NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 2 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 2 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Jamila ta zunguro ta,Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Wai Husna me ye matsalarki ne, baki ga alamun biyan buKata ba?”, .

. . Husna ta dage ta gayyato wani mashahurin —

yake, alamun hankalinta ba ya tare da su,

“Wallahi na ga alamu”.

“Ai malamin nan yayi a rayuwa, abinda ya burge ni kuma yau babu cajin kirki’”. In ji Jamila. :

– Amina ta ce, . * “Nawa ya caje ki? Ni dubu goma ya karba”, Jamila ta amsa, . “Nima hakan ya karba, Husna fa?” . ‘ A sanyaye Husna ta dago ta kalle,su, : “Ni bai. karbi komai ba, ya ce na fara zuwa ” na gwada maganin da ya ba ni” Suka cika da mamaki duk su biyun,Jamila tace, “Na san aikin bokan nankamar yankan wuka, amma sam.ba shi da sauki akan kudi, ya aka yi ke ya daga miki Kafa?” Husna nadariyatace,;,Kila ya hango babu dubu goma a jaka ta, _ dubu biyu natafidaita’. “Ni kuma ba haka na zata ba”. Keto Inji Amina, “Me kika zata?”. Jamila ta tambaya. :

– “Ko gani yayi buKatarta ba-zata biya ba? .

– Inda ya birge. ni abinda ba-zai yiwu ba, ba ya* yaudarar mutum, ni dai, Kiri-Kiri ya fada min cewa, in dai an hana Kamalu kallon kwallo to. – lallai ni kuma zai rakita min kishiya,..Jamila .ta tare ta cikin tsananta dariya,

ZAMU TASHI 

Husna kuwa murmushin yaKe kawai aka bar ta da shi,

Amina na dariya ta amsa, .

“To me yayi zafi ido zai ci wuta? Nace a – bar shi da kallon Kwallonsa har a busa Kaho, kishiya kuma a hana ta ganin Kofar gidansa, faKkat”.

Husna kanta sai da ta dara har ma ta ji Karfin gwiwar tofa tata,

“Ban taba zaton gasKata wani boka ba sai a yau, daga shiga ta ya ambato min sunan Adamu, sannan ya ci min alwashin Adamu ba zai dara – daga wata biyun da ya dibar wa kansa ba zai kawo kansa neman aurena…” :

Duk suka tattara mata hankalinsu saboda sha’awar da zancen ya basu, suka dinga jin imani dari bisa dari tun daga Kasan zuciyarsu.

Husna ta cigaba da cewa, .

“Ni lalle kadai ya ba ni ya ce na Kunsa shi gobe, ya tabbatar min in Adamu bai zo a goben ba to tabbas zai zo jibi’”. .

. Jamila ta sauke ajiyar zuciya ta ce, Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Kawai ki ce mu jira ganin abin mamaki. A lallai in na ga gaggawar aikin ki, tabbas nima zan koma da wata bukatar da ta fi mota”.

. Cikin zolaya Amina ta ce, “Sai ki nemi jirgin sama kawai’. Dukkansu suna dariya.

**********
Ba kamar yadda Admu ya saba ba, da zarar ya shiga gida yayi arba da Salma sai ya manta komai, a yau abin mamaki sai ya ji zuciyarsa ta kasa mantawa da Husna duk da dubun tarairayar da Salma ke bin sa da shi. Ta yi wanka ta feshe gida da Kamshi,

. sannan ga kyakkyawan girki an yi hidimar yi masa, amma: tsakaninsa da Allah yaKe kawai yake mata, daga can Kolin kansa ne ake hana shi

” cusa mata ashariya amma ba don haka ba yauko ba Barbushe ne ya haife shi ba, ya so nuna mata ya san tarihinsa. To babu yadda ya iya haka kawai ya dinga bin ta da ido.
Ta dawo daga kwashe kayan da ya ci abinci tana ta faman wasu-wasin abinda ya taba” mata ran masoyi yau, alhalin ita ta tanado musu

_dukkan farin ciki yau din nan. ; ‘ Ta zauna hannun kujerar da yake zaune tana kwarkwasa,
“Yaya Adamu wai kuwa yau lafiyarka lau?”

. . Ya daga = gajiyayyun idanuwansa da kallonta, sai da ya jima bai tanka ba sannan ya – kawar da kai ya tanka mata, “Me kika gani?”. . Ta Kara tausasa murya, “Duk jikinka a sanyaye, ba haka ka saba ba Yaya Adamu”.“Tun da kika san ni?”. . . Ya ji tambayar ta bijiro ta kuma subuto ba “tare da ya shirya mata ba. – Salma ta dan yi wuki-wuKki. . . Yayi fuska ya sake cewa, . Ki fadi tsakaninki da Allah in tun da kika _ San ni ba haka na saba ba”. ; . Sai ta sake zuba masa ido kawai cikin _ faduwar gaba. _- Bai jira cewarta ba ya sake rausaya kai , muryarsa a raunane yace, .“Da can ni kadai nake rayuwata ina cin ‘ gashin kaina, yanzu kuwa akwai wani shaidani ‘ da ya hau kan zuciyata yake sarrafawa, in kin ga canji wannan ne canjin, tsakani da Allah ba na jin dadin rayuwata yanzu, don komai zaba min ake bana samun wanda na zaba”, Yanzu Salma ta gama tsurewa, sai Kikkifta Www.bankinhausanovels.com.ng 

ido kawai take tana kallonsa, raunin da ta hango a fuskarsa ne ya bata damar Karfin halin yin magana, ta dora yatsa a Kirjinta tana kallonsa, “Har ni zaba maka aka yi ba kai ka zaba ~ ba?”

_ Ya juyo ya kafa mata ido, ga amsar gaskiya na yawo a Kirjinsa da harshensa amma an dauré masa harshen ba zai iya furtawa ba, Karshe kawai

‘ sai ya bige da murmushi ya kada kai ya tashi ma ya shige dakin kwana. Abin haushi sai ga shita bishi. Kafin ta yi magana ya riga ta, .

“Kai na ke ciwo Salma don Allah ki bar’ni na huta”. so ;

Bakinta na rawa ta ce,Me na yi maka na damu Yaya Adamu?”

Yayi yaKe kawai ya kasa tanka mata.

“Amma dai ai ba tarbiyya ba ce kana cikin wani hali a ce na yi nesa da kai; ko yaya ne a dole zan debe maka kewa”.
_Da kyar ya iya mazantakar amsa mata da cewa, – SO , Tarbiyya ce: idan’ abinda nake buKata. kenan, ina son kadaici tsakani da Allah in kin dame ni kin shiga hakKina”. ., –

Jikin Salma a sanyaye ta tashi ta fice falo. Damuwa ta cika ranta fal! Sai ga hawaye ya shiga wanke mata fuska, ta san lallai akwai casgaro a aikin malaminta, kodayake dama Anti Sa’a ta sha sanar da ita dole sai ana yi ana sabuntawa yana iya wargajewa, bayan bikin sau uku tana yi mata tayin ta zo su je wajen bokansu tana gocewa, a nata azancin dan ta sami damar auren Adamu ta bi Malamai, in kuwa ta cigaba

da bin su bayan ta sami biyan buKata, to Karshen batawa kai loakci kenan. .

. Dare ya raba ko wannensu na muhallin da ya zaba yana tsotsar tsamiya. Wajen Karfe biyu saura kwata Salmanu ya kira shi a waya, cikin
fargaba da zaton tashin hankali ya daga wayar, *“Salmanu lafiya?”’ Cikin muryar tausasawa ya amsa masa, _ “Lafiya Kalau Adamu, tuni zan maka”. A dokance ya ce, “Tunin me?”. SO -Salmanu ya dan ja fasali kafin ya tanka, “Salma na kusa?”. Adamu ya rage murya, . “Tana falo”. Salmanu yayi ajiyar zuciya ya ce, . –

” “Wai kuwa kana sallar dare kamar yadda na san ka a baya?”’. ,A raunane Adamu ya amsa, “Adamu fa aka canja Salmanu, ba na samun lokacin komai ni wallahi”. . Salmanu ya shanye takaici, . “Ka yarda ka yi rayuwa Karkashin zabin wasu kenan? Abin mamaki kai kake shan sanar da ni duk wanda aka yi wa gatan addu’a an ba shi – alkhairin duniya da lahira, ba na mantawa ka sha sanar da ni duk abinda mutum yake nema in ya. nema a wajen Allah zai samu, wato yanzu kai ka yarda ka zama asararre?”. “ Adamu zai yi magana Salmanu ya tare shi, “Kar mu ja ta da nisa, ni na kira ka ne in tashe ka ka yi sallarka kamar yadda ka saba, sannan duk abinda kake nema ka roki Allah, kuma duk abinda kake jin yana miuntsinin . zuciyarka ba ka jin dadinsa ka nemi tsarin Allah da shi”.. Bai jira cewar Adamu ba ya kashe wayar. Salma ta ji lokacin da wayar Adamu ta yi Kara, tsarguwa ta tashe ta a guje kasa kunne a bayan labile, amma har suka yi maganarsu suka gama bata fahimci me suka ce ba, haka zalika ba Www.bankinhausanovels.com.ng 

ta fahimci da mace yayi wayar ko namiji ba. Wannan ya Kara tayar mata da hankali ta ji rashin nutsuwar cigaba da zama a falon, ta fi kowa sanin Adamu saboda haka tafi kowa sanin wuyar da zata sha idan ya kwace ragamar zuciyarsa daga hannun Bokanta.

Cikin sanda da ladabi ta shiga dakin.

Lokacin adamu na zaune tsakiyar gado nazari kawai yake, yana jin wasu Kararraki na . tashin kansu a filin kwanyarsa, da Husnan da Salman da ma Salmanun tare da Sallar da ya farkar da shi yayi yanzu sun kawo kansu  zuciyarsa suke, suna neman yayi da su. :

Da salma ta shiga cikin rashin hayyaci ya___ juyo ya dube ta, ita kuma jikinta a sanyaye ta ” zauna a bakin gado tana cewa,

“Yaya Adamu yaya ciwon kan?”. .

Da kyar ya fizgo sauti a maKogoaronsa ya_ amsa, , . . ” Da sauki Salma”. .

Ta sake Kura masa ido, sai faman hada’

. gumi yake tayi, muryrta na rawa ta ce, ; ‘ “Amma gumi kake ta yi Yaya Adamu, ko Inji zan tasa a kunna maka fanka?”. , Zuciyarsa mai hana yi mata musu har zata

sanya shi ya amsa mata da ‘Eh’ amma jarumar ta tuna masa in ta tashi Inji dole ne ya bar sallar ya kwanta, ita kuma ta zo ta shinKime masa a baya. Da wannan jarumtar yayi hanzarin miKewa yana cewa, . “Bar shi kawai, zan yi sallah na kai wa Ubangiji kokena”. ’ Ta ji wani mugun sanyin jiki ya ziyarce ta, “sai ta rasa abinda zata ce masa don tana da yakinin ita ce koken da za’a kai wa Allah. Ta dinga bin’ sa da kallo har ya fice, sai da taji_—shigowarsa falo bayan ya gama alwala a tsakar – gida sannan ta mike da sauri ta same shi yana — _shimfida Sallaya.Yana ganinta ya ji wani sanyin jiki, amma bai ce mata komai ba. Ta yi inda-inda kafin ta yi magana,_ ‘ “Yaya Adamu ina fatan ba wurudin nan zaka yi ba”.  Da yana da Karfin gwiwa cusa mata zagi . zai yi, amma dayake ba shi da katabus sai ya — girgizakai yace mata, -_“A’a”, : Bai kuma jira cewarta ba ya tayar da sallarsa. .Www.bankinhausanovels.com.ng 

Dole ta koma daki nata Kirjin na cin wuta.

******

Kwana biyu Salmanu na kewaye-kewayen tuna wa Adamu Husna, yana ta yi masa jirwaye da kamar wanka, sai da ya ga kwana biyu ta ‘ wuce Adamu bai tunkare shi da maganar Husna ba ya‘san in ya cigaba da shan Kamshi kwaBarsa zata yi ruwa a wajen Husna wadda ya ci wa alwashin nan da kwana biyu duk inda Adamu — . yake sai ya neme ta. _ Da ya ga babu haza sai ya tukare shi kai tsaye da maganar, ‘ “Yau wata nawa da aurenka ne Adamu?”. Yayi masa duban rashin fahimta sannan ya gintse fuska, “Wanne auran?”, . . -“Auren naka nawa ne”. . Adamu ya kawar da kai.ya Bata fuska, “Ni bana son tashin tashina, in ba abin _ arziki zaka tambaye ni ba ka bar tambayarka”. Salmanu ya ce, ” ° “To sha kuruminka abin arziKi _zan tambaye ka”. – . Adamu yayi fuska don a tsammaninsa Salmanu shegantakar da ya saba zai kawo masa.

_ “Yakamata yau ka ziyarci Husna”, . Kamar daga sama Adamu ya ji furucin Salmanu, ya bige da kallon Salmanun kawai don Kwakwalwarsa ta rude ta rasa abinda zata yi. Da Salmanu ya gaji da kallon sai ya tare shi, . __ “Na zo da ta’addanci ko?” . Adamu ya kawar da kai, . “Sai na ji manufarka zan gane gaskiyar”. __ _ Salmanu ya sha kunu,

“Manufar alkhairi ce, ina son tuna maka alKawarin da ka daukar wa masoyiyarka ne, zan . kuma sanya ka a hanyar da zaka bi ka cika don. kar ka zama munafuki, in ka yi haka’ba ni zan amfana ba kai ne”. . Cikin sanyin jiki da kada kai Adamu yace, –

“Haka ne, na -yi wa Husna alKwarin zan koma in aure ta da wa’adin wata biyu, amma a yanzu sai na ji kamar ba ni da bukatar Karin auren..

Salmanu ya tare shi a tunzure, – “Don me, don ka daina sonta ko kuma don Ina kasailarta ta isa mamaye gurbin mata har Shi ma Adamu ya tare shi, amma cikin raunl, ’

“Ni ma ban sani ba wallahi, haka kawai na ji burikana sun yi Kasa, to wai rayuwar ma gaba dayanta nawa ce Salmanu…”.

Wani Kududun bakin ciki ya tokarewa ‘ Salmanu Kirji, ya tare shi a fusace,Www.bankinhausanovels.com.ng 

. “Ba wani nan Malam ni kar ka ishe ni da wa’azin Karya, ka yaudari ‘yar mutane ka cuce – – ta, duk salihancin Karyarka sai an saka mata…”. “Husnan na cuta, na.‘yi mata me Salmanu?”,  In ji Adamu cikin raunin murya. .

Kai tsaye ‘Salmanu ya amsa masa da kaushin murya, Tun “Ba ka da komai, ba ka yi komai ba wanda zai sa yarinyar nan ta saurare ‘ka, hasalima zuwanka gidansu daya talakanka da kai futuk!. – Ka nemi yardar aure ta yarje maka… ban taba ganin son tsakani da Allah ba irin wanda take maka, amma bata san kai mutumin banza ba ne baka san darajar irin wannan son ba…” . Adamu. ya’ rasa. abinda zai ce, da dakusasshiyar murya yace
Haka na’ fada maka Salmanu?”. . “Har sai na jira ka fada? Idan ka aikata‘ni hankalina ba ya gani?’ .

Adamu ya dinga murmushin yake da takaici na tsawon lokaci sannan ya tanka,

– “Zaka iya fadar duk abinda ya zo bakinka Salmanu, don ba ka san hakiKanin rayuwar da ke gudana a zuciyata ba”.

Kawai sai Salmanu ya ja dogon tsaki ya sa kai ya wuce, zuciyarsa kamar ta babbake da Karin tsanar Salma, shi bai ma san wanne irin mummunan mataki zai dauka a kanta ba.

Haka suka basar da komai suka cigaba da aikinsu, ranar ma sun sha baki kuma sun kwashi kudi. . .

Duk kwana uku ko hudu suke tattara kudin da suka samu su raba, a yau tun Karfe biyar Kafa__. ta dauke musu don haka suka zauna zauna zaman kasafi, sai da suka gama tsab Salmanu ya sake tattare na Adamu kamar yadda ya saba, ya jefe shi da yar dubu biyu.

Ran Adamu ya baci sosai, amma dai ya_shanye ya mayar da hankali ga Tanimu mai

. bincikar Salmanu dubu goman da ya ce ya ranta.

“Ba ka dawo da dubu goman nan ba fa”

Kai tsaye Salmanu ya ciro dubu goma a nasa kudin suka sake kasaftawa. .

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *