MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 23
D’aukan wayan yayi rahma ta kalli su zarah wanda idonsu ke kanta,jin yace hello wake magana yasa tayi gyaran murya tare da fad’in nice, yanajin muryanta ya gane Mai magana din, a hankali Ya kira sunanta, ido ta lumshe tare da amsawa, yace wani abu ya faru ne? Tace a’a dama dama yace inaji tace ina gayyatar ka party din da za muyi gobe karfe hudu, ina fatan zaka zo? Yace insha Allah Zanzo, tace nagode tare da kashe wayan, y’an uwanta suka matso suna tambaya Mai yace? Tace yace bazai zoba, khairat tace dagaske k0 wasa? Dariya rahma ta saki sannan tace yace yana nan tafe insha Allah, ajiyan zuciya suka sauke tare da fad’in Allah ya kaimu.
Mama da Ummi da hindu da Amina ne zaune a falo suna fira, mama tace da yaran nan basa nan sai gidan naga ya mana girma, gaskiya yaran nan sune dad’in gidan nan, amina tace hakane gidan sai yayi fayau, ummi tace jibi suka ce zasu dawo tunda sunyi nasara, mama hawaye ne ya zubo mata tace Allah sarki Ibrahim inama yana Raye ya gane amfanin y’ay’a mata, yanda suka jure wuya Dan suga sunyi nasara, Wanda wani namijin ma bazai iya juran abunda su sukajura ba, ummi tace hakane Allah yaji ‘kan Ibrahim amma Kafin ya rasu ya gane irin baiwar da y’ay’a mata suke dashi sannan yayi nadama akan abunda yayi musu, hindu tace rayuwa kenan, suna cikin haka farida ta kawo musu juice da snacks ta ajiye tare da kokarin zuba musu drinks din, ummi tace farida barshi zoki zauna Bari insa, tace a’a ummi barshi ance in dinga motsa jiki, ummi tayi murmushi tace naki motsa jikin yayi yawa, hindu ta cabe da fad’in Wlh kuwa aita motsa da yawa domin Aneesa ta horar damu shegiya itama saita biya abunda ta aikata ta kashe min gudan d‘an uwana, ta karasa maganan cikin karayan zuciya, mama tace Sai hakuri hindu, farida kam d’aki ta koma kwanciya tayi tana kuka domin tunawa da harda faruk a cikin wannan abun domin ta sanadin shine Aneesa tazo gidan, tasan su zarah ba zasu taba yafe Mai ba, kuka ta saki tunawa da cikinta gashi ta kusa haiyuwa komai zata fad’ama d’an nata akan mahaifinsa Idan ya girma wannan tunanin taita yi tana kuka cikin kunarzuciya. Mutane sun hallara wajan party din dan tayasu samun nasara akan filin, sunyi Abun ciye ciye Kala Kala, yaran da suka zo sunata tsalle tsalle da balan balan, mutanan kauyen duk Wanda yazo musu murna sai yace shima yaranshi zasu Fara zuwa makaranta domin samun ilimi dan yanzu sun San amfanin shi, rahma dake zaune bini bini ta kalli kofa, ganin lokaci naja yasa ta Fara jin haushin kanta Mai yasa ta kirashi dama tasan ba zuwa zaiyi ba, muryan zainab taji tana fad’in Yadai tunanin mai akeyi? Bari in cinka uhm uhm Mahmud kina tunanin shine, ido rahma ta kulle tare da flta waje inda yara ke wasa cikin filin gidan dan yana da girma Sosai, dariya su zainab suka saka rahma wajan yaran ta nufa itama tana wasa da balloon din da suke wasa dashi, garin hadari ya had’u Sosai rahma ta sadakar bazai zoba, komawa tayi wajan y’an uwanta tace kunga hadari lokaci d‘aya? Khairat tace rahma waiga ki gani, kaman Karta waiga tana waigawa taga alh Mahmud hannunshi dauke
da ledoji, bata san sanda ta saki wani irin murmushi ba, nufanta yayi tare da fad’in rahma
Ina tayaki murna na samun nasara mi’ka mata ledojin yayi ta amsa tare da fad’in nagode gaisawa yayi dasu zarah, khairat ta matsa inda yake tace Mai yasa kazo late Bayan kasan kaine babban ba’ko? Yace ayimin hakuri, yaran dake wasa suka zo sukajanyo rahma tare da fad’in aunty zo muci gaba da wasa, binsu tayi suna wurga balloons din sama ruwa aka fara wasu daka yaran suka shige cikin baranda wasu kuma suka tsaya suna Wasan ciki harda rahma, idon Alh Mahmud nakan rahma, fita yayi shima cikin ruwan ya nufi inda take tare da ru’ko mata hannu yace I love you rahma, plz ki yarda ki aureni, kwace hannunta tayi daka nashi tayi ciki da gudu, y’an uwanta dake barandar Suma suka bita ciki, zarah tace haba rahma mai yasa zaki tawo baki bashi amsa ba? Shuru tayi batace musu komai ba sai kukan da takeyi,jin muryanshi sukayi yana fad’in rahma Indai baki bani amsa ba yau babu inda zani,jin haka yasa ta tashi ta hangoshi tsaye a kofard’akin ruwa na dukanshi, matsawa kusa da ita zarah tayi tace haba rahma wlh naga sonki a cikin idonshi dan Allah kije ki sameshi Wlh yana sonki, kallon zarah tayi tana son magana zarah tace ya isa kina son kice kina tsoran yasan labarinki koh? Inaso kije ki sameshi ki fad’a mishi komai akan koke wacece, kai rahma ta d’aga alaman Toh, fita tayi ta sameshi ganin tazo yasa yaja hannunta har zuwa motarshi, Bayan ya sata ya rufe sannan ya zagaya shima ya shiga, ban San mai suke tattaunawa ba naga rahma ta fito daka motarjiki a sanyaye bata dad’e da fita ba shima yaja motarshi, su zarah na ganinta suka fara tambayanta lafiya? Tace zarah dama na sani bawai yana sona bane, koda yana sona ba lallai bane yayi rayuwa dani ba Idan yaji Labarin abunda Nayi baya, na fad’a mishi irin rayuwan da nayi ya tafl ba tare da yace komai ba shi yasa nake tsoran wani namiji yace yana sona saboda irin haka…, Ta karasa maganan cikin kuka tare da fad’awa jikin zarah,jin muryan alh Mahmud sukayi yana fad’in rahma ke nake so babu ruwana da rayuwan da kikayi baya tunda yanzu kin daina da sauri rahma ta d’ago daka jikin zarah danta tabbatar k0 shi dinne ………
Murmushi ya sakar mata, sannan yace plz ina son magana dake, fita yayi ta bishi har motanshi, Bayan ta zauna tana dan rawan sanyi domin har yanzu ruwa akeyi, ganin tana rawan sanyi yasa ya dauko dadduma a Bayan motar ya rufeta dashi, magana ya fara kaman haka rahma tun sanda na had’u dake nakejin wani abu a tare dake Wanda sai daka baya na gane sonki ne ya kamani, ba rayuwanki na baya nake soba wannan kuma bai dameni ba a yanda kike yanzu na ganki kuma nake sonki bai dameni ba dan bakiyi karatun boko ba, ni rahma nake so ba komai ba, murmushi ta saki Wanda bata san tayi ba, ido ya kura mata Wanda itama ta d’ago dakai jin yayi shuru suka had’a ido, sunyi wajan minti d’aya suna kallon juna sannan yace rahma iyayena burinsu kullum inyi aure, amma ban sami wacce nake soba sai yanzu, yace mahaifiyata ta rasu wajan shekara uku da suka wuce, tunda ta rasu mahaiflna bai kara aure ba har yanzu tun Bayan rasuwan mahaifina nike kula da kasuwancin shi domin nine kadai d’a d’aya tilo daya mallaka, kullum burinshi inyi aure yau Idan na bashi Labarin na samu Mata Nasan sai yafi kowa murna, murmushi tayi yace Toh na samu karbuwa? Fuska ta rufe tana dariya, yace fad’amin mana plz plz, kin magana tayi ganin shima yayi shuru yasa ta cire hannunta a fuska tare da kallonshi caraf suka had’a ido, saurin kawar da fuskanta tayi dariya yayi Sosai tare da fad’in kina da kyau rahma, a hankali ta furta dare yayi gashi zakai tafiya Mai nisa kuma ana ruwa, ya kamata ka wuce, murmushi yayi yace a nan zan kwana, ido ta bude alaman tsoro tace kabarwasa dan Allah ka wuce, murmushi yayi tare da fad’in ok sai yaushe kuma? Tace gobe zamu koma kaduna sai dai muyi waya kawai, yace karfe nawa zaku tafl? Tace kaman 10 yace OK Allah ya kaimu za muyi waya, tace OK fita yayi ya rakata har ciki sannan ya koma ya shiga motarshi yaja dan tafiya Kano. Kaman yanda yace wajan tara sun gama shiri, suna cikin flto da kaya saiga Alh mahmud da security dinshi, gaida Haulat yayi ta amsa cikin fara’a sannan suka gaisa dasu zarah, ido suka had’a da rahma ya kashe mata ido d’aya, murmushi tayi tare da kawar dakai, kallon Haulat yayi tare da fad’in aunty za’a gina ajizuwa inaso harda secondary Ayi tun daka primary har secondary school, sannan za’a saka malamai, Haulat hawaye ta Fara tare da saka mishi albarka, Suma su zarah godiya sukai tamai tare da taya Haulat murna, mota d’aya ya ware yace su zarah a ciki zasu koma, yasa driver ya kaisu cikin jeep Mai baya biyu kaman cikin seeyana haka jeep din yake ga AC, Bayan an gama saka musu kaya a mota suka shiga ciki amma banda Rahma dake tsaye kusa dashi kallonta yayi yace Zanzo cikin week din nan Dan Ayi maganan auren mu, dan bazan iya Bari ya dad’e ba Kar wani ya kwace min ke, murmushi tayi tare da fad’in ni taka ce, tana fad’in haka ta shige mota da sauri, shikam nanata Kalman data fad’a yaita yi yana murmushi haka suka wuce.
Su ummi na falo suna fira Wanda jiran yaran nasu kawai suke, sai gasu kaman daka sama, da sauri suka nufi iyayen nasu suna murna, gaida iyayensu sukayi cikin farin ciki, nan suka zauna a falo Anata fira, zarah tace ummi Ina farida? Ummi tace tana d’aki kaman bacci takeyi, haka suka ci gaba da fira har suka nufi dinning kowa yaci abinci, nan khairat ta Fara basu Labarin soyayya alh Mahmud da rahma, hindu dake zaune ta kalli khairat tace Kai wannan Labarin ni har naji wani iri yanzu kanwarki sai ace ta rigaki aure gaskiya ya kamata Kema ki kawo naki mijin, khairat barin wajan tayi da sauri tana kuka, hindu jin kowa yayi shuru tace maina fad’a mara kyau a nan? Gaskiya Aina fad’a, duka yaran barin wajan sukayi aka bar Amina da hindu sai ummi, d’akin khairat suka shiga wacce take kuka, wajanta suka nufa Zainab tace haba khairat miye abun kuka? Kiyi hakuri karki d’auki maganan Anty hindu da zafi, Khairat cikin kuka tace zainab abunda Anty hindu tace gaskiya ne, nima Ina son inyi aure bani na hana miji zuwa min ba, zarah tace toh Kema Kinji abunda kika fad’a koh, dan haka ki d’auka komai lokaci ne, haka sukai ta rarrashinta har farida itama tazo ta samesu a haka. Kullum rahma da Mahmud suna nan manne da waya koda yaushe, yauma dai suna falo Su duka ana fira kiranshi ya shigo cikin wayanta amma taki d’auka haka yaita kira taki d’auka, Amina dake zaune kusa da zarah ta kalli zarah tace dan Allah kusa a sako faruk tunda bashi yayi kisan ba, Kam zarah tayi magana mama cikin fushi tace Amina karki kara fad’in irin wannan maganan, zata kara magana mama ta dakatar da ita, rahma cikinjin takaicin abunda mahaifiyarta ta fad’a yasa ta tashi tabar falon, d’akinta ta shiga bata dad’e da shiga ba saiga khairat ta shigo ta mi’ka mata waya tare da fad’in Mahmud yana ta kira kinki d’auka gashi ya kira a tawa wayar, amsa rahma tayi tare da fad’in hello, jin muryanta da yayi yace waya bata miki rai? Tace babu kowa,yace Mai yasa kike fushi toh? Tace ba fushi nakeyi ba, murmushi yayi tare da fad’in rahma muryanki kawai naji na gane ranki a bace yake, shuru tayi ba tare da tace komai ba, yaci gaba da fad’in ban San inga kina fushi haka yaita janta da fira na soyayya harta manta da komai taji ranta ya saki, inda yake fad’a mata cikin week dinnan yana nan tafe dan yayi kewarta, murmushi tayi tare da fad’in Allah ya kawo ka laf’lya.
Kaman yanda Alh Mahmud yace hakan koh akayi sai gashi yazo cikin satin, a gidanshi dake kaduna ya sauka, Washe gari yazo gidansu rahma koda yazo ba ita ya nema ba, gunsu ummi yazo ya gaidasu, nan rahma da y’an uwanta suka cika Mai gaba da kayan ciye ciye amma shi kam idanshi nakan rahma wacce yaga ta kara yi mishi kyau Sosai, su mama sun yaba da hankalinshi Sosai sannan sunyi mishi y‘an tambayoyi inda Ya basu amsa cikin nutsuwa, yace zai turo magabatanshi suzo neman auren rahma, su mama cikin jin dad‘i suka ce babu damuwa tunda har ta yarda kazo Nasan Kun fahimci juna, rahma ce ta tashi tare da fad’in mama bana son wannan auren, kowa dake wajan kallon mamaki yake mata musamman alh Mahmud da lokaci d’aya yana yinshi ya canza ……
Hmm