MAFARIN SO CHAPTER 5
Www.bankinhausanovels.com.ng
Daganan Gidanshi ya wuce a inda ya ajiye Rabi’ah, ya ɗanyi tafiya kafin ya isa gidan da yake akwai ɗan nisa unguwar da gidansu, titin gidan yabi har dai dai ƙofar falon anan yayi parking sannan ya fito. Kai tsaye ɓangaren da take ya wuce yayi sallama sannan ya shiga.
A falo ya iske Gwaggo tana kallo, ya durƙusa har ƙasa ya gaisheta, cikin zaƙuwa ya miƙe yanason ya shiga yaga Rabi’ah.
“bara na shiga na gaishe da Aunty Zee” yace da Gwaggo.
Kafin ta bashi amsa sai ga Auntien ta fito,
“Yau gama Zainabunnan” murmushin yaƙe kawai yayi, itama ya gaishe da ita, sannan ya koma ya zauna kanshi a ƙasa.
Jefi-jefi suke fira, yaji shiru babu wanda yace mishi yaje su gaisa da Rabi’ah, gashi yana sauri akwai abubuwan da zaiyi idan ya fita, miƙewa yayi kaman zai tafi.
“Zan wuce Auntie, zan ɗanje wani wuri, badai abunda kuke buƙata?”
“A’ah Babu”
“Tohm shikenan”
Yaɗan sosa ƙeya yana kallon gefe, “Rabi’ah tana lafiya?”
“Lafiya lau take, sai ciwon da takeson ɗaurawa kanta” inji Gwaggo.
Murmushi Auntie Zee yayi, “lafiya lau ta tashi”
Sallama ya musu ya fito, a hankali yake tafiya harya fita daga falon, sosai yaso ganin Rabi’ah.
A motan ma kasa tadawa yayi, yayi kewar faɗanta, wayanshi ya ɗauka ya tura mata text.
“fito gani ina jiranki”
Ya ajiye yana jiran amsarta, shiru bata fito ba, kuma bata maido mishi da amsa ba.
“jiranki nake fa”, shima sai data ɗauka lokaci sannan ta maido mishi.
“naƙi in fito ɗin, na maka me?”
“Don mijinki na kira sai kinji dalili?”
“miji fa😅 ni ban iya rashin kunya ba, da baka shigo bama ka kyautamun”
“kawai kice kinason ganinah ba?”+
Idan tace batason ganinshi bazaije ba kenan? Tunani take ta rasa amsar da zata mayar mishi, sai da yaji shiru sannan ya fita cikin dakewa ya koma cikin gidan, cikin kaman yana sauri yace da Auntie Zee,
“ina sauri ɗazu, na manta da akwai saƙon dazan ɗauka”
“Ayyah! Gashi kayi tafiya biyu, ka shiga…”
Tun kafin ta ƙarasa ma harya wuce.
Can ya hango Rabi’ah tsakiyan gado, Zaune ta miƙe ƙafa ɗaya, ta ɗage ɗaya tana latsa waya, taɓe baki take tana kallon wayan kaman shine a gabanta, sai da ya gama ƙare mata kallo sannan yace “wannan kallon fa na waye?”
Tsorata tayi ta jefar da wayan da sauri ta rufe jikinta cikin hijab ɗin.
Murmushi yayi ciki-ciki, yana tahowa inda take
“Yi a hankali dai karki ɓatama Amaryatah gadonta”
Taɓe baki tayi, “wanda yafi shima saina mayar mata, naga bani nace ka kawoni gidan nata ba”
“hakane fa, biyoni kawai kikai”
“waye ya biyoka, ka kawoni dai”
“ai da sai kice baki zuwa”
Ajiyar zujiya ta sauke, “meya shigo dakai?”
“wani abu?”
“ni fita ka bani wuri”
Duƙawa yayi dai dai saitin fuskarta, tana ja da baya harta jingina da bangon, “idan naƙi fa?”
Marairaicewa tayi, saboda yanda ta daburce, “Don Allah”
Ya lura da yanayin takuran data shiga, ya ɗaga mata gira ya wuce, sannan ta saukar da ajiyar zuciya.
Saida yabar gidan, yana hanya ya tuna da shine ya hana a taho da kayanta, a cewar zai mata lefe, wayanshi ya ɗauka ya sake mata text.
“Akwai kayan Amaryatah a wardrobe, zaki iya sakawa aro”Riƙe take da waya a hannunta har yanzu bata da alamun tashi, sake jin shigowar texts tayi ta buɗe saƙon da taci karo dashi ne yayi mugun ɓata mata rai da takaicin me Ahmad yake nufi da ita tarinƙa girgiza kai haɗe da juya maganar aranta,
‘wai ita yau za’ace tayi amfani da kayan aro, na aron ma na kishiya taja dogon tsaki ko ina ruwanshi da sa kayana da zai wani dameni da kayan aro, mtssss’ ta sake jan tsaki Allah kuwa tunda na matarsa ne bazan sa ba sai dai yasan yadda zaiyi dani.
Ta koma tayi kwanciyar taci gaba da lallatsa wayarta Amman still bata bar jin ranta na ɓace ba, har aka kira sallah tananan kwance tunanin yadda zatayi da Ahmad da wannan wahalallen auren nasa take, Gwaggo ce ta shigo tace “ke baki ji an kira sallah bane”
Ta turo baki “ai yanzu zan tashi” gwaggo tace
“karma ki tashi kiyi ta zama ja ira mai ɗan banzan taurin kan tsiya” miƙewa tayi ta shiga bayi.
To duk wunin ranar banda sallah babu abunda ke tada Rabi’ah, da tayi Kuma take komawa tayi kwanciyarta. Ahmad ma bai samu damar dawowa gidan ba saboda abubuwan da suka sha kanshi Kuma ya kirata yafi a ƙirga taki dauka sai dai yasa ankawo musu abinci.
Da misalin karfe tara na dare ya shigo haɗe da sallama, cikin doguwar Riga jallabiya sai zuba ƙamshi yake dan gaba ɗaya falon ya rikiɗe da ƙamshi turarensa, Gwaggo naganinshi ta washe baki tana masa sannu da zuwa, ya zauna haɗe da gaishe su suka amsa.
Ahmad yayi murmushi yace “daman nazo na muku saida safe ne, bakwa buƙatar wani abu”
Aunty zee tayi sauri tace “bama buƙatar komai an gode Allah yayi albarka,” ya amsa da.
“Ameen”
hira suke yi da Gwaggo har Gwaggo tace,
“ɗan nan ya kamata ace gobe mun wuce gida”
Ahmad yace, “haba dai Gwaggo da wuri haka kuɗan kara mana kwana biyu”
gwaggo ta baje Ido waje “ayi haka kuwa, kai dai bari mu tafi ai munga wuri Allah dai ya bada zaman lafiya” magana take masa amman shi gaba ɗaya hankalinsa na kan ƙofar dakin da take ya damu yasan a wane hali take duk da bawai sonta yakeyi ba Amman ai yanzu haƙƙinta ya rataya a wuyansa dolensa ya kula da ita. Yana son shiga Amman kunyar su Aunty zee ta hanashi dan haka miƙewa yayi ya musu sai da safe koda ya shiga mota ma kiranta yayi Amman shiru taki dauka har shima haushin ya kamashi, ya ɗaura wayar kan bakinshi to me take nufi daƙin daukar wayar sa?
Text ya tura mata
“na kiraki kinƙi ɗaukar wayata, karkiyi tunanin kodan na damu dake ne, na wuce wurin Amaryatah, hope dai kinyi amfani da kayan aron,”. Sannan yayiwa motar sa key ya bar gida.
Kwance take idanunta na kallon sama, gaba ɗaya hankalinta baya gangar jikinta tana can duniyar tunanin yayanta kewarsa ke damunta matuƙa gashi tunda tazo ko sau daya bai kirata balle taji sanyi aranta, kuma ita kota kira baya dauka, ba abin ta ƙikira Aunty deejah ba tasan mugun hali irin nata ba zai sa ta hadata da yayanta ba, sautin karar wayarta ce alamun shigowar texts ne yasa ta dawo daga tunanin da ta Lula tasa hannu kan bed side dinta ta jawo wayar, dubawa tayi ganin wani sabon banzar text din daya sake turo mata wanda yafi na ɗazu ban haushi yasa ta ɗan gyara zamanta Sosai sannan itama ta aika masa.
“Wannan matsalarka ce ba tawa ba, kai da wahalalliyar matarka ku ƙarata, indai damuwane kam ka damu dani Ahmad”
Tana gama tura text ɗin ta kashe wayar gaba ɗaya tayi cilli da ita tana sauke ajiyer zuciya ‘wlh duk abinda kake ji Ahmad na fika jinsa’ tana miƙewa ta shiga bugun kanta da hannu, kamar shiyasa Ahmad aiko mata da text bata san lokacin da kuka ya kufce mata ba, zarya ta ta somayi a ɗakin tunawa da tayi yanzu Ahmad yana can tare da matarsa kamar yadda ya sanar da ita, tsagaita kukan tayi ta shiga bathroom ta watsawa kanta ruwa ta fito ta tsaya gaban dressing mirrow tana kallon fuskarta da kyau tasa hannuta ta shafa goshinta ganin bbu abunda yayi.
Koda dare yayi mamaki tayi, ta kwanta bacci don rama lodin baccin dake kanta sai ta kasa tarinƙa juyi karo na farko data soma sanin menene’ kishi take gabanta ya yanke ya fadi taji wani abu ya tsarga mata ta Miƙe zaune a tsakiyar gadonta tayi tagumi to ita meye matsalarta dan Ahmad yace mata zai je gun matarsa, gaba ɗaya daren bacci bai dauke ta ba kwana kawai tayi tana juyi akan makeken gadonta dan haka tarinƙa ganin daren yayi mata Nisa da yawa kiran sallar farko a kunnenta aka yishi, tashi tayi taje ta ɗauro alwala tazo ta fara yin nafila bata tashi ba har saida tayi sallar asuba anan ta koma bacci.
Sai wurin 12 ta farka, zaune ta ganshi a bakin gado cikin ƙananan kaya ajikinsa, murmushin data gani atare dashi yasa ta jin mummunar bacin rai da faɗuwar gaba, ‘shi yanzu yaji dadin abinda yayi min yaje ya kwana tare da matarsa yabarni ko kayan sawa banyi mutunci da zai sai min ba sai na aro hakan yayi mishi dadi har zaimun zaune ina barci, na tashi kuma harda wani murmushi rainin hankali. Muryarsa ta doki kunnenta,
“ke me kike Jira da ba zaki sauya kaya ba ko tsabar kazantarce ace har yau kwana biyu kina zaune daga ke sai hijab, nifa banason ƙazanta”
Ta sunkuyar da kanta ƙasa taki yarda su haɗa Ido balle ta amsa masa maganganun sa dayake mata.
Jin shiru ya wuce kai tsaye ya buɗe wardrobe ya zaro wata haɗaɗɗiyar doguwar riga ya nufa inda take ya shiga kokarin zare hijab ɗin jikinta, tasa hannunta ta riƙe hijab ɗin gam sai yanzu ta iya buɗe baki
“meye haka Malam?” ya numfasa sannan yace,
“tambaya kikema? Baki da idone? Kinfi kowa sanin abunda zanyi ae”
tace, “wannan ai iskanci ne zaka zo kana taɓawa mutane jiki”
“iskanci fa kika ce, da sadakin nawa zaki kirani da ɗan iska a cikin gidana? yau ko zaki ga iskanci ganin idonki”
ya haɗe hannuwanta waje ɗaya, Ido ta zaro waje,
“dan Allah malam ka sakarmin hannu, ni ka rabu dani ina ruwanka da rashin sa kayana ne,? ko kulata baiyi ba, ya zare hijab ɗin yayi wurgi dashi.
Sa’arta ɗaya akwai towel ɗaure a ƙirjinta, ta dunƙule waje ɗaya haɗe da tura kanta cikin cinyoyinta
“ni wallahi ka ƙyaleni karka samin kayan aro”
“aikuwa kamar kinsa angama”
Zama yayi ya jawota jikinsa sannan ya zura mata riga ya zare towel ɗin jikinta,
“yarinya dolenki kisa kayan aro tunda bawani ya hanaki zuwa danaki ba, koda yake ina zaki tuna kina ɗokin zuwa gidan Ahmad”
Ta ɗago kanta fuskarta cike da jin haushinshi tace, “Allah ya tsareni, menene a gidan naka da mutun zai yi wani ɗokin zuwa?”
Ya juyo da fuskarta suna kallon juna
yace, “ƙarya kike yarinya”
ya Miƙe yana zura hannunshi ɗaya cikin aljihun wandonsa,
“ni dan Allah ka dameni dayawa ai ba ɗaure maka ni akayi ba. ka sake ni mana ka gani ko zan damu”
“ko baki ce ba yarinya kina kan hanya” haushine ya sake kamata batasan sanda tace,
“wlh Allah ya isa tunda kasamin kayan matarka”
Ya zuba mata manyan idanunshi ya nuna kansa da yatsa,
“ni kike wa Allah ya isa?”
Ko ɗar babu a fuskarta tace “Eh ɗin an yima Allah ya isa me zakayi?”
Ya matsota yana girgiza kai, Kuma har yanzu bai ɗauke idanunshi daga kanta ba, ya ƙaraso inda take, ja da baya ta dingayi, Shi Kuma yana sake matso ta har ta kai karshen bango tana sauke ajiyar zuciya dai-dai saitin fuskarta take jin hucin numfashinsa runtse idanunta tayi gam ga wani kyarma da jikinta keyi idanunshi ya zubawa kyakkyawan face ɗinta yana bin ko ina na jikinta da kallo.
‘Masha Allah’ abunda ya iya furtawa kenan hannunshi yasa ya gyara gashin daya zubo gefen fuskarta dai-dai bakinta idanunshi suka ja birki ya haɗe ya tsunsa biyu ya ɓalle lip’s ɗinta dashi.
A gigice ta saki ƙara, ta kama baki ta riƙe ta soma kuka, “wayyo Allah na!!”
Ta harareshi tana ƙara rufe bakinta, “Mugu kawai, hakanan Yayana ya haɗoni da wanda baisan darajata ba”
“kina iya faɗar duk abunda yazo bakinki, ai ni nan nasan darajarki tunda gashi na rufa miki asiri na aureki har na kawo ki gidana, bacin haka keda kanki kinsan yadda duniya zatayi dake har ‘ya’ya da jikoki sai angoranta musu mamansu tabi wani sun kwana tare ko ba haka ba?” ya ɗage mata gira yana kashe mata idonsa daya,
“Kuma wlh kimin shiru karki taramin mutane a dauƙa wani abu ne, tunda ke kaɗai kike da Bakin magana da idanun kuka Kuma wlh sa kayan aro dole tunda kika shigo gidannanZunguro baki tayi, yasa hannu zai matse bakin da sauri ta duƙe ƙasa, tayi hanyar fita.
“Mugu kawai” ta ƙara murguɗa mishi bakin.
“zonan ki faɗa mana, yarinya yanzu ina da maganinki”
“indai maganina ne baka dashi, an faɗa maka zan zauna kana cin Zali na ne?”.
“Haka kikace?” yayi kaman zai matsota da gudu tabar ɗakin tayi hanyar ɗakin dasu Gwaggo suke. Sai da tazo gab da shiga sannan ta gyara kanta ta shige.+
Aunty Zee ce keta faman haɗa musu kaya, da yake da Yamma zasu bi jirgi su wuce, Saboda Ahmad yace kodan Gwaggo bazasu sake wannan doguwar tafiyan ba a mota.
Aunty Zee ta kalli Rabi’ah da mamaki, “Yau kin samu fitowa kenan?”
Murmushi kawai tayi, “Aunty da gaske dai tafiyan zakuyi ku barni”
“A’ah sauri nake na gama haɗa nawa kayan, naje na haɗa miki naki, ke kin cika maido da abu baya”
Dafa kafaɗarta tayi cikin lallashi, “wannan gidan Aurenki ne Rabi’ah, mun kawoki don haka ki koyi haƙuri da biyayya saiki zauna da mijinki lafiya, wannan shizai faranta ran yayanki harya manta da abunda ya faru kinji ko?”
Ɗaga kanta tayi cikin gamsuwa, “Insha Allah Auntie”
Jinjina kafaɗar tata tayi, “Good girl”
Tuna abunda ya faru tsakaninta da Ahmad tayi a ɗaki, lallai saita canja shiri.
Gwaggo ce ta shigo tana waya, jin ta ambaci sunan Yayanta sai da gabanta ya faɗi, yaushe rabon da tayi magana dashi? Wata ƙila ya yarda su gaisa koda da wayan gwaggo ne, da gudu ta ƙarasa wurin Gwaggo.
“Gwaggo Yayana ne? Don Allah bani shi muyi magana”. Hannu ta nuna mata alaman ta jira, ta ɗan tsaya anma duk da haka kaman ta miƙa hannu ta amsa wayan takeji.
Tanajin Gwaggo tace “Tohm shikenan ibrahim, sai zamu taso ɗin zan kiraka, ga…” kafin ta ƙarasa Rabi’ah ta anshe wayar.
“Yayana, ina wuni, yasu Hayrah? Sai kiranka nake ba’a ɗagawa” tayi shiru kuka nason ƙwace mata, ɗiff taji ya kashe wayan ba tare da yace komi ba.
Ganin yanda tayi sukuku da waya a hannu, Gwaggo tace “ke lafiyanki? Me yace Yayan naki?”
Kasa bata amsa tayi, Gwaggo ta anshe wayarta, “bani wayata tohm tunda banda arziƙin da zaki mun magana”
Jiki a saluɓe tabar ɗakin kawai.
Da marece su Gwaggo suka wuce ba tare da ko rakiya ta musu ba, tayi kuka kaman ranta zai fita, kukan da ko ranar da za’a kaita Yola bata yishi ba, Aunty Zee ce tayi ta lallashinta tana bata haƙuri a haka suka rabo, bayan tasha nasiha mai ratsa jiki.
Tafiyansu ba daɗewa gidan ya fara mata girma, duk da dare bai ƙarasa yi ba, anma tsoro ne ya kamata, wannan ƙaton gida kaman gari babu kowa ciki sai ita kaɗai, sai masu gadi da mai gyaran waje duk suna can ɓangarensu.
Falo ta samu kujera ta rakuɓe, data kunna kallo taa fara, shima hakanan taji kallon na bata tsoro kawai ta kashe ta koma ta zauna, tananan har aka kira sallah, shima don bata son lokacin sallah ya wuceta, ta tashi a tsorace ta ɗauro alwala sannan ta dawo falo tayi sallah, har aka kira isha’i bai shigo ba.
9:30pm ya shigo gidan har ta ɗauko waya tana shirin mishi text,
“Yadai? Zaman jiranah?”. Yana magana yana ɗaukan remote, ya koma ya zauna yana kunna kallo.
“ai da kin kunna kallo, koshi zai rage miki kewatah”
“bashi nazo yi ba, akwai can a gida”
Dariya ce taso kamashi yana bata amsa, “hakane, ni kaɗai ne babu a gida shiyasa kika biyoni nan, tohm gani nazo”
Zaro ido tayi tana kallonshi, lallai mutuminnan ya wuce duk inda take tunaninshi, gaba ɗaya ma ya rufe mata baki.
“Da safe zanje boutique siyan kaya, don bazan ƙara saka kayan aro ba”
“so Funny, ina kika sani a Yolan da zakije siyayyan?”
“You will find it Funny idan naje na dawo, nadai faɗa maka ne a matsayinka na…” ta ɗanyi shiru da alama maganar da zata faɗa tayi mata girma.
“ehen matsayina nawa?”
“what eva it is, nidai zanje siyayya”
“idan na hana fa?”
“ae ba tambayarka izini nayi ba, kawai ina faɗa maka zanje ne”
“saboda me bayan ga kayanan a wardrobe wanda zakina sakawa?”
“kayan aro ba, ni nawa nakeso”
“please Rabi’ah, nifa daman don ke na siya, ba wani na Amarya”
“Haba? Anan fa muka iske kayan, koni makauniyace da za’a shigo da kaya ban gani ba?”
“kafin muzo nayi waya a kawo miki, saboda nama yayanki alƙawarin zan miki lefe anan”
“ko meye fa ni bazan saka kayannan ba, tunda ka riga ka haɗasu dana aro, gobe zanje na siyo kaya an magana ta ƙare”
Dafe kanshi yayi cike da jin haushinta, sai wani lallaɓata yake tana botsarewa, don kawai yana tunanin matsalan dazai samu ne idan ya barta ta fita da bazai ma tankata ba.
“shikenan tunda wannan ne baki so, idanna canja miki wasu fa?”
“Yanzu kayi magana, yaushe zamuje in zaɓo?”
“ki rubuta duk abunda kikeso zanzo miki dasu gobe in zan shigo”
“Awk zan rubuta, anma ban gane in zaka shigo ba, ina zakaje?”
Yaɗan tsaya ya rasa ta inda zai fara faɗa matakaifa nake saurare, kana nufin ba anan zaka kwana ba?”
“inna kwana mezan miki?”
“ba abunda zakamun, anma bazaka barni gidannan ni kaɗai ba”
Yaɗan sassauta murya kaman wani ne zai jiyoshi, “kin gane? Akwai matsala ne idan nace zan kwana anan, indai ina garinnan ban taɓa kwana wani wuri ba gida ba, kuma kinsan dai basu san da maganar aurennan ba”
“akwai matsala kam, don ƙafarka, ƙafata bazan kwana a gidannan ni kaɗai ba”
“kamarya ke kaɗai? Ba gasu Baba mai gadi nan ba”
“wanne masu gadin da ko zan kwana ina ihu ba jiyoni zasuyi ba?”
“indai don wannan ne, ae saisu shigo su tayaki kwanan”
Wani irin kwallo ta mishi har sai da yaso yin dariya, “nifa kar kaga kaman son kwananka nake a gidan, anma fa bazan kwana ni kaɗai ba”
Tun suna faɗan, harya koma lallaɓata anma fafur taƙi yarda. Duk da shima kawai yana faɗane, anma can ƙasan zuciyarshi baison ya tafi ya barta.
“shikenan” ya ɗauka wayanshi ya kira Aunty yana tunanin ƙaryar dazai mata wanda zata faɗama Alhajinsu +
Misalin karfe goma daidai Rabia tagama shirinta tsab cikin haɗaɗɗun kayan baccin da Ahmad ne ya siyo mata, wanda basu da maraba da kayi yawo tsirara ita da kanta tasan kayan sun amshi jikinta ta tufke gashin kanta tsakiya ta feshe ilahirin jikinta da turare masu dadin kamsh kamar mai shirin kwana da miji, duk da daman Rabi’ah akwai son ƙamshi, da tsallenta ta faɗa kan gado jagwab ta Miƙe.
tacewa kanta ‘kai Rabia kina burge kanki da yawa da yanzu wannan banzan ya wuce ya barki ke kaɗai cikin tashin hankali da tsoro’ tasaki murmushin mugunta a ƙasan ranta koba komai dai shima bazai kwana tare da matarsa ba yau,
Kuma ko baku kwana tare ba dai tunda yana cikin gidan hakan zai d
Ɗan rage miki tsoro ta runtse idanunta tana tauna cingum ƙas ƙas wanda duk cikin tsiyar Ahmad ne duk da bai yarda taje shopping din da kanta Amman duk abinda tayi list ya tawo mata da su ta sake gyara kwanciyar ta.
To shima dai Ahmad bayan ya kammala da komai na aladarsa ya nufo ɗakinta dan a tunaninsa idanunta biyu tunda tace bazata iya kwana ita kadai ba da sallamar shi ya buɗe ƙofar ya shigo, tsaye yayi kawai yana mai ƙare mata kallo idanunta a runtse yayi murmushi ƙarfin hali a ƙasan ransa yace ‘tabbas ita wannan yarinyar bata da matsala ko ɗaya baccin ta ma takeyi hankali kwance’ wato dai shi kaɗai ne mai damuwa, shi yanzu yama fi jin umminsa akan kowa, idan maganar nan ta fito ya runtse idanunshi ya soma ta kowa a hankali har ya ƙaraso inda take kwance yana binta da Ido ita Kuma tasake lafewa kamar mai baccin gaske.
sai data ga yana shirin zama kusa da ita Sannan ta buɗe idanunta sharr ta zuba masa tana mai watsa masa wani kallo da bai taba sanin ta iya irin saba. Kuma daman tun shigowarsa idanunta biyu ta dai yi kamar tana bacci ne dan ya fita,
Ya zauna yana cewa
“A’a ashe bakiyi bacci ba”
haɗe ranta
tace, “dan banyi bacci me zan maka?, ta sake watsa masa harara Sannan tace,
“meye na shigomin ɗaki kai tsaye ba excuse?”
shima hararar ya mayar mata yace,
“bansani bayan sallamar da nayi akwai wani excuse dazanyi,”
“to me Kuma ya kawoka ɗakina?”
“zancen kikeso, ba ke kika ce bazaki iya kwana ke ɗaya ba shine dan iskanci zakimin wannan tambayar rainin hankalin”
tayi murmushi kai ma bakaji abinda kace ba,
“cewa nayi bazan iya kwana gidan ni ɗaya ba, ko kaji nace bazan iya kwana ba sai tare da kai? Kuma dai gida nace ba ɗaki ba” ta sake wurgo mai tambaya.
Jin shiru baice mata komai ba tace,
“tambayar ka nikeyi kamin shiru, kaga tashi” ta nuna masa ƙofa da hannunta shiru har yanzu yaƙiyin magana sai ma idanunshi masu daukar hankali daya zuba mata
Sannan yace
“naga dai gidan nawane, bana wani bane, Kuma ma duk part ɗin da naga dama zan shiga kai tsaye ba tare da Ammin izini ba dan kar ki kawo min hauka nan”
Taja tsoki tana taɓe bakinta,
“gidanka ne kam tabbas, Amman baka da muhallin kwanan anan ɗakin ta nuna ɗakin”
Ta nuna ɗakin da yatsanta,
yace “Allah ko yarinya? kinga barima na nemi wurin kwanciya tun dare bai min ba”
“ka dai tashi ka kama gabanka tun dare bai maka ba” miƙewa tayi tsaye tace,
“ni dan Allah malam tashi kabar ɗakinnan dan bazan iya kwana da gardi a ɗaki ba”
ya ware Ido yana nuna kansa,
“nine gardi?”
tace “Eh”
yace, “yau kuwa yarinya zaki gane kinkirani da gardi”
tsaki tayi tasa hannu ta ɗauki fillow zata bar ɗakin, ji tayi an fizgota luuuuuuuu tayi sai saman ƙirjinsa ta faɗa suna kallon juna, ta ta ɗago dara daran idannunta tana zaresu waje ta sauke ajiye zuciya duk at the same time, dan ta tsorata matuƙa,
yace, “ina kike nufin zaki tafi kibar gardinki shi kaɗai?” hannunshi yasa ya zagaye ƙugunta da shi hade tabo wasu sansa na jikinta tarinƙajin wani yanayi mai wuyar fassarawa.
Ranta ɓace ta tura masa baki,
“kaga ni bansan iskancin naka sake ni na tashi”
yace “Allah ko yarinya, kin sake ƙarawa kanki laifi da kirana ɗan iska, Kuma kici gaba da faɗar duk abinda yazo bakinki zaki gane ne,”
tayi yunƙurin tashi Amman ta kasa tun tana masa masifa da borin ƙarya harta gaji ta sassauta muryarta takoma bashi hakuri,
yace “ai baki isa kimin rashin mutunci na ƙyale ki haka ba, kishani banza kenan”
ji tayi wutar ɗakin ta ɗauke gaba ɗaya Amman fan din dakin da AC duk suna aiki, nan ta gane kashewa yayi dan tsabar rashin mutuncinsa, can Kuma ɗakin ya gauraye da wani hasken, ya birkito ƙasa ya haye samanta, yana ganin yadda numfashinta ke sama da kasa, Sannan ya haɗe jikinsu waje ɗaya ya rungumeta tsam a jikinsa gaba ɗaya babu inda baya rawa a jikin Rabia, ko ina ya dauka kyarma tun tana kiciniyar ƙwace jikinta daga gareshi har dai ta haƙura dan ba rungumar wasa Ahmad ya mata ba.
Yakai bakinsa cikin kunnanta cikin sanyin murya, ya raɗa mata.
“ƙarewar kwana ɗaki ɗaya da gardi, yau a jikin gardi zaki kwana, ina san ki mutu kafin gari ya waye kinga ma na huta da dogon bayani da zan wa ummina”
Murya can ƙasan maƙoshi tace “please…..” dai dai wuyanta ya kaiwa lafiyayyen kiss ɗin daya gigita Rabia jikinta ya mutu murus tayi shiru ta lafe ta runtse idanunta gam kamar mai bacci, yaci gaba da kewaye bakinsa a wuyanta, sai da yaga alamun taƙi motsawa ta saduda tagane Allah ɗaya ne dan har numfashinta na neman ɗaukewa saboda mugun rungumar da yayi mata.
sannan yace, “ki kiyayi kanki dani ko a tsirara naganki bazanji komai ba,”
Ya turata can ƙarshen gado haɗe da jan tsaki ya juya mata baya yana sauke ajiyer zuciya gaba ɗaya shima ji yayi jikinsa ya sauya dan haka kwana yayi yana watsawa jikinsa ruwa asubar fari ya bar ɗakin.Tana jin fitarshi ta tashi ta jefar da bargon data rufa dashi, harara tabi ƙofar da ita kaman yana kallonta, tayi mai isarta sannan ta tashi ta shiga toilet alwala.
Sai da tayi sallah sannan ta koma barci, daman ba wani barcin kirki tayi ba tana cike da fargaba, barci sosai tayi har bata san rana tayi ba, sai dai taji kaman ana jaa mata ƙafa can cikin barci.
A hankali ta buɗa idonunta ta saukesu kanshi, sannan ta maida ta sake rufewa, aikam ta ƙarfi ya sake jan ƙafar har saida tayi er ƙara.
“ke tashi mana”
“na maka me?”
“halan kin manta da haɗamun break fast?”
“haɗa maka break fast kuma? Bashi nazo yi ba”
“haba yarinya, wasa kike, kuma ba barci kikazo yimun ba”
Tashi tayi zaune tana murje ido, “wai don Allah miye matsalanka dani da zaka takuramun?”
“Eyeeh! Watau na takura miki ko? Baki ga komai ba kam indai bazaki tashi ki haɗamun break ba”
“bazan haɗa ba ɗin, kayi duk abunda zakayi”
“dolenki nema ki haɗa, tunda kika sakani kwana a gidannan, ya zame miki dole ki bani break”
“nace bazan bayar ba ko baka ji ba? Kai ni duka yaushene ma nazo gidan da zaka fara sakani girki? Ae in faɗa maka har in koma gidanmu bazanyi girki a gidannan ba”
“Yayi miki kyau ai, ranakun komawanki kawai kike ƙarawa” ya tashi ya barta da tunani, yana nufin bazai sallameta da wuri ba kenan ta tafi gidansu?. Katse mata tunanin nata yayi da cewa.
“indai bazaki bani breakfast ba, ki shirya kwana ke kaɗai don banga amfanin kwanan nawa ba” ta buɗa baki zatai magana ya fice ya barta.+
Wanka ta tashi tayi, sai data shirya tsaf cikin riga da siket na english wears, kasancewarta ba mai son kaya masu nauyi ba, sunyi matuƙar yi mata kyau, sannan ta fita da niyyar dafa mishi ruwan zafi kawai ta bashi don tana gudun karya barta ta kwana ita kaɗai.
Tana fitowa shima ya fito daga ɗakinshi cikin shiri, shima ƙananun kayane a jikinshi sunyi matuƙar amsarshi, suna haɗa ido babu wannan bai ayyana kyaun ɗan uwanshi a ransa ba, suka taɓe baki a tare cikin nuna rashin kulawa.
Ta ɗan haɗe rai tana kallonshi, “nifa ba iya girki nayi ba, in kuma zakasha ruwan zafi tohm”
“kin ɗauka da gaske zan iya cin jagwalgwalon girkinki?” ta saki baki tana kallonshi.
“kuma don wulaƙanci zaka tasheni daga barci nah?”
Ƙofa ne tayi ringing, da kanshi ya tafi yaɗan buɗe ya anso saƙo sannan ya dawo, ajiye mata yayi a saman centre table.
Ta ɗan kalla takeaway ɗin, “anma dai wannan ni kaɗai ba?”
“so glad bana cin girkin waje”
“itama wancan sakwarar wani yaci maka ita ba?”
“kamawa tayi”
Daman tunda yayi shirin fita yake tunanin ta inda zai bata haushi kafin ya tafi.
Wayanshi ya ciro yayi dialing number khadija, ganin kiranshi wani daɗi ya kamata ai da sauri ta ɗauka.
“Hey! Masoyiyah”
Ihun daɗi ya kusa kamata, rabon da taji kalmar kulawa daga gareshi harta manta.
“Yadai ko baki tashi ba?”
“A’ah na tashi tun ɗazu”
“yauwah, don banson ace nine na katse miki barcin naki, ina fatan masoyiyatah ta tashi cikin ƙoshin lafiya”
“lafiya lau na tashi, inata tunaninka, Auntie tace baka kwana gida ba?”
“Yh wani abune ya tsaidani, anma kinsan ko a ina nake kinanan a raina ko?”
Ya ɗan saci kallon Rabi’ah da numfashinta har sama-sama yakeyi, ta gama cika tayi fam, yaɗan dara saboda daɗin da yaji ya kunnota.
“yanzu kinsan me? Ki haɗamun break fast lafiyayye, ganinan a tare dake zan karya”.
Khadija mamakin Ahmad kawai take, har ya kashe ta kasa cewa komai, wayan ta ƙara dubawa sosae taga dai numbershi ce, sannan ta tashi tana murna ta tafi mishi girkin.
Yana gama wayar ko kallon inda take baiyi ba, ya tafi, “saina dawo” yana kaɗa keys ɗin mota.
Yana fita data harzuƙa takeaway ɗin ta ɗauka tayi wurgi dashi,
“baza’a ci bama”
Da gudu ta tafi ɗakinta, wayanta ta zaro tayi dialing number Auntie, sai data kusa katsewa sannan ta ɗauka.
“hello MATAR AHMAD” ta faɗa cikin zolaya.
A ranta saida tace Allah ya kiyayemun a kirani da matarshi, sai kuma ta fashe mata da kuka
“subhanallahi Rabi’ah, ni bansan me yasa kuka bai miki wahala ba” kasa cewa komai tayi taci gaba da kuka.
“toh kodai kashewa zanyi sai kin gama kukan na kira muyi magana?”
Jin haka yasa ta ɗan sassauta, “bai sonah Auntie, wallahi tunda kuka barni wulaƙantani kawai yake,”
“Waye wancan mutumin Rabi’ah?” shiru tayi tana share hawaye.
“tukunna ma dai mai yayi miki?”
Shiru tayi tana tunanin me zata cewa Auntien? Laifin meya mata? Duk abubuwan da suke faruwa ta auna babu wani laifi a ciki, sai ma laifin nata, anma indai zata faɗi laifin Ahmad sai dai in sharri zata mar.
Jin shirun yayi yawa, Auntie ta nisa bayan ta sassauta murya kamar wani zai jiyosu.
“bance ki faɗamun sirrin dake tsakaninki da mijinki ba, haƙurinnan dai dana faɗa miki shi zaki ci gaba dayi, ki kwantar dakai ki mishi biyayya don da alama Ahmad mutumin kirki ne, anma dole ne hakan zatana faruwa saboda abunda kuka aikata kafin aurenku, ina laifi ma da Ahmad ya aureki?”
Wani abune ya soki ƙahon zuciyar Rabi’ah, tabbas Ahmad ya ɓata ma Rabi’ah rai, anma Auntie zee ta jefeta da abunda yafi nashi zafi, meyasa bazasu yarda da ita ba? Meyasa bazasu yarda da babu abunda ya shiga tsakaninta dashi ba? Batason ƙarajin wata magana daga bakinta tunda ba masu daɗi bane.
“na gode Auntie, a gaida su Ilham” tana gama faɗar hakan ta kashe wayan zuciyarta cike da ɗaci.Tun bayan da suka gama waya da Aunty zee ,zaune take tamkar an dasata wani irin ɗaci zuciyarta keyi a yayin da hankalinta ke sake tashi, tana jin tamkar ta haɗiye zuciya ta mutu kowa ya huta. Tunda babu mai yarda da ita akan basu aikata komai ba. Kuma babu wani abu daya shiga tsakaninta da Ahmad,
gaba ɗaya duk wani jin daɗi rayuwa sun fice mata rai a hankali take furta kalmar ‘wannan wacce irin rayuwa ce mai cike da muni ta tsinci kanta ciki?,
Yayanta duk duniya bata da kowa sai shi ya juya mata baya, Bangaren Ahmad ma babu daɗi. Ita kam tasan wani abu ke shirin faruwa da ita shiyasa komai ya tabarbare mata.
Tabbas tasan tayi kuskure mara misaltuwa a rayuwar ta tunda har ta yarda ta kwana ɗaki ɗaya da Ahmad alhalin ba muharraminta bane.
wani irin haushin Ahmad ɗin ne ya mamaye duk wani lungu da sako na gangar jikinta.
Tsaki tarinƙa ja akai akai sannan a hankali ta bursar da iska mai zafi.+
Duk wunin ranar akwance Rabia tayi shi ban da salla babu abunda ke tada ita abubuwa sun taru sunmata yawa.
tarinƙa saƙa da warwara a ranta ciki har da yadda zata tsinke auranta da Ahmad.
Misalin ƙarfe takwas na daren ranar Ahmad ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo haɗe da sallama, ya maida ƙofar ya rufe ya jingina bayansa sanye yake cikin jallabiya sai zuba kamshi yake.
Kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kanta don ko sallamar da yayi a ciki ta amsa ta yadda bazai ji ba,
shima kallo daya yayi mata ya gane tana cikin damuwa dan haka karasowa yayi har inda take zaune tana cin magani.
Zama yayi sosai kusa da ita har cinyoyinsu na gugan juna wani irin jimmmmmmm…..sukaji alokaci daya.
Hannuta ya soma lalubowa zai kama cikin nashi da sauri ta zame tana watsa masa mugun kallo tace,
“lafiya dai malam”
Ya sake sa hannu zai jawota gareshi ta Miƙe da hanzari zata bar ɗakin fizgota yayi ta fado jikinsa ta kwantar da kanta dai dai ƙirjinsa inda ƙamshi ya fi yawa luf, ta lafe tana shaƙar haɗaɗɗen ƙamshin turarensa.
A tare suka sauke ajiyar zuciya.
ya ɗago kanta ya haɗe goshinsa da nata yana busa mata iskar bakinsa Lumshe idanunta tayi.
a hankali kuma ta soma ƙoƙarin raba jikinta da nashi.
yace, “ke! meye haka ina zaki kuma bayan kinsan don ke na dawo gidan?”
Ta watsa masa harara
“to ni ina ruwa da dawowar ka, in kaga dama kar ka sake ta kowa inda nike dan ni, Dan haka malam sakar min jiki ko Kuma wani salon iskanci ne yau kuma kazo dashi”
Ya ɗage mata girarsa ɗaya alamun eh sannan ya zuba mata fararen idanunshi yana nazarinta, yana son yasan meye damuwarta da dalilin ganinta cikin halin ƙunci duk da yasan haka take.
Amman na yau yafi na koda yaushe.
Ga hawaye yaga suna silaluwa a fuskarta kamar an buɗe fomfo cike dajin haushi yake magana,
“ke! kukan me kike wa mutane ko tsabar shagwaɓar da kikewa yayanki ne zaki kawo min?”
ta sake watsa masa harara cikin zafi zafi tace,
“meye damuwarka dani ne? eyeh tambayarka nake me ruwanka da kukana? ina ce da idona nakeyi ba da naka ba”
“dan Allah na roƙeka, ka barni da tashin hankalin da nike ciki”
A kausashe yace “wani tashin hankali kike ciki bayan wanda kika baroshi a gidan ku, yarinya dan ma kinsamu an taimaka miki, dana rufa miki asiri na aureki shine har zaki zo kina kawowa mutane rainin hankali”,
ya ja tsaki haɗe da wurgi da ita ta zube ƙasa
yace “inkin ga dama kiyi ta kukan har mahdi ya bayyana babu ruwan Ahmad danshi yana da masoyiyarsa mai sonshi da kula dashi”
Cikin wani irin tashi hankali ta Miƙe tana kuka Gwanin ban tausayi ga wani mugun kishin matarsa data ke ji yana mamaye duk wani saƙo na zuciyarta.
A hankali ta soma magana,
“da baka da maganar daya wuce gorantamun akan aurena da kayi,
Wani ya dole maka dole ne? Still
yanzu an ɗaure maka ni ne? ka sakeni man kaga ikon Allah dan ko second bazan ƙara a gidanka ba,
Kuma dan Allah na roƙeka ka sakeni bana son taimakon naka mugu kawai”
Ya soma takowa inda take cikin zafin nama ita kuma tana ja da baya har takai ƙarshen bangon ɗakin a firgice ta ɗago tana masa kallon ya tausaya mata tana girgiza masa kai.
Murmushin gefen baki yayi yasa hannunshi ɗaya ya dafe bango dashi yana mata dariyar mugunta, numfashi take fitarwa da sauri da sauri saboda tsabar tsoro yana kallon yadda ƙirjinta ke sama da ƙasa.
Runtse idonsa yayi sannan kuma ya buɗesu ya zuba mata Ido, hannu yasa ya matse bakinta ta saki wahalalliyar ƙara,
Yace “wlh bakin nan yakiyayi faɗaman duk abinda yaso, idan ba haka ba zan cire bakin tsiwa kowa ya huta”
Ya matseta da bango yana hukuntata da yatsunsa mutsu mutsun ƙwace jikinta da bakinta daga nashi take Amman ta kasa saboda karfin su ba ɗaya ba.
Sai da ya gaji dan kansa ya saki bakin haɗe da ɓalle mata bakin da ya tsunshi guda biyu,
ta saki kuka mai cin rai tarinƙa tsine masa a zuciyarta a fili kuma tace,
“Allah ya isa mugu kawai, wlh sai ka sake ni ya zuba mata manyan idanunshi yana kallon bakin rashin kunya bai taɓa sanin rashin kunyarta takai haka ba
Dan haka cikin zafin rai baisan sanda ya ɗaga hannu zai kai mata wani gigitaccen mari ba, tsoro yasa Rabia ta tsaya cak da kukanta tana zare ido, ya kauce hannunshi yana huci,
“ki shiga hankalinki dani, idan dai bazaki kiyayi faɗamin duk maganar da ta fito daga wannan” ya nuna bakinta da yatsansa.
Yace,
“baza’a sakeki ba, idan kin gaji da zama ga hanya a bude take ko wani ya riƙeki? stupid girl kawai” fuuuuu…… ya fice daga ɗakin.
Ya kukaji zaman nasu?