MISBAH BOOK 3 CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
karkace daga kan daidai ba ko abin da ya kamala,
ko ba komai Farida kamar ‘yar’uwa take a gare ni,
‘ya’yanta da nawa duk mun zama abu daya, Shamsu
kuwa ni mai iya daukar nauyin matarsa da
‘ya’yansa ne har sai randa Allah ya karbi nawa ran.”
“Haka ne Deeni, kai kanka ka san ba abin da
nake nufi ba ke nan, sai dai kawai juya maganar
dan kauce wa manufata, kwarai kana iya rike
yayan yayanka da na kowane, ni ma nawa dan
yana can hannun wasu, ka ga kuwa ba ni da bakin
magana kan ‘ya’yan wasu, ni mai iya rike su ne
tamkar ‘ya’yan da na haila.
“Farida kuwa kana iya kula da ita duk inda take
wannan abu ne mai kyau, saboda ni ma da nawa
mijin ya mutu Allah ya kawo ka kana kula da ni, ka
aure mi ka ba ni mutunci da dangi da komai da ba
ni da shi, ka ga kuwa ba ni da bakin hana ka, kula
da Farida ko a gidansu ko a gidanka ko a matsayin
matarka ko a gadon barcinka, ka yi duk yadda kake
so, wannan halal dinka ne kuma lada za ka samu
mai dinbin yawa, ni kuwa ba zan taba maka bakin
ciki da samun lada ba ko samun abin da kake so ba,
sai dai munafurci da boye-boye ne ba na so, amma
meye na min karyar cewa ni kadai kake so?, tun
farko abin da kake so me ya sa ka yaudare ni da
cewa ni kadai kake son? me yasa ka min alkawarin
da ka san ba za ka iya cikawa ba, me ya sa ka jela
ni a yanayi da halin da nake ciki yanzu, me ya sa
ka jefa ni cikin danginka kana nuna min kabilanci
da nuna min Farida taku ce wani lokacin har a
Kalamanka kana nuna min kafi kusanci da ita
da ni matarka, ka fi ba ta muhimmanci fiye da ni.ka mai da ni sha-sha-sha?
*Ka sani ina sonka ina ganin kimarka da
darajarka kuma inabin ka ina maka biyayya ina gudun zuciya ko wani tashin hankali da zai shiga
tsakaninmu, zaman lafiva da faranta maka rai shi
na fi so da kauna fiye da komai, ina Fatan Allah ya
ba ni aljanna ta hanyar aurena, sai dai ka sani cewa
duk mutumin da ya min karya ya yaudare ni ya
karya alkawarin da ya min, ya ci amanar yardar
dake tsakanina da shi, to ba na sake gain daraja da
kima da mutuncin wanna mutumin ko waye shi.
Ni kuwa ba na iya zama da mutumin da ba na
ganin girmansa da kimarsa, dan haka idan haka ya
kasance tsakanina da kai ban san wane irin zama
zamu yi ba. Na san ni marainiya ce amma ba zan
zauna inda za a dinga nuna min kaskanci da nuna
min cewa ba ni da kowa ba, ba zan iya wannan
rayuwar ba koda ba ni da kowa ba ni da inda zan nuna bani da wata gata ba ni da uwa ko uba ko
dangi ko ‘yan’uwa da zan nufa, kana ganin kamar
ba ni da yadda zanyi ba ni da zabi sai zama da kai
don saboda ba ni da gata? ina so ka sani Allah ne gatana kuma
“‘Muddin ina raye, ba zan rasa wurin shiga ba,
kar ka dauka zan zauna da kai kuna nuna min
kaskanci, ko da ba ni da kowa ina da Allah ina da
sell respect ina da sell confidence, wannan ba mai
raba ni da su, sai Allah da ya ba ni su, kai da Farida
ba ku isa ku cutar dani ta wannan hanyar ba.
“Idan har jarrabawa Allah ya min da kai a
rayuwa insha Allah zan yi kokarin cin wannan
jarrabawar, ka sa ido ka gani, ka yi duk abin da ka
ke so da duk abin da ka ga dama, ba zan hana ka
ba, ba za mu sake jayayya ko musu da kai ba
“‘Ba zan sake cewa komai ba, ba zan sake shiga
maganarka ko rayuwarka ba sai dai zan dauki iya
abin da zuciyata da raina za su iya ne ba zan iya
daukar abin da ya fi karfina ba, ba zan bari har azo
ranar da za ka budi baki ka min gori ba, saboda halayyarka da
aikinka sun fara nuna
min hankalinka da tunaninka da zuciyarka sun yi wani
wurin kafin bakinka ya furta haka, ka san weakness
dima, ka san yadda za ka karya ni, ba zan bari haka
ya faru da ni ba, na ga rayuwa na ga halayyar
mutane da jama’ a da yawa kuma na karance dasu ba
abin da zai sake ba ni tsoro ko firgita ni, ko ya ban mamaki, weakness daya nake da shi, sai dai shi ma
ba zan bari ya ruguza ni ba, ka sani ba zan taba bari
ka ruguza ni ba, Deeni duk abin da zai ruguza ni
Zan yi saurin karkade shi da yakice shi daga gare ni
Tana gama fadi, bata saurare shi ba tayi
tafiyarla ciki, wani irin bakin ciki da bacin rai ya ji a zuciyaRsa ni faruda ke fadama wadannan maganganun tayi masa mummunar fahimta, macen
da yake ganin tafishi sanin kansa da Kansa, gaba
daya ya ji gidan ya masa duhu, ba shi da sha’awar
zama a gidan ma, Bahijja ta karya masa zuciya da
maganganunta, da ma tunaninta a kaina ke nan,
haka ta dauke ni, haka take kallo na? Ya ji ba shi
da sauran abin da zai iya fada mata dan haka ya sa
Kai ya fice a gidan.
Haka nan bangaren Bahijja ta ji zuciyarta ta
tsaurare ba ta da sha’awar sake gain Deeni ko
zama da shi saboda ta gani a zahiri, manufarsa da
abin da yake son yi ta kuma gane da ma can Deeni
karya ya yi mata da yaudara, da ma damace bai
samu ba na auren Farida yanzu kuwa ya samu
damar shine zai zo mata da wasu maganganu to
gara tayi wa kanta gata ta yakice shi a ranta wanda
a yanzu ma take jin ya fita aranta saboda cin amana da ya mata.
Dan haka, tafiyar da ya yi ma bai dame ta ba
kuma hakan ya kara tabbatar mata da abin da take fadi.
Deeni gidan gonarsa ya tare, ba ya zuwa ko’ina,
Yama kashe wayarsa saboda ba ya son sauran
damuwa da bacin rai, maganganun Bahijja ke yawo
a kansa, suna kona masa zuciya, wai Bahijjarsa da
ya sani ce kuwa ta yi masa irin wannan mummunar
fahimta? Ta rufe ido tana gaya masa maganganu da
duk suka z0 bakinta, shin ko harka da marasa lafiya
masu damuwa da matsalar kwakwalwa da take yi
ne ya sa itama ta soma shafar hankalin ta da
tunaninta?
Haka abin nan ya dinga kona masa zuci a
amma duk bacin ransa ya kasa cire ta a zuciyarsa,
tunanin wani hali take ciki musamman da wannan
tunanin a ranta da zuciyarta, tabbas ya san tana
cikin kunci da bacia rai,
“Bahijja, ban ci amanarki
ba, burina in faranta maki, in sanya ki farin ciki, in
gan ki cikin walwala, me ya sa kika bari tunaninki
ya jawo mana rudani cikin rayuwa? Ina son ki, ina
kaunar ki, ina ganin kimarki da darajarki fiye da
komai, ban maki karya ba, ban ci amanarki ba,
haka ban karya alkawari ba, zamanki cikin kunci
da tashin hankali da rashin fahimta yana daga min
hankali. Bahijja, ba wanda ya isa ya wulakanta ki
ko ya maki gori, ke ba abar wulakantawa bace, ke
abar so da kauna ce, halinki da zuciyarki mai kyaune.
“Me ya sa tunaninki da hangenki zai wargaza
mana rayuwar farin cikinmu? A halin yanzu yana
da kyau mu ba wa juna lokaci saboda muna da
bukatar haka, amma insha Allah zan fahimtar da ke
ba haka ba ne
matsayinki da darajarki a zuciyata da
rayuwata ba karami ba ne, bayan iyayena Bahijja
sai ke, ba ni da na biyunki. Haka ya kasance cikin
kewarta da tunanin halin da take ciki ga bacin ran sabani da rashin Fahimta
daYa. singa kwakwalwarta.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE