MISBAH BOOK 3 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
Nan ya karba yana dubawa sai ya lura hotunansu
ne da Farida suna yara a ciki da irin wasiku da card da suke aika wa juma.
Haka nan ya ji ransa ya baci, ya ajiye su gefe
guda ransa bace, har suka isa suka dauko ta, ta lura
ba walwala a fuskarsa, ta daure ta yi masa magana,
“ba tambayar ya exams din, ko kallonta bai yi ba yace,
“ya exams din? Allah ya ba da sa’a.
“‘Ameen ta masa tana tunanin me ke yawo a
kansa, can dai ta daure ta ce
« Uncle a kai mu yawo www.Dailynovels.com.ng
shopping mana tunda sauran lokaci. Bai yi niyya ba
amma sai yaran suka sa baki
«Eh uncle a kai mu,
please please,
“ba shi da zabi sai ya biye masu, ba
su gama siyayyar ba har karfe biyar, suka dawo
gida saboda yanayin nisa da go slow irin na Lagos,
in yamma ta yi ma’aikata sun taso. Sun shigo gida
suna ta tsalle-tsalle, suka samu Bahijja a falo da su
Baba Audi suna hira, wanda tun karfe uku ta dawo www.Dailynovels.com.ng
nan Farida ta samu dama tana ta kara shisshige
masa don ta ba wa Bahijja haushi, ta ji daci a ranta,
amma sai ta daure ta yi dariya tare da fadin
“sannun ku da dawowa, ya exams din?”
“Lafiya lau,
,” ta amsa kin ga daga nan ma Uncle
Deeni ya kai mu shopping, nan yara kowa ya soma
ciro abin da ya saya ita ma Farida ta ce,
“kin ga na manta ba mu siyo maki komai ba, in
ina tare da Deeni manta komai nake.”
Ta yi murmushi “Ai ba komai kuma duk abin da
kika siyo Deeni ya wadata ni da ninkin baninkin
Su Deeni ya yi murmushi ya matsa kusa da ita yace,
“Ta yiyu a ce Deeni ya fita shopping bai siyo
wa Bahijja komai ba my better half? na siyo maki
abin da kika fi so wanda kuma ba kya gajiya da shi kullum, kuma aka ba ki yana sa ki tsananim farin
ciki favourite dink ma na siyo a ciki, set dinsa
turare hot givincy’ body spray dinsa roll on dinsa
da turarena.
“Wow”! Ta mike da sauri ta yi masa wani irin
kyakkyawar runguma da sumba, ta ce,
“‘na gode
Deeni, really na ji dadi sosai Allah ya bar ni da
MAI SO NA.
“Ameen, ya fada yana murmushi, gaba daya farin
cikin Farida ya dawo bakin ciki, ta ji gaba daya
kokarinta ma aikin banza ta yi, tun daga safe har
yamma, ta harari Bahijja ta ce
“ba zan kyale ki ba,
zan nuna maki in har ina son abu sai na same shi,
ko kina so, ko Deeni naso, ko ba kwa so.”
Deeni ne ya katse ta
‘”zo nan Farida, ina da www.Dailynovels.com.ng
magana da ke, mu je can karamin falo, wannan abu
fa ya tunzura Misbah, duk kokarin ta danne zuciya
ta kasa, musamman da ta ga tsawon lokacin da
suka dauka suna magana ba ta san lokacin da ta
mike a fusace ba ta watsar da su turaren da gudu
tana jin zuciyarta kamar wuta, shi ke nan ya samu
masoyiyarsa, kina da labarinsu ba zai taba daina
son ta ba, ki sa ranki a inuwa, ki dau dangana, ki
bar shi da farin cikinsa, in har kina son sa kina son
farin cikinsa to, ki bar shi da Faridarsa, tsananin
zafin zuciya ya sa hawaye ko digo bai fito a idonta ba ga zafin zuciya ga tsananin fushi, tabbas Deeni
ya shiga a wannan lokaci za su yi ba dadi, dan haka
ta tashi ta sa wa kofar dakinta key ta rufe.
Rana ta farko ke nan da suka fara raba dakin
kwanciya tun aurensu.
A can kuwa Deeni ya kalli Farida cikin zafin
zuciya ya ce
“‘me kike so, me kike nufi?”
ya wurga
mata takardu da hotunan ya ce,
«kina mufin dan kin
tuna min
baya kina wani kirsa da gayu da
kwarkwasa za ki ja hankalina in yi abin da ban yi
niyya ba, ni za ki tuna wa soyayyarmu, ke awa, ke me kika sani game da so Farida? kin canja, ba haka www.Dailynovels.com.ng
na san ki ba, baki san waye Deeni ba ko?.
“Duk ikirarin da kike yi na cewa kin sanni, kin
san ina sonki, har yanzu baki sanni ba, idan ina da
niyyar auren ki ko baki min tayi kin tuna min
wannan shirmen naki ba, ni mai bugan kirji in
aureki ne.
“Wannan shirmen da yarintar da kike yi ba shi
zai sa in aure ki ba; eh naji, na yarda, na amince,
na so ki so na hakika. Sai dai kin manta abu guda,
lokaci ba abin da ba ya mantarwa, ba abin da ba ya
warkarwa, kin iya tuna min soyayyarmu amma ba
ki iya tuna min cin amanar soyayyar ba, baki iya
tuna min halin da na shiga ba, wannan halayyar
naki bai nuna komai ba sai son kai, a neman tuno
min bakin cikin da na manta, dan’uwana dake
kwance cikin kabari kina kokarin tuno min da abin
da ya min, wanda ya wuce na yafe, kullum ina
cikin masa addu’a
da nema masa rahama, mahaifina da na manta abin da yamin, muna zaune
lafiya ina kyautata masa ina neman albarkarsa, kina
nema ki tono min bacin ran da yasa min to, bari in fada maki abu guda,
“ya yan Yaya Shamsu,
“ya ‘yana ne confirm zan rike su, tamkar ni na haife
su, amma fa matarsa ba matata ba ce kuma ba za ta taba zamowa matata ba, a lokacin da kike zaune da
mijinki na taba zuwa gidanki na nemi kashe maki www.Dailynovels.com.ng
aure ko wargaza zaman lafiyar gidanki? dangana
na dauka na yi maku fatan alkhairi, amma ke me ya
sa kike kokarin wargaza nawa gidan da kwanciyar
hankalin gidana?
“Bahijja ba ita za ta hana ni auren ki ba, ra’ayina
ne ba zan aure ki ba, kuma bani da ra’ayin auren
mata biyu kuma babu mai canza min wannan
ra’ayi, gara ki sani, ki bar wani kewaye-kewaye
kamar yadda kika san jiya ba za ta dawo yau ba, HAR ABADA, kai kamar yadda safiyar yau
ta wuce ba za ta taba dawowa da yammacin nan ba,
to yaya kike zaton abin da ya wuce shekaru da
dama zai iya dawowa?
“Soyayyarki ta kare a tun ran da kika auri
dan’uwana, na yarda ba laifinki bane Kaddararmu ce kuma duka mun karbe ta, ta
wuce, a da lokacin da za ki auri dan’uwana ina isa da dagiyar da soyayyar da kike min din take da
ba ki yi protecting ba na yadda, anfi karfinki, kinyi aure kuma kin yi saurin mance ni, kin rungumi
mijinki da ‘ya’yanki, haka nan na yi fama na hakuri
amma ban taba tunanin wargaza auren ki ba.
Dan haka, yanzu kar ki yi wannan kuskuren,
soyayyarki ta wuce shekarun da suka wuce ki cire
wa kanki wannan abin da kika sa wa kanki na cewa
Deeni ya haukace a kan sona, dan haka yanzu zai
dawo da gudu ya sake hankacewa, rayuwata ta kare
a kan mahaukacin Farida ko? Wannan shi ne
tunaninki to, in shine, ki canza saboda Deeni
SHAUKINSA ya sauya na samu sayin shauki na
HAR ABADA.
“Karatu, in ma da niyyar ki shigo gidan nan ne,
to, ki sani ko kin samu ba a gidan nan za ki zauna www.Dailynovels.com.ng
ba, gidan Baba za ki zauna, tunda na lura ke ba
zaman arziki ki ke so a yi da ke ba, kin zama mai son kanki.
” Ya zura mata jajayen idanunsa tare da
watsa
mata takardunta,
“kar ki sake wannan
kuskuren, ni ba irin mazan da kika sani ba ne, ni Deeni daban nake.
Nan ya wuce ya bar ta a
wurin, ta bi shi,
maganganusa sun mata ciwo, ta ce
“to tunda abin
ya zama yar kiri-kiri ya fito na fito to, ina mai
tabbatar maka sai na aure ka, sai na shigo gidanka
kuma sai na tabbatar maka abin da ya shude
shekarun baya yana dawowa, sai na tabbatar maka
shauki baya canzawa, zan shigo gidan ko ta dadi ko
ta rashinsa ko ta tsiya ko ta arziki, nan gidan za mu
zauna da ni da kai da ‘ya’yana matsayin family.
Ya na jin ta amma bai tsaya ba balle ya tamka
mata. Sam, da ba haka Farida take ba, halayyar da
yake son ta dan su gaba daya sun canza, baya ga wanna bai taba ba wa wata mace dama ta shiga
HMMM LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe www.Dailynovels.com.ng