baby ta san bature kam silum har tayi mata alkawarin nemo mata shi ,”
A saboda murna tana tattara ƙudaɗen da ya bata , ta miƙawa samy baby ,”
Ga shi anty na baki gaba ɗaya !1
Da murmushi samy baby take kallon ta , sa hannu tayi ta karɓi kudin ta ƙirga su dubu arba’in da shida ne ,”
Naira dubu goma ta zara a ciki ta miƙawa yakaka sauran ,”
Ki riƙe sauran kuɗin a hannun ki zasu miki amfani kafin na gama shirya yadda zan yi na dawo miki da yarima , wannan wanda na ware kuma , kafin ya dawo ku cigaba da harka dole zamu je asibiti a baki kariya daga samun ciki , kin sai dai ba’a cin moriyar bariki idan ana yi ana kwasar ciki .
Da sauri yakaka ta amince da shawarwarin samy baby , nan dai suka ƴar taɓa hira samy baby tana sake kitsawa yaks shawarwarin yadda zata riƙe yarima idan ya dawo ,2
Falmata tayi jugum a zaune tana tunani, wata irin kewa take ji , tun da yakaka ta samu aikin da take yi yanzu ya zama bata da lokacin ta irin da , duk da cewa dai idan tana gidan tana bata kulawar sosai da sosai bugu da ƙari ga cimaka masu kyau da daɗi da suke samu a yanzu , ga wasu ranakun ma biya yakakar take yi ayi aikin wanke-wanken falmata , amma duk hakan sun gaza samar da farin ciki mai daɗi ga falmata ,yanayin su na farko da ko yaushe suna tare yafi mata kome daɗi , bata da kowa bayan yakaka ,! Ga shi wannan aikin da yakaka ta samu yana neman raba tsakanin su , domin a yanzu duk zata iya ƙirga ƴan awowin da suke yi tare da juna a wuni ,
daɗewar da yakaka tayi yau bata dawo daga wurin aikin ba ya dagula ran ta , tana aunawa da zafin ranar da yake buso ta tare da kusancin ranar da take ji a jikin ta ta tabbatar yanzu rana ta fara kaiwa tsaka ! Ina yakaka take tun jiya da yamma har yanzu bata dawo ba ? A hankali wasu siraran ƙwallah suka silalo zuwa kan ƙuncin ta ,!
Bata ji zuwan ta wurin ba , sai saukar hannun ta taji ta share mata ƙwallar ,!
Cikin ƙaruwar rashin kuzari akan wanda tafiyar youssouf ta jawo mata ganin hawayen falmata ya sake taɓa ranta , ” ta zauna daga gefen falmatan
Falmata na ! Meyasa ki kuka ? Wani abun aka miki ? Ko baki da lafiya ne ?
Yakaka yanzu kin rage kula da ni , bayan kuma kin san ke kaɗai nake da ita wacce take bani kulawa , ” yakaka dan Allah nima ki yadda na dunga bin ki sabon wurin aikin ki nafi son koyaushe muna tare duk inda muke , bamu da kowa sai junan mu ,”
Kiyi hakuri falmata nima daga yau ɗin bazan sake zuwa ba !
Meyasa baza ki je ba ? Ni fa ba nace ki daina zuwa bane , toh shikenan na hakura ki dunga zuwa kin ji ,?
An dakatar da aikin ne wanda nake yiwa aikin ya tafi ,! Sai idan ya sake dawowa watarana ,”
Cikin rashin jin daɗi falmata ta karya wuya ,
Kai amma banji daɗi ba yakaka mutumin yana da kirki , tun da kika fara aiki a gidan su muke samun jin daɗi .,’
Uhum ,!
Cewar yakaka tana mai miƙewa
Bari na sauya kaya na nazo kan aiki ,!
Chan ƙasan kayan ta a kusa da kuɗaɗen niger da agogon sa da ya bata a haɗuwar su ta farko ta ajiye hoton tare da kuɗin hannun ta , a ran ta tana jin hoton sa da agogon sa zasu zame mata abun ɗebe kewar sa kafin samy baby ta dawo mata da shi kamar yadda ta alƙawarta mata !2
Washagarin ranar samy baby ta samu yakaka , suka je asibiti ƙarƙashin jagorar wani nurse abokin hulɗar samy baby , tare da taimakon sa aka yiwa yakaka allurar hana ɗaukar ciki , ba tare da an tsawaita binciken ina mijin ta ba ?, tare da tunasar da ita dawowa sake yin wata allurar duk bayan watanni uku !
STORY CONTINUES BELOW
Yakaka bata ji ko ɗar ba sai ma farin ciki da take ji chan ƙasan ran ta a domin kan hanyar su ta zuwa asibitin samy baby ke sanar da ita a yau ɗin nan zata garzaya barracks wurin nuhu inda zata samu cikakken bayanin inda youssof yayi bigire idan ma ta kama har inda yake sai ta kai yakaka ! har ɗakin kwanan sa ,! Ah to meye bariki ce fah ! A haka suka tsaya .
Sai dai tun dawowar su daga asibitin yakaka ta gaza tsinana wani abun kirki , saboda wani irin murɗawa da marar ta take ta sake , ga duhu-duhu da take gani a idanun ta ,! Gaba ɗaya jin ta take marar lafiya ,’ dan haka ta zari nera dubu biyu cikin kuɗin ta ta bawa madam saly tace bata jin daɗi zata je ta kwanta ,”
Jiki na rawa madam saly ta warce dubu biyu tace ta je ta kwanta za’a yi aikin ta .!
Kafin azahar yakaka ta jigata saboda tsabar ciwon ciki da kwankwaso ta takure a guri ɗaya sai murƙususu take , ! Larki ce ta shigo ɗakin ta tadda ta a galabaice ,” nan take tambayar ta meye yake damun ta tace ciki da baya ,’
Cewa tayi ta bada kuɗi a anso mata magani ƙila ciwon cikin al’ada ne daman yana irin haka ,!
Da rarrafe ta jawo jakar kayan ta ta fiddo da duk kayayyakin ta zaƙulo damin kuɗin ta , ta fidda naira dubu ɗaya ta bayar a anso mata magani ,!
Ta koma ta kwanta gami da runtse idanun ta !
Da kan ta larki ta je ta amso mata magungunan saboda ta hango moriya , ta kuma ƙulla abunda ta ƙudurta cikin ran ta ,”
Ta tsaya a wani ɗan shago ta sayo mata ruwan leda guda biyu !
Lamoo ! ta samu yakaka tana sauraran gangar jikin ta ,”
Ta taimaka mata ta zauna tare da ɓalla mata maganin ta miƙa mata ruwan ta kora , ta koma ta kwanta cikin wani sabon yanayin rashin kuzari da take jin kan ta a ciki .
Larki ta ɗan saci kallon jakar kayan yakaka , ta gan ta a buɗe yadda ta bar ta bayan ta miƙo mata kuɗin !
Yaks bari na tattara miki kayan naki , ai ba’a bar kayan haka ba ko dan gudun masu dogayen hannu kin san ɗakin namu babu tsaro ,’ ,
Idon ta a rufe ta ɗan gƴaɗa kan ta ,!
Da azama larki tayi wa jakar kayan rumfa ta bada baya ga yakaka wacce idanun ta ke rufe ,”
Kayan ta fara mayarwa bayan ta wawuso kusan rabin kuɗin da yake cikin jakar ta chusa a lalitar ta ,”
A ranta tana cewa ! To meye ? Ta san yarinyar sabuwar hannun ce dan haka tana kan ganiyar ta , dan ƴan waɗannan kudaɗen ba kome bane a wurin ta , ƙila ma bata san yawan su ba daga ta shafa ta ji sun ragu , fita zata sake yi wurin masu bata ta sake samo wasu , Dan haka gwara itama ta samu ta wawushe nata , ko ta samu ta kashe wasu matsalolin ta, ta kuma farfaɗo da jarin ta na goro da taba !
Da wannan zancen zucin ta kammala maida kayan tsaf ! Ta juyo da kallon ta kan yakaka domin ta sanar da ita ,”
Sai taga bacci ma take da alama ta samu lafawar ciwon !
Tura jakar tayi inda suke ajiye ta cikin ranta tana ayyana ta samu hujjar da zata kare kan ta ko da ace yaks tayi cigiyar kuɗin ta ,” cewa zata yi bata san wanda ya ɗauka ba ita dai ta gyara mata kayan ta fita ,!
Sai bayan la’asar yakaka ta farka ! Daga baccin da yake cike da mafarkin biyamuradi da soyayyar sa da ta maƙale mata a zuci ! Watsa ruwa tayi tayo alwala , ta haɗa sallolin azahar da la’asar tayi su ,
Tsumu tayi a zaune kan ɗankwalin ta da ta shimfiɗa tayi sallah bisa , ta rasa abun da ke mata daɗi .
Babu laifi taji sauƙin ciwon cikin sai dai sakayau take jin ta ga wani irin ƙuncin zuciya da take ji uwa uba kewa tare da ƙaunar youssouf da take tokarin ta a duk bayan daƙiƙa guda wanda ko da wannan aka bar ta kawai ya isheta cuta ! Ji take kamar ta shekara da barin ganin sa haka ta shafe tsawon daren jiya tana jin kewar sa ta gaza bacci sai juye-juye ,3
STORY CONTINUES BELOW
Cikin sati biyu kachal da suka yi tare da juna ya mata mugun sabo da soyayyar sa mai tsayawa a zuci , duk da cewa soyayyar ba da baki yake ambato mata ba , a aikace yake idar mata , shiyasa gaba ɗaya take jin kewar sa hatta a fatar jikin ta da kowanne saƙo da lungu na jikin ta ,! Har gizo hannuwan sa ke yi mata a sassan jikin ta ,’ ko yaya ta rufe idanun ta fuskar sa take gani tana mata gizo , shi ba ma’abocin murmushi agare ta bane , amma yanayin kamammiyar fuskar sa yana bala’in burge ta , babu shakka a rayuwar ta bata taɓa ganin mutum ɗan gayu mai kyau irin sa ba !1
Yunwa take ji domin rabon ta da abinci tun karin safe ,” sai dai kallo ɗaya tayi wa robar abincin ta da take ajiye a gefe wanda take da tabbacin wake da shinkafa ne a ciki ta ɗauke kai , ‘ abinci daddaɗa bakin ta yake kwaɗayi !1
Jakar ta ta jawo domin ta ɗauki kuɗi taje sayan abinci wurin su kolo
Kallo ɗaya tayi wa kuɗin tasan an taɓa su , da azama ta fiddo su ta ƙirga ta ga dubu goma sha bakwai ne a maimakon dubu talatin da huɗu,!
Jujjuya kuɗin take idanun ta sun ciko da ƙwalla , tana da buri akan kuɗin , so tayi ta kai falmata babban asibitin ido a duba ta domin kwana biyu idon yana ɗan matsa mata da ƙaiƙayi kuma suna yin jaa , cikin ran ta bata fidda rai watarana falmata zata gani da idanun ta ba , ji take watarana falmata zata ga hasken da yake wadace cikin sarari duniya , watarana zata ga fuskokin jama’a , zata ga fuskar ta kamar yadda kullum ita take ganin ta !
, sannan idan kuɗin ya rage ta jaa jari ta fara soya doya da kwai da yammaci zuwa dare , kafin dawowar bature kam silum domin ta ɗanɗani daɗin kuɗi da ƴancin da suke samarwa ga mai su ! Baza ta iya sake zama irin na tsananin talauci tare da walaƙancin da ake musu sanadin babu ba ! idan ya so sa dunga raba ribar tare da madam saly , ta san baza ta ƙi ba !,2
Amma shine wani azzalumin marar imani ya kwashe mata kuɗin ?! Tunanin larki ya faɗo mata arai , ko ita ce ta ɗauka ? Amma larki anya zata ɗauki kuɗin ta ?
Koma waye na bar shi da Allah ! Ban yafe ba .1
Ta furta hakan a sarari tana share guntuwar ƙwallar ta , ta zari naira dubu ɗaya , a ranta tana tunanin chanjin ta da ya rage hannun larki , bata , bata ba ko maganin na dubu ɗaya ɗin ne ? Ita dai baza ta tambaye ta ba idan ma ta cuce ta dan kan ta ! ¿
Kai tsaye ta wuce rumfar su kolo , ta miƙa kuɗin tace a bata tuwon shinkafa da miyar yakuwa , malmala biyu da nama guda huɗu ,
Kolo ta miƙo mata tuwon a naɗe cikin leda tare da miyar a wani ɗan kwanon roba bayan ta gargaɗe ta akan ta dawo musu da kwanon miyar !
Kai tsaye wurin wanke wanken falmata ta wuce , ta tadda ta wanke-wanken sun taru tana ta faman wankewa ana ƙaro wasu , saboda yamma tayi lokacin ciniki ne kuma an kusa gama sayarwa ! Alamun gajiya ya bayyana a gare ta ,ga gumi da ta haɗa fiye da rabin zanen ta a jiƙe yake da ruwan wanke-wanken! Ajiye abincin hannun ta tayi a gefe !
Cikin ruwan kumfan ta sa hannu gami da zare soson daga hannun falmatan ,
Kawo nayi sauri na gama , kin ci abinci falmata ??
Da murmushi a fuskar ta ta cire hannun ta a ruwan gami da goge hannun ta a jikin rigar ta ,’
Ban ci ba yakaka , kin ga aikin yayi yawa wanke wanken ina yi ana ƙaro wasu ,”
Amma yanzu zan samu nayi sallah sai na ci ,”
Da ido kawai yakaka ta bita lokacin da ta matsa jikin fanfo ta fara alwala ,”
Ɗan kwalin ta ta shinfiɗa tayi sallar azahar da la’asar akai , bayan ta idar , tace yakaka ta bata abincin ta ,da ta rufe shi da faranti a gefe ,”
sai lokacin yakaka ta lura da yasashiyar robar abincin falmata da take buɗe , ɗaukar robar tayi tana kallon abincin da ana gani an san ƙarshen tukunya ne ƙanzo-ƙanzo ,babu wani mai da yaji na kirki cincirindon ƙudajen da suka tashi daga kan abinci ya sa ba shiri yakaka ta juye shi a bakin makwarari ta wanke robar ta ɗauraye ,
STORY CONTINUES BELOW
Ta ɗauko malmalar ɗaya ta sawa falmata ta sake gutsuro rabi ta ƙara mata ta juye mata fiye da rabin miyar , ta kai mata tuwon gaban ta ,’ tare da taro mata ruwa a kofi daga bakin fanfo , ita ma ta zauna daga gefe tana cin guntun tuwon ! Suna ƴar taɓa hirar su kamar yadda falmata take so , cikin hirar su take sanar da ita ta shirya gobe zata kai ta ita ma a wanke mata kan ta tare da yi mata kitso !1
Bayan sati biyu
Rayuwa tayi wa yakaka tsanani wanda ba kome ya jawo hakan ba sai rashin bature kam silum , domin cikin satin biyun da suka biyo bayan ranar haɗuwar su ta ƙarshe , kamar yadda samy baby ta alƙawarta mata zata nemo mata shi ta wurin abokin sa ,!
Ta je barracks ɗin sai dai bata tarar da shi Colonel nuhu ba, an tabbatar mata da ya tafi bakin aiki ,! Wanda hakan sam bai mata daɗi ba kuma ta kirayi duk numbobin sa basa tafiya ta rasa dalilin haka ! ?
Zuwan ta daban-daban uku bata samun sa , dan haka ta ɗan tsahirta .tare da cigaba da lallaɓar yakaka wacce ta lura tayi zurfi cikin mahaukaciyar soyayyar mutumin da a yanzu take hasashen yayi wa yakaka nisa , sai dai a nemo madadin sa ! Wanda bata ga alamun samun haɗin kan yakaka wurin nemo madadin na sa ba ! , babu ranar da yakaka bata kuka akan soyayyar bature kam silum , ɗakin samy baby nan ne wurin fakewar ta ta sha kukan ta domin ita tasan matsalar ta ita tasan dalilin kukan ta , kuma ita take zaton zata iya share mata hawaye , sai dai a yanzu labarin ya sha banban kuma wankin hula na neman kai su dare ,!3
A yau yakaka ta tashi bata da ko sisi domin satin da ya wuce ta kai falmata asibitin ido da kuɗaɗen hannun ta inda kuɗin magunguna da wasu aune-aune , ya lashe fiye da naira dubu takwas , a cikin sauran dubu goma sha biyu da ƴan kai da suka rage mata ,
Da sauran kuɗin tayi amfani wurin cigaba da hididimun yau da kullum , musamman abinci wanda shine kan gaba wurin lashe mata ƴan kudaɗen domin kwanan nan ta tsinci kan ta cikin wani irin bala’in kwaɗayi , bata iya cin abincin da bai wadatu da kayayyakin ƙawata girki ba , bata kuma cin abinci babu nama sannan a rana bata sha lemon kwalba “pepsi ” ba tasha guda uku safe rana dare ,’ idan kuwa bata sha ba babu zaman lafiya wani iri bala’in yunwa mai tafe da tashin hankali zata dunga ji ,”2
Da haka kuɗaɗen hannun ta tas suka ƙare !
Duk da tarin damuwar da take cin ta cikin rai , kallo ɗaya za’a mata a gane ta sauya , ta sake fari har tana ɗaukar ido ta cika tayi luwai-luwai kyaun idanun ta kamar gilashi sun sake haskaka ,! Tana zuwa wuri take ɗaukar hankalin jama’ah .
Ture jakar kayan tayi gefe ta ƙarasa bajewa ta zauna daga durƙuson da tayi ta tallafe kumatun ta da hannu, wannan shine karo na uku tana chaje cikin kayan ta a safiyar yau ko Allah zai sa tayi gamdakatar da wani makararren chanji , sai dai koh alamar kuɗi bata gani ba idan aka ɗauke kuɗin sefa ,”niger”, wanda basu da wani maraba da babu a wurin ta ,”
A hankali ta miƙe tana haɗa hanya saboda wata azababbiyar yunwar da take wuji-wuji da ƴaƴan hanjin ta ,’
Ɗakin samy baby tayi wa tsinke ,’
Saɓanin zaton da tayi zata tadda ta tana bacci ta jira tashin ta , sai ta tarad da ita tayi shiri tsaf , tana zaune bakin gado tana shirya kayan ta cikin ƴar jaka ta matafiya ! Gaishe ta tayi cikin ladabi !
Yauwa yaks daman yanzu nake son na tura a ƙira min ke , tafiya ta taso min jiya-jiya cikin dare Honourable yake sanar min zamu yi tafiya tare da shi zuwa abuja inda zai je wani aiki watakila ma mu wuce dubai daga chan ,” ga waɗanan kayan ki ɗauka na bar miki su , ni nasan a chan zan taho da wasu masu zafi ,” ta furta hakan tana mai turawa yakaka wasu kayayyaki da ta ware su gefe,!
Yakaka wacce tun da taji kalmar tafiya jikin ta ya sake yin sanyi laƙwas ,! Ta durƙusa bisa guiwar ta ,’ a gurin samy baby take ɗan samun nutsuwar zuci , take kuma ɗan taimakon ta da wasu abubuwa , baza ta so ba ta tafi ta bar ta a wannan halin tsaka mai wuya da take ciki ,
Cikin sanyin murya tayi mata godiya , bayan ta haɗa kayan ta ƙulle su a ɗankwali ,’
Cigaba tayi da zama tana bin kowanne motsi na samy baby da ido cikin ran ta tana ayyana dama ita ma da bature kam silum ya tashi tafiyar sa ya nemi rakiyar ta mana ? !1
STORY CONTINUES BELOW
Lura da yadda jikin ta yayi sanyi yasa samy baby , ta ce
Ni bani ma lambar wayar ki idan naje ma dunga yin waya , ba kina da waya ba ?
Gyaɗa kai tayi
Amma ban san nambar ba wayar ma tana ƙasan kaya na babu chaji ,
Mts idan banda ke yaks waye zai saka waya ƙarƙashin bacco ? To wannan ai ko yariman ma ya kira ki ba sani zaki yi ba ,” gidadancin ki yayi yawa yaks bari dai na dawo daga tafiyar nan inaga darasi zan fara baki dalla-dallah
Ƴar takarda ta ɗauka daga jakar ta ta rubuta mata lambar wayar ta ta miƙa mata ,”
Ga lamba ta nan ki kira ni idan kin saka wayar a chaji kuma ki daina ajiye wayar a nesa watakila ma shi baturen naki yayi ta nema bai same ki ba ,’
Cikin ɗan ɓurɓushin farin cikin jin an ambaci sunan masoyin ta tace
Toh anty zan dauko yanzu idan na koma ɗaki , anty kuma yaushe zaki dawo ?
Ban sani ba yaks ni ƴar rakiya ce ! Sai lokacin da ya gam Abun da ya kaushi zamu dawo tare .
Gƴaɗa kai ta sake yi !
Toh anty sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya ! ta furta hakan bayan ta miƙe tsaye da ƙullin kayan ta ,” har ta je bakin kofa ta tsinkayo muryar ta
yaks ungo wannan kƴa ɗan sayi pepsi ki sha tun da yanzu naga yayin ɗaga ƙwalbar pepsi kike ! Ta ƙarasa zancen da ƴar dariya
Dubu biyu ta bata , da murnar ta ta ƙarba ,” tana jero godiya
Zuwa tayi ta kai kayan da ta bata ɗaki ta dawo domin yi mata rakiya,
Tare suka jera yakaka ta ɗaukar mata jakar kayan nata , suna tafe tana sake karfafawa yakaka guiwa ganin yadda duk ta bi ta damu da tafiyar da zata yi , har zuwa bakin babban titi inda ta samu “mai adai-daita “, ta shiga tare da yin bankwana da yakaka !
Akan hanyar ta ta komawa gida tayi zurfi cikin tunanin ƴar ƙanƙanuwar duniyar ta ,wacce babu kome cikin ta sai tarin ƙalubale , mutanen duniya tausayi yayi ƙaranci a zuciyar su , son kan su tare da son dukiya sun makantar da su wurin duban na ƙarƙashin su da ƙyautayi da kyautatawa , kaɗai suna duban na ƙasa da su ne idan wata buƙata tasu ta tashi wanda suke buƙatar wannan ya kawar musu da ita ,1
Da ƙarewar kuɗin hannun ta da tsayuwar rayuwar yancin da ta fara dai-dai suka zo domin tun lokacin da madam saly ta fahimci fa yanzu ta koma faƙiriyar ta kuma ta daina ganin gilmawar mutumin da ya tsaya mata tare da jin yayyafin nerar da yake yi mata , ita ma taci burki daga duk wani mutunci da lallaɓawar da take yiwa yaks , ta koma karta mata walakanci tare da bautar da ita ,” ah toh me zata jira ? Ai kawai ungulu ta koma gidan ta na tsamiya , jaki ya tai gidan uban sa !1
Ita ba gallazawar bautar aikin yafi damun ta ba illa yadda ƙarfi da yaji madam saly ta fara kai ta gaban ƴan iska tana tallar ta , ita baza ta jure hakan ba , bayan bature kam silum bata jin zata iya yadda da wani ɗa namiji har suyi abun da suke yi tare da shi , cikin su wanene mai kamannin sa ? Mai tsaftar sa ? Mai wayewar sa ? Mai gayun sa ? Mai irin ƙamshin sa ? Babu ! Idan kuwa haka ne ita baza ta yadda da kowanne ƙaton ɗan iska ba bata son su !1
Zata jure kowanne irin aikin bauta da wahala , amma ban da harkar taimako ta wannan sigar , bature kam silum kaɗai yake da wannan ƙimar a gurin ta , zata zauna zaman jiran sa har ranar da zai dawo gare ta !
Da wannan tunanin ta ƙaraso shagon “fashe mai shayi ! Tace a fasa mata ƙwayaye shidda a soya su da indomi manya biyu , a haɗa mata shayi da madarar ɗari bonbita na hansin ! Ta miƙa kuɗin aka bata ƴan chanjin ta .
Aka sarrafa mata aka zuba a leda ta ƙarba , Shagon gefen sa ta wuce ta sayi lemon kwalba na pepsi mai sanyi ,1
Ran ta ƙwal ta dawo cikin gidan kai tsaye ta wuce cikin ɗakin su falmata , a zaune ta tarar da ita , ta ajiye kayan hannun ta gami da ficewa taje ta wanko kofuna biyu da faranti ɗaya ta zo ta juye musu ,
Falmata matso muci!
Lomar yakaka ta ɗaya ta biyu ta zare hannun ta daga cikin abincin sakamakon ji da tayi zuciyar ta ta wani hautsina ta yamutsa kamar zata fito ta baki , nan take tsinkakken miyau ya taru a bakin ta ,” ta matsa gefe tana jan numfashi .
STORY CONTINUES BELOW
Jikin ta har rawa yake ta balle murfin pepsi da haƙorin ta ta kafa kai tana kwankwaɗa , ba dire ba sai da ta shanye ,”
Sai dai me wani irin ƙugi da cikin ta yayi falmata da kan ta ta jiyo , kafin ta ankara wani kakkarfan amai ya taho mata , nan ta dunga kwarara shi a ɗakin daga bakin kofa , kaf abincin da ta ci tun daga na jiya da dare da bai kai ga narkewa ba har zuwa ƴar indomi ɗin yanzu sai da ta amayo su , amai har ta hanci , ga hawaye da yake ta tsiyaya a idanun ta , yunƙurin aman ta har kofar rumfar su ana jiyo sautin sa ,’ har ta koma sai kakaru bata amayo komai sai koren yawu ,”1
Falmata ta gigice da ya sa ta fatali da kofunan shayin nasu tare da bi ta cikin farantin indomi ta ɓarar da sauran , cewa take
Yakaka yakaka yakaka , meye ya same ki ? Meye ne ? Baki da lafiya ne daman ? Me kika ci kike amai ? Da lalube ta ruƙo yakakar zuwa jikin ta bayan tayi zaune dirshan cikin aman da yakakar tayi ,1
Rashin amsa mata da yakaka tayi wacce take ta yunkurin amai har muryar ta ta shige ciki ya sa falmata fashewa da kuka tare da fara kwala ƙiran neman agaji ,’ ihu take tana neman taimako
Daga bakin maƙwarari inda hema da larki suke wankin dawa suna jin su duk yunƙurin aman da yakaka take sun ji sarai sun kuma riga sun yi hasashen abun da ka iya sanya ta aman dan haka suka yi biris , ! Yo ina ruwan su ? Sun ga ire iren ta yafi sau shurin masaƙi , ‘
Rabu da shegiyar yarinya , ba dai ita tace bariki zata yi wa shigar sojan badaskare ba ? Sama ta ka ba tare da ta ɗau darasi ba , ai kuwa zata ɗanɗani kuɗar ta , wannan somin taɓi ne daga cikin illolin faɗawa bariki ba tare da an nemi ilmin sa ba ,” cewar hema1
ihun da ya yawaita ya farkar da madam saly daga baccin tofon girar da take shaƙa a gigice ta bazamo kan ta babu ko ɗan kwali guiguyayyar ƙeyar ta da sanƙon ta sai ɗaukar ido suke a hasken ranar da ta fara ɗagowa , ” cewa take
Wace masifar ce ta faru da farar safiyar ne ? Waye ya mutu ? Waye ya sha azaba ? Ake faman kururuwa haka ?2
Kai tsaye ta nufi ɗakin su hema inda take jiyo tashin ihun falmata ,”
Turus ta jaa ta tsaya ,” yawata idanun ta tayi cikin ɗakin tana ƙanƙan da ido kafin ta lailayo wata ƙazamtatciyar ashariya ta watso ,” ta ɗora da
Na shiga uku na lalace ni salaha dan uban uban ku yakS me nake gani haka ? Gasar amai kuke koh me ?wace iriyar shegiyar ƙazamta ce wannan irin taku ta ƴaƴan ƙauye kuke gwada min haka a cikin gida ? Tab toh da sakel wallahi baza ku korar min kostomomi ba , yo wannan ai idan ɗaya daga cikin kostomomi na suka ga wannan iskancin ƙazantar da kuke babu ni babu ƙara ganin wani ya zo sayan ruwa ,” dan babu mai yadda ya ci abun da kazamtattu irin ku suka taɓa ,!
Wata irin damuƙa tayi wa kafaɗar yakaka ba tare da ta kula da halin galabaita da take ciki ba , ta hankaɗo su waje tare da falmata wacce ta maƙalƙale jikin yakakar ,” suka tafi suka faɗi tare nan yakaka ta ƙarasa bajewa a ƙasa cikin halin rashin sanin inda take ,
Shegiya tsinanna yo wani ɗan iskan ya aike ki kije ki maƙalo ɗan tayi a mahaifar ki ? Ai ni daman kallon ki kawai nake ina jiran ranar da cikin zai baiyana kan sa , ko ta arziƙi ko ta tsiya , amma tun tuni na farga da shi , shegiya marar sa’a daga fara bariki har kin ɗauko ciki , to kar ki ji da wai ni bana rainon ƴaƴan shegu a cikin gidana dan haka ku san inda dare yayi muku , arziƙi nake nema ba tsiya ba baza ki raɓe ni da shegen abun da yake cikin ki ku maƙalamin asara da rashin sa’a ba ,” yo ƴaƴan halas ɗin ma wasun su amfanin me suke tsinanawa kan su da iyayen su idan ban da masifa ? Haure kafafun yakakar tayi , idan kin gama watangaririyar ki a ƙasa sai ki tashi ku hau shiri , ban ji zan iya ba rainon ɗan shege ! ki bar ni naji da kaina !2
Wani irin bugu zuciyar falmata take da kalaman madam saly suke sauƙa a kunnuwan ta , wai me take cewa ?waye yake da cikin shege ? Ɗan shege waye zai haife shi ? ta san ɗan shege sarai domin kuwa akwai wata ƴar makotan su da ta taɓa yi , iyayen ta suka kore ta , kowa a unguwar su ya tsane ta , jama’ah suka ta yin Allah wadarai da ita , mamar ta ta dunga kuka har ta daina fita layi , bata san ma’anar cikin shegen ba sai da ranar ta nacewa maman su da tambayar ma’anar kalmar,”a taƙaice ta bata amsa haihuwar yaro ba tare da anyi aure ba shine cikin shege,” har garin su ya watse ba’a san inda wannan yarinyar take ba , tabbas cikin shege abu ne marar kyau matuƙa , madam saly tana nufin irin shi yakaka tayi ?
STORY CONTINUES BELOW
Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji yakaka ta jaa wani numfashi tare da sake yin wani yunƙurin aman ,”
Wani sabon ihu ta sake saki ,”
Dan Allah ku taimaka min kar yaya ta ta mutu dan Allah ku taimaka mana ,” yakaka ki min magana dan Allah ki daina shiru , ki tashi yakaka ki tashi ,
Larki ce ta bar abun da take gami da nufar bakin fanfo ta taro ruwa a wani kwanon silver gami da sanya wani bokitin a bakin fanfon , a kaikaice ta ɗago yakaka wacce take ta sakin numfashi’ita ba sumammiya ba ita kuma bata motsin kirki ,” ta kafa mata kwanan a baki ,
Bata wani shaa na kirki ba ta cigaba da yunƙurin aman,”
Aifa lalle kin gamu da wahala , gwara ma idan zaki tashi ki ta shi domin a gidan nan babu wanda zai damu ko mutuwa zaki yi a nan a yashe sai dai a tsallake ki a wuce , masu mutuncin ciki sune zasu jaa ki gefe a samo mai miki salla a je a turbuɗe ki , dan haka ma gwara ki bar lamɓo ciki ba kan ki aka fara ba , laulayi kuma dole ne tun da har kika iya zuwa kika kai kan ki aka maƙala miki maƙalalliya, kin dai ji abun da ,”saly fara,” tace ki fara shirin bar mata gida ,”
Juye mata ruwan bokitin da ta ɗauko tayi akan ta baki ɗaya ta jiƙa su sharkaf har da falmata wacce take ƙwaƙume da yakakar , daga ita har yakaka ba sauraran bayanin bakin larki suke ba ,”1
wacce ita ce ɗaya da ta kula su , ta zo kan su duk da cikin walakanci take musu Abun da ita a wurin ta taimako ne !
Nan ta dangwarar da bokitin gefen su ta wuce bakin aikin ta tana cewa ,”
Sai ke kuma ki tashi ki je ki wanke ɗakin da kuka gama chaƙuɗa shi da kazantar , sakarkarun yara ƙyauyawa !
Sanyin ruwan ya taimaka wurin farfaɗo da yakaka daga halin gigitar da ta shiga ,” da taimakon falmata ta miƙe zaune ,” yadda kan ta yake juyawa tare da wani irin bala’in ciwo ya sa ta kama kan nata da hannu biyu,”
Falmata kaina zai fashe ,’!
Sannu yakaka ki tashi na kai ki ɗaki ki kwanta ,’
A wajen kwanciyar ta, ta taimakawa yakaka ta kwanta , fita tayi ta lalubi bokitin da larki ta ajiye ta ɗauka taje ta taro ruwa a cikin sa ta komo ɗakin ,”ita bata san inda tsintsiya yake ba a gidan , dan haka ta laluba ta tattara kofunan da farantin ta haɗa su wuri ɗaya , kasancewar ɗakin daman Ledar sa ta riga ta ratattake ta zama gutsirarra ,ta wurin da suke kwanciyar , daga tsakiyar sa zuwa bakin kofar dandaryar siminti ne , sai kawai ta kwarar da ruwan ta wuraren da take jin lema-lema , ta sa takalman ta biyu ta kwarfe ruwan ta tura shi wajen kofar ,’
Duk abun da take yakaka wacce idanun ta suke lumshe tana jin ta , karfin tashin ne bata da shi , wata iriyar mummunar kasala take ji tana bin duk gabobin jikin ta , ga juyawa da kan ta yake yi ɗakin kan sa juya mata yake ,”
Gefen yakaka ta dawo ta zauna , cikin ran ta tana fatan lafiya ga yakakar wacce take zaton bacci take ,”
Ko mintoci biyu basu ƙarasa ba suka ji muryar madam saly tana ɗuro musu ashar ,”
Ni za’a kawo wa iskanci da tsaurin ido , dan uban ku ni da gidana ina cewa ku fita kuna yin biris da ni , sai kace da uwar ku muka haɗa kuɗin sayan gidan ?? To billahi minti goma yayi kaɗan zan sa a fitar min da ku bayan an chasa min ku ,” yau naji jaraba da maSifa ,”1
Tana gama hanya ta fito ta durƙusa a gaban madam saly gami da fashewa da kuka ,”
Madam dan Allah wanne laifi na miki zaki kore mu ? Ke kaɗai ce gatan mu dan Allah ki yafe min laifin da nayi miki , idan mun bar nan bamu da wurin zuwa ,”!
Ji min mayyar yarinya ? Ta ina na zama gatan ku ? Babu dangin iya babu na baba ? Na gaya miki yaks ni bana jurar asara , asara ce babba na ci da ke na ci da ɗan cikin ki ? Yo wanne aiki kike min da har ya kai na dunga ci da rai uku a biyan aikin ? Ga ki ga ƙanwar ki kuma ga ƙarin wani yanzu kin maƙalo a cikin ki ,’ idan har kina son zaman gidan nan sai dai ki samo uban cikin jikin ki nayi masa lissafi kuɗin abincin ɗan sa ya lale ƙuɗi na ya biya ni sannan ,! Tab ina zan iya asara ?
STORY CONTINUES BELOW
Ɗa a cikin ta ? Wacce magana ce wannan madam saly take faɗi ? Ko dai kunnuwan ta sun daina ji daidai?
Madam wane ɗa ? Ina ɗan yake ?
Yana ƙundun uwas ki yaks nace yana ƙundun uwas ki , ni zaki yiwa bariki ? Ah lalle fa gwada min firirita irin ta sabuwar karuwa ,”1
Sunkui da kai yakaka tayi kan ta yana sake ƙullewa ,”
Wai zaki ki kira ɗan iskan da ya ɗirka miki cikin ya zo ne ko kuwa kin zaɓi barin gidan ?
Da sauri tace !
Zan kira shi madam
Na baki nan zuwa gobe duk inda ɗan iskan yake ki nemo shi yazo ya biya kuɗin ci da ɗan tayin sa ko kuwa yasan inda zai yi da ke ,! Madam saly ta furta hakan tana mai wucewa ta bar wurin cikin ran ta kuwa tana ayyana irin kuɗin da zata iya samu akan cikin jikin yaks domin kuwa ta san da mutum ɗaya tak yaks tayi harka , bata shakkun shi ya fara sanin yaks kuma shine uban cikin jikin ta , idan kuwa haka ne ai ita ranta ƙwal ,1
tun da ta lura da samuwar cikin take farin ciki tare da ƙulla yadda zata yi wannan ciki ya buɗe mata sabuwar hanyar kama kuɗi a hannun wannan hamshaƙin attajirin da yayi mata ɓarin naira akan taraiyar sa da yaks , wanda bata tantama wani hamshaƙin attajiri ne mai muƙami , ko kuwa dai ɗan attajiran , da har yau take mamakin ina baƙauyiya kamar yaks ta samo shi ,? shi kuma cikin jerin gogaggun matan duniya da suka dace da shi ya rasa ta zaɓa sai ya tsallako kan yaks ? Kai ita tafi danganta tarayyar sa da yaks ma da neman wani cikar burin sa na daban , wata ƙila sa’a aka bashi aka ce ya haɗa da neman kuchakar mace irin yakaka ,wata ƙila kuma wani al’amari ne mai girma ya jirkita tunanin sa da har ta kai shi ga neman yakaka , ita dai ta san ruwa bai tsami banza !2
Koma meye ita gaba ta kaita !
Harƙƴalla da irin su babbar sa’a ce .
Ko batun korar da tayi wa su yakakar , barazana ce kawai ta shirya mata domin ta zaburar ta ta nemo mutumin da ta lura a yanzu bai cikin rayuwar yakakar , da ita kuma take ganin rashin sa a matsayin wani babbar asara , dole ya dawo ya cigaba da harka da yaks ita kuma ta cigaba da samun maƙudan kuɗaɗe ta sanadin hakan ,!
Ta shafe fiye da mintoci biyar a durƙushe nan wurin tana tunani , sai dai duk yadda ta kai ga son fahimtar inda maganganun madam saly suka dosa ta gaza ganewa ,”
Wanne irin ciki ? Ta san ciki ake a haifi ɗan mutum , to amma ita bata da wani sani akan yadda ake a ɗau cikin ɗan mutum ! Tasan dai sai anyi aure ake haihuwar , to ai ita bata yi auren ba ! Kuma da madam saly take cewa tana da ciki , ina cikin a jikin ta ? Cewa take cikin mata huruwa yake ya zama ƙatoto sai a haihu ,? Ita kuwa nata cikin shafal yake ,”babu ko alamun tudu ,”
Wata sabuwar tambayar ce ta kutso cikin tunanin ta , toh kuma waye baban ɗan cikin nata da madam.saly take cewa ta nemo ?
“Bature kam silum” wani sashi na ran ta ya ayyano mata sunan sa a matsayin uban ɗan cikin ta da ake ikirarin tana da shi ,”
Ɗan wani tattausan murmushi ya ratso tsakanin hawayen fuskar ta ya bayyana kan sa ,”
Kome da ya dangance shi sanyata nishaɗi yake tare da farin ciki duk kuwa yadda ta kai ga shiga halin damuwa da tashin hankali ƙaunar sa daban ce cikin ran ta tafe take da wani irin kakkarfan shauƙi mai bata kuzari ,’
Ina son ka dayawa !
ta furta hakan a sarari tana mai dafe marar ta da take ɗan yin ciwo kaɗan ,”
Karaf kalmar ta sauka a kunnuwan falmata wacce jin wucewar madam.saly da yadda ta kaya tsakanin su da yakaka , ya sanya ta fitowa duba yakakar bayan ɗan gajeran zaman jiran shigowar ta ɗakin da tayi domin akwai tarin tambayoyin da take son yi mata ,”
Rashin shigowar yakaka da wuri ya sanya ta gaza jiran ta , sashin ran ta na fatan ba ciwo ne ya sake turnuƙe yakakar ba , sai dai kalmar da taji yakakar ta ambata a kunnuwan ta ya sanya ta sa kalmar a jerin tambayoyin da take son yi mata .
Hannu ta kai ta lalubo kafadun yakaka ta ɗora hannuwan ta duk biyu kan kafadun tana fuskantar ta ta buɗe idanun ta sosai tamkar dai tana Ganin ta ,
Yakaka dagaske ne kina da cikin shege ? Zaki haifi yaro ba tare da kin yi aure ba irin na falta?
STORY CONTINUES BELOW
A hankali ta sauke hannun falmata daga kafaɗun ta , ta rike hannayen cikin hannun ta ,” tare da yin ƙasa ƙasa da muryar ta ,”
Bani da cikin shege falmata ƙarya madam take min so kawai take ta kore mu ,!
Ɗan jim falmata tayi cikin rashin gamsuwa ,! Kafin ta sake jefawa yakaka wata tambayar
To waye ne naji kin ce kina son shi dayawa ? Waye shi ?
Kallon fuskar falmatan tayi a ɗan hargitse tana jin wani yanayi cikin ran ta ,”
Bature kam silum ! ,”yakaka ta furta hakan a ƙasan maƙoshi.
Ɗan zaro idanu falmata tayi tamkar tana ganin ta ,”
Nduwodo bature kam silum ? Ndan shaa noum3 ? ( wanene bature kam silum aina kika san shi )
Kaam shaa banaangndi3 .’ ( mutumin da na taimakawa )
Chaaman shaa ra’amaa ? ( daman son shi kike ? )
Shii shaawa shaa rumiind3 tayd3zin zayyrod3 , ( yana da kyau baki gan shi ba ɗan gayu da shi )
Ɗan murmushi ne ya subucewa falmata wanda ya zarce zuwa dariya , cikin muryar dariyar ta ce
Har naji ya burge ni NIMA INA SON SHI!
