MISBAH BOOK 3 CHAPTER 23 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 23 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

 

tsammani ko tunanin zan samu wata karbuwa ko soyayya daga danginnan tunda suka samu nasu shi ma ya samu abida yake so.

Baba Audi ni fa yau idan aka ce min Deeni yaje

ya karo, wasu matan ba zan yi mamaki ba kuma bazanji ciwo ba ko da cewa yayi na fita na bashi guri zai • maye. gurbi na da wata duk bazan yi mamaki ba kuma ba zai min ciwo ba ina nan ina jiran zaman zuwan wannan lokacin tun farko basirata ce ta toshe na manta ba a alkawari da danamiji ba a yarda da da namiji namijin ma irin Deeni irin wanda idanunsa yana kan mata tunaninsa ya ga mace ta birgeshi ya juya ta yadda yake so idan yammata dari zasu wuce ta gaban Deeni to duk sai ya daga ido ya kallesu kuma sai yaji yana son-ko wacce daga cikinsu. To ki fada min menene abin daga hankali akan irin wannan mazan duk son da

nakewa namiji inda halinsa haka yake to na hakura da shi HAR ABADA.

Bahijja ina hankalinki da tunaninki ya bata kike

iri wanna zancan nasan kina cikin bacin rai ne shi yasa kike fadin duk abin da yazo bakinki.

Matsayina na kamar, mahaifiyarki wanda akwai yadda da amana a tsakaninmu ina mai shawartarki da ki canza tunaninki wannan ba sabon abu bane yana da kyau ki koyi al’adamu ta hausa Fulani ki koyi- zama da kishiyarki ki koyi zama da dangin miji saboda matsayinkin nan da kike da shi kada ya

kufce maki taya zaki bari Farida yarinyar kanwar bayanki tayi nasarar fitar maki da son

miji a zuciyarki amma gaskiya ban zaci haka daga gareki ba nasan kalaman da Hajiya tayi maki amfani masu dadi bane ki dare ki cije kema ki koyi wannan kissar don samun karbawa a gurin dangin miji da mahaifiyarsa da kuma shi kansa. Dole ki samawa kanki matsayi ba  ki tuna fa mace bata da darajar

daya WuCe gidan mijinta duk iliminta duk matsayin idan bata da aure batada wannan

darajar.lokaci yayi da zaki cire komai a ranki ki

kiyi ibadar aure tunda ta fara magana sai yanza ne ta dago kai ta kalle ta ta ce

‘”baba audi ibadar ita ta ajiyeni ,tsoron

Allah da mutuwa ta yasa nake zaune a yadda nake yanzu duniyar da rayuwar cikin ta da jin dadinta ba sune a gabana ba abin da da nasa a gabana in nemi lahirata da duniyata. kuma neman lahirata kuwa da aljannata ba,a sa masa riya ko munafunci ko son

zuciya Baba Audi ban yarda da wannan al’adar ta mallam bahaushe ban kirsa da kisisina da salon yin abu ba don

Allah ba sai dan wasu ko wasu su yabe ka.

Ko danka bata wani ko ka tozartashi, kafin

Ka samu yarda warin Allah saiya kasance ka tsarkake zuciyarka komai zaka yi yi

domin Allah din nan shi kadai ba don ka birge

wani ba ko wani ya soka ko wani ya yabeka

ba,Baba Audi kin kira aure ibada to fada min wane abu nake yiwa mijina wand ba daidai ba ina ha’intarsa?ina danne masa hakkinsa bana masa abin da Allah ya ce mace ta yiwa mijinta ?ina cin amanarsa?

Bana tsare masa amanar auransa sannan bana kare mutuncinsa da nawa?

Baba Audi a iya sanina duk ina yinsu saboda ibada da neman yardar Allah, hakkina na kwanciyar aure da nace na yafe masa da a lokacin ya ce min shi bai yafe ba bai yardaba

da zan dinga bashi hakkinsa ,to amma ya amince kuma na rike Alkawaari da Amana na tsare kai na tareda nisanta kai na da duk wata sha” awa ta jin dadin jikina ko duniyannan ziyaran yan,uwansa ina yi Alheri inayi

musu daidai gwargwadon karfina iya abin da ya kamata inayi idan su sun ga hakan yayi musu kadan to ni iya abin da da zan iya ke nan kuma dama badan su yabeni nake yì ba ko su sonì na yi ba sai don Allah, wanda nayi dominsa ya sanì to menene wani abin daga hankali ba abin da zan yi dan

neman suna da zan yi gurin mijì ko danginsa

tunda su sun mai da hakan al’adarsu to bazan

hanasu ba amma fa nii ba zanbi

sahunsu ba,haka nake zan ci gaba da zama a yadda nake babu mai canzani ko da kuwa Deeni ne ko ‘yan’uwansa ko matarsa ko mahaifiyarsa,.

‘”suka ji muryasa kamar daga

sama wanda ya dawo ne don ya lallasheta sabo da yasan bata ji dadin kalaman da mahaifiyarsa tayi mata ba

maganganun da suke da Baba Audi yayi matukar bakanta masa zuciya sosai saboda yadda ta gama

sallamashi a rayuwarta gaba daya ta tsaneshi rashin kaunar har kai bashi da wani matsayi da za ta yi wani abu dan farin cikinsa ko samun matsayi mai girma akan wanda take da shi a zuciyarsa to amma

ba kowa yake iya jure rashinsa ba a nuna maka a zahiri ba a sonka akwai kona zuciya hakan ya fusata shi ransa yayi mummunan baci da yasa yaji shi ma ta fita a ransa baya bukatar ta a rayuwa. Ya ci gaba da

cewa Deeni da Danginsa da

¡yayensa don basa sonki ba komai bane tunda kema ba sonmu kike ba idan ba kya sonmu ba kyau bukatarmu a rayuwarki to muma bama bukatarki Hajiya Bahijja dukkanmu daga ni harke babu wanda aka daura a kafa aka ce dole sai mun zauna tare da ni da ke mu muka ce munji mun gani yanzu kuma tunda abin ya kai ga haka zaman namu bashi da amfani sai tsana kiyayya da rashin fahimta

ya rufe maki ido da har ba kya ganin sauran komai a tsakaninmu sai zaman dole da kiyayya don haka yau zan kawo karshen zaman.Baba Audi ta mike da sauri hankalinta a tashe tace”A’ah ba za ayi haka ba idan ita mace hankalinta ya bata kai namiji ne bai kama ta naka hankalin ya bataba don Allah kada kayi danyan aiki a yanzu cikin bacin rai.”

“Kyalle shi Baba Audi yau babu mai shiga

tsakaninmu yana da kyau bamu wuri wannan

tsakanina da miji nane Bahijja ta fada cikin kunar zuci.

“Baba Audi ki bar wurin nan” shi ma Deenin ya

fada cikin kaukausar murya hakan yasa ta mike jikinta a sanyaye hankalinta a tashe ta bar wuriN falon.Bahijja ta mai da hankalinta kansa ta ce”‘inaji kuma ina saurarenka

Murmushin takaici yayi da bakim ciki ya

ce” Abin da kike so ne zai faru abin da kika dade kina fadine yau zaki cika burinki da,ma kin min Al’kawarin duk ranar da na

auri Farida zaki kyalleni, ni kuma nayi maki Al’ kawarin bani ba auranta HAR ABADA naci Amanarki Bahijja na karya Al’kawari na auro masoyiyata Farida sai yaya. nina karya ALkawari amma ken a sanki da cika Al’ kawari don haka zan taimaka maki wurin

cika naki Al’kawarinki kafin nan zan fada maki

wani abu Bahijja MISBAH na tsaneki na tsaneki

tsana mai tsanani sanadiyar sani daukar wannan mataki da hukunci tsakanina da ke yasa na tsaneki na kuntata min rayuwa da kike yi na tsaneki na irin yadda kika dauke ni na irin halin da na shiga saboda ke da soyayyarki,na tsaneki na sani jin abin da naji,na ji kiyayyata da tsanar kaina a sanadiyyar nuna min kiyayya da tsana da kike

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *