MISBAH BOOK 3 CHAPTER 25 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 25 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

 

 

Cikin wata guda ta nemi masu siyan asibitin ta

siyar da shi ta tattara komatsanta ta kalli baba Audi ta ce,To yau kam rayuwarmu ta zo karshe ko muna so ko bama so.Baba Audi ta kalle ta fuskarta cike da damuwa tare da tausayawa,ta riga ta fahimci halin da ta

shiga-ta ce,Yata Bahijja babu abin da zai raba mu dake sai mutuwa, Bahijja ta girgiza mata kai wadda take nufin a’a ta ce,Baba Audi ko mutuwa bata raba mu ba rayuwa za ta raba mu dole saboda haka ni kaina ban san inda nayi ba,ina na nufa? Yaya rayuwa za ta kasance ban sani ba? Da ina da inda

zan ajjeki amma yanzu ni kaina banda inda zan ajje kaina kuma ban san ina zan shigaba,ko me zakice ki fade shi yanzu domin ni ba zan iya barinki ba saboda haka duk inda zaki shiga nan zamu shiga tare,domin ba mu da wanda yafi juna. Zan zauma tare dake duk runtsi duk wuya zan kula dake da abin da ke cikinki., Bahijja ta kalle ta cike da mamaki ta ce”Ya akayi kika sani? Ta yi murmushi

ta ce: Saboda ina tare dake dare da rana… Ina sane da ke kuma ina lura da yanayinki..

A shekaru na Bahijja ciki tun yana kankani zan iya gane mace mai dauke da shi,dan haka kar kiyi mamaki kuma kar kiyi jayayya,na tabbatar ke ba mai cuta ta bace dan haka ko ina zaki shiga zan biki ba tare da shakka ko shayi ba,Shi ke nan Baba Audi yadda kike so

haka za’ayi duk da bani da kowa

a rayuwa,Allah ya bani ke a matsayin uwa da dangi me share min hawaye. Kayan sawarsu kawai suka dauka suka bar gidan

zuwa airport suka samu jirgin Abuja duk da bata taba sha’awar garin ko zuwan sa ba amma ta yanke shawarar su shiga

Arewa daga nan su san inda Allah zaiyi dasu.

Ita dai Baba Audi ta kyaleta saboda a wannan

okacin tana cikin zafi da makanta ko me za ta ce mata baza ta gane ba dole ta bata lokaci,haka Bahijja tasa kafa tayi sallama da

Lagos tare da tunanin ta bar shi har abada ba za ta dawo ba. Hmmm

Ya samu Hajiya zaune a bangarenta,kasancewar safiya ce ya

durkusa har kasa ya gaisheta yadda

taga yanayinsa ya sa tayi masa tambaya ba shiri Deeni lafiyarka kuwa yana ganka duk aya mutse jiki a mace ko baka da lafiya ne?

Yayi murmushin karfin hali ya ce” mama lafiyata lau yanayin rayuwa ce nazo in fada maki ni da Bahijja. Na sani ai tayi sauri katse shi, wannan yarinyar ba za ta zauna lafiya ba kuma ba za ta barka ka zauna lafiba ba,tana bakin ciki da farin cikinka dana Farida, to wai kishi hauka ne? tabbas za ta gamu da tsananim fushi na dan ba kyaleta zan yi ba

Ta fada tana huci Deeni yayi murmushin takaici ya ce, mama duk ai ba sai kin kai ga haka ba saboda yanzu Bahijja tayi nisa da rayuwata nayi nisa da rayuwarta igiyar aure ce daman ta hadamu kuma yanzu ta raba mu kamar yadda kike so,yanzu gidana Farida ce da yaranta, miji kuma nata ne ita daya,Bahijja Allah ya kawo karshe zaman mu ba sauran tashin hankali”?In dai akan ni da Bahijja ne ba sauran bacin rai na sake ta mun rabu kuma ta tafi ina neman hutu da natsuwa ina so zan yi tafiya kona wata daya ne

Idan hutun yara ya kare su Farida sai su koma,in na tashi zan wuce daga can nazo muku sallama ne naga Baba bai fito ba ni kuma bana son nayi (missing flight) sai Ki isar masa da sakon kuma in na isa zan masa waya mama dai ta bude baki tana kallonsa tare da

mamakin kalamansa ya saki Bahijja sai kace wani Tatsuniya Deeni da hankalinka ko me yayi zafi da zaka yi saki nasan akwai matsaloli wanda akwai hanyar gyara da yawa ba sai an kai ga saki ba,yanzu yarinyar nan sai da ta kure ka tasa ka sake ta?

‘”‘mama mu bar maganar nan Bahijja ce dai

yanzu ba mu da wani dangantaka da ita ta zama tarihi don Allah na roki Alfarma

karki sake maganarta kar maganarta ya sake hada ni dake koya.Ni zan wuce.Ina zaka”? Sukaji muryar Farida tana cika tana

batsewa idanunta cike da fushi ta matso gabansa gaba daya kishi ya rufe mata ido har ta manta a gaban mama take ta ce”Ka saki Bahijja ko kun hada baki ta tafi zaka bita

Zakuje ku hadu a wani wuri ku hole ni za’a

yaudara zaka ce ka sake ta zaku tafi kuje ku

shakata in kun dawo kace ka maido ta ko? Wai ni Deeni me na maka ka tsaneni ko don ina sonka shi ne laifi na? Ko Daga kai ya kalle ta baiyi ba balle ya bata amsa,ya sa kai ya fice,mama ta kalle ta sake da baki tace”Farida ashe baki da kunya a gaban nawa? Kuma mijin naki kike yiwa rashin kunya? Ina tarbiyarki?

Ta durkusa gaban mama tana kuka,mama kiyi

hakuri abinne ya isheni ya daga min

hankali,Deeni komai Bahijja ni baya ji baya gani na tunda akayi auren nan,ya mai dani abokiyar  gabar sa,ni na tabbatar Bahijja ta shiga tsakanina da Deeni, bokanta yayi nasarar raba mu.mama taji tausayin Farida ya kamata yi hakuri Farida Insha Allah komai yazo karshe ba wani abin daga hankali gashi ai Allah ya kamata auren yazo karshe yanzu zaku gina rayuwarku,kuyi farin ciki ke da Deeni zan dage da Addu’a kema ki dage,ki

kuma bawa Deeni lokaci zakiga zai sauko da

kansa amma ina mai baki shawar rashin kunya ki dai na shi musamman wa mijinki.

Duk yadda zuciyarki tayi zafi ki danne ki kuma

dinga kyautata zato in ba haka ba wata ran

tunaninki zai iya cutar daku duka,haka dai mama tayi ta lallabarta tare da bata baki sannan ta shige ciki duk hayaniyar da sukayi a kunnen Alhaji sai da Faridan ta shiga ciki tukunna. Sannan ya fito ya kalle ta tana zaune tayi zugum ya ce “Anya kuwa kina ganin akwai adalci a cikin lamuranki baki sa son kai da son zuciya ba? Ta dago kai ta kalleshi Alhaji me kake nufi yace, Yaron nan fa Haifansa mukayi ba halittarsa ba kamar yadda muke da hakki akansa haka yake da hakki akanmu sam baki dubi halin kunci da tashin hankali da yake ciki ba sai son zuciyarki wai me yarinyar nan Bahijja ta maki kika tsaneta meye

laifinta? Ki dinga tuna baya fa da Alkhairinta yau sharrinta daya bai kamata ya goge dukkan Alkhairinta ba ki tuna lokacin da mu iyayensa muka kuntata masa muka jefashi cikin tashin

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *