MISBAH BOOK 2 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH BOOK 2 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Kai tsaye ya wuce falon mahaifinsa, anan ya same su duka har da Lukman, yana dariya ya gaishe su. Kallo daya zaka masa kasan yana cike da tsantsar farin ciki.Ya zauna a kusa da mahaifinsa tare da kwantar da kansa a cinyar sa.Baba ka yafe min”.
Alhaji Umar ya dinga ji da ganin Deeni kamar mafarki, sai da hawayen farin ciki ya zubo masa bayan shekara takwas zuwa tara Deeni ya fito daga kejin da ya shiga.Mahaifinsa ya
kalle shi, “Deeni Alhamdulillah, tsantsar farin cikin da nake ciki yau ban san iyakarsa ba. Nima ka yafe min”.

Mama dai ta kasa jurcwa sai da tayi kukan, farin ciki da jin dadin da suka tsinci kansu a ciki, sai godiyar Allah. A nan Deeni ya tabbatar musu da ba zai taba sake daga musu hankali ba.
“Zan yi biyayya a gare ku inshaa Allah”.
Alhaji ya kalle shi, ya ce “Allah Ya maka albarka Deeni, nima na muku alkawari dukkan ku ‘ya’yana ba zan sake shiga rayuwar ku ba, kowa ya yi abinda yake so duk da nasan nayi latti duk kun gama karatu”.
“Bai yi latti ba Baba”. Deeni ya katse shi. “Ko a yanzu zaka iya yin abinda kake so,
ina fatan zaka taimake ni kasa min albarka” “Inshaa Allah Deeni sai inda karfina ya kare”. Ya ce, “Wannan yarinya likita Bahijja Allah Ya mata Albarka”.
Mama ta kalli Deeni, “Za ka kaini har gida
insa mata albarka”.  Ya yi dariya, “To Mama ko yanzu in kin
shirya”.Tayi dariya, “Ba yanza ba, sai gobe”.
Alhaji ya ce, “Nima ba za a barni baya ba”.


Washegari bayan sallar isha Deeni ya tuka su zuwa asibiti wanda anan gidan Bahijja yake, suka yi tambaya don kuwa Deeni bai taba zuwa gidanta ba.
Sun samu Baba Andi ta ce bari ta shiga ciki ta mata magana, anan Deeni ya mike yana zagaye falon nata da yadda ta tsara shi yana murmushi yana jin sonta na kara tasiri a zuciyar sa, soyayyar Bahijja na shigarsa tare da saka masa wani irin tsananin farin ciki da jin dadi.
Yana tafiya yana zagaye wurin har ya hango gurin da ta kebe mai kama da (library) anan ya hango hotunanta da mijinta da danta suna rungume da juna, ya zurawa hoton ido yana tuno Doctor Mislihu. Sai a lokacin ya fahimci mijinta ne.
Wani dan madaidaicin (diary) ya gani da biro a hade alamar bata jima da yin rubutu ciki ba, haka zuciyar sa ta dinga azalzalar sa ya bude, yana kwadayin sanin komai game da Bahijja. Nan ya yi karfin halin budewa duk da yasan hakan ba dai dai bane. Abu na farko da ya fara gani yaji zuciyar sa tayi mummunan tsinkewa shi ne, (To my dearest wife) MISBAH..
“Misbah?” Ya maimaita a ransa. What Bai bata lokaci ba ya ci gaba da karantawa, sai lokacin ya lura Diary din da marigayi mijinta ya rubuta mata ne, yana fada mata irin muhimmancinta da soyayyar da yake mata gami da yabonta na ayyukan kwarai da take, yana mata addu’a gami da sa mata albarka.
Nan ya rufe ido yana kokarin tuno inda yake ganinta da diary din nan mai kama da littafi, da lokacin da take zuwa gidansu wurinsa, da kuma asibiti, in tana zaune bata komai takan dauko littafin tana karantawa.
Sannan wannan shi ne littafin da ta rike da sunan tana karnata masa sabon littafin MISBAH. “Wato Bahijja ita ce MISBAH”. Ya maimaita.
“Author din da nake so tun ba yau ba, Authur din da na hada (special bond) da ita tun lokacin da na fara karatun littafin ta a rayuwata, Bahijja abokiyata wacce take yanzu masoyiyata
ita ce MISBAH na da na jima ina so ina kauna? Wow! Bahijja na ita ce MISBAH na”. Kaunarta yaji yana dada tsuma shi, yana
ratsa shi.Ke din daban ce (special) ce tunda har kika iya min dabara, ni kika mayar marar wayo? Ni kike (fooling), wato dama wannan labarin kirkira kika yi a lokacin shi yasa na nemi littafin nan sama da Kasa na rasa, ashe dama yana boye ne acikin kwakwalwar ki. (I love your smartness) ina sonki Bahijja ‘yar Baiwa, MISBAH na. Sai yanzu na fahimci labarin rayuwata da kika yi kokarin hada min naji yana shiga ta, naji labarin ya tsaya min a rai. Na so inji karshen sa ko zan samu in warware nawa matsalar”.
Ya yi murmushi yana kallon hotonta, “Labarin da kika fara ni zan karasa miki, ba ni kika yi (fooling) ba? Jira ki ga yadda zanyi (fooling) dinki”.
Nan ya yi ta ganin takardunta a wurin daban-daban da irin (article) din da tayi ta rubutawa
“Misbah na ‘yar baiwa ce, inshaa Allah zama ABOKIN RAYUWAR ki da zan,,,,,,, ki kamar yadda kika fada, za kiga yadda zan kawo farin ciki da canji a rayuwar ki”. Ya yi murmushi ya ce, “Yayata Bahijja,
Abokiyata, masoyiyata MISBAH”. Nan yasa hannu ya dauki littattafan da yake so, sannan ya dawo gun su Mama ya samu Baba Andi ta gabatar musu da abin motsa baki, yasa hannu ya dauki (apple) yana ci yana lumshe ido, yana jin kamshin Bahijja ko ta ina a gidan.
Baba Andi ta ce, “Kuyi hakuri na samu ta fara sallah ne”.
Mama tayi murmushi, “Ba komai”.
Bata rufe baki ba kuwa Bahijja ta fito da fara’arta lullube da hijabi, tunda ta shigo falon idonsa ke binta, ya zurawa fuskarta ido me cike da kamala da annuri, murmushin dake kan fuskarta ya kara haska fuskarta, yaga ta masa wani irin kyau da kwarjini.
Wani irin so me karfi yaji yana shigar sa, son da bai taba tsammanin akwai irinsa ba, ashe da wasa yake ba so ba, MISBAH ita ce so, ita ce SHAUKI. Kallonta na kara masa son rayuwa,yana kara masa tsammani, yana sa shi wani irin farin ciki da nishadi. A Yadda yaga tana gaisawa da su Mama da Baba suna ta hira cikin kaunar juna da kulawa ya
kara masa jin dadi da nutsuwa, haka yake burin
ganin matarsa da iyayensa.
Bahijja ta mai da kallonta kansa, ta lura ya tafi wata duniya. Biron dake hannunta ta jefa masa tana dariya, ta ce.
“Abokina Deeni, wacce duniyar aka tafi?” Ya yi mata murmushi, ya ce, “Duniyar abokiyata Bahijja, gidanki ya min kyau, ya birgeni, musamman (library) dinki, cike yake da irin littattafan da nake so” Ta zaro ido tana kallon sa, “Kaji min yaro,
daga zuwa gidan mutane har kasan hanyar (libry)dinsu?
Ya yi mata muryar tsokana, ya ce, “Ba gidan mutane bane, gidan Abokiyata fa Bahijja ne. Sannan kin manta lokacin da kike zuwa nawa dakin kina min yadda kike so? Yanzu lokaci na ne”.
Ta ce, “Gidanku gidanmu ne, ko Mama?”  Mama ta girgiza kai, “Kwarai”. Ta kalli Deeni tana masa gwalo, ta ce
“Gidana kuwa gidana ne ni daya, Baba Andi daga yau in yazo kar ki bude masa kofa”Baba Andi tayi dariya ta ce, “Ni na isa in
shiga tsakanin yaya da kaninta?” Deeni ya yi dariya, ya ce “Yauwa Baba Andi, daga yau kin zama babbar abokiyar, zan shigo inyi yadda nake so gidan yayata”.
Bahijja ta ce,”In kuwa ka yiwa yayarka
barna zaka sha bulala”. Dariya suka yi duka har da Alhaji, Mama ta kalleta ta ce.
“Allah Ya miki Albarka ‘yar nan”.
“Ameen Mama”. Ta fada kanta sunkuye.
Ta ce, “Kuyi ta mana addu’a Mama, kuna sa mana albarka, inshaa Allahu Allah Zai  taimake mu”. Deeni ya kalleta yana dariyar tsokana,zuciyar sa cike da sonta, ya ce, nima nace
“Allah Ya miki Albarka ‘yar nan”,
Ta harare shi, “Mama kinga yaron nan ya
raina ni”.Alhaji ya kalleta yana murmushi, ya ce.
“Zan
baki bulala ki dinga zane shi”.Suka yi dariya duka, ta ce, “Yauwa Baba, gara in fara zane shi don naga girman jikinsa na zolayar sa”. Deeni ya ce, “To wata ma tayi girman jiki
mana”.
Mama ta ce, “Deeni naga alamar nima zan fara maka bulalar”.
Nan suka yi ta dariya suna hira har wurin karfe tara suka yi niyyar tafiya, Bahijja ta raka su har mota. Ta lura da wani irin mayataccen kallo da Deeni yake mata, haka ta ganshi cikin tsananin farin ciki. Sai dai bata zurfafa tunani ba ta kau da abin a ranta amma ta rasa me yasa kallon yake yawan fado mata a rai.
Deeni da iyayensa suka ziyarci su Shamsu tare da sauran dangi, Shamsu da Farida kam sunsha mamakin ganin yadda Deeni ya ware har abinci ya zauna suka ci tare da shi da Faridan da yaransu ana wasa da dariya.
Tun Farida na jin wani iri, tana takura har ta ware tana kallonsa tana mamakin ganinsa haka. Ya kuwa nuna mata shi dan duniya ne, ya dinga janta da hira, “Aunty Farida kaza, Aunty kaza . Tun bata da niyyar sakewa har ta sake.
Deeni kuwa har cikin ransa ya gama da Farida da tunaninta ko soyayyarta, a halin yanzu duniyar sa, farin cikinsa da shaukinsa yana ga Bahijja.
‘Yan uwa da abokan arziki kowa ya yi murna da sabon canjin da aka samu daga Deeni. Farida ta masa murna sosai, amma sai ta tsinci kanta a cikin wani bakon yanayi na rasa soyayyar Deeni da tayi, sai a lokacin ta kara fahimtar abinda yayi, addu’a tai tayi har ta samu saukin abin. Saboda ita har yanzu cikin kasan zuciyarta akwai Deeni a binne, sai dai zata ci gaba da jurewa da kuma rungumar rayuwarta da mijinta da ‘ya’yanta, ba zata taba tono shiba.ba
A cikin wannan lokacin Deeni da mahaifinsa suka yi ta shiga da fita da buge bugen neman makeken fili a kusa da asibitin Bahijja don anan ya cewa mahaifinsa yake so ya yi gidan gonarsa. Shi dai bai tambaye shi dalili ba, ya biye masa don yanzu duk abinda Deeni ke so shi ake yi masa, da sauri ma kuwa. Shakuwa
da soyayya ta musamman ta shiga tsakaninsa da mahaifinsa, gaba daya Deeni ya dawo sabon mutum.
Abinka da masu gidan rana, lokaci kankani aka gama ginawa Deeni gidan gonar sa, aka daukar masa ma’aikata masu taimaka masa da komai. Duk wani abinda yake bukata an sa masa shi ciki, a hankali wurin ya dinga habaka yana yiwa Deeni yadda yake so.
Irin farin ciki da jin dadin da ya tsinci kansa a wannan lokaci ba a magana, yayin da ya sako Bahijja gaba da nasa salon tsokanar wanda ya samo.Wata (number) ya samu yana tura mata (text message).
Tana zaune (office) dinta tana karance karancenta taji wayarta tayi kara alamar shigowar sako, ta dauka ta bude. Gabanta ne ya ba da ras!
“MISBAH” shi ne abinda taga an rubuta. Tayi bala’in rudewa saboda duk duniya
mutum daya ne yasan ita ce MISBAH, wanda yanzu ba ya duniyar. Kafin ta gama fita daga wannan rikicin ta
sake ganin an turo mata wani.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *