UMMI CHAPTER 16 KARSHE
♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE MAITAMA Zaune suke a kan 2-seater kujera a falon shi riqe da hannun juna suna hira yayinda yake kwance a kan 3-seater yana typing a wayar shi… da alama dai abinda yake yi kafin su shigo ne ya cigaba da yi. Hira suke yi sossai na abubuwan da suka faru a rayuwar su amma sam hankalin shi baya tare da su. Maleeka ce tace “na ji kina ta buga turanci.. wai wa ya koya miki?? ko kin shiga school ne??”+ Ummi tana murmushi tace “babu wani school din da na shiga Adda.. A shekaru na wane school zan je? kin ga fa Sweetheart ne ya koya mun turanci lokacin da muke Greece” Maleeka ta girgiza kai tana murmushi tace “amma dai gaskiya kina da qwalwa Ummi.. kinyi qoqari sossai within the period kinyi grabbing sossai” Ummi tayi dariya tace “Adda shima yayi qoqari sossai don wallahi ya iya koyarwa..” Maleeka tace “ni zan fadi miki wannan… lokacin da nake school shine yake koya mun karatu. idan na je makaranta har a gama lecture bana gane komai amma idan na dawo gida muka zauna ya fara koya mun sai in ji komai ya shiga kai na” Ummi wadda ta kula hankalin MK baya tare da su ce ta dan taba Maleeka tare da ta nuna shi tace “Look at him.. yanzu haka fa aiki yake yi.. kin ga tunda muka dawo abinda ya sa a gaba kenan gashi har kanshi yana ta ciwo.. saboda na hana shi shine ya koma yi ta waya” Maleeka ta fashe da dariya tace “ai Honey ko agogo sai haka..” Miqewa tayi sannan tace “wait and see” ta qarasa wurinshi ta zauna gefen shi a bisa kujerar ta sa hannu ta birkita gashin kanshi tace “hey.. ya muna qoqarin entertaining dinka ka share mu??” Murmushi yayi tare da sa hannu ya gyara gashin kanshi da ta birkita yace “Babe sorry I was just trying to..” Qwace wayar tayi tace “you are working ko?? toh baby tace ka bari ko tayi fushi..” Da sauri ya kalli Ummi wadda take zaune tana kallonshi da fuskarta a murtuke. Murmushi yayi yayi yace “Sorry Baby.. kin ga fa akwai wani urgent mail ne da nayi responding to.. amma na gama” Ummi tace “better” Maleeka wadda take zaune kusa da shi ce tace “kayi qoqari ka rage yawan aiki Honey.. ka ga fa yawan aiki zai sa ka tsufa da wuri..” Ta kalli Ummi tace “ko ba haka ba maman biyu??” Ummi dai fashewa tayi da dariya yayinda MK ya girgiza kai yana murmushi. Gani nayi ya janyota ta kwanto a jikin shi yace “Na ji kin kira ta da maman biyu.. kina gani kamar twins zata haifo ko??” Tana murmushi tace “gaskiya I think so..” Da sauri ya kalli Ummi yace “Baby kin ji har Babe ma tace twins zaki haifo ko??” Ummi cikin shagwaba ta shafa cikin tace “ni fa guda daya ne a ciki na..” Dariya suke yi mata yayinda MK yace “but seriously Ina fatan Allah yasa twins ne..” Maleeka ce tace “toh bakuyi ultrasound scan bane? ba ance within 10-14 weeks ana iya confirming ba?” MK ya tabe fuska yace “Baby tace bata so.. wai idan Allah ya sauke ta lafiya za’a gani” Maleeka tana murmushi tace “toh kenan idan mun fara shopping kayan wa za’a siyo?? mace ko namiji?” STORY CONTINUES BELOW Kai tsaye Ummi tace “ku siyo duka.. duk wanda aka samu kin ga sai mu ajiye idan kin haihu sai Babyn ya sa ko ta sa” Maleeka ce ta dan dago ta kalli MK tana murmushi tace “I cant wait to give you a child too honey”1 Wani irin sanyi ya ji a ranshi yau Maleeka ce take fadin she cant wait to give him a child..1 Murmushi yayi yace “me too babe..” Ummi ce tace “Allah ya kawo mana masu albarka” gaba dayan su suka ce “ameen” A haka dai suka cigaba da hira har akayi kiran sallan Zuhr.. MK ya wuce dakin shi don yin alwala ya tafi masallaci yayinda Ummi ta janye Maleeka zuwa sashen ta don suyi sallah. *********** Ko da su Ummi suka idar da sallah zaman su suka yi a dakin suna hira… da alama they really want to get along with each other ne.. Yanzu haka hirar maternity gowns suke yi. Maleeka ce tace “…zan sa a kawo miki.. maternity gowns din sunyi kyau sossai wallahi” Ummi tace “thanks alot Adda” Wayar intercom ce tayi ringing yayinda Maleeka tayi picking… A dayan bangaren ne Inno tace “Ummi an gama abincin rana..” Maleeka tace “toh sannu da aiki..” Cike da mamaki Inno tace “kamar muryar Hajiya qarama nake ji..” Maleeka tayi murmushi tace “ita ce.. ya aiki ya gida??” Tace “lafiya lau..” Daga nan Maleeka tace “toh madallah.. gamu nan saukowa” Bayan ta ajiye wayar ne ta kalli Ummi tace “Maman biyu an gama lunch.. mu je ki ci abinci kar ‘yan biyu su ji yunwa” Ummi tana murmushi ta yunqura ta miqe suka fita. Abin mamaki ko da suka shiga dinning din sun tarar da MK a zaune yana jiran su. Ummi ce ta kwanto ta bayan shi tayi mishi kiss a kumatu tace “Sweetheart yau ka riga ni.. hala yunwa kake ji?” Maleeka wadda take biye da ita ce tace “ba dole ya ji yunwa ba.. yana overstressing kanshi da aiki” Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba.. ya kula matan nashi sun sa shi a gaba ne kawai! Ummi tana shirin fara zubawa ne Maleeka tace “let me do this Ummi.. zauna abinki” Ta zauna tare da fadin “nagode Adda” MK kuwa sa ma Maleeka idanuwa yayi yana mamakin wai yau ita ce haka.. Lumshe idanuwa yayi a ranshi yace “a dream come true for you MK” Muryar Ummi ya ji tace “kai.. na manta fa tuwo miyan kuka aka yi gashi Adda bata ci” Maleeka tana murmushi tace “wa ya fadi miki bana ci??” Da sauri MK yace “like seriously? you mean..” Girgiza kai tayi tace “alot has changed about me.. infact har ma na iya tuqa tuwo yanzu” Cike da farin ciki MK yace “wow.. amma na ji dadi sossai Babe, cant wait to taste your food” Cikin tsokana Ummi tace “me too” yayinda ta kashe ma Maleeka ido daya. Maleeka tana dariya tace “kar ku damu.. Insha Allah zaku ci girkin Maleeka har ku gaji” Haka dai ta zuba musu abincin a plate daya kamar yadda MK ya umurce ta.. farfesun kifin ma ta zuba a plate daya. MK ya janyo plate din gaban shi sannan ya fara ba su a baki.. idan ya ba Ummi sai ya ba Maleeka… Sai da suka qoshi sannan ya fara ci. A haka suka dinga hira. STORY CONTINUES BELOW Maleeka ce tayi gyaran murya tace “Honey..” MK wanda yake rufe goran swan din da ya sha ne yace “yes Babe” Tace “please I need a favor… don Allah kar kace a’a” Murmushi yayi yace “I hardly say No to everything… yeah??” Itama murmushi tayi sannan ta kalli Ummi tace “don Allah ina roqon alfarma akan ka dawo da Ummi Asokoro mu zauna tare” Gani nayi MK ya kalli Ummi wadda itama take kallon shi.. ♧♧♧♧♧♧ Kamar yadda Maleeka ta nemi alfarmar MK ya dawo da Ummi Asokoro su cigaba da zama tare haka aka yi.. Maleeka dai ta ajiye girman kanta a gefe ta rungumi Ummi a matsayin ‘yar uwa.. Abu na farko da ta fara yi shine ta je har gidan Goggo ta bata haquri akan dukkanin abubuwan da tayi ma Ummi. secondly, ta gyara tsakanin ta da Fahad da kuma Fatima.. A yanzu haka idan Fatima ta zo gidan zaka gan su tare suna ta hira, MK ya ji dadin wannan al’amari domin kuwa tun farko ya so ace Maleeka da Fahad sun fahimci juna because they used to be his best people… Haka Jameela ma ta ji dadi sossai da qawarta ta gyara halin ta. A wurin Mummy ne take jin cewar ashe sun san abinda ya faru even before she told them.. ta sanar da ita yadda su Abba suka dage akan lallai kar MK ya rabu da ita da kuma yadda MK din ya dinga turo mata kudi through her dukda fushi yake da ita.. Sossai Maleeka tayi mamaki. Musamman har gidan Abba ta je ta basu haquri akan abubuwan da tayi a baya da how she put their son and his wife through alot sannan tayi musu godiya na hana shi rabuwa da ita da sukayi.. Iyayen su sun ji dadi qwarai da aka samu sulhu a tsakanin Maleeka da MK.. kamar yadda Daddy ya fada cewar Maleeka needed to learn the hard way, tabbas haka ne. Zaman lafiya sossai ake yi a gidan MK.. idan ka ga Ummi da Maleeka zaka rantse ‘yan uwan juna ne ba kishiyoyi ba, zaka rantse ba’a taba samun matsala ba.. komai tare suke yi, tare suke cin abinci, su zauna suyi hira sannan su ba juna shawara a game da sana’o’in su dukda ita Ummi nata non-profit making organization ne.. A yanzu haka duk wani girki na gidan Maleeka take yi sai Inno da take taya ta.. A dalilin cikin Ummi da ya girma sossai bata barin ta tayi komai a cikin gidan… hatta ruwan wanka ita take hada mata.. Duk abinda Ummi take so shi ake yi a gidan. Maleeka da MK wani irin mugun kulawa suke ba Ummi.. ita take dauke da cikin amma kuma su suke rainon shi. Dayake MK is certain cewar ko baya nan Maleeka tana kula da ita yadda yakamata shiyasa ya cigaba da yin aikin shi normal.. har tafiya wadda ba mai tsawo ba yana yi.. Maleeka ce ta dauki nauyin siyo kayan baby… kamar dai yadda Ummi ta dage akan lallai baza’ayi scanning ba haka kuwa akayi.. don haka ne ma Maleeka ta dinga siyan kayan jarirai both na maza da na mata tunda dai basu san wanda za’a haifa ba.. kaya masu bala’in kyau da tsada wadanda 80% daga turai tayi order. Wani ikon Allah as time kept moving, MK became so nervous and anxious at thesame time.. a kullum yana cikin yi ma Ummi addu’a akan Allah ya sauke ta lafiya.. Cikin Ummi dai sossai yayi girma.. babu tantama ‘yan biyu ne a cikin.. idan su MK sun kira ta maman biyu kuma ta dage musu lallai daya ne.. A lokacin da cikinta ya shiga wata na takwas ne ta qara yin nauyi.. Gashi ita ba wani girma tayi ba amma cikin yayi girma sossai.. Ta kai a yanzu ko tashi zata yi da qyar, wannan ne ya sa MK da Maleeka suka bata extra care and special attention more than before. STORY CONTINUES BELOW Duk motsin da zata yi akan idanuwan su.. Likita ta basu shawara akan su dinga fita da ita tana dan zagayawa tunda walk is also a form of exercise and she needed it badly.. A wannan lokacin ne MK ya daina zuwa office gaba daya.. Haka zaka ga shi da Maleeka sun ja Ummi harabar gidan suna strolling.. Wasu lokutta da qyar take dawowa yayinda wasu lokutta take samun wuri ta zauna tace sam bazata iya tafiya ba… a qarshe dai MK ne yake dauko ta. A lokacin da cikin Ummi ya kusa shiga watan shi na tara ne Dr. Zeenat ta bada shawarar kafin EDD din Ummi kawai ayi Mata C-Section because it will come easier for her.. Aikuwa jin haka Maleeka ta ba MK shawarar kawai su fitar da ita turai ta haihu a can.. MK ya amince da shawarar Maleeka domin kuwa ya sani cewar zata fi samun kulawa a can.. ko da ya shawarci su Abba sunyi na’am da shawarar don haka ne suka shirya tafiya zuwa Dubai wanda Dr Zeenat ce ta hada su da wata shaharariyar Gynecologist a asibitin Saudi German Clinics Jumeirah… Nan da nan MK ya hada appointment. Dama dai harka ce ta kudi tuni aka gama komai. MK ya so Goggo ta bi su amma ta qi.. a cewarta zata cigaba da yi ma Ummi addu’a daga nan gida Nigeria don haka ne suka roqi Mamy akan ta bi su… they needed an elderly person with them because daga MK har Maleeka were nervous and anxious at thesame time.. Ko da suka sauka a Dubai daya daga cikin lafiyayyun Suites din Burj-al-Arab suka zauna.. Tuni likitar ta sanya musu date din da za’a yi ma Ummi C-Section. Abin mamaki hankulan su MK a tashe yake amma ita Ummi sam bata tayar da hankalinta ba.. Sossai ta qagara a yi C-section din ma ta huta. Ranar da za’a yi Hatta Mamy da take elder to all of them sai da ta nuna damuwa… Al’amarin ya kai Ummi ce take fadi musu kalamai masu sanyaya musu zuciya.. She kept telling them to pray for her… Gaba daya jikin su yayi sanyi a lokacin da aka shiga da Ummi dakin theater.. A wannan lokacin MK ji yayi ma kawai baya son haihuwar.. for the first time he felt he shouldn’t have insisted he wanted a child…5 Su dukan su suna nan suna ta zarya a waiting room suna ta addu’a ne Nurses biyu suka fito riqe da jarirai har guda biyu Mace da namiji kyawawa farare sol kamar mahaifiyar su.. At that moment MK freezing yayi a tsaye yana kallon kyautar da Allah yayi mishi… Yara biyu a lokaci guda… Runtse idanuwa yayi ya bude yayinda wasu hawayen farin ciki suka fara gangarowa daga idanuwan shi.. da alama bai ma san yana yi ba.. A dream come true for him.. MK dai bai dauki yaran ba sai da ya gan ta.. Uwar ‘ya’yan shi.. wadda ta bashi the best gift in his entire life- Ummi1 Masu karatu.. kalar farin cikin da MK yayi bai taba yin ko da rabin shi ba a duniyan nan.. He was beyond happy.. Mamy da Maleeka sunyi mamakin yadda duk ya bi ya rude.. Yaran sun kasance mishi tamkar wasu long lost treasures da ya gano a rayuwar shi.. ita kanta Ummi bata fahimci what she has actually done to him ba sai da ta bashi wadannan yaran.. Yayi ma yaran huduba da sunan iyayen Ummi.. wato Aishatu da Ibrahim. Sossai Ummi ta ji dadin sunan da ya sanya ma yaranta. Daga baya kuma ta dinga rusa musu kuka a dalilin tuno iyayen ta da tayi da kuma qannen ta da ta rasa wanda Allah ya dawo mata da su a matsayin ‘ya’yan ta. Dayake likitar ta riqe Ummi da babies dinta a asibitin har tsawon sati daya babu shiri dangi kaf da abokanen arziki suka biyo su Dubai din… da alama they couldn’t wait for them to return. STORY CONTINUES BELOW Hatta Hafsah sai da ta zo tun daga Switzerland da tsohon cikinta. Babu shakka wadannan yara sun shigo duniya da qafar dama domin kuwa sossai suka ga so da gata.. A koda yaushe MK yana maqale da yaran da kuma Ummi.. tabbas babu abinda suka fi Ummi da yaran shi muhimmanci a rayuwar shi. A wannan lokacin Maleeka ta qara yin da-na-sanin abinda tayi a baya… she would have been the one receiving the extra love and care but then, what to do right???2 Kafin a sallami su Ummi daga asibiti ne likita ta ba MK shawara akan ayi ma Ummi Contraceptive implant saboda ta samu lokaci sossai kafin tayi wani cikin.. Dalilan ta sune na daya Ummi is still very young sannan kuma ‘yan biyun da ta haifa zasu fi samun kulawa sossai idan she is physically, emotionally and mentally fit. MK ya amince da wannan shawarar domin kuwa shi kanshi baya so Ummi tayi undergoing phase din haihuwa anytime soon. Tunda ta bashi ‘yan biyu bugu guda, he is very much okay… Ko da suka dawo daga Dubai Mamy ta so Ummi ta zauna a gidan ta ko gidan Goggo zuwa wani dan lokaci sannan ta koma gida amma MK ya qi… duk wani abinda zai nisance shi da yaran shi da Ummi baya so don haka akan dole suka sauka a gidan su. Ummi dai ko da suka dawo babu wani taron suna da tayi.. ♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO A yau satin su biyu da dawowa daga Dubai. Ummi ce zaune a kan gadon dakin ta da safe tana cin waina da miyan taushe wanda Maleeka tayi mata tare da taimakon Inno. A wannan lokacin kuwa Maleeka tana zaune a kan gadon tana shafa ma Ameera mai yayinda take ta yi mata wasa.. ita kuwa Ameera sai kallonta take yi tana da dariya. Ameer kuwa wanda yake wurin Inno tana yi mishi wanka sai kuka yake yi. Ummi ce tace “amma dai Ameer mugun qazami ne… shikenan da zarar an sanya ka a ruwa sai kayi ta kuka” Maleeka tana dariya tace “wallahi kuwa.. ga ‘yar uwar shi nan an gama yi mata lafiya lau” Inno wadda take jin su ce tace “ai Ameera halin mahaifiyarta ta dauko.. Haquri da juriya” Maleeka tace “toh shi Ameer wa ya biyo?? ba dai baban shi ba don kuwa Honey yana da haquri sossai” Ummi tana dariya tace “wallahi ban taba ganin mutum mai sauqin kai irin shi ba..” Inno tace “ai kuwa ya kyauta ma kanshi.. ku kuma kun more miji..” Har aka gama yi ma Ameer wanka aka nade shi da towel kuka yake yi.. Sai da Maleeka ta karbe shi ne yayi shiru ya koma yana ta kallonta. Ji nayi Maleeka tace “Ammi a taimaka a ba Ameera abinci.. na san yanzu da ta sha zatayi bacci” Ummi ta turo baki tace “yanzu har ta fara jin yunwa?? ni kam na ga alama sai kun tsotse ni tas sannan hankalin ku zai kwanta” Maleeka da Inno suna ta dariya yayinda Inno tace “kiyi haquri Ummi.. kin ga shiyasa nake ta baki kunun nan kina sha..” A lokacin Ummi ta gama cin abinci ta miqe zata shiga bathroom ne Inno ta tattare kayan abincin sannan tace “bari ma in kawo miki kunun tunda baki sha ba..” Da sauri Ummi tace “don Allah kiyi haquri sai anjima.. wallahi na qoshi” Maleeka ce tace “eh toh Babu laifi tunda kin cinye wainar.. but seriously you need to eat plenty of food saboda ki samu energy na ciyar da yaran nan” STORY CONTINUES BELOW Ummi wadda take wanke hannun ta tana jin Maleeka tace “insha Allah Adda” Bayan ta fito ne ta dawo bisa gadon ta dauki Ameera ta fara shayar da ita. A lokacin Maleeka ta gama shirya Ameer tana riqe da shi yayinda tace “toh babana.. kayi haquri kadan idan ‘yar uwar ka ta qoshi sai ka sha kai ma kafin Abbun ku ya dawo mu tafi mu ba Ammin ku space itama ta huta” Ummi ce ta kalli Maleeka tace “wai yana ma ina ne? tunda ya fita bai dawo ba… ba dai ya je office ba? yau Saturday fa..” Maleeka tayi murmushi tace “ai ke ma kin san bazan bar shi ya je aiki ba.. lokacin da na raka shi dai yace mun zai je airport, like he went to pick up somebody.. I am not sure dai because yayi sounding kamar he didn’t want to share with me”1 Ummi tace “toh Allah ya dawo mana da shi lafiya” Maleeka tace “Ameen” A haka suka cigaba da random hirar su as usual. Bayan Ummi ta gama shayar da Ameer ne shima Maleeka ta dauke shi ta sa shi a cikin cradle din shi kamar yadda ta sanya Ameera cikin nata.. su biyun duk sun yi bacci. A haka suka cigaba da hira yayinda Maleeka take ta gyara ma Ummi dakin nata. Sallamar shi suka ji yayinda ya shigo riqe da yaro a hannun shi. Daga Ummi har Maleeka kallon shi suke yi cike da mamaki.. Ummi dai kallon yaron take yi kamar tana so ta tuno inda ta san shi.. ji nayi tace “wa nake gani kamar Mahmood din Murjanatu..”1 Maleeka ce tayi saurin fadin “Honey ina ka samo wannan cute…” Kamar daga sama Ummi ta jiyo muryarta tana fadin “Zainab ki bi ahankali kar ki fadi” Cikin ihu Ummi tace “Murjanatu??!!” Aikuwa da sauri ta sauka daga kan gadon har Maleeka tana fadin “ki bi ahankali dai.. your stitches” MK dai matsawa yayi yayinda Murjanatu wadda ta qarasa shigowa ta rugo a guje suka rungume juna. Ummi tana riqe da ita tace “Qawata ya akayi kika zo?? ya kowa da kowa a gida?? ya hanya? shine munyi waya shekaran jiya baki fadi mun zaki zo ba ko??” Maleeka da MK kuwa sai kallon su suke yi.. Ita kam har ta miqa hannu ta karbi yaron da yake hannun MK.. wato Mahmood Maleeka seems to like kids alot a yanzu.. babban burin ta bai wuce ta gan ta da Babyn ta ba ita ma.. Murjanatu wadda take ta murmushi tace “kiyi haquri Ummi nima fa jiya baban Zainab yace mun Hamma ya kira shi wai idan da hali ya bar ni in dan zo inyi miki kwana biyu.. shine fa yau muka zo” Ummi wadda tayi saurin kallon MK tana murmushi tace “thank you very much sweetheart.. this means alot to me” Murmushi yayi tare da fadin “anything for you Baby” yayinda ya qarasa wurin cradle din yaran shi wadanda suke ta bacci ya shafa cute faces dinsu sannan yayi excusing kanshi ya fita. A nan me kuma Murjanatu ta shiga gaisawa da Maleeka wadda take amsawa cike da fara’a… Ummi ta kalli Zainab tace “Ya Salam… Zainab ta girma wallahi” yayinda ta riqo hannun ta. Murjanatu wadda ta hango ‘yan biyu a cikin cradle din su ce tace “masha Allah” yayinda ta qarasa wurin su. ************* Zaune suke a kan gadon dakinta suna ta hira.. kayan motsa baki ne kala-kala baje a gaban Murjanatu. A lokacin kuwa ‘yan biyu sun farka yayinda Maleeka ta kwashe su harda yaran Murjanatu zuwa sashen MK.. STORY CONTINUES BELOW A cikin hirar su ne Murjanatu tace “amma dai Adda Maleeka tana da kirki.. babu wanda zai kalli yadda kuke yace kishiyoyi ne ku, kamar fa ba ita ta tsane ki ba a da..” Ummi tana dariya tace “ai abubuwa sun canza sossai qawata. Wallahi sai ma na baki labarin irin kyautatawar da ta dinga yi mun lokacin da nake da ciki… komai fa ita take yi mun. Yanzu haka har rainon yaran nan kusan ita da Sweetheart suke yi” Murjanatu tana murmushi tace “hmmm su Ummi kenan… na tuno lokacin da kika ce bazaku yi abinda ake yi a haifi yara ba.. harda wani cewa wai a matsayin Hamman ki zaki zauna da shi… sai ga ki har da ‘yan biyu” Ummi dai dariya tayi yayinda tace “ai bazaki gane bane qawata” Murjanatu ta harare ta tace “ni kuwa na gane komai… Allah dai ya bar ku tare. Mu kam babu abinda zamu ce sai Allah ya saka da alkhairi.. Hamma yayi mana abin arziki sossai kuma duk a dalilin ki.. wallahi kinyi sa’a a rayuwa.. Allah ya raya muku zuri’ar ku” Ummi tana murmushi tace “ameen qawata” Ta gyara zama tace “ban tambaye ki ba.. kin ji labarin su Daada kuwa??” Murjanatu ta dan bata rai sannan tace “gaskiya Ummi kamar yadda na fadi miki tunda muka dawo Yola ban sake ganin su ba amma dai wancan satin da muka je Rugange na ji labarin Abdallah yana nan yana caca da shaye-shaye, ita kuma Binto tayi aure amma ko kwana uku bata yi ba a gidan mijin ya sake ta a dalilin tana dauke da cikin shege ance yanzu haka ta tafi Lagos yawon bariki.. wasu sun ce ta zubar da cikin jikinta wasu kuma suka ce da shi ta tafi. Baffa kuma yana nan Daada ta daure shi tamau, sai abinda tace shi yake yi don haka duk abinda yake faruwa bai ce komai ba..” Ummi dai tunda Murjanatu ta fara magana take ta zabga salati.. kenan nothing has changed a gidan??? Ji tayi Murjanatu tace “Allah ya taimake ki da Hamma ya zo ya aure ki kafin Alhaji Buba.. qawata wallahi bayan auren ki da ya so yi Allah bai yi ba, Ya auri Mata sama da bakwai kuma duk ya sake su…” Ummi ta runtse idanuwa ta bude tare da sakin ajiyar zuciya tace “ai a duniyar nan bazan taba manta halaccin da Sweetheart yayi mun ba.. shiyasa bazan taba daina kyautata mishi ba a rayuwar nan” Haka dai suka cigaba da hira kala-kala… ********** Maleeka dai zama take yi tare da Ummi da Murjanatu suyi ta bata labarin rayuwar qauyen su Rugange… yawanci labaran duk na ban dariya ne.. haka take zama tana kwasar dariya. She really enjoyed Murjanatu’s Company… Sati daya kawai Murjanatu tayi a gidan amma sossai Maleeka ta saba da ita da kuma yaranta.. Har su Fatima idan suka zo tare suke zama su sha hirar su. Dayake an sanya Zainab makaranta a Yola ta waye sossai… hakan kuwa ya birge Maleeka matuqa. The credit goes to MK for bringing them out of Rugange village ya mayar da su cikin garin Yola. A lokacin da Murjanatu zata koma gida kuwa MK ya bata kudi masu yawan gaske.. Ummi ma ta bata kudi sannan ta bata wasu kudaden ta kai ma Baffan ta da kuma Malam Lawali. Maleeka har shopping tayi ma su Zainabu, kaya dayawan gaske.. MK ya ji dadin wannan abu sossai, Ya tabbatar Maleeka ta zama who he has always wished for her to be.. Bayan tafiyar Murjanatu kuwa suka koma daga su sai yaran su. As usual Maleeka sossai take taimaka ma Ummi wurin rainon ‘yan biyun.. Yaran kuwa sun saba da ita sossai. Ba sai an fada ba akwai wani special connection a tsakanin ta da ‘yan biyun.. Haka nan ko kallonta suka yi sai suyi murmushi ko dariya. Da alama dai sun san tana bala’in son su ne.. Duk wata hidima ta yaran, Maleeka tana kan gaba.. A kullum bata gajiya da yi musu hidima… Dukda Inno tana nan amma lokutta da dama ita take daukar dawainiyar su gaba daya.. Ummi dai kusan daga shayar da yaran babu wani abinda take yi musu. Ummi har tausaya mata take yi na yawan hidimar da take yi mata da ita da yaran ta.. Babban burin Maleeka a yanzu shine ta ganta da ciki itama ta haifi Baby… A yanzu Allah ya jarabce ta da son haihuwa amma shiru.. ♧♧♧♧♧♧♧♧ One year later!!! MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO Zaune take a kan Ottoman din dakinta yayinda take ta kallon shi da yadda yake ta kallon yaran nashi wadanda basu dade da yin bacci ba… as usual dai da taimakon Maleeka- Yaran sun saba sossai da Maleeka.. Suna sonta sossai.. Da zarar Ummi ta shayar da su toh fa shikenan sun gama da ita.. Maleeka dai ita take relieving Ummi wurin rainon yaran.. komai ita take yi musu.. A kullum Ummi tana cikin yi ma Maleeka addu’a akan Allah ya bata nata itama.. Toh gashi kuma har yanzu shiru…+ what is happening??? MK dai bai dade da dawowa daga ofis ba.. wani aiki ne ya tsayar da shi har qarfe tara na dare. Yanzu haka wanka kawai yayi ya nufi sashen ta don ganin yaran nashi kamar kullum. Ji nayi yana fadin “…kuyi haquri yau Abbu bai dawo da wuri ba gashi har kunyi bacci baku gan shi ba…” Ya karanto addu’oi ya tofa musu sannan yace “Allah ya kare mun ku” Ummi wadda take kallon shi tace “Ameen Abbun mu” Gani nayi ya sauka daga kan gadon yana murmushi yayinda ya dawo gefenta kan Ottoman din ya zauna. Qura ma juna idanuwa suka yi ba tare da sun ce komai ba.. Tabbas Ummi da MK are soulmates, they have a strong connection of minds, a mutual respect for eachother, an unconditional love and a total understanding of eachother… they have always been right there with eachother, side by side and they pray it continues to be like that till the end of time.. Ummi dai ganin kallon bazai qare bane ta ja kumatun shi tace “hey.. what is it??” Lumshe idanuwa yayi sannan yace “I love you” Tace “na sani ai” Gashin gaban goshinta ya shafa sannan ya bi gefen fuskarta yana ta shafawa… hakan ya sanya ta lumshe idanuwan ta yayinda take jin dadin abinda yake yi mata… Ji tayi yace “wai ni ban gane ba Baby.. na ga sai wani qara kyau kike yi.. kin gan ki kuwa??” Murmushi tayi tace “Sweetheart wanne kyau bayan yaran ka duk sun tsotse ni nayi losing weight..”1 Hannuwan shi a bisa wuyan ta down to her cleavage zuwa cikinta and finally bisa cinyarta wadda take bayyane a dalilin gajerar nightie din da ke jikinta… Ummi wadda ta shiga wani yanayi na daban ce ta riqe hannun shi da yake ta matse cinyarta da shi tace “Sweetheart please…” Yana kallonta yana murmushi yace “ke kyakyawa ce Ummi, A cikin ko wanne yanayi kina kyau- ko kina kuka, ko kina dariya, ko kina murmushi, ko kina fushi, ko kina yakushi na..” Zaro idanuwa da baki da sauri tace “what???” Kashe mata ido daya yayi yace “kin ma fi kyau a wannan lokacin Baby na..” Duka ta kai mishi a kafada yayinda ta Harare shi tace “hey… stop it” Fashewa yayi da dariya yace “toh na daina tunda baki son jin gaskiya but sincerely speaking you are and will forever be perfect.. to me you are an epitome of beauty” Ya matsa daf da ita zai yi mata kiss ne ta sa hannunta ta toshe bakin shi tare da fadin “ka manta yau Adda ce da kai???” Zare hannunta yayi daga bakinshi yace “ban manta ba… Good night kiss nake so” STORY CONTINUES BELOW Matsawa tayi sannan tayi mishi peck a kumatu tace “good night.. I love you” Ya ja kumatun ta tare da miqewa yace “thank you and I love you too” Har ya bar dakin idanuwan ta suna kan shi.. Bayan ya fita ne ta saki ajiyar zuciya tace “Allah ya bar mun kai miji na..” da sauri nace “Ameen Babyn sweetheart”1 Ah toh… ************* Tsaye take a gaban Vanity Mirror sanye cikin wata Sexy babydoll nighty mai shegen kyau… Fatar jikin ta sai sheqi take yi saboda kyau.. ga wani asirtaccen qamshi da ke fita daga kowanne saqo na jikinta.. In all she looked super gorgeous. Maleeka dai tayi kusan minti Goma a nan tsaye yayinda take ta kallon kanta.. Da na kalle ta da kyau ne na kula tana cikin tsananin damuwa.. Why??? Gani nayi ta dora hannuwan ta biyu a bisa cikinta yayinda ta runtse idanuwanta… Ban ankara ba na ga hawaye na bin fuskarta.. Tsawon mintuna uku tana ta zubar da hawaye wanda daga baya na ji muryarta cikin kuka tana fadin “me ke faruwa da ni ne?? why is this happening to me? how am I not able to conceive har zuwa yanzu??” Daga nan sai gani nayi ta juya da sauri ta nufi kan gadonta ta kwanta ta rushe da kuka. Cikin sallama ya shigo dakin.. Tsayawa yayi cak cike da mamaki ganin ta kwance tana kuka.. what is wrong with her??? Gani nayi ya shafa kan shi sannan yace “not again” Qarasa shigowa yayi ya nufi wurinta ya haye kan gadon tare da janyo ta jikin shi ya rungume ta.. Bayan ta yake dan bubbugawa alamar lallashi yayinda yace “Babe it’s high time you stopped this.. for how long zaki cigaba da kuka akan abinda baki da iko akai???” Qara mannewa tayi a jikinshi cikin kuka tace “Honey I just want a child.. Ina so in ga baby na nima, I just want to…” Da sauri yace “ssssshhhh… Babe please. Kiyi haquri insha Allah you will have a baby.. but still ki duba ki gani, we have worked hard over the past year.. even extra and still babu result.. I am still thinking we should see a doctor don ina ganin kamar wannan matsalar tana da alaqa da contraceptive pills din da kika sha…”3 Da sauri tace “No Honey ba pills din bane…” Da sauri ya dago fuskarta yana kallonta cikin ido yace “ban gane ba su bane ba… is there anything I need to know???” Maleeka wadda take a rikice bata ma san tayi wannan maganar ba.. ita dai ta sani cewar ba effect din pills din bane tunda after the last time da ta sha su ne ta samu ciki… Cikin da ta zubar!! Muryar shi ta ji yace “Babe akwai abinda yakamata in sani ne?? what do you mean by ‘ba pills din bane??’ toh meye??” Komawa tayi jikin shi ta kwanta yayinda ta fashe da sabon kuka tace “…uhm Honey abinda nake nufi shine wadannan pills din basu da side effect.. sai da nayi bincike sossai akan su sannan na sha” MK wanda yayi shiru yana sauraronta ne a ranshi yace “could she be barren??” Da sauri ya furta “No.. it’s not possible..” Cike da Mamaki Maleeka tace “Honey me kake fadi??” Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “Baby ki shirya gobe zamu je asibiti… and this time I wont take no for an answer” STORY CONTINUES BELOW toh fa!! Maleeka wadda take cike da fargaba bata ce mishi komai ba.. ta sani cewar idan tayi dragging this time zai iya yin fushi da ita. Gani nayi ya sauka daga kan gadon ya duqo ya dauke ta cak yace “for now zo mu je daki na in ga kwalliyan nan da kyau..” Dukda tashin hankalin da take ciki sai da tayi murmushi saboda yadda yayi maganar.. A haka suka nufi dakin shi inda suka gurji soyayya mai dadin gaske.. As usual he made her the happiest woman on earth.. Maleeka tana bala’in son kasancewa tare da MK because yana bata wani farin ciki wanda tasan bazata taba samun irin shi ba a ko wane wuri banda a wurin shi.. Dukda haka kuwa tunaninta bai gushe ba akan tafiyar su asibiti gobe.. Me zata tarar?? will everything be okay??? ********** Kamar yadda suka shirya zuwa asibitin washegari tun da safe suka je. Wildot Clinic suka je inda Dr Davis ya hada su da sabuwar Gyneacologist dinsu mai Suna Dr. Agnihotri a dalilin Dr. Zeenat ta tafi qasar Germany yin wani course na tsawon shekaru uku. Dr. Agnihotri dai asalin ta ‘yar India ce.. sossai ta qware a aikinta.. a dalilin qwarewarta ma da ta kalli mace take gane idan tana da ciki ko batada. She is one of the best Gynecologists… Ko da suka gan ta sunyi mata bayanin komai sannan tayi ma Maleeka running several tests.. ta sanar da su there is no need MK yayi undergoing any test tunda yana da matar da ta haihu. Dayake tests din da aka yi suna da yawa ne tace musu su dawo washegari su karbi result.. Haka nan suka tafi jikin Maleeka a sanyaye yayinda take cike da fargaban abinda result din zai yi revealing.. ♧♧♧♧♧♧♧ Washegari!! WILDOT CLINIC ASOKORO Zaune suke a ofis din Dr. Agnihotri suna sauraronta. Tana riqe da test result din Maleeka a hannunta ne tace “uhm Mr. Muhammad Kabir from the test result I have here, your wife is not barren and the contraceptive pills did no damage to her.. but..” ta dan yi shiru tana kallon Maleeka yayinda ta cigaba da fadin “…Madam have you ever had an abortion done???” Da sauri MK ya kalli Maleeka wadda tayi bala’in rudewa.. In a confused tone MK yace “how can she have an abortion done when she never gave herself a chance to conceive???” Dr. Agnihotri ta miqa ma MK report din yayinda tace “well from this result we discovered that your wife had a surgical abortion done on her and unfortunately Asherman syndrome happened”5 Cike da tsananin tashin hankali MK ya kalli Maleeka wadda tuni hawaye sun fara wanke mata fuskarta… shi gaba daya ma bai gane abinda likitar take fadi ba.. Dakatar da ita yayi yace “hey doc.. I am not understanding anything here.. what’s ashman syndrome..” Dr. Agnihotri tace “Its Asherman Syndrome Sir..” Cike da damuwa MK yace “yeah whatever.. just tell me already” Ita dai Maleeka kuka kawai take ta rusawa.. Dr. Agnihotri ta gyara Glasses dinta tace “Asherman syndrome is a rare complication that can occur after a woman has a surgical procedure, and it can potentially damage the uterine lining. The condition can cause scarring to develop in the uterine cavity. This can increase the likelihood that a woman may have a miscarriage or have problems conceiving in the future…” STORY CONTINUES BELOW Da sauri MK ya kalli Maleeka yace “Babe wannan ba test result dinki bane.. you were never pregnant, were you?? you never had an abortion done, did you??” Maleeka wadda take kuka jikinta har rawa yake yi ce tace “nawa ne Honey.. yes I was pregnant and yes I had an abor…” Tun kafin ta qarasa na ga ya dafe kanshi yayinda yake ta fadin “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. and you are just telling me now?? Maleeka kin san abinda kika yi kuwa??” Kalaman Maleeka sun soki zuciyar MK tamkar kibiya.. ashe ma ta taba samun cikin ta zubar? Rashin hankalin Maleeka har ya kai tayi destroying mishi unborn din shi intentionally? tambayar da yake yi ma kan shi ita ce… shin wai Maleeka tana son shi kuwa?? tana tausayin shi?? tana da tsoron Allah a zuciyarta kuwa??4 Hada hannuwan ta biyu wuri daya tayi tace “Don Allah Honey kayi haquri… wallahi…” MK ya girgiza kai tare da daga mata hannu alamar tayi shiru.. Ji yayi Dr. Agnihotri tace “Uhm Sir please calm down.. Asherman syndrome can be treated using a surgical procedure called an operative hysteroscopy…” Da sauri Maleeka ta kalle ta with so much hope yayinda ta cigaba da fadin “…It will be simple and hopefully successful.. A Small surgical instruments will be attached to the end of the hysteroscope and will be used to remove adhesions… The procedure is always carried out under general anesthetic. After the procedure, she will be given antibiotics to prevent infection and estrogen tablets to improve the quality of the uterine lining. A repeat hysteroscopy will then be performed at a later date to check that the operation was successful and her uterus is free from adhesions….” Shi dai MK tunda ta fara zancen ta baya jin komai.. kai da alama ma baya gane abinda take fadi. Tana kallon Maleeka tace “Well, it’s possible for adhesions to reoccur following the treatment, so after the treatment I will recommend waiting a year before trying to conceive to ensure that this hasn’t occurred” Gani nayi MK ya miqe tare da kallon Likitar yace “thank you doctor” Ba tare da ya kalli Maleeka ba ya juya ya fita daga ofis din. Dr. Agnihotri ce ta kalli Maleeka tace “it’s okay Mrs. Kabir… please stop crying. when you get the treatment done everything will be okay” Jikin Maleeka a sanyaye ta tashi tare da fadin “thank you doctor” Haka ta fita yayinda Dr. Agnihotri ta bi ta da kallo cike da tausayawa. *************** Zaune yake a cikin mota yana jiran ta.. idanuwan shi sunyi jajawur yayinda yake mamakin abinda Maleeka tayi. Wato kenan ma she was pregnant even before he married Ummi?? Bai ankara ba ya ji ta bude qofar motar ta shiga yayinda take ta kuka.. Ba tare da yace komai ba ya tada mota.. Ganin MK baya da niyyar yi mata magana ne yace “Honey don Allah kayi haquri..” Shi kam ko kallonta ma bai yi ba… Dukda bai bi ta kanta ba sannan dukda bai tambaye ta ba she just felt she needed to tell him what happened.. even though it was already late!! STORY CONTINUES BELOW Aikuwa anan ta fara bashi labarin yadda ta gano tana da ciki a wannan lokacin da yadda wata likita ta bata shawarar kar ta zubar har zuwa yadda ta tafi turai tayi having surgical abortion… da farko abortion pills ta sha amma cikin ya qi fita shine likitocin suka bata shawara akan tayi surgical abortion din kawai tunda she desperately wanted to take it out.. the truth is ba’a cika samun complication ba after a surgical abortion amma Maleeka got sooo unlucky!!4 MK dai har ta gama bashi labarin bai ce mata komai ba… Hakan kuwa ba qaramin firgita Maleeka yayi ba. Duk duniya a yanzu bata qaunar fushin MK.. tsoro fushin shi yake bata. Haka ta dinga bashi haquri tana kuka amma ko kallonta bai yi ba balle yayi magana.2 Toh fa… ♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO Ummi ce ta fito sanye cikin doguwar Riga ta atamfar Super wax mai bala’in kyau tana magana a waya. Qafarta sanye cikin wani designer flat shoe na Vincci.. Riqe take da wata designer handbag ta Louis Vuitton sai makullin motarta a hannun ta.. Idan ka ganta zaka san lallai ta huta.. fatarta sai sheqi take yi saboda kyau.. Jikinta yayi kyau kamar ba ita ce mai shayar da twins ba.. Gani nayi ta nufi wurin motarta qirar Mercedes Benz GLK-350 fara sol zata shiga.. Magana take yi a waya.. Ji nayi tace “Baraka I am on my way yanzu.. ki tabbatar kin hada komai kafin in qaraso don bazan dade ba.. na bar twins dina a gida..” Bata qarasa magana bane ta hango motar MK ta shigo gidan a fusace.. Da sauri tace “okay Baraka sai na zo..” sannan ta kashe wayar. Rufe qofar motar tayi ta nufi wurin da yayi parking motar a nan parking lot din. Zuciyarta ce ta buga a dalilin ganin MK ya fito ran shi a bace… Kai tsaye tace “Sweetheart me ya…” Kafin ta qarasa maganarta ne Maleeka ta fito tana ta kuka… Da sauri Ummi ta dawo wurinta tana fadin “Subhanalillah… Adda me ya faru?” Fadawa tayi jikin Ummi tana ta kuka yayinda MK ya wuce cikin gida ba tare da ya bi ta kansu ba. Ji nayi Maleeka tana fadin “Na shiga uku Ummi.. wallahi ban san ya zan gyara wannan kuskuren ba…” Ummi wadda ta zama confused ce tace “Adda ban gane abinda kike fadi ba…” ta janyo ta tare da fadin “zo mu shiga ciki” ************* Zaune suke a dakin ta yayinda take bata labarin abinda ya faru.. Tunda ta fara har ta gama kuka take yi yayinda Ummi tayi shiru tana sauraron ta.. Bata taba tausaya ma wani kamar yadda ta tausaya ma Maleeka ba a halin yanzu.. Gashi ontop of everything shi kuma MK yayi fushi da ita.. Gani nayi ta matsa daf da ita tayi hugging dinta tace “please Adda ki daina kuka kar zazzabi ya kama ki.. Nasan cewar abinda ya same ki da ciwo amma ki daure kiyi haquri.. this is surely one of Allah’s test and insha Allah zaki ci wannan jarabawar..” STORY CONTINUES BELOW Maleeka wadda kalaman Ummi suka fara sanyaya mata rai ce tace “Ummi kin ga Honey yayi fushi da ni.. na bashi haquri ya qi yayi mun magana, wallahi Ummi fushin Honey yana bani tsoro.. da me zan ji??” Ummi ta dago fuskarta ta fara goge mata hawaye yayinda tace “ki kwantar da hankalin ki.. tabbas fushi yake yi a yanzu amma kuma kin sani cewar bazai dade yana yi ba tunda mun sani cewar bai iya fushi ba… again he loves you so much and you will forever be his dearest Babe” Wannan maganar da Ummi tayi ce ta sa Maleeka yin murmushi bata shirya ba.. Tana kallon Ummi tace “nagode sossai Ummi.. after everything that has happened in the past, kin dauke ni tamkar ‘yar uwa.. you are always there for me in good and bad times, Ummi nagode sossai da irin kyautatawar da kike yi mun, I am…” Murmushi Ummi tayi tare da Jan kumatun ta tace “we are like sisters.. remember??” Maleeka tana murmushi tace “yes qanwata.. nagode qwarai” Wayar Ummi ce tayi ringing.. ko da ta duba sunan Baraka ta gani. Bayan tayi answering ne tace “Baraka I am so sorry.. wallahi akwai wani emergency ne da ya taso amma zan kira Umar (Lado) in ji if he is free sai ya zo..” Shiru ta dan yi sannan tace “okay Bye..” Maleeka ce tace “Ummi ki je mana tunda neman ki ake yi.. ba daga foundation din ki bane?” Ummi tana murmushi ta girgiza kai tare da fadin “No Adda.. Lado zai maye gurbi na a meeting din, idan an gama zai sanar da ni komai.. let me just call him” Ko da ta kira shi kuwa he wasn’t busy don haka ne yace kar ta damu zai je. Bayan ta gama waya da Lado ne Maleeka tace “ina twins suke ne? na ji su shiru..” Ummi tace “suna can wurin Daada.. yanzu haka na san duk sun fitine ta” Maleeka ta yunqura zata sauka daga kan gadon tace “bari in je in kwaso su toh..” Da sauri Ummi tace “haba Adda.. kiyi zamanki ki dan huta.. Yanzu abinda nake so da ke shine ki shiga bathroom ki watsa ruwa kiyi sallah sai in kawo miki abinci ki ci… afterwards zan kawo miki twins dinki.. kin amince??” Murmushi tayi tare da girgiza kai alamar eh. ********** MK ne kwance a kan resting chair na dakin shi yayinda idanuwan shi suke a rufe… Sossai yake cikin bacin rai. Tsawon lokaci yana a hakan domin kuwa tunda suka dawo ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya shirya ne ya koma kan kujerar ya kwanta… He is supposed to be in the office at the time saboda suna da Meeting amma ya kasa zuwa because ran shi a bace yake. Dayake dama Fahad ya san yana da commitment shi yayi chairing meeting din without even calling him because ya sani cewar tunda bai gan shi ba he wont make it. Ji yayi ana knocking qofar dakin shi amma yayi shiru.. Muryar Ummi ya ji tace “Sweetheart ya da rufe qofa harda key kuma? don Allah ka bude” Muryarta da ya ji a wannan lokacin kuwa sai da ta sa part of his anger yayi subsiding instantly.. Allah ya sani Ummi alkhairi ce a gare shi, he will forever be thankful to Allah da yasa ta shigo rayuwar shi. STORY CONTINUES BELOW Bai ankara ba ya ji tace “Sweetheart are you okay?? don Allah ka bude muyi magana… I….” Kai tsaye yace “hey just go” Yanayin yadda ta ji muryar shi ne ta rude.. Da sauri ta qara qwanqwaso qofar tace “Don Allah kayi haquri ka bude ni.. you are not okay, please…” Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “Ummi just go.. bana son ganin kowa. Ki tafi..”4 Jin haka kuwa ta juya abinta tana fadin “lallai abun nashi dagaske ne. ************* A yau haka aka yini a gidan shiru… banda kai da komowar twins din baka jin wani qwaqwarar motsi. Maleeka dai a dalilin yaran kusa da ita ne ta dan yi walwala.. Dukda damuwar da take tare da ita haka suka yini tare da yaran… A nan dakin Ummi ta shigo musu da abinci suka ci.. shima da qyar da tilastawar Ummin ta ci. Haka dai suka yini Ummi na ta fadi mata kalamai masu sanyaya rai… and it really helped! Wuraren qarfe tara da rabi na dare ne Inno tayi ma twins din wanka suka yi shirin bacci sannan suka maqale a wurin Maleeka.. Tana rungume da su har suka yi bacci. Ummi ta so ta kwashe twins din amma Maleeka ta hana ta… a cewarta she wants to feel them close to her. Sossai ta ba Ummi tausayi, tayi ma Maleeka addu’a Allah ya yaye mata damuwarta ya bata farin cikinta sannan ya cika mata burinta a rayuwar nan- give her a child!! Ummi dai dakinta ta koma don yin wanka tayi shirin bacci sannan ta dawo.. da alama itama a nan dakin Maleekan zata kwana. ************ Zaune take a gaban Vanity mirror din dakinta daure da dan qaramin farin towel tana shafa cream. Kusan minti biyar kenan da ta ji qamshin turaren shi.. ko da ta dago kanta ta cikin mirror ta hango shi tsaye daga kusa da qofa yana ta kallon ta amma tayi kamar bata gan shi ba.. Gani nayi ta janyo sprays ta fesa a jikinta sannan ta miqe zata wuce dressing room. Ba tare da ta kalle shi ba tace “please leave my room” sannan ta shige dressing room din.1 Mamaki ne ya cika MK wanda kuma daga baya na ga yayi murmushi… wato saboda ya kore ta dazu itama shine zata rama! Gani nayi ya bi bayan ta har cikin dressing room din yayinda ya tarar da ita gaban daya daga cikin wadrobe dinta tana qoqarin ciro Nightie din da zata sa. Bata ankara ba ta ji shi a bayanta, ya sa hannun shi a cikin gashin kanta yana yi mata wani gentle massage mai rikitarwa.. Bakin shi ya kai saitin kunnen ta yace “hey.. me nayi ne haka da ake kora ta?” Ummi wadda idanuwanta suke a lumshe tana jin dadin abinda yake yi mata ce ta saki ajiyar zuciya. Composing kanta tayi ta ture shi cikin masifa tace “ni ka qyale ni.. ka koma ka cigaba da fushinka” Qara hugging dinta yayi very tight ta baya yace “Baby ai ba da ke nayi fushi ba.. don Allah kiyi haquri akan abinda nayi miki dazu, I was angry ne..” Ummi dai fuskarta a tamke ta sa dukkanin qarfinta ta ture shi tare da juyowa ta nuna shi da yatsa tace “please leave me alone.. ” Zaro idanuwa yayi yace “how am i suppose to do that? don Allah kiyi haquri.. ko so kike zuciyata ta buga ne?? kin kuwa san yadda nake ji idan kika yi fushi da ni??” Tana kallon shi tace “ya kake ji??” Runtse idanuwa yayi ya bude sannan yace “…Zuciya ta zafi take yi, qwalwa na toshewa take yi, ji nake yi kamar wani bangare na jikina ya bar ni… Baby wallahi Ko da wasa kika furta mun zakiyi fushi hankalina tashi yake yi..” STORY CONTINUES BELOW Kai tsaye tace “Yadda kake ji itama haka take ji a yanzu… infact more than what you are feeling right now..” A fusace ya juya zai bar dakin yayinda ta bi shi da sauri ta tare shi sannan ta riqo hannuwan shi tace “Sweetheart please.. kayi haquri akan abinda Adda tayi maka, abinda tayi ya riga ya wuce kuma tayi nadama. A halin da ake ciki yanzu Adda can give up duk wani abu nata don ta samu haihuwa.. ta damu sossai. She has been crying tun da kuka dawo.. Yanzu fisabilillah da me zata ji?? da rashin tabbas a samun haihuwa ko kuwa da fushin ka?? ka sani cewar kai ne farin cikin mu a gidan nan, fushinka tashin hankali ne a garemu… Again, dukda na san tayi maka laifi kuma you have evry right to be angry but the situation right now is kai kana da yara already, ita fa?? don Allah kayi haquri ka sassauta mata…” MK dai shiru yayi yana kallon ta… Wai wacce iri ce Ummi??? why does she have a heart like this one?? Bai ankara ba ya ji ta shige jikin shi ta rungume shi very tight sannan tace “please.. please… please..” Shi kam Allah ya sani Maleeka ta bata mishi rai.. She was pregnant with his child amma ta zubar.. again she never told him about it sai kwatsam ya ji a bakin likita.. Maganar Ummi gaskiya ne, yana da yaran shi already and it’s the most important thing right now.. idan ma bai yafe ma Maleeka ba me zai yi? afterall shima bazai iya zama for long yana fushi da ita ba.. Soyayyar Maleeka a jinin shi take.. Hugging dinta yayi very tight sannan yace “shikenan komai ya wuce..” Breaking hug din tayi cike da murna tace “yauwa Sweetheart dina.. thank you very much. bari in sa kaya mu je wurinta..” Janyo ta yayi jikin shi yace “…not before I do this baby” Cikin rashin fahimta tace “what??” Hada fuskokinsu yayi ya shiga kissing dinta.. irin wanda ke rikita ta. Ummi kam bata san lokacin da ya zamar da towel din jikinta ba.. tuni ya fara romancing dinta ta ko ina wanda ya kai tsayuwa ya fara neman gagarar su.. Da ta ankara ne ta saita muryarta tace “Sweetheart please.. mu je mu ga Adda mu dawo tukun” Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “okay” Ya nuna ta da yatsar shi yace “amma you promise me zamu cigaba daga inda muka tsaya??” Ta duqa ta dauki towel dinta tana daurawa tace “nayi maka alqawari miji na..” Shi ya zabar mata Nightie din sannan ya taimaka mata ta sa sannan suka fita daga dakin. *********** Kwance take a gefen su tana ta kallon su yayinda suke baccin su cikin kwanciyar hankali. Tabbas ba ita ta haifi yaran ba amma sossai take son su.. ta shaqu da su sossai. Hawaye ne ke bin fuskarta yayinda tayi zurfi a tunani.MK ne ya turo qofar dakin ya shigo, Ummi tana biye da shi. Kai tsaye ya nufi wurinta ya zauna a gefen ta kan gadon sannan ya dan taba ta… Maleeka dai da sauri ta juyo ta gan shi zaune a gefen ta. Tashi tayi zaune tana kuka yayinda ta bude baki zata yi magana amma MK yayi saurin fadin “ssshhhh.. its okay. let’s leave the past in the past and move on” Gani nayi ta fada jikin shi yayi hugging dinshi very tight tana kuka. Gaba daya ma ta kasa magana. abinda ta sani shine zuciyarta ta dan yi sanyi da jin MK ya yafe mata.. atleast half of her problem is solved. MK ne yayi breaking hug din sannan ya fara goge mata hawaye yace “toh ta daina kuka haka mana ya isa.. ko so take ta tayar da yaranta daga bacci” Ummi wadda take tsaye ce tace “dayake ita ce ai ko sun farka bazasu yi mata rikice ba..” Maleeka tana murmushi ta kalli Ummi tace “thankyou very much for everything Ummi.. Kin yi mun abubuwa dayawa a rayuwa wanda bazan taba iya biyan ki ba… Allah ya saka miki da alkhairi kuma ya baki duk wani abinda kike nema” Ummi tana murmushi tace “Ameen Adda.. Ke ma ina roqon Allah ya baki abinda kike nema..” MK ya harare su sannan yace “Ni bazaku yi mun addu’a ba ko??” Ummi tace “Allah ya riga ya baka abinda kake nema sweetheart..” Cikin rashin fahimta yace “like seriously?? kamar me kenan???” Kai tsaye Maleeka tace “Ya baka Ummi, ya baka Maleeka sannan ya baka Ameer da Ameera.. what else do you want??” Ya ja kumatun ta yace “I want a baby from Maleeka.. kuma insha Allah zai bani. ki shirya gobe zamu koma asibiti akan maganar treatment dinki… let’s give it a try, what say??”1 Daga kai tayi ta kalli Ummi tana murmushi yayinda Ummi tace “I say yes.. Allah ya bada sa’a” Suka amsa da Ameen Two years later!! MK SODANGI RESIDENCE MAITAMA-ABUJA A yau da safe ne ta fito sanye cikin hijabi dogo har qasa mai hannu yayinda take riqe da makullin motar ta. Ameera da Ameer ne biye da ita sanye cikin school uniform dinsu yayinda suke rige-rigen isa parking lot as usual. Suna daf da sauka daga porch din gidan ne tayi saurin fadin “be careful kar ku fadi” Inno wadda take riqe da lunch box dinsu ce take dariya yayinda tace “ai yaran nan naki komai nasu sai sun yi gasa..”+ Maleeka tana dariya tace “ni matsalar ma yanzu Ameer ya riga ta ita kuma tayi ta kuka” Ko da suka isa wurin motar ji suka yi Ameer yana ta tsalle yana fadin “ni ne winner..” Ameera kuma ta turo baki tana ta rusa kuka. Da sauri Maleeka ta qaraso wurinta ta dauke ta tare da fadin “haba princess.. me ya faru take kuka?” Nuna Ameer tayi tace “Mom Ameer ne..” Da sauri Maleeka tace “toh ai ba ke bace last.. kin ga daga Ameer sai ke sai ni sai kuma Daada.. don haka Daada ce last” Gani suka yi ta kalli Inno tana murmushi tace “yeey Daada ce last..” Ameer ne ya miqa hannun shi yace “Mom nima ki dauke ni” Inno tana dariya tace “toh sarakan gasa” Maleeka tana murmushi ta bude mota ta sa Ameera sannan ta duqa ta dauki Ameer tace “toh kai ma na dauke ka.. idan kun dawo zan qara daukan ka tunda ka ga yanzu munyi lattin zuwa school ka ji??” Bayan ta sa shi a mota ne Inno ta zuba lunch box dinsu a motar sannan tayi ma yaran bye-bye. Har Maleeka ta shiga mota ta tayar ne Inno ta tsayar da ita tace “da akwai abinda zan taimaka miki da shi ne kafin ki dawo?” Maleeka tace “kar ki damu Daada.. je ki huta abinki, idan na dawo zan yi komai” Inno tace “toh sai kin dawo” Maleeka ta ja mota suka bar gidan. ●●● Flashback!! Kamar yadda MK yayi ma Maleeka alqawarin zasu koma wurin likita don ayi mata treatment shekaru biyu da suka wuce.. hakan aka yi. Anyi treatment din amma kuma wani ikon Allah har yanzu dai bata samu ciki ba. Over the past 2 years Maleeka ta sanya damuwa a ranta sossai akan rashin samun haihuwan nan.. har qasashen waje suka je.. likotocin ma ko da suka ji Dr. Agnihotri tayi treating dinta sun tabbatar musu da lallai aiki yayi kyau because she is one of the very best.. don haka kawai they should try harder and hopefully idan suna da rabo zasu haihu. Sossai Maleeka ta duqufa wurin addu’a akan Allah ya bata haihuwa.. ‘yan uwa da abokanen arziki sun tausaya mata matuqa yayinda suka cigaba da taya ta da addu’a. A cikin wannan shekarun zuwan su Umra da aikin Hajji sossai take ta addu’a tana kai kukan ta zuwa ga Allah amma har yanzu shiru… Maleeka dai har ciwon hawan jini ya kama ta a dalilin mugun damuwar da ta shiga.. MK da Ummi ne suka dinga kwantar mata da hankali tare da fahimtar da ita muhimmancin yarda da qaddara mai kyau ko marar kyau… A hankali kuwa ta rage damuwarta har ta haqura ta rungumi qaddarar ta kamar yadda ta zo mata..3 STORY CONTINUES BELOW Tunda twins din Ummi suka taso sun saba sossai da Maleeka.. wanda bai san su ba zai iya rantsewa Maleeka ce uwarsu domin kuwa they spend more time with her than they do with their Ammi… Ummi da MK sun ji dadin hakan domin kuwa ko babu komai suma sunyi playing major role wurin rage mata damuwarta.. Tuni dai sun koma Maitama da zama.. a cewar MK gidan su na Asokoro dukda babba ne it was not designed purposely for two wives. Wani danqararren gida babba mai kyan fasali ya gina.. Mai karatu ba sai na baka labarin kyan gidan nan ba domin kuwa gida ne wanda zaiyi wuya ka samu irin shi a Maitama presently.. Sossai ya kashe kudi amma fa gida ya tsaru iya tsaruwa. Business din Maleeka yana tafiya sossai, Hatta Collaboration din da ta so yi da Karen kane shekarun baya wanda tayi turning down sun dawo sun daidaita and it was a success.. Ummi ma Charity Foundation dinta yana tafiya daidai wadaida… sossai take tallafa ma yara wadanda basu da galihu. Tana samun support sossai daga wurin mutane da dama, organizations da private companies. (y’all know how it works..) Al-Ihsan foundation became popular ba a Abuja ba kawai hatta sauran northern states na qasar nan domin kuwa har other states tana kai tallafi. Tuni Lado ya kammala karatun shi.. Kamar yadda MK yayi mishi alqawari ya tura shi qasar Ingila don yayi jami’a a can.. Chemical Engineering yake karantawa a can din. Sossai ya mayar da hankali a karatun because he doesn’t want to let his brother in-law down. Jameela ta haihu last year.. ta samu dan ta namiji wanda ya ci suna Aliyu Haidar. Hafsah kuma tuni sun dawo Nigeria.. suna nan zaune a gidan su a Maitama tare da mijinta da ‘yarta Sophia amma ana kiran ta da Maama a dalilin sunan mahaifiyar Daddynta da ta ci. Tuni Maleeka ta shiga islamiyyar da su Ummi suke zuwa.. daga farko ta fara domin kuwa dama a baya da MK yake dan koya mata karatun addinin ba wani dauka take yi ba sossai, don ma ya dage mata ne a lokacin shiyasa ta dan san wasu abubuwan…. da taimakon Ummi tayi saurin picking up. Maleeka, Ummi, Jameela, Fatima, Hafsah da Dr. Bilkisu (dukda ba zama take yi ba) sun zama very close to eachother irrespective of their ages and the relationships they share… Closeness dinsu brought their husbands together and they have since being living a peaceful life together.. Wannan kenan!! ●●● MK SODANGI RESIDENCE MAITAMA Tsaye take a kicin din a gaban waffle maker yayinda take jira yayi.. bata dade da dawowa daga kai su Ameer school ba. Ummi ce ta shigo kicin din sanye cikin wata sleeveless material gown.. gashinta dunqule a tsakiyar kanta.. idan ka kalla da kyau zaka fahimci yanzu tayi drying din shi don kuwa bai ma wani gama bushewa ba.. Ji nayi tace “uhmm… na ji qamshin favorite dina” Maleeka wadda ta ciro waffles tana jerawa a kan plate ce tayi murmushi tace “I made it specially for you qanwa ta..” Ummi ta qaraso da sauri ta dauki daya tace “aikuwa na gode Adda.. wallahi ina son waffles, ban qi in ci shi ba koda yaushe” Maleeka tana murmushi tace “na sani ai.. duk lokacin da kike so zanyi miki” Ummi wadda ta kai waffles din bakin ta ce ta lumshe idanuwa tana taunawa tace “Allah ya biya ki Adda.. dagaske ko turawa da suka qirqiro wannan idan sun dandana naki sai sunyi miki salute” STORY CONTINUES BELOW Maleeka ta fashe da dariya tace “toh samu wuri ki zauna don na san babu abinda santi bazai sa ki yi ba..” Ummi ma dariya take yi ta zauna a kan daya daga cikin kujerun Island tace “yi haquri Adda ban fito na taimaka miki ba.. baccin ne bai zo ba sai bayan sallar asuba… gashi yau ban raka ku school ba” Maleeka wadda take yi mata wani irin kallo tana murmushi tace “it’s obvious ma baccin bai ishe ki ba qanwata.. ya akayi Honey ya sallamo ki this early?”4 Ummi wadda ta turo baki tace “I ran away..” Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda Maleeka tace “haba dai Babyn sweetheart.. kin manta jiya ya dawo daga tafiya? 2 weeks fa baya nan..” MK dai a jiya ya dawo daga America.. Asali dai he went on a business trip ne tare da Fahad na tsawon sati daya, bayan an gama kuma ya tsaya kallon Survivor Series (pay-per-view) wrestling match yayinda Fahad ya dawo Nigeria abinshi.. Ummi ta girgiza kai tace “amma dai kin san cewar shi ya ga damar yin 2 weeks din ko? kar ki manta fa ya tsaya kallon wrestling ne..” Maleeka wadda take dariya tace “wallahi abun har mamaki yake bani.. ace mutum ya kashe kudade masu yawan gaske ya siya ticket don kawai ya kalli kokuwa.. is it even normal??” Gyaran muryar shi ce ta sa suka juyo da sauri suka gan shi tsaye a bakin qofar kicin din yana kallon su.. Qura mishi idanuwa suka yi cike da so da qauna.. Sanye yake cikin three quarter sweatpant da polo T-shirt, sai baza qamshi yake yi.. Gashin kanshi da na fuskar shi sun sha gyara gwanin ban sha’awa tamkar wani baqin balarabe.. Tabbas MK kyakyawan namiji ne, hatta matan nashi bazasu nuna mishi kyau ba sai dai haske. Qarasa shigowa kicin din yayi yace “wannan kallon da kuke yi mun fa?? lafiyar ku kuwa??? first na tarar ana magana na and now kun sa mun idanuwa… why??” Ummi da Maleeka suka kalli juna suna murmushi yayinda Ummi tace “because we love you.. ko Adda??” Maleeka ta kashe mishi ido daya tace “very much” Cike da jin dadin kalaman su ya nufi wurin Maleeka yayi mata kiss a kumatu yace “how was your night?” Lumshe idanuwa tayi sannan tace “it was fine Honey.. I missed you” Ya dauki waffle ya kai bakin shi yace “me too Babe..” Gani nayi ya dago waffle din da ya rage a hannun shi yace “this is delicious” Tana murmushi tace “thanks.. bari in hada maka Cappuccino dinka” Yace “Go ahead my love..” Ta kalli Ummi tace “qanwata.. tea ko??” Ummi ta girgiza kai alamar ‘eh’ Yau din girkin Ummi ne amma kuma Maleeka ce a kicin din.. haka take kasancewa a gidan MK. Bazaka taba gane girkin waye ba saboda sun dauki juna tamkar ‘yan uwa a yanzu.. kowacce tana relieving ‘yar uwarta whenever the need arises.. MK wanda ya zagaya zai zauna ne ya bi ta bayan Ummi.. bata ankara ba ta ji ya ja gashin ta wanda har sai da tace “ouch Sweetheart..” Da sauri ta kalle shi yayinda ya kashe mata ido daya yace “that’s for running away..” Maleeka ce take ta yi mata dariya yayinda ta dinga turo baki. Bayan ya zauna ne yace “my prince and princess sun tafi school ban gan su ba.. I really did over slept kenan” Maleeka ce tace “aikuwa sun so ganin ka su ma.. they kept talking about all the things da suka ce ka siyo musu.. Allah dai ya sa ka siyo” Gani suka yi ya shafa kan shi sannan yace “Ya salaam… wallahi na manta” STORY CONTINUES BELOW Ummi tana dariya tace “ghen ghen ghen… Abbu is in trouble today”1 Girgiza kai yayi yace “serious trouble I swear..” Maleeka ta ajiye Cappucino a gaban shi sannan ta ajiye musu tea ita da Ummi ta kwaso fries din da tayi ta ajiye… Ummi kam har ta ma kusa cinye waffles din nata. Bayan ta zauna ne tace “it’s not late ai.. kawai ka siyo musu kafin su dawo daga school” Kai tsaye MK yace “ai babu inda zan je yau babe.. I am so tired wallahi” Ummi ta bude baki zata yi magana ne wayarta tayi ringing yayinda na ga ta duba.. Sunan Baraka secretary dinta ta gani. Ji nayi tace “Excuse me” Maleeka tace “Go ahead” Ko da tayi answering tace “lafiya lau..” Daga nan tayi shiru tana sauraron Baraka.. Gani nayi ta miqe tsaye da sauri tare da zaro idanuwa tace “what.. dagaske?? tun yaushe aka aiko??” Daga MK har Maleeka kallonta suke yi. Ji sukayi tace “Ya salaam… okay, ki aiko mun da invitation din gida yanzun nan” Bayan ta kashe wayar ne ta kalli MK da Maleeka wadanda su ma ita suke kallo. Muryarta tana rawa tace “guess what.. my foundation received an invitation from the first lady… that she wants to see me today” Maleeka ta zaro idanuwa tace “OMG dagaske??? matar shugaban qasa?? today??” Ummi tace “Wallahi Adda, wai ashe invitation din was on my desk tun shekaran jiya, saboda ban je ofis bane shiyasa ban sani ba” MK yana murmushi yace “Baby this is good news fa.. I am so happy for you” Ummi wadda take a rude tace “toh ai ni jikina duk yayi sanyi ma wallahi sweetheart.. ko meyasa take nema na??” Kai tsaye Maleeka tace “toh ba sai kin je ba zaki ji ko menene?? biko je ki shirya don Allah..” Ummi tace “ai Adda tare zamu je.. kema fa kin san bazan iya zuwa ni kadai ba” MK wanda ya kula jikinta yayi sanyi ne ya riqo hannunta yace “relax Baby.. na tabbatar it’s nothing that you cant handle… you will be okay..” Ummi ta dan yi murmushi tace “nagode Sweetheart” ta kalli Maleeka tace “Adda aikuwa yakamata mu kira Hafsah, Adda Jameela, Adda Fatima da Adda Bilkisu mu je tare ko?? kar su ji labarin mun je su yi ta mana qorafi” Ni kuwa nace toh fa🤣 Maleeka tace “ai kam it’s a good idea… qarfe nawa ne meeting din??” Ummi tace “she said by 2:00pm.. kin ga akwai time da zasu shirya ko??” MK wanda yake kallon su yana kwasar dariya yace “wato zuga zakuyi mata kenan..” Ummi tace “Sweetheart dama ce fa muka samu.. gwara mu je yawon bude ido a cikin gidan shugaban qasa.. ya ma kuke kiran gidan??” Maleeka tace “Villa..” Ummi tace “yauwa Villa.. ai tare da ‘yan uwa na zan je” Cike da tsokana tace “kai ma idan zaka je ka shirya mu je don nasan baka taba zuwa ba..”1 Maleeka ce ta fashe da dariya yayinda yayi murmushi yace “idan na je roqon ta zanyi ta bani daya daga cikin yaranta in aura..” Ummi da Maleeka suka zaro idanuwa suka ce “whaaat??” Cikin rashin damuwa sannan with all seriousness yace “yes.. and I am sure zata bani because I am handsome, charming, rich and hardworking.. ” Kafin ya rufe bakin shi ya ji sun kai mishi duka a kafadun shi wanda har sai da yayi ihu yace “ouch.. meye haka??” STORY CONTINUES BELOW Suna tsaitsaye a gefen shi cikin bacin rai ne Ummi ta nuna shi da yatsa tace “wallahi baza mu je da kai ba..” Maleeka tace “daga mu bazaka qara wata ba..” Yana dariya yace “hey relax.. wasa nake yi. don Allah ku dan matsa baya…” Fashewa da dariya suka yi yayinda Maleeka ta duqo tayi mishi kiss a kumatu tace “I love you” Ummi ta birkita gashin kan shi tace “bari mu je mu fara shiryawa.. ka zauna a gida ka huta abin ka, ka ji??” Girgiza kai kawai yayi yana murmushi.. *************** Tare suka fito daga gidan yana riqe da hannuwan su… da alama dai rakiya ya fito yi. Ummi da Maleeka sun bala’in yin kyau. Wani tsadaden leshi ne a jikin su iri daya amma kowa da kalar nata.. dinkin dogayen riguna ne simple. Simple set na tsadadun Gold jewelry ne baje a jikin su… they looked classy and elegant… Gani nayi sun nufi daya daga cikin motocin Ummi. MK ne yayi saurin fadin “da wannan motar zaku je?” Ummi tace “yes Sweetheart.. meyasa ka tambaya?? Yana murmushi ya fiddo wani key daga aljihun shi yace “because I have a better idea.. ku je da waccan” Da sauri suka juya direction din da ya nuna musu… Nikuwa nace ‘whoa.. It’s the freaking latest Baby Range Rover Evoque..’ Gani nayi sun zaro idanuwa yayinda Maleeka tace “kai amma kuwa ka kyauta Honey.. perfect” Ummi tace “Allah dai yayi mu zamu fara dana wannan motar” MK yana dariya yace “toh ai na ga Villa zaku je.. Yakamata ku je a matsayin Queens din the one and only MK Sodangi..” ya kashe musu ido daya sannan ya cigaba da fadin “…I am sure you wont find this car a cikin Villa considering the fact that shugaban qasar namu baya cherishing luxury kamar predecessors dinshi”2 Fashewa suka yi da dariya yayinda Maleeka tace “wallahi fa Honey.. mutumin kam kamar kaska” hahahaha… a bakin Maleeka muka ji!! Ummi ce ta karbi key din.. dama dai a kullum idan zasu fita tare da Maleeka ita take driving.. Ita dai dama Maleeka bata wani damu da tuqa mota ba idan har akwai wanda zai ja ta. Bude ma Ummi qofa yayi ta shiga ya rufe sannan suka zagaya da Maleeka ya bude mata.. Tana shirin shiga ne na ga yayi saurin riqo hannunta ta juyo tana fuskantar shi.. Gani nayi ya shafa fuskarta yace “Babe me ke damun ki?” Tana kallon shi tace “nothing.. me ka gani??” Yace “na ga kamar kin dan rame ne.. you look pale. kin yi ciwo ne da nayi tafiya??” Ko da na kalli Maleeka da kyau nima na kula ta dan rame infact she looked a bit sick… what happened???1 Murmushi tayi sannan tace “na dan yi zazzabi kwana hudu da suka wuce Honey..” Gani nayi yana ta shafa fuskarta zuwa wuyan ta kamar wanda yake examining dinta.. cikin damuwa yace “and you didnt tell me? kin kira doctor?? did you go to the hospital??” Tana murmushi tace “it wasn’t serious Honey.. na sha PCM kuma qanwa ta took very good care of me so I didn’t need to see a doctor.. ban fadi maka ba because I didnt want to get you worried” Ta nuna jikinta tace “but hey.. lafiya na qalau dagaske” Ya girgiza kai yace “uhm.. okay” Bayan ta shiga motar ne yace “please idan zaku dawo ku biya store ku siyo ma yara na abubuwan da suka ce in siyo musu.. I really dont want to disappoint them” STORY CONTINUES BELOW Ummi ce tace “me da me suka ce ka siyo musu?” Yana murmushi yace “I swear I dont know.. I thought lokacin da suke lissafa mun kun ji su ai” Maleeka tana dariya tace “dont worry.. na san dukkanin abinda suka ce ka siyo musu” Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “thanks Babe.. ai dama na san babu wani abin yaran da yake skipping mind dinki..”1 tana murmushi tace “they are very dear to my heart.. I adore them so much” Ummi ta riqo hannunta tace “and we adore you so much more Mom..” Maleeka tayi dariya tare da fadin “thanks Ammin mu” Wayar MK ce tayi ringing.. ko da ya fiddo wayar daga aljihun shi sunan Fahad ya gani don haka ne ya kalli matan nashi yace “toh my angels.. sai kun dawo.. all the best and enjoy yourselves” Maleeka ce tace “thanks” Yana murmushi ya rufe qofar sannan ya dan matsa yayi answering… Yana kallon su har suka bar gidan sannan ya wuce cikin gida.. Gani nayi yana dariya yace “….yes abokina, wai tayi inviting dinta by 2pm and she decided to take all of them with her.. funny right??” ♧♧♧♧♧♧♧♧ Kamar dai yadda suka tsara tare da su Jameela, Fatima da Hafsah suka je.. Dr. Bilkisu tana asibiti don haka bata samu zuwa ba. A dalilin pass din da yake hannun su ne ya sanya basu samu matsala ba wurin shiga Aso Villa.. Har lounge na office din first lady aka yi musu iso… murna fal a cikin su yau ga su a gidan shugaban qasa. Sai da suka yi kusan minti talatin a zaune ne ta shigo cikin shiga ta alfarma tare da security dinta wadanda suka rufa mata baya.. Dukkanin su suka sanya mata idanuwa.. Matar da formerly a TV suke ganin ta amma yau ga ta live a gaban su…4 Cike da fara’a ta amsa gaisuwar su Ummi sannan ta umurce ta da ta shigo office dinta. First lady dai tayi mamakin ganin cewar Ummi ce mai wannan foundation din.. she was thinking zata ga wata elderly mace amma sai ta ga sabanin hakan… she was really impressed. Asali dai wani grant ne Federal Government take shirin bayarwa don tallafa ma talakawa so it decided to look for the best Charity foundations wadanda ake alfahari da su don ta basu.. fortunately for Ummi, her foundation was among wadanda aka zaba. Nan da nan ta cike wasu takardu yayinda aka bata cheque na 50million naira.. Ummi dai ganin wannan abu tayi kamar a mafarki… bata taba sa ran cewar zata samu this much ba a lokaci daya.. Tayi murna sossai domin kuwa ko banza kudaden MK zasu huta tunda dai it’s a non-profit organization.. banda don tana samun taimako daga wurin different organizations da companies da kuma other random people, he would have been the only source of income.. First lady ta ba Ummi contact na PA dinta akan she should let them know idan tana facing matsaloli don a taimaka mata because she is doing a good job for the country.. Sossai ta dinga yi ma First lady godiya. Har hotuna suka dauka tare harda su Maleeka ma.. an cika su da souvenirs kala-kala sannan suka tafi. Tunda suka fito daga Aso rock kuwa hira suke ta yi cike da murna.. albarkacin Ummi sun samu shiga gidan shugaban qasa sannan sun ga matar shugaban qasa.3 ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ FAHAD USMAN RESIDENCE MAITAMA Zaune suke a dakin Fatima suna ta dudduba turarrukan da aka kawo mata daga Sudan. Dama dai sunyi zasu je su zaba kamar kullum idan aka kawo mata. STORY CONTINUES BELOW Suna dubawa suna hirar zuwan su Aso Rock da suka yi da kuma Grant din da Ummi ta samu. Hafsah ce ta dago wani turare ta sunsuna tace “kai gaskiya wannan yayi..” Jameela ce tace “bani in ji” Hafsah ta miqa mata. Ko da ta sunsuna tace “gaskiya yayi.. nima zan dauke shi” Maleeka wadda take zaune a gefen Jameela ce tace “Jay bani in ji..” Jameela ta miqa mata… aikuwa tana karba ta kai hancin ta sai ji tayi zuciyarta tana tashi.. Basu ankara ba suka ga ta jefar da turaren yayinda ta miqe a guje ta nufi bathroom.. Hankulan su Fatima a tashe duk sun rude. Ummi ta bi bayan ta a guje tana fadin “Adda lafiya?” Ta tarar da ita tana ta kakarin amai… A haka Ummi ta riqe ta tana ta yi mata sannu. Bayan ta gama ne ta kuskure bakinta ta wanke fuskarta. Ummi tace “Sannu Adda… ba dai zazzabin ba kuma??” Maleeka ta dan yi murmushi tace “I dont think so Ummi.. qamshin turaren ne dai bai yi mun ba” Ummi wadda take riqe da ita ce ta janyo ta suka fito. Su Jameela ne suke ta yi mata sannu tana ta amsawa.. Kan Gadon Fatima ta zauna yayinda suke ta kallonta.. Ummi ce tace “Adda ko dai mu kira likita ne?” Maleeka tace “No Ummi..” Fatima ce tace “are you pregnant??” Da sauri Maleeka ta kalle ta cikin wani yanayi yayinda zuciyarta take ta bugawa… Ummi wadda ta cika da murna tace “dagaske Adda?? Ya Salam… Allah yasa she is..” Hafsah ce tace “….wait it’s possible fa. Ya Maleeka you look pale dagaske plus kin dan rame ma..” ta kalli Jameela tace “ko ni kadai ce na kula da hakan??” Jameela wadda take kallon Maleeka tace “gaskiya it’s possible.. nima fa sai yanzu na kula da yanayin ta” Maleeka ta harare su tace “I dont think so ‘yan uwa… kawai fa..” Kafin ta qarasa magana ne Fatima tace “…just take a pregnancy test to confirm.. ai there is no harm in doing that ko??” Miqewa tayi ta shiga bathroom dinta ta fito riqe da pregnancy test strip ta miqa mata tace “try it Maleeka..” Jikin Maleeka kuwa yayi mugun sanyi a yanzu.. abinda ta dade tana nema a rayuwarta, abinda har ta fitar da ran samun shi a rayuwarta… idan dagaske she is pregnant ya zata ji a ranta?? ya MK zai ji a ranshi??? ya iyayenta zasu ji?? idan kuma ba shi bane fa? Muryar Ummi ta ji tana fadin “Adda please kiyi trying..” Maleeka ta karba tace “idan mun je gida zanyi.. yanzu dai ki tashi mu tafi. kin san zamu biya store kuma kin ga su Ameer sun kusa closing daga school gashi sai mun mayar da su Jay gida ma..” A haka dai suka tafi yayinda suke ta addu’a Allah yasa she is pregnant… ♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE MAITAMA Kwance yake a kan three seater na babban falon shi yana kallon wrestling yayinda suke hira da matan shi. Tuni ‘yan biyu sun yi bacci domin a qa’idance basu wuce qarfe tara na dare sunyi bacci. Hirar grant din da first lady ta ba Ummi suke yi. Maleeka tana zaune a qasa yayinda take jingine da kujerar da MK yake kwance.. ita Ummi tana zaune a kan kujera one seater. STORY CONTINUES BELOW Ji nayi Ummi tana fadin “…ai Sweetheart na ji dadin grant dinnan domin akwai wani project on my mind amma kuma da na lissafa sai na ga kudin zasu yi yawa shiyasa nayi suspending.. abu kullum sai dai ka bani in bayar” MK yana murmushi yace “Baby you should have informed me ai.. it’s no big deal. idan ma na kasa ai ga Hajiya Maleeka nan sai ta taro mu” Gaba daya suka fashe da dariya yayinda Maleeka tace “anya Honey zan iya taro abinda ka kasa??? sai dai in bada tawa gudumuwar” Cike da tsokana yace “haba LEEK.. babu qasar da kayan ki basu je ba fa..” Maleeka tana dariya tace “haka ne Honey amma kuma ai all credit goes to you.. kai kayi funding komai tun daga farko har yanzu kuma kana yi” ta riqo hannun shi tace “I will forever be grateful..” Kissing hannun ta yayi yace “anything for you my little one..” Tana murmushi tace “qatuwa da ni kake kira na little one…” Yana murmushi yace “har ki tsufa I will continue to see you as that little cute girl..” Ya kalli Ummi wadda take kallon su tana murmushi yace “ita kuma Hajiya Millionnaire will always be my..” Kafin ya qarasa maganar shi suka fashe da dariya.. Ummi tace “Hajiya Millionnaire kuma??? Sweetheart baka jin magana wallahi..” Yana murmushi yace “toh Baby ai ke yanzu fa kin zama babbar Hajiya.. muna zaune fa first lady ta aiko miki da invitation..” Maleeka tana dariya tace “gashi albarkacin ta mun samu shiga Villa mun ba idanuwan mu abinci..” Haka dai suka cigaba da random hirar su kamar kullum. Ban ankara ba na ji Ummi tace “Adda… mu je??” Ummi dai tunda suka dawo gida take ta matsa ma Maleeka akan ta yi pregnancy test din amma kuma Maleeka kept telling her sai anjima.. da alama tsoro take yi ya dawo negative!! Kafin Maleeka tayi magana ne MK yace “ina zaku je?” Maleeka tayi saurin fadin “babu ko ina Honey.. wasu kaya ne da aka kawo mun shine ta matsa tana so ta gani” Ummi ta turo baki tace “toh Adda ki nuna mun kawai in ya so bazan qara matsa miki ba..” Da sauri ta sauka daga kan kujerar ta koma kusa da Maleeka tace “please Adda…” MK ne yace “ni dai a bani Cappuccino dina first” Gani nayi Ummi ta miqe da sauri tace “bari in kawo maka Sweetheart..” ta kalli Maleeka tace “daga nan sai mu je ko Adda?” Maleeka ta girgiza kai tace “ni kam ban taba ganin mai nacin ki ba… toh shikenan” Ummi tana dariya tace “yauwa Adda..” ********** Tsaye take a dakin Maleeka tana ta kai da komowa yayinda take jiran fitowarta.. Sossai ta qagara ta ji news din kamar ita ce mai cikin ko in ce kamar ita tayi shi ma!!1 Qarar bude qofar bathroom ta ji wanda ya sanya ta juyo da sauri.. Gani nayi ta zaro idanuwa a dalilin ganin Maleeka a tsaye riqe da test strip din tana rusa kuka.. why is she crying??? A guje ta qaraso wurin ta tace “Adda lafiya kike kuka?? what happened? please stop crying..” “I am pregnant Ummi…” abinda ya sanya Ummi yin shiru kenan.11 Zaro idanuwa tayi tace “what?” daga nan kuma ta saki wani irin murmushi tace “Alhamdulillah.. Congratulations Adda.. finally our wait is over..” Rungume ta tayi sannan tace “Adda this is the best news ever.. meyasa kike kuka??” Cikin kuka Maleeka tace “nima ban sani ba Ummi.. gani nake yi kamar ba dagaske ba… wallahi na cire rai a samun haihuwa Ummi.. Nayi tunanin Allah yayi fushi da ni shiyasa yake punishing dina for things I have done.. I..” Da sauri Ummi ta toshe bakinta tace “dont say that Adda.. Allahu gafurur- raheem, Lokaci ne bai yi ba shiyasa amma yanzu da lokacin yayi gashi nan kin samu. Dama fa an ce mahaqurci mawadaci, Gode ma Allah zakiyi ba kuka ba Adda.. Allah ya sanya albarka! cant wait to see Abbu’s face when he finds out” Maleeka wadda take ta sakin ajiyar zuciya ce tace “nagode Ummi.. You are one of the best people I have ever met a rayuwa ta..” Wayar Ummi ce tayi ringing yayinda ta duba ta ga sunan shi. Ko da tayi answering ji tayi yace “wai har yanzu ba’a gama ganin kayan bane?” Tana kallon Maleeka tana ta murmushi tace “yi haquri sweetheart.. gani nan” Bayan ta kashe wayar ne ta riqo hannun Maleeka tace “Adda in roqe ki wata alfarma??” Tace “go ahead” Ummi tace “please kar ki fadi ma Sweetheart cewar you are pregnant..” Zaro idanuwa Maleeka tayi tace “why???” Ummi tana bubbuga hannun ta tace “you trust me right??” Maleeka wadda ta zama confused and curious ce tace “yes I do.. but..” Ummi ta saki hannun ta tace “then please dont tell him..”5 ♧♧♧♧♧♧ Two days later!! MK-TECH SOFTWARE COMPANY MAITAMA Zaune yake a ofis dinshi yayinda yake ta kallon tulin birthday gifts din da staff din shi suka bashi moments ago.. A yau dai birthday din MK, kamar kowanne shekara shi din ba tunawa yake yi ba amma well wishes from F&F, messages da gifts din da yake receiving daga wurinsu suke tuna mishi.. Tunda ya tashi daga bacci ya fara ganin text messages na happy birthday.. Mutanen da bai yi expecting zasu aiko mishi messages ba sun aiko mishi. Abba da baya qasar ya tuno da shi ya kira shi yayi wishing dinshi, Mamy da Hafsah sun Kira sunyi wishing dinshi, su Daddy sun kira shi sunyi wishing dinshi.. hatta Lado da yake wata qasar shi ma ya kira shi yayi wishing dinshi… but surprisingly matan shi didn’t. Yayi expecting matan shi zasu yi wishing dinshi kafin ya bar gida.. especially Maleeka tunda a dakin shi ta kwana! infact he thought ma zasu hana shi fita just like they did in the previous years amma abin mamaki they didn’t…+ Ko da ya shigo ofis din shi he received a warm welcome from his staff.. sunyi mishi waqar happy birthday sannan suka yanka mishi cake.. they each gave him a birthday gift, kai hatta cleaners din kamfanin MK sai da suka bashi gift but his wives?? Cike da disappointment na ji yace “sun manta kenan??”4 Fahad wanda ya shigo ofis din ya gan shi a wannan halin ne ya dan taba shi yace “abokina ya aka yi ne na shigo ina magana hankalin ka yayi nisa? lafiya kuwa??” MK ya saki ajiyar zuciya cike da damuwa yace “abokina I swear I am not happy… I am sad” Fahad ya zauna yace “subhanalillah.. akwai abinda muka yi maka ba daidai bane?? didn’t you like the birthday treat we gave to you??” MK ya girgiza kai tare da fadin “not that abokina.. on the contrary I liked it kuma nagode sossai..” Ya shafa kan shi da hannuwan shi biyu sannan yace “my wives.. they didnt wish me at all. Gaba daya sun manta ko meye yau…” Ya nuna tarin birthday gifts din da suke cikin ofis din yace “Ka duba ka gani fa I just received birthday gifts from all of my staff… hatta qaramin ma’aikaci a office dinnan- cleaners and even securities sun bani gifts but…” Fahad yana murmushi yace “haba dai MK yanzu akan wannan ne ka shiga damuwa?? please stop.. ba lallai bane sun manta, it’s possible they are planning something for you” Girgiza kai yayi yace “nope, I dont think so. Ka san cewar muna breakfast da safen nan suna hira na ji Ummi tana tambayar Maleeka today’s date sai na ga Maleeka ta duba wayarta ta fadi mata.. guess what they did afterwards? they started talking about some event they are going to attend next tomorrow or so… wallahi saboda haushi da na ji ban ma gane me suke fadi ba” Fahad ya dan yi shiru sannan yace “kayi haquri abokina.. I still think surprising dinka suke so su yi..” Kafin yayi magana ne wayar shi tayi ringing.. ko da ya duba sunan Maleeka ya gani. STORY CONTINUES BELOW Murmushi ya saki tare da kallon Fahad yace “finally, daya daga cikin su ta tuna” Da yayi answering ne yace “babe how far..” A dayan bangaren tace “fine Honey.. uhm dama ina so ne in fadi maka akwai wani saqo da za’a aiko mun ta ofis dinka.. please help me receive it” Ran MK yayi mugun baci da jin abinda Maleeka tace. Kai tsaye yace “toh…” Bai jira komai ba ya kashe wayar tare da jefar da ita yace “I cant believe this..” Fahad ma kasa magana yayi domin kuwa shima abin ya dan bashi mamaki.. he remembered last year on his birthday ma hana shi zuwa ofis suka yi kuma ranan he had an important meeting but still he didn’t attend.. Me yasa suka yi mishi haka??? ♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE MAITAMA Wuraren qarfe biyar na yamma MK ya dawo gida. Da ganin yanayin shi ka san he is sad.. Suna zaune a main falon qasa suna ta hira ne ya shigo gidan.. Masu aiki ne biye da shi riqe da gifts din da staff din shi na ofis suka bashi. Ummi da Maleeka wadanda suka miqe tsaye suna yi mishi sannu da zuwa ne suka ga gifts kala-kala ana ta shigowa da su. Kai tsaye Maleeka tace “masha Allah.. yau Abbu yayi ma twins shopping” Ummi tana murmushi tace “ai Adda ina gani kamar shopping din harda mu.. wadannan ai sunyi ma su Ameer yawa..” MK dai ji yayi kamar ya mutu don haushi…2 Bai san lokacin da yayi tsaki ba ya wuce ba tare da ya kalle su ba.. Bayan ya haura sama ne suka kalli juna sannan suka mayar da idanuwan su kan kayan da aka shigo da su. Ummi ce tace “kamar in zauna inyi ta budewa wallahi Adda… Allah ya sani ina son bude gifts” Maleeka tana dariya tace “aikuwa na tuna na last year duk ke kika bude su..” Ni kuwa nace wato dai basu manta ba.. but why didnt they wish him??? *************** Wuraren qarfe tara da rabi na dare yana kwance a kan gadon dakin shi.. Wutan dakin a kashe suke amma ba bacci yake yi ba.. MK dai tunda ya dawo daga sallar isha’i ya shige daki abin shi.. Hatta dinner bai yi ba yau.. yana ta fushi yayinda yake mamakin yadda matan nashi suka yi watsi da al’amarin shi. Yaran nashi ma sun jira fitowar shi su yi wasa kamar yadda suka saba amma shiru.. a haka har lokacin baccin su yayi. Yayi zurfi a tunani ne ya ji an turo qofar dakin shi a hankali. Qamshin turarenta da yake bala’in so ne ya cika shi.. Cikin muryar ta mai kashe mishi jiki ne tace “laaa.. Sweetheart ashe har ka kwanta?” STORY CONTINUES BELOW Kunna wutan dakin tayi sannan ta qaraso wurin shi kan gadon.. Ba tare da ya bude idanuwan shi ba ya juya mata baya.. Ummi tana murmushi ta haye kan gadon ta kwanto kan kafadar shi sannan ta fara jefa mishi kisses dinta masu kashe mishi jiki.. Hannunta ta jefa cikin gashin kanshi tana birkitawa cikin wani irin salo yayinda ta kai bakinta saitin kunnen shi tace “Happy birthday Sweetheart” Wani mugun sanyi ne ya ratsa MK jin tayi wishing dinshi.. a ran shi ne yace “atleast ita ta tuna..” Dukda ya ji dadi har a ranshi sai ya matse.. Gani nayi ta sa hannu ta juyo shi da qarfinta suna fuskantar juna.. har a wannan lokacin idanuwan shi a rufe suke. Tana murmushi ta fara goga fuskarta akan nashi yayinda take ta sakar mishi kisses.. tun yana resisting har ya kasa daurewa. A hankali ya fara mayar mata da nashi salon kisses din domin kuwa Ummin shi is irresistible.. Muryar shi qasa-qasa yace “baby ashe baki manta ba?? wallahi har nayi fushi..” Tana murmushi tace “Yi haquri Sweetheart.. ina shirya maka wani special suprise gift ne shiyasa..” Tana wasa da sajen shi tace “mu je in nuna maka??” Yana murmushi yace “okay baby.. I love you” Ta ja kumatun shi tace “I love you more..” Ko da ta miqe tsaye gani nayi ya qura mata idanuwa yana qare mata kallo.. Sai yanzu ya ga kayan da ke jikinta… Sanye take cikin wata simple sleeveless black jumpsuit.. Sossai ta yi mata kyau domin kuwa tayi revealing duk wani curve na jikinta.. One thing she has managed to do is get back in shape bayan ta haihu.. idan ka kalli Ummi zaka rantse bata taba haihuwa ba.. asali ma shape dinta qara fitowa yayi sossai. Ganin yadda ya kafa mata idanuwa ya qi tashi ne tace “ya haka?? ka dai san bani da qarfin daukar ka ko??” Fashewa yayi da dariya ya miqe tare da janyo ta jikinshi ya rungume ta very tight yace “baby you look extremely beautiful.. I love this dress” Tana murmushi tace “thank you Sweetheart..” Hannuwan shi ne suka fara yawo a jikinta wanda hakan ya sa ta fara yin laushi.. tuni ya hada bakin shi da nata ya fara kissing dinta passionately.. Kusan tsawon minti biyar suna abu daya… Tuni har ya fara sauke hannun rigarta yayinda ta ankara tare da cafko hannunshi.. Da sauri ta zare bakinta daga nashi ta tura shi baya har ya fadi kan gado. Kafin yayi magana ne tace “Sssshhhh… not now Sweetheart” Ta janyo wani blindfold da ke kan bedside drawer dinshi ta nufi wurin shi ta zauna kan cinyar shi sannan tace “kayi haquri zan sa maka wannan” Cike da mamaki yace “but why?? I thought you..” tace “sssshhhh… kar kace komai please” Bayan ta rufe mishi idanuwa da blindfold din ne tayi kissing dinshi a baki sannan ta qura ma kyakyawar fuskar shi idanuwa. STORY CONTINUES BELOW MK ne yace “Baby ki manta da gift dinnan and let us just continue our business here…” Tana dariya tace “no Sweetheart.. ina mai tabbatar maka cewar gift din da zan baka zai fiye maka wannan business din dadi..” A ranshi ne yace “what could be sweeter than her at this point in time?” Haka dai ta riqo hannun shi suka fito yayinda yake ta qorafi akan idon shi yana ciwo.. ita kuwa sai dariya take yi mishi. Bai anakara ba ya ji tace “okay.. we are here. zaka iya cirewa..” Tun kafin ya cire ya jiyo qamshin ta mai dadin gaske.. Da sauri ya cire blindfold din hoping to see the gift amma kuma sai ya ga sabanin hakan.. Lo and behold!! Qamshin wadda ya ji din itace a gaban shi… Maleeka Sanye take cikin wata black strapless shoulder sequins mermaid gown wadda ta bala’in yi mata kyau.. Gashin kanta ya sha gyara ya kwanta a kan kafadun ta.. Murmushi yayi tare da matsawa yayi mata kiss yace “wow.. Babe you look immaculately beautiful… I love your dress” Tana murmushi tace “thank you Honey” Shiru ya dan yi kamar yana wani tunani.. Ummi da Maleeka ma kallon shi suke yi yayinda suke ta qoqarin matse dariyar da ta zo musu. Ji suka yi yace “uhmm.. I am a bit confused here…” Ya kalli Ummi yace “Ina gift din?” Tana murmushi tace “gata nan a gaban ka..” In a more confused tone yace “you mean Babe?? itace gift din?? shine harda blindfold? I mean.. you are kidding me right??” Wannan karon Maleeka ce tace “No Honey.. come here” Matsawa yayi kusa da ita yayinda ta janyo hannun shi ta dora a kan cikinta tace “here is your gift Honey.. your birthday gift..” Tana kallon shi cikin ido tace “I am pregnant.. we are going to have a child insha Allah” Kamar wanda aka yi ma shocking na ga ya zare hannun shi daga kan cikin ta ya dan matsa baya yace “wait what??” Da sauri ya kalli Ummi wadda take murmushi yayinda ya kalli Maleeka yace “you mean..” sai kuma yayi shiru… Da sauri ya janyo ta jikin shi ya rungume ta very tight yayinda yace “Ya salaam.. Babe you are pregnant..” Wani irin mugun farin ciki ne ya ratsa MK.. A dream come true for him finally his Maleeka is pregnant with his child.. Breaking hug din yayi yana kallon fuskarta yace “finally babe..” Yayi kneel down a gaban ta yayi hugging cikinta yace “Alhamdulillah… Allah nagode maka. My wife is pregnant” Wani sanyi ne yake ta ratsa Maleeka yayinda ta cika da murnar ganin yadda MK yake cikin tsananin farin ciki.. ashe haka wannan feeling din yake da dadi?? Bata san lokacin da hawaye suka fara wanke mata fuska ba… sheshekar kukan ta ne ya ankarar da MK yayinda ya dago kanshi ya ga tana kuka. STORY CONTINUES BELOW Da sauri ya miqe tsaye yace “hey.. why are you crying?? you are suppose to be happy. Allah ya bamu kyauta.. cant wait to tell the world that my Babe is gonna give me a child” Da sauri ya share mata hawaye sannan ya hada bakin shi da nata ya fara aika mata da saqon kisses dinshi masu haukatar da ita.. tuni ta mayar mishi da martani… Ummi wadda take tsaye a gefe ce tayi gyaran murya wanda yasa suka ankara.. Cike da tsokana tace “toh lovebirds ko dai zaku matsa daga ciki ne???” Maleeka tana murmushi tace “no Babyn Sweetheart.. yau ke ce mai Honey..” Da sauri Ummi tace “na bar miki Adda.. this celebration shouldn’t end here.. infact both of you will agree with me that it just got started, right??? ina zuwa..” Kafin suyi magana suka ga ta juya ta fita.. dawowa tayi riqe da key ta miqa ma MK tace “a dakin Adda zaka kwana yau” Ta kalli Maleeka tace “kiyi haquri yau na hana ki shiga dakin ki.. I was setting it up for this moment ne. It’s all yours now” MK dai maimakon ya karbi makullin sai ya hada da hannunta ya janyo ta gaba daya yace “thank you very much.. this is surely the best birthday gift ever” Tana murmushi tace “I am glad you liked it Sweetheart.. fatan mu Allah ya sauke Adda lafiya” Gaba dayan su suka ce “Ameen” Maleeka ce tace “uhmm.. dinner fa? na ga kin dafa abinci dayawa and you are…” Ummi tana murmushi tace “naku yana dakin ki Adda..” Ta kalli MK tace “Happy birthday to you once again and congratulations ka kusa zama sabon Abbu… Good night” ta kalli Maleeka ta kashe mata ido daya sannan tace “Good night Adda”3 MK dai har ta fita kallon ta yake yi yana mamakin halin ta… Ummi is a young girl amma Allah yasa tana da hankali sossai.. what she did is not something any other random person will do. Juyowa yayi yace “is there anyone like her on earth?” Maleeka tana murmushi tace “I doubt.. I am glad you found her” Yana murmushi yace “and I am glad you are pregnant my Babe.. I am so happy” Bata ankara ba ta ji ya dauke ta cak sun wuce dakin ta. A bakin qofar dakinta ya sauke ta sannan ya sa key ya bude qofar dakin.. Ko da suka shiga gani nayi sun zaro idanuwa a dalilin ganin yadda Ummi ta mayar da dakin Maleeka.. It looked exactly like a honeymoon suite.. Cike da mamaki Maleeka tace “na shiga uku.. yaushe tayi duka wannan??” Ta kalli MK tace “she is overly nice.. isn’t she??” Murmushi yayi yace “I am speechless..” Itama murmushi take yi tace “she surely is the best thing that has happened to us Honey.. Zuwan Ummi cikin rayuwar mu alkhairi ne.. she is an angel” STORY CONTINUES BELOW Janyo ta yayi ya rungume ta yace “You are an angel too Babe… I love you so much” Daga nan suka fara romancing juna cike da shaukin so.. Sunyi nisa ne ta ankara da abincin da Ummi ta ajiye musu kuma ta san bai ci abinci ba and she wouldn’t want Ummi’s effort to go in vain. Bakinta ta kai saitin kunnen shi tace “Honey abinci fa??” Muryar shi qasa-qasa yace “na qoshi..” Cikin shagwaba tace “ni kuma ina jin yunwa Honey.. I think wannan Babyn mai sa mutum cin abinci ne” Murmushi yayi yace “hey, okay toh mu je mu zauna in baki” Ko da suka zauna shi yayi serving abincin.. Abinci ne kala-kala Ummi ta dafa amma all in small quantity.. daidai yadda zasu iya ci. A dalilin bala’in birge shi da abincin yayi bai ma san lokacin da ya fara ci ba.. Maleeka kuwa ta dinga yi mishi tsiya na yadda yace bazai ci ba sai gashi har ya fi ta ci.. One thing da abincin Ummi is that its irresistible.. ko da mutum baya jin yunwa akwai wani force da yake jan mutum towards her food.. her food is no doubt delicious!! Bayan sun cinye ne ta zuba mishi Cappucino dinshi wanda har yana mamakin yadda Ummi ta hada komai da ta san zasu buqata. Yana sha suna hira… hiran Ummi da kuma unborn din su. Daga nan kuma suka yi reflecting akan rayuwar su- yadda suka taso, soyayyar su, and all the good things that happened in their lives. Ko da suka koma kan gado tana kwance a jikin shi suna ta hira.. in between kuma yana tambayan ta idan cikinta yana ciwo ko wani abu.. MK is no doubt a caring husband and she is blessed to have him!! ************ Aikuwa washegari da news din cikin Maleeka ya bayyana, Sossai iyayen su suka yi murna.. musamman Mummy da Daddy. Finally zasu samu jika. Haka su Jameela ma sunyi murna matuqa.. Maleeka will finally get to see her own child. Ko da Dr. Agnihotri tayi examining Maleeka ta ga komai normal, Cikinta yana zaune lafiya and everything will be ok.. Ita kanta tayi ma Maleeka murna domin kuwa ta san irin damuwa da tashin hankali da ta shiga na rashin samun haihuwa. Maleeka dai ta ga so da kulawa ta musamman a wurin MK da Ummi. Motsi kadan idan tayi sai sun nemi sanin how she is feeling.. Su Ameer kuma qara matse mata suka yi.. idan ba Maleeka zata yi musu abu ba toh fa an shiga uku.. they became very close to her fiye da yadda suke a baya.. Haka itama ta qara zama very close to them. Sossai take son yaran, suna bala’in sa tana jin fadin feeling of being pregnant. Tun Ummi da MK suna complain na yadda take wahalar da kanta wurin dawainiyar su har suka haqura suka qyale ta.. dayake dai cikin nata ba mai bata wahala bane, ita har mantawa ma take yi akwai shi don haka babu wata hidimar ‘yan biyun da bata yi musu. Amma fa banda hidimar yaran babu abinda suke bari tana yi.. komai yi mata suke yi. A kullum tana kan yi ma Ummi godiya na abubuwan da take yi mata na alkhairi.. STORY CONTINUES BELOW A yanzu ta gane cewar lallai Kishiya abokiyar zama ce ba abokiyar fada ba…2 My people.. shin haka abun yake??🤣8 ♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE MAITAMA A yau Sarurday.. Gaba dayan su suna gida. Kwance yake a kan daya daga cikin throw pillows na kujerun babban falon shi a qasa yayinda twins din suke maqale a wurin shi suna ta wasa da gashin kanshi as usual.. News yake kallo amma at the same time yana hira da matan nashi yayinda yaran nasu suke zuba musu nasu zancen kala-kala. Maleeka ce kwance a kan cinyar Ummi wadda take zaune a kan three-seater kujera yayinda take yi mata gentle head massage… Ameer da Ameera sai labarai suke yi musu na teachers da friends dinsu na makaranta. Suna yi suna Jan gashin MK wanda idan Ameer ya kamo wani part sai Ameera ta sa rigima akan ya bar mata.. Sai faman raba fada yake yi. Maleeka wadda take ta yi mishi dariya ce tace “Abbu dai ya shiga uku.. ana ta competition a kan shi…” Ummi tace “da rabon sai anyi massage don kuwa yadda suke jan gashin nan nashi dole kan shi yayi ciwo..” Yana murmushi yace “Gashi kuma sun cika mun kunne da surutu.. ni kam har yanzu ba gama gane maganar su nake yi ba. I swear teachers dinsu na school suna qoqari” Ummi tace “wallahi nima ba duka maganar su nake ganewa ba..” Maleeka tana dariya tace “haba don Allah, yanzu meye baku ganewa a maganar yaran nan? aikuwa na ga sunyi qoqari.. akwai yara their age fa da ko magana basu yi. a’a wallahi.. yara na sun iya magana sossai.. babu abinda suke fadi da bana ganewa. a shekara uku suna magana haka ai kam sun yi qoqari” MK yace “toh ai dole ki gane komai nasu tunda kullum suna maqale da ke..” Haka dai suka cigaba da random hirar su. Wayar Ummi ce tayi qara alamar text message ya shigo.. Janyo wayar tayi ta duba.. Gani nayi ta dan bata rai sannan tace “yau kuma message din daga UNICEF gaba daya???” tayi tsaki tace “haka MTN ke takura ma mutane da messages din banza.. yanzu fisabilillah ya za’a yi UNICEF ta turo mun message kamar ta san ni?” Ummi dai ta san about UNICEF tunda tana running NGO pertaining childern. Maleeka wadda ta ji tace UNICEF ce tayi saurin fadin “bani in gani Ummi..” Ta miqa mata wayar yayinda ta cigaba da yi mata massage. Ihu suka ji Maleeka tayi yayinda ta tashi zaune.. Gaba dayan su suka dago suna kallon ta harda ‘yan biyu.. Ji suka yi tace “Ya salaam… what???” MK ne yace “babe what is it??” Ta kalli Ummi sannan ta kalli MK cike da murna tace “ku saurara ku ji” Gyaran murya tayi sannan ta fara karanto musu saqon kamar haka: Dear Mrs. Umm Aimaan Kabir, We are pleased to inform you that due to the great deal of effort that Al-Ihsan foundation has put towards ensuring a positive difference in the lives of the poor and needy Children in your country, UNICEF has donated a sum of $450,000 to your foundation. STORY CONTINUES BELOW Your Cheque and some relevant documents have been forwarded to you via Courier services. We hope your foundation will strive to continue to provide humanitarian and developmental aid to children in your country. Executive Director, United Nations Children’s Fund. Henrietta H. Fore. Tunda Maleeka ta fara karantawa MK ya zaro idanuwa.. Ji nayi yace “450,000 US dollars?? kun san nawa kudin Nigeria??? Roughly N174m fa..” A gigice Ummi ta miqe tare da fadin “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. Anya ba kuskure suka yi ba?” Gaba dayan su fashewa suka yi da dariya yayinda Maleeka tace “kuskure bayan ga sunan ki sannan kuma ga sunan foundation dinki?? dama fa UNICEF tana bayar da donations to all countries of the world, kamar yadda federal Government ta ga qoqarin da kike yi haka suma suka binciko suka gano ki..” Ummi wadda ta bi ta rude ce tace “toh amma kudin da yawa Adda..” Maleeka tace “kin ga fa darajar kudin su da namu ba daya bane.. a wurin mu tabbas kudi ne masu yawa amma a wurinsu kamar 450,000 naira ne.. biko relax” MK wanda ya kula jikin Ummi yayi sanyi ne ya qaraso wurinta yayi hugging dinta tare da fadin “congratulations Baby.. I am proud of you” Cike da tsokana yace “within a week kinyi bagging N224m.. lallai wannan shekarar kin yi arba da laylatul-Qadr, there is no doubt about it…” Maleeka ta fashe da dariya tace “tabbas.. Babbar Hajiya Millionnaire. I am so happy for you, aikin alkhairin da kike yi shine Allah yake saka miki.. you surely are a great inspiration” Ummi dai ganin al’amarin dagaske ne sai ta fashe musu da kuka.. Yau ita Umm Aimaan, wadda ko makaranta bata taba zuwa ba.. ita ce da tarin kudi haka, she got all of it as a result of her charity foundation… the NGO that is a non-profit organization, Wanda a kullum sai dai ta karba a hannun MK da kuma donations da take samu ta taimaka ma yara marassa galihu, sai gashi ta samu wannan tarin kudaden a dalilin hakan. Wato tun a duniya ta fara ganin reward din Good work din da take yi. Ta sani cewar da iyayen ta suna raye they would be so proud of her. MK??? Shine sanadin duk wani abinda ta samu a duniyar nan.. tunda ta hadu da shi ta samu sauyi a rayuwarta. Ita ba kowa ba ya aure ta, ya so ta tsakani da Allah, ya taimaki rayuwarta, ya taimaki rayuwar duk wani wanda yake tare da ita da wanda ya taba kyautata mata a rayuwa. Shine ya gina mata foundation din yayi funding activities din da take yi gaba daya… All credit goes to him! her husband… her soulmate.. her everything Muhammad Kabir Sodangi. Ji tayi yace “baby stop crying mana.. kin cancanci duk wani abinda kika samu.. even more” Cikin kuka tace “No Sweetheart.. na samu komai a duniyan nan a dalilin ka” Tayi pointing at qirjin shi tace “you are the reason for everything that is happening to me.. bazan taba daina yi maka fatan alkhairi ba.. I am so grateful..” Daga nan kuma ta qara fashewa da sabon kuka. Haka dai suka dinga lallashin ta… hatta ‘yan biyu sai da suka dinga bata haquri har Maleeka tana fadin “Allah sarki basu gane cewar Ammin su ta zama Babbar Millionaire ba shiyasa take ta kuka” wannan maganar kuwa ta ba MK dariya sossai. *********** Ko da su Abba suka ji labarin abin arzikin da ya samu Ummi sunyi mata murna sossai sannan sun sanya albarka.. Goggo ma kuka ta dinga rusawa tana mamakin yadda Allah yake ta sauya ma Ummi rayuwa.. ko a mafarki bata taba tunanin Umminta zata kai wannan matsayin ba. Gaba daya Family and friends were proud of what she has achieved!! ♧♧♧♧♧♧♧ “A soul mate’s purpose is to shake you up, tear apart your ego a little bit, show you your obstacles and addictions, break your heart open so new light can get in, make you so desperate and out of control that you have to transform your life, then introduce you to your spiritual master” Again, Love is magical, it makes you do things you would never have imagined you could do. True love is a lifetime pack of magic, it never ends, there’s beauty in every little moment you share…!!! ♧♧♧♧♧♧♧♧ Seven Months later!! It’s been seven Months.. Rayuwa ta cigaba da tafiya yadda ya kamata… ‘Zaman lafiya’ shine ya kasance Motto din gidan Muhammad Kabir Sodangi. A lokacin da Ummi ta karbi kudaden da UNICEF suka aiko mata tare da wadanda First lady ta bata sossai ta rikice.. tabbas zata dade tana taimakon yara marassa galihu da su toh amma kuma komai daren dadewa wata rana zasu qare idan ba’a juya su. One thing was for sure a lokacin, tana so ta fara profit making business domin kuwa tana buqatar cash inflow for smooth running of her Charity foundation in the near future.. Bai kamata ta cigaba da depending solely akan MK ba idan sun qare nan da shekaru dayawa masu zuwa.. he wasn’t complaining amma kuma ai bai dace ta cigaba da karbar hard earned money dinshi tana juyewa a non-profit organization ba.+ It wasn’t difficult for her to decide wane irin business zata fara yi.. Tunda she was not privileged to go to school she decided to build one.. Ko da ta nemi shawara a wurin mijinta da abokiyar zaman ta Maleeka, instantly suka bata green light. It was a welcoming idea to all members of the family- their parents. Yes.. Ummi tana da kudin da zata iya gina qatuwar makaranta wadda zata fi kowacce makaranta kyau a garin Abuja.. Zata iya hiring best teachers har daga turai.. Zata iya qawata makarantar in such a way that all the Rich kids of Abuja will surely want to attend and it will mean alot of cash inflow for her that she can use for smooth running of her NGO.. Da haka ne akayi putting komai into motion.. Legal and financial formalities were completed and cikin qanqanin lokaci BOOM… Al-IHSAN INTERNATIONAL SCHOOL came into existence. Qatuwar makaranta.. makarantar da ta fi kowacce makaranta girma a garin Abuja… musamman aka dauko teachers turawa da larabawa.. an zuba duk wani abu na buqatar dalibai a makarantar.. everything is to the comfort of pupils and students of the school. Tsarin ginin makarantar kamar Zane.. Mai karatu, makaranta dai ko turai sai haka.. dayawa mutanen da basu san asalin mai makarantar ba sun yi tunanin turawa ne masu ita.. AL-IHSAN INTERNATIONAL SCHOOL ta zama makarantar da kowanne yaro a Abuja yake son zuwa.. Cikin qanqanin lokaci makarantar ta samu karbuwa. Tabbas zaka kashe kudi amma fa akwai result domin kuwa malamai ne aka samu standard and very competent. Yanzu haka wata uku kenan da makarantar ta fara functioning. Tun daga kindergarten through nursery and primary har junior and senior secondary! Daga yaran ta har yaran su Hafsah, Fatima, Jamila da na Bilkisu makarantar aka mayar da su.. and their tuition fee and all other expenses is free har su gama!! ♧♧♧♧♧♧♧ MUHAMMAD SODANGI RESIDENCE MAITAMA Zaune suke a falon Abba suna ta hira.. basu Dade da suka gama lunch ba. A yau dai Mamy ta gayyaci yaranta da iyalin su Lunch gidan ta. it’s something they do once in a while! STORY CONTINUES BELOW Abba da Mamy suna zaune a kan kujera three seater yayinda MK yake zaune a single seater.. Maleeka dai throw pillow ta jefa a qasa ta kwanta.. Tunda cikinta ya tsufa take son yin hakan. Tun MK yana yi mata fada akan kwanciya qasa har ya gaji ya daina.. Hafsah ce maqale a jikin mijinta Sadiq wanda suke zaune a kan kujera two-seater yayinda yake bata fruit salad a baki. Hafsah dai tana dauke da jaririn ciki wanda duka-duka satin shi bakwai kenan amma tana nan tana ta buga shagwaba.. A yanzu haka ko da suka zauna don cin abinci qin ci tayi wai bata so… MK cikin tsokana yace “ita fa Chubby dama ragguwa ce I swear.. ji yadda kike ta ba bawan Allah wahala” Ya kalli Maleeka wadda cikinta ya kai wata bakwai yace “Gaskiya babe ke iron lady ce.. I swear ban taba jin tana complain ba infact she behaves as if she is not even pregnant” Hafsah ta turo baki tace “toh Ya MK wallahi ina shan wahala fa..” ta kalli Sadiq tace “my love cikin Maama na sha wahala haka??” Sadiq ya dan sosa kanshi sannan yayi shiru yana tunani.. if he could remember vividly lokacin cikinta na farko har leave without pay ya dauka just to look after her.. Sossai ya wahala, ya tabbatar ko shi yake dauke da cikin sai haka. Shi fa ya sani cewar Hafsah Ajebor ce ta qarshe.. Gyaran murya yayi yace “My love do you really want me to spill the beans??” A rikice tace “uhm.. uhm.. My love toh ai dai nayi qoqari ko?” Su Abba ne suka fashe da dariya yayinda Mamy ta harare ta tace “you?? I doubt..” Ta kalli Sadiq tace “Sannu da qoqari Sadiq.. Kai kam ka samu aiki..” Sossai suke kwasar dariya yayinda Hafsah ta turo baki cikin shagwaba tace “Abba harda kai??” Abba yana murmushi yace “My princess I just can’t help but laugh..” Maleeka ce tace “Hafsy dont mind them.. kina qoqari sossai. I swear it’s not easy being pregnant” Hafsah tace “yauwa Ya Maleeka.. atleast I have someone supporting me” Mamy ce tace “Allah dai ya sauke ku lafiya”. Gaba daya suka amsa da ‘ameen’ Ummi ce ta shigo cikin sallama riqe da tray mai dauke da qananan bowls na Chocolate Mousse.. Binta (daya daga cikin masu aikin Mamy) ce biye da ita yayinda take riqe da wani tray din. Kai tsaye ta ajiye a kan centre table din falon yayinda ta umurce mai aikin to do same. Bayan sun gama Lunch ne Ummi decided to make Chocolate Mousse as desert for Abba.. it’s his favorite desert! Gani nayi ta dauki bowl guda daya ta nufi wurin Abba ta miqa mishi cike da girmamawa tace “here you go Abba… your favorite with little sugar just as you like it” Abba yana murmushi ya karba tare da fadin “thank you my daughter” Komawa tayi ta dauki wani ta dawo ta miqa ma Mamy tace “Ga naki Mamy na” Mamy ta karba itama tana murmushi tace “Allah yayi albarka Ummi” cike da jin dadi tace “Ameen Mamy” Ko da ta dauko ma MK ta nufi wurin shi sa mata idanuwa yayi yana murmushi.. Duqowa tayi ta miqa mishi tace “this is for you sweetheart..” Kashe mata ido daya yayi tare da fadin “I love you” a hankali sannan yayi mata blowing kiss.. Murmushi tayi tare da lumshe idanuwan ta. Bayan MK ya karbi nashi ne ta kalli Maleeka tace “Adda.. unfortunately I didnt bring any for you..I know Chocolate is your favorite amma kiyi haquri saura kadan” STORY CONTINUES BELOW Maleeka tana murmushi tace “it’s okay Ummi.. ai fa na dai kusa juyewa in koma normal mutum” Gaba dayan su suka yi dariya. Bayan Ummi ta ba Sadiq nashi ne shima yayi godiya.. Hafsah kuwa da ta ga kamar itama babu nata bata ma jira ta ji abinda Ummi zata ce ba tace “Baby yi haquri wallahi nawa ko wata biyu bai yi ba.. ki taimaka mun don rai na ya biya..”2 Wannan maganar sossai ta sanya su dariya. Ummi wadda take dariya tace “calm down.. the last one ain’t mine, naki ne” Gani nayi Ummi ta miqa mata yayinda ta dauki dayan tray din tace “this is for the kids” Su Ameer, Ameera da Maama (Hafsah’s daughter) dai tunda aka gama Lunch suka nufi qaramin falon Abba suna kallon Cartoon.. tun daga nan kuwa ba’a qara ganin su ba. Haka Ummi ta je ta basu nasu suna ta murna.. The twins Love chocolate (possibly saboda favorite din Mom din su ne- Maleeka) Ko da ta dawo komawa tayi kusa da Maleeka a qasa ta zauna.. Gani nayi ta duqo saitin fuskarta tace “do you need anything??” Maleeka tayi murmushi tace “nothing dear.. I am okay” Hafsah wadda take kallon Ummi ce tace “Wato dai saboda ya Maleeka cant take the desert shiyasa ke ma you decided not to take it ko? gaskiya kuna birge ni matan yaya.. wannan bond din naku is just outta this world” Ta kalli MK cike da tsokana tace “Ya MK wallahi idan suka yi ganging up against you.. you will be sooo in trouble” Kai tsaye yace “toh ai sai in auro wata kawai…” “what??” abinda matan nashi suka ce kenan yayinda suka zaro mishi idanuwa, cike suke da masifa… Maleeka dukda nauyin cikinta sai da ta mirgina ta tashi zaune. A tsorace ya dago hannuwa kamar wanda yake neman defending kanshi yace “whoa… relax tigresses! wasa nake yi.. daga ku MK ya rufe qofa” Gaba daya falon fashewa suka yi da dariya. Abba da Mamy dai suna enjoying wannan moment din idan suka gayyaci yaran nasu da iyalin su ana drama… they get fully entertained. Haka suka cigaba da hira gwanin ban sha’awa.. Jikokin nasu ma da suka gaji da kallon Cartoon din dawowa suka yi babban falon suka maqale wurin kakanin nasu suna ta yi musu hirar su kala-kala. Da yamma da zasu tafi ne Abba yayi suprising din Hafsah da matan MK. He gave them each a key to the latest brand new BMW Alpina B7. Aikuwa sossai suka yi murna.. suna ta yi ma su Abba godiya. Hafsah kamar ta zuba ruwa a qasa ta sha don murna.. ita dama tana bala’in son sabuwar mota a rayuwarta.. Kullum Sadiq yana cikin siya mata sabuwar mota, dayake shima fan din latest cars ne sai tasu ta zo daya. wannan wadda Abba ya basu last month aka yi launching dinta.. Ko da suka bar gidan Abba.. su Hafsah gida suka wuce amma su MK sai da suka je gidan Goggo da Daddy sannan suka koma gida. ♧♧♧♧♧♧♧♧ Two months later!! WILDOT CLINIC ASOKORO Zaune suke a daya daga cikin lafiyayyun dakunan asibitin. MK, Daddy, Abba, Mummy, Mamy, Ummi, Goggo, Jameela, Fatima da Hafsah… Maleeka ce zaune a kan gadon dakin yayinda Ummi take zaune daf da ita tana bata farfesun kifi a baki. MK wanda yake zaune a kan wata kujera wadda take kusa da su yana riqe da ‘yar kyakyawar Jaririyar shi mai kama da mahaifiyar ta sak. Maleeka dai a yau da safe ta haihu.. Duka-duka da fara labor da haihuwar batayi awa biyu ba.. Allah ya taimake ta haihuwar ta zo mata da sauqi. STORY CONTINUES BELOW MK was very happy.. finally, Maleeka ta bashi abinda ya dade yana so ta bashi- a child! Yanzu haka yana riqe da Babyn a hannun shi yayinda ya qura mata idanuwa cike da so da qauna. Dago kanshi yayi ya kalli Maleeka yace “Babe kin san me?” tana murmushi tace “tell me” tace “babyn nan looks exactly like you when you were born..” Ya kalli Mummy yace “ko Mummy?” Mummy tana murmushi tace “ofcourse.. na tuna lokacin da ka dauke ta ka hana kowa daukar ta..” Daddy yace “sai da nayi dagaske fa sannan ya bar ni na dauke ta..” Gaba daya dakin suka fashe da dariya. Hafsah ce tace “ashe soyayyar nan taku tun Ya Maleeka tana jaririya ma.. Ya MK kai ne asalin Romeo din” Maleeka wadda take kallon shi tana murmushi tace “nagode sossai dan uwa na for loving me the way you do.. I love you so much” Murmushi kawai yayi tare da kashe Mata ido daya wanda didn’t go unnoticed by everyone. Bayan Ummi ta gama ba Maleeka farfesun ne ta zuba mata kunun da Jameela ta kawo mata tace “you need to take this..” Da sauri Maleeka tace “please no” Mamy ce tace “No Maleeka?? a’a ke kuwa ai yakamata ki sha don Babyn ki ta samu ruwan nono ta sha itama..” Goggo ce tace “gaskiya ki daure ki sha.. na tabbatar da yunwa zata farka” Da wannan ne Maleeka ta karbi cup din kunun ta fara sha. Mamy ce ta kalli MK tace “wai mu ba’a gaya mana sunan da aka yi ma yarinya huduba da shi ba.. ko sai ranar suna ne za’a sanar mana” Murmushi yayi yace “Umm Aimaan…”9 Ummi ce tayi saurin kallon shi tace “na’am..” Yace “sunan Babyn Umm Aimaan” Zaro idanuwa Ummi tayi tare da sakin baki tana kallon Maleeka da MK yayinda ta ji Mummy tana fadin “masha Allah, ashe Takwara aka yi ma Ummi” Muryar Ummi na rawa tace “you mean you named her..” Maleeka tana murmushi tace “…after you?? yeah Ummi” Aikuwa da sauri ta riqo hannun Maleeka tana fadin “thank you very much for this… wallahi it means alot to me and I am very grateful” Maleeka tace “ni ce da godiya qanwa ta.. this is the least i could do for you. Kinyi mun abubuwa dayawa a duniyan nan.. a dalilin ki farin cikina ya dawo gareni..kin sa nayi realizing mistakes dina.. you actually saved my marriage, you gave me hope… this is just another way of saying I am sorry for everything that I have done to you and thank you for everything you have done to me”3 Ummi tayi hugging dinta very tight tace “ki daina fadin wannan Adda… Allah has destined cewar da ke da sweetheart will always be together no matter what has happened between us.. nagode sossai and please ki manta da abubuwan da suka faru a baya..” MK was beyond happy to see how his wives are blending so much like sisters.. Su Mamy ma sossai suke jin dadin yadda zaman lafiya ya samu wurin zama a gidan MK. Jameela tayi ma qawarta murna and she is happy to see this good side of her… ita kam she always knew cewar Maleeka tana da kirki kawai wasu attitudes dinta ne suke getting in the way.. but thank Goodness komai is in order yanzu. ♧♧♧♧♧♧ One year later!! MK SODANGI RESIDENCE MAITAMA STORY CONTINUES BELOW Kwance yake a kan kujerar babban falon shi yana wasa da Al- Fudde wadda take maqale da shi kamar chewing gum… Al-Fudde shine sunan da Ummi take kiran Little Umm Aimaan (diyar Maleeka).. Ma’anar sunan AZURFA (Silver).. Gradually kowa ma yayi adopting pet name din and she became everyone’s SILVER. Al-Fudde dai sossai take son MK, Kamarnin yarinyar da Maleeka sai qara fitowa yake yi.. Kullum zaka ganta maqale da shi. Yanzu haka kamar koda yaushe qoqari take yi ta ja gemun shi amma yana kaucewa… tun tana so tayi kuka har suka mayar da abun wasa wanda idan ya kauce sai ta fashe da dariya.. MK dai yana kaucewa ne ba don komai ba sai gudun wahala.. Sossai take damqar mishi gemu tana ja wanda yake da masifar zafi. Maleeka ce zaune a qasa tare da Su Ameera tana supervising dinsu while they do their home work. Bayan sun gama ne na ji Ameera tace “Mom, when is Ammi coming back?” Maleeka ta ja kumatun ta tana murmushi tace “soon My Princess..” Ameer ne yace “can we call her?? I want to talk to her” Maleeka tace “okay my prince.. let’s call her” Maleeka ta janyo iPad dinta tayi dialling numban Ummi.. A ringing na biyu ne ta amsa. Dayake Video call ne suna ganin ta suka fara murna.. Ummi tana murmushi tace “hello my Angels.. Ya kuke?” A tare suka ce “fine Ammi..” Ameer ne ya cigaba da fadin “…Please come back…” Tana dariya tace “kana missing dina ne Ameer??” Da sauri yace “eh Ammi..” Ameera ma tace “me too Ammi” Tace “toh Insha Allah zan dawo.. I miss you too very much.. where is Abbu, Mom and my Al-Fudde??” Ameer ne yace “Mom is here..” yayinda ya miqa ma Maleeka iPad din. Tana murmushi tace “Hajiya how far..” Ummi tana dariya tace “I am good madam Leek” tare da kashe mata ido daya. Hakan ya sa Maleeka tayi dariya tace ” ya na gan ki a hotel room dinki? when is the programme??” Ummi ta saki ajiyar zuciya tace “in 2 hours time Adda… wallahi I am nervous. How I wish you are here with me” Maleeka wadda take dariya tace “hey it’s okay.. na tabbatar everything will be okay.. I trust you” Ta lumshe idanuwa tace “thanks Adda” Maleeka tace “ga Honey..” Ta miqa ma MK iPad din.. Ko da ya karba gani nayi ya qura mata idanuwa yana murmushi.. Al-Fudde wadda take kwance a jikin shi ta hango Ummi sai kawai ta fara dariya tana taba screen din iPad din tana fadin “A-m-m-i.. ” cikin maganarta da ba’a ganewa. Ummi wadda take cike da kewar yarinyar ce tace “hey My Silver.. how are you?? looking cute as always..” MK yace “you are looking cute too my baby.. ya kike??..” Cikin shagwaba tace “I miss you badly sweetheart” Yace “I miss you too my baby.. Na ji kin ce you are nervous.. please dont be, just hang in there and do what you have to do… I am so proud of you and I love you very much” A haka dai ya dinga qarfafa mata qwarin gwiwa har ta fara samun natsuwa.. ●●● Ummi dai a shekaran jiya da safe tayi tafiya zuwa qasar England a dalilin saqon gayyata da tayi receiving na wani exclusive interview da za’a yi da ita a BBC London.5 STORY CONTINUES BELOW Ummi dai ta so Maleeka ko MK su raka ta amma suka bata excuses dinsu na why they cant go with her… Excuse din Maleeka was zata zauna da yara kuma ga school, Shi kuwa MK cewa yayi akwai wani important meeting da zai yi da wasu Important Clients.. Asali sai ba wai bazasu iya raka ta bane, kawai they want her to do things independently on her own ne.. Over the years suna bata support sossai when it comes to things like this amma a yanzu they decided to let her stand on her own dukda dai this is the first time da ake gayyatar ta daga qasar waje.. ●●● ♧♧♧♧♧♧♧♧ Wuraren qarfe takwas da rabi na dare ne aka fara interview din Ummi a BBC studio na birnin London. Gaba daya ‘yan uwa da abokanen arziki were tuned onto the Channel.. Hatta Goggo da bata jin turanci sai da ta sa Lado ya canza mata zuwa tashar BBC din.. Shi kam yayi mata alqawarin zai dinga fassara mata abinda Ummi zata ce. lol A lokacin da aka fara MK, Maleeka da yaran duk suna zaune suna kallo… aikuwa yaran suna ganin Ummi a TV suka fara ihu- Their Ammi is on TV. ●●●●● Ummi ce zaune a studio din sanye cikin wata lafiyayya jallabiya very simple yet so elegant.. Da ganin wannan jallabiyar kuwa ka san ta ja kudi. Ta nada gyalen jallabiyar a kanta yayinda ta fito tamkar balarabiya.. Babu make up a fuskarta but you could swear she is the most beautiful being you have ever seen on earth. Deep down within her she was nervous amma idan ka kalle ta zaka rantse abu ne da ta saba yi.. she was seated confidently. Riz Lateef, shahararriyar TV presenter dinnan ta BBC ita ce zata yi interviewing din Ummi. Da farko bayan ta bude shirin ne ta gabatar da baquwarta a matsayin Umm Aimaan Kabir the founder of AL-IHSAN INTERNATIONAL SCHOOL AND AL-IHSAN FOUNDATION Nigeria. Daga nan kuma suka fara tattaunawa kamar haka: Riz Lateef: You are welcome to the show once again ma’am Ummi: thanks for having me Riz Lateef: So first off I’d like to clarify this from you.. alot of people are saying you are not a Nigerian, some are saying you are an Arab.. how true is it?? Ummi: Well, my Father was a Nigerian and my Mother was from Mali.. and I guess this makes me a Nigerian right? So Yes, I am not an Arab.. I am fulani by tribe. Riz Lateef: Oh great.. So Ma’am we’ve heard and seen some of your achievements so far. Alot of people are impressed by the fact that your school is amongst the top 5 in Africa this year and your Foundation has become the strongest Charity foundation in Nigeria. Now, what captured so many people’s attention is how you are able to achieve this at the age of 22.. can you briefly share with us how you got this far at a very young age?? Ummi: Well, what can I say?? unfortunately i wasn’t one of the kids born with a silver spoon.. I was born into a poor family. I have always dreamt of going to school but I never attended one because I grew up in a village where girls are prohibited from going to school. I was subjected to child labor after I lost my parents.. and that was the time I lost all hope in life, I saw myself as a girl with no future ahead of her, my dreams were shattered and I had no direction.. at a point where I was on the verge of giving up was when HE took me, he restored my hope, my future came in front of me, my dreams were fulfilled and I had a direction-a path to success… I learnt to never give up. I have always wanted to help the needy especially kids who have no future ahead of them.. HE made it possible for me through AL-IHSAN FOUNDATION.. the languages I spoke back then were my native languages but HE taught me the official language of my country and its thanks to him I am able to sit here today and communicate to the world.. HE coached me on how to manage a business from the elementary to the most complicated aspect of it and I am proud to say that I have become a successful business woman today and I am so much happy that AL-IHSAN INTERNATIONAL SCHOOL is currently one of the best in the whole of Africa. To My beloved husband- Muhammad Kabir Sodangi, I know you are watching this.. I just want to tell you that Your sweet nature is one of the many things about you that always make me think of what my life would have been like if we’d never met. Thank you for that gentle look in your eyes that makes me smile every day.. You are the most amazing person in my life, and I adore and value you so much.. Thank you for being there for me always! I love you very very much STORY CONTINUES BELOW Riz Lateef: Wow.. interesting! who would have thought so right?? I am sure your husband is very proud of you Ma’am. Ummi: Thanks Mss. Riz Riz Lateef: Ma’am, Lets talk about Al-ihsan Foundation. We are aware of the great things your foundation has done so far in Nigeria. Your organization is deeply involved in helping the poor and needy children all over your country especially in the northern part where there is a high concentration of destitute Children.. How do you do this?? Ummi: Our focus though has always been on Education, Rehabilitation and ensuring a healthy life style for children. Education is the first and foremost rights of every human being, it helps Children to set a goal and go ahead by working on that throughout their lives. therefore, We support and provide educational and rehabilitation services for children to go to school- children who are underprivileged, poor, orphan and disabled. Again, thousands of people in Nigeria especially in the northern part flee their homes to seek sanctuary in other places, some are sexually exploited, others are introduced to forced labor not forgetting the high number of Almajiris that are struggling to survive every day. We are trying our best to reduce the rate of human trafficking with the help of the Nigerian Human Right Commission. We are also rendering post rehabilitation services for people who are affected during the boko haram insurgency… we are able to reach out to the IDP camps to help them recover some of what they have lost. We know that the effects of malnourishment are irreversible if they occur at a young age. If not death, it leads to permanent disabilities that render the children ill for the rest of their lives. We are doing our best to Promote a healthy life-style among all children by encouraging physical exercise, healthy nutrition, health assistant, surgeries if required, and also working towards eradication and support for HIV and so on. Riz Lateef: I must commend you for a job well done Ma’am. You are indeed a great inspiration to all. Ummi: thanks Miss. Riz.. Riz Lateef: So tell us, how far are you willing to go? in other words what is your Vison in the near future?? Ummi: Actually there is no limit to how far I want to go.. thanks to the UNICEF and the Federal Government of Nigeria for their unlimited support towards achieving our goal. I believe together we shall strive to ensuring a happy and healthy childhood for Nigeria’s children and the rest of the world. Riz Lateef: One last word?? Ummi: To the general Public, Please dont hesitate to donate to save a life. No matter how little, please make a change….2 ●●●●● Wannan hirar da aka yi da Ummi ta taba zuciyoyin mutane da dama… She left people talking about her, Sannan an jinjina ma mijin ta MK sossai na taka rawar gani da yayi a cikin rayuwarta.. He is no doubt the architect of her success. Ummi ta canza perception na mutane da dama sannan labarin ta yayi impacting positively on the lives of people. Wannan hirar da aka yi da Ummi yayi trending worldwide a social media. MK?? She left him speechless.. Duk tsawon rayuwar shi bai taba yin alfahari da wani ba kamar yadda yayi alfahari da Ummi… he never thought she is as intelligent and confident as this… He is so proud of her and will forever be grateful for having her as a companion. The whole family as well.. Sossai suka yi alfahari da Ummi.2 I am also proud of who she has become.. STORY CONTINUES BELOW ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ Two months later.. AL-BARSHA POND PARK DUBAI MK ne tare da iyalin shi zaune a harabar wurin yayinda suke shaqatawa.. A yau kwanan su uku da zuwa qasar Dubai.. Dayake an bada hutun school shine suka yi deciding su dan je vacation don su huta. Al-Barsha pond park yana daya daga cikin best parks a qasar Dubai.. wurin ya qawatu da abubuwa da dama na hutawar dan Adam. Kayan ciye-ciye ne a gaban su… kama daga chocolates, biscuits, ice cream, drinks da tarkace dai kala-kala Su Ameera suna ta wasa da toys dinsu wanda kamar kullum tare da MK suke wasan. Yaran suna bala’in son Abbun su a dalilin yawan zama da yake yi tare da su suna wasa.. On his part shima bala’in son su yake yi (we all know that right??) Ummi da Maleeka dai suna ta hirar su… Hiran wani sabon collection din Maleeka ne da zata yi launching a America next month. Ummi wadda ta shanye ice-cream dinta ce na ga tana qoqarin bude wani.. Ko da ta bude shi ya riga ya narke don haka ne ta dinga bin sauran tana budewa.. gaba dayan su sun narke. Turo baki tayi tace “toh wai ban gane ba.. Ice cream din duk sun narke kenan?” Maleeka tana dariya tace “kar dai kina nufin duk wanda kika sha bai ishe ki ba??” Cikin shagwaba tace “Wallahi Adda Ice cream din yana da dadi ne.. kuma kin ga idan ya narke baya dadi ” MK wanda tun yana mamakin yawan ice cream din da take sha har ya daina ne ya juyo yana kallonta yace “toh yanzu me kike so?? a karbo miki wasu ne?” Da sauri tace “Yes please Sweetheart… I love you” yayinda ta kashe mishi ido daya. Murmushi yayi ya miqe tare da kallon Maleeka yace “Madam Chocolate.. do you care for more Chocolates??” Tana murmushi tace “No Honey, Gasu nan dayawa a gaba na.. ni kam I am okay” Ji nayi yace ma yaran nasu “my Angels ina zuwa” Ameer da Ameera suka ce “okay Abbu” Tun da ya tashi kuwa daga Maleeka har Ummi kallon shi suke yi cike da so da qauna.. MK is this kind of husband that every lady would wish to marry.. he is such a kind-hearted, caring and loving husband.. he is one in a million!! Ko kafin ya qarasa wurin sayar da ice-cream din ne na ga wata kyakyawar mace mai kyan tsari ta tsayar da shi suna magana har suna dariya.. A lokacin kuwa attention din Maleeka ya koma kan su Ameer yayinda Ummi ta zaro idanuwa cike da mamaki… Ji nayi tace “what the hell..” Maleeka ce tayi saurin kallonta tare da fadin “lafiya Ummi?” Ummi kuwa wani irin abu ta ji ya tokare mata maqoshi yayinda zuciyarta take zafi ganin yadda MK yake ta washe ma matar baki har tana qoqarin nuna mishi wani abu a waya.. Maleeka dai bin direction din da Ummi take kallo tayi yayinda ta ga hango su.. Ko kafin ta ankara sai gani tayi Ummi ta tashi da sauri harda gudu ta nufi wurin su. Tana qarasowa wurinshi kuwa ta ture matar yayinda ta tsaya in between them cike da masifa tace “Husband snatcher or whatever you call your self..” Tayi pointing qirjin MK tace “you see this handsome man here? he is taken by us. when I say US, i mean me and my sister sitting over there with our KIDS” ta nuna su Maleeka. STORY CONTINUES BELOW Maleeka kuwa ganin Ummi tayi pointing direction dinsu ne na ga tana ta kwasar dariya yayinda ta dago musu hannu. Ita dai Maleeka sossai wannan al’amarin ya bata dariya.. Bata taba ganin display na kishin Ummi ba sai yau.. Sam bata damu da wadda suke magana da MK ba domin if there is anyone she trusts a duniyan nan toh fa MK ne.. She could swear cewar bazai taba yi mata kishiya ba if not for halinta na banza da tayi displaying a baya wanda ya bar shi with no option but to take in Ummi.. A yanzu haka zata iya rantsewa as long as suna zaman su yadda suke babu abinda zai sanya yayi musu kishiya… Daga MK har matar sun zama so confused.. Cike da mamaki matar tace “please listen to me Ma’am.. it’s not what you think..” ta kalli MK tace “MK please explain to her..” MK wanda yayi gyaran murya ne ya riqo hannun Ummi yace “Baby wannan fa ba…” Kafin ya qarasa maganar shi Ummi ta janyo shi tace “zo mu tafi.. ni bana son jin komai” Haka ta janyo shi yayinda yace ma matar “I am sorry for this Sara.. I will call you” Da sauri Ummi tace “what?? Sweetheart a gaba na???” kawai sai ta fashe da kuka. Maleeka dai tana nan zaune tana ta kwasar dariya.. MK wanda ya rude gani nayi ya janyo ta jikin shi yayi hugging dinta very tight yace “Baby dagaske it’s not what you think.. wannan fa class mate dina ce, we schooled together a London and..” Tana kukan shagwaba tace “….. and you had to keep smiling at her non-stop har tana nuna maka hotunan ta a waya kana kallo kana dariya??” MK ya zaro idanuwa yace “what?? Baby wallahi hotunan yaran ta take nuna mun.. ta haifi triplets so she was..” Janyo hannun shi tayi tace “mu je…” Wannan karon fashewa yayi da dariya… Ashe dama Ummi tana da kishi haka??? interesting.. Maleeka dai ganin su tayi sun qaraso yayinda Ummi take ta kuka tana masifa.. Allah ya so yaran su were busy with their toys basu kula ba. Ko da suka zauna ji nayi MK yace “toh Ice-cream din fa?” Kai tsaye tace “bazan sha ba.. babu inda zaka je” Maleeka dai sai dariya take yi wanda hakan ya ba Ummi mamaki.. Tana kallonta tace “Yanzu Adda kina gani zai yi mana kishiya amma baki damu ba har ma kina dariya??” Maleeka tayi gyaran murya tace “ba haka bane Ummi..” Ta nuna MK sannan ta cigaba da fadin “kin ga honey? duk duniyan nan babu wanda nayi trusting kamar shi.. na yarda da shi fiye da yadda na yarda da kaina.. kar ki manta tun muna yara muke tare don haka na san halin shi gaba da baya… banda abinki ma ta ya zai yi flirting da wata mace a gaban mu? does it even make sense??” Ummi wadda tayi shiru kamar tana tunani ce ta kalle shi wanda shima ita yake kallo yana qoqarin danne dariyar da ta zo mishi.. Turo baki tayi tace “toh ni fa ban san what came into my head ba.. kawai na kasa jure ganin shi tare da ita ne.. kayi haquri” MK wanda yake murmushi ya kamo hannunta yace “dont worry my baby.. I am glad this happened” Da sauri tace “what??” Yace “yeah.. I got to see this side of you that I have never seen..” Ya kalli Maleeka yace “I swear idan aka hada kishin ki da nata akwai case… na tabbatar duk ranar da nace muku zan qaro aure sai kun kashe ni kafin ma amaryar ta shigo”2 Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda ya riqo hannun Maleeka ya hada da na Ummi yace “listen to me both of you.. Ina so ku sani cewar duk wani abinda nake nema a duniyan nan na riga na samu a wurin ku- Soyayya, farin ciki, kwanciyar hankali, kulawa and most importantly..” STORY CONTINUES BELOW Ya nuna yaran shi da suke ta wasa yace “…these beautiful angels da kuka bani don haka babu wani abinda nake buqata kuma.. Over the past years I have enjoyed seeing you both together- yadda kuke yin komai a tare and the way you watch each other’s backs.. to tell you what, I am so proud of you and I pray we continue to be like this till forever… I cant thank you enough for giving me a peaceful family. I love you both unconditionally.. and if I was granted just one wish, I would ask for a longer life because the number of years I am destined to live on this planet may not be enough for me to keep telling you how much I love you both and our kids” Daga Maleeka har Ummi zuciyoyin su cike suke fal da murna.. Su kam basu gajiya da jin kalaman MK a garesu, kalamai masu dadi wadanda ke faranta musu rai.. Sai murmushi suke yi yayinda ya hada hannuwan su ya kai bakin shi yayi kissing dinsu. Gani nayi sun kalli juna sannan suka matsa suka yi hugging dinshi ta both sides yayinda suka yi mishi kiss a both sides of his cheeks.. Maleeka tace “We love you too Abbu..” Ummi tace “Sooooooo very much..” Kamar ance ma Ameer ya juyo sai gani nayi ya tashi da sauri ya nufi wurin su yayi hugging din MK shima… Ameera ma ganin haka ta rugo a guje itama ta fado musu… Al-Fudde wadda tafiyarta tayi qwari a yanzu itama ba’a barta a baya ba, tuni ta qaraso itama and she completed the family.. Tammat bihamdulillah!! ◇◇◇◇◇◇