Da wani irin yanayi mai daɗi yakaka ta jaa falmata cikin jikin ta tana jin yadda ƙaunar falmatan yake zagaya duk hanyoyin jinin ta , tun da daɗewa ta sani falmata mai taya ta son abun da take so ne kome lalacewar wannan abun shi yasa ƙaunar falmata ta fifita akan duk wata ƙauna da take zagaye jinin jikin ta !
Cikin satin ta ɗan samu sauƙin walakanci tare da bautawar da madam saly take yi mata saboda kullum cikin gilla mata ƙarya take akan uban cikin jikin ta yana nan tafe , wanda har yanzu ba wai ta yadda da cewa tana da cikin bane , neman hanyar da zata sa madam saly ta haƙura ta ƙƴale ta ta cigaba da zama gidan ta take , duk da cewa a halin yanzu duk ta yadda ta ci abu mai ƙarni ko yaya ne sai tayi aman sa wanda yake wahalshe ta sosai , sai kuma a wasu lokutan yawu ya kan ɗan taru mata a baki , bayan hakan babu wani alamun ciki da ya bayyana a gare ta wanda ita a ƙaramin sanin ta zai sa ta yadda tana da cikin ,”
Amma ba’a je ko ina ba madam saly ta farga da cewa ƙarya ce yakaka take gilla mata sumfiri-sumfiri wanda hakan ya fusata ta , ta shiga saukewa yakaka kwandunan bala’i da masifa gami da sanya ta aiki babu dare ba rana tana kuma sake tisa mata a kullum cewa gaf take da ta kore su ,2
Daga yakaka har falmata hankulan su a tashe yake akan tsangwamar da madam saly take yi musu , ita yakaka bata san wata hanya da zata bi ta nemo youssouf ba baya ga lambar wayar sa wacce ita kuma tun kwanaki biyar da suka wuce da madam saly ta turke ta ta sa ta kira lambar sa ƙwaya ɗaya jal da yake kiran ta da ita a lokacin da suke tare , sai dai kiran farko da tayi da ya shiga , har ta gama ƙara ba’a ɗauka ba , to tun daga sannan ko ta kira lambar bata tafiya , daga tayi alamun ta shiga sai ta katse , ga alama an datse hanyar shigar kiran daga computer.
Gaba ɗaya sun fara lalacewa kasantuwar su duk biyun ba ma’abota son tashin hankali bane daɗi da ƙarin tsoron madam saly da suke yi kamar me ,!
Allah Allah yakaka take yi samy baby ta dawo , ko zata ɗan samu sa’ida da wurin fakewa , bakin cikin ta ɗaya akan bacewar ƴar takaddar da samy baby ta zana mata lambar wayar rta bisa ,ta nemi ƴar takaddar ta rasa sama ko ƙasa babu , tafi zaton a tun ranar da ta bata ta yar ba tare da sani ba ,
a haka kwanaki suka tura , zuwa lokacin da lamura suka fara tsananta gare su , laulayi tuƙuru ya sako yakaka a gaba , kome ta ci amai take ,bata da abun so da kuma yake ƙwantar mata da hankali irin ƙamshin turaren youssouf da yake manne da jikin kuɗin sa na Niger da kuma agogon sa, duk dare da su take ƙwaƙume cikin zanen rufuwar ta , idan ba haka ba babu ita ba bacci , ɗan ƙaramin hoton fuskar sa ya zamar mata abu ɗebe kewa a duk lokacin da ta ji son sa ya mintsine ta !1
ga aikin da madam saly ta walle ta ce bata janyen shi daga kan ta a wai domin tana laulayin shegen cikin ta , a cewar ta ma ita ake ƙwara , kullum cikin zagi da aibata yakaka take da munanan kalamai iri-iri a duk lokacin da taji tana amai ,”
STORY CONTINUES BELOW
A halin yanzu duk wani mai shigowa cikin gidan ya san yakaka tayi ciki , ciki kuwa har da ƙawar ta da suka zo gari tare yagana , wacce tun daga lokacin da ta ji da kunnen ta yakaka tana da cikin shege , ta janye mata , magana ta kirki bata haɗa su , haka yakakar zata yi ta bin ta tana so ta bata dama suyi magana amma fir yagana ta juya mata baya taƙi kula ta , ɓaro-ɓaro take nuna ita fa kƴamar ta take yi , da har ta kai a wani yammaci ta gaggasawa yakakar magana ta kuma nemi da ta fice a harkar ta ita ba karuwa bace mai abun kunya irin ta ,”3
a ranar kusan raba dare yakaka tayi tana kuka a cikin zanin rufuwar ta bisa teburin kwanan ta , ji take gaba ɗaya ta muzanta domin a zuwa yanzu ta fara amincewa da tana ɗauke da cikin shege a jikin ta ,”
Sannu sannu rayuwa tayi wahala da tsanani ga yakaka da falmata , domin kuwa a halin yanzu haka suke wuni jibge a gefen ɗakunan gidan cikin yunwa da ƙishirwa , saboda yakaka bata iya yin aikin dalilin rashin lafiya , amai da take ta faman yi ya ƙarar da ruwan jikin ta ga kuma ba abincin kirki wanda hakan ya sa gaba ɗaya jikin ta ya shika yayi yaushi idanun ta har kore-kore suke , babu mai kula ta sai ƙanwar ta wacce ita ma yawan tashi ta zo wurin yakaka idan taji tana amai ko kuma idan tana buƙatar ruwan da take shan sa take dawo da shi , ko kuma ta kawo mata abincin ta da ba iya ci take ba , wannan zirga-zirgar da take yi ya jaa madam saly tace ta dakatar da ita daga yi mata wanke wanken da take yi a cewar ta baza ta yadda falmata ta dunga gwamutsa mata aikin wanke wanke da wankin amai ba ,” ta maye guraben su da wasu fallallun ƴan mata biyu , a cewar ta tun da sun zame mata ƙarfan ƙafa , baza su bar gidan ba to su nemi abincin su wurin kwana kuwa su tsaya daga tsakar gidan zuwa cikin rumfa ,”
Da hakan suka amince domin kuwa basu da wata mafaka bayan nan ɗin yini suke bin inuwar gaban ɗakuna da baccon kayan su da shi ma aka wurgo musu abun su kan su ,
babu mai lura da su , sai idan falmata taji yunwa na neman galabaitar da su ta daidaici lokacin kammala cin abinci ta lallaɓa zuwa bakin makwarari inda take ɗan tattaro musu guntattakin abinci da ƙanzo-ƙanzo da a yawan lokuta ita ɗaya take ci domin yakaka ko son kallon abincin bata yi bare ta kai ga ci ,”
Idan dare yayi kuma su koma cikin rumfa su kwana bisa tebura.
Falmata ta so ta fara fita bara sai dai rashin ɗan jagora ya hana ta , tayi yunƙurin neman taimakon yagana akan ta dunga kai ta bakin hanya wurin barar ta amma sai yakaka ta hana ta yiwa yaganar magana ,”
a cikin wannan halin na tsanani suka shafe fiye da sati uku suna watangaririya cikin rashin galihu , tare da yunwa da kirshirwa ,
kwatsam rana ɗaya sai ga samy baby ta dawo bayan ta shafe kusan watanni biyu da ƴan kai bata nan , nan ta tarar da yakaka cikin mummunan yanayin mutu Kwakwai rai kwakwai , ba shiri ta kwashe su zuwa wani ɗan jeka na yi kan asibiti mai zaman kan sa ,”1
Nan aka shiga bata taimakon gaggawa , har jini aka ƙara mata leda ɗaya bayan ruwa da tarin allurai da ta sha ,
Ba ƙaramin faɗa likitan yayi ba da yadda aka bar yarinya ƙarama da ciki jikin ta cikin irin wannan mummunan yanayi , har ma ya nemi da ya ga mijin ta domin su gargaɗe shi
sororo samy baby tayi tana kallon likitan , kafin ta buɗe baki tace
ciki fa likita ? Waye ke da cikin ?
Ita marar lafiyar da kika kawo/ƙanwar ta ki
kina nufin baki san tana ɗauke da ciki ba har na tsawon sati goma sha biyar da kwanaki shidda ? ?
Goge gumin da ya tsatsafo mata a goshi tayi ,”
Ban sani ba likita kasan bama tare jiya na dawo daga tafiƴa , ta furta hakan cikin rashim sanin takamaimai amsar bayarwa , cikin sanyin jiki ta miƙe ta fito daga ofishin likitan bayan ya sake jaddada mata lalle ta nemo mijin yakaka !
wai yaks ke da cikin??har na tsawon watanni kusan huɗu , wannan wanne irin ɓata wasa ne yaks take son yi masu ? Ita da ta je abuja ta ga yadda alhazan birni ke rububin ƙananun ƴan mata irin yaks , har tayi mata sha’awar samun irin wannan damar ta dawo da niyyar ta sake wanke ta ta shigar da ita aJi na musamman ta samu ilmin bariki yadda zata ci ribar sa su wuce abuja tare ,”1
STORY CONTINUES BELOW
ta huce takaicin duniya “, hatta waɗanda suka raɓe ta ma su huta , amma shi ne dan rashin sa”a zata zauna da ciki a jikin ta har tsawon wannan lokacin , waye ya gaya mata ana haɗa harkar bariki da jego da rainon ƴaƴa ?
Ya zama dole a fidda cikin nan muddin tana so tafiyar ta tayi kyau !
BAYAN SATI ƊAYA .
Jikin yakaka yayi kyau ta murmure babu laifi duk da cewa shi laulayi bashi da wani magani takamaimai amma dai ta samu farfaɗowa daga halin galabaitar da ta shiga , sai ɗan abun da ba’a rasa ba na daga larurar masu ɗauke da ƙaramin ciki , kamar kasala , tashin zuciya , yawu da sauran su .
dan haka yau likitan ke sallamar ta bayan ya kafa mata dokokin kula da kan ta da lafiyar jaririn cikin ta , ya kuma sake jaddada mata da ta fara zuwa awu cikin wata mai kamawa ,”
Yakaka wacce zuwa yanzu ta amince tabbas tana ɗauke da ciki a jikin ta domin kuwa ga cikin ya ɗan fara tasowa kuma kaɗan kaɗan tana ɗan jin taurin sa yana dunƙulewa guri guda ,”
Cikin ladabi ta amsawa likitan tare da sake jero kalaman godiya tana mai satar kallon samy baby wacce tayi kicin-kicin da fuska ta ɗauke kai ,”
Cikin da za’a a markaɗe shi shine har ake jero ka’idojin kula da shi ? Ai suna komawa gida gobe zasu shirya ta kai yakaka a fidda mata wannan alaƙaƙai ɗin , abun da ma yasa bata fitar da nufin ta anan ba saboda ana iya chafke su idan aka ji nufin su ,”
Kai tsaye ɗakin samy baby suka wuce , bayan isar su gida , nan ta shige banɗaki domin watsa ruwa ta bar su a raƙube daga bakin kofar ɗakin , sun yi shiru basa cewa juna ƙala kowacce tana saurarar zuciyar ta , fargabar su ɗaya hukuncin da itama samy baby zata iya aiwatarwa akan su . Ko ita ma korar ta su zata yi kamar madam saly ?
Bayan ta gama wankan ta , ta shafa mai ta shirya ta zo ta zauna ta tisa su a gaba ,
Falmata ɗan bamu waje zan yi magana da yayar ki ,”
Toh anty ,
da lalube ta ƙarasa ficewa daga ɗakin ta fice chan farfajiyar gidan ta tsugunna daga jikin bango .
Yakaka ashe har rashin wayon ki ya kai ki zauna da ciki tsawon wannan lokacin a jikin ki ba tare da kin ɗau matakin rabuwa da shi ba ? Kin kuwa san barazanar hakan ga rayuwar ki cikin wannan halin da kuke ciki ke da ƴar uwar ki ?
Anty kiyi hakuri nima ban san yaya zan yi ba ,” ta furta hakan tana me share ƙwallar da ta silalo bisa kumatun ta ,”
To wai ma ba na kai ki an miki allurar hana ɗaukar ciki ba ?
Kin kaini anty , kiyi hakuri !
Mts kome dai aka yi da jaki sai ya ci kara ,!
yanzu sai ki shirya gobe mu je a fidda cikin nan daga jikin ki ,”dan bazai yiwu ki zauna tare da shi ba1
Ɗas Ɗas Ɗas zuciyar ta ta buga ,”
A jirkice ta ɗago kan ta dake sunkuye ta dubi samy baby da raunanan idanun ta cikin sanyin murya tace
A kai shi ina anty ?
Galala samy baby ta dube ta
a kai shi ina kike tambaya ta ? a subda shi a kwata ya bi makwarari toh meye amfanin sa ?
Shiru tayi tana jin yadda zuciyar ta take faman bugu da wani irin tsananin tsoro da ya kama ta makamanci da na mutumin da ake shirin raba sa da gudan jinin sa .
wannan cikin bashi da wani amfani a wurin ki illa ya jefa ki a wahala tare da ƙuncin rayuwa , kin dai ga kaɗan ɗin sa yadda ta faru da ku a wajen madam saly , to wannan kaɗan ne akan irin wahalar da zaki iya faɗawa muddin kika cigaba da barin cikin nan a jikin ki , ranar babbar nadamar ki da shiga tashin hankalin ki kuwa shine ranar da abun da yake cikin nan naki zai fito duniya ,toh kiyi yaya da shi ? Ki kai shi ina ? Ki raine shi da me ? Ki kula da rayuwar sa da me ? Idan ya girma ya tambayi ina uban sa ki ce da shi me ? Amsar ita ce babu !
STORY CONTINUES BELOW
ke da kan ki yaks kina buƙatar matallafi wanda zai ɗago ki ki tsaya da kafafun ki kema ki taimaki ƴar uwar ki miskiniya , ki tuna baku da kowa baku da kome baku da wurin zuwa baku san kowa ba , kowan ku sun ƙare ,”
mts ta jaa tsaki ni bata lokaci na Ma nake a wofi , ke da na zauna ina faɗawa waɗannan kalaman kin fini masaniya akan su saboda kai tsaye ke suka shafa ,’
Abu na karshe da ni zan faɗa miki shine idan har kika amince muka je aka raba ki da cikin nan ni kuma na miki alƙawarin zan tsaya miki ki shiga harkar bariki da karfin ki , ki ɗaukaka ki tumbatsa ,ki kai gaci , domin garin abuja zamu wuce kina gama warwarewa ,1
idan kuwa har kika nuna ƙin amincewa kamar yadda na hango alamun hakan akan fuskar ki , to ni na janye hannu na akan lamarin ki , ki nemi wurin da zaki baiwa kan ki tare da cikin jikin ki zuwa kan ƙanwar ki mafaka , ni da kike gani ma bazan wuce sati mai zuwa ba zan sake barin gari , ban kuma san ranar dawowa ta ba ,” dan haka zaɓi ya rage gare ki yaks ,! Kiyi tunani daga yanzu zuwa gobe
Daga haka ta ɓalle jakar ta ta fidda naira dubu biyu ta miƙawa yakaka ,’
ni zan fita ga wannan ku ci abincin rana da dare ke da ƙanwar ki , ni sai gobe zan dawo , ku kula min da ɗaki na akwai muhimman kaya na a ciki ,!
Daga haka ta kaɗa kan ta tana mai barin ɗakin , sautin ƙarar cumgum ɗin bakin ta tare da sauran kalaman da ta furta suna amsa kuwwa cikin kunnuwan yakaka ,”
To ita yanzu INA MAFITA ???
Tayi zurfi cikin tunani har bata san lokacin da falmata ta dawo ba , sai ji tayi tana ambaton sunan ta ,”
A sanyaye ta miƙa hannu ta riƙo hannun falmata ,” tana buƙatar mashawarci tana buƙatar a bata ƙwarin guiwa akan abun da ta ƙudurta cikin zuciyar ta , toh sai dai bata da abokin shawara bata da kowa a tare da ita sai falmata ƙanwar ta , dan haka a karo na farko tayi niyyar ta buɗe zuciyar ta ga falmata duk kuwa da ƙarancin shekarun ta amma bata da haufi akan kaifin hankali tare da tsinkaye irin na falmatan wanda halitta ce ko kuwa baiwa daga Allah .
falmata samy baby tace gobe zamu je a fidda min abun da yake ciki na ,! ta ɗora da warware mata duk yadda suka yi da samy baby da irin togaciyar da tayi mata na barin su da kan su idan har taƙi amincewa a fitar da cikin .
Shiru kowaccen su tayi ,”
Yakaka ki bari mu haihu mu zama mu uku muma ,!
Ta tsinkayo kalaman falmata da suka sanya ta ɗan murmusawa ,”kalmar mu haihu ta bayyana ƙauna ta gaskiya da take tsakanin su abun da ke cikin ta ba nata bane ita ɗaya nasu ne su biyu da ƴar uwar ta,”
falmata idan mun haihu aina zamu zauna da yaro jinjiri ? kuma da me zamu yi rainon yaron ?
Zamu ajiye shi cikin jikin mu ruwa da rana da sanyi da iska baza mu bari su cutar da shi ba , zan yi bara na samo kuɗi muyi rainon sa ,
Lokacin da falta tayi irin cikin ki naji mamar su bakura tana cewa Allah ya sa kar ta zubar da cikin ta kashe yaron babu kyau babban zunubi ne ,”
Idan muka bar cikin nan kowa zai cigaba da tsanar mu , duk inda muka je za’a kore mu ,
muna da junan mu yakaka, kina da ni ina da ke , duk inda muke zamu kasance tare kafin abin da yake cikin ki ya fito mu zam mu uku , zamu haɗu mu zama rumfa agare shi har ya girma ,!1
Idan muka tafi wani garin da tace zata kai mu mun sake yin nisa da maman mu , watakila shikenan mun tafi baza mu dawo ba toh aina zamu ga maman mu ? Yakaka ban san ko kema kina jin irin abun da nake ji ba a kullum ji nake watarana zamu haɗu da maman mu tana nan bata mutu ba ,!
kar mu bar garin nan yakaka !
STORY CONTINUES BELOW
Amma ya zama dole mu bar gidan nan falmata !
Mu tafi ina ?
Koma ina ne zamu tafi falmata .
Toh yakaka shikenan ,!
Shiru ya ratsa tsakani a hankali yakaka ta zame gami da kwanciya rigingine tana mai sake zufafa cikin tunani ,
Tun ranar da ta fahimci cewa tabbas fa tana ɗauke da ciki a jikin ta , taji wani ƙaƙƙarfar so da ƙaunar aɓun da yake cikim nata yana huda zuciyar ta yana ƙaruwa a duk wayewar garin duniya ,” ƙaunar sa tana sake ninkuwa idan ta tuno fa bature kam silum shine baban abun da yake cikin ta , wani farin ciki take ji a duk lokacin da ta tuno zata haifi ɗa mai irin kamannin sa ,watakila ma ya gado mahaifin sa wurin gayu da ƙwalisa , a jikin ta take ji watarana zai dawo gare ta , zata nuna masa ɗan sa ko ƴar sa , ko ya ƙarba abun da ta haifa ko kar ya ƙarba ,wannan ba damuwar ta bace ba , kamar yadda falmata tace , zasu yi rainon abun da ta haifa da dukkanin ƙarfin su , zata haɗa shi da falmata ta zamto garkuwa a gare su , zata zamto musu inuwar da zasu tsaya a ƙarƙashin ta su fake zafin rana da dukan ruwan sama , zata kasance bangon da zasu jingina su huta a jikin sa , zata yi kome domin ganin rayuwar su ta inganta ,
Tamkar abun da yake cikin ta yaji irin tunanim da take , sai ya harba a karo na farko ya fara motsawa a cikin mahaifar ta alamun da yake nuna a yau an busa masa numfashi !5
a ɗan firgice ta kai hannun ta saitin inda taji motsin sa tayi kasaƙe tana son sake ji , ai kuwa sai ta ji zil-zil ya sake motsawa da ɗan karfi ,”
Da sauri ta kamo hannun falmata wacce take taɗin zuci ,” ta ɗaga rigar ta tare da ɗaura hannun saitin cikin ,”
Falmata kin ji abun da yake ciki na ya fara motsi ,”
da sauri falmata ta sake manna hannun ta lokaci guda tana washe gajejjerun haƙoran ta , ta ina ne inda na ji ???? Suka dafe cikin tare
Sake yin ɗan ƙaramin motsi yayi , ai kuwa a tare suka saki ƴar sakakkiyar dariyar su ,tamkar masu gasa !
yaron mu INA SON KA , falmata ta furta hakan da sanyin murya
da tattausan murmushi yakaka take kallon ta ,”
NI KUMA INA SON KI FALMATA NA .
5:20am
Falmata falmata ,
yakaka ke tashin ta , jin an shiga sallar asubah ,’
tashi mu tafi lokacin tafiyar mu yayi !
toh yakaka ,
jakar baccon su ɗaya ta ɗaurawa falmatan a kai ita ma ta ɗau ɗayan bayan ta kullewa samy baby ɗakin ta ,tare da ajiye mukullin a ƙarƙashin shimfiɗar goge ƙafa da yake shimfiɗe bakin kofar ɗakin .
Da bin bango suka fita a gidan suka miƙa bakin hanya hannayen su sarƙe da na juna ,
a tsorace suke sosai akan hanyar babu kowa sai jifa jifa suke cin karo da mutane zasu masallaci , zuciyar yakaka sai bugu take da fargabar gamuwar ta da karnuka .
Da ikon Allah suka ƙaraso bakin babban titi , lokacin gari ya fara yin ɗan haske shaa ,’ Alfijir ya keto ,’ cikin nutsuwa suka tsallaka titin , yakaka tana mai waiwayawa kallon kwarin unguwar a ran ta tana jin har abada baza ta sake tako kafafun ta cikin unguwar ba !
.
A cikin rumfar bakin wani shagon da yake jikin kasuwa suka yada zango , yakaka wacce ta gaji tilis da ƴar tafiyar da suka yi sakamakon rashin ƙarfin jiki , ta kwanta a dandaryar sumintin gaban shagon gami da yin matashi da baccon ta , falmata kuma ta zame ta zauna daga jikin bango ,”
Falmata ke zan ajiye ki wurin barar ki na da idan an fito kasuwa ni kuma zan ɗan kewaya na nemi wani ɗan aiki , ko dako ne ma nima nayi na ɗan samo mana wani abu kafin mu ga yadda Allah zai yi da mu koh ?
hakane yakaka , amma ke ki zauna kawai kin san fa baki da isasshiyar lafiya kar ki je kiyi aiki kuma ki cutar da kan ki da yaron mu ,!
bazan yi aikin wahala ba daidai karfi na zan yi falmata .
Toh shikenan yakaka .
Suna nan zaune gari ya waye tangarai mutane suka fara kai kawo masu sana’ar safe suka fara hada-hada gasu nan iri-iri, nan yakaka ta hango wata mai sayar da ƙosai da fanke wanda ƙamshin suyar ta ya bugi hancin yakakar , nan take ranta ya biya ,”
falmata ga masu abin karyawa sun fara mai zan karɓo mana ?
ki sayo mana duk abun da ran ki yake so yakaka !
to ki kula mana da jakar kayan mu sosai .
Toh
Ƙosai ta saya tare da fanke , ta ƙarasa wurin wata mai sayar sa koko ta sayo masu , har zata wuce ta ga mai masa nan ma ta tsaya ta saya ,” tace a zuba mata yajin ƙuli ya ji sosai ,” nan aka baɗe mata kan masar da yajin ƙuli,”
Nan suka zauna suka ci suka gyatse , falmata ta sha ruwa daga randar da take daura da rumfar da suke, yakaka tace ita baza ta sha ruwa yanzu ba domin tana sha amai zata yi ,
anan suka cigaba da zama suna ƴar hirar su jifa-jifa har zuwa tara na safe lokacin da ƴan kasuwa suka fara fitowa ,”
mutumin da yake mamallakin shagon da suka yada zango bakin sa , shi ma ya fito ,
da kallo ya fara bin su da shi cikin shakku da rashin yadda musamman da ya ƙƴalla ido ya ga baccon kayan su ai sai ya jaa baya ,
lura da shi yakaka ta yi dan haka ta fara gaishe shi nan falmata ma ta fahimci akwai mutum a wurin ita ma ta fara miƙo tata gaisuwar amma maimakon ya amsa sai ta ga ya juya ya nufi wata ƴar hanyar da ta ratso tsakanin shaguna ya tafi ya bar su
Nan yakaka ta shaa jinin jikin ta ,”
Falmata kin ga wannan mutumin ƙila nan da muke zaune shagon sa ne , kuma muna gaishe shi naga ya tafi ya bar mu ” ko dai bai yadda da mu bane ? Tashi mu tafi kar ya ƙira mana hukuma a kama mu ., yakaka ta ƙarasa zancen tana miƙewa ,”
nan ita ma falmata ta miƙe ,
mu yi sauri mu tafi yakaka kar a kama mu !
Har sun fara tafiya suka ji an dakatar da su , ta hanyar daka musu tsawa tare da basu umarnin tsayawa ,”
Chak ! Suka tsaya zuciyoyim su na bugun lugude ,!