MAFARI CHAPTER 7 BY UMMU AZAMM

MAFARI CHAPTER 7 BY UMMU AZAMM

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Idan har kunnuwan su sun jiye musu daidai tabbas muryar samy baby suka ji ,” wayyo sun shiga uku , meye ya kawo samy baby gidan ? Kada dai ta san doctor hamza ? Watakila ma ƴar uwar su ce , tunanin hakan ya sa yakaka jin jiri na kwasar ta ,”+

Ya-yakaka ,”kamar muryar anti samy ta gidan madam ?” ,” falmata ta furta hakan muryar ta na ƴar rawa tare da jin fargaba na rufto mata ,”

Muryar samy baby a kurkusa da su da suka ji wacce basu san lokacin da har ta ƙaraso ba ta katse amsar da yakaka ke shirin bayarwa ,”

Ni ce ba kamar murya ta ba , ta zarce da tambayar su ,”

Ashe kuna garin ?

Yaks baki kyauta min ba , sai kawai ku haɗa kaya ku bar gidan babu bankwana ? Kika sa nayi ta bulayin neman ku har da farko na ɗaurawa madam saly laifi nace ita ta kore ku ashe ku kuka kori kan ku , sai daga baya na samu labari a bakin ƙawar ki wai daman kin ce mata zaku gudu kun gaji da aikin wahala ko ? Ina ku ka koma da zama yanzu ? Ina fatan inda kuka koma yanzun yafi inda kuka baro saukin rayuwa ? Ko da yake ma ai ga ku na gan ku shar da ku , meya kawo ku gidan nan ko biki kuka zo ?1

Muƙut !

Yakaka ta haɗiye wani busasshen yawun da yayi guntu a bakin ta , kafin ta tattaro ɗan guntun nutsuwar da ta rage mata ,”

Duk cikin dogon bayanin da samy baby tayi mata tambayar ƙarshe ta fi tada mata hankali ,” aina suke kuma me suka zo yi gidan ??? ,”

Anan-anan kurkusa muke anty samy kuma ,unn unn

Aiko mu aka yi nan gidan mu karbi saƙo ,

ta tsinkayi muryar falmata ta amsa tambayar ƙarshen ,” da ya sa yakaka ta saki wata boyayyar ajiyar zuci .

Sai dai me ? Muryar rahima ce ta ratsa wurin lokacin da take nufo su tana shirye tsaf cikin shirin zuwa party ,

Wow yakaka , fatima , kun gan ku kuwa ? Ɗanɗashi , haka kuka sha ƙunshi ? Ai da nasan har ƙunshi big bro zai kai ku ayi muku da na bi ku ,” kai amma ƙunshin nan ya haɗu , wannan ai ko na amarya bai fi naku kyaun zane ba , ta ƙarashe zancen tana kashe wa yakaka idon ta ɗaya ,”da hakan yake tamkar al’adar ta ce ,”

Murmushin yaƙe yakaka tayi ,tana mai satar kallon samy baby wacce take bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya da guntun murmushi akan fuskar ta ,”1

Da murmushi rahima ta dubi samy baby ,”

Sannu anty samira kuma baku tafi ba har yanzu ?

Bamu tafi ba rahima

Samy baby ta amsa mata a takaice ,

Yakaka baza ku je party bane ? Na ɗauka big bro zai wuce da ku ta chan ,?

A ah baza mu je ba rahima zamu shiga ciki mu taya su aiki sai kun dawo ,”

Yakaka ta bata amsa tana fatan ta wuce tayi tafiyar ta ,” yau ɗaya ta ji surutun rahima ya fara gundurar ta ,’ !

Ok sai mun dawo ,1

Cikin sauri yakaka da falmata suka ɗaga kafafun su suna barin wurin tun kafin samy baby ta farga ,” domun wata ƙawar su ta ƙaraso wurin ta janye hannun ta zuwa gefe suna ƙus-ƙus ɗin su ,”

Ta chan bayan ɗakunan gidan suka samu wuri suka zauna bisa takalman su a ƴar sassanyar inuwar yammaci ,”

Tab yakaka yau Allah ya rufa mana asiri kiris ya rage anti samy ta tona mana asiri , ai wallahi sam ban ji daɗin jin ta da nayi a gidan nan ba , ko me ya kawo ta kuma oho ?2

STORY CONTINUES BELOW

Ni har yanzu hankali na bai wani kwanta ba falmata , inaga kamar zata faɗa musu gaskiya akai na , watakila ma ƴan uwa ne ita da su rahima , “

Allah dai ya rufa mana asiri yakaka ,

Ameen !

ta amsa tare da rashin kuzari

Ba su suka fito daga maɓoyar su ba , sai da suka ga gari ya fara duhu , daga inda suke suna iya jiyo kiraye-kirayen sallar magariba , ga kuma hayaniyar da suke ji da ke nuni da cewa ƴan bikin ne suka dawo ,’ daga wurin party ,”

Da rakaɓe-rakaɓe suka bullo ta cikin gidan , iya ganin su mutane ne ko ta ina da alama an samu ƙaruwar wasu baƙin ,”

Suna tsaye daga gefen kofar falon suna shawarar su shiga ko su koma maɓoyar ta su kawai su kwana a chan , tun da sun san dai ko sun shiga falon basu da takamaimai wurin kwana ,” !

Yauwa , fatima , yakaka tun ɗazu nake neman ku , gaskiya kun wahalar da ni kusan ba ɗakin da ban duba ba a sashin mu , ina kuka shiga haka ?ko kun fita ne ? Cewar rahima wacce take ƙarasowa wurin su .1

Muna daga nan bayan ɗakuna rahima , kiyi hakuri bamu san kina neman mu ba ,! Har kun dawo ?

Mun dawo , daman big bro ne ya ce duk inda kuke na neme ku , kun ci abinci ne ?

Yakaka ta girgiza mata kai ,” bamu ci ba ,”

Yauwaa toh ku zo muje ciki ga abincin ku chan na sa an ɗibar muku,!

Ta cikin falon suka shiga suna biye da ita , suka nufi ƴar hanyar nan da ta hau sama ,” suka bi ta ƙafar benen suka haura cikin wani babban falo wanda ya ƙawatu da kayan alatu , da manyan kujeru da tsadaddun labulaye , ga ƙofofi birjik a cikin sa ,”

Nan ɗin ma dai duk tawagar ƴan matan ne wanda ga alama sun yi ƙaura daga ƙasan ne sun dawo saman ,”

Dararrakin su da shewa sun cika wurin banda ɗan wani sassanya sauti da yake tashi a cikin falon ta cikin wasu mulmulallun sifika da suke a kowacce kusurwa na falon ,”1

Daga bakin kofa su yakaka suka jaa tunga, rahima ta kutsa kan ta ciki ba tare da ta lura da sun dakata daga bin ta ba ,”

Kai tsaye ta nufi wata ƴar hanya sai ga ta ta bullo cikin ɗan Kitchenette ɗin duk da cewa babu wasu tarkace a ciki , amma Kitchen Cabinet ɗin kan sa abun kallo ne , kwarai Kitchenette ɗin yana da ɗaukar hankali , kamar yadda kome na sashin yake da mataukar tsari da kyau , fiye da na ko’ina a gidan , kai tsaye ta ɗauko ƴan madaidaitan coolers ɗin biyu ta fito da su ,’

“, turis ta jaa ta tsaya lokacin da ta lura babu su yakaka a wurin ,”

Ina suke ??”,

ta furta a sarari .

Su waye ?

Hafsa ta tambaye ta daidai lokacin da ta kai hannu tana ƙoƙarin karɓar cooler ɗin hannun ta ,”

Ta janye tana bata amsa da ,”

su yakaka da fatima tare da su fa muka hawo saman , wannan ma abincin su ne da big bro yace na ɗebo musu tun ɗazu ,”

Yamutsa fuska hafsa tayi ,”

Su waye kuma fatima ? Ita har ga Allah ta ma manta da sunayen su takamaimai ,”

C’mon bani abinci naci daman yunwa nake ji tun breakfast wani abun kirki bai sake shiga ciki na ba, “

nima wallahi yunwar nake ji cewar wata daga cikin ƙawayen su da take kishingiɗe a gefe ,”

Ƙanƙance idanu rahima tayi ,

Ki rufa min asiri malama kar ki jawo min fushin big bro , domin sai da ya daɗa jaddadamin na basu abinci…

Kewaye su tayi ta wuce

Bata saurari hafsa ɗin ba da take bin ta da tambayar

Wai su waye ne waɗan da kike ta ambato ,”

Leƙawa tayi ta gan su a rakuɓe daga gefe ,”

Haa’ah ya kuka tsaya anan yakaka ?

Ku shigo mana ga abincin naku ,!

Toh !

Suka amsa suna masu sanyo kafafun su cikin falon ,”

A ɗage hafsa take jifan su da kallon tuhuma ,”kallon ku kuma me kuka zo yi nan ??

Ku zauna ,’ rahima ta umarce su tana musu nuni da kan haɗaɗɗiyar shimfiɗar dardumar da take shimfiɗe tsakanin kujerun gurin ,’

STORY CONTINUES BELOW

A ɗarare suka zauna falmata ta matsu da jikin yakaka a saboda ji da take idanu sun yi yawa a wurin ,”

Yakaka ma kan ta a sunkuye yake saboda kallon banzan da sofi take jifan ta da shi a tun ƙarasowar su falon ,”

Ba tare da karsashi ba suke chakalar abincin duk kuwa da uwar yunwar da taje sasuƙar ƴan hanjin su da kuma yadda abincin yake da matuƙar daɗi ya wadatu da kayan girki na alfarma ,” amma idanun jama’ah ya musu shamaƙi da jin dadin abincin ,

Ƙarar wayar rahima ita ta dawo da sofi duniyar tunanin da ta lula na son hasaso meye ne a tsakanin doctor hamza da waɗannan yakubayin talakawan ƴan gudun hijirar da har yayi musu matsauki a cikin gidan su ya kuma jiɓanci lamuran su da matukar muhimmanci haka ?? ,”

Hello big bro ,”

Gasu nan muna tare ma ,” cin abinci suke ,”

Rahimar ta kai kallon ta ga yakaka wacce kan ta yake sunkuye ,”

Eh tana ci sosai ma ,” to idan sun gama zamu zo yanzu ,”toh !

Yakaka wai inji yayan mu idan kun gama cin abincin muje yana ƙiran ku ,”

Toh suka haɗa baki wurin amsa mata ,”

Ba’a kai mintuna uku ba falmata ta zare hannun ta tare da faɗin ta ƙoshi , ita kuwa yakaka daman ba wani na kirki take ci ba ,” dan haka ita ma ta miƙe bayan ta tattare ɗan abincin da falmata ta zubar ,”

Ƙarƙashin rakiyar kallon rainin da mafi akasarin ƴan matan wurin ke bin su da shi suka ƙarasa barin falon suna jin su wasai tamkar an cire musu wani mugun dafi da idanun jama’ar suka zuba musu ,” daga yakaka har falmatan ba masu son mutane bane ,”

rahima ta jagorance su zuwa wurin da doctor hamza ya ce su same shi ,” daga kusa da kofar sashin sa ,”

Tun kafin su ƙaraso ya nacewa kallon fuskar ta , da ita kuma ta shagaltu da kallon haɗaɗɗun motocin da suka cika harabar gidan wannan tana wace waccen a haɗuwa ,”,

Suna ƙarasowa suka gaishe da shi , ya amsa tare da haɗa musu da tambayar babu dai wata matsala ko ? Kuma sun ci abinci sosai ko ? Suka tabbatar masa da basu da matsalar kome sannan a ƙoshe suke ,”

Manyan ledojin da aka zubo musu kayayayyakin su da ya saya musu na fitar bikin ya miƙa wa rahima , gami da wata madaidaiciyar leda mai ɗauke da tambarin ‘, down town, “

Ungo rahima wannan kayan nasu ne na fitar biki , ki dunga taya su shiryawa ,

Ta sanya hannuwan ta biyu ta karɓa tana ƴar dariya ,”

Eyeeh gobe su fatima za’a chanchare gaskiya fatima kin kwace min fada wurin big bro ,” ta ƙarasa zancen da sigar zolaya , tana kashe idon ta ɗaya ,”

Ɗan murmushi su duk biyun suka yi cikin ran su suna jin daɗin kulawar da yake basu tare da kyautatawa , hakan ke ƙara sa yana sake girma da ƙima a idon su ,”

Ba tare da ya kula da zantukan ta ba yace ,”

Ga shi

tare da miƙa mata ƴan mukullayen sashin sa , daga yau zuwa lokacin da za’a kammala bikin ku dunga kwana ke da su a sashi ne , daga ke sai su , bance ki haɗo min gayyar ƙawayen ki su ɓata min waje ba , ki kiyaye ,”

Ya ƙarasa zancen da sigar gargaɗi fuskar sa babu alamun wasa ,”

Toh

Kai kuma aina zaka dunga kwana ?

Tare da baƙi a sashin baba ya amsa mata yana barin wajen ,” bayan ya basu umarnin su tafi su kwanta dare ya soma shiga ,”

Da zumuɗi rahima tayi gaba suka bi ta a baya ,

Tab lalle yakaka ku ƴan gatan big bro ne , baya fa son kowa ya shigar masa sashi , kana shiga zai fara korar ka kar ka kai masa datti , daga ka fita kuma sai yayi shara ya goge kujerun sa , bala’in tsafta ce da shi kamar mai aljanun tsafta ,” ta furta hakan daidai lokacin da ta sanya mukulli ta buɗe ƴar babbar kofar mashigar sashin nasa ,”

Suna sanya kafafun su ciki ,” kowaccen su tana gaskata kalaman rahima da ta ce yayan ta mai bala’in tsafta ne , saboda tuno haɗuwar su ta farko yadda ta kaya a tsakanin su , ta yadda ya fututtuke ya ci mutuncin su akan ƙazantar da falmata tayi masa a ofishin sa , wanda a lokacin da za’a faɗa musu doctor hamza mutumin kirki ne mai tausayi da kyautatawa irin yadda yake musu a yanzu zasu ce ,”ƙarya ne ,” to ashe aljannu tsafta ne da shi , kamar yadda suka ji daga bakin ƙanwar sa ,”1

STORY CONTINUES BELOW

Ƙamshin furanni tare da sanyin ban ruwa da aka yi a wurin zuwa wani ƙamshi na musamman da yake tashi a ƴar harabar sashin nasa suka haɗu suka bayar da wani irin yanayi mai daɗi tare da samar da nutsuwa ga zukata , “

Lumshe idanun ta yakaka tayi ta buɗe tana mai yawo da idanun ta a kowanne kusurwa ta wurin , ƙwarai yanayin wajen da tsarin sa suka burge ta ,”

Ƴar barandar da take ɗauke da ƙofar falon nasa rahima ta taka ta buɗe kofar tare da tura ta ta sanya kai tana cewa su yakaka ,” su shigo ,”

Sanyi da kalolin ƙamshin da ɗakin yake suka sa falmata sakin wani gauron numfashi da tun shigowar su sashin take ta jaan iska ta hancin ta tana jin wata nutsuwa ta musamman na ratsa ta ,” tsafta tayi a rayuwa ,”

Cikin shauƙin yakaka ta dunga bin falon da kallo ɗan madaidaicin falon da baya ɗauke da duk wani nau’in tarkace , kome ka gani a falon amfanin sa mai muhimmanci ne kuma yana bigiren da ya dace ,

Tun daga kan ƴan madaidaitan kujerun da suka kewaye falon tare da lallausan kafet har zuwa kan labulayen duk suna ɗauke da launi guda ne ,”ruwan madara ,” sai gefe guda kuma girkakken gogaggen teburin katako ne shima ruwan madarar da ƴar kujerar sa wanda aka ajiye wata ƴar computer tare da tulin littatafai akan sa ,” daga ɗaya sashin kuma ƙaramin firiji ne ,’ daga haka babu kome a cikin falon sai sanyin AC da yake daga jikin bangon ɗakin sai kuma ƙamshin mai ɗakin da ya riga ya kama ko’ina na wajen ,”

A ƙasa suka zauna daga su har rahimar da take ta basu labarin party da suka halarta yau , ” lokacin da take zazzage kayan da suke cikin leda ta ɗora da basu labarin , bikin da za’a yi na gobe har sai ya fi na yau haɗuwa da yin kyau domin a na goben har da tawagar ango da abokai/dangin sa waɗanda zasu iso a gobe da safe ,’

Woww wayyo Allah yakaka wanɗannan ɗanɗasa ɗanɗasan rigunan dan Allah aina big bro ya sayo muku ,? Wayyo Allah ,”

Haƙoran ta a buɗe falmata ta fara bata labarin shagon da suka je ,’ a ƙarshe ta zame ɗankwalin ta , baki siɗik ɗin gashin ta mai cika da tsawo tare da ƙauri ya bayyana ,”

Kin ga ma har kai sai da aka wanke mana ,” ta ɗora da tambayar kin ga takalman da ya saya mana koh ? Su ma masu kyau amma ni dai kamar bazan iya sawa ba dana gwada Su naji sun min tudu ,”

haba ! zaki iya sawa mana fatima , kuma wallahi ba ƙaramin kyau zaki yi ba ,

Wanne ne naki yakaka , wanne ne na fatima ,?

Ware mata su tayi

Rahimar ta cigaba da santin kyaun kayan , a ƙarshe tayi alƙawarin taya su ƙwalliya tare da shiryawa ,” inda har ta zaɓar musu waɗannan dogayen rigunan a matsayin kayan da zasu sa a gobe da yamma dai-dai lokacin da za’a fara gudanar da wushe-wushe a ɗora da sanya lalle ,”

ɗaya ledar ta jawo ta cire musu shawarman da take ciki naɗi uku kowacce ta ɗau ɗaya suƙa fara ci suna ƴar hirar su , har zuwa Lokacin da bacci ya ɗauke su ,”!

********

Misalin sha ɗaya na daren Alhamis biyamuradi youssouf ya samu shigowa cikin gari ƙarƙashin umarni da ya samu daga babbar headquarter su dake chan niemey inda aka bashi awanni arba’in da takwas akan ya je yayi uzurin da ya taso masa na gaugawa kamar yadda ya shida musu ya dawo ,”

Shi ya tuƙo kan sa ya keto dazuzzukan da suke da matuƙar hatsari saboda ƴan tawayen boko haram da suka yi bigire a cikin sa ,”

À daren ya so yaje ya gan ta har ma su tattuna cikin awanni arba’in ɗin da yake da damar su yake sa ran zai iya fara gyara ɓarnar da ya tafka ,wanda idan ya samu haɗin kan yarinyar ya na san ran zai wanke hakkin ta da ya ɗauka ya cigaba da istigfari , sai dai yadda garin ya ɗau shiru ya sanya shi barin tafiyar zuwa gobe da safe , ta yadda ko da bai same ta ba kai tsaye zai iya samun abokan hulɗar ta wanda su kuma kai tsaye zasu sada shi da ita ba tare da wata wahala ba ,

STORY CONTINUES BELOW

Da wannan tunanin ya samarwa da kan sa wurin kwana a hotel ɗin da ya saba zama a lokacin da yake sintirin a garin ,!1

*******

Tsabar jin daɗin bacci su yakaka ba su suka farka ba sai ƙarfe takwas da ƴan mintoci , hanzari yin sallah suka yi suna dariyar makarar su ,

duk yadda rahima ta so da suyi wanka a banɗakin dake cikin ɗakin nasa , ƙin shiga ɗakin suka yi , yakaka ta turje tace iyakar su falo nan inda suka kwana baza su shiga masa har uwarɗaki ba ,”cikin zuciyar ta tana gargaɗin kan ta akan su kiyaye zarmewa da yawa ,”

A gurguje rahima ta kintsa masa falon yakaka tana taya ta , suka kintsa falon tsaf tamkar yadda suka same shi ,rahima tayi musu umarnin da su bar kayayyakin nasu a ɗakin tun da nan ɗin yau ma zasu kwana ,!

Tana sanya mukulli tana rufe kofar falon nasa ƙiran sa ya shigo wayar ta ,”

Big bro ina kwana ,?

lafiya rahima ,kun tashi ne ?

Mun tashi big bro, ” Gamu nan ma muna shirin fitowa ina rufe ƙofar falo ne ,”

Ki bar ƙofar a buɗe gani nan zuwa ku jira ni ,”

Toh

tace tana sauƙe wayar daga kunnen ta ,”

A shiryen sa yake tsaf cikin ƙananun kayan da suka amshi matsakaicin jikin sa ,” fuskar sa babu walwala sosai bayan ya amsa gaisuwar da suke mishi yace ,”

Ina zaku fita ku je da wuri haka ? Ku koma ku zauna a ciki har zuwa lokacin da za’a kammala abun breakfast sai rahima ta karbo muku ,”

Ba wani wuri zamu ba yaya dakta zamu shiga ciki ne , ko da aiki mu taya su ,” …

Ke da ba isasshiyar lafiya ce da ke ba shine zaki yi aiki ? Akwai masu aiki , ki kula da lafiyar ki ,’ ku koma ciki ku zauna ban yadda ku fita daga nan ba ,’ !

Big bro amma ni zan iya shiga ciki ko ? Saboda ka ga….

Sarkin surutu ke zaki iya tafiyar ki , amma ki bar musu mukullin a hannun su , idan anyi girki ki kawo musu , ban yadda ki ɗebo gayyar ƙawayen ki ba , ki kiyaye .

Toh big bro ta amsa tana jiran ta ji ya jerowa su yakaka sharuɗan kula masa da ɗakin sa , ga mamakin ta sai gani tayi ya juya yayi tafiyar sa ,1

Da sassarfa ya isa ga motar sa ya buɗe ya shiga ya jaa yana mai barin harabar gidan ya nufi gidan da mahaifiyar sa tayi matsuguni cikin sa , zuciyar sa sam sam babu daɗi ,saboda saƙon da yake ɗauke da shi akan harshen sa zuwa ga mahaifiyar ta sa ba mai daɗi bane

Ya rasa mai ya sauyawa mahaifin su ra’ayi bayan wahalar da ya sha kwana da kwanaki ,wurin roƙon sa akan ya amince mahaifiyar su ta tako gidan ayi bikin zainab ɗin tare da ita , da kyar ya samu nasarar shawo kan sa ya amince da ta zo tayi kwana biyu a kammala biki ta koma , sai dai a daren jiya ya sake birkice masa akan rashin amincewar zuwan ta gidan har ma yayi ikirarin idan har ya samu labarin ta zo zai mummunan saɓa mata ,

Fir yaƙi saurarar sa yaƙi yadda da duk wasu kalaman rarrashi da yake nufin yi masa ,’ yasan mahaifiyar su mai tarin laifuka ce , amma ƙwarai yadda mahaifin su yake nisanta su da ita yana matuƙar damun sa kome lalacewar uwa uwa ce ,”ba’a sauyawa tuwo suna ,”

Da wannan tunanin ya ƙaraso unguwar gami da karya kan motar sa ya gangara , kamar yadda yake a koyaushe unguwar cike take da yara ƙanana suna ta dawurwura a kan hanya , wasun su ko wondo babu , bare takalmi a kafafun su , batun wanka daman babu shi ,” hakan ya sa yake tuƙa motar sannu a hankali yana sakin hon lokaci -lokaci saboda yaran da suke ƙaraƙaina , basa ko tsoron mota ,”

A ƙarƙashin ran sa kuwa har yau bai daina mamaki da son sanin dalilin da ya sa mahaifiyar su zaɓar rayuwar da take yi a wannan ƙazamtatciyar unguwar marar fasali ba , iyakar tunanin sa da tambayoyin da ya sha yi musu daga ita har abban su an rasa mai bashi amsa takamaimai , “

STORY CONTINUES BELOW

sai dai yasan koma menene ya faru ne bayan tafiyar sa makarantar gaba da primary ta gwamnatin tarayya ta kwana ,inda bayan dawowar sa hutun zango na farko na aji ɗaya , ya tarar da baki ɗayan rayuwar gidan nasu ta sauya , na farko dai bai tarar da auntie su RAHIMA a gidan ba sai sabuwar RAHIMA jaririyar ƙanwar sa ya tarar ,’

abubuwa dayawa marasa daɗi ya tarar suna ta faruwa daki-daki wanda a ƙarshe ya jawo rabuwar auren iyayen nasu , da kawo karshen duk wata soyaƴyar da ya buɗi ido ya tarar iyayen su nayi wa junan su , hakan ya jefo mahaifiyar su cikin wannan rayuwar da take wanda yake jawo mata zagi da zargi tare da aibatawa daga dangin mahaifin su da shi kan sa ,,”

abun da hasashen sa yake bashi a koyaushe shine , koma menene ya jawo tarwatsewar rayuwar auren iyayen su yana da nasaba da auntie RAHIMA , wacce har zuwa yau da ake ɗiban shekaru wurin goma sha takwas babu wanda ya san ina take , a wane hali take cikin duniya ???2

Wani ƙaƙƙarfan hon da wata mota dake biye da shi ta sakar masa shi yasa ba shiri ya kauce ya bashi hanya da mugun gudu motar ta wuce ,”hilux”, ce baƙa mai ɗauke da baƙaƙen gilasan da ya sa ba’a iya hangen na cikin motar,”

Ɗan siririn tsaki hamza ya jaa yana aiyanawa a cikin ran sa wasu dai akwai su da wutar ciki ,

Parking yayi a gaban wani ɗan ƙaramin gida mai ƙaramar kofa dake ƙarshen layin ,” ya kulle motar sa ya taka ya hau kan ɗan dandamalin gaban gidan kafin ya leƙa da kan sa cikin ɗan siririn zauren ya rangaɗa sallama har baki uku lokacin da yake kallon agogon hannun sa da yake nuna karfe tara dai-dai na safe ,”

Karfe tara cif tayiwa biyamuradi youssouf a cikin rumfar madam saly , inda ya jaa ɗaya daga cikin kujerun wajen ya zauna ba tare da ya kula kowa ba , rarraba ido yake cikin nutsuwa yana neman fuskar ta a tsakanin fuskokin ƴan matan da suke ta kai kawo a gaban sa ,” suna cigaba da gyaggyara tare da goge kujeru zuwa kan teburan da suke cikin rumfar , domin ba’a riga an fara sayar da burkutu ba tukun ,

Karo na uku yagana ta ɗago kan ta tana sake kallon fuskar sa , tabbas shine wannan ɗan gayun balaraben mutumin da yakaka tace ɗan uwan ta ne ,”

Haɗa ido suka yi ta sakar masa murmushin da ke nuna alamun sanayya ,

Kallon ta yayi ya watsar gami da sake musƙutawa bayan ya daɗa ɗaure fuska tamau , cikin abun da bai fi mintuna biyar ba ya fara gundura da zaman , shi mutum ne wanda bai ƙaunar jira , yafi son daga ya buƙaci abu to ya samu ,”

Ajiye ɗan tsumman goge-gogen da yake hannun ta yagana tayi gami da nufo inda yake ,”

Sannu da zuwa malam.

Yi yayi kamar bai ji ta ba yana nacewa kallon ɗaya daga cikin sabbin ƴan aikin da madam saly ta maye gurbin su yakaka da su ,” farin ta ya jaa hankalin sa daga nesa yayi zaton ko wacce yake nema ce , sai da ta matso kusa ya fahimci ba ita bace domin wannan daga ganin ta ma hasken na bilicin ne ga fuskar tata wani wuri jaa wani wuri ruwan hoda wani gun kuwa brown ne ma , haka take dai dabbare-dabbare , ɗauke kan sa yayi dai-dai lokacin da ita kuma take farga da kallon da yake bin ta da shi nan take ta watsa masa signal da ido tana wani mokaɗe baki !

Gyara tsuyuwar ta yagana tayi ,”

Unm nace ka zo wurin yakaka ne ??

Maida hankalin sa yayi kan ta ji da yayi kamar ta ambaci sunan ta , sai dai matsalar shi bai wani riƙe sunan nata ba , amma tabbas kamar ya ji ta taɓa ambatar sunan ,”

STORY CONTINUES BELOW

Wata ɗiya nake nema , tana aiki anan doguwaa ce fara , tana da tsaga bisa ƙuncin ta , idan kin san ta ki sada ni da ita zan biya ki ,”

Karkaɗe jikin kayan ta yagana take lokacin da ta fahimci bayanin sa wanda yake sake tabbatar mata da zaton ta na ƙarya yakaka tayi mata da tace wai ɗan uwan su ne , domin ga shi ko sunan ta bai sani ba tabbas wata alaƙa ce ta daban a tsakanin su ,”

YAKAKA TAYI CIKIN SHEGE MADAM SALY TA KORE TA DAGA GIDAN NAN, BABU WANDA YA SAN INDA TAKE .1

Ta furta hakan lokacin da take gyara zaman rigar ta cikin halin ko in kula ,

Wani irin abu biyamuradi ya ji tsuwww yana yawo a cikin kan sa tare da kalaman da yarinyar nan ta furta masa ,” kusan bai ma fahimce ta sosai ba , dan haka ya saita idanun sa cikin nata tare da tattaro duk wata nutsuwa da yake da ita ya sake maimaita mata kalmomin da yayi amfani da su wurin tambayar ta ɗaya bayan ɗaya dalla-dallah kamar mai koya mata karatu ,”

Sake maimaita masa amsar tayi kamar farko ,” lokacin da take taka kafafun ta tana barin wurin , tare da turniƙin kishin da ya tattare mata a ƙahon zuci , saboda tashin hankalin da ta gani a fuskar sa baro-baro yana nuni ne da kowacce irin alaƙa ce a tsakanin sa da yakaka mai girma ce ta kuma taka wani matsayi mai muhimmanci a wurin sa , “2

tare suka zo maiduguri da yakaka amma a sarari yake bayyanuwa yakaka ta fita sa’ar shigowa garin ,’ tun akan wannan kyakkyawan ɗan gayun likitan da ya gigice a neman ta ta fahimci hakan ,” wannan mai kama da larabawan kuma ko menene alaƙar sa da yakakar oho ?? Ko ma menene ta sha alwashin sai ta rusa duk wani tubalin nasara a rayuwar yakaka ,”3

Wani irin yanayi na ruɗani ya shiga da tunanin sa yake kufce masa da hakan har ya sa bai ma san lokacin da yagana ta bar gaban sa ba ,” kalmar cikin shege kawai ita ke maimaituwa a ƙwaƙwalwar sa tana fasa kan ta tana sake dunƙulewa wuri guda tare da yin wajajjawa cikin tunanin sa ,” wani irin ƙugi cikin sa yayi da yake bayyana halin tsoro da ya shiga lokacin da tunanin sa ya tattaru wuri ɗaya ya chanko masa yarinyar tana ɗauke da cikin sa ne ba cikin shege ba ,”5

Kamar wanda aka tsikara ya miƙe tsaye akan kafafun sa yana wurga idanun sa kowanne lungu da saƙo yana neman yarinyar sai dai ko alamun ta bai gani ba kamar wacce ta ɓace ,

Wata irin damƙa ya kaiwa kafaɗun wannan koɗaɗɗiyar yarinyar da barin yagana wurin ya sanya ta tahowa gaban sa tana wata ƙwarƙwasa ,

Ƴar ƙara ta saki saboda yadda ƙasusuwan kafaɗar ta suka amsa da jin ruƙon soja ba da wasa ba ,” muryar sa ta tsinkayo da wani irin yanayi da amon ta yake bayyana tsantsar tashin hankalin sa ,”

Ke wacece madam saly ? Yi maza ki sada ni da ita a yanzu yanzu ,”

A tsorace take kallon sa har sai da ta firgita ganin yadda fuskar sa tayi jaa jijiyoyin kan sa suka fito tar kore-kore ,

Ma-ma-madam bata tashi….

Tsawar sa ta katse ta ,”

Ki gwada min inda take nace yanzu yanzu ,”

T-toh sake ni muje na kai ka wurin ta ,”

Wucewa tayi gaba ya bita , har zuwa cikin gidan ƙofar ɗakin madam saly , ta tsaya daga bakin kofar ,”

Madam ina kwana ? Kin yi baƙo ne yake son ganin ki ,”

Daga ciki ta amsa ,

Wanne ɗan»»» yake nema na da sassafen kamar naci bashin uwar sa ban biya ba to bill…..

Wata irin fincika ta ji anyi mata kafin ta fahimci meke shirin faruwa ta ji an watso ta waje daga ita sai wata ƴar guntuwar rigar baccin ta iyakar guiwa irin gumamar makkah ɗin nan , sillalliyar ƙeyar ta sai ɗaukar ido yake a hasken hantsi ,”

STORY CONTINUES BELOW

Kutuma….. Tace tana ɗago kan ta tare da miƙewa tsaye daga dunguren da tayi ,”

Arba tayi da biyamuradi youssouf , fuskar nan tasa yariman sa sak ,”

A take ta gane shi dan haka ta ƙanƙance ido ,’ !

Lalle toh sannu uban uba na da zaka zo ka wani figoni haka toh idan ma ita karuwar taka ce ta aiko ka kazo ka mun wannan rashin mutuncin toh daga ita har kai kun yi kaɗan aikin ban……

Marin da ya waske ta da shi ya hana ta cigaba da bayani sai ma ganin duhu duhu da ta fara , ba shiri tayi faɗuwar ƴan bori tare da sanya wani kakkarfan ihu ,”1

Ihun ta ya sa duk mutanen gidan rugowa da gudu zuwa wajen, Har da ɗan liti da shima yake sawo kan sa cikin gidan , ya ɗebo da gudu har yana bangaje yagana wacce ita kuma take komawa baya saɗaf-saɗaf bayan da ta leƙa ta ga mutumin nan ne tare da madam saly,”

Meke shirin faruwa ,ko kuwa ya faru ? da nake jiyo ihun giwar mata , ai wallahi ramar giwa kunyar daji , ace muna nan tare da ke kike sakin irin wannan ihun uwa wacce maciji ya sara ina macijin yake ??

Ya ƙarasa zancen yana bangazo larki ya faɗo tsakiyar filin

Daidai lokacin da youssouf ya ɗago kafaɗun madam saly tare da saita ƴar ƙaramar bindigar da ya fiddo daga aljihun wandon sa a kanta ,”

muryar sa a kausashe a tsaƙanin maƙoshin sa yace mata

Ina kin ka kaita ? Tana ina ? Duk inda take ki nemo ta ,

Wata irin zilliya ɗan liti yayi ya koma bayan hema ya ɓuya, yana cewa

Na shiga uku an fasa aure nah !2

Wata irin karkawar tsoro madam saly take ganin mutuwa kusa ,” laɓɓan ta suna rawa tace

Wallahi billahil azeem ka dai ji rantsuwar musulma kenan ko ? ba ni na kori yaks ba ita da kan dare ɗaya ta haɗa kayan su ita da ƙanwar ta suka bar gidan nan cikin dare babu wanda ya ga tafiyar su , ko jama’a ? ta maida tambayar ga mutanen da suke tsaye charko-charko an rasa mai cewa uffan a cikin su1

Sake danna mata bakin binɗigar yayi aka ,tamkar zai nitsar mata da shi cikin ƙoƙon kan ta yace ,”

Ƙarya kike ke kika kore ta kin san inda take , na baki awanni ishirin da huɗu ,zuwa gobe iwar haka ki tabbatar kin nemo ta idan ba haka ba kuwa sai na fasa ƙoƙon kan ki da harsashi , ya ƙarasa zancen da sakin ta ta faɗi ƙasa warwas ,”

Da sauri mutane suka dare suka buɗa masa hanya , a fusace ya wuce suka bishi da kallon tsoro ,”

Ihun madam saly ya dawo da hankulan su kan ta ,

Na shiga uku na lalace ni salaha ,wannan shigiyar yarinyar tsinanna ta zamar min annoba da masifa , ta bar gidan ma amma bala’in ta bai bar bibiya ta ba , wai ma wane ɗan …..uban ne ya faɗawa wannan mahaukacin farkan nata ni na kore ta??? Ta jefa tambayar saitin sa’a kerewa”sabuwar ƴar aikin ta da tayi masa jagora ,”

Da sauri ta ɗaga hannunwan ta biyu , ba ni bace sai dai ko yagana ce dan ita ce ta fara zuwa wajen sa suka yi magana ,”

Ina yaganar take ƴar …. Kira min ita , ai kuwa kafin cikar awanni ishirin da huɗun da ya ƙayyade dukkanin mu ba mu ga ta zama ba dole mu bazama neman ƴar** oh ni naga ta kaina , yaks ta sa raina cikin haɗari ! Billahi azeem yagana kin kusa barin gidan nan kema , ” yau naga masifa da idanuna ,!

, liti aina ma kace kana ganin su kwanaki ?

Suna chan a jefe a Bakin kasuwa !

Matsowa yayi kusa da ita yana cewa

Mtss amma madam saly kin ban kunya , yanzu akan ƴar wannan barazanar da kurtun ɗan sandan nan yayi miki duk kika bi kika ruɗe haka ?? Yo kina da kamar mu ko soja ya isa tsorata ki ne bare wani ƙurtun ɗan sanda wanda daga kin manna masa ɗari biyu jal kin saye shi , kai ɗari ma ta ishe sa , ai wallahi ki bar ni da shi bari awanni ishirin ɗin su cika ya dawo kiga yadda zan miki maganin sa ah to meye ɗan sanda ne fa ?……

Madam saly wacce tun da ya tsugunna a gefen ta ya fara magana take hararar bakin sa , bata san lokacin da zuciya ta ɗibe ta cire hannu ta bige bakin nasa ba da bayan hannun ta ,”

Wani tsalle ɗan liti yayi

Kutumelesi ,’saly fara,” meye haka ?? Zaki kumburan baki ki munanan halitta ?? Ai ba ni na kar zomon ba da zaki min haushin kaza huce akan dami ,” ya karasa zancen tare da rama harara da take masa ,”1

STORY CONTINUES BELOW

Wannan abun da na maka ko karkaɗar ƙura bai kai ba akan wanda kurtun ɗan sandan zai maka muddin ka bari kuka haɗu ,”

Ta miƙe tana cewa ni bari na shirya mu bazama neman shegiyar ,”

Sai kun dawo !

Yace yana ƙoƙarin barin wajen ,”

domin shi dai babu shi a zuwa neman waɗannan tabaɗaɗɗun a cewar sa,

*****

Duk yadda doctor hamza yake zaton mahaifiyar su zata ɗau lamarin hana ta zuwa wurin bikin zainab , abun ya wuce nan domin kuwa faɗa ta dunga yi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba , wanda tun da yake da ita bai taɓa ganin tayi makamancin sa ba , duk kuwa da abubuwa dayawa da suka yi ta farauwa tsawon shekaru , a ƙarshe kuma ta rantse da Allah akan sai ta zo ita da mutanen ta na arziki wanda ta riga ta aika musu da goron gayya ta , idan ya so a kira hukuma su fidda su daga gidan ,! Ai ita ma tana da hakkin ta na uwa akan zainab ɗin .

Ganin taƙi sauraran ban hakurin da yake yi mata hakan ya sa shi miƙewa cikin sanyin jiki ,

Amne ! ni zan koma , Allah ya huci zuciyar ki ,

Amin

tace da shi tana kawar da kan ta gefe guda ,’ tare da karkaɗa kyakkyawar kafar ta da ta ji ƙunshi zajir da shi har wani sheƙi yake yana ɗaukar ido akan farar fatar ƙafar ta ,

Langaɓe kai yayi ya tsaya yana kallon ta ,”

Banza tayi da shi domin tana jin ɓacin ran yadda a koyaushe yaran suke goyon bayan uban su akan ta tamkar ba ita ta haife su ba ,

Gajiya yayi da tsayuwa ya sake cewa

Na tafi amne.’

Ka gaida mutanen gida

tace tana miƙewa ta shige ɗaki

Bayan ta ya bi da kallo kafin ya jaa ƙafafun sa a sanyaye ya fice , ko da ya zo jikin motar sa ma kasa shiga yayi ya tsaya yayi shiru ran sa baki ɗaya a jagule yake duk wani nishaɗi nasa ya kau ,

Fuuuuuw ya ji wucewar mota da matuƙar karfi , ya bi motar da kallo motar ɗazun ce dai , kaɗa kan sa yayi yana jimami lokacin da ya ga kiris ya rage motar ta buge wasu yara ,”

Allah ya kyauta

ya furta a sarari yana shigewa cikin motar sa ,’ ya jaa sannu a hankali ya bar unguwar !

*****

Tun safe Ƴan aiki da masu gyaran wurin da za’a yi taron wushe-wushe , suke kai kawo , yayin da masu dafa abinci ma basu zaune basu tsaye domin yin girkin taron baƙi , “tawagar gidan maza da shi kan sa ango da abokan sa da zasu iso a yau ɗin ,’girke-girke ake na alfarma ,

A gefe guda ƙawayen amarya ne zuwa ƴan uwan ta suke ta kai kawo tsakanin tata saloons da gidan domin yin kwalliya da gyaran jiki saboda kowacce so take ta burge so take ta jaa hankali , so kuma take ace ta fi kowa ,” !

Amarya kuwa musamman aka ɗauko mai gyaran jiki da kwalliya daga tata saloons domin tayi mata nata shirin a gida ,’

Duk kai kawon da ake yi fiye da rabin hankalin samy baby bai tare da ƙawayen na su , ya tafi ne ga tunanin son sanin haƙiƙanin ina su yakaka suke da zama , domin kuwa a yanayin su na jiya ta hango rashin gaskiya tare da tsoro ɓaro-ɓaro akan fuskokin su ,

Tayi niyyar ta titsiye su su faɗa mata gaskiyar ina suke da zama yanzu ? A hannun wa suke ? waye ya jiɓanci lamuran su tare da cikin jikin yakaka ? A ƙarshe ta ji dalilin da ya sa suka gudu sannan da manufar yakaka na barin cikin jikin ta wanda yayi girma sosai yanzu ya fito ,”!

Sai dai ko alamar su bata gani ba tun da ta zo gidan ɗazu da safe , yau tazo ne da nufin kwana zuwa gobe da za’a ɗaura aure su juya tare da amaryar garin abuja inda a yanzu ta fi zama a chan saboda yadda harkoki suke gara mata sosai ta haɗu da manyan masu kuɗi suna sakar mata bakin aljihun su tana abunda ta ga dama , “

STORY CONTINUES BELOW

Sofi ita ce ƙawar samy baby ta ƙud-da-ƙud , sosai ta su ta zo ɗaya , wasu halayya ta su suka dace da na juna , kuma ita ce ma ta gayyato ta bikin zainab ɗin a matsayin ta na babbar ƙawar zainab kuma sannan ƴar uwa ta kusa ga zainab ɗin ,”

Tunowa tayi da rahima wacce ta zo tayi musu magana lokacin suna tare , ta ji ta kama sunayen su , ta kuma musu maganar da yake nuna ta san su sosai ,

dan haka a bakin ta zata iya jin wani ɗan bayani akan su yakaka , ko da kuwa inda suke da zama ne ,

domin ita sosai take son jan yakaka cikin irin rayuwar da take a ganin ta gata take so tayi mata duba da cewar su yakakan basu da wani galihu , dan haka gara su tsaya da kafafun su .

Ta maida duban ta ga sofi wacce tuntuni take zaune a gefen ta tana ta faman kiran doctor hamza yaƙi ɗaukar wayar ,

hankalin ta gaba ɗaya bai jikin ta domin tun da ta zo bai yadda sun tsaya sun yi maganar mintoci biyu ba , ‘

ko ta nace sun haɗu a hanya gaisuwar ta kawai yake ansawa ya wuce , a sarari yake gwada mata rashin kulawa tare da rashin ƙauna ,

amma ta gaza yin zuciya ta janye jikin ta saboda yadda zuciyar ta ta riga ta ginu da ƙaunar sa , duk wata harka da take da maza tana yi ne kawai dan jaraba ba wai dan kuɗi ko so ba ,

so ɗaya tak doctor hamza take yi wa , sai dai ta sani sarai shi kuma baya yi da ita , kuma ta sha alwashin dole shima ya so ta , ya kuma aure ta

sannan duk wata macen da tsautsayi ya sa ta shigo rayuwar sa da sunan so zata iya kome domin ganin ta cisge ta daga rayuwar sa ko da kuwa idan ta kama ta ɓatar da mace ne !2

friend ,

Ni ina rahima ne ? Ƙanwar ku ? Ki kira min ita idan kina da number ta zan tambaye ta akan wasu ,”

Samy baby ta ce ga sofi haka ,”

Sai dai ga alama sofi bata ji ta ba domin cigaba tayi da latsa wayar da ba kome take yi akai ba ,illa tana kallon tsawon lokutan da ta share tana ƙiran hamza yaƙi ɗauka , a ƙarshe ma da ta ƙira yanzu jin wayar tayi a kashe ,” ji tayi wani irin ƙunci ya mamaye ran ta tana ji kamar an hura wuta daga ƙarƙashin zuciyar ta ,”

Taɓe baki samy baby tayi gefe guda tana jin haushin yadda ƙawar ta ta liƙewa wannan ɗan uwan nata likita , yana ta faman walakanta ta alhalin ga manyan masu kuɗi suna rubibin ta ,ta na jaa musu aji ,”

Mtss ta jaa tsaki gami da sanya hannu ta zare wayar da take riƙe a hannun sofi ,”

Haba mana friend , ya kike bada kan ki irin haka ga ɗa namiji ? Kina bin sa yana walakanta ki , wallahi tun wuri kiyi wa kan ki faɗa , ni idan banda shan koko ɗaukar rai ban ga ma abun nacewa har haka agun wannan ustazun ba shi ba…..

Wani irin kallo da ta ga sofi tana yi mata da idanun ta da suka kaɗa suka yi jaa ya sa ta kasa ƙarasa maganar da take nufin cewa ,”

Samira ki san irin maganar da zaki dunga faɗa min akan doctor , kin san wallahi zan iya ɓatawa da kowa akan sa dan haka ki kiyaye ,”

mtss

samy baby tace tana ɗauke kai ,”

Dai dai lokacin da rahima ta hawo saman domin ɗaukar jakar kayan ta ,”

Yauwa rahima zo mana ,”

Na’am anty samira ,”

Ni ina yaran na jiyan nan waɗanda na ga kun gaisa da su , su biyu yakaka da falmata aina suke ne ? Ƙira min su mana !

Anty samira nima ban san inda suke ba fa ,

Oh na ɗauka anan kusa suke , ?

Ah ah .

Rahima ta amsa lokacin da take sunkutar jakar ta tana barin wajen ,

A sarari ta fara ƙunƙuni

Naƙi na ƙira muku su ɗin , ku sasu a gaba kuyi ta sasu aiki da aike kamar bayin ku ,ba kyau dai walakanta ɗan adam wallahi !

Ta cigaba da tafiya tana mita ,”2

STORY CONTINUES BELOW

Sashin doctor hamza ta nufa wurin su yakaka , a kwance ta tadda yakakar ta miƙe , falmata na zaune daga gefen ta tana matsa mata kafafun ta da tace suna mata tsuku ,”saboda wahalar aiki da kai kawon da tayi kwanaki biyu da suka wuce ,”

Yau har sun ɗan yi kyaun gani daga jigatar aikin da suka sha ,” tun safe basu fita a sashin ba rahima ita ta kawo musu abinci suka ci anan suka yi wanka , amma kayan jikin su suka maida domin rahimar tace musu su bari sai anjima idan an kusa fara wushe-wushe sai su yi kwalliya su je wurin .’

Da dariyar ta ta ƙaraso ,

Yakaka , fatima , wai anty samira tana tambaya ta ku nace ban san inda kuke ba ,” kun san ta ne ? Nagan ku tare jiya .

Anty samira ? Yakaka ta tambaya tana miƙewa zaune ,”

Ko dai anty samy ?

Falmata ta sake tambayar ta ,

Ita , kun san ta ne ? Ai friends ɗin ta ke kiran ta samy baby ,

Tace wai kuna ina ,? watakila aiki take son sanya ku ,”

Shiru suka yi aka rasa mai ƙwaƙƙwaran motsi ,” samy baby tana son kawo musu matsala cikin zaman su a gidan nan ,!

Yakaka ta katse shirun ,

Mun san ta mun yi aiki a gidan da take kafin zuwan mu nan !

Oho toh ina ga shiyasa take neman ku ashe ta san ku ne !

*****

Karfe ɗaya cif jirgin da ya ɗebo tawagar angwaye ya sauka a maiduguri international airport , tun a Abuja tafeedah yake gwada kiran layin youssouf domin ya sanar da su tasowar su , da lokacin da zasu iso domin ƙwarai suka ƙagauta da su ga juna bayan tsawon watanni takwas da suka yi rabo da juna , sai dai wayar tana ƙara ba’a ɗauka ne ,

ji yayi hankalin sa na neman tashi domin ƙarshen wayar da suka yi a daren jiya misalin ƙarfe tara na dare youssouf ya sanar da shi ya kusa shiga birnin maiduguri , yana kan hanya .

A maiduguri international hotel aka yiwa angwayen masauƙi yayin da iyayen kuma aka tafi da su wani babban gidan da ya kasance mallakin mahaifin su hamza ,”

Tun da youssouf ya baro gidan madam saly yake cikin halin gigita da ruɗani , dakyar ya dawo da kan sa hotel ɗin da ya kama ɗaki, ganin abun yake kamar mafarki , duk shirin da yayi kafin zuwan sa ya rushe saboda wacce yayi domin ta bata nan ta ɓata ba’a ma san inda take ba tukun ,”

gefe guda sabon gingimemen al’amarin da yake neman kutso kan sa dole cikin rayuwar sa na barazanar zautar da shi ,”cikin jikin ta da babu wanda ya danganta shi da nasa ,illa zuciyar sa da tunanin sa da suke masa rubdugu wurin tabbatar masa da babu shakka cikin sa ne , saboda me ?? Yarinyar shi ya fara sanin ta ɗiya mace kuma har zuwa lokacin da ya bar ta bata tare da kowa sai shi ,”

Jayayya yake da zuciya da tunanin sa akan lalle cikin ba nasa bane , ai ba jiya suka rabu ba , rabuwar su yanzu tsawon watanni shidda zuwa bakwai , zata iya yiwuwa bayan rabuwar su ta cigaba da bibiyar maza ne har ta ɗauki ciki ,

Sai dai sam zuciya da tunanin sa sun ƙi karɓar bangaren wannan hasashen nasa mai rauni ,”a kowacce daƙiƙa sake bijiro masa suke da dangantakar dake tsakanin sa da cikin jikin ta ,”

tsawon rayuwar sa bai taɓa shiga halin ruɗani irin haka ba , ya zama dole ya nemo yarinyar ko domin ya samu nutsuwar zuciya akan cikin jikin ta , nashi ne ko ba nashi bane ?,”

Bai yadda ya danganta cikin da nasa ba , sai dai ya san ko da ba nasa bane samuwar cikin a tare da ita wani babban ƙalubale ne akan manufar sa game da ita da irin shirin da yayi na gyara rayuwar ta , shi bai san kome akan ta ba , amma yayi mata shiri mai kyau akan hasashen da yake kan dalilin da ya jefo ta rayuwa a wannan gidan da taje a matsayin ƴar aiki ,” ko dai ta gudu a gidan su saboda rayuwar matsi da wahalarwa, ko kuwa auren dole , ko kuma tsantsar talauci da rashin galihu ya jawo mata neman kuɗi ta kowacce hanya ,”

STORY CONTINUES BELOW

Kowanne daga cikin dalilan nan yayi niyyar tunkarar matsalar ta ya magance mata ita , ya tsame ta daga rayuwar gidan saida burkutu zuwa kyakkyawar rayuwa ,1

ya maida ta gidan su gaban iyayen ta ya gargaɗi iyayen ta akan sakaci da tarbiyyar ta idan ta kama ma yayi musu barazanar haɗa su da hukuma idan ya kama su da laifin wahalar da ita ,

kuma ya tsaya mata tayi karatu, idan ta kama ya buɗe mata account ne ma zai buɗe mata wanda ko da ya bar nigeria saƙon sa zai dunga isowa gare ta , a ƙarshe ya bar mata numbobin wayar sa wanda a duk lokacin da wata matsala mai girma ta taso mata kowacce iri ce ta neme shi ,

Insha Allah zai magance mata idan ta kama ya tado da mutane ne ma daga chan ƙasar su zai turo , shi dai babban burin sa kar ya zamto a dalilin sa yarinyar ta faɗa mummunan rayuwar karuwanci wanda za’a dunga raba zunubin ta da shi , da ya fara lalata da ita ,”

Sai dai ashe ya makaro aikin gama kuma ya gama , ƙarshen lalacewa dai har ciki tayi ba tare da aure ba , “

Sam yaƙi ya bawa kansa dama ya hasaso kan sa a matsayin uban cikin jikin ta , ” ya san tabbatuwar hakan wani al’amari ne da zai iya yin ɗai-ɗaya da farinciki na duk wani mahaluki da yake da girma cikin rayuwar sa , a karan kansa kuwa tunanin sa yayi kaɗan wajen tsinkayo irin halin da zai iya kasancewa a ciki .1

Har tsuma yake lokacin da yake tunanin yadda zai sata a gaba ta kai shi har gurin ɗan iskan da ya ɗirka mata cikin , bai tunano irin azabar da zai gana masa ko da kuwa biyan ta yayi da amincewar ta yayi mata cikin ,” a fili ya furta

Mtss doluwar watakila shima taimakon sa tayi ,”

tsabar kan sa ya ɗau chaji bai ma lura da wanda yake kiran sa ba ya ɗau wayar ya danna ta silent lokacin da ya ji tana neman damun sa da tsuwwa ,”

Ya ɗauki tsawon lokaci a ɗakin yana saƙa da warwara har bai san lokaci ya tafi dayawa ba sai da ya tsinkayi kiraye-kirayen sallah daga nesa ,

Wayar sa ya ɗauka dan ya ga lokaci anan ya tarar da miss calls ɗin tafeedah dayawa , ɗan dafe kan sa da ya fara sara masa yayi , shaf ya mance da lamarin bikin ma baki ɗaya ,” bin bayan ƙiran nasa yayi

mon amie kana lafiya kou ? Ina ka bar téléphone ɗin ka ? je vous ai appelé mais vous n’avez pas répondu ,

Lafiya nake ɗan ouwa , kun kai ga isowa gari ?

Muna a gari yanzou haka ,

Aina kun ka yi masauki ?

Maiduguri international hotel, , ” kai kana ina ?

Barwee hotel ,

nan tafeeda ya tambayi angon da yakasance haifaffen garin yanayin tsaro ya sa suka yi ƙaura daga garin zuwa birnin tarayya ,” ko ya san barwee hotel ? ɗan ouwan sa da yake bashi labari chan yake da masauƙi ,

Nan take ya ce zai tura a ɗauko shi yanzu idan har ya shirya ,”

Da haka suka yi sallama bayan an sanar da youssouf tasowar driver ,

****

Karfe huɗu da rabi angwaye suka iso harabar gidan su amaryar inda anan aka riga aka fara wushe-wushe , dukkanin su sun yi anko na shuɗiyar shadda mai duhu ,” kan su da jajayen hulunan dara ,”shigar su ta kanurai !

Ta ko’ina filin ya ƙawatu da adon gargajiya na kanurai , yayin da makiɗan ,”ganga kura” ( kiɗan kanurai na gargajiya ) suke tsaye daga gefe suna ta buga manyan gangunan su ga masu hura algaitun su na gargajiya suna hura ta tana bin kiɗan da mabanbanta sauti ,

STORY CONTINUES BELOW

Ƙamshin turaren wuta da aka sa a kowacce kusurwa na wajen yana tashi a hankali ta cikin electric burner ,”

Isowar angwayen bai ɗauki lokaci ba amaryar ma ta iso ƙarƙashin rakiyar ƙawayen ta waɗanda su ma suka yi ankon shuɗiyar shadda haɗe da baƙi ,” ( danga-shaw ) sun rufe kan su da jaan gyalen ,”( mandil ),”

Amaryar kuwa wata farar haɗaɗɗiyar lafayyah ce ta naɗe jikin ta da shi , wuyan ta ya ƙawatu da babbar sarƙar mirjani haɗi da siririyar sarƙar gold ,”

Nan amarya da ango suka zauna a mazaunan da aka tanadar musu , yayin da ƙawayen amarya suka fara shiga filin rawa suna bin kiɗan malikii da yake tashi sannu a hankali suka fara rawa ta burgewa mai cike da ƙasaita , ɗaya bayan ɗaya abokan angon ma suka fara takawa zuwa cikin filin rawar kowannen su yana fuskantar ɗaya daga cikin ƙawayen amaryar suna bin kiɗan tare da rawa kamar yadda tsarin rawar kiɗan malikii yake ,”

Nan take guɗa ta fara tashi daga bakunan manyan matan wajen ,

Jayayyar rahima taƙi ta ƙare da su yakaka waɗanda suka tirje kan su fa baza su fita wurin wushe-wushen ba , a ɗaki zasu yi zaman su ,”

Ai wallahi da na san haka zaku min ku ƙunshe cikin ɗaki da ban ɓata lokaci na nayi muku kwalliya ba , sannan shi da kan sa bro ai ya saya muku kayan ne dan ku sa kuyi kwalliya kuma ku shiga cikin jama’a ayi biki tare da ku ,

ta ƙarasa zancen muryar ta na bayyana jin haushin su , bayan kusan mintoci ishirin da ta kwashe tana bin su da lallama akan su zo su tafi ,”

A hankali yakaka ta miƙe tana sake gyara babban mayafin da ta lulluɓe kan ta da shi wanda shi da kan sa doctor hamza ya zaɓa mata shi , jikin ta sanye da doguwar rigar nan , kyau kam tayi sa iyakar kyau , tamkar irin wayayyun yaran matan nan da suka fara tashe a duniyar shahara ,” cikin ta ya ɓoyu a cikin rigar sai an lura da kyau za’a hango tudun sa,”

Yi hakuri Rahima , falmata ta shi muje ,”

Ni kam yakaka ko naje ma me zan yi a wurin ? ni da ba gani nake ba…

Eh dai koma me zaki ce kizo mu tafi har ke ,” ai zaki saurari kiɗan

Rahima ta katse ta da sauri

Miƙewa ita ma tayi tana gyara ɗan siririn mayafin da ta rufe kan ta da shi , ɗan jim yakaka tayi ,”

Falmata ko dai na baki babban gyale na naga wannan kamar yayi ƙarami ? tana bin ƙanwar ta ta da ido ganin yadda kayan suka mata cif-cif kamar wata babbar budurwa ,

Wai ma ji yakaka toh ai haka ake yayi bakya ganin rigar doguwa ce mai dogon hannu ? Dan Allah kar ki ɓata mata kwalliya ku zo mu tafi ,”

A hankali suke tafiya saboda takalman kafafun su da basu saba sa irin su ba , tafiyar kan ta a tsorace suke ji suke tamkar zasu faɗi ,”

Sun baro ƙofar sashin doctor hamza sun ɓullo ɗan wani siririn fili da zai sadar da mutum da harabar gidan falmata ta dogare ta ce ita daga nan zata tsaya , jin yadda take jiyo sautin kiɗan tamkar a gaban ta ,”

Rahima bata tsaya saurarar ta ba ta jaa hannun yakaka tana cewa

Ai sai kiyi ta tsayuwar idan kin ga dama ma ki koma ɗaki ,” yakaka zo mu tafi ,

Ba da son ran yakaka ba ta bi bayan rahimar tana waiwayan falmata , wacce take murmushi jin yadda rahima take nuna jin haushin ta ,” cikin ran ta tana ayyana taje gurin kiɗa tayi me ?? Ita ba gani ba bare tayi kallon jama’a ,’ zata jira su anan har su dawo ,’

Ta tsakankanin jama’a rahima ta dunga kutsawa riƙe da hannun yakaka har sai da suka bullo gaban filin ya zama , suna ganin duk wanda ke tsakiyar filin rawar ,”

Biyamuradi youssouf yayi tsaki yafi a ƙirga , ya kuma yi danasanin zuwan sa wurin wannan hayaniyar , tun asali daman shi ya tsani kiɗa domin ko nasu na masarautar su baya yadda su buga masa a gaban sa suna nufo shi yake sawa a tare su ya sallame su ,”

uwa uba tashin hankalin da zuciyar sa ke ciki , wanda duk wata ƴar sakewa da yayi suka ɗan taɓa hira da abokan tafeedan kawai ɗaurewa yake , sam bashi da nutsuwar zuci , tafeedan da kan sa ya fahimci hakan .

Duk yadda yaso janye tafeeda su bar gidan ƙi yayi a cewar sa shi tsarin yanayin al’adar su ta burge shi dan haka zai ɗaukar wa mairamar sarki hotunan su haɗi da videos ya je ya nuna mata ,”

Da ace ya san kan garin ko kuma shi ya tuƙo kan sa ya zo , da tuni yayi tafiyar sa daga wajen , domin a halin yanzu ma chan gefe ya samu ya tsaya yana faman ciccin magani ,da ginshirin su irin na sarakai ,” ‘”ah toh yarima anan wa zaka yiwa ??2

Gani yayi gurin bai masa ba saboda yadda hankalin ƴan mata dayawa yake kan sa , dan haka kawai sai ya bi wata ƴar hanyar da ya gani daga gaba da inda yake tsaye kaɗan ,” ba tare da ya san ina bane , sai dan gani da yayi akwai alamun rashin mutane ta wajen ,”

Ƴar siriyar hanyar ya shiga inda yake hango wani ɗan tudu da zai iya zama akai , sai da ya isa wajen ya lura da tsayuwar wata yarinya daga gefe a raɓe da jikin bango tana fuskantar ciki ,”

bai kula da wanzuwar ta ba ya zaro wayar sa ya shiga dubawa bayan ya zauna ,”

Tun takun sa na farko a wajen ta ji shi , ta cigaba da jin tahowar sa kafin daga baya ta ji an zauna a ɗan nesa da ita , jin shiru ya sa ta waiwayo ba domin tana son ganin wanene ba sai domin ta fargar da wanda ke wajen samuwar ta a wurin ,”

sun jima a haka shi ya manta ma da ya ga mutum a farkon zuwan sa wurin ,

Kamar ance ya ɗago kan sa , karaf ya sauke akan ta tana nan a inda ya gan ta tun farkon zuwan sa wajen ,” idanun ta fes akan sa bata ko kifta su ,”

Shima kallon ta yayi sosai , ya ga dai ta tsare shi da manyan idanun ta da yake iya hango girman su da sheƙin da suke a sauran hasken ranar da take gaf da faɗuwa , ” kamar shi take kallo kamar kuma ba shi ɗin take gani kai tsaye ba ,”

Yarinya ce a idanun sa bata wuce mairamar sa ba , a idanun sa ma sai ya ga tana yimar yanayi da mairamar yanayin yadda ta tsaya daga jikin bango alama fushi tayi taƙi fita zuwa wajen bikin nasu ,”

ɗan murmushi yayi tunowa da yayi da rigimar mairama yana jin kewar ta na taso masa ,”

Tsintar kan sa yayi da son yayi mata magana tun da ta rasa mai rarrashin ta ta huce,”

Ƙanwa ta ke baki gajiya ne da tsayuwa ??

Wara idanun ta tayi lokacin da ta ji tashin muryar sa , wannan ba doctor hamza bane ,toh WANENE ???

Da sauri yakaka take ratsa mutane tana son fitowa daga cinkoson gurin da ya sake ruɗewa da buɗa haɗi da sowa ana ɓarin kuɗi sakamakon shigowar ango da amarya cikin filin rawar ,”

dakyar ta samu fitowa ta nufi hanyar sashin doctor hamza , duk hankalin ta yayi kan falmata , bikin ya ɗauki hankalin ta har bata san ta ɗauki lokaci haka ba sai da ta ga duhun dare ya fara shigowa ta farga !Ji tayi an riƙo hannun ta ta baya , tana daf da ƙarasawa sashin doctor hamza , fuskar ta da murmushi ta juyo ga zaton ta rahima ce ,”+

    Rahima , Falmata nake son na duba , kin ga dare ya fara yi bana son …..1

   Sauran kalmomin ta maƙalewa suka yi a fatar bakin ta lokacin da tayi arba da fuskar samy baby a maimakon rahimar da take zato ,

    An-anty samy  ke ce ??

