MISBAH BOOK 3 CHAPTER 7 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
mace daya zan iya yi wa adalci a duniya Bahijja,
kin ga Allah ma cewa ya yi in ba’ za ku iya adalci
ba to, ku riki daya, haka nan Allah ya yi ni, kuma
ni na san a mata Bahijja kadai za ta iya da ni, zata
¡ya mani a yadda halina yake da tunani na da
yanayina WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
zamantakewar aure to, na shaida
Bahijja ce kadai za ta iya mani, kin san ni ba ko
wani halin mace zan iya dauka ba
Maganarsa ta soketa sosai, wai ita Deeni ke yi
wa hannunka mai sanda, Deeni da ko sunanta ya ji an kira sai ya shiga wani yanayi amma in mantawa
ya yi zan dawo da shi daidai, tayi murmushin
karfin hali tace
“mun kusa shiga exams, ga
address din inda za mu yi, ko zaka taimakawa ka ajiye ni?
Ba ga driver ba, ina bukatar hutu kafin azahar infita.”
Ta bata fuska ta ce, WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
“haka kawai za ka bar ni a
hannun driver da ban sani ba, don kawai bani da gata wurinka.
Wannan driver mun yarda da shi, mun yi aiki da
shi na tsawon lokaci amma tunda ke tunaninki haka
yake muje in kai ki, amma kar ki zata bata
fuskarki ta sa zan kai ki, adalci zan maki
matsayinki na matar yayana.
Maganar ta soke ta, amma sai ta dake ta yi
murmushi tace, “Na gode.
Nan ya fidda mota, ta
fito danke da wasu takardu hannunta, a hanya ta dinga tuna masa abin da ya faru a baya,
*Deeni, ka
tuna lokacin da kake goyo na a keke ka kai ni
jarrabawa makaranta, duk da makarantar kusa da
gida ne, kuma ka zauna ka jira ni har sai mun gama.
*Kullam muna tare muna hira, tun muna kanana
har muka fabimci muna soyayya, I am your first
love and you are my first love. Ka tuna, komai baya iya raba mu in dai akaga ka dauke hankalinka
daga kaina to Misbah, ya saki littafi, sai da na yi yaki na raba ka da littatafan Misbah
HAR ABADA.
Ya kalle ta tare da katse ta ya ce,
“Abin da za ki
yi ki rubuta a jarrabawan ke nan, wai anya kin san
ma me ya kawo ki garin nan, exams din ne ko wani
abu daban?” Ya kalle ta ya nuna mata shi fa namiji
ne, ba muna maza ba da za ta yi saurin raunata shi
ya ce,
“Confirm you are my first love, amma yanzu
you
are my past love, kin san dai past ba ya
dawowa ko? idan ya wuce ko da da minti daya ne
ya wuce HAR ABADA, daina ginì kan iska Farida, WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
shawara nake ba ki, idan mutum yana da buri a
gaba kuma burin nan nasa bai cika ba akwai ciwo.
Ina guje maki jin wannan ciwon, littatafan Misbah
kuwa da Misbah wanna kaddara tace, wadda
Allah ya rubuta min, ba dan-Adam din da ya isa ya
kawar da wannan kaddarar,
Yana gama fadin haka, suna isowa gate din school
din da za ta rubuta exams din, dan haka ba ta samu
damar ba shi amsa ba sai dai fa ba ta karaya ba,
ta ci alwashi sai Deeni ya dawo kan hanya, sai ta
tabbatar masa da har yauzu akwai soyayyarta a
karkashin zuciyarsa.
Ta kalle shi,
“karfe biyu za mu gama, za ka
dawo ka dauke ni?”
tana yi tana wani kwarkwasa.
Dariya ma ta ba shi ya ce,
“Farida manya, zan
dawo, ba zan bari a sace ki in ba so kike su mama
su sa ni ma a sace ni ba.
Dariya ta yi, suka rabu yana mai ce mata, Allah
ya ba da sa’a, duk da hirar da su ka yi ba haka ta soba, ta so ta tabo emotions dinsa, amma ba ta yi
nasarar hakan ba, amma dai ta ji dadin samun dama
da ta yi na zama da shi na dan wani lokaci, ba
kamar yadda Bahija ta wani kanenaye shi ba, wani
bai isa ya matso shi ba musamman ita.
* Bayan tafiyar Deeni, yana murmushi yana
magana a ransa
“wai ko me mata suka zama suka
mai da maza ko ance
wasu mazan,wani
kwarkwasa kirsa da iya yi, wai don a ja hankalin
namiji wai Farida ta manta na santa tun tana
mitsitsiya, amma ta dage tana kwaikwayo da
Kirkiran yin abin da ba ita ba ce, ba halinta ba ne,
shi ya sa Mishah na daban take, she is just herself
kwaikwayon wani ko yin wani abu da ba ita ba ce,
wannan bata taba gwada shi, in za ka so ta a yadda
take fine ta kan yi abin da za ta iya ne, ko in ce ita
ce haka nan kuma Allah ya mata wata irin baiwa da WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
karisma ga kwarjini, ko kallonka ta yi sai ka ji ta
burge ka, wanda ita norma/kallo ta maka ba wai da
wata manufa ba.
*’Haka nan Allah ya yi ta, akwai tsabta da iya
shiga amma irin nata ba wani heavy make up, haka
nan ba ta taba shigar da zai takura ta, asali ma dai
Misbah, mutum ce da ba ta wuce minti uku zuwa
Biyar a gaban madubi, wataran ma shi ke sa ta
gaba, “yau sai na maki kwalliya kuma sai kin min
shiga irin kaza,
‘” ba musu za ta masa ba amma
tsanani minti goma zuwa ishirin ya yi yawa ta
cire.
“Tafiyarta da abubuwanta komai nata burge shi
yake, tunaninta da ayyukanta duk wanda ya kalli
Misbah ya san ya ajiye mace, ga ilimi ga basira ga
tsabta ga hakuri da kau da kai ga taimako da
tausayi, ita dai wurin harkar da mata suka fi ba wa
muhimmainci shine ta gaza, wannan kwalliya da WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
shiga na dinkuna masu matse jikin nan, ko harkar
kicin, dan mallake zuciyar mai gida, to amma duk
da gazawarta a wannan, bai hana ta mallaki
zuciyata ba,
yayi murmushi daya tuno zancen su
wataran, tayi wanka tayi kwalliyar ta irin nata, tayi
shiga tamkar balarabiya zasu fita ta kalleshi ta
karya muryA Deeni dan Allah kayi hakuri kasoni a
haka, wannan shigan na kasa heavy make up
goggoro heavy jewelry duk wannan ba nawa bane
please ka so ni a haka.
Ya yi murmushi ya rungume ta “ina son ki ko da
kina kasa da haka ina son inner beauty dinki,
personality dinki,
kyakkyaawar
zuciyarki da
manufarki, bayan haka ma Misbah na ta fi min mai
goggoro da mai zuwa beauty palour a yi mata
makeover, natural misbah, natural beauty takan ji
Mishal na daban take, wannan abu yama min dadi tayi murmushi, ta rungumeshi
Gami da fadin mijina, daban yake,
bata taba abu dan
birge wani ko wata ba, sai don kansa, Allah ya,san yadda ya halicce ni da yanayina, sai ya hada ni da mijin da yake appreciating dina. WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
*Allah ya bar ni da Misbah
insha Allah, ke kadai ce mace da zata haifa min ya ya a duniya
da yardar Ubangiji
wannan magana ta yi mata dadi, ta dada rungume shi tana
fadin
“Allah ya bamu ya azurta mu da samun
Zuriyya dayyaba,
Ya amsa yana dariya,
suka fita
Duk da abin da ya wuce, amma da yake tunowa
murmuchi yayi yana dariya yana jin dadio irin
Hirarrakinsu, har ya iso gida ya sami yara, nan
kuwa ya shiga cikinsu suna ta wasa har da hall da sauran games, sun ji dadi sosai ranar har azahar,
sannan ya ce maza su je Baba Audi ta musu wanka
su yi sallah, shi ma zai yi
wanka da cin abinci
Suka fita a mota, Deeni karami da ke zanune gaba
ya lura da wasu takardu ” uncle ga takardunka kar in zauna a kai
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.DAILYNOVELS.COM.NG