UMM ADIYYAH CHAPTER 88 BY AZIZA IDRIS GOMBE
mushi, sannan ya ce, “Shi kenan
hankalinki ya kwanta?” Ita ma murmushin ta
yi a kunyace. Take Dr. Yusuf ya san
lamarin nasu ya wuce basaja.
Haka yana ji yana gani suka fice a ofishin din
ka na ganinsu, ka ga wadanda suke
matukar son juna, daga kallon da suke yiwa
juna, zuwa yadda suke magana da juna
kadai ya isa shaida. Ajiyar zuciya ya yi, ya
daga aikin da ta mika na Project din da
suka bari.
A bangarensu kuwa, tun suna tunanin abin na
dan lokaci kadan ne za ta daina,
amma gadan-gadan! Wannan cikin sam baya
son kamshin Zaid, sai daga baya suka
fahimci ba turaren bane ma baya so, shi karan
kansa ne, daga nan kuwa ya nisanci
shisshige mata da yake yi, sai in ya kama dole.
Wataran sai ya yi kamar zai riketa
yadda ya saba zama kusa da ita, sai ya tuna.
Har tausayi yake ba ta, amma ba