MISBAH BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

 

 

abin da kakeso (have fun) da yammatanka da

kawayenka social network ka kwana ka wuni ka gama kallon duk yarinyar da ka gani ka kuma murji

amarcinka da masoyiyar ka Farida ga fili ga me doki

nabar muku fagen.

ta fisge hannunta ta wuce ta kyaleshi a wurin.

Duk ta gama kashe mai jiki da maganganunta a yadda yake tunani da tsammanin Bahijja har ta wuce nan bashi da sauran kalaman da zai mata magana ta saurareshi ko tasan me yasa gaba ta canza ta rikida ta dawo wata abu ta daban duk abin da ta lissafo masa eh yayi su sai dai ta mishi wani rashin fahimta saboda da zaman lafiya da gudun

bacin ranta yasa bai son amsa wayar mace a

gabanta tare da goge duk wani sako da mace ta masa musamman na yanmatan da ke like da shi dole dole sai ya sosu ko ya aure su, wanda gudun

tashin hankalinta yasa yake boye mata.

To wai da yake biyewa yan matan dan a rabu

lafiya wai da gaske yarinta ce ni yaro ne? dan

kawai ta bani wasu yan shekaru da baifi biyu ba take tunanin ita ta girmemin a tunani da hangen nesa? Bahijja ne tamin wannan rashin mutuncin da mummunan fassara to shin ita wannan ba halin yaran bane tayi?

Tun daga wannan

lokaci yasawa ransa da

zuciyarsa auresa da Bahijja sai Allah ne kadai

yasan iya lokacin da yayi saura amma tabbas in aka ci gaba a haka igiyar auren yana iya tsinewa zafin

kishi da zafin zuciya ya sata mance manners dinta

na aure ta mance ni din nan mijinta ne zan iya

daukar komai amma banda raini amma mu je a yadda takeso in dai nine za ta samu.

Wayar sace ta sake kara har yanzum Farida ce bai bata lokaci baya dauka tare da kiran sunanta

Farida da karfi wanda da gayya yayi dan Bahijja taji cak ta tsaya tana jinsa ya ci gaba da magana

‘”ina jinki Farida sorry naso daga wayarki tun dazu

ina fata ranki bai baci ba? Farida taji maganar a ba zata dan ta zaci jin bacin rai daga gareshi wani irin dadi ne ya lullubeta

“Deeni kai ne kuwa? Alhamdu lillah yau na ji

dadi ban yi aikin banza ba Deeni na yadawo gareni dama nasan KAUNARMU ba zaka taba mantawa da shì ba so na kuwa baza ka taba dainawa ba. Gaskiya ne Farida ya za’ ayi in daina sonki my first love

yana maganar yana kallon Bahijja ga

mamakinsa sai yaga ta juyo ta saki wani irin

kasaitaccen murmushi tare da girgiza kai tayi

dariya har hakoranta suka bayyana sanna ta wuce tayi tafiyarta tare da ja masa kofa me take nufi ya

tambayi kansa fuska cike da mamaki ba haka ya zata daga gareta ba, ba dai duk tsawon zaman da yayi

da Bahijja da irin sanin da ya mata bai gama

saninta ba har yanzu ko dai tsabar mishkilanci ne irin natan haka ya dinga tambayar kansa haka nan

yaji ransa ya kuma baci sosai wanda Farida ma tayi ta surutunta a waya bai ma san tana yi ba harta gaji ta kashe

Dakinta ya bita ga mamakinsa ya samu har tasa kayan barci ta kwanta da alamar barci me nauyi take yi hakan na nufin Bahijja ta dai na sonshi ke nan?

Bata kishinsa bata damu da shi ba? Ya matsa dab da ita ya zurawa fuskarta ido yaji wani irin tsananin son ta da sha’awarta sun kara shigarsa ya tsinci

kansa cikin tsananin shaukinta da kewar Misbah na da ke matukar sona wacce ta sakar min ragamar

rayuwarta ta yadda dani fiye da kanta yau ta juya min baya ina yaddar dake tsakaninmu?

Kwanciya yayi jikinta tare da rungume ta sosai

jikinsa ki yadda dani Bahijja har yau yadda kika sanni haka nake Denin ki bai canza ba banci amana ba kuma ban karya alkawari ba.

Ban taba tunanin (actions) dina na bata maki rai ba magana da friends mata, social network da duk abin da kika tuhumeni da shi ban tabayin ko daya dan in bata maki rai ba gaskiyarki ne laifinane da

nake boye maki banayi a gabanki dan kar ranki yabaci wannan shi ya kawo zargi a tsakanimmu

wannan abubuwa banyisu don bana sonki ba ko don ina bibiyar wasu yanmata sai kamar yadda kikace saboda nishadi da gudun wulakanta mutane amma na yadda laifinane ni na bada dammar yin

haka ni na bada kofar zargi ya shiga tsakanimmu ki

bani dama Bahijja ba zan iya rayuwa kina nuna min tsana da rashin so ba tare da min kallon maci amana wannan aure da kinsan yadda ya kuntata

min rayuwa da zuciyata da baki kirashi da farin cikina ba.

Misbah ke ce farin cikina kece natsuwata da

kwanciyar hankalina haka ya dinga suratai kamar

kwancecce tare da rungumarta sosai yana shaker kamshinta tare da jin son ta na ratsa shi ya lura

barci take sosai tsakanin ta da Allah.

A wanna halin barci ya kwasheshi Bahijja ta

fara farkawa da Asuba ta jishi a jikinta nanta

kalleshi tare da janyeshi a jikinta ta gyara masa

kwanciya tare da lullubarsa ta shiga bayi tayi

wanka tare alwala ta fito sannan ta tasheshi ya bude

ido tare da salati yana kallonta tayi murmushi

“Mallam Deeni, yau za kayi lattin sallar asuba

lallai barci yayi dadi tashi kayi alwala.

Kallon ta yake cike da mamaki fuskar ta kunshe da murmushi tare da walwala ba alamar damuwa a

tare da ita, har yaje masallaci ya dawo zuciyarsa na sake-sake ya rasa ina Bahijja ta dosa ina tasa gaba.

Kamar yadda ta saba ta shirya musu (breakfast) ta shirya tsab domin tafiya aiki,ta leka dakin sa har yanzu kwance yake sanye da jallabiya alamar ba

zai fita yanzu ba ke nan, tayi masa sallama tare da gaishe shi ta ce,

‘”naga kana kwance har yanzu ba

har yanzu alamar bazaka fita yanzu ba ke nan,ga breakfast can na hada ni na shirya zan wuce asibiti.

kallonta kawai yake don ta daure masa kai har

taja kofa za ta tafi ya kira ta yace”BAHIJJA”!

Ta dawo tare da kallonsa alamar tana jiran me

zai ce.ya kalle ta da kyau ya ce,

“wai meye a  zuciyarki da ranki kuma meye hakan da kike yi

yake nufI Ta yi murmushi

“Deeni wani irin tambaya ce

wannan, ba komai a raina sai alkhairi, sannan jiya na kwana cikin sakin rai kuma na tashi zuciyata a

sake na ji dadin yadda yanzu ba wani boye-boye ko munafirci ko rashiN gaskiya isakanimmu ka daina

yaudarata, ka kuma daina yaudaran kanka duk abin

da zakayi kayi shi a fili ka daina boyewa ka daina yaudarata da maganganunka da nuna min son karya.”

Ya kalle ta cike da mamaki “son karya”?

Ta yi murmushi tare da girgiza masa kai ta ce,

“kwarai son karya, karfa kamin rashin fahimta

bance baka sona ba, kana sona amma ba har yadda kake fadi ko kake nunawa ba, sirrin zuciyarka da abin dake ciki ka fini sani me kake so wa kake

so,me ke maka dadi, me kake da buri da bukata duk ka fini sani, dan haka kana da dama da sararin da zaka cika

duka burinka dana sauran

mutane,yammata ne gasu nan ko ta ina sai wacce ka zaba, me ka taba ce min ni bana maka? Nasan

kamantani ina sane kissa,kwarkwasa, kisisina, kaje duk zaka samu masu maka ka cika burinka na

auren masoyiyarka ka kuma cike da tsala-tsalan

‘yammata kaji dadin rayuwarka ka more ta (enjoy your life) tuni zuciya ta kai shi karshe ya mike

idonsa jawur zuciyarsa na ta fasa ya ce haka kikace? Haka kika dauke ni?

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *