MATAR BAHAUSHE🧕 CHAPTER 8 BY Fateeyzah mbs_✍️*

MATAR BAHAUSHE🧕 CHAPTER 8 BY Fateeyzah mbs_✍️*

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

 *GENERAL MUTTAQA GIMBA*, d’aya daga cikin ganarori na hafsoshin nigeria, ya fara aikin soja tun yana d’an shekara ashirin da muk’amin kurtu, wanda a haka yayi ta samun d’inbin nasara da har ta kawosa wannan muk’amin, matarsa d’aya Hajiya Batula wacce ta kasance balarabiyace ta k’asar misra, kyakkyawace ajin k’arshe, duk abunda akeso a jikin mace ta mallakeshi, yaranta shidda da general, maza biyar , sai mace d’aya wato Ramlah, gaba d’ayansu securities agent ne, na farkon ya kasance navy, sai ma biyu air force, na uku custom officer, na hud’u kuma Immigration, na biyar d’insu shine yayi gadon genaral, wato Army officer ne, gaba d’ayansu sunyi aure suna tare da iyalansu a mabanbantan jihohi.

 *_RAMLAH MUTTAQA GIMBA_* ‘Ya mace tilo a wurin Genaral Muttaqa da Hajiya Batula, kyakkyawace ajin k’arshe, don ta kwaso mum d’inta ba abunda ta bari na kamanni, yarinya ce da ta taso cikin gata da kula a wurin iyayenta da yayyinta, saboda kasancewarta mace, kuma sai da Hajiya Batula ta fara manyanta sannan ta haifeta, wannan yasa duk wacce kula ta duniya da soyayya sun d’aura mata, basa son jin kukanta ko kad’an, sannan duk abunda take so shi ake mata, sai dai duk sangarta baisa ta zama wawiya ko shasha ba, don hajiya Batula ba k’aramin training tama Ramlah ba, don acewartaa duk yanda suka kai da sonta, wata rana gidan wani zata, wannan kenan.

Cikin sauri Hajiya Turai ta kira Hajiya Atine take labarta mata yanda suka yi da Alhaji, tsurewa tayi don har ta kusa fin hajiya Turai shiga tashin hankali, don tasan plan d’insu na farko ya wargaje, take suka k’irk’iri meeting wanda zasu yi a gobe, nan suka sanar a group d’insu na manyan mata, wanda zasu had’u a gidan Hajiya Atinen.

 **************************

Tare da Director Alhaji salisu ya dawo gida, domin gayyatarsa da yayi don yin dinner, wanda tun kafin su taho ya kira Hajiya Luba ya sanar mata, nan ta kuma gyara dinning table da taimakon yaranta mata, ko da suka iso direct dinning suka  wuce suna masu hirarrakinsu suna dariya, nan hajiya Luba da yara suka fito musu sannu da zuwa tare da gaisuwa, daga nan hajiya Luba tayi serving d’insu ta bar wajen, da kallo Alhaji salisu yake bin abincin yana murmushi, yayin da Director yake ta had’iyar yawu, don  daga kallon abincin yasan zai yi d’and’ano mai dad’i, sakwara ce da miyar ganye, wacce taji naman rago da ganda zuk’u², gefe kuma ga farfesun kaji dake ta k’amshi, sai kuma kunun aya dake tashin k’amshin  vanilla flavour, bismillah suka yi suka fara aika ma cikinsu, wani dad’i ne ya ziyarci Director wanda har ya kasa hak’uri sai da ya d’ago kao yace “AG gaskiya kayi sa’a, wannan dad’i haka, ya kamata aba ma Madam lamban yabo”.

Dariya Alhaji salisu yayi yana mai cewa ” ba dai ka fara santi ba, toh ba madam za a bama lambar yabo ba, fadila za a ba mawa, don wannan d’and’anon girkin tane”.

Zaro ido yayi yana mai cewa ” fadila fa kace, yanxu ita tayi wannan girkin”.

D’aga gira Alhaji salisu yayi yana mai cewa “of course, training d’in mummynta kenan, sannan da ta kammala secondary  na saka ta wata catering school, wacce anan ta koyo abubuwa da dama”.

“A lallai, kace har ta gama makaranta” cewar Director kenan yana mai kai lomar sakwara bakinsa.

Sauke cup d’in kunnun ayar da yakai bakinsa yayi, sannan yace ” ta gama, yanxu haka level 2 take a state university kasan tayi saurin shiga school, shi yasa tayi saurin gamawa”..

“Masha Allah” cewar Director yana nai ci gaba da cewa ” Hmmm AG wannan dad’in  da nake iba, dama zan ringa samunsa kullun wallahi, kai cefane, madam kuma da fadila girkawa, ai  wannan sai bak’o yak’i tafiya”.

Dariya Alhaji salisu yayi yana mai d’aukar hular Director ya kara maida masa akai a matsayin waigi, sannan yace ” hmmm dako na kora bak’on ai, don zai hanani cin dad’in da familyna suke bani  kullun”‘

Gaba daya dariya suka yi, sannan Alhaji Salisu ya d’aura da cewa”kaga abunda nake fad’a maka, wallahi shi yasa bana jin haushin bada kud’in cefane, don wallahi sa ga har da abunda ban kawo ba, an dafa an bani inci, yanxu kamar dai kaza da gandarna, ni dai nasan  ban kawo ba, amma kaga an sarrafa a zubo mana”‘

” hakane wallahi, kayi 

Sa’ar mata, amma don Allah for the first place, me ya kaika k’arin aure, alhalin ana baka wannab gyarar” cewar Director yana mai tsaresa da ido.

Murmushi yayi had’e da cewa ” wallahi kwad’ayi da soyayya, kasanni ni mutum ne mai son soyayya, inga mace ‘yar soyayya,  amma hajiya sai ta nuna ita ta girma, and inason inga mace na d’aukan dressing, tana saka kaya da zasu yi fitting d’inta, shiyasa kawai naga bari in nemo ‘yar shilla, zan samu yanda nake so tunda ita hajiya tak’i, sai gashi ashe duk kanwar jaa ce”‘

“Hmmm, to Allah ya kyauta, gwara kai, ni da na rasa komai fa, ba soyayyar babu kula”.

Dariya Alhaji salisu yayi, yana mai k’wala ma fadila kira, da sauri ta fito tana nufosu cike da natsuwa, yayin da Director ya zuba ido yana mai mamakin girmanta, don yanda ta zama ‘yar duma², komai yaji ba zaka ce ‘yar seventeen years bace, yana som mace haka, k’arasowa tayi tana mai fad’in ” Daddy sannunku” jin muryarta ba k’aramin shauki ya saka director ba, wanda har bai farga ba har tabar gun bayan ta kwashe kwanukan da suka ci abincin , ganin ya tafi duniyar tunani ya saka Alhaji salisu tab’oshi yana mai cewa ” ya dai director”‘

Firgigif yayi ya dawo daga tunanin da ya fad’a yana mai sosa k’eya tare da cewa ” hummmmm, ina mai mamakin girman Fadila ne wallahi, girman d’an mutum.ba wuya” ya k’arashe magana yana mai k’asa da kansa.

Nazarinsa Alhaji salisu yayi sannan ya  kwashe da dariya yana mai cewa ” hmmmm director ko dai ka polaaa ma d’iyar taka ce”‘

Kallonshi yayi cikin sauri yana mai ceaa ” haba dai², bar wannan maganar, ‘yar kace fa”.

“Ehhhen, and so what, indai kana so wallahi sai in baka, dama bata da tsayayye, don tuntuni na hanata tsayuwa da k’ananan yaran nan masu hure ma yara kunne, shiyasa naje tsaye a lamarinta, in anko goma ne a wata, zan mata, haka kuma katin waya duk sati sai nasa, saboda banso a rud’eta ta haka” cewar Alhaji salisu so proud.

Mirmushi yayi yana mai cewa ” to AG ita zata soni ne, kaga fa na fara tsufa, kuma ni abokin babanta ne”.

” kada ka damu da wannan, indai kana sonta wannan ba wata matsala bace, ni nasan tarbiyar da muka yi ma Fadila nida mummynta, kuma na riga na fad’a maka ban bata damar soyayyar ba, kaga kai se ka kafa taka gwamnatin, ka koya mata sonka”. Cewar Alhaji salisu yana mai cire hularsa.

Nannauyan numfashi ya sauke yace ” shikenan to AG, ka bani kwana uku zanyi tunani, duk abunda na yanke zan sanar maka”.

Amsa masa yayi da “toh sai na jika”,  yana mai.masa kallon tausayi, namiji yakai namiji amma ya rasa kular mace, haka suja ci gaba da hirarsu, daga baya Alhaji salisu ya raka sa ya tafi.

****************************

Shigowa d’akin tayi d’auke da kaya a  hannunta, bud’e wardrobe tayi ta zuba kayan, sannan ta juya zata fita, gyaran murya yayi yana daga kwance tare da cewa ” hadiza zonan”.

Juyowa tayi ta k’arasa wurinsa jiki a sanyaye, inda ta samu gefeb gado ta zauna tana mai cewa “Gani malam” kallonta yake yana mai nazarinta, yayin da ita kuma ta duk’ar da kai tana mai wasa da yatsunta, numfasawa yayi tare da cewa ” dama ba wani abu bane, aure zan k’ara, har an kai sadaki, yanxu haka sati uku aka saka, saboda bazawara ce, don haka nake son zuwa gobe ki kwashe kayanki dake kitchen, zan saka a buga miki kitchen d’in langa² a tsakiyar gidannan, saboda zan gyara ma Amaryata kitchen d’in, don tace tana son kitchen d’inta ita kad’ai”.

Da kyar ta had’iye abunda ya toshe mata mak’oshi tana mai cewa” shikenan, Allah ya kaimu” mik’ewa taiy ta fice d’akin yayin da ya bita da kallo yana mai mamakinta, don ya d’auka zata d’an masa haukan da mata suke yi in miji yace musu zai k’ara aure, amma sai yaga sab’anin haka ita a wurinta, duk da yasan hadiza mai hak’urice, amma kuma ai akwai kishi,”ko dai bata sona ne bata kishina” ya ma kansa tambaya yana mai gyara kwanciyarsa

 _(Ohhhoon maka, so kake ta maka hauka)_ 

Ko da hadiza ta fita, buta ta d’auka ta shige toilet, wanda tana shiga ta durkushe tana kuka mai cin rai, tare da wani kishi daya lullub’eta, tana mai dana sanin auren malam, ta  k’i bin maganar iyayenta ta nace sai shi, yanxu gashi bacin wulak’anci da rashin kulawarsa a gareta da ‘ya’yanta har jajibo aure yayi, yayin da ba tare da lallashi ba, yake sanar mata buk’atarshi, haka taci kukanta, daga k’arsge ta bama kanta hak’uri ta wanko fuskarta ta fito, ko da ta koma d’aki ta tarad har ya fara bacci, dad’i taji, don ko babu komai zata huta da jarabarshi da takura, kafin dare yayi nisa ya tasheta.

 *

********************************* 

Kamar yanda ta kasance jiya, yau ma ko daya dawo ya tarad da d’akin a  birkice, don har yafi na jiya birkicewa, ga kuma kaya da aka kuma k’arawa akan gadon, wanka yayi, ya kwala kira aka masa abincu, wanda yau d’inma munnirace ta kai masa, ko daya bud’e yaga shinkafa da wake da mai da yaji, tsaki yayi ya rufe yana mai ture kayan wankin, yayi kwanciyarsa, ya rasa ta hanyar da zaibi ya b’ullo wa al’amarin Amina, anya ba d’aukan shawarar zuciyarsa zai yi ba, ta hanyar k’ara aure, to wacece zai aura?, ya halinta yake?.

 _(Matar bahaushe sunce gaskiya kawai ka k’ara ma Hajiya amina kishiya, ko tayi hankali)_ 

 A haka yayi ta tunani har bacci ya d’aukeshu, yayin da yake jin hirarraki.da dariyar Amina da yaranta.

 *_Toh fansa, me manyan mata zasu tattauna a meeting d’insa akan auren commissioner da Ramla Gimba?_* 

 *_Wace shawara Director zai yanke akan maganarsa da Alhaji salisu na Fadila, shin kina ganin ya dace ya aureta ko kuwa?_* 

 *_Ga kuma mutumin naku(hariji) zai sambad’o ma hadiza sabuwar Amarya, shin ya zasu k’are?_* 

 _Ga kuma mutuniyas hajiya Ameena, ko Alhaji usman zai bi shawarar zuciyarsa?_ 

 *Duk mu kasance a next page, don jin yanda zata kaya, more comment, daily updates* 

 *_Fateeyzah mbs✍️_* ³⁶ ⁴⁰

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *