NI DA PRINCE CHAPTER 16
Waziri ya kalli sarki yace “bari inje asibitin”. Sarki yace “kana nufin barina zakai anan? Bayan salman da matarsa na asibiti? Wayasan awani hali suke? Waziri yace amma kaga kai bai kamata….. Sarki yakatseshi da cewa “yanzu kaje ka gunsu, nikuma sai ka sanar dani halin da ake ciki da daddare sai inje dakaina”. Waziri ya amsa sannan ya fita. Likitoci sun dukufa akan salman da shine ke jin jiki, salma bayan an mata dressing, sai jini da suke tunanin za’a kara mata. Salman kam sunyi mamakin yanda ya hari ciwo ya kamashi haka, da akamu abin ya dade, da kyar suka shawo kan lamarin kafin su turosu sukaisu d’aki d’aya, dukansu bacci sukeyi sakamakon allurar da aka musu. Ishaq kam duk ya rikece yana ganin waziri yai gunsa da sauri. Waziri ya kalleshi yace ” ishaq ina salman da matarsa?, ya jikin nasu? Abindai ba babba bane ba ko?” Ishaq ya rike hannun Waziri yace “Waziri wad’annan tambayoyin sun min yawa, wane kakeso in amsa?”yai maganar tare da zubo da kwalla. Waziri ya ja hannunshi ya zaunar dashi sannan yace “bari inga likita, dama ba kai yakamata intambaya ba, yahkuri yarima mai jiran gado.” Waziri ya sakeshi yai gun likita,knocking yai daga cikin aka amsa shigo, Waziri ya murd’a kofar tare da shiga da sallama. Likitan na ganinshi ya mike tare da gaisuwa, waziri ya amsa tare da zama, likitan ya kalleshi tare da zama shima. Waziri yace ” nazo ne inji halin da d’an mu da matarsa suke ciki”, Likita ya mike yace “badai wanda aka kawo da matarsa kake nufi ba? “. Waziri yace “eh salman da matarsa salma”, likita yai shiru can yace ” wanda yakawosu bai fad’amana ba hannu kawai yasa akan aiki, sannan a zahiri nayi mamakin yanda akai kuka bari yarima salman d’in ya kamu da heart attack,” Waziri cikin kid’ima yace “what? Heart attack? Likita ban gane ba?”. Likita yai ajiyar zuciya yace ” ka kwantar da hankalinka, ai salman yaro ne dama shi wannan ciwon yana wahalar warkewa ne ga wad’anda suka girma, to Alhamdulila salman yaro ne, saboda haka karku damu, akwai treatment daza’amai sai dai ba’anan ba.” Waziri yace ” bangane ba anan ba?” Likita yace ” akwai wani babban likitanmu *DR BILAL*( mijin ilham tsohon littafina), yana zaune a kasar england to ya sanar mana zai dawo nan da wata d’aya, likitane kwararre dan kwarewarshi ce tasa suka rikeshi, inhar yadawo sai aka salman ya dubashi sai yasan meya kamata amai.” STORY CONTINUES BELOW Waziri yai ajiyar zuciya yace “to Alhamdulila, salma fa?” Likita yai murmushi yace wannan ba matsala kanta ne yabugu sai jini data zubar, munason kara mata jini.” Waziri yace ” Alhamdulila” Likita ya sake murmushi yace “amma tana d’auke da juna biyu na wata 1.” Waziri ya saki fara’a shima yace “kai masha Allah, ta farfado ne?” Likitan yace “eh to yaci ace sun farfado yanzu, muje indubasu a canza musu d’aki,” Waziri yace to yafad’a tare da mikewa sukai hanyar d’akin da aka kwamtar dasu Salman, Ishaq ma na ganinsu ya biyosu. Sun shiga sun tadda Salman a zaune rike da hannun salman, idanunsa taf kwalla, Waziri na ganinshi yakarasa da sauri ya dafa Salman. Salman ya juyo ya kalleshi ya kuma kasa magana, hawayen dake kwance a idanunsa ne suka zubo, mamaki ya kama Waziri tunda yake yau ce rana ta farko dayaga hawayen Salman bashiba hatta Ishaq. Likitan ya kalli Salman yace ranka ya dade kwanta in dubaka, Salman ya kalleshi yace ” ni lafiyata kalau ga wacce nake so inji me kuka mata da ya hanata farkawa?” Likitan ya karaso kusa da Salma ya shiga dubata, ya d’ago yace “lafiyarta kalau komai nata normal, bansan me ya hanata farkawa ba,” Salman ya mike yamai wani kallo yace “baka sani ba?” Likitan yace “zata farfado nan acikin nan da 24hrs in bata farfado ba kafin nan zamu sake running d’in test.” Salman ya zuciya yayo kan likitan Waziri ya tareshi da sauri yace “Salman ka nutsu mana, Salma juna biyu gareta bai kamata a d’inga hayaniya haka ba.” Salman yace “me? Juna biyu? Likita da gaskene?” Salman duk ya rikice, Ishaq wani kishi ya kamashi juyawa yai ya fita da sauri. Salman yabi Ishaq da kallo, sai dai yau farinciki yasa bashi da lokacinsa amma alkawarine dole ya koyamai hankali. Salman komawa yai kusa da Salma ya kamo hannunta bakinshi yaki rufuwa yace ” Beauty ki tashi please, ki tashi mu kula da Babyn mu, Beauty ki tashi please….. Waziri da likita ganin yanda Salman yake kallan Salma yasa suka fita daga d’akin tare da jawo kofa.+ Salman ya kurama Salma ido a hankali yakai hannunsa kan inda aka sa mata plaster ya shafa gun, jiyai jiri nad’an kamashi daga zaune, sauri yai ya kwantar da kansa akan pillow d’in datake, kansa kusa da nata, hannunta ya rike kam. Tunani yafara yi, wato ishaq shi yaso bigewa?Baiwar Allah azal yafad’a mata, sashi akai? Abinda yafad’omai kenan aransa, yanzu da sun mai asarar cikinsa fa? idansa ne ya kad’a yai ja, a mike zaune ya kalli Salma yace ” I won’t forgive them,duk wanda keda hannu a cikin wallahi I won’t let them be.” Ishaq kam gida ya wuce cikin b’acin rai yai b’angaren fulani. Tana zaune acikin kilisa, hankalinta akwance, sai ma farin ciki da take wai ance salman na asibiti da matarsa, itakam jitake ina ma su mutu ko ta huta da ganinsu. Ishaq ne yai sallama ya shigo da sauri, fulani ta kalleshi tace ” yanzu nake nemanka ka tayani murna, Allah ya saukaka mana komai.” Ishaq ya zauna rai a b’ace yace ” wani sauki koma? Banda tashin hankalin danake ciki?” Fulani tace ” wani bakin ciki bayan Salma da Salman na asibiti.” Ishaq yai tsaki yace “Umma nikam kibar wannan zancen, ni fa kishi ya ciwoni naso makeshi, amma Salma ta kare shi.” Fulani ta mike tsaye cikin kid’ima tace “mene? Ishaq kasan me kake fad’a kuwa? Ishaq bangane kai kaje make Salman ba.” Ishaq ya share zufa data ketomai yace ” bama wannan ba Umma, Salman ya ganni yasan ninai.” Fulani tashiga tafa hannu tace “shikenan na shiga uku, Ishaq yanzu yazamuyi? Me yakaika? Nafad’amaka kad’inga tunani da hankalinka.” Ishaq yace “ni dan Allah Umma kidaina min wannan zancen abinda ke damuna ma ya isheni.” Fulani ta zabura yace “meke damunka? Akwai abinda zai dameka daya wuce wannan?.” Ishaq ma ya mike rai a b’ace yace “haba umma ya kikeso inyi da raina? Ina kallo yanzu Salma zata haifi d’an Salman?” Cikin mamaki fulani ta kalleshi sai kuma ta had’e rai tace “da kanaso ne Salman d’in yasata agaba yai ta kallo ko me?” Ishaq yace “ba ciki ne da Salma ba ko ‘ya’ya d’ari gareta nidai ina santa bakuma abinda yadameni da wani Salman ko wani da zai kawomin matsala.” Fulani data rikece jin kalamansa tace “me kace? Ciki? Ishaq me kake nufi?” Ishaq yace “ciki ne da salma yanzu aka fad’a a asibiti, menene?, kema kina tayani kishi ko?” Fulani ta harzuka tace dalla gafara banza, shashasha, Salma nada ciki inta haifi namiji fa? Kai matanka biyi ‘ya’yanka hudu amma duk mata, shine maimakon kai tunanin abin da zai faru gaba shine kakemin zancan wata banzar soyayyarka?” Sai a lokacin ishaq yai shiru, yanzu in bai haifi namiji ba fa? Kenan za’a iya bashi mulki daga baya aba d’an salman, yazaiyi? Yanda ya tsani Salman d’in nan.” Fulani tazauna tare da dafe kai tace “yau nikam da wani hannu na tashi? Wannan bakin ciki kala_kala?” Farha ce ta fito da sauri ta kalli Fulani tace ” zanje asibiti ance Yayana bashida lafiya,” Ishaq yai tsaki yace to salman ya ware, sai dai in Salma zakije ki dubo daganan sai ki tayashi murna tunda sun samu karuwa.” Farha takaraso tace “bangane ba? Karuwa kamar me?” Ishaq yace “ciki gareta.” Farha tace “mene? Ciki? Bangane ciki ba?.” Fulani dake rike dakai tace ” Farha yaz’amuyi Salma dai ciki gareta.” Farha ta zube agun ta d’aura hannu akai ta sa ihu tace ” ciki? Shikenan nasan yaya Salman bazai kulani ba, Amma wannan Salmar akwai yar iska.” Nace ko kuma ku ba….. Salmah kam tana kwance itakam rayuwa mai dadi take acikin baccinta, yau taga fuskar saurayin nan Salman ne suna zaune a bakin ruwa, ta kwanta akan cinyarsa shikuma yana rike da littafin story book yana karanta mata, sosai takejin dadin labarin sai lumshe ido take, Salman ya kalleta yai murmushi sannan ya rufo gefen fuskarta da littafin hannunsa, yakai bakinshi kan lebenta ya sumbata, ido ta rufe cikin murya kasa_kasa tace “in aka ganmu fa?” Salman yace “menene aciki? Keba matata bace?” Murmushi sukai ta kalleshi tace “ka cigaba,” tai maganar cikin shagwaba nan ya cigaba da karatun. Sarki yau farin ciki ba’a magana zuciyarshi kamar ta faso, sai dai yana tsakiyar murnar yin jika dazaiyi ta tsatson Salman waziri ya nisa yace “amma akwai wata ‘yar matsala, Salman nafama da wani ciwo.” Cikin tsoro Sarki yace “ciwo? Wani iri kenan?” Waziri yace “yarima Salman na fama da ciwon heart attack.” Cikin rud’ewa Sarki yace “heart attack? Kasan mai kake cewa kuwa waziri?” Waziri ya tsugunna yace ” tuba nake ranka ya dade.” Sarki ya rike kansa, yama kasa magana. Waziri yace “amma akwai likita, ance inyazo insha Allahu da yardar Allah Salman zai warke.” Sarki yai shiru can yace ” waziri kasani yaron nan kaf cikin ‘ya’yana ba wanda nakejinshi har cikin jikina irinsa, in wani abun ya sameshi bansan yazanyi ba, da alama ciwonsa ma nine sila.” Waziri yace “ya kake fad’an haka ranka ya dade? Kaine sila?ciwo ne dai daga Allah.” Sarki yace “nasani ciwo me daga Allah amma nasan bakin cikin daya kunsa yana yaro shiya jamai wannan ciwo.” Waziri nan ya shiga bashi baki, sai dai Sarki jinsa kawai yake, can yace “naji waziri yanzu ana isha’I kazo ka kaini inga halin dasuke ciki, waye agunsu?” Waziri yace “na kira zeenatu tace tana hanya.” Salman ne ya kallin likitan dayazo duba Salma yace “yanaga bata farka ba?” Likitan yace “karka damu kila itama tanajin dadin rayuwar da takeyi ne acikin baccin, amma zata farka nan bada dadewa ba.” Salman ya kalli Salma cikin tsananin tausayi. Likita yace “amma ina tunanin za’a kara mata jini kad’an.” Salman ya kalleshi yace “akara mata nawa ko leda nawa ne dan kuwa O+ gareni bana tunanin akwai matsala.” Likita yai shiru can yace “amma ina ga kai da bakada lafiya bai kamata aragema jini ba.” Salman yace “jikinka ne ko nawa? Ko kuwa inwani abun yasameta zaka d’au responsibility?” Likita ya had’iyi yawo yace “a’a ayi hakuri yarima, bansan kalmar zata b’atama raiba.” Salman yamaida idansa kan Salma tare da riko hannunta cikin zuciyarsa yace ” Beauty please” Tunowa yai yakamata ya kira Abban ta, to karkuma ya tada musu hankali, ajiyar zuciya yai yace “Beauty yazanyi? Zeena tazo sai dai duk yanda ta roki Salman akan yaci abinci amma yaki, tai fad’an har ta gaji, shikam yama dags akan ta rakashi agwada jininsa su tabbatar zai iya bata, a d’eba asa mata.+ Zeena ta kalleshi tace ” haba Salman mai yasa kake haka? Kabari gobe in an kira ‘yan uwanta sunzo sai a gwadaso asamu wanda yai a kara mata, amma kai baka da lafiya ina kai ina bada jini? Sannan gashi sam kakicin abinci.” Salman ya kalleta yace ” Aunty zeena har dake? Nad’auka ke ba halinku d’aya dasu ba, taya zakice gobe in ‘yan uwanta sunzo, Salma matatace kuma saboda wani abun dabai gagareni ba bazan nuna mata nafisan kaina akanta ba, abinci kuma inkinga naci abinci to tabbas naga matata taci.” Yanakai nan ya fita, Zeena tausayinsa ya kamata, wani irin so Salman kema Salma haka? A da taga ko kallo bata isheshi ba, yaushe abu ya juya haka?. Salman da kanshi yaje lab d’in suka gwadashi sun tabbatar O+ gareshi kuma zai iya bata, wucewa yai gun likita yace “tashi muje ko?” Likitan yace “Yarima dan Allah…..” Cikin fad’a Salman ya katseshi yace “Karka bata min rai, inace inason abu to kamin kafin ranka ya b’aci, nagaji da ganin matata a kwance.” Likitan yace “kayi hakuri ranka ya dade amma matarka badan jini bane taki tashi.” Salman yace ” Naji, amma wuce muje inka kara mata jinin sai nu jira in ta wuce hours d’in daka fad’a hmm bansan kuma mai zan ma ba.” Salman ya juya, da sauri likitan ya fito sukai shigo da kayan aiki d’akin, an saita komai sai da ba’a fara ba mai martaba ya iso shida waziri. Salman na ganinshi ya had’iyi wani abu tare da kara d’aure fuska, Sarki ya karaso kusa dashi, waziri ya kalli Zeena dake gaida Sarki yace inkin gama kowa ya fito yabasu guri, tace to. Kowa ya fita yabarsu su biyu sai Salma dake kwance, Sarki ya kamo hannun Salman ya rike yace “Salman na tsorata danaji ance bakada lafiya na d’auka kaima rasaka zanyi.” Salman ya kalleshi idanshi yai jaa, dasauri ya maida kanshi gefen da Salma take, Sarki yace ” Salman meyasa baka sanar dani larurarka ba? Ina zaune bansan halin da d’ana yake ciki ba.” Salman ya kalleshi yace ” Ina zaka sani Abba? Tunda mukamin ka yafini daraja? Tunda kake dani ka taba tambaya ta yana tashi? Meke damuna? Naci abinci? Bani da wata matsala dake damuna?”hawaye ya zuboma Salman a ido yacigaba” Kun rufe mutuwar Ummana saboda san mulki, kun turani wata kasar dan bazaku iya kula dani ba, sannan yanzu Abba katambayeni wai zancen ciwo na? Ban fad’ama ba?” Ya share hawayen dake zubo masa yace ” kasan wace irin rayuwa nayi? Kai dai kullum kana zaune akan kujerar mulki sai abinda aka fad’ama.” Salman na zuwa nan ya runtse ido, hawaye suka kara zubomai ya share tare da kallan Salma, yace “zan iya jure komai amma banda a tab’a matata.” Sarki da tunda Salman yafara magana kwalla ta cika taf a idanunsa yasani sarai abinda Salman ya fad’a duk gaskiya ne, amma ya zaiyi? Tunda haka mulki ya gada. Kafad’ar Salman ya dafa, ya d’ago ya kalleshi cikin tsananin tausayin d’an yace Salman na sani duk wani abu dake damunka laifinane na sani amma dan Allah Salman ka cirema zuciyarka komai ko ka samu nutsuwa, kaduba matarka, ciki gareta ka taimakeni Salman ka cire komai aranka kafin d’anka ya taso da kiyayyata, Salman kayi hakuri akan duk abubuwan dana maka, nasani sarai abin na damunka amma zuciyata inta ganka sai inji tausayinka bazai bari in tada maganar ba.” Salman ya kalleshi yace ” So nake ka bani izini ind’au matata in bar gidan, dan banasan zama a cikin gidan, nafisan inda zamuyi rayuwa kamar kowa nida abinda za’a haifarmin.” Sarki ya kalleshi tare da jijiga kai, yace Salman banda wannan, zan iyama komai Salman amma bazan iya barinka nesa dani ba, bayan kaine magaji na.” STORY CONTINUES BELOW Salman yace “magaji? Magajin me fa?” Sarki yace “mubar maganan nan Salman dan Allah.” Salman yace ” Abba?” Sarki ta rike hannun Salman yace “Salman kayi hakuri ka yafema wannan mahaifin naka, yasani yamaka laifufuka da dama, amma ka sani kullum kana ranshi dai dai da minti 1 bai tab’a mantawa dakai ba.” Salman hawate suka kara zubomai, yana tsananin san mahaifinsa yazaiyi? Idansa ya runtse baice komai ba, Sarki yai shiru can yace “ance hatsarine, bakasan waye mai wannan d’anyen aikin ba?” Salma ya tuno sanda yaga Ishaq amma sai ya daure yace “ban ganshi ba sai dai koma waye I won’t forgive them.” Sarki yace “ko ni, sai dai in a rashin sani ne amma in har wanda yai da saninsa ne to bazan yafemai ba ko waye kuwa, I promise you this.” Salman yace “Abba karkai Alkawarin dabazaka cika ba.” Sarki ya dafashi yace “Salman kenan, ai sarki na gari baya magana biyu, amma nikam Salma taji jikine? Naga bata farfado ba?” Salman yace” nima bansani ba wlh, yanzu dai jini za’a kara mata sai mu jira nan da wasu awanni kad’an mugani.” Sarki yace “da alama d’ana ne zai bada jini?” Salman yai kasa dakai tare da sosa keya. Sarki yai murmushi yace “naji dadi Salman da yawancin halayenka irin nawa ne, kasan me?” Salman ya girgiza kai Sarki yai kasa da murya yace” Sanda inasan ummanka banajin komai, ganinake komai zan iyayi saboda san da nake mata.” Atare suka kwashe da dariya, waziri da zeena da sauran fadawan dake waje suka kalli juna cikin tsananin mamaki, duk cikinsu ba wanda yataba jin dariyar sarki haka, ko salman d’in ma. Bayan sun tsagaita, sarki ya rungumo Salman yace karka damu d’ana Salma zata warke sumul kamar ba ita ta bige ba, Salman yai murmushi, wani irin farinciki ke ratsatsu, daga Salman har Sarkin. A gaban Sarkin aka kira likitan ya juna kayan aiki nan aka fara karin jini, Sarki ya shafa kan Salman ya fita. Hmmmm tsakanin ‘Da da mahaifi sai Allah An gama karama Salma jini Salman ya mike da kyar dan jiri yakeji, kusa da ita ya zauna tare da riko hannunta, zeena kam jikinta yai sanyi, tana mamakin tsananin san da Salman kema Salma.+ Salman na zaune har barci yafara d’aukansa hakan yasa ya kwantar dakansa kusa da ita, ahankali bacci yai gaba dashi, Salma sai datakai wajen karfe 3, alokacinma mafarki take, wai Salman sunyi fad’a ya juya zai tafi tabishi da gudu tana kira, sai dai kafin ta karaso ya b’ace mata, a firgice ta mike tace *PRINCE*cikin wata murya, dukansu sai da suka tashi zeena, Salman ya kankame hannunta yace” Naam beauty ganinan.” Bata kula da kowa ba kawai rungumeshi tau kam tana hawaye, shima hawayen ne ya zubomai, a hankali ya nemi ya d’agota amma ina….kara k’ankameshi tai, Salman yai ajiyar zuciya yashiga shafa bayanta. Zeena kam tayi mutuwar zaune tana mamaki itakam bata tab’a ganin masu san juna irin haka ba. Salma ta dade ajikin Salman kafin ta d’ago, ahankalita tab’a fuskarshi,sai alokacin abinda yafaru ya dawo mata, a hankali tace “ba abinda ya sameka? Salman ya shafa kanta yace “ba abinda yasameni sai tsoron abinda yasami matata.” Salma ta share kwalla, tare da tab’a kanta datajishi a d’aure, jin plaster yasa ta d’aure tace “na d’auka zan rasaka.” Salman yai shiru, ishaq ne ya fad’o mai arai, sai kuma ya share, tare da kamo hannunta yace abinci fa? Tace zanci, mikewa yai sai alokacin yaga zeena, ya sosa keya, itama Salma sai alokacin ta ganta, dasauri ta koma ta kwanta, ta rufe fuska, zeena tace ” a’a love birds bansan wani salo, angama fitsara agabana sai kuma ashiga rufe ido?” Salman yace “kema yaya zeena da kika ga haka sai ki koma ki kwanta.” Tace “au to ayi hakuri na koma bacci.” Tafad’a tare da kwanciya.1 STORY CONTINUES BELOW Dakanshi ya zubo mata abinci ya sa spoon ya matso kusa da ita, Salma ta mike a hankali tare da kallan agoggo, ta kalli Salman tace “wai ukun darene tai?” Salman yace “eh mana duk kin gama tsoratani, ganin baki farka ba.” Tace ” Yahkuri.” Yace “ci abinci dai tukunna.” Da kanshi ya shiga bata, tayi spoon biyu ta kalleshi tace” kaima nasan bakaci komai ba, sai dai muci tare.” Zaiyi magana tace “please” Yai murmushi yace ok. Tare sukaci, sai da suka koshi sannan ya bata ruwa tasha, ta kalleshi tace “prince mud’anfita?” Kai ya d’aga mata tare da taimaka mata ta mike. Suna bude kofa yaga fadawa da sauri ta koma tace mun fasa, Salman ya kalleta yace “meyasa” Komawa ciki tai tare da zama a kan carpet d’in dakin, Salman ya d’auko bargon dake kan gadon ya karaso kusa da ita ya zauna tare da rufa musu bargon, Salma ta kwanto da kanta kafad’arsa tare da zura hannunta jikin hannunsa. Salman ya sa d’ayan hannunsa kan cikinta yace “babyna dafatan kana cikin koshin lafiya.” Salma ta kalleshi da mamaki tace ” baby?, wa kenan, badai suna aka canzamin ba?” Salman yai murmushi yace “babyna mana dake jikinki, wai ya akai baki sani ba?” Salma ta d’aga kanta daga kansa tace” naam?” Salman ya d’aga mata gira, tace “muga wayarka?” Nan Salman ya mika mata ta amsa tare da duba date, Dagaske ta wuce kwanankin period d’inta da 9 days, amma ya akai bata sani ba? Kallan Salman tai cikin farin ciki tare da shafa cikinta, ko shiyasa kwananan sai tai tajin kwad’ayi?. Salman ya maido da kanta inda yake tare da cewa Beauty kiyi Sauri ki warke mu kula da babynmu, Salma ta d’ago da d’an karfi, jin kanta yad’an amsa tace ahhh. Salman da sauri ya kalleta yace “beauty?menene? Zafi?” Salma tai murmushi tace kan nawa ne sai injishi a d’ad’aure bansaba ba yace ” haka ne ai, sannu, amma beauty da kika ture ni aka bige ki kinsan me kikai kuwa? Kina tunanin zanso wani abu ya sameki akaina?” Salma ta maida kanta tace ” ni alokacin gaba d’aya kaina ya kulle tsoro na d’aya kar wani abu ya sameka.” Kwalla ta cika idanta tace ” namanta da jikina, ni kawai kai nake gani.” Salman yai shiru, tare da lumshe ido, Salma jin haka tace “kasan mafarkin danai? ” Salman yad’ago ya kalleta, tace bazan fad’ama ba siri ne. Yai murmushi yace in ansan siri ne ai ba sai an min zancen ba dan a samin san jin labarin. Salma ta kara gyara kanta tare da rufe idanta, Salman shima ya rufe nasa idan, bacci ne ya d’aukeshi, a hankali Salma ta mike tare da wucewa toilet tai alwala, Sallah tazo ta tada ta rama salolin da ake binta. Da safe zeena dakanta taje gun likita tace ya kamata a sallamesu dan da akama bazasu iya zaman asibiti ba, likitan yace to amma sai zuwa yanma tace to, sannan ta koma ta sanar musu. Salman kam ba kunya dadi yaji. Wajen karfe 9, Farha ta taho damai kawo abinci, tsoron shiga takeyi hakan yasa tace masu kaiwar su shiga dashi, ita kuma ta tsaya ajikin window tana kallan Salman dake zaune kusa da Salma, wani abu ta had’iya idanunta suka kad’a, kamar wasa Salman ya kalli window, Farha ya gani tayi tsuru, murmushi ya mata sannan ya mata alama da hannu akan tazo, Salma ta kalleshi tare da had’e rai, Salman yai kamar bai ganta ba. Farha na shigowa jiki a sanyaye ta d’an tsaya daga nesa yace “kanwata matso mana.” Farha ta d’ago ta kalleshi cikin mamaki, Salma ma kallan mamaki take mai, Farha ta matso kusa tare da gaidashi ya amsa fuska a sake yace” meye na tsayawa acan.” Tace “uhm yaya dama ai…” Ya katseta yace ” inkinzo neman lada ki nema da kyau” ahankali tace to. Sannan ta kalli Salma dake kallanta rai a b’ace tace “in_law sannu da jiki” Salma tace “yauwa”fuska a d’aure, farha tad’an dade kad’an kafin tace “bari in tafi yayana.” Salman ya kalleta yace “to Farha nagode” murmushi tai tace “nice da godiya yayana.” Nan ta juya tai waje, Salma ta bita da harara tace “daka bita ai” Salman yace “ko?to in na batta ke kuma fa?.” Haushi ya kamata tace “ai bakaikad’ai bane a guna.” Ga mamakinta gani tai Salman ya mike, yai waje, ta kalleshi cikin tsananin mamaki, menene hakan? STORY CONTINUES BELOW Salman kam yana fita ya had’e rai tare da bin inda Farha tai, tana tsaye a jikin wata bishiya, tana waya, a hankali ya karasa inda take, jiyai a wayar tace “wlh yaya bai nunamin komai ba” bai ji me akaceba yadaiji tace ” yama za’ayi ace Salma keda ciki bayan ni ya kamata infara haifar mai d’a? Fulani Nifa na tsani Salmar nan, kyau kamar aljanna.” Salman ya kalleta cikin tsananin b’acin rai, ga mamakina sai gani nai ya dawo ta gabanta da murmushi yace na fito miki rakiya ashe kina nan? Tsoro ya kamata ta kalleshi tare da yarda wayarta, Salman yace “ahhh Clumsy girl, yazaki yarda wayarki?” Dasauri tad’auka tare da kashe wayar. Salman yace “da alama rakiyar bazata yiwuba bari na koma gun beauty.” Farha da sauri tace “a’a inaso yayana” Salman yai wani murmushi yace “muje to, ina kikai parking?” A hankali ta nuna mai inda motarta take, dakanshi ya rakata sai daya tsaya ta ja tai gaba, sannan yabi motar da kallo yace ” one by one ni zan koya muku hankali.” Farha kam farin ciki tad’inga jin jitake kamar tai ihu dan dadi. Salma kam ta cika tai fam…….. Nace to fa!!! Kowa da abinda ke ransa….lol