MISBAH BOOK 3 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
murya kasa-kasa sai dai fa dakakkiyar murya
wadda ba wasa ciki ta ce,
“Deeni ina son wannan daddadar rayuwar
tamu ta ci gaba, ina son wannan wutar soyayyar da
kaunar ta ci gaba da ruruwa a zukatammu, ina son
wannan shauki ya tabbata a tsakaninmu wannan
fahimta da jin dadin juna da muke ya ci gaba HAR ABADA
“Deeni ba na fatan abin da zai taba raba ni da
kai, kana fahimtar me nake fadi ko?”
Ya sa hannu yana shafarta tare da jin sabon
shaukin son ta a ransa ya ce,
“Ni ma abin da nake
so ke nan Bahijja.
Tsam ta mike ta tsame jikinta ta fita, tare da
goge jikinta ta daura towel din tana fadin,
“ina son
ka dinga tuna haka kullum, kuma kamar yadda
kullum ba a shiga tsakaninka da duk wani effort
dinka a rayuwa, ni mana roki wannan alfarmar,
karka shiga tsakanina da duk wani Hakkina.
Bata saurari amsarsa ba ta fita ta nufi daki, ya
bita da ido ya yi murmushi tare da fadin, “Allah ya
bar min Misbah na.
.” nan shi ma ya mike ya fita ya
ga determination a idonta da actions dinta.
Bayan ya kimtsa ya same ta wurin da suka saba
cin abinci, sun ci abincin sama-sama suna yi wa
juna kallon kallo kowa da abin da ke ransa, shi dai
bai son tashin hankali da ita don ya san a dane take
dan haka ya danne tashi zuciyar ya kyale ta.
Alkawarin cin abinci da wurin kwana ba sa raba
shi, duk runtsi duk fushin da suke da juna, in daya ya hau daya na sauka, don haka da suka gama cin
abincin suka dare gado tare da ba wa juna baya,
duk da shauki da son da ke cin su a zuci, da jiki
kowa ya danne, ya ba wa dan uwansa baya,
dukkansu kowa da irin tunanin dake zuciyarsa da
hakan har barci ya yi gaba da su.
Washe gari Farida ta yi sammako ta shirya ta
nufo side din su Bahijja sabod ta kudiri aniya a yau
sai ta yi magana da Deeni, sai kuma ta tada masa
da tsohuwar soyayyarsu. Wanda ta tabbatar daga
shi har ita ba su manta ba, sai dai kash, wai
hausawa suka ce, “in sammako ka yi wani a hanya ya kwana’ don kuwa ta tarar da Bahija da Deeni
sun fice a gidan, a bakin Baba Audi take jin wai
sun fita tun karfe bakwai da motar Bahija, don
kuwa ta ga motar Deeni a gida shi ya sa ta yi
tunanin yana nan, wannan lamari. ba karamin
bakanta ran Farida ya yi ba.
Bahijja tana nufin za ta dakile
duk wani
kokarinta da take yi na ganin ta cimma burinita
kan Deeni, abin da ya kawo la garin Lagos ke nan
na musamman, “ba zai yiyu ba, ki ci gaba yanzu.
“Idan har kika kifar min da duk wani kokarina
to, nasan ta inda zan bullo maki. Wanda ina da
tabbas a kan wannan kudirin, a duk randa kuwa na
shigo gidan Deeni nawa ne, aronsa kaddararki ya
baki na wani lokaci Deeni nawane ni kadai.
Baba Audi ta katse ta “Hajiya ta bar sallahu in
kuna son zaga gari ga driver da mota zai kai ku duk
inda kuke so, sannan ga karin kumallo an shirya
muku.
Ta kalli Baba Audi, ta ji kamar ta falla mata
mari don haushi ta ce,
“ba mu da bukatar zuwa ko
ina break fast kuwa ko ba a mana tayi ba mun san
hanyar inda za mu samu, don mu ba baki ba ne,
nan gidanmu ne da ni da yarana.”
Baba Audi dai bata ce mata kala ba, ta tafi ta barta wurin. Bayan gama karyawarsu, yara suka rikice
mata, su fa yawo za su fita, dole ta bar su driver, ya
Fita da su, yayinda ta zauna ita daya a gidan, ta kai
Ta kawo tana saka wa tana kwancewa, ta wuni cikin
takaici da bacin rai
Lokacin da Bahijja tayi wa Deeni tayin fita a
motarta bai yi mata musu ba saboda ba ya son
fitina da tashin hankali, hakanan ta sha yi masa
hakuri da daga masa kafa a kan lamura da dama,
wannan ne karo na farko da ta tada kayar baya.
kiris take nema su yi tashim hankali, shi kuwa ba
zai bye mata ba, haka nan ya fahimci (cars dinta,
sai dai da la san me ke zucivarsa da bata daga
hankali ba, ita kadai dim nan ta ishe shi rayuwar, ha
shi da kuma niyya ko sha’ awar kara aure, ba Farida
ba ma ko da wala mace ce sai dai fa in ta kai shi
bango zai nona mata ba tsoronta yake ko shakkarta
ba, amma ya sa mata ido ya ga gudun ruwanta.
Yana kallon ta tana tuki tana wani cim magani
kamar mai fada da motar, ya kalle ta ya yi
murmushi, mata da kishi, amma shi ya tabbatar
kishin Bahijja daban yake da na sauran mata. Allai
ya sani Misbah na ce farin cikina kuma SANYIN
IDANIYATA “duk yadda Kika kai ga bata min rai,
wannan soy ayyar ba za ta taha gogewa a zaciyata
ba, Allah ya ha ki wata baiwa da kullum in na kalle
ki kara sonki nake, kara burge mi kike, addu ‘a nis da
fatana, Allab ya sa ki haifa min yarinya irinki.
Allah ya min baiwa ya kuma azurta ni da samun
irinki Mishah na. Allah ya bar mu tare har karshen
rayuwa.”
A jikinta ta dinga jin idon Deeni na kanta.
hakan ya sa ta juyo la zuba masa manayan
idanuwanta, tuni ya ji tana tsuma shi da kallonta.
ya vi saurin dage kai, ita ma ta dage kai har suka
isa gidan gonar nasa, ba wanda ya ce wa kowa kala
har sai da ya sauka, ta dage kai ba tare da tana
kallonsa ba ta ce,
*Zan dawo in dauke ka, karle biyar kafin nan ni
ma na gama da asibiti, ina fata za ka jya jira na, in
kuma kana hanzari ka koma gida ne to.
Ya yi murshi yadda take maganar ya ba shi
darya ya ce,
*My Misbah, ba ki sun sauka gida
kuwa, me zan je in yi tun da sarauniyar zuciyata ba
ta gidan,
a dadim gidan sai da Misbah ciki,
wannan gata da kike min, a kai ni wurin aiki a
dauko mi, ai jin dadi ne, ba ko wane namiji ke da
wannan galar ba, sai ni mai gimbiya Misbah.
Ta juyo ta mai wannan kallon nata na isa da
kasaita, la juya ta ja mota ta tali, ya jima a tsaye a
wurin yana kallonta yayin da wannan kallon ya
tsaya masa a zuciya. Lumshe ido ya yi yana jin son