MASARAUTAR JORDAN BOOK 1 COMPLETE BY RAMLAT A MANGA
*BOOK ONE*
Not editing⛳
Page….١~•Tarihin *Daular MasarautarJordan*
A yau kasar Syria ta haɗa kan bayin da tasaya daga yankuna daban daban na africa da kuma wasu yankunar Asia. Daga cikin tawagar bayin da suka haɗa maza da mata, za’a kaisu Masarautar kasar Jordan ne, inda mashawartan fadar suka bukaci haka.
K’asar Jordan tana cikin yanki Gabarta tsakiya, kuma tana makwabtaka da kasashe biyar naduniya, Palestine, Israel, Syria, Saudia,Iran…
Daular Jordan tana cikin yanki jazziratul Arab, kuma yanki ne da Annabawa suƙayi gwagwarmayya a wajejjen, a ruwayyar wasu Malaman sun tabbatar Annabi Ibrahim kafin ya wucce falastinu yabi ta yanki Jordan haka Annabi Isah, ba iyasu ba annabawa dayawa sunyi rayuwarsu tatsakanin gurin domin Annabi ya wucce yankin Jordan kafin ya isa Sham, wato Yanki syria.
Bayan haka khalifofin Annabi Muhammad sun iso da da’awa yankin, har zuwa karni na uku bayan wafatin manzon Allah. Akwai kabilu guda uku dasuka kafa daular Masarautar Jordan.
Hashmiyya daga kabilar Banu Hashim, sai Husseiniyya daga cikin Banu Husein, sai Urdawa. Wanda suka haɗa kansu domin kafa kasar Jordan, tafiya tayi nisa sosai gashi kasar tana cikin kasashe masu ababen tarihi, musan red ocean. Matsalar da ta ɓullo daga cikin daular itace yadda kabilar Banu Hussein suke gallazawa yan kabilar Urd, musaman wanda suƙa kasance ba Musulmai ba, cutar dasu da Banu Hussein take yi bakaramin tunzura su yaƙe ba, karshe suka shiga suka fita tsakaninsu da Isra’ila suka kwace yanki, suka cigaba da gallazawa musulman yankin. Wanda ya janyo akayita fafatawa tsakanin Yahudawa da Larabawan yankin.
Ashekaran 1968 a wata mayu majalisar ɗinkin duniya tare da goyan bayan saudia cire kasar jordan daga yanki isra’ila, inda suka bawa kabilu guda uku na kasar shawaran su dai daita kansu, su bawa kansu damar mulkinsu.
Daga cikin kabilun guda uku, nan aka shiga muhawara me zafi, har yaja hankalin talakawar gari, suka ce abawa Kabilar Banu Hashim wato Hashmiyya. Sai dai tsakanin kabilu guda biyu basu so bawa Banu hashim sarauta ba, sabida su tsarinsu akan addinin musuluncine yayi yawa, kabilune da suke da nasaba da zuri’a Banu K’urash. Dan daga cikin macca suka zo inda suka same kabilar Banu Urd.
Lokacin da akazo zaɓar wanda za’a bawa sarki, a cikin zuri’a Banu hashim, sai aka samu cikin kabilar an sami rarrabuwar kai. A cikin banu Hashim sun kasu gida uku, gida Na farko sun kasance *YASIR ABDULLAH ALHASHMIYYA* shida Zuri’ashi ke jagorantar gidansu. Sai Gidan *ZAID BNI ABU ZARRI ALHASHMIYYA* shi yake jagorancin Zuri’arsu, HISHAM BNI UKSHE ALHASHMIYYA, shi yake jagorantar zuri’arshi, kuma dukkan zuri’ar ALHASHMIYYA, yan uwan juna ne, dan duk Y’aya’an baffanaine, Domin kakansu MUHAMMAD ASHRAF ALHASHMIYYA shi ya haifi iyayensu Maza, ABDULLAH shine Babba, ABU ZARRI ke binshi, sai UKSHE, shine karaminsu, da aka fara Maganar Yasir ya zame kanshi yace baya bukatar mulki, na familynsu ma da aka bashi ya ishe shi, sai ya zama tsakanin Abu Zarri da Ukshe ake takarda, karshe aka ajiye kuri’a, duk wanda yasame kuri’a mafi rinjaye shine zai zama sarki, a tsakaninsu biyu, kafin ranar Zaɓin.
Kafin Ranar zaɓe Ukshe da Abu Zarri sun fantsama bin bokaye dan daisu mallaki mulkin abu guda daya gigitasu dangane da mulkin, ba kome bane face ce musu da akayi dukkansu babu wanda zai mulki kasar amma a cikin kabilarsu za’a samu amma basu ba dan ko zuri’arsu babu wanda zaiyi mulkin. Haka ba karamin haushi ya suka ji ba, akan basune zasu ɗare mulkin garin ba. Dan haka suka zuba ido suga waye zai ɗare mulkin,
Ranar da za’ayi zaɓen Yaseer bni Abdullah ya tafi gun a matsayin me zaɓen Abu zarri sai ga abin mamaki dan gabaki ɗaya Emirate council shi suka zab’a.
Abin bakaramin girgiza Ukshe yayi ba, jinjina abin yayi a ranshi bayan an taya Yaseer Murna, dan suka rungume juna tare da farin ciki koda Ukshe yazo ya rungume Yaseer ya kai bakinshi kunnen Yaseer cikin jin zafi yace mishi.
“Wannan ba farin ciki ya dace kayi ba, kuka ya kamata kayi dan na rantse da karfin ikona sai kabar kujeran da karfin tsiya dama munafurtanmu kayi kace kai baka so nan kuwa kasan ranka ashe kanaso zaka sha Mamakina.”
Yana gama faɗar haka ya janye jikinshi, tare da sakar Yaseer.
Da idanu Yaseer ya raka Ukshe shi a duniyarshi ya tsani fitina, shi yasa har yau baida abokin faɗa. Sai ya shiga damuwa ak haka zuri’asu sukayita murna.
Bayan kwanaki da naɗashi sarkin Jordan na farko, abinda ya fara shine tabbatar da adalci akan kowani kabila, sannan da kuma karɓan haraji, daga attajirai da kuma yan kasuwa cikin tsarin da addin9 ya shar’anta.
Sai bautar da mutane bisa dole, da kuma shagali babu gaira babu dalili wani abun da mutane basu sani ba, Larabawa shagalalulun mutane ne, gashi a cikinsu alkur’ani ya sauka amma dan son more rayuwa sunkan buga tsiyarsu.
Sarki Yasir yana da mata daya da yara uku, Abdullah da Badi’at sai Raziya..
~_~
Zaune yake gaban Bokansa wanda yake gabashin Pakistan dab iyakar india ta kashmir,, cikin d’agawa da Izza yace.
“Ra’eez zan mallaka maka darhami milliyoyi mulkin Jordan kawai nake buƙata kota halin ƙaƙane kuwa.”
Wani irin ruwa boka Ra’eez yake watsawa a cikin wutar dake ci a gabanshi, tashi wutar tayi sama. Ta mutu baki ɗaya, kunna wutar yayi ta sake tashi sama, sannan ya juya ga Ukshe, yana girgiza mishi kai. Yace,
“Mulkin kasar Jordan banaka bane, ba kuma zakuyi shi ba. Sai dai naga zaka zama Uba ga Fadar zaka juya fadar amma bazaka taɓa xama haka ba, kuma ba zaka taɓa nasara akan Yasir ba, lokaci na zuwa da zaka mulke kasar kuskurenka shine barin kasar, da kayi kazo nan zaka ga abinda Yasir ya aikata ga masarautar baki ɗaya.”
Tashi yaƴi ya leƙa cikin wutar malamai ya hango ƙewaye a cikin fadar anata saukar alkur’ani. Ihu ya kwala yana zaro idanu,
“Meye mafita? Ya zanyi Ra’eez?”
A lokaci guda ya jefawa bokanshi ka koma masarautar kome zakayi ka tabbatar kayi amma mulkin ya haramtawa Kowani mugu da azzalumi, babu wanda ya isa hawa kujeran sai adali, karku nemi tsige shi da karfi domin masarautar zata fuskanci abubuwa.”
Haka ya tashi yabar kasar pakistan wato.
.~_~
Sannu tsarin mulkin Sarki Yasir ya gunduri munafuƙai da wasu daga cikin kabilunsa da kuma kabilun, Yahudawa da Urdawa.
Take aka cimma matsaya inda suka zarta da hukunci lokacin Ukshe ya bar kasar zuwa China niman yadda zai amshi mulki babu, tashin hankalin.
Ranar da yadawo ko gidanshi bai shiga ba, yasamu labarin kifarda Sarki Yasir, abinda yaja sanadin mutuwarsa, wanda ba’a fahimci taya ya mutu ba.
Abin mamaki ana sallar gawarsa, aka fara samun matsalar. Ambaliyar ruwa wanda yayi sanadin rayuka da dama. Ba’a dawo daga jimamin mutuwar ba da ambaliyar sai ga rikici ya kaure tsakanin urdawa da Yahudawa, ana cikin haka Zuri’a Yasir suka fara nasu da Zuri”ar Abu Zarri.
Take abinda boka ya gayawa Ukshe, ya dawo masa . Dan karshe shine aka samu da maganar, kallon kujeran fadar yaƴi firgita, abinda yafito daga bakinshi ya girgiza kowa a fadar mikewa yayi yace.
” Yaku Banu Hashim! Ni Ukshe na naɗa Abdullah Bni Yaseer bni Alhashmiyya, a matsayin sarki ki akwai me jane, Kabilarmune shi jininmune shi Kuma bakuraishe ne danmu kuma shine yafi dacewa da mulkin kasar Jordan.”
Dake larabawa nada kishin kabilarsu ba tare da wani ja ba, suka amince dan matukar suka ki amincewa, tabbas tsakanin Banu Nazir Ko Banu Hussein sune za ace subasu mulki, su kuma basaji zasu bawa maguzawa ko yahudawa mulki..
~_~
Bayan shekara ashirin da Hudu abubuwa sun faru. Wanda babu wadda yasan meye silarsu sai dai ancigaba da shimfiɗa mulkin zalinci da cutar da talakawa, ana ɓarnatar da dukiyar kasa, ba tare da sanin Mahakunta ba.
*Syria Damascus 2017*
Janye yake da wata budurwa bakar fata, har inda ake saida mutane fincikota yayi ya wurgata yana faɗin.
“Darhami dubu ɗari.”
Kallonshi kazab yayi tare da fashewa da dariya yace.
“Kai Malam muna sayansu a darhami dubi biyar kai har dubu ɗari.”
Wani kallon Banza yayiwa Kazab sannan yagyara tsayuwa yace.
“Baiwata da kake ganinta, tana da kwarewa a abubuwa irinsu girkinmu na larabawa, tana da kwarewa a gyaran ɗaki kai har dakunar dabobi zata gyarashi tsaf.”
Wani irin kallo suka mishi ya ɓata rai, dan asalin kallon tuhuma suka mishi, take ya dai daita nutsuwarshi. Tare da ɓata rai, tasowa ɗaya daga cikin asakar yaƴi yazo gabansu ya kallesu, kallonta yayi yadda take zaune akasa take mata kafa yayi ta fasa kara, tsaki yayi yana faɗin.
“Da tana da juriya da mun ɗauketa, ka maida ita ƙawai bazamu sayeta ba.”
“Toh nace kasaye tane? Gashi zaka nakasata kalan wani yazo yaganta a nakashe yace bazai sayeta ba, Ba lallai bane ka sami nasara akan burinka ba ama cimma burinka ta kowacce dama shima tankar shafe wasu tarihine, Tashi kinji ai maganin Yan mata irinku kenan, kin baro gatanki dan soyayya kinzo min daga haɗuwar face book, kinga rayuwa nama fasa sayar dake muje na cillaki a ruwa kimutu ma nima na huta.”
Janta ya shigayi ya nufi hanyar da zai maida shi cikin gari, musaman wanda zai kaishi gabbar ruwa.
Ganin dagaske mugun matashin nan yake yasa Kazab yace.
“Mun sayeta Darhami 80! Daga kanshi ba kari,”
Yatsina fuska yayi tare da tureta ta faɗi kasa, yace.
“Jeki suma su san yadda zasuyi sake ni sai Allah ya rabani ds k’aya.”
Kuɗinshi suka watsa masa sannan suka ja igiyar da ya ɗaureta da shi suka jata cikin wani mota kiran bus suka jefata ciki, tare da rufe motar.
Komawa gefe da jikin motar suka ɗanyi kus-kus, sannan suka dawo tare da tadda motar su uku a gaba, dan maza ne su.
Tafiya suka fara idan suka ji harbi sai su tsaya dakyar dai suka fita a yanki mafiya a hatsiri a cikin garin damascus yayinda suka dinga samun madakatai sabida, dubi da yanayin da kasar syria ke ciki, yasa suka samu tsaiko kafin ha na tsawon awowin arba’in da takwas, kafin suka fita zuwa bakin boda.
Koda suka isa bodan nan wani iftila’i ya afka musu, dan ina isa gun bom na tashi sakamakon harin da Kungiyar sakai ya Isis, wanda yaja rasa rayuƙar dinbun mutane dan dole aka buɗe bodar wasu suka fita daga ciki kuwa har da motar da Baiwar nan takeciki.
Abinda yasa aka bar motar sabida alamar tambarin Masarautar jordan da take dashi. Shi yasa suka wucce ba tare da wata matsala ba, a cikin motar kuwa zaune suke su kusan goma sha biyar har da kartin maza, a cikinsu kallonsu tayi tare da kauda kai, haka suka cigaba da tafiya duk da sunyi kwana biyu a cikin garin damascus amma basu samun yancin leka waje ba, sakamakon yanayin garin, tana kallon wata mata da kanta ke jikin wani mutum watar wacce take ɗauke da juna biyu sai juya kai take, alamun tana cikin wani yanayi. Kallon mijin matar tayi tace.
“Matarka bata da lafiya ne?”
Gyaɗa mata kai yayi, cikin damuwa yace.
“Eh!”
Ganin yadda matar take gumi lokaci ɗaya ta fahimci haihuwa ce, dukda bata tabbatar ba. Kallon matan cikin motar tayi tace.
“Ku baje mayafanku,”
Da sauri suka buɗe tare da bazawa, dake cikin motar kaman cikin j5 ne dan haka matan suƙa mike ita kuma ta gyara matar, wacce take nishi tare da kiran sunan Allah. Cikin ikon Allah sai ga jariri ya fasa kuka, ajiyar zuciya matar ta sauke, sannan ta koma ta lumshe idanunta alamun gajiya, dake Allah ya takaita mata wahala har da mabiyar wato Mahaifa suka faɗo da yaron, gyara matar tayi sannan ta duba jakarta yar karama irin ta gefen nan wadda ake ce masa side bag jakar gefe, ta ciro sabon audugar mata da kuma sabon pant tasawa matar, audugar matan sannan ita kuma tasa wndo. Sauke mayaffan sukayi lokacin wata matashiya ta naɗe babyn, tana murmushi tace.
“Yar uwa! Ke nurse ce?”
Kallon yarinyar tayi ta girgiza kai sannan tace.
“Kakata ce unguwar zoma a kauyenmu na taso tana karɓan haihuwa.”
Taka birki akayi suƙaƴo gaba motar kamar……..
Vote MJ# Follow Mai_Dambu…….
_Wallahi Vote ɗinku idan bai kai 300 ba Zan sayar da Book ɗina ba karya….Wannan shine Page ١_
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: *_HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
🏰🏰🏰
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
🏰🏰🏰
_Jordan Historical_
*®2020*
*BOOK ONE*
Not Editing❌
Page-٢
Salati suka saka baki ɗayansu, ba kome ihun mutane tare da dukan motar ana harbi asama yasasu curewa guri guda, tare raba idanunsu ganin ana ƙoƙarin buɗe, tsuru tsuru suka yi. Hankalin kowa a tashe, jin ba’a buɗe ba yasa dukkansu suka sauke ajiyar zuciya lokaci guda kuma a tare, sai kallon juna suƙe can aka tadda motar suka bar gun. Abinda ya bata mamaki a tafiyarsu ba kome bane sai yadda mutanen da suka sayesu basu damu dasu ba, dan suna jin kukan Jariri baisa sun tsaya ganin meye ya faru ba, tunda sun saye su babu ruwansu dasu.
A haka suka cigaba da tafiya basu kuma haɗuwa da kome ba, har suka isa garin jordan, inda aka tsaya a kofar shiga kasar aka fiddasu musaman da karnin jini ya ɗagawa kowa hankali, harsuma mutane, wani gida aka kaisu inda zasu zauna kafin zuwa gobe a shigar dasu cikin garin Amman capital city ɗin Jordan kenan.
Suna shiga gidan suka tadda mata a tsatsaye ga maza ma haka, suma sunata aiki ana tsulla musu bulala.
Kallon juna suka yi sannan aka nuna musu inda zasu zauna ɗaki ne babba sai ban ɗaki guda ɗaya,inda mata zasu zauna kenan sai kuma mazan suma haka.
Suna shiga dakin basu tsaya kome ba, ruwa suka tara me shegen sanyi suka wanke yaron dashi tare da uwarsa. Da sabulun baiwar nan, da take wanke yaron saida kwalla ya zubo mata, sabida kewar nata dangin gashi tarabu dasu.
Sai da tawanƙe shi tass sannan ta naɗe shi a gyaren uwarshi itama tashiga wanka.
Kallon yan matan suke gata bakar fata amma she have pure heart. D’aya daga cikinsu mika mata hannu tace.
“Zahrah sunana! Kefa?”
Murmushi tayi wanda zai nuna maka cewa dabi’arta ce murmushin ta mika mata hannu tana cewa.
“Nafisat! Amma Feener ake kirana?”
Yarinyar da ta ɗauki yaron lokacin da aka haifeshi tace mata.
“Ni kuma Zakiya” wata acan gefe tace mata.
“Mujahida” ta kusada Mujahida tace.
“Hinduh” haka sukayita gabatar da kansu, sannan me jegon tafito tana murmushi tace musu.
“Ni kuma Salmah, daga Afganistan”
Gyara zama Feener tayi tace..
“Ni kuma daga Senegal”
Zakiya tace” Oman daga can nake”
“Algeria daga can nake”
Hindu tace.
“Daga libya na fito” haka suka gabatar da kansu, cikin jimami Salma tace.
“Gashi zamu tafi masarautar Jordan, me cike da mugun hatsari dan matukar kayi kuskure toh sunanka gawa, don Allah kamar yadda muka hadu a nan karku bari arabamu ta hanyar rasa ɗayanmu, musaman ke Feener kece bakar fata, kuma zaki iya fuskarta k’alubale sabida nuna wariyar launim fatar da zasu nuna miki.”
Tsorone ya bayyana akan fuskarta, tabuɗe bakinta zatayi magana aka shigo musu wani bushashiyar gurasa tare da wani wani irin miya, haka suka zauna zasu ci dan tunda suƙa baro syria bushashen gurasa ake wurgo musu, haka zasu ɗauka ci ruwa kuwa a wani gora ake wurgo musu, dan haka suna ganin wannan suka rufa musu dan rabawa dai dai akayi, ta ɗauki nata ta bawa. Salma tace.
“Kece kike bukatar abinci, ni ban damu da abinci ba tun tasowata, bana cika damuwa da ciye ciye.”
Girgixa mata kai Salmah tayi cikin damuwa tace.
“Don Allah kici ni wannan ya ishe ni.”
“Karki damu, ni ba damuwata bace abinci nasaba da rashin cin abinci haka halitta ta take, kici kawai.”
Data ga zasu dameta mikewa tayi ta shiga ban ɗaki tayo alola, sannan ta shigo ta fara sallah, sai da ta sauke bashin kanta sannan ta sallaci na ranar da tarasa shi.
Haka ma duk sauran sukayi, kafin suka shimfiɗa hakarkarinsu a kasa suka kwanta.
~_~
Karfe uku na dare aka tashisu badan kome ba sai dan su fara ganin yadda bayi suke cin mugun wahala, har akayi sallah asuba, suma suƙayi sannan aka sake shigo musu da wata farar shigafa da madara a cikinsa, aka turo musu dake kamar kunu ne shi kan Feener tasha, tana lumshe idanunta. Amma ba sosai ba tabawa Salmah sauran sabida cikin jego. Suna cikin karyawa aka kawo wasu yan matan aka haɗa dasu, karfe takwas suka aka fito dasu, yan matan da akakawo biyu shekarunsu zai kai nasu zakiya, d’aya kuma zasu yi sa’anin da Salma sai wata yar karama wacce Feener na rike hannunta, har suka shiga motar. Babbar cikinsune ta kwace hannun yarinyar daga Feener tace.
“Baki ganinta baka ce zata goga miki bakinta kema ki zama munmuna irinta.”
Kallon Feener yarinyar tayi, cikin danuwa tace.
“Kaltu!!! Wai haka ne zaki goga min bakinki?”
Murmushi Feener tayi tare da girgiza mata kai tace.
“Bazan goga miki baki ba, amma tunda yayarki bata son muzauna tare zaki iya zama gunta kat tayi kartayi fushi dake.”
Haushine ya kamasu Hindu suka ja tsaki tare da cewa.
“Mukan bamu da wannan duhun kan domin itaƙanta alkur’ani da bakar tawada aka rubutata, sannan Babban Ladanin musulunci Bilal , bakin fata daga Ethopia dan haka mu bama cikin larabawan da suke kyamar launin fata.”
Riketa Feener ta ɓata rai dan duk cikinsu har Salmah, Feener ta girmata sosai balle kuma ita kanta yayar Yarinyar
A haka suka shiga motar, suna taɓa hira sama sama, har suka shiga garin Amman. Kafin suka nufi hanyar masarautar, tun kafin su isa masarautar suke kallon garin sannan aka mike hanyar masarautar, anan suka kara tabbatar da kansu sun iso wata nahiya ta daban.
Tafiya ce me nisa wanda ya ɗaukesu mintina arba’in sannan suka isa cikin masarautar wanda idan ka ganshi zaka ɗauka ginin akayi, a wani guri sannan aka ɗauka aka ajiyeshi da gindinsa.
Tsarin masarautar kawai abin burgewa ce, sabida ginshikan da aka gina masarautar, saman ginin inda aka ɗaura wani abu kamar tubali me zubin ruwan gwal, sai kyali yake anyi wani tsarin gini kamar masalaci, dukda masalacin yana bakin kofar masarautar. Wato faɗar yawan tsarin masarautar ɓata lokacine.(Zauren mai dambu sunga hoton masarautar.😹)
Suna shiga masarautan a tsakiyar fada aka tsayar da motar, mutane ne a cike a gun. Daidai an fito dasu, aka fito dasu ganin an janyo wata mata tana kuka tare da cewa.
“Wallahi bani na aikata ba, taya zan kashe sarki Ashraf adalin sarki don Allah ku min rai bani bace, sharri aka min wani katon badakare. Wanda kana ganinshi kaga (Kamal minna😹) tare da wani kato kamar (Jaheedu) suƙa ɗaure hannun matar sannan suka saka kanta akan wani katato, tana kuka tana kome, tace.
“Ya Allah ka kawowa Masarautar nan agaji da ceto, Ya Allah ka kawo wanda zai dakatar da abinda ke faruwa a cikin wannan masarautar.”
Saka takobi sukayi aka gintse kan matar, ya faɗi kasa ihu Mujahida tasaka tare da yankan jiki ta faɗi, a gun. Lumshe idanu Feener tayi dan tabbas wannan masarautar ba kanwan lasa bace, babu sauki a cikinta balle wajenta. Yunkurin kashe sarki kawai an gintsi kan ɗan adam ina kuma kayi wani abun da bai kai haka ba toh tabbas sai dai a cinye namarka ɗanye.
“Kowa ya kwan dasanin cewa, duk wanda yayi yunkurin kashe Sarkinmu, shine zai fara shekawa Lahira dan haka ƙuma bakin Bayi kushiga hankalinku dan ƙuna kuskure zaka buɗe idanunka a lahira ne, na rantse da Allah sarki takobina a washe yake domin cusge kayikan mutane.”
Korasu akayi kamar wasu dabobbi, inda aka nufi wani shashi daban daga masarautar aka kaisu, sunga bayi a cure guri guda suna ƙuka, wani yaro da aka barshi yana birgima yana kiran .
“Ammiih!!!”
Yabawa kowa tausayi dan ga duk alamu ya nuna cewa Uwarsa ce aka tsinke kanta, yadda yaron yake kuka saida yasasu duƙkansu kuka, a hankali Feener taje gunsa ta ɗagashi tare da rungume shi itama kwalla na zuba idanunta, tace.
“Ya isa ukty! Amminka tana cikin aljanna, kuma zata ji daɗi idan kayi mata addu’a.”
D’ago kanshi yayi gana sauke ajiyar zuciya, ya kwantar da kanshi a kirjinta yana ce mata.
“Ammina zata dawo?”
Sake rungume yaron taƴo a wannan karon takasa tsayar da kukanta, domin tsakaninta da Allah take shasheka, wannan wacce irin masarautarta ce haka da dan adam da ruhinsa basu da kima, a yau da tashigo kawai tabbatar da wani alkarya tashigo, a yau tasan duniyar da tashigo, me cike da tsantsar zalinci da mugunta.
Shigowan wasu karfaffan mata yasata ɗago kanta, kallonta suka tare da taɓe baki cikin izgilanci.
“Ke bakar mutum! Daga wata duniya kike?”
D’ago jajjayen idanunta tayi sannan tace.
“Daga Senegal!”
“Yayi kyau, toh ku gabatar mana da kanku dan ace a cikiku akwai wacce take da kwarewa a girki hatta girkin dabobbi ta iya, dan sarkinmu bayi dame girki.”
Mikewa tayi tana kallonsu tace.
“Nice!”
Dariya suka saka mata, sannan suka ce.
“A haka sarkinmu zaici a bincikin? Mutumin da baici na gogaggun turawa ba, amma muje a baki kayanki, mu kuma gabatar dake ga Gajin iko, kafin akai ki shashin da zaki zauna.”
Wani shashi na gidan suka nufa dani, wanda yake da tsari na daban da masarautar. Ginin kawai abin kallone a haka nayita binsu har cikin, wani tangamemmiyar falo muka shiga me cike da kayan more rayuwa, ta sarakuna. Katon hoton wani farin dattiji cikin shigar alfarma. Fuskarshi cike da farin gashi.
Ko cikin falon bamu shiga ba, muka tsaya wata baiwa ce ta fito sakamakon jin sallamar Naja’atu.
Murmushi tayi tace.
“Ina gaida uwar ɗakin bayin Jordan meke tafe dake?”
Gyara tsayuwa Matar tayi, sannan ta nuna mata Feener tace..
“Gata nan mun kawota Gajin iko ya gantane wannan karon har da bakaken wake a cikin masarautar.”
Zuɓa mata ido baiwar tayi kafin ta gyaɗa kanta tashige cikin wani falon, can sai gata tafito tace.
“Ku jira yanzun zai fito.”
“Toh madalla.”
Wasa-wasa sai da suka shafe awa ɗaya a gun kafin dattijon yafito rike da sandar dogarawarsa ta Azurfa kana ganinta sai wani irin shaiki take, zama yayk duk suka zuɓe tare da kai mishi gaisuwa. Jinjina kanshi yayi idanunshi kan Feener wacce kanta yake sunkuye bazato yace.
“Shekarunki nawa? Sunanki? Daga wani yankin duniya kike?”
D’ago kanta tayi taga yayi mata wani irin kwarjini da cika ido, sunkuyar da kanta tayi jikinta na karkarwa, bakinta na rawa har tana tauna harshenta tace.
“Safeenat Hadi! Daga senegal”
Bai kuma ce mata kome ba, ya maida hankalinshi kan agogon falon, sannan ya kalle Naja’atu yace.
“Ku kaita.”
Mikewa sukayi tare da ita suka fita a falon.
Shiru yayi zuciyarshi nakin amincewa da baiwar Sarkinsu, amma bai da hujja hanata.
Can gun bayi aka maida ita, tare da nuna mata ɗaki. Zuwa anjima za’a zo akaita, tare da jera mata dokokin zama a cikin gun girkin.
~_~
Bayan awa gudu sai gasu Naja’atu, kiransu Hindu akayi suka tafi wani bangare na gidan, aka sasu sukayi wanka, sannan aka basu wani riga iyakarshi ya rufe kirji,amma cibiyarsu a buɗe, yana sa guntun hannu, amma tawajen cikin kuwa wasu silala aka saka masu wani irin kara, sai wani wando me tsagu har cinyar gefe da gefe, ga wani jigidar karfen, sai wani awarwaro da aka basu suka saka. A kafarsu wanda yake bada wani kara cuuu.
Sai wani hula shima me karafun, wanda kana juya kai zai bada sautin.
Sakasu akayi a gaba, aka kaisu wani falo na daban gun cike yake da manyan mutane. Suna shiga gun aka sauke sauti dake akwai makaɗa, take aka umarce dasu fara rawa. Irinta larabawan zamanin Jahiliyya. Dake dukkaansu larabawane. Kuma sunsan kan rawan, ita rawan dai anayinta da k’ugune sannan anayi ana juya kowani kusurwa najikin……
VoteMj#Follow Mai_Dambu….
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: *_HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*®2020*
*BOOK ONE*
Page-٣
Wannan dabi’ar da ake a cikin masarautar iya emirater council ne suƙe wannan ɗabi’ar. Banda sarkin dan sam bai ciƙa shiga sabgar ba, kodan kasancewarsa shi ɗin matashine ko da yake baza ace haka ba, dan idan akayi dubi da yanayinsa ba mazaune bane a masarautar, kaisu wani ɗaki akayi nan wata baiwa ta nuna musu yadda zasuyi rawan sannan suka fita zuwa wannan falon.
Inda suka same su da manyan cikin fadar, nan aka sake musu sauti suka shiga rawan yayinda makaɗa suka shiga sake musu sauti, gefe guda manyan fadar suna watsa musu salala, tare da ruwan taccecen inabi…
Duk wannan abinda ke faruwa Sultan Ashraf bai san da haka ba, shigowar Amir Ukshe ne ya tsayar da kiɗan da rawan. Zama yayi a cikin tattausar shinfiɗinsa, yana karewa kowa kallo kafin yakishingiɗa aka cigaba da shagali.
***
Wani kitchen aka kaini mai girman gaske, kome na cikin kitchen ɗin royal colour ne, wato komi na na cikin kitchen ɗin ruwan golden ne hatta cokala da kofuna duk iri ɗaya ne. Bangaje ni da akayi ne ya dawo dani daga duniyar kauyanci, tsaki matar tayi cikin izgilanci tace.
“Matsalar akawo maka bayi daga africa kenan, gashi tazo ta buɗe baki tana kallo kamar wata doluwa, zaki wucce ko sai nasa guard sun zanemana ke”
Gaba nayi ina raba idanuna, bansan me zanyi musu ba dan haka na tsaya a gun ina kallon yadda suke haɗa girki kai kace taro ake. Kafin na ankara sai ji nayi an zabga min bulala a jikina, a razane na ɗago wani murɗeɗɗen mutum ne sanye da farin riga da bakin wando anyi masa tambarin masarautar a gefen kirjinshi ta dama, dariya duk masu girkin suka saka, nuna min aikin wata dattijuwa yayi, an ajiye min, kasancewa an faɗa musu na iya girkin larabawa su gwadani sannan akaini ɓangaren da zan zauna.
A sanyayye na karasa gun na tsaya buɗe panpo nayi na wanke hannuna, sannan na kalle abinda zanyi. Man zaitun da y’ay’anshi, zuma, da tafarnuwa sai kayan kamshi dangin curry masala, da kuma kaza katuwa, sai dankalin turawa da kayan miya tattasai ja da kore tumatir manya guda huɗu, sai wani maggi wanda yake da faɗi sai albasa, dafa kafaɗata tsuhuwar tayi sannan tace min.
“B’akuwa wannan shine irin abincin da Sultan Ashraf yafi so, da fata..”
“Kee! Tsuhuwa koma bakin aikinki ko kuma jikinki ya nusardake inda kike.” inji mutumin da ya zane ni, da sauri matar koma bakin aikinta.
Shiru kitchen ɗin ya ɗauka baka jin kome sai karan ajiye filet ko wani abu ko kuma cokali. Cikin sauri na fara aikina, ana wanke kazar ajiyeta a matsami ruwan ya gama ɗigewa, sai a koma kan irish ɗin shima a yanyankashi ba yankan chips ba. Yankar albasa akwance, za’ayishi sai a ajiye a cikin wani bowl akoma kan kayan miyar shima yanyankasu ke, a zuba akan dankalin, sai a zuba man zaitun da zuma a cikin kayan miyar tare da maggin da y’a’yan zaitun nan a cakuɗasu guri guda, sai a ɗauko kazar a zuba a cikinta, idan dama an raba kazar ta kirjine sai a saka zare da allura a ɗinketa, idan kuma ta kasa aka buɗeta sai a juye takasar, amma larabawa sunfi buɗeta ta kasa.
Sai a ɗinketa sannan a sake niman bowl azuba man zaitun, da maggi a haɗa ashafa a jikin kazar sai a saka an pan ɗin oven a saka a cikin.
Duk bayan mintuna goma zai ayita buɗewa ana zuka wuka a ciki, yadda za aji dahuwarsu.
…….. Bayan mintuna talatin da biyar aka ciro, matar da take da alhaki kula damu, itace zata fara dubawa. Tana gama dubawa ta kalleni tura min tayi gabana, cikin tsukewar fuska tace.
“Kici.”
Cikin sanyin jiki na yanki namar na kai bakina naci, suna ganin naci suma suƙa rufawa namar, tass suka cinye.
…… Daga nan suka sani dafa normal tea. Irin nasu na larabawa wasu ganyenma bansan su ba sai yau, ina gama suka sake bani aiki. Kai nasha azaba dan kafata har rawa yake. Dakƴar suƙa sallame ni daga kitchen ɗin.
***
Ina shigowa ɗakinmu nasami Yan matan nan, suna kuka cikin sauri na karasa gunsu na zauna a tsakiyarsu. Daura kansu suƙayi a jikina tare da fashewa da kuka, suna cewa.
“Feener! An wulakantamu anci zarafinmu, bayan munyi musu rawa sai da suka nemi yin lalata damu. Feener har da Sarkin ma.”
Zaro idanu nayi waje, Zakiya tace.
“Feener Mujahida an mata fyaɗe tana bay..”
Turesu nayi na shiga ban ɗakin na sameta tsugune rungume da jikinta tana wani irin kuka, durkusawa nayi na rungumeta. Cikin kuka tace.
“Feener! Narasa darajata, dama haka bayi suke fuskanta? Na rasa iyaƴena a yakin syria ban taɓa kuka irin nayau ba gashi akan idona sarkin wannan masarautar yake tamin haddi bayan sun wulakantamu. Feener zan gudu.”
Girgiza mata kai nayi cikin kuka nace.
“Kiyi hakuri”
Narasa me zan gaya mata, dakyar nasata tayi wanka, sannan tafito a hankali abincinmu aka kawo mana, a wulakance aka ajiye mana, nice na cigaba da lallashinsu har suka taɓa abincin zan fara ci kenan aka buga kofar mikewa nayi na buɗe.
“Kizo mu kaiki shashin Sultan Ashraf yau zaki fara aikinki.”
Fitowa nayi na bi bayan mutumin. Fita mukayi daga shashin bayi sannan muka nufi cikin wani shashi wanda yafi kowani shashi kyau da haɗuwa,
Tazarar tafiyar da yake tsakanin get ɗin gidan da cikin tafiyace ta minti arba’in da biyar, amma cikin sauri muka isa gidan, bansan yadda zan kwatanta muku yanayin gidan, domin baka jin motsin kome a gidan sai takuna, kasancewa takalmina flat ne toh kuma yana bada sautin, tun da muka haura barandan. Masu tsaron gidan suke bina da kallo sabida sautin takalmina, falon farko da muka shiga, aka dakatar damu, wani bulalar me kama da itace aka zabga min a kafana, sai da nasake kara.
“Shiiiii!” shine abinda me tsaron kofar falon, ganin haka mutumin da ya kawo ni yasake murmushi can kasa makoshinsa ƴace.
“Ghaniyu muna godiya da tarɓan da tasamu,”
D’aga mishi hannu mutumin yayi, muka wucce, kwalla ne ya shiga saukowa a idanuna, tare da tarin dana sanin mara amfanin da nakeyi tun bamu isa cikin ba. Falon farko babba ne na fitar hankali, ga kaƴan alfarma a cikinsu. Sannan muka ratsa falon dan mun samu da mutane suna zaune babu wani hayaniya ko magana asalima zaman hutawa suke.
Haka muka wucce su babu wanda ya dago ya kallemu, balle kasa ran zasu mana magana, wani dogon korido mai tsayi shima tafiyar minti goma zakayi ya kaika kofar falo na biyu.
Muna zuwa aka buɗe mana kofa, muka shiga ciki mun sami mutane biyu a zaune kowannensu da abinda yake yi, sannan muka wucce, inda mukayi tafiyar minti ashirin da ɗaya, sannan muka nufi wani tafkeken falon me cike da abubuwan burgewa, irinta gidan sarauta. Babu kowa a falon sai tv da yake aiki. Tsayawa yayi a gun sannan ya kalle ni tare da mika min, takarda yace.
“Idan Allah ya nufa zamu sake saduwa toh sunana Sheik, zaki iya tsayuwan jira har lokacin da ya fito sai kisan yadda zaki bashi takardan domin yasan da cewa kece bakuwar da zaki fara girka mishi abinci sannan kiyi takan tsantsar da aikinki domin nan ba’a san kuskure ba kina yin abu kaɗan zaki ji a jikinki.”
Yana gama faɗar haka ya juya ya tafi, abinshi.
Jingina nayi da bango ina kallon Inda Allah ya kawo ni. Bayan wasu mintoti, na gaji da tsayuwa na zame na zauna, na cigaba da tsammanin fitowar sultan, shiru kake ji.
Awa ɗaya ya wucce wasu awowin suka wucce bai fito ba. Can da naga har lokacin sallah yayi bai fito ba, sai na juya na fita niman inda zanyi alola da sallah. Karshe dai sai da na dawo shashin bayi nayi sallah sannan na koma.
Ashe ina fita shima yana fitowa, ganin takarda asaman kujeran falon yasashi sanin an shigo falon yana ciki bai bi takai ba yayi ficcewarsa, zuwa masalaci. Koda ya dawo a falon farko ya tsaya sabida mutanen da suka zo masa dubayya, da kuma mishi Jajjen ya jiki. Suma dai matasane sa’aninshi kuma yan Kabilarsa na Banu Hashim, daga cikinsu kuwa har da Jikan Amir Ukshe.
A hankali nake takowa sabida ba’a son karar takalmina ko sautin da zai dame mazauna gidan.
Da sallama na tura kofar na shiga duk sunji sallamar amma babu wanda yayi yunkurin amsa min, asalima kamar basa gun kare musu kallo nayi anan na fahimci dukkansu yan bana bakwai ne.
Abinda yasani cewa haka kuwa ba kome bane sai dan luran da nayi dan akala bazasu wucce 28-29 ba, domin babu wanda ya haura talatin. Taɓe bakina nayi na wucce,
Har inda aka kaini, tsayuwa na cigaba dayi, wasa wasa banga idanun sarki ba sai bayan sallar la’asar, na gaji da zama na mike zan koma can shashin bayi, ina rike handle kofar zan fita shima ya rike zai shigo. Bazata muka buɗe kofar tare, har sai da kaina yayi karo da kirjinshi.
Da sauri nayi baya ina zare idanu, bai tsaya bin takaina ba yayi wuccewarshi, bin bayanshi nayi da ido tare da dafe goshina nace.
“Wayo ni Safinatu! Toh waye sarkin ne? Toh ko wannan ne? Amma ai lokacin zuwanmu baya falon mutane huɗu muka wuce a falon farko, na biyu kuma mutane biyu ne, ai ko shine Sultan Ashraf ɗin?”
Ni kaɗai nayita lissafin can nace.
“Toh kenan sarkinsu yarone, taɓ dole yayi abinda ya gadama,”
Tsaki nayi cike da takaici.
“Mugu azzalumi sai da ya ɓatawa Mujahida rayuwa dan sun ɗauki mulki sun bashi, Allah ya is….”
Ganin fitarshi nayi da sauri nabi bayanshi ina cewa.
“Ji mana! Don Allah zoka min iso da Sultan Ashraf.”
Nayi haka ne dan na cire tantamar dake raina, ko kallo ban ishe isheshi ba, sai ma masu tsaron lafiyarshi da suka tare ni suka kaini wani dakin duhu. Me kula da bakin kofar ɗakin ya shiga yayita zane ni. Har sai da nayi laushi, wanda yaja har na suma, sannan suka watsa min ruwan kankara, a firgice na farka sabida azaba ko kuka ban samu damar yi ba,, cikin kakkausar mutumin yace.
“Daga yau ko tsuntsu kika ga zaiyi kuka wanda zaisaka Sultan cikin damuwa ke zaki kora mishi,, sannan ki tashi kije kiyi aikin da aka kawo ki yi, Sannan sultan baya son hayaniya koda kuwa ta fashewar abune toh zaki ji a jikinki”
Jawo yayi ya watsa a waje tankar kayan wanki. Dakyar na mike zuciyata na min zafi, lura da nayi dare yayi sosai yasani niman hanyar can shashinmu.
Koda naje buɗe kofar falon na biyu najishi a rufe dole na dawo falon Sultan, abin bakin ciki koda na shima nasa a rufe karshe sulalewa nayi na zauna, na fashe da kuka.
“Wani tsautsayine ya raboni da gatana nazo nan ana wasan kura dani.” abinda nace knn ina kuka.
***
“Yallaɓai Alexandra mun mun sami labarin an sami wata Yar african da.”
“Benjem kaje kasan meye ya kawo Yar african masarautar jordan.”
Daga haka yayi shigewarsa ciki dan yayi imani da abinda bokanshi ya gaya mishi.
***
Fitowa yayi zai tafi masalaci ya ganni a zaune na cusa kaina cikin cinyoyina, kauda kanshi yayi ya bar gun. Saukar bulala naji yasani mikewa zubur ina sosawa ciki mutumin ya nuna min na shiga, yana bina har kitchen ya nuna min, sannan ya nuna min bango inda aka kafa wata yar allo da aka saka jerin sunayen abincin da za’a girka……
#HZƘ
#MJ
#MD…..Follow me: Mai_Dambu
Oum Muwadda…
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITER’S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_
_Jordan Historical_
*®2020*
*BOOK ONE*
Page.٤
Time table ɗin na duba naga jerin abincin kamar haka.
Break Fast:+ Roasted nut & Bedouin tea
Lunch:+ Kunafa & Zarb tea & fatter.
Dinner:+ Mansaf & Shawarma &Fresh Juice.
Na yau kenan, abinda na fara kayan haɗin na nima musaman na karyawan safiya. Wanda nagani a cikin store abinda na fara shine niman wasu bread masu zubin gurasa, na haɗa kayan haɗi kasancewa ana haɗa roasted nut da y’ay’an cashew ko gyaɗa, kuma naga haka na haɗa dukda bani da tabbacin zai ci, bushashen ganyen shayi na bedouin na haɗa da minannas da citta da kanunfari na dafa. Kamar yadda naga Nannah tana dafawa idan ina gida.
Kafin karfe shida na gama sannan na gabatar da sallah a kitchin ɗin nayi har da alola dan kitchen ɗin har da bayi a ciki.
Ina idarwa na shiga juye abincin a manyan warmer, ina fita dasu falo inda aka tanadar da dinner table. Ina gamawa na koma kitchen ɗin na wanke kayan da na ɓata sannan na goge ko ina nafito dan kome na kitchen ɗin black & whiter ne.
D’an jimawa da nayi a kitchen ɗin na fito, ganin masu tsaron lafiyarshi a gaban table ɗin abincin sun zagaye abunci. Juyawa nayi zan koma rigana ya kama wani flower kafin na tare ya faɗu kasa, fassss ya bada sauti sai da gidan ya ɗauka. A fusace sukayo kaina jikina ne ya ɗauki rawa, kafin nasan abinyi sun rufe ni da bulala, sai da suka min tiliss sannan suka sani tattara kwalaɓen, na zuba a kwandon shara.
Sake sani a gaba sukayi har gaban abincin cikinsu ya sunkuyo da kanshi dai dai fuskana yace.
“Ki ɗiba kici.”
Kwallar ke zuba a idanuna ga zazzaɓin da yake cin jikina na dukar jiya, ga kuma na yau a hankali na kai hannuna na buɗe warmer na shiga ɗiban abincin na ci sai ruwan bedouin tea nasha, da kuma normal ruwan kwalba nasha, ina gamawa suka tattara abinci aka fita dashi. Can sai gasu sun dawo suka zuba kwanika, babban ya kuma sunkuyar da kanshi yace.
“Girkin yayi kyau, amma Sultan bazai ci abincinki ba kasancewarki bakar fata dan haka zaki zauna a nan kina dafawa karanunkan da kuliyoyinsa abinci sai gyaran gidan kece zakiyi tayu za’a kawo wanda zai na girka mishi nasa abinci naki girkin dabobine.”
“Taɓɗijam wa mage da kare zan zauna ina girka musu abinci”
Abinda nake faɗa knn a raina, bansan sun bar gun ba, sai da na ɗago naga duk sun bar falon.
Wato haka kogin kaddara ta kwasoni zuwa bakin gaɓɓar da bani da hanyar gottawa.
Koda na maida kwanikan kitchen zama nayi na fashe da kuka dan duk jikina ciwo suke min ga wani zafin azabar da shatin bulalar yake min.
Duba agogon kitchen ɗin nayi naga takwas har da rabi, da sauri na fito na duba Machine ɗin shara na shiga share ko ina, na falon. Ban gama sharewa ba sai karfe goma tsabar girman falon.
Sannan na shiga goge gidan tsaf na gama, wani show glass na hango cike da turaruka, tsautsayi ya ja ni zuwa gun. Wai nasaka a falon, ina zuwa zan buɗe naga hangoshi sanye da kayan sport wando da rigar ta kamfanin R&B. Hannunshi rike da goran ruwa, sai zufa yake gogewa. Bansan ya akayi ba jikina ya kama rawa ba kafin dai san abinyi nasha wani kwalba ya faɗo, tasss ya bada sauti.
(😂 Feener kin cika shishigi ina ruwanki ki tsaya inda aka ajiyeki mana)
Wallahi kaman a kunnen kartin nan fasa kwalbar sai gasu sun shigo kallona sukayi, nima kuwa na tsura musu ido dan har na fara kwalla. Basu duke ni ba sai dai sun sani kwashe kwalbar turaren sannan suka fita dani, aka kaini d’akin sanyi. Suka wurgani. Sai da nayi minti talatin sannan suka fito dani bana numfashi. Ruwan zafi suka watsa min har sau biyu.
Kaii Jama’a bawa baida yanci kuskure kaɗan zakayi kaji ajikinka.
Dakyar na farka suka sani a gaba har shashinmu na sake sauya kayana, babu yan matan nan kuka nake ina dana sanin zuwa na masarautar jordan, dole Ashraf yayi mugunta yaro karami ne fa, taya zai ji tausayin mutane.
D’aga sider bag ɗina nayi naga wata farar takarda da wani kunshi.
D’auka nayi naga anyi rubutun da bazasu gaza layi shida ba.
_Barka da zuwa Masarautar jordan, a cikin jakarki akwai waya da bluetooth, sai wannan kunshin kuɗine ki ji daɗinki sannan muma zaki mana aiki idan kika ki toh zaki buɗe idanunki a lahira_
Wayyo Allah na, nashiga uku ina ne na kawo kaina, buga kofar akayi na tashi da sauri zuwa nafita, suna tsaye sun min zuru zuru. Wuccewa nayi a gaba suka rufa min baya, bansan dalilinsu na biyo ni ba. Amma ba mamaki yana nasaba da sarkinsu.
Bayan sun kawoni na wucce ciki a falon farko naji wani abin mamaki, manyan mutane fa dan akalla zasu kai shekaru sittin da ɗauriya. daya yace.
“Akwai dukiyar da nake son fitarwa daga cikin kasar nan zuwa Amurka, shine na kawo takardun yana ciki an kai, dan ma Amir Ukshe yasa baki yanzun haka takardan yana gunsa.”
D’ayan yace..
“Nima manda ake hakowa a cikin kasar nan musaman mallakin masarautar akwai wasu turawa da suke sone zan sayar musu shine na kawo takardan yasa hannu, da taimakon Amir.”
Hmm na iya cewa a raina, yadda suke hiransu. Muna shiga cikin gidan naji kamshin falon ya sauya. Hangoshi nayi ya naɗe kafa ɗaya akan daya, sanye yake da doguwar jallaɓiya ga wasu mutanen a tare dashi, sallamar da nayi wani daga cikinsu ya amsa. Duk mutanen sun ɗago sun kalleni banda shi. Shin dama mulki idan ya shiga jikin mutum haka yake. Tsohon da aka kaini gunshi, shine yaketa magana cikin rarrashinsa da yasa hannu a cikin takardan da yake gabansu.
Wuccewa kitchen nayi bansan ya akayi ba dan sune suketa magana, sai dai jin da nayi suna sanya mishi albarka tare da jin daɗin har da godiya,
“Anya Masarautar nan tana cikin tsari kuwa? A sani na sarki Fada yake zuwa wannan sarkin toh.”
Nace a raina kar nayi gajen hakuri da saurin yanke hukunci.
***
Kwana na uku a cikin gidan kuma kullum girkina sai dai akaiwa Kare da Mage. A rana na huɗu, ne aka kawo wani balarabe, ya fara girkin sultan. Zamana da Samin yasani sake kara sanin halayar larabawa, dan ido da ido yake nuna min kabilanci da wariyar launin fata. Uwa uba, tsangwama.
Tafiya yayi nisa dan kuwa na kara fahimtar cewa Sultan Ashraf sarkine a zahiri amma a baɗɗili ba shine sarkin ba Amir Ukshe da Amir Abu Zarri, duk wani abinda zai fita daga masarautar ta hannunsu ne, sannan rayuwar Sultan Ashraf kamar a hannunsu yake dan sai yadda sukayi dashin, sannan akwai abin alajabi dan yake damuna, game da sultan duk lokacin da aka kawo mishi takardu baya buɗewa sai dai yasaka musu hannu, baya taɓa bincika meye takardan.
***
Yau na cika sati huɗu da aka kawo ni cikin kurkuku sultan a yanzun na kiyyaye abinda zaisa a zane ni sosai. Da wuri na gama abincin mage da karen. Nafita zuwa shashin bayi.
Lokacin da naje nasame Yan ɗakinmu jungun jungun. Ganin babu Zakiya yasani cewa..
“Kanena ina kanwata Zakiya.”
Kuka ne ya kwace musu suka sani a gaba da kuka cikin tashin hankali nace.
“Lafiya kuke kuka.”
Mujahida ce ta iya cewa..
“Kaltu Feener! Zakiya an yanke mata hukuncin zaman gidan kaso har na shekara uk.”
A tsorace nace.
“Akan wani laifin?”
“Sabida ta kare kanta lokacin da Amir Sauban ya nemi keta mata haddi ta fasa masa kai da kwalb…..”
Ban gama jinsu ba na fita daga gidan, da gudu. Sai gidan Sultan raina a ɓace na shiga yana zaune a falo. Kai tsaye na nufi inda yake cikin kuka nace.
“Shin kai wani irin sarkine da baka samawa talakawanka adalci?”
Idan dutse zai amsa min toh Sultan Ashraf ya tanka min.
“Wato ku kanku kuka sani, daga ku sai danginku, ta rasa ahalinta a yakin siriya tazo nan dan rufawa kanta asiri.”
Ji nayi an fizgo min, fita dani suka fara yi cikin ihu nace.
“Kayiwa kanka Adalci.”
Tunda suka kaini ɗakin suke zane ni, sai da suka na daina numfashi sannan suka kyale ni. Sai da nayi kwana uku a ɗakin duhu sannan aka fito dani. Tunda aka fito dani hasken waje ya ɗauke min gani na.
Sai da nayi awa uku sannan ganina ya dawo dai dai.
…… Koda na shiga kitchen Samin na kallona ya kauda kanshi, yace.
“Sorry Feener! Kiyi a hankali dayiwa Sultan Magana kai tsaye, dan zaki iya rasa rayuwarki baki ɗaya, ai da sai kinyi sati za’a fidda ke toh dabobin da kike musu abinci an kai musu abincina sunki ci shine suka fara niman mutuwa shine mai kula da Arduwan yace a fidda ke in ba haka ba mutuwa zasuyi. Sultan naji da kare da magen kamar rayuwarsa.”
Gyaɗa kaina nayi kwalla na zuɓo min, haka nasa hannu nayi girki aka kai musu. Na fito zanje shashim bayi aka hanani. Wai ance kar na kuma fita daga shashin har sai sultan yabar kasan, dan saura kwana uku zai bar kasan.
Kamar na daka tsalle zai tafi zan koma cikin gidan gun bayi Yan uwana.
Haka na koma kitchen dan anan nake zaune bani da inda yafi nan.
Tsabar na kagu ya tafi bansan ya akayi nayi Mansaf yayi yaji ba, ranar sai da naci duka bayan an sani sabon abinci wai kare da mage hauka sukayita musu dake suna can gefen gidan ta baya, shine aka kira likitan dababobi ya gano yajin da na cika a cikin abinci Sultan da kanshi yace.
” ku mata kaman yadda tayi musu.”
Wato su bani abinci me yaji kamar yadda na musu
Kare mishi kallo nayi bai wucce sa’an Abdullah kanina ba wai shine yake bada umarni a zane ni, ina da matukar zuciya da fushi, shi yasa ban cika shiga tsabgar kowa ba, sai na yaba da halinka. Bansan lokacin da nace masa.
“Na zata sawa zakayi a kashe ni kamar yadda kasaba sawa ana kashe mutane.”
Bai taɓa tsayawa ya kalle ni ba, sai yau, kaɗa kai yayi yace.
“Ku jiyar da ita azaba wanda gobe ko hango ni tayi zata sauya hanya.”
Lumshe idanunshi yayi aka suka fita dani, zuwa ɗakin azaba. Wato wani irin wahala suka bani wanda yasa ko tsayuwa na gaggari yi sai kwalla kawai.
***
*Banu Hussein*
Yake shi da kabilarsa, kowannensu sai shawara suke badawa yadda zasu kwace mulkin Jordan, da karfin cin tuwo har suka gama sannan ya zauna cikin izza yace.
“Na bawa Sultan Ashraf Rania!”
“Amir Adna kasan abinda kayi kuwa? Ka ɗauki Y’arka kabawa.”
“Shakur! Mulkin jordan muke so! Idan Rania tashiga tasamu ciki ta haihu da Ashraf tankar mulki ya dawo cikin kabilar Banu Hussein ne kuje kuyi nazari.”
Yana gama faɗar haka ya bar musu falon baki ɗaya.
***
*Gidan Amir Ukshe*
“Abbie!”
Gyara zama mutumin yayi cikin girmamawa yace.
“Abbie! Sahel ta amince da zaɓinka! Amma meye kasonmu idan Ashraf ya aureta?”
Kura mishi ido Amir Ukshe yayi sannan yace.
“Me kake tunani akan mulkin Jordan bayan bamu kaɗai bane muke kwadayin mulkin, akwai Kabilun Banu Nazir da Kabilun Hussein, ko da wasa bazaka taɓa samun koda taki ɗaya ne na mulki tunda Yasir ya sadaukar da karagar babu wanda ya isa ɗarewa da karfin tsiya ka cire ranka a cikin sha’anin mulkin gidan nan. Zaka iya tafiya”
Jikin Amir Marhum ya mike zuciyarshi cike da haushin Mahaifinsa.
***
*Banu Nazir*
“Zoya! Naji Ashraf zai koma Germany ki shirya na nima miki masters a can, kafin ku dawo ki tabbatar da kin shawo kansa, inta kama ma kanki ne ki mika mishi dole na ruguza Daular banu Hashim da hannuna…….
*Ku nutsu labarin cike yake da sarkakiya karku min korafi akan duk abinda zai faru idan kuka duba sunan labarin kunsan kome zai faru no more any korafi*
#MJ
#HZƘ
#Mai_Dambu
#VOTE MJ…
Oum-Muwaddah…..
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITER’S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Page.٥
Wato ɗakin da aka kaini yafi kowanne axaba, dan yadda kasan gidan bread haka cikin ɗakin yake , ga hayakin tire gas, nasha mugun wuya kafin suka fiddani.
A kitchen suka watsar dani zan iya cewa ban taɓa cin azaba irinta yau ba nasan mutane zasu so jin taya akayi na bar iyayena nazo nan ake wulaƙantani kaɗan daga cikin tarihina.
Safinat Badr Kyari shine ciƙakken sunana. Mahaifina ya fito daga kabilar Kanuri ne daga kasar Nigeria.
Mahaifiyata kuwa Shuwa arba ce dan ko hausa bana ji sosai sai turanci da shuwa sai larabci.
Nice Babba a gidanmu ina da shekaru 32 sai, kanina Abdullahi wanda yake tsaƙanin 28/29 Yana da mata har da yara biyu sai Nanah Asma’u wacce take da shekaru 25 tana da aure da yaro ɗaya na batarta da tsohon ciki. Sai. Sai Fatima tana da shekaru 21. Kafin ɗan autanmu Khalil yana da shekaru 17 bana ya gama scndry.
Mahaifinmu nada mata biyu har da Umminmu uku kenan Hajiya Amnah babarbariya ce daga Bama, tana da Yara huɗu.
Maryam suna kiranta da k’iose Tana da shekaru 25 sa’a Nana Asma’u ce. Sai Kaltume tana da shekaru sha tara, sai Sa’ar Khalil dan rana ɗaya suka haihu da Ummi ana kiran yarinyar da Khalilah, Hajiya Amnah muna kiranta da Umma. Sai Hajiya Nuratu fitinanniyar gidanmu kenan,
Matar tasaka ni a gaba sosai musaman da taga Nannah ta janye ni ta kuma nuna musu tafi sona sama da kowani yaro a gidan, Hajiya Nuratu wacce muke kiranta da Ammin tana da yara maza babban ɗanta sa’an Fatima ne yana da kusan ashirin yana jami’a shi dasu fatima, sunanshi Abba lawan, sai Salamn shima sa’ansu Khalil ne, sai Ruwaidah tana da shekara goma sha uku, da ɗan karaminmu Anas.
Mu goma sha biyu ne cif a gidanmu, Abbanmu haifaffen garin Amman ne nakasar jordan, sabida Mahaifin Ibrahim yayi aiki a karkashin , Sultan Yasir tun kafin ya zama sarkin jordan kasancewarshi na likitar har zuwa lokacin aka kifar da mulkin sultan Yasir, ya tattaro ya dawo maiduguri. Daga baya masarautar ta nemi ya koma bakin aikinshi yaki. A lokacin Abbanmu yana aiki a babban asibitin maiduguri ya auri Umminmu. Da Kakanmu yaga ya dan manyanta sai ya tura Abbana Masarautar jordan.
Ya tawo da ummi ya cigaba da kula da sarki Abdullah har aka haifeni, a lokacin Sarki Abdullah ya auri Nana Asma’u daga Masarautar Oman. Tazo tasamu ina da shekara biyu, zuwanta yasa abubuwa suka fara faruwa, ganin haka muka dawo gida ni da Ummi. Sai dai duk bayan wata shida Abba yana zuwa mana. Ina da kusan shekaru bakwai Abbanmu ya dawo shi da Nannah inda tazo tayita jinyar zuciyarta sabida rabata da sukayi da d’anta. Wanda suke sa’anin da Abdullah dan shekarun Abdullah uku.
Taso jan Abdul yana ɗibe mata kewar D’anta wanda bata kiran sunanshi. Sai Abdul yaki. Karshe nice taja, ni kuwa a lokacin da mugun son jiki tunda ta fara jana a jiki na sake zama sakaltacciya. Abba ya ya hajiya Amnah, wacce tana zuwa taga Nannah aikuwa hankalinta ya tashi, dukda Abba yana aiki amma albashin baya kai mishi yadda ya dace, ga fitinar Hajiya Amnah akan sai Abba ya kori Nannah yaki shine tayi fushi har da daka yajinta. Lokacin kuwa Allah ya saukarwa Abba wani iftila’i domin kuwa an koreshi a gun aiki ganin abinda zamu ci zai fi karfinshi Nannah ta kirashi mika mishi jakar da aka bata a masarautar jordan tayi, tace.
“Badar! Bazan iya biyan abinda kai min ba, dan ka ɗauko ni daga kasar jordan har nan kasarku, ka kuma ɗauki nauyin cina da sha, kana ɗawainiya dani, dukda kaki faɗa min an koreka a gun aiki ga ɗawainiyar Iyali gana yaranka ka ɗauki wannan dukiyar dan ni bansan me zanyi dashi ba, sun bani a matsayin sayan ɗ’ana sukayi, ina tsoron abinda ya faru a kan sarakunan baya ya komo kansh.”
Muryanta ne ya shiga rawa alamun kuka zatayi fitowa nayi daga ɗakin naje kusada ita na ɗaura, kaina akan kafaɗarta cikin larabcin da take koya min nace..
“Nannah kiyi hakuri, idan na girma zan kawo miki d’anki nan kinji, kiyi addu’a na zama babba kinga sai kome yazo min da sauku.”
Tunda tabawa Abbanmu kuɗin Allah yasanya mishi albarka, sai ma wani irin bunkasa dukiyar yake, dan kasuwanci yake daga dubai, lokaci yaja sosai dan har na gama primary schl zan shiga scndry a lokacin Nannah ta fara bani labarin, masarautar jordan. Dan bani mantawa na taɓa ce mata.
“Nannah taya zan shiga masarautar har na dauko miki shi?”
Dariya tayi sannan tace.
“Ke ba kamar sauran mutane bane kuma idan aka san zuwa kikayi zaki tafi dashi kashe ki zasuyi, ina son ganinki zama tankar sarauniya ki bar tunanin wancan duniyar.”
Tura baki nayi cikin kunkuni nace.
“Nannah! Ni ki gaya min taya zan shig.”
“Safinat! Masarautar babu tausayi ko imani, dai dai da kwalba idan kika fasa, hukuncine, sai kin wucce get huɗu da masu tsaronsu kimanin mutane ɗari uku, sannan ki isa cikin gidan bayan kin wucce dogon baranda kafin ki isa falon farko, wanda yake ɗauke da karti majiya karfu mutane goma suna tsaron falon farko, ki shige tacikin falon kije falo na biyu inda zaki samu. Wasu masu tsaro har mutane ashirin. Sannan ki yi tafiyar minti arba’in da zai kaiki cikin inda Sultan Ashraf yake. Taya zaki shiga? Wani hatsari zaki fuskanta na matsayinki na Y’a mace? Shin zai yarda ya biyo ki? Idan mugayen da suke tare da shi zasu barki ki fito musu da shugabansu? Idan suka san kudirinki na sace musu shugabansu me kike tunanin zasuyi don Allah ki rufa min asiri karki saka haka a ranki kinji yarinyar kirki.”
“Amma Nannah ina ganin fit ..”
Rufe min bakina tayi cikin damuwa tace.
“Ina gudun faɗa miki kome mutanen suna da nuna kabilanci musaman ke da kike da duhun fata. Suna kyamar bakaken fata.”
Shiru nayi dan a lokacin banfi shekara goma sha biyu ba. Aukin tambayar tsiya.
Bunkasar da Abba yayi ne ya tattaramu muka koma abuja da kasuwancinsa dan yafi karfi tacan da lagos.
Bayan na gama scndry naki karatu a jami’ar kasan nan, rimi rimi akayi min kome a medicine inda aka kaini Ghana, ina zuwa can na koma Mass com, inda na shiga karatun babu wanda yasani a gida sai da nayi shekara ɗaya nazo hutu. Suka sani ranar nasha faɗa a gun Abba, ganin faɗan yaki karewa Nannah tafito tasa baki take Abba ya hakura, amma ya ji badaɗi.
Wannan dalilin yasa Hajiya Nuratu take kara jin tsanata. Musaman da yanzun kome Abba zai yi sai yaji tabakina.
Har na koma. A sannu gidanmu ya fara cika, kafin na gama jami’a gidan an cika ba laifu. Shekaru biyar na dawo daga Ghana, naje bautar kasa a Imo. Ina gamawa nasamu aiki da gidan radio na kasa dake Kaduna,
Amma Nannah taki dole aka dawo dani Abuja, dukda shakuwar da mukayi da Nannah baisa idan nayi laifi ta ɗaga min kafa ba, faɗa take min sosai.
Lokaci ya tafi dan bayan na fara aiki na koma makaranta nayi degree na biyu, abin mamak shine na koma kamar me cutar junnu dan bana kaunar maganar aure, kuma lafiyata lau, ganin haka ya ɗaga hankalin Iyayena. Murmushi nannah take kawai idan taga sun sani a gaba suna min faɗa, bata hanasu dan nima da nawa shegantakan, cikin ruwan sanyi manema suke zuwa min karshe basa kwana biyu na koresu, fata fata kuwa. Ni a tunanina idan nace zanyi aure waye zai cikawa Nannah burinta shiyasa naki auren kowa, tunda nasa a raina zan dawo mata da ɗanta na kuma ji na gani.
Na taso da wannan burin a raina ko iyayena basu san da shi ba hatta itama Nannah bata sani ba dan tabar min maganar, ni kuwa tausayinta yasani kudirawa a raina sai na dawo mata da ɗanta.
Bayan shekara biyu da rabi na gama degree na, na biyu. Wanda yayi dai dai da haɗuwana da Anim. Sabon shugaba gidan radionmu, da wasa muka fara sama sama, sai gashi mun kulla soyayya, wanda yaje har gaban iyayenmu. Aka tsayar da magana maganar aure a tsakaninmu, tunda naga haka hankalina ya tashi. Karshe na nemi Aliee dan kasan jordan ne na zaunen syria ne, mun haɗu dashi a ghana ne yaje wani course. Nan nima n kirkiro tafiya course ɗin shekara guda. Dakyar aƙa d’aga bikinmu, dan ma Anim yana da mata har da yara biyar.
Kuma dan bokone sosai irin mutanen nan masu akidar boko, dan haka ban sha wuyar shawo kanshi ba ya amince aka. Kwana uku tsakani na wucce jordan. Sau uku ina niman aiki a cikin masarautar suna hanani, karshe sai Aliee ne ya faɗa min basu bani aiki ba dole sai nazo a matsayin baiwa, banso haka ba. Amma babu yadda na iya idan na tuna yadda a gidanmu, dukda an aurar da ƙanena haka bai taɓa damuna ba Ammi tayi min gori har dasu habaici baisa na damu ba, a yanzun nayi na damar tsallake auren Anim da nayi gashi ba biyan bukata, tunda nazo a baiwa dole naga tasku. Da gatana nazo ana wulakantani dan ko Aliee ban faɗa mishi abinda ya kawo ni ba.
***
Ajiyar zuciyar na sauke, tare da goge kwallana. Dakyar na mike na shiga jan jikina zuwa ban ɗakin na watsa ruwan zafi me mugun zafi, sannan na fito na maida kayana. Abinci Samin ya ajiye min na ɗauka naci. Cikin jimami yace min.
“Me yasa kike da taurin kaine? Ki bar katsalandan a cikin masarautar nan.”
“Samin kenan aiko mutuwa zanyi sai na faɗawa Sultan gaskiya, mulkin zalunci akeyi a wannan masarautar da cin zalin.”
“Zaki sha wahala!”
“Kasan wahala ita shirya masa ake ba”
“Kinsan yarone bai da hankali a matsayinki na babba ya kamata kija girmanki, ki kiyayye doka.”
“Ni zan faɗa maka Ashraf yarone tunda. ”
Ganinshi mukayi akanmu, kamar bai ji me muke cewa ba, ya shiga kitchen ɗin ya ɗauki abinda zai ɗauka yafita, yau babu mulkin babu bada oda toh ina ma yake magana, kullum fuskar nan a ninnike, sai kace wanda aka aiko masa da sakon mutuwa.
Ina jin Samin ya gma abinda zai yi, bayan ya min sai da safe. Ni kuma na baza hakarkarina a gurin……
😩 Insha Allah ina kaiwa page 10 zan ajiye typing….
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITER’S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Page.٧
*Banu Hashim*
Watsawa Amir Ukshe wasu takardu, Amir Abu Zarri cikin mugun ɓacin rai da fusata, ya daki table ɗin gaban Amir Ukshe yace.
“Baka isa hanani rawan gaban hantsi ba, dukkanmu kabila d’aya ce kuma manufarmu d’aya ce, sannan burinmu d’aya. Taya zaka kange kome dan zalimci ka hana wasu? Raziya ta kawo takardunta kace bazaka saka baki ba, akan me? Ita kaɗai ta rage a Ashraf ya kira danginsa amma ka hanata samun kusanci da yaron meye nufinka? Ga takardun kuma dole a samata hannu itama dan dukiyar ba naka kai kaɗai bane.”
Mikewa Amir yayi ýa tawo inda Amir Abu yake, hannunshi yakai zai taɓa Amir Abu Zarri, cikin sauri yaja da baya, yana nuna shi da d’an yatsa yace.
“Macuci baka da bakin gaya min kome nasan kai waye, kuma dole ayi kashe muraba. Ka duba jaridar can da na kawo maka karka manta yarjejeniyarmu na bawa juna goyan baya maciyi amana.”
Yana gama gaya mishi haka ya juya tare da barin ofishin.
Idan ran Amir Ukshe yayi dubu sai da suka ɓaci. Fuskarshi har ja tayi tsabar ɓacin rai, danna wani karfe yayi sai ga masu kula dashi sun shigo, nuna musu takardun yayi, suka tattara sannan suka zuba a kwandon shara suka fita.
***
Wani irin rikicine ya taso daga cikin kabilun Hashimiyya, wanda yaja hankalin, sauran kabilu guda biyu suka zuba ido suna kallon yadda wasan zai kayya, kuma abin takaici ba kome yaja wannan rikicin ba, sai dukiyar masarautar da suke watandarshi, karshe dai wasu daga cikin familyn Yasir sune suka, shiga alamarin inda aka dai daita ba tare da sanin Sultan Ashraf ba.
…….. Takardun da zaisa hannun suka, na kalla suna kan wani table na daban, dake Allah ya ɗaura min karambani, zama nayi a kujeran table ɗin, na shiga ɗauƙar takardun ina dubawa, a hankali na shiga duba abubuwan da takardun ya kunsa, mamakine ya kamani sakamakon ganin zunzuruntun dallolin american da zasu cire daga baitul mali. Masarautar, jin motsin yasani mikewa nabar gun, kitchen na shige. Ina hango shi ya fara samusu hannu ko duba takardun bai yi ba. Mamaki ne ya kamani na fito daga kitchen ɗin tsoro da fargaba dake raina bai hanani fitowa ba nuryana na rawa jikina na ɓari nace .
“Sultan!!!” bai ɗago ba kuma bai fasa abinda yayi niyya ba, na cigaba da cewa.
“Allah ya baka mulki ne dan ya gwada imaninka bawai ka zama azzalumi ba, wannan sa hannun da kake yi ka duba meye ya kun…”
D’ago kanshi yayi idanunshi sunyi jajjur, takanta fuskarshi tayi ja. Ainun balle kuma ace meye a zuciyarshi, kura min ido yayi sannan ya danna ɗan kararawar. Sai da naji cikina ya murɗa, shigowa suƙayi idanuna cikin nashi, bai janye ba nima kuma haka, cikin kasa kasa da murya suka ce.
“Umarninka muke jira”
“Ku tafi da ita, taji a jikinta.” yace, idanunshi cikin nawa,
Lumshe idanuna nayi cikin karfin hali nace.
“Me yasa bazaka fahimc…”
Juyar dani suka fitar dani, cigaba yayi da aikinshi.
Wato idan akwai mugayen mutane bayan larabawa ne, suna fita dani, suka wucce dani wani ɗakin ruwa. Suna shigar dani suka kifa kaina cikin ruwan sai da naƴi minti uku zuwa huɗu suka fidda, kuka nasaka ina jin numfashi dakyar naja numfashina, kafin na daidaita an sake tsumbulani cikin ruwan, har kusan minti biyar, bansan yadda zan muku bayani irin azabar da nake ji, amma bari na muku misali da kwarewa, idan wani kware da ruwa ya kuke ganin yake ji balle ni da ake tsuma kaina cikik ruwa bana jan iska, sai ruwa zalla nake ja.
Kusan minti ashirin suka ɗauƙa ana horani da ruwa, nayi laushi na masifar gajiya, suna ciro ni suka jefani gefe guda ina sauke numfashi ga kwallar wahala da nake fiddawa.
……. Bayan awa guda suka mai dani cikin gidan suka watsar a kasan kitchen ɗin da sauri Samin yazo inda nake ya ɗaga ni, kuka na saka mishi, coffee ya haɗa da sauri ya bani nasha, ina kuka, ganin yana juye ruwan coffee a cikin wani butar shan shayi, ya jera kofuna biyu. Zai fita dashi nayi maza na amsa, dan haka kawai naji ban yarda da coffee ɗin ba, dan a madadin ya bani na cikin tukunyar, a’a sai ya dafa min wani a cikin wani tukunyar ga kuma wanda ya dafa. Olready cikin siyasa na mike tare da cewa.
“Bani na kai mishi.”
Ba musu ya bani, ina fita falon, da gayya nasake tiren ya faɗi a kasa, kome ya zube. Da gudu Samin ya fito bai yi wata wata ba ya tsinka min mari, dai dai fitowar Sultan ga kuma masu tsaronshi sun shigo, sakamakon jin karan fashewar abu. Cike da jin haushi ya kuma d’aga hannu zai mare ni, Ghaniyu ya dakatar dashi. Ƙasa ƙasa yayi da murya yace.
” Kina da dangantaka da bakakken aljanune, yanzun aka dawo dake daga ɗakin horo amma har kin kuma wani laifin, ke ko tsoron sul….”
Bai kai karshe ba na tsinkawa Samin Mari, duk suka zaro idanu. Hatta Sultan ɗin mamakine ya kamashi, dukda a tsorace nake. Nace,
“Bani da lokacinku idan kun damu da abinda nake wanda kuke kira da Sultan yayi magana.”
Zasu yi magana ya d’aga musu hannu, takowa yayi har inda muke ya kalle su gabaki ɗaya suka fita daga falon takowa yayi gabana, d’ago kaina nayi naganni yar karama a gabanshi, tsaki yayi ya min sannan ya bar falon, komawa nayi kitchen. Ina shiga Samin na finciko ni, haɗani yayi da bango, tare da toshe min baki da hannunshi cikin zafin rai yace.
“Ina kyale kine sabida, baki cikin tsarina, wannan ɓarnan ƴa zams nakarshe da zaki min in ba haka ba zaki mutu. Dan ni an biyani kuɗin aikina ke da baki da rabo kita zama matsiyaciya.”
Sororo nayi ina kallon Samin kenan zuwa yayi ya kashe D’an Nannah, bansan lokacin da nace masa.
“Sai dai in bana numfashi matukar ina raye sai dai ka mutu. Amma ba Sultan ba yarda yasa ya daukeka aiki ko dan wannan yarda bazaka taɓa cuta….”
Shake min wuya yayi cikin mugun ɓacin rai yace.
“Na lura baki iya da harshenki ba, zan baki mamaki.”
Daga haka Bai kuma kulani ba ya koma bakin aikinshi, tun daga ranar nasaka ido sosai akan abinda yake, karshe idan yayi girki kifarwa nake, sultan yasa a zane ni. Tafiya tayi nisa inda na shiga renawa kowa hankali musaman masu zane. Idan suks ɗauƙe ni zasu ciks umarninsu, sai nayi tsagal nace.
“Kunga ni karku kaini wancan ɗakin wannan zaku kaini.”
Ko sai an shigar dani nace.
“Gaskiya nan bai min ba can zaku mai dani.”
Haka xasu dawo dani. Karshe dai sai an fasa hukuntani sabida renin hankalin da nake musu, sam na manta da mutanen da suke bibiyar alamarin. Ashraf kawai burina nasami shiga jikinshi.
***
Yau kwana uku kenan da bana ganinshi tawani fuska naji sauki tunda babu wanda zaisa a zane ni, tunda na fahimci har Samin baya nan take naji hankalina bau kwanta ba, tambayar ghaniyu nayi yace min ai sultan ya tafi dashi Germany, kamar zararriya haka ns koma. Burina na maidawa Nannah ɗanta gashi ya tafi da makashinsa.
***
*Germany*
Kofin Coffee da Samin ya kawo ya ajiye a gaban Ashraf, yayi nisa a karanta jarida. D’ago kai yayi yana kallon kofin, sannan ya juya ga Samin da yake tsaye, sannan ya juya ya kalli kofin.
Mikewa yayi ya fita can sai gashi rungume da yar magensa, zama yayi ya ɗauki kofin ya kai bakinta ta lashi coffee ɗin,
Tasha kaɗan sannan ya kalle Samin, da sauri ya ɗauki kofin yana jin haushin abinda ya faru. Yanzun ya fahimci wani abu wato tsabar rashin yarda irin na Ashraf ko abincin kowa baya ci ya gwamace ya ajiye kayan zaki a ɗakinshi yayita ci, dake shima ba me yawan ciye ciye bane dan tunda aka kai mishi hari sau biyu yake gudun cin abin hannun kowa.
***
*Bayan wata uku*
*Middle easth club*
Wani haɗaɗɗen club ne dake cikin garin Amman, shiga gun sai yaran wane da wane. Club ɗin ya cika makil da matasan larabawa da turawa kai har da tsirarun, gefe can yarima Nu’yam ne zaune tare da yan matansa, babban jikan Amir Ukshe, d’an Amir Marhum. Yana zukar shisha, wata yar kabilar Banu nazir tazo wuccewa ta bayanshi dake ya jima yana kwaɗaituwa da ita. Musaman shigar da tayi wani ɗan mini skirt da farin shirt, sai wata baby top da ta ɗaura kana ganinta kaga ma’aikaciya a cikin club ɗin, tazo wuccewa ya kai mata duka akan tuwaiyarta(bombom)
Juyawa tayi cike da kunya, dan yana kai mata duka mutanen gun suka fasa ihu da sowa dake larabawa sunfi yawa a cikin club ɗin, bakin ciki yasa ta kife shi da mari. Shiru gun ya ɗauka, sakamakon marin da aka mishi,ture yan matan da suka zagaye shi yayi, ya tunkareta inda ya rufeta da duka kamar mahaukaci. Ganin haka yan kabilarta suma suka rufawa Nu’yam, basu kyale shi ba sai da suka kashe shi, sannan suka fita da gudu. Cikik club ɗin duk aka watse.
Kafin kace me har larabi ya shiga cikin masarautar, Amir Ukshe da Marhum sai Amir Uzaifa. Kanin Marhum suka je club ɗin anan suka sami gawar Nu’yam, a yashe kamar gawan mara galihu.
Dake Yan sanda sun iso da wuri, ɗaukar gawan akayi zuwa Asibiti ana gama bincike aks basu. A daren suka kira Ashraf.
Dole aka jinkirta yiwa Gawar Nu’yam sallah.
Karfe sha biyu na rana. Sultan ya iso, sannan aka sallaci gawar aka kaita gidanta na gaskiya. Bayan sun dawo aka fito masa da file ɗin abinda ya faru, matasan sun gudu sai Yarinyar, dan haka an kamo yarinyar dan har an yanke mata hukuncin kisa, umarnin Sultan ake jira.
Dukda bansan zai zo ba na gyara gidan, tunda ya hana a barni na koma shashin bayi.
Kuma dama kaman jiranshi sukr kowa ya ɗauko cuwa cuwarsa, ya kawo Sultan yasa mishi Hannu.
***
*Banu Nazir*
Zubewa a gaban Alexandra wani farin tsoho yayi yana kuka sosai yace.
“Ya Shugabana! Angela itace kaɗai ta rage min, kuma matukar aka kasheta bani da kowa a duniya, asalima yaron shi ya fara mata rashin d’a’a har yakai da ya rufeta da duka, badan su Thomas sun taimaka ba da gawarta zasu kawo min kuma babu yadda na iya.”
Shiru falon yayi sai kuka Tsohon yayi, mikewa Shugaba Alexandra ya ficce daga falon yayi ya nufi can masarautar yaje dan su fahimci juna abun bakin ciki sam suka ki barishi ya gana da Ashraf. Karshe haka ya dawo da bacin rai wanda ya kuma tunzura zuciyarshi ga dole sai ya hamɓarar da Sultan Ashraf. Dan tsakani da Allah Ami Ukshe ya nuna musu kabilanci…
Kuma idan baku manta ba tun shafin farko na faɗa muku yadda Larabawa suke da nuna kabilanci……
*😂 “Anyan Kuna Fahimta kuwa Zauren Mai dambu nasan sunfi Yan Wattpad fahimta Musaman Fatima Da Maman Abba Kd jiya na hango ku Laaaa Sister Meeshaz da Queen Hafcy ku bar Harara na ko na tsuma kanku cikin ruwa😹”*
#MJ#Mai_Dambu#Vote&Share
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITER’S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*®2020*
*BOOK ONE*
Page.٦
“Yaro!!”
*Samin Ni zan faɗa maka Ashraf Yarone.”
Abinda yayita kai da komowa kenan a ranshi, baji haushin Samin kamar yadda yake jin haushin wancar bakar fatan, kallon kanshi yayi a madubi. Girman jikinshi ya kalla, da irin yadda Allah ya masa kira irinta lafiyayyun maza, matashin me ji da kuruciyarsa, wato Ashraf dogone me matsakaicin jiki, yana da dogon hanci wanda ya karawa fuskarshi kyau, sai idanunshi an dai-dai, yana da cikar gashin gira. Sai kayataccen sajen da zagaye fuskarshi, me haɗe da gemu ɗan cass. (Da zaku san crown prince Muhammad Bini Salman, wato yarimar saudiya me jiran gado, toh haka Ashraf yake)
Takaicine ya turnike shi bai san lokacin da yakaiwa madubin naushi ba har sai da kome ya tarwatse, kalamar Yaro ne yake yawo akanshi, babu wanda ya taɓa masa kallon Yaro sai wancar bakar fatan, haka ya tarwatsa kome sannan ya danna wani karfe sai ga masu kula dashi sun shigo..
Dafe yake da goshinsa yace..
“Ku ɗaukota.”
Fita sukayi dan cika umarninsa, ina kwance sai ji nayi anyi sama dani, kafin na wartsake an dire ni a cikin fasassun kwalaɓe, dan suna shiga yayi musu nuni da cikin kwalbar dan haka suka cika umarninsa. Suna dire ni cikin kwalbar na sake kara da.
“Auuchhhhh Ya ilahi”
Fesa turarenshi yayi yasa kai ya ficce a ɗakin, kuka ne ya kwace min. Duk yadda na motsa kwalabe ke shigewa cikin kafana, na ruɗe na kiɗime. Ga baki ɗaya nayi danasanin shigowa Rayuwarshi. A gigice nayita taka kwalaɓen har na fita a cikinsu na zuɓe a gefe guda ina jawo kafafuna, ina dubawa manyan kwalaɓe da kananu dakyar na ciresu. Ga jinin dake fita a kafar.
Bansan iya adadin lokacin da na ɗauka ina cire kwallar da kuka ba, ina gama cirewa na rarrafa na ficce daga ɗakin.
Ina fita na mike ina dangala kafata a kasa har na isa kitchen na, ban ɗaki na shiga na zauna dirshan tare da fashewa da kuka, wanke kafar nayi na saka cikin ruwan zafi ga uban azabar da nake ji, haka na gasa kafar. Ina nufar gun kayana na fahimci an taɓa min side bag ɗin, ina buɗewa nasamu takarda a saman anyi rubutu haka.
_Zamu fidda ke daga masarautar ki tabbatar kin zuba mishi wannan gubar a cikin abin shansa baya kisa farat ɗaya, sai ya gama cin jikin mutum_
Hannuwana biyu na ɗaura akai na fashe da kuka, tare da cewa.
“Na shiga uku na lalace.”
Mikewa nayi na ɗauki jakar na sakala. Dai daita tsayuwata nayi, na shiga takawa a hankali sabida ciwona.
Cikin sanɗa na fara tafiya har na isa bakin falo, ba a kashe ba haske . Saka hannuna nayi naja kofar abin mamaki a buɗe take, ina zura kaina zan fita. Naji motsi a bayana alamun an buɗe kofa.
A sannu na juya Sultan a tsaye sanye da kayan barci dogon wando da rigar me guntun hannu farare kwal, kallo ɗaya zakawa kayan kasan asalin auduga ne, yana tsaye harɗe da hannunshi a kirji, Mujahidah ce ta faɗo min a raina, gashi ya zuba min ido ni ban fita ba ban kuma shiga ba. Lokaci ɗaya na shiga tattara inda ya bayyana a jikina, musaman kirjina ina karesu takowa ya fara, kallon shi nayi naga inda nake yake zuwa.
A hankali na shiga ja da baya, jikina na rawa. Abin dariya yana zuwa ya ficce daga falon, ajiyar zuciya na sauke dole na koma naje na kwanta. Ban runtsa ba a daren sai kusan asuba. Barci ya ɗauke ni, saukar ruwa naji a kaina na mike firgit, na zauna tafin kafana sun kumbura tam.
Haka kawai nake jin na ɓata jikina, dan ina lissafin kwanakina na har da kusan sati ɗaya. Kallon basamuden da ya watsa min ruwa nayi cikin raunaniyar murya nace.
“Kai baka da imani ne? Idan shi ya baku umarnin zalinci sai ku aikata, yanzun daka watsa min ruwa meye ribarka?”
“Eyye! Bakar fata da maganar banza a cikin masarautar larabawa.” yace min.
Cikin jin haushi nace.
“Zaka iya sauya rubutun alkur’ani zuwa farin tawada?”
Kura min ido yayi cike da mamaki bakinshi buɗe yace.
“Lallai zaki wayi gari a barzahu. ”
“Idan na wayi gari a can kai kayi gad…”
Dake ɗaga muryana nake, kusan masu kula da lafiyar Sultan sunji mu. Kafin na karasa sun shigo amadadin su tambayi ba asi. Sai suka shiga zane ni. Da gayya na fara ihu. Yana can ɗakin hutawarshi yaji hayaniya dan sun daina dukana kokari suke nayi shiru, sai ga Amir Ukshe tare da d’anshi Marhum da kuma Amir Abu Zarri. Tare da Wata mace sun shigo gidan, jin hayaniyanmu yasasu leko kitchen ɗin. Cikin kasa kasa da murya Amir Ukshe ya rufesu da faɗa, har ya dakatar dasu. Ni kuma aka kira likitan masarautar da nurse suka zo aka duba kafana sai da suka min dress sabida akwai kwalaɓe.
Ana gama min, nurse ts rike ni muka koma can shashin bayi, ranar da muka ga juna munci kuka babu Zakiya. Kwana goma nayi ina jinyar kafar a lokaci kuwa Azrah tazo yakai sau goma akan lallai ina warkewa na koma bakin aikina dan sabida jinyata gashi karen da Sultan ƙe kiyo ya mutu, dan kwana uku ana kai mishi abinci yana kin ci har dai ranar da yunwa ta buwaye shi, ana kai mishi abincin yafarwa mutane garin a san yadda za’ayi dashi ya zarge kanshi, a take ya sheka. Nayi Imani da Allah sai Sultan ya azabtar dani akan haka. Ina zaune na buga tagumi dare yayi su Hindu sun tafi gun rawansu. Dauke wuta kwan ɗakinmu yayi, jakata na shiga lalluba zan kuna torch ɗin wayar da aka saka min naji karan buɗe kofa. D’ago kaina nayi dan har waje baka ganin haske sai duhu.
Komawa nayi da baya na hantsila kasan gadonmu cikin sauri na shige kasar gadon.
“Ki fito!”
Aka ce min, shiru nayi na ɗauke numfashina. Amma ina saukewa a hankali. Ko ya aka san ina kasan gadon sai ji nayi an finciko ni, ihu nasaka akayi maza aka shafa min abu a hancina ban kuma fahimtan komi ba….
***
“Alexandra! Na faɗa maka karku taɓa barin a nima masa baiwa indai ba daga Yankin nan tafito nan gaba babu wanda ya isa raba Larabawan nan da mulki sabida shigowarta cikisu zata ankarar dashi abinda yake ɓoye, dukda ba kai ɗaya kake bibiyarshi ba, ina jiye maka ranar da zai fito zahirin sarkinsa dan larabawa suna da kishin kansu balle kuma d’an kabilarsu, kuma bazaku taɓa cin nasaran kifar dashi ba, sai dai ku addabi rayuwanshi ita kaɗaice bata da mugun nufi akanshi ban sani ba ko tazo amma zata zo ɗin. Sai dai kuma shi muslimin kwarai ne babu ta inda zaku kuntattashi ba tare da Allah ya warware mishi ba, sai dai zan baka shawara ɗaya karku nuna sai kun hamɓarar dashi, mafi alkhairi kunemi mafita.”
“Buli! Ance min an kawo baiwa yar yankin african ko itace.”
D’agowa tsohon yayi ya ɗibi kasa yashiga zanawa aka wani tire me kama da kwalba. Ya jima sannan ya girgiza kai yace.
“Banga kome ba, sai dai tabbas zata zo kamar guguwar k’ak’a, si ta tafi da kome.”
Yana gama faɗar haka ya mike, tare da barin gidan baki ɗaya.
Bayan fitar bokan ya shiga sintiri a falon yana saka da warwara karshe dai ya shige ɗakinsa yana nazarin ta inda zai addabi rayuwar Sultan Ashraf.
***
Ba zance ga abinda ya faru ba. Dai na farka natsinci su Hindu suna kuka tashi nayi na zauna bana jin kome a jikina sai ma barcin da bai ishe ni ba. Mika nayi ina binsu da ido nace.
“Lafiya kuka zuba min ido.”
Dawowa jikina Mujahida tayi. Yace,
“Kaltu da fatan babu abinda ƴasame ki, ina nufin ba ayi miki fyaɗe ba”
Zaro ido nayi na diro a gadon banji kome a jikina ba ajiyar zuciya na sauke kafin na dafe goshina nace.
“Me yasa kika min tambaya haka?”
“Sabida munzo mun same ki kwance babu kaya.”
Tsoron da nagani akan fuskarsu yasa na gaza faɗa musu kome, shafa abin wuyana nayi naji yana nan inda yake, da sauri na ɗauki jakata ban iya ce musu na tafi ba. Dan bansan da wani kalma zan faɗa musu abinds ys faru bana cikin hayacina.
Hmm wato yadda na fara tafiyan har nabar cikin gida bayi ban samu matsala ba, sai da na nufi hanyar da zai kaini gidan Sultan, nan ne wani mugun tsoro ya kamani, domin lokacin dare yayi sosai. Ina tafiya sai naji kamar ana bina, da na ɗauka takuna ne. Sai da na saka ido sai naga abu kaman inuwa nabin bayana, an nan ne na shiga karanta ayatul kursiyu, ga wani masifaffen tsoro da ya turkeni ina karanta addu’ar ina sauri ina waige – waige.
Cikin ikon Allah na isa get ɗin farko, tun daga nan ban kuma cin karo da kome ba har na isa cikin gidan. Da sallama na shige falon farko ba kowa haka nayita ratsa falon har na isa falonshi.
Kamar kullum ba kowa a falon, sai karan da naji na ruwa a kitchen. A tunanina Samin ne da sauri na shiga, turus nayi ganin Sultan a gaban gas yana gani na ya tsuke fuska fiyye da kullum. Turus nayi ina zare idanu, ba kome yaja haka ba sai dan kwarjinin da yake dashi, kasancewarshi sarki. Komawa nayi da baya, har ya gama abinda zaiyi ya fita,
Mamaki nake yau da banga Masu tsaronshi ba, vibrate naji a jakata na saka hannu na cikin na ciro wayar da aka ajiye min tun kwanaki, sako na gani.
*Har kin razana ne da abinda ya faru, bamu miki kome ba kawai mun miki gargaɗine kawai matuƙar kika ce zaki bijire mana har cikin gidan Sultan zamu biyo ki*
Goge sakon nayi dan babu amfanin ajiyewa, zama nayi cike da damuwa bayan na shiga kitchen. Tallafe fuskana nayi na rasa meke min daɗi ban ɗaki na shiga nayi alola. Sallar na gabatar sannan nakwanta.
Zuciyata cike da sake sake, can da yunwa ta buwaye ni na tashi na fara niman abinda zanci kaman ance na buɗe friji nayi arba da kunafe, cirowa nayi, na kuna micro nasaka ina jin ya tirara na ciro na fara ci hannu baka hannu kwarya, ina ci ina kwalla ina sha’awar abincinmu na gida, irin biski, indalayi wani kunun kanuri ne, ɗan wake da tuwo miyar kuka, miyar ganye asalin taushe musaman miyar hajja kakata, dan har da kaɓewa take yanyankawa tasaka tantakwashi, idan za a ci da biski a zuba manshanu. Bansan lokacin da kuka ya kwace min ba, da gatana ina kwanciya a kasar tiles ga sanyin da yake shigana haka wata ran nake tashi na zauna akan kujera anan zan karasa kwana a zaune sabida bani da Yanci………..
#MJ#Mai_Dambu#Vote….
*Dalilin da yasa nace zan ajiye typing ni a gaskiya ban iya Editing ba kuma na faɗa muku ban iya gaskiya na, babu amfanin baɗi ba rai gwara na ajiye rubutun kawai dan wallahi ban iya ba, ai nayi kokari ma, ni Yar arewa ce amma a kudu aka haifeni kuma na taso acan, dawowarmu Bauchi shekara goma cif, ina ga idan ba ajinjina min ba toh kar a kushe min dan ko haifaffun arewa bazasu kalubalance ni ba, wannan shine iya gaskiya… Idan nayiwa wani laifi ya yafe min…..👏👏*
Oum Muwaddah….
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: *_HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Page.٨
……. Kakan Angela yazo har gun Ashraf, amma fir aka hanashi ganin Ashraf, ni kuma nazo zan fita naga ana koran tsohon. Sai roko yake kar a kashe masa jikarsa. Komowa ciki nayi na duba inda aka ajiye takardun, na ɗauka na juya zan bar falon, mukayi kiciɓis dashi, kallona yayi yadda jikina ke rawa takardan sai da ya nemi faɗuwa, bai ce min kome ba ya raɓa gefena ya shiga duba sauran takardun, nima juyawa nayi na mai da mishi takardansa, cikin sassanyar murya nace.
“Ranka shidaɗe! Ana mulki a cikin masarautarka ba bisa ka’ida ba, sannan kuna nuna fiffikon kabila akan sauran kabilun, Sultan katuna Allah ya baka mulki da izza dan gwada imani. Ka duba abinda kake aikatawa baya cikin tsarin addinin musulunci kwata kwata, abinda kake yi tankar na larabawan zamanin jahiliyya”
Don Allah meye laifin wannan kalman.
D’ago idanu yayi ya kalleni a sace, sannan ya maida kanshi cike takardun da yake yi, haushine ya kamani dake jikina ya saba da wahala, nace.
“Tun da nake ban taɓa ganin lusarin sarki irinka ba! Me kunyar nunawa duniya ko shi waye, an mai daƙai wawa suna shargalensu kai kuma sun mai da kai banza ana goga maka kashin kaza a idanun talakawanka, sam baka dace da zama sarkin alumma ba sai dai sarkin lusarai.”
Mikewa yayi, ya zagayo gabana, cikin matsanancin ɓacin rai ya shake wuyana, ina kakari tare da niman kwatar kaina, nace.
“Kaga Yarantar ba! Ka tsaya ka fuskanci gabanka ba faɗa da mace ba.”
Cillar dani yayi cikin ɓacin rai ya take min kafa, kara nasaka. Ina riƙe da wuyana cikin karfin hali koda tsaga jikina zakayi bazan daina gaya maka gaskiya ba, dan banga dalilin zuba maka ido kana aikata abinda ka gadama ba.”
Zuwa yayi ya kamo karamin hijab din dake kaina tare da gashina ya shiga jana, har cikin dakinshi ya cillani saman gado, ɓalle aninin rigarshi ya fara, da sauri na dira daga gadon zan gudu ya cafkoni tare da maidani da karfin tsiya ya fara niman rabani da kayan jikina, rike hannunshi nayi. Cikin tashin hankali nace.
“Don Allah karka min haka, ban taɓa zina ba, kayi tunani idan y’ar uwanka ko y’arka , ƙo kuma mahaifiyarka….”
Cak ya tsaya da abinda yayi niyya, cikin ɓacin rai ya sauka a gadon ya fita daga ɗakin,
A hankali na sauko nima, jikina a sanyayye na fito, babu abinda yayi min. Amma tsananin tsanarshi da kunya sun dame ni, a raina kuwa nace.
*Insha Allah sai na kai ka gun Mahaifiyarka kuma yanzun na fara maka katsalandan*
Ban ganshi a gidan ba, ga baki ɗaya har tsawon kwana biyu.
Ashe a wannan shashin ya daina zama yana nan a gidan, na gaji da zaman shiru na shirya zan tafi gunsu Hindu. Ina zuwa falon tsakiya najiyo muryansu Amir Ukshe yana lallaɓashi, a raina nace.
*D’an banza dole kayita yadda kaso wato a nan lallaɓaka suke ni kuma ina maka hawan kawara.*
Duk yadda suƙa so yayi musu abinda suke so yaki, komawa nayi da baya, dan ko magana yaki musu, mutum sai kace bebey. Haka suka bar gidan cike da damuwa,
***
“Barka da Zuwa! Shugaban Kabilar Husseinniyya! Adnan Bini Bilal Alhusseinniyya! Kaine har ofishina.”
Cewa Amir Ukshe,
Murmushi dattijon yayi ya mika masa hannu sukayi musabaha, zama sukayi sannan Adnan bini Bilal, yace.
“Sai ka gannin kwatsam,”
“Eh wallahi!” inji Amir,
“Nazowa Ashraf da kyautane mai daraja, idan bazaku damu ba na bashi auren Y’ata karama Rania, kwanan nan tagama karatunta na chemistry.”
Shiru Sultan yayi kafin yace.
” Toh amna ina ga me zai hana muje kaji ta bakinshi.”
Cikin jin daɗi mutumin yace.
“Nagode! Kayi hakuri ban maka ta’aziyar rashin da kayi ba, kuma naga har yanzun baku ɗauki mataki ba, haka zaku bar jinin yaron ya zuba a banza kenan, ya kamata kusan abinyi.”
Murmushi Amir yayi suka fito daga ofishin dake cikin fadar masarautar, Amir yayi musu jagora har cikin gidan Sultan, yana zaune ya saka wasu takardu a gaba. Zai saka hannu akan za a fidda wasu mahaukatan kuɗi, wanda ya fito ta Ofishin Amir Uzaifa, amma kamar wanda akawa dabaibayi.
*Sun maida kai lusari!!! Wawa said yadda sukayi da kai*.
Jin kalmomin yake kamar an watsa masa fire, abin haushi abinda yaso aikatawa da wancan kaskantacciyar baiwan, ya godewa Allah da bai kai ga aikata kome ba dan yasan da yayi d’an danasani a rayuwarsa,
Da sallama suka shigo ya d’ago kanshi, ya kallesu, fuskarshi a sake. Bai ce musu k’ala ba, suka zauna tare da mika mishi hannu.
Ajiye biron yayi suka gaisa, sannan ya maida hankalinshi kan takardan gabanshi, Amir ne ya gabatar mishi da Shugaban kabilar Husseiniyya, da kuma kudirinsa na bashi Y’arsa.
D’ago kai yayi cikin kasaita ya kalle Amir Ukshe yace.
“Allah ya tabbatar”
Shine abinda yafito bakinsa cike da mamaki Amir ya kalle shi, haka kawai yaji ranshi yayi mugun b’aci tun yaushe yake binshi da maganar Sahelah, amma yaki tsayuwa ya saurareshi sai yanzun da aka bashi mace daga wata kabila ta maguzawa zai amsa, murmushi yake. Amir yayi sannan suka mike zasu fita.
Ya d’ago kai yace.
“Amir! Ina niman Uzaif”
Gyaɗa kai Amir yayi har suka fita zuciyarsa kamawa take da wuta, shugaban Kabilar Husseiniyya murna yake, abinsa amincewar da Sultan yayi babu ja balle bincike, dole suma a haifi sarki a cikinsu fatanshi d’aya Rania tana shigowa ta haifi ɗ’a namiji, dole daular Jordan ta dawo karkashin ikon Urdawa.
Bayan tafiyarsu ya tattara takardun ya dawo dasu gidan, ina jin motsinsa ban fito ba, da gayya ya sake glass cup ya fashe, masu tsaronshi da suka rakoshi zasu nufi kitchen ɗin ys ɗags musu hannu, fita sukayi a ranshi yace.
*Wancar bakar shaiɗaniyya ce idan akabi nata kullum sai an gutsire naman jikinta*
…..
Wuccewa ɗakinshi yayi ya samu kome a shirye, wanka ya faɗa, yayi sannan ya fito kayan shan iska yasaka wandon 3qrt rigar shirt me guntun hannu . Tare da fitowa, yana zama Samin yana kawo mishi tea, har ya ajiye zai tafi yace.
“D’auƙa kasha”
A razane samin ya juya cikin inda inda yace.
” Ranka shidaɗe ai akoshe nake”
Gyaran murya yayi sai ga Samudawarshi sun shigo.
“Ku bashi ya sha.”
Ina daga kitchen, wato abinda na fahimta mulki yabi jikin Ashraf baya iya tsawaita magana, dakyar maganarsa suke haura kalmomi uku huɗu.
***
*NIGERIA*
Abuja…..
Zaune take ta zurfaffa tuninta, hankalinta kwana biyu a tashe yake, sabida yawan mafarkin Feener da take, balarabiya ce kana ganinta kasan hutu ya zauna mata, dan ya ɓoye shekarunta. Wayart ta ɗauka a sannu ta latsa number. Dake da sunan
Bint
Abinda wannan yar babyn kamfanin wayar tasaba ce mata kullum yau ma haka tace mata, bata taɓa jin haushin yar babyn ba kamar yau(😂 ai babu abin takaici da ya wucce sai kasakanƙance zakayi hira su maka babu kosisin da zakayi hira😂)
Badar ta nima cikin damuwa, ta kirashi ɗauƙar ƙiran yayi tace.
“Badar bazakayi wani abu akan tafiyar Bint na damu.”
“Karki damu nasa a bincika mana inda take, harshi Anim ɗin ma yana kokartawa gun taimaka mana.”
Kaman yana gabanta gyaɗa kanta, sannan tace.
“Allah ya sa lafiya ne shirun nata dan bata taɓa yin haka ba.”
“Insha Allah, lafiya ne.”
Da haka sukayi sallama, Nannah tasa damuwa sosai a ranta musaman mafarkinta najiya, yafi kowani mafarki muni.
***
*JORDAN*
Shigowar Uzaif falon da sallama yasa ya ɗago kanshi dan yana shigowa yaga ana fita da Samin, zama yayi cikin cushion ɗin falon ya mikawa Sultan hannu suƙayi musabaha. Shiru ne yabiyo baya kafin Uzaif yace.
“Sultan! Amir yace kana nimana”
Idanunshi nakan tashar aljazzira new na harshen larabci, kaman bai san da zaman Uzaif ba, haka ya share ya cigaba da kallonshi, gyaran murya yayi sai ga Ghaniyu ya shigo.
“Umarninka nake jira.”
Maida bayanshi yayi ya jingina, sannan ya lashe lips ɗinshi cikin mugun miskilanci ya motsa da lips ɗin yayi magana kasa kasa.
“Ta kawo mishi ruwa.”
Juyawa Ghaniyu yaƴi ya shigo kitchen ya samu inata mita, gyara murya yaƴi sai da na razana, murmushi yaƴo sannan yace.
“Da alamu zaki amshi aikin samin domin mun kamashi da laifin yunkurin kashe Sultan, ki kawowa Bako abin taɓawa, dan Kawunsa Uzaif ne yazo.”
Kurawa Ghaniyu ido nayi sannan na taɓe baki nace.
“Hmm baya tunanin na shafa mishi baki.”
Bai kulani ba ya fita abinsa, haka na shake tire da abin taɓawa sannan na kai na dire a gaban Uzaif.
Ina ajiye masa na bar gun, na dawo abuna na cigaba da sabgana, ina kewar gida sosai.
……. Taɓa abinda na ajiye Uzaif yaƴi sannan ya sake maida hankalinshi gun Sultan, zai magana Sultan ya wurga mishi tambaya kamar haka.
“Me zakayi da dalla billion 450?”
Zufa ne ya shiga karyo masa, nan ya shiga cewa.
“Sultan! Dama za’ayi kwaskwarima wa masarautar za mucire tsofin kayan ciki kasancewa watan ramadan ya k’aratu, sannan zamu sauya wasu abubuwan.”
Mikewa Sultan yayi sannan ya nufi hanyar fita, cike da takaici Uzaif yace.
“Sultan tafiya zakaƴi?”
Girgiza kai yaƴi cikin ko in kula yace.
“Tsayuwa zanyi”
Ba yawa ba daɗi. Haka ya ficce yabarshi, bakin cikine ya turmushe zuciyar Uzaif, tunda yake bai tab’a gamo da mara mutunci irin Sultan ba…
*Yaushe Ya koma haka?*
Tambayar da yayiwa kanshi knn da hanzari ya bar falon….
***
Zaune yake gaban wani sirritaccen ɗakinsa, ya gama karanto wasu kalmomi, wani haske ne ya bayyana. Har sai da ya kare fuskarshi cikin kaskantar da kai yace.
“Ya shugabana! Yaron nan ya fara bijire min!”
Dube dube yayi, sannan ya ɗago kai, ” Akwai matsala ƙuma daga gareka ne, kabar sauran yan uwanka su more shi,dan yanzun haka Raziyah tana hanya dawowarta daga turkiya itace ta lalata naka aikin,, snnan Alexandra shima, ga Abu Zarri wanda shi yasa ayi mishi dole katashi tsaye kuma ka bar kange musu arzikinsu tunda kama kana ci.”
Buɗe baki Amir yayi zaiyi mgn Ra’ees yace.
“Yaki amsar tayi auren Sahela amma ya amshi tayi Adnan toh ai koda auren masa su akayi bazai zauna dasu ba dukkansu ba matansa bane, matarshi tana kusa da shi, kuma bata cikin ksbilarku. Itace zata zauna dashi babu dogon buri a tare da ita, amna shawara karku barshi ya shigo da ita dan tun kafin ya shigo da ita zata zabtare muku kimarku, sannan ka dakatar da Marhum yunkurin ganin bayan Ashraf tabbas nan gaba hukunci zata haura kanshi akwai zoɓen azurfa ka bashi ita a matsayin kyautar karin shekarar haihuwarsa ku haɗa mishi shagali ita zoɓe zatq kasance me jin umarninka ce ba tasa ba, karku sake ya shiga fadar domin idan ya taka ciki kome zai faru ciki har da abinda ya faru da iyayensa, kuma ya fahimci haka toh baki d’ayanku zaku zama baki a lahira hatta nima bazan tsira ba jiki magayi.”
Yana gama faɗar haka ya ɓace daga jikin Madubin.
……….
*Hello ina son ku duba yanayin labarin da kyau gabaki ɗaya daga Jazziratul Arab ne, naso aro sunaye ganin navawa mutane wahala a cikin Abu Khadija yasa nayi amfani da sunayenmu na yau da kullum, zaku ji dai bakon sunayen ya zama dole asaka ne Musaman Rania, itace matar Sarkin Hussein Muh’d na kasar Jordan a yanzun, sai irinsu Alexandra Angela, Zoya Sahela, da sauransu arone kasancewa labarin larabawa da Yahudawa ga kuma Kabilun Urud…… Nasan kafin ni akwai marubutan da suka shiga yankuna na duniya dan labari amma Labarin masarautar jordan, dabane sabida har cikin littatafan. Tarihi irinsu Siratu nabiyyina Muh’d (S.A.W) Islam biography, Islam dictionary da sauransu nagode da fatan zaku fahimce ni.*
#MJ#HZƘ#VOTE……Ku taimaka da Vote na fara jin lalaci fa😂
Oum Muwadda….
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: *_HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Page.١٠
Mik’ewa nayi Cikin Sanyi jiki. Ina kallonshi kauda kai yayi sannan yayi gyaran murya, ghaniyu me shigo cikin girmamawa yace.
“Umarninka make jira.”
Kamar bazai magana ba. Ya d’an motsa labb’ansa YA tauneta sannan ya d’an lasheta, kasa-kasa yayi da murya yace.
” ka canza min wani”
Kallon mamaki nake musu, Ina tsaye aka sake sabon kujera, zuwa yayi ya zauna tare da juya kan kujeran, bansan ya akayi tsaki ya kwace daga bakina ba, bai d’ago ba Dan yasan nice zanyi haka,
Mamakine ya ya rufe ghaniyu, tunda yake ba’a tab’awa sultan abu bai sa ayi hukunci ba sai yau, a madadin ya sallamemu sai ya kyalemu a tsaye ya cigaba da aikinshi.
Wasu takardu ya kwaso zai fara cike musu, dukda ban duba tarkadun ba, amma na fahimci na cuwa cuwa ce.
“Wallahi Allah sai ya tambayeka , abisa dukiyar alumma Da ake b’arnatarwa, anya kana tsoron Allah.”
Fuskarshi kawai zaka kalla ƙasan maganar ta buge shi sakamaƙon yadda jijjiyar goshinsa suke fito ɗara ɗara.
“Kai min ita ɗaki.”
Ji nayi cikina ƴa hautsine, ciƙe da damuwa Ghaniyu ya kai hannunshi zai kamo ni nace.
“Basai ka kaini ba! Ni zan kai kaina ka gane ai ba yau ka fara ba. Amma nasan daga yau bazaka kuma ba, idan nice kai basai san kaini ɗaki ba ko a iya nan zak….”
Ɗagowa yaƴi idanunshi har suna wani oil tsabar ɓacin rai gashi sunƴi jajjur.
Ya kalle kofar fita juyawa Ghaniyu yayi ranshi ba dad’i, har yakai bakin kofa ƴa juyo. Cikin ƙanƙar da kai yace.
“Ya shug….”
Yadda ya kalleshi yasa shi fitar dole, ji yake kamar kanwarshi za’a tozarta,
Takowa yayi gabana, ganin yadda nake haɗiye yawun tsoro, dukda shi ba ma’abocin dariƴa bane sai da ya sake fuskarshi, lashe pink lips ɗinshi yayi sannan yashafe kwantacciyar sajenshi, juƴawa yayi yabarni a gun.
Ajiƴar zuciya na sauke, sannan na koma kitchen fitar da bamuyi ba kenan, bamu kuma haɗuwa ba sai da karfe biyu, lokacin abincin rana. Yau a tantirance ya fito min dan daga shi sai gajeran wando iƴa gwiwa, da singlet fari ƙal. Sau ɗaya na kalle shi ban kuma ba, dan tsabar tsoro jikina rawa ya kama, kusan dalili sabida ban saba ganinshi a haƙa ba, ban saba ganin kanena suna wannan shirgar ba.
Gashin kansa ke ɗigar da ruwa, yana sauƙa akan karamin towel ɗin dake kafaɗarshi. Zare towel ɗin yayi ya cilla min a fuskana,
“Ƙambu” nace a fusace, *”Me wannan ɗan renin hankalin yaƙe nufi nice zan goge mas.”*
Buɗe mishi kular abincin nayi zubawa Mansaf ido yayi. Na fahimci ita yake so, zuba mishi nayi sannan na saka mishi falefale, a gefe sai dafeffen ƴ’aƴ’an zaitun da karas, wanda na ɗiga man zaitun da khaltufa.
Sai fruit juice wanda na jefa mishi ƙanƙara.
Kin cin abinci yayi, kanshi na duke.
Ɗaukar towel ɗin nayi naje bayanshi, jikina narawa na fara goge masa jekakken gashinsa. Wanda nake shakar kamshin sinadarin da aka wanƙe gashin da shi.
“Hand drie”
Sake goge kan naƴi na nufi ɗakinsa, ina zuwa nasamu akan gadon har na ɗauka zan fito sai na koma jikin mirorr ɗin na kai hannuna zan ɗauki mai sai na fasa wani ɗan karamin kwalbar turare na gani.
Tsautsayi yasani ɗauƙa, kaman wanda aka maƙe hannuna ya faɗi aikuwa ya fashe.
(🙊😏 Zaki sani bake wauta ba)
Zaro ido nayi, na shiga tattara kwalban. Na zuba a cikin mazubin shara, daƙe cikin ɗaƙin. Banda rashin kai irin nawa sai na goge turaren da ya taɓa hannuna, a jikina sannan nafito. Ina zuwa ya shaki kamshin turaren, cigaba yayi da kwasan gyara bai bi takaina ba. Tsauwar jiranshi nayi har ya ƙare cin abincinsa.
Sannan na jona wayar na fara busar mishi da gashin.
“Kinsan kuɗin turarene?”
Shiru nayi ban iya cewa kome ba dan nasan nayi masa ɓarna ko ma dai nawa ne,
Ina gamawa yayi gƴaran murya sai ga Ghaniƴu, komawa cikin falourn ƴayi, sannan yace.
“Ku kaita ɗakin horo.”
Zaro idanu waje nayi, kamar zan fasa kuka nace.
“Yarintar ta motsa ko?”
Banga fuskarshi ba amma ina da yakinin yaji ciwon abinda nace masa,
………
Fita dani ghani ƴayi, sai da ƴa masifance ni, sannan yace.
“Don Allah ki bar lakatanshi, sam bai san meye kawazuci ba.”
Dariƴa nayi sosai nace.
“Toh ai gashi a bayanka.”
Hmmm Sultan Ashraf mugune na bugawa a jarida, dan daga ni har Ghaniyu jikinmu sai da yayi laushi kuma ya sauyawa Ghaniyu gun zama zuwa bakin get, aka kawo wani me kiran mutanen farko Irifan.
Gaskiya zan iya daga jiya zuwa yau na zama kamar jaka, matsalar da na fara fuskata shine Irfan ɗan iskane, dan koda ɗakin horo zai kaini toh ƙoƙarinsa yakai hannunshi kirjina.
***
Ƴau saura kwana uƙu bikin murnan zagayowar ranar haihuwar Sultan wanda aka shirya a babban falon shashinsa.
Sun kawo takardun list ɗin abinda suƙe bukata na gyara falon da Cake ɗin da za’a kawo mishi na ranar, zunzuruntun sun kware a sata, wasu mahauƙatar kuɗin suƙa yanka mishi.
Kai tsaye ya soƙe musu yasa abinda yake ganin shi zasu buƙata.
…… Sunji Haushi dan wanda ya kawo takardun Abil ɗan Raziƴa. Da fushi ya nemi barin gidan amma ya dakatar dashi.
Kawo mishi ruwa nayi zan wucce naji ya kai min duka a baya, juyawa nayi na tsinka mishi mari. Fuska Sultan yayi ya cigaba da kallonshi, kamar baya gun, yasa fuska. Mikewa Abil yayi cike da mamaki yadda na zabga mishi mari, amms Sultan bai ce kome ba.
Finciko ni yayi tare da murɗa min hannuna sai da kashin yayi kara. Ihu na saka ciƙe da jin azabar a hannuna, bai fasa ba murɗa min hannu ba har sai da yaga ina kuka sosai sannan ya hanƙaɗe ni na faɗi, sake take min kafa yayi, ihun da naƴi ne sabida ji min ciwo da yayi a yatsun kafana,
Bai ƙƴale ni ba sai da yaji min ciwo a duk kafa, sannan ya suri takardan yace.
“Na kƴaleki amma kika ɓari na kamaki, sai na jiyar dake azabar da baki taɓa gani ba, dama ance ku kajin african sunfi na ƙo ina zaki dan.,”
Gyara murya Sultan yayi sai ga Irfan ya shigo, ciƙin girmamawa yace.
“Gidan ladabtarwa zaka kaishi”
Aikuwa suka kaɗa keyarshi zuwa gidan ladabtarwa. Mikewa yayi ya bar falour, dakƴar na iya jan ƙafana zuwa kitchen. Nayi kuka sosai dan sai da na gasa kafar. Dukda ciwon bai sa Sultan hakura da abincin dare ba sai da na abinci mara nauyi….
Ƙin ci yayi ya sunkuƴar da kanshi yana latsa wayarsa. Ga azabar ciwo ga wulakanci, na koma cikin sauri na fara ƙoƙarin ɗaura wani sai jin murƴan mutane suna dariƴa irinta abota. Kaman ance na leko Sultan ne da wani matashi me sanye da kayan gidan abinci. Murmushi kawai yake doƙawa, mutumin sai dariya yake,
Suna hira zuwa yayi gun dinne table ya ɗauki filet yaje ya juƴe abinda ya kawo masa, yasa a gaban sultan ɗin.
Maqbul ce sai kamshin citta da garlic yake, ji nayi raina yayi mugun ɓaci ina can ina fama ciwona ashe ɗan renin hammatan yana can yayi odar abinci.
Sauke abinda na ɗaura nayi na zauna akan kujera, ji nayi duk na kuntatta baki ɗaya,
…… Ina jin hirar su har suƙa watse, amma baƙon yafi surutu, dan ɗan akida baya faɗar kalmar da ta haura uku,
***
Washi gari da safiya, sai ga Amirah Raziyah tazo, bansan shigowarta ba sai ji nayi an rufe ni da duƙa, ta ko ina.
Duka sosai yana ɗakin motsa jiki yaji hayaniya, shine ya fito har zuwa kitchen ganin kanwar Mahaifinshi tana ɗaukar doka a hannu kamar yadda ɗanta ya ɗauki yayi rashin hankali.
“Ina jiranki idan kin gama.”
Yau kam naji har ya kara da na kullum, juyawa tayi a fusace tace.
“Ashraf! Akan me zaka sa a wulakanta min D’ana.”
Ba kulata ba yayi wuccewarsa ciki biyoshi bayanshi tayi, kamar zata tashi sama.
D’akinshi yashige bai fito ba, sai da ya share awa biyu cur, sannan ya fito ƴa zauna gun cin abinci, buɗe abinci nayi.
Kallon roasted nut yayi da kuma, soyayyar kwai, sai golden macarroni, wanda na dafa da namar gwangwani, na zuba masa, mai da dubansa yayi kan butar Coffee, garin zuba masa kwalla da suƙe zuba a idanuna ya zuba cikin tea ɗin, duk abincin haka kwallana ya sauka a cikin.
Mika min towel yayi nazo bayanshi ina goge masa gashin kansa, Amirah Raziyah ce tazo ta zauna, daƙe bai bani damar nasa mata ba, ita da kanta ta zuba kome. Tana shirin fara ci sai ga Amir Ukshe. Zama yayi shima, Amirah ta zuba mishi abinci.
“Hand…”
Bai kai karshe ba na bar, ina gab da shiga ɗakin yace.
“Don’t touch anything.”
Shigewa nayi, kallonshi sukayi sannan suka maida kallonsu ga junarsu.
Kowannensu yana fatan samun nasara akan abokin gwabzawansa.
Ina shiga naga wata arniyan suit ɗin da zai saka, silver ce tayi kƴau iya kyau, kallon laptop ɗinshi nayi wacce take kunne, haka kawai naji ina son duba. Email ɗina tunawa da nayi yace kar na taɓa kome, ya sani juyawa, aikuwa mukayi karo dashi. Inda kaina ya bugi kirjinshi bai damu ba ya raba gefena, ya kalle ni da wutsiyar ido, a ranshi yana cewa.
*Bata jin magana*
Fita nayi ya ɗauki files ɗinshi, ƴa fito ƴazo ya same ni a tsaye zama yayi naje bayanshi na fara aikina, ina gamawa na bar gun dan na lura da magana a bakunansu.
Ina barin gun kuwa Amirah Raziyana ta ajiye coƙalinta tace.
“Ashraf!!!”
“Sultan zaki ce” kanshi a duke yayi maganar kamar bashi ba, cikin kuluwa tace.
“Naji Sultan a wani hujja zaka rufe ɗan uwanka? Me yasa baka abu da tunani ne, ka rufe min yaro”
Miƙewa yayi ba tare da ya kallesu ba yace.
“Ina son zama daku?”
Mikewa Amir Ukshe yayi cikin ƙanƙar da kai yace.
“Sultan! Gobe zagayowar ranar haihuwarka, wanda yayi dai dai da ciƙa shekaru ashirin da shida a matsayin sarkin Jordan na huɗu.”
Gyaɗa kai yayi sannan ya juya, yayi taku biyu cike da kasaita yace.
“Gobe!!! Ranar zagayowar Mutuwar Iyayena!!! Gobe zan buɗe fadar sarkin Jordan A Gobe Inshs Allah zanƴi abubuwan da na gaza yinshi na tsawon shekaru da dama”
Juƴawa yayi abinsa yabarsu tsaye,
” Tabbas ƙome zai lalace gobe”
Inji Raziyah,
Taku kaɗan Amir yayi cikin ƙaɗuwa yace.
“Zan dakatar da kudirinka gobe.”
Fita suƙayi cike da tashin hankali fitowa nayi cikin murmushi nace.
“Insha Allah nan da wata biyu zan rabaku dashi.”
Kowa idanunshi ya rufe, musaman Amir da Ra’ees ya gargaɗeshi akan kar su bari Sultan ya shiga fada, yau gashi ya ambaci mutuwar iyayenshi da maganar mulkinsa kenan dole ƴau ya nemi ra’ees.
Itama Raziyah tana komawa gida takira bokanta na Turkiya…..
Ɓangaren Sultan kuwa tunda ya shiga binciƙe a laptop ɗinss…..
_Alƙawari ya ciƙa ƙo…..Burinsu d’aya muradinsu ɗaya…. Nashine ya banbamta da nasu….Itama nata burin nan….Nawaye zai ciƙa_
”’Allah nagaji……Kuƴi manege idan nasamu hali toh amma banyi alƙawari ba…..dan bana ɗaukar alƙawari…..✌”’
*#MJ#HAZAƘA#VOTE*
Oum Muwaddah
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
_Fatan alkhairi gareku yan team ɗin A koyar da ita yadda ake magana😂 Wato Sultan Ashraf….Sister Meerah Uwar ɗakin Sulfeena, da Kuma Yar ɗakin Ashrafeena Rukayya Abdul…. Ga kyautarku nan_
Page.٩
Gabaki ɗaya ji yayi hankalinshi yayi mugun tashi, ranshine yayi masifar ɓaci. Badan karya saɓawa Ra’ees ba da….. Sai kuma ya mike daga zaman da yake yasaka kayansa dan dama zaune yake daga shi sai wani jan kwarjalle, (Wato kwarjalle daga yanki Asia aka amfani dashi zaku sai danfarin kyalle da yan kudancin india suke amfani dashi a film ɗinsu) shine a jikin Amir.
Yana gamawa yafito, ta cikin uwar ɗakinshi. Waje ya fito tare da wasiwasin abinda Ra’ees ya faɗa mishi, kawai sai yaji bai amince da maganar Ra’ees ba karo na farko a rayuwarshi, mikewa yayi ya koma ɗakin ya buɗe inda Ra’ees yake ajiye masa abu nan yaga zoɓen ɗanyen azirfa. Dauka yayi yana kallon zoɓen wanda aka zagaye samanshi da jan Diamond, dan kyau zoɓen ya haɗu. Dauka yayi yasaka a cikin aljuhunsa sannan ya dawo falourn inda yasami Uzaif yana xaman jiranshi,
Kallon Uzaif yayi sannan ya zauna tare da mai da hankalinshi ga baki ɗaya kan Uzaif.
“Abbie!”
D’aga mishi hannu yayi cikin tsukewar fuska yace.
“Kacewa Marhum ya dakatar da abinda yake, in ba haka ba duk abinda ya dawo mishi yayi kuka da kanshi.”
Gyaɗa kai Uzaif yayi, sannan yace.
“Abbie maganar fidda kuɗin nan Sultan ya nemi hujja”
Kurawa Uzaif ido yayi kafin ya janye, kamar bazai ce kome ba.
“Me kace masa?”
“Abbie wallahi bansan me bakina yace ba dan Yaron akwai wani ɓoyayyen sirri a tare dashi.”
“Ba tambayar da na maka ba kenan me ka gaya mishi nake son sani.
Shiru yayi sannan ya faɗa mishi yadda sukayi da Sultan.
“Hmm” kawai Amir ya iya cewa, sannan ya sallame Uzaif.
Bayan fitar Uzaif juya alamarin Sultan, yake tabbas akwai matsala, matuƙar ya bari su Raziya sukai galaba akanshi har abada bashi da ikon akan Masarautar dan itama bata ki abata mulkin ba.
……
Fitar Uzaif gidan Marhum ya wucce, gaisawa sukayi sannan ya gaya mishi sakon Amir, riƙe yake da kofi me ɗauke da taceccen inabi, bai san lokacin da ya maka kofin da kasa, sai da ya tarwatse baki ɗaya.
Zubur ya mike ranshi a ɓace.
“Wani munafukine ya gaya Abbie ina kaiwa Ashraf hari?”
Juyawa Uzaif yayi yabar falourn, dan shi bai damu da mulki kaman yadda Marhum da Mahaifinsu suka damu mulki ba.
***
*NIGERIA*
Abuja…..
Tashin hankali ya dadda samun mazauni a cikin gidanmu musaman da aka rasa inda Nake, dukda Ummi tana ɓoye damuwarta bai hana ranar da Labari yazo musu bana makarantar da naje yi a kasar waje sai da ta yanki jiki ta faɗi. Hajiya Nuratu ta sake dariya sannan tace.
“Eh k’uwwa bayan hari kuke, yarinyar da ta tafi karuwanci kuke damuwa da ita! Ku jira idan tazo muku d….”
“Amma Nuratu baki da hankali, da kike faɗan haka meye ribarki. Kodan Allah bai baki mace bane, amma ai ga yaran da kika ɗauko riko kalamanki zasu koma kanki.”
Inji Hajiya Amnah.
Dukkansu Ummi najinsu amma bata jin zatayi magana, ita fatan ta ɗ’aya na dawo gida lafiya,
Shigowar Nannah shi ya tilasawa Hajiya Nuratu tayi shiru, cikin mutuntawa suka gaisa. Sannan ta zauna tana tambayar ya Ummi taji da jiki, duk suka ce da sauki. Shiru ne ya gitta a tsakaninsu, can sai ga Matar Abdullahi da yaranta, hannunta ɗauƙe da basket ɗin abinci itama tashigo zama tayi ta gaishesu.
Sun jima sosai kowannesu da abinda yake juyawa a ranshi…
Da dare Anim yazo ya gaida Ummi bayan yafitane ya samu Abba da maganar yasa a bincika sosai dan an samu ganin kiran da nayi daga U.S zuwa dubai daga nan ba a kuma ganin wani wani motsi nawa ba…
Sun jima suna tattauna batu akaina, kafin suƙayi sallama.
***
*JORDAN*
Haɗin girki na fara hankalina kwance,
Ina na fara kokarin dafa Felafel cikin kwarewa na fara haɗawa, ina gamawa na juye a cikin wasu manyan kuloli, sai lemonada. Shi kaman shaka yake.
Sai Zarb bbq wanda nayishi da naman karamar daba.
Fitarwa nayi, naje na jera akan dinner table, haka na ɗauki kwalɓar ruwa na kai, sannan nazo na fara cin abincina, ina ci ina jin wani iri a raina dan yau jina nayi a jikina ana nima na, gashi ina niman kusan wata bakwai, dan a yanzun wata huɗu a cikin masarautar, watana uku kafin shigowa cikin masarautar gashi bani da hanyar da zan samu labarin mutanen gidan tunda bani da y’ancin fita.
….. “Ke Yar African kizo Sultan zai ci abincinki.”
B’ata rai nayi cikin gatsali nace.
“Idan banzo ba ya kwana da yunwa.”
Zaro ido mutumin yayi kafin yace.
“Ni bazan iya kai sakonki ba, dan ina da yara da kanne mata, ke zaki iya kaiwa da kanki ko kuma na ɗauke ki dan naga rashin aukinki yafi…”
“Wato baka tsoron Allah sai wancar yaron?” fita yayi ni kuwa na cigaba da cin abincina, ina gamawa na mike tare da wnke hannuna, na fita.
Ina zuwa na same shi ya maida kujeran baya sannan ya ɗaura ɗaya aƙan ɗaya, idanunshi ɗauke da medical glass yana duba jarida.
Zuwa nayi na tsaya a tsaye akanshi, yaji zuwana amma yayi kaman bai san da mutum a gun ba, nima kuma ina jin shariya ne dan haka na cigaba da tsuyuwa, ni a tunanina yunqa zata sashi min magana, karshe mikewa yayi yabar min jaridar a gun yafita.
Kaii jama’a wallahi ban taɓa ganin ɗan renin hankali irin Sultan Ashraf ba, tsakani da Allsh cikinka ma sai ka nuna masa kai ɗan jan wuya ne.
…… Karshe haka na juyewa su Ghaniyu, dare ma haka da na gama na same shi ne a zaune ina gama jerawa ya mike, gyaran murya yayi su Ghaniyu suka shigo.
“Umarninka muke jira.”
“Ku kaita gun Azrah.”
A gaba suka sani har shashin bayi, inda suka kaini gun tsohuwar nan, tsayawa sukayi a bakin kofa. Na shiga na samu tana sallah. Zama nayi ta idar sannan muka gaisa, kallona tayi tana murmushi tace.
“Yau kece kika kawo min ziyara? Hmm anya ba Sultan bane ya aikoki.”
Gyaɗa mata kai nayi, alamar eh. Matsowa tayi kusadani ta riƙe hannuna tana kallona, tare da cewa.
“Bansan me yasa nake jin bakin ciki idan naga yadda kome yake tafiya na rayuwar Sultan a hangunce bayan nasan kome amma bani da ikon yin kome akai, kodan nice nayi renonshi daga lokacin da aka kaini a matsayin me kula dashi ba, ina rokonki idan har biyanki akayi ki cutar dashi don Allah ki taf…”
Shiru tayi can kuma tace.
“Kiyi hakuri na tsaya ina miki shirme, akan abinda bai shafeki ba. Zaki kiyayye abubuwa guda goma sha ɗaya, na farko idan kika gama abinci kika jera zaki tsaya a gun har lokacin da ya fito, na biyu zaki buɗe kwanonin abinci yaga abinda yake so, na uku zaki maida hankali akan abinda idanunshi ya tsaya akai, na huɗu baya cin yaji da gishiri, yafi son ganye da y’ay’an itace, na biyar baya cin abinci a kala d’aya inso samu ne kiyi sama da kala biyar, sannak yafi son ruwan kankana da abarba, na shida idan kika saka masa zaki fara ci, dukka abincin. Sannan na bakwai zaki tsaya akanshi gudu kar ya kware, na takwas zaki na bashi kananun labari wanda zaija hankalinshi yaci abincin sosai. Na tara dole ki zama me hakuri dashi dan koda yaci abincin in bai masa ba zai dole ki sake dafa masa sabo, na goma idan ya gama godiya zaki masa sabida cin abincinki da yayi abu na sha ɗaya idan ya shiga ɗakin motsa jiki zaki bishi da ruwa tare da karamin towel sai y’ay’an itace d’akinshi kam akwai masu kula dasu iyakarki falourn ɗinsa.. Wannan shine dokokin ciyar da Sultan Ashraf.”
Shiru nayi ina lissafo duk uban bayanin da tayi min, wanda nake jin babu ɗaya da zan iyayi tsallakewa, dan saura wata biyar na bar kasan koda ban same kanshi ba zanyi kokarin masa abinda dole wata rana ya nime ni. Toh meye kenan, mutum ba sakin fuska ba, ba hira….
Dafa kafaɗana tayi cikin tausassiyar murya tace.
“Ban sanki ba! Amma tunda naga ya turoki akwai wani abu na daban, kiyi hakuri da zama dashi sabida. Ya tashi babu kowa a tare dashi sai ni, nima ɗin iyakata kula dashi amma an hananin shakuwa dashi, balle na nuna mushi muhimmanci rayuwa, akwai binannun abubuwa sosai, tashi kije.”
Mikewa nayi nasakai na fita dan jikina yayi mugun sanyi,
shi yasa yake abubuwa son ranshi bai tunina, toh me yasa Nannah taki gaya min kome, akwai abinda Azrah tasani na rayuwarshi amma tsoro da gudun faɗawa damuwa yasata yin shiru, meye yasa toh? Me take ɓoyewa akanshi, indai zata shiga damuwa akanshi tabbas akwai, ɓoyayyen alamarin da yafi karfinta. Dan haka kawai bazata tayi kokarin sanar min da wasu abubuwan da ke damunta ba,
*Shin Meke faruwa ne A Masarautar Jordan?*
Abinda na tambayi kaina kenan babu amsa, tunda ba wani na ajiye zai bani amsa ba.
***
Washi gari sai da na kusan makara, dan jiya da tunanin waye Sultan Ashraf na kwana, da gari ya waye na shiga haɗa mishi abin karyawa, banyi wani abubuwa ba dan babu lokaci..
Ina gama jerawa yana fitowa, ina tsaye a gun yazo saka mishi nayi, sannan nabi kan abin karyawa na ci, ɗaukar fork yayi yare da karamin wukar cin abinci ya fara cin y’ay’an Zaitun da na dafa, sannan ya shiga cin sauran abincin a yangance yadda yake taunar kaman wadda bakinsa ke ciwo tsayuwa nayi ina kallon abin mamaki dan ina kallon maza a rayuwata karo na farko da naga wanda yake cin abinci a yangance kamar ba cikinsa zai saka ba, ita kanta ruwan da zai sha kurɓa ɗaya ake mata a ajiye, wato babu abinda mulki bai sawa mutum yayi. Kaɗan yaci yasha ruwan coffee mara madara shima kurɓa yayi yabar sauran. Sannan ya mike tare da barin falourn da uwar harara na rakashi, wallahi bani bin kowani dokarka, dan baga dalili ba.
Haka na tattara abinci, nakai kitchen, sannan na dawo naga Ghaniyu a tsaye kamar bazance kome ba can nace masa.
“Lafiya?”
Girgiza kai yayi sannan yace.
“Meye ya haɗaki da Sultan?”
Zaro ido nayi ciki fargaba nace.
“Meye kuma nayi.”
A raina nace.
*Muguntar sarki Zalimun ya motsa kenan yau*
Shiru yayi ganin yadda na ke kokarin ɓoye tsorona, yace.
“Wai idan kin shirya akaiki kasuwar zamani ki duba abinda kike amfani dashi na yau da kullum.”
Boyayyen ajiyar zuciya na sauke sannan na koma kitchen ɗin na kintsa kome, na wanke hannuna, ina fitowa na kalle tulin takardun da suke kan table ɗinsa, page na ɗauka da biro na zauna akan kujeran shi na shiga, rubuta abinda nake bukata, kamshin turarenshi yasani ɗaga kai, yazo zai zauna kawai yaga na ɗare kujeran inata rubutu, shine ya koma gefe ya coge, tare da harɗe hannunshi a kirji,
(Ina ruwan shiga uku fitar takaba da molo😂)
#MJ#HZƘ#VOTE nd Share…….
Oum Muwadda…….
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: I just published “Page.١١” of my story “MASARAUTAR JORDAN!!!”. https://my.w.tt/zCGf0qyIi3
*_HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Labarin yasha da sauran_*
Sadauƙarwa ga masu ruɗewa😂😝
Page.١١
Washi gari aka tashi da shagalin musanman irin nasu na larabawa,shuwagabanin kabilu sun zo har cikin dakin taron masarautar. Tun safe da na gama abin karyawa yazo ya karya na goge mishi gashin kanshi, ya koma ciki ya sanya farar jallaɓiya, da alkƴaba ruwan zai ba. Wato golden coloure. Takalmi kamfanin Gucci yasaka. Ina cikin gyara falon ya fito.
Kallo d’aya nayi mishi a hankali na furta “Masha Allah.”
Yau kam fuskarshi a sake kana gani kasan akwai Burbushin mutunci.
Zama yayi na zuba mishi aBinci. Yaci sosai sannan ya ɗago kanshi ya kalleni a sace sannan ya kauda kanshi yace.
“Gyara min ɗakin”
Ɓata rai nayi bansan lokacin da na tura bakina ba, ina magana kasa kasa.
“Yau ina cikin jin daɗi bani da loƙacinki amna Irfan zai min maganinki.”
Shiru nayi dan natsani ya haɗini da Irfan ɗin nan. Ganin yadda na shiga hankalina yashi mikewa ya fita, da harara na rakashi cikin. Mita nace
“Yau anyi abin kai fitsari da kumfa.”
Ni ɗaya sai mita nake da na gaji na zauna akan kujeran gun cin abincin na shiga tunanin gida, dan nasan ban kyautawa iyayena ba. Da Anim me zance musu idan na ka gida, ina naje? A gurin wa na zauna? Wannam sune tambayar da suke hanani sukuni, musanman idan na tuna da halin da Ummina zata shiga, ko a wani hali taƙe oho?
***
“Karka bari wani ya raɓe shi, dan yin haka zai haifar da damuwa. Ukshe ka kiyaƴƴe maganata, na gaya maƙa ka kiyayye maganata, na kuma gaya maka ka kiyayye maganata.. Na rantse da abin bautana idan ka kiyeyya abinda na gaya mulkin kasar jordan ya haramtawa Ashraf ka kiyayye maganata, kuma kayi ɗamara dan yanzun jordan zata dawo karkashinka, amma sai ka fuskanci kalubale daga kabilarƙa.”
Gyaɗa kai Amir yaƴi cike da farin ciki yace.
“An gam…”
“Ba an gama zaka ce ba. Ukshe rayuwata na bada sabida kai, ko min kashin ƙusƙure mutuwa zanyi, ƙuma zan ɗauke hankali mutane akanshi yadda zaka manta da shi baki daya, Ukshe karka bari kowa ya raɓe shi.”
Kusan kashedin da Ra’ees yayitawa, Ukshe kar asami matsala dan rayuwar ra’ees ne a cikin hatsari, sakamakon wani shirin da yayi na kawar da Ashraf daga mulkin ƙasar Jordan.
……… “Abu Zarri! Yaron nan yau zai shiga fadar can fa.”
Murmushi Amir Abu Zarri yayi sannan yace.
“Bani da matsala dashi, kuma ai dama ance yana cika ashirin da tara zai amshi mulƙinsa, kuma ya ciƙa gara ya amshi mulkinsa. Ko wasu zasu rage son zuciya.”
….. Karamar dariya Amir Uƙshe yayi sannan, yace.
“Kana ƙoƙarin adana ɓacin ranka, nan gaba ma sai magana yafi karfinka, ka gya…”
Shigowar Ashraf cikin ɗakin meeting, yasa shi yin shiru tare da mikewa tsaƴe. Masu kula da lafiyarsa suka ja masa kujeran.
“Bismillah.”
Ya furta a hankali, idan baks lura da leɓɓansa da suka motsa, bazaka fahimci basmalla yayi ba.
Ajiye masa yar briefcase ɗinshi akayi, ya kare musu kallo sannan ya buɗe jakar a hankali ya zaro takardun ya ajiye a gefe, sannan ya ɗago kai yace.
“Gashi ku nemi sauran ku basu.”
Mika musu takardun irfan yayi, suka gama dubawa sannan Abu Zarri yace.
“Doka ta goma da ta sha ɗaya batayi tsauri ba, sannan yaushe zamu yarda mu bawa Yahudawa dam..”
“Dokata ce haka”
Murmushi Amir Ukshe yayi sannan yace.
“Banga wani abin d’aga hankali a nan ba, dan ni dokar tayi min.”
“Kace doksr tayi?” ya wurgawa Amir Ukshe tambaya,
Gyaɗa kai yayi, cikin gamsuwa Sultan ya ciro wani takarda ya turawa Amir Ukshe, yace.
“Case ɗin Angela”
Dauka yayi yana dubawa, sake tura mishi wani yayi cikin sanyin murya yace.
“Wannan kashedin Marhum ce”
Dauka Amir yayi yana dubawa, cikin sakin fuska yace.
“Insha Allah haka bazai sake faruwa ba, yarinya taci albarkacin sarki ya shiga Fada, mun gode.”
“Sultan!! Ka janye bawa Banu Nazir muƙami, gwara Banu Hussein dukkansu musulmai ne.” inji Amir Abu Zarri
“Duk yadda kuka gani.”
Shiru sukayi Abu Zarri ya Amshi takardun ya suƙe, wannan sai na gomane ya bari dan shi an saka babu bambancin Kabila duk wanda aka kama da laifin ya kashe wani da gangan hukuncin kisane,
doka ta farko ce idan aka kama wani yayi yunkurin kashe sarki hukuncisa shima kisace, doka tabiyu kuma, duk wani shugaban da aka kamashi yana bin bayan me laifi zai sauka a mukaminshi ne kowaye shi kuma ba iya sauƙa ba har sai ya ajiye taran kuɗi, sannan ana jan kunne da cire ƙuɗi a baitul malin masarautar.
Daga ɗakin taron ɗakin shagali Amir Ukshe yajashi suƙa tafi. Inda yasamu mutane musanman attajirai da wasu daga kabilu guda biyun nan.
***
Bayan tafiyarshi akazo aka korani zuwa, shashin bayi, nayi mamakin faruwar haka. Amma ban d’aga hankalina ba, nasan kodan cikinsa zai nime ni.
……. Bazance me ya faru ba, sai dai naji kishin kishin ance yabar garin, ya koma gun aikinsa.
Yau kwana biyar kenan, kullum sai anzo an ɗauki yan matan ɗakinmu ba, ba’a dawo dasu sai dare. Ashe da ina cikin kariya ce zamana a shashin Sultan ƴanzun kuwa, ina cikin hatsari domin kuwa sau biyu ana farmaka na,
Karshe komawa d’akin Azrah nayi, naje na zauna. Ita kam ana ɗan shakkarta.
Maidani kitchen akayi na cigaba da aikina, sam hankalina yaki ƙwanciya da tafiyar da akace Sultan yayi.
Azrah nasamu da cewa.
“Mama! Hmm nifa ina jin akwai matsala zanje na duba gidan Sultan.”
Shiru tayi tana kallona can tace.
“Ki bari mana idan ya dawo sai muje dake ko?”
Gyaɗa mata kai nayi badan nason ba, dole na hakura dan kwanakin da zanyi ya fara karatowa, dan yanzun saura wata ɗaya da sati biyu.
***
Sati biyu da suka wucce.
A ɓangaren Sultan kuwa, tunda ya shiga gun shagalin aka cigaba da hidima, har loƙacin sallah ya wucce, bayi ba, sai dare wajen sha biyu ya koma gida, dake sun sunja hankalinsa sosai har yasha wani ruwan inabi, tun daga sa’ilin yaƙe jin shi a buge, koda ya dawo gidan dakyar yayi sallah ko addu’a bai yi ba, ya kwanta.
Tunda ya kwanta yake jin wani irin sanyi, a hankali yaji wani iska me karfi ya shige shi, bargo yaja ya rufe kanshi.
Daga nan kuma bai same ke faruwa ba.
Washi gari da asuba Amirah Raziyah tazo taga halin da yake ciki tafita bayan ta kwashi kusan awa guda a cikin gidan. Da karfe goma Amir Ukshe yazo. Yaga halin da yake ciki jan kofar shiga gidan yayi ya rufe.
A sannu gidan ya koma kamar irin mugayen gidan nan matattaran shaidanu. Gidan yayi wani irin datti, yanar gizo gizo. Sannan daga nesa kaga gidan zaka rantse yakai kimanin shekara ɗari ba kowa, sannan Masu tsaron gidan ma Yanzun ba kowa, suma sun koma cikin fada.
****
A cikin wata guda kome ya nemi lalacewa, daga ciki har da samun gawar Angela, wacce Sultan ya saƙeta.
Wanda ya haifar da wani irin rigima, gashi yaki ci yaki cinƴewa dan kullum sai anyi kamar za’aƴi bata kashi. Karfi da yaji Amir Ukshe yake gudanar da Zalimci. Da Abu Zarri yaga haka shine yaje har gidansa nan ya samu Raziyah itama tana ruwan bala’i.
Cikin son zaman lafiya Abu Zarri yace.
“Meke faru? Sannan ina Sultan? Me kuke ɓoyewa.”
” Me kuwa zan ɓoye muku bayan kunsan baya gari kunemi shi mana.”
“Wannan shine karya! Kai kasan me ka masa.”
Inji Raziyah.
Duk yadda suƙa so Ukshe yayi magana yaki sai suka shiga, koƙarin sanin gaskiya.
…….. Nima nayita bin Azrah amma taki bani goyan baya, abinda na fahimta akwai abinda taƙe ɓoye mim dan har anzo an min barazana za’a kashe ni matuƙar na shiga maganar sultan.
Nayi Imani da Allah akwai me ƙoƙarin kai gulmata, dan haka na shirya ranar bayan sallahr asuba, dake kitchen zan nufa sai na fita daga gidan na wucce gidan shi, dakyar na shiga, sabida yanar gidan. Ina tafiya sai naji abu ya wucce da bala’in gudu ta bayana ina juyawa zanga ba ke.
A haka har na tura kofar ɗakinshi bakina ɗauƙe da ayatul ƙursiyu.
Ihu akayi wanda ya tada tsigar jikina, har sai da na toshe kunnena.
“Meye ya kawo ki duniyata. Nasame gangan jiki zaki zo ki rabani dashi.”
Dif naji an faɗo a bayana ina juyawa na ga Ashraf a cikin mugun yanayi ihu na saƙa, aikuwa yayi wurgi dani sai da na bugu da bango. Gabaki ɗaƴa jina da ganina suƙa ɗauƙe na wuccin gadi.
Tsalle yayi ya diro gaba, kafin na yunkura yasake kwallo dani, sai da na bugu da gadon sosai.. In samu arzikin ihu ma gatane, ƙoƙarin shiga.kasar gadon na fara yazo ƴa finciƙe ni ya cillani da jinki mirorr, tsabar wahala har sai da nayi aman jini.
Ya karan buɗe kofa naji idanuna dishi dishi, banga waye ba. Sabida bana gani sosai.
Gurnanin shi naji ashe wai nima yake, dan gun mirror ɗin aƙwai shirgin da ya tara, mikewa nayi tare da kama jiƙin mirror sai gashi dif kamar an jiwo shi daga sama, ja da baya na fara, ina son yi addu’a amma bakina yayi nauyi.
Cafke wuyata yayi dan wani irin zafin yake da kafin kayi wani yunkuri ya cin maka.
Ina ambaton Allah ihu yayi tare da cillar dani , na mike zan fita mukayi karo da Ghaniyu, da sauri ya cilla ledar da yakawo mishi, sannan ya jani muƙa fita.
Ya kulle ƙofar, sai da muka bar cikin gidan ya hankaɗani cikin tuhuma yace.
“Ba yau na fara zarginki ba, dan sam baki kama da baiwa ba ƙo wacce ta tashi cikin wahala wacece ke?”
Goge jinin dake baƙina nayi sannan na sunkuyar da kaina.
“Bazaki min magana sai na kaiki gun Amir Ukshe?”
Idanuna ne suka ciko da kwalla nace masa.
” Safinatu Badr Ibrahim”
Kura min ido yayi cike da mamaki yace.
“Ke! Wani hauka ne ya kawo ki nan, haba shi yasa kika nace da yawa ashe ke Jinin Badar ce toh zan baki shawara ki haɗa kayanƙi ki bar garin nan ko kuma ki su wulakantaki.”
Girgiza kaina nayi cikin gaji nace.
“Babu inda zanje, dan nayi alkawarim sai na maidawa Nannah D’anta.”
“Kin hauƙace?”
“Eh da alama amma bacan can ba, yawwa kaga halin da yake ciki ƙo zaka taimaka min ka nima mana malamin da zai taimaka mana ayi jinyarsa dan naga abin nashi kamar jinn n”
“Lallai baki da hankali nima zuwan da kika ga inayi, abinda zai ci nake kawo mishi idan aka san cewa muna zuwa nan dagani har ke sunanmu matattu. Kinga muje kafi.”
Kwace arm ɗina nayi da ya riƙe, cikin ɓacin rai nace.
“Me kake kawo mishi?”
Katsaye yace min.
“D’anyen nama.”
Ban san loƙacin da amai ya tazo min ba, sai da nayi tukun nace.
“Wani irin rashin imani ne haka? Taya zaka bawa mutum me rai ɗanyen nama?”
Cikin damuwa ya kalleni sannan ya ce.
“Amir Ukshe ne yasani dan har da jin..”
“Jini??? Kamar mayye sabida Allah zaku maida ɗan adam kamar Daba aiko kuraye da karanunka basa shan jini, ni dai ka nimo min, gidan wani malami mu kaishi idan bazai yuwwu ba mu kaishi ba, sai ina aka taɓa yin haka.” na faɗa cikin faɗa.
Kallona ya tsaya yi ganin yadda na kafe kamar kaska, ajiyar zuciya yayi sannan yace.
“Zan nima miki amma babu ruwana.”
“Ai idan zaka cire babu ruwanka ka cire , domin ana kama ni kai zance kasani ka gane.”
Kallona yayi ciƙe da takaici yace.
“Amma baki hankali ke mahaukaciyar ina ce? Da zaki min sharri”
Gaba nayi abuna dan nasan dole yayi min abinda nace Har na kusan fita yace.
“Karki a ƙowa yasani amma ki faɗawa Azrah” nan ne na cibirki na juya na gaya mishi yadda muƙayi da ita.
“Eh ai nasani dan mun yanƙe hukuncin karmu gaya miki sabida yadda kika damu akanshi.”
zaro ido cike da takaici nace.
“Ta ina na damu? Kawai naga bai dawo da wuri bane shine nake tambayarta.”
(😾 Malama stop firintandi😰)
“Koma dai menene kibi a sannu gudun karki wurga kanki cikin matsala.”
_Sorry ban muku alƙawari ba, amma idan nasami kaina zaku ganni Kamar kullum muna fama da rashin wuta_
#MJ#Vote#Sulfee
Oum-Muwadda🍢
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: *_HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Labarin daban yake da sauran…_*
Page.١٢
“Iƴakaci suka kamani nace kaine kasani yin kome kuma kaga dole a yanke mana hukunci tare mu mutu tare.” na gaya mishi haka,
“Kee mahaukaciyar ina ce da zaki ce nine na saki wallahi karki jefa ni cikin matsala.” yace min kamar zai fashe da kuka,
Kauda kaina nayi tare da fashewa da dariya nace.
“Ka shiga hannuna, kuma dole ka amshi hukuncina.”
Ɓata rai nayi sannan nace.
“A kunnen Amir.”
“Shikenan na amince.” murmushi nayi sannan nace.
“Yawwa yaron kirki.”
Da sauri na bar gidan, ina addu’ar Allah yasa karsu nime ni, Allah cikin ikonsa, kuwa na shiga kitchen ina cikin taya wata, aikin sai ga Sahela. Tashigo duba girkin da muke tayi sannan ta kalleni cikin harshen turanci tace.
“Daga wata ƙasar kike?”
Kauda kaina nayi sannan nace mata.
“Senegal!”
Shiru tayi tana kallona, sannan tace.
“Ina son a girka min abinci me kƴau dan ina da bako daga masarautar marocco inda hali ayi mashi irin girkinsu, sannan a tsaftacce kome gudun faruwan matsala. Idan yaci lafiya ya koma gidanshi lafiya kuntsira idan aka samu matsala kuyi kuka da kanku.”
Tana gama zabga kashedinta ta cikawa bujenta iska. Ranar a kitchen muka wuni. Dan sai Biyar muka gama abincin. Shashinmu na nufa naje nayi wanka tare da gyara jikina, ina gamawa Ghaniyu na aikowa yana nima na.
… Da sauri na fita. Ina zuwa na same shi bakin kofar fita daga masarautar, a gaggauce yace min.
“Anjima zan zon da Sheik Habibullahi, dan ya duba Sultan.”
Gyaɗa mishi kai nayi san.nace
“Ince ba dai malamin tsubu bane?”
“Eh gaskiya wannan baya cikin malam da kike tunani. Dan yasan abinda ya dace.” yace min,
Shiru mukayi dukkanmu muna sakawa da kuncewa a ranmu, katse shiru nayi da cewa.
“Dai ka tafi, anjima zan xo.”
Nace mishi tare da komawa cikin gidan.
***
*BANU NAZIR*
“Ya shugaba! Sun kashe yarinyar ta hanyar bata guba ne da karfin tsiya, bayan Sultan Ashraf ya saketa, sannan ba iya kisarce matsala ba su shida suka mata fyaɗe, sam basu kyauta ba, sanadin haka kakanta ya kashe kansa.”
“Ba kashe kai bane! Kisan kaine kuma sun lakato tsuliyar dodo dan sai na girgiza masarautar baki ɗayanta, idan banyi haka ba, bancika ɗan halak ba.”
Inji Alexandra,
Shiru manyan fadar Alexandra sauƙayi, kafin wani dattijo wanda ya fisu shekaru yace.
“Idan zaku yanke hukunci, ku dinga dubawa meke faru? A yanzun haka nasami labarin Sultan Ashraf ba lafiya.”
Yuuuu sukayi da idanunsu akanshi, suna jiran kanun labaran daga bakinshi. Gyara zama yayi ya faɗa musu abinda yake faru.
Nan suma suƙa kulla tasu ta yadda zasu rusa jagorancin Amir Ukshe.
***
Da dare na fita tare da nufar gidanshi. Ina zuwa nasamu babu kowa, basu iso ba. Tsayawa nayi daga waje gudun farun irin wancan dukar dan har yanzun jikina ciwo yake.
……
A can cikin garin kuwa bayan lokacin da Ghaniyu yaje, yasamu an kawowa Malam Habibullah wata mara lafiya, yana fama da ita. Dan haka ya tsaya jiranshi.
***
“Ukshe! Yayi nasaran raba Ashraf da mulki tabbas dole na dakatar dashi dan bazan cigaba da ganin yana aikat…”
Bai karshe ba ya rike wuyarshi sakamaƙon shake mishi wuya da Irfan yayi, suna cikin wannan kokuwar sai ga Ammar babban ɗan Amir Abu Zarri yashigo ganin, yadda ake shirin kashe masa mahaifi, bai san lokacin da ya ɗauki wani kwalba ya jefi keyar Irfan, sake Amir Abu yayi ya faɗi kasa sumamme,
Shi kuma Ammar yaje kan Babanshi ya ɗauke shi suƙa fito daga cikin ɗakin, ya kuma bawa masu tsaron kofar izin karsu bar Irfan ya fita, shi kuma ya wucce da mahaifinsa Asibitin.
***
Daga falour bakin Amir Ukshe Raziyah tafito fusƙarta cike da farin ciki, shima bayanta ya biyo ƴace.
“Ki kula sosai, dama Abu Zarri ne ya tsare mana gaba, indai Ashraf ne bani da matsala dashi. Dan wannan halin da yake ciki ma ya ishe shi, haka zai zauna har karshen rayuwarsa kowa ya manta.”
“Ni haka ma bawai yayi min bane amma bazanki shawaranka ba ai da kasheshi mukayi haka zai fi alkhairi.”
“Me kike ci na baka sauka, ki jira nan da wani loƙaci mulki zai dawo hannunmu,”
“Dukda haka naso da kashe shi baki ɗaya dan ina gudun kar wani abu yazo ya lalata mana shirinmu”
“Idan muka kashe shi zaiyi wuya muma mukai labari, haka ma wadatar dashi.”
Haka suka tashirya yadda zasu kawar da duk wanda zai kawo musu shunku.
***
*NIGERIA*
Abuja…. 4pm
A firgice Ummi tafarka daga barcin la’asar ɗin da tayi akan abin sallarta, salatinta yasa Khalil da Fatima wacce muke kira da Batul. Da sauri suƙa nufin kanta, mika mata ruwa Khalil yayi wanda tasha kafin tayi sallar la’asar.
“Sannu Ummi! Lafiya..?”
Inji Khalil, janshi baya Batul tayi tare da dakatar da shi.
Sallama yayi tare da shigowa falon ganinsu cirko cirko akanta yashi tambayar “Lafiya?”
Inji Abdullahi, ” Ya Abdul Ummi ce mukaji tayi salati, shine muka bata ruwa ko Adda Batul” Inji Khalil,
Zama yayi kusada Ummi ya ɗaurs kanshi akan kafaɗar, yace.
“Ummi! Don Allah ki rage sanya damuwa a ranki, Insha Allah duk inda Safinah take zata dawo lafiy…”
“A’a Abdullahi! Safina tana cikin hatsari, naji haka a jikina tana gab da faɗawa cikin hatsari na ganta cikin mugun yanayi tabbas tana cikin mawuyacin hali.” a raunane ta kai, kafin waninsu yayi magana tasake wani irin kuka mara sauti tasake a hankali me mugun taɓa zuciyar me sauraro tace.
“Ƴa Allah nayi tawassali da sunayenka tsarkakku masu daraja ya Allah ka jarabce ni da abinda zuciyata zata iya ɗauka Ubangiji baiwarka tana cikin wani hali ya RahamanRahim Ya Allah badan na iya ba Ya Allah dan karfin mulkinka ka kare Safinatu a duk inda take.”
Addu’ar da tayi kenan, duk falourn sai da suƙa zubda kwalla, shigowar Nannah baisa su fasa kuka ba, Abdul ne yayi ta maza ya faɗawa Nannah abinda ke faru, itama dai ƴau tun safe take yawan jin faɗuwar gaba tare da tunanin Safinah da ya addabi zuciyarta, gefe guda kuwa na zuciyarta yana son tabbatar mata da zarginta amma bata amince da hakan ba.
“Maman Bint ki daina kukan nan haka, Insha Allah Bint tana nan dawowa, Insha Allah ki daina takura zuciyarki da tunanin wani abu zai same ta da izini Ubangiji alkhairi ne zai faru da ita.”
Da kyawawan kalamai Nannah tashawo kan Ummi tayi shiru, ita ba ƙome ke ɗaga mata hankali ba ƙome bane sai idan ta tuna cewa Safinah mace ce, me rauni ce bazata iya kare kanta ba idan wani abun kare kai yazo mata babu shakikinta a tare da ita, waye zai kare mata wani abun waye zai ceceta idan wani ya farmaketa cikin kuka tace.
“Mamin Bint!! Mace fa bata da karfi, idan wani ya farmaketa fa? A wannan duniyar da imani yayi karanci idan wasu suƙa cutar da ita fa, kasancewarta Ƴa mace me rauni taya zata tsira, wallahi nasan babu makawa Safin…”
Kwarewa tayi wanda ya haifar mata da tari me karfi, sai da aka bata ruwa tasha, ajiyar zuciya ta sauke tace.
“Allah kai kafini sanin halin da taƙe ciki”
Daga haka bata kuma magana ba, sai dai kwalla yaki barin idanunta……
Nannah bata bar gidan ba sai karfe biyar da rabi, lokacin Alhaji Badar ya dawo.
***
*JORDAN*
9:pm
Ganin dare na kara duhu, ga wani tsoro tare da faɗuwar gaba, yasani juyawa zan bar gidan, ban taɓa tsamanin zan ganshi ba sai ganinshi nayi a gabana, wani irin yanayi naji tare da tsoron da ya cika min zuciya baya nayi a razane na juya da mugun gudu cikin gidan, aikuwa ya rufa min.
Sakamaƙon duhun falon, bansan meye a gabana ba nayi tuntuɓe dashi take na zuɓe a gurin, zan mike naji kafar tayi min nauyi. Dole na mike da sauri kafin nace zan gudu ya bangajeni da kirjinshi na faɗi can gefe akan hannuna, sai da naji karan kashin hannuna. Kuka ne ya kwace min dukda falon akwai duhu sosai nasha mamakin yadda yake gane inda nake, matsawa nayi da sauri na shige ɗakinsa, nasamu na tura ƙofar zan rufe ya kaiwa kofar doka, kuka ne ya ƙwace min miƙewa nayi na shiga bin bango da bayana,, hmm ashe makunin wutar ɗakin na ta inda nake ja a jikin bango aikuwa wutar dakin ta kunnu, ashe jiya a duhu na ganshi, ƴau kam a haske nayi ido biyun dashi.
Bansan lokacin da ihu ya kwace min ba na rufe idanuna da mugun karfi, fincikoni yayi ya cillani saman gadonshi kaina ya bugu da allon gadon, bibiyu na fara ganinshi, yunkura nayi zan mike yayi maza ya diro kaina, kuka ne ya kwace min nace.
“Karka min haka Ashraf, don Allah karka rabani da kome na, gwara ka kashe ni kawai.”
Kifeni da mari yayi wanda ya ɗauke min jina da ganina, kafin na dawo daga hutun rabin lokaci Ashraf ya keta min rigana har cikina, duka na kai mishi tare da yakushe fuskarshi, amma ina yaci karfina, kuka nake kalaman Nan yana dawo min.
_Taya zaki kare kanki? Karki tsomma kanko cikin wancan masarautar kyaleshi inda rai da rabo zamu gana, a matsayinki na ya mace taya zaki fuskancesu har ki samu damar ɗauko shi? Don Allah karki aiƙata abinda zanji na tsani kaina, dan matuƙar suƙa ganoki kasheki zasuyi idan ƙuma basu kashe ki ba zasu cut…”
Wani irin azaba ce tA dawo dani daga gajeriyar tunanin dana faɗa, tureshi nayi da mugun karfi na kwaci kaina, amma, kasancewa karfinmi ba daya ba, sake kamoni yayi ya shake min wuya. Ina ji ina gani na rasa kimata, darajata, budurcina, tun daga shekaran da na balaga nake tattalinsa, Ummi da Nannah suka tayani tattalinsa ta hanyar faɗa min sharuɗar da zan kiyayye, wanda bazan rasa shi ba, nima nabi. Yau gashi garin taimakon da tausayi nazo inda aƙa bautar dani, aka wulakantani, uwa uba aka rabani da Alfarmata. Ni Safinatu na rasa Darajata na yaudari iyayena, har da mijin da zan aura na tsallakesu na tawo ciƙawa Nannah Muradinta, gashi hakkin Iyayena da Anim ya kamani.
Ganin yadda yake kara tsaga jikina nayi wani yunƙuri nacire hannunshi ɗaya a wuyana, garin ya maida hannun zoɓen azurfan hannunsh……
*_A koda yaushe labari takan sabunta kanta, musaman wanda kake muradin isar da sako….Zan baku dama faɗi ra’ayoyinku….
Meye ya jefa safinah cikin wannan matsalar… Idan na gama page 13 naga Writerup ɗinku da sakon da wannan shafin ya kunsan zan sake muku musaman Whatspp grps ɗina ƙune zaƙu fara karanta Page 13 hmmm Wattpad kan na baƙu 12 ku more gobe nayi muku posting tunda rowar vote kuke._*
#MJ#HZƘ#VOTE&Share…
Oum Muwaddah….💅
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: *_HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Page.١٣
Kwalla ne ke bin fuskana da ace ban hannun agogo zai dawo da na maida abinda ya faru matsayin mafarki, ajiyar zuciya ya sake tare da atishawa me karfi akai akai, har sau bakwai. Ji yayi gabaki ɗaya karfinshi sun kare, lokaci guda kuma fitinannen sha’awar da take rura zuciyarshi ta kara zaburar dashi, dan haka ya cigaba da abinda yake. Kwalla na sauƙa ta gefe idanuna na girgiza shi cikin kuka nace.
“Ash”
Rufe min baki yayi da hannunshi d’aya ya cigaba da abinda yayi. Sa’a kanina ne yau yake yadda yaso dani, Sa’an Abdul.
……Kwallar dake bin fuskana nake jin ɗigarshi har gefen kunnena, idan nace ban wahala ba nayi karya, na bar iyayena nazo na rasa kome na,
… Sai da yayi kusan mintuna hamsin da biyar, loƙacin bana cikin hayacina sannan ya janye daga jikina ya koma gefe tare da jan bargon ya lulube kanshi ya kama wani irin barci.
***
Faruwan alamarinmu yayi dai dai da fashewar madubin tsafin Amir Ukshe, acan kashmir kuwa gidan guru ne ya kama da wuta, har dashi gurun bai tsira ba..
Duk yadda mutane suka so taimaƙonshi abin yaci tura, haka suna ji suna gani ya ƙone ƙurmusu. Gidan da yake ciki kuwa ta rubta cikin kar kashin kasa, kamar ba a taɓa wanzar dashi ba a gun.
*Karshen taɓaɓɓe kenan*
***
Amir Ukshe kuwa wani mugun mafarki yayi, ana binshi da gudu garin ceton ranshi ya faɗa cikin Rami.
Da Ihu ya farka sai me bakinshi a karkace, gefenshi na dama tashanye har da bakinsa, duk yadda yaso magana ya kasa karshe dai tashin hankali da baƙin ciki yasanya yayi sumar dole.
…… Alhamdulillah Abu Zarri jikinshi kam da sauki, dan kuwa har yayi magana bayan amfito dashi daga gobe da nisa.
…….
Bayan kwana uku…..
A hankali nake buɗe idanuna har suka buɗe tar Hindu, Salmah, Mujahidah, Azrah sune nagansu a zagaye dani a ɗaƙin Azrah. Mikewa naso yi, Azrah ta mai dani tana cewa.
“Kiyi a hankali jikinki da ciwo fa,”
Mai da kaina nayi tare da lumshe idanuna, kwalla na zuban min. Juya musu baya nayi, kuka nake sonyi taki zuwa. Ji nayi kamar na jika jikina na saka hannu zan duba naji an rike min hannuna. Juyawa nayi naji tsigar jikina ya tashi da wani irin tsoro ya cika min zuciya ba kowa bane ya rike min Hannu sai Abil ɗan gidan Amirsh Raziya.
Ja nayi da baya, ina girgiza kaina, tare da sauke wasu kwalla masu zafi. Cewa yayi.
“Ku fita dasu, naji da wannan kazar wajen.”
Kuka ne ya kwace min haɗa hannuna nayi cikin tashin hankali sabida har yanzun ban daina tuno muguntar da Ashraf yayi min ba. Yau ga wani zai kara min, haurowa gadon yayi tare da niman taɓani, na sake kara me karfi na faɗi kan matashin ts baya, murmushi yayi sannan yace.
“Taimaƙonki zanyi naji ance wani ya kwashi daɗi a jikinki shine nima nazo jin ya tak…”
“Yana da kyau ka tsaya a kan abinda ya zame naka bashiga hurumin da bana kaba, ku kaishi gidan horo.”
Inji Sultan Ashraf wanda Ghaniyu ya turoshi a keken guragu, sakamakon yadda baya juran dogon tafiya.
Fita akayi ds Abil, kura min ido yayi yana kokarin tabbar da kanshi da gaske abinda yaƙe jin kamar mafarkine ya faru. Dagaske ne daman,
*A’a mafarkine? Anya ƙuwa Wacecen ita? Daga ina take? Meye ya kawota?*
Tambayar da bai da amsarsu shine yake tayiwa kanshi. Danna wani abu yayi a jikin keken ta turashi gaban gadon, hango goran ruwa yayi, ya ɗauka tare da buɗe bakin. Ya tashi daga keken ya koma bakin gadon, ya haura sosai. Ruwan ya kurɓa ya furza min a fuska.
“Wayyo Allah Ummina! Don Allah karka min.”
A firgice na tashi, tare da ƙamƙame jikina, na fashe da kuka kai. Kai hannunshi yayi zai taɓa ni, na kuma sake masa kara tare da zuɓewa a sume, kallona yayi cikin tashin hankali sak irin wannan muryan yaji a mafarkinsa, gyara min gashina yayi sakamaƙon hautsinewar da suƙayi.
Shafa gashin yayi yana jin yadda suke da laushi da tsantsi loƙaci ɗaya, karewa fuskana kallo yayi. Wato mutumin da bai da tsoro ranar da ya tashi tsorata yafi kowa tsorata.
Sauka yayi daga gadon, har zai juya idanunshi ya sauka akan jinin da ya ɓata inda nake ƙwance.
D’agani yayi yaga baki ɗaya kayana sun jiƙe, ta baya.
“Ghaniyu!!”
“Umarninƙa nake jira!”
“Dr Fu’ad.”
Sauka yayi daga gadon ya koma gefe yana kallona, cike da tashin hankali. Bayan kamar minti goma sha biyar sai gasu nan fita Dr Fu’ad yace suyi. Ya cigaba da dubani, sosai ya fahimci matsalata sannan ya shawo kanta, fitowa yayi ya miƙa musu takrdan magani, yace.
“Ranka ya daɗe, karku takura mata har yanzun bata fita daga firgici bane dan da alamu wanda yayi mata fyaɗen ya gwada mata rashin Imani dan yaji mata mugun ciwo wanda yayi sanadin da sai da nayi mata ɗaki a ciki, ciwon da tajine ya haifar mata da zubda jini amma Insha Allah nan da sati zata warke.”
Kanshi a sunkuye ya jinjina maganar da Dr yayi mashi,
Bayan fitar likitan , ranshine ke ɓaci danna abinda zaisa keken tafiya yayi ranshi na kara ɓaci kamar zata kama da wuta, duk yadda Ghaniyu yaso taimaƙa mishi abin yaci tura.
Cikin fada ya wucce, ba zato batsamani, ya wucce buɗe masa kofa aka fara yi,.har ya isa cikin fadar kujearan da yake mallakinsa ya tunkara tashi yayi ya zauna.
Duƙ wani wanda yake da ruwa da tsaki a masarautar sai da ya shigo faɗar, kanshi a sunkuye yace.
“Ina Amir Ukshe? Ina Amir Abu Zarri? Meke faru? Na bada awa goma a tattaro min duƙ wani abinda ya faru daga ranar da nacika shakaru Ashirin da tara, zuwa yau, ko kuma nasoƙe mukamanƙu. Daga yau na dawo kan kujerata babu wanda zai umarcrni sai dai ni na umarta duk wanda na kama da laifi wallahi billahil azim zansaka Shafiq ya gutsire masa kai”
Yana gama faɗar haka ya sauka ya koma kan kekenshi sannan Ghaniyu ya turashi suƙa bar cikin fadar. Ranshi kara ɓaci yake idan ya tono abubuwan da suka faru suna shiga cikin ya juya tare da kallon Ghaniyu yace.
” Ka gaya min meke faru? Shin nine na lalata mata rayuwarta? Ka gaya min meye ya faru da ita.”
… Kan ghaniyu a kasa ya shiga bashi labarin abinda ya faru.
“Lokacin da muka zo nida Sheik Habibullah, munxo mun sameku cikin wani mugun yanayi, ita tayi dogon suma. Kai kuma kana barci, nan dai muka kira Azrah taxo ta fidda ita tare da kawayenta, kai Sheik da almajiranshi suka maka ruki’a anan aljanin yake cewa daga cikin masarauta aka turoshi amma wanda yayi aikin ya mutu, karfin zamanshi a jikinka zoɓen nan ne, abinda ya faru daku, shi ya karya kashi sittin na karfinsu koda aka kaita can gun bayi.Azrahce take kula da ita ga kuma Amir Ukshe da Amir Abu dasuma ba lafiya.. Har samun labarin da naji Abil zai kai mata farmaki har zuwanmu…”
” Da gaske ba mafarki nake ba? Na cutar da ita?” shiru Ghaniyu yayi fashewa da kuka yayi sosai sai da yayi ya ishe shi sannan yace.
“Ghaniyu ban taɓa zina ba a rayuwata. Me yasa sai ita? Ga mata birjin me yasa sai wacce takame kanta ghaniyu na cuceta Innalillah..”
Rike kanshi yayi wanda yake masa wani irin sara kamar zata fashe. D’akinshi ya koma ya zubawa gadon ido bakin ciki na ƙara ciƙa mishi zuciya ji yake kamar ya haɗiyi zuciyarshi,tsanar mulkin ya kara cika mishi zuciya. Wani mugun ɓacin rai yake ji tabbas a wannan yanayin duk wanda ya kuskura tunkareshi da wani abu zai iya bada umarni a sauke mishi kansa yadda yake ji ba sauki sai na Rabbi.
………
A can shashinmu ban kuma farkawa ba sai bayan sallar magrib, a hankali na sauke kafafuna daga gadon sannan na mike akan kafaffun sai ji nayi jiri ya kwashe ni zan xube. Azrah ta tare ni.
“sannu ki barƴin kome da karfi.”
Tace min, gyaɗa mata kai nayi. Cikin nutsuwa na wucce ban ɗaki tsarki nayi sannan nayi alola nafito. Abin sallah sallah nasamu tashinfiɗa min, a sannu na fara gabatar da sallar dake kaina, inda yake bani wahla, ruku’u sabida cinyoyina da suke ciwo.
Ina gab da idarwa dan har nayi tahiyya, kawai sai ji nayi kaman Ashraf ya rungume ni, bansan lokacin da na fasa ihu ba na shiga kame jikina,
Wasa wasa sai ga sanadin haka yana shirin taɓa min kwakwalwata, dan sai da Azrah takira Ghaniyu shi kuma yaje ya gayawa, Ashraf tunda na ganshi na rufe idanuna gam tare da rike jikina, ina sauke a jiyar zuciyar daga karshe na kama barcin dole.
Ficcewa yayi daga ɗakin. Kafin gari ya waye Ashraf yayi kusan sawu goma yana xuwa dubani, zuwanshi na karshe ne ƴazo yasamu ina sallah, dukda tausayin da yake ji bai hanashi cewa Ghaniyu idan na warke na dawo bakin aikina, dan ina bukatar na…..
#MJ#HZƘ#Vote……..
Oum Muwaddah…💄
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: *_HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
_Hey da akwai yadda zanyi da nayi muku sai dai kuyi nazari sosai bana son shiga hakkin Iƴalina ne shi yasa shafin yake zuwa kaɗan ƙaɗan_
Wannan page kyautane gareƙu Allah yabar Zumunci Musaman Mom Abul My Aunty Fati, My Sister Samirah….. Da sauran mutane..
Page.١٤
Lokacin da naji saƙon Ashraf ban sa’ilin da na mike ina zare idanuna ba, kafin kuka ya kwace min jikina na rawa nace.
“D’an Uwa Ghaniyu don girman Allah kace bazan dawo ba, b….”
Haɗiye maganar nayi sakamaƙon shigowar da yayi yajingina bayan shi da jikin bango, fita ghaniyu yayi Azrah ma tafita, matsowa ya fara yi, nima ina matsawa da baya, sai da muka bangon ɗakin, makurewa nayi tare da k’amk’ame jikina, jin numfashinsa tare da jefa min tambaya.
“Ya jikinki? Da fatan babu matsala ko? Hmm sannan me kike gayawa Ghaniyu?”
Yadda yaƙe fitar da maganar a gajiye zaka ɗauka wani babban aiki yayi, a hankali na d’ago kaina ina bin hannunshi da ido wadda ya dafe bango da ita, ganin babu wani rata tsakanina dashi yasa zuciyata bugawa da mugun karfi, d’ago kaina nayi sai cikin idanunshi, yatsare ni da ido. Duhu ne ya mamaye min ganina kafin, secend biyu na zuɓe a jikinshi ban kuma gane kome ba, sai bayan awa uku, inda na farka.
Ganin ba kowa a ɗakin yasani mekewa a sannun na shiga ban ɗaƙi ruwa na watsa sannan na fito,.na samu an kawo min abinci alfarma a cikin irin warmer din da nake zuɓa mishi abinci, sallah na fara gabatarwa.
Sannan na koma bakin gado na fara cin abincin,
*Dole ki koma bakin aikinki kuma kicire tsoro da fargaba ki karasa abinda ya kawo ki, saura yan kwanaki suka rage miki*
Lumshe idanuna nayi sakamaƙon kuskuren da zan aikata na karshe a rayuwata bansani ba ko zan kai labari ko bazan kai ba. Da wannan na tsayar da shawara d’aya tak.
……. A can fada kuwa an tattaro duk wani bayani an kai ofishinsa, koda ya shiga ofishin ya tara da takardun. Zama yayi ya shiga duba takardu, ya samu abubuwa da yawa da suka faru, musaman kisar Angela da kaiwa Abu Zarri hari da akasa Irfan.
Fita yayi daga ofishinsa, ya nufi cikin gidan Abu Zarri, yana shiga yasame shi akwance a falon an sanya mishi wannan dan abin wuyar, zama yayi kusadashi, sannan ya kalle iyalinsa da suke zagaye dashi, mikewa suƙayi baki ɗayansu, suka barshi da Abu Zarrin.
Rike hannunshi Sultan yayi cikin kulawa yace.
“Meke faru? Nasan bazaka rasa sanin ta ina matsalar take ba, gashi na samu kana cikin wani yanayi kace min wani abu.”
….. Mikewa yayi ya zauna cikin jinjiki.
“Wallahi bazan iya furta maka kome ba, dan duk wanda yake cikin wannan masarautar yasan an zalimceka, har na tsawon shekaru, kayi hakuri zaka iya samo gaskiyan amma ba a bakina ba.”
Mik’ewa yayi tare da zuba hannunshi cikin aljuhunsa ya fita, ranshi na kara ɓaci waye zai faɗa mishi meke faru, komawa ofishinsa yayi ya rufe takardun ya sakasu a cikin locker ya fita.
……….
Amir Ukshe kan yana asibiti dan jaraba cewa yayi a sallame shi, dukda ɓarin damarshi bata aiki haka bai hana zuciyarshi sakat ba dan a halin da yake ciƙi ji yake yanzun ya dace ya buga wasan yadda ya dace, ya kuma kauda hankalin kowa akansa. Tunda yana da goyan bayan Raziyah.
……… A cikin ƴan tsakanin nan bana ganin Sultan ko sau ɗaya tun ranar da na suma a jikinshi ban kuma ganin idanunshi ba, kuma nima ban dam ba, nafi mai da hankalina kan shirin da nakeyi akanshi na karshe.
***
Karfe goma na safe jumma’a duk sun nutsu a fadar ƙowa na baza kunne yaji wani hukunci Sultan zai yanke.
Shigowarsa shida Ghaniyu yasa duk manyan cikin fadar suƙa mike, sai da ya zauna sannan suma suƙa zauna banda Amir Ukshe wanda kai da wuya sukw karkace.
Mik’awa magatakardan wani zungurerren takarda Ghaniyu yayi, ya koma bayan Sultan ya zauna, wanda ya harɗe kafarshi wato yayo crossing leg, fuskar nan a tsuke ba wasa a cikinta. Bayan sallamar da magatakarda yayi sannan ya shiga koro bayani cikin tsantsar harshe larabci me cike da balaga.
“Ina muku fatan alkhairi a safiyar jumma’a nan, dalilin da yasa na taraku anan ina son ku bani goyan baya a bisa hukuncin da zan yanke, abu na farko ina mika sakon ta’aziyata ga Zuri’a banu Nazir, tare da biyan diyyar Angela, sannan ni Muh’d Ashraf ins bawa Alexsndra haƙuri abisa abinda ya faru, Sannan masu hannu a cikin kisar sun haɗa.
Amir Ukshe wanda ya bada umarni a kasheta, sai Irfan da dawod, Abbas da Abil… Ni Muh’d Ashraf na yanke musu hukunci gaba ki ɗaya rayuwarsu zasu yishine a gidan kaso, sannan fyaɗen da suka mata za a musu bulala, tamanin tamanin. Sannan a yau ni Sultan na huɗu na soke Amir Ukshe a matsayinsa na Wazirin Masarautar jordan, Sannan na mishi iyaka da shiga wani hurumi
Na cikin mulkin kasar nan, sannan abu na gaba na bawa Uzaif bin Ukshe Alhashmiyya, rikon kwarya. Kafin na ajiye alkalamina zan kuma sake zarta da wani hukunci na sauke Amir Abu Zarri a matsayinshin na Galadima, na maida Ammar d’anshi, nayi hukunci abisa kafaɗun Ahalin Banu Hashim, idan akwai wanda hukuncin bai mishi ba zai iya kalubalantana, sannan idan akwai wanda yasan anyi wani laifi ya rubuto a kawo ofishina, haka ma idan wani haramtaccen d’abi’a da akeyi a masarautar karku ɓoye ku faɗa Insha Allah zabi hakkinku.”
“Kai waye zaka sauke Amir Ukshe sannan kabawa Uzaif mukamin mahaifinmu, wallahi baku isa ba.” Inji Marhum, ko kallo bai ishe Sultan ba, hannunsa da suke harɗe da juna, ya ɗan buga, Ghaniyu da sauran guard ɗinsa suka rufe Marhum da wani jahilin duƙa suka rufeshi da shi tare da ɗaukarshi suƙa fitar dashi kamar matacce.
Mik’ewa yayi tare da ɗan takawa kaɗan yace.
“Duƙ shugaban da aka kamashi da laifin kowani irine toh ya wajaba a gareshi ajiye mukaminshi cikin lumana ko kuma a karɓa da karfin cin tuwo.”
Daga haka ya fita yabar fadan, yayinda wasu ke murna wasu kuwa bakin cikine ya ciƙa musu zuciya sakamaƙon huƙuncin sultan.
***
Alhamdulillah naji sauki sosai dan yanzun ina iya dogon tafiya, saidai ina fuskantar tozarci a cikin masarautar sakamaƙon nuna ni da ake haka yasani jin tsanar Ashraf da kuma kaina, domin bana kaunar ganinshi ko sau ɗaya ne, matuƙar zan ganshi toh nakanrasa nutsuwata, karshe da ya fahimci haka sai ya daina zuwa inda nake, cikin wannan yanayin na koma bakin aiki cikin gidanshi, ranar da naje Ghaniyu ya nuna min ɗakin dakr gefen nashi yace a nan zan zauna, dukda a tsorace nake da gidan haka na amshi key ɗin ɗakin tare da godiya, tunda nashiga na zauna a bakin gadon, a sannu na fashe da kuka. Sosai sai da nayi kukan me isata sannan na mike zan fita, ganinshi nayi a bakin kofa, bansan lokacin da na maida kofar da karfi zuciyata na bugawa.
Ban fito ba sai da na tabbatar baya cikin gidan na fito, na wucce kitchen ɗin, dake bana cikin nutsuwa haka na girka abinci gishiri da yaji kamar zasuyi magana, ina aikin ina juyawa. dan gani nake zai kuma farmaƙata ta baya.
…… Yana cikin ɗakinshin tare da kunna tv da ya haɗa da Cctv, ganin yadda nake aiki ina juyawa, tare da gyara jikina. Dafe goshinsa yayi ranshi ba daɗi, yana ganin lokacin da naje zuba gishiri jin motsin abu yasani zabura aikuwa gishirin ya kwace sosai cikin miyar. Haka ma yaji,
…… Dake ban iyq girki in ɗanɗana ba,.kuma nasan aladarsu ce idan na kai abincin zasu sani ci, yasa ban fahimci aika aikan da nayi ba, haka na juye na kai inda zai ci.
Sannan na tsaya can sai gashi ya fito sanye da farin shirt me dogon hannu wandon brown, abincin na zuba mishi bayan ya zauna, na ajiye a gabanshi, towel ya ajiye a gaba sannan juyar da abinci da nasaka mishi, har da spoon ɗin. Kallonshi naƴi naga shi ko inda nake bai kalla ba. Jikina ne ya ɗauki rawa, a sannu na ɗibo abincin na kai bakina, rintsa idanuna nayi tare da buɗewa akan abinci, rike bakina nayi ina kallonshi.
Hannunshi yakai zai amshi spoon ɗin ya riko hannuna, a loƙaci guda wani shock muka ji wanda yasamu kallon juna loƙaci guda fauce hannuna nayu zan wucce ɗakina yace.
“Kin manta sauran aiki..”
Wato na busar mishi da gashinsa, dawowa nayi na ɗauki towel ɗin na ɗauka bansan loƙacin da kuka yazo min ba, na duk yadda naso maidashi na kasa, yajin saukar kwallarta a wuyarshi baisa yq damu da yasan halin da nake ciki ba, ina gamawa yace.
“Hand drie!”
A nan nace.
“Don Allah ka barni hka, ni banason,,!!”
Tashi yayi yazo gaba yana kare min kallo yayi cikik hucky voice yace.
“Saƙe faɗa abinda kika ce”
Sunkuyar da kai na nayi kwalla na zuba daga idanuna, hannunshi yakai zai shafo fuskana baya nayi, da sauri matsawa yayi kamar yadda nayi bayan, girgiza kai nayi cikin kuka matsawa yayi shima, hannunshi yakai zai taɓa ni a razane na sake a jiyar zuciya, duhu ya mamaye min idanuna ban sanya akayi ba dan da baya na zube, hannunshi yakai bayana da mugun sauri ya tare ni, kallon fuskana yayi.. Murmushin da bai zato ba ya kwace mishi, a hankali ya sunkuce ni yana kallon fuskana shi da zai kaini d’akina sai ga Bawan Allah ya wucce dani turakarsa(wai meye haka Sultan😰)
Zuwa yayi ya kwantar dani, zare hijab ɗina yayi. Dama abinda yake son gani gashin kaina yake son gani, yana mamakin yadda bakar fata kamana nake da gashi me laushi da santsi ga uban tsayi.
(Not maganar gaskiya wasu daga cikin kanuri da shuwa arab Allah yayi musu baiwar gashi ga tsayi ga laushi. Balle kuma Feener da babanta kanuri da mamanta Shuwa arab, dan haka babu inda za’awa feener gorin gashi ko kuma ace karya ne)
Murmushi yayi tare da shafa lips ɗina, yana jin wani sabon fitinanne feelings yaƙe taso masa, dafe maranshi yayi yana rutsa idanunshi, mikewa yayi yana jan wani irin nishi,
…… Da sauri yafita zuwa ɗakina, ya kwanta rubda ciki, yana danne abinda yake taso masa, kamshin laylatuƙ sahara da naƙe amfani dashi idan nayi wankin kayana, tashi yayi yaja jakana ya shiga cire kayana. A hankali yazaro har da pant ɗina da bra(🙈🙊) shinshina kamshin yayi tare da sauƙe ajiyar xuciya, kaman wanda aka mintsina ya fita zuwa ɗakin, gadon ya haye ya kwanta a bayana tare da rungume ni kam, kamar zai koma cikin jikina, yana goga goshinsa a kafaɗana, kuka ne ya kwace masa loƙaci guda.
“Me yasa? Nake jin haka ban taɓa karya dokar Allah ba yau gashi nayi abinda ban taɓa ba, Ya Allah kayayye min wannan masifar da nake ciki.”
… Jikinsa ne yq ɗauki rawa sabida yanayin shi ba karamin daga mishi hankali yayi ba, sabida gabaki ɗaya zandariyarsa ta mike, tacika wandonsa.
*(Not wani abun da nake son kusani A gurin Sultan Safeenah baiwa ce asalima ko sunanta bai sani ba, sai wani abu na gaba shine duk cikin jinsin maza babu fitinannun maza irin kabilar larabawa, sabida sutasu ɗabi’a halittace, kuma wasu daga cikin matan da suka je makka umra ko tukari suna faɗa haka, musaman waɗanda sukaje aikatau a cikin gidajen larabawa, Sun faɗa wasu abubuwa wanda babu loƙacin da zan kawo muƙu shi yanzun)*
Mikewa yayi cikin tashin hankali yana dafe maranshi, a sunkuye ya fita kwalla na bin fuskarshi yayi na farko baya fatan kuma aikata wani dan hka yafita da sauri. A falo ya sami Ghaniyu cikin shakewar murya yace.
“D..r….f..u.a..d…..” zuɓewa yayi a gun a sume……..
Wayyo nagaji😾
#MJ….#HZƘ#Vote……
Oum Muwaddah
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: *_HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Gaskiya naji daɗin yadda wasu suƙe tambaya game da Nasabar dake tsakanin Safeenat da Sultan, wasu kuma suna tambaya akan meye dangatar Kabilu guda uku nan… Idan me karatu bai manta ba ya ƙoma shafin farko na labarin inda na faɗi kabilun da suƙa kafa masarautar… Duk da na warware muku kabilun amma har yanzun kuna rayuwarƙu tana cikin ƙwale ƙwale😁😂 May god bless oll ɗinku_*
Page.١٥
Da sauri Ghaniyu ya ciro wayarsa ya kira Dr Fu’ad, ya gaya mishi halin da Sultan yake ciki, cikin mimtuna ashirin da biyar ya iso gidan, yasame Ashraf kwance ya rike marar shi baya ko numfashi buɗe akwatinsa yayi ya dauƙo drip ya saka mishi sannan ya gyara mishi kwanciya ya kalle ghaniyu yace.
“Yaushe ya fara wannan ciwon?”
Shiru ghaniyu yayi dan baya son tona sirrin uban gidanshi, kawai ya fahimci tun ranar da ya samemu cikin mugun yanayi ya jefa Ubangidanshi cikin mugun yanayi, har zuwa yanzun da ya faɗi.
Cigaba da aikinsa Dr Fu’ad yayi yana gamawa ya miƙawa Ghaniyu takarda yace.
“A nima masa maganin nan zai taimaka masa gun rage ƙarfin abinda yake ji.”
Tattara kayanshi yayi yace.
“Allah yasawwaka idan ruwan ya ƙare ga yadda zaka zare mishi.”
…… Bayan fitar shi Ghaniyu sai da ya zauna har drip ɗin ya kare, sannan ya zare daga jikin sannan ya cigaba da gadinsa har ya farka….
Dakyar ya miƙe yana dafe goshinsa, kauda kanshi yayi cike da kunya, ciji lips ɗinshi yayi yana shafe gashin kansa tsuke fuska yayi sosai yana wani cin magani yace.
” Fu’ad yace wani abu?”
(Wai nace ɗan renin hammata cin maganin naye😏)
Sunkuyar da kai Ghaniyu yayi sannan yace.
“A’a ya shugabana, ga takardan maganin da ya bani”
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.
“Toh wancan yarinyar fa?”
Cike da mamaki da ban dariya, yace.
“Wacce yarinya kenan?”
Takar wanda ghaniyu ya shika mishi ashar ya kuma tamke fuska cikin jin haushi kamar ya rufe ghaniyu da duka ya kauda kanshi bai kuma magana.
“Tuba nake ranka shida. Safina kaƙe nufi tana c…”
Fitowata yashi yin shiru kasa kasa yace.
“Ranka shi daɗe gata nan tafito.”
Mikewa yayi ya wucce cikin ɗakinshi, ni kuma na wucce kitchen na shiga kokarin ɗaura abincin rana.
***
Wani irin rayuwa muke a cikin gidan, tsakani da Allah Ashraf ya hanani sakat, idan yana gida bana iya sakewa dan yadinga bina da ido ƙenan. Yadda bazan fahimci ni yake kallo ba.
Lokaci guda kuma magoya bayan Amir Ukshe sun shiga zanga zanga, akan soke shi da akayi, dukda manyan cikin fadan sun haɗe kansu dan su nuna mishi suna sama dashi, kuma sun fishi a shekaru. Shi kuwa ya shiga dakatar dashi, dan sun rantse ba zai kai labari ba, dake kainuwa ne Allah ya cigaba da kare shi duk yadda sukayi babu abinda yake raguwa sai ma karuwar da yake, samu na karfin iko.
Kuɗin da Amir Ukshe ya kwasa shi ya dinga cusa musu suna mishi bori, shi kuwa ya musu tsiya inda ya datse asusun su baki ɗaya, ya kuma saka aka katse musu wutarsu tare da iskar gas ɗinsu. Yaransu da suƙe makarantu a kasashen waje ya saka aka dakatar dasu, duk wani logonsu sai da Ashraf ya karya kafin yasami nutsuwa, suma suka shiga hankalinsu dan yanzun sun fara shakkarsa har suna cewa ya fara mulƙin kama karya.
Dama ya-ya mutanen da suƙe ji da izza da jin kai ina kuma ya haɗu da mulki, lokaci guda salon mulkin matashin sarki ya taɓa zuciyar mugaye suka cigaba da mishi kallon angulu da kan zabo.
***
Yanzun kusan sati uku kenan, da farun tsautsayina da wancan shashashan.. Sunan da zuciyata ta amince min nakirashi da ita kenan. Ina jera abinci ya fito dashi sai dogon wando da bakin singlet, kau da kaina nayi, da sauri na bar gun ko kallon abincin bayi ba ya zauna a kujeran falon yana kallo,
Zuwa nayi na dauki filet ɗin na fara kokarin zuba mishi abinci.yace
“Ina azumi.”
Kutt nace a raina, wato ga yar iska na gama wahala yace min yana azumi, kallon agogon nayi naga karfe tara haushi naji na fara cin abincin juyawa yayi yaga na zauna ina ci.
Shafa sajenshi yayi sannan ya kara karan, tv yadda ya kure volume ɗin, haka kawai naji zuciyana ya fara tashi, cigaba da tura abincin nayi dan kuma tun ina girkawa karnin namar kasar take hawa min kai, yunkurin amai nayi na tashi da sauri na faɗa ɗakina naje nayita kwarawa, sai da nayi ya ishe ni. Sannan na zauna na wucce gajiya, kafin na gyara ɗakin tass.
Na fito daga ciki nazo na tattara na waje, ina cikin gyara gun da aman ya taɓa sai ga Dr Fu’ad, tawowa Ghaniyu yayi yace.
“Yar uwa! Kizo ga liƙita zai duba ki, ashe baki ji daɗi ba.”
“Ni kuma za a duba kai ni lafiyata lau, kace yaje abinsa. Ni bani da matsalar kome.”
Duk yadda suka so dubani fir naki, nace lafiyata lau.
…dan hka likitan yayi tafiyarshi.
…… Abin mamaki baya karewa ina gab da karasa abinda ya kawoni, na fara wani irin zazzaɓi da dare zan kwana banyi barci ba sai asuba, kullum sai na makara, ga wani shegen yawun da bana iya haɗiye shi, idan nayi yunkurin haɗiye shi toh amai zantayi kamar hanjin cikina kamar zasuyo waje.
Sam ban taba duba wani abu yana damuna ba, kawai na ɗauki haka a matsayin zazzaɓine.
Yau na tashi da wuri dan idar da kudirina, dan haka ina gama abin karyawa na buɗe kwalbar guban na zuba a cikin ruwan coffee ɗin da nasan da ita yake fara sha. Dukda nasan cikin biyu za ayi ɗaya, ko na mutu ko shi ya mutu tabbas hukuncin kisa ne a kaina amma bani da zaɓi, dole ta kaini ga aikata haka, ɗauƙar abincin nayi na fito dasu. Na shiryasu kamar kullum, sannan na tsaya yazo ya zauna. Nasha mamaki da bai ce na fara ci ba. Yana zama tea ɗin ya ɗauka yasha sannan ya fara cin abinci. D’ago kaina nayi naga babu kome a cikin cup ɗin, kallon agogo nayi naga loƙaci yana tafiya, janye idanuna nayi daga agogon na maida kanshi.
Abinda idanuna ya gani yasani jin wani irin faɗuwar gaba, ba kome bane sai sauƙar jini daga hancinsa,
Innalillahi nayi tare da niman kiran Ghaniyu, wallahi ban taɓa ƙashe ko ɓera ba, riko hannuna yayi lokacin kumfa ya fara fitowa daga bakinshi. Dawo dani yayi yace.
“Wacece ke? Nawa suka biya..k..”
“GHANIYU!!!” na kwala mushi kira da sauri ya shigo, ganin halin da yake ciki. Yasashi kiran wasu aka fita dashi. Ni kuma yasaka wasu suka kamani.
Zuwa gidan yarin dake cikin gidan, kafin kace me. Maganar ta yaɗu kamar wutar daji, dan haka manyan masarautar suka fara zaman akaina, yayinda suka so a yanke min hukunci, Amir Uzaif da Amir Ammar suka ce a jira aga tashinsa.
……….. Ƙoda aka kaishi asibitin, cikin gaggawa suka amshe shi, abin yazo musu da sauƙi dan kuwa gubar bame karfi bane sun shawo kan matsalar,
….. Ni kuwa tunda aka kaini muka haɗu da Zakiyah nan muka rungume juna tare da murna, nan na bata labarin kowa nasan na faɗa mata dalilin shigowata gidan, kuka tasamin haka mukayi me isarmu, sannan mukayi shiru.
Tun daga ranar na fara mugun ciwo, bana ci bana sha. Nayi zuru zuru dani, nayi wani mugun lalacewa, daga kwanciya sai ƙwanciya, sau ɗaya ghaniyu da Azrah suka zo anan nasa musu kuka so kawo min Apple da abarba da kuma lemo, kallona Mama Azrah tayi jikinta yayi mugun sanyi, koda suka fita bayan awa guda sai ga Ghaniyu da Apple, kamar nacinye da ledar,
Haka rayuwata ta koma bani da abinci sai apple, har tsawon kwana goma kafin aka zo aka wucce dani Fada.
Tunda aka shigar dani, kaina a sunkuye, ina sanye da sarka hannu da kafa, sau ɗaya ya kalle ni bai kuma kallona ba, magatakarda ya gabatar min da zargina da ake, shiru nayi naki magana, haka sake mai maitawa ban ko ɗaga kaina ba, abin ya masifar ɗaga musu hankali, dan haka. Marhum yaci da zuci yace.
“Me ake jira da ita da baza a yanke mata hukunci ba, idan ma turoki akayi idan kika mutu ai magana ya kare.”
Zuciyata ce tayi min nauyi, na saci kallon inda yake. Sannan na maida kaina kasa, mikewa yayi ya kalle su tare da cewa.
“A ɗaga zaman nan da kwana uku zanyi yar tafiya.”
Bansan dalilinsa nakin sauraron jawabin Amir Marhum ba, kuma haka ya taɓa zuciyar mutanen cikin fadar amma basu damu da haka ba, sun ba abin zuwa nan da kwana ukun kar yadda yace.
Lokacin da aka mai dani, na gaji ga jirin dake damuna, ina shigar ɗakin na kwanta, rub da ciki ina mai da kwallar da suke son zubo min,, kukan da nake dannewa ne ya kwace min sai da nayi sosai, irin rayuwar na jefa kaina.
…… Wargi yayi da kome daga dake falon, a zafaffe ya juya ga Ghaniyu ya cukume kwalar rigarshi ya rike tare da cewa.
” Wacece ita? Me yasa take son kashe ni? Kodan abinda ya faru mune Yasa taƙe son ɗaukar fansa.?”
“A’a ranka shidaɗe ba fansa bane?”
“Toh me nene?”
“Tuba nake amma kaje kaji meye ya kawota dan Safinatu b..”
“Ya isa.”
Zama yayi cikin damuwa yace.
“Me yasa ta addabi rayuwata? Me yasa shiga min rayuwa? Itace silar sani aikata kuskure, dole nasan wacece ita. Dan kuw..”
Miƙewa yayi ys fita tare da ghaniyu, gidan yarin ya nufa, koda suka isa kai tsaye ɗakinda nake soka zo, ina kwance bayan nagama aman abarban da nasha, ana ce min gashi yazo na mike zaune, zuba min ido yayi kafin ya juya min baya, daga ni sai shi.
,”Wacece ke?”
“Kaima waye kai?” na ce mishi haka bayan na gyara zamana, juyowa yayi cikin zafin rai, yaga yadda na tsareshi da ido, cikin zafin rai yace.
“Ina tambayarki kin maida min tambayata.”
“Kai ma bakasan kanka ba, sannan baka taɓa damuwa da kasan kanka ba, Muhammad Bini Abdullah Alhashmiyya, Jinin Banu kura’sh jikan sarki na biyu Yasir bin Alhashmi, D’a ga Nana Asma’u bint Safwan Yar sarkin Oman……….
#MJ#HZƘ#Vote……Wallahi zaku shafa kuji banyi typing ba dan voting yayi kasa😰😒
Oum Muwadda…..
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: *_HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Page.١٦
Mik’ewa nayi na zub da yawun bakina yanzun abin ƴana niman d’aga min hankali, da zaran na fara magana zai cika min bakina, dawowa nayi na zauna bayan na zub da yawun, na kalleshi. Sannan nace,
“Yanzun abinda ya faru shekarun baya zaka sani me yasa suka baka mulki? Baka da amsa, me yasa suka haramta maka shiga fada na tsawon shekaru baka da amsa bari kaji abinda ya faru da sarki Yasir kafin Mahaifinka.”
*Mafarin Labari.*
Duk wani adalci da ake bukatar sarki yayi, duk sarki Yasir yayi kuma yana kanyi kuskuren na raba mukaman shi ga zuri’a Banu hashim baki daya, sannan yaki jan wasu kabilu a jikinsa, kasancewa yana da halayar kishin kabilarshi.
Sai wani abu guda Sarki Yasir yaki barin kowa yayi facaka da dukiyar baitul mali, haka ba karamin d’aga musu hankali yayi ba, kuma dama Amir Ukshe yana can yana fatuttukar sai ya ɗare kujeran mulkin, duk da haka duk inda yaje maganar ɗ’aya ce bashi ba mulki sai dai ya zama jigo ga mulki.
***
Kasancewa Dr Ibrahim shine likitan masarautar, dan haka Sarki Yasir dashi yake shawara ga duk abinda yake faru a gareshi, inda yake faɗa masa abinda ke faruwa, abinda Dr Ibrahim ya ce masa shine.
“Suma kabilun ka basu shuwagabancin kabilarsu haka. Haka zaisa zasu fahimci mulkinka sannan idan da hali idan zakayi kaso a cikin masarautar ayi dasu. Kabilu guda biyun sun haɗa Banu Nazir da Kuma Banu Hussein. Dan haka suka amshi tayin abinda ya basu.
……. Bayan shekara guda da ba shi mulki, Amir Abu Zarri da Shugaban Kabilar Banu Hussein, Harris bini Hussein tare da wasu manyan Attajirai suka shirya meeting, akan basu son mulƙinsa, su shuwagabanin
Kabilun sun bada goyan baya ne dan yaki basu mukami a cikin masarautar,.Attajirai kuma ya tsawalla musu akan haraji. Yan kasuwa kuma yasasu sun karyar da kayansu sabida talakawa, abin bai tsaya nan ba tunda suka haɗa kai, basu nemi kabilar Banu nazir ba, gashi Amir Ukshe baya kasar yatafi can kasar china domin niman mulki.
A ranar da zai dawo a wannan ranar jerin shuwagabanin tare da jagorancin Amir Abu Zarri, suka kifar da mulƙin Sultan Yasir, garin ya kare kanshi suka masa kisar gilla.
Ana cikin jana’azartasa aka fara fuskartan matsaloli,
Lokacin Amir Ukshe ya shigo garin, yasamu anyi ambaliyar ruwa wanda ya kashe ɗinbun alumma, dan haka abinda ya fara an kara dashi kenan dan dama an faɗa mishi yazo ya kuma bar baya da kura, dan haka yayi maza ya koma kafin abin ya shafi kowa da kowa, koda yaxo sun gama abinda ya faru, kuma suka ɓoye mishi,
… Dr Ibrahim kuma suka sakashi a jirgi dan dole ya dawo kasarshi.
Bayan kifar da Yasir aka kuma sake shiga sabon muhawara, karshe dai Amir Ukshe ya bawa Abdullah me shekaru ashirin da uku mulƙin Jordan.
A lokacin Amir Ukshe da kanshi ya nemi Ibrahim ya dawo, sai ya turo Badar,”
D’ago kaina nayi na kalle shi, idanunshi sunyi jajjur, gashin goshinsa sun tashi ruɗa ruɗa,, murmushi nayi sannan na mike na zubda yawun na dawo inda yake na zauna sannan nace.
“Kasan waye Badar? Toh shi ɗin Mahaifina ne!!!”
Cike da mamaki yake kallona, kauda kai nayi, sannan na cigaba da cewa.
Kamar yadda suka maidaka haka suka maida Abbie ɗinka, sai da ya shekara uku suna juya shi kafin ya haɗu da Nana Asma’u, Mahaifiyarka. Tazo karatu nan, ranar da suka gama makaranta, suka haɗu da farko taki faɗa mishi ita wacece sai da yaga motar masarautar Oman, bai kuma bin takanta ba tana komawa ya tura wakilanshi, suka je masa. Ita kuma taki amincewa sai dai yaxo da kanshi.
Shiryawa yayi, ya tafi har Oman tun daga karɓan da aka masa yasan ƴa samu karɓuwa, sun zanta a tsakaninsu sannan ya koma ga iyayenta, suka tsayar da Magana.
…..
Bayan wata uku da dawowanshi kayi bikinsu, tunda Nannah tashigo masarautar ta fahimci sunan Abbienka sarkine a baki a zahiri kuma Amir Ukshe da Abu Zarri sune sarakin.
Dan haka tashiga faɗi tashi har ta samu damar maida mijinta me cikakken iko, ganin abubuwa sun fara faruwa Abbana yasamu a jirgi muka dawo maiduguri.
A lokacin shekaruna huɗu a duniya,tun da muka dawo. Duk bayan wata shida Abbana yana zuwa.
Bayan an haifeka kome ya kuma jagulewa dan kuwa, sun fara nuna halinsu nakin mulkinsa, dan har sun fara masa barazana. Bai fasa abinda yayi niyya ba, Amir Ukshe yana nunawa a gabanshi yana sonshi a bayan idanunshi kuwa shi yake kara rura wutar rigimar da yake faruwa.
Ranar da zasu kashe shi, ya haɗa kayanka da kuma Nannah, ya mikawa Abbana yace.
“Badar ga Ahalina! Don Allah karka bari wani ya cin maku, ya zauna a hannunka karka taɓa barinshi ya dawo.”
Jin Ana dukar kofar yajasu zuwa wani kofa, ya turasu.
……. Suna barin gidan, suma mutanen na shigowa, suka same shi a kujeran da ake bala’i akanta, murmushi yayi sannan yace.
“Daga kaina bazaku kuma kashe wani sarki ba, bazanyi fatan jinina ya mulkeku ba. Am….”
Rufa mishi sukayi da sara har sai da suka ga baya numfashi, abinda yabasu mamaki shine ganin murmushi akan fuskar gawanshi, suna fitowa suka sami Amir Ukshe da Sauran manyan fadar, har da Amirah Raziƴah, murna suka fara Guru Ra’ees ya bayyana musu cikin shiga na alfarma fuskarshi a murtuke yace.
“Kun kashe maciji baku sare kai ba, kuƴi maza ku dawo da yaron nan biyan bukatarku yana ga yarone ku mai dashi kan kujeraaa”
Daga haka ya ɓace ɓat.
Umarni Amir Ukshe ya bada akan a dawo da Yaron,
***
Gudu sosai suƙe Abbana yana rike da Kayanku, Nannah tana ɗauke da kai, faɗuwa tayi tare da kai. Dawowa da baya abbana yayi cikin haki da gajiya yace.
“Uwar gijiyata, ɗaure ki tashi mu tsira da rayukarmu.”
Cire kanta tayi cikin sarewa tare fidda tsammani ga rayuwa tace.
“Badar kuje kawai. Nagode kabarni a nan.”
“Ba zan iya ba, ki daure muje zan ɗauki yaron ma.”
Haka ya ɗaukeka ya kuma ɗauki jakarka, ya kuma riko hannunta suka fara gudu. Dukda gudun ba wani sosao bane. Duk tagaji basu kai ga barin cikin garin Amman. Suka cin masu. Basu musu kome ba yaron suka amsa bayan sun wurga mata jakar kuɗin dallar U.S, sannan suƙa mata gargaɗin da karsu kuma ganinta a kasar ko kuma su kasheka, domin kai ka rayu ita ta bar kasar baki ɗaya, domin kai tabar mahaifarta, dan tasan matuƙar ta koma kasarta zasu abin zai zama kamar yak….”
Mikewa yayi yana me zuba hannunshi cikin aljuhun wandonshi, ya kalle ni a sace sannan yace.
“Meye ya kawo ki.?”
“Tausayin Nannah da irin son da take min, yasani jin zan iya kome dan tayi farin ciki, dukda ta gargaɗe ni da zuwa nan ɗin.” sunkuyar da kaina nayi tare da fashewa da kuka, nace.
“Nagama aikina. Amma na rasa tawa farin cikin, na rasa abinda zai cire zargi a zuciyar duk wanda zan au…”
Fita yayi daga ɗakin, na kuma rushewa da kuka, sabida son nagyarawa wasu zuciyarsu ni tawa zuciyar ta lalace. Taya zan fahimtsar da Anim, wallahi yasan halin da na jefa kaina ciki har abada bazai kuma haɗa hanya dani ba,
***
Ƴau kwana biyu kenan tunda ya tafi nake cikin damuwa, ga ciwon kullum yake, sam ban taɓa kawo wani abu a raina ba, kawai bar haka a matsayin typhord. Ranar da aka mai dani fada ina tsaye aka gabatar da laifina. Suƙa nemi nace wani abu amma naki magana, shima yace wani abu yaki magana, haka suka mai dani tare da masa caaaaa kuma dama sun sami labarin yaje gidan yarin dan haka Marhum ya faɗawa Amir Ukshe, sun tattauna akan Sultan.
***
Ina zaune ya shigo tare da mika min password ɗina, gyara tsayuwarshi yayi sannan yace.
“Nasamu a cikin kayanki, sannan nayi miki booking ɗin jirgi wanda zai tashi karfe sha ɗaya na rana zuwa jakarta na kasar Tunis, sannan ki rubuta min address ɗinki da Number wayar gidanku. Idan nagama abinda naƙe zanzo naga Ammina.”
Jikina na rawan sanyi na rubuta mishi number Nannah sannan na mika mishi, garin karɓa ya shafi hannuna da sauri ya d’ago kanshi yana kallona yace.
“Baki da lafiya ne?”
“Fever ne, amma nasha magani, idan na isa gida zanje Abdul ya duba ni.”
Tsare ni da ido yayi sosai, sannan ya taɓe baki yace.
“Waye Abdul? Ko shine zaki au.”
Girgiza kaina nayi cikin gajiƴa nace.
“Kanina ne?”
Fita yayi daga ɗakin, kwanciya nayi a gadona wani irin farin ciki na cika min zuciya,
…….. Washi gari aka mai dani, kamar da yadda aka saba naki magana, shima bai ce kome ba.
“Idan na fahimta Sultan Ashraf na kare mai laifi, bayan kuma shi ya saka doka….”
Bai kai aya ba Ashraf ya mike, daga kujeran ya cire duk wani abinda ya shafi na sarauta ya ajiye musu, sannan yace.
“Ni Muh’d Ashraf na ajiye muku mukamin ku, sannan zan tafi karku taɓa sakaƙancewa, dan dole wata rana ku nime ni.”
Yana gama gaya musu maganar ya dawo inda nake ya riko hannuna muka fita, inda aka ajiye motarshi muka nufa Ghaniyu yaja motar, Zuwa Airport, naso muyi sallama dasu. Amma ban samu halin haka ba.
…… Tunda muka isa na zauna sukayita zirga zirga, sannan ya dawo da wata jaƙar takarda ya mika min sannan yace min.
“Kije ki sauya kayanki kowa kallonki yake.”
Mikewa nayi jiri ya tafi dani. Da sauri ya tare ni, na zuɓe a kirjinshi ajiyar zuciya na sauke, ina rungume a jikinshi ya nufi gurin sauya kaya, shigar dani yayi sannan ya fito nasaka kayan na fito dakyar, dawowa yayi ya sanya hannuna a kafaɗarshi yana rike da k’uguna muka fito, dake ticker VIP. Ƴa saya min, muna fitowa ya kaini can. Zama yayi kusadani yana ce min sannu, zuba min ido yayi ganin yadda nake share kwalla. Ajiyar zuciya ƴa sauke sannan yace.
“Da zan tafi Madina ne karɓo takarduna, amma ganin halin da kike ciki yasani zan biki zuwa Nigeria, Naga ƴanayin j..”
Da sauri na katse shi ta hanyar gyara zamana nace.
“Lafiyata lau, kawai ciwon jikin dukar da nasha a hannun samudawarka ne.”
Kauda kanshi yayi sannan ya mike yace.
“Insha Allah zan zo nan da wata biyu.”
…….. Gyaɗa mishi kaina nayi, tare da janyen idanuna akanshi,.yau ce rana tafarko da nake jin ba dad’i rabuwa da wani, shima ban san dalilinshi nakin tafiya ba, zuba min idanu yayi ya sauke a jiyar zuciya sannan ya fita, ina zaune can sai ga wata ma’aikaciyar jirgin tashigo rike da wani takarda mika min tayi, na amsa buɗewa nayi, zoɓe ya faɗo. Tare da wani ƙaramin rubutu aka ce.
*_Nasan bazan biyaki abinda kika rasa ba, bansan me yasa haka ya faru ba amma ina me baki hakuri da ki yafe min dan na zalince ki na rabaki da kimarki na Y’a mace ina kara baki hakuri , idan kin isa ki sumbaci goshin Ammina ina nan zuwa gareta_*
Lumshe idanuna nayi, zuciyata na min ciwo. Ainun ina jin sa,ada jirgin ya tashi,
……. Bayan tashinm ya kalle Ghaniyu cikin damuwa, yace.
“Yarinyar can bata da lafiya”
“Eh ranka shi daɗe, gaskiya Safinat bata da lafiya, tana da hakuri da juriya ne kawai, amma kana kallonta kasan bata da lafiya.”
Haka sukayita tattaunawa har lokacin tashin jirgin Ashraf yayi.
Suka yi sallama da Ghaniyu, sun rabu cikin jimami.
***
*NIGERIA*
Abuja…..
Shakar iskar kasata yasani lumshe idanuna, a hankali naƙe saukowa daga matakalar jirgin. Har na iso arriver, ɗan jakata na ɗauka tare da fita daga cikin gun, ina fita nasame taxi, na gaji ga jirin dake damuna.
Sunan unguwarmu na faɗa mishi a gajiye, yace min.
“Madam 1.5₦” gyaɗa kaina nayi na shiga, tsoro da farga duk suƙa ciƙa min Zuciya.
……… Tafiyar awa ɗaya ya kaimu, ƴana tsayuwa a kofar gidanmu Khalilah tana fitowa zata taka kawayenta da suka zo jajjen ɓata na, yayinda Abdul ya zo zai shiga gidan. Na fito a hankali,
“Addah Feener!!!”
Wani irin kwalla ne ya zubo min, fitowa da gudu Abdul yayi lokacin na mike tsaye ya karaso guna, faɗawa jikinsa nayi tare da fashewa da kuk…….
_A ɗauri kashine ko a ɓata igiya😎_
MJ#HZƘ#VOTE….
OUM MUWADDA😇
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITERS ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Maidambu ki zubda cikin nan na tsani cikin, Oum Muwadda don Allah a cire cikin Maman Walid don Allah karta samu matsala da family ta…..Chaiiiii ina kuke so na cusa kaina… Bari na ware muku wani abu da tunda ya shige Muku duhu Kaddara da Rabon dake tsakaninta da Sultan, haka kawai dan taga halin da mahaifiyarshi take ci taxo, sai kaddarar Ubangiji, aurenta aka saka amma aka fasa sabida karfin rabo, da anyi auren tabbas Anim Mutuwa zai yi ko kuma aje auren ba daɗi, Shi alamarin Ubangiji babu ruwanshi idan ya shirya ya shirya kenan har ranar da duniya zata tashi…. A ranar da abin zai faru taso komawa amma dake Allah ya nufa haka sai ya faru sai ya kasance tabbas wannan bangare na labarin ya tuna min kanwata Ya Allah ka bamu ikon cinye Jarabawarmu…..Shin A matsayinki na Uwa ya zaki amshi Feener Shawarar da zaku bada tayu Ummi ta fahimta ko kuma Abba Nagode👏_*
Page.١٧
Numfashi nake sauƙa da sauri da sauri, rike rigarshi nayi kuka ya ƙwace min, ɗauƙa na zai na girgiza mishi kaina, raɓani yayi a jikinshi muka nufi cikin gidan, me taxi ɗine yace.
“Kuɗina fa!”
Kawar Khalilah ce ta tambaye shi ya gaya mata ta ciro a cikin jakarta ta mika masa, sannan yaja motarsa yayi gaba.
Kai tsaye Abdul ya shige dani falourn Ummi inda Yan uwanta daga maidugurin suka zo mata jajje, ga wasu danginsu Abbanmu. Kakarmu Hajja Kaka kanwar Baban Abbanmu, tana zaune kanta naɗe da laffaya, casbi ne a hannunta,
Ganin Abdul rike da mace yana shigowa yasa duk suƙa mike, kwantar dani yayi a kan kujeran falon, yace.
“Ummi! Alhamdulillah Allah ya dawo mana da ita, Khalilah jeki cikin motana zaki ga memo ɗin Asibitinmu ɗauƙo min maza.”
Da gudu tafi, Mutanen da suke falon suka haɗa baki suka ce.
“Allahu Akbar! Allah maji roƙon bawansa, Allah mun gode maka da kadawoma da ita gida lafiya.”
(Wai nace Hmm)
Nan suka shiga hidima akaina, karshe dai Hajja kaka ta matso cikin kulawa tace.
“Bawan Allah ko zaka wucce da ita asibitine?”
Lokacin har Khalilah ta shigo da takardan rubutu yayi har dasu magunguna ya fita da sauri.
Ummi kam tunda ta zuba min ido bata ɗaga ba, sam taki cewa kome kallona kawai take, Shigowar Hajiya Amna da Hajiya Nuratu wato Mame da Umma yasa duk suka ɗaga kansu, cikin alhini Umma tace.
“Barka da Arziki Safinatu, sannu Allah ya baki lafiya.”
“Amin Amnah,” inji Hajja kaka,
Zama Hajiya Nuratu tayi, tana kallona taɓe baki tayi sannan tace.
“Nikam ba makaranta kika tafi bane? Ko wani kika bine? Ya miki halin Yan dun…”
Zama hajja kaka ta gyara, tare da rike tasbinta tace.
“Nuratu kenan! Ai ba awa motar gawa dariya, idan bai ɗaukeka ba ya ɗauki Uba nai ko uwatai! ehtoh a bakinki muka fara ji, tsalle ɗaya ake a faɗa rijiya, sai anƴi dubu ba a fito ba, harshenka kamaninka”
“Ayya Hajja daga tambaya sai ya zama laifi”
“Oho ke kika ji gun ai hannun hagu ba bakon wanƙe kashi bane.,”
Shiru falour ya ɗauka, shigowar Nannah wacce Anas yaje ya gaya mata na dawo, kamar zata kifa cikin farin ciki da murna ta riko hannuna tace.
“Bint!!! Alhamdulillah, sannu bint”
Ga baki ɗaya duk ta rud’e sai kiran sunana take, tana share kwalla. Shigowar Abdul yasata mikewa daga inda nake ta koma gefe, ruwa ya samin tare da allura,
Har aka kira magrib ban tashi ba sai karfe uku na dare na farka, Ummi da Nannah na gansu zaune akan abin sallah tashi nayi na zauna, ina kallonsu. Zare karin ruwar nayi na shiga wanka, dan zafi nake ji.
Ina fitowa na buɗe wardrob ɗin Ummi na ɗauki.Hijab da doguwar riga na saka, sannan na tadda sallar dake kaina ina idarwa masalci suna sallah.
Mikewa nayi na gabatar da sallah, sannan na fara addu’a. Ina idarwa barci yace gani nan nazo…
Kallon Nannah nayi tare da sakar mata murmushi nace.
“Nannah kafa suna min ciwo musaman nan.”
Na nuna mata gun kaina na ɗaura a cinyar Ummi, nace.
“Ummi don Allah sosa min kaina.”
Zare hijab ɗin nayi ita kuma ta shiga sosa min kai Nannah na matsa min kafar, kafin kace minti biyar barci yayi gaba dani.
……… Suna ganin nayi barci Nannah ta ɗauko pillow tasa min, hira suka taɓa sama sama,, sannan suƙa kwanta.
…… Ina farkawa naga abokan aikina na gidan radio duk sun zuba min ido mikewa nayi ina murmushi yawu ya cika min bakina, zubda yawun nayi tare da ɗaukar sabon brush a locker ban ɗakin, na wanke bakina sannan na fito nasamu sunyi min kunun tsamiya, da kosai. Murmushi nayi na fito falour dan sun fita abincin aka bar min a ciki,, fitowa nayi nima da abincin na zauna a tsakiyar falourn, ina zama Abbanmu na shigowa.
“Ina kwana Abba!”
Zama yayi a kan kujera ya amsa da ” lafiya ya jikin naki”
“Da sauki” na bashi amsa a takaice,
Nan sukayita hira da abokan aikina, ni dai bana iya dogon magana sabida amai.
….. Can suka mana sallama zasu tafi, tambayata sukayi yaushe Zan koma aiki nace musu wata sati.
…… Ga baki ɗaya wani irin kulawa nake samu daga iyayena har ƴan uwana, jikina kam da sauki babu duƙ abinda yake min yanzun wani mugun kwaɗayi ke ɗawainiya dani, musaman Nanah da Abdul.
Kuma cikin ikon Allah babu wanda ya tambaye ni, ina naje har yan uwan Ummi suka koma, aka bar Hajja kaka kuma dama tana zuwa ta huta sai ta koma.
Satina ɗ’aya na koma aikina, xuwan Anim gidanmu sau uku naki masa magana asalima bana fita sai na kwanta nayi barcin dole, yau muna gama aiki muka fito zuwa sallah, yaxo ya sha gabana.
“Feener Kyari ki faɗa min me kike nufi dani? Laifin me nayi miki da zafi?”
Gefenshi na raɓe zan wucce naji ya riko hannuna bansan lokacin da na ture shi ba, cikin ɓacin rai nace.
“Dole ne? Ka rabu dani tunda kaga naki kulaka.”
Daga haka nayi wuccewata kowa na mamakin yadda na mishi wulakanci.
……. Haka nake zuwa aikina duƙda na fara fuskantar matsaloli daga Anim bai dame ni ba, dan ba zamansa nake ba.
……..
Muna zaune ni da Muwaddah da Sabirah, sai tsiya suƙe min wai na gaya musu wani magani nake sha ne nayi kiba haka, dariya nayi nace.
“Shaka fashe.”
Sabira ta fashe da dariya sannan tace.
“Ni kuwa yanayinki kama da masu ciki yake min.”
Dariya nayi nace.
“Ba’..”
Maganarce ta makale sakamakon faduwar da gabana yayi, ina yunkurin mikewa Anim yana zuwa, da sauri na ɗauki jakata na fita bina yayi da ido, shima ya biyo bayana da sauri kafin ya iso, har nayi ribas da mugun gudu sai yanzun abubuwan da suke faruwa ya dawo min kaina, dakyar na isa asibiti dake a rikice nake, har na shiga ban tsaya tunanin inda nazo ba, asibitin da Abdul yake aiki nazo fa. Tsabar ruɗewa.
Ina kan sai share kwalla nake, har Wani abokin Abdul yazo wuccewa, yaga ina kuka shine ƴaje ya gaya mishi kaina a sunkuye, sai ji nayi an riko hannuna, dago kaina nayi naga wani sabon kuka ne ya kwace min, dago ni yayi muka wucce ofishinsa, zaunar dani yayi a kujeranshi. Ya durkusa a gabana ganin yadda nake kuka wiwi, ya kura min ido sannan yace.
“Safinah meke damunki?”
Muryana na rawa nace.
“Nazo ayi min test ne!”
“Test ɗin meye? Za a miki?”
Rufe bakina nayi da hannuna, ina girgiza kai nace.
“Kusan wata ɗaya da wasu kwanaki bangan shi yazo ba”
A ruɗe ya mike yace.
“Kwanta a wancan gadon.”
Jikinshi na rawa ya kunna computer scanner ɗin, sannan ya sani ɗage rigana ya zuba min luquid ɗin, ya ɗaura abin ya hasko mishi Abinda yake son tabbatarwa, dan tunda ya ɗaura nace “wash”
A hankali ya shiga duba kwanakin cikin, sati shida cif.
“Cikin Sati shida Why Safina?”
Wani irin gigitacce kuka ne ya ƙwace min ina girgiza kaina.
Wayarshi ya ciro ya shiga niman number Ummi, ya kirata.
“Don Allah kizo karki gayawa kowa.”
Juya bayana nayi, na kuma cigaba da kuka, tun daga ranar da abin ya faru nake kuka har iyau kuka nake, sallamar Ummi yasake kara kuka na, kujera ya ja mata ta zauna, zuɓewa yayi a kasa gwiwarshi duk a kasa, sannan ya ɗaura kanshi bisa cinyarta, a hankali tashiga shafawa kanshi, zuciyarta na rawa.
“Abdullah! Meke faru?”
D’ago kanshi yayi kwalla na zuba daga idanunshi ya rike hannunta cikin kuka yace.
“Ummi! Shin bayan uwa akwai mutumin da zai iya jure zafin fitar ɗ’a daga jikinsa?”
“Babu Abdullah uwace kawai take jure zafin fitar ɗanta a jikinta”
“Ummi indai har haka ne tabbas babu uwar da zata gaza tsayawa d’anta, indai har zata iya tsaya masa tabbas ita kaɗai ce zata yarda da kaddararsa, indai har haka ne itace kawai zata iya amincewa da bukatarsa, indai har haka ne itace zata iya share masa kuka, Ummi duk duniya bamu wata bayan ke, Ummi indai har kika amshi kaddarar da tasamemu nayi.Imani da Allah bazaki taɓa ta gaiyara ba.”
Shafa kanshi tayi cikin karfin hali tace.
“Ina jinka!”
“Ummi!!!!”
“Na’am!!!”
Nuna mata gadon yayi cikin kuka yace.
“Tarbiyarki ce! Renonki ce! Shekara ɗai ɗai har talatin bata taɓa saɓa miki ba bata tab’ayin abin Allah wadarai ba, sai gashi a cikin shakara na talatin da d’aya tazo miki da kaddara shin zaki amsheta.”
Kallona tayi zuciyarta na wani irin bugawa,
. Sannan ya cigaba da cewa.
“Ummi baki ce kome ba”
Murmushi kawai ta iya sakewa akan fuskarta.
Goge kwalla yayi sannan cikin karamar murƴa yace.
“Cikin sati shida gareta.”
Rike hannunshi tayi da mugun karfi tana ambaton sunayen Allah sai ta tayi guda ɗari ba ɗayan nan cif kafin ta iya buɗe idanunta da ta runtsa, mikewa tayi ta gyara hijab ɗinta tace.
“Tasauko muje.”
Jikina ba kwari na sauka a gadon na ɗauki jakata, koda muka fita ban iya jan motana ba.
motar da ya kawo Ummi nabi kwanciya nayi a baya, idanuna suƙa cigaba da kwalla, muna isowa ana fito da kayan Anim da ya kawo na aure, aka zuba a mota.
Da sauri na shige cikin gida, ina saka kafana a falourn kunne na jiyo min……..
#MJ#HZƘ#VOTE…….
Oum Muwadda……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITERS ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Sadaukarwa ga Ummu Sayeed naji daɗin Yadda kika tafi bincike Yasin wasu rubutun kawai suke karantawa basa bincike balle su tabbatar da labarin gaskiya ne ko karya ne,😂
Page.١٨
“Alhaji Idan karya aka mata ai gata nan ka tambayeta ba da kanka zata faɗa maka,,
“Zo nan uwata!!”
Wani irin rawa jikina ya ɗauka tare da mugun tsoro da firgici, juyawa yayi ya haura sama.
Ban taɓa sanin haka yan matan da sukayi ciƙi a waje suke fuskarta tashin hankali ba, sai yau da ya faru a kaina. Rike Ummi nake cike da tashin hankali,
“Sai anyi magana ace lokacine bai yi ba, nan kuwa ana yaudaranmu ce da cewa miji bai zo ba, ashe anje gun wani katone ya zuba nasa basirar.” Inji Mame Hjy Nuratu.
Lumshe idanu Ummi tayi da gudu Abbanmu ya sauko ganinshi ni kuwa na nime guduwa D’akin Ummi, cafko ni Mamie tayi tare da falla min mari. Akan fuskana. Sam idanun Abba ya rufe kawai ya rufe ni da mugun da wayar chajin laptop ɗin, zafi da azaba da suka gaurayani, kai ko dukar da samudawan Jordan bai taɓa tsoratani ba kamaemr dukan Abba kodan akwai tsoro ne a raina yasa duk na firgice.
“Ai gwara ka daketa yarinya ta zama annobar mace, mahaifinki na zaman lafiyansa kinje kinje ki ɗauko mishi ɗan gaba da fatiha, sai anyi magana ace ai mijine bai zo ba makira kuwa kinje sun gama dake shine zaki kwaso abin kunya ki zo masa da shi wannan da nice na haife ki yau zaki bar min cikin gidana dan ba zan iya rikon asara ba..”
A yadda na fahimci Abba babba burinshi bai wucce dukar cikina ba da kafarshi, ina gano nufinshi nayi maza na k’amk’ame ummi, jikina na rawa nace.
“Ummina ki cece ni bazan kuma ba. Wayyo Allah Ummina bazan kuma ba.”
“Kaji ko Alhaji! Uwarta take niman ta kareta.” inji Mamie.
Finciko ni yayi Ummi ta rike ni gam, cikin hargagi da kuma ingiza me kantu ruwa, yace.
“Maryam! Saketa ko kuma ranki ya ɓaci”
“Rayukarmu ne zasu ɓaci, ban hanaka hukunci ba, amma idan zakayi ka fara aiki da hankali yafi aiki da agogo, a cikin shekarun da tayi. Bata taɓa yin abinda zai ɓata maka ba, tun tasowarta take kare kanta, da sunanka. Shin d gangan haka ya sameta ko kuwa karfi aka gwada mata, yarinyar da ka ɗauketa zuwa ghana dan tayi karatu yau dan tazo maka da akasin kaddara sai ka juya mata baya, ka nunawa Ubangiji bai isa ya jarabeka ba, kanunawa Ubangiji baka da karfin Imani, kai Uba kenan ina kuma ni da nake Uwa.”
“Wannan matsalarki ce! Alhaji idan baka ɗauki mataki ba hatta fita waje sai yafi karfinka, cikin shege taɓ ɗan gaba da fatiha fa. Da sakel an ba wa me kaza kai.”
Gabaki ɗaya sake haukacewa. Abba yayi cikin tashin hankali da ɓacin rai yace.
“Nuratu! Ɗauko min wuka a kitchen idan ban kashe Safinah ba nayiwa kaina karya bani.”
Abin nima ya samu, da gudu Mamie ta shige kitchen, sai da tayi rawa💃💃💃💃💃 “Shegiyar yarinya ta hanani rawan gaban hantsi yau dole ki bar gidan nan.”
Da gudu ta ɗauki wukar tafita zuwa palour, karɓa yayi yayo kaina. Na fasa ihu tare da rike Ummina, kamar zata faɗi.
“Zaki faɗa min uban da ya miki ciki ko sai na miki yankan rago?”
Ya daka min tsawa, duk na kara rikicewa, jin ihuna yasa Umma da Hajja kaka suka fito da sauri, Nannah ta rufa musu baya. Finciko ni yayi yasa min wukar a wuya. Cikin kuka nace.
“Ummina karki tafi ki tsaya.”
Cak ta tsaya ita batayi gaba ba, ita batayi baya ba. Taki kuma juyawa ta kalle mu, Nannah ce tasaka hannu ta amshi wukar, cikin ɓacin rai tace.
“Banda ina ganin girmanka, tabbas da na mareka wallahi.”
Wurgar da wukar cikin zafin rai Hajja kaka tace.
“Yau naga jakar uba! Yo da kaɗauki zungureren wukar nan wata uwar zaka yi da ita”
“Hmm! Ai da zaku ji abin kunyar da yar gwal ɗinku tayi da bazaku ga laifinsa ba, domin d’an gaba da fatiha ne a kwance cikin mahaifarta.” Inji Mamie ta faɗa tare da kumbura fuska tana hura hanci.
Tsaki Hajja Kaka tayi cikin ko in kula tace.
“Sai me dan tayi cikin shege! Ai gwara ita, wasu asalinsu idan kaji har duniya tatashi bazaka haɗa iri da suba, amma da kaddarar rabo ya haɗa aiki gashi ana zaune lafiya, wai kura na cewa kare mayye, yo wani dare ne jemage bai gani ba, ai sai daren mutuwarsa, abin kunya gaba ta bashi ba baya ba, kuma ba kanta farau ba, kuma ba akanta karau ba, wasu nasu kazantar ko kuda bazai so hawa kai ba. Balle yarinyar da tayi zaman a wata duniya na tsawon shekaru, dan yau ta dawo sai a nemi kashe min ita, don Allah yankata dan kwal ubanka, wato dan bani ce na haifeka ba, ka nuna min dan ban taɓa haihuwa ba shine zaka kashe yarka ko shawara dani bakayi ba ai da na gaya maka hanya mafi sauki da zaka kasheta. Ke Amnah ɗauko min igiya ya ratayeta ina ga irin wannan kisar ba a ciki tsananta bincike ba ko.”
Wani katon harara ta masa sannan ta dawo kaina riko hannuna tayi, tare zaunar dani jikina bai fasa rawa ba, ta kalle ni cikin jin haushi tace.
“Yar banza da shege idanu kamar yayan kurna, taya kika bashi ya ɗirka miki ciki, yo yanzun da duniya ta cigaba, aiko wannan kororon roba yasaka, codan yako ko me.” (Just for fun😂 Hajja kaka wooo)
Sunkuyar da kaina nayi dan na lura yau barikancin hajja kaka ya motsa,
Taɓe baki tayi cikin ko in kula tace.
“Toh haka ma yayi koma me nene, duk ciki Yaran maryam kece me shegen taurin kai kamar ganda, baki jin ko fiɗis, da wasu soyayyun idanunki nan kamar soyayyer gyaɗa, kik cika fitina bana wasa ba, gaji duk hakurin irinta Badaru sai da kika sashi yaƴi miki biɗibiɗi, haka kawai kin zauna ana jibgarki kamar wata lusara. Shashashar wofi”
B’antara goronta tayi cikin nutsuwa tana taunawa, Umma tace.
“Wallahi Alhaji ka bani mamaki yadda, ka ware karfinka akan safinatu, yarinyar da tun tasowarta muke zargin aljanu ne da ita, shine zaka ware karfinka akanta dan wannan abun ya faru. A cikin gidan nan har kake zargin yarka dan kaddara ta faɗo mata, toh kasheta.”
Ummi kan falon ta bari, bai kulasu ba ya nufi dakin Ummi, wacce ta fito ban ɗaki zatayi sallar azhar, cikin bala’i yace.
“Kice ta bar min gidana kafin na dawo.”
Ko kallo bai isheta ba tasaka hijab ɗinta ta tadda sallah,
“Na gaya miki ta fita tabar min gidana”
Banza tayi da shi, har ya fito ya dawo cikin zafin rai yace.
“Idan kika fita, dan kareta ban yaf.”
Mika alamuranta tayi ga Ubangiji ta cigaba da sallarta, tana idarwa ta shiga zuba kayanta a cikin babban a kwatinta, sannan tafito zuwa falon ta kalle ni yadda nake kwance na takura guri guda ina kuka, tace.
“Ki shiga ɗakinki ki kwaso kaƴanki.”
Mikewa nayi na kalleta naga ta kauda kanta, girgiza kai nayi cikin tashin hankali nace.
“Ummi!!!”
Yatsar hannunta ta ɗaura bisa bakinta alamar nayi shiru.
Mikewa nayi naje nayi yadda tace,
Ina gama hada kayana najanyo akwatin na fito dashi, dai dai shigowar Nannah, a firgice tace.
“Ina zaki Binti”
Sunkuyar da kaina naƴi nace.
“Ummi ce tasani na fito da kayana!”
Riko hannuna tayi, na ɗago tare da kallonta, kwantaccen gashin dake gefen fuskarta sak da nashi, har ɗakin ta kaini tace.
“Maryam lafiya?”
Murmushi me ciwo tayi sannan tace.
“Yace tabar mushi gidansa, toh meye amfanin zamana a gidanshi tunda bai yarda da kaddara ba. Ni yanzun damuwata Safinatu ce, ko zata gaya min cikin waye.”
Jingina a jikin bango na zame a hankali tare da sake kuka mara sauti nace.
“Allah na na cuce kaina ko na gaya muku cikin waye bazaku yarda b..”
Ji nayi an shure ni da kafa, tare da ɗago ni a zafaffe akayi waje dani, har bakin get ya cillani na zuɓe a gun.
Ummi naga itama tafito tare da Nannah, sam Abba kamar wanda ya fita hankalinshi, ranar wanda bai san meke faruwa ba ya sani, a gaban ɗinbu mutane Abba yace min.
“Kisaka a ranki ke matacciya ce, kin jima da mutuwa a cikinmu, bamu da ke a cikinmu, karki kuma takowa cikinmu kije duniya ta isheki riga da wando, kamar yadda kika kwarar min da mutuncina naki sai yafi nawa zuɓewa, kuma idan baki bar min kofar gida ba yan sanda zan kira miki, bana son ganinki.”
Yana gama gaya min haka yasa key ya rufe gidanshi, ya kalle Ummi yace.
“Idan kika saka kafarki kiƙa tsallakw bakin get ɗin nan a bakin aurenki.”
Zuwa nayi nayita buga get ɗin ina kuka tare da cewa..
“Don Allah Abbana karka kore ni, daga gareka don Allah ka rufa min asir…”
Ji nayi an riko hannuna, na juya a sannu Abdul ne idanunshi sunyi jajjur, yaja hannuna a har cikin motarshi, zanyi magana ya rufe min bakina da yatsar hannunshi.
“Ya isa muje gidana.”
Gidanshi muka nufa wanda yake can doctors quarts, muna shiga get ɗin gidan Matarshi Sophia, ta fito fuskarta a murtuke ta tare kofar shiga gidan, wani irin kallo take mishi. A sani na Abdul yana da matuƙar hakuri da rashin son magana, kuma ban taɓa tsamani a kaina zai iya zarta da hukunci har haka ba sai da naji yace.
“Ko ki bani hanya na shige ko kuma ki wucce gidanku na sake ki sa…”
“Abdul!!!”
Na kira sunanshi a raunane, na girgiza mishi kai cikin kuka nace.
“Don Allah karka ka rasa, ni na hakura zan nime wani gurin tunda bata son zama dani, duk nice na fara. Kabarni na amshi hukuncina daga makusantana.”
“Koda za a hukuntaki, bata wannan hanyar ya dace ba a nemi wani mana.”
Tunda taji ya saketq jikinta ya fara rawa, ta shiga kuka. Ɗakinta ta koma tare da ɗauƙar wayarta ta kira Layin babanta ta gaya mishi, shi kuma ya kira Abba. Ina zaune Abdul na gefe muka ga Abba a kanmu, a razane nayi bayan Abdul, cikin faɗa yace.
“Zo ki ficce musu makira kawai zaki kashe masa aure tunda ke bakiyi ba bari ki raba na kaninki ko kunya baki ji ba kin ɗiɓo jiki kinzo gidan mutumin kirki zaki lalata masa gidanshi zoki fita.”
Rike rigar Abdul nayi tare da kifa kaina a bayanshi ina shashekar kuka, maganar da Abdul yayi shi ya kashe ni da mamaki, yace.
“Idan Safina tabar gidan nan wallahi Sophia tabar gidan kenan har abada, kuma gabaki ɗaya fa, ba wai zata dawo bane. Can gidanka ne kana da ikon koran kowa nan kuma Abba nawane, ina da ikon zama da kowa. Dan haka da safina da cikinta su zauna a nan hae inyi nawa na kaina. Sannan ni a yanzun son cikin nake tana haihuwa zan haɗa da nawa baki ɗaya na rike su.”
“Abdul!! ” na girgiza shi tare da kiran sunanshi………..
Chaiiiiiiii Yasin nagaji Anya Book 2 bazan saka shi a kasuwa ba😒…….
#MJ#HZƘ# Vote……
Oum Muwaddah….
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITERS ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*Wayyo Feena na tausaya miki ina Ashraf kazo😂 Team Sulfee2020 ko😉*
KYAUTAR SHAFIN NA KU NE MATAN QUARTS MUCH LOVE❤
Page.١٩
“Ni kake gayawa Magana Abdullahi! Ni da nayi wahalarku. Dan na nuna ɓacin raina zaka saki matarka, ni Abdullahi!”
“Abba yadda kabi ba haka kowani dattijon Uba yake yi ba, sam abinda ka aikata tamkar a zamanin da ilimi bai wadatu kowa ba, kai….”
“Kafito kace min Jahili mana! Sai masan kaji haushin abinda naiwa Yar uwanka, kuma dole tabar gidanka yau ɗin nan” ya faɗa a zazzafe,
“Indai Safinah zata bar gidan nan toh wallahi Yar abokinka zata bar gidan nan ba makawa, dan gidana ne ina da iko akan kome na gidan, tunda fa shigo me fidda ita sai ya shirya.”
Wallahi ban taba shiga matsananci tashin hankali a rayuwata irin na yau ba, rigima ta kaure tsakanin Uba da D’a, ba zan iyace na fahimci kome ba. Sai dai n daina jin kome da kuma ganinsu sannu sannu duhu ya mamaye idanuna na zuɓe a kasa.
Kaɗa rigarshi Abba yaƴi ya fita tare da kashedi zabga min rashin mutunci idan na mutu kar a qawo mishi gawar karuwa gidansa, sannan ya bawa sophia dama da zaran na mata iskanci ta min tijara, karta raga min.
“Wannan ikon a gidanka zakayi ba a gidana ba, kuma koda wasa kika taɓa min ran Yar uwa zawarci ya aureki.”
Yana gama gaya mata haka ya ɗauke ni zuwa gun motarsa, buɗe masa motar me gadin gidan yayi. Shi kuma ya sakani sannan ya koma ma zaunin drive ya tadda motar muka fita bayan an buɗe masa,
***
“Maryam! Har kin haifi d’an da zai gaya min magana ko? Toh na zare hannuna akan Abdullahi da Safinah, suje su nemi wani uban bani ba,”
Cikanka Ummi bata ce mishi ba, tayi cikin da sauri ɗakinta dan taji karar wayarta.
D’auka tayi ta kanga a kunne.
“Ummi na kawo Feener asibiti! An bata gado.”
“Toh Abdul zan duba na gani ko zan sami zuwa. Koda ban zo ba Nannah da Hajja zasu zo”
Ta gaya mishi cikin wani irin murya me cike da sanyi da tarin damuwa. Kashe kirar yayi
***
Tunda muka isa su uku har dashi huɗu suka rufa min, jini na yayi masifar hayewa. Kusan ɗari biyu da 220. D’aya daga cikin abokan aikinsa yace.
“Dr Kyari! Wannan mara lafiyar ta tsallake rijiya da baya sabida jikinta da ya haura, ya taɓa zuciyarta amma sakamakon bugun zuciyar babyn cikinta jinin dake zuciyarta ya sauka, sannan cikin jikinta yana cikin koshin lafiya, sai dai dole ta rage damuwa dan zai iya tab’a zuciyarta”
Shiru Abdul yayi kawai dan bai da abinda zai iya cewa, haka suka gama ceto rayuwata, sannan nurse suka turoni zuwa ɗakin da zan kwanta.
***
*Ko ina labarin Sultan Ashraf*
Da misalin karfe huɗu na asuba suka sauka a king Abdul Aziz international Airport… Har suka son inda za ɗauki kayanshi.
Yan sandar saudia suka kewaye shi, cike da mamaki ya kalle su kafin yace.
“Wani abu ne?”
“Musamu labarin kashigo mana da bom daga kasar jordan aka turo mana.”
Gyara tsayuwarshi yayi cike da mamaki bakinsa a sake, jakarshi suka janyo tare da buɗewa, sai ga bindigogi kirar ak47, kananun bindigo gi biyar. Sai wani waya ɗauke da numbers tada bom, gefe guda kananun bom ne masu zubin abun wasan Yara,
D’ago kanshi yayi a rikice yana kallonsu, cikin ko in kula suka buga mishi ankwa.
(Grp ɗin matan quarts da fatan zaku hararo gaba)
Hukumar saudia ta kama Ashraf da mugun laifi, kuma hukuncinsu ba kamar na kowacce kasa bane domin su shika suke (😂 ) kuma abune daga hukumar kasarshi suka turo da sanarwa.
Hmmm idan baka mutu ba, makiya bazasu taɓa barin ka ba……..
***
Nannah tazo asibitin tunda tashigo take kallon yadda na koma, jikinta ne yayi sanyi dan idan hasashen da take gaskiyane tabbas Safina Jordan ta fito. Dan taga takardan da Ashraf ya turo min kafin jirginmu ya tashi tare da zobe da ya bata. Ta fahimci haka ne bayan ta tsinci takardan da kuma stamp ɗin masarautar… Tabbas a can binti ta ɗauko cikin jikinta.
“Ya Allah kasa binti tasan waye ya mata wannan aika aikan, tabbas sai sun biya abinda suka aikata bazan taɓa kyale su ba, abinda sukayi na shekaru shirin da shida bazai tafi a iska ba, kodan binti zan koma gida.”
Haka tayita magana ita ɗayarta har lokacin sallar magrib yayi ban tashi ba, sallah ta gabatar tana zaune Abdul ya shigo da abinci, karɓa tayi fuskarta kawai zaka kalla kasan a dame take.
“Abdul!”
D’ago jajjayen idanunsa yayi, ya kalleta a hankali yace.
“Na’am, Nannah.”
“Binti Jordan taje fa…”
Zaro idanu yaƴi waye zuciyarsa ba daɗi, kafin yace.
“Taƴa haka ya zai kasance,”
Mika mishi takardan tayi, a hankali ya warware. Sannan ya karanta abinda yake jikin takadan.
*_Nasan bazan biyaki abinda kika rasa ba, bansan me yasa haka ya faru ba amma ina me baki hakuri da ki yafe min dan na zalince ki na rabaki da kimarki na Y’a mace ina kara baki hakuri , idan kin isa ki sumbaci goshin Ammina ina nan zuwa gareta_*
“Nannah baki karanta wasikar bane?” ya tambayeta,
yana tsareta da idanu. Girgiza kanta tayi cike da damuwa tace.
“Bansan me zan gani ba, ina tsoron abinda ke rubuce a cikinsa.”
“Ina kyautata zaton Ashraf ne ya rubuta mata.”
Karɓa takardan yayi dai dai da farkawata.
“Ruwa Dudu.!” na faɗa a hankali, goran faro da yake cikin kwalinsu ya ɗauka tare da buɗewa ya tsiyaya a cup ya kawo min tare da ɗ’agani ya bani sai da nasha, sannan ya jinginar dani a jikin bangon yasa min pillow.
Shafa kaina yaƴi tare da cewa .
“Sannu kinji! Ina ke miki ciwo?”
Idanuna ne ya sauka kan takardan dake hannun Nannah, kallonta nayi tare da sunkuyar da kaina, kwalla na saukar min daga idanuna. Mikewa taƴi ta zauna a kusadani,
“Bansan da can zaki ba! Da bazan taɓa barinki zuwa can ɗin ba, me yasa da zaki baki gaya mana ba.”
D’ago manyan idanuna nayi cikin dishashiyar murya nace.
“Nannah! Bansan me yasa naji ina son zuwa ba, kodan kaddarar da zata ribta dani ne yasani zuwa can ɗin, Nannah nasha wahala. Amma ya zama a banza tunda gashi na dawo gida babu abinda naje samowa sai sheg.”
Rufe min bakina taƴi cikin tsananin damuwa tace.
“Yanzun cikin waye, zaki gane me cikin dan zan tsaƴa miki har a sama miki adalci.”
Girgiza kai nayi kuka ya kuma kwace min, sosai sai da nayie isata sannan na ciro kaina a hankali ina jan zuciya nace.
“Cikinsa ne!”
“Waye shi ɗin!”
Lumshe idanuna nayi, kwalla masu xafi suka sauƙa da mugun gudu dakyar na haɗiye yawun bakina nace.
“Nannah sorry!!”
Rike hannuna tayi sosai, cikin kulawa tace.
“Gaya min waye shi.?”
Sake girgiza mata kai naƴi na zame tare da kwanciya na lumshe idanuna, yau na janyowa kaina abinda yafi karfina, na faɗi sunanshi abun ya gaggara.
Shigowar Fatimah da Khalila. Da kuma Ƙhalil sai mijin Nana Asma’u, da itama tare da babynta da ta haifa bana nan.
Zama sukayi a kafet ɗin da Nannah tazo dashi aka shimfiɗa.
Koda suka zo sama sama muka gaisa, tunda na amsa musu na rufe idanuna. Ban kuma buɗewa ba har suka fita bawai nayi barci bane kawai bana jin na amsa musu ne, sai da safe suka mana, har Abdul shima ya tafi . Bayan tafiyarsu na tashi tare da shiga ban ɗaki nayi alola tare da watsa ruwa na fito. Sallar da ake bina nayi koƙarin saukewa sannan na koma na kwanta. A hankali kome yake dawo min, babu inda yaki tafiya kamar inda Ashraf ke gwada karfinshi ya shiga jikina, a nan kuka ya kwace min. Tabbas nayi kuskure amma bata wannan hanyar ya dace a hukuntani ba, yadda naga rana haka na ga dare. Kawai ina tuna irin azabar dukar da nasha a hannun Ghaniyu kafin mu shirya. Da irin hidimar da nasha a gun Ashraf.
Ni da yadace nayi murna yau nice na dawo gida da guzirin me albarka, ehmana cikin da na dawo dashi waye zai yarda cikin Ashraf ne, sannan idan sun yarda Abba bazai yarda, tunda an gama masa ingiza me kantu ruwa..
***
*JORDAN*
“Ni nafi dacewa a bani sarkin jordan na biyar.”
Wani irin kallo Amir Ukshe yabi d’anshi da ita, cike da ɓacin rai ya kuma watsawa Marhum wani banzan kallo,
“Baba baka ce kome ba. Sai bina kake da idanu, kuma nasa a sake min mutane na da wancan jakin ya saka aka kama min, su.”
Tura keken Amir Ukshe yayi cikin jin takaici da kuma tuna wahalarshi na shekaru, ya tashi a banza knn.
A fizge kamar yadda kullum idan zai magana yace.
“Marhum, mulkin jordan bana ka bane sabida tun fil azal akwai me faɗa akan kujerar kum……”
Duƙar glass Marhum yayi cikin d’aga murya yace.
“Waye ne shi? Ni nafi dacewa da jordan ba wani jaki ba.”
“Wanda ya dace da jordan shi yake yadda yaso da Jordan ba kai ba…….
*_Hmmm! Anayinta Feener Abba ya koreta! Ashraf Saudia sun kama shi! Jordan akwai me juyata inji Amir! Wannan chakwakiya ya min tsauri Anya ban ɗibo da zafi ba, Ana Dara ga dare….. toh Akafta mana_*😂😉
#MJ#HZƘ#Vote….
Oum Muwaddah……😂
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITERS ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Page.٢٠
“Waye shi? Waye zai min iyaka da muradina? Na rantse sai na kashe su.”
Tura kekensa Amir yayi tare da barin ɗakin, da gudu ya riko keken Amir Yace.
“Waye shi?”
“Ko waye ne baya bukatar gabatarwa, idan lokaci yayi zaka ga kowaye.”
Yana gama faɗar haka ya tura keken yayi gaba abinsa.
Wato wani irin rikici ya ɓarke a kasar jordan, dangane da mulki wanda yakai duk wanda yayi tari akayi akan mulkin sunanka matacce. Tsabar mulkin zalimci kuma kujerar gata nan amma ta haramci mutane dayawa.
Dan haka sai aka fara samun yan hatsaniya da yamutsi. Wanda ya kuma sabunta rigima a tsakanin mgadarar masarautar suna tankawa junarsu. A gefe guda kuwa Banu Nazir da Banu Hussein suna nan suna nasu shirin..
…..
Sati biyu kenan da Ghaniyu ke niman Ashraf bashi ba labarin,, ya damu sosai da rashin samunshi a waya.
***
*Nigeria*
Abuja…..
Kwana na goma kenan laulayi ya sani a gaba, bana iya cin kome sai ruwa aketa ɗaura min, magana me tsawo ma bana iya yinshi sosai. Ga zubda yawu amai kam ba a magana. Bani da karfi a jikina sai yadda akayi dani.
Ina matukar jin wahala, har na tsani cikin da me cikin dan wallahi da zanga Ashraf a gabana zan iya mishi abinda ban tsammani ba. Dan ya gama lalata min rayuwata da kuma farin cikina.
……. Dafani Nannah tayi , ajiyar zuciya na sauke sannan na k’akaro murmushi tare da sunkuyar da kaina. Dan yanzun ina matuƙar jin nauyinta,
Ledar hannunta na kalla naji yawun bakina yatsinke, agwalimace a cike da yar karamar bakar ledan nan, gyara zama nayi ina jin wani mugun daɗi ya cika ni.
Juyewa tayi a wani bowl ɗin da Ummi ta kawo min salat, ta wanko min A banɗaki ta kawo min,
Dake ɗakin da muke VIP Ward ne, mu kaɗaine a cikin ɗakin. Tunda na amshi agwalimar nake mata wani irin kallo, sannu na fara sha kamar nasami tuwo. Har wani lumshe idanuna nake, shigowar Abdul yasani buɗe idanuna tare da sakar masa murmushi. Dan ya zame min jiki bana magana sai murmushi, shida wata mace yaki ya matsa min naga wacece.
Sai lekata nake ina son ganin wacece, karshe matsawa yayi.
“Ummina ce”
Wancakalar da bowl ɗin nayi tare da dira da karfi naje na rungumeta, kuka ne ya kwace min. Rungume ni tayi tana buga bayana, cikin mita Abdul yace.
“Yanzun dan girman Ubangiji meye haka, baki san akwai abu a tare dake bane, wallahi wannan tsalle kamar a zuciyata kika yishi. Kuma ina kishi, kuma ina taya babyna jin b….”
Wani irin kallo na masa, dan duk abinda ake bana kaunar maganar cikin, kauda kaina nayi cikin kuka nace.
“Wallahi idan bai zo ba zubda cikin zanyi dan cikin y.”
“Wallahi kika taɓa lafiyar cikin nan sai kin kare rayuwarki cikin bakin ciki da nadama,, kuma na rantse wani abu ya faru da cikin ni dake ne, nonsense.”
Haushi yasashi ficcewa,
Kukane ya kwace min, Nannah ta maidani bakin gadon, cikin damuwa zatayi magana na dakatar da ita.
“Nannah! Meye laifina dan nace zan zubda cikin nan, Ummina nifa taimako naje. Na gaji da ganin Nannah tana zubda hawayenta, Ummi nasan keda Nannah zaku fahimceni. Wallahi ba yadda kuke tsamani bane na same shi tunda yazo a haka me zai hana na zubda shi.”
“Waye me cikin?” Inji Ummina.
Kaina a sunkuye, na ɗago shi cikin rawan murya nace.
“Ba zakiyi fushi dani ba? Idan na gaya miki.”
“Akan me zanyi fushi dake? Ai da zanyi da ban saurareki ba kamar Yadda Abbanku yayi miki haka zan miki.”
Kallon Nannah nayi cikin kuka nace.
“Am sorry Nannah!”
Girgiza kai tayi tare da nuna min tana ji na.
Shigowa Abdul yayi yace.
“Ummi naga kiranki.”
Bata bi tankashi ba, kallonshi nayi tare da mika mishi hannuna, zuwa yayi tare da rikewa, ya zauna a kusadani. Daura kaina nayi a bisa kafaɗarshi kwalla nabim fuskana lumshe idanuna yayi tare da fashewa da kuka sabida hango ranar nake a idanuna, da yadda nayita rokon Ashraf yakyaleni amma abin yaci tura, haɗiye kukan nayi amma naki buɗe idanuna nace.
“Cikin…”
Shiru nayi tare da mugun fargaba ya cika min zuciya, matse min hannuna Abdul yayi cikin kwarara min gwiwa yace.
“Faɗa Safina, kina inda baza’a kalubalance ki ba. Karki ji tsoro mun yarda da kaddara me kyau ko mara kyau muna tare dake,”
“Na Sultan Muhammad Ashraf bin Abdullah Alhashmiyya.”
Mikewa Nannah tayi jikinta na rawa, ta riko hannuna cikin wani yanayi, tana kallona kawai sai tasa sake hannuna tabar ɗakin baki ɗaya, tasowa Ummi tayi tazo inda nake ta kifa min mari, Abdul zai tare ta daga mishi hannu, ta kuma ki faɗa min mari,
“Ummi”
“Hmm” tace mishi.
Sake kifa min marin tayi na sake wata gigitacciyar kuka nace.
“Na tuba nabi Allah da manzonsa na biki.”
Iska taja sannan ta kare min kallo, tace.
“Ko yanzun na rage nauyin da yake dankare cikin zuciyata, da kika san jordan zaki me yasa baki gaya min ba, shine marin farko da na miki na kigane rashin gaya mana zaki tafi. Mari na biyu, da kika tafi da kin kira kin shaida mana halin da kike ciki da bazamuyi kasa a gwiwa ba, zamu cigaba da miki addu’a har Allah ya dawo dake ya kuma kareki dagq duk wani mugun abu. Mari na uku, shirun da kikayi bayan Abdul ya gano kina da ciki da tun lokacin kik gaya mana cikin waye, ba maƙawa Abbanku bazai fusata ba gaki kin girma amna har yanzun tunaninki irina Anas ne, shashashar banza shashashar wofi, kawai kin jefa zukatarmu cikin fargaba, kinsan yadda nake kwana kuwa, idan na tuna cikin jikinki. Ji nake kamar ana cenawa zuciyata wuta, ina son nayi barci cikin salama abu yaci tura da zaran na kwanta kukanki ne yake hanani rintsawa gani nake kina fama da ciwo a rayuwarki, sabida ke yau har sake ni Badaru yayi dan na nuna mishi ke nake so sama da kome, kin barni ina tuninan baki san waye Uban cikinki ba, tunda ance mana kin shiga yanki Syria, ashe Safinah bakinki cike yake da magana kike kallon kowa ganga ba rufe, wallahi kin ɓata min fiyye da kima, kin sani cikin zulumi. Kinsani naji na tsani kome raina, Ya Ubangiji karka ka mata da laifin wahalar da zuciyata ya Allah ka kawo mata karshen wahalarta Allah ya shirya mana Zuri’a alummar musulmi baki ɗaya. Sakarya kawai.”
Tana gama gaya min haka taficce Abdul yabi bayanta, komawa nayi na kwanta, hawaye nabin gefen fuskana, sosai nayi kuka tare da ɗan da nasanin abinda na aikata.
Na jima kwance ina kuka, jin kaman wani na kusadani, yasai buɗe idanuna, Anim nagani zaune idanunshi sun kaɗa jajjur.
Tashi nayi na zauna tare da takure kaina guri guda, domin yanzun idan ba Abdul ba bana kaunar na keɓe da wani namiji.
Tashi yaƴi yaje ya rugo kofar, ya shiga tawowa yana ɓalle botton ɗin rigarshi, ja da baya nake. Cike da tashin hankali na fara girgiza masa kai cikin kuka nace.
“Karka min haka Anim! Wall..”
Zame wandonshi yaƴi ya kuma tun karoni, juyawa ɗakin ya fara min kafin wani lokaci duhu ya rufe min ganina baki ɗaya, gyara wandonshi yaƴi tare da rigarshi ya share kwallarsa. Zuwa yayi ya zauna yana kallon yadda na kara kyau, kwalla ne ya zubo mishi daga idanunshi. Shafan fuskana yayi cikin raunanniyar murya.
“Wani irin kaddara ce ta rabani dake? Me yasa cikin bai zo a kaddararmu ba yazo a kaddararki ke ɗaya, yau kwana goma barci ya kaurace min, bana jin daɗin kome sai tunaninki, matata da ta dame ni korarta nayi, Why Kyari? Ban kai irin namijin da kike buƙata bane da zaki samu. Nasan nafi wanda yayi miki wannan illar kome, dan nayi imani ina da makamin da zata cika miki kugunki ba sai kinyi tunanin wani namiji ba, sannan na miki Alkawarin zama dake har da yaron cikinki dan Ina sonsu Allah ya nufa a can zasu fito dan haka y’ay’ana ne daga wannan na cikinki har wanda zai zasu zo bayan aurenmu. Zaki haifa mim yara dozin dozin…”
Haka yayita sambatu, karshe da ya gaji yasa kai ya ficce yana share kwalla.
Zuwan wata nurse taga halin da nake cikine yasata fita takira Abdul. Yazo ya duba ni. Da yaga na farfaɗo ya saka ya fita.
………
Bansan me kuma yan gidanmu suke bukata ba dan yanzun sun tsananta fushi dani, kowa ya kaurace min. Baki ɗaya tun daga ranar da Nannah tafita bata kuma zuwa ba. Ummi ma haka, Umma ce da Nana Asma’u suke zuwa sai dare su koma.
Na kuma shiga damuwa fiyye da kima, abinda ban taɓa tunani ba shi yake zuwa min. Zan iyayi ba kawai dai na kosa da nagan ni a gida.
Satina biyu aka sallame ni zuwa gidan Abdul.
Abinda ban sani ba kuwa, tunda na faɗawa su Ummi me cikin. Nannah taje tasame Abbanmu da maganar, dan su fahimci juna. Da fari jikinsa yayi sanyi amma lokacin da shaiɗaniyar matarsa ta saka baki a maganar sai gashi an juya maganar da cewa Ummi da Nannah suka turani Jordan, karshe dai Mamie tayiwa Nannah tijara, kuma Abba bai hanata ba, karshe dai Nannah ta basu hakuri, da kuma rokon idan na haihu zata nimawa Ashraf aurena, Mamie tace.
“Bazamu bashi aurenta ba, dan aƙwai yayana da yake da mata uku shine ya nemi aurenta kuma Alhaji ya bashi ita dan ya karɓi sadakinsa. Kije idan kun gadama ku zubda cikin.”
Kan Nannah a sunkuye yake a sannu ta d’ago kanta idanunta sunyi wani irin ja. Hatta fuskarta sunyi ja murmushi tayi, sannan ta mike tace.
“Safina ta haramtawa kowani ɗa namiji sai Ashraf, ki rubuta ki kuma ajiye babu namijin da ya isa tsayawa a gaban Sarki na huɗu, Nuratu mijinki yasan gidan da nafito. Dan haka ki kiyayye harshenki, idan wani abu yasami cikin jikinta.”
Dariya tasa sannan ta ficce, sai da ta isa bakin kofa. Ta juyo cikin izza tace.
“Idan wani abu yasamu jikana dake jikin Binti! Toh wallahi sai na ɗaure kaf ahalinku sai an bawa manyan kifaye namarsu ke hatta Badaru da yake Uban Binti hukuncina bazai tsallake kanshi ba, kuma koda wasa wani yayi wa Binti kallon Banza ko ya ambaci cikinta da wani kazamin suna, wallahi na rantse da Allah idan jinin sarauta ke yawo a jikina sai nasa an yanke masa harshensa ko an cire idanunsa. Idan wasa kuke ganin a gwada, zan baku nan da sati biyu kuyi yadda yayi muku, kuyi abinda ya kamaceku, zan tafi Oman kuma zan dawo dan cikin Binti.”
Fita tayi bata kuma bin takansu ba taje ta ɗauki passport ɗinta, ta bar gidan tare da kiran Abdul, ya kai yata Airport. Shi da Ummi,
Dama Ummi ta koma gidan yayanta dake Suleja, Alhaji Ahmad Kamfut.
Ba sosai take zuwa ba dan ma suna fushi dani, fitowa nayi daga ban ɗaki ina ɗaure da towel. Naji an bankaɗo labulen ɗakin, Siphia ce hijab ɗina na shiga ja zan saka tayi tsaki, tare da cewa.
“Aikin banza karuwar banza kawai, ba a gidana xaki haifa min shege ba wacce ta zamewa Iyayenta bakar kaddarar ”
Saka kayana nayi ban kulata ba, na cigaba da saka kayana. Ina son zan fitane ina gama shiryawa na ficce a gidan sanye da bakaken kaya, na nufi wani shagon saida magani. Dukda ina tsorace amma haka na mika musu kuɗin suka bani, juyo tare da dawowa gida, kitchen na shiga zan ɗauki ruwa, ta hanani ta hanyar ce min.
“Nan gidan tsaftattatun mutane ne, ba masu kazamta ba. Masu zuwa aikata zina yanzun ma an dawo daga gu…”
Tsinka mata mari nayi cikin ɓacin rai nace.
“Kin isheni, gwarani tsautsayine ke kan bansan me zai faru dake ba nan gaba bana miki fata.”
Na tureta sannan na ɗauki goran ruwa na fito cikin d’aga murya tace.
“Karuwa kawai.”
Tsabar ɓacin rai ina shiga ɗakin maganin guda uku na ɓalla tare da haɗiyesu lokaci guda. Sannan na ɗauki abin maganin nasaka a cikin bahaya na sake mashi ruwa ya tafi.
Dawowa nayi na kwanta, dukda ina kokarin ɓoye tsorona amma a haka nake bawa kaina kwarin gwiwa.
Barci me karfine yayi gaba dani, har na minti talatin kafin maganin ya fara aiki, wani mugun murɗane ya taso min, na buɗe idanuna dakyar, tashi nayi naga yadda jini ke malala a bakin gadon, wani masifaffen tsorone tare da mugun ciwon ciki. Wanda yana murdamin jini yana ketowa da mugun karfi, har wani fuuuu yake.
Maida kaina nayi jikin gadon, nasake yunkura zan tashi wani jiri ya dawo dani tare da tsinkewar Jini tsuuuu. Sharaf na koma idanuna suna masu kafewa……………
*Toh burinku ya cika ciki dai ya zuɓe kowa ya huta kar naji any korafi😎😏*
Wallahi ku bar tambayata daga farko😭
#MJ
#HZƘ
#Vote
Oum Muwadda……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITERS ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
INA JI DAKU ZAUREN MAI_DAMBU FANS CLUB MUSANMAN, AMMYN KHAIRAT, SAMEERA,MAMAN DADDY, MRS YUSIF…GA KYAUTARKU nan bayawa…..😹😎 Sai dai na fahimceku ai kodan Albarkacin Binti Nannah zata ɗ’aga musu kafa….. Amma wata tace.yadda tasan larabawa da kaunar y’ay’a. toh ba asan maci tuwo ba……
ZAUREN MAI_DAMBU NOVEL GRP ga tukwaicinku nan Yan amincin Sultan Ashraf
@Mom Sayeed @Smartzeezee @Ummulkhairi Muhammad Sani @Maryam Kolo @Oum Nawal @Naja’atu Sani
@Meelat Ib
@My Meerah
@Maman A3 and M2 @M Muhammad
@Hafsat Abubakar
@Aichatou Mani Kane
@lubabatu shehu shayi
@Fatima Madaki
Fatan Alkhairi HZƘ FANS musamanku…..
@🌹Maryama🌹
@🍇MOMYN ILHAMA🍇
Page.٢١
A hankali bakina ke motsawa ina son kiran Sophia, amma ina numfashina yabar gangan jikina, ina cikin wannan halin sai ga Abdul ya kawo min, rake dake tunda na dawo yake kirana da Mommyn Littil dan haka yana shigowa da abinda ya fara cewa kenan.
“Mommyn Littil boy!!!”
Ya buɗe kofar kawai yayi mugun gani, watsar da abin hannunshi yayi ya shigo da gudu kuma duk sai ya ruɗe, ya koma da baya yaje ya buɗe motarshi ya dawo ya ɗauke ni jikinshi na rawa, sai cewa yake.
“No..no..no, Safina buɗe idanunki. Ga Dudunki nan don Allah karki rufe gani nan zan kaiki asibiti kinji Yayata buɗe don Allah.”
Duk ya birkice sakani yayi cikin motar sannan ya koma mazaunin driven yaja motar da mugun karfi yakure motar duk wanda yaganshi sai ya matsa mishi a hanya, sabida gudun da yakeyi. Allah kaɗai ya kaishi asibiti, yana shiga yayi wani irin parking ya fito da mugun sauri ya cinciɓeni ya shige cikin dani yana kiran “Dr!!! Nurse ku kawo min agaji jininta zai kare.”
Dake ansanshi, kuma ana ganin mutuncinsa, da sauri aka kawo gadon ya ɗaurani. Aka wucce dani ɗakin yan ɓari. Rike dr Muhsin yayi cikin tashin hankali yace.
“Frnd! Ina son dukkansu a raye, don Allah.”
Rike hannunshi Dr Muhsin yayi cikin kwantar da hankali yace.
” Insha Allah zanyi iya kokarina.”
Haka ya janye hannunshi har likitan ya shiga, zama yayi akan bencin da yake gurin…
*OMAN*
Zaune take tayi kuka har ta godewa Allah, Yayanta sarkin daular Oman ya sata a gaba sai taci abinci kamar magani take haɗiya, kallonshi tayi cikin kuka tace.
“Akkhi haka zan cigaba da rayuwa makiya suna galaba a kaina, da shi Muh’d ɗin.”
Gyara zama yayi cikin rarrashi yace.
“Tun ranar da naji kasar saudia takama shi, na tura lauyoyina da kuma wasu daga cikin aikatan sirrin da na tura Amman dan lura da lafiyarshi, a yanzun haka ana bincike ne, idan aka same shi da laifi toh Allah ya kare.”
Share kwallarta tayi, sannan tace.
“Naso komawa Nigeria amma zan zauna a nan har Allah ya fitar dashi sai muje baki ɗaya.”
Sun tattauna sosai, sannan tabar gun yayanta zuwa shashinta..
(😂 Nannah ta makale😉)
*SAUDI*
Tunda hukumar saudia ta kamashi, bata azabtar dashi ba sabida ya fidda passport ɗinshi da lasisin zamanshi a kasar, kasancewa yayi karatunsa na degree a nan saudia a fannin Islamic law, yaje Germany ya karanci law har na tsawon shekara huɗu. Sannan ya dawo saudia degree dinsa na uku a fannin law ɗin.
…… Ashraf a idanun masarautar jordan karatun boko yake. Amma a zahirin gaskiya karatunsa ta fannin musulunci ya zurfaffa. (ku biyo ni a sannu dan ji waye Ashraf ne)
Daga saudia an tura masarautar jordan domin su san halin da yake ciki, kin saurarra dan sakon sukayi karshe ya dawo da bakar magana. Haka ya harzuka jami’an jakadancin Saudia a nan Amman, inda suka fara yunkuri yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. Saiga sako daga kasar Oman. Wannan dalilin yasasu hakura da yanke hukunci aka fara sabon bincike.
***
*Nigeria*
Wasa farin girki, dr Muhsin ya zata zai iya ne, sai da abin yashiga bashi tsoro dan tsakani da Allah suka min alluran da zai tsayar da jinin, amma yaki tsayuwa asalima jinin sake zuba yake, a gigice ya fito yana zare glass ɗinsa ya kalle Abdul.
“Dr Kyari sisternka zata iya mutuwa fa, wallahi jinin yaki tsayawa, duk da mun mata allurai amma kamar karashi ake.”
Shiga ɗakin Abdul yayi ji yake kamar zuciyarsa zata buga, shigowar wasu likitoti guda uku yasashi juyawa, biyu bakakken fatane, ɗayan kuma ɗan kasar india ne. Yana zuwa kaina ya ɗauki takarda ya rubuta sunan magani, ya mikawa Abdul da sauri ya fita. Kallon sauran likitan yayi bayan yasaka handglove ya shafo jinin da yake ɗiga a kasa ya kallesu. Shinshina jinin yayi, ya kaɗa kanshi yace.
“Tayi amfanin da maganin zubda ciki da karfin tsiya, ko kuma an bata taci bata sani ba. Ga jinin yana karnin maganin kuma idan ba ayi da gaske ba mahaifarta zata iya samun matsala dan maganin tayiwa jininta karfi.”
Abdul na shigowa ya mika mishi maganin, buɗe kwayar yayi ya yaye zanin da aka rufa min ya kauda kanshi ya saka min maganin a cikin jikina, sannan ya ɗago hannunshi ya kalle Abdul yayi masa bayani, janyo machine ɗin scanner yayi ya ɗiga min luquid ɗin sannan ya shiga dubawa yana musu baya yace.
“Toh cikin yafita fa!”
Cigaba yayi da dubawa karshe ya ɗaga daga jikin cikina yace.
“Dr Kyari am so sorry we lost the baby”
Gyaɗa mishi kai Abdul yayi cikin jin zafina, wanke hannunshi likitan yayi yace.
“Idan ta farka za a mata wankin ciki.”
Gyaɗa kai kawai Abdul yayi, sannan ya fita, suma fita sukayi. Nana Asma’u yayi ya gaya mata halin da nake ciki, ta kira mijinta ta gaya mishi.
Ummi ya kira ya faɗa mata, ita kuma ta kira Fatima akan tazo ina asibiti kafin gobe tazo.
Gidanshi ya wucce yasami gidan yadda ya barta cire kayanshi yayi yasaka a cikin machine din wanki, ya saka Ariel. Tare da ruwa sannan ya komo ɗakina ya gyara tare da goge ko ina yasaka room fresh.
Yana fitowa yaga Sophia da kayanshi da yasaka a cikin machine ɗin wanki. Ta watsar dama a tafashe yake niman abokin taƴi yake, sai akayi dace itace ta taro match ɗin, ba faɗa ba zagi ya kwashe kayanshi ya zo ɗakinshi ya wanke sannan yaje ya shanya, ban ɗaki ya shiga yayi wanka sai cizon lips ɗinsa yake, dan ya lura hatta yaranshi ta kwashesu takai gidan iyayenta, wai kar a lalata mata tarbiyansu.
Yana gama shirƴawa ya nufi masalaci daga can ya shige asibiti. Yasame Nana da Fatima suna ɗakin jum, ajiye take away ɗin da yazo da ita yayi sannan yace.
“Bata farka ba ko?”
“Eh Baban Affan har yanzun ga abinci nazo maku dashi. Wallahi tausayi Didi take bani, daga wannan sai wannan, kasan da nacewa BABAN Sabir dukanta Abbanmu yayi,kamar ya rufe ni da duka. Karshe har kaurace min yayi wai abba bai kyauta ba,tuntuni bata lalace ba sai yanzun da kaddara ta faɗo mata, wallahi badan yana kunyar Ummi ba da ya maka abba a kotu.”
Zaro ido Fatima tayi tace.
“Abban Affan da fatan cikin bai zub…”
“Na nawa kuma ai ta zibda cikin naso ta haifi yaron da Abba yaganshi, cikin safina ba gama garin ciki bane, dan cikine da yake da gata gaba da baya, akan cikin nan kuwa nasan sai Safinah ta zama abin alfahari a cikin danginmu amna dake lusara ce dan farin cikin Abba ta zubda shi.”
Rike baki Fatima tayi tana zare idanunta, kafin tace.
“Amma wallahi akwai kura! Dan kuwa Anyi rigima akan cikin…”
Nan ta gaya musu aikuwa Nana Asma’u me zatayi banda dariya, tace.
“Lallai akwai wuta a gaba.”
“Ai ni zan faɗa mata gaskiya Safina ce ta zubda cikin, kinsan da zata tafi me tabani, wallahi wani akwati ta bani zallar sarkoki da yan kunaye ne a ciki a na sayar na dinga saya mata abinda take so, kinga wannan alert ɗin yau da safe aka turo shi da dallar amurka zunzuruntu kaunar da takewa wancan sakarya, da abin cikinta, ɗazun sai da takirani ya take ya cikin wallahi yau sa safina kasa dani take tana tashi sai na mata dukar kawo wuka.”
Shiru sukayi kowa da abinda yake yawo a ranshi, har Baban Sabir yazo tare da Annur.
Sai karfe tara da rabi suka tafi, aka barmu daga ni Fatima. Abdul ya koma gida.
……..
Washi gari da safe Nana ta kawo mana abin karyawa, karfe goma sai ga Ummi tazo. Har lokacin ban farka ba.
Sai karfe uku da rabi na farka dishi dishi na fara buɗe idanuna, a hankali idanuna suka buɗe. Ummi da Abdul na gani a zaune Fatima ta tafi makaranta, Nana kuma ta koma gida yin abincin rana.
Gyara zama Ummi tayi cikin ɓacin rai tace.
“Zubda cikin kikayi? Duk wahalar da naƴi da rasa aurena da nayi ya zama a banza, na koma gida a matsayin bazawara Kin min adalci Safinah, laifin meye Muka miki da zaki zaɓi zub da cikin, Wallahi idan Hajiya Asma’u taji abinda kika aikata har abada bazata taɓa kallonki da kima ba, nagode da abinda kika aikata min, banda Hjy Asma’u daga ce mata cikin jikinki na D’antane har da rawan jikinta ta amshiki, toh wallahi zan gaya mata cewa cikin ba na Ashraf bane har kin zubar da shi.”
Lumshe idanuna nayi, tare da komawa na kwanta. Kwalla nabin gefen fuskana, ji nake kamar na fasa ihu. Fita tayi Abdul yayi yana share kwalla, domin ina jin sautin kukan Ummi, kokarin tashi nake amma bani da karfi komawa nayi na kwanta na cigaba da kuka.
……… Sai da Nana ta kawo abinci Ummi ta koma dan tace matuƙar ta cigaba da ganina bakin cikina ne zai kasheta, Ummi da Abdul fushi suke dani, ina samun sassauci ta ɓangaren Fatima da Nana, Khalil da Khalila, Abba Lawan sau ɗaya yazo ya koma, dan Umma ta gaya mishi. Ganin halin da nake ciki ya ɗaga mishi hankali, dan sai da ya same Abba da maganata. Karshe yayi masa bibiɗi, suka rabu dutse a hannun riga.
Kwana na biyu aka sallame ni, koda na dawo gidan Abdul bai nunawa Matarsa muna rigima ba, sai dai ya ɗauke min wutane sosai. Duk sai na shiga damuwa, amma ina kokarin jan saura kimata da ta rage. Dukda naso kin biyewa Matarshi da take min iskanci, idan ina jin yunwa Atm ɗina nake ɗauka da keyn motana, tafiya gidan Abinci nake naje nasayo abincin da raina ke so.
***
Kwanaki sun haura satitika, satitika sun haura watanin, a yanzun kusan wata Huɗu babu Ashraf ba labarinsa, nayi kuka sosai gashi babu wanda ya faɗawa Nannah cikina ya zuɓe.
…….. Duk iskancin da Sophia take min ban tankata ba, haka zata zo idan ina falo tayita habaici har sai na bar falourn zata hakura.
Wani abin da yake damuna, yawanci kamar jaka. Idan nasaka abinci a gabana sai naga bayan kwanu, ga kuma kwaɗayi. Idan naji kamshin girkin Sophia kamar xanyi hauka, amma dan rashin mutunci bata bani. Yau ina jin kamshin abincin da ya cika gidan na mike a hankali dan kwana biyu jikina nauyi yake min, ga ciwon jikn da bansan dalilinsa ba. Na nufi kitchen ɗinta tana fama da aiki na shiga da sallama nace.
“Don Allah Sophi abincinki zaki samin ko kaɗane”
Wani kallon banza tayi min sannan tace.
“Toh kwartonki bai kawo miki bane? Ko kuɗin da ake min burga ya kare ne.”
Girgiza kai nayi cikin tsananin bukatar abinci nace.
“Dan girman Allah ki bani koda kaɗane kika ce na biya zan biyaki.”
Dariya ta fasa tare da tafa hannunta tace.
“Wow kice kwartonki yana sake miki kuɗi, ok ga Acc numberna naji 50k”
Jikina na rawa na koma ɗaki ma ɗauko wayata na tura mata, tsabar wulakanci kuɗin na shiga tace.
“Zan baki amma sai kin min wanke wanke, ki wanke min kayana sai nima nasaka miki.”
Sunkuyar da kaina nayi tabbas duk macen da ta zubda kimarta sai an wani gari sa’an kaninka shi zai sakaka aiki, murmushi nayi tare da cewa.
“Bani wankin, na fara dash..”
“Bazaki wanke ba! Ni Sophia kika ciwa mutunci yayata kikewa haka? Ba damuwa Didi jeki ɗaki zan kawo miki abincin da kuɗinki.”
Kamar zanyi magana sai na fasa, shiga kitchen ɗin yayi itama ta ɓata rai tace.
“Ai nayi kokari tunda Uban da ya haifeta ya kor…”
Abincin ya ɗiba har yazo bakin kofa yace.
“Ki ajiye mata kuɗinta, sannan kuma ki haɗa kayanki idan zan koma zanyi ajiyeki a gidanku, aai kuma ina miki albashir da next week zanyi aure idan na kaiki ki musu bayani azo a kwashe kayanki………
**** Ban kar zo man ba …🏃
……
*(Ina kira gareku ban manta Ashraf ba, ina sane dashi babu yadda saudia zata yanke mishi hukunci har sai ta sami shaidu da kwarara akanshi ku biyo ni cikin labarin me cike da ban haushi da ban tausayi sadaukarwa soyayya, makirci hassada kiyayya rashin fahimta kyashi mugunta,munafuci zalunci, yaudara cin Amana)*
#MJ#HZƘ#Vote….
Oum Muwaddah……. 😎
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITERS ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Page.٢٢
Tawowa yayi ya kawo min abincin, sannan ya ajiye min kallonshi nayi zai fita nayi maza na rike hannunshi, cikin rawar murya nace.
“Kayi hakuri Dudu.”
Murmushi yayi min kaɗan sannan yace.
“Kici, idan bai isheki ba a karo miki.”
Girgiza kai nayi, nasaka abincin a gaba na fara ci, har zai fita nace mishi.
“Abdul! Don Allah ka kaini suleja ina kewar Ummina.”
Gyara tsayuwarshi yayi, sannan ya shafe kwantaccen gashin kansa yace.
“Ok ki gama sai na kaiki in yaso jibi sai ki dawo.”
Gyaɗa mishi kai nayi, shi kuma ya fita.
Sosai naci abincin sannan naje ban daki na wanke bakina bayan nayi wanka, na shirya cikin bakakken kaya, doguwar riga da bakin gyale, sannan na ɗibe kayana sosai. Sannan na fito na same Madam sophia a tsaye. Yana fitowa ya ɗauki jakana, muka fita, gaba ya buɗe min na zauna yasa jakar a baya itama tashiga yajamu muka tafi.
…….. Har gidan iyayenta ya kainta wanda yake kusada gidanmu, kallonshi nayi zanyi magana muryarta ƴa katsemu tace.
“Karuwa hankalinki ya kwanta, kin rabani da mijina. Muguwa azzaluma baiki aure ba harkin kashe auren kaninki, a haka zaki kare.”
Ji nayi kirjina yayi min nauyi, dakyar nake jan numfashina, tabbas an taɓani amma ba kome. Bai damuwa yaja motar muka bar layin. Tunda muka ɗauki hanya bai ce min kome ba. Nima haka muna dab zamu shiga suleja naga masu fura da nono..
“Dudu! Zansha fura.”
Sauka yayi a gefen hanya sannan ya fita, yaje ya sayo min. Yana shigowa ya mika min, naji jikin goran yayi matuƙar sanyi, buɗewa nayi na fara sha, wani sanyi daɗi tare da garɗi me shiga rai ya gauraya furan ina kurɓa tare da lumshe idanuna, komawa yayi da baya yasake sayo min gora biyu, dan tun bamu bar gurin ba na kusan shanye goran.
Kafin mu isa gidan Uncle Ahmad na shanye goran farko na kuma buɗe na biyu shima sai da naga bayan rabinsa naji cikina ya cika, kwanar da zai kaini gidan. Muka hango mai sayarda gashen masara, tare da ayaba a gashe. Bani manta lokacin da na gama karatu aka turani Imo naci ayabar da gyaɗa.
“Dudu! Ayaba da Masara,”
Tsayawa yayi yasaya min sannan muka wucce gidan, Yaran gidan suka taremu da murna gasu da tarbiya, karɓan kayan sukayi tare da kai mana ɗakin Ummi, Gaida Mama Saratu mukayi tayi mana yar nasiha sannan muka wucce, ɗakin Ummu tana zaune akan abin sallah ɗan karamin part ne har da kitchen a ciki, koda zata so wani abu ta dafa da kanta, ajiyar zuciya na sauke. Sannan na zuɓe a jikinta tare da sake ajiyar zuciya. Murmushi ta sake tare da ɗan tureni cikin tsokana tace.
“Abinda Dudu bazaiyi ba shi kika fi aukinyi, baki san kin girma bane.”
Tura baki nanayi gaba sannan na kara, kwanciya jikinta ina sauke ajiyar zuciya tare da maida kwalla, kamar yadda nasaka kaina akan cinyar haka Abdul ya ɗaura aƙan kafaɗarta muka shiga hiran. Cikin gajiya da mutuwar jiki nace.
“Ummina na gaji jikina ciwo yake min tare da mugun nauyi gashi bansan waye zai min tausa ba amma jikina na mugun damuna.”
Gyara zama Abdul yayi sannan yace.
“Tun yaushe haka ya fara damunki?”
Juya idanuna nayi cikin jin daɗi yadda Ummi take matsa min kafafuna nace.
“Dudu kusan wata uku kenan, tunda abin nan ya fita.”
Na karshe maganar a raunane.
“Tashi muje a dubaki.”
Abdul yace min.
Taɓe baki nayi nace.
“Allah bani zuwa ko ina, bana son fita yanzun ma baka ji yadda nake jin amai bane, da zaka ce min mu sake fita.”
“Kyaleta tukun ko zuwa gobe zansa Abideen ya kaita.”
“Yawwa Ummina, Mother like no Other. Ilove you so much.” na gaya mata ina lumshe idanuna,
Zaro ido Abdul yayi, sannan yace.
“Ina bolar mutanen da aka tsana Ummi kinganta ko akan idanunki kenan”
“Dudu har yanzun baka daina kishin nan ba.” nace mishi tare da gwalo.
Gyara zama yayi sannan ya sunkuyar da kanshi, ya faɗawa Ummi abinda yayiwa Sophia.
Dariya tayi tare da cewa..
“Toh su me yar uwa shine har da koran yar mutane gidansu, baka ci riba wallahi ai bazata damu ba kaje kadawo da ita kuma ka Safina bazata koma ba, in dama dan itace ta zauna a nan, idan kayi hakuri zaka sha mamaki yanzun ka maida ita ɗakinta batun aure kuma ka jany..”
Cike da jin haushi na mike nace.
“Ummi kince ya maidata ya maidata, amma Aure kan wallahi sai yayi nice ma zan haɗa maka kaya ko sisinka karka kashe.”
Make bakina tayi, cikin fushi tace.
“Me garinku! Ce miki akayi auren haka zai yi ba lissafi, dan ta miki laifi sai ku mata ramuqar gayya, kul kada naji ko na gani, aure bazan hanaka ba, amma ba yanzun ba kaje ku sasanta tukun.”
Fuuuu na mike a falon na shige inda nake tsamani kitchen ne naje na saka furar sannan na fito zuwa ɗakinta ina shiga na zube a bakin gadon, tare da kwanciya.
Ban san tafiyar Abdul ba dan ban tashi ba sai uku saura, a gurguje naƴi alola, tare da gabatar da sallah. Ina cikin addu’a Ummi ta leko.
“Yakolo me kike so zaki ci.”
Kasancewar sunan da take kirana dashi kenan sabida sunan Kakata ce dani. D’ago fararen idanuna nayi masu cike da barci nace.
“Taliyar murji da miyar jajjage amma Ummi na manja, sai ko alale duk wanda nasamu zanci.”
Shiru tayi can tace.
“Ina ga alalen zaki samu taliyar zance a kawo min daga kano aƙwai Asiya kanwar Matar kawunku zatazo wani sati.”
Gyaɗa kaina nayi, ita kuma tafita, akan sallayar na gungura. Karfe huɗu da rabi na farka, tare da mika, sannan na nufi ban ɗaki nayi wanka. Anan na karewa kirjina kallo sunyi wani irin cika. Dan wani lokacin idan nasaka bra ciwo suke min, dake kuma bani da irin mugun halittar nan. Sai haka ya tafi da jikina, amma maganar gaskiya nayi mamaki cikar kirjina, domin sunyi girma ba laifi dan suna tsaye ne car..(😎 kar a fassara min maganata)
Marata na shafa naji yayi min ɗim, ɗan latsashi nayi naji yayi min tauri ga zafin da yake min dole na hakura na fito.
Dukda ina da matsala a duk lokacin da watana yaƴi amma nakan share wata biyu ana uku nayi hailata sai dai tunda nayi yunkurin zubda cikin. Ban kuma ganin hailata ba gashi har wata huɗu.
…….. Ina idar da sallar la’asar na fito falon nasamu har Ummi ta gama min, zama nayi jikina har da rawa, ga yaji a gefena. Ci nake ina wani lumshe idanuna tsabar daɗi, ina cinyewa ta kuma kawo min karɓa nayi na cinye. Zaro ido tayi.
“Yakolo cikinki yayi yawa fa.”
“Wallahi kuwa Ummina, bari na sha furar nan inaga zan koshi.”
Ina shiga kitchen ɗin ta bini da ido, cike da tausayi. Bata san na fito ba sai da na shiga shan fura me sanyi, ina shanyewa na tuna da masara da ayaba. Ɗauka nayi na fara ci ta kwace.
“Haba ina zaki kai su?”
Tura baki nayi sannan nace.
“Ummi bana jin daɗin bakina babu tauna don Allah taimaki jaririyarki mana”
Yadda na mata sai da tayi dariya, sannan ta mika min ina karɓa na kwaɓa fuska nace.
“Ummina bari na ɗumama su.”
Tashi nayi naje ɗumamawa, ni da naje abu daban sai gani na koma yin wainar fulawa, lekowa Ummi tayi taga abinda nake. Murmushi tayi tazo ta ja kujera ta zauna ina kwaɓa fulawar.
Har na fara soya tana murmushi, dan tun da nafara nake cin ɗaya ɗaya, kafin na gama na cinye kusan rabi.
“Anya Safinatu cikinki nan ba rowa yasaki ba.”
Wanda zan kai bakina ne ya faɗu kasa, cokalin hannuna shim Ya faɗi.
“Kina mamaki bayan kinsha magani yafita ko? Ai tunda Allah ya tsara shi a kaddararki ba makawa sai kin haifeshi, shawara ɗaya ce ki nutsu har Allah ya rabaku lafiya, tunda na amince da kaddararki ina ga babu amfani ki sare, idan kikayi haka zan ɗauka dan mahaifinku kikayi idan kika haifa min cikin zanyi farin cikin ansar kaddararki hannu biyu. Kuma zanyi alfahari dake, shi yasa nace bazaki koma ba ki zauna a nan ki haihu.”
Wani iri nasiha Ummina take min wanda yake bin jikina da duk wani gabba yana kashe min su.
Ga wani irin soyayyar da take gwada min akan cikina da kuma ni kaina, bansan wa tabawa aika ba sai ga kayan baby. Cikin katon jaka, kunya ya hanani ko kallon kayan, dan wallahi yadda na tsani Ashrf haka na tsani cikin jikina ya yaudareni da cewa zai zo kuma ya barni cikin hatsari.
…….. Yau monday na fara zuwa asibiti, ina bin layi aka zo kaina. Sunana suka tambaya na gaya musu, sai da suka ce.
“Sunan Mijinki fa, kin bamu safina kawai.”
Shiru nayi cikin tashin hankali na lalube wayata na turawa Abdul text lokacin yana tare da Anim, turo min yayi da “kisa Abdul”
Haka kawai sai naji zuciyata tayi min nauyi.
“Ashraf!!”
Nacewa matar kaina a sunkuye, “Amma baki jima da aure ba ko? Irin wannan kunyar har ina.”
*Da kinsan matsayin cikin da kallon banza zaki min* nace haka a raina.
Nasha yawo a cikin asibitin dama privet ne, ina gamawa Abideen yazo ya ɗauke ni, sai wash wash nake. Shi kuwa yayita dariya wai nafi kowa ragonta.
***
*SAUDI*
Shiru lawyershi yayi yana kallon yadda ya koma, can lawyer ɗin yace.
“Yallaɓai!”
D’ago kanshi yayi cikin kokarin ɓoye damuwarshi yace.
“Ina jinka”
“Kayi magana man, wallahi mahaifiyarka tana cikin damuwa, sai.”
Naɗe hannunshi yayi sannan ya koma jikin kujerar yace.
“Kace mata karta damu haka Allah ya nufa, ta roka min ita wacce tazo dominta da ta yafe min, sai me?.”
“Baiwarka Safinah!”
Kuraqa lawyer idanu yayi kamar zai cinye shi da su. Sannan ya sauke su akanshi tare da kauda kanshi, haɗiye yawu lawyer yayi sannan yace.
“Tana ɗauke da cikinka?”
Dunkule hannunshi yayi kamar zai kai naushi, ya ɗago tare da bin lawyer da ido, sannan ya mike zai bar gun lawyer yace.
“Tana cikin halin rayuwa dan sanadin cikin zuri’arta sun tarwatse.”
Bai saurari Lawyer ba. Ya koma ciki kwalla na zubo mishi. Tabbas har da hakkin Safinah ke ɗawainiya dashi, ya lalata mata gobenta ya kuma ɓata mata rayuwarta, gashi har da rabo a tsakaninsu.
Gwara ya amince da laifin dan bai san yadda zai fuskanci safinah ba, shi da yace nan da wata biyu…… Lumshe idanunshi yayi.
***
*Abuja*
Shan gabanshi tayi cikin bala’i da masifa tace.
“Nice zaka munafutarta bayan kaji abinda karuwarka tayi na ƙunya aka fasa maganar aurenku shine yanzun ka koma binta. Na rantse sai naga bayanku ada can ma sabida Innarka na amince a yanzun kuwa zaka gani dani kake zance.”
Bai kulata ba yayi ficcewarsa. Ya rasa inda zai kai fitinar Rabi wallabi ta buwayi rayuwarshi, bai san inda tajiyo ya koma niman Safinah ba, shi abinda yasani yana tare da Abdul, kuma yana samun labarinta kuma Insha Allah sai ya aureta.
***
Shiri nake amma jikina a sake, dan bana son zuwa asibitin dukda yanzun cikina watanshi na biyar kenan, ina jin yadda yake juyawa. Gashi yayi wani mugun girma, har ma yana son fin wataninsa, a yanzun babu takalmin da yake min sai silifas, duk zuwan Abdul sai yayi min tsiya wai na tara tsokoki kumatai, tabbas haka ne dan a wata biyar na zama ruguzun ruguzun. Gashi na kara buɗuwa sosai, ina gama shiryawa na fito. Yau babu Abideen da zai kaini, sallama nayiwa Ummi nayi addu’ar fita a gida, sannan na nufi bakin titi. Ina jirar taxi sai ga wata Audi, me tintec. Sauke glass ɗin akayi na kauda kaina. Me motar yace.
“Malama Safinah! Shigo na kaiki mana.” da mamaki na kalle shi sai na kauda kaina.
“Kishigo cikin ruwan sanyi dan duk nan da kike gani akwai mutanenmu, kuma zasu iya sakaki a cikin motarda karfin tsiya, kawai ki shigo.”
Shafa cikina nayi a hankali naji yadda yake juyawa sakamakon bugun zuciyata, kwalla ce ta zubo min me zafi, nasaka hannu na buɗe motar, bakina ɗauke da addu’ar niman kariyar Allah. Ina jan kofar ana sako hannu tabaya aka shaka min ɗan farin kyale, bingirewa nayi da barci ….
#MJ#HZƘ#Vote……
Oum Muwadda……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITERS ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
GA KYAUTAR SHAFI NAN NOVELLA Ku kaɗanku…
Page.٢٣
Bansan iya adadin lokacin da na ɗauka ina barci ba, ni dai yunwar cikina da kuma wutsilniyar yaron cikina yasani na tashi, mika nayi tare da addu’ar tashi daga barci. A sannu na kebin ɗakin da kallo hannuna dafe da cikina, a karon farko da naji tausayin yaron cikin ya cika min zuciya, sunkuyar da kaina nayi ina shafa cikin a raina nake cewa.
*Kai ma kashiga cikin kundin kaddarata ko? Gashi tun baka zo duniya ba na fara wahalar da rayuwarka daga wannan sai wannan*
D’ago kaina nayi cikin nutsuwa ina karewa ɗakin kallo, kome na cikin ɗakin farine. Hatta kayan jikina fari ne, *Waye ya sauya min kayana?”*
Tambayar da ban same amsarta kenan, murɗa hannun kofar akayi. Da sauri na ɗago kaina ina jiran shigowar wanda yayi nasaran kwamusheni.
Turo kofar yayi ɗan karamin bakinshi ɗauke da sallama. Mikewa nayi jikina na rawa, haka ma bakina ya kasa furta kome, sai nuna shi nake da yatsa kamar mareniya nace.
“Anim Kamil Matawalle! Meye nayi maka ne da zafi? Wa….”
“Anna shigo min da abincin.”
Take wata baturiya ta turo abincin a keke. Raina a ɓace tsiwa nacina nace.
“Uwar me na maka da zaka satoni? Nd ina nan?”
Bangaje shi nayi na fita banga hanya ba, dan naga kamar hotel ne. Zan iya cewa na manta da ciki a jikina na zura a guje, nayita ratsa kofifi da manyan faloka har na sauko kasa, ganin kofar karshe yasani karawa da gudu, ina tura kofar na zaro idanuna. Fisgoni yayi baya.na kwace kaina na fasa ihu nayi tare da zubewa lokaci guda na fashe da kuka me tsanani. Ina hango inda nake wani bakin cikine ya kamani. Na tun kari kofar yayi maza yasha gabana cikin tausassiyar murya yace.
“Pls ki saurareni!”
D’ago jajjayen idanuna nayi, a sannun na lumshesu. Nace,
“Anim! Why me? Nayi chanchanci haka daga gareku ko? Me yasa duk wata damuwa sai nice zaku ɗaurawa, a bisa tsautsayi na tafi can kaddara rubta dani, yau gashi dan son kanka karabani da iyayena, kai ma jikin nawa kake bukata ko? Ince jikine yake ruɗarku kuke ganin wani abin arzikine, ya ɗauki nashi kason kaina muje na baka, tunda haka Allah yayi ni kowani namiji ya ɗibo dattinsa ya zuba a kaina, muje na baka.”
Tunkara shi nayi raina a ɓace, sai masifa nake.
“Kyari!!! Ni…”
“Me zaka gaya? Ehhe meye zaka gaya min?
“Amma ya dace ki saurareni” ya faɗa da sigar lallashi.
“Wallahi Allah sai yasaka min mugu azzalumi, macuci.”
“I heard that daga bakin Rabi’atu.”
Tsaki nayi na juya zan koma ɗakin, yana biye dani sau biyu ina ɓata kafin na amince yayi min jagora zuwa ɗakin, ina shiga na fara niman wayata nasameta a kasar pillow, ɗauƙa nayi naganta a kashe, ina kunna wayar naga babu service, fita nayi na koma har hanyar ɗazun babu service babu alamarshi.
“Ai bazaki taɓa samun service ba sai ini ne naso ki samu, ki bani.”
“In baka wata uwar? Lallai Anim baka da kunya da mutunci nice zan baka kain…”
“Ke ni bana son hauka! Ki bani lokacinki muyi magana na gaskiya, Step Mother ɗinki ce taje gidanmu ta faɗawa Innata, kome ina shirin na tambayeki gaskiya na kuma jin irin haka a bakik abokan aikinmu, nifa ban taɓa kallonki da sigar sha’awa ba sabida nima Ubane ina da nawa yaran bazan so..”
“Don Allah get out” na nuna mishi hanyar kofa..
Murmushi yayi sannan ya shiga ɓalle rigarshi, dafe cikina nayi a tsorace nace.
“Na haɗaka da Allah karka cutar da Yaron da bai san waye shi ba.”
Murmushi yayi cike da kwarin gwiwa yace.
“Toh zaki saurareni?”
Gyaɗa kaina naƴi kwalla na zubo min,
“Ok zauna kici abinci!” yace min.
Ba musu na zauna tare da wurga mishi tambaya nace.
“Ina ka kawo ni?”
“Atlanta Ocean muna cikin jirgin ruwa ne” yace min a takaice, tausayin kaina ne ya kamani. Me yasa rayuwa take wasan kwallo dani.
Zama yayi ya shiga zuba min sannan ya fara ɗiba zai bani na kauda kaina yace min.
“Hmm”
Babu wasa a fuskarshi, amsar abincin nayi a sannu yayita bani, har naci kaɗan, sannan nakauda kaina nace.
“Yaushe zaka maidani gun Ummina da Duduna”
Taɓe bakinsa yaƴi sannan yace.
“Sai lokacin da naƴi niyya.”
Kura mishi ido nayi jikina yayi mugun sanyi,
“Duk akan me?”
“So!!!”
“Cuta dai! Matawalle wannan ba so bane cutane.”
Shafa fuskana fuskana yayi fuskarshi cike da damuwa yace.
“Cutie sabida so na ɗauko ki, naga mutane zasu min shamaki ne dake, Dudu, Innata, Rabi’atu. Zasu min katanga dake suna shirin min bakin ciki. Kinga yadda ciki yayi miki kyau, ina son ganinki a haka shi yasa na kawo ki nan, pls ki barni na taɓa ki.”
Zaro ido nayi ina ja da baya tare da girgiza kaina, bakina na rawa nace.
“Karka min haka, Anim wallahi ni ba mazinaciya bace.”
Ina matsawa yana matsoni, sai da muka kure gadon, rufe idanuna nayi. Kwalla ya shiga zuba min. Hannunshi naji a kan cikina yana shafawa a slow, tsigar jikina ya mike. Kwalla masu zafi suka shiga zuba da mugun gudu. D’ago kanshi yayi yaga yadda kwalla suke wasan tsare akan fuskana, abinda najine yasani buɗe idanuna,
*Allah sarki Sultan banda wannan abinda ya faru damu bai taɓa kuskuran taɓa ni ba*
“Anim!!” na kirashi a hankali,
“Hmm! Cutie.”
Girgiza mishi kai nayi, hannunshi naji a bayana, kuka nake wiwi ina tureshi haka Anim ya cigaba da, bin jikina.
“Ashraf!!!”
Na ambaci sunanshi, d’ago kanshi yayi da jajjayen idanunshi Jijjiyar kanshi yayi raɗa raɗa, yace.
“Uban cikinki ko? Safina meye yasa?”
“Wayyo Allah na! Nace da karfi, ina rike hannunshi. Mugunta zalla ya min, danne cibiyata yaƴi.
“Idan kika kuma kiran sunanshi sai na illata wannan abun domin kuwa shi ya hanani ke shi ya rabani dake,”
Bansan wata irin rayuwa nake ba, daga wannan matsalar sai wannan. Ji nake ina ma banq cikin duniyar nan, sai da yayi da kanshi ya kyale ni, anan na kwanta na cigaba da kuka.
***
*Suleja*
Kallon agogen falon Ummi tayi. Karfe biyu saura na rana Safina babu dalilinta, mikewa tayi ta fito har part ɗin Mama ta zauna cikin damuwa tace.
“Maman Abideen har yanzun Yakolo bata dawo ba, kuma karfe goma take dawowa. Kinga har biyu fa.”
“Maman Safinah kina da hankali kuwa, yarinya tun goma bata dawo ba, shine baki faɗa ba yau da ita ɗaya ne ai da sauki mace da ciki fa.”
Kamar zata rufe Ummi da duka haka take ji, ta shiga kiran Abideen yana ɗauka ta gaya mishi sannan ta kashe.
Shima asibitin yaje akace bata zo ba, tashin hankali wanda ba asa masa rana. Ummi takira Abdul ta gaya mishi halin da ake ciki, shi kuma ya faɗawa su Nana da Abba.
Lokacin da Abba yaji labari, tsabar tsoro ɗaukar takai mishi yayi ya ɗaura akanshi, hularsa a hammatarshi. Yakira Abdul yace.
“Gimbiya Asma’u tasani ne?”
Abdul yace.
“A’a bata sani ba.”
“Shi kenan takare min, dan mutuwa zanyi tace bata kyale kowa.”
Hankalin kowa a tashe yake, Mamie kam gani take kamar wasa Nannah take, kuma tana da masaniyar sace Safinah dan yayita bin Abdul ya gaya mishi inda take amma fir yaki, da yaga tana bautawa kuɗi sama da kome shine yayi amfani sa kuɗin ya tambayeta tace bari ta tambayi khalil. Zuciyarshi ɗaƴa Khalil tana tambayarshi ya gaya mata, tana Suleja. Jim kadan takira Anim ya gaya mishi.
Shi kuma yayo hayar kwararru a kidnapping suƙa kwamushe. Baiwar Sultan mamar magajin gobe (😥😹😂)
***
*OMAN*
Kallon ruwan dake gudu a lambusu take jikinta na bata akwai wani abu, dake dab da faru. Kawai ta ɗauki wayarta ta kira Abduƙ bugu biyu ya ɗauka,kamar ya kifa yace.
“Nannah! Akwai matsala.”
Tashi tayi kamar zata zuba da gudu tace.
“Ba dai wani abu yasami Binti ba.”
“Nannah an saceta.”
Mikewa tayi wayar ta subuce a hannunta, zama tayi jikinta kamar wacce bata da karfi.
Zubur ta mike ta nufi cikin gida……..
A ranar ta baro kasat zuwa nigeria
***
Duk inda ake tsamani zanje an duba bana gun jikinsu yayi sanyi, da farko sun zata kamar yadda nayi wanca tafiya, sai da aka je har airport aka duba, gabaki ɗaya, hankali kowa sai da ya tashi kwana biyu tsakani sai ga Nannah. Abin ba a cewa kome dan kuwa Nannah tana isowa batabi takan kowa ba, aka shiga bincike da lokacin……..
Kuyi hakuri, Waleed ba lafiya jiya kwana mukayi bamu runtsa ba yanzun ma ina rubutun kamar wacce aka sani dole in Barar Addu’arku……..
#MJ
#Vote
#HZƘ…..
Oum Muwadda….
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITERS ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Allah yasaka da alkhairi nagode sa addu’arku jiki yayi sauki sosai
Page.٢٤
Zare jikina nayi cikin na Anim, a hankali naja bargon da ya lulluɓemu na sauka rigata da na hango a kasa, nayi maza na suturta jikina. Sannan na shiga ban ɗaki, fitsari nayi. Jin cikina ya takure guri guda yasani shiga cikin kwanon wankan na cika da ruwan ɗumi na fara wanka. Ina idarwa na lumshe idanuna, tausayin makomar rayuwata nake.
Buɗe idanuna nayi cikin sauri bansan shigowarsa ba, sai hannunshi nayi a kirjin, buge hannun nayi.
“Wai meye ne haka? Ni bana son iskan….”
Buge min bakina yayi bansan lokacin da nace.
“Allah ya isa min”
Sake buge bakin yayi. Sannan ya cigaba da murza dukiyar fulani na,
Wani munafukin nishi na sauke, tare da tura kirjina gaba. Ina lumshe idanuna, loƙaci guda kwalla na zuba daga idanuna.
Shiga cikin ruwan yayi, tare da kwaɓe kaƴansa. Hannunshi naji yana shirin wuccewa kasata, nayi maza narike, idanuna akanshi muryana na rawa nace.
“Don Allah karka min haka! Karka manta kaima Ubane zaka ji zafi idan akawa Yaranka ha…”
“Ki bar gaya min Maganar banza domin ai baki min adalci ba da kika watsar da aurena, sannan kika dawo min wani abu daban, ina raye kika watsar min da virgin ɗinki abinda na tanadawa kaina, kika bawa wancan ƙaton bayan kinsan akwai mamallakinsa, sannan banyi magana ba nazo inayin abinda yadace zaki min Allah ya isa.”
Bakinshi ya kai wuyata yana lasa tare da kai hannunshi kan cinyata yana shafawa a hankali, bani da abinda zanyi kuma bana jin zan iya yin kome, sai kuka zan iya cewa na tsani kaina da rayuwata badan kashe kai haramun bane da na rataƴe kaina na huta da masifar rayuwa.
Ganin yadda nake kuka wiwi yasa shi ɗaga hannunshi a jikina cikin takaici yace.
“Amma shi balaraben da ya same a ɓagas ince bashi kanki kikayi ba tare da gardama ba sai ni da muka ajiye maganar aure a tsakaninmu. Wai ni kam meye laifina son da nake miki shine laifi ko kuma soyayyata a gareki.”
Mikewa nayi tare da ɗauraye jikina na fara kokarin fita yayi maza zai fincikoni na dafe cikin tare da kura mishi ido. Murmushi na sakar mishi tare da cewa.
“Ina ga baka san abinda ake kira da sarauta da mulki ba, sabida baka taso cikin gidan da suke da nasaba da mulki ba, kana k’etare iyakarka. Idan har jarumar Uwa zata iya sadaukar da rayuwarta dan soyayyar d’anta me kake tunani zatayi akan soyayyar jikanta, ba barazana nake maka ba kayi a hankali da shiga hurumin daular da babu irinsu a cikin yankin Jaziratul Arab.”
“Tsoratani kike!?”
Ban kalle shi ba, nace.
“Shawari nake ba.”
Fita yayi daga cikin ruwan cin matsanancin ɓacin rai yace.
“Ke kin isa?”
Wani banzan kallo na mishi sannan na fito, ba kaya yafito tare da niman nayi magana ya ɗirka min tijara, ni kuwa bani da lokacin haka. Falo na fito tare da kwanciya a dogon kujera, tun da nasan inda nake ban kuma fita ba, na mikawa Allah alamarina sannan ta ko ina sallah nake, dan bansan inda alkibilar take ba. Bana jin daɗin kaddarata amma yana iya tunda a juye tazo min, nayi imani da Allah rayuwata bata da amfani, dan daga wancar matsalar ta toshe still wani zai buɗe, a iyakar rayuwata ban taɓa jin bakin cikin d’a namiji ba sai yanzun.
Tunda naga na kwanta shima sai yazo ya kwanta a kujera me cin mutum biyu, ya zuba min ido ganin yadda nake barci. Haka ya matuƙar burge shi, dan haka ya ɗauko tap ɗinshi ya fara min hotuna.
…. A yanzun na daina mishi magana, kallonshi ma banaƴi abinci kuwa sai naga zai taɓa min lafiyar cikina, zanci amma ina cikin damuwa sosai, a cikin kwanaki uku zuwa huɗu har kafafuna sun kumbura. Gashi ko nan da ban ɗaki na shiga haki nake, duk sai naji na masifar gajiya. Sai mugun ciwon kan da ya sani a gaba musaman idan na kwana tunanin Ummina da yan uwana, toh nan ne fa, zan tashi fuskana a kumbure.
***
*Suleja*
Duk inda ake tsammanin ina nan babu ni babu labarina. Mamie tana sane da haka amma tayi banza da kowa ta cigaba da tsabgar gabanta.
Tunda Abba yaga Nannah batabi kansu ba shima ya shiga hidimar gabanshi, dukda tazo da kwararru a sarafa na’ura amma abin takaici, babu abinda suka samu sai tarin bakin ciki, domin mutanen da suka sace ni, gwanayen ne a harkan kwamusa.
……. Zaune take riƙe da casbi, tayi nisa a tunani. Nannah ta dafata cikin damuwa tace.
“Don Allah ki rage damuwarki akanta Insha Allah zata dawo cikin Amincin Allah.”
Murnmusawa tayi irin me ciwon nan sannan tace.
“Nannah! Ba tunanin Safeenah nake ba, sabida nasan ita ɗin kamila ce. Dukda bata faɗa min yadda tasami cikin ba nasan haka kawai Safeenah bazata mika mutuncinta wa kowa ba, sai mijin aurenta, Nannah tausayin cikin jikinta nake, dan nasan Safeenah damuwar da take ciki bazai bata damar nutsuwa taci wani abu ba. Shine tunanina,”
Dafe goshi Nannah tayi, tace.
“Har yanzun bincike ake, Insha Allah zata dawo lafiya.”
“Hmm” Ummi ta iya cewa, dake babu wanda ya taɓa tunanin Mamie tana da masaniya inda nake, karewa ma kamar bata san ɓatana ba gudun kar a zargeta sai da abin ya faru tafi kowa damuwa, gefe guda tana zuga Abba wai karuwanci nake, gwara yasan nayi kafin nahaifi shegen, idan ba haka ba kuwa sai an cika mishi gida da shegun jikoki, jin haka ya kira Ummi yayi mata cin mutunci na fitan hankali tare da cewa idan na dawo daga yawon duniya tasani na fidda miji ko kuma ya badani sadaka.
***
*Saudia*
Yana kwance a ɗakinsu idanunshi a lumshe, yana jinjina karfin cin amanar da Ghaniyu yaƴi masa, Ghaniyu yaƴi masa domin shi ya shirya masa kayanshi, hatta wanda zai saka shi yashirya masa, shi yasa lokacin da suka zo rabuwa yake share kwalla, tunawa da yayi matuƙar ya amsa bashi da masaniya akan kayan idan aka tambayeshi waye yake zargi zai ambaci Ghaniyu yasa yayi shiru, kuma a bisa dokar matuƙar ka bawa kotu wahala sai an ɗaureka bayan an wnke ka, sai an baka wani watanin a cikin gidan yarin kabawa shara’a wuya. Lumshe idanunshi yayi cikin mugun kewar rashin kunyarta, juya bayanshi yayi, yana tuno abubuwan da ya shiga tsakaninsu, musaman lokacin da yayi mata fyaɗe. Da zaran ya tun kareta zata sume mishi. Ba karamin tausayi ta bashi ba, dan yayi imani idan ba ita ba baya tunanin akwai macen da zata ɗauke shi, sai ita kuma baya jin sha’awar wata mace, tun bayan faruwar kome. Shi yasan sha’awarta yake a yanzun dan haka koda yayi nisan kwana, bazai tirsasa mata ta zauna dashi ba, amma zai nemi alfarma kodan albarkacin ɗansu ko yarsu ta zauna dashi idan taki kuwa zai kwace abinsa, yazo ya reni shi da kanshi yadda.
“Ashraf!!?”
D’ago kanshi yayi a hankali sannan ya mik’e.
“Lauyanka na jiranka!”
Mikewa yayi daga gadon, sannan ya fito zuwa inda Lawyer yake, zama yayi yana kallon lawyer, har lawyer ya. Buɗi baki zai magana. Ashraf yace mishi.
“Ghaniyu! Kodan na rayu da abinda ke cikinta.”
Sunkuyar da kai Lawyer yayi cikin mutuwar jiki, yace.
“Yallaɓai! Ina me baka hakuri da abinda zance, a halin yanzun an nime Safeenah an rasa, dan an saceta.”
Lumshe idanunshi yaƴi sannan ya gyara zamanshi, kauda kai yaƴi sannan yace.
“Idan Ghaniyu yaki baka haɗin kai ka sace kanwarsa sannan ka shiga ɗakina ka buɗe Computer makulinsa shine Baiwata (My Slave.) dashi number zai haɗa maka da hotunanrta sai ka kajerasu yadda zai bada harufar baiwata.”
Yana gama faɗar haka ya mike yabar gun. Yaki bawa lawyer daman ya tambaye shi, sabida kar ya hango tashin hankalin da yake cikin kwayar idanunsa ne.
***
*Atlanta Ocean*
Sati biyu da satoni, ina kwance nayi wani irin kumburi na fitan hankali idanuna sun shige cikin fuska, hakan ya farune sakamakon tunanin da nake yawanta yi, tashi nayi na jingina da gadon. A hankali na sauke kwallar dake cikin idanuna. Na sauko a gadon fitsarin da ya cika min mara naje nayi sannan na dawo. Tare da zama a kasa. Kurawa guri ɗaya ido nayi hawaye nabin fuskana, da mugun gudu.
Murɗa kofar akayi, na juya ina kallonshi sannan na kauda kaina.
“Tashi muje ga likita can na jiranki.”
A sannu na mike dan nima ina son ganin likita yau kwana uku yaron cikina baya motsawa yadda ya dace.
Ina fita likitan ya fara min tambayoyi, ina bashi amsa. Sannan ya gwada jinina nan yaga hawansa 199 saukar shi 180, kallon Anim yayi cikin damuwa yace.
“Idan ba akaita asibiti ba za a iya rasa Uwar da abin cikinta, dan jininta ya haura sosai. Kuma kaji cikinta bai kai Bakwai ba balle muce zata iya haihuwar prematura.”
“Kawai ka bata magani amma batun kaita asibiti bai taso ba.”
“Ok!”
Magani ya rubuta sannan yace.
“Ayi kokari a nimo sannan aƙwai yunwa sosai a tare da abincin.”
Fita likintan yaƴi Anim ya bishi da ido, sannan ya sauke a kaina. Zai magana, nace.
“Ina haɗaka da Allah badan ni ba, dan sonka da Annabi kabarni na tafi Mahaifiyata da abin cikina kabarni na koma cikin dangina, idan kai min haka tabbas zan iya amincewa kana kaunata amma idan kaki amincewa. Zan maka kallon baka kaunata, Amma zan gaya maka wani abu kasani hakan da kaƴi baxao taɓa baka ni ba. ”
“Idan naki maidaki fa?” ya tambaye ni,
Murmushi nayi sannan nace.
“Tabbas zaka wayi gari ka tsinci gawata.”
Ina gama gaya mishi na mike a hankali nabar falon ina kuka, dan iya cutuwa na cutu. Ni yanzun wallahi tsoron maza nake, kai hatta Ubana tsoronshi nake dan shima da girmansu tsofai tsofai yasake mana Uwarmu, tunda na shiga ɗakin nake kuka me cin rai, ga jagwalgwalani da yake son ranshi, ga muguntan da yake min. Zan iya cewa cikina rashin kuzarinsa ya faru ne tasanadin matseni da yayi a ban ɗaki, indai haka ake soyayya har abada zance nayi retire. Dan niso bai kareni da kome ba sai tulin takaici. Tunda gashi ina cin azaba a gun Anim, wanda bansan ranar karewarta ba, *Allah sarki Ummina*
Abinda nace kenan a raina, ina matuƙar kewarta da kuma kowa nawa, *Ayya ko ya Nannah zata ji*
“Da kike cewa mahaifiyarki, lokacin da kika tafi yawon tazubar kin tuna da ita? Ko yanzun da kike son ki juye mata abin kunya yasa kike tunata, Safina nifa abin arziki na miki bana tsiya ba, amma kike niman rabuwa dani, toh kome zakiyi kiyi amma bazaki bar nan ba sai da igiyar aurena, dan ko yayya nayi sake dake nayi mugun asara, tunda naji labarin Uwar kwartonki tana can ana bincike bata san mu yan Naija zuwa ɗaya mukewa abu mun mun gama ba, sannan ina son ki sani wayarki ma na wurgar da ita……….
*_Duk wani fararre abu zaka samu yana da dalili da kuma hujja, nasan ban kyauta muku ba amma iya adadin kuskurena zaku duba da kuma kyautarawata zaku ga akwai rata me tarin yawa,karku sake jikinku ga wannan alamarin dan bana son cin amanar zuci ya faru tsakaninmu ina muku fatan alkhairi………_*
Oum Muwaddah..
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Labarin daban yake da sauran._*
_FATAN ALKHAIRI ZAINAB MUSTAPHA nagode da kauna🌹_
ZAUREN MAI_DAMBU KU BAR KULA UMMU MUH’D…. Dan na lura da ita duk sai ta mannawa kowa hawan pure water😂 Ina gaida uwar dakin Anim bayan My Zahra yau ga wata me kare yan ta’ddan novel😹
Page.٢٥
Kwanciya nayi tare da juya masa baya,zuciyata na zafi ji nake numfashi na kamar ina kokuwar dawo dashi, cikin ikon Allah da ambatonsa, duk yadda naso kuka na kasa, haka na cigaba da kwanciyar ina jin ɗan motsi kaɗa, shafa cikin nayi zuciyata cike da tausayin Yaron cikina haka kaddara ta kawo mu wata nahiya na daban..
***
*Jordan*
“Nazone abisa ka faɗun ahalin Banu Hashim, banzo dan muradina ba Ukshe nasanka sarai na kuma san waye kai, Ukshe kana da hannu a cikin alamarin Ashraf, mulki kuke so ya barmuku dukiyar da kuke bukata ya barmu, tsinke na masarautar bai ɗauka ba. Amma kuka zuba mishi makamai a jakarsa dan b’ata suna ga alummar musulman duniya, abinda kuka yi sam baku kyauta ba, daga ni har kai bazamu taɓa mulkin Jordan ba koda kuwa, babu wata a kasa amma ka kasa gane haka.”
“Karka dame ni, idan baka da abinyi ni ina dashi.” ya gayawa Abu Zarri.
“Ni keda abinyi kuwa dan yanzun haka nasa an tura videon yadda kuka zubawa Sultan Ashraf Mugayen makamai,karka matso kusadani, domin yanzun nasan inda ke min ciwo, sannan da kake gani na a nan ansan da zuwa na, kuma idan ban fita ba kaima rayuwar ɗanka tana cikin kazamar hatsari.”
Cire hannunshi yayi daga cikin alkyaba, ya mika mishi Tap, yace.
“Taɓa cigaban mana! A duniya babu wanda yakai balarabe fasaha, dan haka karka manta jini ɗaya ke gudana a jikinmu, indai har zaka iya kasa fuska ni ɗin zaman me nake da bazan iya ba, shawara guda ɗaya na baka ka rabu da Ashraf kamar yadda ya zaɓi mace akan mulki, idan kuma kaki zaka iya fuskartan mutuwa dole.”
Yana gama sambaɗa mishi magana ya amshe tap ɗin, ya kalle kan screen, Marhum ne an ɗaura mishi bindiga a goshi.
“Kana nufin d’ana da ka kama zan ji tausayinsane? A cikin zuciya ake gini buri da muradi! Dan tunda na fahimci ina da ikon juya sarki da mukararrabansa,naji a raina koda bala’i sai na cika masarafar ikona, wallahi ku mika shi ga Saudia ni kuwa kuncika min burina na zama Sarki, domin yaso min iyaka kuma nasanshi akan naci, godiya nake.”
Cak Abu Zarri ya tsaya mamaki cike da zuciyarshi, a sannu ya juya ga Ukshe.
“Kai baka da kawazuci ne?”
“Kawazucina akan mulkin jordan ne kuma nasamu hakan dan haka zaka iya fita.”
Murmushi Abu Zarri yayi sannan yace.
“Idan bana raye kenan?”
“Amma nagode maka da tuna min da kanka, idan baka raye fa? Zan zama sarki na har abada.”
Abu zarri bai kula shi ba dan ya lura kaunar mulki da haukar son rike madafun iko ya zararra da Ukshe, sai dai su cigaba da masa fatan shiriya.
Yana fita ya bada izinin a tafi da Marhum kawai, dan ba zasu cigaba da kalle rashin adalci ba, sannan ya mikawa lawyer da yazo hannun suka gaisa, ya juya ga Ghaniyu yace.
“Nasan an zalimceka! Tunda a sanadin haka ka rasa kanenka da mahaifiyarka, ina ga ka ɗauki matarka kabi Ashraf duk inda zai je ka zame masa kariya amma karka manta a yanzun ba zai yarda da kai ba, sai kasan yadda zaka faɗa mishi gaskiya dan ya amince da kai. Akwai jaka karama me ɗauke da kuɗin amurka ka bawa Ashraf. Sannan duk inda kuka je ka tabbatar da ka gaya mana kodan halin rayuwa, sannan ka roka minshi yafe.”
Daga haka yayi wuccewarsa, ba tare da yabi takansu ba,
(Ku cigaba da bin sarkakken labarin a hankali zan warware muku,)
Motar da aka ɗauki Marhum tare da jami’an tsaron kasar Jordan aka fita dasu daga masarautar, suka nufi airport
Basu same matsala ba, suka bar kasar dashi,
***
*Nigeria*
Suleja…..
Sheik Hayatudden Kamfut ne zaune shida y’an uwansa, Kan Ummi na bisa cinyar wata dattijowa, ta lumshe idanunta. Sai a jiyar zuciya take saukewa dan yau tun safe ta bar Suleja zuwa abuja, tun asuba tacewa Ummi ita tana zargin Mamie da Badar, akan ɓatar Binti. Kuma ta tafi kome zai faru(😎😏 Mamie mek sho yu run)
Sai da ya gama Addu’a sannan ya kalle Ummi cikin tausayawa yace.
“Mariamah kukan zuci kike? Karki zubda kwallarki dayawa a duk inda Safinah take Insha Allah yau zuwa gobe zata dawo gareku, da Allah muka dogara ba da wani ba, Allah da kanshi yace alkur’ani waraka ce.”
Tunda Safinah ta ɓata har yau Ummi bata zubda kwallarta ba, sai dai kawai zata zauna tayi ta sauke a jiyar zuciya, kimanin sati uku zuwa huɗu kenan.
Alkur’ani aka raba irin bugun sokoton nan. Dan a cikin jakarsa yake, ya bawa kowa falle uku-uku, sannan ya fara da fatiha…..
***
Tunda Mamie ta isa garin Abuja tasa Abba ya kira kowa, cikin ruwan sanyi ta gabatar da abinda zatayi sannan ta fidda takarda tace.
“Aranar uku ga watan biyar, Nuratu kinyi waya da wannan number sau uku, ana saura sati Safina zata ɓata. Bayan kwana biyu acc ɗinki na bankin Access sun amshi naira dubu ɗari shida, daga wata acc ɗin, bayan sace Safina. Ranar goma ga watan shida kunyi waya da wannan number bar aka kuma turo miki da naira dubu ɗari bakwai, sannan an kiraki ne daga can tsakiyar ruwa atlanta ocean, ranar ashirin da ɗaya ga watan shida an kuma kiranki, tabbas kinyi kuskure. Waye shi?”
Zuba ke karyowa Mamie sosai duk yadda taso rike fitsarinta kasawa taƴi, dan ta jika inda take zaune jagwab
***
Yana shigowa ya ganni na kifa kaina da jikin gadon yana ɗago fuskana yaga na bishi sharaf na zube a jikinsa, ga bakina ya koma gefe. Yawu na fita me yauki haɗe da jini.
“Safeenah” ya shiga girgizani. Ganin bana motsi yasashi ɗaukata dukda nauyin da na kara. Haka bai dame shi ba ya fita dani da sauri. Kamar zai tashi sama, filin da aka tanada dan saukar privet jet ya nufa dani tare da kiran masu tuka jirgin. Suka taimaka mishi aka sani a ciki sannan ya kallesu yace.
“Ku tabbatar da kun kaita Abuja akan lokaci, idan wani abu ya sameta kuyi kuka da kanku.”
“Yes sir!” suka ce mishi, tare da fara tada jirgin, sumbrta Goshena yayi, sannan yace.
“Kece sila! Ina sonki da zuciya ɗaya kika maida min so cuta. Allah ya baki lafiya zanzo na aureki.”
Rufe kofar yayi, tare da juya musu baya, har suka tadda jirgin har suka tashi sama.
D’aga kanshi yayi yana tare da bin jirgin da ido har suka ɓaccewa ganinsa. Tafiyar awa biyu ya fitar damu yankin tekun.
A cikin awa uku da rabi suka sadani ga wata karamar asibitia cikin abujar gudun kar a kamasu yasa suka rufe min fuskana, sai da suka gama kome sannan suka bar asibitin. Dr Muhsin shine yazo kaina domin dubani. Dake yaga sun rufe min fuska, kamar bazai buɗe ba, sai wani tunani yazo masa ya ɗaga mayafin.
“Safeena!!!”
Ya ambata da karfi, gumine ya shiga karyo masa, wayarsa ya lalluba ya shiga niman Abdul cikin tashin hankali ya same Abdul yace.
“Duk inda kake ka tawo asibitin Alheri.”
Bai barshi yayi magana ba ya datse kiran, Abdul kuwa yana can, Nannah tana yanta Abba da Mamie.
….. Bayan minti ashirin ya iso, tsananin faɗuwar gaban da yake ciki, ya hanashi fitowa. A sannu ya tattaro yar jarumtarsa ya fito daga motar tare da rufewa ya nufi cikin asibitin, kiran layin Dr Muhsin yayi yana ɗauka yafito daga ɗakin da aka sakani, a sannu ya isa ɗakin. Tare da kura min ido, zuwa yayi bakin gadon ya ɗaga lulluɓen fuskana. Ji yayi kamar zai faɗi Dr Muhsin ya tallafeshi, kamar yaro karami yace.
“Da gaske Safinatu ce!”
“Be a Man! My frnd karka sa nace ka rako maza mana, ka tsaya mu taimaketa, yanzun nake son ɗiban jininta aje a gwada ko akwai sugar sai musan abinyi dan kaga yadda ta kumbura za a iya rasa Uwar ko Babyn.”
Fita Dr yayi shi kuma yaja kujeran ya zauna, yana kallon kumburarren fuskana, har dr muhsin ya shifo tare da nurse da kuma, da bututun shakar iska, wato oxygen aka samin sannan ya bada dama aka ɗibe jinina, suka fita zuwa lab, can bayan wani lokaci suka dawo aka samin, mika mishi report ɗin yayi cikin lallashe yace.
“Bata da matsalar kome sai kumburin da tayi, zuwa an jima zamu kaita ɗakin gwajin zuciya. Sannan yana da kyau kakira mutane gida ka gaya musu.”
Wayarsa ya ɗauka ya kira Ummi da suke tsaka da addu’a. Ya sanar mata,
Sannan ya kuma kiran Nannah ya gaya mata, tuni ta kyalesu Mamie wacce aka musu ɗaurin wulaƙanci aka watsa a bayan kanta.
……..
Lokacin da Nannah ta gama zayyanowa Mamie abinda tasamu akanta, cikin rawan jiki ta amsa. Ba tare da jin kume ba Nannah tasa aka tafida ita har bayan gidan aƙa fara tsoma kanta cikin ruwan swimming pool. Da taga zata mutu shine ta buɗi baki zatayi magana Abdul ya kira Nannah.
Kota kanta bata bi ba, tafito inda tasa drvn gidan ya kawota asibitin.
Kafin awa ɗaya yan uwana da dangina sun cika asibitin, kowa yana min fatan samin lafiya, sun samu cikin ya fara kuzari nice ma dai ban farka ba. Sai da na share awa uku biyar cur sannan na farka, tunda na farka nake kare musu kallo dan gani nake kamar mafarki nake, ina son magana harshena yaƴi min nauyi, dan haka na sake lumshe idanuna barci yayi gaba dani.
Ban kuma farkawa ba, sai washi gari da misalin sha ɗaya. Buɗe idanuna nayi naga Ummi da Nannah, hannuna ɗaya na kai kan cikina naji yana kicking yadda ya dace. Murmushi na sake tare da cewa.
“Babynsu Nannah”
Kura min ido Ummi tayi taga nasake magana, tasowa tayi sannan tace.
“Kina son wani abu ne bama jin abinda kike cewa.”
“Ummi baku fahimtar me nake cewa kenan.”
Nan ma Nannah tazo tace basu fahimci nake cewa ba. Saka hannuna nayi na shafa fuskana naji bakina ya koma gefe. Kuka nake son yi amma na kasa, da karfi na rufe idanu na, na shiga sauke ajiyar zuciya. Ina jin Ummi tana kiran Abdul tare da gaya mishi halin da nake ciki.
Barcin dole ne yayi gaba dani, dan ban farka ba. Sai karfe biyu ina buɗe idanu na, sai akan Anim. Mugu ɗan masara ana goyaka, kana karya uwarka. Kukan da ban samu damar yi bane ya kwace min na shiga fisge-fisge saura kiris na faɗo daga gadon Abdul da Nannah suka tare ni, fita ABDUL yayi sai gashi tare da Dr Muhsin. Alluran barci suka min Idanuna na kan Anim.
Ajiyar zuciya Nannah ta sauke, tare da cewa.
“Abdul ko za a cire abin cikine wannan wahalar tayi yawa, kullum babu sassauci daga wannan sai wannan, gabaki ɗaƴa Safinah ta fita hayacinta.”
“Ai matsalar shine cikin bai cika bakwai ba, amma da zaran ya cika bakwai insha Allah zamu cire babyn, dan girman cikin ma yana rinjayarta.” Inji Abdul,
“Ni a ganina ku bar cikin ya shiga watansa in yaso sai a cire mata, dan nima na karaya da alamarin Safinah, na yau daban na gobe daban.”
“Kuma ana cire mata yaron zan bawa Alhaji Zubair yayan Nuratu it….
👏👏👏
_A cikin duniyar nan kowa ya tara abin fada, amma kalilan suke iya ajiye nasu, ba sauki rungumar Alamari me wahala ga karamar irina, Hidimar miji da Hidimar yara…. Ba abu me sauki bane ɗaukar nauyin da bai zame maka tilas ba, idan kiɗa ya sauya dole rawa ya sauya….._
Uom Muwaddah…
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITER’S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Wai me akayi tukun bamu gama book one ba har kun fara gajiya hmm da naso da Rayuwar Safeena zan kira book ɗin amma sabida shiga Ahalinta Masarautar jordan yasani ambatar labarin haka duk abinda ake a nan ba kome bane idan zaku iya hakuri ku bini toh bismillah dan labarin ba takaitacce bane kamar sauran shi yasa nace muku ya sha banban da sauran👏_*
YAUSHE NAYI ALLAH YA ISA A BOOK Ɗ’IN MJ😏…..
Page.٢٦
“Kuma wallahi bazan fasa kudirina ba” ya faɗa yana zare idanunshi, kura mishi ido nayi ina jin ba daɗi yau Abbana shi ya juya min baya mutumin da yake kokarin saya min farin ciki da hannunshi da dukiyarsa, yau shine yake juya min baya.
“Bar kallona da kifi-kifin idanunki kamar na yan matan ɓera, shaiɗaniya kin rabani da mata ta da d’ana har mutanen arzikin baki bar min su ba, Anya Safeenah ba canza min ke akayi ba a can inda kika je yawon banzanki.” Allah tijarar da Abba yayi min ba sauki dan nayi kuka sosai nayi danasanin tafiya jordan yafi sau dubu, wancan makaryacin kuwa na mishi Allaj ya isa yafi sau ɗari, ga Anim wanda banda kar ace min zararriya da ina tashi rufeshi da duka zanyi mugu azzalumi.
Ahankali barci me nauyi yayi gaba dani.
……. A iyakar rayuwata bansan meye kunci ba sai da nasaka kafata a kasar jordan, tun daga ranar da Ashraf yayi tarayya dani kome nawa ya wargaje, na rasa farin cikina na rasa duniyata kome na rayuwata. Ya lalace, ji nake kamar na gudu na bar kowa naje naƴo rayuwata ni ɗaya.
Dan rashin kunya Anim har gida yaje ya sami Abba, suka gaisa sannan yayi kasa da kanshi kafin yace.
“Abba dama akan Safeenah nazo kayi hakuri da abinda ya faru da ita, babu wanda ya isa ya tserewa kaddarar sa, indai haka ne kaddarar. Ni naji na gani ina sonta dan wannan rabon cikin ya kaita can kuma nasan wacece ita bazata taɓa watsi da tarbiyanku ba, tunda ba yau tasaba zama wani waje, da halintane tabbas da tun tuni ta tarama jikoki sama da haka don Allah ka dubeta da idon rahama ka sassauta mata, ni ina sonta kuma zan kula da abin cikinta idan ta haifa,”
Da wannan maganar Anim ya gama kashe Abba, ya kuma dinga amayarwa Abba yadda ya hau bishiyar kace, a kaina suna cikin haka Mamie tazo tana ganin Anim ta shiga ɓara ɓare tana jin abinda yakawo shi take ta shiga masa kamfe, da zai tafi ya ajiye mata kuɗi me mugun yawa, ai kuwa baki yaki rufuwa, bayan tafiyarshi ta dubi Abba tace.
“Gaskiya yaron nan d’an gidan albarka ne kaga zuwan yau kawai ya ajiye min dubu ɗari biyu, nan gaba bansan me zan samu ba, Allah yasa kar Maryam ta mata bakin ciki dan naga bata gaji arziki ba sai tantagaryan tsiya da talauci.”
“Hmm! Ai ina ɗaga musu kafane sabida Uwargijiyata in ba haka ba abinda zanwa maryam sai garin Abuja ya ɗauka toh babu yadda na iya ne, basunce cikin na Ashraf bane bari muga abinda zata haifa, tana haihu babu batun shayarwa zan ɗaura AURENTA da Anim.”
Haka sukaita tattaunawa har lokaci yaja sannan Abba ya bar gidan.
***
Wani shishigin da Anim yake a cikin Yan uwana ya wucce misali dan tsakaninshi da Allah yake nuna kulawarsa A kaina. Muna cikin wannan halin aka kira Nannah daga Oman babu dogon shiri ta haɗa kayanta ta koma can.
A yanzun hankalin Ummi ya kwanta da Anim sabida irin hidiman da yake min, ga baki ɗaya. Da zaran yazo Ummi zata fita tabarmu, tana fita zai zo ya sani a gaba da iskanci. Kamar zan mutu dan bakin ciki sai dai bani da yadda na iya tunda ba gane maganata ake ba, babu abinda ke kara min takaici kamar yadda ya takurawa nonuwana, da zaran Ummi ta bamu guri toh zaija kujera yayita murza min so, na gaji sosai yau ma kamar kullum yana zuwa Ummi tana bani abinci suka gaisa, rike mata riga nayi. Kwalla ya fara sauka min, wanan na sauka wani na koro wani.
Ganin zatq mike na maza na rike zaninta ina girgiza kaina, dawowa tayi ta zauna, na ɗaura kaina a jikinta ina sauke wani irin kuka mara sauti, ajiye filet ɗin tayi ta shiga shafa kaina har nayi shiru. Kallona yaƴi yana min kallon kasa kasa, ni kuwa na tura mishi bakin dake gefe guda. Lashe lips ɗinsa yaƴi sannan ya sunkuyar da kanshi. Sama sama yaƴi hiran sannan ya tafi gidanshi dama zuwan dare yake.
Yana fita na sauke ajiyar zuciya, kallona tayi cikin nutsuwa tace.
“Baki son zuwansa ne?”
Gyaɗa mata kai naƴo, idanuna akan abarban data yanka min da gwanda da kuma kankana,, tashi tayi ta ɗauko ta fara bani ina sha ina kallonta, a hankali na motsa bakina nace.
“Am sorry Ummina”
Kallona tayi sannan tace.
“Kince wani abune!”
Rike cokalin nayi na ɗiba itama na bata, girgiza kanta taƴi sannan ta shiga bani.
“Eyye ɗaurewa bariki gindi! Tayo shegen ma ana riritata, kai Ni naga duniya ni Nuratu Alhaji yaron nan Anim yaƴi kokari da Jahadi dan ni ina tsoron kar a lakatawa ɗan uwana damuwa, Uwa da y’a sun zauna suna soyawa. Kagani ba ita murna take dan yarta ta ɗauko magana.”
Take fuskar Abba ya koma tankar red emoji, sai hura hanci yake, yanawa Ummi wani kallon hadirin kaji. Irin lallai ma kun renani.
Daga ni har Ummi shiru mukaƴi zai fara tijarar sa, Dudu ya shigo Ajiyar zuciya na sauke, kallonshi Abdul yayi sannan yace.
“Meke faru?”
“Kaniyarka ce ke faru! Kaji min mara mutunci yaushe rabonka da kazo gaishe ni wato an muku ingiza me kantu ruwa, an rabani da y’ay’ana da a nuna min sanabe toh kayi maza ka dawo da yar mutanen da ka tura gidansu, dan iskanci akan wancar abar wallahi Abdullahi ka fita idona na rufe”
Shiru mukayi har ya gama sauke buhun masifarsa sannan ya ficce shi da jelarsa.
D’ago kai Ummi tayi tana kallon Abdul, wanda ya sunkuyar da kanshi. Jikinshi yayi masifar sanyi yace.
“Ummi Am sorry! Naso na gaya miki amma kuma..”
“Karka damu, ai tayi laife ne kuma ko zaman gidan da tayi yaci ace tasan laifinta kayi kokarin dawo da ita in ba haka ba yadda naga Abbanku ya koma zai iyawa kowa rashin kirki bavu ruwansa. Kuma ba damuwarsa bane yayi maka a gaban kowa don Allah ku kiyayye abinda zai ja muki rigima da shi.”
“Thank you so much.”
Ya faɗi haka tare da ɗaura akanshi a kafaɗar Ummi yana min gwalo.
Murmushi nayi nima na masa gwalo.
***
Yau ma kamar ko yaushe idan yaje yawonshi zai dawo yaƴi wanka a cikin gidanshi, tana zaune a bakin gado ya fito ɗaure da towel a kugunsa hannunshi ɗaya rike da karamin towel, yana goge kanshi.
“Zargina ya zama gaskiya! Kana zuwa waje kayi lalata da yan mata sannan ka dawo min gida kana wanka sabida rashin adalci Anim meye na rageka dashi? Da har ka gwammaci kaje waje kayi lalatarka sannan ka ɗibo min datti zuwa gidana.”
Dan wulakanci irin na mijin bahaushiya. Ya Kare mata kallo yana kuma dubata sama da kasa sannan yace.
“Dukda tafiki a shekaru, amma nonuwarta kullum a tsaye suke kamar zasu tsone maka idanu, idan ka taɓasu tankar audiga. Laushin fatarta kuwa ya wucce ayi misalinsa, bakinta kuwa idan kana sumbatarta kamar alewa aƙa saka maka a ciki, ban taɓa ganin macen da ciki yayi mata kyau irinta ba, ga sura kamar ita ta zaɓa tayiwa kanta, dukda kinfita kyau ita kuma tafiki cikar halitta.”
Kura mishi ido tayi bata san lokacin da hawaye ya fara zubo mata, cikin kuka tace.
“Wacece haka ?ka gaya min ita wani irin tsafi tayi maka da kake da na roketa ta faɗa min inda taje nima naje a karya ko zaka kalle ni a matsayin mace.”
Tsaki yayi tare da zama a kan stool ya ɗauki cream ɗinsa ya fara shafawa, kaman bazai magana ba yace.
“Safeenah”
“Safeenah!!!?” banza yayi da ita kankamce idanuta tayi cikin zallar kishi da bala’i tace.
“Wallahi ba zaka taɓa auranta ba sai dai ayi babu kai.”
Tsaki yaƴi cikin ko in kula yace.
“Fita min a ɗakina barci zanyi.”
Fuuu ta fita abin na masifar kona ranta, wato ta hanashi ya aurota shine yanzu suke baɗalar a waje. *Kai Allah ya isa min* tace da muguɓ karfi kallon hoton aurensu tayi ta ɗauki wani turarenta ta jefi hoton saida glass ɗin ya tsage tare da zubowa.
Kuka ne ya kwace mata tanayi tana fasa kome na ɗakin ga alwashin da ta ɗaukarwa kanta matukar tana raye.
***
Daga Asibiti Gidansu Sophia Abdul ya nufa, tunda yayi sallama. Aka ce ya shiga falo ya zauna yana jiransa aka kawo mishi ruwa bai taba ba ya cigaba da jiranta can sai gata tafito rike da Affan kauda kanshi yayi daga kallonta ya mikawa Affan ɗin hannu da gudu yaron ya shige jikin babanshi. Cikin sanyi jiki ta zauna a kujeran dake kallon nashi, dukda yana cikin matsanancin kewarta haka bai sashi jin tausayinta ba, zamewa tayi daga kujeran ta fashe da kuka sosai, yana jinta kamar bazai kula ba , ya mike yacewa Affan..
“Jeka gurin kaka ta baka bobo.”
Da gudu yaron ya fita, maida dubansa yayi gareta sannan yace.
“Kin sani a gaba da kuka zan tafi fa.”
D’ago manyan idanunshi yaƴi ganin yadda ta rame yasashi tambayar lafiyanta kuwa.
Nan take bashi labarin bata da lafiya, amma da sauki.
“Hmm! Me yasa kika saka a ka kirani”
“Ina so zan koma ɗankina ne don Allah ”
Kura mata ido yaƴo yana kallon yadda take motsa bakinta yayi, ɗauke kanshi yai tare da jan wani mugun iska tare da fesar da iskar bakinshi, yana matukar kewar matarsa da ɗanshi amma baya jin zai maidata cikin sauki, kauda kanshi yayi sannan yace.
“Kin manta keda bakinki kika ce na zauna da yar uwana ta maye gurbinki, ina ga kin mantane ƙuma gashi na tuna miki, duk ranar da kika san yadda zaki gayawa mutum magana zan dawo dake, ko kuma kije ki roki wacce kika wulakanta, idan ta yafe miki maybe zanyi tunani akanki da kuma makomar rayuwarmu.”
Yana dire mata aya yq mike zai fita da gudu taje ta rungume shi ta baya, tana kuka tare da cewa….🏃🏃🏃🏃😂
*Kuna nan kun zuba ido muna jira…. Anya nan gaba bazaku juya min baya ba😢😭*
Oum Muwaddah…..
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITERS ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
_Na sadaukarda wannan shafin ga Iyaye mata masu fafutukar kare Yaransu….A cikinsu Har da Mahaifiyata Allah ya jikanki da Rahama👏_
Page.٢٨- 28
” Ban tab’a karo da mutum mara mutunci irinka ba, banza mugu fasiki, mujirimi kawai. Kafit.”
Maganar da ban karasa ba kenan na haɗiyen dole, sakamakon jin bakin d’an iska da nayi cikin nawa, duka nayita masa. Tare da ture shi da karfin tsiya, na kuma tofa mishi yawunsa a fuska, kazamin banza shafo yawun yaƴi, tare da lashewa har yana lumshe idanunshi, girgiza kai yayi da takaici ya kamani. Bansan lokacin da na ɗauki kwallo goriba na kwalle goshinsa, kam uban bala’a alkur’an sai akan idanun Abba. Tsabar na tsorata garin na yunkura zan mike sai da naji bayana ya amsa, tare da zuban abu a jikina.
“Safinah! Rashin mutuncinku har ya kai ya taɓa mutumin da yake jeka ka dawo akanki, yau zaki gaya musu.”
Dakyar na mike dan naga yana gun Anim wanda goshinsa ya fashe, zasu fita ni kuma na shige gurin Ummi, ga baki ɗaya na birkice domin dakyar nake ɗaga kafana, ga cikin da yawo kasa baki daya.
“Ummi!”
Na kwala mata kira da karfi sannan na durkushe a gun, sabida jikina wani irin rawa yake, har cikin kashin jikina rawa suke. Ga zufan da yake karyo min haɗe da wani mugun sanyi me shiga jikin mutum.
“Safinah! Haihuwar ce.”
Gyaɗa mata kai nayi cike da azabar da yake addabar gangan jikina tare da yin dagadaga da ruhina, duk sai ta ruɗe kamar bata taɓa haihuwa ba, komawa ban ɗaki tayi ta ɗauko kujera ɗan tsuguno, ta nuna min yadda zan ɗaura hannuna a kai tafita da sauri, sai side ɗin Umma.
“Amnah zoki taimake ni Safinah ina ga haihuwa c..”
Ai Ummi bata gama maganarta ba Umma ta fita da sauri, suka nufo side ɗin Ummi, umma tace.
“Har cikin yakai haihu ne?”
“Eh toh ina dai tunanin bakwai kenan.”
Suna shigowa kukan ɗan karamin jariri na musu maraba da zuwa, da sauri Ummi ta ɗauko hijab ɗinta ta mikawa Umma ta saka jariri a kai, ta shiga niman inda kwalin rezanta yake. Tana samu ina sake wani nishi tare da cewa.
“Ummina ki yafe min”
“Iƙon Allah har biyu? Sannu da aiki Safina.”
Inji Umma yanke cibiyar ɗayan akayi dan basu samu hankalinsu da su fahimci gender yaran, yanke ɗaya cibin sukayi, kara na saka sannan na zuɓe a gun ina tauna harshena, ranar Ummi tashiga mugun tashin hankali, Umma ce tayi maza ɗauki wani. Karamin roba ta cusa min a bakina, tare da nima min doguwar riga suka saka min, hawaye ke zuba a idanun Ummi, kota kan yaran basu bi ba.
“Maryam! Babu lokaci kira mana Dudu.”
Jikinta na rawa ta fara niman wayarta, wadda yake kan dress mirror, amma sam hankalinta bai je gun ba. Asalima birkicewa tayi sabida ganin jinin dake zuba. Umma ce ta gani bata cewa Ummi kome ba, ta ja hannunta ta zaunarda ita a kusada jariran, sannan ta kira Abdul.
“Maza kazo Safinah ta haihu, kuma tayi sarkewar hakori muna cikin tashin hankali.”
“Gani nan a cikin gidan.”
Kashe wayar tayi, sannan ta kalle Ummi tace.
“Karki manta Allah yana tare dake karki bari Safina taga karayarki akan idanunki, yin haka shi zai ta shiga sabo..”
“Ummi zaman me kuke yi baku san rayuwarta na cikin hatsari ba, Ummi ki jida yaran ki yanke musu cibiyar tunda sun tawo tare, sannan ki naɗesu kufito Zakari ya kawo ku dan ɗakin yan bakwaini za a kai su.”
. Sa hannunshi yayi ya cinciɓeni tare da fitowa waje dani, Umma na bin bayanshi, ganin ya ɗaukoni yasa Zakari ya buɗe masa motar yasakani, shiga Bayan Umma tayi, shi kuma ya zagaya zai shiga mazaunin drve. Abba ya shake mishi wuya, tare da kifa mishi mari.
“Abba don Allah ka bari na kaita asibiti, rayuwarta na cikin hatsari.”
“Idan ta mutu uwarka ce? Ni zaku renawa hankali ku haifa min shege a gidana, dan.”
“Abba!!!”
Ya kirashi da karfe, cikin ɓacin rai ya kwace rigar yace..
“Wallahi idan ban takeka da mota ba Allah ya tsine min Albarka.”
Ganin da gaske yake Ummi ta daka mishi tsawa.
“Kul!! Bawan Allah, muje ka rabu dashi Allah ya kyauta.”
Gabar motar ta shiga, dole Abba ya matsa, Abdul ya fita sai huci yake, tare da dukar kan motar, Har suka isa asibitin. Dauka na yayi, tare da shiga ciki dani, su Ummi suka rufa mishi baya.
Yana shiga nurse da likitoti suka, tare shi aka shige dani ciki. Sannan ya faɗawa wata nurse ta amshi yaran, ta wucce dasu ɗakin kula dasu, ni kuwa suka rufa min dan cito rayuwata.
Idan ka rayu babu jarabta a rayuwa ka binciki imaninka, Aslhamdulillah nagodewa Allah da yake jarabta rayuwata, kuma bana bakin ciki da haka sai godiyar Ubangiji. Da nake ba dare ba rana.
……..
“Hmm kagani ko! Ai na gaya maka Maryam ta rabaka da yaranka musaman wancar karuwar, tunda ai ba yau ta fara cikin ba. Sau nawa tana zubda cikin a ɓoye daga ita sai wancar munafukar balarabiy…”
Wani mugun kallo ya bita dashi wanda yasata haɗiye maganarta, cikin fushi da ɓacin rai yace.
“Balarabiyar mutum ce! Daga cikin mutanen kirki ita tankar waliyiyya ce, domin zuciyarta takai kololuwar kyautatawa, duk abinda nake bata min magana sabida dalilai guda biyu ne. Dalili na farko tabani dukiyarta ina kuma cin gajiyarta, ko sau ɗaya bata taɓa saka idanunta akai ba, Dalili na biyu sabida, sadaukar da rayuwata da nayi sabida ita, wannan dalilin Yasa Gimbiya Asma’u bata da kataɓus akaina, dan tana gudun kar tamin magana nace dan taga ta tallafi rayuwata shi yasa tayi min magana, ban taɓa jin kunya a rayuwata irin na yau ba, da Abdullahi yace zai take ni da mota, sabida yar uwansa, idan na cigaba da tsawallawa. Wata rana zuciya bata da kashi zasu tanka min, dan ma Allah ya basu jarumar Uwa, wacce duk abinda nayi mata bata duba a bisa laifi sai dai ajizancin ɗan Adam.”
“Kenan..”
“Don Allah fita ki bani guri bana son damuwa gabaki ɗaya kin chaxa min kai da wanne zanji da naki ko da na yarana, zaki iƴa fita.”
Ya nuna mata hanya, fuuuuu tayi waje.
***
Sun kai awa biyu kafin likitotin suka fito, babban cikinsu wanda zai kai kimanin shekaru arba’in ya fara fitowa cikin ɓacin rai yace.
“Dr Kyari! Sam baku kyauta ba, wani irin abune haka, ban da Allah ya takaita wallahi mutuwa zatayi, kun bar mace a cikin mugun yanayi, ina ma mijinta yake?.”
Shiru duk sukayi, “Oh sorry bansan ya mutu ba, kunga kodan tunanin mijinta zaisata cikin damuwa, don Allah a kiyayye gaba.”
Gyaɗa kai sukayi kaman wasu dolaye, suna tsaye aka turo ni zuwa ɗakin hutu, shafa kaina Ummi tayi cikin juriya tace.
“Allah ya baki lafiya ya shirya zuri’arki.”
“Amin” Umma da Abdul suka ce, tafiya Abdul yayi gun biyan kuɗi, aka ce masa Dr Hameed Zaki Katagum ya biya, kome har na yaran sannan zuwa an jima za a maidata ɗakin VIP. Mamaki ne ya kamashi, dan yasan Dr Hameed Zaki Katagum, mutum ne da babu abinda yasa a gaba sai aikinshi baya shiga rayuwar kowa, sannan baƴa kyautatawa kowa, ga tsananin masifa, kowa shayinsa yake sabida mutum neda yatsaya akan gaskiyarsa, baya karya duk abinda ya faɗa iya gaskiyar ce. Basi jima da rabuwa da matarsa, Zuwariyya ba, sabida ta zubda masa cikinsa dan tana shayarwa a cikin asibitin yayi mata tijara, Murmushi Abdul yayi sannan yace.
“Mungode.”
Ya bar gurin, dawowa gun Ummi ya faɗa musu abinda ke faru, godiya sukayi tare da sanya mashi albarka.
“Ummi bari naje gida na dawo.”
“Allah ya tsare a dawo lafiya.” suka ce mishi, da sauri ya tafi.
……..
Sophia ta gama abincin rana tana saka kayanta ya shigo gidan, kallon jikinsa tayi a tsorace tace.
“Baby lafiya ? Waye yaƴo a tsari.”
“Kwantar da hankalinki Honey, Feener muka kai asibiti ta haihu, amma ba lafiya, babys ɗin suna ɗakin kula da jarirai.”
A ruɗe ta kalle shi, “Nikam bari nasa kaya ka kaini.”
Ganin yadda duk ta ruɗe yasashi riko hannunta yace.
“Honey! Tana lafiƴa fa muje ki yi min wanka, sannan wai yaushe zaki fara sallah ne na gaji wallahi bayana da marana daurewa nake kawai amma…”
Rufe mishi baki tayi da nata, sannan ta zare towel ɗin ya faɗi kasa, shigewa jikinshi taƴi tare da ɓalle botirin rigarsa, daga nan suka zube gado,
( toh ina zan iya wannan kallon🏃🏃🏃)
…….. Bayan wani lokaci suna rungume da juna, sai mita take masa shi kuma yana, shafa bayanta.
“Baby jikina ciwo! Yake min.”
“Meye yasa kikayi tsarin iyali? Kuma da zakiyi baki gaya min ba ko baki san zan fiki sanin wani tsari zaki yi ba, gashi ina zaman lafiƴa kin janyo min duƙ wata sai kinyi jini sau uku, plss duk abinda zakiyi ki faɗa min, sabida ni likitane, kuma ina da hanyoyin da zan kiyayye dan ɗauƙar ciki, nima kuma ina son ki huta.”
“Kayi hakuri bazan bazan kuma ba.”ta faɗa mishi a raunane, tasa mijinta yana da yanayi da mabukatar maza kuma tasan hakuri yake mata, in wani namijine tuni ya tsunduma bin matan layi, tare sukayi wanka sannan suka fito.
Ta ɗauki babban flask ɗinta ta cika da ruwan zafi, kana ta haɗa da manyan kofina guda biyu, sai abincin da tayi tasan bazai ci wani abu a halin yanzun ba. Ta haɗa kome sannan suka fita, can gida yaje ya ɗauki kayanmu a cikin wata karamar akwati ya fito daga gidan.
A bakin get ya haɗu dasu Batul da Khalila, da kuma Khalil ya gaya musu haihuwa,, Batul na shiga cikin gida ta kira Nanah Asma’u ta gaya mata na haihu.
……..
Suna isa ana canza min ɗaki, sannan, suka nufi ɗakin. Har dasu Ummi, ajiye kayan yayi zai fita sai ga Masijan ofishin Dr H.Z Katagum, ya kawo kaya niƙi niki, ya shiga dashi, sannan yafita ya sake shigowa da wasu kayan. Bakinsu Ummi a buɗe suke kallon wannan abin mamaki, yana gama shigo da kayan yace.
“Inji Dr Zaki Katagum.”
“Mun gode.”
Yana fita, Umma ta shiga buɗe kayan. Ledar farko kayan tea ne danginsu Madara ovalti, milo bournvita, cornflas, goldenmo, sugar me iyali, garin coffe, leda na biyun, kuma madaran jarirai ce, da pampas, wipes sai set na kayan sanyi, da kuma kayan jarirai irinsu Overolly, pink nd purple, da kuma wasu yan kananun safarsu. Leda na uku gashashiyar nama ce, wacce taji yankankun kabeje da albasa da tumatir gashi yasha yaji.(😎😏 saura naga cutar kwadayinku ya tashi ni dakune )
……. Mamaki ne ya kamasu Dole Abdul ya fita, zuwa ofishinsa. Koda yaje yasamu baya nan, dole ya dawo. Yana shiga yasami Nanah Asma’u tazo.
“Abban Affan muje ka nuna min jariran.”
Karban kayan yayi suka tafi, suna shiga Nurse ɗin da take kula dasu. Tace,
“Dr Zaki yazo ya duba yaran sannan yace za a kawo kayansu,”
Mika mata kayan yayi, ta amsa, sannan ta mika musu safar hannu, ta kaisu har inda yaran suke, kura musu ido yayi an mannasu da juna, suna jin ɗumin junansu. Abin gwanin sha”awa, karewa yaran kallo Asma’u tayi, sannan tace.
“Dukda bansan Babansu ba Dudu yaran nan kamar an raba gardama ne. Domin babu abinda suka ɗauƙa na Didi, hatta farcensu irin ɗaya ne da na Nannah, duba sajensu mana.”
Juyawa yaƴi ya kalle nurse ɗin yace .
“Maza ne ko mata?”
Murmushi taƴi sannan tace.
“Dukkansu Matane, Dr ban taɓa karɓan yara kyawawa irinsu ba, kyansu kamar yaran laraba”
Me karatu kayi nazarin kyau irin na Ashraf, asalin balarabe ne dan haka kyan yaran ya zarce ayi bayaninshi a rubuci kalleshi da mahangarka, yaran sun haɗu wai dama bakwaini ne……..
Oum Muwadda…..👏👏👏
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITERS ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Page.٢٧
“Kayi hakuri Baby bazan kuma ba insha Allah zan bata hakuri Baby ka maidani ɗakina. Bazan kara ba ka maidani ɗakina kaji baby.” ta karshe maganar cikin kuka, jawota yayi gabanshi yana kallon fuskarta a sannu jikinshi na kara sanyi wani irin kewarta yake ji, d’ago haɓɓarta yayi suna kallon cikin idanun juya yace.
“Ina jin tsoron kar na mai dake ki hanani aikata alkhai.”
Rufe masa bakinshi tayi da hannuta tare da girgiza kanta.
“Wallahi tallahi bilahi Azim, bazan cuce koda kiyashi ka kawo cikin gidan da sunan naka, bazan taɓa cutar dashi ba dan Allah ka yarda dani.”
“Toh irin wannan dadumar kin manta a gidan surukaina nake, don Allah sake ni kafin ki kayardani kin min fyaɗe.”
Murmushi tayi tare da kifa kanta a kirjinta, tace.
“Baby I miss u”
“Ke dai faɗi gaskiya, daga ganin ɗ’an Ummi kanin Didi Feener kin gigice” duka ta kai mishi irinta masoya tace.
“Sai na gayawa Didi kana gulmanta,”
Raɗa mata abu yayi a kunne, ta ɗago kanta da sauri tana kallon fuskarshi, gyaɗa kanta tayi tare da ɗaura kanta a tafukan hannunshi. Janye hannunsa yayi ya riko hannunta suka fita, har sun isa gun motarsa.
“Affan fa?”
“Kyaleshi Baby muje kaji.”
Murmushi me sauti yayi sannan yace.
“Ban gane ba sai wani rawan jiki kike, ina tsoron karki cinye ni ɗanye.”
Dariya tayi sannan tace.
“Ai in danye ne da sauki, if i catch.”
“Yarinya ki bi a hankali sau nawa ina win ɗin ki yau ma muje a sake gwada.”
“Wayyo Allah ni banja muyi haka da kai ba.”
Haka suka isa gidansu sosai suka shirya tsakanin miji da mata ya tabbata.
***
*SAUDI*
“Abisa hujjojin da kotu ta haɗa, mun sallame Sultan Ashraf akan zargin da muke masa, tare da bashi hakuri sai kuma muna gargaɗinsa da kar yakuma yin shiru akan gaskiyarsa, dan haka kotu ta ɗaure shi har na tsawon wata goma babu tara dan ya zama gargaɗi da izina ga mutane irinshi, sannan a gefe guda Mun mika Marhum ga Hukumar kasarshi kamar yadda jami’in jakadar Kasar Jordan ya bukata, alkali na gama bayanin ya mike, nan mutanen cikin kotun suka ce kotuuuuu.
***
Nigeria.
Yau aka sallame ni a asibiti bansan ya akayi ba, sai ganin Dudu naƴi ya wucce damu gidan Abba, kallon Ummi nayi itama ranta a ɓace yake, kana ganinta kasan ranta yakai kololuwar ɓaci, lumshe idanunta tayi taki magana. Kwantar da kaina nayi a kafadarta a hankali kwalla ya shiga sauko min, daga idanuna riko hannuna tayi cikin rarrashi tace.
“Kiyi hakuri kome na duniya me wuccewa ne,Insha Allah wata rana sai labari.”
Gyaɗa kaina nayi dan na kasa cewa kome har muka isa gidan.
….. Abinda ya faru kuwa, kwana biyu da suka wucce Anim yaje gun Abba dan ya fahimci da zaran aka sallame ni, Suleja zamu koma da Ummi shine munafuki ya sami Abba da cewa ya maida Ummi wannan ba darajarshi bane ace yar shi da uwargidanshi basa gidanshi kuma ai haka zai zamewa Safeenah abin gori, kuma a matsayinshi na babba me mutunci ya kamata ya kankaro darajarshi a idanun jama’a kar ya bari mutane su fahimci matsalar gidanshi.
Nan Abba ya amince, sannan yaje har Suleja, ya sami Yayan Ummi sukayi magana yace yaje ya same Babban yayansu dake Maiduguri, dan haka yana dawowa. Suka tafi da Anim inda aka maida Auren Ummi da Abba ba tare da izinta ba. Koda suka dawo Sheik Hayatudeen Kamfu ya kira Ummi yayi mata nasiha sannan ya gaya mata,abinda sukayi. Hankalin Ummi yayi mugun tashi data gayawa Abdul kwantar mata da hankali yayi sannan yace karta bari nasani dan ya fahimci ina ganin laifin kaina akan faruwan kome, parking da yayi ya dawo dani daga duniyar tunani. Na kurawa gidanmu ido, gashi nan na sake dawowa. A hankali Ummi ta fita, bangarena Ummi tazo ina fitowa ta miko min hannu na riketa sannan na fito a sannu, ganin Umma tafito ita da bakuwarta ya sani juyawa cikin mota da dan sauri, Ummi ta rike ni tare da girgiza min kai tace.
“Duk wanda yayi miki dariya ko habaici bai san kan rayuwa bane, idan kasan kan rayuwa baka dariyar motar gawa.”
Riko ni sosai Ummi tayi, har muka iso gunsu Umma kaina a sunkuye.
“Hajiya Maryam! Ya me jikin dai? Kuyi hakuri ban zo muku jajje ba, sabida ina gudun kar nazo ace gulma ko wani abu na daban, dan kinsan duniya ba a iyar mata.”
Murmushi Ummi tayi sannan tace.
“Hajiya Barakah ai duk wanda yazo gulma ko ganin wani abu toh zan iyacewa bai san me ake kira da kaddar bane, amma idan kasanta toh babu ruwanka da kalubalartan nawani.”
“Hmm! Hajiya Maryam abar kasa a cikin gashinta, nima kamar yadda ya same ki nima ya taɓa samuna, domin kuwa Rashmar ta taɓa kinkimo min magana, wanda sanadinsa tunda muka rabu da Alhaji har yau bamu dai-daita ba, amma ni na zubda cikin gaskiya sabida damuwar zata min yawa ina zan kai damuwa dan a lokacin ji nayi ina ma bana raye.”
Riko hannuna Dudu yaƴi muka shige, yana ce min.
“Kin tsaya bin nasu Ummi, da wancar maganarniyar matar sam magana baya damunta, da kuma suka zubda cikin ai gashi Rashmar ɗin haryau bata sake samun ciki ba, da sun bar mata cikinta maybe da tana da ɗanta na kanta.”
“Nima da na rasa wannan babyn maybe har na koma ga Allah bazan rike ɗan kaina ba.”
Matse min hannu yayi sannan yace.
“Karki damu Allah ya tsare.”
Jingina kaina nayi a hankali nace..
“Dudu! Maganata ta dawo.”
“Kuma munata binki ki gaya mana waye yasa a sace ki kinki faɗa sau nawa yan sanda na zuwa sai kice baki sanshi ba.”
Bansan me yasa naki gayawa Mutane cewa Anim ne ya sace, kodan yadda ya nuna kulawarshi akan ciwona ne ban sani ba, amma wallahi na tsani Anim fiye da kome a duniya dan bana raba ɗayan biyu yana cikin sawun munafukai, sabida yadda yake pretending a gaban dangina da yadda yake cewa idan ya kama wanda ya sace ni sai yasa an minshi wulakanci da bakar izaya, sai na buɗe baki nayita kallon ikon Allah, mutum ya zama annamimi.
***
Jordan…..
Yau jumma’a bayan sallar Abu Zarri yazo zai shiga mota aka, kuskuran harbinsa. Bobyguard ɗinsa suka ture shi ya faɗi, daga nan aka shiga musayan harbi. Dakyar yan bindiga daɗin suka ware bayan an harbi mutum ɗaya a cikinsu. Koda suka koma gida jikinshi rawa yace.
“Ukshe!!!”
Ya kira da karfi, ɗauka rigarshi yayi. Ya fita da sauri sai gidan Ukshe yana zaune akan keken guragu, cikin zafin rai yakaiwa Ukshe tokari. Cikin izza irinta larabawa yace.
“Duk wanda yayi niyya ya fasa shege ne, idan na kyaleka Wallahi ba jinin Banu Hashim ke bin jikina ba. Wallahi tallahi Ukshe mu fara daga yau har ranar da duniya zata tashi.”
“Abu Zarri! Na rantse da Ubangiji sai na hanaka farin ciki, Abu Zarri.”
“Idan ka fasa kai shege ne. Banza mara mutunci. Banza kawai wallahi sai dai muga bayan juna.”
…….
Banu Nazir..
“Alexandra!! Nazo maka Da tayu me gwaɓi, tsakanin Ukshe da Abu Zarri yayi tsamari, idan muka amshi mulkin kaga jordan ya dawo hannunmu, kuma zan ka goyan.”
“Adnan! Kaje babu ruwana da haɗakar kowa, idan ina bukatar mulkin da kowa, iya ni zan kurmushe kowa.”
“Zanyi murna idan ka nemi goyan bayanka ɗari bisa ɗari.”
“Bana niman goyan bayan kowa Iyani kaɗai gayya. Zaka iya tafiya.”
…..
Wato wani zazzafar bala’i ya ɓarke a jordan ga arziki ga mulkin babu sarki, sannan ga kaiwa juna harin bazata dan kowa yunkurin kashe junansu. Kuma duk wannan bala’in babu wata hukuma da tayi yunkurin shiga rigima, sabida an bar abin akan iyakar zuri’a guda suke wannan tashin hankali.
Ammar da Uzaif an barsuna matsayin sune masu, sulhu idan ka gansu sai sun baka tausayi sabida tsabar tashin hankali da ya addabi masarautar, kuma a wannaj yanayin Marhum ya dawo dama duk shirin Ukshe ne, idan yasa aka dawo dashi zai san yadda zai fito dashi, a cigaba da fafatawa.
***
Mikar da kafafuna nayi Anas yana matsa min, ni kuma ina rike da magarya, sai tsotsa nake ina gyaɗa kaina, dan ina sauraron kira’ar sheik Abdul Basi. Cikin suratu Maryam, shi kuma yaron ya dage dai matsamin kafar yake, a lissafina dai wata bakwai kenan, cikin yayi wani mugun girma, idan Abdul yazo zama yake yana min dariya, yace.
“My Mom Babys! Kinga hancinki kuwa kamar tukunyar miya musaman nan ɗin nan” buge hannunshi nayi tare da tura bakina, nace.
“Dudu! Kafita idanuna mana kasani a gaba da maganar hancina ya cika girma. Sai na gayawa Ummina.”
“Toh kajina har kun fara raba halin ko? Maza karɓa wannan kisha, yana taimakawa gun haihuwa.”
Wato wannan alamarin yana matuƙar kwantar min da hali, domin kuwa bana jin daɗin Abba da matarshi Amma Umma babu ruwanta, mamie uwar yaɓ zakale kan ba acewa kome.
“Eyye lallai kuwa, wato ga bawa nan, kinga banza. Bari kisa min d’a aikin akan cikin shegenki, toh wallahi a hir ɗinki dan na rantse da Allah kika kuma samin ɗa aiki sai na miki rashin mutunci, tashi muje shashashar banza kawai, karuwa tasi ba fasinja.”
“Alhamdulillah ni cikin shege nayi wasu kuwa, abinda suke aikatawa na shirka yafi karfin kare yaci.” na gaya mata tare da mikewa, aikuwa a zuciye tayo kaina zata dake ni, Ummi tace.
“Amma rashin hankalinki ya girmama Nuratu zaki daki Mace da ciki ko? Hmm lallai kuwa bar ganin kina abu bana magana, kika sake na fusata wallahi kika taɓa min Y’a da ciki sai kinyi danasani, dan ko Badaru ne ya taɓa min ita sai duniya tajimu dashi dan ni yanzun ina zaune da kowa sabida Safinatu ne idan babu ita wallahi bazan zauna da shi ba, kisa kai ki ficce min a falo mara mutunci.”
Bata taɓa ganin ɓacin ran Ummi ba sai yau, dan haka tuni tasa kai ta fita tare da kwafa, zata rama. Kaina ne a sunkuye ina zubda kwalla, sam bana son fitina, shi yasa har na jure wahalar da Samudawar Ashraf gashi yau gidanmu ana rigima sabida ni, Allah kaɗai yasan ma’anar kwafar Mamie dan naga Babu Allah a cikin alamarinta.
Mika min hank akayi na ɗago kaina, ina kallon Anim, bansan lokacin da na galla mishi harara ba, tunda na fara magana yake sake son yaji me zance amma bai samu danar haka ba, dake Ummi tana gama gayawa Mamie magana ta shige ciki, shi yasa basu gami ba, jin hannunshi nayi a cikin zanina yana shafa cinyata, bansan lokacin da na tsinka mishi mari, dafe kuncinsa yayi. Yashafo marin yakai bakinsa ya sumbata, sannan ya kai kan bakina na buge hannun, leka kofar Ummi yayi, da sauri ya sumbaci goshina, na ture shi, nace.
“Bana cike da iskanci Mugu Azzalumi kawai kai ko tunani haɗuwarƙa da Allah bakaƴi sai iskanci da kasa a gaba wai kana kira da so.”
……..
Oum Muwadda……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITERS ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
_Na sadaukarda wannan shafin ga Iyaye mata masu fafutukar kare Yaransu….A cikinsu Har da Mahaifiyata Allah ya jikanki da Rahama👏_
~_Ina muku fatan alkhairi Masoyan MJ daga Whatsp,Wattpad, Face book nagode_ ~
Page.٢٩-29
Daukar ɗaƴa yayi ya musu addu’ar da musulunci ta tanada domin ayiwa jarirai, yayiwa tafarkon wacce aka sayawa bam pink, sannan ya ɗauki wacce aka sanya mata purple bam, yayi mata kana ya maidasu cikin gadon.
“Dudu! Don Allah ɗaukesu a hoto sun min kyaune zan ɗaura a Status ɗina.”
Tsuke fuska yaƴi tam sannan yace.
“Koda wasan wasa kar naga hotonsu akan social media, dan zan saɓawa kowa.”
Tura baki tayi sannan tace.
“Plss zan ɗaura akan Dp ɗina,”
Hararar ta yaƴi sannan ya fito daga ciki ta biyo bayanshi, tana murmushi tace.
“Abban twins!”
Murmushi yayi ya tsaya, “Plss”
Mika mata wayarshi yayi ya barta ta koma, wani abinda ummi tayi ya kara haɗe kanmu ba kome bane sai cusa mana soyayyar junarmu, idan abu yasamu mutum ɗaya kama ya samu saurane, duk wani dabi’a irinta sako da sako duƙ bamu dashi, sam yadda take da sanyi hali haka muma muƙa ƙasance dan ita har wasu nace mata baci suna maryam ba, amma ko yayya ne mu dai muna son Uwarmu haka, dan tayi na mijin kokarin ganin mu tashi da tarbiya, akasin kaddara da ya faɗa min ne kawai zan iya ce wani abu.
D’akin ya dawo yasame Umma tana son komawa gida, Ummi da Sophia tare da Nanah suna nan, Abdul ya dawo da Umma ya kuma kwasosu Batul ya kawosu. Zuba min ido Khalil yayi sannan ya dubi Ummi yace.
“Allah yasa karshen matsalarta kenan”
“Amin” duk ɗakin suka amsa,
“Toh Ummi ina yaran suke?” Inji Khalilah, mika mata wayar Nanah.
“Duba gallary,”
Da sauri ta amsa, har suna rigayen karɓa, duba gallaryn tayi sai ga hotunan yaran,
“Masha Allah! Haka yaran suke da kyau,”
Aikuwa Khalil ya amshi wayar ya shiga bin hotunar yaran, sai murmushi yake sakewa.
“Ummina Didinmu ce ta haife su, masha Allah bari na ɗaura a Tweet..”
“Sai kasan amsar da zaka bawa Babansu dan Dudu ya hanani.”
Inji Nanah,
“Ahtoh na hakura, tunda yace kar asaka.”
Duk wannan yana cikin tsarin tarbiyan Umminmu domin idan babba yace kar ayi abu toh karami bai isa yayi ba, kuma koda laifi karami yayi bata taɓa kallonshi zata barshi da yayunsa su masa faɗa, sannan itama ta ɗaura da nasiharta, tunda Ummi ta haifeni har na girma Ummi bata taɓa dukana ba, sai tsawa shi yasa lokacin danaje jordan nasha wuyar jibgar sa suka min.
Basu bar Asibitin ba sai dare, aka bar Ummi, bayan tafiyarsu Dr HZ. Katagum ya shigo duba ni, sam Ummi bata san shine yayita hidima ba, cikin mutunta juna suka gaisa sannan. Ya kama abinda ya kawo shi yana gamawa yafita, ita kuma ta cigaba da laziminta.
***
Washi gari dakin ya kuma cika da yan uwana. Da mutanen arziki tun safe Abdul ya kira Nannah ya gaya mata haihuwar.
Tsabar murna kamar tafito ta wayar. Karfe biyar na yammacin ranar na farka, a sannu abubuwan da suka faru ya dawo min, lumshe idanuna nayi tare da fashewa da kuka. Kukan nawa ya sanar musu farkawata, Batul ce ta fita. Taje ta kira likita. Can sai gasu tare da Dr Katagum, yana shiga yace.
“Ku haɗa min tea! Sannan ku ɗan bamu guri, amma Mama karta fita ta tsaya dan taimaka min.”
Duk suka fita, shi da Ummi aka bari. Ya ɗauko auduga tare da wani almakashin ɗaukar auduga, ya karɓi wani kofi. Da kanshi yakawo kwanon silve ya mikawa Ummi sannan ya umarce ni na buɗe bakina, ina ji ina gani ya wanke harshen tass, sannan ya kalle yadda nake kuka sosai,taɓe baki yaƴi cikin gatsali dan matsalarshi bai iya magana ba. Yace
“Yanzun ɗan wannan abin kikewa kuka, kika iya haihuwa sai wanke baki ne kike zubda hawayenki, toh ai sai ki ɗaura ɗammara dan yanzun zaki sha hot tea.”
D’ago idanu nayi tare da kallonshi. Karɓan tea ɗin yaƴi sannan ya kurɓa, kana ya mika min.
“Ki godewa Allah da yabaki Jarumar Uwa! Inda nine da zafi zakisha, dan haka zuwa an jima zan dawo ki adana hawayenki”
Yana gamawa ya juya ga Ummi yace.
“Sannu Mama! Zaku iya amso mata yaran ta fara shayar dasu.”
“Toh mun gode sosai,” tace masa, har zai fita tace.
“Don Allah kaine Dr Katagum!”
Cike da jin kunya ya gyaɗa kanshi.
“Mungode sosai, da Hidima Allah yasaka da alkhairi.”
“Amin, Mama!” yace sannan yabar ɗakin, da kallo nabishi sannan na kalle Ummi ina jiran karin bayani, karɓan tea ɗin tayi. Taje ban ɗaki ta haɗa min ruwan zafi sannan ta fito ta riko hannuna muka shiga ciki, Lallai na yarda Ummi Jarumar Uwa ce, ita da kanta tamin wanka tass bayan ta gasa min jikina yadda ya dace, sannan ta fito tace.
“Ki wanke jikinki kuma kisa ruwan zafi a gurin, banda shirme dan matuƙar baki gyara gurin ba kece a ruwa. Babu abinda ya dame ni.”
Murmushi nayi a raina nace.
*Ummi kece kuwa me shiga damuwa*
Wanka sosai naƴi sannan na fito, riga da zani ta bani na saka, bakina yaƴi nauyi, dan haka bana magana sabida harshena.
Zama naƴi sai gasu da yaran, tea ɗin na karɓa ina sha tare da matse kwalla, ina gamawa ta mika min magani nasha, sannan ta shafa mun bonjula, akan harshena, ina gamawa tana samin yarinyar farko aƙan cinyata, d’ago kaina nayi na kalleta, murmushi tayi sannan tace.
“Idan da duniya zasu haɗu domin dakatar dake alokacin, tabbas rabonsu zan iya kashe mutumin da ya nemi dakatar dasu, Safinah rabon y’ace nada zafi tafi kowacce halitta zafin, Kuma ki duba da kyau yara biyu, ki godewa Allah da ina raye haka ta faru, da bana raye ko kuma Dudunki ba me kula bane, nayi imani da Allah mutuwa zakiyi, tunda kika ga sunzo toh ke baki isa dakatar dasu ba.Allah ya albarkaci rayuwarku dake dasuma.”
Kuka nake sosai, ina kallon yaran, nama rasa me zance dan nayi kuskure a rayuwata, nice Babba kuma nice na fara zubda mutuncin gidanmu, ribar taurin kai har da shegu. Dafe goshina naƴi sakamakon sara min da yake Ummi tayi maza ta riko babyn.
Kallon Ummi nayi ina girgiza kaina nace.
“Ummina! Ni bazan shayardasu ba, kawai a shayar dasu Madar.”
Make min bakina taƴi cikin wani irin ɓacin rai, wanda ban taɓa sanin tana dashi ba, ta kuma ɗaga hannu zata mare ni, haka ta kasa marin, saukewa taƴi ranta yana tafasa, ta dire min jaririyar ta ɗauki hijab ɗinta tace.
“Nagode.”
Tasa kai zata fita, Khalil yace.
“Ummi! Ke da kika haifemu kikayi fushi da alamarinmu ina kuma wani na daban, Ummi idan kikayi fushi da ita bazata ga daidai ba, don Allah kiyi hakuri Didi bazata kuma ba.”
Kallona yaƴi cikin jin haushi amma yayi kokarin haka yace.
“Didi baki kyauta ba ɗauketa ki bata abincinta ba a shayarwa ke aka shayardake,”
“Ibrahim sheg…”
“Ke kan wallahi baki da hankali.” Inji Umma da tashigo ganin Ummi a tsaye yasa tsayawa a gun, gashi taji abinda Khalil ya faɗa min, uwa Uba katoɓarar da naƴi. Hmm bakin ciki yasa Ummi barin asibitin, ba ita ɗaƴa ba hatta yan uwana, dan Alakatafur naki bawa yaran nono, har Abdul sai da yaji haushina. Maida yaran akayi ni kuwa na cigaba da kuka na, Umma kaɗai aka bari. Muna zaune sai ga Dr Katagum ya shigo da yaran yana ɗauke da daya, nurse tana ɗauke da ɗaya..
Yana zuwa ya ja kujera ya zauna sannan yace min.
“Maza basu nono.”
D’agowa nayi a tsiwa ce, muna haɗa ido naga ya cika min ido, dole na sunkuyar da kaina, na buɗe rigar na rasa ya zanyi da babyn, nurse yayiwa magana, sannan ya juya gun Umma da take min faɗa da harshen shuwa, tana gamawa, ta shiga masa godiya.
Nuna min yadda zan bawa babyn nono tayi, sannan ta ajiye min ɗayar, ta fita.
Babyn tana kama nono na lumshe idanu, sabida zafi.
Haka mukayita dambe da Babyn sannan ya amsheta ya sakata a kafaɗarsa, sannan yanuna min ɗayar.
Na ɗauka fita Umma tayi dan ana kiranta a wayarta bata ji.
Tana fita sai bumm muka ji kamar an wurgo shi ɗakin, ɗ’ago kaina nayi, bansan lokacin da yawu ya sarke min ba, tari na fara. Dr Katagum ya mike yazo ya amshi yarinyar ya kwantar da ita, sannan ya zuba min ruwa a kofi na zafi sannan ya ɗauki na goran faro ya zuba min, tare da mika min, da sauri na amsa.
Takowa Anim yayi yazo ya kalle yaran, cikin mugunta yace.
“Sannu uwar yan biyu, riba har da uwar kuɗi kenan.”
Rike rigar Dr nayi ina girgiza kaina, kallon Anim yayi ciki mamaki yadda yake murmushi.
Gashi yana kokari taɓa yaran, cikin kuka nace.
“Karka barshi ya taɓa min su!”
Aikuwa ya rike hannunshi, tare da maidashi baya, dariya Anim yayi..
“Kice anan ma kin kuma samun aboƙin tayi, toh su yaran ubanansu nawane haka?”
Kuka ne ya ci karfina sosai.
“Wai Anim me yasa kake son cin mutuncina ne, laifin me na maka ne da zafi,me na tare maka a rayuwar duniya? Nayi danasanin saninka a rayuwata, kuma Ubangiji sai yayo min sakayya.”
“Dalla rufa min baki, meye kika min, bayan kin lalata min nawa rayuwa, kika je kika kwaso wasu shegu a rayuwarmu.”
“Yarana ba shegu bane, domin sa Ubansu sai dai kaine dai basu ba.”
“Keee! Ni kika zaga?” cikin kwarin gwiwa nace.
“Eh ɗin na zageka.”
Dukda ciwon dake harshena bai hanani kare mutuncina ba, kaina yayo zai dake ni, Dr Katagum ya dakatar dashi ta hanyar mai dashi baya.
“Dalla malam matsa min, dakai ba kaine aka yaudara ba, ka tmbayeta abinda ta min, da sadakina taje wank katon iska ya lalata min tanadina,”
Dafe goshina nayi hawaye na zuba wannan na ƙoran wanan. Dr yace.
“Shin wani irin tanadi aka lalata maka?”
“Bada mutuncinta na ace da tayi shine tanadina.”
Murmushi Dr yayi sannan yace.
“Kenan dama ba ita kake so ba, Budurcinta ƙake hari, da zaka samu a waje bazaka taɓa damuwa da taje gidanka ba, ko kuma kana aurenta kaji yadda take ana kwana biyu zaka saketa ko?”
*Wacce amsa Anim zai bada???*
Oum Muwaddah……👏👏👏
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITER’S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Labarin daban yake da sauran._*
Page.٣٠-30
Wuri-wuri Anim yayi da idanunshi zuciyarshi tana wani irin buga, kankance idanunshi yayi ranshi na kara ɓaci. A fusace yace.
“Kai waye? Da zaka sani a gaba da tambayoyi! Ita ɗin dadironkace, ko abar kaunarka ce? Gata nan da cikin jikinta na shayar da ita madaran jikina ko karya ce na miki? Da kanta tazo gurina muka tsallaka tsakiyar taku da ita har na wata gud..”
“Azzalumin macuci Allah sai ya gwada maka iyakarka, wallahi babu abinda ya taɓa haɗani da shi, Wallahi ni ba fajira bace” na faɗa cikin kuka,
“Toh cikin da kika haifa taya kika same su?”
Dafe goshina nayi dan tsakanin da Allah Anim yake son lalata min farin cikina, a yanzun da nake kokarin tattara d’an kuzarin da na rasa shine bari ya lalata min su, ban tsammaci jin magana me kyau daga bakin Dr ba sai da ya doki dodon kunnena.
“Malam! Idan na fahimta kana yin haka ne dan taki amincewa da kai ? Ni a tunani na idan kana son mace kuma ka ganta a gidan karuwai, babu abinda ya dameka ɗaukota zakayi ka aureta, sai gashi kaddara da rabo sunsa kana cutar da zuciyarta da ruhinta, kuma kana kiran haka da *SO* bayan babu wani masoyin gaskiyan da zai so cutar da abokiyar soyayyarsa, zan faɗa maka wani abu guda ba a haka zaka nuna soyayyarka ba, dan kana kusantata da ɓacin rai yana rage kima a idanunta.”
Tsaki yayi zai magana, sai gashi ya fita. A zafaffe Dr ya juya gareni tare da tsare ni da mayun idanunshi masu, matukar karfi da haiba.
“Taya kika same su? Iya gaskiyar da kika faɗa shi zai bani damar dakatar dashi.”
D’ago kaina nayi na zuba masa ido, a sannu nayi kasa da kaina. Sannan na fara basu labari dan bashi kaɗai bane a ɗakin har da Umma da kuma Abbanmu wanda ya kira Abdul ya kawo shi.
Da nazo inda kaddaran cikin yaran kasa faɗa musu kome nayi, kuka na sake me taɓa zuciya da ruhin me sauraranshi, sai da nayi ya ishe ni sannan na ɗago kaina na cigaba da cewa.
“Sam baya cikin hankalinshi, dan sun masa sihiri da ya samu taɓen hankali, nasan waye Ashraf dan na zauna dashi kafin faruwa alamarin bai taba kallona cikakke na sec, balle na mint. Mutum ne da ya kame kanshi daga masha’a da ace zai min haka da tuntuni yayi min, amma haka ya tsare kanshi har na shiga rayuwarshi.”
Ɗago kaina nayi na kalle Abba, tare da girgiza kaina nace.
“Abbana! Nasan dalilinka na korata dan zan zubar maka da kimarka, wallahi ko da wasa ban taba barin wani ya taɓa kimarka ba, da sona ne yaran nan bazasu kasance a raye ba, amma sun zame min kaddara wanda bazan iƴa kankaresu ba, don Allah ka kira Nannah ta ɗaukesu zan zauna da kai kuma zan maka biyayya.”
Kura min ido yayi cikin zubda hawaye yace.
“A’a ki shayar da yaranki!”
Girgiza kaina nayi cikin kuka nace.
“A’a Abbana! Ta tafi dasu kawai tunda suna da gatansu, kuma bugu da kari kabilar larabawa basu cika baiwa Yaro nonon mahaifiyarshi ba, dan sukan ɗaukesu zuwa gun reno.”
Duk yadda suka so na amince da yaran fir naki, abin ya basu mamaki, haka suka watse zuciyarsu ba daɗi. Ni kuma dalilina nakin yaran ba kome bane yaja haka sai dan karsu fuskanci matsala. A rayuwarsu kuma bana son shakuwa ya shiga tsakaninmu yadda rabasu dani zai zama matsala.
***
Washi gari aka kuma tashi akan batu ɗaya, nima kuma na kafe akan ra’ayina, da aka kawo abin karyawa har da kunun tsamiya, aikuwa nasha sosai, bayan awa guda nonuwana suka cika sosai. Har ya kai dakyar nake d’aga hannuna, sabida cikarsu na kuma yi shiru. Dan kar ace na bawa yaran nono. Shigowar Dr yasa aka kawo min yaran, ina tura bakina ina kunkuni haka na basu suka sha har suka koshi, kallon Umma nayi cikin mamaki nace.
“Ummanmu! Yaran nan da shegen wayo suke dubi yadda suke shan nono kamar wasu mayunwat…”
Maganar tamakale min ne sakamakon shigowar Nannah da wasu tawagar mata da maza, har da Ghaniyu kamar na watsar da yaran nace.
“Akhee Ghaniyu!”
Murmushi yayi cikin girmamawa yace.
“Amirah Safinatu, sannu uwar gimbiyoyin Jordan, Ina mika gaisuwata ga Sarauniyar gobe a birnin Amman, Umarninki nake jira Sarauniyata.”
Duk sai naji wani iri lokaci guda wani irin girma da dauk’ak’a sun hau kaina lokaci guda, haka tawaga Nannah suka shiga mika min gaisuwa, wasu mata suka zo gun yaran suka fara dubasu, abinda bamu taɓa lura dashi ba kodan ba a gun mu suke ba, tsakanin kirjinsu zuwa bayansu akwai wani abu kamar tasiwera(Map) wanda ya kara tabbatar musu yaran nasune, take suka shiga ambatar barakallah.
Cikin murmushi nan ta kalle wata dattijuwa tace.
“Amirah Humaidah na gaya miki binti bazata taɓa min karya ba, kinga shaidar toh haka ma Ashraf shima akwai tasweran masarautarsu a jikinsa.”
Ni dai ido nake binsu dashi nan suka shiga godiya da kuma ban hakuri ga Umma, fita sukayi da yaran. Nace
“Allah yasa su tafi dasu nima na huta.”
Make min bakina Umma tayi, dake sun fita. B’are musu baki nayi tare da sake kukan saƙalci kamar karamar yarinya nace.
“Allah bana son yaran! Gwara su tafi dasu.”
Shafa sajenshi Dr yayi cikin murmushi, yace.
“Kina fama da yaranta! Babu wanda ya isa rabaki da yaranki.”
Galla mishi harara nai tare da murguda mishi baki, nace.
“Ai kana da nono ka bas..”
Sake buge min bakina Umma tayi, cike da takaici tace.
“Amma baki da mutunci Yakolo, rashin kunyarki ya shahara, kuma ki fita idanuna.”
Kuka nake har da majina,
***
A gidanmu kuwa, cikin girmamawa Ummi ta amshi bakin dan tasan da zuwarsu, hidima sosai aƙa musu, dan har Sophia da Nanah Asma’u suka haɗu akayi musu abubuwan tarɓa. Nannah tana gaya musu irin rikonda aka mata, godiya sosai sukayi. Sannan suka bawa Ummi da Abba hakuri da kuma irin abinda ya faru. Murmushi Ummi tayi dan haka kunya ya hana shi magana.
“Babu kome jarabtace kuma babu wanda ya isa kaucewa kaddaranshi, Allah yasanyawa rayuwarsu albarka.”
Sunji mugun daɗi, tare da godiya. Sannan sukayita godiya, tare da alkhairori masu yawa, sannan Nannah ta gabatar da Nurse ɗin da zata kula da yaran har da ita kanta.
Kyauta masu daraja suka bawa yaran dani kaina, wasu manyan akwatina glass aka kawo suka ajiye a gaban Ummi sannan suka buɗe nan aka ciro wasu kambu, na yaran wanda akayi su da farin zinari wato (Whiter gold) sannan aka bisu da wasu beart na diamond(Lu’ulu’u)
Mikawa Abba Yarinyar farko Nannah tayi, tace.
“Ka zaɓa musu sunaye masu daraja, da kima.”
Karɓa yayi ya musu huɗuma sannan ya mika mata, ta mikawa Dattijuwar, Aka sake bashi d’ayar yayi mata Huɗuma, sannan ya mika mata. Cikin girmamawa, Ghaniyu ya sunkuya gare shi yace.
“Kakan gimbiyoyin Jordan wani suna ka sanyawa uwanye ɗakina?”
Kallonsu yayi cikin nauyin baki yace.
“Tafarkon na mata Huɗuba da Asma’ulHusnah Tabiyun namata Huɗuba da MaryamSajida”
“Allahu Akbar!!!”
Kunya ya hanashi ɗago kai sai kwalla da yake sharewa, Ummi kan takasa magana, sai bin Abba take da ido. Kowa a falon jikinsa yayi sanyi, dan Abba bai taɓa cin karo da nadama irinta yau ba.
Mikewa Bakin sukayi sannan suƙa ce.
“A faɗawa Sarauniyar Jordan na gobe sun gode zasu koma idan yaran sunyi kwari akai musu suga dangin Kakarsu.”
“Insha Allah zasu zo.”
Inji Abba, rakasu duk yan gidan sukayi sai da suka ga tafiyarsu sannan suka dawo, Abba da Ummi suka dawo min da yaran, har da nurse sun zo sun samu anata rigima dani. Dudu yana tare dasu Nannah, har dasu Nana.
Cikin ɗaurewar fuska Abba ya ajiye min yaran, sannan yace.
“Shayarda su.”
Ba musu na basu, sai da suka koshi sannan na cire su. Ban ɗaki na shige na sake ruwa sai da nayi kuka ya ishe ni na fito, lokacin Nannah har ta iso, gani nayi ana tattara kayanmu. Dr ya kalle ni sannan ya ajiye min kwalin waya, ta kowa yayi gaba dan har sun fita ni ɗaya ce, na rage zan saka hijab ɗina.
“Kiyi hakuri ki shayar dasu.”
“Bazan iya ba, sanadin cikinsu na shiga garari.”
“Karki butulcewa Allah rahamar da yayi miki” yace min a hankali.
Ina jin idanunshi a cikin jikina, dakyar na d’ago idanuna sai naga ya cika min ido nace.
“Ni ka kyal.”
“Bashi zaki faɗa ba, me yasa kika kasa faɗa.”
Cikin mutuwar jiki na ɗ’ago a karo na uku nace.
“Abinda nayi niyya kenan”
Zuba hannunshi yayi cikin aljuhunshi, tare da lashe lips ɗinshi. Lumshe idanuna nayi sabida ya tino min da Ashraf, bansan ya akayi ba sai ji nayi nace.
“Ina kewar Ash.”
“Kina kewar Ashraf ko! Toh haka ma yayi ga waya nan hot8 ce bata da tsada ki rike sai ki welcome back, akwai numbeta zan na kiranki ina jin yarana ya suke. Sanna wancan shashashan bazai kuma damunki.”
Motsin da naji a bakin kofa yasani lekawa,Abdul ne ya buɗe sai kuma ya koma, raɓa gefenshi nayi na ɗauki hijab ɗina, ban kula wayar ba.
“The phone!”
A hankali nasaka zararan tsintsiyar hannuna na ɗauƙa, na fita ahankali yana take min baya, duk wanda ya kallemu a lokacin sai ya kuma kallonmi, sabida munyi wani irin dacewa ne da juna, musaman da ya kasance fatarmu kusan ɗaya ne, dan shi ya fini hasken fata.
Wucce ni yayi yaje ya buɗe min motar, na shiga a hankali. Sannan ya rufe tare da cewa.
“Ki kula da yaran don Allah.”
“Hm” nace mishi, haka Abdul yaja motar yana tsaye a gun.
Shafa kanshi yaƴi zuciyarshi fess, yana hango yuwar nasara a cikin alamarinsa, dunkule hannunshi yaƴi ya ɗan daki gefen kirjinsa, yana cewa.
“Miskilancinki ya girmama anan.”
Yayi tap ɗin gefen kirjinshi, har da wani lumshe idanunshi.
***
Koda muka isa gida, side ɗin Umma aka wucce dani, ita kuma Nannah ta wucce side ɗinta, nan aka shiga hidima dani. Kamar ba gobe.
Hmm idan nace larabawa suna da mugun son yara banyi karya ba dan na gani akan idanuna, da dare aka kawo min yaran na basu nono fir naki nace barci nake ji. Fita nurse ɗin tai sai gata tare da Nannah, cikin rarrashi ta bani Takwararta. Amma kam naki bata karshe nasaka musu uku.
“Kiyi hakuri ki basu abincinsu mana Binti.”
“Shegune zan basu nono n?”
Wani ba hangon mari Aka tsinka min, tare da kara min. Jikinta har rawa yake, a razane na ɗago kaina,mukayi ido biyu da Ummina, cikin fusata tace.
“D’aukesu nace! Ki kuma kiran da wani suna ni dake ce.”
Kuka na fasa tare da yin baya nace.
“Wallahi bazan basu ba, dan ai.”
Ban taɓa ganin ɓacin ummi sama da yau, dan hannunta har ɓari yake, tana niman abinda zata min rutsi da shi sai akan kwalbar Humra. Kafin mu farga. Sai rutse min kai tayi, ta kuma ɗauke yaran ta mikawa Nurse dan Nannah tun da nakira yaran da shegu. Da kuma marin da Ummi tayi min, tasa kai tafita. Tana kuka sosai dan ta hango kiyayyar yaran a idanuna, sam bana kaunar yaran kamar yadda bana kaunar Ubansu.
Allah ga jego ga caskaleni da Ummi tayi, sai da taga bana iya jan numfashi sannan tafita, ta kuma kawo min yaran ta buga min tsawa tace.
“Tashi ki basu? Wallahi kika bari Nannah ta bar kasan nan da yaran nan Safinatu Wallahi! Tallahi!! Baki bina bashin rantsuwa sai na miki Allah ya isa……”
Dagske Nannah zata tafi da yaran bayan ta hango kiyayyarsu a Idanun Safinah?
Shin dagaske Anim ba zai sake dawowa Rayuwar Feener ba?
Shin wacce nasara Dr Yake ganin yuwar samunsa?
Shin Safinah zata amince ta shayar da yaran?
Wani hali Masarautar jordan take ciki?
Tsakanin Ukshe da Abu Zarri waye zai hakura ɗan uwanshi ya mulke shi?
Adnan daga Banu Hussein yaje gurin Alexandra, na Banu Nazir dan niman Haɗinkai, shin da gaske Alexandra zai amince dashi.
Ya Makomar Sultan Ashraf A magarkama…
Yanzun muka zo rabin labari book one…
Intermission..
Oum Muwaddah..
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITER’S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Labarin daban yake da sauran._*
Page.٣١-31
Fita Ummi tayi ta barni da ciwon jiki, Umma ce tazo ta taimaka min na gyara jikina, sannan tayo min faɗa taje ƙuma ta ɗauko yaran a gurinsu Ummi. Ta bani so na shiga bawa Asma’ulHusna, kwalla na sauka a idanuna yana ɗiga a fiskar yarinyar, buɗe idanunta tayi yan kananu dasu. Wallahi sai naji wani irin tausayinsu ya cika min zuciya, ina ganin ta koshi dan ta zare bakinta, na ɗauke na kwantar da ita, sannan na dauki MaryamSajida. Itama na shiga bata nonon, kwanciyar rigingine nayi na kifa Sajida a kirjina dan tafi kankanta, Husna akan cikina dan tafi Sajida girma.
Shigowa Ummi taƴi taga duk muna barci, ɗaukar su tayi tabarni ni ɗaya. Ina barci,
***
Washi gari dan tun cikin dare da. A farka naga basu nan nasan Ummi tazo ta dauke su, dan haka ban bi tankasu ba. Na shiga bayi nayi wanka, ina fitowa na sai ga Ƙhalil. Turata nayi taje ta ɗauko min, kayana yar dogowar riga iya gwiwa, sai wandon legings dark blue, kasancewar atamfar holland ce, fari ne me ratsin dark blue, sai nake hadawa da Legings ɗin. Simple makeup nayi sannan na yane kaina da gyale kashka, dark blue me stone fari, haka ma takalmina farine me ratsin dark blue, kallon kaina nayi naga nayi wani fayau. Agogon ɗakin na kalla, sannan na lumshe idanuna na dauki agogon na makala, bayan na saka yan kunne na. Ban saka lips stick ba, na shiga kallon kaina naga nayi mugun kyau.
Komawa nayi gurin kulolin abinci na zauna kunun gyaɗa na garin tamba, shi na fara sha a hankali. Har na koshi buɗe ɗaya kular farfensun kan rago na sha kaɗan. Tunawa da kalaman Ummi na jiya ya dawo min ban san lokacin da na mike ba, na nufi cikin falournta. Ina shiga naji ana gaisawa, Dr ne zaune Yarinya ɗaya na kan cinyarshi Dudu yana dauke da ɗayar, wani boyayyen ajiyar zuciya na sauke, ganin yaran. Fitowa Nannah tayi Ita da me renonsu, Ghaniyu ya shigo zai ɗauki kayansu, cikin girmamawa ya gaishe ni. Hankali na baya gareshi sama sama na amsa mashi, sannan na kalle Ummi wacce fuskart ta nuna Alamar farin ciki a takaice zance kowa murna yake zasu tafi da yaran, sai Nannah ce ta kalle ni taga na sadar da kaina kasa, ina wasa da bazaar gyalena.
Takowa tayi har gabana. Sannan ta riko hannuna cikin murya me sanyi tace.
“Na tafi da yaran?”
D’ago idanuna nayi, kuka ya kwace min, girgiza mata kai nayi.
“Umminki ta miki dole ko? Idan baki sonsu zan tafi dasu na rene su cike da soyayyarki.”
Tuna girman Allah ya isa da Ummi tayi min, yasani cewa.
“Zan shayar dasu.”
“Anya Binti! Ba dole aka miki ba?” banda sokanci irin tawa sai na kalle Ummi, na sunkuyar da kaina nace.
“Ko ɗaya kawai zan shayar dasune”
“Idan kinsan zaki cutu na tafi da su, ke kuma Allah ya baki lafiya.”
Gyada kaina nayi tare da cewa “Amin”
“Binti zan koma gida, dukda Umminki tace min na tafi da Nanny da nakawo idan akwai matsala ki gaya min zanyi kokarin magancewa da Izinin Ubangiji, don Allah ƙarki ji haushin yaran dan basu da laifi.”
Gyaɗa kaina nayi, ina kallon Dr da Dudu suƙa rakata, ni kuwa kamar an dasani a gurin.
Sai da Ummin tace min.
“Hmm! Sakarya sokuwa kawai, kalleki kamar me hankali nan kuwa babu wanda yafiki shashanci.”
Tana gama faɗar haka tayi wuccewarta. Shiru nayi dan ina gani ta ɗauke yaran ta barni a tsaye, jan kafana nayi na bita ɗakin, na zauna a bakin gadon. Tana haɗa musu madara, cikin sanyi naja Sajida, na ɗaurata akan cinyata. Sannan na ja zip ɗin rigana wanda yake gefe na shiga bata nonon, tana kamawa sai da nayi tsigar jikina ya mike, dan tun da aka fara takaddama ban taɓa jin kome ba, sai yanzun da naso susha dan kaina, aikuwa ɗan mitsitsin bakin nan ya rike nipple ɗin, sai hakan ya matuƙar bani sha awa, ban san lokacin da na janyo wayar Batul dake kasan pillow na ɗauki hotonmu tana sha, duƙda da karama ce amma fa da kuzarinta, ina ganin ta koshi na cire nonon na bawa ƴar uwan, sam na manta da Ummi da take ɗaƙin, sai ɗauƙarsu hoto nake. Sai da tace
“Indai nono zaki basu toh ko ajiye wayar in kuma hoto xaki yi fita min a ɗaki.”
Ajiye wayar nayi na cigaba da basu abincinsu.
Suna koshi ta mika min wani kofi me ɗauke da tea, an zuba wani gari kamar kuka, na kafa kaina na shanyetass.
Har ina lashe bakina, cikin ɗaurewan fuska tace.
“Maganin bayamma ce, kuma ki kula da ciye ciye dan basuyi kwarin da hantarsu zata ɗauki kowani kwamacalarki.”
Tana gama faɗar haka tayi wuccewarta ban ɗaki.
Bayan dawowarsu Dudu ya gaya min dr na falour kamar bazan fita ba, na dai daure na fito.
Zama naƴi a kujeran da ke kallon nashi, nace.
“Ina kwana?”
A dakile ya amsa min
“Lafiya!”
Kamar wanda na masa dole, ganin zai min iyaye bai san ni miskilan. Nima a jinina yake, ga kuma wanda na koyo a gurin wancan gayen, banza nayi dashi sannan na mike zan koma ciki, sai da yagana kusan shigewa yace.
“Baki ji ba”
Waiwaye nayi na fara niman wacce yake nima, ban samu ba.
“Kana niman wata ce?”
Kauda kanshi yayi kamar baya falon yace.
“Kamar haka!”
Dawowa naƴi na tsaya abayan kujera nace.
“Hmm!ina da abinyi”
Kallona yaƴi sosai, a ranshi kuwa cewa yake.
*Na haɗu da miskila*
Kauda kaina naƴi na cigaba da kallon kofar falon, can yace.
“Ban ji daɗin abinda kikayiwa Mahaifiyar Baban twins ba.”
D’ame bakina nayi snnan na tura gaba, kura min ido yaƴi yana jin wani yanaƴi na daban,
“Shi yasa nake miki uzuri dan har yau kina fama da kuruciya.”
Wurga mishi harara nayi tare da murguda bakina nace.
“Ai ni sa’arsu Twins ne.”
“Nima naga alama, dan su ɗin ma sun fiki wayo. ”
Zaro ido nayi tare da sake bakina, mikewa tayi ya sakai har zai fita sai ga Anim, kamar an jehoshi.
“Wallahi baki isa ba! Indai ina numfashi sai na hanaki farin ciki, kuma zanga shegen da zai aureki.”
Buɗe baki nayi zan magana, na sun fita tare da Dr.
Taɓe bakina nayi, zan mike sai ga Ummi ta fito, sabida jin hayaniya.
“Ke da waye?”
“Wancan wawan man sun fita da Dr!”
“Wa kenan?”
“Anim matawalle!”
Na bata amsa a takaice,
“Shine yake fadan maganganu haka!.”
D’aga kafaɗa naƴi alamun oho shi yasani.
“Baki tunanin zai iya aikata kome? Ya kamata ki sami Abbanku da maganar a dakatar dashi fa.”
Cikin rashin son tsawaita maganar nace.
“Ummi kyale ɗan wahalan ni dai nasamu Allah ya rabani dasi yaje can ya karata.”
“Allah ya kyauta!” tace.
“Amin ya Allah”
Daga haka duk muƙa bar zance.
***
“Anim! Kana son na gayawa Feener gaskiyar abinda kake aikatawa ne?” Wani kallon banza wani kallon banza yayi Dr!
“Me kasani a kaina? Da har zaka min barazana”
“Eh toh idan na gaya mata
cewa, Anim kawali ne wanda yake da jirgin ruwa, inda ake baɗala ya kake tunani zata ɗaukeka.”
Zufa ne yake keto masa kamar wanda ake juyewa ruwan zafi.
“Toh wannan kenan idan kuma na gaƴa mata cewa. Kana shan magani fa? Toh ni fa bani da damuwa kawai ina son ka janye kudirinka akanta.”
“Dr kenan! Idan itama tana dashi fa?”
“Karka damu nasan bata dashi, domin shine last test ɗin da mata, karka ji kome gashi ka duba.”
Takaici ne ya kara kamashi cikin harzuka yace.
“Dr kana wasa da wuta!”
Gyara zama dr yayi a cikin motarshi yace.
“Shi nafi son nayi wasa dashi. Tun tasowata,”
“Toh tabbas wutan zai zama ajalinka.”
“Idan ya kashe ni shi gadin duniya zai, kana damun Safinah, baka taba tunanin idan wanda zak sota da gaskiya ya fusata ko tokarka baza a samu ba. Karka manta tana da Uba! Kani! Uwa Uba masoyi! Idan har ɓacin ran mutane uku nan ya ta azzara ya kake tunanin karka fusatani, dan Wallahi da bugu ɗaya zan saka a ɓatar min da labarinka, ba kai ba hatta Uban matanka wanda kuke kwaryan sama da na kasa, shima ba kyaleshi zanyi ba kafita harkanta.”
Gyaɗa kai yake kamar kadangare,
“Idan kuma nami fa?”
“Kana wasa da rayuwarce.”
Sunyi musayan kalamai masu zafi alwashin da Anim yaci bana wasa bane, fita Dr yayi daga motar.
***
Sbigowar Dr rayuwata ba sauki dan a cikin lokaci kalilan ya tafi da zuciyata, amma tsabar jan aji da miskilanci tare da ɗan taurin kai, naki amincewa dan Kullum Ummi sai tatuna min yarana da suke hannuna, gefe ɗaya ga Nannah da muke video call kullum itama, Ga wani irin soyayyar da yan gidanmu suke nunawa yarana.
***
Leke leke take murƴanta kasa kasa tace.
“Na maka alkawarin zan cika maka burinka nima yanzun hankalin Mahaifinsu ya koma kan shegun jikokinsa, har da Uwar yaran……”
Me kuma ake kullawa…😹
*Toh yanzun Muhawara zai ɓarke dan nasan ayan tambaya za a wurgawa Dambuje😎😏😒😂*
Oum Muwaddah….
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITER’S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Labarin daban yake da sauran Ina son ku sani duk cikin labaruna babu ƙamar wannan ba dan kome ba sai dan tsayinshi da faɗinsa Ina ga yaka mata ku nutsu ku bi labarin Idan nai kuskure ku an karar dani domin na gyara dan babu wanda yake cikakke Yanzun muna Book 1 ban gama ba shi yasa na zaɓi na baku Book one Kyauta sauran labarin zaku iya saya a saukakkakiyar Furashi! Masu ganin Feener ta wahaltu a barta haka toh ashe kuwa da sauran kallo, Waye zata aura? Shin meye makomarta? Masu ganin a sake Ashraf! Idan naga comments ɗinku dariya nake, idan kuka bi kome a sannu zan warware wasu kulin na book one kafin na shiga book 2 ku duba wasu abubuwan me kyau na labarin ku zubda marasa kyau na cikin labarin dukda dai duk abinda Marubuci zai saka sai ka samu akwai me kyau akwai mara kyau fatanmu muyi tarayya akan aikin Alkhairi👏_*
Page.٣٢-32
“Toh munafuka annamimiya! Allah ya toni asirinki, wato dake
Za a haɗa baki a cutar da gidana Nuratu me na tsare miki yau zaki bar min gidana Makirar banza makiran wofi” kwace wayar yayi yaga. Alhaji Anim.
“Em…em.. Alhaji ba wan…”
“Gafara can zaki kula min wani makircin toh anyi walkiya, kuma Wallahi kiƙa sake wani abu yasami Y’ata da jikokina, ni hukuncina me saukine, hukuncin da Nana Asma’u zata miki wallahi Allah kaɗai yasani.”
Yana gama faɗar haka ya juya tare da barin falonta, cizon yatsarta tayi tare da cima wani kudiri.
***
Rayuwarmu sai muce Alhamdulillah wani irin kulawa muke samu ta bangagori daban daban, Uwa uba Dr da ya zame min wani jigo na rayuwata, dan karfi da yaji ya zamewa su yan biyu Uba, musaman ya kawo min danshi Adil. Ya kwana biyu dake yaron yayi wayo. Kusan shekara huɗu. Da zai koma ni dasu Ummi muka mishi siyayya aka cika babban jaka,dake me ɗa wawa ne ganin Abinda mukayi kamar yayi hauka. Dan murna gani yake kamar na amshi tayin da yake, ni kuwa kallonshi nake kawai bawai me min bane, haka kurum nake ji ban masa adalci ba. Kuma dole duk wanda ya fito nima na yayi hakuri har sai na yaƴe yarana,
Daga ni har yaran jego ya amshemu, munyi bulbul. Dan ruwan none yana isansu sosai, sabida Ummi tasan abinda zanci ko nasha ruwan nono ya kawo. Gefe guda tana gyarani ta ciki da waje. Dukda na koma ɗakinta amma bana yawo kafana ba takalmi a cikin ɗakin, balle kuma na zauna babban mayafi ko hijab.
Ina samun kulawa gaskiƴa yadda ya dace, dan dudu ma ba abarshi abaya ba, Rigakafi da ake zuwa ni a gida ake zuwa min, abu guda da gaza fahimta shine anki barina ko sau ɗaya na fita koda kuwa bakin get ne.
***
Gyara zama Alhaji Kamil Matawalle yayi fuskanshi cike da zallar ɓacin rai. Kallon Abba da Dr sai kuma Dudu. Cikin cunku shashiyar murya yace.
“Ina me baku hakuri da abinda Anim yake muku, kuma Insha Allah zan tsawatar mishi.”
“Ba kome Alhaji! Mungode da ka sauraremu. Allah yasa mudace ”
“Nine da godiya.”
Mikewa sukayi sannan suka fita, a waje suka haɗu dashi, kowa ya ɗauke mishi wuta, shima ko a jikinshi ya shige.
……
Mikawa Ummi Sajida nayi na mike zan shiga ban ɗaki naji wayata na tsiwa. Ban ɗakin na shiga sannan na fito banbi takan wayar ba na ɗauki Husnah wacce take lashe bakinta, murmushi nayi cikin jin daɗi nace.
“Ummi! Aami ta cika niman rigima kalli yadda take lashe bakinta, kamar bata ci kome ba.”
Dariya tayi sannan tace.
“Aikinga ita Aani bata da rigimarta, ga hakuri.”
“Hmm! Allah yasa karsu ɗauki miskilanci wancan shashashan uba…”
D’im naji an kaiwa bakina duka, da sauri na ɗago kaina ina dafe bakina cikin rawan murya nace.
“Ummi bafa da Dr nake ba, wancan yaro.”
Sake buge min bakina tayi, na rike kaman zanyi kuka nace.
“Ummi sabida Ashraf.”
Wani dukan takawo min na kauce, cikin jin haushi tace.
“Uban yaranki kike kira da shashasha? Har da cewa yaron can ga shaidan yarontaka a hannunki, ima yarone sai ki girmama shi kodan yaranshi, balle.”
Shiru tayi kodan girman maganar da zai fito bakinta,
Ko yayya kika ga ɗ’a namiji ki girmama alamarinsa, da kike kiranshi yaro ai sa’an Abdul ne kuma kinga Abdul yana da mata me yasa baki taɓa kiran Abdul da Yaro ba sai Uban y’ay’anki! Bana son reni, ba mamaki Allah ya nuna miki iyakarki ne dan renashi da kike yi, ko ba haka ba?”
Abunka da sokuwa(😹) sai na shiga bata labarin artabun da mukayi, har lokacin da abin ya faru da kuma dawowa na gida.
Cikin tausayawa ta kalle ni sannan ta kalle yaran, tayi murmushi sannan tace.
“Lokacin da kika ki maganar auren, kowa yayi mamaki, amna da kika ce karatu zaki, sai naji sam ban amince da tafiyarki ba. Dukda haka na kasa dakatar dake, har Abbanku na gayawa bana son tafiyar dan jikina na bani babu alkhairi.”
Siraran kwalla suka sauko mata, gogesi tayi tare da sumbatar goshin takwaranta. Sannan tace.
“Da nayi yunkurin hanaki, ba mamaki rabonsu ya zama ajalina, tunda Allah ya nufa sai sun zo ɗin toh babu wanda ya isa dakatar da ikon Allah, naji daɗi da taimako kikayi. Allah yasa hakan ya zame miki izina da duk masu taurinkai irin naki. Sannan kafin Nannah ta tafi taga ya min Baban yaran yana can a saudiya a rufe.”
A razane na dago kaina inakallonta, jikina sai rawa yake. Nace,.
“Ummi! Me ya faru da Sultan ɗin? Kinsan sabida ni yayi murabus. Innalillahi”
Kuka ne ya kwace min, ba kome yasani kuka ba sai makomar yarana, ubansu a rufe.
Ta gaya min dalili rufe shi, bayan naci kuka na koshi nace.
“Zai rina! Dan mutum ne me tsananin ko in kula, ga wani miskilancin da yake ji dashi Ummi Wallahi maganar da kika ga Ashraf yayita sosai ki duba girman Alamarin, maganarshi bata wucce harrufa huɗu, itama ɗin dan ta zama dole ce. Ban taɓa ganin miskili irinshi ba, zan iya cewa idan da zaki matse shi bai sai meke faru a cikin masarautar ba, shi yasa suka kayi amfani da yardaddenshi ya zuba mishi makaman.”
“Allah ya kyauta! Wallahi na tausya mishi, yaro karami a cikin miyagu.”
“Hm! Ummi kenan wallahi na tausayawa matar da zata aureshi dan wallahi makiyanshi sunyi nisa kiyayyarsu akanshi babu sauki zasu iya zubda jinin kowa dan suga bayanshi, kuma abinda zan iya cewa nayi shine ankarar dashi kurakuranshi, da ace har yanzun yana sarkine da na tunatar dashi matan da suke a wulakance a cikin masarautarshi, Ummi kinsan abinda na fahimta ga mulki ga dukiya amma sun gaza samin nutsuwa dashi, gani suke kamar ya hanasu watayawa. Shi yasa sukayita kokarin sai sunga bayanshi, Allah yana kareshi. Akan shi naji na tsani mulki da sha aninta bana kaunar milki, Alhamdulillah ina cikin farin ciki da yaranshi matane kuma basu da gurbi a cikin masarautar da mulkin.”
“Toh Allah ya tsare! Amma abun da ɗaure kai.”
“Indai akan mulki da dukiya ce babu ɗaure kai dan kowa yasamu rana zai baza shanyarsa son ranshi.”
Munyi masa fatan ya cinye wa’adinsa, lafiya.
***
*SAUDI*
Mika mika mishi iPad ɗin Lawyer yayi cikin girmamawa, amsa yayi, ya kalli yaran cikin wani masifafan soyayyarsu.
“Har ta haihu??”
“Kamar yadda na gaya maka yarinyar ta fuskanci matsala a rayuwarta, sannan Fahad ya tabbatar min akwai mutane biyu da suke bibiyar rayuwarta, d’aya likitane. Babu sharri a tare dashi ɗaya kuma Fahad yayi bincike akanshi shi yasaceta, lokacin da cikin yaran. A halin yanzun bata fita sabida gudun kar ya kuma saceta.”
Dunkule hannunshi yayi idanunshi sunyi wani mugun ja ya kuma buɗesu, sannan yace.
“A tura masu tsaro”
“Yallaɓai! Ghaniy..”
Yadda ya ɗago kanshi sai da yabawa lawyer tsoro dan har jini jini yake ganin ya kwanta akasan idanunshi,
“Baiwata da Yarana! Kome ya faru kaine. Saura wata takwas na fito.”
Yana gama faɗar haka ya mike,
Har ya isa bakin kofa,
Cikin yaren Urdu yayi magana(Jama’a me Ashraf yake nufi da canza yare😎😒😏 Gulmar ma baza a barni nayo cikin salama ba)
Shi kuma Lawyer yace
“Toh! Yallaɓai”
Lawyer na komawa masaukinshi ya ciro laptop ɗin Ashraf ya fara aiki
***
Yau yarana watansu Uku, wanda yayi daidai ɓarin da matar dudu. Tayi, dukda Ummi ta hanani zuwa ji nayi hankalina ya tashi, dole na shirya yaran na saka jakar goyon baby na Sajida Wacce nake kira da Aanih, sai Husnah wacce nake kira da Aamih. Aanih a gaba Aamih a baya, sannan na fito tare da bawa Zakari daman ya kaimu asibitin kamar zaiyi kokari sai ya fasa muka fita,
Muna barin cikin gidanmu, wata jibgegiyar mota tana rufa mana, kamar zasu bi takanmu Zakari ya matsa musu yana mita, munzo traffic, sai ga wata mota tazo da mugun gudu, zata shege damu. Abin mamaki sai gani mukayi wata babbar tanka tabi ta kanta.
Ai ganin haka yasani fasa ihu, tare da kamkame jikina, karan jiniyar yan sanda da fire service,
Da sauri nasakai zan fita naga an shigo tare da ture Zakari gefe, akayi baya da motar, zanyi magana dani har zakari aka watsa mana hoda.
“Eh kome ya kammala karkashin jagorancin D28 Code 29 grps”
Iya abinda na iyaji kenan, sannan wani kafirin barci yayi awon gaba dani.
***
Fitowar Dr kenan daga Asibiti, zai shiga motarshi,, sai ji yayi an Duke keyarshi da abu, durkushewa yayi tare da rike keyar, sai ganin mutumin da ya duke shi, ya faɗi a kasa, ko shurawa. Sakamakon harbin da aka mishi ta keya har sai da yafito goshinsa, lumshe idanunshi yayi sannnan ya yanki jiki ya faɗi a gurin.
***
Buɗe idanuna nayi a hankali na sauke akan Ummi wacce nake hango ɓacin rai a idanunta, mikewa nayi da hanzari kaina yayi mugun sarawa dole na koma, ina lumshesu nace.
“Ummina! Yarana fa?”
Wani banzan kallo tayi min cikin matsanancin ɓacinrai tace.
“Dk cikin yarana, kece kika fita zakka. Ko yayya na saka doka sai kin rusa min ita, yanzun badan Allah ya kare ba, me kike tunanin zai faru. Wallahi Safinah ki fita a idanuna na rufe.”
“Don Allah Mariama ki rabu da ita haka, da muka samu duk suna raye barka zamu sannan mu godewa Allah, sai Dr shima ya farfaɗo Insha Allah, Ubangiji zai shiga tsakaninmu da duk me nufarmu da sharri, yanzun haka munyi magana da Hukumar yan sanda, kuma Allah zai bamu nasara.”
“Alhaji hankalina bai kwnta ba Ina ganin Safinah ta tattara tabi tafi Oman zatafi samun kariya a can.”
Shigowar Mataimakin IG, yasata yin shiru, gaisawa sannan yace.
“Alhaji Badar! Mun sami labarin kaida iyalinka tare da Dr Katagum ake hari, amma abin mamaki ba maharan bane suka turo mana sakon D28 Code 29Grp”
🏃🏃🏃🏃🏃Yacn kaina har ciwo yake,
_Domin cancare chakwalkwalin Chakwakiyar zaku iya sheke naira 150 a cikin asusun bankina kaitsaye domin dakon Book 2, idan kuma Katine zaku iya Kumdume katin Mtn na naira 200, Mu kafta saura pages 28 na karkare Book One ga wata Chakwakiyyar ta fashe kune min taku…Karku manta idan transifer ɗin kati Vtu 200 ne idan kuma kaitsaye ne zuwa asusuna na banki 150 ne sayan nagari mai da kuɗi gida Arashin araha ake barin tayi, koda kuɗinka sai da rabonka abin dace ne ɗan fari ya mutu idan kun shirya naji motsinku daga marubuciyarku wacce bata san raggonci ko lalace ba ƙullum suburbuɗeku take da labarai sinki sinki_
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
UMMU ALMUSTAPHA kina girmama Chakwakiyya,
MAMAN SADEEQ ta zauren Sainah ina jin daɗin comments ɗunki.
Fatan Alkhairi gareki Aunty Umma🍀
Uwar miji uwar kankanba, BabarTankwali me katon kai😂😹 Daga ke sai Aunty Umma kuka nuna min Sonso nagode……
Masu tambaya Number da Acc kuyi hakuri na shiga page.40 zan saka muku, ku fara booking👏 Ina muku sonsoriya😹
Page.٣٤-34
Murmushi nayi cikin jin wani farin ciki ya lulluɓe ni, na tura mishi.
*Don Allah ka nutsu idan kaje gaban shugaban kasa karka kwafsa*
Ina tura mishi na kashe wayar dan nasan yanzun zai addabi rayuwata da sako.
Komawa bakin gado nayi na zauna, na gaji da asibit gaskiya.
Cire hijab nayi na ninke, sannan, ina idarwa Ummi tana shigowa, kallonta nayi cikin zolaya nace.
“Ummina! Gaskiya munyi fushi ni su. Princess”
Taɓe bakinta tayi cikin ko in kula tace.
“Ai zamanku nake dasu, sai ku sani a koma inda na fito.”
Kunshe dariyana nayi sannan nace.
“Haba! Hajiya Ummina ai bai kai haka ba, tunda gashi har da sammako kikayi, dan ganinsu. Shi yasa nake jin kishinsu.”
“Sabida sun kwace miki fadarki ko?”
Naji muryan shi, kallonshi nayi tare da masa magana da ido, baka shiga meeting ɗin ba.
Kallon Ummi yayi ita kan hankalinta nagun ajiye min abin karyawa,
Gefen kirjinshi ya zana da yatsar hannunshi, sai ya kama tare da ɓata fuska, sannan ya watsa yatsunsa, ban san lokacin da nace.
“Ta fashe!!”
A razane Ummi ta juyo tace.
“Wacece?”
“Dr mana!”
Ina juyawa babu shi babu alamarshi, itama kallon kofar tayi, taga bakowa.
Dafe goshina naƴi nace.
“Baki ganshi ba anan har yace min su Aanih sun kwace min Fada”
Kallon Mahaukaciya tayi min, share zance nayi na cigaba da kallon kofar.
Kunna wayata nayi na ajiyeta a kasar pillow. Abin karyawa da Ummi ta kawo min na ɗauka zan ci sai na tuna banyi brush ba. Kawai na shiga ban ɗaki zan wanke bakina, da fari ina buɗe panpo ruwa ya zuba na fara wanke bakina, kamar ance kalli madubi. Sai naga yayi dishi dishi kamar an buɗe ruwan zafi gogewa, me zangani Anim ne bakinshi na ɗigar da jini. Ya ka turo hannunshi da mugun zafin nama zai shake wuyata.
Addu’ar niman kariya daga miƴagu da shaiɗanu nayi da mugun karfi har sai da madubin ya tarwarse. Shi kuma na nemishi na rasa, burushin da banyi ba knn, na fito bakina duk kumfa.
“Ummi!!!”
Na kirata babu ita babu dalilinta babu kuma abincin da takawo min, kara wayata tayi naje nasaka hannu zan ɗauka, sai naji kamar a cikin ruwa na tsoma hannuna, ina zarowa jini ne.
A tsorace na cigaba da addu’a take jinin ya ɓace, Ummina nagani cikin rawan jiki nace.
“Ummina!!!”
“Ina kika shiga ne! Gamu nan zuwa da abin karyawa.”
Wasu siraran hawaye ne ya zubo min nace.
“Ummina akwai matsala!!”
“Name?”
“Sai kunzo ”
***
A hanyarsu ta zuwa suka haɗu da wasu mabarata har zasu wucce.
“Zakari ɗan tsaya na bada sadaka.”
Tsayawa yaƴi sannan ya dawo da motar baya, duba jakar tayi taga babu karamar chanji. Sai dubu ɗaya cirowa tayi ta mika musu sadakar, Dukkansu makafine, sai da ta buɗe kofar ta saka musu a kwanon.
“Allah ya bada lada, ya kare miki gabanki da bayanki, ya kuma maidawa masharratan sharrinsu.”
“Amin!” tace Zakari yaja motar, dan shi yaji sauki baya tare da wata damuwa. Nima sabida Aanih muke asibitin.
Suna barin gurin makafin nan babban cikinsu ya kallesu yace.
“Zuciyar Maryama da yaranta me kyau ne, yanzun zamu biya bashin da mukaci.”
“Kawu ina Tanimu Dari!”
“Yana saudiya ”
Shiru sukayi can suka ɓace.
***
Ina zaune duk tsoro ya gama cinye ni, murɗa kofar ɗakin akayi. Ummi ce da Zakari suka shigo kallon tsoro nake masu.
“Lafiya Safinah?”
A hankali na isa gabanta, kura mata ido nayi cikin kuka nace.
“Ummina!!”
Kallona tayi zatayi magana, damshi naji akan hancina, na share a hankali, jini ne yake ɗigowa daga hancina, zan buɗi baki nayi magana naji abu ya cika min wuyana zuwa bakina, kasa nayi da kaina sai ga gudar jini ya faɗo. Mikewa nayi.
Lokaci guda duƙ wani kafar jikina zubda jini yake, mikewa nayi jiri ya kwashe, na zube a jikinta.
…… Suna meeting wata Nurse ta shiga, dama hankalinshi yana kaina.
‘Dr Zk! akwai matsala fa, matar nan fa tana zubda jini.”
Mikewa sukayi shida Dudu, suka fito har suna bangaje junarsu.
A tare suka shigo ɗakin, kafin Dudu ya ɗauke ni, har ya ɗauke ni yayi waje dani, har lokacin zubda jini nake. Dakin gobe da nisa suka shiga dani, aka fara kokarin tsayar da jinin amna abu yaci tura.
Sunfi awa biyu akaina babu wani labari, dafe goshi Dr yayi. Sannan suka fito,
Kafin wani lokaci yan uwana duk sun shiga damuwa,
Zuba min ido yayi zuciyarshi ba daɗi, zama yayi ya sarkafe hannunmu, ya kai gefe fuskanshi. D’aya hannunshi yana shafa kaina,
“Safinatu! Na miki alkawarin zama dake a kowani hali. Kuma zan tabbatar miki.”
A hankali ya mai da min hannuna, sannan ya fita.
……..
Cikin fararen kaya suka bayyana a cikin ɗakin.
“Kawu wannan wani irin sihirine?”
“Eh toh Iqibal! Wannan mugun sihirine da mugaye a cikin bil Adam suke aikatawa,”
Shiru wanda aka kira Iqibal yayi sannan yace.
“Kawu taya za a lalata sihirin?”
“Allah zai kawo yadda za a warware.”
***
Duba agogon Hannunshi yayi ya ga lokacin na kure mishi da sauri ya fita, ya kalle Dudu.
“Kyari bari naje Villa na dawo, daga nan zan wucce gidan gun Ammahna ko zata taimaka tazo taga halin da Safinatu take ciki.”
Gƴaɗa musu kai yayi.
……..
Tafiya yake da mugun gudu, taka birki yayi a tsorace ya fito sakamakon mahaukaciyar da ta shige gabanshi.
Tana dariya sosai tace.
“Ka koma bazaka ga Shugaban kasa ba, kaje mayanka acan aka tsuma yar tsanar.”
Kaucewa yaƴi ya barta tana ta , haukarta. San baya tunanin maganarta gaskiya ne,
Kiranshi shugaban kasa yayi ya gaya mishi, zai shiga meeting.
Bai damu ba ya koma gidanu, yana shiga, katon Mansion ɗinsu ma aikata suka shiga gaida shi, bai bi takansu bai yi ba.
Ya shiga gidan a gigice yana kwala mata kira..
“Ammahna!!!”
Wata farar dattijuwa ce ta fito hannunta rikeda farin casbi. D’aya hannunta rike da sanda, murmushi tayi ciki dattako tace.
“Son! Lafiya!”
“Ammahna! Tana cikin wani hali.”
Murmushi takara a karo na biyu tace.
“Safinatu ko?”
Gyada kanshi yayi, addu’o’i ta bashi sannan tace.
“Kaje ɗakin akwai Shafin shaiɗanu ka ɗauko a shafa mata shima yana taimakawa.”
Ta kuma gaya mishi yadda zasu kula dani,
***
Cikin kwana biyu rak na koma abar tausayi, dukda ana addu’a. Da maganin gida, karshe dai aka dawo dani gida. Inda na cigaba jinya.
Ganin yadda nake wari ya ɗagawa kowa hankali, musaman Dr.
……… Ya gama duba wata mara lafiya ya dawo ɗakin ya kwantar da kanshi akan kujera, wani barci me mugun karfi yaƴi gaba dashi.
“Tun ranar da ciwon ya faru muka ce maka kaje mayanka, ka duba inda jini ke zuba zaka samu anan suka lankaya yar tsanan amma kayi biris sabida mahaukaciya ce, toh maza ka ɗauki ɗan uwanta kuje can Insha Allah rabb zaku ga waraka.”
Firgit yayi tare da mikewa, ya fita daga ɗakin, ofishinsu Dudu ya nufa, yana zuwa yace.
“Kyari zo muje.”
……. Da sauri suka fita, a mota ɗaya, suna barin garin abuja motarsu na lalacewa, dole suka ajiye motar suka sake niman shatar taxi.
Nan ma dai sai da suka fara tafiya, sannan motar itama ta lalace. Dakyar da ikon Allah suka isa mayankar, nan ma sun sha wuya kafin suƙa, sami yar babyn, suka fidda shi, ba tare da wata wata ba. Suka xuba mata fetir tare da wurga mata ashana dan akwai wasu mahauta a gurin.
Suna gamawa suka jiyo abinsu.
***
Buɗe idanuna nayi a gajiye. Na kalle Ummi da take rike da casbi.
A hankali nace.
“Ummina! Ina yarana?”
“Alhamdulillah! Safinatu, sannu bari na kawo miki su.”
Dauko min yaran tayi ta sakaminsu kusadani, sannan tafita can sai gata ta dawo ɗauke da magani.
Tallafe ni tayi taban nasha, kiran Abdul tayi ta gaya mishi, sai gasu tare da Dr.
Wanka Ummi tayi min sannan na fito nasa kayana, zama nayi, a ɗakin sabida bani da karfi.
***
“Hmm! Bansan yadda akaƴi suka sami makarin ba, amma tabbas ta sami lafiya sosai. Dan yanzun na dubata sai cin abinci take”
Tsawa ya buga mata, tare da cewa.
“Bashi na tambayeki ba, taya kome yake lalacewa? Sannan waye yake kareta?”
A gigice Mamie tace.
“Yallaɓai!Allah mana. Don Allah ka kyaleni karka sakani a damuwa.”
Kashe kiran yayi tabi wayar da kallo kamar doluwa.
***
*SAUDI*
Zama yaƴi ya ɗaura ɗaya akan ɗaya, hannunshi duk biyu ya jinginasu akan kujeran, ɗame bakinshi yayi baƴan lauyan ya gama masa bayani.
Lumshe idanunshi yayi, sannan yace.
“Ya yarana suke?”
“Ai yallaɓai! Duk lafiyansu lau dama Asma’uHusna ce Uwar ta kwanta akanta, Amma jikinta da sauki”
Buɗe idanunshi yayi, sannan yace.
“Da fatan babu matsala!”
“Eh toh babu kenan amma Fahad ya tabbatar min Uwar yaran ba lafiya.”
Gyaɗa kanshi yayi sannan yace.
“Meke faruwa A jordan?”
“Gaskiya Yallaɓai iyakata Nigeria ka bani damar na tura wasu, Wallahi bani da masaniya da abinda ke faru.”
“Yayi kyau.”
Yana gama faɗar haka ya mike, tare da barin ɗakin ziyaran ƴa koma cikin gidan.
***
*Jordan*
Alamura sun tsananta sosai, dan har takai ana nunawa juna yatsa tsakanin Ukshe da Abu. Dakyar Ammar da Uzaif suka shawo kansu.
Shi Abu Zarri yace bazai bi shugabanci Ukshe ba dan babu Allah a cikin mulkinsa. Shima kuna Ukshe yace bazai bi Abu Zarri ba, kafin lokaci kalilan sun hautsinawa juna lissafi dan kamar zasu kashe junan,
Ana haka Marhum ya shigo naaarautar domin farautar duk wanda yaje cewa shi zai zama sarki, da duƙ me hannu a kamashi sai da ya kashe manyan cikin masarautar har mutane biyar.
A sannu zubda jini yazama abin ado a cikin Birnin Amman, domin an samu rabuwar kai wasu nacewa A baiwa Ukshe wasu na cewa Abu Zarri.
Ga kuma Marhum da yake kokarin ganin bayan kowa ya amshe mulkin.
***
Zaune muke ya sani a gaba, sai kunnani yake da tsokana naki kula shi.
“Insha Allah! Idan na kama mutum sai na cinye bakin tsiwar nan, wanda yake kin magana.”
Dago idanuna nayi cikin nutsuwa nace.
“Amma baka da lafiya”.
“Haka kowa ke faɗa! Wai tunda na haɗu dake na hau bishiyar kacen sonki.”
“Kasan me kace kuwa.?”
Na tambayeshi,
“Eh nasani mana! Gaskiya na fada ina sonki! Amma kinki ki bani amsa sai guduna kike Why Safinah ko na miki tsofa ne. Ni ba kamar Anim sa Babansu Aanih ba. Ni na girma ko ba haka ba? ”
Kauda kaina nayi na cigaba da kallon gefe nace.
“Babu ruwan so da tsufa ko na kasa, kawai abinda nasani……..
Oum Muwaddah……. Kuyi hakuri na isa Page.40 zan saka muku yadda zakuyi payment ɗin…..Nagode
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAƘA WRITER’S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Labarin daban yake da sauran._*
_Kun gane Nufina kuwa? Book One free ne daga page 1 to 60, Book 2 zuwa inda zan tsaya na kuɗine wai ina gaya muku ne ku shirya tsaf_😹
Page.٣٣-33
Zaro idanu nayi waje, tare da kifkifitawa, nace.
“Ummi ina yarana?”
Buɗe min bakina tayi cike da jin haushi matar da tun da tahaifeni ban taɓa jin tayi zagi koda Qaniyarki bata taɓa faɗa a gabana, sai yau wai itace ke ce min.
“Suna gidan Qaniyarki”
Zaro idanu mukayi hatta Abba sai da ya kalleta anya ita kuwa.
“Ummi zagi kikayi fa!” inji Khalil, juyawa tayi a fusace tace.
“Qaniyarka zan fasa muku kai, haba jama’a ke ɗaya kin addabi rayuwar kowa, Haba don Allah Safinah anya kina son ganin dai-dai a rayuwarki kuwa, ke ko damuwa da rayuwar yaranki bakyayi, toh idan Sajidah ta mutu sai ki san yaren da zaki gaya Ubanta da Kakarta, ina ga baki san ina kika saka kanki ba.”
Mikewa nayi tare da dirowa a gadon, jikina na rawa. Fita nayi da gudu, ni kaina bansan inda zani ba, dan su Abba sun biyo ni da sauri mukayi karo da Dudu, rike hannuna yayi na fashe da kuka, tare da faɗawa jikinshi nace.
“Dudu! Aanih! zasu kashe min Yarinya bansan me zancewa Abie ɗinsu ba.”
Riko hannun yayi muka nufi ɗakin da aka kwantar dasu, tana kwance tare sa yar uwanta, ita tana barcin wahala. Wani mahaukacin soyayyarsu ce ta daki zuciyata na kura mata ido, sai yanzun na lura da bata kai Aamih haske ba, tana a haske amma me duh. Dan idan ka cika saka ido zaka ga fatarta har wani sheki yake, yayinda Aanih kuma tafita haske sosai dan itace Ashraf a fuska, amma a zahiri Aanih ta fita hakuri.
Sumbatar kumatunta nayi ruwan kwalla ya sauka a fuskarta motsi tayi, tare da sake yar kara irinta wahala. Kamar ance d’ago kai, harɗe hannunshi yayi a kirji. Kanshi yasha bandeji murmushi ya sake min. Na kauda kaina tare da mai dasu kan yaran, haka kawai nake jin wani abu na fisgana, wani irin yanayi nake ji akanshi.
A sannu nasake satar kallonshi, gira ya d’age min tare da kashe min ido, kunya ya bani na kauda kaina. Ina murmushi ƙasa ƙasa,
Har inda nake ya iso yana kallon yadda nake shafa kan Aanih, ina kuma jin idanunshi na yawo a jikina, lokaci guda ya saukar mun da mugun kunyarshi tare da ganin tulin girmanshi da ya cika min ido.
Hannunshi yakai zai ɗauki Aamih, hannunmu ya haɗu da juna. D’ago ƙai mukayi a tare muka kurawa juna ido, janye idanuna nayi daga gare, mai dashi nayi kan Aanih da take barci.
“Ina jin bakon yanayi a tsayuwarmu na yau idan kika bani dama.”
Gyara kwanciyar yarinyar nayi na raɓe gefenshi zan bar d’akin, sai ji nayi ya riko hannuna. Tsigar jikina ne ya mike sabida ban taɓa shiga irin wannan yanayin ba sai yau. Duk abinda Anim yayi wasu abubuwa a tare dani ban tab’a jin kome a game dasu ba, kai ko Ashraf da shi na fara sani a duniyata ban ji kome ba, ina jin kewarshi na kata’i sabida halayarshi da suka min, ina son halayarshi fiye da kome.
Dawo dani yayi gabanshi, ya zuba min ido cikin sanyin murya yace.
“Zan iya hakuri har ki yayyesu, amma bazan jure shirunki ba. Am 45 now na rabu da Aieesha, pls ki taimaki gwauro irina ki bashi gurbin.”
Dakyar na had’iye yawun bakina cikin inda inda nace.
“Abban Adil! Ina son fita.”
“Zama da Sultan ya maida ki miskila irinsa ko? Ga sona a cikin idanunki but kina pretender kamar baki jin kome a kaina, ki bani dama na karshe rayuwata dake.”
Ga baki ɗaya na gaza furta kome domin bansan wani irin yanaƴi nake ji ba, sake hannuna yayi sannan ya kwantar da jaririyar, addu’a yayi musu. Sannan yasani a gaba har bakin kofar da aka kwantar dani.
“Safinatu!!! Zan baki dama daga nan har ki yaye yaranki, don Allah karki cutar da zuciyata.”
Jikina ne yayi mugun sanyi, sunkuyar da kaina nayi ina wasa da farcena wanda ban jima da musu lalle ba.
“Ina son mace me lalle! Haka yana kara mata martaba da kima.”
Takowa yayi har gabana, dukda mutanen da suke kaiwa da komowa, bai hanashi sauke nauyin dake cikin zuciyarshi ba.
“Safinatu! Ki bani amanar kanki da rayuwarki, Insha Allah bazan baki kunya ba.”
*Wayyo Allah na ashe haka mace take ji idan tasame me sonta ji nake nafi kowacce mace sa’a.*
Ɗ’agowa naƴi da niyyar ce wani abu ina haɗ’a ido dashi sai naji bazan iya ba, haka nayita motsa bakina. Karshe na juya da sauri na shige ɗakin, na rufe kofar tare da sauke wata ajiyar zuciya.
“Wannan mutumin zai kashe ni da salonshi, mutum sai kace majnun”
“Didi ke kuma Lailah, eyye Our didi falling in love”
Ware idanu nayi dan ban tsamaci yan butan uwa suna cikin ɗakin ba, take na bone fuska.
“Toh Didi! Idan babansu Aamih yazo ya zaki yi?” inji Batul,
Wani tsuke fuska nayi, cikin ɓacin rai nace.
“Kinga nayi miki kalar matar yaro? Ai Ashraf saike Batul ni nafi karfin Yaro karami.”
Bakinsu a sake suke kallona, cike da mamaki, fahimtar abinda yake yawo a zuciyarsu ya sani fara kame kame, Ummi tana kallonmu bata ce cikanku ba, sai dai da alamu bata ji daɗin furucina ba.
Dukda na jefa musu kokwanto haka suka share batun amma tabbas suna nazartan Alamarin fiye da tunanina, karshe ina zaune bayan tafiyarsu Ummi tare da jagorancin yan sanda. Karshe gidanmu sai da aka saka mana yan sanda.
“Didi!” d’ago ido nayi na kalleta, dake ina chatt da Dr.
“Dama da naji kince Abie ɗinsu Aanih Yarone sai ni! Am sorry da tambayar da zan miki, kuma wallahi ba cin fuska bane, kince yaro taya.”
Tsuru tsuru tayi tana kallona jikinta na ɓari.
Saukowa nayi daga gadon na mikar da ita, sannan na bata labarin abinda ya faru.
Kuka sosai tayu tare da bani hakuri, tace.
“Bai kyauta ba”
“Eh amna kaddararmu”
Na gaya mata kamar ance ɗago kaina Dr na gani, fuskarshi a haɗe. Shigowa yayi sai da yazo kusadani ya hura min iskar bakinshi, tare da sake murmushi.
“Kinga fuakarki kuwa! Haka kike da jin tsoro? Gwara ki zama jaruma.”
Murguɗa bakina naƴi cikin jin haushi naki ma cewa kome, ina hararanshi.
Hirarsu suka yi shi da Batul, sun jima kafin ya fita, ko minti biyu bai yi ba sai ga sakonshi ya shigo min har da fuskar mage.
*Am so sorry Angel😿*
*Toh meye kuma?😒*
*Ina son wannan kallon da alamu an tura that cute lips ɗinan*
Rike bakina nayi cike da mamaki ina ware idona akan screen ɗin na tura mishi tambaya nayi.
*Taya kasan na tura bakina?😙”
*Tun daga ranar da Kyari ya kawo ki a sume bayan kin same matsalan nan, bayan mu miki allura. Naga alamun Yar Ummi sakaliya ce*
Cizon lips ɗina nayi na kashe data.
Sai ga kiranshi ya shigo min, kin ɗauka nayi karshe da ya dameni nasaka mishi busy.
Ban kuma bin takan wayar ba, sai da yamma zanje bawa yaran nono ina shiga, na same shi yana riƙe da Aamih ta dawp normal sai zare idanu take, nuna min gurin zama. Cikin nutsuwa na zauna sannan ya mika min Babyn kallon agogon da yake ɗaure a tsintsinyar hannunshi yaƴi sannan ya fita.
Can da ta koma barci sai gashi ya shigo amsarta yayi ya kwantar da ita sannan ya ɗaura min Aanil. Itama fita yayi ina maida nonon cikin rigata yana shigowa, kwantar da ita yayi sannan yaja kujera ya sani a gaba, yana kallona kamar wanda yasami majigi. Ni kuwa kunya yake bani naga babba kamanshi yasani a gaba yana min rawan kai.
“Toh kice wani abu mana!”
Lashe lips ɗina nayi a hankali sannan nad’ago a hankali na saci kallonshi, aikuwa muka haɗa ido da sauri na kauda kai, cikin zolaya yace.
“Allah duk ranar da na kama mutum sai na cire ƙunyar nan na barshi sintir”
Mikewa naƴi na fita da sauri, ya biyo bayana yana dariya, manyan da kananun likitoti sai mamakin Dr Zaki suke, su abin dariya yake basu, wai lokack guda ya zama madness in love.
Kuma karku manta nifa har yanzun na kasa cewa ga Ajin da nasaka Dr ba, amma ina jinshi a cikin raina da zuciyata ƙo motsi yayi ina jinshi in my Body, balle kuma yayi magana sai naji kamar nafi ko wacce mace Sa’a. Da farko dai Dr ba baki bane dan shi yafini ma haske, yanayinshi sak da irin mutane Madaras, idan yana abu zaka rantse kace Shivarao ne, Babban jarumin andraprudashe, na kasan India, dukda ya, yana da tsari da zubin halittan manyan maza, mutum ne mai yawan gargasa, dan ko hannunsh zaka ga haka, balle kanshi dan a yanda na fahimce irinshi ba mamaki after 2weeks yake askin gashin kanshi.
Idan zance a cikin zaratan maza waye gwanina zan iya rufe idanu nace Dr, dan takowani lungu ya iya saita soyayya meyin lugulugu da zuciyar D’aya mace. Balle ni kuma da nake uwarsu wance, A iyakan rayuwata wannan karone na fara son ɗa namiji bawai shirmen da nayi tayi aka Anim, Idan da Dr na samu a farko zaiyi wuya na, tsallaka na bar aurenshi, sabida irin mafarkin danake yau gashi na same shi, mijin da zai girmama Alamarina. Na sameshi, ya fahimce ni,kuma ya fahimci kaddarara, kuma tsaf yake ya zauna dani, gaskiya ina cikin farin ciki.
Haka mukayita shirrita dan kana ganinmu kasan sabin shigane a love, dan mun kasa ɓoyewa a gaban kowa.
***
Washi gari ina zaune akan abin sallah, inata jiran kiranshi dan ya sabar min da haka,
Tura mishi sako zanyi sai ga nashi sakon ya turo min.
*Ina da Meeting kuma zanje ganin shugaban kasa sabida nike duba lafiyanshi By Angel*
Sai naji ba daɗi, tura mishi sakon fatan alkhairi nayi nace.
*Ok Baby! Allah ya bada sa’a! Ubangiji ya kare min Honey.”
Sai da sakon ya tafi naji kunya ta kamani.
*Alhamdulillah ni kika kira da Baby ina son sunan kibar honeynan Baby ma ya isa*
*_Bawai ku turo min kuɗin ku nake nufi ba, na gaya muku ne kafin na gama Book One Free ne, bana son sai na gama nace muku Two na kuɗine tsaf wasu zasu zageni akan haka, kuma Am Sure that akan na maida na kuɗi dayawanku zasu daina Comments da Voting sai dai nasan haka bazai sani kasa a gwiwa ba._*
Oum Muwaddah…
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
*Alhamdulillah Barka da zuwa bakuwar duniya Ku tayamu Murna Malamata ta sauka An sani baby girl Um Nass marubciyar Yarda Da kai Allah ya raya babƴ ya kuma baki lafiyar shayarwa*
Rubutuna dai dai nake jera number idan baki ga wani number ba ki tambayar……
Page.٣٥-35
“Sannan da kake maganar kodan ka manyanta ne, ni banga haka ba. Dan ni a mutum nagari nake kallonka, rashin amsa maka kuwa ba kome bane sai ina tsoron kar na faɗa sonka daga karshe ka bani wahala ne, na haɗaƙa da Allah idan kazo da niyyar cutar dani kaje nagode, karka gasa min ruhina da zuciyata.”
Tasowa yayi yazo gaba ya zauna kusadani har ina iya jiyo kamshin turaranshi, lumshe idanuna nayi. Sannan na sake ajiyar zuciya,
“Ina son haka! Kin amshe ni kenan”
Ware idanuna nayi tare da satar kallonshi, shima ni yake ƙallo.
“Idan kika kuma satar kallona, sai na kai karanki gun Ummi ko Ammahna.”
Har da murguɗa min baki,(😏)
Buɗe bakina nayi ina kallonshi hura min iskar bakinshi yayi, kamshi Cool fresh
Doki hancina, sunkyar da kaina nayi ina wasa da hannuna.
“Baki ce kome ba Safinah?”
Na kasa d’aga ido na kalle shi, sabida kwarjininsa, tare da girmanshi da suka cika min ido,
Sai wasa nake da yatsina, kallon yadda nake yatsun ya ɗago tare da kallon fuskana da yake sunkuye yace.
“Baki ce min kome ba, ga lokaci na tafiya.”
Dakyar na haɗiye yawun bakina nace.
“Na amince.”
Ina faɗar haka na tashi da sauri zan bar falon cikin d’aga murya yadda zanji yace.
“Tafiyar tafi kome jan hankali, musaman yadda zubin halittar yake”
Da sauri na shige cikin ina dariya, shi kuma ya mike yana darawa.
***
A hankali na warware, dan haka Abba da kanshi ya nima min visa zuwa Oman. Amma naki sabida nasan nisa da Dr, har Ammahnshi ya kawo min ita. Naji daɗin da tazo dan haka nayita hidima da ita, kin kawo mata Yan biyu nayi muna cikin hira sai ga Mamie matar da sai nayi sama da sati uku ban kalleta ba itace yau har cikin falonmu, dake ta ɗauko dakon min tijara sai gata tazo.
“Feener ina shegun yaranki masu shegen kukan tsiyar nan?”
Ji nayi kamar kasa ta tsaga. Na shige ciki na huta da bakin ciki,
“Subhanallah”
Ammah tace tare da kallon yadda na sunkuyar da kaina ƙasa, janye idanunta tayi a ƙaina ta maida kan Mamie tace.
“Baiwar Allah! Yanzun ke zaki ji daɗi a kalle idanunki a kira d’iyoyinki da shegu.”
“Hajiya ai yaran gaba da fatiha ne, dan haka ba wani abin kunya bane dan nakirasu da shegu tunda bamu san Ubanso ba, garin kwadayi akwaso yan daka kuka. Batun a kira yarana da shegu bata taso ba, dan ban taba barin iyayena na tafi yawon karuwanci ba, kuma Ubanau kaɗai nasani ba wasu karti ba, idan zaki cewa Dr ya hakura toh idan kuma bazaki ce masa ba cutar zamani tayi ajalinsa.”
Tana gama faɗar haka tafita tabarmu a falon, jikina yayi sanyi hawaye ke jika min hijab ɗin dake jikina, jikina na rawa har mun zata tafi sai gata ta dawo tace.
“Hajiya! Kice ta kawo miki su kiga jinin masu fararan kunne sai ki tabbatar da abinda na gaya miki, hmm.”
“Nuratu!!!” Ummi ta bugata tsawa, cikin tsananin ɓacin rai tace.
“Fitar min a gida kafin na mugun baki mamaki.”
Da sauri ta fita tana cewa.
“Maryam uwar karuwa kakar shegu.”
Tashi na shige ɗakina da gudu na rufe kofar tare da sake kuka me mugun karfi, ina buga kaina da karfi a jikin bango.
“Safinah buɗe mana kofar karki kashe kanki,” Inji Ummi, itama Zuciyarta tayi rauni. Ammah itama tazo tayita magana amma fir naki bari, ga yaran suma sun tashi sai kuka suke.
Naki kulasu. Kafin wani lokaci har gidanmu ya cika, da yan uwana har da Abba, ga Dr da Ammah takirashi.
Dudu yayi na buɗe kofar naki ina kuka, tare da cewa.
“Ku kyale ni na mutum da bakin ciki.”
“Toh ai matsalar bakiwa AbdulHameed alkawarin zaki kashe kanki ba, hanya mafi sauki ki buɗe kofar nazo miki da allura sai ki cika kiwa kanki.”
Kuka ne ya kwace min me tsuma rai, na buɗe kofar a hankali.
Na tsaya a gabanshi. Shigowa yayi ya ɗauki Aanih ya mikawa Dudu, sannan ya dauki Aamih ya mikawa Ummi sannan ta tura kofar, ya jingina da jikin kofar harɗe hannunshi yaƴi a kirjinsa, yace.
“Zo nan Beauty!!”
Dakyar na d’aga kafana na isa gareshi ina shashekar kuka, hannunsa yasa ya d’ago haɓɓana yace.
“Wani ya taɓa ce miki kina da kyau kuwa! Ban taɓa ganin wacce kuka ke mata kyau kamat ke ba.”
Janye hannunshi yayi daga haɓɓana ya cusa cikin aljuhun wandonshi, yace.
“Dukda na shaku da Ammahna, ban taɓa tuɓ kararta da maganar ina son mace ba, sabida girma da kunyarta, kuma sai akayi dace niɗin bantaɓa samun mace ba, dan ko Balkisu hadamu akayi, amma haɗuwana dake”
Kara kusantoni yayi yadda nake iya jin saukar numfashinsa, “d’ago ki kalleni”
D’ago fuskana nayi ina zubda kwalla.
“Ina haɗuwa dake naji bana tsoron kome, da naji kome akanki naji zan iya baki dukkan nutsuwata, ko kwana biyu na gaza yi da kamuwa DA soyayyarki na faɗawa Ammanha, kinsan me yasa, sabida a haɗuwa dake nasan me ake kira da jajjircewa, da tsayawa akan kaifi ɗaya, koda na faɗawa Ammahna kaddararki murmushi tayi tace min.
“Idan tayi maka kana sonta ni yar rakiya ce tare da Addu’a, bazan taɓa hanaka farin cikinka ba, batun Yara musulunci ita yabawa, amma idan Ubansu yana ganin zai rukesu ba damuwa da nan dacan duk ɗaya ne.”
Kinji abinda tace min tare da bani goyan baya Safinah! Nifa ba kome nake so a tare dake ba, kece muradina, kuma mafarkina ce ke! Don Allah a duk lokacin da wani ya kuntatta miki ki tuna da mutanen da zasuyi kuka da kukanki, ki tunada mutanen da zasuyi dariya da dariyarki, a wannan zamanin Y’an mata dubu nawa suke sayarda kimansu dan abu kalilan amma ke rabo da kuma sadaukarwa, tare da kariyar Ubangiji ya rushe aurenki da wancan kawalin, kuma yarinya da yanzun ya cuceki ya haɗaki da damuwa, dan wallahi bayi da lafiya.”
Zaro idanu nayi ina kallonshi alamun mamaki da tsoro, dariya yasaka har da dafe cikinsa yace.
“Matsoraciya! Daga jin batun ciwo ta kama zare kananun eyes ɗinta.”
“Na gaya miki gaskiya, muje ki kisamu su Ammah zata koma gida.”
Haka ya shiga gaba ina binshi a baya, har falon.
“Ya Dr me ka gayawa Didi! Ita da take sha’awar zama shekakkiya sai gashi ka dawo mana da ita, me ka gaya mata.”
“Baby kace ta bari.” na faɗa a shagwaɓe.
“Batul Amor bata son ki rabu da ita, ko ana dole ne ta fasa sheke kanta sai ya zama abin tuhuma. Kinga kowa ya haɗiye tambayar da take bakinshi in ba haka ba zan cika iska a cikin allura nawa mutum kai tsaye yake tafiya ga zuciya. Lokaci guda sai dai aga mutum ya yanki jiki ya faɗi. Sai mutuwa.”
Dariya suka kowa ya saka, Abba ya kalle shi cikin mutuntawa yace.
“Toh Dr! Nagode.”
Kallona yayi yasa hannunshi a fuskarshi kaman zai rike haɓɓanshi yana murmurshi nima, nayi maida mishi tare da gyaɗa mishi kaina.
Da ido yayi min Alama da na same shi a waje zai fita, d’aga kafaɗana nayi,
Motsa bakinshi yayi alamun plss.
Girgiza kaina nayi tare da kwaɓa fuskana alamun..
“No”
Mikewa yayi yace.
“Batul! Jiya na ganki da wata yarinya ko zamu je ki bani address ɗinta.”
Kura musu ido nayi na kuma saka kunnena ina jiran amsar da zata bashi. Dake itama bakar munafukace, sai gashi ta mike tare da bin bayanshi.
Raina ne ya ɓaci duk suka bani haushi. Ummi da take mika min yarinyar na amsheta tare da dangwarata akan cinyata ina zumbura bakina, karshe na mike tare da barin falon, ina shiga na hango waya tana kawo wuta, da sauri na isa gareta na ɗauka. Sakonshi ne ya shigo min,
*Heartbeat zan tafi tunda kinki zuwa zanje gurin kawar Batul I holp babu matsala.”
Tsuka naja masifa na cina na tura mishi.
*Allah ya raka taki gona! Thank God bani ce na kawoka ba kai zo da kafarka.*
Dariya yaƴi sannan ya kalle Ammah yace..
“Ammahna Yarki fushi take dani.”
“Gwara tayi,in nice ma fasa son katon gauro irinka zanyi.”
Shafa sajenshi yayi fuskarshi ɗauke da wata sirritacciyar murmushi, haka ya cigaba da jan motar har ya isa gida, tana sauka ya wucce Asibiti. A hanyarshi na tafiya asibiti yaga kamar ana binshi, yazo wani kwana. Sai ga wata Hilux sa mugun gudum tana zuwa ta daki motar da take binshi, tuni motar ta hantsila gefen hanya, me hilux ɗin yayi cilla a guje.
Dawowa yayi da baya kasancewa mutane sun taru ana kokarin ciro mutanen da suke cikin motar. Ya kutsa kanshi. Matasane duk jini ya ɓata musu fuska,
Karan wayarshi yaji ya fita a cikin mutanen ya koma cikin motarshi ya dauka.
“Kayi Babban Sa’a a rayuwa da jana’izarka za ayi anjima”
“Dakiki! Daba irinka ce maka akaƴi ni jahili ne? Ai duk wanda ya yarda da Allah baya taɓa tsoron mutuwa, amma dake kai gidahumi ne wai kana min barazana da mutuwa bayan rigata ce.”
“Matukar ina raye bazan taɓa barinƙa ka samu nutsuwa da Feener ba, sai naga bayanka.”
“Toh sai kaƴi gadin duniyar.”
YA ALLAH MUNGODE KABAMU IKON CINYE JARABAWAR😭😭😭👏Ina cikin tashin hankali nida Family na ina baran Addu’arku Allah ya kawo mana ɗauki👏😭
Oum Muwaddah…
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Alhamdulillah nagode sosai👏👏
Page.٣٦-36
Tsaki Dr yayi sannan ya kashe wayarshi ya bar gurin, yana mamakin halin Anim.
***
Anim Kamil Matawalle, D’a ne ga tsohon Daraktar gidan Radion na kasa, Alhaji kamil mutumin kirki ne bashi da abokin faɗa, haka ma Hajiya Balaraba. Mahaifiyar
Yaransu Uku, Anim ne Babb sai , Saifideen, sannan Ummulkhairi, Tun farko haɗuwasu da Feener ba yazo yana sonta bane an sashi ya sace ne ya ɓata mata suna, sabida tana jagorantar wani shiri na yaki da tafautaci da Yara da Mata.
Ganin tana tawayarwa mutane kai da kuma nuna musu illar bayarda yaransu, kuma mw gidanshi shiine ke jagoranta fitar da mata da yara a cikin kasar nan. Dan haka tabi kauyika tana wayarmu musu da kansu, har mutane suƙa fara hankalta. Dan haƙa suka daina bada yaransu.
Haka ya janyo karyewan arzikin Ubangidanshi, dan haka lokaci guda ya bawa Anim Hotonta da adress ɗin, ya kuma nima mishi aiki a gidan radion da Feener ke aiki, a hankali suka fara aiki A tare har kuma shirin suƙe gabatarwa tare.
…… Ahankali mutane suka fara zargin suna son juna, dukda dai Feener bata ɗauki abun ba sai daga baya ta mika wuya suka fara soyayya sama sama, har dai yakai gaban iyaye.
Anim yana da mata da yara Biyu mata, kuma bayi da lafiƴa yana fama da ciwon Hanta(😁😂😹 Yo na lura kun ra ja’a a wancan nikuwa labarin a kintse take) kuma cutar hanta tana cikin cututtuka masu hatsari. Sun taɓa haɗuwa da Dr saubiyu loƙacin shi an gayyace shi domin yayi musu lectures akan yadda zasu kare kansu da kuma gudun jefa wani a cikin matsala, har an gama kome na maganar aurensu kwatsam sai Feener ta fito da maganar zuwanta Jordan, kuma dama A nufinsa idan zasuyin Hoton prewedding toh anan zasu, cima burinsu, kuma abinda zai baku mamaki an bawa Anim kuɗi dan yayi aikin bayan shi ɗin kawaline, fasa auren da tafiyarta ba karamin asara yaja mishi ba, har maigidanshi ya kwace rabin kuɗin.
Abinda yafi ɗaga mishi hankali dawowarta da ciƙin dukda baya jin sonta, Dawowarta yaji yana masifar kaunarta dan da farko tafiyarta ji yayi kamar ya bita, sabida tsabar sonta da yake, karshe ya maida musu da kuɗinsu, baƴan tace bata sonshi.
Tsakani da Allah Anim yahakura, sai dai an sami matsala ranar da yaje dubata a asibiti, ya fito kenan ranshi a ɓace. Ya shiga motar garin tukin gangancin da yake, karshe yaje wata mota tabi takanshi….
Dakyar aka ciro shi suna zuwa Asibiti aka fara bashi taimakon gaggawa.
Duba wayarshi akaƴi suka sami lambar Mamie, kiranta akaƴi tazo taganshi. Shine takira wata kawarta ta gaya mata,ita kuma tazo da wani mutum suka fita dashi daga Asibitin……
Wannan shine asalin Abinda ya faru ina Mamie suka kaishi Oho…..
***
Ƙallon mara lafiyan yayi cikin sakin fuska yace.
“Yanzun ina ke miki ciwo?”
Girgiza mishi kai tayi cikin murmushi,
“Ok gashi Allah ya sawwaƙa”
Tura mata takardan yayi. A madadin ta ɗauƙa sai ta ɗaura hannunta akan nashi, janyewa yayi cikin ɗaurewan fuska yace.
“Hidayya! Bana son haka, duk zamanki a cikin asibitin kina cewa baki da lafiya nasani amma na shareki, pls ki rabu dani ina da matar da zan aura.”
Rausayar da kai tayi cikin yanga da yauki, irinta goggagun Yan mata sannan tayi fari da idanuta tace.
“Dr! Nifa na jima ina sonka Nashiga a tabiyu”
Murmushi yayi tare da jingina a jikin kujeran da yake Yace.
“Ke tun lokacin balki kike bina, karki manta kefa kawarta ce, zaki dame ni”
Naɗe hannunta tayi a kirji tare da kallonshi tace.
“Wannan matsalar balki ce! Ni takaina nake.”
“Hmmm! Yayi kyau”
Sako ya turo min tare da cewa.
*Hey Beauty har yau fushin ne? Ina kewarki sosai har da yarana*
Yana ta jiran reply amma fir naki tura mishi.
“Dr Magana nake da kai! Fa kuma kayi min shiru.”
D’ago idanunshi yayi ya ɗaura akanta, sannan ya maida kan wayar ya kuma turo wani sakon
*Beauty kina gasa ni don Allah kiyi hakuri! Wallahi bani da wata bayan kenan*
“Ina magana ka share ni.”
Tattara abubuwanshi yayi da sauri ya mike zai bar officer ɗin, tayi maza tasha gabanshi cikin marairecewa tace.
“Don Allah kace min wani abu mana”
Duba wayarshi yayi da sauri ya fita ta gefenta.
Takaicine ya turmusheta ranta na kara ɓaci cike da jin haushi tace.
“Allah dan ni akayi ka, itama balkisun nice na rabaku.”
Ta kuma bi kofar da harara, kamar shi yaƴi mata wulakanci.
***
Farcena nake kankarewa zan kuntsa lalle a hannuna da kafana, naji Sallamar Hajja Kaka, watsar da rezan nayi na tafi da gudu na rungumeta ina cewa.
“Wayyo Amaryan Dudu tazo ku fito mu fara Celebrat.”
Tureni tayi cikin sababi tace.
“Dalla can, me kika samu wan salebirita. Zagi a fakaice, ina d’iyoyin albarka”
Shareta nayi nacigaba da gyara farce, dama can mun saba duk lokacin da muka had’u na nuna farin cikina sai ta disgani. Kuma tayi burinta ya cika, karan sako naji na jawo wayar naga sakon Dr..
*Gani a waje ina jiranki don Allah”
Banza nayi dashi.
“Ke hafiran banza akaina miskilancinki zai motsa,”
Shigowar Zakari da kayanta, ya sani kallonshi nace.
“Malam Zakari don Allah kacew..”
Ban karasa ba sai gashi ya shigo,
“Ke miskilar banza ba magana nake dake ba?”
Share su nayi nace.
“Malam zakari zaka iya tafiya.”
Sannan na mike zan bar falon, rike baki tayi cikin salati da salami tace.
“Amma wannan yarinya anyi yar banza.”
Beauty!!”
Cak na tsaya ni banyi gaba ba ni banyi baya ba, karasowa yayi yana kallona yadda nayi kicin kicin da fuska, murmusa min yayi sannan yace.
“Don Allah bani minti ɗaya mana,”
“Ah barka da zuwa, Hajja! Dr kaima kazo kenan.”
Cike da kunya ya sosa kanshi yace.
“Hmm! Eh.”
Cikin mutuwar jiki ya bini da kallo ganin na tafi na barshi, dawowa yayi ya zauna a kujeran dake kusada hajja kanshi sunkuye yana jin ba daɗi yace.
“Ummi! Ko zaki mata magana wallahi zolayarta nake, bawai da gaske ba, zaki iya tambayar batu. Amma duk Safinah ta ɗauki zafi dani sosai bana jin daɗin haka.”
Taɓe baki Hajja tayi cikin kunar rai tace.
“Yo naga sokanci, toh kuka zakawa Maryam ɗin dan wancan me zubin lomar tuwon taki kulaka,, sai me ita da tayu kwantai yo ina abin moruwa a jikin kasusuwa, yarinyar da nonor arziki babu duk ya tsofai, itace zaka hana kanka sukuni, toh sai kacigaba in yan mata ne, yanzun ake haihuwar wasu, kazo kana ihu dan wancan me kugun kamar na zanzaro tana fushi da kai ka damu, dube ka jibgege irinka kazo kana damun kanka akan wancar me kiran bulogarin.”
Bai da niyyar dariya haka yayita dariya, fitowa nayi na shiga kitchen naji irin tanadin da Hajja take min, tsuka nayi ƙasa ƙasa a raina nace.
“Zamu gauraya da juna idan muka haɗu.”
Tunda na shiga kitchen ɗin baɓ fito ba. Sai dai naji Ummina tana bashi hakuri, da gayya naki fitowa yaran ma naki kawo mishi su.
Bansan me Ummina tace mishi ba, sai da nafito naga bayanan taɓe bakina nayi a raina nace.
*Kaji dashi gulmame kawai*
Haka muka share kwana uku bama niman juna, ni dai a cikin kwana uku na watsar da kome amma Dr sai da mukayi sati biyu yana horani, ba kira ba txt duk sai naji ba daɗi na rasa wanda zan tunkara da maganar ana haka sai ga Dudu da matarshi ya kawota wuni zuwan Hajja. Dake a gurguje ya kawota, ko shigowa bayyi ba ya tafi.
Sai da dare da ya shigo ɗaukarta, nake mishi ba’a nace.
“Dudu kaida Uban gidanka kuna fushi dasu Twins toh sunyi fushi daku.”
Zaro ido yayi dan bai fahimci kome ba, yace.
“Ai dama baku haɗuwa ne? Ai kullum yana zuwa gidan nan ko Batul?”
Kallon tuhuma nayi mata lokaci guda ta shiga yin tsili tsili da idanunta, cikin ɓacin rai na daka mata tsawa.
“Meye matsalarki da Dr? Wallahi Ummi ki ja mata kunne zan karyata akanshi.”
“Toh ba a gidana zaki fara kishin banza ba, kishin wofi toh ba a gidana ba, idan kin matsu kidaina share shi mana ki ga ko zai kula min Y’a sakarya kawai.”
Tashi nayi na bar falon cikin ɓacin rai na kuma banke kofar ɗakina,
Ina shiga ja wayata naga sakonshi sama da 15 tun sati biyu da suka wucce, rubuta mishi sakon nayi da cewa.
*Dama ka shigo rayuwata ce ka azabtar da zuciyata da ruhina? Me yasa ka koya min sonka bayan ba sona kake ba Why Hameed!*
Yana meeting yaga sakon, da sauri ya mai da min da cewa.
*Wallahi bashine manufata akanki ba! Manufata So da Kauna, Alhamdulillah tunda kin turo min sakon biko*
Zare idona nayi cike da mamaki dama bikonshi nayi taɓ ɗijam, *Aji Down*
Nace a raina, sannan na maida mishi da cewa.
*Allah ya kiyayye min nayi bikonka*
Dariya yayi kasa dan ma yana cikin manyan likitoti, shi yasa bai sami matsala ba, kuma taɓa irin Dr akwai matsala dan ko albashin da ake biyanshi na kula da lafiyan shugaban kasa, karshe ne balle kuma asibitocci uku yake aiki dasu a garin Abuja banda Alheri dan nashine nakanshi.
Ƙamar ya mike dan farin ciki sabida sun shirya da Beauty.
Ana gama meeting ɗin Dr Shahban na mishi magana suna da shiga tiyata bai kula ba yayi gaba abinshi zuciyarshi na gurin Yar Ummi.
… Bayan shiga ɗakina Hajja ta bankawa min harara, ciki sababi tace.
“Banda masifa! Wancan jibgegen katon take ihu akan banda so bai mata adalci ba ina ɗan kugunta zai iya ɗaukar shi, tana nan kamar lomar mayyu, kananun mata da jaraba yanzun ita a tunaninta zata ɗauk…”
Sulalewa Ummi tayi, yayinda Dudu da Batul tare da Khalil suke dariya kamar cikinsu zai ciwo. Haka Umma da Ƙhalila da suka shigo take gaya musu abinda yake faruwa tace.
“Amnah tunda Uwata ta haifeni ban taba ganin jarababbiyar mace irin Yakolo ba, ko ina zata kai wancan katon da take barbaranshi, Ina gaya muku duk ranar da ya rotseta sai kun kai mata a gaji dan yadda na ganshi karkarfa za ayi, shi yasa zan bawa Badaru shawara yasat, tafidda wani dan wallahi wannan ya haye ruwan cikin yar banzan can toh ta kare mata, dan sai kunyi dogon biki, ai manyan maza bana irin Yakolo bane kyanta ta sami dai dai irinta ɗan cas ko likita bokan turai”
Dariyar Dudu yaki tsayuwa, har da rike ciki haka ma Sophia itama dariyar ce, kowa a falon dariya yake. Bansan meye matsalar Hajja akan Dr ba wai ita dole na rabu dashi, na nemi wani tsabar barikanci matar nan ranar ido da ido tace min.
“Wallahi kika sake, wancan katon ya hayeki toh billahilazi, karshe da yoyon fitsari zaki wayi gari na dai gaya miki.”
Da ta bani haushi nace.
“Toh ko D’an uwanki Alhaji Ibrahim Kyari zaki aura min,”
“A’a bai kai can ba, nia tawa tunanin ki hakura idan Uban yaran nan yazo sai ku taru kurufawa juna asiri,”
“Wa? Ni jikar Ibrahim walƙahi ko cikin Yan biyu tsautsayi yasa shi min fyaɗa m, ina ni ina Yaro wanda bai gama mallakar hankalinshi ba,ai idan nasake wani abu ya kuma shiga tsakanimu renani zai yi dan haka bar batunshi yaron da ba a gamawa tsarki ba shine zan barshi ya mallaki jikina, Yo Hajja banda yana cikin hauƙa yaushe zai nemi wani abu daga gareni ainni matar Manya ce irinsu Dr ba sa’an Dudu ba.”
Rike baki tayi cike da alajabi tace.
“Amna ai ya cika miƙi mahaifa da mara da ruwan jikinshi, yar banza kafira. Idan ba namijin duniya ba babu namijin da zai iya ɗauraki saiti yar wofi wancan jibgegen, kwakuleki zai yi ya barki da azaba.”
Ai tunda na lura aljanun batsarta suna kusa na sharta ban kuma yarda mun sake maganar ba dan bana ciki da iskanci😂
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 25 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Sorry da spelling error
Page.٣٨-38
“Idan kina kuka ni kuma nayi ihu kenan? Meye amfanin kukanki d’aga min hankali zai yake, idan kinga da matsala.”
“Bani ce da tafiyar ba Abbanmu ya shirya, wai kar Nannah taga kamar mun rike mata jikoki da gaya.”
Shafa fuskana yayi sannan ya sumbaci goshina, sannan yace.
“Toh haka ma yayi Allah ya dawo daku lafiya, idan nagaji da jiranki zan biyo ki.”
Shiru mukayi dukkanmu zuciyarmu ba daɗi,janye jikinshi yayi ya lakaci fusƙana yace.
“Bari naje asibiti ina da marasa lafiya.”
Tunda yasa kai ya fita nake tsaye a gurin kamar wacce aka dasani, kuka nake kamar wacce aka min mutuwa. Dakyar na tattara na koma ciki,
***
Kwanakin da suka biyo baya da sauki, sai dai Dr yaki mu haɗu. Sai txt amma fir yaki muyi magana ta waya, ana jibi zamu tafi na sayi Data ta banki, playstore na shiga na sauke whatsp. Nayi sitting da layina, buɗe data nayi. Sannan na shiga sakwanine suka shiga saukowa, suna gama sauka na shiga duba Dr.
*Zuciyata tana kewarka*
Ina cikin sakon ban fita ba, can yayi min reply da cewa.
*Nima haka haske rayuwata! Na zata kin tafine*
Harara na tura mishi me cike da jin haushi nace.
*Haka ma zaka ce min!😏”
A dame ya turo min saƙon ban hakuri.
*Kiyi hakuri aiki yayi min yawa*
Cike da jin haushi nace na shiga voice not.
“Nagode ka cigaba da azabtar da zuciyata dan baka kaunarmu, nagode.”
Yana gama sauraron voice ɗin wanda nake magana har da kuka, sai ga video call.
D’auka naƴi na ajiye agabana ina kallonshi. Kurawa juna ido mukayi wallahi har ya faɗa.
“Kiyi hakuri.”
Cikin rawan murya nace.
“Ko dai kana guduna ne sabida Abinda ya faru har nayi hmm wallahi ni ba yar iska bace, kawai na rasa yadda zanyi ne amma bazan kara ba”
Murmushi yayi tare da gyara zamanshi, ya zuba min ido sannan yace.
“Toh keda ma kiss ɗin baki iya ba, shine kika dami kanki da cewa dan kin sumbace ni na gujeki! Ki duba abu ɗaya nifa ba wani abu nake muradi a gunki ba sonki nake da zuciyata baki ɗaya, dan haka idan kiƙa ce min nazo zaki kara min wani sumbar tare da rike wuyata kamar za a tsinke min ita.”
Rufe fuskana nayi ina dariya, cikin jin kunya nace.
“Don Allah kabar faɗan haka. Kana sani jin kunyarka sannan ina baka hakuri da abin wallahi bansan zaka.”
“Ba damuwa indai ana kula da tsoho irina ta hanyar zazzafar sumba haka ai ko waje alkur’an bazan fita ba, na dinga adanaki kenan”
Jan karamin pillow nayi tare da rufe fuskana nace.
“Pls Baby ka bari mana”
Dariya yaƴi sannan yace min.
“Ina da aiki, zan leko anjima.”
“Ok Allah ya kaimu.”
Nace mishi, da dare kuwa sai gashi munyi hira sosai. Har ya gama ya tafi.
***
Yau zamu bar Abuja zuwa Oman, amma ji nake kamar zan mutu tsabar bakin ciki. Da maraici jirginmu zai tashi kamar, zanyi hauka haka nake ji dan Dr yaki zuwa. Tun ina raba idanu har lokacin tashinmu yayi ba dr ba labarinshi, sai da aka fara kiranmu. A sanyayye na saɓi Aamih a kafaɗata hawaye na zuba daga idanuna.
Ji nayi an zare Aamih, ajiyar zuciya na sauke sakamakon kamshin turaren Adidas.
Cak na tsaya, a sannu yazo yaja hannuna muka shiga tafiya sai da ya kaini har cikin jirgin. Ya kaini gurin da zan zauna, ajiye min ƴarinyar yayi, a bazata naji lallausar lips ɗinshi ya sauka akan goshina yace.
“Zanyi kewarku Allah ya dawo daku lafiya. Idan kin sauka pls kk kirani.”
Gyaɗa kaina nayi yasakai ya ficce daga cikin jirgin, naji ba daɗi wai ma dan ban zama matarshi ba kenan.
***
*SAUDIA*
Shigowa yayi ya zauna, idan ka ganshi za ɗauka yafi shekarunsa sabida ya wani tara kasumba da da gemu sai fuskarshi tafito ɗan das, zama yayi. Sannan ya kalle lawyer cikin son karin bayani.
“Yallaɓai! Gimbiya Safinah tare da Gimbiyoyin suna hanya gobe Idan Allah ya kaimu, nima yau zan koma”
Murmushin da yajima bakyi ba itace ta kwace a fuskarshi yace.
“Idan sun huta akawosu”
Gyaɗa kanshi yayi sannan yace.
“Yallaɓai dukkansu har da Mahaifiyarsu.”
Cikin ko in kula yace.
“Idan zata zo ba, idan kuma taki koda karfin a kawo min yarana su naƙe buƙata.”
Tsakani da Allah Ashraf ya nuna shi ya ranshi yake so, dan haka yake cewa lawyer idan yaga ba suda matsala a karɓa a hannuna dan yana gudun kar na lalata mishi yara da rashin kjnya.
Da haka suka gama tattauna, sannan lawyer ya tashi dan komawa masaukinshi.
***
Mun isa Oman da karfe biyu na dare, Nannah da wasu mutanen tare da Yan uwanta suka zo tarɓana, na gaji zaman guri ɗaya, ina sauka a jirgin na hangota cikin bakar abaya. Sakar beharen, tayi kyau da tanaɗe kanta da bakin mayafi.
Fuskana cike da kunya da nadamar ɓata mata rai danaƴi ta bar kasan, kallona tayi cikin farin ciki tasa hannu ta amshi, Aamih. Tana shafa kanta tace.
“Barka da zuwa Oman Y’ata takaina”
” Barka dai Nannah. Mun sameku lafiya ya bayan rabuwa.”
“Alhamdulillah Safinah yasu takwara da fatan basu wahalsheki.”
Murmushi nayi, muka isa gurin motar da aka jera, ɗaya daga ciki. Kiran Rover range. Aka buɗe mana muka shifa tare, sai hira take min ina binta da eh aa.
Har muka isa wata haɗaɗɗiyar masarauta, iya haɗuwa ya haɗu, shima tafiya muke a hankali har muka isa inda zamu sauka.
Kallon yadda kowa ke sha aninsa babu wani tunanin. Dare yayi, duk inda muka wucce sai an zube ana gaishemu.
Har muka isa cikin gidan, anan naga tarba na musaman. Dan kamar Ashraf ɗinsu suƙe ganina.
Har dakin Nannah takaini anan naga wani irin duniya da aka narkan, a cikin ɗakin jikina ne yaƴi sanyi ganin yadda matar ta zauna a gidanmu kamar mara galihu, sai jikina yayi mugun sanyi.
A bakin gado ta zaunar dani sannan tashiga hidima da ni, masu aiki sunayi da jikonkinta, abinda ta fara bani madara da tumaric, nasha sai jikokinta kuwa wanda ama tasaka aka haɗa musu, ruwan wanka har da wasu irin turaruka, wanda yake cikin wani fure.
Gaskiya mun same tarɓa me kyau, ina fitowa doguwar riga nasama na gabatar da sallar dake kaina kafin na juya na kwanta, lokaci guda barci yaƴi gaba dani, ban san lokacin da aka dawo min da yaran ba dan barci yaci karfina.
Koda ta leko tasamu ina barci ga yaran da suƙe gefena suma suna tabarci, ɗakinta ta wucce. Inda tasame yan uwanta ana hira..
Abisa aladar Larabawa basu cika barci da dare ba, sunfi gane suyita yawo ko a zauna ana hira ana kurɓan shayi, Da safe kuma idan manyane su rama barcinsu idan yarana ne. Idan sun dawo makaranta zasu yi ina nasan ban wucce Oman ba tsabar barci yayi daɗi, banji kukar Aanih sai da ita Nannah taji tazo dauketa, taba ta ruwa tasha sannan ta.
Tashe ni na bata nono. Ina bata ina gyangyaɗ, dakyar na bata tasha ina ganin ta koshi na tintsira sai barci nima muka nayiwa kaina masauki, haka Nannah tafita tare da min addu’a.
Ta rage mana karfin Ac ɗin, sannan ta lulleɓe mu da babban bargo sannan tafita a dakin, jin d’umi yasani gyara kwanciya ashe bani ɗaya bace har da yaran
***
*Baya bata kad’an*
Jirginmu na tashi yan uwana da Dr suka fito, kawai aka fara…..
*Aka fara Me……”
Kuyi hakuri da pagen ba tsayi…😎
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 25 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
MOM SAYEED, RAHAMA AHMAD, MAMAN KHALIL da MY ZAHRA sauran Yan Team ɗin Hajja Ƙaka, toh tana miko GWS……
Wannan Naki ne sis FAUZIYAH kiji daɗinki…
Page.٣٧-37
” Nadai gaya miki ki rabo da wancan me zubin Inyamuran, ina dalili! Me zakiyi da mutum dinkinkina.”
Ta shigo min ɗakina tana mita, zuba mata ido nayi cike da takaici kamar zanyi magana sai kuma na kyaleta, sabida karan wayata ɗauka nayi na manna a kunne Cike da jan aji tare da miskilanci.
“Hmm!”
Murmushi ya sauke wanda ya doki dodon kunnena, lokaci guda ya saukar min da wata kasala, har sai da na lumshe idanuna.
“Beauty! Ina jiranki pls”
Ajiyar zuciya na sauke tare da sake wani munafikin murmushi nace.
“Ok!”
“Thank You!”
“Are Welcome My Beauty” ya faɗa, bai kashe kiran ba. Nima kuma haka muna manne da wayar a kunnenmu, sai murmushi muke sakewa junanmu.
Sake baki Hajja tayi tana kallon Ikon Allah, musaman da taga sai murmushi naƙe sakewa kuma ban kashe kiran ba, zama tayi a bakin gadon. Tace,
“Da alamu sai Badaru ya ɗauko masu maganin Aljanu dan bana tunanin lafiyarki lau, kin manna abu a kunne ke ɗaya sai dariya kike ai wani taga haka yace ba lafiya dalla aji.”
Katse kiran nayi a kufule nace.
“Meye matsalarki Hajja.”
Na mike ban ɗaki nashige dan bazan iya da hajja ba, sam bata da kunya kome zata faɗa a tsirarar shi take faɗa kuma bata damuwa da abinda zai fito bakinta kome tafamjama famjam.
Nasan na ɓata lokaci gurin wanka, ina fitowa daure da towel tana zaune abinta, zama nayi na fara gyara fuskana da jikina sai da na kyalkyale ko ina, sannan na ɗauko bra ɗina zan saka amma dake matar nan yar duniya ce, karkata kanta tayi.
“Hmm. Me zaki sanyawa rigar nono, ba dai wannan abun ba? Abu sai kace me kirgan dangi, wai ma na tambayeki taya kike shayarda yaran nan ne dan naga sun musu miri-miri.”
Juyawa nayi na kalli bakin kofa na tabbar ba kowa juyar sa kaina nayi, cike da bakin ciki nace.
“Zoƙi ficce min a ɗaki! Dan ke ɗin nan sai kija ayiwa mutane girgizan kasa ana zaman lafiya da maganarki nan da kike yi mara daɗin ji balle gani.”
Haushi na bata aikuwa tatura min baki, tana taune asuwakin bakinta, gown ɗin Atamfa nasaƙa, wanda aka fidda min shap ɗina sosai ganin yar sa’idon bata fita ba na ɗauki pant ɗina da under na shige ban ɗaki sororo tayi tana kallona, cike da alajabi har na fito. Taɓe baki tayi irin ko ajikina, na zata har zucine sai da nazo ina fesa turare tace.
“Yanzun Yakolo saka kayan ma, sai a ban ɗaki wata uwar zan gani, kika iya saka kwanseti a gabana sai wandone zaki gudu ban ɗaki, ko ce miki akayi zan kalleki ne.”
Naɗe gyale na nayi cikin sauri nace.
“Ke kika damu”
Na fita da sauri, rakani tayi da harara tana dafe gwiwarta zata mike daga bakin gadon, na sake shigowa da sauri na kalli fuskana sannan nafita da mugun sauri.
“Ba dole kita sauri ba, sam yarinyar bata da auki, sai kace bulaliya.”
Ita kaɗai tayita mita tsabar masifa nacinta.
…..
Tunda na fito ya kura min ido. Ko kiftawa bayayi, zuciyarshi cike da farin ciki, yayinda fuskarshi taki ɓoyewa sam. Har na iso jikin motar na tsaya hannuwana harɗe a kirjina , nace.
“Assalamun Alaikumun”
“Amin Waalaikumun Salam, Beauty! Barka da zuwa.”
Buɗe kofar yayi tare da zaro kafafunshi waje, a hankali ya yunkuro yafito, sai yanzun na lura da girman da Hajja take cewa yayi min, tsayi yake dashi sai faɗi. Kuma yana da murɗaɗɗiyar jiki, kana ganin tarin tsokoki, lumshe idanuna nayi sakamakon kamanceceniyar da suke da Ashu, sabida shima yana da k’iran irinta zaratan mazaje.
Hura min iskan bakinshi yayi. Fuskarshi ɗauke da murmushi yace.
“Kina tunanin Babansu Twins ko?”
Ya ɗaga min gira, tsuke fuskana nayi tare da tura bakina gaba nace.
“Baby!!”
Ware idanunshi yayi, cikin jin haushi nace.
“Ba halin nayi tunani sai kace na wncan yaron nake yi”
Dariya sosai na bashi, dan yakasa rikewa yasai yi yake kamar yaga taɓaɓɓiya, haushi ya bani na juya zan koma cikin gida yayi wuf tare da riko hannuna, a tsiwace na buɗe baki zanyi magana, muka haɗa ido dole na haɗiye sannan na kalle hannuna da ya riƙe.
“Kiyi hakuri mana” yace cikin wani irin murya, d’ago idona nayi na kalle shi. Bansan lokacin da kwalla ya shiga saukowa daga idanuna ba, sake min hannuna yayi sannan yace.
“Kiyi hakuri, wallahi bansan dariyar zai sakaki kuka ba, kiyi hakuri bazan kuma ba.”
Buɗe motarsa yayi ya ɗako tissue ya mika min, goge kwallar nayi, kaina a sunkuye. Dan kunyar kaina nake ji na kukan da nayi akan abinda bai taka kara yakarya ba.
“Kinsan me yasa na miki dariya! Sabida kin kawo abinda hankali bazai ɗauka ba, tabbas Babansu Twins yarone kamar yadda kika ce, amma ya kamata ki ɗaga shi daga cikin jinsin yara ki kaishi cikin na manyan sabida, Yan biyu, da kuma nan gaba zan kara fahimtar dake abinda nake son ki gane.”
“Meye haɗinka da kawar Batul?” na tamvaye shi tare da tsare shi da idona,
D’age min gira yayi cikin tsokana, ya shafa kanshi sannan yace.
“Idan kin amince, rana d’aya za a kawo min ku.”
Kallonshi nayi bakina har rawa yake nace.
“Kana nufinm”
“Eh ku biyu zaku zauna,”
Kauda kaina nayi cike da zafin rai nace.
“Ok, kaje ka zauna da ita dan ni ba zan zauna da sa’ar Batul muna gogayya da ita ba.”
Mamaki na bashi yadda na ɓata rai, akan yace mu biyu zamu zauna, murmusa min yayi sannan yace.
“Kin cika kishi! Bana fatan rike mata biyu, amma ki sani kishi ke haifar da kishiya, ki sassauta kishinki ni mijin mace ɗaya ce
tal.”
“Wacece a ciki ni ko Ita.”
Na tambayeshi, gyara tsayuwarshi yayi tare da kura min ido, yace.
“Banda sai anyi aure zaki halatta min wallahi da idan ɗauke ki yanzun na kaiki cikin gidana, babu wanda zai kuma kallon tafin hannunki.”
Kallonshi nayi cikin wani bakon yanayi, haka kawai naji ina tausayawa ƙaina, lokaci guda idanuna ya fara da ruwa. Sunkuyar da kaina nayi sabida saukarsu. Suna d’isa a kasa.
“bansan me yasa ba, bansan me nake ji ba, kawai ina tausayawa rayuwata ce idan na rasaka, Dr ka tafi kawai dan ina jin tsoron kar na fara sonka kuma nazo na rasaka.”
Takowa yayi gabana tare da soka hannunshi a cikin aljuhunsa d’aya yace.
“Ki d’ago kanki ki kallr cikin idanuna, ce min kina sona.”
Girgiza kai nayi wani irin kuka ya kwace min, dafa jikin motar nayi, nace.
“Ko baka ce ba, ina sonka mahaukacin son. Wanda zai iya tarwatsa zuciyata idan na cigaba da ɓoyewa, Hameed kaje kawai idan kacigaba da zama dani bazaka karu da kome ba, sai tsantsar damuwa”
“D’ago kice min na tafi ni kuma zan iya juyawa.” ya faɗa min yana kusantar inda nake.
“Bana son Adil da Ammah su.”
“Ke! Lafiyarki kuwa kinzo kinsa garjeje a gaba , kina kuka shi kuma da yafiki shirme yabi ya rikice kai jama’a duniya tayu lalacewar zabi.”
Da gudu na shige cikin gida ina kuka, koda na isa falon ban tsaya ba na shigesu Ummi da suke zaune.
Bin bayana yayi da ido, bai masan me hajja ke cewa ba, shi damuwarsa nice, haka ta gama surutunsa.
Haka ya shiga motarsa ya bar gidan zuciyarshi ba daɗi, na rasa gane meke faru dani matukar zan haɗu da Dr tausayinshi nakeji haka mukayi kusan kwana goma, dakyar ya dakatar da shirmen da nake mishi. Tsakanina da Hajja kuwa toh ko Tom nd Jerry sun sallama mana, domin kuwa taƙanzo tamin maganar banza ni kuma na shareta idan ta buwaye ni ce mata nake Hajja ko zamu nimo tsohon irinkine a ɗaura muku aure, bata kuma bin takaina.
…….. Tsakanina da Dr soyayya ɗoɗarr domin kuwa na gabatar dashi har anyi magana, karewa ma Sadakinsa na hannun Iyayena, an bari sai na yaye yarana wanda suke da wata huɗu zuwa biyar.
***
Watansu Aanih bakwai aka shirya mana tafiya zuwa Oman, tsakani da Allah nasaka Ummi agaba ina kuka bazani ba, dan nasan idan naje sai su nemi rike min yarana wanda nake ji yanzun kamar rayuwata ce su ɗin ko ciwon hakori suƙe tare muke dasu, dan har tsokanata Dr keyi wai amka uwar son yara, bana jin kome, gefe guda har da tunanin dr yake hanani tafiya, dake Ummi ta harbo jirgina sai tashiga rarrashina da cewa.
“Ayya Uwata kwana nawa ne kamar yau ne fa, har kun dawo.”
Da ire iren magana masu daɗi da laushi, tasamu na amince amma sati biyu zanyi, murmushi tayi a ranta tace.
*Ta yaro kyau take bata karko*
Kin gayawa Dr nayi, ranar da yaji. Ya kirani amadadin nai mishi magana sai na saka mishi kuka, na rasame zance mishi.
“Ya isa Beauty! Dalilin da yasa kika ɓoye min kenn bazaki iyafaɗa min ba sabida kuka zaki min? Karki damu duk inda kike kisa ranki muna tare, insha Allah zan biyoki soon, an jima zanzo.”
Daga haka ya kashe kiran, ranar nayi kuka me cin rai sosai dan gani nake kamar basu min adalci ba,.
Da dare da yazo kasa sake jiki nayi inata ɗari ɗari, dake yanzun a falon Abba muke hiran haka ya gama shirunsa sannan ya ajiye min rafan kuɗin Oman har guda uku, sannan yasa kai zai fita. Cikin sauri nabi bayanshi na rungume shi tare da sake kuka ina cewa.
“Kayi hakuri bazan kuma ba”
Wani irin yanayi yaji ya sauko mishi tare da kasala me mugun kashe jiki, janye hannuna yayi wanda nasa na kamkame shi, ya janyo ni gaba cikin damuwa yake kallona.
Lumshe idanunshi yayi cikin damuwa yace.
“Toh ya zan miki! Nazo amadadin ki tarɓe ni da kalamai masu daɗi sai kuma kika sani a gaba da kuka, kinsan yadda nake ji. Banda kar na shiga hakkin yaran nan ba, wallahi bazan bar gari yawaye ba tare da kin zama mallakina ba.”
Lumshe idanuna nayi tare da saka hannuna a wuyarshi na kara tsayina tare da d’aga kafana, haɗa fuskarmu nayi kafin yayi yunkurin dakatar dani, na haɗe bakinmu guri guda. Kallon fuskana yake musaman yadda kwalla ke sauka wannan na koran wannan a guje, a sannu ya buɗe min bakinshi na rasa yazanyi, kawai sai na nemi janye bakina daga gare shi, rike bayana yayi da hannunshi duk biyu ya zura harshenshi cikin tare da lalluɓo nawa, buɗe idanuna nayi da sauri. Lumshe nashi yayi sannan ya buɗe. Yana kallon cikin kwayar idona yake, lumshe nawa nayi, a sannu na kwace bakina ina sauke ajiyar zuciya, kuma sai na fashe da kuka tare da kifa kaina a kirjinshi ina kuka, sunkuyar da kanshi dai dai kunne na yace.
“Thanks for thi hot kiss”
🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃
Yau nayi batsa😎😏 naji cass…
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 25 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Page.٠٤-40 Masha Allah..
*Na shiga uku na lalace! Ni Safinatu ba dai wancan yaron suke nufi ba*
*(Kuji min Safinah da bidi’a a wasan kwarzo da kuka buga antashi 1-0 shine zaki kirashi da yaeo😎😏😒 Salon Mom Sayeed tasami abik fada bana son reni)*
Kululu naji cikina ya bada sauti, ga kirjina da yayi min nauyi, tsinkewar gaba. A lokaci guda narasa kuzarina da ɗan karsashina.
“Sarauniya Safinatu! Ga kyautar jauhari da Lu’ulu’u daga Gimbiya Khadijah, sai katafaren gida a can wajen gari daga Yarima Ubadullah, sai kyauta me girma daga Sarki AbdulMuttalib ya bada kyautar manyan shagunarshi na zamani dake cikin garin.”
Haka sukayita faɗa min abubuwar da muka samu na kyauta ni da yarana, amma bana fahimtar kome. Sakamakon jin abinda ya nemi kundume min tunanina.
Ana gama bayyanin muka wucce gurin cin abinci, shima cin abin kamar baza aci ba. Sabida izza kallonsu nake kawai. Yadda suke cikin abinci a nutsu kuma baka jin kome sai karan cokula.
Ban iya cin wani abin kirki ba sabida damuwa da tashin hankali. Dakyar na iya ɓoye halin da nake ciki dan kar Nannah ta shiga samuwa, yar autar sarki Safyanu itace ta mike cikin yatsuna fuska tace.
“Alhamdulillah, muje Amatullah”
Mikewa yarinyar tayi dukkansu yan mata ne basu wucce Batul ba, amma idanunsu a tsakar ka yake, dan ina lura da ita yarinyar farkon wacce suke kira da Natasha, tunda aka gabatar dani take cika tana batsewa.
Ina ganin Nannah ta ajiye cokali nima na ajiye nawa, sun ɗan tab’a hira sannan duk suka mike har dani, ɗakin Nannah muka waccey shima idan nace zaɓ faɗi haɗuwarshi ɓata lokacine.
Muna shiga na zauna a falo har lokacin zuciyata ba daɗi sabida kiɗimar da nake ciki. Gaskiya zuciyata tana cikin ruɗani. Bansan ya akayi ba na iya haɗiye tashin hankalin da nake ciki.
Can sai gata tafito, ita da Yan matan nan. Suna gani na suka fara harara ta, basa gaba damuwar dake cin zuciyata ya isheni.
Kaina a sunkuye suka zauna a can gefe dani, suna zagina cikin larabci sai da suka ji muna magana da Nannah, suka tsorata.
Cikin kulawa Nannah ke tambayana kwana nawa zan musu.
Wasa na fara da farcena sannan nace mata,
“Sati biyu!”
Murmushi tayi sannan tace.
“Safinah gashi na tambayi Abbanki zaki min wata biyar, har Abbansu kawayena ya fito tunda saura wata huɗu ya fito”
Kamar zanyi kuka nace.
“Toh Nah Allah ya nufa.”
Kallona tayi cikin nutsuwa tacigaba da magana.
“Idan kinga zamu takuraki, kiyi kwanakinki ki koma in yaso daga baya zamu zo”
Cikin jin kunya na girgiza kaina nace.
“A’a Nah ba kome zan iya zama”
Shiru tayi ta share kamar babu magana abakinta, kallonsu Natasha tayi cikin ta nuna musu hanyar waje.
Da sauri suka fita tare da jin ba daɗi. Kallona tayi cikin nutsuwa tace.
“Abbanki yace kin tsayar da miji ko?”
Da sauri na ɗago da kaina loƙaci guda zuciyata tana wani irin bugawa. Gyaɗa mata kai nayi idanuna na ciko da kwalla.
“Safinah! Ni a tunani na da ki auri wanda zai miki gori. Ina ga ki auri Mahaifin yaranki mana dagake har shi Ashraf ɗin zuciyarku zai fi samun nutsuwa.”
Girgiza kaina nayi lokaci guda hawaye na zuba daga idanuna nace.
“Don Allah kiyi hakuri na rigada na bawa Hameed zuciyata, karkuyi kokarin rabani da abinda zuciyata kedo, yin hak Zai sani jin ba daɗi.”
Kura min ido tayi tana jin haushi, murmushi tayi tare da ɓoye abinda yake ranta tace.
“Bar kuka! Bazan miki dole ba shawara ce kawai na baki, tunda kina da wanda kike so Allah ya nuna mana lokacin.”
Goge kwalla nayi tare da ce mata.
“Kiyi hakuri Nah”
Girgiza kai tayi cikin nuna ba kome tace.
“Ba kome, ki kwantar da hankali.”
A haka muka tab’a hira sama sama.
Har lokacin sallah yayi muka mike. Tunda na dawo na zauna nake nazarta halin da nake ciki.
****
*Mumbai*
Tunda suka iso garin aka fara kokarin ceto rayuwar sa cikin Yarda da kai suka sadaukar da lokacinsu anyi aikin cikin natsara da takatsantsar. Cikin ikon Allah sai gashi sun sami damar ciro bullet ɗin. Sannan suka fito dashi, dukda sunyi booking ganin liƙitan ta Onlind shi yasa basu tsame matsala ba.
Sai dai muce Dr Allah ya baka lafiya.
***
“Wallahi Ummi duƙ sai na ruɗe na rasa me zance mata sabida ta rutsani sosai.”
“Allah ya kyauta”
Iƴa abinda Ummi tace.
Tana mamakin irin son da nakewa dr.
***
Saudia…
Yau ya fito fuskarshi nan a cunkushe ya zauna a kujeransa.
“Sultan! Maman Yan biyu tana can masarautar da yaran”
“Asaka ido akanta da yarana”
Gyaɗa mishi kai yayi cikin nutsuwa har ya bar gurin, zuciyarshi na cike da farin ciki da jin daɗi yaranshi suna kusadashi.
*Alhamdulillah*
Sosai yayita murna kamar wanda aka bawa aljannah.
***
Wato wani irin rayuwa na fara fuskanta. A cikin masarautar wani mugun tashin hankalin wanda yasani kuka a ɓoye, dan lokaci guda Nannah ta hanani yarana, kuka nake zama naƴi tunda Nannah taga ina damuwa, sai ta shiga kawo min yaran, sau biyu ina basu nono ni kuwa, so. Yarana da kaunarsu ya cika min zuciya. Lokaci d’aya na fara jin za araba Uwa da yaranta.
Shigowa tayi ta same ni ina share kwalla zama tayi sannan tace.
“Gwara ni, ina da sauki sosai
Domin kuwa Idan mahaifinsu yazo zai rabaki dasu ne shiyasa na miƙi tayi aurensa.”
D’afo kaina nayi a raunane sai ga kwalla sharrr. Duk yadda naso hana kaina kuka sai da nayi me isata, kuma bata hanani ba.
“Toh Nah ni narigada na tsayar da Dr bana jin kowa a raina sai shi, don Allah sau ɗaya kubarni na bi muradin zuciyata mana, Hameed shine mafarkina, ya tanadar min soyayya da farin ciki, Nah!”
“Ya isa Safinah bazan miki dole ba tunda kina da wanda kike so, amma kisani ko zaki koma keda d’aya zaki koma, domin kuwa haka muke al’adarmu zamu amshesu a nimo larabawan kauye a koya musu larabci.”
Cikin shashakar kuka nace.
“Nah! Karku rabani da abinda zuciyata ke so!”
Girgiza kai tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace.
“Safinah! Yaran Shegune!”
A razane na ɗago kaina cikin raina nace.
*Shi kenan Sun rabani dasu*
Wato shi yasa Malam bahaushe yace magana d’an aikene duk yadda kayi shi wata rana sai ya dawo maka, yau gashi ya dawo min.
“Nannah dan girman Allah karki rabani dasu, wallahi zuciyata bazata iya d’auka ba ina mahaukacin sonsu dan jikina suka tsaga, qaddara ce tasa na samesu ta baibai… Amna ba gama garin shegu bane don Allah ki rufa min asiri ki barni yau na koma.”
Sam bata jin dadi kukana amma bata zaɓi da yafi haka, mikewa tayi ban kuma ganinta ba sai a gurin Cin Abinci na gansu har da yaran, suna rikici.
Tabbas larabawa mugayen mutane ne akan yaransu, yaran suna gani na suka fara mika min hannu, dan yau tunda ta shigo aka kawo min su, na basu suka sha, har yanzun da kusan karfe biyu na rana.
Tunda nasa abincin a gaba sai juyawa nake yi, kukansu jinshi nake a cikin brain ɗina, duk yadda naso dakewa na kasa, juya abincin nake zuciyata na wani irin bugawa. Ajiye cokalin nayi a raina nace.
*Badani da goyan mayyu ba*
Mikewa nayi naje na amshi yaran na raɓa ɗaya a kafaɗa, ɗaya kuma na riketa a kweɓina na fita daga falon cin abincin.
Murmushi Nannah tayi ta cigaba da cin abincinta ranta kwal, suna gamawa Yayanta yace.
“Nana Asma’u! Karki sa yarinyar can ta tsane ki! Dan uwa ce zata iya jure duk wani tashin hankali akan yaranta, haka da kike mata zai sanyata taji bazata iya ganinki da kima ba.”
Jinjina alamarin tayi cikin yarda da shawaranshi, bata ce uffan ba har ya tashi ya fita. Maman Natasha ta kalleta sannan ta kalle Natasha da tayi raurau da idanu tace.
“Amirah kina ganin haka da kikayi zai.”
Juyawa Nannah tayi cikin murmushi tace.
“Safinah! Nake so,, sai da taja numfashi sannan ta cigaba da cewa.
“Natasha bazata iya da halayar jama’ar jordan ba, amma Safinah tasan halayar wasu ciki har da Ashraf ɗin tasanshi fiyye dani saninda na masa, a halin yanzun Ashraf baya bukatar jinin Sarauta a cikin rayuwarshi, domin bazata bashi gudummawar da nake bukata ba, shiya kuka ga ina nisantata da yaranta, nisan tazara dake tsakaniksu shi zai sanyata amincewa amma bazan taɓa mata dole akan D’ana ba dan tasha wuya a hannunshi.”
Tana kaiwa aya ta mike abinta, tafita daga d’anki cin abinci.
***
Ina kwance nasaka yaran a gabana bayan na gama basu nono, har sun same barci, ni kuwa kuka nake sosai sabida tashin hankali da tararadi. Dafani tayi na mata banza sai da tajuyo gabana tace.
“Kiyi hakuri! Ki amshi tayina.”
“Nah! Haramun ne nima a cikin nima, Sadakinshi na hannun Abbana! Kuma bana jin zan yafewa kaina cin amanarshi don Allah kiyi hakuri ki nima mishi auren Batul ko Khalilah”
“Kece Masarautar take bukata! Kece zaki iya abinda muka gaza yinsa! Kece kaɗai zakin iya tankwarashi.”
“A’a Nannah! Ni bazan iya ba don Allah kubarni haka Ni zuciyata Hameed kad’ai nabawa Muwahalin gina fadarshi, sannan Shi Ash”
Kasa faɗar sunanshi nayi sakamakon nauyin da yayi min, kallon yaran nayi kamar zan saka kuka nace.
“Nah! Ki maidani gida.”
“Zan maidaki, amma sai yadawo yaga yaranshi,”
Tana gama faɗar haka tasakai tafita.
Zama nayi cikin damuwa, wayar da tabani na ɗauka tare da kiran Ummina, ina kuka nace.
“Ummina! Don Allah ki gayawa Nannah na amshi Sadakin Hameed tasani a gaba da amsar tayi D’anta.”
Cikin sanyin jiki tace.
“Safinah! Baki ganin zatace kin kawo karata ce? Kiyi hakuri tunda Hameed kike so baza a miki dole ba, amma ki cire son yaran nan a ranki zaki fahimci dalilin haka.”
“Ummina bazan iya basu Yarana ba! Domin musulunci ya bani su don Allah Ummina karki sare min kwarin gwiwata, Ummi rabani sa yarana zasu yi, wallahi za a kawo miki gawata.”
Kashe kiran nayi ina kuka sosai. Kara wayar tayi na duba My Dudu na gani, cikin sauri na ɗauka tare da mannawa a kunnena nace.
“Dudu! Zasu kwace minsu.”
“Ya isa ki kuma nutsu ki saurareni”
Haɗiye kukan nayi ina gyaɗa kaina, kamar ina gabanshi yace.
“Koda su Abba sun amince zasu tilasaki auren wanda baki so I promise you bazan taba barin haka ya faru ba kinji Yayata, sannan shawara ɗaya. Kicire idanunki akan yaran idan tasa aka kwashesu kema ki fita harkansu da yaran, sai abu nagaba karki kara barin idanunki su zubda hawayenki, kinsan me yasa suka biyo miki ta jikin yaran sabida sunsan yaran sune Rauninki weakpoint ɗinki, idan kika sake zuciyarki tayi rauni zaki dawo kasar nan ba tareda yaranki ba, abinda zan gaya miki shine kifita batun yaran suna sonsu kina sunsu, sai kubuga wasan yadda dole ɗayanku ya hakura, ke sunsan bazaki iya hakura ba akan yaran kema sai ki duba ta yadda zaki rama sai a tashi wasan 1-1 amma sai kin koyawa zuciyarki jarumta, in ba haka ba toh ba makawa ranki zai ɓaci kiyi tunani dakyau, na barki lafiya Yayata”
“Nagode Duduna ai na bar maka girman dan nice yayar a baki amma a zahiri kaine yayan nice kanwar nagode Dudu.”
Murmushi yayi sannan ya kashe wayar duƙ abin duniƴa ya dame damamiya irita, na kuma shiga tunanin taya zan kwaci kaina kamar yadd Dudu yace.
Dan Wallahi bani bada yarana ina zan iya wannan ɗ’anyen aikin na gama shan wahala da ciki a kore ni da cikin yau dan sun fito sun zama mutane ace za a rabani dasu Wallahi karya kenan….
Kuyi hakuri jiya na gama Typing hmm ya goge😭😭 ban sani ba ko wannan pagen zai yi ma’ana shi yasa sai na koƙa gado naja bargona na kwanta Bazan iya bakin ciƙi biyu ba😭
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 25 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Page.٣٩-39
Sun fito zasu inda motarsu take kawai aka buɗe musu wuta, cikin sa’a suka sami Dr a kirjinshi gefen, take ya zube a gurin.
Dudu dasu Ummi da Abba kuwa basu same su ba, ana cikin haka wasu maharan suka zo aka fara musayan wuta, abinda ya kuma ɗaga kowa hankali dan ba karamin d’agawa mutane hankali yayi ba dan har cikin inda mutane suke harbin ke shiga.
Haka sukaƴita harbim juna har masu harbin baya suka samu kashe mutanen da sukayi harbi Dr, wani abin mamaki wadancan sunfi su iya sarafa makami, kuma sun iya harbi a nutse kamar suna, shi yasa suka same damar kashesu, suna gaba kashe su. Suka dawo kansu Abba.
“Kutashi ga mota can zai kaiku gida, sannan shi Dr zamu wucce da shi Asibiti.”
Dake a kwai tsoro a ransu haka suka mike, tare da bin umarninsu har cikin motar, suna shiga ana tadda motar zuwa gida.
Komawa kan dr sukayi tare da kamashi suka sakashi a motarsu zuwa Asibitinshi. Cikin gaggawa aka amshe shi, ana kokarin ceto rayuwarshi.
Cikin kwarewa su Dr Shahban tare da wasu drs suka rufa akanshi, hankalinsu yayi mugun tashi. Kafin wani lokaci labarin harbinshi ya karaɗe ko in, har takai shugaban kasa da kanshi yazo asibitin domin duba lafiyarshi,
Tsawon awa takwas akayi ana faman ceto ranshi, amma ena abun ya faskara dole shugaban kasa yasa hannu aka fiddashi da jirgin fadar shugaban kasa zuwa. India, sabida bullet ɗin ya kuskuri zuciyarsa, abu mafi hatsari a tare da ciwon shine da zaran akace za a cire bullet ɗin da karfi toh tabbas mutuwa zayi. Shi yasa duk suka birkice akanshi suka rasa ya zasuyi dashi.
Dole aka tattarashi sai Mumbai.
***
Wani irin mafarki nayi me cike da firgice, akan dr zubur na mike tare da janyo jakata na ciro wayata, na fara kokarin niman gida. Abin haushi ashe number kasata ce bazatayi a kasar ba, tilas ni wurgi da wayar ina tsaki, tun bayan sallar asuba na koma barci, duba gun yaran nayi naga suma barci suke, saukowa nayi a gadon, na nufi ban ɗaki.
Wanka nayi sosai sannan na fito, na same Nannah tana zaune tasa jikokinta a gaba, tana kallonsu. Dake akwai rigar wanka a jikina, har kusan kwanjina na nemi guri na zauna nace mata.
“Barka da safiya Nanna”
Fuskanta ɗauke da murmushi ta kalleni cikin sakin fuska tace.
“Binti! Kin tashi lafiya, ya kwanan kawayena? Naga sai barcinsu suke”
“Hm! Ai haka suke ko a gida basu cika rikici ba, sai dai ko idan suna jin yunwa.”
Kallona tayi taga hankalina nakan jakata ina kokarin ciro mai na da nake shafawa. Girgiza kanta tayi, dan tun kafin n iso tasame labarin abinda ya faru, dan haka tayi kokarin ɓoyewa dan kar naji na ɗ’aga hankalina tsaf tasan halina zan iya juyawa gida.
Ina gama shafa man, na zuge akwatina tace.
” Binti ga kayanki a nan!”
Ta nuna min wall dress drower, a sanyayye na juya gurin drower. Zan buɗe sai ga wasu yan mata su uku sun shigo cikin unifoam brown, suna gani na a tsaye suka zo ɗaya ta rike ni tamaidani bakin madubi, ta zauna dani akan stool. Sannan ta buɗe wani drower set na kayan makeup ne, ta cirosu ta fara bazasu saman dress mirro ɗin, d’aya kuma ta buɗe gurin kayan sawa ta fara cirowa tana ajiyewa. Dogayen riguna ne masu masifar kyau da tsada.
Wani irin kwallayi suka min me matukar ɗaukar hankali, Nannah tana kallonmu sai murmushi take, karku manta larabawa a harkan kwalliya da k’awa daga su sai India. Dama dama turawan Uk, suma suna cin Uwar dukiya ga.
A hankali suka gama min kwalliyar sannan, suka shiga nuna min kayan. Musaman Nannah ta nuna musu ɗaya gefen aka buɗe, royal gown ne masu mugun ɗaukar hankali,
A hankali ake fiddasu ɗaya bayan ɗaya, aka suka fiddasu sosai wata maroon na hango wanda akayi combinet da Golden, na nuna musu.. A sannu suka ciro rigar aka ajiye min kallon Nannah nayi, ta sakar min murmushi, mikewa nayi na shiga inda zan sanya inner wear, ina gamawa na ɗauki rigar nasaka, ban zuge zip ɗin, fitowa nayi suka gyara min zip ɗin.
A hankali suka gyara min zaman rigar , sannan na zauna suka gyara gashina suka saka min wani siririn veil da karamin crown. Safar hannu suka samin, sannan suka buɗe inda takalma suke na nuna musu wata golden tare da pouse ɗinshi, abin haushi ana fidda takalmin naganshi heel ce, kamar zanyi kuka nace.
“Babu flat ne? Nifa ban iya amfani da heel ba.”
“Ma! Ai duk shigar da zakiyi dole takalmar kenan.”
Juyawa nayi na kalli Nannah da take jinmu hannunta rike da wayarta.
“Binti size ɗinki kamar yadda nasani ne ko?”
Gyaɗa mata kai nayi cike da sakalci, murmushi tayi sannan tace.
“Mantawa nayi na gaya musu baki saka takalmi masu tudu. Amma yanzun zasu kawo, bano bace na shirya miki kayan ba, Aunties ɗinki ne. Amirah Zahra da Amirah Khadija, sune suka shirƴa miki,”
Muna cikin haka sai ga manyan bags an shigo dasu takalmar ce kaman na farko aka shiga shirya min su. Sannan suka ciro min takalmin nasaka. Suna dabda gama shirya ni sai ga masu kula dasu Aamih, kallonsu Nannah tayi. Naga sun dukar da kansu kasa, suna niman afuwarta na makarar da sukayi, cikin sauri suka isa bakin gadon, ɗaya ta wucce ban ɗaki ta haɗa musu ruwan wanka, ɗaya kuma ta zauna tana shafa kan Aanih, cikin nutsuwa tanayi tana hura mata iskar bakinta a kunne, mika yarinyar tayi, a hankali tasa hannu ta ɗauketa tare da mikar da ita yarinyar tayi mika sosai sannan ta maida ita kafaɗarta. Ta shiga zare mata kayan jikinta. Sannan ta ɗauki wani farin showel ta lulluɓata dashi, suka nufi ban ɗaki bakina a sake nake kallonsu, duk wannan shirin da ake min babu wani motsin arziki sai aikinsu kawai, haka ya ankarar dani inda nake, masarautar me daraja na takwas a daular jaziratul Arab, wato yankin gof. Dan haka dole kome zasuyi susa nutsuwa da hankali, dole su maida tunaninsu kan abinda ake, zan iya cewa a sanina Nannah mace ce mai faranfaran da jama’a. Amma zuwana jiya. Na fahimci kaskantar da kanta tayi,sabida rashin ɗanta, da kuma rashin gida. Yau gani ga ita sai murmushi wanda ada itace kejana da hira yanzun jinin sarauta haɗi da Izza suna yawo a jininta, gata dai amma ba magana ba kome sai murmushi.
Suna gama shirya ni, suka shiga fesa min wasu turaruka masu karfi, wanda yasani atishawa. A kiɗime ta ɗago ta kallesu cikin rawan jiki suka shiga min sannu.
“A’a babu kome, jikina ne baya son turaren amma ina lafiya.”
Na faɗa musu a sanyayye, nuna min kusada ita tayi na zauna, ina jin kewar gida.
“Bari su shirya Kawayena sai mutafi ki karya ki kuma bi yan uwa da iyaye su ganki.”
Gyaɗa mata kai naƴi, ina son sabon sim amma narasa yadda zanƴi kaina kasa nace.
“Nah ina son kiran yan gida.”
Mika min wayar hannunta tayi, na ɗ’ago kaina zan mata magana lumshe idanunta tayi. Karɓa naƴi na mike zan ɗauko jakata, D’aya daga cikin yan mata tace.
“Amirah! Me kike bukata.”
Murmushi na mata, sannan nace.
“Jak”
Ban rufe bakina ba ta ɗauko cikin girmamawa ta mika min, sannan tace.
“Kina da daraja me girma a cikin masarautar nan, duk abinda kike bukata basai kin wahalar da harshenki ba, nunawa zaki yi. Mukuma zamu idar miki, dan ke kamar y’ace a cikin gidan, Sabida Sultan Ash.”
D’aga mata hannu Nannah tayi ta haɗiye maganar cikin girmamawa, duk sai naji ni banbarakwai. Wayata na ciro na fara niman Ummi wayar akashe, sai na nimo Abba shima haka, a dame na kalli Nannah nace.
“Nah wayarsu bata shiga.”
“Ki duba Dudu.”
Shima da nasaka ban same shi ba, sai da na gwada sau uku kafin nasame shi a sakalce nace mishi.
“Dudu!!! Me yasa wayarku yaki shiga ne? Tun ɗazun nike nimanku.”
Muryanshi a sanyayye yace.
“Kiyi hakuri kinsan jiya, wayar Ummi ta faɗa uwa. Na Abba ina ga yasa a chargi.”
“Toh yayi kyau! Kana asibitine ina son kiran Dr, ko ya shiga tiyata ne?”
“Ohh! Sorry dr ya bani sako na gaya miki kan cewa sun kai shugaban kasa India ba lafiya sosai zasu ɗauki dogon lokaci yayita nimanki yau bai same ki ba, amma yace na gaya miki bazaki jinsh ba, sai Shugaban kasa ya sami sauki Insha Allah.”
Jikina ne yayi matuƙar sanƴi nace.
“Shine bazai kirani ba! Ok Allah ya dawo dasu lafiya kace ina gaida Ummina da sauran Yan gidan.”
“Toh zasu ji, kishafa min kan My lovely kids.”
“Hmm” na iya ce mishi dan jikina ya bani suna ɓoye min wani abu amma bani da hujja akan haka, sai dai taya Dr zaiyi tafiƴa bai gaya min ba anya hankali zai ɗauka.
Haka na watsar da zance na mikawa Nannah wayarta,Girgiza kanta tayi tace.
“Ki rike a gurinki”
“Thank You Nah.”
Karamin murmushi tayi sannan ta mike nima nabi bayanta, masu kula da yaran suka rufa mana baya, Shashin Sultan AbdulMuttalib bini Abu Safyanu, shashine mai girma me tattare da kayan k’awa da ado tare da kwalliya irinta Sarakunar larabawa, faɗar yanayin shashin tankar lalata lokaci ne, sabida iya tsari da kƴau shashin sarki AbdulMuttalib yayi, mun same shi tare da ahalin gidan bani ɗaya suna zaune.
Muna shiga wata babba baiwa tare da wasu bayin suka fara gud’a irintasu, harshensu suƙe kaɗawa, tare da ɗan bubuga baki.
Kallona Nannah tayi cikin nutsuwa tace.
“Me zaki bawa masu miki maraba da zuwa, masarauta na takwas a cikin Nahiyar larabawa,”
Duk sai na diriri ce. Ma rasa me zan basu, kawai sai na shiga cire awarwaron zinarin da kuma wani irin zobe me haɗe da sarka tare da abin wuyar, yan kunnaye, sarka kafa da zubunarsu na cire na mika masu shi da hannu biyu.
Gud’a sosai aka saka tare da, sake sauti irinta kidansu na larabawa, suka shiga cewa.
“Tarihi ya maimaita kanshi. Yau Mun amshi Sarauniya ta uku na daular Hashmiyya Sarauniya Safinatu Binti Badar Bni Ibrahim Kyari, kin shiga kundin tarihin masarautar Oman. Dan kece ta uku da tabada kyautar kayan adonta ta fanshi kimarta a hannun Bayin da suka tarɓeta, Sarauniya Jasmin Matar Sarki Yasir da tazo ganin Sarauniya Nana Asma’u irin kyautar da tabawa bayi kenan, sai Sarauniya Nana Asma’u itama tabada wannan kyautar ga Baiwarta Azrah a masarautar Jordan wannan abin yazame me muku tarihi dan duk wacce zata zama sarauniyar gobe toh sai tayi wannan makamancin kyautar mungode kuma a kema za a baki kyauta masu daraja a duniya”
Tsabar tsoro da firgici kamar zuciyata zata dirko daga kirjina zuwa waje, sabida kaɗuwar da nayi. *Sarauniyar Gobe? Tarihi ya mai maita kanshi? Na shiga uku Hameed ɗina*
A ɗimauce na ɗago kaina sai arba nayi da wasu manyan tire har guda biyu ɗ’aya shake yake da Lu’ulu’u wato diamond wadda akayi wani abin wuya da tsayinshi daga wuyata har kirjina haɗe da yan kunnaye da zubunarshi, da babban abin hannunsa. Daga Amirah Zahra….
😬😡 *Koda wasa kubar tunanin Tarihi zai maimaita kanshin dan Feener Rabon Dr ce heee😎😏😒*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 25 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah….
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
_Allah ya kyauta hmm 😹😹😂 Wuya makarantar Kare: Godiya ga MJ 2 paid grp inayin kowani member na cikin grp ɗin da sadaukarwa da kuka min😍😘_
Page.٤١-41
Shiru nayi ina tunanin toh taya zan fara, shin ta ina zan fara nan da nan na takura kaina da tunani, kafin wani lokaci ciwon kai ya sakoni a gaba, ajiye kome nayi nace daga baya na duba alamarin.
***
Jikin Dr da sauki sosai don har ya farka, a hankali yake magana sabida harbin ya taɓa zuciyarshi dole ya kiyayye duk abinda zai yi dole yayi cikin nutsuwa da takatsantsar.
Sati biyu kenan da aikin kenan, kuma za ace anyi nasara tunda ga alamu sun tabbata, India suna cikin jerin kasashen da likitotinsu suka iya aikin zuciya da koda, shi yasa mutane suka fiya damuwa da zuwa can. A yanzun dai yana kwance ne. Za aiya cewa Alhamdulillah tunda kome nashi lafiya.
***
Jordan.
……..
Shiru Fadar tayi sakamakon mahawaran da ake tsakanin Magoya bayan Abu Zarri da Ukshe.
Can wani daga cikin tsofin masarautar ya mike ya fara magana da cewa.
“Dole D’ayanku ya hakura d’aya yayi mulki na tsawon shekara d’aya in yaso wata shekara wani ya karɓa yayi shekara d’aya. Wannan shine kad’ai shawaran da zan baku matuƙar kuka amince toh ba makawa za asami zaman lafiya da fahimtar juna idan kuka k’i za a fuskanshi zubda jini a tsakaninku, mu kuma bama fatan nulkin yafita daga cikin Banu Hashim dan yin haka tankar kwarawa Makiyan Allah karfine, don Allah ku dubi maganata da fuskar tausassawa bata fuskar kausassawa ba. Idan kuma kunga bazaku iya hakuri ba toh sai dai mu dawo da me guri gurinsa.
“Kai!!! Tsohon kwano Wallahi babu wanda ya isa ɗare wancan kujeran sai ni ko Ubana ne yace zai zaune kujeran sai na aikashi garin da ba a dawowa Wallahi kuma na kara maka da tallahi ni Marhum sai na zama sarki na biyar a cikin jordan. Kamar yadda aka kashe min d’ana ya tabbata haka zamana a wancan kujeran ya tabbata.”
Cewar Marhum wanda shigowarshi kenan cikin Fadar, ya kuma jiyo abinda Tsohon yake fad’a.
Zai wucce inda kujeran yake, D’an Uwanshi kaninshi wato Amir Uzaif wanda aka bawa Matsayin Mahaifinsu Ukshe, waziri yayi maza yasha gabanshi tare da girgiza mishi kai yace.
“Wannan kujeran ɗauke take da jinin Adilai, babu fajiri ko fasikin da ya isa hawarta ya zauna lafiya in ma daga sarkine ko zuri’arsa ba zasu taɓa zama lafiya ba, shekaru dubu d’aya da hamsin bayan wafatin manzon Allah larabawa da kabilu daban daban sunzo kuma sun kafa daula amma dake babu adalci basu kai labari ba, har zuwa lokacin da Kabilar Banu Hussein suka amshi mulki aka kifar dasu, dukda musulmai ne bai hana su jagoranci mulkin zalinci ba. A sanadin zalincinsu Yahudawa suka amshi kasar da karfin tsiya.”
Kallon cikin idanunshi yayi cikin nutsuwa yace.
“Shekara ashirin d’aya Musulman jordan sukayi suna fuskartan Azaba da iziya daga Yahudawa Isra’ila.”
Takawa yayi gabanshi cikin jin zafi da kuma kishin kabilarshi da Hashim, karkace kanshi yayi cikin ɓacin rai yace.
“Idan kaga na barka ka jagoranci jordan Numfashina ya katse daga doran kasa, amma matukar ina numfasawa Jordan ta Muh’ad Ashraf ce dashi da duk abinda zai haifa wannan itace alkawarina da na ɗauka na kare wancan kujeran, karku manta su Masoya da Makiya haihuwarsu ake akan turba mabanbanta, haka Nasara da Faɗuwa samar dasu ake daga jinsin D’auk’ak’a.
Yau ya faɗi yaja da baya…”
“Uzaifa!!!” Ukshe ya daka mishi tsawa har sai da fadar ta amsa.
“A’A baba! Karka fara kun kirkiri kiyayya kuya kuya, haka zalika kune kuka kafa tarihi, dole yasa aka haifi me shafeta, ita fansa kishiyarta ramuwa ce, na rantse da Allah bazan taɓa barin koda kiyashine ya kusanci wancan kujeran kuma da zaran an sake Ashraf zan dawo..”‘”
“Sai kasheka!!” inji Narhum,
“Ya isa!!!” Ukshe ya daka musu tsawa cikin ɓacin rai yace.
“Ku same ni a gida”
“Kuma nasami labarin an sake Irfan na zarta da duk wanda yaga Irfan ya kashe shi.” inji Uzaif.
“Wai kai waye ya tsaya maka da zaka bada umarni mubi! Ko shi wanda kake karewa ne ya baka kuɗi ka kare shi? Nawa ya baka? Nawa ƴa saye kA? Wallahi naji bakin cikin haihuwarmu a ciki ɗaya, nayi alwadar zamanka d’an uwana kuma da kai da Ashraf nine ajalinku.”
“Kace nawa aka saƴe ni! Nawa ya bani, toh bari na tuna maka wani abinda baka sani ba ko nace ka manta, Shi d’aya aka haife shi, kuma kabilarshi suka masa lakani da Al Amin, sabida gaskiyansa. Kishinsa K’uraishawa suke, dukda ya bijiro da wata addini bai hanasu yarda dashi ba, toh irin yardan da suka bashi alokacin da suke kiranshi Al Amin kasan meye sunanshi? Itace ake kira da Kishin kabila. Wallahi idan bakayi da gaske ba zaka mutu.”
“Ni kakr gayawa Magana son ranka! Eyye sai na kasheka.”
Dakyar aka shiga tsakaninsu, kowa ya jinjina wannan kasadar na Uzaif sabida kishin kabilarsa da kuma yarda da Ashraf da ita kanta daular ƴa bada rayuwarsa kuma ashirye yake ya bada rayuwarsa dan cigaban masarautar.
Janshi Ammar yayi cikin rarrashi yace.
“Haba Uzaif me yasa ka zama mara hakuri ne. Mulkin jordan ko Ashraf yana nan ko baya nan Allah zai cigaba da kare masarautar, bai dace kayi wasa da rayuwarka ba, idan yau aka kasheka ya kake so Meenar tayi da yaranka.”
Idanunshine suka cika da kwalla wanda suka sami damar saukowa, yace.
“Kasan kama Ashraf da akayi da Hannun Mahaifina da D’an uwana, taya zuciyata zata yafe min abinda suka aikata, tunda kaga Sabida mace Ashraf ya bar masarautar nan ga abinda suƙa masa, toh tabbas bazai kuma dawowa ba, idan ba wani ikon Allah Ashraf yayi fushi damu kenan”
“A’a zai dawo Insha Allah, muyi koƙarin ganin mu daidaita wasu abubuwan in yaso ana sake shi sai muje mu dawo dashi.”
Juyawa yayi yabar Ammar a gurin. Ya mafita daga cikin Fadar gidansu Ghaniyu yaje, yaga gidan na kone babu kome a ciki, kwallar tausayi da bakin cikin kasancewarshi D’an Ukshe ne ya zubo mishi dan yaƴi Imani da Allah da sa hannun Mahaifinsa.”
“Hmm! Mulkin zalinci da ake gudanarwa a kasar nan Allah ya kawo mana ɗauki dan mun rasa gane waye sarki waye yan baran danshi, tunda muke bamu taɓa ganin fuskar sarkinmu ba, mudau muna bin azalimai kawai Allah ka kawo mana agaji.”
Shiru Uzaif yayi jikinshi na kara mutuwa, juyawa yayi ya kalli tsohon. Wanda yake cike da wahala, dole yaja kafarshi zai bar gurin tsohon yace.
“Ku kula da kyau dan akwai masu shirin ganin masarautar Banu Hashim ta wargaje sabida rashin adalcinku.”
Tafiya tsohon yayi yaki bawa Uzaif damar ya masa magana.
Haka ya gama ɓata lokacinsa ya bar gurin.
***
Oman….
Ina jin yaran na tsalla ihu nayi banza dasu, dan ko jiya Sai da Natasha tazo ta ɗaukesu bata dawo dasu ba sai da jikin Aanih yayi zafi ta dawo min dasu. Ban da ikon hanawa da zasu ce min nice bare kuma bakar fata ban isa rabasu da jininsu ba.
Shi yasa yanzun ma da suka dawo min da Aamih tana kuka naki kulasu, sai ma gyara kwanciyana da nayi, bawai dan bana jin kukan ba sai dai dole na koyawa kaina share kukansu, sabida nasan nan gaba dasu za ayi amfnin cutar dani, tunda gashi an fara za a ɗauke su karfi da yaji a tafi dasu. Suna kuka amna na fahimci basa kai yaran gurin da Nannah take dan bata kaunar jin kukansu itama, cike da jik haushi na mike na zauna ina karewa Aamih kallo. Dan takaici take bani, inda aka sasu kuka daban ni da suka zo suna min daban. Jawota nayi ta fasa wani irin kara tana shiɗewa. Da sauri nayi kanta tare da cire mata. Zaro idanuna nayi ganin yadda kafadarta ya kumbura.
Kuka ne ya kwace min, cikin tausayawa nake kallonta. Duba Aanih nayi itama hannunta dai dai gwiwar hannunta a kumbure, tana kuka ɗaukarsu naƴi na fita dasu zuwa ɗakin Nannah wacce take zaune ana tirara mata gashinta, tana ganina ta mike da sauri ta amshi Aanih tace.
“Safinatu meye yasami Maryam da Asma’u.”
Bakina ya gaza furta kome girgiza kaina nake cikin kuka. Bata iya cewa kome ba, ta kalle me tirara mata gashi, ɗaukar wayarta tayi ta mika mata, a hankali tashiga lalubar number can ta manna a kunne tace.
“Yanzun nake son ganinka.”
Kashe kiran tayi sannan ta zuba min ido cikin ɓacin rai tace.
“Me ya faru dasu?”
Har na buɗe bakina zan gaya mata gaskiya sai kuma wani tunani yazo min da zaran na faɗa ba yarda zatayi ba, tunda iyakata kawo minsu suke bazance ga abinda ake musu ba. Sai nace mata,
“Faɗowa sukayi daga gado!”
Sunkuyar da kaina nayi, kallona tayi cikin rashin yarda tace.
“Toh daga yau idan kun kwana acan kuzo nan ku zauna sai lokacin kwanciya yayi kukoma.”
Sam banji daɗin haka ba, amma babu yadda na iya tunda tafini Iko da yaran dan haka na gyaɗa mata kai alamun amincewa. Muna haka likitan yazo ya dubasu nan ya gano gocewa ce, ya musu gyaran amma sunsha kuka, ana gama musu na shigar dasu cikin d’akinta na basu nono sai da suka koshi har sun fara barci sai ga Natasha tashigo, da uban gadaranta tazo zata ɗauki yaran na dakatar da ita, ta hanyar cewa.
“Kinzo ki karasa min sune wanda kukayi bai isheku ba sai kin kara da wani, karki kure hakurina.”
Cike da rashin kunya ta kalli tsakar idanuna tace.
“Kinsamu ma ana ɗaukar shegun yaranki marasa daraja a cikin msarautarmu, idan kika kuskura masarautar jordan tasan da ke yanke miki wancan siririn wuyartaki zasu yi, banza karƴa mara daraja.”
Kura mata ido nayi bansan me zan faɗa mata ba. Amma ina kallon yadda ran Nannah ya ɓaci dan tashigo lokacin da Natasha take zagin gudan jininta, har da dalilin haka naki magana.
“Natah!!! A razane suka juya ita da Kawarta Amah, jikinsu na rawa matsa musu tayi suka wucce. Itama tabi bayansu, har cikin gidan sai da tayi musu tass sannan ta gargaɗesu akaina sannan tace.
“Yara bazan rabaku dasu ba. Amma Uwarsu basa’arku bace, nice na hana maganarki da Ashraf ba Binti ba, kar na kuma ganinki a gurinta……
😇😇😇😇
*Inayinki Mommy Sayeed keda sauran…..Mom Abul ƙema na gaisheki*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 19 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah….
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Page.٤٢-42
“Idan kuwa kika bari na kuma kamaki da laifi makamancin haka toh raina zai ɓaci kuma zan hasala, ita ɗin bakuwarmu ce kar na kuma ji kar na kuma gani.”
Tana gama faɗar haka ta juya abinta dama faɗar ce ta kawota kuma ta gama, nima bata kyale ni ba da tashigo.
“Me yasa baki rama ba? Eyee bata kai Batul ba sa’ar Khalil ce dan haka daga yau duk wanda ya taɓa ki karki kyaleshi idan kuma na samu an taɓaki kinyi shiru zan baki mamaki.”
Tana gama faɗar haka ta fito tabarni ina fama da yaran, karshe da taji kukansu yayi yawa ne tashigo ganin duk na rasa yadda zanyi dasu yasata taimaka min da ɗaukar Maryam, muna rarrashinsu har suka samu barci.
***
Wani irin d’akine me cike da tarkace kaman na bokanci, Juya musu baya yayi cikin ɓacin rai yace.
“Kowani wayewan gari ina kara jin nisar dake tsakanina da ita, itace burin zuciyata amma mutuwa tayiwa gangan jikina iya ka da ita, me yasa kuka dawo dani bayan can yafe dacewa dani? Bazan iya hakura da ita ba dole mutafi tare dole tabini mu cigaba da rayuwarmu a can.”
“Ranka ya daɗe ai”
“Karka min kome Nuratu! Kece kika dawo dani idan narasa Safinah.”
Daga haka ya koma jikin Wani abu ya kwanta.
Fitowa sukayi Hajiya Nuratu ta kalle Kawarta Salmah a dame tace.
“Salmah! Nayi danasanin tadda wannan alamarin gashi yana niman zame min alkakai”
“Karki damu Nuratu zamu san abinyi babu abinda zai faru sannan kiyi ƙoƙarin ganin Yarinyar ta dawo.”
Gyaɗa kanta tayi dan ta gamsu da shawarar da Kawarta ta bata, har gida suka ta sauke Salmah, sannan ta wucce gida. Jikinta a mace sabida bata san ta yadda zatawa Abba Magana ba, dan tana gudun kar ya d’agota. Dan haka ta ajiye a ranta zuwa ranar girkinta ta masa magana.
***
Duk yadda naso kauda kaina akan wancan fitsarariyar yarinyar na kasa, domin iskanci take min a bayan idanun mutane, ranarda ta kaini bango munxo cin Abinci Nannah tafi nima mana visa, zamu tafi Umra daga nan ita zata duba yaronta.
Ni da yarana muka fito gurin shan iska, ashe ita da kawayenta suna can gefen lambun da muka zo, ina rike da wayar da Nannah ta bar min, yau ma gwada sa’ata nake ko zan sami Numbersa. Amma shiru takaici ya ishe ni.
Aamih ce naga tana kokarin mikewa tsaye bakina a sake, dan naga basuyi wani rarrafe ba, dan yanzun ne ma Aanih take ja, ita kuma Aamih take rarrafen zaki. Abin alajabi sai gashi ta mike tsaye, aikuwa ta fashe da dariya, shiru nayi ina lissafin wataninta, sai naga basu wucce wata bakwai ba, dan yanzun kusan watanmu biyi kenan À Oman. Ai ganin haka itama Aanih ta shiga kokarin mikewa dariya na musu tare da rungumesu, ina cewa.
“Aanih kiyi hakuri kawai Aamih ta fara, tunda itace Babba.”
Ihun Aamih tayi tare da rungume ni, ɗago kaina nayi ina mamakin. Ashe Natasha ce ta kawayenta. K’amkame ni yaran sukayi suna kuka, murmushi nai tare da rungumesu.
“Ayya! Yaran karuwa kuna tsoronmu ko? Karku damu uwarku ce zata iya ja muku dan tana koƙarin shiga hurumin Sultan Ashraf, dan shi ɗin mallakina ne, idan kuma kikayi gigin shiga gonata toh tabbas zanyi abu, kiyi tunanin irin wuyar da kika sha. Mana na haihuwarsu saura wata d’aya a sakoshi idan na kuskura naganki dashi.”
K’ak’aɓe hannunta tayi sannan ta harɗesu a kirjinta, a gadarance tace min.
“Zan ɓatar dasu.”
Shiru nayi jikina na kara sanyi, har tabar gurin ban iyace Uffan ba sai da masu tayani renon yaran suka zo sannan na mike bayan sun ɗauki yaran nabi bayansu. Tun daga wannan lokaci nake gujewa kaina abinda zaisa Nannah haɗi da Ashraf.
Bayan kwana biyar muka tattara sai macca, inda muka sauka a wani gida mallakin sarki Abdul Muttalib, daga nan zuwa harami ba nisa tafiyar minti goma ce. Tunda muka shiga garin muka isa idan muka tafi Ibada bama dawowa sai inzamu ci abinci. Idan muka dawo kuma bamu sake fita sai lokaci la’asar.
Daga maka muka wucce Madina ziyara, daga can kuma Nannah tasani a gaba muka koma riyad acan ake rufe dashi.
Kamar nace bazanje ba haka nake ji amna babu yadda na iya, bamu isa da wuri ba. Sai biyar dan haka bazamu same zuwa kurkukun ba, dole sai washi gari..
A masaukinmu nida yarana Masu renonsu har su biyu, Natasha da Nannah a ɗaki ɗaya,
……. Ina kwance naji karan shigowar sako.
*Hey Beauty ya kike*
Zubur na mike zaune ina zare idanuna gwada kiran wayar nayi yaki d’agawa, bansan lokacin da kuka ya kwace min b, da nasake kiran nabiyu ya dauka, yana jin shashkar kukana. Kashe kiran yayi ya kuma turo min da sako.
*Toh ya isa mana! Ina tare da shugaban kasa kinga ba halin nayi magana da kowa.*
Cikin kuka na tura mishi da cewa.
*Amma me yasa ka kashe kiranka kasan ydda nake ji kuwa! Ji nayi bani da farin ciki don Allah karka hukuntani da laifin da bansan nayi ba.*
*Beauty ba haka bane ina cike da kewarki, musaman cutie lips ɗinki nayi kewarsu, ji nake kamar nafito ta waya na cigaba da cinye bakin da me bakin.*
Zaro idanu nayi tare da kallonsu Aanih da suke barci kunya ta kamani na tura mishi.
*Baby! Ka fara bani tsoro da kunya don Allah bar maganar haka*
Dariya ya turo min tare da cewa.
*😹😂 Beauty ai dole kiji tsoro nidai wallahi duk ranarda kika shigo hannuna, zaki faɗi gaskiyarki domin kuwa sai na cinye ba iya, kuma bazan koshi dake ba, hmm karki sani faɗar maganar da zanji kunya nan gaba.”
*🙈🙉🙊 Wayyo Allah na don Allah bar maganar haka, dan zaka iya sani daina kulaka dan ni kuma kunya nake ji.*
*Kunyar me? Ai ni bana fatan kiji kunyata, idan likita irina yaji kunya toh kawai ya ajiye aikinsa, dan kunya batashi bace! Safinah kece macen da zuciyata ta buɗewa kofarta kika shiga, don Allah ki rike min ki dan kece nake jin zan iya raba farin ciki dake Ina miki so da duk zuciyata.”
*Baby!!!”
Shiru yayi sai na rasa abinda zance mishi nace .
*Don Allah muyi magana ta Whatsp.*
*Ba yanzun ba Baby dan nasan video call zaki ce muyi, daga hiranmu na yanzun na fara jin bakon yanayi a jikina musaman na tuna da sumbatar nan me zafi jinina na ta fasa komena yana harbawa fiye da kima plss karki kirani dan zan iya shiga wani hali.*
Wallahi bansan lokacin da tsoro ya kamani ba na tura mishi da *Hmm mukwana lafiya ni wallahi tsoro kake bani.*
Dariya ta turo min tare da cewa.
*Sai ma kin shiga hannun namijin duniya kiga yadda ake jiyar da mace soyayya da jin daɗi toh nan ne zaki fahimci tsoronki na gaskiya*
Sakon na shigowa ina kashe wayata, ina zan iya da manyan magana sam dr bai da kunya yanzun, dan ma baya tare da hajja wallahi sai ya lalace dan ita magana bai mata nauyi ko laushi.
……….
Washi gari tun asuba da na kunna wayata nake ganin sakonshi. Murmushi nayi cikin jin daɗi nake walwala, har sai da Nannah ta fahimci ina cikin farin cikin sai ta zata ko dan zamu je ganin Ashraf ne. Itama sai ta kama murna, bayan mun karya ne aka kwashemu sai can tare da lawyershi.
Koda muka isa ajiyemu akayi na wani lokaci kafin aka fito dashi.
Wato tsarin gidan yarin da ban mamaki yake, akwai gefen masu mugayen laifi wanda za a zarta musu da hukuncin Shika(😜) akwai gefen masu karamin laifi na iya waadi, akwai kuma gefen irinsu Ashraf, zan iya cewa shi a gidan Yaran an ajiyeshi ne dan baya tsinana kome sai dai a girka a bashi ya kwashi gara, shifa tsabar gata kome yi masa ake gashi ana turo mishi kuɗi da wasu abubuwan bukata, sabida yana da galihu. Tunda muka isa inda zamu ganshi kaina ke sunkuye kirjina na bugawa, ga wani irin tsoro da ya mamayeni.
Sallamarshi ya dawo dani daga duniyar da na nutsa, cikin farin ciki Nannah taje ta rungume shi tare da sumbatar goshinsa, murmushi yayi wanda yasa dimple ɗinshi luɓawa yace..
“Ammihna ai da kun hakura nan da sati biyu zan dawo.”
Girgiza kai tayi, cikin farin ciki tace.
“Idan na mutu kafin lokacin fa?”
Karan Aamih yasashi kallon inda muke.
*Sarki ya tabbata ga Ubangijin makagin halittar farko da na karshe*
Abinda ya faɗa kenan a ranshi sakamakon tozalin da yayi da Aamih takwaran Nannah, wacce suke fitinannen kama dashi, karasowa yayi har inda muke yasaka hannunshi ya ɗauketa dan tana kan cinyata..
Ko kallona baiyi ba, ya rungume yarshi, lafewa tayi a jikinshi har tana lumshe idanunta.
“Maryam itama baka ganta ba.”
Dan ita tana hannun Natasha ce, juyawa yayi ya amsheta tare da rungumesu a kirjinshi, kwalla na zuba mishi na tausayin yaran, yace.
“Ammihna! Ina sonsu fiyye da kome a duniya, sai dai kaddararsu tazo a hangunce, amma haka bazai hanani nuna musu kauna ba.”
Sai ya sumbaci wannan ya sumbaci wannan cikin zakalewa Natasha tace.
“Sultan nima zan tayaka kaunarsu .”
Da wutsiyar ido ya kalleni yaga kaina a sunkuye ina fama da waya, mamakine ya kamashi wai kowa yana murnan ganinshi amma ni hankalina yana kan waya, zama yayi suka fara hira. Can Nannah tace.
“Binti! Baki baku gaisa da Ubangidanki ba”
D’ago kai nayi cikin nutsuwa nace.
“Nah! Ban lura bane muna magana da Dr ne.” sannan na ɗan kalle shi nace..
“Sannu!!”
Banza yayi dani kamar badashi nake ba, sai da Nannah tace mishi.
“Habibi! Binti tana gaidaka.”
“Ammihna! Yaran nan sun kai na yayewa ne?”
“Baka gaji bane Umminsu tana gaisheka”
B’ata fuska yaƴi sannan ya kalleta ya kuma kalle ni yace..
“Bafa gurina tazo ba! Tunda tazo ta rungume phone ɗinta”
Da mamaki na d’ago kaina yadda take iya dogon magana, ba tare da gajiyawa ba, shi da yazo ya ɗauki y’arshi ko kallona baiyi ba sai nice da nace masa sannu zaki amsawa, tsuke fuskana nayi tare da haɗe girana. Sakamakon
Jin tana lallashinsa wai ya amsa gaisuwata kodan yaran,
“Yawwa”
Yace min, satar kallonsk.hi nayi ya kara girma zance kenan dan yanzun yafi da, sannan ga Uban kasumbar da ya bari, sai fuskarshi tayi kallar ta mage.
D’an karamin pink lips ɗinshi ya ɗaura a goshin Aanih ya sumbata, kauda kaina nayi naga sakon Dr har goma. Na shiga bashi amsa muna hira, jin dariyan Aamih sosai take kyalkyalewa, wato idan ba abin dariya ba yaran nan basa min dariya, amma yau d’aya da suka ganshi sun manta dani, d’ago kai nayi muka yi ido biyu mukayi dashi, sake haɗe rai nayi tare da hararanshi da wutsiyar idona dan sai yanzun,
Kauda ƙanshi yayi cike da mamaki *Yaushe yarinyar nan idonta ya buɗe?* yake tambayar kanshi.
(Ni kuwa nace tun ranar da akayi zunguran farko😯😂)
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 18 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Page.٤٣-43
Mamaki ne ya kuma kashe shi lokacin da muka haɗa ido na murguɗa bakina, sai da ya zaro ido waje cike da alajabi.
*Yaushe reni ya shiga tsakannmu? Yarinyar da duƙ haɗiwarmu sai ta..*
“Habi tunanin me kake? Me kake so a tanadar maka idan ka dawo.”
Lumshe idanunshi yayi tare da yin shiru, mikewa yayi ya kawo min yarinyar wacce take kananun kukan niman ruwa kp nono kallon cikin idanuna yayi nayi maza na kauda kaina yace.
“Amminha! Duƙ abinda aka tanadar min zanso, a ciki kuwa har da y’antattun kajin waje.”
Sai da ya kalli cikin idanuna, ya ajiye min yariyar akan cinyata, ya kusanto da fuskarshi kamar zai haɗa da nawa, nayi baya dashi, garin rike yarinyar hannunmu ya haɗu da juna, da sauri muka kalli juna. Sabida wani spark ɗin da muka ji lokaci guda. Cikin idanuna yake kallo sosai kafin yace.
“Ni kika murguwa baki?”
Sunkuyar da kaina nayi, kawai jin bakinshi nayi a goshina, cikin sauri na d’ago da kaina, aikuwa sai ga bakinmu ya haɗe, laɓɓena na kasa ya cafke. Da sauri na tureshi.
Abin mamaki sai ya kai hannunshi ya rufe idonshi d’aya tare da kane min d’aya irin zamu haɗu.
Ran Natasha ya baci kuwa Nannah kan bata san iskancin da d’anta yake min ba sai da taga na tureshi ta kalle da sauri tace.
“Binti! Lafiya?”
Kamar zanyi kuka na mike na fita da sauri, murmushi ya sake zuciyarshi sawai.
Jijjigani Nannah tayi na dawo daga duniyar tunanin da nashi, gani nayi har ya koma. Dafe goshina naƴi, tare da kallon Nannah da take rike da yarinyar da ya karɓa, *Wai Dama tunani na shiga duk abinda ya faru ba gaskiya bane?*
Wai me yakaini yin tunanin abinda bai faru ba, kuma duk abinda na gani ashe a tunanine, karamin tsaki nayi. Tare da share zancenshi a raina.
Har muka dawo, tunda muka koma macca muka shiga sayayyar tsaraba ni wanda zan kai gida ne, kwanarmu sha tara muka dawo Oman a cikin kwanakin dawowarshi munci kwana huɗu dan saura goma ya dawo.
Wani irin hidima ake a cikin masarautar har da canza fentin, gefe guda kuwa nima muna cinye junarmu da soyayya, dan har Dr yayi min alkawarin zai zo muwucce gida tare, dan haka nafi kowa murna.
***
Ranar wata alhamis Muh’d Ashraf ya diro garin Oman tare da wasu daga cikin manyan masarautar, wani irin hidima ake sai ka rantse biki ake, duk sunsha ƙwalliya ban dani da iyata riga da zani ta atamfar Vlisco ce a jikina, idan baka lura ba zaka rantse doguwar riga ce. Me zip a gaba, kayan sun ɗauki jikina ya zauna dis. Ina zaune a falorn Nannah ya shigo, hankalina yana kan hira da Dr wanda yace min jibi yana hanya. Dan haka na maida hankalina muka buge da hira.
Kukan Aanih yasani d’ago kaina, ganinsu nayi tare yana rungume da ita, dake Aamih tana barci kusadani. Suna shiga sai ga Nannah tafito ranta a matuƙar ɓace tace.
“Safinah! Taya zaki bar yarinya ta tafi gurin kayan kallo badan Babanta ya shigo aƙan lokaci ba ai Allah kadai yasan abinda zai faru.”
Shiru nayi kaina a sunkuye ina mamakinsa daga zuwa sai haɗa guri.
“Kiyi hakuri!”
Iya abinda na iya cewa kenan.
“Ki kiyayye gaba!”
Tana gama faɗar haka ta juya tabarni buɗe da bakina, ina jinjina irin kaunar da sukewa yaran, bayan kamar minti talatin sai gasu sun fito tare.
“Safinah! Hmm ko zaki samarwa Habibi abinda zai cine!”
Kan uban can lallai ma nice zan girka mishi abinda zai ci, kamar zan fasa ihu na mike sai wani cin magani yake, ajiyewa Nannah yarinyar yayi ya shige ɗakinshi dake kusada nata, yana shiga ya taradda falo madaidaici, sai ɗakuna biyu sannan ya shige ɗaya, zubewa yayi a gadon ya huta sannan ya mike tare da cire rigar jikinshi, singlet ɗinsa ya cire tare da zame dogon wandon jeans ɗinsa. Kasa sannan ya zauna a hankali yazare kafar, safe goshinsa yayi ya mike tare da buɗe sif ɗin kayanshi ya ciro farar jallabiya ya saka, sannan ya fito inda Nannah take zama yayi kamat bazai ce kome ba, ya ɗauki yarshi ya ɗaura a kirjinshi yana shafa bayanta.
“Hm ruwan wanka Ammih!”
Kura mishi ido tayi ciƙe da soyayyar gudan jininta, har ta buɗi baki zata kirani sai ga Natasha ta shigo.
“Yawwa Nata! Kije ɗaki…”
“Ba ita mamar yaran nan” daga haka ya lumshe idanunshi, cikin mamaki tace.
“Amma Habibi kai kace ta girka maka abinci ko? Tana girkin zata.”
“Ammihna! Ita ɗin baiwata ce!” ya faɗa kasa kasa da murya dan kar Natasha taji ina har taji abinda yace.
“Binti!!”
Nannah ta kirani, da sauri na fito ina goge hannuna.
“Ki rage karfin gas ɗin ki shiga ɗakin Habibi ki haɗa mishi ruwan wanka.”
Kallonshi nayi kamar zanyi magana sai na fasa a raina kuwa cewa naƙe.
*Na shiga uku! Mulkin ma a ko ina sai an nunawa duniya kenan? Ince da shi yake haɗa abinshi wato ganin gabar banza ga yar bello badin tazo za a fara juyata kamar waina*
“Toh Nannah!”
Nace sannan na wucce kitchen na rage karfin wutar na wucce ɗakin.
Ina shigewa da yan mintuna ya mike da yar ya nufo ɗ’akin, yana shigowa ya kwantar da ita, lokacin ina cikin ban ɗakin, ina zuba masa sinadarin kamshi da gyara fatarshi, hankalina yayi nisa gurin karanta jawabin jikin wani kwalbar turaren wanka, ashe har ya shigo yana tsaye kugunshi ɗaure da towel. Ina gamawa na ajiye kwalbar tare da juyawa, ban san lokacin da naƴi baya zan faɗa cikin ruwan ba. Gyara tsayuwarshi yayi sannan ya shiga takowa, cikin tsiwa nace.
“Wallahi karka kuskura ka taɓa ni dan zan wanka maka mari! Ni karka maidani yar iska. Na gaya maka ka tsaya a gurin fa zan maka rashin Mutunci.”
Kunce towel ɗinsa yayi aikuwa na rufe idanuna da karfi tare da ɗauke numfashina. Bawai naga kome bane tsoron mugun gani ne yasani rufe idanu, shikam abinda yake gabanshi ya dame shi, ina jin ya shiga ruwan nayi maza na isa bakin kofa ina murɗa kofar, najita gam.
Karan key ɗin naji a bayana, juyawa nayi naga ya ajiyeta a gefe, ya nutsa a cikin ruwan ko fuskarshi baka iya hangowa.
A hankali na saɗaɗa naje gurin na kai hannuna da niyyar ɗaukowa, sai ji nayi an cafke hannuna.
“Ni kasake min hannuna! Wallahi zan maka rashin mutunci fa, ka sak.”
Famjan!!!! Ruwan ya fantsamu a ko ina, fidda kanshi yayi tare kallon inda sabon soso da sabulu yake, ko kiftawa idanunshi bayayi gurin kawai yake son na kalla.
Sharce ruwan fuskana nayi, na dubd shi cikin mugun ɓacin rai nace.
“Allah Ya isa min fasiki kawai! Yaro karami da kai amma ka iya shaiɗanci.”
Kokarin mikewa nake, amma mara mutunci ya rike ni, idanunshi a rufe, da karfi na ƙwace kaina tare da zabga mishi harara,
Dawo dani yayi da mugun karfi yace.
“Wanka zaki min! Idan kika ki kuwa! Hmm abinda zai biyo baya bazai miki daɗi ba.”
Tsorone ya kamani tunda ya faɗi haka tabbas kome zai iya faru, kwalla ce ta fara zuba daga idanuna, na mike tare da ɗauko shapoo da sauran abubuwan wanke kai, na zuba a kanshi. Na fara wanke mishi kanshi idanunshi a lumshe, duk tsoro ya cikani dan gani nake kamar wani abu zai min, sai da na gama wanke mishi kanshi. Sannan na cuɗe masa baya da kirjinshi, a nan ne ya buɗe ido yana kallon yadda nake cuɗashi, dukda ina jin yadda yake kallona, ni kuwa naki na kalle shi. Ina gamawa nayi maza nafita dan naga idan nabi na rashin kunyarsa tabbas zan ce na wanƙe, Y’ay’an gwaibarsa da ayabar.(😉)
Duk najike jagab, babban towel na ɗauka na juya mishi baya, ina rike da towel ɗin.
“Bani towel”
Kamar na fasa ihu haka nake ji. K’in juyawa nayi, har sai da ya fito dan yasan bazan taɓa juyawa ba, takowa yayi ya iso bayana ina jin numfashinsa a bayana, tsorone ya cika min ciki, saka hannunshi yayi, ya janyo ni jikinshi. Rawa jikina ya ɗauka sabida ina jin yadda kayan aiki ke taɓani.(😹😎)
Bai karɓa towel ɗin ba ya dai sanya hannunshi ɗaya a tsakanin cikina, cire hannunshi nayi na mika mishi towel ɗin, sannan na wucce jikin kofa da sauri. Shi ko a jikinshi ya ɗauro towel ɗin, wani drower dake ban ɗakin ya buɗe ya ɗauko towel, sai da ya tawo tare da matse ni kaɗan a jikin kofar ya lalluɓe hannuna ya mika min towel ɗin, sannan yasaka hannunshi ta cikina ya sanya ket ɗin kofar ya buɗe, sannan ya janye ni da jikin kofar ya fita yabarni a gurin, yana fitowa yasami Natasha a tsaye, tsabar miskilanci, kamar baiganta ba, ya zauna a bakin gadon hannunshi rike da karamin towel, yana goge kanshi na fito ɗaure da towel ɗin iya cinya, duk sai naji a muzanta, kamar zan juya ban ɗakin, dukda babu abinda ya shiga tsakaninmu amma babu wanda zai gannin a cikin wannan yanaƴi bai zargemu ba, fuuu tajuya zata fita.
“Tasha!!!”
Cak ta tsaya bata fita ba, kuma bata juya ba.
“Tunda ban isa ba jeki”
Kamar shashasha, ta juyo idanunta na zubd ruwa. Nuna mata cinyarsa yayi , cikin shagwaɓa da sakalci ta isa gabanshi, ta zauna a sanyayye.
Mikamata towel ɗin yayi cikin rawan jiki ta fara goge mishi, sai ga ja’iri ya ruko k’ugunta tare da kifa kanshi akan cikinta, komawa ban ɗaki nayi na saka kayana na ajiye mishi towel ɗinsa na fito nasamu Nannah bata falon ɗakina na nufa na shiga nayi sabon wanka. Sannan na cire kayan na wanke na raɓa akan ɗan karfen da nake shanya pants ɗina da bra. Karo na farko a rayuwata danaji ina sha’awar manyan Nono, dan nima na burge Dr, musaman irin shigar da Natasha tayi ya mugun burgeni dan har kana hango tsakanin manyan nonuwarta, nima dai nawan ba laifi, amma dole na nime wasu maganin koda namu na hausa, zan nima na fara sha. Ko zasu kara auki.
Fitowa nayi na ciro doguwar riga. Lemon green me manyan stones yana haɗe da hularsa, nasaka ban saka bra ba sai bon short da nasaka taciki, sannan na ɗan gyara fuskana na murza kwali. Ina gamawa na fito falo na sameshi da Natasha suna cin abinci….
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 17 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Page.٤٤-44
Wucce su naƴi naje na ɗauki Aamih da take kwance na wucce da ita ɗ’akina, muka kwanta barcine ya soma fisgana naji kiran sallah dole na mike na shiga ban ɗaki nayi alola.
Kukan Aamih naji na fito da sauri wanda yayi dai dai da shigowarsa shida jelarsa, ganin yarinyar a dungure yayi maza ya ɗauketa, tare da saɓata a kafaɗarshi yana jijjigata,.
Juyawa yayi ya kalle Natasha, take tafita ya juyo ƙaina. Yarinyar tana kafaɗarshi ya cigaba da shafa mata baya har tayi shiru, d’ago yayi yaga bakinta na zubda jini alamar taci da bakine, d’ago kanshi yayi. Ya zuba min idanunshi wadda suka kankance da zallar madarar masifa, kauda kaina nayi naje na ɗauki Hijab ɗina da sallayar.
Na shinfiɗa zan tadda sallah, ganin naki na kula shi balle har ya kai ga munyi fada, ya sashi juyawa ya fita a d’akin tare da yarinyar ni kuwa nayi sallahta a nutse. Ina idarwa wayata na kara, number Dr.
A gurguje nayi addu’a sannan na ɗauki kiran da na uku kenan.
Hira muka buɗe yi, ina lura da Ashraf sau biyu yana shigowa da yarinyar ganin yadda nake hira da shagwaɓa ga rigimar da nake tayiwa Dr yasashi koma D’akin Nannah ya ajiye mata Y’ar, ya zauna tana ta janshi da hira can ya kalleta sannan yace.
“Ammi!! Me yarinyar can take nufi da Yarana?”
(😎😏 Ji min wani kinibibi Safinarce Yarinya😒 zamu jone)
Fuskar Nannah da mamaki take kallonshi, domin share tantamarta tace mishi.
“Wacce yarinya kake nufi? Ai ko Natasha kake nufi?”
Gyara kwantar da kanshi yayi a sama kujera ya shareta. Sai da tasake nanatawa sannan ya d’an buɗe idanunshi yace.
“Mamar Yarana!”
Wani kallon renin hankali ta mishi tare da ɓata rai tace mishi.
“Safinarce yarinya? Bana son reni”
Ciki ciki yayi da fuska sannan yace mata.
“Afwa!”
Daga haka ya mike bai kuma magana ba ya bar falour, wasa wasa. Haka ya wuni ko abincin da zai ci yaki ci. Koda ya shiga ɗ’akinshi kin fitowa yayi. Har dare ni nazata ma ya fitane dan haka na fito wajen gidan ta dogon baranda na tsaya muna musayar kalamai da dr, wanda yace min ya kusan tasowa. Banda shagwaɓa bana mishi kome, shi kuwa sai rarrashina yake cikin harshen turanci nace masa.
“Idan kazo tare zamu koma ko? Ina kewar Ummina.”
“Karki damu idan nazo tare zamu koma, dan bazan taɓa tafiya na barki ba, kiyi shiru.”
“Taya zanyi shiru, bayan ina wata duniya kana wata duniya ni dai kazo mu tafi.”
Dariya yayi sosai sannan yace.
“Beauty! Idan nazo me zaki bani na tarɓa?”
“Baby me kake so? Fada ni kuma zan baka koma meye”
Dariya yayi sosai har da kyalkyalewa yace.
“Beauty! Just kiss i need!”
Kashe kiran nayi tare da rufe bakina, ina dariya cikin naji kamar ana kallona, da sauri na juya fuskarshi ba sauki kana ganinsa yadda ya ɓata rai sai ka rantse zaginsa akayi.
Zuwa yayi ya tsaya a gaba har ina jiyo hucin ɓacin ransa.
“Ni bazan miki iyaka da rayuwarki ba! Amma idan kika kuskura garin shirme wani abu ya same yarana wallahi sai na rufeki babu abinda ya dame ni.”
“Hahaha! Lallai kuwa yaran banza yaran wofi idan ka fasa rufe ni baka cika.” matse ni yayi jikinshi na rawa, kokarin kwace kaina nake amna na kasa, muryana na rawa nace.
“Bana cike da iskanci da ranshin kunya, idan baka rabu dani ba wallahi akan yaranka zan sauke.”
Ture ni yayi tare da barin guna, yaje ya kwashe yaranshi ya koma ɗakinsa dasu.
Taɓe bakina nayi sannan nace.
“Can dasu gada…. Zomo yaji kiɗar maharba.”
Nima ɗakina na shige na kwanta, abuna ko ba kome yau zanyi barci cikin salama babu shan nonon dare.
…… Cire kayana nayi na faɗa ban ɗaki nayo wanka sannan nazo nasaka kayan barcina sannan na gyara kwanciyata. Addu’a nayi na mike a gurin sannam na kashe wutar ɗakin nayi.
***
Cikin barci me nauyi naji ana ciro nonona waje, na zata mafarki nake, sai da naji ana murza nipples ɗina naji tsigar jikina ya mike, saka hannu nayi na kunna wutar ɗakin kirjina na bugawa.
Maza nayi naja bargon na rufe kirjina, cikin masifa nace.
“Wannan iskancin fa!?”
Kallon yaransa yayi tare da taɓe baki yace.
“Abincin yarana nazo abasu!”
Wani kallon banza da na mashi yasashi kauda kanshi, nace.
“Bazan bayar ba! Kaje ka basu na kirjinka, kuma Insha Allah na kusan tafiya nabar wannan masifar yaro karami dakai dan kasami duniya shine zaka addabi rayuwata da jaraba, har kana taɓani banza d’an iska kawai.”
Sauka yaƴo daga gadon ya fita, can sai gashi da madara a feeder, ya zauna ya basu suka sha, sannan ya kwashesu ya fita dasu, bai dawo ba sai can. Har na fara barci, kawai naji ana tsotse min nono (🙈🙊🙉 Dama ya aka kare da larabawa mayyun mata)
Ture shi nayi tare da kai mishi duka, ya d’ago fuskarshi da idanunshi cike da desire, matsawa yayi sosai. Sannan ya kai hannunshi zai kamoni na hantsila kafin na mike, ya rigani.
“Abincin yarana nazo sha musu! Tunda ni d’an iskane shi yasa zan tabbatar da haka.”
“Wallahi ka taɓani sai na jimaka ciwo.” na faɗa ina lalluɓo kwalbar ruwa, murmushi yayi tare da shafe fuskarshi yace.
“Zanso faruwar haka! Idan har kika iya dakatar dani, toh tabbas zan ya hakura mu barki da Allah idan kuma muka karɓa sai kiyi hakuri damu, dan ke baiwar Ubansu ce da kuɗinsa aka sayeki.”
Allah ya zata da wasa nake bazan iya make shi ba, sai da yazo zai rutse ni. Allah ya bani sa’a na make shi a goshi, rike gurin yayi. Yana murmushi ya tako har inda nake, yasaka hannunshi biyu ya fara balle botir ɗin rigarshi.
Kuka ne ya kwace min, ina girgiza mishi kainna fara tare da haɗe hannuna nace.
“Don Allah kayi hakuri! Iya abinda nake dashi ya rage min kenan, karka rabani da sauran abinda ya rage min, shi ɗaya kawai zan mallakawa mijin da zan aura don Allah kayi hakuri.”
Jifa yayi da rigar tare da sake murmushi jin daɗi zai yi maganin fitsara.
Aikuwa yayo kaina tare da kai hannunshi ya ɗagone na fasa ihu,, yayi maza ya rufe min bakina kuka nake ina dukanshi. Amma sai da ya cillani gadon yabi kaina ya zuba min karfinshi tare da d’aga rigana ya shiga tsotse nonon da karfin bala’i, ganin ina dukanshi tare da yakushinsa yasashi d’ago kanshi yace.
“Idan kika cigaba da dukana! Zan miki cin da sai kin kasa tsayuwa, iya abincin yarana nazo amsa, idan kuma aka ki ni zan caccaki yarinya da kayan aikina”
Shiru nayi ina jinshi sai da ya shanye tass ya mike, tare da cewa.
“Idan kika kuma zagina! Ba nonon zan sha ba, can zan sha.”
Tunda na kifa kaina nake kuka kaman raina zai fita, haka ya ficce a ɗakin hankalinshi kwance kamar wanda yazo yasha abin arziki.
Kusan kwana nayi ina kuka, ji nake kamar na mutu dan bakin ciki. Ina kwance har akayi kiran farko, na samu na tashi na gabatar da sallar nafilla.
Ina gurin zaune har aka shiga sallar asuba, na mike nayi ina idarwa naciro wayata a charge na kira Dudu, ina kuka tare da ce masa.
“Dudu! Kazo ka ɗauke ni na gaji.”
Yadda yaji nake kuka yayi masifar ɗ’aga mishi hankali.
“Kiyi shiru Didina! Gaya min me Ka miki”
Sabon kuka na rusa mishi ina cewa..
“Ni dai kazo na gaji”
“Toh ba Dr zai zo ba? Ki kwantar da hankalinki zan kirashi nace mishi ya tawo dake”
“Dudu ka gayawa Nannah kartace bazan dawo ba.”
“Wai niƙam Safinah meke faruwa ne?”
Ya tambaye ni damuwa, kuka nasake saka mishi sannan nace.
“Dudu! Kasan jiya yaron Nannah ya dawo, toh tunda yazo yaƙe min rashin d’a’a, dudu abin ba daɗi gani balle faɗa, don Allah kayi wani abu.”
Duk sai yaji ba daɗi, sam a duniya baya kaunar ganin na zubda ƙwalla, balle kuma yaji ina kuka me cin rai.
Kawai sai ya katse kiran.
…… Kaman ance d’aga kai kawai na ganshi a tsaye a bakin kofa, karasa shigowa yayi cike da izza da kuma takama, tunda na ganshi na takure guri guda tare da cusa kaina tsakankanin cinyata.
Yana zuwa ya kai hannunshi zai taɓa ni, na sauke wata irin ajiyar zuciya tare da ɓingirewa a dunkule nan.
Da sauri ya ɗago ni tare da girgiza fuskana, amma ban farka ba, kwantar dani yayi ya shiga banɗaki ya ɗako ruwa ruwa a wani ɗan abu yazo ya watsa min ban farka ba, sai da ya buɗe bakina yayita hura min iskan bakishi a firgice na farka, ina ganinshi akaina idanuna suƙa sake luuu zasu rufa yace.
“Wallahi kika kuma sume min sai nacinyeki tsaf.”
Lumshe idanuna nayi tare da kokuwa da numfashi, kuka na sakamishi na kauda kaina gefe naki kallonshi, sauka yayi a gadon ya fita.
…….. Karan wayata naji na lallaba na ɗauƙo sannan na kara a kunne na, sabida idanuna sun min nauyi.
“Beauty meke faru ne?” Dr ya kara tambayata, kuka nasaka nace.
“Hmm? Kawai kazo.”
Abinda nayi niyyar faɗa shine he try to rape me again, sai na tsinci kaina da rufa mishi asiri a matsayinshi na Uban yarana ko ba kome bai cancanci tozarci daga gareni ba, rigimarmu da ban kimarshi daban, kuma Dr shine mijin da zan aura da zaran na gaya mishi any nonsense zai rike a ranshi kuma zai cigaba da kallonshi da haka, kuma dadin daɗawa shi ɗin Shugaban alumma ce wanda yake rike da kasa guda yin haƙa takankar zubda mishi darajarsa ce, kuma nayi Imani yau koda ban Auri Dr ba dole zasuyi zumunci da Ashraf, dan haka sirrin Ashraf sirrina ne. Shine namijin da na buɗe idona nasani a gabana, tun kafin wannan abun naso saninshi dan natashi da muradin ganinshi a rayuwata, dan haka zumuncina dashi bana son wani ya shiga balle har asami wata ɓaraka.
“Hello Beauty!”
Kashe kiran nayi na cigaba da kuka, jin motsi a jikin gurin kayanmu yasani d’ago kaina, kayan yaranshi yake cirowa.
“Me yasa baki gaya mishi ba?”
Banza nayi da tambayar da yayi min. “Karki damu ni bani da….
*Kuyi hakuri Yan Paid grp daku nake yau na dan shiga ribibi ne amma ga wannan zuwa dare Insha Allah……*
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 16 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Page.٤٥-45
“Sam karki damu ki gaya musu na shanye miki nono, dan ni banajin kome idan na kawo yarana ne dai aka k’i a basu nono toh ba makawa, zansha kuma bazai min kome ba. Idan kina son kanki da lafiyarki toh yarana a basu kulawar da ta dace, idan kuwa aka k’i Abie ɗinsu zai ɗauka musu fansa, idan haka ya gaggara Allah ya hore min lafiya ta yadda zan cinyeki ba kakkautawa.”
Juya mishi baya nayi dan na fahimci wannan da hajja kaka tafiyarsu d’aya ce, sam baya jin kunya ko girman maganar da zata fito bakinshi famcamata yake son ranshi. Ina jin fitarshi sai da na sauke ajiyar zuciya da naji ya fita, tare da nutsuwa.
Ina jin wayata na tsiwa amma naki ɗ’agawa, haka har barci yayi gaba dani. Ina cikin barci naji ana tab’ani ina dubawa naga yaran ya kawosu. Tare da zuba minsu ya koma kan restchair yayi crossing leg yana kallona, Allah sarki yaran sai ture ni suke za susha, abinka da Uwa sai naji zuciyata tayi rauni. Tashi nayi na jingina da pillow, sannan na cirewa Aanih ta kuwa rike har tana zunguɗina, sannan na cirewa Aamih, tazo ta kama, duk sai suka bani tausayi. Haka suka sha ɗan abinda wancan lusarin Uban nasu yabari, sannan suka sake. Bawai dan ya ishesu ba, ina tunanin kawai sai ga Maid ɗinsu ta kawo feeder ɗinsu, sannan tafita, tashi yayi ya amshi d’aya ya mika min sannan ya ɗauki Aamih ni kuma na ɗauki Aanih.
Daga bakin kofa Nannah take kallonmu, haka yayi mata daɗi a ranta kuwa har addu’a take Allah ya tabbatar mata da wannan mafarkin nata.
Juyawa tayi tafita, ranta na mata daɗi. Wannan d’abi’a daga larabawa sai turawa, su kaɗai ne mutanen da suke hidima da yara, sabida girmama mace da kuma bata lokacinta na kanta, itama ta huta.
Muna gama basu yazo ya kwashesu ya kaiwa Maids ɗinsu, ni kuma na cigaba da kwanciya, shigowar Nannah yasani tashi. Zama tayi abakin gadon tana kallon yadda nayi zuru zuru, tace..
“Meke faruwa? Dan Badaru ya kirani wai akwai wanda zai zo ɗaukarki, ku koma gida, gashi kowani shakuwa Habibi baiyi da yaranshi ba zaki ɗaukesu ku tafi.”
Shiru tayi tana kallon yadda nake goge kwallar dake sauka a idanuna, kaina sunkuye sannan ta cigaba da cewa.
“Tabbas zai biki! Dan bazai iya hakuri da yaran ba, ni kuma meye ribata. A yanzun nake bukatarshi, duƙda kece kika kawo min shi gashi zaki sake ɗauke minshi, shi yasa naso ki hakura da wancan ki amshi Uban yaranki dan bana son yayi min nisa, amma kika k’i safinah me kike so na baki dan ki xauna min da Farin cikina, Muh’d da yaransa sune farin cikina gashi zan rasa sabida ke. Zan baki nan da wani lokaci kiyi tunani akan haka dan bazan iya hakura a sake rabani dashi ba, shine kaɗai abinda ya rage min shida zuri’arsa.”
Tana gama faɗar haka ta mike zata fita cikin kuka nace.
“Nah!”
Cak ta tsaya bata juyo ba, na mike zuwa gabanta kaina a sunkuye nace.
“Bazan taɓa yafewa kaina ba, idan na rabaki da farin cikinki, Nannah zan tafi nabarsu indai haka zai sanya ko farin ciki Nah zan barsu, don Allah ku barni nima nayi farin ciki ko sau ɗ’aya ne.”
Ganin Yadda nake kuka yasa jikinta mugun sanyi banga laifin Nannah ba ko sau ɗaya shekaru ashirin da shida tayi bata tare da d’anta yau ta same shi kwatsan zan tafi dashi dan wallahi tsaf Ashraf zai bini akan Yaranshi, kuma zai iya kome domin yaranshi.
Fita tayi ta barni a d’akin yana zaune a falon tawucce shi yana musu wasa, yaran sai walwala suke.
…….
Bayan fitarta na janyo jakata wanda muka zo dashi ko taɓawa banyi ba, na fitar sannan na ɗauƙo na yaran na ajiye, sai hand bag ɗina da na ɗauko na buɗe na shiga tattara kayana ina zubawa a ciki, wata abin charging na. Sai wasu kayan amfanina man shafawata da sauransu, na zuba. Dan nasan idan ya shigo da yamma maybe zuwa dare mu bar kasa.
Na gama shirya kayana tsaf, shigowar maids da shi kansa yasani d’ago kaina, kauda kaina nayi daga garesu na cigaba da shirya kome, kallonsu maids ɗin yayi suka ajiye abinda suka shigo dashi suka fita manyan jakukkuna ne har uku, ya zauna yana kallona yadda idanuna suke tsayayyar da hawaye.
“Wato na lura dake a duniya kina kaunar kuka”
Yadda yayi maganar yana nishi sai ka zata block inch tara ya ɗauka, ban bi takanshi ba na faɗa ban ɗaki na ciro Innerwear ɗina, duk na cusa a jakata.
Mikewa yayi bai kuma bin takaina ba, har yamma ina kwance da jikina sanye da arabia gown, naji karan wayata, ina dubawa naga Baby, mikewa nayi dakyar na zauna sannan na saka a kunnena nace.
“Baby! Ka iso ne?”
“Eh gani tare da Yarana har da Babansu.”
Gabana ne ya faɗi badai wannan yaron ya same shi da wani shirme ba, a hankali na mike tare da gyara fuskana na fito, a sannu ina raba idanuna. Murmushi nayi lokacin da na hangoshi,, a sannu na isa gunshi mikewa yayi tare da riko hannuna ya zaunar dani. Sannan ya zauna akan kafet yana kallon fuskana yadda ya kumbura yace.
“Beauty! Kina lafiya? Kinga yadda idanuki suka kankance, meke damunki.”
Ya kai hannushi zai taɓani hawaye suka zuɓo daga idanuna suka sauƙa akan hannunshi, riko hannuna yayi cikin raunin murya yace.
“Ina tare dake, duk wuya duk daɗi bazan taɓa barinki, ki zubda kwalla ba, share hawayenki bazan bar garin nan ba sai sake.”
Duk sai yaji bai aminta da zamana a cikin gidan ba, cikin damuwa yace.
“Naso sai gobe zamu bar garin nan amma dole yau na nima mana ticket zuwa gida.”
Kamar wacce aka hana cewa kome, haka na zauna ba hmm ba hmm, fitowar Nannah daga cikin ɗakinta ganin halin da nake ciki yayi mugun kashe mata jiki, haka kawai take ji a ranta taso kanta dayawa bata da adalci ta nuna son kai muraran a cikin alamarin toh ya zatayi bata da wani zaɓe da ya wucce haka, ita kaɗai tasan yadda take ji akan D’anta da jikokinta.
Zama tayi kusadani sannan tace.
“Dr ina ga ko zaku fitane, dan tunda bata taɓa fita ganin gari ba.”
A dame ya kalleta yace.
“Akwai abinda aka mata. Wanda ya hanata magana, amma ina gani idan muka fita zata ɗan sake a ranta.”
Ciro hank yayi ya mika min dakyar na amsa, ya mike nima na mike, tare muka fita hannuna cikin nashi, har gurin motar hotel ɗin da ya ɗauko. Muna shiga motar na kifa kaina a kancinyata na fashe da wani irin kuka me cin rai. Gayawa drvn yayi ya kaimu airport.
Can muka tafi ya shiga nima mana ticke, mun samu Oman toh Abu Dhabi. Jirginmu zai tashi uku na dare, dan haka ya dawo dani bayan ya rarrashe ni.
A sannu nake takawa bayan tafiyar Dr zamu haɗu airport, ina shiga ciki na samesu a zaune kallona Nannah tayi, cikin ɓacin rai tace.
“Wannan wani irin rashin hankaline da zaki tafi ki manta da yara, duba agogo karfe tara har da rabi.”
Shiru nayi kaina a sunkuye, takowa yayi har inda nake yace.
“Meye matsayin Yarana a gurinki?”
Baya naƴi kaɗan dan naga haukar tashi zata motsa, cikin inda inda nace.
” Na yayesu ɗazun nan, idan kuma matsayi ne, toh su kaddaratace wnda na amshesu hannu bibiyu, haka yayi maka.”
Juyawa yaƴi yabar barni a tsaye cikin karfin zuciya nace.
“Karfe uku jirginmu zai tashi, zuwa biyu zan tafi Nah idan na miki laifi kiyafe min.”
Shiru tayi sannan ta bar min falon.
Nima wuccewa nayi jikina a sanyayye, haɗa kayana nayi tare da zama ina share kwalla, tashi nayi naje nayo alola sannan na gabatar da salla, Addu’a nake kawai Allah ya nuna min karfe uku na dare na tafi, na gaji da wannan rayuwar. Karan sako naji.
*Hey Beauty baki yi barci ba ko? Plss kwanta kisa Alerm 2:15*
Murmushi nayi sosai a raina ina cewa.
*Idan nasami Dr a rayuwata na more miji, dan kuwa zai jiyar dani daɗi da soyayyarsa, zai kaini wata duniya na daban, kuma zai girmana al’amarina*
Wani sakone ya shigo nayi maza na tura mishi,
*Baby kai me ya hanaka barcin?*
Murmushi yayi cikin zolaya Ya turo min da sakon da ya bani haushi.
*Ina hira da wata budurwan da muka haɗu da ita an Mumbai ce mai suna Arundhati*
*Toh ai sai kaje gurinta dan naga haɗin zai bada citta karka kuma nimata*
*Wayyo kiyi hakuri wasa nike miki waye ni da zan nime wata mace bayan kina nan*
Cikin jin haushi nace.
*Matsalarka kenan! Ni kan ai ko baka aureni ba zan iya hakuri na rungume kaddarata. Tun*
Cikin sauri ya turo min da.
.*Tun me?*
Share shi nayi naki magana, can ya kuma turo min da cewa.
*Plss tun me?*
Cikin jin haushi na tura mishi da cewa.
*Tunda bani da abinda zan fanshi dare mai daraja a gareka ba*
Kirana yaƴi cike da damuwa, ina gani naki dauka dan bana son bacin rai yanzun sai na sauƙe mishi rigimar da banshi yakar zomon ba, saƙo na tura mishi.
*Idan mun haɗu gobe zamuƴi magana akan haka.*
Kashe wayar nayi na gyara kwanciyata.
*02:00am…….*
Toh fa me zai faru kuma…..
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 15 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Page.٤٦-46
02:00Am…..
Dake nasaka a raina zan bar garin har mafarki nayi wai tsakanin Ashraf da Dr sai faɗa suke akaina wannan na jana wannan jana, kowannensu so yake ya tafi dani. A na haka sai Allah yabawa Dr nasara fauce ni, a zubur na tashi. Zaune na tadda Nannah, da sauri na dira daga gadon na nufi Ban ɗaki naje nayi bukata ta nafito.
Cikin sauri na gyara fuskana, sannan na koma na zauna kusada ita.
“Yanzun Binti tafiya zakiyi ki bar yaranki? Ko tausayi basa baki?”
Ta watso min tambayar fuskarta cike da damuwa, sunkuyar da kaina nayi idanuna na cicciko da kwalla nace.
“Nah kiyi hakuri na tafi nice na bar miki su.”
Gyaɗa kanta tayi sannan tace..
“Tashi ku tafi yana jiranki a waje.”
Fita tayi daga ɗakin, sai ga maids sunzo zasu fitar min da kayana, ɗauka sukayi har da na yaran nidai bance kome ba, har gurin mota Nannah ta rakani, inda ta rike hannuna cikin sassanyar murya tace.
“Binti! Idan na rabaki da farin cikinki ban miki adalci ba, sabida cika min tawa muradin kika rasa taki, idan nace bazaki tafi da yaranki ba, toh na zama muguwa mara halacci, dan haka ki ɗauki kome da ya faru a matsayin kaddara ga yaran can mun bar miki har kiyayyesu, sai dai nasan dole zai zo amsarsu mungode kiyi hakuri da sanyaki kuka da mukayi kinzo cikin farin ciki yau gashi zaki koma ranki ba daɗi, ki gafarcemu. Sannan kyautarki da kika samu a masarautar anyi gaba dasu da fatan zaki yafe mana kura kuranmu.”
Hawaye ne ya zubo min daga idanuna, nace.
“Nah karki damu ni ban taɓa rike kome a raina ba.”
Buɗe min mota tayi na shiga.
“Nagode! Ki gaida mutanen gidan, suyi hakuri ban musu sallama ba.”
Lumshe idanunta tayi tare da murmushi, ban sami nutsuwar zuciya ba sai da motar tashi. Ina ɗaga mata hannu tana ɗ’aga min.
Sai da muka bar cikin masarautar, na sauke katuwar ajiyar zuciya, sam banyi tsammanin ganin yaran ba, sai nagansu sunci kwallayi, har da abin wuyar wanda akayi ɗan kwaɗon da shap ɗin heart, na diamond. Kiran saudiya,
Wayata na ciro daga jaka, na haska fuskarsu, suna barci hankalinsu kwance, murmushi nayi.
“Kinji daɗi hakan?”
A zabure na leka, Wallahi Ashraf ke jan motar.
“Koma ki zauna”
Zama nayi zuciyata cike da tsoron kar ya min tsiya, koda muka isa shi da kanshi ya fidda min kayana, ya kaini har ciki sannan ya juya ya sumbaci yaranshi, ko Allah ya kiyayye bai ce min ba. Nima kuma ban damu ba, na zauna inata raba ido ta inda zanga Dr.
Biyu da rabi sai gashi nan yatawo fuskarshi ɗauke da murmushi, yazo ya zauna kusadani. D’aura kaina nayi a kafaɗarshi nace.
“Alhamdulillah! Ina cikin farin ciki.”
“Shagwaɓaɓɓiya kawai! Kinsa hankalin kowa ya tashi sai kirana Dr kyari yake.”
Murmushi nayi a raina nace.
“Kaine bakasan abinda wancan yaron yake kokarin min bane.”
Muna zaune har karfe uku muna hira, lokacin da aka fara sanarwa muzo, ya ɗauki Aanih da jakarmu, ni kuma na ɗauki Aamih, da ɗaya jakar.
Sai da ya kai gurin aunawa sannan ya dawo ya kwashi sauran, babban burina na ganni A cikin jirgi, kawai ana gama duba kayana, kodan jakukkunar suna da tambarin masarautar ne yasa ba a tsananta bincike na ba.
Sai da muka zo mika passport nan ne nawa yace.
D’auke ni a hankali
Ji nayi zufa na karyo min, a raunane na kalli Dr nace.
“An sace min passport ɗina”
Kawai na fashe da wani irin kuka.
“Ki kira Nannah mana!”
Da sauri na ɗauki jakar na ciro, jikina na rawa sai da ya amshi wayar ya kirata, ya gaya mata halin da muke ciki sannan ya kashe kiran ya faɗawa matar da take amsar passport
…..
Da sauri na tashiga ɗakina, ta sameshi zaune, yasaka passport ɗin A gaba. A karo na farko da ranta yayi mugun ɓaci, tana zuwa ta kifa mishi mari, wanda yasa bakin fashewa.
“Duk yadda akaƴi kaine kasanya Binti a gaba ta bar gidan nan wannan wacce irin masifa ce? Yarinya ta gama lalata rayuwarta a kanmu kai kuma ka biyata da haka, kai mata adalci kuwa?”
Share bakinshi yayi cikin takaici ya mike zai fita tace.
“Kazo ka ɗauki passport ɗinta ka kai mata.”
Zuwa yaƴi ya ɗauka.
“Ni da bani da gata na mutu ko Ammih, Yarana fa zata tafi dasu ko sabawa dani basuyi ba, Ammih kina son kar na miki nisa amma su yarana kike son su nisance ni, ni dai wallahi bazata tafin da yarana ba”
Yana gama faɗar haka ya fita a cikin ɗakin,
……. Nayi kuka har nagodewa Allah dan ina ganin suna gargaɗi na karshe.
“Kaje kawai zanzo nan da wasu lokutar, bani da sa’a ce shi yasa kome nawa yake juyewa wata iri, Amma Insha Allah next haka bai kuma faruwa.”
Jikin Dr yaƴi sanyi zuwa yaƴi zai amshi nashi suka ce yaƴi hakuri an rigada an turashi, ina ji ina gani Dr ya tafi ya barni, yaki juyowa. Balle naga halin da yake ciki.
Kaina a sunkuye ya zauna kusadani, cikin sanyin murya yace.
“Kiyi hakuri! Bazan iya rabuwa da yarana bane, kuma ina son ƙasancewa dasu har karshen rayuwata shi yasa na sace miki passport.”
Yana gama faɗar haka yaje inda ake booking bansan ya sukayi ba, ya zo ya ɗauki jakata ya kai gun mota yasaka, kaf kayana ya kashe sannan ya ɗauki yaran ya kaisu mota, yazo ya zauna kusadani yace.
“Tashi zuwa gobe da safe akwai jirgin Addis Ababa, shi zaki bi kinji.”
Ban ce mishi kome ba kaina a sunkuye, haka ya gama maganarshi ban d’ago kaina ba, karshe da yaga zan bata mishi lokaci sai ji nayi ya ɗauke ni, rufe idanuna nayi ban buɗe ba, har ya kaini gaban motar ya saka, sannan ya koma ma zaunin drive, yaja motar, muka wucce cikin garin Oman, wani kayataccen hotel ya kama, sannan ya kwashi yaran yakai ɗakin ya dawo yasani a gaba muka wucce dakin, tunda na shiga na zauna. Ban iya ce mishi kome ba, dan bani da abinda zance masa, yayi juyim duniya na ɗago kaina kai shi magana ma na mishi amma fir naki kaina na sunkuye, shi dakanshi ya fahimci na kai makura na bacin rai dan haka bazan taɓa cewa kome ba.
Kiran sallar asuba yasani mikewa nayi alola nazo na fara sallah, sai a lokacin abinda ya tokare min wuyana ya sauka, na fashe da wani irin kuka.
Inayin sallar amma kuka yaci karfina, dakyar na idar, sannan na cigaba da kuka sosai. Dake ya fita zuwa masalci. Dawowa yayi ya same ni a zaune, ina kuka.
Zama yayi ya buga tagume, yana kallon yadda na lalace, a cikin kwana biyu da zuwanshi, har yaran suka tashi, yayi musu wanka. Sosai sannan yazo ya shiryasu. Ina zaune aka kawo abincin yaje ya amsa sannan yazo ya ajiye min, ko kallon abincin bany ba, zuwa yayi ya haɗa min ruwan wankan.
“Ko zaki shiga wnk ne! Karfe tara jirgin zai tashi.”
Jin haka yasani mikewa ɓa wucce shi naje nayi wankan, ina fitowa nasamu baya ciki shida yaran zama nayi na shirƴa. Kaman yasan na shirya sai gashi ya shigo, da yaran zubasu yayi sannan ya wucce ban ɗaki ya shiga wannan, fitowa yayi daure da towel. Hannunshi rike da karami yana goge kanshi.
Sunkuyar da kaina nayi, yana jin an buga kofar ɗakin yaje ya buɗe,jakar takarda ya ansa har guda biyu, yazo ya zazzagesu, riga ce Fari me guntu hannu sai wando, jeans dark blue. Da takalmi fari,sai man shafawa.
Sai a lokacin na lura da wata hegiyar gyaran gashin da yayi, a raina nace.
*Yaranta na yawo da Ashraf shi yasa baya jin kome dan ya cusguna min*
Kauda kaina nayi, dan ya kamani ina kare mishi kallo.
Yana gamawa ya fidda kayana. A hankali nace.
“Wahalalle”
Haka ya kwashe kayan sannan yazo ya ɗauki yaran, sannan nabi bayanshi, muna zuwa ya min kome. Yana kara rungumar yaranshi, ya sumbaci wannan ya sumbaci wannan, d’agowa yayi idanunshi sunyi jajjur. Har kana hango kwalla cikin eye ball ɗinsa, suna maiko, mun jima muna kallon juna. Kafin na kauda kaina, yana gama min kome ya rakani har cikin jirgin yaga yadda muka zauna, sannan yace min.
“Kice min wani abu mana”
Shiru na mishi haka ya gaji da tsaƴuwa ya juya zai fita sai da naga ya kusan fita nace.
“Thank you”
Juyowa yayi dan bai tsammaci godiyata ba, kauda kai naƴi ina kallon waje, ta window.
Fita yayi, nabishi da ido. Jingina kaina naƴi da jikin kujera. Zuciyata tayi min sanyi tunda nasamu nayi kuka tun ina sallah naji tayi min sanyi.
Ban sami nutsuwa da ƴarda da kai ba, sai da naji ance mu ɗaura belt nasamu nutsuwa, jirginmu na tashi ina sauke ajiyar zuciya.
…….. Daga airport kamar zai wucce gida, sai ya nufi hotel ɗin da muka kwana, yaje ɗakin. Ya zauna. Can ya shiga dubawa ƙo nayi mantuwa, yana shiga ya sami pant ɗina da na wanƙe, ɗauka yayi ya matse sannan ya saka a cikin ledar hular wankan da yasaka a cikin aljuhunsa, ya fita ya duba babu kome.
Sannan ya sauko ya basu key ɗinsu ya fita, gidan ya ƙoma yasamu Nannah tanata fushi, sunkuyar da kanshi yaƴi kasa, bata ce mishi kome ba, ta wucce ɗakinta, shima ya wucce ɗakinshi ya zuciyarshi cike da kewar Yaranshi.
Zama yayi sannan ya fidda pant ɗin ya ɗaura akan pillow ɗinshi,
(Mayye kawai😡😒😞)
……… Ranar ko Natasha da tazo ba ganewa kowa tayi a gidan ba, dan dukkansu kewan yaran na damunsu, baran ma Ubansu dayafi kowa shiga damuwa sukusuku, yake. Abinci ranar bai iya shaba sai
Coffee, har dare bai kurɓi komd ba sai coffee ɗin koda dare yayi ɗakin da nasauka yaje ya zauna a tsakiyar gadon ya jingina bayanshi da allon gadon, zuciyarshi ba daɗi.
***
Kun isa Addis Ababa karfe biyar na yamma, mukayi hutun awa guda sannan muka bi jirgin Abuja, tunda muka shiga jirgin naji wani farin ciki ya kamani, karfe d’aya na dare muka iso, amma banyi gigin niman gida ba, dan kar tsautsayi ya faɗa kan yarana, sai yanzun nake jin wani shegen tsoro ya kamani, domin zuciyata ta tuno min da chakwakiyar da na tafi na bari, rungume yarana nayi, sakamakon kallon da wasu mutane ke min, fuskarsu babu annuri.
A iya sanina mutane biyu ne dan tsigar jikina na tashi, bansan lokacin da bakina ya fara ambatar.
“Hasbiyallahu La’ilalaha ilahuwa Alaihi tawwakallatu wa huwa arshin Azim”
(Don Allah idan nayi kuskure a cikin addu’ar ku ankarar dani.)
Sau bakwai na karanta, ina d’ago kaina na nimesu na rasa, ajiyar zuciya na sauke, sannan na cigaba da addu’ar, shi wannan addu’a yana kariya sosai babu mugu ko shaiɗanin da ya isa cutar maka, sai in Allah yaso faruwar haka…..
(Jazakillahu Alkhair Ummyn Aiman)
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 14 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Page.٤٧-47
Sosai nake Addu’a jikina ya gama sanyi fatana Allah ya kaimu gida lafiya, ina zaune a gurin har akayi sallar asuba, gari na fara wayewa na duba jakata, na ciro wayata na na cire layin Oman nasaka Mtn ɗina, yana hawa kan wayata sakonin suka fara shigowa, a hankali na shiga niman numbers Number Dr na fara cin karo dashi dan haka na kira.
Cikin muryan barci ya d’aga kiran nace.
“Baby! Kayi sallar Asuba ma kuwa dan naga kamar baka tashi ba ma”
“Beauty!!!” ya kira sunana da karfi, cikin zolaya nace.
“Malaminsu ba ita bace! Mrs Zaki ce”
“Kina ina yanzun!?”
“Baby Ina airport, kuma gaskiya ina jin tsoron bin mota.”
“Ki zauna gani nan zuwa kiyita Addu’a nan zuwa.”
Yace min, ya kashe kiran nima na kashe,
Ina gurin zaune ina addu’a sai gashi sanye da jallabiya, ash colour. Mikewa nayi tsabar farin ciki, fuskana ɗauƙe da murmushi
Yana zuwa ya hura min iskan bakinshi. Dariya na saka tare da saukar kwalla,
“Baby! Ina farin ciki sosai.”
D’aukar kayan yayi. Sannan yace,
“Sai ma kin zama tawa, nan ne zaki yi farin ciki ranar da na mallaki wannan ɗan bakin.”
Lumshe idanunshi yayi sannan ya buɗe, yana bina da wani shu’umin kallo, irin kallon zaki shiga hannuna idan muka jone.
Tura baki nayi gaba ina cewa.
“Wallahi kabar min irin wannan kallon, dan tsoro yake bani jifa sai kace wanda ya tsinci dami a kala.”
Wani kallon kurilla yayi min, wanda yasani sunkuyar da kaina tare da wasa da Aanih. Fita yayi yana girgiza kanshi, a ranshi kuwa cewa yake.
*Ya Allah ka mallakamin Safinah badan na isa ko na kai ba.*
(Ni kuwa nace Amin😎 Team Ashraf ya dason life finku)
Ina tsaye ya dawo sannan ya amshi yarinyar muka fita, muna hira dukda safiya ce hira muke sosai, yana tuki ina bashi labarin yadda na same Passport ɗina, dan ce masa nayi na manta akan gado.
Murmushi yayi hankalinshi nakan hanya yace.
“Safinah kenan! A kalla nasan na baki sama da shekaru sha uku! Ba tantama ne, kuma abinda yasani sonki gaskiyarki, dukda bana son jin kome amma yana da kyau ki nutsar da zuciyarki guri guda, idan nine toh lokaci yayi da zan mallakeki, idan kuma Babansu Maryam ne ni bani da matsala da haka.”
Cike da mamaki na kalle shi, bakina na rawa nace.
“Hmm! Kana zargina kenan?”
“Ko d’aya bana zarginki! Sai dai ina da karamin kokwanto ne, Passport a jakarki ace ya faɗi a gado kodai Uban yaranki ya ɗauka dan karyayi nisa dashi, hmm. Taya ma zaki auri lebira irina, wanda baya samun hakkinsa sai karshen wata, bayan kin baro inda arziki yake, Safinah ban yarda ni kike so ba, ima ni kike so toh tabbas, kin jefani cikin kokwanto.”
Bakina da idona da hancina duƙ asake ina ƙallon Dr yadda yake karyata son da nake mishi.
“Nagode”
Iyakar abinda kenan matuƙar nace zanyi magana toh ba makawa kuka zanyi, lumshe idanuna naƴi burina mu isa gida lafiya, ina jin ya tsaye tare da danna horn nayi maza na ɓalle murfin motar na fito hankalina kwance, na ɗauki yarana. Na shiga gida dai dai Abba zai fita daga gidan ya ganni na shigo ai tsayar da motar yayi. Yafito da sauri ya amshi, Aamih tare da sauke murmushi yace.
“Yanzun airport zani, Sultan Ashraf ya kira yace mana kin taso. Amma yana tsamanin saukar cikin dare zaki yi.”
Maida kwallar cikin idanuna nayi nace.
“Abba na iso cikin dare! Toh ina tsoro kar wani abu ya samemu yasani zama har gari ya waye. Mun sameku lafiya,”
“Lafiya lau.”
Nayi gaba dan naga Dr na karasowa, ni kuwa raina yadda yake ɓace zan zabga mishi wulakanci iya ganin idona.
Nan yake gayawa Abba ai kiranshi nayi ga kayanmu a cikin motar, ina shiga cikin gida ya kaceme da ihu, da farin ciki.
Take yaran suka shiga makale min, da zaran an ɗaukesu sai su fasa kuka, nan suna kiuya.
“Ina yar shamurmurar take, lange lenge me ramar keta. Wannan Y’a mijin da ya aureki ai shine za a kira a ɗauri kashi ko a ɓata igiya sam babu kayan mora.”
Basu Ummi da Umma ba hatta Abba da yakawo Aamih, sai da ya direta da sauri ya fita, taɓe baki tayi cikin ko in kula irin ko a jikina ɗin nan sannan ta cigaba da cewa.
“Taya wancan Malohon ya tawo ya barki a can”
*”MALOHO???”*
Bakinmu a haɗe muka zaro idanu. Gyara zama nayi ina son sanin sanin Waye malohon da Maloho. Zumbura baki tayi gaba tare da watsa hannu gaba irin jaraba da masifa nacin ranta ta zabga mana harara sannan tace.
“Waye kuke tambaya ya wucce wancan gabjejjen tsohon da ya makelewa Safinah.”
“Lallai ma kuwa! Na rantse kika kuma kiran Baby da wannan sunan sai na zuba miki shinkafar ɓera kinci kowa ya huta da batsar da kike mana nan, haba kin ishemu da maganar banza.”
Ina gama balbaleta na mike tare da barin falon na nufi ɗakin Umminmu, alola nayi dan nabar sallah a kaina. Sai da na gabatar dashi sannan na kwanta dan dukkanmu duk mun gaji. Tuni barci yayi gaba dani.
***
Karfe biyu saura na muka farka nida yaran, fitowa Ummi tayi daga ban ɗaki tace.
“Nikan a cikin wata huɗu ne yaran nan suka ɗauko mugun kiuya haka. Tun kafin ki tashi naso musu wanka, amma yan butan uwa ina zuwa kusadasu zasu shige jikinki kamar sunga Dodanniyya.”
Tashi nayi ina dariya, nace.
“Wallahi a cikin kwana biyu da dawowanshi. Suka ɓaci haka da mugun kiuya ai dalilin barowa ta can wai dan”
Bansan lokacin da nayiwa bakina linzami ba, tabbas a cikin wawaƴe ni babbar wawuya ce, dan tsakani da Allah nake shirin facala mata iskancin da Ashraf yayi min.
(Nace ko baki kira kanki wawuya ba Fans ɗin Ashu zasu kiraki dan kar suƙe kallonki.😏😎😏)
“Au dama sabida yaranshi kika gudo?” Ummi ta watsa min tambayar.
Take na fara firitendi(😹 ina son turancina) da cewa.
“A’a kawai kinsan larabawa da son yara, kuma ɗaukesu yake bani sake ganinsu, kuma bayan haka ina kewar gida. Shi yasa nace azo a ɗauke ni.”
Murmushi taƴi dan taji nine kawai amma bawai ta yarda bane.
“Ai sai kije ki musu wanka, kar ruwan ya hucce.”
Na mike cikin sauri na shiga da Aamih na cire mata kaƴanta da pampes, na shiga, ita kuma taja Aanih ta cire mata, ina fitowa da Aamih ta amsheta sai ihu take tsalla mata,, ina gamawa yar uwan na kawota nima naje nayi nawa, sannan na fito ina goge jikina.
D’aya daga cikin jakar da nazo dashi, Ummi ta buɗe. Kayan yarane masu mugun tsada, da kyau. D’ago kayan tayi kuma iri ɗaya sai banbanci kala.
Su kansu kayan irin shigar masarautar Jordan ce, kome na ciki golden da ratsin ja.
Ciro musu wani Overall taƴi light blue da ɗigon pink, a ciki sannan takamasu tasanya musu pampas, da kayan ta kuma kame gashin kansu a tsakiya. Sai kukan banza suke mata, ni kuwa ina ta dariya dan fadarsu da yaran ya burge ni, sai ta gama kare musu zagi, sai ta dangware goshinsu. Aikuwa su fasa kuka(😂) sai tace musu.
“Na dakeku dan kofar masarautar garinku masu idanu a tsakarka, dube su.”
Ta kuma dangwaresu, aikuwa takwarata Aamih taja kuka, tana kallonta tare da jan kukan ta tsalla.
“Kaii! Ummi da alamu zaki gigita Sultan wallahi ya kirani yafi sau ashirin, a bashi yaranshi.” inji Dudu.
Yana rufe baki kiran na sake shigowa, ɗauka yayi yace. “Gani a gidan! Amma taƴa zasu.”
Kara wayar yayi a ƙunnen Aanih, wacce take wangale bakinta kamar kofar garinsu, shiru tayi tare da sake bakinta.
Amsar wayar nayi na kara a kunnena. Shirme fa yake gaya musu, tare da shiririta sannan shi kanshi yadda yake maganar zaka rantse da ALLAH matseshi akaƴi, Kashe kiran nayi ban kai ga mikawa Dudu wayar ba ya kuma kira.
“Don Allah ka buɗe wata jaka zaka ga kwalin Ipad, a saka a caji tare da wifi ɗinsa yake, zan na kiransu ta nan.”
“Ok.”
Dudu yace da sauri yana buɗe jakunkunar, can ya samo sannan yakai jikin Abin canji.
Ni dai ina kallon duniya, yaushe akayi wannan sayayyar, koshine fitar da yayi lokacin muna hotel ɗin nan da na shiga wanka, *oho* nace a raina.
Tsakani da Allah Dudu ya biyewa Shirmen Ashraf, yafita can sai gashi da layin Mtn, tura mishi number yayi. Duk wannan bidirin da ake ko sau ɗaya baice ina nake ba, sai Ummi ce ma da suke buɗe kayana, suka ga dukiyar da masarautar Oman suka bani, take suka shiga Sharhi akai, Sophia da Nana Asma’u da suka zo. Min sannu da zuwa suka fara kiyasa kuɗin manyan abin wuya da yan kunne, take suka shiga niman jin kuɗaɗensu, ina jinsu, dan sai lokacin nake karyawa, Umma da tashigo itama sai da tayi girmama alamarin, Madam kan da tashigo kasa hakuri tayi cikin son mu shirya tace.
“Yar nan ga inda arziki yake, ki saki wancan dukundukun, ki kama Ashurafa, tunda yarone ai zaki mori kuriciyarsa. Kinga wancan Malohon tsufar dake zai yi jininshi tayi kauri, wannan kuwa jininshi harbawa take, sosai kuma zaki ce na gaya miki.”
Salin Alin na bar ɗakin, sabida maganar wannan tsohuwar ba kan gado, kunya sai ya kasheka ita kuwa bai sumar da ita ba.
“Kilaki an dawo daga barbaran D’an taurene?” ko ban faɗa ba kusan wacece. Murmusa mata nayi.
“Eh magajiyar karuwai Uwar ɗakin Yan daudu, na dawo ban kawo miki kasonki ba, ba saikin zo amsa ba, dan duk inda kilaki take dole asamu uwar dakinta, zan kawo miki kasonki dan shin basarake ne yafi karfin taure.”
“Toh mara mutunci yar isa wacce ta ajiye y’ay’an gaba da fatiha.”
“Eh mana, nida natashi karuwancin riba biyu nasamu, ga Yara ga Dukiya, kuma ni yau zanyi karuwanci wallahi nafi karfin matsiyacin me kuɗi sai irinsu Sultan Ashraf wanda suna cinka zasu ajiye maka arzikin yanke talauci, nan da Kanwarki Ade tazo kafin ta koma sai da ta sace min dubu goma taje aka cire mata ciki, dake ita nata Asirin ya rufu shine bari ki bankaɗe na wasu, sannan Hunaidah da kuke cewa tayi aure mijin yarasu shine dangin mijin suka kwace dukiyarshi hhhhh! Mamie. Ko dai taje an juye mata fetir a cikin injin ɗinta kuma batasan wani gidan mai ne aka mata wannan juye, bane ni me sa’a ce ko yau nashiga wani gida bani da kaico sabida Ubansu ya mallaki abinda zai rukesu har karshen rayuwarsu, ki iya da harshenki, idan yarana shegune toh tabbas ina Alfahari da cewa Ubansu ya mutu akan kaunarsu, dan koda wasa wani yayi gigin lakatarsu hmm wata miyarsai a makota ni kaina bansan meye balaraben Kasar Jordan zai aikata ba, amma nasan ya kware a bada umarnin a yanƙe kan mutum daga gangar jikinsa, Allah ya baki sa’a haukarki ta taɓa mishi idanunshi.”
Duk yan cikin ɗakin Umminmu cirƙo cirko sukayi, dan ba karya Mamie ta kaini bango kuma na fyaceta na huta da iskancinta, kuma wallahi ta taɓawa Ashraf Y’a toh wallahi idan ya haukace zanga me iya dakatar dashi.
“Wallahi Nuratu kinyi asara! Yaushe zaki daina kishi da Safinah wad’ancan murɗa murɗan yan matan da kika kwaso ba a miki magana ba sai kece zaki sanya yar masu gida a gaba, muguwa me kashin awaxa kashin tsiya”…..
(Kaii Hajja Kaka matsalana dake Ove Acting, kome sai ta faɗi abinda babu shi a cikin kundin balaga😹🏃)
_Yan Paid grp kuyi hakuri mu gama book One, Insha Allah 8 more kullum amma sau ɗaya idan kuma zaku amince 4 more da safe insha Allah da dare 3 more toh Insha Allah zan baku a Book 2-3 da yardan Allah in yaso wannan book one tunda free ne du kare a 3 more ko yan lelena ina ji daku kamar yadda nake ji da Yar magen makotarmu😹😎_
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 13 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
*Don Allah ina baku hakuri ga mutanen da suka kirani ba wulakanci bane bamu da Wutar nepa ce, Alhamdulillah an gyara*
Page.٤٩-49
Rungume shi tayi ta baya, tare da goga mishi kirjinta, amma mara mutuncin nan ko a jikinsa sai ma, kwace jikinshi da yayi abunshi, aikuwa ta bishi har ban ɗaki, amma fir yaki biye mata asalima rufe idanunshi yayi duk abinda zatayi tamishi dole haka ta fito tana kukan bakin ciki da damuwa, ta zauna a ɗakin har ya gama abinda zai yi ya fito, kallonta yayi tare da kallon kofa, mikewa tayi tafita dan taga ruwan bala’i a fuskarshi, Cikin rufawa kai asiri ta ficce.
***
Zaune nake ina ta faman gyara gashin Aanih sai cizon lips ɗina nake, tare da turashi gaba. Gashi nasha wata katuwar rigan sanyi, dan munan abuja mun fara tunkara damina ne, kuma tun asuba ake mana ruwan sama, gari yaƴi mugun sanyi da dadi. Rigar sanyin kasar bangaladash sakar ulu ce, tana da matuƙar ƙyau, dan har igiya gareta wanda zaka iya ɗaurewa tagefe, zan iya cewa suit dan yanayin rigar kenan, ta sauko har gwiwa haka ma hannuwanta dogaye ne, wuyarta kuwa a rufe take, karamin veil nasaka a kaina, kananun kalabar da Batul ta min yana reto. Na nutse sai taune bakina nake, wai ni nan kitso zan gwada masu. Sau uku inayi amma tsabar laushin gashin da tsantsi warwarewa yake, yatsina fuska naƴi, sannan na ɗanyi murmushi sabida tuno wani hikima, abin dariya sai da na gama kitsewa sai ya warware. Raurau nayi da idanu.
“Beauty! Ki hakura da kitson nan mana, na jima a tsaye fa.”
Ajiye matsefin nayi tare da harɗe hannuna a kirji, ina masa wata duba. Kaɗa kanshi yayi cikin niman rigimata yace.
“Beauty! Hmm ina magana dake, amma nasan kina jin abinda zanyi zaki daina kulani karshe ma kice kar a kara barina na shigo gidan nan.”
Kura mishi ido nayi zuciyata na bugawa, na kalleshi a nutse naga babu alamar wasa, tattaro hankalina nayi gareshi cikin zakuwa nace.
“Ina jinka!”
Shiru yayi tare da tsareshi da idanuna, ina jiran abinda zaice.
“Beauty! Ina son zanyi aure ne in yaso dag.”
D’aga yatsana nayi tare da nuna mishi hanya, zuba min ido yaƴi ganin babu wasa a fuskana yasashi fashewa da dariya, yace .
“Beauty! Kishi ko? Ki rage don Allah ko dan gaba, sannan yaran nan a barsu haka kar a ji musu ciwo”
Pillow na ɗauka na kwala mishi cikin jin haushi nace.
“Wallahi ka kuma zuwa min da maganar aure zakayi sai na.”
“Sai kinyi me?”
“Sai nacinyeka ɗanye.”
Kasa yayi da murya sannan yace.
“Ranar can ma aikin cinye min bakina yauma dan kin cinye ni ma bazanyi mamaki ba, sai dai.”
“Kayi shiru kar wani yajika a sami matsala”
Wai gawa nayi dan kar wani yaji mo, kasa da murya nayi cikin jin haushi nace.
“Wai meye haka? Idan Ummina taji wallahi zataji ba daɗi pls mu bar haka kodan kare kimarmu A idanun ahalinmu.”
“Toh naji yaushe zaki biyani sumbatana.”
Kauda kaina nayi, ina leka kofar ɗakin Ummi, ina juyo da fuskana sai akan nashi, ciƙe da mamaki da alajabi. Nake kallon cikin idanunshi, ina son zare bakina na kasa, lumshe idanuna nayi tare da ture shi, na ɗauki Aanih da sauri muka bar falon, dariya yayi shima ya fita a gidan.
Ina sakata nafito a hankali naga baya nan ɗaukar Aamih nayi zuwa ciki.
Haka rayuwarmu take tafiya da daɗi ba daɗi, ga karin kalubale ta ko ina,
***
Jordan….
A yau aka wani gari da mugun labarin na samun gawar Shugabar kabilar Banu Hussein Shugaba Adnan. An mishi kisar gilla tare da wuka me alamar tambarin masarautar jordan, take muhawara ya zafaffa, wadda yaja aka shiga sa’in’sa tsakanin kabilun Banu Hashim, wannan alamarin ba karamin tada hankalin kowa yayi ba dan takai sau uku, ana kawo harin ɗaukar fansa a kofar shiga masarautar.
Duk wani me faɗa aji na masarautar sunyi shiru, can Abu Zarri ya gyara murya cikin nutsuwa yace.
“Kisan da akayi! Da wukar masarauta, kuma an tabbatar da cewa a cikin masarautar nan akayi kisar sannan aka fitar dashi waje na ɗaya kenan, sannan an tabbatar da Adnan ya shigo masarautar nan kafin ya mutu inda ya nemi ison ga Ukshe biyu kenan, sannan shugaban kabilar Banu Nazir shima yazo cikin masarautar nan, idan na fahimta akwai wani abun da ake kokarin rufe mana, amma bincike zai fidda kome.”
“Abu Zarri!!! Me kake nufi dani? Zargina kake kokarin yi.”
“Eh Ukshe tabbatarwa zanyi.” ya bashi amsa fuskarshi ɗauke da murmushi, shigowar askarawa cikin fadar Abu Zarri ya nuna musu Ukshe dake kujeran guragu, yasa kowa na fadar mikewa.
“Ni zaka wulakanta Abu Zarri!?” cewar Ukshe.
“Aikine ya biyo takanka. D’an uwana, kuma idan da gaskiyarka babu wanda zai riƙeka idan kuma baka da gaskiya toh ko karen cikin masarautar nan bashi da ikon kareka.”
Hawayen bakin cikine ya zuba daga idanun Ukshe yace.
“Nan da mintuna arba’in zakaji anyi belina, Magajin wancan kujeran ya kusan bayyana, tsohuwar matan sarki Abdullah Malika, d’anta Bilal wanda yake D’an uwa ga Ashraf yana gab da isowa kujeranshi, mulkin jordaɓ zata dawo min, Boyayyen sarki ya kusan bayya duk sai kun faɗi gaskiyarku.”
Turasi sukayi tare da ingiza keyarshi,
Lokaci Fada ya ɗauki hayaniya waƴe Bilal?
Kafin wani lokaci alamarin yasake zafaffa, inda sukayita bincike. Shiru Abu Zarri yayi kafin ya kwalla kara yace.
“Bazai taɓa saɓuwa ba, Yahudawa bazasu mulki Daular Musulinci ba.”
(Da kyau an sake faɗa sabon kitimurmura nasan Me karatu zai kagu da son sanin Wacece Malika? Taya Sarki Abdullah ya aureta? Ina take? Waye Bilal da ake tunanin shine Next Sultan ehhe😜)
***
Oman……
Shiru yayi yana juya cokalin hannunshi, muryan da bazai taɓa mantawa yaji. Cike da manaki ya d’ago kanshi yana kallonshi.
“Ghaniyu!!!” ya furta sunanshi a can kasar makoshinsa, shigowa yayi, shi kuma Ashraf ya mike zai bar falon, yayi maza ya durkusa a gabanshi tare da zare takobin da yake gefen kugunshi ya miƙa mishi da hannu biyu cikin kaskantar da kanshi, yace.
“Raina fansa ga zuri’arku baki ɗaya. Domin goge cin amanar da nayi maka shugaba na takobi nan kasare kaina yabar gangan jikina, shine hukuncina, amma kafin nan kasaurare ni ko sau ɗaya ne.”
Raɓa gefenshi yaƴi zai wucce. Ghaniyu ya d’aga murya yace.
“Sadaukar da Ahalina nayi, kafin na iya cin amanarka, sun kona min kowa sai Rubina ita kadai ce gareni bani da kowa sai kai da Sarauniya da kuma. Mahaifiyarka, idan ka koreni bani da inda zan zauna Shugabana ka amshi ya fita.”
Juyawa Ashraf yayi yazo ta d’agashi sai da yazo bakin kofa ya turashi waje.
“Don Allah karka kore ni, ka barni na cigaba da zama dakai Maigidana.”
Banza dashi Ashraf yaƴi, jikinshi na kara sanyi, yana goge kwallar wayarshi ya zaro ya shiga niman number baida zaɓe da ya wucce ya gayawa Sarauniya Safinah ko zata taimaka mashi, dukda baida yakinin zai sameta, yana gwada kiranta kuwa sai ya shiga. Cikin tashin hankali ya gaya mata kome, sannan yayita mata godiya.
….*
Yana shiga d’akinshi dunkule hannunshi yayi tare da zabgawa bango naushi sai da yaji kashin hannunshi, yayi kara. Jin karar wayarshi yayi, cikin ɓacin rai ya d’aga tunda ya manna a kunne yayi shiru.
“Bai zama dole ka yafe mishi ba, sai ka duba kafin yaci amanarka, meye ka tsare mishi.? Shin ahalinshi suna cikin kariya danutsuwa kamar yadda kai yake baka kariya, shin yana cikin wadata kaskanci. A duk lokacin da yardaddunmu suka ci amanarnu, abinda zamu duba ba kome bane me yasa Wane ya cutar dani? Ta ina na tauyeshi idan nasamu baka tsare mishi abinda ya dace ba, toh tabbas kaine silar sashi aikata haka, idan kuma dan raɗin kanshine, baya kaunarka. Sannan sabida yaki amincewa akayi garkuwa da ahalinsa, sabida kar ya zame musu matsala suka kashe mishi kowa sai matarsa, kayi tunani dakyau.”
Mikewa yayi tare dabin waya da ido, shiru yaƴi sannan ya maid Wayar kunnenshi tacigaba da cewa.
“Ba Safinatu bace! Umminta ce kai shugaba ne, kayi kokarin kyautata alakarka da kowa sai a zauna lafiya kuma Alumma suyi farin ciki da tsarin mulkinka, amma tun daga gida baka shimfiɗa adalci ba toh tabbas bazaka iya jagorancin mutane nasu ɗinbun yawa sai anjima ka gaida mamarka.”
Shiru yayi jikinshi a mace, mikewa yayi yazo kofar falon ya buɗe , takawa yayi har gaban Ghaniyu. Kamar bazai mashi kome ba, aikuwa Ya tsinka muahu mari, sannan ya rungume shi, tsaf tace.
“Kai ba bawana bane kai abokina ne kuma d’an uwana.”
Sosai suka rungume juna cije da farin ciki ghaniyu yace.
“Nagode shugaba!”
“Kana son muyi faɗa. Ashraf ni yanzun ba Kowa bane, kamar sauran Mutane nake.”
……*
Jordan…
“Waye Bilal? Wacece Malika? Abie zaka faɗa min ko sai na kashe kowa na cikkn……..
Hankalin Me karatu karya tashi…..😎🏃🏃🏃
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 11 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
Kuyi maneji
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
*Alhamdulillah nagode sosai da gyaranku akan addu’ar da kuka gyara min*
Page.٤٨-48
Takowa Ummi tayi har gaban Mamie, cikin murmushi tace.
“Bazan hanaki wucce iyaka ba, amma ki sani ba kowani iyaka kake da karfin tsallakawa ba, ki cigaba wata rana zaki isa inda bazaki dawo ba.”
Fiki-fiki tayi da idanunta tana son magana, Hajja ta dakatar da ita da cewa.
“Kina raraba idanu kamar kinyiwa sarki karya, munafukar banza munafukar wofi.”
Watsewa akayi muka barta a gurin. Karfe bakwai sai ga Duduh, ina cikin shirya Yaran zasu kwanta, ya shigo gurin Ipad ɗin yaje ya cire a charging sannan ya kunna, tare da sitting ɗin kome, sannan ya kawo musu. Ciro wayarshi ya kirashi. Yana ɗauka ya gaya mishi number..
Kashe kiran yayi can sai ga Ipad ɗin yana tsiwa ɗauka dudu yayi ya ajiye mishi yaran, sannan ya nemi pillow ya saka a bayan ipad d’in.
Sanye yake da farin shirt haka ma wandon fara ce, mikewa nayi na bar gadon ya cigaba da hira da yaranshi, su kuwa sai kura mishi ido suke.
***
Alhamdulillah tun dana dawo na same nutsuwa sai dai rashin jituwarmu da Dr yana mugun dawona, dan tsakani da Allah naji zafin irin kallon da yake min,
Sai da mukayi kusan sati biyu ina share shi, a sati na uku ya turo min sakon.
*Duk Abinda ya same ni kece Sila*
Tsaki nayi sannan na tura mishi.
*Matslarka ce ba tawa ba.*
Kirana yayi cikin sassanyar murya na ɗauka.
“Hmm!” nace mishi,
“Beauty! Kiyi hakuri ban san zan ɓata miki rai ba da b..”
“Da baka faɗa min abinda kace ba ko? Bansan yaushe zaka yarda dani ba, sam ni duniya bata burgeni. Balle kwaɗayi da kawazuci su kaini ga halaƙa, abinda nasani nake dashi ina da taurin kai, da kafiya bayan haka bana jin magana ko?”
“Beauty duk ki manta da haka, mu gyara gabanmu.”
“Ina kayi hakuri kawai! Zan nime Anim mu dai daita,”
“Beauty!!!”
Ya buga min tsawa tare da dukan table ɗinsa wadda naji karanshi, lumshe idanuna nayi. Cikin son na tabbatar da kishinr yasashi haka ko dai yayi hakan ne dan sani farin ciki.
Kashe kiran nayi san sai na bashi ciwon kai kafin na amshi, hakurinsa.
Bayan minti talatin sai ga kiranshi wai nafito gashi, kashe wayar nayi. Tare da gyara kwanciyata, kamar da wasa barci yayi gaba dani. A haka na shanya Dr tun karfe d’aya saura yake cikin mota yana jirana, har karfe biyu da rabi.
Shigowar Khalil ya ganshi cikin mota, yana zaune shine yaje suka gaisa yace.
“Ya Dr! Kaine anan?”
Murmushi yayi tare da cewa.
“Eh nine, ina jiran Didinku ce.”
Shiru Khalil yayi, sannan yace.
“Ok bari nai mata magana.”
Baba Garba ne ya tareshi ya gaya mishi ai Ya jima a gurin tun d’aya yake gurin ai suka je masalaci tare suka dawo, shiru yaron yayi sannan ya shige ciki.
Ina kwance yazo ya bubuga gadon farkawa nayi, nace.
“Auta Lafiya?”
Zama yayi akan stool yace.
“Didi! Meye laifin Dr? Da zaki shanyashi, koma meye ya miki bai dace ki wulakantashi ba, wallahi in nine shi tuni zan barki, da baki san me aka mishi akanki ba, harbinshi akayi akanki, kamar bazai rayu ba. Yana tashi daga jinya ke ya fara nima, amna dan rashin tausayi kina wulakantashi, dan kawai yana sonki. Aini ba a haifi macen da za a kashe ni sabida ita ba, idan zaki iya kije yana jiranki.”
Shiru nayi har ya fita ina cikin jimami ashe abinda ya faru dashi kenan, mikewa nayi na shiga ban daki na wanko fuskana, na zura gown ɗin Atamfa na fito da sauri. Na isa gurinshi, tun kafin na karasa ya fito, tare da rufe kofar motar ya jingina da jikin motar, yana kallona.
Kamar na fashe da kuka lokacin da na isa gurinshi muryata tana rawa nace.
“Baby!”
Sai ga kwalla zirrrr ya sauka daga idanuna.
“Ya isa beauty! Wallahi bana jin daɗin kukan nan naki, kiyi shiru don Allah.”
Wata uwar harara na masa, tare da isa gabanshi nace.
“Wallahi badan bani da karfi da na maka mugun duka, akan me bazaka gaya min an harbeka ba sai yau, me yasa ka ɓoye min.”
Tsayawa nayi inata masifa sai ka rantse d’ana ne a gabana yadda nake masa faɗa, shi kuwa ya zuba min ido sai murmushi yake, ganin na koma gefe tare da haɗa kaina da jikin motarshi na sake kuka.
Matsowa yayi kusadani, ya tsaya tare da leka fuskana. Aikuwa na zabga mishi harara, murmusawa yayi cikin jin daɗi yace.
“Ko kefa! Amma kin zauna kina kuka kamar small baby nan.”
Murguɗa mishi baki nayi tare da kauda kaina gefe, so yake yayi tsoƙana amna yasan halina tsaf sai na juye maganar ya koma babban alamari, zuba min ido yayi dan bai da tacewa, rike kunnenshi yayi tare da kwaɓa fuska ya shiga motsawa. Dariya ya bani, ganin yadda ya dage wai shi yana tsallen kwaɗo cikin dariya nace.
“Ka ganka kuwa! Sai fuskarka ta koma shigen ta mage”
“Koma me kika ce na amince, burina naga farin ciki akan fuskarki, kuma Alhamdulillah naga haka, babban burina a duniya na mallakeki ni ɗaya, ki ta haifamin yara masu kyau irinki, ina kuma rokon Allah yasa idan zan mutu, na mutu akan cnyarki zuwa kirjinki domin na tabbatar da soyayyata a gareki gaskiya ce, kaunar dake miki rubutacciya ce a zanen Kaddarata, hakan zai sa na tashi a cikin mutanen da sukawa So bauta.”
Ya karshe maganar tare da dage min gira.
Kura mishi ido nayi ko kyaftawa banayi.
“Wato kai ko! Ka iya gaya mutum magana yadda zuciyarshi zata tarwatse, yanzun don Allah meye ya kawo batun mutuwa a nan, da zaka zo ka gaya min, saresarin zuciyata ta buga, ni dai karka kuma gaya min zaka mutu. Ita mutuwar ma a kan hannu, maybe so kake tsoro ya kashe ni. Don Allah karka kuma gaya min irin wannan maganar dan wallahi zan daina kulaka.”
Gyaɗa kanshi yayi cikin sanyin murya yace.
“Yes Ma!”
Rike baki nayi cike da mamaki da takaici nace.
“Kai zo nan”
Na yafeto shi da hannuna, rairai yayi da idanunshi, ya shiga matsowa kamar yaron da yaƴi laifi, ya matso har da sanya hannunshi a fuska irin yaji tsoron nan, dariya ya bani nace..
“Dr wallahi zaka sani ciwon ciki duba fa ka koma like Adli, kai nan kaji tsoro ai idan akayi bikinmu, idan kayi min laifi bulala zan saya na ajiye sabida kai, idan kayi min laifi no mercy zan zaneka kuma ba ruwa na.”
Girgiza kai yayi tare da buɗe motarshi ya shiga yana dariya yace.
“A min izini naje gida cikina yayi kasa, zuwa anjima zanyi shutdown”
D’aga kaina sama nayi sannan nace.
“Zo muje ciki kaci biski.”
Shima d’aga kanshi yayi sannan yace.
“Ammahna ta hanani cin abincin ko. Sai nata ko na matata! Tunda bani da matar bazanci abincin kowa ba, gwara naje mrBi.”
“Wallahi duk ranar da mutum yazo min yaci abincin layi sai na rufe mishi kofar gida, kuma na hanashi fita har na kwana uku, daga cikin horon kullum sai na zane hannunshi da kafarshi, kana na sace tayar motarshi.”
Zaro ido yayi irin yadda yara keyi yace.
“Dan naci abincin waje!?”
“Ai ba kawai bane, domin matsalar dake damun mazanmu na arewa da hausawa kenan, mace zata gama juye basiranta a girki da gyaran jiki tsafta da gyaran gida da yaranta. Abin haushi mijinta nacen tabirin me shayi yana shan tea me kauri an juye rabin gwangwanin peak, milo ko ovaltine. An saka nescofe guda, kwai guda huɗu an fasa sadine, ga tsire ko balango an juye. Dan rashin imani a gida ya bar Larai da tuwon datsa miyar kanta kafura, daga ita sai kafi manja ma idan tasamu toh barka za ace Wallahi lahira akwai kallon.”
Yadda nake magana sai bin bakina yake da kallo, musaman yadda nake motsa bakin, murmusa min yaƴi cikin niman rigima yace.
“Ai babu gidan abincin da ban sani ba a cikin garin nan, dan haka hakuri zaki yi dani, dan sai na gama cin duk abinda kiƙa lissafo, na kuma shiga gidanki ina gyara murya, alamar toh ga boss ya shigo a matsa min ko nayi hukunci, kina kawo min abincin zan kauda kaina. Nace
Ke larai zo ki ɗauki abinci daga ganinshi ko nuna tuwon baiyi ba ga miyar kukan sai warin daddawa take, domin girmama hatsi shine zai hanani kwallo dashi amma badan haƙa ba, kwallo da tiren silverki da kwaniƙan zanyi”
“Kaii!”
Jan murfin motarshi yaƴi ya rufe tare da fashewa da dariya ina tsaƴe a gurin har ya fita, yana ɗ’aga min hannu. Naji daɗin daidaitawa da Dr, ina da yakinin zai sanyani farin cikin da narasa, kuma ina jin haka a raina sai dai ina shiga zulumi idan na tuna meye zai faru gaba.
****
Oman….
Sam ya rage walwala dama kuma ba d’abiar shi ba, kusan tunda Safinah ta tafi da yaran, yake jin ba daɗi, dukda yana kiranshi ta ipad yana kallonsu, babban abinda ya ɗ’aga mishi hankali hangota da yayi tana shayarda yaran, da wani rigar barcinta light blue. Har yana hango yan nonuwar, bai san lokacin da ya kashe tap ɗin ba sabida haniniyar da zandariyarsa take, ga wani ciwon maran da yake damunshi, a duk lokacin da ya tuna da nonuwar sai maranshi ya murɗa, a yanxun haka kwance yake yayi rub da ciki, hannunshi yana dafe da maranshi, yana matsa maranshi da tayi tauri. Ga azabar da take mishi, sai juyar da kanshi yake.
Da sallama Natashah tashigo sanye da doguwar riga ta a baya. Ganin yana kwance. K’ugunshi ɗaure da towel, zare rigarta tayi ta haura gadon, daga ita sai bikini. Tunda ya dawo take maitar lasar zumarsa amma D’an butan uwa, sai wahalar da ita yake. Sai yayi kamar zai cita, sai ya juya mata baya(😹😂😎 Dan banza da Safinah ce da ka hanata sakewa)
Yau da taganshi ba kaya, haɗiye yawun tare da ɗannewa bayanshi ta fara mishi tausar dole, yadda take mishi tausar tare da shafa shi yasa shi juyowa. Tsabar miskilanci yana jin daɗi amma ya shareta, haka ta cigaba da matseshi, har zuwa zandariyarshi. Tana kai hannunta yayi maza ya riketa. Mikewa yayi ta zauna cikin tsukewar fuska yace.
“Karki taɓa min kayan baiwata”
Kamar zata fasa ihu ta ɓalle ɗan bra ɗin, tare da tura kirji.
Yatsina fuska yayi kamar wanda yaga kayan amai yace.
“Ke rufe min wannan abin bakyan gani, ”
Kura mishi ido tayi. Cikin masifar sha’awarshi tace.
“Sultan don Allah kayi ko sau d’aya ne”
“Ke!! Saukar min a gado! Idan kika kuskura na kara ganinki cikin ɗ’akina sai na ɓatar dake.”
Kuka tasaka wiwi, jikinta har rawa yake.
“Don Allah ka rufa min asiri kayi”
Mikewa yayi tare da ɗauka towel, zai shiga ban ɗaki aikuwa ta bishi da gudu, tare da….
1.803 shine cif words ɗinku kuyi hakuri transforman mu tayi bindiga, Allah yasa nan da dare musamu wuta…..
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 18 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Page.٥٠-50 الحمد الله
“Waye Bilal? Ka faɗa min ko kuma na kashe ƙowa dan har ofishin askarawan zan biyo ka.”
Murmushi Ukshe yayi masa, sannan yace.
“Dama lokacin da nake jira kenan, kuma yazo kai ma bazaka taɓa sha ba. Duk wanda ya kalli wancan kujeran tabbas mutuwa ce sakayyarsa, ka gudu dan tsira da ranka.”
…….
“Abu Zarri! Kasanya zukatarmu cikin damuwa wacece Malika? Waye kuma Bilal.?
Mikewa Abu Zarri yayi kwalla.
” na zuɓo mishi hak’ik’a munyi kuskure barin Ashraf ya ajiye Mulki, babban tashin hankalin zuwa Bilal da Malika! Tankar shigowar Yahudawa ne cikin wannan masarautar, kuskuren bana kowa bane sai na Ukshe shi.
***
Oman….
“Ranka shi daɗe! Jordan fa ya riƙice sosai, abubuwa da dama suna faruwa ko zaka koma ne can.”
Latsa wayar hannunshi yake cikin kwanciyar hankali, kamar ba dashi ghaniyu yake ba.
“Kyale shi Ghaniyu! Nima bana son komawarshi can ɗin, gwara ya zauna a nan kusadani. Ina jin motsinsa.” Inji Nannah,
Da wutsiyar Ido ya kalleta ganin hak’ik’anin gaskiyar abinda ta faɗa, wato ita dan kanta tarike shi. Bayan ta rabashi da wani giɓɓi na rayuwarsa, yaransa sune farin cikin rayuwarsa cikar burinsa. Amma haka ta rintsa ido ta masa katanga me tsayi da rata, ajiyar zuciya ya sauke. Zuciyarshi cike da kewar yaranshi da ita wancan matsoraciyar.
Karamin murmushin gefe baki yayi sannan ya kwantar da kanshi a jikin kujera, tare da lumshe idanunshi, sautin takalmin Natasha yaji. Lokaci guda ya lumshe idanunshi sam baya kaunar ganinta, ta addabi rayuwarsa. Ta takura masa ya rasa yadda zai da ita.
Zama tayi a kusada Nannah, tana kallonshi. Kamar mayya idanunta nakan ɗan karamin pinklips ɗinsa, wanda yake kewaye da gargaza. Jin alamun ana kallonshi yasashi buɗe idanunshi sai akanta, fari tayi masa da ido tare da lashe bakinta.
Mikewa yayi cikin mugunta yace.
“Ghani! Karka bar kowa ya shigo min d’aki.”
Aikuwa taji haushi ba kaɗan ba, ɓata rai tayi tana jin zafin ghani.
***
Nigeria…..
Yau yarana suka cika shekara guda, dan suna takawa. Shi yasa aka shirya musu Birthday party, Allah ya gani bana son party nan wai ma a cikin gidanmu za’a shi yasa nasami nutsuwa. Zan iya cewa tunda muka dawo babu abindaya kuma faru, amma nasan ba haka kawai Anim yayi shiru ba.
Kusan sati d’aya dana gayawa Nannah, za ayi musu shagalin karin shekara har tayi min alkawarin zata zo, toh munata zuba ido bamu ganta ba.
Zan iya cewa tun da aka saka ranar party nake jin ba daɗi wata zuciyar na kwaɓata dana bari karmuyi wata kuma na nuna min nayi, karshe dai na tsayar da ra’ayina guri ɗaya, kuma zanyi.
Jikina a mace na fito wanka, karar da wayata tayi zan ɗauka naji ana ihun zuwan baki. Agurguje nasaka kayana, na fito turusss nayi sakamakon abinda idanuna ya gane min, dukda yawar mutanen dake falon, bai hanani hango kamilalliyar fuskarshi me cike da tsantsar izza da mulki ba.
Boya nayi a bayan wata mata a hankalina furta sunanshi.
“Sultan Ashraf!!!”
Kamar wanda yaji, haka ya d’ago kanshi. Yana rarrabashi, da sauri na silale zuwa ɗakin Ummi kirjina na bugawa, kara wayata. Takuma na ɗauka idanuna a rufe nace.
“Waye!”
“Sanin koni waye bazai amfanar dake kome ba, sai kara shiga tashin hankali. K’in zata zaki sha e? Hmm kafin nan ki fara duba taurari guda biyunki nan, kai Y’ay’an Larabawa da kyau suke, ji gashi. Gasu sun girma sosai kamar ba yan shekara guda ba! Da alamu zan biya bashin gabata akansu, dan naga zasu iya ɗaukata.”
“Wayyo Allah na Anim ka rufa min asiri, karka musu kome ni na amince zan baka kaina hatta rayuwata.”
“Yanzun naji batu. Karki kuskura wani yasan da haka, idan kina son su rayu cikin farin ciki toh kifito yanzun idan kika kuskura wani yasan inda zaki wallahi sai na kashe yaranki bayan nagama lalata musu rayuwa.”
“Toh shikenan zanzo don Allah karka musu kome.”
Kashe kiran yayi.
…….
Da sauri na mike tare da zaran key motar Khalil na fito, falon sai gaishe gaishe. Ake banbi takansu ba na fita.
Bin bayana yaƴi da ido, lokaci guda yaji yarasa nutsuwarsa dan tunda yazo baisa biyunsa a ido ba, a zafaffe ya mike ba tare da yace kome ba.
Yana fitowa ya makala abu a kunnensa, sannan ya matsa smart phone ɗin hannunshi.
“Kubi diddigin layinta.”
Tuki nake kamar mahaukaci, ga wayata da take ruri, ɗauƙa nayi cikin tashin hankali naji Murƴan, Aanih tana kuka tare da kiran Didi!
“Anim!!!”
N daka mishi tsawa, cikin kuka nace.
“Bana ce maka zanzo ba! Karka taɓawa Sultan Yaranshi dan yafika hauka da bala’i. Indai nice zanzo kayi yadda kakeso amma karka ɗauki wani mataki akan yaran, dan Uban mayunwancin Zakine wanda tasa abinda zai ci a cikin dawa.”
“Barazana kike min? Ko tsoratani? Yanzun yarana zasu nuna miki koni waye.”
Kafin na bashi amsa, sai ji naƴi an daki motana sai da na hantsila baki ɗaya, dariya yake sosai. Sau uku na hantsila. Take motar ta kama hayaki,, mutane suka firfito daga cikin motarsu, masu babura suka sauka, tare da kokarin cironi a mota, ana cironi wani ya nuna musu motarshi har da takardan shaidan aikin dan haka suka barshi ya daukenk ya kuwa cilla a guje ya.
***
Komawa ciki yaƴi yana kallon kowa. A hankali yace,
“Ina Yarana suƙe?”
Nan kowa ya shiga dube dube, tare da cewa..
“Badai fitar Safinah wani abu ya sami yaran ne?” Inji Ummi, ta faɗa a,
Murmushi yayi lokacin da ya lura da duk mutanen gidan babu abinda ya damesu, sannan ya gyara zama. Yana kallon yadda duk suka ruɗe. Cikin lokaci kalilan, sunkuyar da kanshi yayi kamar baya cikin damuwa.
“Me yasa suka sace min Yarana? Me yasa basu sace Uwarsu ba? Me yasa sai yarana? Na ɗibo jiki da farin ciki zanga sanyin idanuna ashe bakin ciki zan tadda. Baku damu dasu ba sai kanku kawai.”
Mikewa yayi dai-dai kira ya shigo masa.
“Zaku iya nima min zama da Jakadar Oman nan kasar, amma dole sai na nimo”
Dafe goshinsa yayi kamar wanda yake tunani.
“Waye me Toyota Camry?”
A tare suka ce.
“Mamie!!”
Shiru yayi yana niman karin bayani, Nannah tace.
“Matar Badar ce! Kuma dama akwai rashin jituwa a tsakaninsu da Safinatu.”
“Tabbas ita ta kwashi yaran”
A hargitse Abba yace.
“Taya kaganta.”
Kamar bazai magana ba ya kauda kai, sannan ya fara cewa..
“Muna shigowa naga fitarta yaran suna d’aga hannunsu, amma ana zauna dasu.”
Tsakanin Ummi da Abba tsere tsere suke zuwa d’akin Mamie, wacce take barcinta cikin sallama da nutsuwa, suna shiga suka rufeta da duka.
Abba har da fincikota, suka wurgota kasa, tare da mata duƙar kawo wuka, dakyar aka kwaceta..
“Wallahi kifito min da jikokina ko kuma ki mutu dan wallahi kin taɓo abinda ya dameki.”
Cikin kuka tace.
“Alhaji me ya faru? Wallahi bansan meke faruwa ba, wasu jikokinka zan fito maka dasu.”
“Ina kika kai Maryam da Asma’u?” ya jefa mata tambaya tare da zabura zai turmusheta, d gudu tayi Bayan Dudu, tana cewa.
“Wallahi tallahi billahi azim ban taɓa maka jikokinka ba, asalima yau bani da lafiya. Ko waje ban fita ba, ka yarda dani!
Cirko cirko sukayi kowa zuciyarsa kamar zataƴi waje, da gudu Dudu ya fita, har waje. Dai dai bakin get ya samu babu kowa, ga Motar Mamie a fake. Leka d’akin Me gadi, a tsorace yayi baya, kamar zai faɗi.
Sai da Khalil ya rike shi, sulalewa yayi a gurin.
“Sun mishi yankan rago.”
Cikin lokaci kalilan alamarin ɗaukar yaran ya zafaffa, domin kuwa bayan ansami gawar Me gadi, sai Zakari drive wnd aka sanyashi cikin bayan motar gidan aka rufe.
Yan sanda sun karɓi case ɗin yayinda Ashraf ya zuba musu ido, dan yaki magana. Da yan sanda suka dame shi tashi yayi.
Tare da amsar key mota, zai fita Nannah ta rike shi.
“don Allah karka tafi su maka wani abu kai ɗaya gareni.”
Fauce hannunshi yayi cikin ɓacin rai yace.
“Ya isa haka! Ki kyale ni. Dan na miki biyayya na zauna, na kuma bar mata yarana. Amma sam baki fahimci kawaicin da nayi ba, ai ko mutuwa zanyi sai na dawo da yarana, amma ba makawa zan tafi. Tunda ta iya sadaukar da kanta domin ke, ta kuma rasa Kimarta sabida ke! Nannah ke Uwace amma nasan Umminta tayi kuka da bakin cikin abinda ya sami Yarta sabida ke! Bazata gaya miki bane sabida kaunar da suke miki, keda kanki kika ce har koran kare Mahaifinta ya mata a cikin unguwar, amma yau domin ita da Yarana kike kokarin dakatar dani, Hmm bazan taɓa dakatuwa ba, koda kuwa ita suka ɗauka zan fita nimanta, sabida niman na samu kusanci dake, saura kiris a yanke mata hukuncin kisa. Duk abinda zan Mata bazan taɓa biyanta ba. Ghaniyu muje,”
Fita yayi shi da ghaniyu. Suna fita wata jugaurd tana parking a gabansu shiga sukayi. Aka mika mishi laptop.
“Yallaɓai! Munbi diddigin kiran maharin ya boye, sai dai ita ɗin tayi hatsari kuma.”
Yadda ya kafeshi da idanu yasashi haɗiye maganar sabida wani ja da idanun sukayi ga wasu jijjiyoyi da suka taso raɗa raɗa, a goshinsa da hannunsa. Zufa ke karyo mishi yace.
“Ina jinka.”
“Toh! Gaskiya munbi layinta yana inda tayi hatsarin, toh dake tun daga fitarta har tayi hatsarin muna biye da ita ga inda muka samu akayi da motar da aka ɗauketa.”
****
Ruwa sanyi kalau aka watsa min, wanda yasani sauke ajiyar zuciya me mugun karfi tare da sunkuyar da kaina.
“Didi!”
D’ago kaina nayi nagansu tuɓe, daga su sai pampers suna miko min hannunsu, ganin an ɗaure ni, akan kujera yasani fashewa da kuka.
“Anim! Nice na maka laifi ba yarana ba, ka ɗauki kowani irin akaina. Su basu san kome ba.”
“Toh! Toh na fahimci zaki iya bada rayuwarki akan waɗanan shegun, haka ma yaƴi dan nima naji daɗin haka, toh amma akan idonsu zan ji daɗina da uwarsu.”
Ya faɗa yana fashewa da dariya, girgiza kaina nake cikin kuka nace..
“Anim! Karka tozartani a gaban yarana, dan haka zai zauna a cikin kwakwalwansu. Don Allah ka sirranta mutuncina karka zubar min da kimata a idanunsu.”
Murmushi yayi cikin tsabar mugunta yace.
“Toh shikenan, idan nayi dasu fa.?”
Hawaye ke zuba daga idanuna, yana sauka, bibiyu kuwa ba ɗaya ba.
“Toh kazo kayi dani! Akan idanunsu idan ka gama ka kasheni kayi tafiyarka. Allah ya sani ni ba mazinaciya bace, duk abinda ya faru dani zan iyacewa Zanen Qaddarata. Wanda bazan taɓa tsallakeshi ba sai na fuskanci kalubale, iya haɗuwarmu na soka, koda naki ka banyi hakan dan cusguna maka ba, amma kai ka maida haka wata fuska na daban, har yau ban tab’a cewa Iyayena kaine kasaceni sai da ka faɗa da bakinka Anim idan kwanciya dani shu zai kashe maka wutar kiyayyata zo kayi yadda kakeso dani, daga Mahaifinsu babu wanda na kuma haɗa shimfiɗi dashi sai kai, zoka ɗauki abinda ka rasa.”
Zuwa yayi cikin zafin rai ya kifa min mari, wanda yasa hancina da bakina fashewa.
“Nine na Tura Hidayah ta ɗauko min Yaranki!…..
*1Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 18 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Page.٥١
“Hidaya!? Wacece ita!? Meye haɗina da ita!? Ka cire ni a tamtama mana, ka cire ni a kokwanto mana! Anim idan da alkawari ruwa bazai ci d’an kada ba! Yau kome nayi maka ban cancanci haka, haba Anim ka tausayawa yarana mana.”
“Akan me zai cire miki tantama, shekara goma ina dakon soyayyar Dr Zaki! Dan tun ina scndry na fara sonshi, har na shiga Jami’a. Ina gab da gaya mishi manufata, balkisu tazo ta aure min shi, ban damu ba sabida na yarda da kaina. Nice nan na bata shawara tazubda cikin jikinta. Karshe ya saketa, ina gab da cima burina kiƙa shigo rayuwarshi mara mutunci kika rabani dashi.”
Wani katako dake can gefe ta ɗauka ta make min gefen fuskana sai da na hantsila da kujeran, ina kuka me cin rai dan ihu banza nake.
Saka takalminta tayi ta take min kafana,ina kuka da ihu. Rarrafawa yarana sukayi, suna kuka da kirana.
“Didi!!!”
Suka zo jikina tausayi suka bani, sabida ni yau suma suna fuskarta matsala.
Kamo fashinAanih tayi ta cillata can gefe sai da tasake wani irin kara ban kuma jin motsinta ba. Cikin tashin hankali na kwala mata kira.
“Asma’uHusna!!'”
Da mugunkarfi, sake kama gashin Aamih.
“Naji me kike so ka miki karki taɓa min ita na haɗaki da Allah, kinji gaya min na shirya na miki biyayya don Allah, karki min haka kema mace ce! Zaki iya fuskarta halin da na shiga na miki alkawarin bin umarninki.”
“Hahaha! Kyalkyalkyal! Bana bukatar kome nafiso nayi destroying d’in rayuwarki ƙamar yadda kika min, na sanya miki ciwo a ranki da rayuwarki”
Kuka nake tare da girgiza mata kai, amma dake zuciyarta babu Imani haka ta cillar min da y’a ihu na fasa tare da cewa.
“Ku wasu irin Mutane ne marasa Imani da tausayi! Mugaye azzalum…..”
Wani irin duka ta kai min da itace hannunta, can na koma gefe tare da kifawa a kujeran, ban kuma sanin duniyar da nake ba.
***
Dr tare da wani jami’in ɗan sanda sai Dudu, wanda suke bin track ɗin wayar hidaya. Kuma suna gane inda take, da gudu suka wucce su Ashraf. Suma suka rufa musu baya ya zamana ana bambam tubam bam. Can kusada Zuma rock a cikin dajin dake kusada dutsen, suka nufa sosai sukayi mamaki inda suka shigo, tsayar da motar sukaye a gefe guda.
Ashraf da mutanenshi suka fito, tare da karewa dajin kallo. Cikin nutsuwa ya isa gurin dasu ya kalli d’an sandan yace.
“Ya kafito babu kayan aiki?”
Ciro yar bindigarsa d’an sanda yaƴi, murmushi yayi kawai. Abokan tafiyarshi ne suka fito da wani dan karamin jirgi sak drum, suka kunna shi, sannan suka ɗauki remot control ɗinshi wanda sukayi connecting da Tap ɗin hannunsu, sannan suka tadashi sama sosai, suna kallon inda yake ɗaukowa, tafiya me nisa yayi kafin suka hango wank waje hayaki na tashi, suna binshi yana dadda tafiya har ya isa inda Gidan Anim yake,
Kallon Dr Ashraf yayi cikin ko in kula yace.
“Daku koma sabida wasan bazai dace da ku ba.”
Dai dai yana ciro bindiga wacce tafi ta hannun Dan sandan. Girma janta yayi d’aya daga cikin mutanenshi yace.
“Sir! Rabonka da bindiga shekara biyar, tun kafin dawowarka Jordan da….”
Wani irin kallo yayi masa take ya haɗiye maganarshi ba tare da ya karasa ba, kallon Dudu da Dr yayi yace.
“Ku shiga wancar motan, tana bawa kanta kariya.”
Girgiza kai Dr yaƴi yace.
“Bani da wata kariya sai naga halin da Beauty take ciki.”
Tabe baki yayi suka shiga dajin a hankali suna masu taka tsantsar da wasu abubuwa, dake sun rufe salansar bindigarsu, a hankali suka farawa su Anim! Ɗauki ɗ’ai ɗ’ai, har suka samu damar hayewa katangar gida, anan aka san sunzo.
Duk yadda Ashraf yaso karsu Dudu da Dr su koma fir suka ki.
…….
😝 Yasin Anim ya kwaɓe zai kashi gara kenan yaji karan harbi, ai a sukwane ya ɓace. Aka bar Hidaya da faɗawa koman.
….. Dakyar suka same damar shiga gidan, suna kutsawa ya tsaya turus tare da juyawa ya cire rigar jikinshi, ya tawo har inda nake ya rufa min, bana ma cikin hayacina, ɗaukana yaƴi ya nufi gurin Dudu, zai mika mishi…..
Ya hango tawowar Harshashi, dab gurin Dr tureshi yaƴi. Haka harshashin ta huda ta baya sai da yafito tawaje. Juyawa sauran abokan tafiyarshi sukayi, suka buɗewa mutumin wuta.
Hmm faɗuwa yayi dani, Dr zai karɓeni ya girgiza mishi kai, kallon Dudu yaƴi, shi ya matsa tare da amsata.
“Taimakeni da yarana!”
Da sauri suka nufi Inda yaran suke, suma aka ɗaukesu. Tare da kama Hidayah. Amma Anim yayi ya tsere.
***
Dr yana kula da Ashraf ni kuma Dudu na kula dani, sai dai wani abin mamaki tsakanin Dr da Ashraf sannu baya haɗasu. Dan kowannesu miskilin kanshine, zan iƴa cewa nice na sauyashi daga shiru zuwa me magana, amma Ashraf kam dama can maganar a kayyade suke, duk yadda kaso baya iya juran magana, ga wani shegen girman kan da yakewa Dr.
Yara kam nasu da sauki amma b’angaren Safinah ba a cewa kome domin kuwa, ta bugu akanta. Amma tana samun kulawa sosai.
Baro ofishinsa yaƴi tare da shigowa d’akin da Ashraf yake kwance, ganinshi yayi zaune tsre da yaran suke kiran Didi.
“Da fatan kasha maganinka?”
Kamar bazai amsa har dr ys gama dubashi zai fita yace.
“Eh! Nagode.” ya faɗawa Dr a dakile,
Female ward dr ya tawo yasame Dudu da wasu likitoti suna tattaunawa, koda suka fita jan kujera yayi ya zauna yana kallona, ya jima sosai sannan ya fita. Komawa d’akin Ashraf yayi, ya ɗauki takardan sallama ya gama rubuce rubuce ya mika masa.
Har dr zai fita sai ya gaza hakuri cikin zafin rai yace.
“Me kake nufi!? Zaka sallame ni ciwona bai warke ba!? Hmm ko kana da shakkune a kaina.”
Murmushi Dr yayi tare da juyawa.
“Karka damu Kaninmu! Ai bana tsoron kome dan well kome ma kace.”
Juyawa yayi zai fita.
“Hmm! Idan naso kayi yadda ko ba, a zauna lafiya zanyi idan kuma aka kureni, zanyi abu, dan ita baiwata ce.”
Murmusa mishi dr yayi tare da fita a d’akin. Sai dai yaji zafin Abinda Ashraf yayi masa, yaso share abin sai ya kasa ya zuba ido har lokacin da Safina zata same lafiya.
***
Shi kaɗai sai cika yake yana batsewa sabida an sallame shi, Ghaniyu sai kunshe dariyarsa yake ya rasa gane kan Ashraf, akan Safinah mutum sai kace me tambotsai, nan jiya Nannah take ce masa.
“Habibi ko kana son Safinah ne.”
Tsuke fuska yayi ciki ciki dasu, sannan yace..
“Ina ruwa da ita! Taje ta zauna da wanda ta zaɓa.”
Shiru sukaƴi suna kallonshi, sake kafin yace.
“Duk ya hana kowa sakat akanta sai kace danshi aka halicceta, ya wani tsareta. Abin haushi na kai yaran su sha abincinsu ya hanani isa gareta dole ya kira wata Nurse ta amshesu, na gaji wallahi idan yace zai cigaba da nuna min iko akanta zan masa wulakanci.”
Shiru sukaƴi kowa na girmama niman rigamar Ashraf domin idan ba rigima ba, meye ya haɗasu da Dr da ya zauna yana bala’i har haka, koda Dr yazo cewa yaƴi. Ya tafi kar ya taɓashi yaje kawai,
Shine kuma Dr yayi amfani da haka ya sallameshi, tunda baya bukatar magani…….
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 8 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
*
Page.٥٣
Rasa tacewa nayi, cikin damuwa nace.
“Kasami Abba kayi magana dashi, tunda sadakinka na hannuna”
Zuba min rikitattun idanunshi yayi, zuciyarshi cike da farin ciki yace.
“Yau zan sami Abba! Insha Allah zamu zama ɗaya soon”
Buɗe murfin motar nayi zan fita, cikin sauri ya rike mayafina yace.
“Idan na takura miki na hakura!”
Murmushi nayi cike da ƙunya nace.
“Baka takura min ba, kawai ina jin ba daɗine dan nasan zai amshe min yarana.”
Jikinshine yayi sanyi, banyi tsammanin abinda na faɗa zai sashi, a damuwa ba sai da yace min.
“Ok! Indai haka zai rabaki da yaranki toh ina ganin zan hakur.”
Cikin sauri na rufe mishi baki shi da hannuna, ina girgiza kaina nace.
“Kayi hakuri! Bansan zaka ji ba daɗi ba koda amsar yaran yayi zan zauna da kai a haka, Dr ina sonka.”
Da sauri fita shima yafito da sauri, har na kule cikin gida. Sam hankalina yayi cikin gida har muka bangaje juna, ɗauƙe kaina nayi kamar bansan da halitta a gurin ba, bai damu ba ya nufi inda Dr yake tsaye ya zuba hannu a cikin aljuhu. Cikin izza da jinkai haɗi da mugun yaranta dake ɗibanshi, duk shirmen da Ashraf yake kallonshi Dr yake, dan haka ma yanzun da ya tawo ko takanshi Dr bai bi ba, ya shige motarsa.
Cizon lips ɗinshi yayi mishi. Ya mishi wani irin zagi da yatsu, (Fuck u).
Murmushi dr yayi dan ya fahimci rashin d’a ‘a na damunnshi.
Da sauri yaja motarshi dan matukar ya cigaba da biyewa Ashraf zaayi tsiya dashi.
***
Alhamdulillah, an gama maganar aurena da Dr, dan har an tsayar da rana nan da wata biyu, Ashraf bai sani ba, sai da muka zauna ana hira. Abba yake gayawa Hajja, Kan kuturun bala’i.
“Badaru!!! Yanzun dan tonawa kai asiri, wancan dundurumin katon zaku bawa yarinyar da ɗuwawun arziki bata dashi, tsabar rashin mafaɗi ga Uban yaranta amma ku ɗauki yar aba ku bawa wancan me zubin arnan daji, yo mutum ne gingimemmen zaku bata toh wallahi ku shirya.”
“Wai Nikam Hajja meye matsalarki da Hameed ne da kika tsane shi? Wallahi ina jin kunyarki na rantse zan kafta miki rashin mutunci haka kawai zaki addabi rayuwata, ce miki akayi kowa.”
“Yakolo!!! Wucce ki bani guri”
Fuuu na bar musu falon, dan raina yayi mugun ɓaci.
Tunda muka fara magana kanshi yake sunkuye, mikewa yayi ya fita. Ranshi na tafasa bayan shi har wani zai.
Lumshe idanunshi yayi lokacin da ya shiga part ɗin Nannah na gidan.
Yana shiga ɗakin ya zauna a bakin gado, tunda yake bai taɓa zubda kwalla akan abu ba. Yau shi yake zubda kwalla sabida yana ganin zai rasata.
“Me yasa zaki nemi rabuwa da Yarana! Bayan sun saba dake! Tabbas zan dakatar da haka. Ba zan taɓa bari.”
Wayarshi ya ɗauka tare da kiran layinta.
……. Ina kwance raina na kara ɓaci, kira ya shigo min bansan number ba, amma sabida tsaruwar number na ɗauka, manna wayar nayi a kunnena nace.
“Hmm! Dawa nake tare!?”
“Na tayaki murna! Toh sai dai naga Malamar tana murna ko? Idan kina son kome ya tabbata kizo nan, yanzun nike son naji duminki idan kuwa kika ki tabbas wata biyu da suke zuwa, na laulayin sabon dashena ne, idan kika sake wani yasan wannan rigimar toh zan ɓatar dashi yanzun haka yana asibiti karfe huɗu zai koma gida, zuwa dare zai wucce duba lafiyar shugaban kasarku, toh ya idan kika ji labarin an tsinci motarshi babu shi ba me kama dashi, toh ai ba kome indai Lailah ta kiyayye toh tabbas majnun zai kai labari.”
Bai bani daman magana ba ya kashe kiran,
Idan hankalina yayi dubu sai da ya tashi, mikewa. Nayi tare da zura hijab ɗina, na fita ta kofar kitchen. Na nufi cikin gidan,
Baya falo cikin uwar ɗaki na shiga yana kwance, dogewa nayi daga bakin kofa. Ina binshi da wani kallon tsana,
“Ashraf! Ka tashi muyi magana, dan ita ku kuskura ka bari na fito toh zan baka mamaki iyakar rayuwarka.”
Shanye da toka fuskarshi ya mike zaune ya zuba min ido. Takawa nayi har gabanshi cikin zafin rai na tsaya a gabanshi ƙafin na fara magana cikin ɓacin rai nace.
“Halacci da sadaukarwa da nayi! Ban tsammaci zai zame min sharri ba, iya ƙokarina na janyoka ga mahaifiyarka, dan burintane ka ajiye mulkin da kake kai ka dawo gareta, kuma nayi nasaran haka, inda nayi amfani da damar da nake dashi na shanye duk wata wahala daga gareka,hmm”
Sake murmushin bakin ciki ina kallonshi, sannan nacigaba da cewa.
“Idan da dan kuɗine ko ɗaukakar duniya bazan taɓa damuwa naje inda kake ba, tausayin zuban hawayen Uwa da take kwaranya yasani, satar fita naje nimanka ka dawo gareta, Shin na taɓa zaginka dan abinda ya faru tsakaninmu? Ashraf ban taɓa sanin halin son kai irin naku ba sai da dalili ya haɗamu, iya kokarina nayi muku, duk abinda ka min ban taɓa damuwa ko nunawa wani hakan, sabida darajar Y’ay’ana. Wallahi a duk lokacin da kayi min wani abu yaranka suke hanani na rama, duk baka gani. Duk iya kokarina sai da ka kaini karshe, toh ai ba damuwa. Tunda har iya biyo yar african bakar fata wacce ta ciyar da kai da karanunkaka, ta kuma ɗauki nauyinka, dukda baka wucce sa’an kaninta ba, kaga ashe da sauki. Ba dai sha’awa bace zokayi yadda kake so, amma kasani ko da ciwon kaine yasamo Dr wllahi bazan kyaleka ba, sai an hukuntaka.”
Cire hijab ɗin nayi wulli dashi sannan naje gurinsa, na cigaba da cewa.
“Ai na fahimci banda son kai babu abinda ke zuciyarka, dan haka zo ka ɗauki abinda ka barmin”
Mikewa yayi cikin kunar rai ya naushi iska, ɗaukar Hijab ɗin yaƴi ya mika min. Tare da cewa,
“Jeki! Kiyi aurenki. Ina kuma baki.”
Shiru yayi sabida nauyin magana, dakyar yace.
“Am sorry”
Saka hijab ɗina nayi, cikin rawan murya nace..
“Don Allah ka barni na zauna a gidan mijina lafiya kaima Allah zai baka wacce tafini.”
Gyaɗa min kai yayi cikin sanyin jiki, ya juya min baya. Tausayi ya bani sosai, haka na fita daga gidan na nufi cikin gida, tunda na shiga nake kuka amma a ban ɗaki, kwanciya nayi sabida jin motsin shigowar Ummi bansan lokacin da barci yayi gaba dani ba.
***
Bayan fitarta ya shiga haɗa kayanshi, yana gamawa ya nufi gurin Hoton yaranshi ya ɗauka tare da sumbata, sannan ya fita da sauri.
***
Da safe nake jin wai yabar gidan ya sanyi gida a wani estates.
Taɓe bakina naƴi cikin farin ciki dan ko ba ƙome haka yayi min daɗi. Ina karyawa sai ga yarana da gudu suka ɗanne min cinya, Khalila tashigo tana dariya tace.
“Didi! Wallahi twins basu da kirki kinga tsiyar da suka min dan ina shiryasu banda nakai zuciya nesa, amma ɓa gama musu sai dai kinemi wasu.”
Dariya nayi nace.
“Babu ruwana, yarankine.”
Tura baki tayi tana kunkuni tace.
“Ba wani yarane!”
***
Tunda Ashraf yabar gidanmu na fahimci nayi kiba, bani kaɗai ba harda Dr, soyayya muke bugawa son ranmu.
Ina zaune hankalina ya tafi ga chatt, sallama yayi na d’ago kaina na kallesu sau ɗaya sannan na kauda kaina. Shida yaranshi……
Plss kuyi hakuri barci nake ji sosai😴😴😴
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 7 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
*Ana tare Masoyan gaskiya Ga comments a paid grp ga Vote a Wattpad nagode da kuka nuna min kune masoyan gaskiya😂 shi yasa nace akanku zan iya tsinkawa soja mari a kofar barrack😹🏃 naji ance kalya ne😎😏😒 Allah akwai comments ɗinku da yasani jin kunya wai Dr ya d’anna sai kace mota😹😒*
Page.٥٢
San Dr baya kaunar tashin hankali musanman nan Asibitin dake masa kallon Babban mutum.
Dukda Dudu ya fahimci yar tsamar dake tsakaninsu hakuri ya bawa Dr sannan ya same Ashraf a mutunce yayi mishi magana, amma dake rashin mutunci na azazalarshi sai cewa Dudu yayi.
“Kodan shi ɗin maigidanka ne? Idan domin haka da kuma dan albashin da yake baka na karin kumallo zan gina maka asibitin da yafi nashi, na kuma zuba maka kayan aiki da masu aiki. Sannan albashin da zan na biyan aikanta da zallar dollas ce, dan haka ka cire bakinka akan maganarmu.”
Gyara tsayuwa Dudu, cikin jin zafin maganar da Ashraf yayi masa yace.
“Zan kyaleka sabida haɗa jinin da mukayi da kai! Amma matuƙar ciki d’aya muka fito da Safinah! Sai na hanaka ganinta ma, yara kuma ka kwashi kayanka naje dasu, Y’ar uwata so da kauna take nima tare da kulawar miji ba ita taje kula da wani can ba, kar na kuma ganinka a cikin asibitin dan zan baka mamaki.”
Wato tunda Ashraf yake bai taɓa haɗuwa da mutanen da basu san shakka ko tsoro ba sai Familyn Safinah, dan yaga Dudu ma yaci kaniyar Safinah. Tunda ita bata kallonshi ta gaya mishi magana, yau gashi ido da ido Dudu ya gaya mishi magana.
Dukda tafasar da zuciyarsa keyi amma fir yaki magana asalima kafe Dudu yayi da shanyayyun idanunshi nan, fuuu ƴa fita daga asibitin har yayi nisa ya dawo kwasan yaranshi, da suke Ofishin Dr suna masa ɓarna shi kuwa yana aikinshi, yana shiga ya tokari kofar ofishin, d’ago kai Dr yayi zai magana. Amma ganin Ashraf yasashi cigaba da aikinshi, yasami ya ranshi suwa Dr kaca-kaca da ofishin inda sukayita wasa da chocolet ɗin da yasayo musu, ga wasu daga cikin takardun Dr a kasa, sun zubda ruwa. Akan capter ɗin da ya shimfiɗa musu, Aamih tana tsakanin kujeranshi tana son buɗe wordrob ɗin da yake ajiye wasu documents, Aanih kuwa cire babbar wayarshi tayi, tana waya idan tasaka a kunne sai tace..
“Didi”
Sai tamako wani bagwaren larabcinta ta maka, sannan tayi dariya. Jikinshine yayi mugun sanyi, musaman da yaga dr bai damu da ta adin da suke mishi(😹😁😂Kun tuna Anatullah da Amatujabbar na cikin Matar Malam Shuwagabanin ɓarna)
Aikuwa Aamih ta janyo wayar charging laptop ɗinshi ya fado, tsabar tsoro tasaka ihu tare da rike kafarshi a rikice ya d’agota tare da ajiyeta a saman table ɗinshi ya sunkuƴa ɗauko laptop ɗin da zan iya cewa ya tashi aiki, ai ganin Aamih a sama itama Aanih tayi wulli da wayar hannunta tasaka mushi ihu, ajiye laptop ɗin yayi ya koma kanta. Nuna mishi sama tayi, bai damu ba ya ɗauketa ya ajiyeta a kusada yar uwanta, sake kofar Ashraf yayi bayan ya shigo, ɗaukar yaran yayi ya saɓa a kafaɗarshi. Aanih ta fasa kuka tana mikawa Dr Hannu da kiran.
“Daddy”
Fita yayi ranshi na kara baci wato Dr ya sha gabanshi ta kowani fuska, ya shige jikin Dangin Safinah, ya shige jikin Yaranshi. Tunda ya dawo dasu yake muradin jin sun kirashi da Daddy amma bai samu ba, sai Uncle suke kiranshi, a cikin mota ya ajiyesu. Sannan ya shiga ya zauna.
Lumshe idanunshi yayi, ranshi najin zafin kowa ma, haushi yake bashi, da ace lokacin da Safinah ta dawo suka tawo tare da babu wani ɗan iskan da ta isa masa kinibibi.
Jin yaran zasu d’aga mishi hankali, ya daka musu tsawa. Curewa guri guda sukayi tsoronshi ya gani muraran a idanunsu, kai hannu yayi da niyyar taɓasu. Aikuwa suka fashe da kuka, dafe goshinsa yayi tare da cewa.
“Kuzo bazan muku kome ba.”
Sake k’amk’ame juna sukayi suna kuka, bada Umarni yayi aka kaisu gurin wasan yara, duk yadda yaso ɗaukar hankalin yaran sunki sakin jiki dashi haka ya lodo musu chocolet ya ajiye musu, sai sun kalli juna sai su saka mishi kuka suna kiran Didi da Daddy.
Dakyar ya dawo gida dasu, yazo ya zubawa Batul su, ya fita.
Da mamaki suka bishi da ido.
Suna al’ajabin halinshi sam bai da dariya, kullum cikin dakewa da basarwa, ga wani izzar da yake damunshi sosai.
……..
Shi kuwa a ɓangarenshi ba karamin haushin yake ji ba, tunawa yadda duk aka manna mishi hauka, dan haka dole ya dakatar da kowa. Ya kuma nuna musu yafisu iƙo da ita.
****
“Wayyo Allah na karki kashe min Yarana! Ku min kome karku taɓa min yarana.”
Da wannan sumbatu na farka, tare da mikewa zan sauka a gadon, aka ririke ni. Shigowar Dudu tare da Dr yasake sani birkicewa, tare da ture masu rikeni.
“Dr Kyari riketa! Sai na mata allura.” inji Dr,
Kafin Dudu yayi abinda Dr yasashi sai ganin Ashraf sukayi yazo ya ɗanne gadon tare da rungume, cike da izza murmusawa Dr yayi tare da mikawa Dudu Alluran. Sannan yafita daga d’akin dole ayi d’aya cikin biyu. Shi bazai iya fitina ba amna tabbas dole Safinah tayi wani abu idan shine toh ayi magana, idan kuma Ashraf ne tuni yajanye daga gareta.
Duk yadda yaso ya kiyayye shiga sabgar Ashraf sai da ya kureshi, karshe sai ya bar zuwa asibitin, tunda ba a nan kadai yake aiki ba, nan ne asibitinshi na kanshi, sauran asibititocin aiki yake musu, da kuma kasancewar likitan shugaban kasa.
A fusace Abdullahi ya ajiye Alluran tare da finciko, Ashraf. Ya zabga mishi mari. Tare da cin akwalar rigarshi, ya fidda shi waje.
“Idan na kuma ganinka da Yar uwata, zan shayar da kai mamaki, haba me kake son tayi tace bata yinka ka rabu da ita kaje ka ɗibi yaranka.”
A fusace Ghaniyu yayi kan Dudu.
“Karka taɓa shi! Kanin Matata ce ”
Cak ghaniyu ya tsaya yana kallon Ashraf.
“Eh mana! Dole ta aureni koda kuwa zasu mutum”
Goge bakinshi yaƴi wanda yake zubda jini, kaɗa kai yayi suka bar asibitin.
***
A hankali na buɗe idona ina binsu Ummi da sauran mutane da ido, dr nake nima bakina yaƴi nauyi. A bakin kofa na hangoshi rike da kayanshi. Murmushi ya sakarmin,
Mika mishi hannu nayi, ya shigo ciki a sannu. Ya zauna a kujeran da Ummi ta tashi, duba ni yafara tare da gwaje gwaje, yana gama yace.
“Sannu Beauty! Kin auna arziki, har ina tunanin ko za’a fita dake asibitin Dr Al’amin makarfi, sai gashi brain ɗinki ya koma aiki normal, sannan babu ke babu hidaya dan ynx haka tana jail.
Yaranmu suna hannun Daddansu.
My Luv kitashi haka! Ganinki a kwance yasanya min zuciyata cikin damuwa, don Allah tashi mu ɗaura daga idan muka tsaya.”
“Toh bugun zuciyata! Zan tashi amma sai Allah yaso, ni dai karka guje ni.” na faɗa mishi a hankali,
Rike hannuna yayi tare da sumbata, yama rasa me zaice.
Bammm mukaji an rufe kofar dukkanmu sai da muka bi kofar da kallo. Yarana nagani a tsaye suna jan zuciya.
Buɗe musu hannu yayi suka shiga da sauri, suna sauke ajiyar zuciya, ɗagosu yayi ya dire minsu. Kwanciya sukai a jikina.
***
Bayan kwana biyu na warware sallama na Dr yayi, dan ba karamin shiga hakkin aikinsa muke ba, haka kawai zan kirashi nasa shi a gaba ina shagalina, haka zai biye min. Idan zai shiga aiki dakyar muke rabuwa, wannan soyayyar takara mana wani irin shakuwa fiye da baya, musanman da muka fahimci haukar da Ashraf yake akaina, sai na sake buɗewa Dr daman mushifimɗa soyayya.
Bayan sati biya Nannah ta takoma, dan taso su koma tare yace bai gama abinda ya kawo shi ba.
Sauri nake dr yazo, ina gyara zaman agogona zamu je gaida Ammah da bata ji daɗi ba, shine zanje gaidata.
“Didi! Na kai kayan motar Daddynsu Twins”
“Nagode Auta, agogona nake son daurawa yaki.”
Riko hannuna yayi zai ɗaura min.
“Didi!”
Amsar agogon yayi a hannun khalil, wuccewa Khalil yayi ya barmu A tsaye, zai kai hannunshi. Nayi baya cikin ɗaurewar fuska nace.
“Bana ciki da iskanci kark.”
Finciko hannuna yayi tare da murɗa minshi baya yayi, ya haɗani da jikinshi. Kiciniyar kwacce hannuna nake, amna yaki kuka nasaka mishi kuka.
“Ki kyale wancan gayen Safinah! Nine daidai ke, ni kaɗai zan ciki miki maranki, wan.”
“Allah ya min tsari na kiraka miji ko maza sun kare bazanyi fatar ka zauna dani ba,”
Sake ni yayi na wucce inda motar Dr yake, ina shiga na fashe mishi da kuka, jan motar yayi muka bar gidan. Shi kuma Ashraf ya wucce gurin Hajja Kaka ya zauna cike da damuwa. Yana kallon yadda take shan dafaffiyar madara, gyara zama yayi kafin yace.
“Yau ma ba nasara! Ta bishi sun tafi.”
Kare mishi kallo tayi takaici ta taɓe bakinta sannan tace.
“Ai sai katattara kabar garin nan! Domin kuwa aikine a gabanka tunda wancan kafaffiyar ta nacewa wancan nanatacce, toh kai kuma miskilin banza bazaka iya shiga tsakaninsu ba, yo sau nawa ina dakatar dasu, yar banza kana ganinta, kaga ruwan zuganda, amma fir dake ance sirarran mata jaraba ce dasu, ahi yasa take nanike mishi, wallahi tausayi take bani, domin duk ranar da ta faɗa hannunshi. Hmm”
Murmushi yayi kawai dan ya lura sam Hajja bata kaunar Dr.
***
A gidansu Dr mun samu Balkisu tazo, gaida Ammah itama. Nan Dr ya gabatar mata da nice zai aura, jikinta yayi sanyi har tanemi mu keɓe da ita.
Can lambun gidan muka je da ita, shiru mukayi sannan ta katse shiru da cewa.
“Hmm! Kinyi Sa’an miji na gari mutumin kirki wanda yake sa kyakyawan zuciya Safinah, Hameed tasan yadda zai kyautata miki, ya kuma kyautatawa duk wani na kusa dake, A farko bana sonshi har Allah ya nufa na haifi Adli. Iya girmamawa Ya nuna min ya kuma mutuntani, kuma ya min adalci a zamanmu, abin takaici ashe zanzo nayi kuka, tunda gashi Hidaya taja min nayi asaran miji na gari, gasu na haɗu da wanda baisan kimata ba don Allah ki zauna dashi da zuciya d’aya.”
Sosai ta bani tausayi balkisu ta haɗu iya haɗu ba karya. Amma matsalarsu ba abar gyarawa bace, tunda tana auren wani.
Duk sai na rasa me zance mata, sabida tausayinta, musaman da nake hango soyayyarshi a idanunta,
….. Sai karfe biyar da rabi muka dawo, bayan Ammah tayi min sha tara na arziki. Yana kawo ni ya juya yana sannan ya fara cewa.
“Safinah!”
D’ago kai nayi ina kallonshi dan duk lokacin da yayi min irin wannan kiran, babu wasa a maganarshi da zai min, kura mishi ido nayi zuciyata na bugawa.
“Ina son ki gaya min meye kike nufi dani? Kinsan na fara gajiya da abinda wancan yaron yake min, karki manta sadakina na hannunki saura shaidu, idan shine toh nasani idan nine cikin nan da wata ɗaya ɗaura mana aure.”
Duk sai na rasa meke min daɗi kuma yafimu gaskiya dan ko mawaye akawa haka zai ji zafi balle kuma shi da ya……
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 8 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Page.55
Sannan kuma ya cigaba da cewa,
“Ranki shi dad’e fushi ko jin zafin safinah bamu bane, asalima mu nuna mishi bamu san halin da yake ciki ba haka zai sanya shi fahimtar muhimmancin rayuwa, inso samune mu barshi da kulawar yaranshi hakan zai ƙara mishi sanin darajar mutane.”
Ajiyar zuciya Nannah tayi dan ta amince da shawarar da Gani ya bata, kuma zato aiki dashi.
Tabbas tayi kuskure me girma nafifita gudanar d’anta d’aya akan sadaukarwa da safinah ta musu, Kuma Inda ALLAH zata gyara daga yau.
***
Jordan….
Hankulan al’umma ya yashi ainun kasancewar Basu san Sultan Ashraf baya kasan ba, sai da aka kashe Shugaban Kabilar Banu Hussaini. Tunda ake rikicin masarautar ba a tab’a fuskantar tashin hankali haka ba, amma yau an wayi gari Jordan tana shirin zama magudanr jinin al’ummar kasar.
“Abba!!! Wai me ke faruwa ne? Gabaki d’aya al’amuran sai rinceb’ewa yaƙe, Ni na kasa fahimtar kome, na tabbatar akwai kulin da kuke b’oyewa amma bayan takurawa kaina ba, dan kasan ba zaka Laraba gaya min ba, amma ko ba kome duk abinda yaƙe faruwa a Jordan kana da masaniyar haka, ka bud’i baki kayi magana amma k’i cewa kome.”
Shiru ya ratsa tsakaninsu, Abu Zaria ya shafi tare da kallon Ammar, wanda ya shiga damuwa saboda, halin da masarautar tashi ga, da ciwon ya fad’awa D’anshi cewa da hadin bakinshi aka aurawa Sultan Abdullahi Bayahudiya, amma ya zaiyi Dole ya fad’i gaskiya koda itace hanyar rasa rayuwarsa da ya cigaba da ganin ana salwantar da rayuwar mutanen da basu ji ba basu gani ba,
“Ammar! Gaskiya ɗaya ce daga k’inta sai bata. Mun gina kanku da zuciyarsu saboda don zuciyar mu, muka kuma juyawa D’anshi uwanmu baya saboda ya samu d’auk’ak’a, idanun mu ya rufe da k’iyayyarsa. Burinmu shine mu hanb’arar da mulkinsa,
Bayan tab’a yafewa kaina ba, har sai Ashraf ya hukunta Ni, abisa laifin da na aikin.”
Nan ya bawa Ammar labarin abinda ya faru, sannan ya cigaba da cewa.
“Lokacin da Abdullahi, ya cika shekara Ashirin da uku, ya kai ziyara Palastinu, a can suka hadu da Malika Alexander, bansan ya akayi ba. Sai Bayan ya dawo da wasu watanni ya gabatar da Ita a matsayin matar da yake son aura, Ni naso dakatar da haka. Amma fir Ukshe ya hanani, eh ya hanani sabida Kusancinsa da Abdullahi, yafi kusancinmu. Haƙa na hakura na cigaba da bibiyarsu, cikin lokacin ƙalilan aka gabatar da bikisu a Cikin masarautar.
Bayan me ya faru ba,bayan bikin da wata biyu suka rabu, ta tafi dan har lokacin bamu san takamaiman abinda ya haɗa su ba. Sai daga baya Alexander ya Turi aka karba mishi takardar saki, tare da raba dukiyar Abdullahi biyu aka basu, bayan mutuwarsa da kuma bawa Ashraf mulki, Malika ta dawo mana da Yaro me tsananin kama da Abdullahi. Dole muka sallame ta, domin Bilal ba asanshi ba, kuma ba dukkan suka sanshi ba sai nayi ƙoƙarin an maida su tun kafin su had’u da Ashraf alaka Bilal yabawa Ashraf shekara biyar, dan haka a yanzu yana da Kusan shekaru talatin da shida zuwa da bakwai. Nayi baƙin cikin faruwar haka amma ya na iya tun da ya shiga cikin Zanen Qaddara ba makawa, wai ya tsallaka kowani zane kafin ya cimma muradun sa, da burkina.”
Ajiyar zuciya Ammar ya sauke Kafin yace.
“Tabbas kun makare! Domin kuwa Bilal shine Sarki na gaba, tunda Babu wani Sarkin toh mu namu mubaya’a ce, domin Yaron nan ba karamin shu’umi bane.”
Jikin Abu Zaria ba karamin sanyi yayi ba, asalima na samar rayuwar shi yaƙe dan ji yake kamar ya had’iye zuciyarsa ya huta da wannan halin da yaƙe tunkaro su.
Haka Ammar ya fita ya bar shi a dalilin yana tunanin halin da Ashraf yake cikin. Karo na farko kenan da yaji yana bukatar sanin halin da Ashraf yake cikin.
***
Nigeria….
*Hello! Beauty yakike?*
Murmushi nayi tare da gyara kwanciyata, na tura mishi.
*Lau! Ka bud’e data ina don ganinka.*
Ina don ya fannoni sabida d’aukeni da Ummi tayi, ta kawo Ni gyare-gyaren jiki har da nasu🙈 nona da na Headquart. Kuma tunda aka fara, Yasin naga canji, dan ma. Ina kin shaye shaye. Kafin naso ina jinta tayi booking Zumar goran tula, a gurin Maman Naseem, dan taji Ammyn Khairat suna hiran a mufarka mata, shine tasami Ammyn Khairat ta bata number, Aunty Mai Dambu, ita kuma ta bata number Maman Naseem, wacce take Gombe,sosai Ummi take son na rikitarwa Dr lissafi.
Shigowar kiranshi ya katse min tunaninsu, dauka nayi tare da gyara gashi na da ya kulle ce min fuskata,
Kuri yayi min da ido, ko kyaftawa had’iye yawu, cikin rawan Muryar yace.
“Beauty! Kina niman rayuwata ko!?”
Girgiza mishi kai nayi ina tsotsar Alawar da Aunty Yanayi tabani, na saukar da ni’ima, nace.
” Jikan na shiga Uku! Idan ka mutu dawa zanyi rayuwa, bar kira min mutuwa. Kawai nayi haka ne dan mu gaisa tunda bai maka ba, bye.”
“No karki min haka bangaji da ganinka ba. Bank’i na kare wunin yau ina kallon ki ba, Anya Safinah bani kasadar Aurenki ba, domin naga kinfi karfinsu ke matar Manyace, Ni kuma fakiri irinsu wanda dukkan kuɗaɗen asusun da basu wucce na.”
Katse kiran nayi dan raina ya b’aci, taya Dr zai min haka yadda nake fad’i tashi dan ganin na bawa zuciyar mu adalci amma rutsa idanunsa yake, sako ya turo min
*Dan girma Allah ki saurareni*
*Akan me? Kaje kawai yanzu na fahimci nice nake haukata akan ka, amma kai ko sunanta bakayi, kaje Nagode da kaunarka a gare Ni.*
*Don Allah nace kiyi hakuri mana*
Wani irin baƙin cikine ya kamani na tura mishi.
“Karka kuma kiransa Daga yau”
… Aikuwa naga naci, dan sai da ya had’ani da Ammahnshi.
Dr Abdulhmeed Zaki katagum’ ya fito daga yankin Arewa maso gabacin Nijeriya, wato bauchi, dan yanki Katagum cikin karamar hukumar Azare, mahaifinsa ya jima da rasuwa, Mahaifiyarshi me suna Hajiya A’ishah, su biyar ta haifa. Dr Hameed shine Babban dan, sai Khaulat, tana aure bauchi, sai Rafi’ah wacce take auren wani soja tana kunna, sai Saleem wanda shima yana can jami’an Kolkata, na kasar India. Sai Surar su wacce bata, jima da aure ba, tana da tsohon cikin.
A Yanzu haka Babban yaron Dr me suna Abubakar, yana da shekara bakwai, dake yaki maganar aure sai karatu tun bayar zubar mishi da cikin da Balkisu tayi, bai Kuma marmari sake aure ba, sai yanzun.
……. Ai tsabar naci sai da na ɗauki kiran nasamu Lafiya dan wuni nayi ina tara kiranshi,
Abinda yace min yasani kwarewa.
“Beauty! Gaya min sunan unguwar gani nan nazo.”.
Cikin inda inda, nace..
“Kunshe!”
Katse kiran yayi, ranshi kal Bayan mintinan ƙalilan yakirani.
“Please kifito! Ki min jagoran bansan gidan ba ”
Fitowa falo nayi masani Aunty Yaanah tana had’an min wani sabulu, zama nayi kusa da ita kaina a sunkuya nace..
“Aunty! Dr yazo!”
“Ko dai kika kirashi! Idan jini hakuri, saura yan kwanaki ƙalilan suka rage,. Idan kuma kika kuskure gajen hakuri ya kai ko kuka bari ya kirkiri Toh babu ruwa, tsabar fitina sai da kika gayyato shi zaki kama min iyayi, kishiga d’akina akwai farar Humra ki gogan a jikin ki.”
Duk wannan masifar da take bata d’ago ta kalleni ba balle nasa ran zata ga yadda nake ba. Da sauri na shi d’akinta naga kwalaben Humranu har uku, sai naji bari nayi Mix🙊 ashe akwai na tada fitina, na gama Sannan nafita. Na shiga kitchen na had’a mishi ruwa a tire, na ajiye na fita.
A can karshen layin na ganshi tsaye a jikin wata benz shi da wani mutum, suna hira.
Cikin jin kunyarsu na isa gurinsu, nace.
” Sannunku.”
Wani munafikin kallo yake nuna dashi k’asa-k’asa, tare da lumshe idanunsa, motar muka shiga,’ na cigaba da nuna musu hanyar gidan, muna isa na fito nazo na bude musu falon baƙin, sannan naje na kuma shigo dasu, sannan na koma ciki na haddi musu kayan tab’awa, na fito musu dashi. Ina ajiye wa na tsaya muka sake gaisawa.
“Amma Baby! Baka gaya min kana hanya ba.”
“Abba Ghana! Kaji ko? Itace da ta daga min hankali nazo tana gaya min haka, nayi magana tace ina laifi.”
Cikin dariya tare da niman tsokana Abba Ghana yace.
“Toh! Kai da aka bawa muƙamin baby ai bazara damu ba, kuma shi dama a rayuwarmu ta yau dole sai da hakuri, ina ba haka ba Toh sai zama yaki dad’in mafiya yawancin rigimar da ake fuskanta, a gidajensu daga waje muke asassata, dan mukan jingina niman da karya tare da rashin gaskiya, a duniyar nan idan kace haka zaku zauna Toh ba makawa bazaku taba fahimtar juna ba, sannan kai Namiji ne. Kafita hangen nesa, sama da ita ya kamata duk abinda zaka fada ya zama me kyau ne, sannan kaka girmanka tun kafin lokaci ya kure maka. Dan kane da gidan, sai kema Safinah. A kala zan iya cewa Dr ya baki kusan shekaru goma sha, bai dace kunshi abin da tun yanzun ya dace ki bashi girman shi ba sai kunshi ga ciki ba, bana don ace gauraye irinsu suna samun sab’ani tun kafin su shimfida rayuwar aurensu don Allah muyi hakuri da juna, haƙa zai sama mana zaman lafiya me daurawa a gidan mu.”
Sosai yayi mana nasiha tare da nuna mana muhimmancin rayuwa, naji dad’i dan da ya gama tafiya yayi. Ya barmu da Dr.
Sai aka barni da sunkuyar da kaina, bansan ya akayi ba. Sai jin saukar numfashinsa a kusadani. D’ago kaina nayi, ya tsare Ni da ido, yana hukunta Ni da kaifin idanunsa, sunkuyar da kaina nayi. Cikin shekarar Muryar nace.
” Shida saura! Kaci ka kama hanya.”
Murmushi yayi min sannan yace.
“Bani zuwa ko ina sai an biyani bashin kiss daina.”
Zaro ido nayi, ina kallon yadda ya lumshe idanunsa, gefen shi kuwa ba kome ke damunsa ba sai kamshin Humranu da yake d’aga mishi hankali, jan iska yayi sannan ya fesar. Bude idanunsa yayi cikin wani irin murya yace.
“beauty! Ina son kamshinki”
Kallon shi nayi da wutsiyar idona naga yadda ya matso kamar zai shige jikina,cikin sauri na matsa. Matsowa yayi sosai kamar zai shige jikina, Muryar na rawa nace.
“Dr! Please karka.”
Hannuna yarike yana jin kamshin da yake fita a jikina yace.
“Bayan iya cutar dake ba, kawai kamshinki ne yake fisgata, hmm.”
Mikewa yayi sannan yace.
“Baki haɗa Ni da Auntynmu b.”
Mikewa nayi tare da cewa..
“Toh bari na mata Magana.”
Sai ji nayi ya rungume ni ta baya, a razane na shiga tureshi, haɗa Ni yayi da jikinsa yace..
“Perfume d’inki ne ya sanya i cikin wani yanayi.”
Cikin hikima da dabara na kwace kaina, na gudu cikin gidan ban yarda na fito ba sai da Aunty Yaanah, muka fito cikin k’amewa…..
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 6 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE….
Page.٥٤-54
“Didi!” suka tawo a guje, buɗe musu hannuna nayi suka shiga, baku sani bane da ya tashi tafiyarshi har da yarana ya tafi, yazata zan d’aga hankalina ne, sai yaga ban damu ba, asalima uzurin gabana yasha kaina, kuma nayi alkawarin bazan taɓa damuwa da yaran ba, dan zai iya amfani dasu a matsayin weakpoint ɗina.
……. Dake Allah yayi musu baiwar barna suna zuwa d’an dambun naman da nake ci, tare da fruit salad, zubda dambu sukayi. Sannan suka koma zasu ɗauka min salad. Ɗauke bowl ɗin nayi, aikuwa Aanih ta fasa kuka tana bin bowl ɗin.
“Ke! Bana ciki da fitina! Wucce ko na ɗauko bulala.”
Juyawa gurin Uban tayi tare da faɗawa jikinshi tana gwaranta mishi larabci, murmushi yayi sannan ya d’agata sama yace.
“Yi shiru Mamana! Ya kuka iya tunda anyi muku yankan kauna, an yaye ku lokaci baiyi ba, sannan anki an zauna sabida ku! Shima abin da zaku ci sai an muku gori, kuda kome kuke so nunawa zakuyi sabida isarku da mulkinku, amma duniya tayi muku yankar kauna.”
Ko isata kallo basu ba, sabida na rena yinsu, cak naji an ɗauke bowl ɗin aikuwa suka fasa dariya, ajiye musu yayi dan kinibibi, wai yaran nan sune ke shan fruit da cokali.
“Barkan da zuwa Ashraf! Kwana biyu shiru!?” inji Hajja,
Share su nayi na cigaba da abinda nake, ina jin hajja na cewa.
“Hmm! Allah ya baka ta gari, amna abin ba magana, daɗin abun kai kafi karfin a kiraka sankan han, gaka jarumi me jini a jika, bandama zubda kima ina basarake ina.”
D’ago idona nayi na kallesu, tuni ta waske, harararta nayi sannan na mike zuwa kitchen na ɗauko tsintsinya da abin kwashe shara nazo na gyara inda yaran suka ɓata.
Ina jinshi yake ce mata ya kawo yarane su gaisa zasu tafi Oman ne, zai kaisu kafin bikin zai kawosu dan yana son su saba da Amminsa.
Kiran Ummi tayi suka gaisa dashi sannan ta gaya mata abinda yace. Fuskar Ummi ɗauke da murmushi tace.
“Ai bani ce uwar Yaran ba! Safinatu zaku gayawa dan ita musulunci ya bawa kaso me girma, sannan kuma yabata damar ta rike yaranta, amma a wata fuska tunda tasame wanda zai rike mata musanman mahaifinsu, toh yana da kyau ta barsu dashi kodan kare martabarsu toh haka ma yayi zaka iya tafiya dasu. Amma bari na maka magana da ita tunda naga ta koma ciki.”
.
Ina zaune a bakin gado, yaran suna kwance a jikina, Ummin tashigo, zama taƴi tana kallona yadda na zurfaffa a cikin tunani. Zama tayi a kusadani cikin barkwace tace.
“Anya bazan kira Dr yayi hakuri ba Balaraben Jordan ya ɗauke masa hankalin mata?”
Gyara zama nayi cikin damuwa nace.
“Hmm! Ummina! Tafiya da yaran zai yi, ni bana son haka. Dan nice nafi dacewan basu tarbiyan da nake so, amma babu yadda na iya tunda nasame wanda zai taimaka min.”
Na karshe maganar tare da sunkuyar da kaina..
” Ki barshi ya ɗauki yaranshi, ya tafi dasu dan haka shine gatanki, kuma rufin asirin tare da suturan yaranki, amma idan akwai matsala toh zaki iya dakatar da haka, ni a nawa hangen tafiyarsu shine rufin asirinki.”
Lumshe idanuna nayi tare da sauke ajiyar zuciya. Sannan nace
“Toh ba damuwa! Amma Ummi zai na kawo min su.”
Yadda naƴi maganar ya karyar mata da zuciya sosai da sosai, fita tayi a ɗakin, tabarni cikin kewarsu tun basu tafi ba, dan yaran suna da mugun shiga rai, musaman idan suka haɗu da ɓarna, lumshe idanuna nayi raina na baci, wato nayi sirfen nayi dakar na tankaɗe yazo ya ɗauke garin EH mana, kura da shan bugu gardi da amsar kuɗi ko ba haka ba.
Ware idanuna nayi cike da bakin ciki, sai dai na rigada na gama magana, bazan ce zan kuma.
Maganar da taje kunnen Abba, yaji ba daɗi dan yayi mugun sabo da jikokin da yaki a baya yau gashi, yana jin ba daɗin rabuwa da su.
Dudu da yaji maganar shi da Nanah Asma’u basu ji daɗi ba, kai tsaye suka ce zasu makashi a kotu, sai da Ummi tayi musu faɗa. Nima ban ɓoye musu ba nace.
“Da asirina ya rufu shine zaku bankaɗe min, don Allah ku barshi ya tafi da yaranshi, dan yadda kuka ganshin nan tsaf idan ya birkice min toh wallahi bazan ya lakwasa shi ba, don Allah ku barshi yayi tafiyarshi, ba dai ya amsa nashine ba, ai ni ya gama min kome wallahi yaje dasu. Ai ba rikesu yace zai yi ba zai dawo dasu dan haka suje.”
Duk sai jikinsu yayi mugun sanyi, muna cikin jimamin ita kuma wancan damanmiyar tsohuwar tazo da nata buhun rigima.
“Yo ba dole ya ɗauke yaranshi ba, tsabar son kai ku hanashi yarku kuce zaku hanashi yaranshi, Wallahi ya kyauta min yaje dasu ba kuna gadara dan wancan me kirjin kamar ta ɓera ce ta haifesu ba, sai me kurike yarku, shima ya rike yaranshi. Ban da bakin ciki da cutar kai har yaro kamar wannan yazo nimanki ki badawa idanunki toka, kice baki kaunarshi! Shin da zai auru guzuma irnki ba damu ba sai ke da kika samu rana bari ki baza haɓɓar zaninki kiyi shanya son ranki sai me dan baki aureshi ba iya dai dai gwargwado uwarshi ta muku halacci.”
“Iya halaccin da tayi kika gani! Ni wanda nayi sai da ya jefa kowa nawa cikin garari. Sadaukar da kaina da rayuwata nayi na shiga turmushi halaka. Ke kinsan irin azabar da nasha a hannunshi, kinsan wahalar da naci a hannunshi, banda rabo ajali me zai kaini Jordan, idan banda tsautsayi da kaddara me zai kaini jordan, ke da kanki kika so dakatar da Abba kar ya kore ni, amma yaki saurararki ya jefar dani a kofar gida, domin mahaifiyarshi domin zuban hawayenta, hajja wancan yaron ya keta min haddi, ban zargeshi ba banji haushinsa ba. Kawai nayi abinda ya dace shine kike ƙalubalantana, Hajja duk abinda yayi miki ki gaya min, duk abinda ya fito bakinki ki faɗa min bazan tab’a jin zafinki ba saima nayi ƙoƙarin gyara kuskuren da nayi abaya.”
Jikintane yayi mugun sanyii cikin raunanniyar murya tace.
“Bana son da kuruciyarki, ki fara raba kan yarankine! Burina ki zauna akan yaranki kamar kowacce mace, ina cusa miki kiyayyar likitane dan Uban yaranki, Amma kiyi hakuri, bansan zan cusguna miki haka ba.”
“Hajja kenan! Dake ce aka sace na wani lokaci bazaki faɗi haka”
Ina gama gaya mata maganar nayi wuccewata, ina shiga ɗaki na fashe da kuka, wannan dalilin ya hana kowa maganar Ashraf dan sun lura banda dole bana kaunar wani abu ya shiga tsakanina dashi, gani suke matuƙar suka min maganarshi zan ɗaukesu marasa adalci, tundasu Jiyaune ba ganau ba, akan halin da nashiga, dan haka suka zuba min ido tunda dole nice zan dakatar da shi, kuma nayi nasaran haka bana fatan na kuma kamanta rayuwar baya, wanda yake cikin zanen qaddarata.
***
Washi gari ya zo yakwashi yaran ban ɗaki nashiga tare da buɗe panpo, karan panpon ya hana aji sautin kukana. Kuma Allah ya taimaka har nagama na fito babu wanda yaji ko ya gani, dan ina gamawa na kwanta tabbas ina kewar yarana, tun basu min nisa ba na fara jin kewars.
…… Da yamma da dr yazo yake tambayana ina suke nace.
“Sun tafi Oman dashi.”
Shiru yayi cikin damuwa yace.
“Sai nake ganin kamar mun zalimce shi! Domin.”
Wani irin kallo na mishi wanda yasashi yin ayan dole a maganarshi.
“Meye muka mishi na cutarwa? Ni a ganina hakan shine adalci yaje dasu ma na bar mishi su nima Allah ya dubeni da idonun rahama.”
“Amin! Insha Allah ni!” ya nuna kanshi cikin tsokana sannan yace.
“Uku zan loda miki once!”
Buɗe motar nayi cike da jin kunya nace.
“Ka gama lafiya ni nayi cikin gida bazan iya jure zantuttukarka ba zasu iya toshe min majiyana.”
“Zo man yan mata! Nifa ina da.”
Ban tsaya jin me yake dashi ba na cikawa bujena iska.
***
Oman….
Da motar masarautar Oman akazo ɗaukarsu, Yaran sun makaleshi kam. Sai zare idanu suke, dan basu gane kowa ba.
Koda ya isa gidan, a falo ya zuɓe kanshi na mugun ciwo, lumshe idanunshi yayi wanda sukayi jajjur,jijjiyar goshinsa tare da na saman idanunshi sun tashi raɗa raɗa, ita kanta Nannah da taganshi sai da ta razana sosai, cikin sauri ta iso gareshu tana taɓa goshin taji kamar wuta lokaci kalilan ta birkice masa, duk yadda yaso nuna jarumtarsa ƴa kasa, dan dole ya kwanta akan cinyarta yana zubda hawaye ga ciwon kai ga ciwon da yake ji a zuciyarshi na rabuwa da safinah, dan sai yanzun yasan da yayi mugun sabo da ita, bai taɓa ɗauka cewa kallon da yake mata na baiwa yana da nasaba da zuciyarshi ba, sai yanzun da yake jin duk wani bugun da zuciyarshi take da sunanta yake bugawa, duk wani kuzarinsa da sunanta yake sarafata bai taɓa tunanin zata zame mishi karfen kafa ba sai yau, ji yake kamar tare aka haliccesu. Idan da za a barshi zai iya kiranta da wata shashin rayuwarsa ce ita, amma ina kodan sadaukarwa da ta mishi tilas shima ya mata, kodan tsayawa da tayi har yasan waye shi dole ya nisanceta. Idan haka zai sanyata farin ciki a shirye yake yayi nisan kilomita miliyoyi dan ita, ta rasa kome nata dan shi da mahaifiyarshi,dan haka baya jin zai nuna sonkai a gareta ba. Baya jin zai zubda sauran mutuntakarshi a gareta ba, iyayinta tayi toh me zasu yi dan fansar kansu, shi dan kanshi y Lalata mata gobenta, yau dan tana niiman yanci ya gaggara bata farin ciki a yanzun da tasamu bazai zama mugu ga samun N’imarta ba, Safinatu tayi iya kokarinta a matsayinta na mace ta shiga jordan ta ɓadda kama a cikin bayinshi, tasha wahala ainun dan haka ya barta tayi farin cikk domin yayi wani abu kamar butulcewa Ubangijine da kuma son zuciya. Dan haka ya hakura da ita koda abinda tayi musu a rayuwarsu.
Dafe kirjinsa yayi a hankali sabida zafin da yake masa, cikin rawan murya yace.
“Ammina! Kirjina zai fashe.”
A gigice ta fasa kuka tare da kiran Ghaniyu aka, fita dashi zuwa Asibiti.
Cikin gaggawa aka amsheshi, aka shiga bashi kulawar, cikin yardan Ubangiji aka samu numfashinsa ya dawo sai lokacine Nannah ta tuna da yaran da tabari.
Sam Nannah taji zafin abinda ya faru dan tsare Ghaniyu tayi da tambaya, shima ya gaya mata iya abinda yasani bawai gulma ko munafunci ba, just ya gaya mata halin da Ashraf ya tsinci kanshi, kuma ya roketa da kartayi wani abu a cikin alamarin, dan shi yayi imani da Allah akwai wani abu na daban da Ubangiji ya ɓoye shi yasa haka ta faru a tsakaninsu, sannan kuma idan tayi magana. Iyayen Safina bazasu ji daɗi ba, don Allah badan kome ba kodan Ashraf tabar maganar Safinah tayi aurenta, dan koda anyi aurensu toh ba makawa zaman lafiya zaiyi karanci a tsakaninsu, sabida dukansu sun rena juna, basu san girman juna ba, amma yin auren Safinah zai sanya Ashraf sanin muhimmanci mutum a rayuwarshi, zai kuma san girman so a duniyarsa, zai kuma san abinda ake kira tausayi da taimakon mabukaci, wanda duk yasan halin Safinace, amma idan yawayi gari yayi koyi da hakan tankar wata nasara ce da Safinah tasamu akanshi, dole ya rabu da izzar mulki da kuma jin kai, dole ya ajiye alfahari da takama. Yadda yake jinsa, dole ya koyi mu’amala da kowa idan ba haka ba, bazai taɓa zama shugaba ba, idan za ace shugaba bayi da tausayi ga talakawarsaa, bai da shauki a duniyarsa toh bazai taɓa jagorantar Alumma ba, suma Abokan gabanshi zasu cigaba da cin karensu ba babbaka, sannan ya kara da cewa dole ya koyi mu’amala sa mutane, domin yin haka zai sanya talakawa suci gajiyar shugabancinsa dan haka idan ya tashi muma tsaya mishi zamuyi, dan ya zama wani gobe bawai su gurgunrtan masa da tunani ba, a yanzun da yake cikin zafi ya dace a sauya mishi tunani……..
_Don Allah ku gafarceni dama nayi muku Alkawari Yan paid grp duk rintsi bazan rasa muku ba, nagode da kaunarku a gareni😊_
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 6 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: I just published “Page 56” of my story “MASARAUTAR JORDAN!!!”. https://my.w.tt/u5WG6DdY03
_HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
_Don Allah ina cigiyar Wata baiwar Allah Mrs Sadeeq idan taga sakona dan girman Allah tayi min Magana 🙏🏼🙏🏼😭_
BOOK ONE….
Page.56
Koda muka shiga da Aunty Yaanah, suka gaisa sai bina yake da Idanunsa ban damu ba daina fadawa tunanin da nayi bansan fitar Aunty Yaanah ba, sai kunshi nayi kamar zai shige jikina, a tsorace nayi baya. Ya kuwa bini har muka kure bangon falon, kuka naso saka mishi. Amma ina cikin zafin nama ya rungume ni yana sauke a jiyar zuciya, yayin da yake jin Wani sabon fitina na ƙara bijirewa mishi, duk yadda yaso kar abin ya girmama, sai da hakan yaso faru dan badan Allah ya shigo al’amarinmu da babu bazai faru ba, bakina kuwa saura kiristoci a cinye min su banda nonuwata da suka sha matsa a hannunsa. Kuka nasaka mishi tare da tare da tureshi, ina cewa shi nace.
“Don Allah ka kyaleni! Wai me haka?”
“Beauty kece kika daga min hankali, Beauty wani irin turaren ne haka me mugun tasiri, Beauty bana jin zan.”
Rufe mishi bakinshi nayi da tafin hannuna, cikin rawan Muryar nace.
“Don Allah! Karka lalata aurenmu a nan kayi hakuri bazan kuma sakawa ba sai nazo gidanka.”
Dakyar da jini ya rabudani Ni, inda Abokinshi yazo ya ɗauke shi zuwa Airport, bai b’oyewa Abokinsa halin da yake ciki ba, kafin su isa Airport, ya tsaya a wani babban janyo gurin sayar da maganin ya saya mishi Allura yazo yayi mishi dake shima likitane. Suna isa Airport din ya soma jin sauƙin al’amarinsa.
Bai bar Maiduguri da ciwon ba, dan yaji sauƙin alluran Abba Ghana.
……..
Yana isa Abuja, ya kirani a kasalance.
“Beauty! Na iso guda lafiya. Kiyi hakuri da abinda ya faru Wallahi bayin kaina bane.”
“Ince ka isa gida lafiya?” Na tambaye shi,
“Eh Wallahi na isa yanzun haka ina kwance a falon Ammahna.”
“Good biyu!kayi barci me dad’i har da mafarkina.”
Shafa kirjinshi yayi, sannan yace.
” Zan kiraki bari nayi sallah kisan a gajiye na dawo.”
***
Kamar munafuka haka na shige cikin gidan bayan bakwai tiren kitchen, d’akina na shige tare da fad’awa ban daki, naso nayi Allah sai nake shakku. Kawai nayi wanka tare da alolar na fito. Nima na tada sallar. Ina idarwa ban tashi ba sai da na maida Isha da shafa’i da wutir.
Sannan Aunty ta shigo min da fruit da nake sha dan shine abincin darena, ta mika min tsareni da ido tayi cikin rashin walwala tace.
“Karki kuma min gangancin da kika yi nan, daga yau hiranku iya waya idan ya kuma zuwa sai na kira Aunty Mariama na gaya mata, ai bawai bata iya bane bata don ki zauna a can yana ganinki ne ba zai daukansu dake ba, shine da kawo min ke Ni bari ki min iyayi gayyato shi Wannan ya zama na farko da na karshe.”
Wallahi Ni a tunanina turaren da nasara zata balbaleni Ash’ari ita can wai dan na gayyato Dr ne, Ni sai yanzun abin ke bani dariya,.kuma wa wani zai min dariya sai naji haushi fa?(☹️)
Bayan nice nake jefa kaina cikina matsala, kuma banda shirme irin yawa wai an ce nashafa daya sai da na hada da guda ukun dake wajen Yasin da Zata san abinda nayi sai ta kusan dafani d’anye ta cinyeni. Allah nima d’in nan bani da sauki da, zan iya cewa fitinata Yarana suka d’auke, ga shegen son yin gwaninta. Amma abin takaice karshe nice a ruwa (🤭)
Dan haka nayiwa kaina alkawarin bazan kuma gayyatar Dr ba, yayi hakuri idan naje gidanshi ya cinye i yadda ya kamata.
Sosai Aunty Yaanah take bani kulawa, dan wannan ramar da Hajja take mita akai na ciko. Yan kananun nonuwata sun ƙara girma da cika, tunda dama lokacin yaye su Aanih zo ba na yayyesu.
Bani da damuwa sai na yarana, dan cike da soyayyarsu. Wanda nake ji ko wuka aka sanin na tabbatar zan iya sadaukar da rayuwata dan su. Shi yasa da Ummi takirani nake tambayar ta ko Ashraf ya kirata ya haɗu ta da yaran sai tace scale tunda ya tafi bai kira ba, hmm nace mata, tare da manta batun na shiga Uzurina.
***
Oman….
Zare farin glass din fuskarshi likitan yayi cike da damuwa, ya zubawa File d’in Ashraf ido yana rasa me zai ce, a sannu ya d’ago tare da kallon Nannah da Ghaniyu, cikin sanyi jiki yace.
“Ma jinyacinku yana fama da mugun damuwa, wadda zai iya kaishi da kamuwa da yawan jini ko bugun zuciya lokaci daya kuyi kokarin ganin ya samu Abinda yake so inba haka ba, Toh gaskiya zaku yi hakuri da shi, dan zuciyar sa tana cikin damuwa sosai.”
Ɗan jim yayi sannan yayi yar rubuce-rubuce, ya mikawa Ghaniyu.
“Zaku iya sayo wannan magani ne da allurai ”
Amsa Ghaniyu yayi tare da godiya, ya fito zuwa dakin da yake kwance. Zauna take aka kujerar da yake fuskanshi, ta kura mishi ido, yaki take da zuciyarta akan al’amuran yaronta gani take shawarar Ghaniyu zai iya jefa mata d’a cikin mutuwa, dan yanzun haka ta fara jiyo kamshin mutuwarshi.
“Eh bazan iya ganin gawarka ba, India Binti ce muradun karni zan nima maka ita, zan cika maka burinka. Bazan rasaka ba zan baka farin ciki da lafiya da karfina.”
Safe goshi Ghaniyu yayi lokacin da yaji abinda take cewa, *Shi kenan ta zata lalata kome! Ya Allah ka nisanta Safinah da Ashraf dan girman kudirar ka, Ya Allah lalata duk wani shirin Mahaifiyar sa, Ubangiji kaine mafi girma da daukaka Ya Allah karka basu nasaran aurawa Ashraf, Ubangiji kafini sanin halin da kasata take ciki, Ubangiji ka cusa mishi soyayyarta yadda zai iya fuskantar Al’ummar cikinta, Ya Allah nayi wannan rokone dan ka sauya rayuwar shi daga me zafi ya koma Mutum me nutsuwa da Adalci, me kaunar Al’ummar sa da duk zuciyar shi.*
A ranshi yayita biye Addu’a
(🙄 Yo ai Nina zata kaima kana ciki ne ashe dan wani burinka ce kai ware 😏)
……
Tsayuwar yayi tare da ajiye takardar da aka rubuta. Yace,
“Gashi nan ya rubuta mishi wasu maganin da allurai, zanje na sayo.”
D’agowa tayi cikin tsare gida tace.
“Gobe Insha Allah zan tafi Nigeria!”
Cikin girmamawa ya gyada mata kai, tare da cewa.
“Allah ya kai mu.”
Daga haka bai kuma tofawa ba, har ya fita sayo maganin bayan tabashi Atm card.
….. Yaran kuwa suna gurin Amirah Zahrah, ita ta d’aukesu. Duk sai suka koma wani iri, ba walwala duk sun koma kamar marayu, dan rikicin da barna sam babu farin ciki a tare dasu.
****
Nigeria….
Wato a garin Abuja kawo kayan lefe aka daga gidansu Dr. Kayane na alfarma, zan iya cewa kayan daga India. Dan ya kirani yake tambayata ina saka sari. Nace masa eh, shi yasa Nannah Asma’u da ta turo min na fahimci ga Kayan ba a kasar nan aka saya ba.
…… Gaskiya Irin karɓan da aka musu yayi musu dadi, ina wanka ya kirani, ina fitowa naga 3 miss call. Ɗauka wayar nayi na tura mishi.
“Baby yanzun na fito wanka, an sorry”
Myrmushi ya turo min, tare da cewa.
*Beauty! Saura kwana nawa zaka dawo, Wallahi zanzo da na gaji da abinda ake min*
A ruɗe na fara niman abinda zan fada mishi ya hakura,
*😩 Baby! Zaka jefani cikin matsala ce fa,kaga wancan zuwanka kashiga damuwa sabida don Allah ka hakura, sauran yan kwanaki na zamataka gabaki d’aya sai yadda kayi dani.😢*
*Beauty! Wallahi nayi hakuri fa,ranar da aka daura auren. Ba makawa Ni zanzo na d’aukeki dan na fara nima mana visa*
*Wayyo Allah na, Dr ince nasaka min kome ba ko?🤭*
Dariya ya fara turo min kafin yace.
*🤣😂😆 Yarinya kifara shirin haduwa dani, dan babu sauki a tare dani, idan na ƙamari zaki wahaltu.*
Zuciya tace ta shiga kunci da damuwa,sosai me zan bawa Dr a matsayin dandano darena na farko dashi, tura mishi sako nace
*😪😭 Amma sorry Baby bani da abinda zan baka for de first nyt.*
Kirana yayi na dauka ina kuka, sosai me tab’a zuciya me saurarena, yace.
“Beauty! Waye yace miji Ni Budurcin nake hari, kicire Ni a cikinsu, Ni wannan bakin nake so. Idan kullum za a bani a matsayin abin ƙaryata na safiya dangi kowa murna, sannan wannan daren bakin kawai nake so a barin shi nayi yadda nake so, dan akwai wani sirri a gurin. Beauty ina d’inki da zuciya daya ba wani abu nake bukata a gareki ba, yarda ki da amincewarki ya isheni, don Allah karki ce min oo.”
Murmushi na sauke nace.
“Baby! Nagode”
Dariya yayi sannan yace.
“No need, dan akwai lokacin da zaki ce min haka, Ni kinji labarin yarana kuwa ina kawar su.”
Yar dariya nayi sannan nace.
“Baby! Wallahi nima banji motsi su ba,”
Mun jima muna hira sosai kafin muka yi sallama, gyara kwanciyata nayi ina tunani yarana, jan wayata nayi na duba kudin ciki sannan na shiga niman Ghaniyu.
Dakyar ya dauka cikin zakuwa nace.
“Yayana! Ka manta dani kanwarka”
Jim yayi sannan yace..
“Ayya koyi hakuri abubuwan sun min yawa, bani da lokacin kaina sai na Sultan Ashraf.”
Ban damu da masana make faruwa ba, nace.
“Ayya sannu, dama zan tambaye ka ne, idan kana kusadani Yaran nan ka basu naji Muryar su.”
Sai ya rasa me zai ce min kawai yace.
“Bana gida ina asibiti!”
A dame nace mishi,
“Waye ba lafiya?”
“Sultan! Tun ranar da muka dawo,Amma yanzun da sauki tunda jiya tashi da kanshi.”
“Allah ya bashi lafiya, kana kusadashine?”
“Eh!”
“Toh bashi wayar”
Mika mishi wayar yayi.
“Assalamu alaikum”
Can kasa ya amsa min. Ban damu ba, nace mishi.
“Ya jikin? Don Allah badan na isa ba sai dan Allah da kuma Al’ummar da suka sa ran su akanka, da kuma yaranka, karka cutar da kanka, Ashu! matsayinka a gurina babba ne, dan ina maka kallon Kaina Abdullahi ne, yaran da suke tsakaninmu ka d’aukesu amatsayin ƙaddararmu. Ashu Don Allah ka cire damuwar.”
“Cizon lips dinsa yayi sannan yace.
“Waye! Yace miki sabida ke nake ciwon, sannan da kike cewa kin dauke Ni kamar kaninki jifa kin rena Namiji da ya tsorataki a dare daya shine zaki kirani a matsayin kaninki, Safinah da kika jefa min yara cikin mareicin uwa shine zaki ƙara min da wani rashin kunyarki zaki min Maganar banza, kashe waya ko na biyo iska na baki mamaki.”
Cikin karfin hali nace.
“Dalla can! Bani guri har ka isa ka bani tsoro, da kake cewa na sanya yaranka maraice, dama zuwa nayi dasu Kayan ka ajiye kuma kazo ka dauka, kuma sai akayi ya-ya auren nace banayi, indai dan fyaden da ka min ne kake alfahari, kaje Ni na Barka da Allah mugun azzalumi macuci ka lalata min rayuwa ka cutar da iyayen, ALLAH yasa ka mutu ma………
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura4 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
_Don Allah ina cigiyar Wata baiwar Allah Mrs Sadeeq idan taga sakona dan girman Allah tayi min Magana 🙏🏼🙏🏼😭_
BOOK ONE….
Page.58
“Zan tafi dukda bana hango nasara a tafiyar ba amma ba zan cire raina ba, zanyita da duk zuciyata koda haka sai rage min tarin darajar da suke ganina da shi. Bazan taɓa barinka cikin damuwa ba,zan iya ƙoƙarina akan haka, ka nimeta ka bata hakuri.”
“A’a Ammina! Karki mata dole, kibarta ta zauna da zabin ranta. Kar muso kanmu da yawan haka,kar dan son kai mu sayowa kanmu zubewa kimarmu,kyaleta ta zauna da abinda ranta yaƙe so karmu mata dole.”
Jikinta ne yayi mugun sanyin, zuciyar ta take jin ba dadi, tausayi shi da na yan jikokinta ne ya cika mata zuciya. Girgiza mishi kai tayi cikin Kwari gwiwa, tace.
“Abubuwa guda biyu a duniya ana iyayi yaki domin su, So da kuma dukiya.”
Kallon shi tayi sosai cikin kwarin gwiwa tace.
“Akan SO! Da kuma kai zanje na dawo maka da abinda da ranka yaƙe Muradi.”
“Hmm nifa bana sonta! Makomar Yarana nake dubawa, idan da zata amince, tazo ta zauna da yaranmu yafi taje tayi Wani auren.”
“Baka sonta kake shirin mutuwa sabida ita, ka rufe min baƙin ka. Safinah dakai ta dace, bada wani namiji ba! Kaina farin cikinta kaine darajarta kaina duniyar, tun fili azal na gina maka soyayyarka a zuciyarta, son da take maka yasa ta iya zuwa daukoka, dan tana da kwarin gwiwa idan taje zata dawo dakai gareni.”
“Ammina! Safinah bata sona Abdulhmeed take so, bazan iya zama da matar da zuciyarta yake ga wani namijin kiyi hakuri ki barta tayi zamanta, zanje Nigeria nima kodan yarana zan maida matasu su, bana son ganinsu cikin bakin ciki da kewar Mahaifiyar su bayan tana raye, ba mutuwa tayi ba.”
“Toh sai dai mutafi tare tunda haka ne amma kasa a gwiwa ba, dole na nima maka aurenta.”
Haka suka yi ta tufka da warwara, har likita yazo ya sallame Ashraf. Suka dawo gida, inda suka fara shirin tunda bikin saura sati Uku.
……….
***
Jordan…
A yau aka sake Ukshe! Yana fitowa yasa aka fara, kwaskwarimar masarautar. Zuciyar shi cike da farin ciki Wato yadda ake kawar masarautar sai abin ya baka sha’awa balle kuma part ɗin da Bilal zai zauna, anyi mishi wasu Irin ado na musamman ga gyaran da yake samo. Saboda kuɗin Baitul malin masarautar ake diba ana zubawa, a aikin idan ka duba ko ina da sauran mutane kowa a kage yake yaga abinda yasa akewa masarautar kwaskwarimar. Tunda Abu Zarri ya fahimci shirin da ake, ya tattara cikin dare zai bar masarautar, amma aka hana shi fita. Haka ba karamin d’aga mishi hankali yayi ba, tabbas Ukshe ya gama shirya masa tsotsa.
…… Koda suka tare shi, har ya juya zai koma yaji muryan Ukshe yana cewa.
” Hana kai kuwa har kasar ne! Ni da ake son kaga yadda ake shimfida mulki iya ganin idanunka, Abu Zarri na rantse maka tari me kyau sai naso kayi balle kuma farin ciki da zaran Bilal ya shigo toh duk cikin zaku koma kuna lasar ƙasar takalmina ne, kai hatta Uzaif! Da yake D’ana. Bazan barshi yasha ba dan yashi ga sahun makiyana, sai na murkusheku baki d’ayanku, sai na mutsuke ku, kamar yadda nake mutsike takalmin kafata, sai na d’and’ana muku madarar azaba, Kana da uƙubana sai kunshi kuna rokone na baki damar kashe kanku, ina cewa ku ɓace min da gani. Dole ma na dauki fansar abinda kuka min.”
(🤣😂 Yacin akwai bala’i a jordan)
Murmushi Abu Zarri ya sake masa cikin ƙarfin zuciya ya taka har gaban shi, ba tare da ya damu ba ya tsinka mishi mari.
“Maza murkushe Ni!” Ya kuma tsinka mishi mari yace.
“Shayar sani madaran Azaba”
Sake kifa mishi wani marin yayi cikin izza ya nuna mishi yatsa yace.
” Ni sai nasaka ka gudun niman mafaka a cikin masarautar nan, kai azabtar damu zakayi Ni kuma hana ka farin ciki zanyi kana ji kana gani sai ka rasa inda zaka tusa kanka, kai da ka gayyato su kai zaka fara d’and’ana Uƙubarsu banza shashasha, wanda bai san ciwon kanshi ba Wallahi da ka bari na fusata sai na karya maka karasa ka mutumin banza kawai.”
Haka Abu Zarri ya gama kiikkifa mishi mari amma Ukshe ya kasa cewa kome, kuma da gaske marin sun shige shi.(🤣😂😜). Haka ya ja kekenshi zuciyarshi cike da bakin ciki Irin tozarcin da Abu Zarri yayi mishi ina laifin ya bishi zuwa gida.
Haka aka shirye-shirye, ga bayin da ake sake dibansu, dan ashe da suna cikin rahama ne lokacin Sultan Ashraf, yanzun kuwa kowa cin uwarsa yaƙe.
Iskanci kuwa ya ci Uban na da, dan yanzun har part ɗin bayi ake zuwa azo yi musu fyade da karfin bala’i.
Wannan rawan da suke a da can baya Cikin sutura me dan mutuncin Toh yanzun kusan naked suke yinshi, dan wani d’an kafen suke sakawa wanda ya rufe gabansu, bayan ɗuwais dinsu a waje sabida iya bayan wando siririne, Duk Kusan ɗuwais yana waje. Dake dama suna shakkar kar Ashraf ya sani ya lalata musu shiri yasa basa bari ayi wannan shigar toh yanzun.kuwa baya nan dole su kare su babbaka.
***
Nigeria….
Yau saura sati uku bikin aure na dawo daga, Maiduguri nayi mugun kyau. Duk wanda ya ganni sai ya kuma kallona, ina shigowa gidan da Hajja muka fara haduwa, tura min baki tayi tare da b’allar goranta
tace.
“Hmm! Duk wannan shirin wa wancan dindinkeken, ke! Wallahi idan kika kuskura kika tuna da shawarar da na baki sai na zabga miki rashin mutunci, tunda ana nuna miki Annabi kina rutsa idanunki, na rantse wancan ji gefen turmusa d’aya zai miki kin tashi aiki, dan yadda yaƙe nan za’ayi fitina. Shi yasa nake ganin tunda kinfi kowa sanin Ashraf, kiyi hakuri ki amince da Ashraf zakifi samun nutsuwa akan wancan katon ba wato.!
Kura mata ido nayi,raina na ɓaci dan na lura da wannar matan, idan ba batsa na mata ba bazata daina damuna ba. Ta kawa nayi gabanta nace.
“Shi Ashraf ɗin da kike Magana akanshi kinsan abinda yayi min a daren da muka hada shimfida dashi, hmm Toh suma nayi a hannunsa. Keni bazan iya dashi ba dan kuwa yafi karfina, bazan iya da a”
Ummi na gani cikin bacin rai, sam takawa magana sai juyawa tayi ta koma dakinta. Jikina yayi mugun sanyi.
Ina shiga dakin ta rufe ni da fada kamar data dokeni, tace..
“Wato har kinsan namiji da har zaki gaya mata shi, Safinah wai yaushe zaki same nutsuwa a rayuwarki, dan rashin kunyarki zaki gaya mata. Allah ya miki shiryar addini musulunci, amma akwai aiki a gabanki.,”
Haka tayi ta fada har tashi ta kyaleni. Wato Hajja ta lakatoni nayi magana Ummi taji haushi.
….. Da dare kuwa Dr yazo, muna Cikin motarshi. Kallona yayi cikin wani shaukin yace.
“Beauty! Me zaki bani tsaraba.”
Kauda kaina cikin jin kunyarshi nace.
” zan daina kulaka,”
Hannunshi naji a samar gwiwata, juyawa nayi zan masa magana, ya wani narke min nayi kasa da kai.
“Baby! Kayi hakuri nan da kwanaki zan zama taka idan kana nuna min zallamarka sai na fara jin ko jikina kake bukata bani ba.”
Janye hannunsa yayi, cikin Kunya.. sam sai yaji a ranshi bai kyauta ba.
“Kiyi hakuri! Wallahi ina Cikin bukatarki ce amma ba jikinsu nake bukata ba ke nake so, kinji kiyi hakuri.”
Murmushi nayi sannan na cire hannunshi a samar gwiwata, na maida mishi kan motarshi, mun jima muna hira. Cikin so da kauna, kamar ya tafi dani haƙa yake ji.
Fita nayi a cikin motar ina kallon yadda yake ja motar, daga mishi hannun nayi har ya fita.
***
Shiri sosai Ummina suke musamman Kayan gara wanda shi kawai yakan iya ja maka mutunci a gurin dangin miji, duk wanda yaga yadda Iyayena suke shirin bikina kaman ba a taba bikin kowa ba, gashi har Nannah sun ce wata sati zasu zo.
…….. Satin na zagayowa Nannah da iyalinta har da Natasha, yadda muka karɓe yayi musu dad’i, Nannah yazo da Amirah Khadijah tare da Amirah Zahrah, domin su shiga maganar nimawa Ashraf.
A ranar da suka zo da dare, muna tare da Dr sai hira muke, ina ta dariya. Mun jima sannan muka yi sallama, yana tafi ana dauke wutar, da sauri na shige cikin gidan. Dan koridon da zai kai Ni cikin gidan akwai duhu, kuma ban fito da wayata ba, sauri nake tsabar tsoro ina shiga gurin, Na hango shi tsaye da waya abinda ya fara zuwa raina shine.
*Ajiye wayar ko nabiyo iska*
“Bala’i” na furta a hankali, kafaffuna ne suka shiga harɗewa, ga wani curewa da cikina yayi, Wallahi duk rashin kunyata, ina shakkar Ashu. Kamar na juya da Baya haka nake ji, amma haka na aro jarumta na shiga tafiya da sauri, dan gani nake kamar bana sauri.
Sai da nazo kusadashine, zan wucce, cikin zafin nama ya fincikoni na faɗa jikinshi, bai damu ba ya cigaba da danna wayarshi, hannun shi daya tana sakale a k’uguna.
“Ina son na baki hakuri ne! Kuma na faɗa miki zaki iya Aurenki, a yanzun ke ba baiwa ta nace, kema Y’ace me yanci kamar kowa, sannan ina kuma baki hakuri akan abinda ya faru. Kuskure.”
Cikin tsiwa da gautsi nace.
” Sai kuma akace ka rungume Ni tsabar iskanci.”
D’ago kaina yayi da mugun ƙarfi zai haɗa bakinmu nace.
“Amma yanzun kace ina da yancin!
Zuba min idonsa yayi cikin damuwa fuskarshi a haɗe, yace.
“Sam bani da burin cutar dake, kece kike kaini bango hakuri nazo baki zaki bata min rai.”
Dake ina son rabuwa dashi, sunkuyar da kaina nayi, a raina kuwa tsiwa nake masa tare da zaginshi tsaf, kuma da zarar ya kyaleni sai na masa rashin mutunci, a zahiri kuwa marairaice fuskana nayi, har kwalla na saukowa, cire hannunshi yayi daga k’uguna, ya nuna min hanya ina gaba yana baya na, sai da naji na shiga falon yadda bazai iya biyo NI ba nace.
“Allah ya isa mugun macuci, dan iska kawai, yaro karami da kai sai jarabar bala’i, kuma sai kayi mugun.”
A zagaye ya juyo min, Ni kuwa ma arta ciki da mugun gudu, na shige d’akina ina haki, yarana da suka baje suna barci na shige tsakiyarsu.
…… Murmushi ya sake wanda ya b’oye ɓaci ranshi yana cewa.
“Zamu hadu Safinah da Ni kike zance, sai na shayar dake mamaki, ”
Murmushi ya sake sakamako tunawa da yayi da tattaunawarsu da sukayi dasu Abba akan auren da suka zo nima da kuma shawara da aka tsayar, lumshe idanunsa yayi yana kara hango masa ita a kwance gabansa had’iye yawu yayi tare da dake maranhi dake caccakarshi saboda bijirowar desire, me ƙarfi murmushi yayi Irinta mugunta dan yana hango yadda zai baje basirarsa gurin cinta….
******
🏌️
******
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 2 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: I just published “Page.57” of my story “MASARAUTAR JORDAN!!!”. https://my.w.tt/dwheBgbN13
_HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
_Don Allah ina cigiyar Wata baiwar Allah Mrs Sadeeq idan taga sakona dan girman Allah tayi min Magana 🙏🏼🙏🏼😭_
BOOK ONE….
_Saura 58-59-60-Insha Allah_
Page.57
“Dan kasamu ina baka shawara shine bari ka kawo min reni kaje banza dan is.”
Sai naji kalmar tayi min nauyin faɗa.
” Ki karasa zagina mana! Idan Ni dan iska e ke kuma me zan kiraki? Tabbas ni dan iskane, amma kece kika lalata tamin tarbiyya, duk iskancina ban taba tsallake iyayena ba. Ashe ni karamin d’an iskane ke da kike babbar yar iska tsallake maganar su kikayi tare da shiga duniya yawon karuwanci, ko ba haƙa? Da kika tashi komawa da cikin shege kika koma musu! Ke Safinah Ni ina zargin yaran da kika na dauko ba yarana bane zan dawo miki dasu ki nema musu Ubansa tun dare bai miki ba ki nemi Ubansa.”
Kashe kiran yayi zuciyar shi fesss. Dan ko ba kome ya cusa min baƙin cikin kuma ya gargadi Ghaniyu akan ya rufeni yadda bazan sameshi ba.
….
Ban taɓa jin bakin ciki Irin maganar da Ashraf ya gaya min. Kuka nake riris, naji ciwon sharrin da Ashraf yayi min, karshe dai haka nayita nimanshi dan na cimashi mutunci ban samu ba, ranar nayi na danasni babu iyaka, ƙarshe dan baƙin ciki sai da zazzaɓin ya rufe ni.
Dakyar Aunty Yaanah ta matsa min nashafa magani. Wayar ma na kasheta baki daya, Abuja.
….. Dama bahaushe yayi gaskiya da yace. Idan kasan na faɗa bakasan na mai dawa ba, gashi nice na fara, kuma ya rama yayi min zafi. Idan na tuna sai naji zuciya kamar zata tafaɗo kasa. Tabbas Ashraf ya cuce ni. Karewa ma ya sheganta yaran da shi yayi min cikinsu.
***
Bayan kwana biyun har lokacin ina jin zafin maganar Ashraf, domin babu macen da za’a gaya haka bata ji ciwon maganar ba, layin Nannah ta kuwa d’auka, tashi nayi na zauna, sannan na sake mata kuka, bata kashi kiran ba nima kuma ban kashe ba. Sai da taji ina jan zuciya tace.
“Binti!! Kiyi hakuri, waye ya taɓa min ke!”
Cikin muryan kuka nace.
“Nah!!! Shine ya ci min mutunci kwana biyu da suka wucce”
“Shi waye? Ban fahimci maganar ki ba, waye ya ci mutuncinki?”
Kamar tana gabana na sunkuyar da kaina, kuka na shirin kwace min, nace.
“Abi su yan biyu!?”
A ruɗe tare da gigita tace.
“Mene ya hadaku?”
Ai kaman jira nake ta antayo min tambaya, na sake kukan da nake ajiyewa, ina kuka ina gaya mata Irin maganar da ya gaya min.
“Nah! Ya dace ya gaya min haka? Nah ke kisan tarbiyyar da nasamu, badan ke ba bazan je Jordan ba, ya buɗi ya kirani da karuwa wacce ta gama yawon barikin, har yana cewa wai zai dawo da yaran dan yana zargin ba nashi bane, Nah ji nake kamar zan mutu. Kirjina ƙamar zai fashe.”
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace.
“Duk da bansan me ya hadaku ba, amma zan baki hakuri. Karku ɓata kyakkyawar Alakar dake tsakaninku ai ko dan darajar yaranku zaku ajiye kome, ku rike mutuncinku.”
Nan tayi ta bani hakuri, tare da rarrashina. Haka dai na hakura amma tabbas Ashraf ya cuce Ni ba kadan ba, yayi min mummunan tabo, ya lalata min rayuwa gabaki d’aya tsabar Kaina nake ji nake ina ma na mutu na huta da wannan rayuwar,
***
Oman…
Gabaki d’aya taji kome ya tsaya mata ranta ba dadi ta isa Asibitin, yana tsaye a jikin window, yajingina da jikin window yana kallon yadda mutane suke wucewa, tankar da zuciyar shi suke wucewa, haka kawai yake jin duk wani sarai da kwarin gwiwa da yaƙe da ita duk babu yanzun, ji yake duk abinda zai fito bakin shi dayan biyun sunanta ce zai fito. Bai sai yaushe tayi mishi illa haka ba, sai da ya gaya mata maganar nan yaji ba dadi, ko wani ne ya gaya mata Magana haƙa sai inda ƙarfin shi ya ƙare amma shi da kanshi ya sunanta mata yara, ya kuma kira da karuwa, wacce ta tafi yawon barikin, tuno zumar da take a baya idan ya nemi taɓata, lumshe idanunsa yayi cikin jin ba dadi, ji yake ya tsani kanshi da duk mugun halinshi.
“Habibi!” Ta kira sunan shi, ajiye kofin da yaƙe dauke coffee, ya koma baƙin gado ya zauna tare da kallonta.
“Habibi! Me ya haɗaku da Binti? Har ka Iya gaya mata Magana masu zafi haka, Ni da nake kokarin ganin naje nima maka aurenta, shine ka lalata kome me yasa kake da bak’ar zuciya ne! Me yasa baka aiki da ƙwaƙwalwa, duk lalacewa Binti matsayin biyu take dashi a gurinka da gurina, kamar yadda kake d’ana haka take Ƴata, sannan ko Kunyar kiranta karuwa bakayi ba, Wallahi ka mugun ɓata min rai, dan ji nake kamar na rufeka da duka, tunda kayi haka. Ban isa inje niman aurenta ba, tunda ta sami wanda zai share mata kuka,”
Kanshi a sunkuya har ta gama Maganarta bai iya d’ago yace mata cikanki ba, domin kuwa yasan yayi laifi me girma, shi aka batawa amma sai yake ji sam bai kyauta ba, domin kuwa ai Safinah tayi mishi gata, ta sadashi da Mahaifiyarshi, a sannu ya motsa bakinshi. Amma harshen shi tayi masa nauyin, sake tattaro iya jarumshi yayi cikin matukar danasani.
“Ammihna! Kiyi hakuri.”
Girgiza kai tayi cikin ɓaci rai tace.
“Aini baka min laifi ba! Ita uwar yaranka zaka kira ka bata hakuri, Yarinya tayi kokarinta madadin a mutuntata, a kuma girmama alamarinta. Sai kuma abinta da bak’ar magana, Wallahi shekarun ashirin da shida ina tare da yarinyar nan taɓa kamata da mugun hali ba, koda ciki ya bayyana a cikinta kuma tace mana Jordan, naji jikina ya bani akwai matsala, koda tace min kana gaisheni na fahimci cewa duk yadda akayi kana da alaka da cikin ko bana kabane Toh zaka iya sanin wani abu akan haka, daga baya ta faɗa mana cikin nakane bamanyi musu ba, dan masana haƙa na iya faruwa. Idan kaga Irin halin da tashi ga saboda cikin sai kaji bazaka iya bari hawayenta ya zuba ba, amma kaine kasata zubda kwalla! Ka kirata ka bata hakuri.”
Sosai Nannah tayi mishi fada, shi kanshi yaji matuƙa Kunyar abinda. Dan haka har Nannah tagama fadarta bai magana ba, sai ma sunkuya da kanshi da yayi.
Shigowa Ghaniyu tare da yaran yasan shi sauke ajiyar zuciya, saboda kuwa suna ganinshi suka shiga ƙoƙarin sauka daga ɗaukar da Ghaniyu yayi musu, Aanih ce ta fara zuwa ya ɗauke ta tare da cilla ta sama, sannan Aanih itama ya ɗauke ta ya cilla ta sama, dariya suka saka. Kwanciya a jikin shi sukayi tare da kallon shi.
“Didih unku!” Inji Aanih, kwantar da kanta yayi, tare da shafa kanta, cikin tausayata, wato tana nufin Didih Uncle! Tana niman uwarta, karɓar wayar Ghaniyu yayi. Ya cireka a blacklist, sannan ya shiga niman number. Tana shiga ya mikawa Aanih yace.
“Ga Didinku”
Jin yana gayawa yaranshi yasa, ta kashe wayar baki d’aya. Kuka yaran suka saka mishi tare da kiran Didi! Kwallar da yake rikewa ne ya kwace masa. Tausayi yarane ya cika mata zuciya, wannan shine karo na biyu da yayi kuka sanadin Safinah.
Maganar da Nannah take da cewa.
“Ina ga ya zama dole na tafi Nigeria domin ku kai da yaranka. Idan na samu nasarar toh……
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105…*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 3 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah……
[2/14, 10:04 PM] Ramla GRA: _HAZAK’A WRITERS ASSO…._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
_Don Allah ina cigiyar Wata baiwar Allah Mrs Sadeeq idan taga sakona dan girman Allah tayi min Magana 🙏🏼🙏🏼😭_
BOOK ONE….
Last free rage=59-60
Tunda na fahimci na tsira kuma ina d’akina a raina nace naga hegis din da zai biyo, mikawa nayi na shiga ban daki, na cire kayana. Sannan na tara ruwa na zauna a baƙin abin wankan ina tino hiranmu da Dr, abinda ya Gaya min ya sani jin kunyarsa.
“Beauty! Warhaka nan da sati biyu muna rungume da juna, ke nifa har wanka tare zamuyi. Kome, girki, wanke-wanke, gyaran gidanmu, game, zuwa visiting, da kuma mene?”
“Da kuma zuwa aiki a tare, gani ga mijina”
Murmushi ne ya kwace mishi yace.
“Kuma mu haife kyawawan yara irinki.”
Abinda Ya samu dariya kenan na fito ina dariya, da naji ruwan yayi min yadda nake so na shiga ciki, a hankali na cuɗanya jikina. Da showel gel, sai da na cika ruwan da kumfa ina wankan amma tunanin Dr ya cika min zuciya. Buga Kofar bayin akayi nayi maza na dauraye jikina, na fito daure da towel.
Ummi na samu zaune idanunta sun kumbura,alamar tayi kuka sosai, zama nayi kusa da ita, jikina a sanyayye. Na bud’i baki nace.
“Ummi! Nayi wani laifine?”
Girgiza kanta tayi sai ga hawaye sharrrrr tace.
“Dazun Abbanku yazo min da wani magana wai Gimbiya Asma’u tana nimawa Ashraf Aurenki, bayan sunsan da maganar Dr”
“Wani irin nimawa Ashraf aurena! Bayan haramun ne nima akan nima, wannan shine hauka. Wallahi ko Ni dashi muka sauran a duniya bazan aureshi ba, Wato yazo yayi amfani da kudi, isa, mulki, tare da izza, shine za abadani kamar wata mata daraja, yaron da ya renani”
“Mariamah don Allah karki tozarta Ni, a cikin mutane da suke gani na da kima, sannan ke Safinah ki fahimci Wani abu guda ɗaya, Ashraf shine rufi asirinki dubi da halin da yaranki. Shi yasa na yanke shawarar zan bawa Dr Batul.”
Ban gama jin maganar shi ba na fashe da kuka, tare da daura hannuna akai ina kuka wi-wi. Fita suka yi Ni kuma na cigaba da kuka.
Da sauri na fita daga dakin na nufi inda dakin da Ashraf yake, dama daga Ni sai towel, sai kuma babba hijabi dina, ina shiga na sameshi zauna, ya cire rigar shi singlet. Ko sallama banyi ba wurgi nayi da hijabi na sake towel din, naje gabanshi na durkusa cikin kuka nace.
” Gani nan kayi yadda kaso sani, amma don Allah ka barni na auri abinda zuciyata ke so.”
Wallafa ko ya san ina gurin, ya rike wayarshi gam, matsawa nayi jikinshi, tare da rokon shi yayi kome dani kawai ya janye a maganar niman aurena yabarmi na auri Dr kawai.
“Fita nace!!!”
“Bazan fita ba sai ka gaya min akan me kake bibiyata! Na gaji tun da nashiga rayuwarka nake girba matsala, daga wannan sai wannan ya kake son nayi da rayuwata, na gaji kayi abinda kaga zaka iya na karasa sauran rayuwata haka.”
Sam yaki kula ni karshe sai, daka min tsawan da yayi tare da mika min, towel da hijabi na ya koroni, ya datse kofar. Zama nayi nayi kuka har kaina ya fara ciwo.
Dakyar naka jikina na shige gida,. Wani Irin tashin hankali na shiga wanda na kasa fahimtar kome, kwana nayi idanuna biyu barci ma ya gaggareni karshe tashi nayi na gabatar da sallar dare sai goshin asuba barci me ƙarfi yayi gaba dani. Ban farka ba sai karfe shida saura, ina tashi na nufi banɗaki nayi alolar nazo na gabatar da sallar asuba
Tunda na idar nake kwance a gurin baki tashi ina jin yaran suka tashi sannan suka fara kuka, ban d’ago kaina ba, balle su sami karban arzikin. Kwanciya na gyara na kuma cigaba da kukan zuci. Kuka su ne ya tsananta, sakamako faduwa da sukayi daga gadon, naji zafin haka amma bakin cikin da Ubansa da kakansu. Suka kula min yasani tsanar yaran.
Da suka ishe Ni daka musu tsawa nayi tare da nuna musu hanyar waje, fitina min sai da suka sani na mike tare da bud’e musu kofa.
ALLAH sarki garin rufe kofar na matsawa Aanih hannunta, wani ihu ta cilla wanda yasa kowa na cikin gidan ya fito, abin tausayi sai yar uwan taje jikin kofar, tana jan hannun tare da kallon yar uwan, Aanih kukan tane ya dauke sai ajiyar zuciya, buga kirana ake amma fir naki bud’ewa Ni na zata wani damuwa ce, sai da naji Muryan Abba yana cewa. “idan taki bud’ewa ku nimomin Yan sanda su tafi da ita a yunkurin yin kisan kai,”
Da sauri na bud’e kofar, kawai naji an kifeni da mari, rike fuskana nayi naga Ummi ce.
“Ashe ke mutu iyar banza ce? Dan rashin imani zaki kashe musu ya, Wallahi kifito idona ”
Marin da Ummi tayi min ya fansheni a gurinsu Nannah, Amma Ubansu ya kulaceni, kuma yadda yake ji nan kamar ya rufeni da mugun duka, daukar yarinyar yayi suka fita, abinda da farar fata yatsu yayi jajjur.
…..
Ran kowa ya ɓaci, Ni kuwa da naji haushi na rufe kofar baki fitow. Balle nadan halin da suke ciki,
. A gaskiya na shiga damuwa sosai, domin kuwa fushi kowa yake dani musamman Ummi, ina cikin tsaka me wuya domin na fita hayacina, sosai suka ɗauki zafi a kaina. Ido da ido Ashraf yake gaya min magana, wai na haifi yarane kawai dan babu yadda na iya amma ya fahimci bana kaunar su. Zuciyata da kwadayin namijin ya rufe min idanuna akan yarana burina make a jagwalgwalani.
Cikin ko ina kula nace mishi.
“Kaine dai jarabawar, mara kunya wanda bai san darajar kanshi”
Bai kulani ba yayi tafiyar shi, matukar ya cigaba da takalmin ko Ni matakai shi, Toh muna gayawa juna magana, dan ya renani. Sosai dan iskancin da yake min ko Didi bazai min ba.
***
Duk wani zirga zirga, tare da Natasha muke, tunda ta fahimci bana yin Ashraf sai hankalinta ya kwanta, dariya ta bani domin ni bangaren abin so a jikin yaron da ba a gama mishi Tsarki ba, kuma ta sake jikinta dasu Batul ana ta shagali tunda na amai kayana daga ɗinkin na shiga rufe kaina bana son damuwa da Kowa. Wannan ware kaina da nake yana mugun d’aga musu hankali haka za azo ayita buga Kofar d’akina dakyar nake fitowa, nace.
“Lafiya!?”
“Kizo kifi abinci!”
Tsuke fuskana nayi sannan nace.
“Na koshi;”
Duk sai suka ji ba dad’i Nannah tazo har dakin amma naki saken jiki da ita, ka haka ta gama rarrashina tafita, sam yanzun haushinta nake ji. Yadda nuna dan farin cikin d’anta take kome .
……… Baki saura sati Daya, dan haka duk hankali.kowa ya koma kan kan bikin yayinda ko wani second ji nake kamar na mutu dan baƙin ciki, hmm.
Ina kwance suka shigo da gudu, suna kirana nakiya amma nayi banza dasu, garin hawa gadon da Aamih zato yar uwan takaita sai ji kake kwal ta fadi a kasa, ihunta yasani tashi ina jan tsaki, tattara su nayi tare da fito dasu falon suke can su karata.
A hankali kwanakin bikin ke gangarawa, nan aka fara shagali sun hada da kamu wanda nace bazanyi ba. Sai family ne Friend, sai walima, shi daya kawai nace zanje.
Sanan suka cigaba da hidimar Ni ina falon, ana gobe za a sakamakon a lalle da yamma naje saloon, nayi kyau. Ina shigowa gida, sako na shigowa ta wayata.
_*Ina tayaki murna Me Zaki_*
Shiru nayi ina nazarin waye haka!?
……….
Washi gari da wuri na tashi saboda me zanen lalle tazo haka na zauna akayi min.
Idan kaga yadda gidan yadda ya cika da yan bikin, babu matsala tsinka.
Hmm Dr kuwa Sanyashi nayi a blacklist, dan shima zai iya yakirani….
A cikin haka Aunty Yaanah. Tazo itama, tazo min da Kayan harka, na karba ina jin kunyar ta.
****
Laraba…
Tun daga ranar Laraba aka fara biki, abinda muka yi ranar Laraba, shine shigar al’adar ba yaushe muka yi wanda yayi mana kyau. Kowa sanda.
Washi gari Alhamis muka gabatar da Mother’s nyt. Ranar juma’a aka gabatar da Walima wanda muka gayyato Dr Isa Ali,
Yayi mana nasiha sosai akan hakkin miji da danginsa, suma mazaje be kyalesu. Sai da yi musu nasiha sosai
Gaskiya anyi barna da kudin sosai, dan yan uwan Dr da suka zo kome na walima so da abasu nasu rabon.
Da dare aka shirya Mana sister nyt, amma naki zuwa sabida da mijin zan je Ni Kuma ban Don ganin mijin dan nadan sun tabani da me sona tsakanin da Allah.
Washi gari kuwa, tun safe naci kwalliyya na, ina zaune sai shiga da fita ake, kunsan amarya da farin jini, kowa so yake yazo yaga amarya ko wacce irine sonta ake.
Hankalin Mu’awiyah yanzun yana masallacin domin karfe sha d’aya za a daura auren, dan haka idanuna na kan agogo. Sha daya da rabi aka fara bayani yadda auren zai kasance, dakin dake ana surutu baka jin abinda ake fada, dan haka na koma jikin window na zauna dan har yanzun ban cire raina da Rahamar Ubangiji ba.
Iska ne ya fincikoni sanarwar inda ake cewa.
“An daura auren Safinatu Badar da Angon A……..”
Timmmmmm na yanki jiki na fadi sakamakon jin harafin *A* da aka kira wanda nake da yakinin Ashraf ne. Salati yan dakin suka saka.
wanda yayi dai dai da faduwar Wayata sabuwa dal da nake rubutun da ita, ta kuwa ci screen, dole gobe na mike zuwa wunti domin nasadata ga masu gyaran ta………
_Me karatu Sunan Ashraf Ya fara da *A* Hakazalika Dr Sunanshi ya fara da *A* Abdulhmeed Toh waye daga cikinsu? Jordan na can cikin gautsi cewa Shin Ya Bilal zai gudanar da Mulkinsa? Amin! Yana nan kuwa? Shin me yasa ya zama kamar aljani dan idan me karatu bai manta ba bacewa yayi! Me yasa ya koma haka? Kai-kai-kai ku biyo NI cikin tafiyar ko waye Angon_
_Alhamdulillah a nan na gama book one ga musu bukatar book 2-3 zasu iya min Magana ta nan👇_