NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 13 KARSHE END BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 13 KARSHE END BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Salmanu ya kawar da kai wani shegen haushi na naushinsa a Kirji. Ai a duniyar nan duk wanda yayi maka sihiri ya juyar maka da lissafi ya gama da kai, wai sammatacce irin Adamu ne ke fatan matarda ta sammace shi. bata zuwa wajen bokaye, wannan kayan takaici da me yayi kama? Ga abin duka Adamu, amma babu dama. Tanimu dayake shi ma wani gabon ne kawai sai ya karkace kai yace,
“Yo Adamu wannan kundubar matar taka in ba ta je wajen boka ba, ta ya za’a yi ka zauna da aurenta? Ni wallahi ko da marsandi aka hada min ba zan zauna da wannan raka ni kashin ba, aiba ta da wani amfani in ba kashin tsakar dare ne ya rarako mutum yana tsoro kuma ya rasa dan rakiya…” Da dai Salmanu ya lura da cewa duk hararar da yake wa Tanimu bai kula ba kuma ba shi da niyyar diga aya nan kusa a kundin cin fuskar da ya budewa Adamu, kawai sai ya dauki wani kofin ruwa ya jefe shi da shi, cikin sa’a kuwa ya same shi a baki har ya dan yi masa jini.
“Ka ji ka nan wani banza, kai ko raka ni tusa kana da ita ne?”.

ZAMU TASHI 

Tanimu ya shiga goge jinin, amma bakinsa bai mutu ba, .Na rantse gara na mutu gwauro da dai na shigo cikin gida wannan kunduBar ta yaKe min . baki a matsayin matata…” Salmanu ya Kara Kuluwa da ya kula duk Adamu ya muzanta, sai kallon Tanimu kawai yake kamar zai barke da kuka. – Ya kuma sunkutar wani kofin. zai jefi – – Tanimu da shi amma ya mike yana dariya. Cikin tsananin fishi Salmanu yace, Www.bankinhausanovels.com.ng
Allah in baka yi wasa ba Tanimu kai ne mahaukaci na farko da zamu fara tsarewa a gidan nan, wannan wanne irin rashin hankali kake fama da shi, yaya mutum ya zo da Katon abinda za’a – taya shi jimami amma _ kana Kara masa wata damuwar da wani nau’in na haukanka?”. Tanimu bai damu ba, yayi gaba yana cewa,“Sake fada, dama

magabata sun ce Karshen duniya duk wasu masu gaskiya za’a dinga . daukarsu mahaukata…”, Yana ta dariyarsa ya fice. A sanyaye Salmanu ya. juyo ya ‘dubi – Adamu, , : “Kar ka damu Adamu, ka san. tsiyar tanimu, wata ran ma sai ya zage ka ya zaci yabonka yayi..Adamu na Www.bankinhausanovels.com.ng murmushin yaKe, maimakon ya zarce da maganar sai ya canja wata, Yaya kuka yi da Honorable?” salmanu bai so haka ba, amma haka shi ma ya basar, . Ya zube mana kudi dubu dari uku ka.gan su. Ya tura masa ledar kudin yana zarcewa da yi masa wani bayanin, ‘ Na shigar da shi cewa, in ana son aikin ya
ci da sauri sai ya biya wa almajiranmu kudi zuwa saudiyya su je ka’aba su yo addu’a, ya ci alwashin biyan kudin kujerar mutum daya…”. Duk da har yanzu Adamu cikin damuwa da rashin Kwarin jiki yake, bai kasa zabura ya tashi zaune ba,.
“Kai da gaske Salmanu? Dama wannan sana’ar ta samun irin wannan maKudan kudin ce muke zaune tuntuni”Salmanu yayi dariya, .“Ka gani dai, dan kaza-kazan mutum an ce yana da tarin maKota talakawa amma an ce sai azumi kwano bibiyun shinkafa ke hada su da shi, –
wai yan jagaliyar jam’iyar ma basa jin dadinsa, muguwar rowa ce da shi, shiyasa ma aka ce wai baya yawo da kowa saboda rowarsa ba ta sanyawa ya -debi mutane, daga shi sai direbansa…”.Da yanayin nuna jimami Adamu ya ce,“In haka ne da ba mu je wajen wancan. tsinannen bokan samo masa sihirin da zai saa — ture wancan da ya ciabashiba…Salmanu na dariya ya ce, .“Ayya Ai duk shegun ne na uwar_. tsintau, shi wancan in ka ji halinsa ma ai sai ka kusa guduwa, gara ma wannan din ko banza zaka tatsi rabonka a jikinsa…Yanzu Adamu ya fara sakin fuskarsa duk _ da can cikin ransa akwai tarin damuwa,_Yanzu me ye abin yi? Wa zai tafi saudiyya wa zai zauna?”.Salmnu ya dan ja fasali kafin ya amsa, “Ka bari zamu tuna wannan zuwa gobe, dole ma ka ga mu nemo hujjojin da zamu kare tafiyar tamu tun da ka ga dai a gidajenku kai da Tanimu babu wanda ya san cewa ku malaman tsubbu ne, gara ma ni bani da gatan da zai tuhume ni inda na samo kudi na tafi Saudiyya” Ya Kare maganarsa da yin dariya duk da ya gan shi ba abinda dariyar ya fada ba, amma hausawa sun ce fadan da ya fi Karfinka kawai ka mayar da shi wasa. Adamu kuma dariyar yayi ya kawar da kai, zuciyarsa na raya masa kamar ma Salmanu yafi shi gata, tunda yana cin gashin kansa Www.bankinhausanovels.com.ng yanzu, amma shi duk wata asara akansa ta Kare tunda ya auri naman daji ya ajiye a gida a matsayin mata kowa na gani, Sannan ma in aka bibiya mai bin
kwartayen malamai irinsu Basaraken boka. ”’ .
Salmanu yayi KoaKarin bin sa da kallo a tausaye, sannan ya kada kai, “Dole dai Adamu sai ka damu da maganar Ti
Dasauri Adamu ya girgiza kai, Wallahi ba haka ba ne, in na ce maka ba na jin ciwon ganin Sa’a a gidan ‘bokan nan na yi maka Karya, Kari a kai shi ne ban san ta hanyar da zan bi na sanar da Alhaji ko kuma ita na hana ta zuwa wajen bokan ba..
Salmanu ya ji wani mugun takaici ya Kara naushinsa, shi dai yana takaicin Adamu yayi ta hango laifuffukan mutane amma ba zai taba hango na Salma ba, ya so Adamu ya cigaba da zargin Salma ma na zuwa wajen bokan in ya so ya yi masa zugar da zai sa shi ya Kuga mata saki ta koma gidan ubanta, to amma Adamu ya Ki dauko wannan turbar, sai janye-janyen laifukan mutane yake alhalin ya Kunshe tsinanniya a dakinsa. Kamar Tanimu ya san abinda Salmanu yake rayawa, Www.bankinhausanovels.com.ng sai gashi kamar an jefo shi. “Ka san Allah Adamu, shawarar da zan baka ita ce ka je ka sallami Salma ta tafi gidan Ubanta, wallahi in na rantse maka ba zan yi kaffara ba ita ma tana zuwa wajen la’anannen mutumin nan”Abinda ke ran Salmanu kenan kai tsaye, amma tunda shi yana cuda lamarinsa da siyasa ba shi da dama ta irin gabuntar Tanimu, dole kenan ya tsawatar don kar a yi abinda kai tsaye — duk su duk din su zasu a jingina musu Tir! Cikin fusatar karya ya miKké yana nuna wa Tanimu Kofa,“Ka ga zo ka fice ka bar gidan nan sai gobe — ka dawo, yau dai mun yafe maka. Tanimu abu ne mai sauki ka dinga duban tsabar idon miji kana sanya shi sakin matarsa? Wannan in an bar ka zaka iya kisan kai”.Tanimu ya kuwa juya ya fita yana cewa, “Ai kuma magana ta wuce tun da ka ce na tafi gida, dama ina da sabgogin yi. Allah huci . zuciyar kowa”
Ya sa kai ya fice, nan ya bar wajen shiru duk su biyun sun ma rasa abinda zasu ce.

************

Dama kafin Sa’a ta wuce gidanta sai da ta biya ta kai wa Salma nata aiken, dab da magariba sannan a gaggauce ta nufi gidanta don Alhaji ya sha fada ba ya son unguwar dare… ,-. _-.Ta bar Salma cikin fargaba da doki ta shiryawa tarar MAigida Adamu tare da kila wa kalancin yadda wannan waki’ar tasu zata wuce. ” Ta jike goro da fitsari ta rasa inda zata tura shi, KarKashin gadon da Adamu yayi wa yaji ko kuma Karkashin kujerar da ya koma da kwana yanzu? In kujerar ce kenan nan zata biyo shi su kwanta? Ta shiga rudu! Amma daga Karshe dole ta zabi tura shi Karkashin gadon musamman da ta ‘ tuno da gatsalin da yayi mata na cewa in tana da bukata, ai zai iya sam mata mintuna. Yau daya dai zata runtse ido ta ci wannan alfarma ta mintuna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kamar jiya Salmanu ya riKe shi, bai shigo gida sai daya saura, yau ma bai waiwayi abincinta ba yana zuwa ya _ haye kujera ko takalmi bai cire ba ya fara gurzar baccin Karya da zummar in ta fito ta tarar shi yana bacci. Ko minti biyar bai yi da kwanciyar ba sai ga ta a falon, ‘ta yi masa magana da muryarta wadda tsoro da fargaba suka cika, amma suke Boyewa. “Wai Adamu ina kake zuwa yanzu ba ka shigowa sai dare ya raba?” Dayana da Karfin hali yayi niyyar ya bude’ ido ya’ce mata, “Sai maimaita magana daya kike” Tunda ba hali sai ya shanye kalubalen ya ci gaba da sauraronta cikin baccin karyarsa. – . _ Salma ta yi kamar ta taba kafarsa da ~ zummar tashinsa da ta tuna mahangurbar da ta sha jiya sai ta ja da baya da sauri ta cigaba da mitar kiransa, har sai da wata irin zuciya ta taso masa ya tashi zaune zumbur yayi tsaye yana kallonta a fusace. Ta tsorata, amma ta maze. . _ “Wannan fusatar fa Yaya Adamu?”Yayi fuska, “Ke baki iya tashin mutane bacci ba” Ta yi ajiyar zuciya ta tafi ta nemi kujerar da ke fuskantarsa ta zauna tana dan murmushin da bai fice na yake ba. ,“Ai ni komai ma ban iya ba Yaya Adamu, wadda ta iya ai ta kusa zuwa ko?” Yayi mugun bata rai, ya kuma jima zuciyarsa na lalube kafin ta lalubo abin cewa, –
Ni ba na son cin naman mutane, bai kamata don mutum ba ya kusa a yi da shi ba”. Takaici ya sake cika Salma ta ji shi kansa Adamu ta fara tsanarsa, ta tsaya kawai tana yi _ masa kallo mai kama da harara.Shi kuma yayi fuska yake neman komawa ya kwanta, ta yi saurin tare shi muryarta a cushe, “Na ga Yaya Adamu yabonta na yi ba zagintanayiba’. Dakyar ya daure ya saki nishi, . – “Hmn”, Ta ji. tana neman mutuwa saboda takaici, muryarta da Www.bankinhausanovels.com.ng numfashinta a sarke ta yi ta maza tace,  “Ka zo mu je daki mu kwanta”.Tana rufe baki ya amsa mata, “Ai nan ne ya fi iska”
Ta jima cikin shiru nauyi da kunya na _ dawainiya da ita, in ta biye musu kuma ta cutu, ~ maganinta ya sha ruwa tana ji tana gani a zankado mata wata aba kishiya, Tir! Sai da Adamu ya juya mata baya da zummar fara bacci sannan ta-kuma yafito magana,
“Wai ka daina cin abincin gidan nan ne?”yA amsa mata, “Yau dai na koshi”.- – ‘ “Amma wanka fa? Ka ga fa da takalmi a _ kafarka ma ka kwanta Yaya Adamu”. Salin alin bai tanka ba ya sabule takalmi ya juya zai cigaba da baccinsa. . Salma ta sha kokawa da nauyi da kunya kafin ta iya fadar abinda ke ranta, –
To ka zo mu je a sam min wasu mintuna kafin lokacin sallarka yayi’. Ya jima daga shi har zuciyarsa ba su san. yadda suke jin kansu ba, shi ya shata mata raddin nan cikin gadara, gashi nan zai cutar da shi a — lokacin da kwanyarsa babu abinda take buKata sai nutsuwa da rarrashi, so yake kawai ya ji wani yaKini na cewa Salma ba ta zuwa wajen dan akuyan boka, so yake ya rufe ido ya bude ya tarar — ganin da yayi wa Sa’a mafarki ne ba gaskiya ba, ya san duk wannan dalilin damuwar ba na matsayin Sa’a a matar wansa ne kawai ba, A’a na matsayinta uwar goyon Salma wadda a duk dangi aka shaida ShaKuwarsu, in haka ne duk inda Sa’a ta sanya Kafa lallai Salma na sa wa.
Ba ta dalilin mugun son yake jin wannan gobarar Www.bankinhausanovels.com.ng kishin na Kona masa zuciya ba, shi ya ~ yarda da hakan, kawai ta dalilin kasancewarta iyalinsa ko ya Ki ko yaso ne. -Ya daga kai kai yana kallonta cikin cije lebe, tsawon wani lokaci sannan a sanyaye yace . mata,

“Ina zuwa, bari na yi wanka”.

Wasu hawayen tausayin kai suka ciko wa. ‘Salma a ido, wannan wacce irin wahala ce? Allah ya yanke mata ya sanya wa Adamu sonta don Allah ba son boka mai kama da na inji ba; sai ka. ce wani na’ura kullum sai ana sabunta masa caji. in ba haka ba ya mace mudis. .  Cikin rawar murya ta kada kai tana yi masa godiya ta wuce cikin daki ta fara shiri.
Ya jima a kwance sannan cikin sanyin jiki ya tashi ya nufi bayan gida yayin da zuciyarsa ke ta yi masa dauke-dauken hotunan Husna, shi yasan da ita yake aure ba irin wannan rayuwar zai “yi ba, ji yake ma shi wani kwararren maye ne daga mayun maza, amma na Husna kadai. .

************

Zuciyar Adamu ba ta taba cukurkudewa kan lamarin Salma irin ranar yau ba. Ya baje basirarsa wajen tunanin sama mata matsayi na -tsantsar Ki ko dolenci, amma ya kasa nasarar samar da amsar daya.  Yana nan kwance har Salma ta shigo bayan — ta dawo wanka nata ran tas! Tamkar ta fara ihu tun yanzu ta fada wa duniya cewa Adamu nata ne ita
kadai babu wata mace da ta isa ta shigo ” musu rayuwa. = Tun da ta shigo dakin ya sanya mata ido Www.bankinhausanovels.com.ng duk inda ta bi yana bin ta da kallo, tun bata lura ba har ta fara ankara, ranta ya kara yi mata tas, don haka ta canja taku da shan Kamshi tana ta . faman kai wa da kawowa tana yauki. Shi kuma – Adamu bai gajiya ba ya cigaba da bin ta da kallo amma bai nemi tankawa ba. So . Ita don kanta ta zo ta same shi tana nuna masa agogo, “Yaya Adamu lokacin Sallarka fa ya kawo kai?” Ta yi masa wannan maganar ne da zummar zungurin cikinsa da gwajin tasirin maganin Bokanta, sannan in da hali tun yanzu ta rushe auren da Adamun ke jajibowa.Amma sai ga Adamu ya fara yunkurin tashi yana A’uziyya. Ranta bai so hakan ba ta yi KoKarin ta shanye kuma ta kasa,Amma dai. yakamata ka dan kwanta ko bacci ko na mintuna sha biyar ne ko don tanadin lafiya…Ya tare ta cikin tausasawa,
“Dan adam a wannan rayuwar ba ya buKatar wata lafiya bayan wadda yake nema wajen Allah, sannan baya neman wata buKata sai a wajensa, duk abinda kike so ki je ki tsaya a kofarsa zai karbe ki zai ba ki”.
Salma ta yi saroro tsaye tana kallonsa da jin maganar tasa kamar gugar zana. Yana dab da ficewa daga dakin sai ga shi ya jefo mata wadda ta fi wannan Karfi, tana tsaye ta ji ta kamar a kwance saboda rudewa, don sai da ya juyo ya_ dube ta da kyau sannan ya ce mata,
“Akwai wata makusanciyarki da aka gano min ita a wani waje da bai kamata ba, lallai ni dan adawa ne da irin wannan lamarin, duk wanda bai san fishina ba zai iya ganinsa a nan bangaren, don haka.nake ba ki shawarar ki bi hanyar da na bi, ita zata bulle da ke, duk duniya ba shegen daya isa siyo maka soyayyar wani kuma ba shegen da ya isa hana abinda ubangiji ya hukunta, in ba ki sani ba ma ki sani, yawancin malamai da bokayen daga ‘yan iska sai yan damfara, sai kuma wadanda suke nesanta mutum da rahmar Ubangiji fau-fau!”. – Bai saurari cewarta ba ya kada kai ya fice ya bar mata dakin. Www.bankinhausanovels.com.ng
-Sai ya barta.da jirin da ta ji yana neman kwada ta da Kasa, da Kyar da jan gindi ta ja kanta ta leka KarKashin gadonsu inda ta gano ludayi.: .dumanta yana nan zaune inda ta bar shi, ba shi Adamu ya gani ya janyo mata wadannan ayoyi ba da gaske Anti Sa’ar aka gano masa? Sun shiga uku sun lalace!.

Sai mu tara a littafi na hudu, – Taku bar kullum, Maimuna Beli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *