RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 13 KARSHE END BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 4  CHAPTER 13 KARSHE END BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA

Baban Justina ya Kwace Umma daga hannun matarsa Rabeka, ya dubi su Umma ya ce, “Me ke tafe da ku?”  Umma ta nuna Nasreen da Naufal ta ce, “Wadannan ‘ya’yan sune Saudatu ta Haifa. Ina . nufin jikokinku ne.” Rabeka ta kafe su Nasreen da idanu, a lokaci guda Nasreen ta Karasa kusa da ita Www.bankinhausanovels.com.ng hawaye suna zuba, tana jin za ta fi yin alfaharida_ – su, fiye da mahaifinta. Ta rungume Rabeka ta saki kuka. Rabeka ta rungume Nasreen ta hada da Naufal. Gaba daya kuka suke yi. Sai bayan sun zauna ne Umma ta nuna Sultan, sannan ta gaya masu duk yadda aka yi. Sultan yasha albarka, haka sun Karyata maganar da ake fadi akan musulmai, sun tabbata a cikin musulman akwai na Kwarai akwai kuma bata gari. Sun yi alKawarin zuwa suga gidan Nasreen. 

ZAMU TASHI 

Nasreen kuwa taKi tafiya tace a tafi a barta, tana son yin hira da Kakanninta, tana son jin labarin mahaifiyarta. Dole Sultan ya tafi ya barta, cike da takaicin rabuwa da ita na kwana daya. Tana kwance a cinyar Kakarta sai zuwa ake ana ganinta, ta ji alamun shigowar saKo ta wayarta. Ta bude tana karantawa, “Baby kin sami su Kaka kin mance da ni ko?” Murmushi ta yi, domin ita kanta tana kewar mijinta. ‘Sorry Deena, kana cikin raina, sai dai kasancewata a cikin dangina ya fiye min komai dadi. Amma kai kasan babu inda zan je in manta ° da kai.” Yana ganin saKon ya yi murmushi yg ce, “Haba yarinya, aronki kawai muka ba su, mune * asalin danginki, da dangin uba ake ado ba dangin uwa ba.”


Murmushi ta yi ta ci gaba da sauraron Kaka, kada ya dauke mata hankali ya hanata shan labari
Cikin dare daga ita har shi babu wanda ya yi barci, suna manne a waya suna shan hirar su.
Washegari da kansa ya zo -ya tafi da ita. Yanzu Nasreen ta zama ‘yar gata agun dangi, kowa ji da ita yake yi. Haka Baba Sani ya tabbatar mata shi ne mahaifinsu su dauke shi
matsayin uba. Ita kanta Ummi duk motsi sai ta ji -dalili. Zakiyya kuwa baKin cikinta da take fama da shi, yasa taci burika kala-kala akan Nasreen. Da dawowarsu Nasreen ta fara fama da Infection mai bala’in zafi. Wasa-wasa abu ya fara nisan da ko Sultan bata son gani a kusa da ita, saboda azaba. Hankalin Sultan ya Kara tashi a sakamakon shi ma ya kamu da cutan sanyi. A wannan karon ma Yumniah ce ta sake ba su lambar Abun yabo, winda ya warkar da ita daga cutar jinnu, ta tabbatur masu idan dai maganin sanyi ne, sai dai su ji wasu suna yl, ba dai su ba. Wannan karon ta waya suka yi magana, aka turo da maganin ta mota..raba daya suke amfanr da shi, a sati daya suka nemi ciwo suka rasa. sun warke ras. ”
Yau ya fita office yana jin natsuwa a ransa idan ya tuna yau Nasreen dinsa ke da girki, haka yana da tabbacin zai sami natsuwar da ya rasa ta a kwanaki biyu. Lokaci zuwa lokaci yakan tuna da case din Baba Mu’azzam wanda gobe za a yanke masu hukunci. Shi kansa yasan_ ko hukuncin kisa ko hukuncin daurin rai da rai Yana kula da yanayin Nasreen kwana biyu tana cikin damuwa gosai. Da isarsa gida ya sami Nasreen tana yashe kamar bata motsi. Hankalinsa ya tashi, ya girgiza ta shiru, kanta yana fitar da jini. Cikin gaggawa ya mike ya shiga dakin Zakiyya a nan ya ji tana waya, “Shegiyar tana can a yashe a falo na kwada mata kwalba. Daga ina mata magana, kawai ta dinga yi min kallon banza ni kuma kinsanni ba ayi min in bari. Dambe sosai muka yi, gudun kada ta kada ni na kwada mata kwalba. Eh ya fita tun dazu hankalinsa yana tashe za a yankewa Mahaifin Nasreen din hukuncin kisa. Suna zagin wasu ashe su sun fi kowa abin kunya’ Zakiyya ta dan saurara sannan ta saki shewa tana bayar da labarin yadda aka yi suka turawa Nasreen aljanu, da kuma yadda akayi aka mallake Sultan daga baya ya kubuta, da irin maganin da take sa masa kafin ya sadu da ita. Daga Karshe ta yi maganar da ta gigita shi wato zuwa da ta yi aka yi mata dinki dan ta koma budurwa, da haka ta raina masa hankali.
Sultan ya shigo dakin yana dubanta, hakan yasa ta saki wayar a Kasa tana rawar jiki. Fizgo ta ya yi ya shiga duka babu ji babu gani, sai da ya tabbatar da ya sabauta mata kamanni sannan ya jawo hannunta ya watsar da ita waje ya kwalawa Dan sandansa kira, ya ce maza ya kaita tasha ya tabbatar ya sanyata a motar haya, ya hadata da kudin mota. Da sauri ya koma ciki, ya dauki Nasreen yasa a mota aka ja su sai asibiti. Gabadaya ya mance bai hada ta da takardarta ba. Bayan an gama yi mata Dressing ta farfado babu wanda ya iya cewa komai, sai da za su wuce gida ta riko hannunsa cikin sanyi ta ce, “Ka kaini gidan Yumnah in zauna kafin ka sama min wani gidan, ba zan zauna anan gidan ba.”
Rungume ta ya yi ya ce, “Kada ki damu mu je gidan.” Bata sake magana ba, suka koma gida., Har ta gama shan magungunanta babu wanda ya ce Kala, haka bata ga Zakiyya ba, tana son’ – tambayarsa amma kuma barci yana cin idanunta. ~” Anan ta zube tana barci. Har washegari da Sultan ya matsa mata su je Kotu Nasreen bata san Zakiyya bata gidan ba. Abin mamaki sai ga su Naufal da su Umma, harma da Abba da Anti Mairo. Suna nan zaune har aka yanke masu hukunci, wanda hukuncin daurin rai da rai aka yanke masu.Baba Mu’azzam ya dubi sashen su Nasreen da take kuka kamar ranta zai fita, ta kawar da kanta, Ya tsaya ya dubi su Nasreen ya ce, “Idan baku yafe min ba, na shiga uku. Idan ba ku kirani da Abba ba, bansan yadda zanyi da hakkinku ba.” Sai a lokacin Nasreen ta kula ashe ‘ya’yansa dukka su shidan sun iso wurin har da mahaifiyarsu.
Dukkansu suka Karaso suna kukan halin da mahaifinsu ya shiga. Nasreen ta dago tana duban Abba, ya gyada mata kai, ta dubi Sultan shima kai ya gyada mata. Cikin sauri ta Karaso gabansa, a lokacin da Naufal ma ya Karaso kusa da shi, suka hada baki suka ce,” “Abba.” Sai kuka ya goce masu. Nasreen tana girgiza kai ta ce, “Abba ka kashe mana rayuwa, ka mayar da mu marayu. Ka jawo mana abubuwa da yawa. Abba babu wani da da zai ga mahaifinsa a cikin wannan halin ya ce zai juya masa baya. Na jima da yafe maka, albarkacin Deedi. Abba ka sa mana albarka.” Naufal da Nasreen suka durkusa Kasa. Ya dinga sa masu albarka yana gode masu, har aka tafi da shi. ‘Ya’yansa da su Nasreen suka rungume juna suna kuka mai ciwo. Har akayi kwana biyu Nasreen bata daina damuwa ba, sai da Sultan ya yi ta mata nasiha sannan ta dan sarara. Sultan ya kira Umma a
waya ya ce mata, “Umma ciwon da kike ta matsawa kina tambayar wanda ya ji wa Nasreen ba kowa ba ce Zakiyya ce. Ban ce maki komai bane saboda matsalar Baba Mu’azzam. Don haka ni na gaji sosai.”
Ya kwashe dukkan abinda ya ji ya gaya mata, sannan ya Kare da cewa, “Umma na saki Zakiyya saki daya. Kuma ina sake rokonki ki fita harkar Hajiya Ladidi ba. masoyiyarki ba ce. Ciki kuma da take cewa tana da shi babu komai.”Umma ta gyada kai, “Kayi min dai-dai Sultan kuma ka haifu. Hajiya Ladidi tun ranar da ‘yarta ta dawo ba mu sake shiri ba. Ashe har Babanku ta je tana nema, banda bata ni da ta yi agunsa duk yaki amicewa. Ni yanzu ina lallaba rayuwata ce. Jiya kuma iyayen Salim sun zo gidan nan, sun roki ka saki Salim sun amince za su ci gaba da kulawa da Hafsat har ta haihu, idan ta haihu sai a daura masu aure. Don haka ka sake shi kawai, ko.a haka ai ya horu.” Sultan ya shafi kansa, “Babu damuwa yadda kika ce haka za ayi. Ina Anti Mairo?” Umma ta kwadawa Mairo kira ta mika mata wayar. Sultan ya ji dadin wannan hadin kan, yana da tabbacin yanzu mahaifinsa zai dawo da jikinsa, haka gidansu zai dawo tamkar da.  Nasreen tana ji an saki Zakiyya hankalinta ya tashi, za ta yi magana ya hanata, dole ta zuba masa idanu. Ita kanta ciki gareta ba tare da dukkansu sun san da cikin ba. Yau suna kwance tace, “Wai inane asalin su Umma?”
Sultan ya ce, “Cewa za ki yi ina ne asalin ku? Mu ‘yan asalin Maiduguri ne, a Karamar hukumar Biu, Umma kuma ‘yan Katsina ne, da yake gaba daya dangi an dawo Kaduna, babu sauran ‘yan uwa na kurkusa a can, sai gaba daya muka koma muka saje da ‘yan Kaduna. Kin ji asalin mijinki kin ji asalinki. Ta jinjina kai ta ce, “Ya maganar su Anti Nova? Wani taimako za a ba su?” Murmushi ya sakar mata ya ce, “Su Ashmaan sun gama komai, har sun _ karbi musulunci, haka su Kaka sun karbi musulunci agun Ashmaan.”
Nasreen ta tashi zaune tana dubansa, idanu a waje, “Kana nufin yanzu su Kaka musulmai ne? Me yasa baka gaya min ba Dee?” Kunnuwanta ya kama ya rike, “Tuba nake yi ina son in baki mamaki ne, in dauke ki in kai ki gidan, bansan me yasa bakina ya subuce na gaya maki yanzu ba. Babu abinda zan cewa su Ashmaan, sai fatan Allah ya biya su. Sunyi abinda, naira daya nawa ciwon kai, kowannansa ya ajiye dumbin aikinsa, ya zo ya tallafa min. Yanzu haka na shirya mana dukkan mu zamu fita Kasashe uku domin yawon bude idanu. Daga Karshe zamu dire a Saudiya mu gode wa Allah bisa dora mu da ya yi akan maKiya ya kuma bamu ikon warware komai cikin nasara.” Nasreen ta rintse idanu ta ce, ““Wato dee duk yadda nake ganin muna da hadin kai, ku mazajen mu naku yafi namu Karfi. Ina-rokon Allah ya dauwamar da kwanciyar hankali a cikin wannan zumunta. Ina son in koma Islamityya domin samun daman zuwa Gasar Alqur’anin da ake yi duk shekara.” Gyada kansa ya yi yana jinjina Karfin wayonta. Kamar an tsikare shi ya ce, “Ke wai yaushe rabon da kiyi al’ada a gidan nan?” Ta daga kai sosai sannan ta ce, “Wata biyu kenan.” Murmushi kawai ya yi bai ce komai ba_ a. Cikin hukuncin Allah cikin Hafsat ya zube, bayan ta sami lafiya sosai, aka daura aurer ta da Salim, da yake ta rawar Kafa, wanda dama yana sonta, sal kuma tsoron Yayanta Sultan. Haidar ya samu fitowa a matsayin Soja, mai ji da kansa. Ranar da suka zo gida Sultan yana tsaye yana duban yadda Haidar ya Kara girma da kyau. Haidar ya Karaso yana dariya, ya ce “Wato Yaya Sultan kwarjininka na daban ne. Ya za a yi ina sanye da kakin’sojoji, amma ka firgitani haka?” Sultan ya yi murmushi ya dafa bayansa suka Karasa gun Abba. Hankalin Abba a kwance ya yi kyau da Kiba. Yana ganin ‘ya’yansa ya saki murmushi, “Allah ya yi maku albarka. Allah ya sakawa Khamis da alkhairi. Yanzu saura aure ko?” Haidar ya dubi Naufal da shima yake gaf da dora kakin ‘yan sanda yace, “Abba amma dai a bari Naufal ya fito sai a hada mu dukka ayi mana. auren.” Gabadaya dakin suka yi dariya. Naufal ya ce, “Ai na ga kai Kanwata kake so, da alamun ni zan koma inzama yaya.” Abba ya zaro idanu ya ce, “Ba dai Badiyya yar wajen Alhaji Mu’azzam ba?” Naufal ya gyada kai, “Ita kawa Abbana.” Haidar ya ce “To gara dukkan mu a tona asirin kowa. Shi ma Rufaida yake so ‘yar wajen Baba Sani.” Abba ya yi murmushi ya ce, “Wato dai Hafsat ce kawai ta fita daga cikin dangi ko? To Allah ya nuna mana lokacin yasa ayi komai cikin nasara.”
Sultan ya yi murmushi yana satan kallon  Nasreen sannan ya ce, “Abba Nasreen fa bata da lafiya.”
Nasreen ta kalle shi kamar za ta yi kuka, ta ce, “Ayya Abbana ba gaskiya bane, lafiyata kalau.” A nan duk suka fahimci abinda Sultan yake nufi, aka yi ta mata dariya. Cikin ‘yan kwanaki Ashmaan, Aslaf, Alameen, Barr Tajjud da su Khamis da Mahbub suka shirya da matansu za su fita Kasar, kowannen su cike da farin: ciki, domin ansan sabuwar soyayya za a bude a can. Sai mu ce Allah ya dawo da su lafiya.

BAYAN SHEKARU HUDU

Nasreen ce zaune tana baiwa Danta Lukman wanda ake kira da Asaad, ya ci sunan Abban Sultan abinci, yaron dan shekaru uku da rabi
yi wayo abinsa. Kanwarsa Saudat wacce ake kira da Yesmeen watanta biyar a duniya tana ta sharar barcinta. Sultan ya shigo hannunsa dauke da ledoji.
Cikin sauri ta tare shi, ta amshi kayan ta ajiye a Kasa ta rungume shi sosai a jikinta, “Barka da dawowa yallabaina. Tun kana hanya naji Kamshinka ashe da gaske kana tafe.” Kallon Asaad suka yi gaba daya a ya yin da ya shige sakiyarsu yana fadin “Deedina Oyoyo.” Nasreen ta zaro idanu, “Ka ji min yaro da Kwace. Deedinka, ko Deedina. Maza kaje ka . nemo Dee dinka a gidan Babanka Naufal, ko Baba Haidar.” ° Yaron ya noke kafada yana miKawa Sultan hannu. Sultan ya dauke shi yana juya shi, sai KyalKyatan dariya yake yi abinsa. Sannan ya sauke shi yana cewa, “Ina Mamana farin cikina? Don Allah dauko min ita.” Nasreen ta ce, “Ayya Dee barci take yi.” Ya Karaso har in da take kwance ya ce, “Kema kinsan duk barcin da take yi idan na dawo sai na tashe ta. Bana tunanin zan iya zama na minti biyar a gidan nan babu uwata a kusa da ni. Ita fa ta Haifa min matar da nake so fiye da kowacce.” Nasreen ta jawo Asaad ta rungume tsam, ta ce, “Ni kuma ina ji da wannan gwarzon wanda ya Haifa min miji na gari, ya kuma tsaya tsayin daka ya taya mijina renon matarsa. Bana jin ina da abinda zan iya biyanka da shi Abbana.” Gaba daya suka dubi juna suka yi murmushi. —_ ‘ .

ALHAMDULILAH MASHA ALLAH ANAN MUKA KAWO KARSHEN WANNAN KAYATACCEN LITTAFIN MAI SUNA RUBUTACCIYA WANDA MUKA FARA TUN DAGA LITTAFI NA DAYA HAR IZUWA NA HUDU ALLAH YA BAMU IKON AMFANA DA DARUSSAN DAKE CIKINSA

SAIKUN JINI CIKIN WANI SABON LITTAFIN NAN BADA JIMAWA BA KUDAI KU KASANCE DA WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG A KODA YAUSHE DOMIN KARANTA NOVELS KALA KALA A KULLUM KUMA A KODA YAUSHE FATAN ALKHAIRI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *