MAIRO
CHAPTER 4
Kuka Mairo take sosai kanta na saman ciyar Gwaggo sai yanzu take jin ba daɗi kamar kar su Gwaggo su tafi.
“Kiyi hak’uri Mairo ai Aure haka ya gada”
Da kuka Gwaggo tayi mata maganar tana buga bayanta,
Momi ta mik’a hannu ta rik’ota “Yi hak’uri kinji Maryam ai ba nisa zatayi miki ba duk lokacin da kika so ganin su ai sai a kaiki kuma suma akai-akai zasu rik’a zuwa”
K’ara rushewa tayi da kuka ta kwanta jikin Momi,
Gwaggo ta share hawayen ta ta kalli Momi “Ga Amana nan mun baki ki rik’e ki kula da ita in kikaga tayi ba dai-dai ba ki ɗorata a hanya”
Momi ta ɗaga kai “In’sha Allahu zan rik’eta Amana”
“Toh Allah ya tayaki rik’o ya bata ikon yi miki biyayyah”
“Amin Gwaggon yara”
Momi ta faɗa tana ɗan dariya.
“Bari naje na dubo girkin can karya kone”
Momi na tashi Gwaggo ta janyo hannun Mairo.
“Mairo ki rike hajiya Uwa kinji kinga dama can Uwar ki ce barre yanzu dan haka ban saɓa mata ko ta baki umarni ki k’i bi kiji?”
Kai ta ɗaga mata idonta a kumbure
“Kuma bari kiji na faɗa miki duk kikaga Qasimu yayi miki wani abu da baki so ko matarshi toh ki faɗa mata dan naga sunan wannan matar kuma karki saurara mata duk tayi miki can mutunci Ki mata Idan kuma ta nemi zaman lafiya toh ku zauna da tayi miki wani abu Ki fada ma maman shi in kikaga bata ɗauki matakiba ki bugo min waya”
Nan ma kan ta ɗaga
“Kuma ki bi mijinki sau da k’afa banda rashin kunya duk huɗubar da nayi miki karki zubar da ita”
“Toh Gwaggo amman dai zaku k’ara zuwa ko?”
“Zuwa ai dolene Mairo dole ne na rik’a zuwa ina ganin yadda zamanku zai kasance dan naga wannan matar tashi ba kirkirne da itaba koda yake naga kowa gidan shi daban (Part) dan jiya ya kaimu munga gidan”
Kwantawa tayi jikin Gwaggo tana shan majina
***
Kwance take saman jikinshi suna kallo,
“Dear”
“Na’am”
“Amman dai ba zaka raba mana gida da ita ba ko?”
Cike da mamaki ya kalleta “Miya kawo wannan maganar kuma keda baki son maganar ta?”
“Ba komai kawai dai naga hakan zai sa na ɗan rage abinda nake ji a kanta”
“Toh Allah yasa ni daman banida niyar raba muku gida”
“Toh Allah ya haɗa kan mu”
Da mamaki yace “Amin dear Allah ya cigaba da shirya min ke”
Ya faɗa yana shafa saman kanta.
Sun daɗe a haka sannan ya tashi ya shiga bathroom.
Wanka yayi ya shirya cikin k’ananan kaya ita kuma har lokacin tana kwance.
Kiss ya mana mata ya fito ya nufi part ɗin Momi,
Koda ya shigo ya tararda su Gwaggo parlor driving na saka musu kayansu both
Saida ya gaida su sannan ya zauna kusa da Momi yana kalln Mairo “Mi akayi mata?”
“Ba mata komai ba wai dan zasu tafi take kuka”
Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba har aka k’are saka kayan.
Sallamar k’warai Qasin da Momi sukayi musu daman Abbah tuni yayi musu tashi sallamar dan tun washe garin zuwansu ya wuce Abuja.
Har motar su ta tashi Mairo bata daina kuka ba daker Momi ta lallaɓata tayi shiru.
“Haba ko ke fa amman tun ɗazu kukan nan ne kawai kike kinsan kuka fa baya da kyau”
“Toh Momi ba na daina ba”
“Yauwa toh nima ba gashi na jindaɗi ba Allah yayi miki albarka”
“Amin Momi”
Qasin ya ɗan murmusa “Maryam tashi kije kiyi wanka mai ɗinki na nan zuwa ta auna ki”
Da sauri ta tashi ta nufi upstairs.
Momi ta k’ara mata “Kuma kici abinci”
Daga can ta amsa da “Toh”
Tashi yayi yana faɗin “Nima bari na lek’a office”
“Ok sai ka dawo”
Hannayenshi yasa aljihu ya fice.
Sai goman dare ya dawo gidan.
Kai tsaye part ɗin Momi ya nufo hannun shi rik’e da bak’ar leda.
A parlor ya tararda Mairo zaune sqman doguwar kujera idonta na akan tv.
“Ke aljana dare ne ranar kallon ki ko?”
Da sauri ta kalli k’ofar
“Yaya har ka tsorata ni Wallahi”
Zaunawa yayi kusa da ita “Allah ko?”
Murmushi tayi “Eh mana ina wuni”
“lafiya kalau mai ɗinkin tazo?”
“Eh tazo Yaya ashe ko’ina aunawa take”
“Eh mana saboda kar ɗinkin ya matseki ko yayi miki yawa”
Yayi maganar yana k’ok’arin bude ledar
Cinyar kaza ɗaya ya ɗauka ya mika mata ledar da gorar yagot
“K’arɓi ki ci dan nasan baki ci abinci ba kuka kika wuni kinayi ai yau sai kinyi mafarki su”
Dariya tayi “A’a ba zanyi mafarki su ai sun riga sun tafi”
“Ko sun tafi sai kinyi mafarkinsu”
. “A’a Allah ba zanyi ba”
“Toh mu k’ulla in kikayi mafarki su saina miki horo”
“Eh na yarda amman ni kuma in banyi mafarki su sai na maka horo ka yarda?”
“Eh na yarda yarinya gobe zaki yabawa aya zak’inta”
Dariya tasa mishi “Kai dai zaka yabawa aya zak’inta zaka ji jiki”
Dariya yayi sosai harda kwantawa a kujerar “Lallai yarinya nime zanji jiki? Zaki dai ji jiki idan ranar jin jikin tazo”
Hannu ya kai kan ledar da sauri ta tashi tare da ledar “A’a Yaya ka ci naka fa wannan nida Momi zamuci”
“Ai Momi bachi take kuma yayi miki yawa ba zaki iya cinyewa ba”
“Wallahi idonta biu tana ɗakinta”
Tashi tsaye yayi da sauri “Da gaske Momi ba tayi bachi ba?”
Gira ta ɗaga mishi as respond tana murmushi.
Da sauri ya fice yana kallon stairs.
Story continues below

_Washe gari_
Tunda akayi sallar A’suba Mairo ta dawo parlor ta zauna sai rabon ido take can kuma ta tashi ta kunna tv.
7 da yar mintuna Momi ta sauko k’asa da sauri Mairo ta risina ta gaisheta “Momi ina kwana”
Momi tayi murmushi “Lafiya kalau an dasa dag inda aka tsaya kan kallo ko?”
“A’a Momi daman wannan film ɗin nake so kuma sun k’are”
“Toh muje kitchen a hada breakfast”
Remote ɗin dake hannunta ta aje suka nufi kicin ɗin tare.
Aikin kawai suke amman hankalinta na wani guri da taji motsi sai taje ta lek’a.
Kacar taga sun gama aikin ta ɗauko ta kawo saman dining,
“Momi naje na kira Yaya Qasin?”
Momi ta aje kula tare da kallonta “A’a ai kinsan ba nan yake breakfast ba”
Ta marairaice fuska “Dan Allah Momi daga yau bazai k’ara ba wani abu zan faɗa mishi”
“Indai wani abun zaki faɗa mishi jeki amman breakfast kan ba nan ba”
“Toh”
Da gudu ta juya Momi ta kwala mata “Maryam zo ki ɗauki ɗan kwali”
“Toh bari nazo”
Momi ta girgiza kai “Oh Allah ya shirya”
Da gudu ta faɗo parlor Mansura bata lura da Qasin dake tsaye jikin windo ba ta nufi k’ofar ɗakin shi.
“Ke…”
Da sauri ta juyo suna haha ido ta gaidashi
“Ina kwana?”
“Lafiya kalau an tashi lafiya”
Ido ta ɗan sakar mishi sanye yake da gundun wando mai kamar na bachi jikinshi babu riga.
Kasa tayi da kanta ta juya ta nufi k’ofar fita.
Gudu yayi ya kamota “Ina zaki?”
“Yaya jikinka babu tufafi”
Kallon jikin nashi yayi sannan yaja suka zauna saman kujera.
“Miya kawo ki nan?”
Fuskar zolaya tayi mishi tana dariya “Banyi mafarki su ba”
Hancinta yaja yana murmushi “Oh kedai faɗamin gaskiya Dan nasan fa sai kinyi mafarki su”
“Banyi ba ai na faɗa maka sai kaji jiki”
Dariya yayi ya rumgume ta Yana faďin “Wai ke baza kibar cewa sai naji Jilin nan ba ko?”
Wani yarrr taji kamar an tsoketa da alura. Duk tsigar jikinta ta tashi.da sauri ta ɗago tana kallon fuskarshi,
Bai kula taba ya sake maida ita cikin faffaɗan k’irjinshi ya rumgume ta tsam-tsam.
Can zuciyashi ta yayo mishi Mansura dake bachi.
ba zai iya da matsifar taba duk da yasan ba haramun ya aikata ba amman yasan in yanzu ta tashi daga bachi ta gani ba k’aramar drama ra’ayiba.
D’agota yayi “Momi ta haɗa breakfast?”
“Eh tare mukayi amman tace karka zo wai ba nan kake breakfast ba” Ta bashi amsa idonta a kulle gam.
Murmushi yayi “Toh jeki gani nan zuwa”
Saida ta sauka saman jikinshi sannan ta buɗe idon ta fice.
Koda ta dawo ta tararda Momi na break ita Usman da Nura kujera taja ta zauna tana murmushi.
Batayi minti biyar da zaman ba ya shigo sanye da doguwar jallabiya, a kujerar da ya saba zama ya zauna bayan sun gaisa da Momi.
“Mi zakayi?” Momi ta tambaye shi ganin ya janyo plate
“Breakfast Maryam tace nazo naci abinci”
Momi ta watsama Mairo harara.
Da sauri Mairo ta kalleshi “Lahhh” ganin babu alamun wasa a fuskarshi yasa tayi shiru ba tace komai ba.
Sai suka magama cin abinci sannan ta kalleshi “Yaya ni naci yanzu mi zakayi min?”
Momi tace “Ke kikaci mi?”
Da sauri ya tari numfashinta “Wai abinci take nufi jeko kiyi wanka kamin na tashi sai na faɗa miki”
Tashi tayi har ta juya sai kuma ta juyo “Wai Momi ina Siraj?”
“Yana Abuja Asabar ɗin da za kuzo ya tafi da safe yanzu can yake aiki”
Bata sake cewa wani abuba ta nufi ɗaki.
Bayan su Usman ta tashi Momi ta kalli Qasin a natse tace “Yanzu matsayinka ya canja nauyi biu ne a kanka ko wace dolene ka bata hak’inta ban zalumci shi aure sai anyi hak’uri tun a Mansura ka gani balle Maryam da ba wani wayau ne da ita ba.
Amanace aka baka bana son naji wani saɓani a tsakaninku”
Sai da ya nisa sannan yace “In’sha Allahu Momi babu abinda zai faru zan rike ta amana zanyi adalci a tsakanin su”
“Toh Allah ya taimaka ya baka iko kuma bana son tayi zama mai tsayo agurina dan haka kasa himma gurin shirye-shiryenka ku tare”
“Ai ni banida wani shiri Momi inba kayanta dake gurin ɗinki ba sai kuma kayan ɗakin da Abbah yayi mata oda ne basu iso ba amman nasan cikin watan nan komai zai kamala In’sha Allah”
“Toh Allah ya taimakamin haka nake so Allah Baku hak’urin zama”
Amsaba yayi da “Amin” Ya Tasha ya fice.
Wanka Mairo tayi ta shirya cikin bak’ar abaya.
Sai lek’e-lek’e take har bayan Azahar bata ga Qasin ba ganin Momi na bachi yasa ta nufi part ɗin shi,
Sallama ta ɗingayi tun daga bakin k’ofar har takai tsakiyar parlor.
Mansura ta fito kicin “Ke Uban mi kika zoyi part ɗina”
“Ubaki!” Kai tsaye Mairo ta bata amsa Tana wani turo baki.
Mansura ta daki k’irji “Kan uba ke ni zaki zaga?”
“Aini ban zage ki ba ke kikace uban mi nazo ni kuma nace ubanki kuma ni bama gurinki nazo ba Yaya nake nama”
“Aini ban zage ki ba ke kikace uban mi nazo ni kuma nace ubanki kuma ni bama gurinki nazo ba Yaya nake nema”
K’ofar ɗakin shi Mansura ta nuna mata “Shiga yana nan ciki”
Juyawa tayi ta nufi k’ofar ɗakin.
Tana shiga Mansura ta rufa mata baya, tana shiga ta cakumo wuyanta “Uban kike zagi?”
Nan Mairo ta marairaice fuska “Ba ubanki ba ba keba dan Allah kiyi hak’uri”
Mansura bata saurara mata ba ta watsa mata mari.
Uhu Mairo tasa mata ta fashe da kuka Mansura bata saurara mata ba ta danneta a kasa tana dukan ta har sai da ta fasa mata baki,
Da gudu Mairo ta baro part ɗin ta nufo part ɗin Momi tana kuka bakin k’ofar parlor ta faɗi tana murje-murje.
“Wayyo na bani na lalace ta kashe ni wayyo Gwaggo Momi wayyo Allah wayyo Babana”
Da gudu Momi ta fito tana tambayar ba’asi,
Zaro ido tayi tana faɗin “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un miya fasa miki baki haka Maryam”
Cikin kuka ta nuna part ɗin Qasin “Mansura ce ta dake ni”
Momi ta rik’a ta “Mi kikayi mata?”
“Ban mata komai ba wai dan naje neman Yaya Qasin shine tace na shiga ciki yana ɗaki dana shiga sai ta rufeni da duka Momi na shiga uku kasheni zatayi”
Kai Momi ta girgiza cike da ɓacin rai ta rik’a Hannunta suka suka shiga ciki,
Bathroom Momi ta shiga da ita ta wanke mata bakin da fuska sannan suka fito.
Waya Momi ta ciro ta danna ma Qasin kira.
Yana isowa Momi ta nuna mishi fuskar Mairo tana masifa,
“Dubi fuskar yarinyar nan kalli yadda matarka tayi mata duka”
“Duka kuma?” Ya tambaya “Mi kika mata?”
“Ban mata komai ba wai dan naje neman ka”
Zaunawa yayi saman kujera “Ke kuma Maryam miye na zuwa nemana in banda abinki”
Momi ta tari numfashi shi “Miya kai wannan wace irin magana ce ko babu Aure tsakanin ku ai zata iya zuwq part ɗinka balle yanzu da take Matarka,
Yadda fa kake Auren Mansura haka kake aurenta kuma duk hak’in da kasan yana kanka na Mansura haka na Maryam yake kanka.
Kawai ka takawa matarka birki karta sake dakar min, ya dan amanace agurina ba zan sa mata ido tana dukanta ba tunda ba haihuwarta tayi ba”
Tunda Momi take mashi faɗan idonshi na kan fuskar Mairo da ta ɗan kumbura.
Hannu yakai ya taɓa kumatunta. Nan ta saki uhu ta fashe da kuka,
Momi tace “Kagani ko zafi take ji taji mata ciyo sosai”
Ajiyar zuciya ya sauke “Tashi muje pharmacy”
Tashi tayi tana kukan da ban raba shi dana munafurci ba ta shiga ɗaki ta ɗauko mayafi suka fice.
A pharmacy dak’er ta tsaya aka sa mata maganin sai ihu take tana kiran Abban ta,
Bayan sun dawo ya kawota part ɗin Momi tare da maganin da aka bata. Da zai fice saida Momi ta k’ara jaddadamishi “Kafa jawa matarka kunne karta sake dukanta dan itama haihuwarta akayi kamar kowa ba sassak’ota akayi ba”
“In’sha Allahu Momi zanyi mata magana ayi hak’uri”
Kawarda fuska Momi tayi shi kuma yasa kai ya fice.
Tun daga yanayin shigowarta ta fahimci yana cikin damuwa dan ko Sallamar shi kamar a kasale yayi ta.
Bayan ta amsa ya zauna kusa da ita. “Sannu da zuwa”
“Yauwa sannu Mansura mi yasa kika daki Maryam mi tayi miki?”
Taɓe baki tayi “Oh an daki yar’gol ko shine kabi ka haɗe rai toh an dake ta ɗin ko zama mata zakayi?”
Wani kallo yayi mata mai cike da jin haushi. “Bazan rama mata yanzun ba amman duk kika sake dukanta zan rama mata dan ita mutunce kamar ke kuma abokiyar zamanki ce ba yar aiki ko ya ba dan haka karki sake sa mata hannu”
Yana kaiwa nan ya tashi ya nufi bedroom ɗinshi. Tintsirewa tayi da dariya ta taɓa hannu “Lallai Qasin ni zaka faɗawa haka saboda kayi yar tsakin Amarya? Wato anci moriyar ganga za’a yada korenta ko toh baka isaba wallahi dan kowa yaci tuwo dani miya ya sha kuma indai dukane sai na mata shi sai dai in bata shigo part ɗin nan ba”
Haka ta dinga faɗa ita ka ɗai cikin parlor
Washe gari Mairo k’in cin abinci tayi duk yadda Momi ta lallaɓata k’in ci tayi ita la dole ga mai ciyo a baki.
Saida Qasin ya shigo ya sata a gaba sannan ta ɗanci ko shi bawani abin kirkiba.
Haka sukayi ta lallaɓata shida Momi har suka samu ta warke.
_Ranar Assabar…_
Duk da yake yau ba rabar aiki bace bai hana Qasin fita tun da safe ba,
Momi ma sha biu na bugawa tasa Mairo tayi wanka saida ta fito sannan itama ta shiga. Koda ta fito Mairo ta ɗanɗasa kwaliyarta ta shirya cikin koriyar atamfa ta cika janbaki a bakinta yayi mata yawur.
Murmushin jindaɗi Momi tayi daman haka take son ganinta kullum, Hijab Momi ta ɗauko tasa tana faɗin “Karkije ko ina saina dawo kinji na faɗa miki ko?”
“Eh naji amman karki dade Momi”
“Bazan daɗe ba danayi gaisuwar zan dawo”
“Toh Allah ya tsare”
“Amin”
Har bakin k’ofa Mairo ta rako ta saida ta shiga mota sannan ta dawo parlor.
Batayi minti 8 da fita ba taji tsayawar mota da sauri ta lek’a ta windo, Qasin ta tsinkaya ya fita daga motarshi ya nufi part ɗin shi.
Da gudu ta fito ta nufi part ɗin ita. Zauna ta tararda shi yana shan ruwa gora.
“Yaya sannu da zuwa”
Saida ya kare mata kallo sannan ya amsa.
“Yauwa sannu zo nan” Ya mik’a mata hannu.
Ba musu ta mik’a mishi nata hannun ya rik’a ta ya zaunar kusa dashi “Wa yayi miki wannan kwaliyarta?”
Murmushi tayi “Ni nayi nayi kyau ko?”
“Sosai ma kamar ba keba”
Dariyar jindaɗi tayi.
Bakinta ya sakarma ido daga bisani yakai nashi bakin cikin nata.
Sai da ya tsotse janbakin tas sannan ya yanje bakinshi yana lumshe ido. Tofarda yawu tayi tasa hannu tana goge baki,
“Wai kai Yaya nace ka daina min haka bana so k’azanta nake ji amman kullum sai kayi gashi nan duk ka goge min janbaki”
Kamar ta rusa kuka tayi maganar tana buga k’afarta a kasa.
Murmushi yayi “Toh yi hak’uri bari na ɗauko miki janbakin matata ki shafa kina so?”
“Eh amman babu ruwana in tayi maka faɗa”
“Ai bata nan ta tafi kasuwa ta siyo abun bak’i zatayi”
“Toh ɗauko min”
Tashi yayi rike da gorar ruwan ya nufi ɗakinshi kayan dake jikinshi ya rage ya koma daga shi sai rigar shan iska sannan ya fito ya nufi ɗakin Mansura.
Story continues below

Kale-kalenta ya kai idonta kan cake ɗin dake gefen kujera.
Ta sauri ta tashi ta nufi gurin daman tun dazu take jin k’anshi.
D’aya ta fara ɗandanawa da taji yayi mata daɗi sai ta hau cin abinci tana lasar hannu,
Qasin na fitowa ya hango aikin da take daga can ya katsa mata tsawa “Ke waya kaiki bak’ifa zatayi ta siyo musu cake ɗin shine kika zauna kika ci? Aiko mai rabaki da ita yau sai Allah”
Ragowar dake hannunta ta aje “Toh ni bana ɗauka naka nabe”
“Nawa zan aje nan ban bakai miki naki ba bak’i fa tayi ta siyo musu kuma yanzu kar ta iskomu da munje mun tsiy…”
jin tsahawar motarta yasa yayi shiru.
Da sauri Mairo ta tashi tsaye “Itace ko?”
“Itace kuma ni babu ruwana ke da ita can”
Tana tashi ta niyar guduwa Mansura ta turo k’ofar parlor ta shigo.
Da sauri Qasin ya k’arasa saukowa ya tareta “Kin dawo?”
Bata amsa mishi ba ta watsama Mairo harara “Mi kikazo nan?”
Duk bata ga aika-aikan da tayi mata ba sai da ta kusa kaiwa kusa da ita.
“Kan Uba uban wa ya aikeki taɓa min cake?”
Gabanta Qasin yaci ya rik’ota “Yi hak’uri Mansura bata san naki bane bari na siyo miki wani yanzu”
Janbakin dake hannun shi ta kalla “Waya ɗauko min jan baki mi zakayi dashi?”
Matsowa Mairo tayi kusa da ita ta turo bakinta tana nuna mata.
“Shine ya tsotse min janbakina shine yace bari ya ɗauko min naki na shafa amman na fasa shafawan gida zani”
Baki Qasin ya saki ya juyo ya kalli Mairo,
“Ke miyasa karya bata miki wahala ne?”
Sake juyowa yayi ya kalli Mansura “K’arya fa take”
Uffan ba tace mishi ba ta mika mishi hannu “Bani cake ɗin”
Yana duk’awa ya ɗauko mata nan ta cire takalmin ta mai tsini ta saita kan Mairo ta k’wala mata shi.
Wata mahaukaciyar k’ara Mairo ta saki. Jini ya malalo mata daga saman kai,
K’arasa jefa mat takalmin Mansura tayi tana faɗin “Gobe in kikaga na sake ganin na aje abu ki ɗauka ciki wai har kike faɗamin janbakinki ya tsotse ke tsohuwar karuwa ko?”
Da gudu Mairo ta bar parlor dafe da kai.
Jefeta Qasin yayi ya cake ɗin ya wanke mata fuska da mari hudu masu kyau. Da sauri ta dafe kunci tayi baya-baya tana kallonshi “Qasin saboda na fasa mata kai ka mareni”
K’ara mata na biyar yayi “In bakida hankali sai kiyi shi saboda taci miki cake ɗin banza zaki daketa ki safa mata kai haka aina fada miki duk kika sake sa mata hannu sai na samiki”
“Lallai Qasin kai butulu ne yaushe aka ɗaura maka Auren da ita da har kake fifitata a kaina? Koda yake halinku ne maza haka kuka gada”
Cikin kuka take mishi maganar.
“Ke in banda rashin hankali mi zakiji a jikin Maryam in kika daketa?”
“Abinda kasan a naji shi zanji mai abin kunya yasa k’aramar yarinya a gaba yana kiss”
“Toh haramun nayi har abinda yafi kiss sai nayi mata tunda matata ce”
“Bazan iya zama da kai ba Qasin sun riga sun shiga tsakanin mu yaushe kayi Auren nan amman gashi har ka fara canja min bazan iya zama da kai ba har sai ka zaɓa koni ko ita”
Tsaki yaja ya fice ya bar mata parlor.
_A ɓangaren Mairo_
Da gudu Mairo ta shigo parlor tana kiran sunan Momi.
“Lafiya Maryam?”
Jin muryar Yarima yasa ta juyo da fukar jini ta kalleshi. Baya-baya tayi tana cigaba da kukan.
Da sauri ya rik’ota “Ke Maryam ba wani abin zanyi miki ba miya sameki haka?”
Cikin kuka ta bashi amsa “Matar Yaya Qasin ce ta fasa min kai”
Baiyi wata-wata ba yasa hannu ya ɗauketa yana faɗin “Muje na kaiki asibiti”
Tirjiya ta shiga mishi tana k’ok’arin k’wace kanta.
Sauketa yayi “Trust me Maryam bazan miki komai ba asibiti zan kaiki”
Ganin bata da mafita yasa ta kyale shi kodan zogin da take ji yaja hannunta suka fice.
Koda Qasin ya shigo bai tararda ita ba duk saida ya bikaca gidan amman babu ta babu labarinta,
Fitowa yayi ya nufi gurin mai gadinsu yana tambaya shi ko yaga Mairo.
“Eh ranka ya daɗe naganta a motar Yarima sun fita”
“What!?” Da k’arfi Qasin ya tambaya
“Yaushe Yarima ya shigo?”
“Bai daɗe da shigowa ba sai kuma naga ya fito tare da ita da gudu ma ya fita”
Kai Qasin ya ɗaga mishi ya nufi part ɗin shi.
D’akinshi ya nufa yana jin kukan Mansura. bai ta kanta ba ya ɗauko keys ɗin matar shi ya fito.
Yana kawowa parking space ya tararda Momi ta fito daga mota.
Yanayin yadda ta ganshi yasa ta tambaya “Lafiya dai?”
Shiru yayi yana kallonta ya kasa bata amsa, “Qasin da kai nake magana lafiya na ganka haka?”
Kanshi ya sosa “Momi Maryam ce tayi faɗa da Mansura shine ita kuma ta fasa mata kai kuma nazo yanzu ban ganta ba ance Yarima ya fita da ita shine zan bi bayan shi”
Momi ta zaro ido “Wa aka fasama kai?”
“Maryam”
Wani irin Momi tayi kamar ta fasa kuka “Ta mutu ne?”
“A’a Momi kaɗan fa ne ma aka fasa mata kan”
Motar Momi ta rufe ta nufi cikin gida idonta da k’wallah.
Rufa mata baya yayi tana kwantar mata da hankali,
Saman kujera Momi ta zauna dafe da kai.
Nan shima ya zauna “Dan Allah Momi ki kwantar da hankalinki bafa wani mugun ciyo bane taji kawai..”
Hannu ta ɗaga mishi “ɗan Allah ka rufe min baki ka naji da wane da raunin da kukayi mata ko da surutunka”
Shiru yayi yana shafa kanshi. duk abin duniya ya ishe shi ya rasa da wanne zaiji ɗayan ɓangaren zuciyashi yana gurin Yarima da tafi mishi da Mairo.
nan kuma yasan Momi ba saurara mishi zatayi ba.
***
Pharmacy mafi kusa ya nufa da ita k’in yarda tayi a dubata saida Yarima ya rumgume ta.
Da kuka akayi treatment ɗinta sannan ya suka bata wasu maganin nika ya sata mota suka ɗauko hanyar gida.
bataana isa yayi horn kamin a buɗe mishi ya mik’a hannu ya riko hannunta yana sauke ajiyar zuciya
“Ina sonki Maryam ina sonki”
D’ago kai tayi tana kalloshi har aka buɗe mishi gate ɗin ya kunna kai cikin gidan.
Bayan yayi parking ya fito ya nufi parlor Momi still yana rik’e da hannunta,
Daga Momi har Qasin tashi sukayi Suna kallonshi. nan Mairo ta shiga k’ok’arin kwace hannunta. Iya k’arfinshi yasa ya rik’e hannun gam. Ko motsin kirki ta gagara yi.
Cikin wani irin zafin nama Qasin ya k’araso kusa dashi ya ɗaga hannu zai mareshi. Da sauri Yarima yasa ɗayan hannunshi ya rik’e mashi hannu yana mishi wani kallo.
“Kayi kaɗan kasa wulakantaccen hannunka a fuska ta”
Damk’e hannu Qasin yayi da k’arfi kamar mai dambe ya kai mishi naushi dai-dai k’ahon zuciya.
Zaro ido Momi tayi ta ɗora hannu aka “Qasin mi kake k’ok’arin aikatawa haka?”
Baiyi wata-wata ba ya sake aika mishi wani bugun.
Ba shiri ya saki hannun Mairo ya faɗi durk’ushe dafe da zuciyar. Ture Qasin Momi tayi idonta cike da k’wallah “Wai baka da hankali ne Qasin so kake ka kashe shi fice ka bar parlor nan”
Hannu Mairo ya fisga sukabar parlor tare.
Part ɗin shi ya nuf har lokacin yana rik’e da hannunta.
Bai sake ta ba sai da ya sata cikin ɗakin shi sannan ya jefar da ita saman kujera ya zaro belt ɗin shi ya hau dukanta.
Mairo bata san zafin duka ba sai yau tunda Gwaggo bata taɓa sa mata hannu ba kuma bata bari kowa yasa mata.
Ihu ta dinga yi tana kuka baji ba gani tun tana iya ɗaga murya har muryata ta dakushe.
Saida yayi mata dakan da shi kanshi ya gamsu ta daku sannan ya jefar da belt ɗin yana faɗin “Daga yau duk kika kuskura kika sake bari wani namiji ya rik’a miki hannu sai na karya ki”
Yana kaiwa nan ya juya ya fice.
Saida yayi kusan minti 30 da fita sannan ta samu ta rarrafa ta fito.
Tana kawowa parlor Momi ta zube k’asa ta rushe da sabon kuka. Da sauri Momi ta k’arasa ta rik’o “Inna lillahi wainna ilaihi raji’un dukanki yayi Maryam?”
Kai ta ɗaga mata tana wani irin kuka. Dak’er Momi ta lallaɓata tayi shiru sannan taja hannunta tana matsifa suka shiga ɗakinta.
Sai da Momi ta shiga ta haɗa mata ruwan ɗumi sannan ta shigar da ita bathroom ɗin ta gasa mata jiki. Bayan ta k’are ta sake haɗa mata wasu ruwan wankan ta fito.
Mairo wanka take tana kuka har tayi ta gama. Koda ta fito ta tararda doguwar rigar atamfa aje saman gado. D’auka tayi ta saka ta hau tsakiyar gadon ta kwanta tana sauraren ciyonkai da ya kawo mata ziyara.
***
Bayan Sallar Isha’i Qasin ya shigo side ɗin Momi k’asa-k’asa ta amsa mishi sallamar da yayi muryarta na ɗauke da damuwa.
Kusa da ita ya zauna tana kallonta tare da sauke ajiyar zuciya,
“Momi kiyi hak’uri Zuciyata ce ta rufe shiyasa”
Kallonshi Momi tayi “Amman kuma dan zuciyarka ta rufe saika aikata abinda in badan Allah ya gyara ba da zai iya kaimu ga dana sani? Daker Yarima yabar parlor, saboda mugun Bugun da kayi mishi duk kuma haka bai maka ba sai da kasa Maryam gaba ka dinga dukanta kamar an aiko ka”
“Momi Yarima dai ko kashe shi nayi inada hujja tunda shi ya kawo kanshi har cikin gidan nan ya kuma ɗaukar min mata ya fita da ita Maryam kuma inba duka nayi mata ba ba zata samu natsuwa ba”
Kai Momi ta girgiza “Ko kaɗan Qasin duka baya gyara sai dai ya ɓata faɗa ya kamata kayi mata ba duka ba bazan yarda ba,
Ba kuma zansa muku ido ba kai ka daketa matar ka ta daketa ba jaka bace dan haka karka sake sa mata hannu”
Bak’ar ledar dake gefen hannun shi ya mik’a mata yana faɗin “Naji Momi ayi hak’uri bazan sake ba ga wannan maganin a bata tasha”
Saida Momi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta k’arɓi ledar tana faɗin “Ka turo min Mansura zanyi magana da ita”
“Bata nan Momi nima koda na dawo ban tararda itaba daman da zan fita naga tana haɗa kayan ta”
“Fushi tayi kenan akan wani dalili?”
Kafaɗunsa ya ɗaga “Oho mata nidai bazan je bikonta yanzun ba tunda bani nace taje ba kuma ba wani abin akayi mata ba”
Taɓe baki Momi tayi “Toh Allah ya kyauta”
Saida ya amsa da “Amin” sannan ya tashi ya nufi dining.
Momi kuma ta nufi ɗakinta.
Story continues below

Zaune Momi ta tararda Mairo tana cin kankanar dake gabanta da ɗai-ɗai. Ruwan goran dake gabanta Momi ta ɗauka ta k’ara zubawa a kofi sannan ta kankare maganin ta mik’a mata.
“K’arɓi kisha jikinki zai ɗanyi sauki kamin gobe”
Ba musu ta karɓa ta sha. ta cigaba da cin kankanar.
A hankali Momi ta shafa kanta “Maryam dan Allah ki rik’a jin magana kinji in nace kiyi abu ki rik’ayi ki ɗinga karatun ta natsu
Kinga har makaranta nayi maganar zan saki amman sai naga natsuwarki tukuna”
Da sauri ta kalli Momi “Na daina Momi ina son makarantan ina ne? Bazan sake ba”
Murmushi Momi tayi “Toh sai dai naga natsuwarki tukuna dan karatu natsuwa yake so balle ba subject ɗaya za’ayi muku ba kinga za’a koya Miki yadda zaki iya saka tufafi, da tafiya, da iya magana, da dafa abinci, da zaman gidan Aure, da rubuta da karantawa,
Har sana o’i duk ciki za’a koya muku kuma kuɗi da yawa ake kashe dan haka nafi son sai kin natsu dan bana son kuɗina suje a banza”
Shiru Mairo tayi kamar mai tunani.
Momi ta cigaba
“Makarantar ba nisa nan ne gurin Abdullahi Fodio Road sunan makarantar gyara da kanki nima a radio naji ta na ɗauki number malamar na kirata mukayi magana kuma Fitar da nayi ɗazun gurin gaisuwa ma saida na biya naga makarantar,
Dan Allah ki natsu kinji ki daina duk wani abu da kikasan baya da kyau”
Kai kawai ta ɗaga mata taja fillo ta kwanta Momi taja zane ta rufe mata jiki tana faɗin “Ina tafar dai kinyi sallar I’sha ko?”
Nan ma kai ta ɗaga tasa hannu a baki.
Washe gari Mairo a ɗaki tayi breakfast su Momi ne kawai sukayi a dining room.
Nan na Momi take tabartawa Qasin maganar makarantar. Bai yi unk’urin hana taba duk da wani ɓangare na zuciyarshi baya so fatan alheri kawai yayi mata ya tashi ya fice.
Wasan ɓoya Mairo ta dinga yi da Qasin sam bata yarda ya ganta duk gun da tasan zai iya ganin ta daina zama.
Sai da Momi tayi mta faɗa sannan gaisuwa ta dinga shiga tsakanin su kuma daga gaisuwar bata wuce ba data gaisheshi ya amsa zata tashi ta bashi guri,
Hakan kuma sai ya soma damuwar Qasin ganin bata sakewa dashi.
Saida Momi ta tabbatar da taji sauki sosai sannan ta ɗauke ta da kanta ta kaita makaranta akayi mata komai da ake buk’ata. Daman suna da school bus ga mai buk’ata. Kuɗin bus ɗin Momi ta biya wadda za’a rik’a zuwa ɗaukarta kullum da k’arfe 10am a dawo da ita 5pm.
Maida hankali tayi sosai gurin karatun gashi Momi kullum cikin jaddadamata take kar tasa tayi hasarar kuɗinta
Wata irin natsuwa ce ta sauko mata tunda ta fara zuwa makarantar kwata-kwata ta cire wasa gefe ta aje ta tattara hankalinta gurin ɗaya ta kama karantunta
A makarantar darussa aka dingayi musu kala-kala tun Mairo na ganin abinda kamar lalata tarbiyane yana bata haushi har ta daina sannu-sannu abin ya fara shiga ranta.
*****
Ranar wata Jumma’a da misalin karfe goma sha ɗaya na dare Qasin ya shigo parlor Momi.
Mairo na ganin shi tayi saurin tashi daman ita ka ɗai ce parlor ta gaishe shi bayan ya amsa ta aje remote ɗin dae hannunta ta juya da niyar tafiya.
Da sauri ya riko hannunta “Ina zaki Maryam?”
Ba tare data juyo ba ta amsa mishi “D’aki kwantawa zanyi”
“Baki tashi yin bachi ba sai da kika ganin wai miyasa kike wahalar da nine Maryam bayan kuma kin kore min mata”
Sai a lokacin ta kalleshi “Nikan ban korar maka mata ba ita dai taga dama tayi tafiyar ta”
“Amman dai ai saboda ke ta tafi ko?”
“Amman kuma ni bance ta tafi ba ganin damarta ne”
Wani dogon numfashi yaja “Fine tunda kin iya jayayya”
B’ata fuska ta ɗanyi “Ni ba jayayya nake ba ai jayayya ba kyau kawai ina faɗan gaskiya ne”
Taɓe baki yayi yaja hannunta. Saida suka kai bakin k’ofa sannan ta fisge hannun ganin zai fita da ita “Ina zamu?”
“Part ɗina mana”
“Na maka mi?”
“In mukaje zaki gani”
Yana sake rik’a hanunta ta fisge.
D’aure fuska yayi “Kinsan bana son musu ko ba dai canye ki zanyi ba ba kuma dukanki zanyi”
Shiru tayi ta ɗanyi k’asa da kanta.
Bai bari ta tsaya tunani ba ya sake jan hanunnata a karo na uku suka nufi Part ɗin.
Sama gadon shi ya zaunar da ita.
Ita kuma gaban sai faɗuwa yake bedside drawer ya buɗe ya ɗauko wani dan karamin box Red color ya ya kalleta yace “Rumtse idonki”
“Kamin mi?”
“Ai dai bazan cutar dake ba ko Please close your eyes”
Rumtse idon tayi gam tana haɗiyar yawu.
Wani daddaɗan K’anshi ne ya daki hancinta hakan yasa ta buɗe idon a hankali.
Arba tayi da wata kyakkyawar sark’ar gold “Yaya kamar zinari na wanene?”
Ta tambaya idonta a zare zuciyar na bugawa da sauri.
“Gold ne ba kama bace kuma ke na siya ma ko baki so”
Da sauri tasa hannu biu ta karɓa ta kuma durkusa k’asa “Inaso yaya na gode sosai Allah ya bika Jazakallahu khar”
Murmushi yayi ya ɗan tsosa bakinshi “Ur welcome dear” Ya tado da ita yasa bakinshi cikin nata.
Batayi k’ok’arin hana shiba har saida ya gaji dan kanshi ya zare bakin daga nata.
Tashi tayi da sauri “Bari naje na nuna ma Momi”
Kunkurumta ya rik’e “A’a Momi yanzu ai tayi bachi kuma kinsan bata son a tashe ta”
Kai ta ɗaga mishi tana murmushi mai fitar da sauti har cikin zuciyar ta take jindaɗin.
Laptop ɗin shi ya janyo “Zauna na nuna miki wani abu” kusa dashi ta zauna tana ciki da jindaɗi.
Kunna laptop ɗin yayi ya shiga nuna mata wasu pictures ɗin da bata san lokacin ya ɗauke suba.
Dariya ta dingayi ganin wasu bachi ma take “Lahhh Yaya yaushe ka ɗauka?”
“Kina bachi na ɗauka ba kece kike tsayawa kallo a parlor ba”
Murmushi tayi ta k’asa da kanta kamar wace taji kunya.
Nan ya shiga nuna mata nashi hotunan da yayi a k’asashe waje. Ganin ta fara jin bachi yasa ya janyota ya kwantar da ita saman jikinshi.
Aiko nan da nan bachi ya buget. Qasin kamar mai jira ya rufe laptop ɗin, bai ko bari bachi nata ya nina sosai ba, ya kwantar da ita kan gadon ya rabata da rigar jikinta ya shiga shafa ta yana aika mata kiss ta ko’ina.
Wasa yayi da ita sosai sai da yaji ya gamsu sannan ya tashi a wahale ya shiga bathroom. Wanka yayi ya fito ya saka kayan bachi sannan ya nufo ta ya mayar mata da rigar,
Itakan sai bachi take abinda bata masan yayi ba. ɗaukar ta yayi kamar baby tare da sark’ar ya kawota part ɗin Momi ya kwantar saman doguwar kujera ya aje mata sak’ar aje.
Ya daɗe tsaye yana kallonta sannan manna mata kiss a goshi, ya kashe wutar parlor tare da Tv yaja mata k’ofa.
***
Asubar farin Momi ta tashi ta daman haka take mata kullum saboda zuwa makaranta tunda har Asabar da Lahadi zuwa suke basu da ranar hutu.
Cikin magagin bachi ta motsa tana faɗin “Yaya duk sunyi kyau”
Momi ta jijjigata da k’arfi “Ke tashi kiyi wanka kiyi sallah wane yaya kuma?”
Muk’a ta shiga k’ok’arin yi sannan ta tashi, sark’ar dake gefenta ta faɗo. Bata kula ba ta wuce ɗaki tana murza ido da mamakin ganinta parlor Momi ita da bachi ya ɗauke a part ɗin Qasin.
D’aukar sak’ar Momi tayi ta rufa mata baya bayan ta k’are mata kallo, Sai da tayi sallah ta shirya sannan Momi ta tambayeta ina ta samo sark’a.
Dariya tayi “Ashe da gaske ne ni na ɗauka duk mafarki nake Yaya ya bani jiya da dare”
Momi tayi murmushi “Aiko ya kyauta tunda daman bakida sak’ar zinari kuma ya siya miki mai tsada ina fatar dai kin mashi godiya dan godiya tana ɗaya daga cikin abin da take saka Namiji jindaɗi idan yayi miki kyauta koda kusa kyautar bata kai ta kawo ba”
Kular abincinta ta ɗauka tana faɗin “Nayi mishi Momi bari naje ga motar makarantar mu can ta iso”
“Toh Allah ya tsare ya kiyaye”
“Amin Momi sai na dawo”
Kai Momi ta daga mata tana murmushi, iya natsuwa yanzu kan tasan Mairo ta samu saidai wayou ne ba tada tabbaci ko tayi amman da tasan ko minene dai sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba’aje ba.
”’**”’
Bayan Sallar Azahar Qasin ya shigo part ɗin Momi, sun ɗan daɗe suna fira anan ne take mashi zance sark’ar daya ba Maryam tana godiya.
Dariya yayi “Haba Momi dan naba Maryam sark’a sai kuma kimin godiya?”
“Eh mana ai idan kayima Maryam abu kamar ni kayima tunda Maryam yata ce”
“Amman dai Momi bata ce miki wani abuba ko?”
“Kamar na mi kasan ai yanzu ta rage yawan zubar nan wani abun kace tace ne?”
Kai ya girgiza “A’a”
“Wai Qasin ya maganar tarewarku ne?” Yana unk’urin tashi tayi mishi maganar hakan yasa ya koma ya zauna yana faɗin “Momi toh ai ke nake jira”
Momi tace “Jiya Abbah ka yayi maganar daya kirani a waya har nake ce mishi akwai kayan da ba’ahada ba yace zai turo kuɗi ayi komai,
K’auye ma ance tambaya kawai suke Gwaggo ku sai fama matsifa take”
“Nima dai Momi shi nagani yanzu dai babu wani abinda ake jira”
“Idan ya turo kuɗin zan siya mata duk abunda ake bukata sai asa ranar tarewar taku”
Murmushi yayi “Hakan yayi Momi Allah ya taimaka”
“Amin amman dai kasan dole ne kaje bikon Mansura ko da baka tare daga kai sai ita ba ka kyale ta can”
“Momi ai Mansura bata gari”
“Bata gari kuma?” Momi ta tambaya.
“Eh wai taje raka yayarta a indiya duba lafiya”
“Da gaske?”
“Allah kuwa nima a bakin Sadiq naji kinsan yana Auren k’anwarta kuma dana kira wayar yak’i shiga”
“Amman da izinin waye taje kai kasan da tafiyar ne?”
“A’a sai bayan ma taje ne nake ji”
Momi ta rik’e baki “Amman dai gaskiya daga ita har iyayenta basa da tunani Allah ya kyauta”
“Amin ai sai ta gane kuskurenta bari naje nayi sallah naji kiran La’asar”
Maganar yake yana kallon agogon hannun shi, Momi tace “Nima ai bari na tashi naje nayi sallar”
Tashi yayi ya fice, ya bar Momi tana mamakin hali irin na Mansura.
”’** ** ** **”’
Da murmushi Momi ta sauko downstairs tana kallon kujerar da Yarima yake zaune,
“Masha Allah Yarima har an iso?”
Ba tare daya kalleta yace “Eh miyasa kike nema na?”
Ruwa Momi ta ɗauko mishi da cup ta dire mishi sannan ta zauna a ɗayan kujerar tana faɗin “Ya gida ya kowa da kowa”
Ya daɗe yana kallon zoben hannun shi sannan ya amsa mata “Lafiya kalau”
Momi tayi gyaran murya cikin fuskar manya ta soma magana “Wata alfarma nake nema a gurinka Yarima”
Sai a lokacin ya kalleta “Allah yasa zan iya”
“Zaka iya dan bata gagareka ba kuma kana da ikon aiwatarda ita”
Shiru yayi yana murza yatsunshi, yasan Momi da wayo kuma gashi she’s look so serious akan ko minene.
Sai da ya busar da iskar bakinshi ya ɗora k’afarshi ɗaya saman ɗaya sannan ya kalleta kamar mai karantar abu a fukarta.
Ya daɗe yana kallonta sannan ya ɗauke kanshi “Ina jinki”
Momi saida ta sauke ajiyar zuciya sannan tace “Aure nake son kayi Yarima”
Nan ya sake kallonta yana ɗan murmurewa.
“Yes dole kice nayi Aure tunda kinga burin ɗanki ya cika ko banyi tunani zaki iya sakani a gaba ba kiyi min irin wannan maganar”
“Yarima shekaranjiya Hajiya ta kirani ta faɗamin kace kai ba zakiyi Aure toh akan wane dalili? Kaine kaɗai ɗan data haifa kaine farin cikin ta miyasa baka tunanin kyautata mata kayi mata abinda zai sata farin ciki”
Taɓe baki yayi “Inayi abinda nasan zan iyane kawai dan kinsan ko Allah baya kallafawa rayuwa har sai abinda rayuwar take iyawa da kanta so idan kina da wata maganar kiyi”
“Bani da wata maganar wannan ce kawai kuma a tunani na isa nace kayi kayi shiyasa na rik’e ka dan wannan matsalar ce kawai take damun mahaifiyarka da kuma duk wani masoyinka”
Tashi yayi tsaye yasa hannayenshi aljihu.
“Ko zanyi Aure ba yanzu ba so maganar Aure ta daina damunku have a wonderful day”
Yana kaiwa nan bai tsaya jiran abinda zata ce ba yasa kai ya fice.
Ko kaɗan Momi bata jindaɗi yadda yayi mata ba duk da yake tasan kaɗan ne daga halinshi babu wadda ya isa ya sashi abinda bai tashi ba.
As usually biyar dai-dai motar makarantar *KOYI DA KANKI* (gidan sisto😉) ta sauketa k’ofar gida.
Tana shigowa kayanta karatunta kawai ta aje ta nufi bathroom, wanka tayi ta shirya cikin wani farin material sannan ta nufo dining room,
Saida ta cika cikinta sannan ta tashi tana hamdala, ta dawo saman kujeara ta zauna tana shafar ciki.
Sallamar Momi ce tasa ta ɗago kai ta kalli k’ofa “Wa’alaikissalam Momi sannu da zuwa”
“Yauwa sannu kin dawo?”
“Eh tin ɗazu har naci abinci nayi wanka Momi ina kikaje?”
Upstairs Momi ta nufa tana faɗin “Gidanki wasu kaya na kai”
‘Dauke kai tayi ta cigaba da kallon tana cikama bakinta iska.
Daga can cikin ɗakin Momi ta kwalama Mairo kira,
Tashi tayi tare da amsawa “Na’am Momi”
Shiga tayi cikin ɗakin tana faɗin “Momi gani”
“Zo ga kaya nan ki buɗe”
Duk’awa tayi gaban sait ɗin akwatunan ta shiga buɗewa “Momi na waye ne tun ɗazun na gansu?”
“Naki ne shine lefen da mijinki yayi miki”
‘Dauke hannayenta tayi tayi k’asa da kanta.
Murmushi Momi tayi tace “Ranar Asabar mai zuwa za ayi walima In’sha Allah kuma za’ kaiki ɗakin mijinki kuma ki shirya gobe mai dilka zata zo ta fara gyaraki”
B’ata rai ta ɗanyi kamar bata jindaɗi ba. Ta tashi jiki a kasale ta bar ɗakin,
Shiru Momi tayi kamar mai tunani can kuma ta shiga duba kayan da kanta.
Tun daga lokacin Mairo bata sake walwalah ba, Momi kuma bata bi ta kanta ba ta cigaba da shirye-shiryenta da take mata hankalin Momi bai kwanta ba sai taga komai na gidan ya kammala.
Kullum mai dilka sai tazo tayi mata Momi ta ɗaukar mata hutu a makaranta cikim yan kwamakin Mairo ta zama wata irin mace abar sha’awa, jikinta yayi kutil-kutil sai sheki take tayi wani assirtattaccen fari,
Ranar da akayi mata dilkar k’arshe ne take tambayar Momi ko su Gwaggo zasu zo,
Momi tace “Bana tunani zasu zo dan bn fada musu ba kinga ai ko mun nan mun isa tunda akwai yan’uwan nan ko a nan bayan kin tare zan faɗa musu sai suzo so ganki kinji?”
Kai kawai ta ɗaga mata ta tashi idonta cike da hawaye ta fice.
Washe gari Jumma’a tunda safe mai kitso da lalle tazo aka hau aikin gyara ta, wunin ranar komai bata sa abakinta ba har akayi aka k’are,
Kallon ɗaya Momi tayi mata ta fahimci tana cikin wani yanayi mai wuyar fassara.
Bayan Sallar Isha’i Momi tasa Mairo gaba tana faɗa mata wasu abubuwan da ya kamata ace ta sani da kuma jan kunneta akan abubuwan da tasan tana yi masara kyau.
Kamar yadda Momi tace washe garin Jumma’a wato Assabar akayi Walima. Ba laifi anyi taro dik da ba wasu mutane sosai Momi ta gayyato ba yan’uwan da suke garine kawai sai abokaninta da kuma wasu daga cikin abokanin Mairo yan makarantar su,
Story continues below

K’arfe 9 motocin ɗaukar amarya suka zo, huɗuba sosai Momi tayi mata itako tana ta aikin kuka.
Daker aka fitar da ita daga gidan aka sata mota. Har aka zaunar da ita saman gadonta kuka take kamar ranta zai fita.
Mutane da suka kaita suka rik’a bata hak’uri har suka gaji suka kyaleta, basu fi awa ɗaya da zama ba ango ya shigo shida abokaninshi nan sukayi musu tasu huɗubar suka sannan sukayi musu sallama.
Har bakin k’ofa Qasin ya raka abokaninshi sai zolayarshi suke shi dai in banda murmushi babu abinda yake,
Yadda ya barta haka ya dawo ya sameta tana aikin kuka.
Kusa da ita ya zauna ya kai hannu a hankali ya yaye mahafin data rufa da shi. Nan ta ɗago kai ta kalleshi da jajayen idanunta dake cike da kwallah.
Hannu yakai ya taɓa gefen fuskarta “Mi kike yima kuka haka Maryam?”
Daker ta iya tsayarda kuka tayi mishi magana “Yaya wani yanayi nake jin kai wadda ban taɓa jin kaina a ciki ba”
‘Daya hannun shi yasa ya shafe mata hawaye ya kwantar da ita saman jikinshi yana buga bayanta alamar rarrashi.
Sai da ya tabbatar da kuka ta ɗan tsaya mata sannan ya ɗago kanta yace “Tashi muje muyi Sallah kinji?”
Kai ta ɗaga mishi ya rik’o hannunta bayan ya cire babbar rigarshi suka nufi bathroom.
Tare sukayi alwalar ya sake rik’o hannunta suka fito. Da kanshi ya shinfiɗa musu carpet ya buɗe akwatinti ya ɗauko mata hijab tasa sannan ya kabbarta sallar.
Raka’ah biu sukayi suka sallame saida suka yima Allah godiya sannan sukayi ma Annabi sallati bayan sun k’are ya juyo ya rik’a kanta ya karanta Addu’ar da Annabi Rahama (S. A. W) ya koyar da mu, har lokacin hawaye take.
Tashi yayi ya ɗauko Plate da cups. Ya dawo kusa da ita ya zauna ya buɗe ledar kazar dake saman drawer ya zuba a plate kofunan kuma ya cikasu da juice.
Daker ya lallaɓata taci koshi kaɗan ta hau saman gadon ta kwanta,
Bayan ya k’are ya ɗauke plate ɗin ya chanja kayan jikinshi zuwa na bachi sannan ya hau shima ya kwanta bayanta.
_Washe gari_
Tara da rabi Momi ta aiko musu da breakfast saida ya ɗora kulolin dining sannan ya shiga ya tashe ta tayi brush sannan suka nufo dining tare.
Shida kanshi ya zuba mata abinci sannan ya zuba kanshi yaja kujera ya zauna,
Suka soma kalace.
Daf da zasu gama cin abincin wayar shi tayi ringing. Hakan yasa shi tashi tsaye ya ciro wayar a aljihu yana duba mai kiran.
Ya daɗe yana kallon wayar sannan ya ɗora ta saman dining ya cigaba da cin abincin ba tare da yayi picking ba,
Mairo kamar ta mishi maganar sai kuma wata zuciyar ta hana ta tashi tayi tana goge baki.
“Har kin k’oshi?”
Kai ta ɗaga mishi tana ɗan murmushi. Ta nufi ɗaki,
Da rana Momi ta aiko wata daga cikin ‘ya’ yan k’awayinta suka kawo masu abincin rana ita kadai suka tararda sai mak’otanta dn Qasin ya fita lokacin,
Sun daɗe suna taya ta fira. Nan duk ta sake dasu ta jindaɗi.
Saida sukayi mata kwaliya suna gyara mata gidan sannan suka fice.
Da dare direba Momi ta aiko ya kawo musu tuwo da drinks haɗin gida.
Haka Momi tayi ta musu kuma kullum sai ta kirata a waya ta tambaya ko da wani abun tace mata babu,
Ranar da tacika sati ɗaya da dare Qasin ya shigo musu da kuloli. Tashi tayi ta tarbo shi ta karɓi kulolin takai dining ta aje tana faɗin “Yau kai aka aiko”
“Naje can ne shine tace na wuto dasu kuma ta bani sak’o na faɗa miki”
Nufi shi tayi tana faɗin “Minene mi tace?”
Kumatunta ya rik’a ya manna mata kiss “Bazan faɗa ba sai nayi waka munci abinci tukuna”
Dariya tayi “Toh je kayi ina jira”
Matsowa yayi kus da ita ta yadda zasu iya shak’ar numfashin junansu ciki kashe murya yace “Ni kaɗai zanyi?”
Matsawa tayi baya ta ɗan mashi fuskar shanu “Toh kai da wa zakayi?”
Kafaɗunsa ya ɗaga “Nidai baki ji nace kizo muyi ba ai ko?”
Gira ta ɗaga mishi “Good boy je kayi wankan ka”
Kanta ya shafa yana dariya “Oh i like you baby”
Dariya itama tayi ta cigaba da kallonshi har ya shige ɗaki.
***
Bayan sun gama cin abincin ya rik’o hannunta suka dawo saman kujeara suka zauna.
“Yaya dan Allah fada min minene Momi tace tun ɗazu sai jamin rai kake”
Janyota yayi ta kwanta saman kirjinshi “Kamin na faɗa miki abinda Momi tace ina son fada miki wani abun”
“Toh ina jinka”
Shiru ya ɗanyi sannan ya shiga shafata “Ban da gobe idan Allah ya kaimu Mansura zata zo ta gyara ɗakinta so bana son ki kula ta koda ta tsokaneki kinji?”
Faɗuwa gabanta yayi ta dan daɗe kamin tayi magana “Ba Momi tace min taje k’asar waje ba kota dawo ne?”
“Ta dawo ita ta aiko gurin Momi tace zata zo ta gyara ɗakinta dan ni na faɗa mata ba zan je bikonta ba tunda bani ne nace taje gida ba”
Taɓe baki tayi “Yau ni ina ruwana da ita tazo tayi duk abinda zatayi nidai faɗa min abinda Momi tace”
Sai da ya shafa kanta sannan yaja hannunta yasa a bakinshi ya ɗan cijeta,
“Cewa tayi na cije miki ɗan yatsa”
Kukan shagwaɓa tayi mishi “Allah sai na rama Momi ba zata ce ka cijeni ba”
Dariya yayi yaja mata kunne “Ke cewa tayi na faɗa miki daga gobe ki fara girki da kanki”
Kallonshi tayi “Wasa dai kake?”
“Allah ba wasa nake ba haka tace in kuma baki yarda ba na kira miki ita a waya yanzu kiji”
“Ai Momi ba zata ce haka ba gaskiya dani ruwan tea kawai na iya dafawa”
“Tace komai kika iya kiyi babu ruwana nidai na faɗa miki sak’onta”
“Toh naji Yaya dan Allah zaka kaini gurin Momi gobe?”
“Yaushe kika zo gidan da har zaki fara fita?”
“Itace tace a kawo ni ɗazun a waya baka jiba?”
“A’a k’arya kike batace koma tace bazan kaiki ba”
“Toh kai da kake fita fa?”
“Namiji ai bai gaji zama ba”
“Nidai gaskiya ka kaini ko na maka kuka”
“Tashi ki shirya na kaiki gurin Gwaggo”
Dariya tasa mishi “Wasa kake min nasa ni ai”
Hancinta yaja “Au ashe kina da wayo”
Ita kuma tayi dariya ta kwantar da kanta.
Story continues below

Da safe shi y haɗa musu breakfast sai da ya kammala komai sannan ya yaje ya tashe ta,
Tare suka wanke baki sannan ya tallabota kamar yar baby suka nufo dining. Sai da ya k’osar da ita sannan shima yaci.
K’in tashi tayi daga gurin ta marairaice mishi fuska, “Minene wai baby na?”
“Gun da ka ɗauko ni zaka mayar dani”
“Au daga na miki alfarma na ɗauko na kawoki sai kuma kice sai na maida ki”
“Eh ai bance ka ɗauko niba”
Dariya yayi yasa hannu ya lak’atar mata hanci “I love you Maryam”
Murmushi tayi ta rik’e mishi hannu “Yaya Qasin… ” sai kuma tayi shiru.
Risinawa yayi daidai kunne ya busa mata iska “Faɗi maganar Yayanki yana jinki”
Ido ta sakar mishi tana murmushi.
Can kuma ta ɗauke ido ta tashi yana rike da hannunta suka koma saman kujera.
“Faɗi maganar ki baby na”
“Momi nake son ka kira min a waya ko kuma ka kaini”
“Zan dai kira miki ita a waya amman zuwa can kan ba yanzu ba kin yarda”
“Eh kira min ita”
Wayar shi ya ciro ya danna kiran yana faɗin “yanzu kuwa yar gidan Momi”
Bata daɗe tana rawa ringing ba Momi ta ɗauka sai da ya gaisa da ita sannan ya mik’awa Mairo, tana karɓa ta tashi ta nufi ɗakinta da gudu,
Da ido ya bita har ta shige sannan yayi murmushi.
Saman gado ta zauna tana yima Momi ina kwana “Momi an tashi lafiya?”
“Lafiya kalau Maryam ya gidan?”
“Lafiya kalau ina Usman da Nura?”
“Suna nan kalau ko jiya sai da sukayi maganar ki”
“Momi kice ina gaida su”
“Toh zasu ji lafiya dai ko?”
“Lafiya kalau Momi wai jiya Yaya Qasin yake faɗa min Mansura zata dawo”
“Eh haka ne toh mi akayi?”
Shiru tayi, Momi tace “Maryam kaki saka tsoro a cikin ranki karki kuskura mayar da kanki ballagaza a gaban kishiryar yanzu fa kin tashi daga matsayin da kike na da kin koma *BABBAR MACE* kada ki shashanta kanki ki wulakanta kanki kin gadai mijinki yana sonki,
Kuma zaman Aure ya kaiki karki biye mata ki kyautata mishi dab haka ne zai k’ara mishi sonki karma ki shiga sabgarta ban kuma idan tayi miki abu karki rama ba.
yadda take mace haka kike matsayinta da naki duk ɗaya ne dan haka karki soma min wani complain indai akan Mansura ne kuma bari kiji na faɗa miki karki yarda ki nuna mata kina tsoro ta dan ba’a nunawa kishiya haka”
Ajiyar zuciya ta sauke cikin sanyi murya tace “Toh Momi zanyi”
“Wai Maryam miye anfanin makarantar da nasaki waike ba zaki waye ba kima kamar sauran mata? Yaushe zaki fara ɗaukar darasin da ake koya miki a makarantar?”
“Daman Momi ni ba wani abin zance zanji ne kawai inda gaske ne zata dawo”
“Toh yanzu ai kinji zata dawo kae naji kin mayarda kanki wata kalar mace ki rik’e k’imarki Allah ya haɗa kanku ya baku zama Lafiya”
“Amin Momi na gode a gaida gida”
“Gida zaiji ki fara girkinki yau dan bazan sake aiko muku abinci ba”
“Toh Momi”
Dariya ta dingayi har Momi ta karshe wayar.
Sannan ta tashi ta koma parlor, kusa dashi ta zauna ta mik’a mishi wayar “Gashi nan na gode”
Karɓa yayi “Toh kun gama sirrin?”
“Eh mun gama sai gobe kuma”
“Da wayar wa?”
Tashi tayi taja mishi kunne biu “Da kunnen ka” ta watsa da gudu ɗaki.
***
Jalof ta girka da rana da dare kuma tayi mishi Tuwo da miyar akusi,
Sosai Qasin ya jindaɗi ya kuma ci abincin sosai yana sa mata albarka. Da safe ma da dumamen tuwon ya karya.
Sai goma na safe ya shirya ya fita,
Saida ta gama gyara gidan ko ina gwanin shawa’awa sannan ta shiga tayi wanka ta shirya cikin koriyar atamfa. Ta nufo parlor.
Tana k’ok’arin zama taji an buga k’ofa basa zaman tayi ta nufi k’ofar tana tambayar waje ne,
“Khadeeja’tu ce mak’ociyarki”
Da far’ah ta buɗe mata “Ah Khadeeja sannu da zuwa”
“Yauwa sannu Amarya ina dai fatar angonki baya ciki?”
“Shigo baya nan ya fita”
Shigowa tayi ta zauna Mairo ta ɗauko mata drinks,
Sannan ta zauna tana tambayarta ya gida,
“Gida lafiya Amarya kin gyara gida sai k’anshi yake”
Murmushi Mairo tayi “Kai Khadeeja’tu kullum baki rasa magana a bakinki”
Dariya tayi suka cigaba ta ɗauko mat wani zancen.
Suna cikin fira Qasin ya shigo.
Da sauri Khadeeja’tu ta tashi suna haɗa ido ta sakar mishi murmushi ta gaishe shi sannan ta fice,
Mairo kuma ta nufoshi tana faɗin “Har ka dawo?”
Tsaye yayi yana kallonta fuskarshi ɗauke da murmushi “Kinyi min kyau baby na”
Ita ma murmushin tayi “Na gode dear”
“Haka kawai zaki ce?”
Murmushi ta sakeyi dan tasan mi yake nufi ta hau saman Kujera ta kamo tsawon shi ta sakar ma kumatunshi kiss.
Rumgume yayi ya ɗauketa suka nufi ɗaki, saman gado ya sauke ta ya bude drawer ya ɗauki wasu k’ananan documents sannan ya rik’o hannun ta suka nufo parlor,
Dai-dai bakin k’ofar parlor ya tsayar da ita yana shafa gefen wuyanta “Yau mi zaki dafa?”
“Mi kake so?”
“Dambu ai kin iya ko?”
Wani fari tayi mishi da ido wadda ita kanta batsan tayi ba “Sosai ma”
“Toh shi nake so”
“Zan yi maka”
Murmushi yayi zai sake magana yaji horn.
Juyawa yayi daga shi har ita suna kallon motocin da suka kunno kai gidan,
Ko ba’a faɗa ba yasan Mansura ce da muk’arrabanta. Juyowa yayi ya kalli Mairo “Baby na bari naje office na jirana but please karki kula su kinji ba zan daɗe ba yanzu zan dawo alright?”
Murmushi “Okay Allah ya tsare”
Murmushi yayi mata as respond, har ya juya sai tayi saurin kamo hannun shi ta sakar mishi kiss.
Daɗi yaji ya shima ya sakarma goshinta kiss, har ya shiga mota murmushi suke sarkarwa juna. Bayan yayi mata key ya ɗago mata hannu har ya fice bai kalli gurin da Mansura take ba.
Yana ficewa Mairo ta juya ta shige parlor,
Duk abinda suke Mansura na tsaye tana kallonsu ita da k’awayenta da kuma Sisters ɗin biu. ‘Daya daga cikin k’ awayen ta tabe baki ta kalleta “Amman Wallahi Qasin ya iya cin mutun da Auro miki wannan yarinyar a matsayen kishiya”
Nan suma sauran suka hau saka nasu baki suna zugata,
Sun daɗe tsaye a gurin suna cak-cakar ta sannan suka nufi cikin parlor.
Basu sallama hakan yasa Mairo bata bi ta kansu ta cigaba da kallonta, “Kee baki ga mutane bane hala?”
Nan ma banza tayi dasu. ‘Dayar ta kalleta tana wata dariya “Wayyo ni Allah wai wannan ce Kishiyar ki?”
Sai a lokacin Mairo ta kalleta “Eh nice ya ranki?”
Duk tintsirewa sukayi da dariya Mansura tace “Ita kin ganta kamar k’ aruwa ko?”
“Lallai kuwa k’amar karuwa baki ga har da mishi kiss ba daman dai taba inba haka ba duk yaushe akayi Aure da har zata sake jiki tana irin wannan karuwancin?”
Faɗar sister Mansura.
Tashi Mairo tayi tsaye ta ɗanja baya ta taɓe baki
“Daɗin abinda dai karuwancin mijina nayi ma kuma duk mace da kika ta zama karuwa a gaban mijinta toh ta isa ne”
Mansura ta rike baki “Lalala ke yar k’auye yaushe kika zo da har zaki tsaya faɗa min magana Wallahi in kikayi wasa saina miki shegen duka naga uban da zai rama miki”
Ba k’aramin ɓaci ran Mairo yayi ba cikin zafin rai tace “Yar k’auyen da kike rainawa tafi ki dajara a gurin mijinki da nice Wallahi bazan dawo matukar baje bikona ba dan hakan ya nuna mijina bai damu dani ba ko kuma baya sona”
Tana kaiwa nan ta juya ta nufi kofar ɗakinta, da k’arfi Mansura ta fisgota ta watsa mata mari. Jefar ita tayi saman kujeara da niyar dukanta. Da sauri wata friend ɗinta fa rik’eta “Haba dai ke kuwa daga zuwan mu zaki daketa ai wannan tsakanin ku ne daga ke sai ita kiyi mata yadda kike so ke k’aramar yarinya kamar wannan ta isa ta raina miki wayo har ta faɗa miki magana haka kawai ki bari sai kin zauna saiki gyara mata nata zaman”
Sakinta tayi tana faɗin “Ai da kin barni naci uban Shegiya”
Mairo na tashi ta nufi ɗaki ta sauri tana kuka.