MAFARIN SO CHAPTER 2
Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai kallonshi take ta kasa ko k’ifta ido, guy ɗinnan ne da suka haɗu zataje wurin lalle, guy ɗin da take iƙirarin duk dunia babu wanda ta tsana kamanshi, yau sai gata kwance male-male a ƙirjinshi, wannan wanne irin baƙar rana ne take gani?.
A hankali yaɗan hura mata iska a idonta, ta dawo daga tunanin da take har lokacin idanunta na kanshi, da idanunshi ya kalla inda ta rirriƙeshi da hannu ta kasa saki, sannan ya sake kallonta, alaman yana mata tuni da riƙon data mishi kenan.
Da sauri ta sakeshi tana gyara tsayuwarta, ta juya gaba ɗaya mutanen wuri su suke kallo, ɗan matsowa yayi dab da ita, ya raɗa mata a kunne,
“Kinsan kuwa ko rigan nawa ne kika cukuikuye?”, ta buɗe baki zatai magana ya dakatar da ita, a hankali ya sake furta mata wata maganar, da sauri ta tureshi yana dariya, juyawa tayi tabar hall ɗin ko su Zahra batai ma bankwana ba,
Koda ta isa gidama, ɗakinta kawai ta wuce, ta rufe wayanta ta jefar ta kwanta ko kaya bata canja ba, tunani ta ringayi kala-kala, haushinshi da tsanarshi na k’ara yawa a zuciyarta, wata zuciyar tace ‘taimakonki fa yayi, da ƙasa kika faɗa da kinji jiki’, taja tsoki, ‘aeni yamafimun in faɗi k’asan da rikon da yamun’ haka dai ita kaɗai ta ringa zancen zuci, ranar kam don barci na ɓarawo ne kawai ya iya saceta,
Daman bata kwana da niyyar ƙara zuwa wani Shiri na bikin ba, sai kai Amarya kawai, don haka yau kodata farka, ƙin fitowa tayi, daman taga text ɗin yayanta ya tafi aiki, tananan ɗaki sai dai su Hayran suka shigo tayata fira, da taga zasu damewa ta kunna musu tarihi suna kallo ta shigewanta,
Tana cikin tunani sai ga Hayrah ta shigo ɗakin, sai dai taji an taɓata har saida ta firgita, “Aunty Rabi’ah me akai miki?”
Murmushi tayi, “Ba komai Hayrah me kika gani?”
“Duk yau baki fita ba, kuma baki zauna munyi kallo tare ba”
“Ai nace ku fara zanzo”
“Um-um nidai Auntie kallon babu daɗi ba bakinan”
Hayran ya shigo da gudu, “Auntie ya ƙare, zamuje siyen chocolate ɗin?”
“A’ah ku bari sai gobe”
“gobe fa akwai tahfiz, please Auntie, please, please!!!”
“Naji toh! Kuje ku shirya” da gudu suka fita suna Murna, sannan ta tashi itama ta shirya, tana gamawa sai gasu,
“Kun faɗa ma Momie?”
“A’ah, zata hanamu ne”
“bazata hanaku ba, muje a faɗa mata” ta kamo hannunsu suka fito, suna ganin tayi hanyar bangaren Aunty deejah duk suka saki hannunta, suka rigata fita wurin motar”
Ita kaɗai ta shiga, “Auntie deejah mun fita dasu Hayran Shopping”
“wanne irin shopping kuma? Salon dai ki koya musu yawo irin naki da kullum baki zaman gida, toh babu inda zasuje komai suna dashi, inma suna buƙata zanyi wayane a kawo musu”
“haba Auntie ai sun ɗan fita suga gari, daga makaranta sai makaranta, kowanne yaro fa yanason wasa, kuma idan sun fitan zasuji daɗi”
“oho! Nace dai bazasuje dake ba”
Taɓe baki tayi, “saimun dawo” ta juya ta barta.
Ta ƙwala murya tana faɗin, “awh! Tafiyar zakiyi dasu? Ni daga yau in zaki fita gantalinki ƙarama ki daina faɗamun, tunda ko nayi magana ba jina kike ba, kuma bari yayan naki ya dawo, nidai na gaji da wannan abu” ta ringa faɗa ita kaɗai cikin gida.
Wuraren wasannin yara da yawa ta kaisu, ita kanta ta ɗanji sauƙi a zuciyarta, sai da sukasha yawo sosae, Yamma liƙis sukaje wani babban Shopping mall a garin katsinar, siyayyan kayan zaƙi sukayi sosai masu tsada, tana riƙe da ledojin a hannunta suka fito,
Sun kusa fita daga wurin, Hayrah yace “Auntie kawo na riƙe nima”
“A’ah, ae babu nauyi” ta duƙa tana mishi magana, ɗagowan da zatayi sai dai taji tayi karo da mutum, gaba ɗaya ledojin hannunta sun faɗi, komai ya zube.
Ɗagowa tayi da niyyar fara faɗa, suka ƙara haɗa ido da wannan guy ɗin dai data tsana wanda ko sunanshi bata sani ba, girgiza kai yayi yana kallonta, yau ko murmushin bai tsaya yi mata ba sai dai kallon mamakin daya bita dashi,
“kedai baki taɓa duba gabanki idan kina tafiya?”
“ni dakai dai, ai kaine ya kamata kana kaucewa”
Ta kamo hannun Hayran daya duƙa yana tsince sweets ɗin, ta kamo hannunshi, “ka barsu anan ka tashi mu tafi”
Ya miƙe, Guy ɗinma ya riƙo hannunshi harta juya zata tafi ta tsaya,
“sake mishi hannu”
Ɗaga kafaɗa yayi, sannan ya girgiza kai, ta ƙara jan hannun Hayran zata fizgeshi ta kasa, ta juyo tana hararanshi, ya sakar mata murmushi yana ɗaga gira, ya cema Hayran,
“Abokinah muje nima ka rakani” suka wuce, ta bisu da harara, sannan taja hannun Hayrah suka bar wurin a zuciye.
Sun daɗe a mota tana jiran Hayran, harta fara ƙosawa da jiran duk ranta ya gama ɓaci, sai shawaran ta tafi take, wata zuciyar na hanata, idan ta koma gida babu Hayran kam tasan ko ya dawo, Aunty deejah sai tayi sati tana aikin masifa, ba tsoranta takeji ba, anma bazata ita barishi ba, tananan zaune a mota sai saƙar zuciyah take, ta hangosu yana riƙe da hannunshi, suna labari suna dariya harda tafawa.
Siyayya yayima Hayran sosae, harma tafi wadda sukayi a farko, ya kawoshi har wurin motar ya buɗe mishi ya shiga ya rufe, su Rabi’ah sai kumburi take,
Ta tada motan zata tafi, “Sai Anjima Auntie Rabi’ah” ko kallon inda yake batayi ba, ta fizgi motan ta tafi,
Tana tafiya Hayran sai bata labarinshi yake, wani irin tsawa ta daka mishi har saida ya tsorata, don tunda suke ko faɗa bata taɓa musu ba,
“na tambayeka labarinshi ne? Watau bakajin magana ta sai tashi ko, nace karka bishi harda juyawa da binshi”
Kaman zaiyi kuka yace “yi haƙuri Auntie, ke kikace muna yin abunda manyanmu sukace”
“kasanshi ne? Idan ya sayar dakai fa? Kuma wayace ma ka faɗa mishi sunana?”
Duk ya tsure da yaji tace zai iya siyar dashi, “Tambayana yayi, kuma naga yana da kirki…..”
“kaimun shiru nace” nan ya kame bakinshi yayi shiru, sai da suka kusan ƙarasawa gidan yace “Anma dai Auntie ba mai siyar da mutane bane ko? Kirkine dashi sai fira yakemun”
“ai wayau yake makane, yanda zaiji daɗin kaika a cire kan” aifa nan take idanunshi har sun kawo ƙwalla, Hayrah ma jikinta har ɓari yake ta rirriƙe ɗan uwanta,
Ita kam Rabi’ah fuska tayi, duk da sunso su bata dariya, anma ta dake don guy ɗinnan ya gama bata haushi.
Da suka isa gidan, suka biyota da ledojin siyayyan har ɗakinta,
“Auntie ga kayannan”
“kuna so kuci ku ɓace ko? Ku kaima Baba mai gadi, in kukaci babu ruwana”
“nidai bazanci komai ba Auntie”
“nima ba ruwana” suka juya da kayan, itama bin kayan tayi da harara, ‘ko wayace yana bukatar siyayyanshi?’
Yar gatana taken naki nada banne kin wuce kawa kin wuce aminiya kin zama yar uwa kuma gudan jini *My Amnoor Allah ya kara mana donkon zumunci da kaunar juna😘*
Cikin jin haushi tace, “ko wayace yana bukatar siyayyanshi?’
Ta koma kan gado ta kwanta cike da takaicin wannan gayen aranta tace “dama wanka masa mari nayi”
Hayran ne tsaye a bakin kofar dakin Rabi’ah, ya jinginar da ledojin jikin bango dan a tsorace yake da kayan, tunda Antynshi tace za’a cire masa kai,
Anty deejah ce ta fito neman Hayran din, dan taga Hayrah adakinsu tana Game, tana hangoshi tace, “kai tsayuwar me kake anan? “
“Bakomi”, yabata amsa
“To muje ka kiyi wanka ka kwanta”
“To momie ya fada yana kokarin kare ledojin dan kar tagani,”
Bata kulah dasu ba tayi gaba abinta, shima Hayran ya tafi dakinsu,+
Washe Rabi’ah ta fito zata shiga kitchen saboda yunwar da takeji, gashi kuma tanason yima yayanta girki, Abakin kofa taci karo da kayan da dan rainin hankalin guy ɗinnan nan ya bama Hayran Sunan da ta raɗa masa kenan, a zuciya tace ‘kenan Hayran bai kaiwa Baba megadi wannan tarkacen ba ko,’ ta ƙwafa ta wuce,
Kitchen din ta nufa tabar kayan nan A inda suke, kunun alkama tayi, da ƙosan dankalin turawa wanda yaji nama a ciki, ta hada da ruwan zafi ko zaisha tea,
A tire ta jera komai, bayan taa gyara wurin data ɓata, sannan takai ma yayanta nashi, ta fito da nata a falo ta zauna tana ci,
Anty deejah ce ta wuce taga ban Rabi’ah kaɗan ya rage ta ɓarar mata da abinci,
Rabi’ah kaman bazata tankata ba, ganin tana sane yasa tace, “ashe gidan namu harda makafi.
“Anty deejah tace yayanki ne makaho kuma ya aje makauniya”,
Abin daria ya bama Rabi’ah azuciyarta tace ‘daman nasan jira kike na tanka”,
Azahiri kuma cewa tayi “Lahh! Aunty deejah ce kiyi hakuri ban kula ke bace shiyasa” banza ta mata sai harare-harare take, Rabi’ah na riƙe dariyar da take ta sake cewa.
“bismillah ga break fast,”
Mamaki yakama Anty deejah takasa cewa komi wai Rabi’ah ce ke bata hkr kode gamo Rabi’ah tayi,
Taɓe baki Aunty deejah tayi, sannan tace “naki na haƙuran, wani salon rashin mutuncine zaki fitomin dashi ko dan kinga yayanki na gida,”
Rabi’ah batasan tabiyewa deejah ne dan karta ƙara hauda mata wata damuwa bayan wacce gayen nan yasakata, Kayan da taci abinci ta haɗa ta kai kitchen tabar Anty deejah a palon, itama deejah tanata faman masifa tabar palon,
Tana fitowa daga kitchen ɗin ɗakinta tanufa, sai alokacin ta kula da wata karamar takarda manne jinki lodojin dayan an rubuta (this is for uh Aunty Rabi’ah) dayar kuma ansa (and this one is for my kids)
Dayar tatace dayar kuma ta su Hayran ce,
Kawai taji zuciyarta nason sanin mike cikin ledojin, sau biyu tana kai hannunta za ta dau ledojin sai ta fasa, A na uku ne ta daure ta daukesu ta nufi dakinta da su, na su Hayran ta fara dubawa taga chocolate kala kala, kayan wasa niƙi-niƙi, kayan ya jibgo masu su dayawa, A ranta kuwa cewa tayi wannan mutumin akwai ɗan rainin hankali, ya gama ɗagamun kai harda wani siyayya zai musu, ta kwashi kayan tanufi hanyar dakinsu hayran, zata kaimasu, abakin ƙofar dakin su ta tsaya to idan suka tambayeta idan sunci baza su mutu bafa ko kansu ya fita, ta bata lokaci tana tunanin me zata fada masu kafin ta shiga dakin, ta tura kofar da sallama, da gudu suka taso suka tareta, “morning Auntie”
“Morning, Ya kuka tashi?”
“lafiya lau”
“yauwah naji daɗi, ga siyayyan kunan kusaka kowane inda ake ajiyeshi, ga kayan wasa kuma gasu chocolate,” Ai fafurur suka ki daukar kayan wai kar acire masu kai tasha wuya kafin su yarda bazasu zama doya ba idan sunci, Hayra kuwa cewa tayi zata fadama Abbanta koda anga tazama doya to Uncle ne ya saida ita, daria sosai Rabi’ah take, tace “hayra kenan kinaso Daddy yamun fada ko”
“A’a Auntie” Hayra ta fada,”
“kar kifada ma Abbanku” tace,
“To Anty bazan fada ba, Hayran kuwa har ya fara shan dadinshi, ta tayasu suka jere kayansu sannan ta koma dakinta,
Tana shiga ta buda dayar ledar daman duk ta ƙagu dason taga wacce siyayyarne aciki, ta fara ciro manyan turaruku masu tsadar gaske kala biyar,
“lallai ma mutuminnan, an faɗa mishi na rasa turaren dazan shafane?” ta fada a zuciyanta, sannan mayuka masu kyau sosai da kwantar da fata, sannan kayan Make Up masu tsada sosai ya siyamata, ta kara ciro wata leda daga cikin ledar da take dubawa, tace “nan kuma miye?” Yage ledar tayi dan taga Meke ciki abinda tagani yasakata suman zaune (Pants, brezia, cutton), ita tama manta data siyesu a cikin siyayyar da sukayi, a fili tace, “Anma mutuminnan ya gama dani, ɗan iska kawai, ɗan rainin hankali” har hawaye ya fara zubo mata tsabar jin kunyar kanta,
Rabi’ah ce zaune abakin gadonta sai cika take tana batsewa, tama rasa wane irin wulakanci ne guy dinnan ya mata, ita zaya maidawa siyayyar underwears, ina ma yanzu ta fita ta ganshi aida tamasa wulakancin kare dangi,
Wayar tace ta ɗau ruri alamun kira yashigo tana dubawa taga Amrah ce,
“Hello” tafada murya ba alamar walwalah,
Amrah tace “Haba wai miyasa koda yaushe kikeson ɓata mana lokaci yanzu gashi ke muke jira kuma kinsan zuwa anjima zamu tafi kai amarya,”
“Kibarni kawai Bestie yau irin ɓacin ran danake ciki tunda aka haifeni ban taɓa shiga irinshi ba, banajin zan iya zuwa koda ƙofar gida ne,”
“Miya faru kawata” inji Amrah
Rabi’ah tace, “menene ma bai faruba? kinsan gayen nan rashin mutuncin da ya Shukamin kuwa,?”
“kekam a ina kika ƙara ganinshi? Naga jiya bakizo kamu ba”
“a shopping Mall mana, wai ni zaya sayawa Underwears,”
Daria sosai takama Amrah, Anma ta dake saboda sanin halin ƙawar tata, tace
“har yaushe Soyayyar ku tayi girman da zai saya mikin irin wanan kayan kuma?”+
Wani baƙin ciki ne yadaki zuciyar Rabi’ah “Siya nayi, mukayi karo komai ya zube nabar mishi na tafi, shine fa ya riƙe Hayran saida ya sake mana wani siyayyan”
“kema da laifinki, tunda kinsan akwaisu cikin siyayyan ai da kosu kaɗaine kin ɗauke”
“Hmm ni ɓacin rai ma yaa barni na tuna?”
Rabi’ah ta kara nisawa sannan tace “Natsane shi, bana sonshi, da zanganshi dana nuna masa kuskuransa na farko a rayuwa,” kamar zautatta take fadin wadan nan kalaman,
Amrah tace, “kiyi haƙuri kawai kizo muje kai amarya, kinsan bamu kyautawa stylish ba idan bamuje ba”
Sai a lokacin Rabi’ah ta tuna da taganshi wajen dinner, “Yauwa ƙawata ganinan zuwa”
Amrah cewa tayi “Allah ya kawoki lafiya”
Toilet Rabi’ah ta shiga tayi wanka ta ɗauro Alwala tana fitowa da ɗauko sallaya da kayan Sallarta ta gabatar da Sallan La’asar, sannan ta dauko lallausar Man shafawarta ta shafa, Rabi’ah akwai son gayu, wata tsadadiyar Material ta ɗauko kalar Golden da maroon wacce ɗinkinta yayi masifar kyau da tsaruwa, tasaka ɗinki yayi ɗas ajikinta kamar dan ita, yar ƙaramar sarƙar zinari tasaka da ɗan kunne, da awarwaro, ta ciro gale golden da takalmi golden, ta ajiye gefen gadon ta, ta nufi inda kayan shafe shafenta suke hoda da kwalli da lip’s kawai tasaka, sannan ta dauko ɗan kwalinta ta dauran naɗin zamani, Har takusa mantawa da ɗaukar fansa zata je, Turarenta mai ƙamshi ta feshe jikinta dashi.
Tayi kyau sosai, ta fito ta nufi ɗakin Yayanta,
“Hayran! Hayrah!!” kuna ina ta faɗa
“gamu anan” suka fito daga inda suka buya suna daria , Hayrah tace
“kinyi kyau Auntie” Hayran yace “Eeh wallahi Auntie,”
Kama Hannunsu tayi, “Kuzo muje wajen daddy in mishi bankwana zanje kai amarya”
“To Auntie” suka faɗa a tare,
Ta jasu zuwa hanyar ɗakin daddynsu Hayrah,
Da sallama suka shiga, Ya Amsa sallamar sannan ya ajiye wayar shi akan ɗan karamin table ɗin da ke cikin palon da Alama waya ya gama
Rabi’ah tace “ina wuni yayana”
“lafiya lau kanwar ina zuwa haka?”
“Kaa manta kai Amaryan da mukayi magana”
“Ohh! Inane na za’a kai amaryar?”
Rabi’ah tace “A kano ne Yaya,”
“toh kar kiyi dare sosai kinji ƙanwata, kinga ba kwana zaki ba dakin ga gidan ki dawo da wuri”
“tohh Yaya insha Allah”
“Kuɗi fa? Nawa zasu isheki zuba Mai?”
“Ina da mai, kuɗin liƙin rannan ma banyi amfani dasu ba”
“Tohm shikenan, sai ki canja mota tunda tafiya zaki mai nisa,”
Daman tunda Aunty deejah taga tayi Hanyar ɗakin yayanta ta biyota da sauri, daga inda take laɓe ta fito tace “ka bata sabuwar mota mana taje tayi karyar data saba cikin ƙawaye sukuwa suna binta kamar wata sarauniya,”
Daria ce takama Rabi’ah anma ta dake, ta cewa Yayanta ya musu Pictures ita da su Hayrah, wayar shi ya ɗauko ya dinga daukarsu photo sunyi kyau sosai sannan suka dauka ita da Yayanta, Anty deejah kuwa ta kawo iyah wuya,
A haka ta barsu ta wuce gidansu Amrah.Tana tafiya a mota tana tunanin guyn nan da batasan ko sunanshi ba, da sauri take tafiya da motan don ta isa da wuri, ba tafi mintuna 15 ba ta isa gidansu Amrah, bata ko zauna ba akace ta tafi gidan biki, ta gaishe dasu Mamansu kawai ta juya zuwa gidan bikin.
Tana zuwa ta tarar da
Amrah ta rako wata ƙawarta bakin ƙofar gidan tana fira da saurayinta, da Alama sabon kamune tayi cikin Abokan ango,
Amrah na ganin Rabi’ah ta ƙaraso wajenta tana faɗin “sai yanzu kikaga damar zuwa,”
“Rabi’ah tace naji dai mikike a ƙofar gida?” Amrah ta mata nuni da wace take firah,
tace “kice takin baya kika fito toni na na shiga da ga ciki idan tagama kun sameni aciki,” da “Ok” Amrah ta amsa sannan+
Rabi’ah ta wuce cikin gida tana zuwa babban palon inda amarya take, zata bude kofar taji an turo ƙofar, ƙofar ta datse mata dan yatsa na ƙafa,
Wata razananniyar ƙara tasaki cikin muryar kuka, hakan yasa wannan ya buɗe ƙofar saurin fitowa dan yaga mike faruwa, karo yaci da ita ta duƙar da kanta ƙasa ta riƙe ƙafa, shima ganin ƙafar ya sashi saurin riƙe kafar yana mata sannu.
“kiyi haƙuri wlh bansan kin tafo bane,” duk ya nuna damuwarshi, Jin muryarshi yasa gabanta yayi munmunar faɗuwa, anma tadage ta ɗago da kanta
tace “eeh lallai rainin hankalinka, da rashin kunyarka bai isheka ba, yanzu har neman kashe ni kake ko?”
Sai lokacin ya lura da itace, sakin ƙafar nata yayi ya miƙe,
Yace “Uhm ashe kam farko da nayi tunanin kece banyi kuskure ba? Ana faɗin mata wurin natsuwa in suna tafiya, anma ke sam bakya duba gabanki, ko ko dai nine kike bi duk inda nayi ne?”
“Oh! Aeni ban ɗauka kana da bakin magana ba, kajimun ciwo a ƙafa kuma kana mun hayaniya akai?”
Abokan Angon da suka tafo bayanshi ne ke tambayansu “Meya faru ne?”
“Ku tambayeshi mai laifin” ta saka takalminta zata wuce, ae yana gogar wurin sai da ta ƙara sakin ƙara, a haka dai tana ɗingisawa ta wucesu, binta kawai yayi da kallo yana murmushi, ba ƙaramin kyau ta mishi ba, hakanan yaji yana tausaya mata bugewan da tayi.
Tana shiga suka ringa gaisawa da ƙawayensu, kowa ce mata yake tayi kyau, sai dai tayi fari da ido cikin jin daɗi tace, “Na gode” daman an gama shirin zuwa kai Amarya, suka fito anata shiga mota,
Wata ƙawarta Mai suna Sadeeya ta ƙaraso inda take, “Ƙawata nikam in tambayeki mana”
“Tohm ina jinki”
“Don Allah miye tsakaninki da wancan babban Abokin Angon?”
“Wa kenan?”
“wancan kyakkyawan mana” ta nunashi da Hannu, juyawa tayi don taga ko wayene, dai-dai lokacin shima ita yake kallo, ya ɗago mata hannu alaman “Yadai?”
Harara ta sakar mishi sannan ta juya, “Babu abinda ke tsakanina dashi”
“Haba Rabi’ah, koda numbernshi ne kawai ki bani, zan kula da sauran”
Cikin ƙulewa tace “Bani da ita, gaki gashinan ae sai kije ki amsa”
“Allah ya baki hak’uri, ai bansan Saurayinki bane”
“Saurayina? Allah ya kiyayemun” lokacin Sadeeya ma tayi tafiyanta, su Zahra da Amrah kuma sun k’araso,
“wai bazamu tafi bane? An riga da an tafi da Amarya fa kowa ya kusa tafiya”
“toh muje mana, ta juya tana nufar wurin motarta”
“Ina kuma zakije?”
“Bada Motana zamu tafi ba?”
“A’ah muma duk anan zamu bar namu, tafiya mai nisa ce fa, akwai wadatattun motoci”
Ba don ranta yaso ba, suka shiga ɗaya daga cikin motocin Abokan Angon, jinta take duk a takure bata saba zaman bayan mota ba, tana jinsu Amrah na firansu, wani lokacin Abokin Angom ya saka musu baki, anma tayi shiru kaman ba ita ba.A haka suka isa Kano, A gidan amarya suka tsaya gaba ɗaya,
Anyi adu’a sosai dan samun ɗorewar zaman lfy, wa ma auratan.
Sannan wasu daga cikin abokan angon sukaje siyan Abincin da za suci kafin masu komawa katsina su dau hanyan, wata restaurant suka nufa, sukasa aka hada masu abinci kalah kalah, dan kowa yazabi kalar daya keci, dan tafiyar tazama ba mutun daya ba,
Angama haɗa masu komai sannan suka shiga wani kayatancen mall, suka sayi drinks kala-kala da ice cream, sannan suka koma gidan Amarya,
A palo suka ajiye abincin sannan suka kira ƙawayan amarya da sufito suci, duk suka fito kowace ta ɗauki kalar abinda takeson ci, Rabi’ah kuwa tace sakwaran doya takeso, Abba ne cikin abokan angon yace,
“kin ci Sa’a kuwa dan bamu sawo sakwaran doya, bamu jira ba abinda ke akwai dai mukace abamu, shiyasa muka taho ba mu tsaya ansaba,”
“Anma mun bar *Ahmad* acen Allah yasa ba iya cikinchi zai sawoba,”
suka Amsa da “Ameen”
Rabi’ah kuwa cewa tayi “Allah nidai ina son cin sakwaran idan ya siyo iya cikinsa saide ya hakura da ita ni naci,”
daria suka samata dan tabasu daria, Abba yace, “ina laifin dai kuci tare anma kice sede chi ya hakura, kinsan shimafa ita kadai yakeson ci,”
tace “To kuci abincinku ni zansha Ice cream kafin yazo,” ta ɗauki roba guda ta koma inda take zaune ta fara sha, “Assalamu alaikum” wata cikakkiyar murya Me cike da haiba, da kwarjini, ta fada gaban Rabi’ah ne ya fara dukan tara-tara, jin muryar Me sallama, Abba ne yace “yauwa Rabi’ah ga *Ahmad* ɗinnan yazo, kitaso kuci”
Ahmad yace “lafiya malam daga zuwana zaka faramin gayata?, kuma kasan iya cikina nace zan siyo ko? Abba
yace “yi hakuri Rabi’ah ce takasa cin komai sai sakwara kuma naga kaima ai itace kasawo ko, kaga sai kuci tare”
“Ah OK na fahimta Ahmad ya faɗa” yana murmushin mugunta
“to ta taso muci ko, dan ni yunwa nakeji, kuma idan tasa jan aji wlh zan cinye, dan bana jure yunwa ni,”
Abba yace da Rabi’ah
“kitashi kici mana”
“A’ah”, kawai ta iya fada dan ganin guy din jitayi komai ma yafita ranta,
Amrah tace “miye kuma haka bestie? kije kuci abincin mana yanzu fa zaki koma katsina kinasan yunwa tamiki illah kafin kikai gida ko,”
Abba sarkin surutu yace da Ahmad “Aboki kaɗan matsa mana kuci karka cinye ka kyaleta” harda wani kashe mishi ido, Alamar yaje kawai,+
Ahmad ya ɗauki plate ɗin abinci ya ajiye gaban Rabi’ah yace “to bismillah muci ko” yana mata wani irin kallon da bata aminta da shiba duk se taji ta takura, kuma bazata iya musa mishi ba, ta ɗauki cokali tasa cikin plate ɗin ta ɗebo zatakai baki yace,
“wato gulma na ma kike masu ko,”
kasa kai abinci tayi bakinta kuma ta kasa ce mashi komai sai uwar harara da take zuba mashi,
Kashe mata ido yayi can ƙasa yace,
“wannan kallon son fa? Ƙwalelenki dai” ta buɗa baki kenan zatayi magana yace wa Abba “Aboki ka sakani nadawo wajenta gashi ma takasa cin abincin,”
Abba yace “kici abinci Rabi’ah dan zai iya gamawa da shi idan baki ciba,”
“To” tace wa Abba dan tanajin maganarshi sosai, Ta sake kai cokalin bakinta, Ahmad yace
“Kinga ni banson kinibibi, kina sona anma kin kasa faɗamun, kiyi bayani ko zan iya taimakawa na amsa soyayyarki”
Rabi’ah ta kawo iya wuya plate ɗin ta dauka ta juye masashi akai, nan take miyar ta bata masa fararan kayanchi, kowa ya zabura yana kallonsu, ta sunkuya dai-dai kunnuwanshi
tace, “bari kaji na faɗa maka ko ba maza duniya ba abinda zanyi dakai,”