KUSKUREN MU CHAPTER 1 BY ZULAIHAU ALIYU MISAU
Www.bankinhausanovels.com.ng
Government Girls Secondry
School Zaria.+
Break Time
Bebygirls mai ziyyah takeyi a group din Housewife’s? Kwana biyu sai wani kuskus sukeyi, ko ni kadai na lura da hakan?. Kin san ziyya da shishshigi ai, Allah yasa ba wani tsiyar take kulla musu ba.
daya daga cikin yan matan ta fada tana tabe baki. Bari tazo koma me nene yau sai tayi mana bayani dayar ta fada tana faman shan rakenta, da alama yana mata dadi sosai.Asmau( Asma), Fatima (tima), Aisha(Ashty), Halima(haly). Kena yan matane kyawawa ajin farko, duka- duka basu wuce 17 years ba.
Wadda suka kira da Ziyyah ce ta iso inda suke dauke, da murmush h!!! Bebe meye labari? Fatima ce ta fara magana yana wurinki, don duk nan jiranki muke muji, meye hadinki da Housewife’s group? Ziyya mai zatayi ban da dariya. Sake baki sukai suna kallonta, inda sabo sun saba da halinta, saida tayi mai isarta sannan tace” Ta samu” karan ararrawa ne ya katse musu zancen. Aisha tace”bari kawai sai antashi kinga yanzu zaa koma break. Ok no prb. Mikewa sukai gaba daya suka nufi class. SS 3A naga an rubuta a saman class din, kujerune masu daukan mutun hudu jere, gafe da gefe da wasu a tsakiya. A hankali kowacce ta nemi wurin zamanta. Sit dinsu ne a farko by right. Ziyya ce ta mike to nikam na koma tsakiya, don wannan dan akuyan yanzu zai tsigo,niko ba ganewa nake ba. Ok kawai sukace, can desk din tsakiya by right ta nufa,
Hi frends ta fada tana musu murmushi, owoo!!!! Ziyya I’m not going Any were. Daya daga cikin yan matan ta fada. Haba maryam bama haka dake, karkisa a mana dariya mana. Ziyya ta fada da fuskar ban tausayi. Maryam tace nima fa yau karatun novel zanyi don nima ba ganewa nakeba. Zoki zauna ni bari in koma can din. Ta kusa da maryam ta fada, tashi tayi taba ziyya wurinta, ta koma wurin ziyyah. Baki da mutunci maryam. Ko kuma bamu da mutunci ba. Ta mayar mata.
Yauwa Akwai sabon littafine? Ziyya ta tambayi maryam. Maryam ta bude jakarta tafito da books sunkai biyar, kin gansu sababbin fitowa ne, ziyya ta zabi biyu 1&2. Oya ban kudina yau ba bashi. Yau maryam na lura rashin mutunci kikeji yau. Ta ciro 40 ta mika mata.
Book din biology ta dauko ta saka novel dinta a ciki, kai ka rantse da Allah biology take karantawa. Ga m bello nan zuwa, abin da naji daya daga ciki ta fada da karfi, nan danan kowa ya gyara zamansa. Wai gawar da zanyi naga Asmau ta dirka ta windo fatima ta jefa mata jakarta, ta gyara zamanta kamar ba’ayi komai ba.
Asmy na hango bayan wata bishiya, ta zauna.ta bude jakarta karamin qurani naga ta fito dashi da note book, da pen. Suratul Ankhabut ta bude, ta fara rubuta ayoyin tana bita. Kyan rubutun da yadda take karatun cikin fitarda harruffan tajwid din ya burgeni na shagala sauraron zazzakar muryarta. Kararrawar changing period ne ya kada. Maida komai tayi jaka , cikin sanda da gudun kar wani ya hangota ta nufi class dinsu.
tayi saa m. Bello ya fita, ta windo ta haura. Ashty ce tace ina kika tsaya? Tun dazu ya fita. Na tsaya hadda tane, ban rubuta ba, kin san yau m. Kabir zai karba. Wayyo Allah na, sis na manta nima banyi ba wallahi, na shiga uku. Ta fada tana daura hannu akai. Kafin next teacher ya shigo kiyi sauri ki rubuta. Muna komawa gida kiyi kokari ki haddace kafin time din islamiyyah. Asmy ta fada mata tana mika mata quranin.
A hanyar dawowar su daga sch. Yauwa ziyyah, bamu lbrn abinda ya hadaki da yan houswife group.Ashty ta fada tana tsare ziyya da ido. Ziyya mai zatayi banda dariya, har suka fara jin Haushinta.
Bebs kunsan me? Ta fada tana kokarin maida dariyarta. Kun san dai graduation dinmu ya kusa, ga ashobi da contribution na party. Ni kuma banda kudi, ban da in da zan samosu. Ina tunanin yadda zan hada kudin sai idea ta fadomin. Kun san mai? Duk sun kagu suji mai za tace. Zan fara business wanda zai kawo kudi in no time. Asmy ce tace kamar mefa?
Maganin mata…….Idawuwa suka zaro, cike da firgici akan abin da ziyya ke fada.+
Haly tace”Kekuwa wane irin rashin tunanine ya sa kika zabi wannan sana’a? Ki tuna duka shekarunki nawa? Ko aure bakiyi ba. Duk yawancin matan da ki kaga suna irin wannan business din za kiga basu da kunya”.
Nikam nama rasa abinda zan ce. Inji Ashty.
Kufa wani lokaci sai a slow, nikam nariga na gama tsara kayana, har na samu costomers.
Lamarinki sai ke ziyyah. Cewar tima. towai ma ina zaki samo magun gunan da zaki siyar din?
Yauwa yanzu naji bayani, gobe in sha Allah zanzo dashi, sannan in muku bayani dalla -dalla. Kudai pray for me Allah ya kawo kasuwa.
Ta fada tana murmushi. Sudai sun rasa bakin magana, kowa da abin da yake sakawa dangane da lamarin ziyya.
Har suka zo inda ziyya da Haly zasu dauke hanyar su. Sukai sallama da juna.
Asma, Ashty, da tima sai samra (sim _sim) da bata samu zuwa ba a ranar layukansu na jere da juna.
Ziyya da haly su suna gyallesu, suna da dan nisa tsakanin su
Tsaye yake a bakin get din gidansu, sanye da blue Jen’s da white shirt me layi_ layi blue. Kannan yasha gyara sai daukar ido yakeyi. Baki ne ba wuluk ba, kyakyawar fuskarshi me dauke da madaidaicin hanci, ba kamar biro ba, ba nakusashshe ba. Da madaidaicin baki. Idon sa madaidaita ne farare, kamar hakoransa, wanda su suke kara haska fuskarshi. Dogone mara jiki.
Bello muh’d kenan da ga Alhaji Bello( tunbin kudi).
Tun da suka karyo kwanan layisu ya zuba musu ido. Ashty ta zunguro Asma “kin ga mutuminki”
Asma taja tsaki wahalalle dai, kin san Allah ya takura min saura kiris in hadashi da yaya babba. Har suka zo suka wuce idon sa na kan asma, sai aika mata da kallo Mai cike da shauki.
Sai dai sam batama san yanayi ba don tun da suka matso kusa dashi ta sauke idon ta kasa taki dagowa har suka wuce shi.
Yarone ya biyosu yana mika ma Asma wani envelop ” gashi in ji wancan yace in baki” ganin bata da alamar amsa yasa Ashty karba.
Tima tace” beb kina gara bawan Allan nan, ki bashi dama mana.” tab kema kin san baya cikin tsarina, cewar Asma.
Saboda me? Ashty ta tambaya tana kallonta.
Ta dora da cewa” yana matukar sonki, gashi kyakyakyawa, dan gidan mutunci, kowa yasan mutuncin baban sa, gashi da ilmi, ga Addini. To me kike nema kuma?.
Kema kya fada. Cewar tima.
Duk abin da kika fada haka ne, but akwai abu daya zuwa biyu, da zai sa in ki bashi damata.
First ina da kishi duk wanda zanso sai na tabbatar ba type din da mata zasu dinga rububi bane. A takaice nafison mummuna. Second nafison talaka, Mai rufin asiri.
Baki a sake suka bita da kallo. Saboda sudai tunda suke basu taba jin mai wannan tsarinba.
Da sun dauka Abin nata wasa ne, sai yanzu suke abbatar da iya gaskiyarta take fada, ba wasa a ciki.
lallai kina da aiki. Cewar tima. Ita kam Ashty kai kawai ta girgiza. Allah ya kyauta. Tace a hankali.
Sunyi sallama da tima ta shige layinsu, suma suka shige nasu.Malamin addinin islam ne, kuma limami a babban masallacin Gyallesu.+
Haifaffen garin gyambu, ta jahar Adamawa, Neman ilmine ya kawoshi zaria, tun yana da shekara sha bakwai a duniya.
Matansa biyu, Hajiya Asmau wadda akafi sani da Hajjajo, Da yaranta hudu :
Ibrahim, Sulaiman, Abubakar sai autarta Maimunatu.
Sai Amaryarsa Hajiya Fatima (ummi) mai yara biyar : Khadija, Maryam, Hafsat, Saratu, sai ismail.
Duk yawanci sunyi aure da ya’yayen su.
Saratu da ismail ne kawai yan zu a gaban sa wanda basu yi aure ba,
Sai yaran yan ‘uwa da abokan arziki da yake rikewa.
Saratu na SS3 ISMAIL shima yanzu yake SS 1, Gidane mai cike da ilmi na addini ,yaran sun samu kyakywar tarbiyya, Kuma sheikh ya tsaya sosai ganin sun samu ilmi na zamani.
Zama lafiya da kwanciyar hankali ake a gidan saboda ko wacce mata tana da part dinta, girkima kowa nata takeyi.
Hakan ya matukar taimakawa wurin samun zaman lfy, duk da ba haka shi sheikh yaso ba, amma hakan yafi mai kwanciyar hankali, Wannan kenan.
Ibrahim da Abubakar na zaune a tudun wada zaria, Gidane mai dauke da plat guda uku.
3 bedroom plats da yalwataccen tsakar gida sai dakunan samarin gidan daga farkon shigowa gidan, Wanda mallakin ya’yan na sheikh Gyambu ne kamar yadda ake kiransa.
Ibrahim lecturer ne a collage of Education, Language dep. Shine Assistant HOD, ya nada mata daya Sadiyah (ammy) da yara biyar : M Sale( ya babba ), M Salim ( yaya), sai twice Zainab da Juwaira, sai Aisha (Ashty).
Abubakar shima lecturer ne a ABU kongo Accounting dep. Yana da mata daya, Fatima( ya fannah) yaran na kiranta Yahh da yaransu biyar: Za’id ( ba gana ) Abdullah (yayanmu), Abdurahman( abba kaka), Asmau Asma, sai Aliyu.
Zaman lafiya da kwanciyar hankali ake a gidan in ba kasani ba baka gane wannan dan wannane wan nan dan wancan ne, Suna matukar son junansu, kan iyayen su a hade yake, daga matan har mazan. Yara ne kyawawa, hankali ga ilmi na addini dana zamani.
Gidan kyawawa kenan, ko kace gidan farare. Wani abun burgewa kuma kusan duk kamarsu daya, da alama jinin sheikh nada karfi don kaf zuri ‘arsa kamarsa suke dauka, sai kadan daga ciki, da suke surkawa da na iyayensu mata.
Asmau da Aliyu ne kaf gidan kamarsu daban in ka dauke jar fatar su, Da suka dauka na sauran yan gidan. Asmau kakarta ta Hajjajo ta biyo kamar tayi kaki, Shiyasa aka samata sunanta, Wanda kowa yasan kaf gidan tafisu kyau.
In ka dauke Aliyu, wanda sheikh yace yana kama da mahaifin Hajjajo.
Sai Sulaiman major Sulaiman. Soja ne yana zaune a kaduna, da matansa biyu. Kharimatu mai yaya hudu : Abubakar, Umar, usman da Afra.
Sai amarya Hafsat mai yara biyu: Asmau( ihsan) da Aliyu.
Akwai zaman lfy a tsakanin matan sai dai dan abin da ba’a rasa ba. Maimunatu na aure a Yola garin su Hajiya Asmau (hajjajo) wadda ta kasance haifaffiyar cikin adamawa.
Bafullatanar usul, Mijin maimunatu Alhaji Habib dan kasuwane da yaransu shida: Muhammad, Ibrahim, Asmau, Amina, Maryam sai Fatima.
Suna zaune cikin rufin Asiri da kwanciyar hankali.
Yaran Hajiya Fatima (ummi) khadija da Hafsat, na aure anan zariya da yaransu, sai maryam dake aure a yola itama da yaranta, Sai Hafsat tana SS3 tare dasu Ashty, ismail shikam ya fita zakka, don sam baison karatu ko kadan, Burinshi ya zama dan kasuwa, yaci ace ya gama secondary tun tuni amma rashin maida hankali yasa har Hafsa tazo ta wuceshi.
Shiyasa basu cika shiri ba da sauran yayyen nasa maza.
Ibrahim da Abakar basu dogara a albashin su kawai ba, Suna da gidan gona a Dagaci, Wanda yake samar masu da kudin shiga, Kifi, kaji, shanu tumaki, da sauran tsuntsaye duk sunayin kiwonsu, duk da gonar ba wata babba bace,
amma Alhamdulillah suna karuwa sosai. M Sale, M salim, M Zaid, Abdullah, Duk sun gama degree din su.
Abdallah yana service. Samarin nada shagon dinki a kofar gida suna dinkin maza dana mata, Kuma Alhamdulillah suna samu sosai dan suna taimakawa iyayen, su mu samman ta fannin karatunsu, da suka daukewa iyayen.
Yan zu haka admission suke jira su jona masters.
Zainab da Juwaira sun gama secondary sch. Suna NCE 3 a F C E zaria.
zainab na karanta Biology, Juwaira na karanta Chemistry.
Sai trouble makers Aisha da Asmau dake SS3 sai Auta Aliyu Primay 2 kalen hanji.
Duk yan gidan makarantar kudi sukayi.
Staff school dake cikin ABU Kongo. Sai 2 trouble makers, bayan sun gama primary school, a staff school
Suka nuna sun fi son government girl secondary school dake Zaria, saboda yawancin kawayen su Chan zasu.
Ganin cewa makarantar tana da kyau yasa iyayen basu hana ba. Burin su dai yaran suyi karatu, kuma Alhamdulillah,. Suna yi, kuma sun samu good baground.
2 trouble akwai kokari, ga rashinji, tsokana, Duk nasu ne.
wannan kenan…….Fatima (tima), samra (sim_sim) kawayene ga Asmau da Aisha.
Sun hadu ne tun shigarsu Makaranta staff school, sannan islamiyyarsu daya. +
Layukansu na Jere Dana juna.
Halima Haly sun hadu ne a js 1
Ajinsu daya, sannan hali yazo daya.
Duk kansu yan tudun wadane, In ka dauke Haly dake gyallesu, Gidansu na kusa da gidan sheikh Gyambu.
Sun shiga SS1 suka hadu da ziyyah,
W
adda ke zama da kakarta a gyallesu, saka makon rasuwar iyayenta, ta dawo wurin kakarta.
Da tana zama da kanwar mamanta a minna, kafin dawowarta zaria.
Nan fa aka bude sabon shafi na rashinji, Ba tsoron a alamuran su, duk fadin school din ba wanda bai sansuba.
Gasu ba wani girman jiki ba, amma sai rashinji. A fannin karatu kuwa ba’a magana don ko akwai kokari musamman Asmau da Aisha. Don abun a jinin sune. Position din su a jere 1 to 6 su suke dauka, Shiyasa duk rashin jinsu malaman na alfari dasu,
Don duk wani gasa da za’ayi, su suke fidda sch. Dinsu a kunya.
In kaga suna shiririta to m Bello ne malamin biology, Sam basa son teaching dinsa a cewarsu yana magana yana sake baki. Asmau kam cewa take kallonsa na sata ciwon kai, So yana shigowa take gudu.
Ya bata punishment har ya gaji ya hakura, hakan kuma bai sa ta fasa cin course din ba, Gashi dai bata text bata da attendance.
Haka dai rayuwa take ta tafiya, gashi yanzu baifi 3month ba su fara W.A.E.C .
Asmau gajera ce, ba daf da kasa ba, Mai karamin jiki, Tana da kyakyyawar sura mai daukar hankali
A
kwai iya taku, Kyakyyawace fara, mai madai daitan ido farare, tanada dogon hanci, da dan karamin baki, mai dauke da siraran labba, masu haske, hakoranta farare jerarru masu dauke da wushirya yar siririya, Tanada dimple duka kumatunta biyu, wanda ko magana take suna lotsawa, A kwai zakin murya, kamar ana busa sarewa, Tana da yalwar gashi mai tsawo ga cika, Bashi da laushi sosai, Bakine sidik, Gashin girarta kamar an zana, kwance lub_bub, Gashin idonta yana da tsawo kamar anyi piecing din shi. Akwai son kwalliya ga kamshi, Saboda maman ta babarbariyace, kowa yasan bare Bari da son kamshi.
Tanada dogayen yatsu kafa da hannu, masu dauke da kunba masu tsayi da kyau, Wanda ko yaushe suna cikin jan lalle ko baki, Asmau kenan, Sha lelen Hajjajo.
Aisha ma ba barta a bayaba wurin kyau, Farace tana da tsayi kadan, Hancinta daidai mai kyan tsari, karamin baki da kyawawan hakora, Yalwataccen gashi mai laushi da tsawo, Gashinta yafi na asma tsawo da laushi, A kwai san kwalliya ga kamshi, kamar yar’ uwarta, Komai nasu mai kyau ne.
Duk kayan da suka sa, zaka ga kamar dansu aka yishi, Basa rabuwa, ayi fada ayi dadi, Komai tare ake musu, Aisha taba Asma 3 month.
Zainab da Juwaira kamarsu daya in ba ka sansuba baka gane su, Suna kama da Aisha Sosai, sai dai su suna da manyan ido, irin na Ammy.
Da sallama suka shigo, ba kowa a compound din.
Part din yahh suka fara isa tana zaune suna cin abinci da Aliyu,
Sukai sallama ta amsa suka shiga, “sannu da gida” suka fada a tare.
“Yauwa sannunku second twin’s din Ammy, ya sch.” ” Alhamdulillah” suka fada. Asma ce ta faki idon yahh ta zungure keyar Aliyu, da tun shigowar su ko kallon su bai yiba.
“Yahh kin gantako!! “Asma ce tai sauri cewa” toni mai na maka daga dawowata.”
Yahh ta wurga mata harara “oya zo ku wuce,” tana nuna musu kofa.
“Kalan hanji kawai.” Asmau ta fada tana ficewa da saurinta.
Part din ammy suka nufa da gudu suka shiga da ” salamu Alaikum.”
Su da sallamar bansan wanda ya riga shiga ba? Kamar wa’anda aka koro.
Kwance take kan doguwar kujera, tana kallon manara tv.
Da gudu suka rungumeta “ammynmu mun dawo” cike da so da kauna, ta fara shafa kansu. “Oyoyo yarana Sannunku!! Kunsha rana.”
“Ammy daga ke sai abi kuke sonmu a gidannan, kowa ana kaishi a daukoshi a makaranta, banda mu.”
“In an kaimu an watsar damu shikenan.”
Aisha Ta fada tana kokarin cire rigar jikinta., da ta fara jikewa da zufa.
Ammy tai dariya “muna sonku sosai, kar in sake jin kuna ba’a sonkun.”
“To ai shikenan mudai ai mun san gaskiya.” Cewar Asma.
“Kunga kubar wannan zancen maza kuje ku cire uniform. You mutumin ku nayi.”
“Allah ya barmana ammyn mu,” suka fada suna Kara rungume ta.
Dakinsu suka nufa ska cire kaya Ashty ta fara shiga wanka, ta fito, sannan Asma ta shiga.
Sun shirya tsaf cikin dogayen riguna, na atamfa, Atamfar da dinkin duk iri daya. In ka gansu kamar ka sure don kyau.
Ammy ma kasa dauke idonta tayi a kansu. “Masha Allah, barakallahu fihh.”
“Yanmatana kunyi kau.”
“Thank u ammyn mu”, suka fada a tare.
Kitchen suka wuce suka sa abinci, Ashty na rike da plate, Asma na rike da ruwa da goran zobo, Suka shigo falon suka nemi wuri suka xauna.
Suka fara cin abincinsu, cikin natsuwa, Sai da abinci yazo karshe Asma ta kwashe naman tai waje da gudu tanaci, Ashty ta bita, sukai ta zagaye a tsakar gida, sai da ta tabbatar ta cinye, sannan ta tsaya tana maida numfashi.
Ashity na zuwa ta rufeta da duka “wallahi bazan yaddaba, kullun muka zauna cin abinci ke kike cinye nama, ana ban hakuri yau bazan gyale kiba, Wallahi.”
Nan kokawa ta balle, Ammy na daga daki tana jinsu, ko uffan bata ceba.
Sai ma gyara kwanciyarta da tayi, In da sabo sun saba, Ba’a shiga fadansu, yanzu sa baka kunya.
Sai da suka daku tukunna suka tsaya suna maida numfashi, “Wai!!!!! Na gaji wallahi” In ji Asma.
Ashity ta wurga mata harara ” banza kawai, mayyah.” Asma dariya tayi, mayu dai, banza zo kiji” matsowa ashty tayi bansan mai ta radawa Ashty a kunne ba, sai dai naji sun bushe da dariya sun tafa.
“Good idea.”
Ammy na daga kwance tai dariya. “Allah ka shirya mana, yara sun girma amma har yanzu sun kasa yadda sun girma”.
Aliyu dake tsaye a barander yah, yana kallon su, Yiyi tsaki ” kajin gidanmu sun dawo” ya fada yana yatsina fuska.
Gaba dayansu sukai kansa, da gudu yayi dakin yah yana kwala mata kira…
Da gudu suka shigo dakin, Aliyu kuwa yana boye a bayan yahh yana lekensu, tare da musu gwalo.+
Tsayawa sukayi suna kallon kallo. ” ku fita daga nan manyan banza, an girma ba’a san an girma ba.” yahh ta fada cike da fushi.
“Yahh kaji fa yace mana” Inji Ashty. “
“karya yayi ba kajin bane? Out!!!!” Da gudu suka fita. Asma tace “Zaka fitone, sai na lallasa yaro.” “Ki tabamin yaro kiga abin da zan miki, marasa kunyan yara.”
Part din Ammy suka nufa, suka tattara kayan da sukaci abinci suka share wurin, sukayi mopping, Sunayi suna mitan abinda Aliyu yake musu, tare da hukuncin da zasu masa in sun kamashi. Sun dawo islamiyya suka samu su zainab sun dawo.
Anty juwaira pls ban aron wayarki in kira Afra. “Bazan bayarba yan rainin wayo, jiya da Ashty ta daukarmin waya, Kudina kaf ta karar, don haka ba wadda zan sake ba wayata”.
“
Haba Anty na bama haka dake fah.”
“Mun fara daga yau, don ba wani dadin baki da zakimin” ” Karki bayar din dadin abun bake kadai bace mai waya a gidannan ba.” “Naji din badai zan bayar ba eheeee” Zainab ma hanata tayi.
Ashty tace “gyalesu muma wayarnan dai mun kusa yinta, Mu huta da wulakanci a gidannan, Wayarma da ko WhatsApp batayi, ake mana gwadara.”
“Duk yar banzan yarinyar data sake min magana akan waya zanci gidansu, in kunji haushi yanzu in ga mutun da waya.” Zainab ta fada.
S
aboda zainab akwai zafi, ba kamar juwairaba mai sanyin hali. Ammy suka lallaba ta basu wayarta, sai da suka garar da kudin kaf suka lallaba suka ajiye mata.
“Yah ina abincin su yaya zamu kai masu shago? Abincin ta basu” saura ku barar dashi a hanya don ba hankali ne dakuba” gefe suka samu suka tsaya, cokali naga Asma ta fito dashi ta bude miyar ta tsamo naman ta fara ci, Ashty ma ta matso sunci yakai yanka uku – uku, suka gyara bakin kwanon sannan suka kai musu sauran, suna dariya.
Bayan sun gama homework suka nufi tsakar gida, inda ake zaman hira, musamman lokacin zafi. Iyayen su maza da matan da samarin gidan Duk sun hadu, Wasu a kujerun roba wasu a tabarma. Ana hira da raha cikin kwanciyar hankali, da soyayyar juna, Gwanin shaawa. Abi da Abba suna cin abincin su tare cike da nishadi.
“
Saturday family mitting, Wannan karon dukkan mu zamu je, No excuses” cewar Abba.
“Allah ya kaimu” suka amsa atare. Asma ce tazo daidai kunnen juwaira dake zaune a kan kujerar roba.
“Za’asa ranar auren wasu, su tafi ko ma huta.” Zaro ido juwaira tayi aiko, da gudu tabi asma sukayi dakin Ammy. Dole ta hakura ta kyaleta, saboda ta shige dakinsu tasa key,
“Bude min” Muryar Ashty taji ta bude, “Shegen tsoro” ni nama manta da sakonki na dazu, ta fada tana mikawa Asma lettern da m. Bello ya bata dazu, Tsaki tayi, wahalalle. Karanta muji, Ashty ta bude tana “Allah ya shirye ki.”
” salamu Alaikum
Don Allah ki taimakamin da number dinki? I want to talk to u, about something important.”
M Bello
“Bani kiga mutumin nan ya fara shigamin hanci da kudun dune, gara in dau mataki tun wuri.”1
“Mezakiyi?” ” Ina ruwanki?” ” Sorry Ashty” ta fada tana barin dakin.
Tsakar gida ta fito tana dube dube, bata ganshi ba. “Ya salim, ina yaya babba?”
“Daki” ya fada a takaice ba tare daya dago ba, yana ci gaba da daddanna computer dake gabansa.
da sauri ta nufi dakin sallama tayi, Ya amsa sai da yace ta shigo sannan ta shiga. Kujerar falon ta zauna, ” Ina wuni yaya,” ” lfy 2ndtwince, Meya faru kuma this time a rawn?”
Letters din ta mikamai saida ya gama dubawa sannan yace “ya akayi?” “Yaya Abokinka din nan dan gidan tunbin kudi ne, ya takura min, kullun in muka dawo school sai yayi ta kallon mu, kamar maye, Shine ya ke aiko min da wa annan letters din.”
Girgiza kai kawai yayi, “to yanzu ya kikeso ayi?” “Kawai ka gaya mishi ya fita hanyata, in ba hakaba zan gurza mai rashin mutunci.”
“Ke meyasa bazaki gaya masa ba da kanki? Ni dan aiken kine?” “Aa” ta fada tana zaro ido, Gani nayi abokinka ne, shiyasa, kuma ina ganin girmanshi, kaga bai dace na mishi rashin mutunciba ko?” Ta fada tana shakwabe fuska. “Meye aibun M Bello? Ya hada duk wani qualities da ake bukata wurin mijin da za’a aura, ki bashi dama mana!!!” “Tabdijam nikam ban son shi, inyi yaya da dunbin yan matansa.?” Sai yanzu yaya babba ya gane inda matsalar take, murmushi yayi ” ki rage kishi, nasan ba komai ke damunki ba sai kishin banza.” “Ki je kiyi tunani akai, duk abinda kika yanke kizo ki gayamin” “ni dai kawai yafita hanyata bana son sa.” “Kin tabbata?” Kada kai tayi “eh!!!” ” Shi kenan jeki, zanyi magana dashi.” ” Na gode yayanmu, Allah barmana kai.” Murmushi kawai yayi yana girgiza kai, Har taje bakin kofa ta juyo, Afra na gaisheka, Ta kwasa da gudu tana dariya.
Shima murmusha Yayi “troublemakers” Sai da sukayi shirin bacci sannan ta bawa Ashty labarin abin da ya faru. “Amma ke kin tabbata bakya sonsa?” “Wai so nawa zan fada miki ne? Kina abu kamar baki sanni ba.”
“Yau banga sweetheart dina ba?” Asma ta kalleta tare da hararar ta, kina ban haushi wallahi Ashty kina ta haukarki shi baima san kinayi ba, koda ya sani wannan miskilin ba lallai bane ya kulaki, kema kin san haka.” Ashty ta kamo hannunta “pls ki tayani Addua wallahi I’m so much in love with him, Kuma inaji a jikina shima zai soni, nidai addua kawai nake nema ki tayani dashi.”
“To ai shi kenan tunda bakyajin shawara kin fisan kikai kanki in da xaa wulakan taki.” “Asma baki san so bane shiyasa kike fadin haka, duk lokacin da kika hadu da Mr right, sannan zaki gane abinda nakeji.”
“Allah ya tabbatar da alkhairi. Amma ina tausayinki wallahi, don yaya zaid zakiyi aiki.”
Shigowar juwaira ne ya katse musu zancen da suke.
” wanne plane kuma ake hadawa, don nasan duk a ka jiku shiru to trouble ke biyowa baya”.