UMM ADIYYAH CHAPTER 1 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya fi sau goma tana Karewa takardun da ke gabanta kallo, saboda ta gano inda ta yi kuskure, amma sam! Ta gaza samo wuri koda daya ne, ita kanta ta san ta Kona
lokacinta wajen tsara wannan rahoton, domin ta bi komai daki-daki cikin tsari,
sannan ta yi rubutun.
Agogonta ta kalla, domin kuwa lokacin da ya dibar mata ya cika, ga shi an kusa Www.bankinhausanovels.com.ng
tashi, saboda haka dole ta san abin fada masa. Kodayake ta riga ta san
lokacinta ma take yi, domin kuwa tunda ya rantse, sai ya ga kasawarta a duk abinda
ta yi, ba abinda za tayi masa ta burge.
Wannan ya sa ta hada kan takardun ta jera su, sannan ta shigar da abin da ya
kamata ta shigar a na’ura mai Kwakwalwa cikin shafin kamfanin. “Ai idan ka san
wata, ba ka san wata ba.” Ta furta Kasa-Kasa gudun kar su Oga Akim su ji ta.
Kasancewar su uku suka rage a cikin ofishin nasu, sauran ma’aikata ukun yau sun
fita aikin fili, (Field work).
Jakarta ta daga ta kimtsa komanta a ciki, cikin shirin tafiya gida saboda ta kula
lokacin tashi ya gabato, sai a lokacin ta mulke hannunta man kariya daga Kwayoyin
cuta, (Sanitizer) da ke cikin Jakarta, wanda kadan daga cikin dabi’un Oga Musa da
ta dauka kenan a iya fara aikinta da su watanni uku da suka gabata.
Umm Adiyya Zubair, Umm A. Kamar yadda kowa yake kiranta ko kuwa Ummu
“Yan gargajiya ko manyan cikin dangi. Ta mika duka aikinta na ranar ga shugabanta
wanda yake duba ayyukanta kafin a mika su ga Oga kwata-kwata. Sai dai yau a
maimakon ya yi mata fara’a hade da sai da safe. Alama ya yi mata da ta zauna, bari
ya duba, idan ba matsala, sai ta wuce.
Shiru ta yi tana kallon mutumin da _tsakar kansa yake sheKi, tsabar yadda yake tal!
Ba ko burbudin gashi, ga wasu gilasai rau a idanunsa masu Karin Rarfin idanu. A
ganin farko, ba za ka ce Oga Akimu yare bane, saboda yadda kullum za ka gan shi
cikin shiga na hausawa, sannan fuskarsa tamkar wani bafulatani, sai ya budi baki zai
yi magana, za ka fahimci tsantsar bayarabe ne, na Karshe, don ko turanci yake yi za
ka fahimci haka.
Bayan shi kuwa teburin Jamila ce a gefensa, wacce a halin yanzu ba ta nan sun fita
tare da Oga Musa, wanda yake kusan matsayinsu daya da Oga Akimu a ofishin. Ba
laifi, daga fara aikinta tare da su, sun saba Kwarai, idan ka debe rashin sukuni da
take samu daga wurin mugun murdadden shugaban kamfanin, ko ma menene
dalilinsa na ba ta aikin, tunda ya tsaneta, har haka oho?
Ita ma maganinta kenan, da har ta mika takardar neman aikin a nan. (Application), Www.bankinhausanovels.com.ng
da ace ta fahimci asalin shi mai kamfanin da tuni ta tsere, tunda kaf garin ba shi
bane mutum na Karshe da za ta iya aiki da ma’aikatansa.
Koda yake ita ta dorawa kanta wannan masifar, da ta nace ita sai NGO ko kuma
kamfani mai zaman kansa za ta yi aiki. Idan banda haka, ayyuka nawa ta tsallake ta
yiwo nan, da har za a zazzare mata idanu ana sha mata Kamshi?
Hannu ta sa ta karbi takardar da Oga Akim ke mika mata, “Ga wannan mabudin,
shiga shafinmu na yanar gizonki, ya samu (Password), wanda aka fitar bayan
gyagije shafin kamfani.
Ga naki nan da aka bude miki, saboda haka ko daga gida za ki iya Karasa wasu
ayyukan.” Ya fada cikin turancinsa mai cike da harshen yarabanci.
Murmushi ta Kago masa, ta yi godiya hade da saba jakarta ta yiwa Ayo (Ayodele)
ban-kwana, wanda bai cika magana ba, duk ofis din, sai ku wuni bai ce maku komai
ba, dama da shi da Oga Musa ne, shiru-shiru, dan surutu kam sai Hasan, ita ma
Ummu A. din haka ta fi so, don sam ita ba ta ra’ayin ta zage tana ta shewa tana
surutu da ma’aikatan ofis dinsu.
Sai da ta faki Kayataccen babban falon da ya hada Kofofin ofis-ofis na kamfanin, ta tabbatar ba za ta hadu da damuwa ba, sannan ta danna kai, cikin dan falon wanda
aka Kayata da kujerun silba masu sulbi suna sheKi, ko ina shimfide da marbles, ga
Kamshi ga sanyin iyakwandishin da ke ratsa ko ina, saboda duk baKon da ya zo ya ji
dadin tarbar da aka yi masa.
Ganin ta wuce sumul ba tare da wani abin daga hankali ba, ya sa ta kawo ajiyar
zuciya ta sauke hade da lumshe idanu, ai kuwa kan ta bude su ta ji ta hadu da wani
abu mai tauri da Kamshi da dumi, da sauri ta bude idanunta, gudun ko ta ji ciwo.
Ko me take tunani, ba ta ga abu a gabanta ba… Nan ta yi turus! Domin kuwa ba abu
bane wanda dai take ta Kokarin gujewa, shi din ne ta fada kuma rigimarsa, domin ko Www.bankinhausanovels.com.ng
ba ta fadi ba, wannan kallon na tsantsar rigima ce a tare da shi, hakan ya sa ta kauce masa cikin sauri.
“Yi hakuri!” Kawai ta iya fadi, domin ba za ta
ma iya ce masa Yallabai (Sir) din ba, saboda dalilai masu dama.
“Idanun naki dama ba su gama warkewa bane, ki ka cire tabarau din?” Ta san
magana ya fadia mata, amma ba ta nemi tanka masa ba, kafin ma ta ce wani abu ya
ce, “Sannan, meye dalilinki na tauye min lokacina?”
A razane ta dago idanu aka yi rashin sa‘a idanunsa tsab! A kanta suke, “Ko kuwa
Karfe hudu da rabi ki ka ji an fada miki shi ne lokacin tashi a aiki?”
A hankali ta sauke numfashi sannan ta ce, “Ayi min uzuri, ina da abu mai
muhimmanci ne da ya taso min, shi ya sa.”
Ba tare da ya sake cewa komai ba, ya hade ran nan, uwar hadewa, sannan ya sa
kai cikin falon hace da saKala hannunsa daya a aljihun wandon suit dinsa na Hugo Boss, yayin da ta samu daman shigewa, amma ba tare da ta gagara jin tasirin
Kamshin turarensa a cikin ranta ba, domin kuwa Kamshinsa kadai ke sawa ta
haukace idan ta tuno abubuwa da dama, bare aje ga idanunsa masu rigima.
Da Kyar ta samu hannunta ya bar rawa har ta iya tada motar, ba wai tsoron Oganta
ne ya haddasa mata wannan halin da ta fada ba, tsoron abinda Ogan nata zai iya yi
game da ita, shi ya fi daga mata hankali.
A gaggauce ta wuce cikin gida, sai da ta yi wanka ta shirya, sannan ta nemi Maami
wacce ta baro a Kasa, ita ma dawowanta kenan daga kotu inda take aiki a (Court of Appeal).
Ta fi minti goma a zaune a falon ba tare da sanin abin da ke gewaye da ita ba, har
sai da Fa’iz Kaninta ya yi mata ihu a saman kai, ya sa ta firgita za ta hau shi da fada
ne. Fa’iz ya ce, “Adda Ummu, dole ya yi miki ihu ai, don kin yi nisa. Maami ke
tambayarki ko kin bada saKonta kan ki dawo?” Sai lokacin ta kula da Maamin ma a falon.
“Wai meke damuna ne?” Ta fada a Kasan
ranta, gaya zuciyarta ce ta ba ta amsa da,
“Me yake damunki kuwa? Banda tunanin Zaid Abdur-Rahman?” Take ta ture
wannan tunanin, “Allah ya sawwaka na yi tunaninsa, akan wane dalili? Mutumin da ya haramta gareni?
Ko bai haramta ba, da ni da tunanina mun yi masa fintiKau, babu abinda zai sa
tunaninsa ya zama halastacce a gareni. Saboda babu wanda na tsana duk duniya, irin sa.”
“Umm Adiyya lafiya ki ke kuwa?” Jin muryar Maami ya sa ta yi saurin yake baki,
cikin murmushin kawar da damuwar da take ciki ta ce, “Maami lafiya Kalau, kawai Www.bankinhausanovels.com.ng
dai na gaji ne. ” “Sannu, ki huta mana sannan mu ci abinci.”
Shafa dan shafal din cikinta ta yi, cikin yatsina fuska ta ce, “Maami ku fara kawai, a
Koshe na ke.”
Kallon tsab! Mahaifiyarta ta bita da shi sannan ta ce, “Kin tabbata ba wani abu ko?
Ba dai Za…” Da sauri ta kada kanta ta ce, “Ba komai Maami. Ku ci bari na yi shirin
sallah na ga maghrib, ya gabato.”
Ta dade tana azkaar, bayan ta idar da sallah, sannan ta sauko falon daga dakinta
da ke sama, sai dai turus! Ta yi ganin mutanen falon, wani irin abu ne ta ji ya taso ya
turniKe mata zuciya yana yi mata ciwo. Daidai lokacin da abin tuhumar nata ya juyo
suka hada idanu.
Tunda take, ba ta taba ganin mugun mutum marar kunya irin Zaid Abdur-Rahman ba. Ta so ta juya, amma ganin su Maami ya sa ta fasa, ta shigo falon ta gaishe su
sama-sama, don tare suke da Yayanta SaadiK
Har ma yana tambayarta, “Umm A. Da fatan dai wadannan ba su ba ki wahala a wurin aikin?”
Murmushi ta yi har sai da kumatunta ya loba, sannan ta ce, “Mutanen da suka bi ni
har da roKo, saboda na yi masu aiki ba sau daya ba ba sau biyu ba, ai ka ga ba za
su yi garajen ba ni wahala ba, don haka ina aiki na cikin kwanciyar hankali, with full
amenities. Ko ba haka ba?” Ta fada cikin dan murmushinta hade da harde
hannayenta saman Kirjinta.
Idanunsa ya zuba mata tamkar mai karantar duk wani motsi da ruhinta yake yi,
“Saadik, dole mu kula da Adiyya, saboda ko ba komai ta san yadda take amfani da
Kwakwalwarta, she’s very smart.” Ya Kare maganarsa cikin murmushi.
Tsumewa ta yi hade da aika masa kallon banza. Dole ka ce ku na kula da Adiyya, Www.bankinhausanovels.com.ng
banda dan karan wuyar da ku ke ba ni, me ku ke yi? Kullum na yi aiki, sai an
Kwakulo kuskure a ciki, ko me ya kai shi dauka na aikin ma tun farko, oho? Barin
falon ta yi zuwa kicin, inda ta yi zamanta a can ta ci abincinta.
Bata sake bi ta kan falon ba, bare ta san lokacin tafiyarsa. Tana kwance kan gado
sai aikin saKe-saKe take yi, abu daya ke yawo a Kwakwalwarta, kuma hanya daya
ce da za ta bi don magance wannan damuwar, ita ce ta bar aiki a AZ IT Consultants.
A karo na uku!
Ko su kadai suke daukar ma’aikatan da suka karanta fagenta, ta yafe wannan aikin
da irin uKubar da take shiga kullum wayewar gari. “To ma wai aikin dole ne?” Umm
Adiyya ta tambayi kanta, ba tare da sanin dalili ba, ta samu kanta tana tsiyayar
hawaye. “Duk har da laifin Abba ma, yaya za ayi bayan na fada masa komai kuma yace naci-gaba da aiki da su?”
***********
Babbar yatsar hannunsa na dama yake kadawa kan sitiyarin motar, yana tafe yana
tunanin abubuwa da dama. Kwarai ya san cewa ba Karamin kuskure ya yi ba da ya
sake barin Umm Adiyya ta shiga rayuwarsa.
Koda kuwa ta fuskar aiki ne, duk da kasancewar ba yadda za ayi ya yakice ta daga Www.bankinhausanovels.com.ng
rayuwarsa, saboda abin da ya hada su ba Karamin abu bane da zai warware a dare
Daya, abin da ya hada su dangataka ce da ba ta rabewa ba, a tunaninsa ya mance
da ita, ya sa ta a gefe, ba za ta taba tayar masa da abubuwan da ya zaci ya
adanasu ya boyesu a wani lungu a can cikin Kirjinsa ba, sai dai yau abin da ya gani
a tare da Adiyya, sun motsa masa abubuwa da dama masu dadii da masu daci.
Amma ya zama dole ya dubi Dangaren daya dace ya yi aiki da shi, saboda hakan zai
fi fishe su, daga shi har ita. Har rana mai kamar ta yau ba zai taba mance abinda ya
faru ba. Birki ya ja da Karfi, a dalilin wata motar da suka kusa yin karo, ashe tsabar
tunani, ta sa ya bar kan hanyarsa ya hau wata daban.
“Zaid Abdur-Rahman ka wuce haka!” Ya fada a bayyane, yayin da ya yanki kwanar
(Darussalam Close da ke Wuse 2), inda shiryayyen gidansa yake.
##########
Zaid Abdur-Rahman Nafada da na uku a cikin yara goma sha bakwai wurin
mahaifinsa, mutum ne da ya taso cikin gatansa dai-dai gwargwado, mutum ne kuma
da ya saba samun duk abin da ya nema, ko ya yi burin samu, saboda hazaKarsa da Www.bankinhausanovels.com.ng
kuma jajircewansa.
A garin Gombe ya yi Karamar makarantarsa kafin ya wuce zuwa sakandirensa a
birnin tarayya Abuja, a Kwali. Wannan ya yi mafarin zamansa gidan Baffansa Kanin
mahaifinsa Builder Zubair Nafada.
Tun daga lokacin kuwa zaman shi ya fi yawa a hannun Kanin mahaifin nasa, don ba
kowane hutu ma yake zuwa gidansu ya yi ba. Sai a nan Abuja yake hutunsa. Koda
ya tashi tafiya jami’a. Baffansa (Abba) ne ya yi masa duk wani abin da ya dace har
ya wuce India, inda ya karanci aikin Injiniyar sadarwa. (Telecommunications Engineering).
Kallo daya za ka yiwa Zaid, ka fahimci shi ba mai yawan magana bane.
Bayan ya kammala karatunsa na digiri ne, ya wuce karo ilimin Masters dinsa inda
ya tafi jami’ar Hertfordshire da ke United Kingdom, duk dai kan IT, ya karo ilimin.
Mutum ne wanda ya riki neman ilimi da tsantsar muhimmanci, haka nan yana da
karambani wurin yawan bincike da nemo sabon abu, wannan ya sa ya yi suna har ya
yi fice. Dalilin haduwarsa da wani bayarabe ma kenan wurin wata gasa ta Kasa har
suka zamo abokai.
Kowa yana inda yake, yayin da Zaid yake aiki da ma’aikatar kimiyya da fasaha ta
Kasa. Femi yana aiki a Warri, amma a hankali suka zame suka tada wani dan
kamfaninsu na gina Softwares da kuma Kera gamayyar kwamfuta (Hybrids), a Www.bankinhausanovels.com.ng
hankali abinsu na bunKasa har suka gamu da wani mutumin Adamawa Sufyaan. Shi
ma ya zuba hannun jarinsa, aka ci-gaba da tafiya, ga shi yanzu bayan watsa kayan
kamfaninsu da suke yi cikin Kasa, suna shigo da na waje, sannan suna bada
shawarwari wa masu neman shawara .
Wannan ya sa suka yi fice kan ka ce meye (AZ IT Consultants), ya yi suna a fadin
Kasar, don ba inda ba su shiga domin hada Networks da kuma Kaddamar da sabbin
Softwares, kama daga bankuna da kamfanoni, asibitoci zuwa ma’aikatu da kuma
kafa na’urar tsaro na kamfononi da ma’aikata har ma da gidaje.
Zaid Abdur-Rahman mutum ne tsaurarre da ba ka taba gane alKiblarsa kuma mutum
ne murdaddde, idan ba ka yi sabo da shi ka dade da fahimtar cewa hakan yake ba,
za ka dauka ba wanda ya kai shi fadiin rai. Wannan ya sa duka abokan Www.bankinhausanovels.com.ng
kasuwancinsa guda biyu suke mamaki, idan suka samu abokin ciniki, (Client) ta dalilin Zaid.
Ganin kamfaninsu ya bunkasa ya sa suka yi masa tsari na zamani suka samu ofishi
na musamman suna kuma diban ma’aikata, har makarantar horar da mutane kan
harkar Kera Softwares da kula da Komfutoci, (Maintainance), suna da shi a wannan
kamfanin. Yanzu shekaru bakwai kenan da fara wannan harkar tasu.
Yawan kamewarsa ce ta sa bai ganin amfanin ma ya tsaya wai bin mace, tana ba
shi wahala. Wannan ya sa shi sam mata ma ba su gabansa bare wata aba wai
soyayya. Soyayyarsa daya ce, ita ce ga Komfutarsa. Idan har ka ga yana sakewa
mutum fuska, to ‘yar-uwarsa ce, mutum daya ce jininsa ya hadu da nata wato
Asma’u.
Abinda ya sa kuma ba ta daukarwa kanta halayyar shisshigewa da namiji ba,
sannan kuma tana da gudun zuciyar mutum. Tun tasowarta yake kulawa da lamarinta, domin tasu ta zo daya.
**********