  Ba tare da samy baby ta saki hannun ta ba ta fara tafiya tana nufar cikin gidan da ita sashin su rahima , ba musu ta bita tana waiwayen hanyar sashin doctor hamza , da fatan ko zata hango falmata , yayin da ran ta yake cike taf da fargaban abun da samy baby zata bijiro mata da shi ,”

Waye ne a anan ?

Falmata ta furta hakan tana mai sake wara ƙwayar idanun ta ,”

Shiru youssouf yayi  tare da kafe ta da ido ,

  Watau dai ita mace kome ƙanƙantar ta mace ce ,” ji wannan ƴar yarinyar ma wai dan kawai nayi mata magana shine har zata min gwalangwaso da fi’ili ta nuna ma bata ma ganni ba sam.,”  tsaki ya jaa gami da mayar da hankalin sa kan wayar sa ,

Sarai ta ji tsakin da yayi mata kasantuwar ta mai nisan ji , ko yaya abu yayi motsi tana iya ji tun daga ƙasan ran ta ,” jikin ta taji yayi sanyi ,” koma waye bai gane bata gani ba , ” ba laifin ta bane ,”

Dan haka ta juya a hankali tana laluben jikin bango da nufin komawa ɗakin doctor hamza ,”

Kiran wayar sa da Tafeedah yayi shi ya sanya shi miƙewa bayan ya ɗaga kiran inda yake sanar da shi ya zo su tafi masallaci daga chan kuma su wuce masauƙin su sai kuma gobe su dawo ɗaurin aure !

Da sassarfa ya bar gurin da daman jin sa yake tamkar akan ƙaya !

Tsumu yakaka tayi a gaban samy baby wacce ta tsare ta da tarin tambayoyi wani kan wani ,”

Sake ɗagowa tayi a karo biyu ta dubi samy baby kafin ta muskuta cikin yin ƙasa da murya tace :

   Antƴ samy a gidan nan muke da zama ni da falmata , kuma yaya dakta shi ya kawo mu ,”

   Wanene yaya doctor ? Kina nufin likita yayan su zainab ?

Gyaɗa kai tayi

  Shi ne !

Daman ya san ku ne ? Ko ƴan uwan ku ne ??

  Kawai ya taimake mu ne bamu san shi ba amma tun farkon zuwan mu garin nan tun muna sansanin mu yake taimaka mana !

  Jimm samy baby tayi tana aunawa tare da juya zantukan Yakaka cikin ran ta ,”

   Meye tsakanin ku da shi ? Ya taɓa cewa yana son ki ne ?

Da sauri ta girgiza kan ta

  A ah ni baya so na !

Bai tambaye ki akan cikin jikin ki ba ?  Me kika ce masa game da cikin ?

Cewa yayi waye ya min cikin ? Ni kuma ban faɗa masa ba , tun daga ranar bai sake tambaya ta akan cikin ba , sai ya kawo mu gidan su nan , yace mu zauna , yana kula da mu sosai ni da falmata , har asibiti yake kai ni ayiwa baby photo dan Allah kar ki sa su kore mu anty samy bamu da wani wajen da zamu je a yanzu da ya fi nan ,

   Ta ƙarasa zancen hawayen da take tarawa a ido suna silmiyowa ,”41

Guntun murmushi tayi

  Ni bazan sa su kore ku ba yaks , ki daina kuka ,!

     iyeeh watau har hoto aka yiwa baby ? kice dai kin shirya zama uwa sosai yaks

   jaan numfashi tayi kafin ta sake  wurgo mata wata tambayar da ta sa zuciyar yakaka tsalle ,”

   Ya labarin yarima uban cikin jikin ki ko har kin haƙura da neman na shi kin daina son shi saboda kin samu gidan hutu ?1

  Ban – ban daina son shi ba anty samy kullum yana raina inason sake ganin sa , ban san yadda zan yi na gan shi ba ne ,! Ko kin samu labarin inda yake ?

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi tayi

   Nasan inda yake yaks !

Zuruf ta miƙe tsaye batare da ta ji nawin cikin jikin ta ba ta matsa ta kamo hannun samy baby ta riƙe gam.,

   Aina yake anty samy dan Allah ki kaini wajen sa , wallahi ina son shi , ina son na gan shi ki taimake ni !3

Koma ki zauna yaks ba abun gaggawa bane , ki nutsu akwai maganar da nake so muyi da ke , amma….

   Shigowar sofi ta katse abun da samy baby take nufin cewa ,

   Da wani irin hargitsatsen kallo ta bi yakaka , kafin ta juya akalar hararar ta ta kan samy baby ,”

   Ke kuma me ya haɗa ki da wannan koɗaɗɗiyar ƴar gudun hijrar ?? Ko wani aiki zata miki ? Nifa na tsane su yi sauri ki sallame ta duk ta cika mana  wuri da tsami da hamami ,”

  Ba tare da samy baby ta amsa mata ba tace ga yakaka

Ta shi ki tafi abin ki ,

Cikin sanyin jiki yakaka ta miƙe tana satar kallon sofi ,haushin ta na cinkushe mata rai ,” sam ran ta bai so ba da zata bar gurin ba tare da taji wani ƙwaƙƙwaran bayani game da bature kam silum ba ,”  ta so ta ji ina yake da zama da babu abun da zai hana gobe ta je ta gan shi ko da kuwa da kwatance ne!12

Dai-dai tazo barin ɗakin ta waiwayo suka haɗa ido da sofi wacce take bin ta da kallon banza ,” bata yi ƙasa a guiwa ba ita ma ta galla mata harara tana mai ƙarasa barin ɗakin ,”

Duka samy baby ta ɗakawa sofi a cinyar ta wacce take ta faman baloƙoƙo akan hararar da yakaka tayi mata sai faman zagin ta take tamkar zararriya

   Ƙawata ke fa banza ce yanzu akan wannan ƙanƙanuwar yarinyar kike ta ɗaga murya haka ?  Alhali ma tayi tafiyar ta ,” ko dai haushin kaza kike huce akan dami ,” hala shi autan mazan ya miki abunda ya saba ?

  Cisge ɗankwalin kan ta tayi jelar gashin dokin da tayi manyan kitson ghana suka watsu akan kafaɗun ta,”2

Bari kawai kawata wannan ɗan tahalikin yana son ƙure gejin hakuri na akan sa , ” bai san cewa akan sa kaɗai sashin zuciyata mai mutunci take iya tasiri ba , amma tunda yaƙi ta  mutunci toh fa ko da tsiya -tsiya wallahi sai ya so ni kuma ya aure ni , sannan na juya shi yadda na so a lokacin da na so , Naga shege ko shegiyar da ta isa yin min katanga da cikar burina , wallahi ko gyatumin sa sun yi tsororo !  Hamza nawa ne ni kaɗai ,4

Da kallo samy baby ta bita tana nazarin kalaman ta tare da ɗauko kulawar da hamza yake bawa su yakaka tana haɗa su tare da yin dogon nazari ,

ita tasan wacece sofi tasan bala’i da kaidin sofi , bata fata ko kusa ko kaɗan ace wani sha’ani na adawa ya ratsa tsakanin ta da yakaka ,1

wacece yakaka ? Bata tunanin ko uwar yakaka ta isa karawa da sofi akan abun da take ƙwalafacin so bare yakaka ,1

tana tausayin yakaka da gaske baza ta so ba ta faɗo hannun sofi ta wannan mummunar hanya , ta sani sarai cikin ƙanƙanin lokaci sofi zata ɓatar da yakaka daga doron ƙasa ,”1

Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji sofi tana cewa

   Wai kin kuwa san ma me yayi min ? Bata jira amsar samy baby ba ta ɗora ,

   Tsawa fa ya min a bainin nasi , dan kawai na nemi ya tsaya muyi hoto ,”

   Ta ƙuta , ai wallahi bashi ya ɗauka , zai kuma biya da tsada lokacin da ya shigo hannun na ,1

   Ta miƙe tana mai nufar bathroom ,

Da kallo samy baby ta bita ,”  ya zama dole tayi wani yunƙuri domin ganin ta hana wannan yaƙin faruwa tsakanin ƙaramar yarinya yakaka da sofi , dole ta zare yakaka daga rayuwar hamza muddin ta gano yana da manufar soyayya da yaks ɗin kamar yadda ta hasaso , ” ai idan ka ga kare na sunsuna takalmi ɗauka zai yi ,” kuma banza bata kai zomo kasuwa ,”1

10:30pm

Duk yadda Tafeedah ya kai ga son sanin meke damun Youssouf da har ya firgita shi ya zama barazana ga nutsuwar sa , Youssouf ɗin yaƙi faɗi masa , iyaka yace masa ya gaji ne da zaman nigeria yana son komawa ƙasar su ,

STORY CONTINUES BELOW

wanda shi Tafeedah ko kusa zancen bai shige sa ba , tayaya Youssouf masoyi ga aikin sa kuma jajirtatcen jarumi a fagen daga zaƙwaƙuri wurin bawa ƙasar sa kariya tare da sadauƙarwa zai ce ya gajiya ? Babu shakka akwai wani abu wanda yayi girman da yake neman jirkita masa tunanin aboki da shi bai kai ga sanin wannan lamarin ba ,”

Kallon sa ya mayar ga Youssouf ɗin wanda yake kwance bisa gado ya takure cikin bargo gami da bashi baya , ji yayi duk wani ɗan kuzarin da yayi saura a jikin sa yana barin sa , bayan tsawon watanni tara da rabuwa da ganin junan su , yau sun haɗu amma babu wani armashi a haɗuwar ta su kamar yadda suka saba ya haka idan aiki ya shataa layi ya raba su , toh fa duk ranar da suka haɗu kusan raba dare suke suna hirarraki da dararrakin su ta hanya bawa juna labarukan bayan rabuwar su , “

Youssouf amini ne a gare shi ƙari kuma ɗan ouwan sa ne na jini , amintakar su mai ƙarfi ce ta yadda idan ɗaya ya kasance cikin damuwa ɗayan ya kan gaza sukuni har sai sun haɗu sun samarwa da kan su mafita , damuwar sa a yanzu bai wuce yadda Youssouf ɗin yake kokarin boye masa abun da ke damun sa ba , da hakan yake baƙon lamari a tsakanin su  sai dai ko ma menene zai bi a sannu har ya kai ga sani ,

Ga Youssouf ɗin kuwa damuwa ce ta yi masa katutu , kan ɓacewar yakaka , mafi girman lamarin shine cikin da aka ce tana tare da shi , tunanin sa idan ba’a kai ga samun ta ba har ya bar nigeria yaya zai yi ?? Shikenan zai tafi ya cigaba da rayuwa alhalin wata na nan ta wanzu tana aikata babban zunubi ana raba musu tare ??

Wannan lamarin ya girmama a gare shi danasani kuwa yayi ta yafi sau shurin masaƙi , a bayan kowacce daƙiƙa damuwa ke sake masa lullubi , ya ƙagauta gari ya waye ya sake komawa gidan madam Saly ya ji yaya aka kwana  ? 

Yawan damuwar ita ta bayyana kan ta ga Tafeeda wanda a zahiri bai shirya ba baya kuma fatan wani nasa makusanci ya san irin ta’asar da ya aikata a rayuwar sa , duk da yasan Tafeeda aminin sa ne , amma bashi da karfin guiwar sanar da shi wannan auka-aukar da yayi , to ma me zai ce ? Ta ina zai fara ?

Ko babu kome shi ɗan nasaba ne , ɗan sarauta , ɗan manyan mutane wanda wurin su ake hangen kyaun tarbiyya tare da nagarta har mutane suyi koyi ,

yana jin zuciyar sa na nawi a duk lokacin da ya tuno da matsayin sa tare da martabar sa ga idanun tarin wasu mutane YARIMA ne shi wanda ake sa ran bayan shuɗewar wani lokaci idan da rai ya zama SARKI , JAGORA kuma SHUGABA abin KOYI ,1

Anya-anya shi bai faɗa cikin wata babbar musifa ba kuwa ??

Ya ɗauki tsawon lokaci a haka yana kwance ba kuma bacci yake ba har zuwa lokacin da ya tabbatar bacci ya ɗauki Tafeeda , sannan ya miƙe gami da shiga banɗaki ya ɗauro Alwala ya zo ya fuskanci Al-Qibla yana mai fatan Allah ya kawo masa mafita ya kuma yafe masa zuban sa !

Kewar da take binne cikin ran yakaka tare da tsananin son biyamuradi youssouf sune suka yi toroƙo suka hana ta sukuni tun bayan rabuwar ta da samy baby , har ƙamshin sa ta dunga jiyowa lokacin da ta sanya kafafun ta cikin sashin doctor hamza wanda yayi mata jagora har zuwa cikin falo , illahirin tsukin wajen ya ɗauki kamshin kakkarfan turaren biyamuradi youssouf wanda yayi tasiri matuƙa wurin ƙarasa lugui-guita rarraunar zuciyar yakaka ta ƙarasa narkewa cikin so da begen biyamuradi ,2

Hatta Falmata da Rahima sai da suka fahimci tana cikin damuwa , juyin duniya suka nemi sanin meke damunta ?? Tace musu babu kome a ƙarshe da ta ga sun damu ,musamman Falmata da ta gaza cin abinci dare na kirki , kamar yadda ita ma yakakar ta gaza ci , sai kawai tace kan ta ne ke ciwo , ” nan ma dai wani sabon tashin hankali ne ga Falmata domin kuwa kalmar ,”sannu,” bata yanke daga bakin ta ba har bacci ya ɗauke su !1

STORY CONTINUES BELOW

Washegari 

Misalin ƙarfe 8am Hamza ya ƙira Rahima a waya inda yake sanar da ita su buɗe masa ƙofa zai shigo ya shirya , ”  daman sun riga sun jima da tashi dan haka.saƙon nasa kawai ta sanar ga su yakaka su dukkanin su suka miƙe ,

A bakin kofar sashin nasa suka haɗu da ladabi suka gaida shi ya amsa cikin gaggawa yana amsar ɗan mukullin sa da yake hannun rahima,’

  Ku jira ni anan na gama shiryawa yanzu na fito , kar ku tafi ko’ina ,”  ya furta hakan yana shigewa ,”  har yayi ciki sai kuma ya kira Rahima suka shiga tare ,”

     Hankalin yakaka ya kai ga manyan rumfunan da ta gan su a kakkafe a harabar gidan birjik wanda bata san lokacin da aka samar da su ba , ana ta faman shimfiɗa manyan dardumai da kilisai a ciki , babbar ƙofar gidan a wangale take ana iya hango kai kawon da ababen hawa suke akan titin da ya bi ta gaban gidan , wata mota ƙirar bus ce ta tsaya a ƙofar gidan ,

Manyan Mata ne su rai shidda suka fito daga motar sai kuma ƴan mata sun kai su biyar , dukkanin su suna yanayi da juna farare ne sol-sol dogaye , mafi akasarin su lafaya ce a jikin su wacce bata ƙarasa ƙasa ba iyakar sangalalen kafafuwan su, hannun su zuwa kafafun su da manyan zanen lalle , jazir “

Manya-manyan jakar bacco sun kai guda biyar suka kinkimo zuwa cikin gidan , waccen da wannan sun kama wannan ma da waccen sun kama , uku daga cikin manyan matan ne basu sa hannu ba wurin ɗaukar kayan ,

Daga gefe suka tsaya tare da ajiye kayan hannun su ,

Ɗayar da ta tsaya biyan direban motar itace ƙarshen shigowa ,

Magana tayi musu kafin ta nufo sashin Hamza kai tsaye , su kuma suka dakata daga inda suke ,  duk abun da suke idanun yakaka yana kan su ta nacewa kallon su , yanayin su ya mata daban da na mutanen da ta saba gani ,

Idanun ta ya sauka akan matar da take nufo su , wacce ita ma hankalin ta ya kai kan su yakaka , sosai suke kallon juna ita da yakaka lokacin da take ƙarasowa gurin ,”

Da wata irin murya da ta fito da sauti sosai tace RAHIMA ,

   Dai-dai da fitowar Rahima wacce jin sautin muryar da ko a mafarki baza ta mance ta ba tana ƙiran sunan ta ya sa ta ƙarasa takowa da gudun gaske ta rungume ta bakin ta na kiran ,1

  Amne ! Amnee !

   Rungume Rahimar itama tayi idanun ta na nacewa kallon yakaka wacce ta sunkui da kai tare da riƙo hannun falmata , saboda wani irin yanayi da take hangowa a cikin idanun matar mai kama da idon wata wacce tayi wa farin sani ,”2

A hankali ta zare Rahima wacce take ta murna tana dariya daga cikin jikin ta ,

Abnatay wacece wannan ?  Ta furta hakan tana nuna mata yakaka da hannun ta da ya sha awarwaro da jaan ƙunshi ,

Yakaka da Falmata ne ,

Su waye su ƴan uwan ku ne ?

Da ɗan murmushi tace , ” ƴan gudun hijira ne yayan mu ya kawo su ,” ta ɗora da jawo hannun yakaka ,

   Yakaka ga maman mu ,”

Nan take yakaka da falmata suka buɗe haƙoran su suna dariya kafin duk su kai guiwowin su ƙasa ,

  Mama sannu da zuwa ina kwana , suka haɗa baki wajen gaishe ta ,”

  Da sauri ta ɗago yakaka ,

  Tashi – tashi yarinya ta babu kyau durƙuso a halin da kike ciki , sannun ku kuna lafiya ?

   Lafiya lau duk su biyun suka amsa ,”

STORY CONTINUES BELOW

Ɗauke idanun ta tayi daga kan yakaka tana saita nutsuwar ta tace ga Rahima

Ina yayan ku ??

Yana ciki ta bata ansa 

Janye idanun ta tayi daga kan su falmata ,lokaci guda ta miƙa hanya zuwa ciki wajen Hamza , 

zuciyar ta na cigaba da kambama mata wasu kamanni masu karfi dake tsakanin yakaka da Rahimar ta , da a tashin farko da ta ɗaura idanu akan ta ta firgice , ƙewar  ƴar uwar ta na mamayar ta har idanun ta suna tara ƙwallar tunowa da ita a take taji gidan ya fara mata duhu ,

kome yana da sanadi kome yana da mafari , nan gidan , nan sashin shine mafarin kome , nan inda dugadugin ta ke takawa a yanzu shine mafarin tarwatsewar rayuwar Rahimar ta da yayi sanadin rabuwar su  , ko tana ina ?? Allah shi kaɗai ya sani ..1

sai dai jikin ta na bata Rahimar tana raye kuma zasu haɗu zata dawo gare ta , abu ɗaya ne fargaban sa ke guiguiyar ran ta kullum wayewar gari shine Rahimar zata dawo mata ne a matsayin Rahimar ta ƙanwar ta , ko kuwa zata dawo ne da ƙudirin ɗaukar FANSA  ,…… ?2

******

Nan sashin Hamza , mahaifiyar sa tare da ƴan uwan ta da tsirarun ƙawayen ta , ‘tayi bigire daga yau zuwa gobe da zasu yi tafiyar su !

tsakanin ta da dangin mahaifin su Hamza kallon nesa-nesa ne ko gaisuwar fatar baki bata haɗu su da kannen mahaifin su hamza ba ,tamkar ma gudun haɗuwa da junan su suke ,

saboda ta riga ta ƙullace su irin ƙullata mai tsanani domin tana musu ganin sune SANADIN KOME , kowanne daga cikin su su rai shidda yana da tabon sa a idanun ta idan aka cire UNCLE SALMAN wanda shi kuma a halin yanzu baya raye a duniyar ,…

Su ma a ɓangaren dangin mahaifin nasu kowannen su ya ɗarsawa ran sa tsanar AMINA AL-ARABI SHUWA , saboda wasu manyan dalilai nasu ,”1

Cikin awa ɗaya jal da haɗuwar ta da su yakaka , ƙaunar yaran ta gauraye zuciyar ta , dan haka bata jinkirta ba wurin tambayar su labarin su da na iyayen su ,

Cikin sakewar da suka yi da ita suka bata labarin su tirƴan-tiryan , kafin su gama tausayin su ya sa zuciyar ta tayi laushi , sau uku tana maimaita musu tambaya game da mahaifiyar su akan menene sunan ta ,

   Amsar su ɗaya ce , su basu san ana kiran ta da wani suna ba bayan maman Yakaka , su kuma suna kiran ta Mama ,!

     Ta jinjina da jin cewar mahaifiyar ta su kurma ce bata magana, ta kuma tausaya , sannan ta cire tsammanin da take ko yaran suna da wata alaƙa ta kurkusa da ita/da Rahimar ta , tasan Rahimar ta ba naƙasasshiya bace ba cikakkiyar lafiyayyar mutum ce , dan haka ta danganta kamannin da take gani na rahima tare da yakaka a matsayin kawai halittar ubangiji ,”3

Karfe 10am aka ɗaura auren zainab da angon ta colonel Tahir Ma’aji , inda aka zarce da walima wanda mahaifin Amarya ya shirya ƙarƙashin jagoranci tare da kulawar Hamza ,

A daddafe Biyamuradi Youssouf ya tsaya aka ɗaura auren tare da shi , saboda hankalin sa da yake a tashe da son tafiya gidan madam saly dan jin ko an kai ga samun ta ,? ” 

A gurguje yayi wa ango gaisuwar taya murna , sannan ya jaa Tafeeda gefe ,

Ɗan ouwa ni zani koma bakin aiki ,ils ne me donnent que quarante huit heures , zuwa lokacin da nake issa bakin aiki , awanni sun kai ga cika ,”

Bai damu da kallon tuhumar da Tafeeda ke bin sa da shi ba , ya miƙa masa hannu suka yi musabaha ,

Idan ka cimma gidaa ka kiraye ni ɗan  ouwa ,’ Allah shi kiyaye hanya ,saduwar Alheri

Zame hannun sa daga cikin na Tafeeda yayi tare da juyawa ya fara taku domin barin wurin ,”

A takaice Tafeeda yace da shi ,”

STORY CONTINUES BELOW

me zan ce ga hajiya umma tare da mai martaba idan sun ka tambayeni halin da na riske ka ciki ??

  Juyowa yayi da wani guntun murmushi a fuskar ka kace da su ,”

   Yarima na a halin lafiya a bigire mai tsaro ,! Sannan ina miƙa gaisuwa ta a gare su tare da fatan Alheri !

Gyaɗa kai Tafeeda yayi yana mai juyawa ya shige taron jama’a cikin ran sa ya ƙudurce dawowa ya cimma youssouf su fuskanci matsalar sa tare , yanzu ma domin yana cikin ujila ne shi da kan sa awanni arba’in da takwas ɗin aka ba shi , dan haka su dukkanin su basu da isasshen lokaci a halin yanzu  !

Motar sa ya jaa da gudun gaske ya ɗauki gwadaben da zai sada shi da unguwar madam saly ,

Bai ko rufe motar ba ya taka ya shiga gidan , ” a ƙufule ,” sai dai tun daga bakin rumfar ya fara fahimtar sauyin da yake wurin domin dai babu kowa a cikin rumfar hatta kujerun cikin rumfar a tattare suke a gefe , da alamu yau ba’a shirin yin aiki ,”

Kai tsaye ya sa kan sa cikin gidan hanyar da ya bi jiya ita yau ya bi ya zo har bakin ƙofar ɗakin madam saly , har lau bai ga giftawa kowa ba tamkar gidan ba kowa ,”

   Garam ! Ya ga ƙofar ɗakin madam saly garƙame da ƙwaɗo har biyu ƙarami da wani fankacece iri na rufe ƙofar babban gareji ,”

  Duka ya kaiwa ƙofar ɗakin da ƙafar sa da matuƙar ƙarfi wanda ba domin ƙofar ta ƙarfe bace da ta karye,

  Ya ɗaga murya yana cewa

  Ina masu gidan ??

  Ina masu gidan ??

Ko giftawar kadangare bai gani ba , bai buƙatar a sanar da shi , ya fahimci sun gudu ne ,” nan take wani malolon bakin ciki ya maƙale masa a maƙoshi ,”1

Murza fatar goshin sa yake yana kokarin saita kan sa lokacin da yake kan hanyar barin gidan cikin ran sa yana aiyana zai dawo kuma haɗuwar su ta gaba baza ta taɓa yiwa madam saly kai dama duk mutanen gidan kyau ba ,

    Cikin takun da bai ko duba inda yake jefa kafafun sa ya bar gidan yana jin yadda zuciyar sa ke azalzalar sa da ya ɗan kora ruwa ko zai samu sa’ida azabar damuwa da yake ciki ta isa haka , amma tunowa da tafiyar ratsa daji da take gaban sa ya sa shi yakice tunanin shan barasa a wannan lokacin ,

ya fisgi motar da matsanancin haushin rashin cikar buri ya bar wajen bai ko kula da taron ƴan cha-chan da suke baje akan wata babbar tabarma daga ƙarƙashin bishiya a gefe suna faman yin karta tare da dara , da ya watsawa ruwan kwatami daga jikin su har zuwa fuskokin su ba , 

   Wucewar sa kenan ɗan liti ya fito daga banɗaki inda yayi maɓoya , bayan ya tabbatarwa da su madam saly su watse kaf su bar shi shi kaɗai a gidan zai jira zuwan kurtun ɗan sandan , ayi wacce za’ayi ɓera ya zubda garin kyanwa!4

Banten uba ! Kuturi ai yau da na yadda ya ganni sai ɗan buzu na , ai wallahi da sai dai Baba malmo ya auro wata safara’un ta haifi wani ɗan litin ba dai ni ba ,! Chab kai ka ga mutum kamar safurarren doki ??? Yana tafiya haka – haka – haka ,”kamar jarumin sadauki a fagen daga ??    Ko a mafarki na gan ka ai nayi sadaka !10

     Ahayyeee saly fara ta zo ta lale min kuɗin gadin gida da nayi mata ta biya ni ,,” kurtun ɗan sanda kuwa cewa zanyi na gama da shi ,” ah to meye ?? Ko banza ai na shaƙi tsoro da bugun zuci, ”  Rikicin duniya kuwa ai da me rai ake yin sa ehe ,!7

****

  Bayan kammala bikin zainab da sati guda doctor Hamza ya sanya yakaka a makarantar islamiyya da Rahima take zuwa , amma ta ta bangaren matan aure take zuwa kullum da safe karfe 8am.zuwa 12pm falmata kuma aka cigaba da koyar da ita arabi da bokon a gida ,’11

A makarantar yakaka ta san sabon sunan da doctor hamza ya laƙaba mata a matsayin sunan ta na yanka ,watau AMINA MUSTAPHA DILMARI ,2

Sosai take mayar da hankalin ta kan karatun ta kamar yadda doctor hamza kullum yake gargaɗin su , a gefe guda kuma cikin ta na cigaba da bunƙasa ta yadda har girman sa ya so yin yawa dan haka a awun da ta je cikin satin nan aka hana ta shan su madara da sauran cimakar da take sa yaro ya girma sosai a cikin mamar sa ,”

STORY CONTINUES BELOW

   Da wata safiya tayi shirin makaranta ta fito zata tafi sai ga motar samy baby ta tsaya a gaban ta , gaban kaɗan da gidan su doctor Hamza

    Nan ta nemi ta shigo suyi wata maganar da take tafe da ita , tayi murna ma da suka haɗu anan waje ,”

ba musu yakaka ta shiga motar tana murna sake ganin samy baɓy a dai-dai wannan lokacin da ran ta yake cike taf da son sani game da youssouf

   Nan cikin motar samy baby ta fara yiwa yakaka huɗubar da ta zamto kuskure na biyu da yakaka zata afkawa a rayuwar ta ,3

A sanyaye ta fito daga motar bayan ƙarasowar su gaban makarantar , ta luluƙa a duniyar tunani , ta yadda har bata san lokacin da samy baby ta jaa motar ta tayi tafiyar ta ba ,”

  Idan aka zo ga batun ƙaunar ta ga youssouf kome kunce mata yake , tana son shi sosai , yana birge ta fiye da kowanne mahalukin da ta taɓa cin karo da shi a rayuwar ta , amma anya ? Anya girman son da take masa ya kai mizanin da zata dai-daita shi da falmata ? Ƙanwar ta jinin ta ? Abar batun cikin jikin ta shi wani sabon abu ne da yanzu yake kan hanyar shigowar sa cikin rayuwar ta , duk da cewa akwai ƙauna irin ta ɗa da uwa a tsakanin ta da abinda yake cikin ta wanda tasirin son da take yiwa shi youssouf ɗin yake mamayar abun da yake cikin cikin nata tare da ninka mata ƙaunar son gudan jinin sa da ke tare da ita ,

To amma falmata ba ?? Falmata haske ce kuma sanyi ce sannan cikamakin farin ciki ce cikin rayuwar ta , tun asali akwai shaƙuwa da so mai tsanani a tsakanin su fiye da wanda aka saba sani tsakanin saƙo-da-saƙo na haihuwa , ya zarce ƙauna irin ta tsakanin ƴa da ƙanwa sai dai a kwatanta shi chakuɗuwar jini da soyayya irin ta tsakanin tagwaye wanda ƙarya ɗan adam ya zare wannan tsananin wannan son da shaƙuwar da ya samo asali tun daga ranar faruwar halitta a cikin mahaifiya , sai dai fa ikon rabbi ,”

Zata iya kome domin ganin ta samarwa da falmata farin ciki a kowanne bigire na rayuwa fatan ta a koyaushe ta hango farin ciki bisa fuskar miskiniyar ƙanwar ta , sai dai wannan lamarin da yau anty samy ta zo mata da shi , yarda da shi tare da yin aiki da shi tamkar ta ɗau takobi ne ta gille duk wani farin cikin da Falmata zata iya shinshinowa a rayuwar ta , tamkar ta kassara ruhi da gangar jikin falmata ne , wacece FALMATA idan babu YAKAKA ???3

Ba ta san ta kawo karshen makarantar ba sai da ta ji ta kaiwa bango karo ,

Zamewa tayi ta zauna dirshan a cikin ƙasa gami da fashewa da kuka , a sarari take furta kalmar,”  bazan iya ba , bazan iya ba, !2

****

Cikin satittikan da suka biyo baya samy baby ta cigaba da zirya tsakanin makarantar su yakaka inda take killace ta tana cigaba da cusa mata ra’ayin da take ganin zai iya tsallakar da yakaka daga faɗawa hannun sofi , ta hanyar yin amfani da kalaman yaudara da wayo ta cikin amfani da makahon son da yakaka take yiwa Youssouf ,

har ta kai ga nasarar samun haɗin kan yakakan ta wani ɓangare ba tare da ita yakakar ta san haƙiƙanin meke cikin ran samy baby ba,

iyaka son youssouf tare da ƙwaɗayin son samun sa a matsayin miji ya sa ta fara amincewa da shawarar samy baby , ɓangaren zuciyar ta dake gargaɗin ta tare da tuno mata da so tare da tausayin dake tsakanin ta da falmata ya fara samun rauni , ! Soyayya tayi ƙarfi ta yadda ta fara rufe mata idanu !

Sannu sannu , yau da gobe zuciyar yakaka tare da taimakon huɗubar samy baby da ta shaiɗan , ta ƙeƙashe da son ganin cikar burin ta na mallakar youssouf a matsayin mijin ta , kamar yadda samy baby ta wanzu tana ƙara ƙwaɗaitar da ita ,

bata ko duban hidindumu tare da gatan da doctor hamza yake gwada masu ita da ƴar uwar ta musamman ma ita da komen ta yake mai matuƙar muhimmanci agare sa , ko sau ɗaya bai taɓa burge ta ba , Koyaushe ɗaukar sa take a matsayin me kirki me TAIMAKON SU,2

STORY CONTINUES BELOW

hankalin ta a kullum daɗa tafiya yake ga youssouf wanda a yanzu hoton sa ya zama abun ɗebe kewar ta kullum dare har ma ta kan ɗan zanta da hoton idan dare yayi nisa wutar so kuma ta ruru iya ruruwa , sai ta fara sakin sambatun so ,

Sai dai tana ƙoƙari wurin boyewa musamman ga doctor hamza , wanda watarana a cikin ranaku ya kamata tana kici-kicin ɗaura agogon da youssouf ɗin ya bar mata a tsintsiyar hannun ta ,

ta shagala cikin bege sai murmusawa take har haƙoran ta na bayyana , sakamakon yadda idan ta ɗaura agogon yake zamewa daga hannun ta idan ta sauke hannun ,  sai tayi maza ta taro agogon ta chafe shi ta sake mayarwa cikin hannun ta , tana lailaya shi kamar tana ganin fuskar youssouf ɗin a jiki ,3

Ya ɗauki lokaci dogare a bakin kofar yana kallon ta cikin shauƙin ƙauna , sosai tayi kyau a idanun sa tana sanye da atamfa buɗaɗɗiyar riga da zane, tayi ƴar madaidaiciyar ƙiba ta buɗu kaɗan , sai ɗaukar ido take

Hankalin sa ne ya koma kan agogon da take wasa da shi a hannun ta , yana iya hango girma tare da ƙƴallin agogon daga inda yake tsaye ,” ya shaida agogon maza ne ,” 

Takawa yayi ya ƙarasa cikin falon bata lura da zuwan sa ba , sai gani tayi hannun sa ya riga ɗayan hannun ta chafe agogon lokacin da yake silmiyowa daga tsintsiyar hannun ta ,”

Ɗaga agogon yayi yana ƙare masa kallo daga gani ba tambaya agogon mai matuƙar tsada ne , da samun irin sa sai a hannun goggagun attajirai ,”

Cikin taushin murya da nutsuwar da take mahaɗin cikar kamalar halittar sa yace ,”

    Agogon waye ?

Shiru tayi tare da sunkui da kai, tun usul ƙarya bata cikin halayyar su , basu ma san yadda ake yin ta ba idan ba yanzu da duniya take ƙoƙarin koya musu ba ,”5

  Ganin sa ya janye daga kan agogon ya maida kan ta , tare da ɗan ƙara sautin muryar sa ,

   Wannan agogon na waye ne ??

A firgice ta ɗago kan ta jin kamar ya mata tsawa , matuƙa take shakkar sa tare da gwada yi masa biyayyah

Ba-ba-baba Agogon – agogon Baba ne !

  Ta harhaɗo kalaman da suka fito a baibai ,”  idanun ta na yin ƙwalƙwal .

Agogon Baba ?

  Hamza da Falmata suka haɗa baki wurin tambayar ta !

wacce take ƙarasowa wajen da lalube daga cikin ɗakin saboda jin tashin muryar doctor hamza domin ta gaishe shi ,

Agogon Baba ? Yakaka ina agogon Baban mu ? Daman Baa yana da agogo  ,

      Falmata ta furta hakan cikin tsananin murna kasantuwar ta mai matuƙar ƙwalafacin iyayen ta , hakan ya sa ta ma manta da abun da ta fito yi ,”gaishe da doctor hamza ,” ta himmantu wurin son a bata agogon ta riƙe , doctor hamza ne ya ɗaura mata agogon bisa hannun ta ,1

bai sake cewa kome ba ya juya yana barin falon zuciyar sa cike da wasi-wasi akan kalaman da yakaka ta furta na dangana wannan tsadadden agogon ga mallakar mahaifin su ,

A sanyaye falmata ta ɗago kai daga barin shafa agogon da take yi ta saita idanun ta a inda take zaton yakaka na zaune ,

    Yakaka kika ce wannan agogon Baa ??

    Da ido yakaka ta kafe ta kamar tana son ta gyara mata sokuwar ƙaryar da tayi ,” wanda ta hango rashin yarda da zancen nata ƙarara a idanun doctor hamza

   Miƙa hannu tayi ta zare agogon daga hannun falmata ,

   Falmata muje ɗaki na kwanta ki ɗan danna min kafafuna ciwo suke min ,

STORY CONTINUES BELOW

  Da sauri ta amsa da

  toh sannu yakaka

Tun daga ranar yakaka take koƙari wurin boyewa kowa duk wani abinda ya shafi soyayyar da take yiwa youssouf ciki kuwa har da Falmata ,

Da samy baby kaɗai take hirar sambatun soyayyar youssouf , wacce take daɗa ƙaimi wurin shiryawa yakaka gadar zare , tare da bugun cikin ta a koyaushe tana jin tsakanin ta da doctor hamza ,1

irin kulawar tare da hidimar da yake yiwa yakaka yake sake bata tabbacin zaton ta gaskiya ne , doctor hamza son yakaka yake , soyayyar kuma mai tsanani ta aure ,

wanda a koyaushe idan ta tuno sofi da irin mahaukacin son da take yi masa da irin mummunan alwashin da ta sha a kan sa , sai taji abinda take kokarin yi da nufin raba tsakanin sa da yakaka dai-dai ne, a ganin ta taimakon yakakar zata yi , har ma tana danganta yunƙurin ta a matsayin CETON RAI ,” 3

Lokacin da yakaka ta shiga watan haihuwar ta hamza ke sanar da ita daga wannan satin zata daina zuwa makaranta , baza ta dunga zuwa ko’ina ba daga awu , sai dai ta fita motsa jiki da dare ,

Da farko ta shiga damuwa , da hukuncin da ya yanke na hana ta zuwa makaranta ganin cewa a makarantar take samun damar haɗuwa da samy baby duk lokacin da samy baby ta so ,”

Amma lokacin da ta sanar da samy baby sai ta ga bata wani damu ba , suka cigaba da hirar su da fiye da rabin hirar maimaici ne tare da tisawa akan yadda tsarin samy baby yake da yadda kome zai kasance , har zuwa gamuwar ta da muradin zuciyar ta kamar koyaushe yakaka ke ƙarasa hirar da sambatun yadda haɗuwar tasu zata kasance da youssouf da ɗokin zuwan ranar ,

Bayan gama hirar su , sai samy baby ta ciro ƙaramar wayar ta , ta kamo hannun yakaka ta danƙa mata ,”

    Zamu cigaba da tattaunawa akan waya yaks , saboda kin ga bana son mutanen gidan su san da alaƙar mu domin kar a zarge ni har a bibiye ni bayan kammaluwar kome , ki tabbatar babu kowa a wurin a duk lokacin da zamu yi waya , ki dunga min flashing idan kina son magana da ni , sannan kuma daga mun gama magana ki dunga kashe wayar , kar ki bari kowa ya san da wayar ,

Idan chaji ya kusa ƙarewa ki sanar da ni , ni zan san hanyar da zan yi na karɓi wayar nayi mata chaji ,”

Abu na ƙarshe shine kar ki manta da tsarin mu ko cikin dare kika ji ciwon haihuwa na zama mutum na farko da zaki fara sanarwa kafin kowa , kin san dai shirin mu zai fara ne daga haihuwar ki ,  ai kin gane ko ?

  Naji anty samy kuma bazan manta duk tsarin da kika shirya min ba , nagode sosai da taimakon da kike min a kullum tunda muka haɗu , Allah ya saka miki da Alheri ,!

Murmushi mai wuyar fassara samy baby tayi,

    Ameen yaks ,

Tun bayan da doctor hamza ya sawa yakaka dokar hana fita unguwa , ya zama kullum da dare tare suke fita ita da Rahima , da misalin karfe 8pm , su ɗan yi tattaki su zagaya unguwar zuwa 9pm sai su dawo gida ,

Ƙwarai yakaka take jin daɗin fitar tasu saboda yadda a kwanakin take jin nawin cikin kafafun ta duk sun ɗan kumbura , ga kwonkwason yana mata tsuku idan ta daɗe ,”

Tare suka fito da Rahima daga sashin su , Rahimar tana ta mitar Yakaka ta katse mata kallon TV da take ta dame ta akan tazo su fita ta raka ta motsa jiki ,”

     Yakaka ni fa yau baza mu yi wani nisa ba , zamu dawo kin ga dai garin da sanyi ma , ga duk hazo ya rufe sama , ni ba dan kin nace ba ma wallahi yau baza mu fita motsa jikin nan ba duk ƙura ta bi ta shigewa mutum hanci ta sa mura ,”

STORY CONTINUES BELOW

  Gyara zaman burmemen hijabin ta yakaka tayi tana murmushin jin daɗi domin tun basu yi nisa ba ma ta fara jin kafafun ta na warwarewa ,”

     Ni kuwa Rahima daɗin yanayin ma nake ji , kiyi haƙuri kin san ba laifi na bane yaya dakta ne ya ce kar na dunga fashin fita motsa jikin ,”

   Doctor hamza ne ya shigo ta ƙaramar ƙofar gidan jikin sa sanye da ƙananan kaya ya rufe bakin sa da hancin sa da abun tare ƙura ,”Mask ,”1

Idon sa ya sauke a ƙan su lokacin da suke ƙarasowa ,”

     Gaishe shi suka yi ya amsa musu ya ɗora da

    Za’a je motsa jiki ko ?

Da sauri Rahima ta tari numfashin sa , big bro daman an bar zuwa motsa jikin nan yau sai gobe , ji fa garin duk hazo wallah ,”

       Rahima dan Allah kiyi haƙuri muje yakaka ta ce , tana marairaicewa ,”

      Cuno baki Rahimar tayi taƙi cewa kome , “

     Murmushi hamza yayi ,

   Koma ciki abin ki Rahima yau an ɗaga miki ƙafa sai gobe ,

     Da sauri Rahimar tayi juya tana dariyar murna , dan kar yace ta dawo ma har da ɗan gudun ta , ta ƙarasa shigewa sashin su , “

   Ganin sa ya mayar kan Yakaka , wacce ta sunkui da kai tana wasa da hannun ta ,”

      Noori

  Ya ƙira ta

   Na’am

  Tace tana ɗago kan ta ta dube shi kafin ta sake sunkui da kan ,” ba wani sanin ma’anar sunan tayi ba , ita dai tasan yakan ƙira ta da kalmar a irin lokuta haka da suke su biyu kaɗai !

         Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji yace mata ,

  Bismillah mu tafi ,’ ya buɗe mata ƴar ƙaramar ƙofar

  Tare da shi zan tafi ?

Ta tambayi kan ta lokacin da take sanya ƙafafun ta da ta cusa wasu ƴan takalman roba na mata ,” kumburin da ƙafar ta ta tayi ya sa takalman suka ɗan kama kafar ,”

    Ta ina-da-ina kuke bi idan kuka fito ?

      Ta nan muke bi tace da shi da ƴar siririyar murya ,”

    To yau ba nan zamu bi ba , zo mu bi ta nan , ya ce mata haka yana nuna mata hanyar da tayi baya wacce take da rangwamen mutane da hayaniya ,”

   Ba musu ta bishi ,

  Suka fara tafiya sannu ,sannu ,  rabin hankalin sa baki ɗaya na ga inda take sanya kafafun ta , “

    Ɗan takaitatcen shiru ne ya biyo bayan fara tafiyar ta su ,”

   Kafin Hamza ya lalubo hirar da yake ganin zata fi armashi ga yakaka ,”

    Noori , ya ƙira ta ,”

    Wanne suna kike tunanin zamu sawa baby ?

     Yana hango lallausan murmushin da ya bayyana a fuskar ta da taimakon hasken fitulun bakin hanya, kafin ta ɗan sunkui da kan ta ,”

    Nima ban sani ba yaya dakta , kawai duk wanda ka zaɓar mata ,”

 

  Ɗan murmushi yayi kafin yace ai uwa ita ce mafi soyuwa ta zaɓarwa ƴaƴan ta suna ,

    Ni mata ta duk ita zata dunga zaɓarwa yaran mu suna , dan haka mu fara da wannan babyn , ki tuno suna mai kyau da asali a addini da za’a sa mata , “

  Kasaƙe tayi ita a dole tana son tuno da sunan ,!

     Mama ?

tace masa da sigar tambaya ,”

    Mama! 

shima ya maimaita yana kallon kwarar idanun ta ,”

    Eh

tace da shi tana sunkui da kai ,”1

Toh kin samar mata da laƙabi ,” ya furta hakan yana mai yi mata murmushin da ke bayyana sautin sa ,

    Ita ma ƴar dariya tayi , tana jin yadda farin ciki ke mamaye mata rai , kafi ta ɗan cije baki a hankali tace na gaji ,

    Yawata idanun sa yayi , nan ya hsngo wani ɗan tudun da aka yi da siminti a bakin hanya , domin zama ,

     Muje ki zauna a chan yace da ita ,

Ƙarasawa suka yi ta zauna shi kuma ya tsaya daga gefe ,” , ƙura ta taso tare da ƙasa ba shiri suka kare fuskokin su ,”

    Sai bayan da ta lafa ya mayar kallon sa kan ta ,” mask ɗin fuskar sa ya sanya hannu ya ƙunce , ” a hankali ya miƙa mata ,”

          Karɓi noori , ki saka ƙura tayi yawa ,” kar ya cutar da ke ,”

      Da hannu biyu ta karɓa , ta fara juya mask ɗin a hannu bata san yadda ake sawa ba ,”

       Fahimtar hakan da yayi , yasa yace mata yana mai kwatantawa da hannun sa,

    Haka zaki sa ,

  Sake juyawa shi tayi ta fara ƙoƙarin ɗaura shi ba dai-dai ba ,”

   Bani ki ga

  Ya zare mask ɗin daga hannun ta , 

Zagayawa yayi ta bayan ta ya daidaita mask ɗin a fuskar ta tare da ɗaura mata shi , dai-dai kan hamcin ta zuwa haɓar ta ,”1

STORY CONTINUES BELOW

    Ya dawo ya tsaya , yana kallon fuskar ta , suna haɗa ido ta sunkui da kan ta tana jin wani irin yanayi marar ƙarfi chan a gefen ran ta ,”

  A hankali ta motsa laɓɓan ta

  Nagode ,!

Bai amsa mata ba illa zura hannun sa da yayi a aljihun sa tare da kai kallon sa sama yana ganin yadda garin yayi jaa hazo ya lulluɓe sararin samaniya ,

Wani irin so da shauƙi mai ƙarfi yana fusgar sa bai ƙi ba suyi ta kasancewa anan daga shi sai ita ,

    Shiru suka yi na ɗan wani lokaci kowa da abun da ke saƙawa cikin ran sa ,”  ya katse shirun da cewa

   Zamu ɗan ƙara gaba ne ko mu koma gida ?

      Mu koma gida yaya dakta , da rahima bama nisan haka ,”

  Ok

  Yace da ita .

Suka kamo hanyar komawa gida suna tafe kakkarfar iskar juyin yanayi na shigowar Hunturu , na bugun su , rayukan su sun cika taf da mabanbanta tunaninnika ,!

*****

  Tun asubahin ranar juma’a Yakaka take jin ciwon baya da mara sai zirga-zirga take tsakanin banɗaki , ta gaza gane yanayin da take ji ,

   Misalin ƙarfe tara Rahima tayi shirin ta zata karbo result ɗin ta na SSCE ,

   Tayi musu sallama har tana tsokanar Yakaka ko zata raka ta ?

   Uhum tace tana yamutsa fuska saboda ji da take kamar ciwon na ƙaruwa ,

    Bayan fitar Rahima ya rage daga ita sai Falmata domin Hafsa ma tun bayan bikin Zainab ta tattara ta koma Hostel da zama baki ɗaya tana fuskantar jarabawar su ta ƙarshe ,

Doctor hamza kuma yayi kwanan asibiti , bai kai ga isowa gida ba ,

Karo na barkatai ta yunƙura da kyar ta tashi ta shiga banɗaki , sai dai a wannan karon ba tsugunno tayi ba wayar ta ta zaro daga cikin zanin ta ta kunna ta gami da fara neman layin samy baby tayi mata flashing ,

Tana addu’ar Allah ya sa ta tashi a bacci yanzu , domin wayar ma gaf take da kashe kan ta chajin ya kusan cimma ƙarshe ,

Ta kuwa yi sa’a  cikin ƙasa da mintuna biyu sai ga ƙiran samy baby ,”

Hello yaks ya Kike ?

Bani da lafiya anty samy bayana kamar zai ɓalle nake ji ,”4

        Miƙewa samy baby tayi daga kwance ,”

    Yaks ko dai haihuwar ce ?

  Da ƙyar take magana saboda ciwon da take ji yana sake tsungulin ta ,”

   Inajin ita ce anty samy  daman haka haihuwar take da ciwo ??

  Gintse dariyar da take taho mata samy baby tayi , sannu yaks , ki tabbatar dai bamu samu kuskuren aiwatar da nufin mu ba , yanzu zan je harabar asibitin da kike awun na tsaya da mota ta , na jira zuwan ku kin ji ko ?

   to

tace tana sauƙe wayar daga kunnen ta ,”

  Falo ta dawo tana cigaba da murƙususu , tare da nishi ƙasa-ƙasa

    Tsai Falmata tayi daga barin tilawar Al-qur’anin da take yi cikin suratu,”Duhaa,’

    Da sauri ta miƙe tana laluben inda take jiyo nishin Yakaka ,”

  Yakaka ,Yakaka , Yakaka ,nydan3 ? Aiyii waaz3n ? Manan3 Yakaka , Aiyii ? 

    Buguwar da tayi da kujera ta faɗi shi yasa Yakaka wacce take durƙushe daga bayan kujerar rarrafawa ta fito , tazo ta kama hannun Falmatan , wacce bata kula da zafin da ɗan yatsan ta yake ba wanda ya fashe yana tsastsafo da jini , “1

STORY CONTINUES BELOW

Bani da lafiya Falmata , yakaka tace da ita da wata ƴar murƴa chan ƙasa , tana mai zamewa ta kwanta gami da ɗaura kan ta akan cinyoyin Falmatan

Wani irin ciwo take ji marar misaltuwa tana jin kamar wani abu ya tokare ta , da zata iya zata sanya hannun ta zaro shi ,”

Ta gaza rarrashin falmata wacce ruwan hawaye ya ɓalle a idanun ta , tana iya hango tsoro tare da matsanancin firgicin da ya cika ƙwarar idanun Falmatan , nan take taji wani yanayi ya karci ran ta marar daɗi ,

A gajiye ya shigo falon bayan fitowar sa daga sashin mahaifin sa inda ya fara yada zango a tun shigowar sa gidan ,

   Tana maƙale a ran sa shiyasa ya gaza wucewa yaje ya kwanta ya huta kamar yadda gangar jikin sa ke muradi , sai da ya biyo domin ganin fuskar ta ,

       Nishin ta tare da sautin kukan Falmata ya fara ji kafin idanun sa su hango masa su a tsakanin kujera ,

da wani taku da yafi dacewa a ƙira sa gudu ya ƙaraso wajen , kallo ɗaya yayi mata ya fahimci halin da take ciki ,

  Rahima , da hafsa har ma da zainab waɗanda basa gidan su ya fara kwalawa ƙira , saboda ruɗewar ganin ta a ciwo , “

   Bai ƙarasa jin Falmata wacce take mar bayani cikin muryar kuka akan , su Rahima basa gidan fa ,”3

ya fita da gudu yayi sashin sa ya sanya mukulli ya buɗe , kai tsaye wardrobe ɗin da ya nufa ya ciro manyan ledoji ukun da suke ɗauke da tambarin ,”Today’s,’  da suke shaƙe da kayan haihuwa zuwa kayan baby da duk wani abun da za’a iya buƙata a yayin sabuwar haihuwa ya tanada ,hatta dogayen riguna biyu da mai jego zata sa a jikin ta bayan haihuwa , zuwa dogon wondo har da panties  duk ya saya ya adana , da babu wanda ya san hakan daga Allah sai shi ,,’2

Da gudu ya koma gidan bayan ya zuba kayan a bayan mota , Fatima kama ta mu tafi asibiti , 

   Toh

tace tana mai kamo Yakaka da kyar suka miƙe tsaye , , da kyar Yakaka take cira ƙafa jin yadda cikin ya dunƙule guri guda , baya da ƙugun ta kuwa , ta tabbatar sun ɓalle, bakin ta ya rufu gum , ba un ba un-un .

Da gudu ya jaa motar kasancewar akwai rangwamen ababan hawa ya sa basu ɗauki dogon lokaci ba suka iso asibitin yayi parking kusa da wata brown ɗin mota matrix,”

Da sassarfa ya shiga ciki , sai ga shi sun dawo tare da nurses biyu da wasu ma’aikatan asibitin su ma biyu ,

Suka kama yakaka suka ɗora ta akan wheelchair , suka tura ta zuwa cikin asibitin da matuƙar sauri , Doctor Hamza da Falmata suka bisu a baya da hanzari ,”

Duk abun da suke akan idon samy baby wacce take cikin motar da take gefen ta Doctor Hamza , ta riga su zuwa wajen kamar yadda ta al’ƙawar ta , sake gyara kishingiɗar ta a jikin kujerar motar tayi , cikin ran ta tana addu,”ar kome ya tafi yadda ta tsara ,!1

Da hawa gadon ɗakin haihuwa da haihuwar Yakaka duk abune wanda ya faru a tsakanin mintoci talatin ,”

Haka kuma baza ace anyi haihuwa a ɗakin ba saboda jaririyar kukan farko da tayi na zuwa duniya tun daga nan ta lalubi ɗan yatsan ta ta danna a baki tana tsotsa a hankali , tayi luf kamar mai bacci ,

Har aka ɗauke ta aka shige da ita wata ƴar kofa inda aka tafi duba lafiyar ta ,

Yakaka kuwa wacce take jin ta sawai kuma garau , tamkar ba ita bace wacce take jin ciwo kwatankwacin na mutuwa mintoci talatin da suka wuce , sai tsokanar ta tare da jaan ta da hira likitar da ta ƙarbi haihuwar ta take yi , tana kuma ƙara jinjina mata akan namijin ƙoƙarin da tayi wurin haihuwar , sam Yakaka bata da raki irin na wasu matan musamman haihuwar fari ta yadda za’a ji idan sun zi haihuwa suna ta faman ihu tare da sambatu marasa alfanu ,!2

STORY CONTINUES BELOW

Hankalin ta baki ɗaya baya ksn likitar , ys tafi ga son sanin ya suke akan tsarin su , ita dai babu wayar a hannun ta a halin yanzu bare ta kira samy baby , bata fatan ace shirin su ya ruguje domin ta riga ta ƙwallafa son cikar burin ta a ran ta , shiyasa take ƙoƙari gurin kaucewa duk wani abun da zai sa mata tarnaƙi ya sa ta fasa nufin ta , hakan ya sa ko jaririyar bata duba ba,  da tun da ta iso duniya bakunan nurses tare da likitar da ta karɓi haihuwar bai gajiya ba gurin faɗin “,Masha Allah , Tubarakallah ,” Tana jin yadda suke amfani da mabanbantan kalmomi gurin koɗa kyaun jaririyar , “

   Har ɗaya daga ciki take faɗin ita tun da take karbar haihuwa bata taɓa ganin mai kyaun wannan babyn ba Tubarakallah ,”

   

Likitar tana gama gyara ta da tabbatar da lafiyar ta , ta wanke hannuwan ta ta leƙa waje , inda  Doctor Hamza yake ta kai kawo Falmata kuma take zaune daga kan kujerar da aka tanada domin zaman jira ,”

  Yana ganin Doctor ta nufo shi shima ya ƙara taku zuwa wajen ta ,”

Da murna da fara’a take sanar da shi cikin harshen Turanci , matar sa ta haihu lafiya ta haifi kyakkyawar ɗiya mace , a halin yanzu bazai jima ba za’a fito da uwar zuwa ɗakin hutu daga bisani kuma idan an gama duba Lafiyar jaririyar za’a kai ta wurin mahaifiyar ta , “

Wani irin farinciki yake ji yana huda shi tamkar dai matar sa ce ta haifa masa ɗiyar sa da gaske bakin sa yaƙi rufuwa sai kalmomin godiya yake jerawa ga ubangiji, “1

Juyawa yayi lokacin da likitar take komawa ciki , ya nufo Falmata wacce bata kai ga fahimtar me suka tattuna shi da matar da ta ji tashin muryar ta ba ,”

  Kallon ta yayi yana aina ya zama dole ya samo mai taimakawa yakaka a halin yanzu da ya san jikin ta ba ƙwari ,kuma haihuwar farko ce tana bukatar wani babba a kusa da ita  Falmata , yarinya ce kuma miskiniya baza ta iya bawa yakaka taimako ba a wannan gaɓar ,”

   Amne ita ce ta faɗo masa a rai , ya lura tana son yaran musamman ma Yakakar , kusan koyaushe suka yi waya sai ta tambaye shi game da yaran , dan haka ya san baza ta ƙi ba idan ya nemi ta kula da yakaka ,”1

   muryar sa wasai yace da ita ,

      Fatimah , ki jira ni zan je na zo da Amne yanzu , Yayar ki ta haihu , kar ki je ko’ina ,

   bai jira cewar ta ba ya wuce da sauri yana duba agogo , saboda gudun lokacin juma’a ya shigo , “

ya bar Falmata da tarin farinciki cike fal da zuciyar ta , tare da son sanin a wanne hali yayar ta da jaririyar su suke ciki a halin yanzu??

samy baby tana ganin tashin motar Doctor hamza , da fitar shi daga asibitin ta fito daga cikin motar ta gami da gyara zaman hijabin kan ta bayan ta ɗauko wata babbar leda baƙa da flask ɗin ruwan zafi ta nufi cikin asibitin da ta riga ta zo shi sau dayawa ta yawata a ciki ta san kan shi tare da hanyoyin cikin sa ,”

Ta gaban Falmata ta zo ta wuce ta ƙarasa daf da kofar ɗakin haihuwar ta tsaya , tsayuwar mintuna uku tayi jal , aka buɗo kofar ɗakin gami da turo Yakaka akan kujerar ɗaukar marasa lafiya ,”

   kallon kallo suka yiwa juna kafin su sakarwa juna murmushin da yake bawa nursese ɗin tabbacin sanayya a tsakanin su biyun , Yakaka ta sunkui da kan ta ƙasa

  Ba tare da sun cewa juna ƙala ba aka cigaba da tura Yakaka samy baby na take musu baya suka zo suka gitta ta gaban Falmata dai-dai lokacin hawayen da suke idanun Yakaka suka fara sauka yif-yif , tana hango ƴan kyawawan kafafun falmata dusu-dusu , sakamakon ruwan hawaye da ya cika idanun ta ,

Aka wuce da ita zuwa ɗaKin hutun ,samy baby da sai da suka shiga ɗakin tayi magana ,”

   ta kama yakaka ta kwantar ta a kan gado tana ta faman jera mata sannu ,”1

STORY CONTINUES BELOW

   Sannu ƙanwa ta , sannu kin yi kokari ,!

   Ah tayi kokari sosai cewar nurse ɗin da take ƙoƙarin ɗaurawa yakaka  ƙarin ruwa ,”

    Ƙanwar ki ce ko ? Ina mijin nata ?

   ai ga shi kuna kama , farar fatar ku ɗaya , ki kula da ita zan je na zo da baby , ki haɗa mata tea mai kauri sosai !

    a jimlace samy baby ta amsa da

  Toh

  Lokacin da nurse ɗin take barin ɗakin ,”

  Tana fita samy baby ta miƙe ,

Tashi tashi mu tafi Yaks , bamu da isashen lokaci ,”

  Da wani irin yanayi a fuskar yakaka ta miƙe zaune lokacin da samy baby take cire mata ƙarin ruwan da aka maƙala mata ,”

   FALMATA

tace tana mai share ambaliyar ruwan hawayen da ya zubo mata ,”

  Meye haka yaks ? Zaki ɓata mana shirin mu ne ?

Anty samy Dan Allah ki bari mu tafi tare da Falmata ,

    No no no yakaka kar ki ɓata mana tsari idan kin  haƙura kin fasa zuwa wajen yarima ɗin ne ni sai nayi tafiya ta , daman taimakon ki zan yi kamar yadda na faɗa miki tun farko , shi yace na zo na kai ki gurin sa ,” idan kin fasa sai na koma na faɗa masa ke yanzu bakya son shi kin samu wanda ya fi shi ,

   share hawayen ta tayi da bayan hannun ta ,”

   Toh ki barni naje na faɗa mata kome , na faɗa mata kar ta damu zan je muyi aure da baban baby na dawo na ɗauke su ita da baby , bana son Falmata ta samu matsala sakamakon barin ta da zan yi ba tare da sallama ba , nasan zuciyar Falmata baza ta ɗauki rashi na irin haka ba , Falmata Bata da kowa bayan ni ,4

  mtss samy baby ta jaa tsaki lokacin da ta sunkuya ta ɗau ledar da ta zo da ita ,”

    yaks ni kin ga bari na tafi tun da duk tsawon lokacin da muka ɗauka muna tsara yadda kome zai kasance yau da ranar ta zo kin rusa kome da kan ki , sai kiyi ta zama , cikin rayuwar da gaba kaɗan zaki yi danasanin taɓa wanzuwar ki cikin ta idan kika haɗu da kaidi tare da masifar da take yanyame a cikin ta ,

  Ni kin ga tafiya , tace tana nufar bakin kofa ,”

Wani irin tsalle zuciyar yakaka take , auren Youssouf babban nasara ne tare da cikamakin duk wani farin ciki na rayuwar ta ,”

   Ki tsaya anty samy , na YARDA ZAN BIKI KI KAI NI WURIN BATURE KAM SULUM ,”3

  Wani shu’umin murmushi samy baby tayi kafin ta dawo cikin hanzari ta buɗe ledar hannun ta tare da zaro wasu manyan hijabai har ƙasa guda biyu ,

     Ta zurawa yakaka ɗaya ita ma ta sauya na jikin ta ta kamo hannun yakaka , wacce duk take a ruɗe a gigice , cikin rasa gane takamaimai a yanayin da take ciki , “

   ki saita tafiyar ki mai kyau kin san ta gaban a ɗakin haihuwar zamu zo mu wuce  , samy baby tace da ita haka lokacin da suke barin ɗakin ,”

  

    Ta gaban ɗakin haihuwa suka wuce da ya kawo su har gaban Falmata wacce take zaune jugum har lokacin idanun ta kafe guri ɗaya ,” duk jikin ta yayi sanyi haka kawai take jin bugun zuciyar ta na sauyawa tare da tsikar jikin ta da take ta tashi akai akai , kwalla na taruwa a gurbin idanun ta ,

   Da hannu Yakaka ta toshe bakin ta domin hana kukan da take yi fitowa sarari yayin da ta runtse idanun ta gam ,  da taimakon hannun ta da samy baby ta matse tsam suka wuce ta gaban falmata ,

    Wucewar su ya zo dai-dai da zubowar ƙwallar idanun Falmata , sannan kunnen ta na jiyo mata tamkar takun kafafun Yakaka suna nisa da ita ,”

    Yakaka ki fito na gan ki

   ta furta a sarari , tana mai saita idanun ta inda kamar take jiyo takun kafar Yakakar

Sun kusa fita a kan doguwar hanyar suka tsinkayo kukan jaririyar da ya karaɗe wajen ,

     Chak yakaka ta tsaya ,

A sarari ta furta MAMA , tana mai waigawa da sauri , daga inda take tana hango jaririyar a naɗe cikin wani ɗan kyakyawan baby pink ɗin mayafin da aka naɗo ta ciki , sai wutsil wutsil take da hannu , ga alama hakurin ta ya ƙare ,tana neman abincin ta

idanun ta ta sauke akan Falmata wacce ta kafe hanyar da suke da ido , idan ba gizo idanun ta ke yi ba tana iya hango kyallin hawaye a idanun falmata ,

Wani abu ta ji ya yanki zuciyar ta , cikin ta ya ƙarta , ta ji kamar ta zura da gudu , ta rungumi waɗannan bayin Allah guda biyu da take shirin bari cikin maraici ,”

   bata yi aune ba ta ji samy baby ta fusgi hannun ta lokacin da ake shigewa da babyn hanyar ɗakin da aka bata , Falmata tana mai juyar da kan ta inda take jiyo tashin kukan jaririyar da take jiyo shi da wani yanayi mai girma da yake huda zuciyar ta yana taɓo ƙasan ran ta,”

Da wata irin dusashiyar muryar da kuka yaci karfin ta take kiran sunayen su su biyu lokacin da samy baby take jaan hannun ta zuwa gurin motar ta ,”1

  FALMATA , MAMA ,

Tana zuwa ta buɗe mata gidan baya da taimakon ta ta shiga , ta zagayo ta buɗe mazaunin direba ta shiga , tana jin yadda tata zuciyar ma take yin rauni da matsanancin tausayin rayukan da yake lulluɓe ta ,tana tuhumar kan ta Anya Anya kuwa ita SAMIRA ta kyauta ???2

Da gudu ta bar hsrabar asibitin ta fito kan babban titi , ta miƙa hanya sosai ta nufi kwadaben barin gari , kasantuwar daman da shirin ta tsaf , sai kawai ta ɗaɗɗaga gilasai lokacin da ta hau kan babban titin da ya nausa ya nufi wajen gari , sashi na ran ta na ƙarfafar ta akan ƙudirin ta ,

a hankali yakaka ta sauke hijabin da ta ja ta rufe fuskar ta baki ɗaya da shi ta ɗaura jajayen idanun ta da suka rine suka kumbura hatta fuskar ta tasa ta saita ganin ta akan titi tana kallon manya bishiyoyi da ƙananun dazuzzukan da suke kusa da gari ,”

zuciyar ta na wani irin ƙuna , ƙuna mai tsanani , tana jin ta empty , tana jin ta kamar tana kan guguwa tana walagigi da ita tana jin tamkar ta rasa kome da kowa , tana jin tamkar tayi KUSKURE MAFI GIRMA A RAYUWAR TA .!2

A hankali ta maida kan ta jikin tagar motar ta kwantar tare da runtse idanun ta , zuciyar ta na dawo mata da hoton Halin da ta bar FALMATA DA MAMA a ciki , kunnuwan ta na amsa kuwwar kukan JARIRIYAR TA …4

WAI

    Wai

       Wai2

Assalamu Alaykum kowa da kowa , ina gaishe ku tare da fatan Alheri , nasan kun yi dogon jira na tsawon sati biyu cif yau ‘ da fatan zaku dunga min uzuri , domin da ace ɗaya daga cikin ku ya san tarin aiyukan dake jibge akai na wallahi da babu mai yin ƙorafin rashin ganin cigaba akai akai ,

duk da haka zan ji daɗi idan ku ka cigaba da min uziri , ɗan adam a koyaushe yana buƙatar ɗaga ƙafa tare da bada dama !!1

  Nagode kwarai da yadda ku ke bibiyar rubutuna , tare da ku da taimakon ku rubutun har ya miƙa ya haka ,, ina fatan zaku cigaba da bibiya ta har mu cimma matsaya ,”1

kofar shigar da ƙorafi ko gyara tare da ra’ayoyi a buɗe take a gare ku , kai tsaye zuwa gare ni , zan ji dadi kuma zan yi amfani da shawarwarin ku muddin bai saɓawa ainahin tubalin ginin labarin ba .1

  Nagode !

  Da sauri Doctor Hamza yake tafiya ,” Amne na bin bayan sa , lokacin da suke kutsawa cikin asibitin , bayan sha da kyar da suka yi a cikin cinkoson ababen hawa da ya fara haɗuwa akan titi sakamakon kusantowar lokacin sallar juma’a ,”+

Sai dai tun da ya dosa bakin ɗakin haihuwar taron mutanen da ya gani kama daga likitocin asibitin zuwa kan nurses da securities ya sa shi rage takun sa ,”

Maganganun da ya ji suna faɗa cikin harshen turanci tare da kama sunan AMINA DILMARI shi yasa shi zabura ya kutsa tsakanin su ,

What’s happening/ Me yake faruwa ?

yace da su cikin wata irin muryar ,

Calm down sir , Babban likitan da asibitin yake mallakin sa yace yana kamo kafaɗun doctor Hamza ,

Muje office muyi magana ,” zame kafaɗun sa doctor Hamza yayi lokacin da yake fuskantar likitan ,

Ina patient ɗina ? Yace da buɗaɗɗiyar murya , “

Shiru likitan yayi ,”

Wani irin bugu zuciyar Hamza take kamar zata fito waje ,” kasancewar sa cikakken likita yasan yanayin da suke yi a duk lokacin da suke son sanar da mutanen marar lafiya wani mummunan labari game da marar lafiyan su,!

Ta mutu ?

Ya tambaya yana jin yadda zuciyar sa ke matsewa da tasowar ɗacin kalmar har akan harshen sa ,”1

Da sauri likitan yace

Bata mutu ba amma zai fi kyau idan muka je nayi maka bayani a nutse.

A sanyaye Doctor Hamza ya bi bayan likitan bayan ya nunawa Amne wurin zama a gefen Falmata wacce tayi zugui idanun ta sun yi jaa sakamakon hawayen da take ta gogewa kan rashin sani halin da ƴar uwar ta ke ciki har kawo wannan lokacin ,

Mun rasa gane yadda akayi ko dalilin da yasa matar ka tare da ƴar uwar ta suka bar asibiti kuma suka bar ƴar jaririyar ta ba tare da mun sallame ta ba , sannan Alamu suna nuna kai ma baka san sun tafi ba ,”

Ɗan tsayirtawa likitan yayi yana nazarin fuskar doctor hamza wanda yayi saƙare yana kallon sa , kamar dai bai kai ga fahimtar bayanin da yake masa ba ,” ɗan ƙwanƙwasa bakin biron hannun sa yayi akan ƴar takaddar gaban sa,”

Idan har an tabbatar tana gidan zamu iya sallamar ku tare da jaririyar domin ayi gaggawar sadata da mahaifiyar ta domin ta shayar da ita nonon farko ,”

Cikin jirkitattacen kallo Doctor hamza yace wacece ta gudu tare da ƴar uwar ta suka bar jaririyar ?

Tamkar dai sam bai ma fahimci bayanin da duk likitan nan ya masa ba ,”

Ba kai ne mijin AMINA HAMZA DILMARI BA ?

Maimakon ya amsa sai ya miƙe tsaye ,

Kana nufin ita ce suka gudu tare da ƴar uwar ta ?

A taƙaice likitan yace

Haka muke zato domin an duba duk inda yakamata cikin asibitin nan ba’a gan su ba , sannan masu tsaro/securities sun tabbatar mana da sun ga fitar mata biyu farare sanye da hijabai sun hau…..

Ankarar da yayi doctor hamza ya juya daga ofishin ya sanya shi miƙewa ya biyo shi ,

Wurin da ya bar Amne da Falmata nan ya dawo ,”

Fatimah , kun haɗu ke da yayar ki ?

Da sauri ta ɗago kan ta !

Bamu haɗu ba Yaya dakta har yanzu ba’a kai ni inda suke ba ita da baby , ko basu da Lafiya ne ? Dan Allah ka kai ni wajen su ,’!

Wani gumi yaji yana tsatsafo masa daga illahirin ƙofofin gashin jikin sa ,”

Amne ta taso ta matso kusa da shi ,”

Ina mai jegon ne ?

wai ba’a gan ta ba yace da wata irin murya chan ƙasa , Amne dake kusa da shi kaɗai ta iya jin mai yace

Wanne irin ba’a gan ta ba inji amne ,’

Lokacin da likitan ke sake ƙarasowa tare da wasu nurses da wasu securites ,

Kuyi haƙuri sir , a fara duba gida ko suna chan , domin tare da ƴar uwar ta suka fita ,”

Wata kakkarfar tsawa doctor hamza ya yiwa likitan ,

Ka daina cewa tare da ƴar uwar ta suka fita , “

Ga ƴar uwar ta nan , ya juya yana nuno musu Falmata wacce ita ma ta miƙe tsaye tana rarraba ƙwayar idanun ta da son sanin meke faruwa?

Ita kaɗai ce ƴar uwar ta , ya zama dole ku nemo ta , ba gudu tayi ba sace ta aka yi , Yakaka baza ta gudu ta bar Fatimah ƙanwar ta ba baza ta gudu ta bar baby mama ba , noorie baza ta min haka ba , ya ƙarashe da rawar murya yana jin yadda zuciyar sa ke cika da tsoron tabbatuwar hasashen mutanen asibitin ,”

STORY CONTINUES BELOW

Sir kayi haƙuri amma matar ka ba sace ta aka yi ba ita da ƙafafun ta suka fita tare da wacce tace sister nata ce , bayan tafiyar ka matar ta zo , tanan muka wuce da ita , wannan yarinyar da kace ita ce ƴar uwar ta tana zaune a wajen bata nuna ta san yarinyar ba basu mata magana ba su duka biyun , sai da muka je ɗakin , suka yi magana , kuma lokacin da nake fitowa da baby domin kai ta wurin mamar ta naga bayan wasu mata biyu suna fita , ina hasashen su ne , domin su ne kaɗai matan da aka ce an gani sun fita da hijabi tsukin awannin nan ,” ka zo ma na nuna maka shaidar flask ɗin ruwan zafin da matar ta kawo , har yanzu yana ɗakin !,

Cewar wannan nurse ɗin da ta kai yakaka ɗakin hutuwa ,”

Bai ce ƙala ba ya bita a baya zuwa ɗakin , anan ya tadda flask ɗin da ta ambata tare da wata ɓakar leda da sauri ya ɗauki ledar ya buɗe ,

Babu kome a ciki sai hijabin yakakar wanda ta zo da shi asibitin ,” hajabin da yayi wa farin sani domin shi da kan sa ya saya mata su guda biyar mabanbantan launika .

Shiru ne ya ratsa ɗakin ,”

Doctor hamza yayi shiru kan sa a sunkuye da alama ya zurfafa cikin tunanin me yake shirin faruwa ne ? Da gaske ta gudun ne ? To meyasa zata yi haka ?Anya tana cikin Hankalin ta ? Ko dai gida suka koma tare da RAHIMA ? Idan ba haka ba yaran wa suka sani ? Ina za ta ? Basu da kowa ƴan gudun hijira ne .

Ina baby ??

Da sauri babban likitan yace a je a zo da baby , yana fatan Allah ya sa wutar masifar da take son kunnuwa masa a asibiti kar ta kai ga ruruwa har ta ɓata masa sunan asibiti .

Nurse ɗin ta dawo tare da Baby wacce ɗumin tsaftatatcen ruwan da aka cika mata ciki da shi ya sa ta fara bacci ,”

Miƙa masa ita aka yi ya karɓe ta , bai ce ƙala ba ya jiyo ya fito daga ɗakin ,”

Wajen da ya bar Amne da Falmata nan ya dawo

Mu tafi gida yace da su ,!

Ita Yakaka ta koma gida ne ? Meyasa ta tafi ta bar baby wanne irin shirme ne wannan ?

cewar Amne ,

Yaya dakta Ina yakaka ɗin ? Bata da lafiya ne ?

Shiru yayi bai amsa musu ba , ya tsinci kan sa cikin ruɗani ,

Kai tsaye gidan Amne ya nufa da su , Amne riƙe da jaririya tare da Falmata suna baya a zaune shi kuma yana jaan motar ,”

Takamaimai bai san tunanin me yake ba , abu ɗaya ne yake fata , shine ya je gida ya tadda ta tara da Rahima sun koma gida , wani tsoro-tsoron tabbatuwar bata gidan ya sa shi kin ɗaga waya ya ƙira rahima yafi so yaje gidan da kan sa ,”

Ku shiga gida Amne zan je na duba ta wataƙila sun koma gida ita da Rahima , ya furta hakan ba tare da ya bari sun haɗa ido da Amne ba wacce take kallon sa

Wai me su likitocin suka ce maka ne ? Cewa suka yi sun tafi gida ita da rahima ?

Waigowa yayi ya dube ta , da hannun ya nuna mata Falmata tare da yi mata Alamun roƙon tayi shiru ta bar maganar tukun , ” duba da yadda a halin yanzu ma Falmatan duk a hargitse take tunda suka hau motar bata ce uffan ba sai faman share ƙwalla take tana jaan hanci ,”

Fita yayi ya buɗe mata kofar motar ,

Amne bata sake magana ba ta kamo hannun Falmata suka fito tare da jaririyar zuwa cikin gidan ta ,”

Komawa yayi cikin motar ya zauna ya ɗora hannuwan sa bisa kan Steering motar yayi shiru , zuciyar sa na kai kawo ,”

Ƙwanƙwasa gilashin motar da aka yi shi yasa shi ɗago kan sa ya sauke akan matashiyar yarinyar da ke tsaye a jikin motar sa ,”

Murmushi tayi masa ya ga lokacin da bakin ta ya motsa alamun gaisuwa ,”

Gyaɗa kai yayi kafin ya juyar da kansa ya fara ƙokarin tashin motar ,”

Zaton sa irin ƴan matan unguwar ne take gaishe sa ,”

Ƙara ƙwanƙwasa motar tayi da ɗan ƙarfin ta , tana masa magana ,”

Tsaki ya jaa mai sauti kafin ya sauke gilashin motar ,”

Kalaman ta suka doki kunnuwan sa da yasa ba shiri ya zuro kafafun sa wajen motar gami da miƙewa tsaye ,”

Me kika ce ?

Ɗan matsawa tayi baya kaɗan tana wani guntun murmushi tace

Yakaka ce ta aiko ni , tace na sanar da kai ita ta tafi Abuja wajen Baban Ƴar da ta haifa domin a ɗaura musu aure , dan haka kar ma ka sha wahalar neman ta bayan auren su nan da watanni kaɗan idan sun gama moneehmoon zata dawo kuma tace wai……

Marin da ya kwashe ta da shi ya hana ta ƙasara zancen ta ,sai da tayi taga-taga ta sunkuya , tana ɗagowa ya sake ƙara mata wani ,”

Shoƙo gelen wuyan ta yayi ya maƙure ta , “

Ina kuka kai ta ? Ke da su waye kuka haɗa baki kuka sace ta ? Zaki nuna min inda take ko sai na sada ki da jami’an ƴan sanda sun lallasa ki ,”

STORY CONTINUES BELOW

Idanun YAGANA sun fiirfito tace wallahi gaskiya nake faɗa , yakaka ƴar uwa ta ce tare muka zo garin nan , tun a sansani muke tare , cikin shege tayi madam ɗin da muke yiwa aiki ta kore ta , shine yanzu bayan ta haihu suka haɗa baki ita da uwarɗakin ta ta gudu zata koma wajen shi suyi aure ,”

Angaje ta baya yayi ,”

Ƙarya kike yi ,”ƙarya ne noorie ƙaramar yarinya ce bata isa shirya wannan wasan ba , ban yadda da ke ba , dole zaki faɗi gaskiya idan kika ji duka a wajen hukuma , wayar sa yake ƙoƙarin zarowa lokacin da ya ji tace ,”

Idan ƙarya nake bari na ƙira uwarɗakin nata ka ji muryar yakakar ma wallahi ,”

Bata saurari amsar da zai bayar ba ta danna ƙiran number samy baby bayan ta saka wayar a hands free , wacce daman jiran ƙiran yagana take , “

Dan haka ta rage gudun motar tare da gangarawa gefen hanya tayi parking sannan ta ɗauki wayar ,

Hello Doctor tace da shi , bata jira amsa sa ba ta juya harshe zuwa turanci ,”inda take cewa

Nasan zaka yi mamakin yadda abubuwa suka faru , wanda a zahiri ba wani abu bane na ban mamaki duba da yadda idanun ka suka makance basirar ka ta toshe , zuciyar ka kuma ta mace akan son yarinya yakaka , ita ma haka tata zuciyar ta mace , ta samu toshewar basira tare da makancewa cikin son wanda zuciyar ta ta zaɓa har ma ta daɗe da mallaka masa ruhi tare da gangar jikin ta baki ɗaya , ” ba wani bane wannan illah uban ƴar ta wanda soyayya ta sa ta bashi kan ta , har kuma ta zaɓi rabuwa da ƴar ta tare da ƙanwar ta saboda ta tsira da shi , kana mamaki ko ? Ko kuwa zato kake ƙarya ne ,” tunanin ka shiri ne koh ? To bari ka ji kasan daman waƙa a bakin mai ita yafi daɗin sauraro ,”

Juya harshe tayi ta dawo hausa ,

Yaks ,

Yaks ,

Ke yaks

A hankali ta ɗago kan ta da yake bala’in sara mata ta kalle ta da idanun ta da suke cike taf da hawayen tausayin kai ,” duk da daman tana jin ta tana waya da turancin da ba fahimtar sa take ba , ba bacci take ba ,

Na’am anty samy ,”

Ga Yariman naki ko kuwa me ma kike ƙiran masoyin naki ??

Cikin sanyin muryar tace Bature kam silum ?

Eh shine akan wayar riƙe kuyi magana ,”

Anty samy kice masa kawai ina zuwa zan zo wajen sa zaki kawo ni , bana jin yin dogon magana , zuciya ta ciwo take min ban san a wanne hali Falmata take ciki ba ,”

Cije baki samy baby tayi tana hararar yakaka da ta lura tana son ɓata mata shiri ,”

Bana son kinibibi bake kika yadda zaki wajen nasa ba ko na mayar ki ne ?

Shiru tayi bata ce e ba ko a ah

Karɓi wayar ki masa magana ya ji ki ,”

Alo Bature kam silum , gani nan zan zo wajen ka , anty samy zata kawo ni , amma gobe nake so mu dawo mu ɗauki su Falmata da mama , sai muyi aure mu zauna tare da su Dan Allah bazan iya zama babu su ba ina son ku ku duka sosai ka yadda koh ?

Ƙarɓe kan wayar samy baby tayi tana murmushin nasara , ta koma turanci

Sauran ƙarin bayanin da zai iya gamsar da kai yana cikin kayan ta tare da wayar ta da ta bari a gidan ku , da fatan zaka rungumi haƙuri , ka nemo matar da zata iya mallaka maka ruhin ta tare da sadauƙarwa irin wanda yakaka tayi ga masoyin ta ,” idan kunne yaji …. ? Tace da shi tana sauke wayar a kunnen ta tare da latse ta ta kashe ta tada motar tana fincikar ta da ƙarfi ..

Tun kafin ta gama furto zantukan ta yake jin wani abu mai kama da hayaki yana lullube masa zuciya wani irin ƙaƙƙarfan kishi da tsanar yarinyar suka tarwatsa masa rai da ya sa jin kan sa na juyawa , tabbas ta yaudare shi , yaudara mai girma , ta ha’ince shi ta kuma butulce masa ,”

Amma anya , toh Anya gaskiya ne anya ba tursasa noorie aka yi ba ,! Anya tana da wayo tare da hikimar yin mummunar yaudara irin haka , sashin zuciyar sa da soƴayyar ta tayi ƙarfi ta kafa rassa ke son kawo uziri ke son bata kariya ke son wanke ta , ke son fidda zargi a tsakani ,1

Bai bi ta kan yagana ba ya faɗa cikin motar sa ya jaa da ƙarfi gami da nufar gida domin ganin shidar da aka ce akwai ,

Gyara gelen ta tayi wanda ya cukurkuɗe , kafin ta ce

Wannan Banzan har mari na yayi akan wata banzar sokuwar yakaka , oho dai a yau zan yi kwanan farin ciki sanin cewa yakaka tayi nisa da garin maiduguri baki ɗaya , ” babu ranar dawowa !

STORY CONTINUES BELOW

Kai kuma marin nan wallahi bashi ka ɗauka , zan rama shi ta wata hanyar da baka yi zato ba a kuma lokacin da baka yi tsammani ba ,

Wucewa tayi ta kutsa cikin unguwar da daman take ta su , tana hararar gidan Amnee inda take da tabbacin ciki jinin Yakaka suka yi bigire ,”

Cikin ran ta ta fara saƙa da mummunar zaren da zai iya zargewa har da ita ,”

Kusan da gudu-gudu ya shiga sashin su Rahima bai ko tsaya rufe ƙofar motar sa ba ,”

Rahima , Rahima , Rahima yake ƙwalawa ƙira ,

Da gudu ta fito daga ɗakin ta tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwalin ta ta shirya tsaf domin zuwa asibitin wajen su Yakaka , jin shirun yayi yawa tun hantsi har ga shi ƙarfe uku ta ƙarato.ta tabbatar zuwa yanzu ta haihu ,”

Na’am big bro , ina su Yakaka ya jikin nata ? Ta haihu ,? Me muka samu ?

Ina wajen kayan su yake ? Yace da ita haka idanun sa sun kaɗa ,”

Kayan su wa ?

Fatima .

yace da ita

Wani abu zan ɗauko maka ? Me zan ɗauko maka big bro ta haihu ko ? Me ta haifa ?

Ina wajen kayan su nace miki , ya daka mata tsawar da ta firgita ta ,

Da hannu ta nuna masa ɗakin su

Yana cikin wardrobe ,

Kayan yayar fatima nake nufi

Duk kayan su a haɗe suke big bro , ta furta hakan tana karya wuya , ran ta cike taf da jimamin abun da ya hatgitsa musu ɗan uwa haka ,”

Watsi yake da kayan su yana hautsinawa , har zuwa lokacin da idanun sa suka sauka kan ɗan ƙaramin hoton tare da agogo haɗi da damin kuɗin niger da suke chan ƙasan kayan ta ,”

Zuciyar sa na bugawa ya ɗauki ƙaramin hoton fasfo ɗin gami da kai idanun sa kan fuskar kyakkyawan bamarɗen ingarman saurayin da bai fi sa’an sa ba jikin sa sanye da kakin soji na ƙasar niger , hoton a zamunance yake babu wani alamun tsufa ,”

Tabbas shine ba tantama kome gaskiya ne , ya aina haka cikin ran sa lokacin da yake sake jujjuya agogon da rannan ya gan shi a hannun ta , tace masa na BABAN ta ne , tunowa yayi da ranar da ta nace ya kai ta bakin kasuwa , tace cikin kayan ta akwai hoton BABAN ta , ashe duk ƙarya take masa , ashe yaudarar sa take , ashe ganin yarinya ƙarama yake mata ita kuma tana masa kallon soko ?

Sakin hoton yayi tare da agogon suka faɗi ƙasa kan suturun ta da ya saya mata ya fara taku da nufin barin ɗakin

Lokacin da ya ji kafafun sa sun sauka akan ƴar ƙaramar wayar da take jefe a ɗakin , sunkuyawa yayi ya ɗauka ,

Ya kunna ta ,

Call logs ya shiga nan ya ci karo da number da aka rubuta HUBBY BB a jikin ta ,

Bi ya dunga yi yana ganin yadda suke ƙiran juna ita da number kusan kullum sai sun yi waya , ” tun wajen wata guda da ya wuce , ” ji yayi idanun sa na shirin kawo hawaye , a sarari ya furta ta yaudare ni , BATA SO NA BATA TAƁA SO NA BA ,”

Jefar da wayar yayi yana barin ɗakin cikin ran sa yana tunano irin baya-baya da take yi da shi a tun haɗuwar su , yadda take janye jiki daga mu’amala da shi , yadda baya ganin fara’ar ta , bata sakin jiki tayi magana da shi , bata ɗaukar sa da wani muhimmanci ,

ashe bata son shi ne , ashe tana da wanda take so suka yi soyayya mai girma da har ta kai su ga aikata zina , ashe shiyasa take son cikin jikin ta kamar ba shege bane , soyayyar uban cikin ne ta shafi ɗan , ashe son da take yiwa wannan mutumin ya wuce son da take yiwa ƴar cikin ta tare da ƴar uwar ta ?? Tunowa yayi da kalamar ta ta ƙarshe inda tace TANA SON SU SU DUKA ,” ji yayi duk wani jijiyar da ta kafa so da ƙaunar ta cikin ran shi tana tsinkewa , son ta da ƙaunar ta suna mutuwa ,”

Bai san ina yake taka ƙafafun sa ba saboda yadda zuciyar sa ta shiga ruɗani , sai tsintar kan sa yayi a tsakiyar falon Baban su ,

Ɗago kan sa professor Mustapha Dilmari yayi ya dube ɗan nasa , tashin hankali da damuwar da ya hango a fuskar ɗan nasa ya sanya shi ajiye doguwar jaridar “daily trust” ɗin da ke hannun sa ,” yace da shi

Doctor yaya yarinyar nan ta sauka lafiya ?

motsa bakin sa yayi maƙogoran sa na kai kawo , ya haɗa jimlar kalmar da ta tabbatu ta fito tun daga Ƙasan ruhin sa ,

TA MUTU

STORY CONTINUES BELOW

innalillahi wa innaa ilaihi raji’oon , ta rasu ,? Wajen haihuwar ? Allahu Akbar , yi sauri ka sanar da jama’a a zo ayi mata sutura , ina abun da ta haifa ko tare suka tafi ,? “

An mata sutura a chan asibitin kamar yadda aka saba yiwa ƴan gudun hijira ƴan uwan ta idan sun rasu ba’a jiran mutanen su ,”ma’aikatan asibiti tare da sauran Al’ummar musulmai suke sallatar su a wuce da su makwancin su ,,”

Daga haka ya miƙe ya bar mahaifin nasa yana jero addu’o’in da ake yiwa mamata ,

Bai jin yayi kuskure akan kalmar da ya furta ga mahaifin sa , ƙwarai ta MUTU a cikin zuciyar sa kamar yadda cikin kowanne daƙika ɗaya yake sake yakice ta tare da nesanta ta da duniyar sa nisa irin na har abada ,

Shi yayi ƙarya ga mahifin sa da ƴan uwan sa , ya wanke ta ya rufa mata bargon asiri tare da kyautata mata zato da kyakkyawar niyyah, yanzu da kome ya bayyana gare shi ya fahimci wacece ita , dan haka ya sake yin wata ƙaryar da yake fatan ta zama babbar ƙarya ta ƙarshe da zai yi a rayuwar sa yayi amfani da ƙaryar ta hanyar zare ta daga rayuwar duk wani da ya shafe shi tare da shafe babin ta cikin rayuwar duk wani nasa domin ita ɗin bata chanchanta ba …

Shiru shiru Amne bata ga dawowar hamza ba da take tsumayen ganin sa tare da yakaka tayi ta ƙiran wayar sa shiru ba’a ɗauka

Ga kuma baby da take ta faman tsanyara kukan yunwa duk da cewa tun shigowar su ta ɗaura ruwan zafi ta wanke jaririyar tas ta sauya mata kaya tare da diaper a cikin kayayyakin ta da suka zo da su daga asibiti , amma daga lokacin da aka haife ta tun hantsi zuwa yanzu la’asar sakaliya dole jaririyar ta ji mummunar yunwa ,

Gefe guda ƙarin damuwar ta na ga Falmata wacce tun tana kuka ƙasa-ƙasa , zuwa yanzu kuka take riris tana ambaton sunan yakakar babu tsahirtawa , tayi rarrashin duniyar nan Falmata taƙi shiru , taƙi ci taƙi sha , sallah ma sai da tace ta tashi tayi addu’ar Allah ya sa yakaka na a halin lafiya sannan ta tashi tayi ,

Ganin dare na neman yi babu abun da zata bawa ƴar jaririyar nan ya sanya ta rufe kai ta nannaɗe jaririyar da kyau ta ɗau kuɗi mai ɗan yawa ta fita nemo mata abinda zata ciyar da ita da shi ,” kasantuwar a kusa da kasuwa unguwar tasu take , dan haka bata sha wahala ba wurin samun madarar jarirai mai kyau tare da feeding bottle a ɗaya daga cikin shagunan da suke jikin kasuwa wanɗanda basu kai ga rufewa ba ta saya , ta tsallako titi zuwa gida,

Wurin da ta bar falmata nan ta tadda ta zaune kan ta haɗe da jikin bango ,

Bata bi ta kan ta ba kamar yadda falmatan ma bata nuna taji motsin ta ba , ta kwantar da jaririyar ta wanke feeding bottle ɗin ta haɗa mata madarar dai-dai yadda aka ka’idance da ruwan ɗumi , ta ɗan bar ta ta huce dai-dai yadda jariri zai iya sha ta ɗauke ta tayi bismillah , ta fara bata ,

Nan take kuwa ta kama bakin feeder tana jaa ,

Sannu sannu sai da ta sha fiye da rabi , bacci ya ɗauke ta ,

Ganin ta maida kan falmata bayan ta shinfiɗe jaririyar ,”

Tausayin falmatan ya tsarga mata , cikin ɗan zaman da tayi da yaran lokacin bikin zainab ta fahimci yadda yaran suka shaƙu da juna suke kuma ƙaunar juna tare da tattalin juna ,

Ɗan ƙaramin tsaki ta jaa lokacin da take ɗaukar wayar ta domin sake ƙiran Doctor Hamza ,

Ni ban san ina ya bar wayar ba haka , ina ta ƙira baya ɗauka ya bar mu cikin fargabar halin da yarinyar nan ke ciki bari na ƙira Rahima naji ko yana gidan ne ,”

Bugu ɗaya Rahima ta ɗauka ta ɗauka

Abnaty ina yayan ku ne ? yaya an san inda yarinyar nan ta tafi kuwa ?

Shiru Rahima tayi tana ƙoƙarin tsayar da ƙwallar idanun ta ,”

Yayan mu ya dawo tun ɗazu hankalin sa a tashe , ya shiga sashin sa ya kulle , sai yanzu da naje gurin Baba , yake sanar da ni wai ashe yakaka ɗin ta rasu ne wajen haihuwa ,”

Innalillahi wa inna ilahi raji’oon Amne ta ƙara da salati ,

Bata ce kome ba ta sauƙe wayar daga kunnen ta , tare da kai kallon ta ga falmata wacce tayi kasaƙe tana son fahimtar menene ,:

Muryar ta ƙasa tace Amne wai me Rahima tace ? Wani abu ya samu yakaka ko ? Amne Dan Allah kar ki ɓoye min ni da yakaka bama boyewa juna kome , yakaka ita ce kome na , ita ce mama na , baba na yaya ta kuma ƙawa ta meye ya same ta ? Dan Allah ku kaini na gan ta ,

ta furta hakan tana me sake fashewa da wani sabon kukan da yasa hawaye silmiyowa bisa ƙuncin ta , tana jin wani tsohon miƙi makamancin raunin da zuciyar Falmata ke ciki yana ɗanyencewa cikin nata ran , amsa kuwwar kalmai makamanta wannan da suka fito daga bakin Rahimar ta yana maimaituwa a kunnuwan ta ,”

STORY CONTINUES BELOW

Sai ta gaza rarrashin Falmatan .

Washegari

Bayan fitowar doctor Hamza daga masallacin sallar asubah kai tsaye sashin mahaifin sa ya shigo kamar yadda ya saba , kan shi a ƙasa suka gaisa da mahaifin sa wanda yake nazarin ɗan nasa ba tun yau ba ya fahimci akwai wata ɓoyayyar manufa a zuciyar ɗan nasa game da yarinyar ya bari ne yaga iya gudun ruwan sa , amma tundaga yadda ya ɗau komen su da muhimmanci ya fahimci yana da ra’ayi akan ɗayar su ,”

Tausayin sa ya ji mutuwar yarinya da irin birkicewar da yayi ya sashi fahimtar wataƙila ita zuciyar sa ke ra’ayi

Addu’a ya sake yi masa sannan ya ɗora da tambayar sa ina ƴar uwar ta ?

Nan yayi shiru ,

Kafin yace

Suna gidan Amne ita da jaririyar da uwar ta bari ,

Nan take fuskar professor ya sauya

Gidan Amina ?

Me kuma ya kai su gidan Amina ?

Na kai su ne wai dan ta kula da su musamman ma jaririyar .

Ita Amina MACE ɗin ce za’a bawa kulawa tare da tarbiyyar yara mata har biyu ? ? To ban amince ba maza idan gari ya gama haske kaje ka zo da su , tunda ka kawo yaran nan gidan nan ikon su ya bar hannun ka ya dawo ƙarƙashi na , ni nake da ikon kulawa da su , nima ina ƙwaɗayin samun ladan rikon marayu da marasa galihu , kan Ji na ko ?

Toh Baba

Ya amsa yana jin wani sabon tirniƙin ɓacin rai na taso masa sam sam baya son wani abu ya sake haɗa shi da kome ƙanƙantar abu wanda ya shafi yarinyar nan , daren jiya kwana yayi bai yi bacci ba saboda yadda ran sa yake ƙuna game da abun da yarinyar tayi masa , juyi ya dunga yi yana mamakin halin MACE ,1

Shi a son ran sa ya bar su a chan wajen Amne ɗin lokaci lokaci yana zuwa yana kai mata abunda zasu buƙata domin a zahiri shi fatima da jaririyar ma bai son ganin su ,” gani yake ita ma ƙanwar tata ta san kome tare suka haɗa baki , ” shi yanzu ya bar ganin ƙanƙantar su tare da musu kallon matausaya ,” ya tsinke akan lamarin MATA3

Ba yadda ya iya haka ya shirya kafin ya wuce aiki yaje gidan Amnen inda ya tadda ta tana yiwa baby wanka jikin ta duk a sanyaye ta kwana da zancen mutuwar yakaka sosai yarinyar ta shiga ran ta saboda yanayin kamanni sosai da take da ƙanwar ta Rahima ,

Bai yadda ya ɗora idon sa kan jaririyar ba suka gaisa da Amne tana sake jajanta mutuwar yakaka tare da yi mata addu’a ta ɗora da tambayar sa aina aka yi jana’iza

Kaucewar tambayar yayi ta hanyar cewa ina ita ƙanwar tata ??

Tana wanka tun jiya take abu ɗaya ,”kuka ,” kuma har zuwa yanzu bata kai ga sanin mutuwar ƴar uwar ta ta ba , ban ma san wanne irin hali zata iya shiga ba idan ta samu labari ,” sai dai ka san hanyar da zaka bi ka kwantar mata da hankali kafin ka sanar mata da mutuwar nan

Cikin ƙagauta Hamza yace

Wane rarrashi Amne kowa ai zai mutu ki gaya mata kawai yayar ta mutu , kuma ki bata baby ta zo mu koma gida Baba ya ce na mayar su gida …

Ƙarar faɗuwa da suka ji shi yasa Amne fitowa da gudu bayan ta shinfiɗe jaririyar ,

Doctor hamza ko gizau bai yi ba hasalima tun tsayuwar falmata a gun ya gan ta , yi yayi kamar bai gan ta ba , da hikimar sa na son fahimtar ko falmatan ta san kome da ya faru ?

Ganin yaƙi fitowa yasa Amne kwala masa ƙira ,”

Ka fito ka ga abun da yarinyar nan take yi , kar ita ma ta mutu ,” tace da shi cikin ɗaga murya

Shi da kan sa ya tsorata ya kuma ji tausayin yarinyar lokacin da ya fahimci ciwon ta na asthma ne ya tashi , gaba ɗaya numfashin ta ya siƙe yana neman ɗaukewa bata cikin hayyacin ta ,

Da taimakon Allah da dabarun sa na likita , numfashin ta ya dawo ,

STORY CONTINUES BELOW

Zumbur ta miƙe zaune tare da kufcewa daga riƙon da Amne ta mata , lalube take tare da faɗin

Ina yaya daktan , ina kake yaya dakta , Dan Allah Dan Allah ka kai ni wajen Yakaka , naji kun ce wai Ta mutu , wai yaya ta ta mutu , ai wasa kake ko ? Yakaka tana gida ko ? Yaya za’a yi yakaka ta mutu ta bar ni ? Alhalin ta san bani da kowa sai ita , bani da ƙarfi kun gani fa ni miskiniya ce Dan Allah kar ku min irin wannan wasan ,”

Yaya dakta ka min magana mana , tace haka lokacin da ta samu nasarar chafko rigar sa ta rike tamau ,

Yaya dakta Dan Allah

Ta sake cewa muryar ta tana wani irin harɗewa ,

Ji yayi wani mugun tausayin ta ya rufe shi yaji ina ma bai ambaci kalmar mutuwa ba , cikin ƙwarar makafin idanun ta da suks firfito suka sauya launi tamkar ba nata ba yake iya hango irin firgici tare da azabar da zuciyar ta ke ciki ,

Kukan da baby ta tsanyara shi yasa ta yunƙura da gudu tayi sashin da taji tashin muryar jaririyar , kafin su taro ta har ta faɗa ɗakin kasantuwar ɗakin da ɗan zurfi ya sa ta faɗa ciki sakamakon jefa ƙafar da tayi nan take ta gurɗe ta tafi ta faɗi , bata haƙura ba ta rarrafa da gudu sashin da take jin kukan jaririyar

dai-dai da shigowar su

da lalube ta ɗauke ta ta riƙe ta gam a cikin jikin ta , “

Idan ni bakwa tausayi na Dan Allah ku ji tausayin jaririyar nan ku kai ta wajen maman ta ni da yakaka mun yi Alƙawari zamu haife ta mu rene ta mu biyu mu bata kulawa mu biyu ,

Meyasa yanzu zaku ce Yakaka ta mutu ? WAYE NI DA BABY IDAN BA YAKAKA ? WAYE ZAI KULA DA MU ?

ALLAH shine zai kula da ku Fatima , Amne ta ce tana sharar ƙwallar tausayin yaran , shi da kan sa hamza idanun sa sun kaɗa , tsanar yakaka na sake taso masa ,”

Wani irin kuka falmata take har tana tsuma ,”

Baba , Mama , yaana , Bulama Yakaka duk kun mutu ? Kun mutu kun bar ni ni kaɗai ? Ni meyasa ban mutu ba nima ??

Kiyi haƙuri Fatimah kowanne me rai zai mutu lokacin sa kowa yake jira , kiyi musu addu’ a

Kawo baby na shirya ta ku tafi ,” Amne ta furta hakan tana mai ƙoƙarin amsar jaririyar ,

Wani irin janyewa Falmata tayi da ƙarfi ta sake ƙanƙame yarinyar ,”

Ki bar min ita kar kowa ya taɓa ta bani da kome bani da kowa sai ita , ita ma haka , ita ce jini na kaɗai a duniya ita ce ƴar uwa ta madadin dangina gaba ɗaya , ita ce HASKEN da zan iya gani da ido na , kar kowa ya taɓa ta , kar kowa ya taɓa ta , kar kowa ya taɓa ta , ta dunga maimaitawa kamar bata cikin hankalin ta ,

Da ƙyar ta yadda Amne ta sanyawa babyn diaper tare da kayan sanyi tana riƙe a hannun ta ,

Wani irin yanayi take ciki , kamar ɗaukewar ruwan sama hawayen fuskar ta suka tsaya , ta kuma haɗe labban ta wuri guda bata cewa ƙala , sai ajiyar zuciya da take akai akai , lokaci zuwa lokaci laɓɓan ta na motsawa ,”

A haka suka fito Amne ta kama ta ta sanyata a mota tana rungume da jaririyar da ruwan ɗumi ya ratsa ta take ta baccin ta kasantuwar tun farar safe Amne ta cika mata ciki taf da madara ,”

Motar su tana tsayuwa Rahima wacce daman tana dakon jiran zuwan su , ta fito da gudun ta tana kuka ta rungume Falmata ,

Wacce take ƙiƙam bata kuka kuma bata ce ƙala ba , “

Sashin Baba ya kai ta , ta ɗurkusa guiwar ta biyu a ƙasa tana rungume da baby ,

Muryar ta chan ciki ta gaishe shi kan ta a sunkuye , ta’aziyya yayi mata kafin ya ɗora mata da nasihu , ” a ƙarshe ya ɗora da shaida mata cewa “,Hajja mai wurya,” dattijuwar dake yi masa girki ita zata cigaba da kulawa da jaririyar har zuwa lokacin da zata yi ƙwarai , bata ce kome ba kan ta a ƙasa ,

Rahima ƙarbo jaririya ki kawo ta nayi mata huɗubha , wanne suna kike so a sa mata ??

Zare jaririyar Rahima tayi ta miƙewa baban su ,”

Ya sake maimaitawa wanne suna kike son a sa mata ,

YAKAKA ,” tace da shi a taƙaice

Jimm yayi yana mai maida duban sa ga hamza , “

Wannan ba suna mai asali bane ki faɗi wani sunan Fatima ,” Baba yace da ita ,”

YAKAKA , ta sake maimaitawa hawaye na kwararowa daga idanun ta ,

Shikenan za’a mata laƙabi da Yakaka, .

a take yayi wa jaririya huɗubha ya miƙawa rahima ta mayar ta hannun yakaka ,”

Suka miƙe suna barin falon ,

STORY CONTINUES BELOW

Abuja Nigeria

Ƙarfe shidda na yamma su Yakaka suka samu isa garin Abuja ,” gajiya da ciwon kai da ciwon ciki irin na ssbuwar haihuwa, zazzabi tare da dumuwar da take cinkushe cikin zuciyar Yakaka suka haɗu suka yi ligi-ligi da ita , , ta zama marar lafiya sosai sai numfarfashi take , bata ko iya buɗe idanun ta sosai ,

Unguwar “Gwarimp Samy baby tayiwa tsinke , tana shiga unguwar bata yi nisa ba tayi parking a bakin wani ɗan madai-daicin gida mai ɗauke da ƙaramar ƙofa da ɗan madaidaiciyar ƙofar shigar da mota da mota ɗaya zata iya shigewa ,” fita tayi ta sanya ɗan mukulli ta buɗe ƴar ƙaramar ƙofar ta shiga ta ciki ta buɗo ƴar babbar ta dawo ta tada motar tare da sanya shigar da motar cikin gidan , bayan ta kashe motar ta zagayo gami da bude ƙofar bangaren da yakaka take ta taimaka mata ta fito , “

Da kyar ta iya sanyo ƙafafun ta waje sakamakon yadda marar ta take karta mata , tana fitowa taji jiri na kwasar ta taku ɗaya ta iya yi jinin ya fara bin ƙafafun ta da gudu ,”

Wayyo Allah ciki na

Ta furta lokacin da tayi baya luu ta faɗi , da sauri samy baby ta taro ta tana ,”

Na shiga uku ke yaks meye haka ? Ni samira kar ƴar mutane ta mutu a hannuna daga zuwa ,” abun arziki bai karɓi kare ba ,”

Kama ta ta sake yi ta mayar ta motar da sauri ta sake buɗe gidan ta fitar da motar ta kulle gidan gami da cilla motar a titi zuwa asibiti mafi kusa da ta sani tana tuƙi tana waiwaiyen yakaka wacce ta fara fita hayyacin ta ,”

Wani asibiti mai zaman kan sa ta kai ta inda tana zuwa aka karɓi yakaka ana tambayar samy baby meya same ta , nan ta shaida musu haihuwa tayi ɗazu da safe ɗan ya koma ,”

Nan dai suka shiga bata taimakon gaggawa bayan sun tsayar da gudun zubar jinin suka mata Allurai tare da ɗaura mata ƙarin ruwa , ba’a ɗauki lokaci ba ciwon ya lafa ta samu bacci ,,”

Agogon hannun ta Samy baby ta duba kafin ta jaa tsaki , har ƙarfe 7:40pm , wayar ta ta zaro daga cikin ƴar jakat hannun ta nan ta tadda miss calls ɗin samarin ta daban-daban , number da tayi wa suna da “Dude” ta bi bayan ƙiran ,”

Hello boo ya kake ?

Daga chan ya amsa mata , yana tambayar ta inda ta bar wayar nan ta sanar da shi ta zo da ƙanwar ta wacce ta gaya masa ɗin , amma bata ji daɗi ba ne ,”

Kuna wanne asibiti ya tambaye ta

Nan ta sanar da shi asibitin da suke ,”

Ba’a ɗauki lokaci ba ya iso asibitin , mutum ne magidanci da ya tasamma shekaru arba’in da biyar ,

Babu kunya samy baby ta mannu da jikin sa tana masa ƙwarƙwasa lokacin da suka haɗu , kafin ya nemi da ta haɗa shi da Casher na asibitin , nan tayi masa jagora ,”

ba ɓata lokaci ya dire naira dubu ɗari , aka rubuta takaddar shaidar biyan kuɗin aka ba samy tare da sharaɗin idan chanjin su ya rage zuwa lokacin sallamar marar lafiyar za’a mayar musu da ƙuɗin su , idan kuma su zasu yi ciko ma sai su ƙaro , “

Basu tsaya sauraran sauran bayanan nasa ba suka yi wucewar su samy baby tana manne da jikin sa ,”

Ɗakin da aka kwantar da yakaka suka je ,

Har yanzu Alluran da aka mata wanda akwai na bacci a ciki basu sake ta ba , dan haka suka tadda ta tana ta baccin ta ,”

Wani kallon ƙasan ido yayi mata ,”

Yane baby na kin san fa nayi shirin daren yau tare da ke , sai kuma ga marar lafiya mun samu ,”

Karkaɗa masa ido tayi ta wani rausaya ,

Boo yadda kake so haka za’a yi , zamu iya tafiya mu bar ta ai ƙarƙashin kulawar ma’aikatan asibitin , ni da kaina nayi tanadin daren yau domin ka , ta ƙarasa zancen tana kashe masa ido ,”

Wata shashar dariya ya sake kafin ya juya yana cewa

Baby na kenan shi yasa nake daɗa jin ki a cikin jini da tsoƙa ta , bari naje mu gama da ma’aikatan asibitin game da waɗanda zasu kula da ita , sai na dawo mu wuce ,”

STORY CONTINUES BELOW

Samy baby tare da farkan ta , basu yi tunanin a irin halin da ƴar mutane zata iya farkawa cikin dare ba , suka yi tafiyar su sheƙe ayar su suka bar ta ƙarƙashin kulawar biyu daga cikin nurses ɗin asibitin waɗanda Alhaji Gali ya danƙa musu hatimin nasara a hannun .

Yakaka ba ita ta farka ba sai wajen ƙarfe uku na sulusin dare , ta tashi bata jin ciwon kome illah rashin ƙarfin jiki da kuma ƙirjin ta da take ji yayi nawi a sakamakon ruwan nono da ya zo ,”

Yawo tayi da idanun ta , ta tabbatar babu kowa a ɗakin sai ita kaɗai , miƙewa tayi ta zauna tare da zuro ƙafafun ta ƙasa tana bin ɗakin da take da kallo wanda yake wadace da hasken lantarki ,

Hotunan abubuwan da suka wakana tun daga safiyar jiya su suka yi ta dawo mata ɗaya bayan ɗaya , kamar a lokacin suke faruwa ,”

Wani irin kuka ta fashe da shi lokacin da tunanin ta ya kawo ta dai-dai wurin da take sanya ƙafafu tana wucewa ta gaban falmata ba tare da ta tsaya ta mata magana ba barw tayi mata sallama,damuwar da ta hango a idanun falmata a lokacin da ta waiwaye ta da kallon ƙarshe a jiya , ta tabbatar damuwar da take kwance idanun falmatan ya assasa ne ta dalilin rashin sanin halin da take ciki , ji tayi zuciyar ta ta kumburo da ta lalubi son sanin halin da falmatan take ciki har ta kwatanta a yanzu ,

Wayyo Falmata na ta furta a sarari tana dafe ƙirjin ta , yunƙurawa tayi ta tashi da sauri ta nufi ƙofar ɗakin , kamar wacce aka dakatar kuma sai ta tsaya , tsayuwar ta baya rasa nasaba da tunowa da tayi a bigiren da take a yanzu wanda yake da tazara mai tarin yawa tsakanin ta da inda ta baro Falmata ,”

Ruwa mau ɗumi ta ji yana kwarara ta cikin rigar ta da ya sata saurin janye rigar ta ga menene ??

Ruwan nono ne yake zuba ,” tuno da ɗiyar ta da ta bari ba tare da ta kai ga ko ganin fuskar ta ba tayi , kukan da ta baro ta tana yi wanda ta tabbatar na yunwa ne sautin sa take iya jiyowa tamkar a yanzu take ji , wani irin tausayi ne tare da wani iri lamari mai girma da ya zarce nadama taji yana bin jijiyoyin jikin ta da gudu kafin ya zo ya watsu cikin zuciyar ta , “

Zubewa tayi akan guiwowin ta ta baje a ƙasa tana sake sakin wani ƙaƙƙarfan kukan da yake ɓullowa tun daga ƙarƙashin ran ta ,”

Ƙarfe shida na safe nurses ɗin da aka bawa ajiyar yakaka suka shigo ɗakin da take su biyu , ɗayar riƙe da magunguna tare da allurai .,”

Turus suka yi lokacin da suka ga gadon da take babu kowa , a tsorace suka ƙarasa shigowa ɗakin ,” i

Ina take suka haɗa baki wajen tambayar junan su ??

Kamar ance su waiga suka hango ta zaune a ƙasa daga jikin bango ta takure ƙafafun ta ɗora hannayen ta bisa guiwowin ta gami da kwantar da kan ta akan hannuwan ,”

Kin tashi ne ? A ah ya kika zauna anan ?

Ɗayar nurse ɗin ta tambayi Yakaka suna matsowa kusa da ita ,

Ko gizau bata yi ba Duk da cewa idanun ta a buɗe suke ta kafe su a jikin bango ,”

Kallon juna nurses ɗin suka yi ,”

Patient da ke muke fa , ko bakya jin hausa ne ?

Motsa bakin ta tayi ƙasa ƙasa tace

Ina anty samy ?

baki da lafiya ne ? Kizo ki hau gado mu auna ki kisha maganin ki na miki allura kafin doctor naki yazo , yayar ki bata kwana a nan ba sun fita da mijin ta sun ce zasu dawo da safe ,”

Wasa gaske , ƙememe Yakaka taƙi miƙewa daga gurin da take takure a zaune , a ƙarshe dole suka haƙura suka bar ta a wajen suka yi tafiyar su shirye shiryen tafiya gida saboda masu aikin safe zasu karɓe su , suka rubuta a cikin folder nata taƙi yadda ta sha magani kuma taƙi yadda ayi mata allura ,”

Tara na safe ta gota aka turo ƙofar ɗakin aka shigo , samy baby ce ta shirye tsaf cikin wani ɗanɗasheshen yadi , hannun ta riƙe da ɗan kwando wanda ta zubowa yakaka abun ƙarin kumollo ,

Ita ma sai da zuciyar ta tayi tsalle da ba ta hango yakaka saman gadon asibitin ba ,

Chan gefe ta hango ta , da sassarfa ta nufi wajen ta tana

Yaks ya kike zaune a ƙasa lafiya dai ko ?

Tana jin muryar samy baby ta miƙe tsaye gami da takowa da gudu ta riƙe hannun samy baby ta shiga roƙon ta ,”

Anty samy Dan Allah kiyi sauri ki kaini wajen sa , ya mayar da ni gida na koma wajen su Falmata , ji nake kamar zan mutu ,

Da ido samy baby ta bita tana iya hango tashin hankali tare da ruɗani gami da tsantsar rikici a idanun Yakaka ,”

Ke yaks bana son shirme ki nutsu , haka kike so na ɗauke ki yarkace-yarkace daga gadon asibitin na kai masa ke ??

Ai wannan sai ya kore ki

Bazai kore ni ba anty samy shi zai kai ni a min gyaran jiki ,”

Mtss samy baby ta jaa tsaki ,

Ki zo kici abinci Yakaka tun jiya rabon ki da abinci , nurse ɗin sun baki magani tare da allura ? Ki ci abinci ki gyara jikin ki kafin likitan ya zo ,”

Warce hannun ta da samy baby ta riƙe tayi , ta durƙusa gami da haɗa hannun ta ta shiga yi mata magiya tana gunjin kuka akan lalle fa ita a yanzu zata kai ta wajen bature kam silum kuma a yau zata koma wajen su Falmata ,”

Tun samy baby na ƙoƙarin rarrashin ta tare da yi mata dabara har ta suƙe ta fara yi mata masifa ,

Faɗan da ta fara yi mata bai haifar da kome ba sai sake rikicewar Yakaka domin kuwa yunƙurawa tayi da gudu tana ihu ta nufi ƙofar ficewa daga ɗakin da nufin komawa gida ,”

STORY CONTINUES BELOW

Da gudu samy baby ta ruƙo ta kafin ta kai ga ficewa daga ɗaƙin , hankalin ya fara tashi ita ma , sam bata yi zaton yakakar zata birkice mata irin haka ba , ” sai tayi da gaske tare da taka tsantsan idan ba haka ba zata jawo mata jangwam kowa ya san haƙiƙanin abun da ya faru daga ƙarshe ita ce zata iya faɗawa hannun hukuma ayi ram da ita ,”

Ke yaks Ke yaks ƴar iska meye hakan kike min ? Ina cewa da yardar ki da amincewar ki muka taho ? To shikenan gyara jikin ki ki sauya kayan ki da wannan rigar ta miƙa mata wata doguwar riga a cikin leda tare da audugar mata da sabbin panties , shirya mu tafi ,”

Ba musu yakaka ta karɓi rigar tana jan ajiyar zuciya irin na wanda ya ci kuka sosai , ta shiga banɗakin wajen ta gyaro jikin ta gami da sauyo kayan ta ,”

Kwandon abincin samy baby ta ɗauka suka fito daga asibitin ba tare da sun yiwa kowa sallama ba bare su bi ta kan chanjin su da samy baby ta tabbatar akwai ,”

Gidan da yake mallakin ta ne wanda ta fara kai yakaka jiya nan ta sake yada zango ,inda tayi wa yakaka umarni da ta fito ba musu ta fito , ta taka ta bi bayan ta zuwa cikin gidan inda ta sa ɗan mukulli ta buɗe wata ƴar kwatatciyar ƙofar madaidaicin falon suka shiga kai tsaye samy baby ta wuce jikin wata ƙofa da take daga gefen hagu a cikin falon ta sanya ɗan makulli ta buɗe kofar ta sanya kai ciki ,

Yakaka tana dogare daga bakin ƙofar falon ta ji muryar samy baby na ƙiran ta daga cikin ɗakin da ta shiga ,

cikin ɗakin ta shiga gami da durƙusawa daga baki-baki tace

Na’am Anty samy

Tashi ki ƙaraso yakaka nan ɗakin ki ne , na shirya miki shi tun kafin na kawo ki , ga banɗaki nan shiga kiyi wanka na haɗa miki ruwa mai zafi sosai da zaki gasa jikin ki , idan kin fito ga gado ki kwanta kiyi bacci idan ya so in kin farka kin cin abinci kin nutsu sai muyi magana ,”

Tunda ta fara magana Yakaka ta ɗago idanun ta tana kallon ta ,gama maganar ta ya zo daidai da silalowar ƙwalla daga idanun Yakaka , da kyar ta harhaɗo kalmomin da zata iya amfani da su

Anty samy cewa kika yi shi yace ki kaini wajen sa , na ɗauka tun jiya zaki kai ni ? Dan Allah ki kai ni bazan zauna anan gidan ba ,”

Kallon baki da hankali samy baby ta watsa mata ,

ai kuma sai kiyi tunda ke kunnen ƙashi ne da ke bakya jin maganar mutane , tace tana kewaye ta ta fice daga ɗakin har ga Allah ta fara ganin gangancin kan ta da ta ɗauko yarinyar nan ta zo da ita nan ba tare da ta mata bayanin haƙiƙanin gaskiyar manufar ta ba , kar fa ta zame mata matsala !

Zama tayi akan ɗaya daga cikin ƴan kananun mannanun kujerun da suka zagaye falon suka yi ɗas gwanin sha’awa ,

Ta ɗauki wayar ta da nufin ƙiran ƙawar ta ,”

Yakaka ta gani ta fito ta tsaya akan ta jikin ta sanye da dogon hijabin da ta bata jiya ,”

Ɗurkusawa tayi a gaban ta cikin wata irin murya chan ciki tace

KI MAIDA NI GIDA ANTY SAMY ,”

Da sauri samy baby ta miƙe tsaye

Ke Yakaka kar ki min iskancin banza da rashin kunya ,

To bari ki ji na faɗa miki Gaskiya ni taimakon ki nayi na tsamo ki daga cikin hallakar da wannan Doctor yake neman jefa ki ta hanyar ƙulla soyayya a tsakanin ku , alhalin ya san cewa sofi na nan na dakon soyayyar sa shekara da shekaru ,

ni nasan irin Alkaba’in sofi da Alwashin da take ci akan duk wata mace da ta raɓi Doctor Hamza , da bana fatan ko kusa ki faɗa cikin kaidi tare da masifar ta , shi yasa na zare ki daga cikin rayuwar doctor baki ɗaya na kawo ki nan waje na domin na inganta miki rayuwa na tsaya miki ta yadd watarana za ki zama macen da ire iren Sofi da waɗanda suka fi ta zama annoba ma basu isa ɗaga miki ɗan yatsa ba , amma dayake ke ƴar iska ce WAWIYA JAHILA ,kina neman butulce min akan wani sakaren makahon son abunda baza ki taɓa samu ba da kike yi ,1

ki buɗe kunnen ki kiji da kyau ni ban san inda wani yarima yake ko wa ? Ban san inda yake ba abokin sa nuhu da kan sa bama tare , dan haka dabara kawai nayi miki tare da aiki da ILMI NA , dayake ke wawiya ce kika yadda kika amince wani ɗan sarki wai yana ƙiran ki ,

Ɗan sarkin da kuka yi tarayyar kwanaki kaɗan domin samun muradin zuciyar sa kaɗai , ɗan sarkin da ya miki ciki ya jefar ki kan titi ya yi tafiyar sa ya bar ki ba tare da ya sake waiwayar ki ba , ɗan sarkin da dake da babu duk ɗaya ne a wajen sa , ya ma jima da mantawa kin taɓa wanzuwa a rayuwar sa , wanda yayi watsi dake tsawon wannan lokacin amma shine kika yadda wai yana ƙiran ki wai yana ƙiran ki a hakan nan naki ,!

Ta ƙarashe tana nuna ta da ɗan yatsa kafin ta kwashe da dariyar walaƙanci ,”

Kin san meye yaks , idan zaki tafi Ban hana ki ba ga hanya ki fita amma ki sani nan Babban birnin tarayya kike Abuja , cike take da mutane mabanbanta wanda masifar da take tare da wasun su ta kai girman da ya zarta tunanin ki , abune mai sauƙi a sace ki a ɓatar da ke ɓata na har abada ,”

Zaɓi ya rage gare ki ki zauna tare da ni ki gina kan ki ta yadda watarana zaki koma ki ɗauko ƴar ki tare da ƙanwar ki ki musu rumfa ki zama gatan su , ko kuma ki fita da nufin komawa masu amfani da mutane wurin yin tsafi suyi gaba da ke su hallakar ki ,

STORY CONTINUES BELOW

Wataƙila ki samu nasarar komawa garin maiduguri kije ki auri doctor Hamza, sofi ta taso bisa kan ki a ƙarshen ƙarshe ki hallaka a hannun ta , masifar sofi bazai tsaya iyakacin kan ki ba , har makauniyar ƙanwar ki tare da ƴar da kika haifa sofi sai ta ɗau fansar raɓar mata doctor da kika yi ,”

taku ta fara yi tana barin falon bakin ta na sake furto kalmar ,shawara ta rage gare ki BANZA WAWIYA JAHILA ,

Kalma-bayan-kalma kalaman samy baby ke yin dawurwura cikin kunnuwa suna zarcewa ga kwakwalar yakaka , sai dai fassarar su sun gagari ƙarfin tunanin yakaka ,

Meye tace ne ? Me take nufi wai ? Anty samy tace ni wawiya ce jahila amma ai bata ce ni mahaukaciya bace , alhalin kuma ni nasan na haukace ne ,”

Zamewa tayi ta kwanta a tsakanin kujerun gurin tare da curewa ta duƙunkune cikin hijabin jikin ta , fata take a mata wani mummunan mari , ina ma fankar da take juyawa a sama zata faɗo ta daki kanta ko zata samu ta farka daga mummunan mafarkin ido biyun da take ,”

Wai Anty samy duk daman ƙarya take mata , wai Anty samy yaudarar ta tayi , wai daman ashe Bature kam silum ya jefar ta ne ba tare da ya taɓa neman ta ba , ashe ya manta da ita , ita ke dakon soyayyar sa , wai ashe ashe an raba ta ne da Doctor hamza mai taimkon su ita da ƙanwar ta , tuno da shi tayi da tashin hankali tare da tausayin da ta hango ɓaro-ɓaro cikin ƙwayar idon sa lokacin da take cikin magagin ciwon naƙuda , ajiyar zuciya ta fara saki da sauri da sauri tana jin yadda tsokar jikin ta take ƙarƙarwa sakamakon wani mugun sanyi da taji yana lulluɓar ta ,”

ME NAYI WA ANTY SAMY DA TA JEFA RAYUWA TA A WANNAN MASIFAR ?? Tambayar da ke yawo cikin zuciyar ta kenan lokacin da take rufe fatar idanun ta da ko ɗiris babu ɗigon ƙwalla , “wani tashin hankali yafi gaban kuka ,”

Sai yamma liƙis samy baby ts fito ta sha wankan ta ta haɗe cikin wata diguwar rigar roba mai bin jiki , kasantuwar ta ƴar chas-chas sai tayi kyau a cikin kayan ,” bata ga yakaka a falo ba dan haka sai ta leƙa ɗakin da ta mallaka mata nan ma har cikin banɗaki ta leƙa babu alamun ta shiga cikin sa dan haka ta fito da sauri da nufin leƙa waje ko dai ta fita ɗin ne da gaske ???

Cin karo tayi da ita kwance a inda ta bar ta tun safe , ta Ƙudundune daga kan ta har ƙafafun ta , wani irin tausayin yarinyar ta ji ya taso mata , ita da kan ta ɗazu ta jima bata yi bacci ba da ta kwanta tana ta saƙawa da warwarewa , ganin laifin kan ta take , akan ƙaryar da tayi mata ta zo da ita ba tare da Aminccewar ta ba yayin da wani sashi marar ƙarfi kuMa ke ganin ai daidai tayi taimako tayi kamata yayi ta Gode mata ,

Sunkuyawa tayi tana tashin ta a hankali ,”

Yakaka , wacce daman ba bacci take ba ta janye hijabin ta ɗago kan ta tana fatan ta buɗe ido ta ga kome mafarki ne , ta gan ta a ɗakin su da Doctor hamza ya mallaka musu , tare da ƙanwar ta , baby mama kuma tana fatan taji motsin ta a cikin cikin ta ,

Ganin samy baby ce ke tashin ta cikin gidan da ta tabbatar nan ƙaddara ta jeho ta rayuwa cikin sa , yasa ta ji zuciyar ta na yadda da abunda tunanin ta ke tabbatar mata cewa ba mafarki bane , kome ya faru ne a zahiri , ita yakaka a duniyar da take yanzu ita kaɗai ce jal , babu Falmata babu abunda ke cikin ta babu kuma Doctor Hamza mai taimakon su , duk tayi musu bara’a ta tsallake su bisa jagorar wawancin ta tare da jahilci da suka biyo ta kan mummunar rufa-rufa tare da gadar zaren da samy baby tayi mata , da taimakon ta ta aikata babban kuskuren da baza ta taɓa yafewa kan ta ba ,”

Kallon samy baby take kamar yadda ita ma samy baby ke bin ta da kallon tausayi ,

yakaka ki tashi haka Dan Allah ki je ki ci abinci kiyi wanka ki gasa jikin ki , kin san fa jego kike ina miki tsoron kar jikin ki ya lalace ,

Toh

tace tana mai yunƙurawa ta mike , da sauri samy baby ta kama ta kai tsaye banɗaki ta kai ta tare da sake haɗa mata ruwa mai zafi tace tayi wannan sosai ,”

Toh

ta sake amsa mata ,” cikin daɗin ran fara samun haɗin kan yakaka samy baby ta nufi ɗan kitchen ɗin da taje da shi a gidan domin dafawa yakaka ɗan wani abu mai sauƙin dahuwa da zata iya ci ,

Nan da nan ta dafa mata indomie ruwa-ruwa da soyayyen ƙwai guda biyar ta haɗo da ruwa ta kai mata ɗakin , nan ta tarar da ita zaune akan tiles ɗin ɗakin ta har lau tayi wanka ta maida kayan jikin ta da hijabin da ta cire

Yakaka kul ki daina zama haka a ƙasa jego kike ba’a son mai jego tana zaman ƙasa tashi ki koma bakin gadon ga abinci ki ci , zan kawo miki wani kaya ki sauya kafin ki warware muje ayi miki sabbin ɗinki kin ji ? Toh

Tace tana miƙewa ta zauna a bakin gadon kamar yadda tace .1

STORY CONTINUES BELOW

Wasa-wasa cikin sati guda da samy baby tayi tana gida kullum tana kula da yakakar , ta lura tamkar yarinyar ta koma shiru-shiru , wacce ta samu taɓin hankali bata un bata un’un kome tace mata kawai “toh” take cewa

Hirar duniya wacce take bukatar bada amsa samy baby tayi wa yakaka amma yakaka taƙi cewa uffan , iyakaci idan ta bata umarnin yin abu take zata yi babu gardama,

Ranar da ta cika sati da kawo ta gidan ta shiga ɗakin yakakar da safe , cikin ran ta tana aiyana idan har ta tabbatar yarinyar nan ta samu matsalar taɓin hankali ne , sauri zata yi tasan yadda tayi ta maida ta inda ta ɗauko ta , ah to ita ina zata iya rainon mahaukaciya ?

Zaune ta tadda yakakar tayi jigum tana kallon windown ɗakin ,”

yaks ya kike jin jikin ki yau ?

samy beby ta tambaye ta ba dan tana sanya ran samun amsar yakaka ba , ga mamakin ta sai ta ga yakakar ta juyo da kallon ta kan ta , cikin wata muryar dake fitowa da sauti marar amo tace

ANTY SAMY KI KAINI MAKARANTA , KI SAKA NI A MAKARANTA INA SO NAYI KARATU INA SO NA SAMU ILMI.

Wata irin dariyar murna samy baby tayi tana mai zama gefen gadon ta riƙo hannayen yakaka ,

Yaks , yaks ko kefa ? Kin fara fahimta ta ko yaks ? A yau yau zan sanya a fara nemar miki makarantar da za’a sanya ki , nayi alƙawarin karatu sai kin gaji yaks , Ilmi ai shine gishirin rayuwa bari ki ga ina wayata ? Bari naje na ƙira Alhaji Gali , makaranta sai wacce kika zaɓa yaks , tace tana ƙarasa barin ɗakin har da ɗan gudun ta ,

Da ido yakaka ta bita cikin ran ta tana sake ɗaura ɗamarar goge kalmar JAHILCI daga gare ta da tafi bada tabbacin kome da ta aikatawa kan ta da wanda wasu mutane suka wanzu suna aikata mata , ya faru ne ta dalilin

Jahilcin ta , Kalmar wauta kuwa a cikin satin ta fara nesanta kan ta da ita , domin a ɗamarar ƴakin da ta ɗaura bata da buƙatar tafiyar tare da wannan kalmar ta wawanci da aka danganta ta da ita , “1

Bata sani ba ko zata iya , ko burin ta zai kai ga cika , ko watarana zata cimma manufar da ta lulluɓe cikin ranta a tsawon sati guda da ta wanzu babu dare ba rana tana saƙawa tare da kuncewa cikin ran ta , tana matse zuciyar ta tana ƙwanƙwasar ƙwaƙwalwar ta har ta samawa kan ta mafitar da take ganin zata iya kaiwa gaci ta hanyar ta ,

bata sani ba shawarar zata kai ta inda take so ko kuwa zata ɗora ta ne kan wani kuskuren , bata sani ba ta raba kan ta ne da kalmar wawanci ko kuwa ta sake tafiya ne bisa jagorancin wani wawancin ? Ko ma meye ta bar kome ta janye hankalin ta daga kan kowa da kome ta ɗaura ɗamarar yin YAƘI DA JAHILCI .”

Maraɗi Niger

Tafeeda ne zaune a gaban hajiya umma ya tanƙwashe ƙafafun sa babu kowa a falon ta na ciki daga shi sai ita ,

Ka tafi zouwa nigeria ka zo min da bayani mai gamsarwa a game da abokin ka. Tabbas yana cikin wani yanayi wanda yake boyewa daga gare mu , kayi gaggawar taryar sa a chan a magance matsalar tun kafin ya samu isowa da ita zouwa cikin gidan nan , kasan dai duk wata matsalar da ta shafi yarima idan har ta shigo gidan nan ta shafi mutanen cikin masarauta ne baki ɗaya ,”

Toh ranki ya dade cikin yardar ubangiji a gobe zan fara neman iznin tafiya daga shugaba na wurin aiki , zouwa ƙarshen sati na kan iya samun iznin tafiya , ki kwantar da hankalin ki , babu abunda zai faru ga Biyamuradin maraɗi

Allahu shi sa haka , haka muke fata , Allah shi muku Albarka baki ɗaya ya kare ku daga faɗawa tarkon Maƙiya , kana iya komawa yaro na ,”

Ameen Ameen yake amsawa , ya miƙe kan sa a sunkuye yana faɗin ki tashi lafiya ranki shi daɗe ,”

shiru hajiya umma tayi tana nisawa cikin tunanin meke faruwa ga yarima youssouf haka mai girma da yasa take jin damuwa har a cikin amon muryar sa , ?? Jikin ta yana bata wani abu ya faru ko yana shirin faruwa gare ta ita kan ta kyakkyawa ko kuma akasin sa , koma menene tasan yana da alaƙa da youssouf ɗin ta domin akan sa kaɗai wannan soyayya mai girma take bayyana tasirin ta a kaf cikin ƴaƴan ta !

Cikin satin kamar yadda tafeeda yace ya gama shirinsa tsaf , yayiwa nigeria tsinke ,

Bai wani sha wahala ba yayi wa kan sa jagora zuwa garin maiduguri bayan da jirgi ya sauke shi a garin abuja , ” sai da ya samarwa kan sa masauki international hotel ya huta , washegari ya bada kuɗi aka sayo masa layin nigeria ya cire layukan sa na niger ya sanya ns Nigeria , hajiya umma ya fara ƙira ya sanar mata da samuwar sabon layin nasa da zasu dunga magana ta hanyar sa sannan , ya kashe ya fara laluben number biyamuradi youssouf wanda bai kai ga sanin isowar Tafeeda nigeria ba rabon da suyi waya ma sun tasamma kwanaki goma abun da kusan hakan bai taɓa faruwa ba a tsakanin su sai fa yanzu da biyamuradin yake cikin wani hali na tsantsar damuwa tare da ƙarin zafafawa kan sa aiki da yayi ta hanyar rashin hutu ba dare ba rana yana zabarin rundunar dake ƙarƙashin sa suna matsa ƙaimi wurin farautar ƴan tawayen Boko haram ,” duk a ƙoƙarin sa na son yakice tunanin damuwar sa daga cikin ran sa da kuma kusantowar lokacin da aka ɗibar ma su na kammala aikin su da nigeria yana gaf da ƙarewa tsakanin kwanaki arba’in masu zuwa nan gaba zasu cika shekara da aka ɗibar musu za kuma su koma ƙasar su ta haihuwa ,”……!Biyamuradi youssouf bai samu damar shigowa cikin garin maiduguri ba sai da Tafeedah ya samu kwanaki biyu a cikin garin yana dakon jiran sa ,”saboda yanayin aikin sa ,”+

Kai tsaye hotel ɗin da tafeeda yayi masauƙi ya nufa , kasantuwa tsawon watannin da ya samu yana ɗan shigowa garin ya fara gane hanyar guraren da kafafun sa ke yawan zuwa ,”

Bayan sun gaisa cikin raha sosai irin ta aminan junan da suka shaƙu da juna , Tafeeda ya nisa yana kallon Youssouf ɗin tare da nazartar sa , ƙwarai ya fahimci har yanzu bai shirya sanar da shi damuwar sa ba , duba da yadda yayi ƙoƙari ya boye damuwar ta sa fiye da wancen haɗuwar tasu , cikin rashin sanin damuwar ɓaro-ɓaro ta bayyana kan ta a cikin ƙwarar idanun sa ,”

Kai tsaye Tafeeda ya doshi Youssouf da maganar da ta taso shi takanas daga ƙasar su ƙarƙashin umarnin hajiya umma , inda yake cewa

Ban san ba ko rabuwar mu ta ƴan watanni ta sauya alaƙar mu da kai ba ɗan ouwa , ta yadda har ta kai ka shiga boye min wani babban lamari da ya shafi rayuwar ka wanda ya kai ga tsunduma ka cikin damuwar da hatta Hajiya umma ta shina ,

ita ma kuma damuwar ta shafe ta ta kuma sanya ta a firgici , ka riga ka san kome na daga yanayin gidan da munka taso cikin sa , ka san kou kai wanene , kasan yadda hajiya umma ke takatsantsan da du wani lamari naka ,

hakan ya sa hajiya umma ta titsiye ni tana son san sani game da abunda yake faruwa gare ka , na shaida mata ko ɗaya bani da sani game da halin da kake ciki nan , sai tayi gaugawar turo ni domun naji shin menene damuwar ka Yarima Youssouf ?

Shiru ne ya ɗauki ɗakin ,

A haƙiƙanin gaskiya Youssouf yana kunyar buɗe baki ya sanar da wani mahaluki laifin da ya aikata tsakanin sa da ubangijin sa , laifi mai girma kuma irin wannan , to amma hajiya umma ita wata halitta ce mai girma gare shi bazai so ba ko kusa shi ya zamto silar samar da damuwa ga ruhin ta , abun zai masa yawa ,”

To amma wanne hali zata shiga idan ta ji dalilin shiga damuwar sa ? Wane alfanu sanar da ita damuwar sa zai samar ? Idan ta ji laifin da ya aikata da har ta kai shi ga shiga halin da yake ciki ƙara mata damuwa zai yi daɗi da ciwon zuci ko kuwa ma hawan jini ,” ! Kai anya ma kuwa zata yafe masa ??

Tunanin halin da zata iya shiga ciki kawai ya sanya gumi tsatsafo masa a goshi , hannun sa ya kai ya rufe fuskar sa da tafukan sa , ya goge gumin ,

Ɗan ouwa , nayi kuskure mai girma cikin rayuwa wanda giya ta zam sanadi , na haiƙewa ƴar mutane , nayi tarayya da ita har ta samu juna biyu , a yanzu haka mariƙiyar yarinyar ta kore ta ta shiga duniya .1

ɗan ouwa ka faɗa min ya zan yi ina zan tahi na same ta ? Yaya zan yi na gyara kuskuren da na aikata , ɗiyar mutane zata zama kilaki sanadi na , yaya rayuwar ni nawa ɗiya mata zasu ƙarƙe ?? Yaya nawa ƙanne zasu samu kariya , tayaya zan katange iyalina ? ….

Kallon sa kawai Tafeeda yake idanun sa sun kaɗa jazir da ɗai bai taɓa jin zance mai munin wannan ba , ashe yarima bayan shan barasa har fyaɗe yake yiwa mata ? Har zina yake yi ? Har ɗa ya samar ta hanyar haram ? Anya anya Yarima Youssouf ya chanchanta ??

Miƙewa yayi ya soma haɗa kayan sa ,” baya so ya cigaba da kallon sa , ganin sa a halin yanzu zai ɗarsa masa tsanar sa , zai rushe amincin da suka faro tun ƙuruciyar su ,” yana so ya tafi , yana so yaje ya lallashi hajiya umma da tausasan kalamai domin ita ɗin a yanzu abar a tausayawa ce , da ɗai bazai yadda kunnuwan ta su ji waɗannan munanan laifukan da ɗan da ta ƙwallafawa rai ya aikata ba , ɗan da hatta shi da kan sa yaci albarkacin samun tsaftatatciyar tarbiya daga gareta sanadin raɓar Youssouf da yayi amma sai ga shi , ! Kai kaicho

Da sauri Youssouf ɗin ya miƙe yana riƙe hannun Tafeeda da yake harhaɗa ƴan abubuwan buƙatun sa cikin jaka ,

Warce hannun sa yayi da wani irin zafin nama

Kar ka taɓa ni Youssouf , babu wata sauran Alaƙa a tsakanin mu , manzon Allah yace mu guji munanan abokai, mu mu’amalanci mutanen kirki ,” kai baka chanchanta ba Youssouf

Ƙwallar da ya kamata ta zubo tun watanni da suka gabata amma rashin samun damar kukan ya hana ta zubowa tare da taurin rai irin na soja gami da jin kai na jinin sarauta ita ce yau ta silalo ,

A hankali ya zauna a bakin gadon , bai yi aune ba ya fara kuka shaɓe-shaɓe da hawaye kukan nadama kukan tsanar kai kukan neman mafita ,”

STORY CONTINUES BELOW

Share shi Tafeeda yayi tare da cigaba da haɗa kayan sa tsaf ya ɗaura agogon sa gami da ɗaukar ƴar jakar sa na matafiya,

Kallon Youssouf ɗin yayi ,

Zuciyar sa ta raunana , ganin hawayen sa abune da tun zamanin ƙuruciya rabon sa da gani , kai zai iya ƙirga yaushe da yaushe ya ga kukan Yarima Youssouf tun a ƙuruciyar su , to ɗan sarki ne , ɗan gata yarima , da kowa tattalin sa yake , a yau ya san cewa zuciyar sa ta luguiguita matuƙa da har ya kawo zubar hawayen sa a karon farko cikin shekarun girman su ,

Ƙauna ta haƙiƙa irin ta shaƙiƙan aminai ta taso , ji yayi bazai iya tafiya ya bar shi ba ya zama dole ya tsaya su samar da mafita , kamar yadda suka saba tallafar junan su idan wata maysala ta riski ɗayan su kome girman ta ko ƙanƙanta,

Ina yarinyar take ?wanne hali take ciki ? Ina cikin jikin ta ? Gaba ɗaya martabar gidan sarautar maraɗi na cikin barazana , !

Dawowa yayi ya zauna a gefen sa gami da kautar da kai ,”

Sai ka faɗi wanne yunƙuri kayi wajen neman gafarar ubangiji gami da nemo yarinyar tare da wanke kan ka , ka fa sani Yarima Youssouf ɓacin sunan ka daidai yake da zubewar martaba da ƙimar mahaifin ka “Maimartaba,” tare da gaba ɗayan masarautar mu ,”

A yau Yarima shi ya koma tamkar bawa da ake ba umarni babu ja ya shiga bawa Tafeedah labari tun daga ranar da kome ya fara wanzuwa a tsakanin su irin mawuyacin halin da ya shiga akan ɗiya mace a lokacin da yadda kome ya cigaba da gudana har zuwa ranar da ya tafi ya bar ta ,”

Tsumu Tafeeda yayi yadda yake zaton kome ba haka ya ji ba , tabbas ya san Youssouf bai yin ƙarya da garaje , yayi zaton da son ran sa ya aikata kome , amma a yanzu da ya saurati bayanin bakin sa idan kuwa gaskiya ne tabbas akwai lauje cikin naɗi ,”1

Ya zama dole a nemo yarinyar nan tare da cikin jikin ta ,” domin mu samu tabbacin abun da ke cikin ta bashi alaƙa da kai , domin kai ma baka tabbatar ba , bani fatan ya zam naka ne ,” ya kuma zama dole ka gyara kuskuren ka ɗan ouwa kamar yadda kayi niyya nima ina goyon baya ɗari bisa ɗari ka taimaki rayuwar yarinyar nan son samu …ka aurar ta ga wani !

Basu gushe ba suna tsara yadda lamura zasu musu sauƙi wajen samun ta har dare ya shiga , nan suka bar duk wani shirin su zuwa gobe ,”

****

9pm

Doctor Hamza ya kammala duk wani shirin sa da ya ɗau tsawon kwanaki goma yana yi kafin rubuta hutun ƙarshen shekara da yayi na tsawon sati shidda da zai fara daga gobe ,

Kamar yadda ya tsara a goben zai bar garin zuwa zaria inda yake so ya ƙare hutun nasa a chan Jami’ar Ahmadu Bello , sashin horas da likitoci inda ya ƙirkirawa kan sa wani guntun shiri na faɗaɗa ilmin sa da bincike akan sashin da yake da ƙwarewa ta fannin sa na tsawon sati shiddan

, duk a ƙoƙarin sa na son ganin ya yakice duk wata damuwa da Yakaka ta ɗarsa masa cikin ran sa domin kuwa bai san yana son ta har haka ba , bai san son da yake mata yayi masa mugun kamu , ya kafu yayi rassa a cikin ran sa ba ,

sai cikin kwanakin da suka biyo bayan gudun da tayi ta bar shi , ya kuma gano duk wata rufa-rufa tare da yaudarar da tayi masa , kullum da tunanin abun yake rayuwa cikin ran sa ,

ko kaɗan bai jin sa dai-dai kewa tare da tsantsar tsanar ta da ya cusawa kan sa na barazana ga walwalar sa ,

aikin sa da kan sa ya fara samun tsiko a cikin sa , bai tare da kwanciyar hankalin da ake buƙatar irin sa cikin aikin sa , hakan ya sa ya rubuta Annual leave na dole , kuma a karo na farko cikin shekaru shida da fara aikin sa ,” bai taɓa rubuta hutu ba sai fa wannan karon da So ya jefa shi a damuwa ,!

STORY CONTINUES BELOW

Dan haka ya zaɓi yayi ɗan nisa da inda ta taɓa zama da duk wani abun da ya shafe ta na ɗan wani lokaci ko zai samu ya danni zuciyar sa ya yakice ta baki ɗaya daga cikin tunanin sa ya fuskanci rayuwar sa ta gaba , cikin taka tsantsan da duk wani lamari na mata , haka yake fata haka yake buri.2

Ya gama tanadar kome da mahaifan su zuwa ƙannen sa zasu iya buƙata na kimanin watanni biyu a gaba , gefe guda bai ƙi ba , bai ɗauke kai ba , bai kuma yi fatali da marayun da yakaka ta wofantar ba duk da cewa ya so yin hakan da farko amma tausayi da ya riga ya zama bangare mafi kyau a cikin jerin halayen sa ya sanya shi gaza yin ko oho da lamarin Falmata da baby mama ,

toh meye laifin su ? me suka yi masa ,? basu da laifin kome basu kuma yi masa kuskuren kome ba, su ɗin Raunana ne abun a taimakawa

Duk da cewa ya ɗauke ƙafafun sa daga cikin saboda kiyaye zuciyar sa da tuno masa da yakaka da take yi , amma cikin tanadin da yayi akan tafiyar da zai yi bai manta Falmata da mama ba su ma ya tuna da su ,

Ya sayi Cartons na madarar baby mama zuwa daiper , wiper , da tarin kayan jarirai himili guda , Falmata kuwa cikin kuɗin da ya danƙawa Rahima yace ta raba uku ta bada kashi ɗaya ga Fatima ,

Bayan ya kammala haɗa duk wasu abubuwan da zai buƙata Zama yayi akan kujera ya miƙe ƙafafun sa aƙasa tare jingina kansa da fuskar kujerar ya ɗaga kan sa sama , “

Tunanin da bai so shi ya fara , kafin kunnuwan sa su fara jiyo masa kukan ta char-char -char tana yi babu ƙaƙƙautawa , shiru yayi yana jin yadda tausayin ta ke lulluɓar sa , yasan ba kukan kome take ba illa kukan rashin jin ɗumin jikin uwa ,

Lumshe idanun sa yayi yana jin sunan da wani sashi na zuciyar sa ya ƙira yakaka da shi ,”muguwa ,”

Ji yayu kukan ya tsawaita , kuma kasantuwar dare ne tamkar a gaban sa take yi , har cikin ran sa yake jin kukan nata , dan haka ya mike cikin rashin kuzari ya sanya takalmun sa ,” gami da yiwa cikin gidan tsinke ,

A tsaye ya tarar da su su uku , Falmata Rahima , Da kuma hajja mai wurya ,” Baby mama tana rungume tsam a kirjin falmata hajja mai wurya da Rahima sunyi sunyi ta basu ɗiyar su gwada rarrashin ta taƙi , sai faman jijjiga ta take tana hura mata kunne , idan ban da kuka da mimmiƙewa babu abunda jaririyar take yi ,”

Meye same ta ?

Yace da su lokacin da yake ƙarasowa inda suke ,”

Da sauri Falmata ta nufi inda taji tashin muryar sa ,”

Muryar ta tana karkarwar kukan da ta riga ta fara yin sa tun tuni , tace

Yaya dakta Dan Allah duba min Ita meya same ta ko bata da lafiya ne ? Tun ɗazu taƙi shiru ,

Bani ita yace yana karɓar ta daga hannun ta ba musu ta sakar masa ita , ta kafe inda take jin tashin muryar sa da ido , “

Jujjuya ta yayi a hannun sa , kafin yace ungo ta hajja rage mata waɗannan dogayen kayan ,

Zuruf Falmata tace kawo ta yaya dakta na iya cire mata , kuka take yi baza ta tsaya a cire mata a hankali ba , kar hajja ta ji mata ciwo ,”

Sakin baki hajja tayi cikin hasken falon ta dallawa falmata harara ,

Zata yi magana Dakta hamza yayi mata alama da hannu tayi shiru ,

Miƙewa falmata baby mama yayi,

Ga mamakin sa tsaf ta cire mata kayan jikin ta ta barta da diaper tana ta sharar ƙwalla , ta miƙa masa ita dudduba ta yayi ya tattaɓa cikin ta inda nan take ya gane cikin ta ne ya kumbura ,

Ɗaura ta a kafaɗa yayi a hankali ya shiga shafa mata baya yana ɗan jijjiga ta , ba’a fi mintuna huɗu ba ta fara fitar da iskar da ta cika mata ciki , a hankali kuma kukan ya fara lafawa , kafin mintuna goma ƴar jaririyar tayi bacci abin ta ,

STORY CONTINUES BELOW

Sauƙe ta yayi ya rungume ta a ƙirjin sa , yana kallon ƴar zagayayyar fuskar ta da take ruwan hoda dan fari , gashin da ya kwanta a gaban goshin ta har ya haɗe da girar ta , ,”irin na maman ta ya aina cikin ransa ,”

Da sauri ya miƙawa Falmata ita

Ungo karɓe ta Fatimah , nan gaba idan zaki bata madara ki tallafo kan ta , sannan bayan kin gama bata ki ɗora ta akan kafaɗar ki ki dunga shafa bayan ta kar ki kwantar da ita sai kin tabbatar tayi gyatsa , sannan kar a bata madara da ya zarce ka’idar da aka umarta a bata ,

waye ke hada madarar ?

Ita take haɗa mata cewar Rahima

Ita kuma ? Tayaya zata auna ? Meyasa ke bakya haɗa mata ?

Kafin tayi magana Hajja mai wurya tayi wuf tace ,

Yo wannan yadda take ƙwalafacin ƴar nan da wa ta yarda ? Ko fa ɗaukar ƴar bata yarda ayi , koyaushe tana ƙunshe a hannun ta kamar lalle ,!

Cikin siririyar murya falmata tace ina ganewa yaya dakta , idan na ɗibo madarar a cikin ɗan ludayin ɗibar madarar sai na shafe kan sai na zuba a robar bata madarar, sai nasa ruwan ɗumi dai-dai zanen layin na biyu ko ?

Hakane , haka zaki cigaba da yi mata

yace , yana kama hanyar barin wajen ,

Yaya dakta

Ta ƙira sunan sa .

Chak ya tsaya kafin ya waiwayo ta

Na’am Fatima

Mun gode da kome , Mun gode da taimako, Allah ya ninka maka ya saka da Alheri,

Jim yayi kafin yace mata

Ameen Fatima , gobe zan yi tafiya ki min addu’a

Allah ya kiyaye hanya , Ya dawo da kai lafiya , Allah ya baka sa’a

Ameen Yaa Rabb

Yace yana ƙarasa barin falon , cikin ran sa wani irin yanayi yake ji na taso masa , Ina ma ? Ina ma ? Kai ina ma daga bakin ta waɗannan kyawawan addu’o’in ke fitowa ?

Washegari

Ƙarfe bakwai na safe Doctor Hamza yayi wa mahaifin su Sallama bayan doguwar hirar da suka yi tun bayan sallar asubah , duk wata nasiha da yakamata tare da tunasarwa sai da yayi masa ,

A ƙarshe da ya miƙe zai tafi ya bishi da addu’o’in tsari da fatan samun nasara suka yi sallama , ya shiga motar sa yana barin gidan ɗauke da niyyar biyawa yayi sallama da Amne kafin ya ɗau hanya !

Ƙarfe tara ta sami colonel Youssouf tare da colonel Tafeedah a babbar headquarter na soji da ke garin ,”Giwa barrack ,” inda bayan ƴar gutuwar mahawar tare da gabatarwa aka haɗa su da gungun sojoji kimanin su goma sha biyu akan su raka su , a je a kwaso mutanen da colonel Youssouf yace sun ɓoye masa ƙanwar sa ,”

Hilux biyu ta soji ɗauke da bindigogin su suka yiwa unguwar su madam saly tsinke ,.2

Tunda suka doso unguwar matasa da ma wasu daga cikin magidantan da suke da tsoffin laifuka suka fara guje-guje , kasancewar unguwar kusan cike take da marasa ji ƙananu da manyan masu laifuka sai kawai aka hargitse da guje-guje , saboda sun san haka tsigau gungun sojoji basu kauce hanya su gangaro musu cikin unguwa ba shakka wani ne yayi wata ta’asar aka zo yin ram da shi ,

Basu kula kowa ba suka bi hanya ƙarƙashin jagoranci Conole Youssouf da yake hakimce gaban motar farko .

Tun daga nesa madam saly da Ɗan liti da suke zaune daga cikin rumfa kan kujeru suna jajantawa juna game da asarar maɗuɗai da suke jajen sun same su , suka fara jiyo jiniyar motar sojoji ,”

Gefe guda kuma ma’aikatan tane baki ɗaya kowa na aikin sa , masu goge-goge da share-share na yi , ta ciki kuma masu wanke-wanke da haɗa ruwan barasar nayi .

STORY CONTINUES BELOW

Ɗan liti da ke karkaɗa ƙafa yana tsuma yace

Hmm ai ke dai saly fara bar tuna min ,”cin kazar daren farko ,” ban son ko tunawa da yadda waɗannan magudan kuɗaɗen da Bala manci yayi mana ta leƙo ta koma da su , ai ƙwaranƙwasa da mun kama su da mun tsalleke kogin talauci , naira dubu ɗari tara fa saly fara ? Kuma ke a ganin ki da mun biya masa buƙatar sa ba zai cikace mana ya zama miliyan bane ??1

Kai dai bari liti wallahi ni sai yanzu nake jin takaicin gudun tsinannun yaran nan ƴan gudun hijira yaks da ƙanwar ta , ka ga wannan ƴar luɓu-luɓun ƙanwar tata ai ita ce irin wacce Bala ya nemi da mu kai masa , ƴar ƙwailar da take gaf da balallagewa , “

Uhun ni na tabbatar ke ce mai baƙar ƙafa saly dan duk wata harka indai ta kuɗi ce idan na haɗo da ke ban ganin falala a cikin ta , ƙwaranƙwasa da na sani da juwai me kala-kala na kaiwa harkar nan da yanzu tuntuni kuɗaɗe na sun nuna sun yi ligif a hannu na ,”dan nasan ko ramin kura ta shiga ta nemo irin wacce bala ya nema ,”

Wani kallon sheƙeƙe madam saly ta jefawa ɗan liti ,

Lalle kuwa liti , yo yaushe daren yayi nasa tuwo a ido ?? To idan ka fasa kaiwa juwai me kala kala harkar ka ta samun kuɗi nan gaba kai ba ɗan halak bane liti muna nan da kai zaka dawo da ƙafafun ka ni ɗuwawu ce dole a zauna da ni ,

Rama kallon banzan yayi ya murza yatsu,”suka bada sautin ,” ɓas

Ni ce ma ke saly fara , nace ni ce ke , gaba asara baya asara ai wallahi , ki ji ni da kyau idan ido ya mutu kwalli bai tada shi , ke da kan ki dai kin san kome yanzu ba irin na da ba ne , anbar yayin 504 Yanzu 406 ce ke kada maza ahaayye ji min saly fara zata gwadan salon su na tsofin bariki ??

Ta buɗe baki da nufin maida masa martani suka ga ƙartin mazan da ke karta ta waje suna shigowa da gudu suna tsalleke katangar da take ta ƙarshen filin gidan, miƙewa su duka biyu suka yi , dai-dai da shigowar wani gabjejen ɗan busa hayaƙin da ya sha yayi manƙas da gudun ma da ƙyar yake wondan sa a hannu ,1

kai idi meye ya faru na gudu ? Inji madam saly

Ta wajena ki arce kiyi ta kan ki idan ba gungun rundunar sojojin Nigeria kaf ne suke shigowa gidan nan ba ,”1

Mts ɗan liti ya jaa tsaki yana komawa ya zauna ,

Zauna muyi hirar mu saly fara yanzu haka wannan na maliyan sha yayi tafi ƙarfin ƙwanyar sa , yazo yana mana subaɗaɗi , wai gungun sojojin nigeria ? Ahayyee asha ruwa ayi tamɓele .1

Anya kuwa ɗan liti baka zuwa ka dubo mana ko ƴan sanda ne ? Kasan su fa matsayi ta ne ba mutunci ne da su ba yanzun nan sai su chafke mutum su sha janin sa ,”

Bazai wuce su,” Corporal garuje ” ne suka zo samame ba suna neman na shan matala Kin fa san wata yayi nisa kum…

Kamar ɗaukewar wutar lantarki madam saly ta ji ɗan liti ɗif,”

Kan ta ankara ta ga gungun sojojin da suke ɗurowa cikin gidan , ” cikin ta taji ya murɗa nan take laɓɓan ta suka ɗauki rawa ta gagara cewa ƙala ,”

Na ƙale , wallahi na ƙale , nayi surrender !

Ɗan liti ya furta haka yana kai guiyoyin sa ƙasa bayan ya ɗage hannuwan sa sama2

Kai tsaye sojojin suka dunga kutsawa ɗakunan gidan suna wurgo mutanen cikin ɗakuna waje ta ƙarfin tsiya , cikin mintoci kaɗan sai ga mutanen gidan rankatakaf a filin gida ,

Kowannen su ciki ya ɗuri ruwa, sai waige waige suke , suna bin sojojin da suka saita su da bakin bindigogin su da kallo ,”cikin son sanin meke faruwa ? Wanne laifi suka yi ? Amma ba halin tambaya soboda tsoro

Tsakiya colonel Youssouf ya fito cikin muryar sa mai amo da yake buɗe ta ya haka a bakin daga yace

Ina yarinyar da kun ka boye a cikin gidan nan ? Ina take ? Ina Kun ka kaita ? Kuyi gaugawar fiddo ta kafin harsashai su sauƙa a kawukan ku baki ɗayan ku ,

STORY CONTINUES BELOW

Cikin maƙyarƙyatar muryar da tsoro ya riga ya bayyana kan sa a ciki ɗan liti yace

Wallahi Tallahi ranku ya daɗe ni ban san kome ba , ni yanzu shigowa ta gidan ma karbar saƙo wallahi ko jinjirin kiyashi bazan iya cutarwa ba bare ɗan mutum , ɗan mutum ma irin wannan mai darajar dan ….

Dukan da sojon kusa da shi ya kai masa da ƙafa ya sa shi sakin ihu tare da zaman ƴan daɓaro a ƙasa ,

Matsowa Youssouf yayi , kan madam saly

Kin samo ta ko kouwa a ah ? Zaki fiddo ta ko kouwa sai kin ji ƙamshin mutuwa ,??

Idanun madam saly da suka sake shigewa ciki saboda tsoro suka kawo ƙwalla,

Wallahi ranka ya dade na duba , mun duba mun cigita , mun yi neman saƙo da lungu amma ko wanda yace ya ji ɗuriyar su ma ita da ƙanwar ta bamu ji ba , wallahi ranka ya daɗe ba ni na kori yarinyar nan ba raina yana son ta ina ƙaunar ta ita da abun….

Marin da ya ɗauke ta da shi ya hana ta ƙarasa dogon labarin ƙanzon ƙuregen da ta kwaso ,”

Ku musu duka ku kai su mota mu wuce da su barrack , idan sun ɗanɗani azaba zasu faɗi inda take , ” cewar Yaoussouf

Kamar jira suke suka fara ƙwallo da su nan take guri ya ruɗe da ihun matan banza da kururuwar ɗan liti da ya buɗe maƙogoro yana zurma ihu tamkar ana watandar tsokar jikin sa , ya buɗe muryar sa ta asalin garjejen namiji ,”1

Kora su suka fara yi waje da shirin tafiya da su barikin su na soji ,”

Nan fa idanun Yagana ya fara raina fata wacce ta sha manyan bulalai huɗu ,

Ita tasan aka kai ta wannan barikin sojin sai ɗan buzun ta ,” ta tsoraci soja ba kaɗan ba domin ta ga irin yadda basu ɗauki kisa a bakin kome ba ,

Bulalar belt ɗin da wani soja ya sake sauƙe mata a gadon baya yana tunkuɗa ta ita ta gigita ta ,”

Wayyo Allah bayana , fatar bayana ta sulluɓe , dan Allah ku tsaya wallahi na san inda take zan kai ku , zan kai ku Dan Allsh kuyi haƙuri kar ku tafi da ni ,

Matsowa gaban ta yayi ya bar chasa madam saly da ta riga ta fara galabaita da bulalar soji ,

Kin ka ce kin san inda take ? Tana ina ? Ki kai ni yanzu – yanzu idan kin ƙi zan harbe ki ,”

Muryar ta tana sarƙewa tace

Nasan inda take kuma ma ai ƴar uwa ta ce zan kai ku yanzu , Dan Allah kar ku ji min ciwo kar ku tafi da ni ,wallahi nasan inda YaKaKa take ,”

Finciko ta yayi ya miƙar ta tsaye , muje ki kai ni

Yace yana tunkuɗa ta gaba , kafafun ta ko takalmi babu ,

Ku cigaba da tsare su , idan mun same ta zan sanar da ku ta téléphone sai ku ƙyale su idan bamu same ta ba zaku zo mouna da su barrack ,

Ɗaya daga cikin motar suka hau , Yagana da Youssouf da Tafeeda ,

Ki gouda muna hanya,” yace da ita

Ba’a yi wata tafiya mai nisa ba Yagana tace a tsaya ga gidan

Tana yi musu nuni da gidan Amne ,

Su suka fara fitowa shi da Tafeda suka tasa ƙeyar yagana kai tsaye suka sanya kai cikin gidan .

Amne tana kishingiɗe akan ƴar daddumar ta tana shan hantsi ta ga tsayuwar sojoji akan ta ,”

Miƙewa tayi zaune tana kallon su a tsorace ,

Wannan ce ta ɓoye su

Yagana tace haka tana nuna Amne da ɗan yatsan ta ,

Da sauri ta miƙe tsaye ,

Ranku ya daɗe lafiya ?

Wanne laifi nayi dan Allah ?

Yarinyar da kin ka boye zaki fiddo mana ita yanzu mu tahi da ita ,ƙanwa ta ce ,

Wacce yarinyar ?

YAKAKA

Yagana ta bata amsa tana matse ido

Zuciyar Amne ta buga da ƙarfi dan razana ƙwarai ta gane yakaka yarinyar da ta mutu wurin haihuwa , ƴan gudun hijirar da ɗan ta ya taimakawa yake riƙon su a gidan su , ganin jami’an tsaro suna neman ta yasa hantar cikin ta kaɗawa ,

STORY CONTINUES BELOW

anya baza su harbe ta ba idan ta gaya musu ai wacce suke nema ta mutu ?? Ko su tafi da ita barikin su na soji su wahalshe ta a banza , bata da mai karbo ta , ɗan ta yau-yau yayi tafiya , ya bar garin , dole tayi taka tsantsan kar ta ɗaure kan ta !

Mahaifin su Hamza babban mutum ne ba abu mai sauƙi bane a tozarta shi musamman ma da ta san basu yi wani mummunan laifi ba , tana da yaƙinin idan ta sada su da shi kome zai zo da sauƙi , shi zai iya musu bayani su fahimta ,

Ni ba nice mariƙiyar su ba riƙon kwana ɗaya jal nayi musu , a halin yanzu suna gidan mariƙin su , zan iya kai ku gidan na dawo ?

Ta ƙare jawabin ta da sigar tambaya ,?

Ki gouda mana gidan , idan har kin san gaskiya kin ka faɗi ,”

Gaskiya ne wallahi , muje na kai ku ,

Babu Ɓata lokaci Amne ta kai su har Unguwar su Doctor Hamza ta nuna musu gidan daga nesa ,

Kuna iya komawa muhallin ku Tafeeda yace da su, Youssouf zai yi magana , ya masa alama da yayi shiru ,”

Gudu-Gudu Yagana ta tare mai napep ta shiga ,

sansanin ƴan gudun hijira zaka kai ni ,”

tace da shi tana waiwayen bayan ta ,

Ta ɗan madubin gaban napep ɗin ya dube ta , wanne daga cikin sansanin ƴan gudun hijirar zan kai ki ??

Na hanyar bulunkutu tace da shi ,

Cikin ran ta tana kitsima gara ta koma sansanin ƴan gudun hijirar inda samun ta zai yi wahala , zata ɓace a cikin dubunnan ƴan gudun hijira ƴan uwan ta domin ta san ta yarda ta bari wannan sojan ya san da haɗin bakin ta aka gudu da Yakaka har wani garin da ita kan ta ma baza ta ce ga sunan garin ba , bata da hanyar saduwa da samy baby , toh fa tasan ba abunda zai hana shi harbe ta har lahira ya kashe ta !

Tattaki suka fara suna nufar gidan da kowanne cikin su ke yiwa kallon sani ,

Kusan a tare suka ce da juna wannan ai gidan da munka zou biki kwanakin baya ,”

Babu shakka shine Yarima Youssouf ya amsa ,

Maigadin gidan ne ya tare su , cikin ladabi ya gaishe ya ɗora da tambayar su ina suka nufa ?

Suka shaida masa gurin maigidan suka zo ,” nan ya shaida musu zai shiga ya sanar da shi zuwan su , har youssouf zai yi magana , Tafeeda ya sake dakatar da shi , bayan wucewar sa yace da shi ,”

Ɗan ouwa mu bi kome a sannu , kar muyi garaje .

Bai ce da shi kome ba , suna tsaye maigadin ya fito yayi musu iznin shiga gidan ƙarƙashin jagorancin sa ,”

Har cikin falon yayi musu jagora , prof yana zaune suka shigo bayan sun sunce ƙwafta-ƙwafatan takalman su daga waje ,

Da kallon rashin sani yake bin su bayan sun gama taƙaitatciyar gaisuwar da ta shiga tsakanin su ,”

Samari daga ina kuke ? Ban shaida fuskokin ku ba !

Ɗan jim suka yi suna tattaro nutsuwar su , kafin Tafeeda da shine ya tsara kome yace

Baba munzo neman watta ɗiya da anka ce kana riƙo sunan ta Yakaka , ” wannan mijin ta ne ,

Ya ƙarasa zancen yana nuna youssouf

Ɗan jim prof yayi, wacece yakaka ? Ko dai yarinya ƴar gudun hijira ? ,’

Yaya kamannin ta yake ? Kuma a wanne yanayi take ,”

Doguwa ce fara , tana da tsago a fuskar ta , sannan , sannan kuma tana ɗauke da juna biyu ,

Youssouf ya ambata

Kaine mijin ta ? Prof yace da shi fuskar sa na nuna jimami ,”

Ni ne baba

Ya amsa

, cikin zuciyar sa yana fatan tambayoyin su tsaya iyaka nan , tare da zaƙuwa da son a ƙira masa ita ya gan ta , Allah sarki ashe ma ƴar hijira ce ,

Tunanin sa ya tsaya chak lokacin da yaji prof yace

Yaro ina baka haƙuri tare da tunasar da kai akan cewa duk wani mai rai mamaci ne , yarinya yakaka ƴar gudun hijira ta rasu a wajen haihuwa bayan riƙon su da muka yi a gidan nan tsawon watanni bakwai , ta rasu ta bar ɗiyar da ta haifa tare da ƙanwar ta da muke riƙon su tare …

Ji yayi wani irin yanayi mai kaifi yana ratsa zuciyar sa wanda ya zarce kaifin tsoro ko firgita , tsintar kan sa yayi a hali na shuɗewar tunani na wucin gadi , jikin sa a take ya ɗauki rawa , da wannan yanayin ya watsa idanun sa kan Baba prof ,”

Yarinya yakaka ta mutu ? Ta mutu a wajen haihuwar abunda ke cikin ta ? Ta mutu bamu gana na nemi yafiyar ta ba ? Ta mutu ban gyara kuskuren da nasa muka aikata tare ba ? Ta mutu Alhalin ban nuna mata godiya ta akan irin taimakon da ita take tunanin ta mun ba ? Meyasa ta Mutu ta bar min nawi mai girma bissa kaina ni kaɗai ?

Tafeeda ne ya riƙo shi ganin yadda yake surutai kusan bai cikin hayyacin sa , tabbas shi da kan sa ya ji mutuwar yarinyar , kome kuma ya kunce masa , zuciyar sa kuma ta raurawa ,

STORY CONTINUES BELOW

Kayi hakuri yaro mutuwa na kan kowa bari na ƙira a kawo maka ɗiyar ka , ƙanwar ta ma ta zo ku gaisa ,”

Waya yayi cikin gidan akan a zo da Falmata da baby mama ,”

Ya maida hankalin sa kan su Youssouf da tafeeda yana nazartar su , akwai tambayoyi dayawa da yake son yi musu ba wai dan bai yarda da su ba , sai dan a farkon kawo yarinyar gidan Hamza ya sanar da shi mijin yarinyar ya mutu boko haram sun kashe shi , sai kuma ga shi yanzu ya ga jami’in tsaro a matsayin mijin ta ko daman ɓata yayi ba mutuwa ba tsawon wannan lokacin ?

Shigowar Falmata riƙe da mama tare da rahima , shi yasa biyamuradi Youssouf ɗago kan sa ,”

Idanun sa so suke su ga ɗiyar , so yake ya samu rangwame ta hanyar fahimtar bashi da alaƙa da ɗiyar da aka samar ta hanyar banza wacce zuwan ta yayi sanadin mutuwar mahaifiyar ta me tarin rashin galihu , bai so lamuran sa su sake munana ,

Sai dai wani yanayi da ya tsinka jinin jikin sa lokacin da hasken fuskar ƴar jaririyar da ya ɓanɓare daga hannun falmata ba tare da ya jira sun ƙarasa shigowa falon ba yayi tattaki da sassarfa ya taro su ,

Yanayin mai ƙarfi ne da bai taɓa jin kwatankwacin sa ba da ɗai duniya ,

Jin sa yayi a wani yanayi wanda ya so ya saɓawa wanda yake cikin sa kafin ɗora idon sa akan ƴar da yaji ya gaza gane wacce matsaya yayi mata a halin da yake ciki ,

Kallon ta yake tamkar yana son ganin abun da ke lulluɓe cikin fatar jikin ta , kallon da yake mata ya sa duk wata suffa tata jeruwa cikin tunanin sa tana juyawa tare da girma mataki-mataki har zuwa lokacin da kammanin ta da mahaifiyar sa suka gama fitowa tsaf , tamkar kobo da kobo ,

Bai san lokacin da idanun sa suka samar da ruwan hawaye ba sai kawai ganin ɗigar su yayi akan fuskar ta , wanda ya nutsar da idanun sa kai babu shakka yana iya kallon ƙofofin gashin jikin ta ,

Sauƙar ruwa a fuskar ta ya sanya ta buɗe idanun ta a hankali ta wara su akan sa , fes ! da shi ma ya sake ware nasa idanun tare da ɗage duk girar sa biyu abun da ya kan yi idan yana cikin yanayi na shauƙi ,

Yamutse fuskar ta tayi cikin salon su na rikicin jaririyar zata yi kuka ,

Da sauri ya ɗago ta zuwa dai-dai fuskar sa ya sanya kan karan hancin sa yana goge mata ƙwallar sa dake kan kumatun ta da yake zaton ita zata sa ta kuka ,

Ai kuwa tamkar ya kunna ta sai kuwa ta sa kuka ,

Kukan ta ya zo dai-dai da fashewa da kukan falmata wacce da kyar Rahima ta banbare hannun ta daga cukumar da tayi wa rigar Youssouf , cewa take wanene anan ?

Rahima waye ya kwace min baby ?

Ka bani ita dan Allah ka bani ita kar ka sa ta kuka ? Kai waye , ? Rahima kika ce min Baba ne yake ƙiran mu ,? To waye ne ya karɓe min Yakaka na ?

Muryar prof ta sa ta ɗan samu nutsuwa har ta sassauta riƙon da ta yiwa youssouf , rahima ta samu nasarar janye hannun ta ,

Amma kukan yarinyar da take jin sa kamar ɗigar narkakkiyar dalma ya sa ta kasa tsayar da kukan ta , “

Ganin kukan ta yayi yawa ya sa Tafeeda tasowa ya dafa kafaɗun Youssouf , yana kallon fuskar sa , muryar sa babu ƙarfi sakamakon halin da ya ga Youssouf ɗin ya shiga tunda ya ɗaura idanun sa kan ƴar , yana nufin ɓullowar wani gagarumin lamari Masarautar Maradi .

Ɗan ouwa bada ɗiyar nan ga mariƙiyar ta , ga ta sai kuka take , !

Dauke idanun sa yayi da kyar daga fuskar ƴar ya mayar kan Tafeeda , da wata muryar da bata da amo yace ,”

Ɗiya tawa ce Tafeeda , wagga Ɗiya jini na ce , Ɗiya ta ce , A yau ni Uba ne , Uba ne ga wagga ɗiya da tsautsayi tare da kaddarar zuwan ta duniya ya sa kome ya faru kamar yadda ya faru ,”

Ɗan satar kallon prof , Tafeeda yayi yaga yadda hankalin sa baki ɗaya ke kan su , amma kasancewa falon me girma ne da ƴar tazara a tsakanin su ,

Wallah ka lura Ɗan ouwa idan ba hakka ba kana iya ɓata mouna kome ,

STORY CONTINUES BELOW

Hannun sa ya kai da nufin karɓe ƴar daga hannun sa , wata irin zamiya Youssouf ɗin yayi ya janye ƴar jaririyar sosai zuwa cikin jikin sa ,”

Baka ganin kuka take ?? Ka bari na lallashe ta ,

Haɗiye firgicin sa Tafeeda yayi , ka bada ita Yarima uwar goyon ta zata mata lallashi , akwai abubuwa dayawa a gaban mu ,

Ina uwargoyon ta ?

Yace yana mayar da duban sa kan su Falmata da duk budurin da tayi na cukume sa da kalmomin ta duk bai ji su ba , ruɗanin da yake ciki ya toshe masa kunnuwa daga barin jin hayaniyar ta ,

Da ɗan yatsa Rahima ta nuna masa Falmata wacce tayi shaɓe-shaɓe da hawaye sai ajiyar zuci take ,

Ga ta nan ,

Matsowa yayi , ya miƙa mata ƴar

Karɓe ta , ki kula da ita kar ki bari kome ya cutar da ita , kar ki bari tayi kuka ban lamunta ba ,”

Hannun ta miƙa saitin inda take jin hucin sa , ta karɓi ɗiyar tana jin wani sanyi na ratsa zuciyar ta yana kore tunanin da zuciyar ta ke son kawo mata akan kamar ta taɓa jin amon murya kwatankwacin wannan ,!

Da kallo Rahima ta bi shi , kamar shine ? Kamar fa shine na jikin hoton cikin kayanYakaka , babu shakka ma shine ,”

Ku koma ciki Rahima , prof yace ga su ,”

Toh ,

suka ce suna kama hanyar barin falon ,”

Youssouf zai magantu , Tafeeda yayi saurin yunƙurowa yana faɗin ,

Mun gode Mun gode Baba , Allah ya saka da Alheri ya bada ladan Taimakon da kayi mana , yanzu zamu koma saboda a bakin aiki muke amma muna dawowa cikin kwanaki biyu masu zouwa da yardar Allah ,”

Ameen toh babu kome Allah ya nuna mana kwanaki biyu masu zuwa Allah ya ƙara muku haƙurin jure rashi, idan kun sake dawowa zamu yi magana ,..

Youssouf zai yi magana ,

Tafeeda ya sake katse shi yana jan hannun sa

Ɗan ouwa tashi mu tafi ,

Jaan hannun sa yayi suka fito daga gidan suna fitowa Youssouf ya zare hannun sa daga na Tafeedah ,

A tare suka haɗa baki wajen tambayar junan su ,!

Ɗan ouwa meye haka kake shirin yi ?

Kana nufin nan zan tafi na bar ƊIYA TA ?

Hannun mutanen da ban san su ba ?

Kallon baka da hankali Tafeedah ya yi mass kafin ya fara taku ya nufi wajen motar su , ‘,kazo muje muyi magana a tsanaki ,

Ran sa bai so ba ya faɗa motar ya shiga Tafeeda ya fara ƙoƙarin tada motar lokacin da yake magana da sojojin nan akan su bar su madam saly an samo inda yarinya take ,” ya sauƙe wayar yana hawa kan titi ,

Da fitar su Prof ya ɗaga waya ya ƙira Doctor Hamza bayan sun gaisa , yace

Yanzu mijin yarinyar nan ƴar gudun hijira mai rasuwa ya bar nan gabana tare da ɗan uwan sa , ka ga ikon Allah ashe shi bai mutu ba , ya zo ya ga gan ta tare da ƴar sa yana…

Wani mummunan cin birki da Doctor hamza yayi wanda hatta prof sai da yaji ,

Subahananlahi , Hamza ban hana ka ɗaukar waya alhalin kana tuƙi ba ? Da fatan dai baka yi haɗari ba ? kana jina ?

Muryar sa ƙasa ƙasa ya amsa bayan ya ɗauke kan motar zuwa gefen hanya bakin daji ya tsaya ,

Ina ji Baba , a bashi ƴar sa tare da ƙanwar matar sa ya tafi da su kar su sake dawowa Baba ,”

Jimm prof yayi ,

Kafin yace

Toh babu kome idan sun nemi hakan ai sai a basu daman ai hakan ya kamata , ka dunga kula hamza ka daina ɗaukar waya alhalin kana tuƙin mota , kana ina ne yanzu ?

Ina jigawa Baba , insha Allah zan kula baba , ka min addu’a baba , zamu yi magana idan na isa .

Toh Allah ya tsare hanya daga ka isa ka sanar da ni ,

,”To ,” yace yana sauƙe wayar

Cije gefen leben sa yayi , watau dai kome gaskiya ne , ga shi nan duk yadda suka shirya yana faruwa daki-daki , watau har sun yi auren ta turo shi ya zo ya ɗau ƴar sa da ƙanwar ta ,

Zuciyar sa tayi duhu , me na miki da zaki yi wasa da zuciya ta irin haka ? Ashe sakayyar da zaki min kenan ?1

STORY CONTINUES BELOW

Wani irin kishi mai ɗaci yake ji a ran sa , shan alwashi yake daga yanzu bai ƙauna sake jin ko me suna irin nata , bai ƙaunar sake jin duk wani abu da ya shafe ta , bashi da wani sauran uzuri da zai iya bata kariya da shi , ya yarda ya amince ta yaudare shi .

Tada motar yayi a hankali ya hau titi , yana nisawa cikin tunanin mace a yau !

Sojojin nan basu bar su madam saly ba sai da suka sake chasa su yadda ran su ke so ,” Ah soja birgimar hankaka ne fa ?2

Suka yi ficewar su suka hau motocin su wasu a tsaye a bayan hilux wasu a zamne , suka yi tafiyar su ,”

illahirin gidan a ruɗe yake da kururuwar matan da aka lallasa , sai ɗuruwa ake ganin su ana tambsyar me ya faru ? Me suka yiwa sojoji ?

Ɗan liti wanda muryar sa ta dashe saboda tsabar ƙwarmato , ya dubi madam saly wacce bakin ta ya kumburo yayi suntum sakamakon haƙorin ta ɗaya da ya fita ,”

Cikin dusashiyar muryar sa yace saly fara yau wacce rana ce ? Kuma a wanne wata muke nawa kuma ga watan ??

Da ido kawai madam saly ta bi shi tana jin yadda raɗaɗi yake ratsa tsokar jikin ta ta ko’ina gefe guda ga bakin ta da take ji kamar an cusa garwashi ,”1

Ya cigaba ,

Na rantse ki rubuta ki ajiye ido na idon wannan tsinannan yarinyar yagana sai dai uwatta tai naƙudar wata , wai ace kana zaune da makashin ka baka sani ba ? Ashe tuntuni ita ta san ana nan ana shirin far mana da yaƙin basasa ,amma tayi funfurus ta ƙi faɗa mana bare muyi ta kan mu ,ki tsoraci ɗan adam ƙuzazje mai tafiya da ƙafa biyu saly fara ,4

wai yanzu ace tsawon lokacin nan ashe shegiyar yarinyar nan mai kama da takanɗa ta san inda yaran nan su yaks suke , shine bata taɓa yunkurin faɗa ba “ko daya ai yake hannun hagu ba baƙon duwawu bane ,”duk jirgi ɗaya ya kwaso su ,” to ƙwaranƙwasa ba’a daki bulus ba, farautar ta zan shiga yi ba dare ba rana ,” wayyo wayyo ni liti du mazauna na sun yi tsami sun ɗuri ruwa , saly gane min ko dai farfashewa mulamulai na suka yi ?

Ya juyo mata duwawu ,5

Kawar da kan ta tayi tana miƙewa da kyar ta nufi cikin gidan tana aiyana irin mummunan matakin da zata ɗauka akan Yagana , ai ita ba’a zubebeniyar ƙwaryar rashin mutunci da ita mutum ya kwashe ƙalau ,”

*****

Bayan komawar Biyamuradi Youssouf tare da Tafeeda ɗakin hotel , kowannen su shiru yayi yana saƙa cikin zuci ,

Ta bangaren Youssouf abu biyu ne zuwa uku , na farko mutuwar Yakaka da ta girgiza shi ta kuma bashi tsoro , ya wanzu yana tunanin da yanzu shi ne fa ya mutu ? Me zai cewa ubangijin sa akan tarin laifukan da ya wanzu yana aikatawa , tausayin ta yaji yana ninkuwa a ransa , tare da alwashi da yake ɗaukarwa kan sa na wanzuwa yana yi mata addu’a neman gafarar ubangiji har zuwa tsayuwar nasa numfashin ,

Ƙaunar ƴar jaririyar da kafin ɗora idanun sa akan ta suks tsara da shi da tafeeda akan cewa ko abun da aka haifa ya/ta nuna wasu alamu a halittar sa/ta dake nuna cewa nasa ne baza zai amince ya dangantar ɗa/ƴar da cewa jinin sa ba ne , kasancewar ya riga ya faɗawa Tafeeda yakaka ƴar talakawa ce sun san cewa ba wani tsananta binciken su gwajin jini a tsakanin sa da ɗa/ƴar da aka haifa za’a yi ba , dan haka suka tsara zasu barwa yakaka abunda ta haifa amma zasu taimaka mata tsayin daka kamar yadda tun farko Biyamuradi youssouf ya tsara ,

Sai dai fa kome ya sauya ya birkice masa lokacin da ya rungume ƴar sa a ƙirjin sa , ya ɗora idanun sa akan ta kamannin mahaifiyar sa duk suka bayyana kan su a halittar ƴar , ta buɗe idanun ta ta kalle shi , so irin na tsakanin ɗa da iyaye yayi tasirin sa cikin ƙudurar ubangiji , wani irin so mai yawa mai tafe da tausayi da tsantsar zallar ƙauna marar gauraye irin ta iyayen da suke da matuƙar ƙwalafaci da ƙawa zucin ƴaƴan su , suka taso suka lullube zuciya zuwa idanun YARIMA YOUSSOUF ABDUL-AZIZOU BASKORE2

STORY CONTINUES BELOW

Yaji zai iya sadauƙar da kome da ya mallaka domin ya tsira da ƴar jaririyar ƴar da tayi rashin ɗumin uwa tun daga ranar zuwan ta duniya , rashin maihaifiya a tare da ita ya kassara illahirin gaɓɓan jikin sa , ji yake ina ma yana nan ranar da ta zo duniya alhalin uwar ta bata tare da ita , da tun daga ranar zai fara gwada mata ƙauna da tattali mai tudu biyu irin na uwar ƙwarai kuma jajirtattcen uba , tausayin ta yake , tausayin da bai taɓa jin yayiwa wani mahaluki irin sa ba , bai ƙi ba ace tun daga ranar haihuwar ta har zuwa lokacin da zata mallaki hankalin kan ta ƙirjin sa ya zama wajen kwanciyar baccin ta , so yake yayi mata rumfa ya zama mamar ta , kuma baban ta , ya zama ya cikace gurbi na duk wani makusanci da yaro zai nema cikin rayuwar sa na ƙuruciya , bai son ta tashi cikin maraici , tunanin hakan kawai na sauke ƙwalla a idanun sa , yana kuma katange tunanin sa daga duk wani ƙalubalen da kasancewar ƴar a rayuwar sa zai iya samarwa ,1

kou yanzou baby ta daina kuka ?

Ya tambayi Tafeddah wanda ya rafka tagumi hannu biyu ya zurfafa cikin tunanin yanayin da ya hango da alamomin da suka bayyana kan su ga Yarima daga lokacin da ya ɗora idanun sa kan ƴar jaririyar da a yanzu yake hango alamun zamantowar ta barazana ga farin cikin mutane da dama da suke kewaye da yariman , shi yasan wanene youssouf ,

a lokuta da dama ba sai ya masa bayani ba yake fahimtar abunda ke cikin zuciyar sa , sai dai ya san wannan karon Yarima zai zo da wani Al’amari mai girma muddin ya nuna son ƴar ta tsaya tare da shi cikin rayuwar sa ,

Abunda hakan zai haifar ba abune mai daɗi ba , bai son ko tunawa , yau ace yarima youssouf ya doshi cikin masarauta tare da ɗiyar da ya haifa ba tare da amre ba , al’amura zasu rinchaɓe,

kai ka kawo yake cikin tunanin sa yana son samar da hanyar da zai bi ya dakatar da yunƙurin yarima ya bar ɗiyar nan a inda ya dace ta zauna,

Tunanin sa ya katse lokacin da yaji youssouf ɗin nayi masa magana ɗagowa yayi ya dube shi

Me kake faɗi yarima ban ji ba ?

Ɗiyar nan ko ta daina kuka yanzou ? Wacce iriyar madarar jarirai ake bata ?

Sasarere Tafeeda yayi yana kallon youssouf ,

Anya kou ranka ya dade yarima ba’a bar batun jaririyar nan haka nan ba ?baka gani Allah ne ya doube mu ya kawo hanyar da zamu samu masalaha akan wagga lamari ya kawar da uwar ɗiyar domin mu samu mafita ,”1

abun da ni nake gani shine ka bar ɗiyar nan wajen masu riƙon ta tunda ba mu riga mun sanar da wani abu da ya shafi asalin mu ba ga mutanen nan ba, sai mu juya baya mu tahi abun mu ba tare da kowa ya san inda za’a same ka ba , ta iya yiwuwa ka dunga yin aike ta wata hanya mai nisa wadda zai dunga isowa ga ita ɗiyar nan , domin fa ka sani ita wannan ɗiya babbar barazana take a gare mu yarima da ma masarauta baki ɗaya , ko kouwa me kake tounani ne yarima ? Ko kouwa masalaha bata zou mana ba ??

Ya ƙarasa zancen yana kwantar da muryar ganin yadda Youssouf ɗin yake masa wani irin kallo mai karfi dake bayyana ɓacin ran da yake cikin ran sa ,

Tafeeda me kake faɗi haka mai kaushi , kana nufin na bar ɗiya ta jaririya nan nigeria hannun mutanen da ban sani ba ? ƙaƙa kake son rayuwar ƴa ta ta kasance cikin wahala tare da rashin galihu ? Baka tounanin tarihi zai maimaita kan sa ga ɗiya ta , rashin galihu yasa ta faɗa kwatankwacin halin da mahaifiyar ta ta shiga har ya zama silar faɗawar ta halin da ya zama silar samar da wagga ɗiya ? INA SON ƊIYA TA TAFEEDA , DOUNIYA ZATA KASSANCE TARE DA NI , DUK RUNTSI NI AI MAHAIFIN TA ,

A hasale Tafeeda ya miƙe tsaye

Amma ka san ita wagga ɗiya take ba ta halali bace kou ? Ita ɗin baka samar da ita ta tsafatataciyar hanya ba , ita ɗin barazana ce ga martabar iyayen ka da dangin ka baki ɗaya , barazana ce ga hawan ka ƙaragar mulkin masarautar mu , ƙazanta ce ita wacce ya kamata ka ji kunyar bayyana ta ba…..

tsawar da Yarima Youssouf yayi masa ya hana shi ,

Kome zai yanke tsakanin mu idan ka sake touzarta ɗiya ta Tafeeda , ita ɗin batta da laifin kome , ni ai nine za’a hukkunta , ita wagga ɗiya bata tare da dauɗar kome , ita ai abun a tausayawa ce ,3

ita ce kaddara ta Tafeeda ina roƙon ka da Allah ka taimaka mouna ni da ɗiya ta , ka tsaya tare da ni bisa lamurran ta ni nasani me tarin laifuka ne , ka duba wnnan ɗiya mai tarin rauni ,

Yarima youssouf ya ƙarasa zance tare da share ƴar siririyar ƙwallar da ta sauko masa ,

So yake ya samu mai taya shi son ɗiyar sa , so yake a bashi karfin guiwar tsaya mata , tafeeda yana da muhimmanci cikin rayuwar sa bai son ya juya masa baya a wannan gaɓar ,

Tare da wani irin yanayi yake kallon sa , bai son tausayin sa da ya fara ji ya rinjaye sa har ya taya shi aikata abunda yasan zai cutar da shi mummunan cutarwa , zai kawo tsaiko akan cigaban rayuwar sa , idan yayi haka shi yasan bai kyauta ba Amintaka bata cika ba, kuma hatta shi fushin iyayen yarima sai ya shafe shi , kai shi fa basshi da ƙwarin guiwar da zai bada goyan baya ga yarima a wannan gaɓar ,”

Yarima idan ka ɗau ɗiya jaririya irin wannan ka tahi da ita zouwa ina ?

Zan yi amre na bada riƙon ta ga maimounatou zata riƙa min ita ,”1

Kana da tabbacin ƴar sarkin agades ɗiyan gata irin ta zata yadda tayi maka riƙon ƴa ?

nakan iya haƙourewa dagga amren ta muddin batta riƙon ɗiya ta.

Murmushin takaici tafeeda yayi

kace da maimartaba da hajiya umma , da ƴan uwan ka me ??

Kaddara ta ce ta zou a haka , nasan umma zata fahimce ni ta fahimtar da maimartaba ƴan uwa zasu min uziri da afouwa ,”

wanne irin tanadi kake tounanin maƙiya zasu yi ta hanyar ɗiyar nan su kawo naƙasu cikin rayuwar ka tare da lalata mana sunan masarauta ?

Maƙiyi shi ai kullum maƙiyi ne , shi kuwa jajirtatcen namiji badda maƙiyan sa yake ,2

gƴaɗa kai tafeeda yake yana iya hasaso gingimemen rikicin da Toussouf yake neman tsunduma kan sa cikin rayuwa ,

Allah shi badda sa’a yarima

Amine !

yarima ya amsa yana jin daɗin ganin kamar tafeeda ya sauko zai goya masa baya ,

Yaushe zamou kouma ka ga ɗiyar nan ɗan ouwa ?

Gobe iwar hakka na hantse a ƙassa ta ta haihouwa ,

Gobe kake koumawa ɗan ouwa ?

toh zaman me zan yi a nan na baro aiki na ? Gobe da iznin Allah nake koumawa .

Allah shi kaimu ,

Yarima Youssouf yace yana ƙarasawa gaban window ɗakin ya yaye labulen yana kallon rana da tayi yamma take gaf da tafiya ,

Ran sa cike taf da son sake ganin fuskar ɗiyar sa ….!!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *