NI DA PRINCE CHAPTER 7
Salma da salman zaune a gaban fulani, sun gaisheta ta amsa fuska a sake tare da cewa salman da ai jiya kasa hakuri nai nafara tunanin inje inga salma da kaina dan randa aka kawota banganta sosai ba saboda mutane dake bangarena😀. Salman ya kalleta yasani sarai munafurci ne amma sai yai murmushi shima yace gashi ai tazo gaisheki, fulani ta kalli salma tace salman kayi dace yarinyar tamin sosai😊, ya kalleta sannan ya kalli salma yace nima tamin fulani😊, salma ta kalleshi tasan sarai karya yake amma batasan meyasa ta jin wani abu aranta? Salman ne ya kalli fulani zai yi magana yaji an turo kofa, baijuya ba dan yasan su ishaq ne, dasauri ishaq ya karaso ya zauna kusa da fulani, ishaq ya kalli salma yace Amaryarmu ya kike? Salma tad’ago ta kalleshi ganin yanda yake kallanta yasa tai kasa dakai tace lafiya, yace kanina dai baya wahalar dake ko? Takalli salman, tai murmushi tare da cewa a’a, ishaq yad’an hade rai yace salman akula da ita fa? Salman yace basai ka fad’aba, maganar taba ishaq haushi amma ya daure harsu salman suka fita yai tsaki yace ni wlh an cucen. Fulani datasan halin d’anta sarai inyaga kyakyawa tace kul! Wlh ishaq ka fita daga idona, yace menai kuma? Tace nafad’amaka dai dan nasanka. Salma kam suna isa d’aki ta kalli salman tace kai nafijin dadin fulani kamar kunfi shakuwa😀 gaskiya tanada mutunci, amma…..wani mugun kallo yawatsa mata yace will u keep ur mouth shut?tace me kuma nai? Dan nace fulani nada..karasowa yai ya jawota jikinsa yace what did u know? Idanta a runtse, ahankali ta bude idanunta ya kalleta jiyai wani abu na tsirgamai dasauri ya saketa, ya juya baya yace in bakisan komai ba kiyi shiru banasan magana😏 itama ta juya tace to. Falo salman ya fita, ya kunna tv, ta fito ta tsaya a jikin labile tace aran waya please? Ya juyo yakalleta yace bangane ba? Tace uhm Abbana nakesan ma waya, yace sai kije kimai ai🤔tace to ai banda waya☹. Kallenta yai tare da murmushi ya taso ya shigo d’akin tare da d’auko wayarsa dake kan side bed, ya kalleta yace baki da waya?tace eh mana baka kula ba? Yai dariya yace in these era? Tace to dole ne? Yace a’a ba dole bane amma in har kinaso inbaki aran wayata kidinga waya tofa dole kidinga bin umarnina😉 , tace da bana bi🙄? Yace inafa kike bI? Tai shiru can tace ai kai din ne, yace ni me? Tace kaima kasani ai yace bansani ba, tace to yanzu dai kaban nai waya sai musa rule din daga baya, yace a’a banyarda ba, ta turo baki tace to naji zan d’inga bi bani nai wayar, ya mika mata tare da zama akan gadon, takalleshi tace bazaka fita ba? Yace infita kimin bincike a waya? Tace ni😳? Yamata alama da ido yes, ta koma can jikin kujera ta danna number Abba, ringing biyu ya d’aga. Tai sallama ya amsa tace Abba salma ce, yace salma nagane ya gida? Tace lafiya Abba yasu umma? Yace duk lafiya, tace Abba yaya kamal fa? Salman dake zaune ya d’ago ya kalleta dama tanada yaya? Sai dai yanda yaga ta kalleshi ta kuma sa hannunta ta toshe wayar yasa jikinshi yabashi da wani abun, Abba yace salma meke damunki? Wani kamal kuma? Tai kasa da murya tace nasani Abba so nake naji ko yana gari ko ya koma? Abba yace bansanI ba kuma indai akanshi zaki dinga kira to karki sake kirana tace Abba…..jitai an kashe tace Abba☹. Salman ne ya taso tare da fizge wayarsa yace daga wayar farko harkim b’atamai rai? Tace bafa haka bane😕yakoma jikin gado ya tsaya yace bari inkira inji dakaina me kikai?tunda ke dama haka kike dasan b’atama mutum rai😏. Dasauri ta taso tace dan Allah karka kira, takaraso gunsa tace karka kira plz, ran Abba baci zaiyi inyaji kanannan nai waya, salman yace ohhhh kinsan bakida gaskiya kenan, kamal ko? Tace a’a mikon wayar ingoge number Abba, yace naki yafad’a tare da d’aga wayar sama, tafara dage tana kokarin kamowa, kafarta tad’anyi rawa tafada jikin salman wanda shikanshi d’agen yai dama kafarsa ba a daidai takeba nan sukai baya dukansu suka fad’a akan gado, salma tafad’a saman sa. Ahankali suka bud’e ido, zuciyoyin biyu suka shiga bugawa salma kallanshi take shima haka, dasauri tafara neman tashi salman yai saurin sa hannunshi a kugunta ya rikota ta kalleshi, yaI murmushi yace haka kikeso dama ina kuma zaki gudu? Tace yaushe nace haka nakeso? Tafad’a cikin shagwaba, ya kwaikwayi maganar ta, ta turo baki tace sakeni plz? Ahankali salman yasaketa ta mike dasauri tai toilet, shikanshi jikinshi tsima yakeyi key yad’auka yai waje…. Hmmmmm Salma ta dade a toilet ba abinda takeyi tana tsaye, jin motsin bude kofarsa yasa ta fito daga toilet din, akan gado ta zauna tare dayin ajiyar zuciya. + hanne ce ta kwankwasa mata, ta bude tare da cewa hanne ya akai? Hanne tace ranki ya dade bakiga gidan ba o tai murmushi aranta tace wani gida gtunda basan juna muke ba, afili tace muje kirakani, tare suka dinga shiga salma tayi mamaki ashe akwai wani d’akin bayan tagama dubawa tad’an zauna a falo, hanne ce ta kawo mata madara nan salma ta amsa tasha, salma tace wai haka zanta zama ba abinda nake? Hanne tace eh mana aikinki shine ki huta, salma ta mike tare dacewa nama tuno, littafinta na makaranta tad’auko tafara dubawa, itakanta tausayin kanta takeyi tanasan karatunta amma batasan kozata cigaba ba. Yauma sai 9 salman ya dawo lokacin salma na d’aki rike da littafinta salman yashigo tare da sallama, salma ta amsa batare data kalleshi ba ya shigo yare da cewa yau kuma karatu ne ya motsa? Tace eh thanks to someone, I can’t even finish what I start🤔 salman ya karasa kusa da ita yace is that someone Me? Yafad’a tareda nuna kansa👉🏻. Ta d’ago tace eh mana, ya juya tare da cewa ko kika ja ma kanki ba? Tace hmm wai kai yaushe zaka koma skul? Yace ke share sai sanda nai ra’ayi tace ra’ayi? Yace eh ko kinada ja? Ta tabe baki a hankali tace dama mutumin da bai zuwa makaranta ina zaici jarabawa?. Salman yace I can hear you, dasauri ta rufe baki tace wannan wani irin mutum ne? Can tace hmm nikam zan koma d’akincan da kwana😞yace ban bada permission ba, tace ehye? Yace kin manta menace miki ko? Tace banmantaba amma….kallon daya mata yasa tai shiru, ta kike ta fita ganin ya shiga toilet, pillow da bargo tad’auko a d’akin ta dawo, yana fitowa ya kalleta baice komai ba ya kwanta. Tanaso ta tambayeshi yaci abinci? Amma takasa. Salman kam yana kwanciya yai bacci, salma tayi shimfid’a ta kwanta, sai dai ta dade kafin bacci ya d’auketa. Yau kwanansu 8 da aure sai dai rayuwarsu tananan ayanda take. Salma kwance Cikin bacci takejin kamar ana nishi, idanunta ta bude tare da kalan gadon da salman yake, da yake da haske yasa taganshi a durkushe, da sauri ta mike ta matsa kusa dashi, ganin yanda yake zufa gashi ya rike kirjinsa sai nishi yake da kyar yasa dafashi cikin kid’ima tad’an birketoshi kankameta yai yana *inalilahi wa ina ilaihi Raji’un* salma ta kankameshi itama tace prince menene? So yake yai magana amma ya kasa ta kara rikecewa, tunda take bata taba ganin wani a irin wannan yanayin ba cikin rudewa tace bari insa akira likita tafad’a tana mai zare hannunsa daga jikinta, kara rikota yai ya girgiza mata kai. Hawaye ne yafara zubo mata tace banganeba, kaganka fa😰? Ya d’aure azabar dayakeji ya nuna mata drawer din jikin gadon, ta kalleshi tare da budewa, ganin magani a ‘yar farar roba yasa ta mikamai tare da janye jikinta ta miko mai ruwa, ya amsa ya had’iya ahankali yafara jin relief, can ya saki ajiyar zuciya,salma kam hawaye kawai take gani takw kamar mutuwa zaiyi, tariga tasa a ranta indai yasha magani bai warkeba ba ruwanta nemowa zatai akaishi asibiti ko a kira likita. Salman ya d’ago ya kallI hannunshi data kankame tana hawaye,ganin ya d’ago yasa itama ta kalleshi, yace is ok I am alright, cikin hawaye tace wani irin ciwo ne wannan? Kana zuwa asibiti kuwa? Salman ya kakaro murmushi yace Is not a big deal fa, ta janye hannunta tare da mikewa zata wuce, hannu yasa dasauri ya kamo hannunta ta tsaya batare data juyo ba har a lokacin hawaye take, salman yace please karki fad’awa kowa, kinji? Ta juyo a fusace tace abinda zakace kenan? Wace irin rayuwa kakeyi? Bakada lafiya baza’a sani ba? Ya runtse ido batare da yai magana ba yasaki hannunta, dasauri takara matsowa tace jikin ne😰? Ya bude ido ahankali yace bacci tai ajiyar zuciya. Salman bacci ne yai gaba dashi saidai salma takasa bacci kusa dashi tazo ta zauna tai shiru, batasan sanda bacci yad’auketa ba, cikin baccinta mafarkin rannan tasakeyi gata da wani hannunsu a rike suna kallan ruwa, sosaI dadin mafarkin takeji, dan murmushi harkan fuskarta. Salman daya farka ya kura mata ido tana kwance tana bacci sai dai da alama mafarki me dadi take, abinda yaban mamaki shine ganin shima salman ya saki wani murmushin. A hankali ta bude idanta salman ta gani kusa da ita tad’an turo baki tace ya jikin😞? Yace I am ok👌🏻zatai magana yace a haka kika kwana? Ta kalleta akan kujerar jikkn madubi data jawo take a zaune ta kwanta a jikin gadon, tace hmmm, yai murmushi tare da mikewa, haryaje jikin toilet ya juyo yace tnx 4 ur concern😉 Kallanshi tai tad’anyi murmushi, salman ya wuce toilet itama ta mike ta maida kujerar inda take, bayan salman ya fito ya wuce massalaci itama ta shiga ta d’auro alwala, bayan ta idar da sallah haka kawai tasamu kanta da d’aga hannu sama tana rokarma salman saukin wannan ciwo nashi😰. + Ga mamakinta daya dawo daga massallaci bai koma bacci ba itama hakan yasa ta zauna tare da d’aukan qur’ani, wajen 7 salman ya mike yakalleta yace zan shiga makaranta, salma ta rufe qur’anin tare da kallanshi, tad’an kakaro murmushi tace to, yace do u resent me? Ta kalleshi tace sosai ma☹, yai murmushi tare da wucewa toilet. Tabi bayanshi da kallo, salman bayan ya fito yad’au kaya ya koma toilet yasa, kananan kaya yasa yayi kyau sosai, salma ta kalleshi tace ka fad’amusu a kawoma abinci ne? Yace nop bana cin abinci da sassafe, tad’an tabe baki tace hmm. Salman ya dau waya ya fita, takalleshi tace jakar makarantar fa? Yace mezan da ita? Tace au haka ake zuwa? Yai tsaki yace nidai na wuce najib na jirana, takalleshi aranta tace tab. Mikewa tai tafara kad’e gado, maganin jiya tagani, ta kurama maganin ido, tace ko maganin meye? Ta bud’e drawer ta side_bed ta ajiye zata rufe taga wani karamin album hannu tasa ta jawoshi, ahankali ta bude, hoton wata tagani, suna tsananin kama da salma ga hoton na da ne hakan yasa tai tunanin mahifiyarsa ce, takara budewa hotunan salman ne wanda baifi d’an 20yrs ba alokacin shida wata yarinya, kana ganinsu kasan suna cikin farin ciki, ice cream sukesha, wani gurin kuma suna kan keke, wani kuma suna zaune a kan grass carpet, murmushin dake kan fuskar salman ne ya bata mamaki, bata tab’a ganinshi a cikin farin ciki haka ba, zata bude wani gun taji an fizge album din. Dasauri ta d’ago, salman ne tsaye ranshi a b’ace yace bincike kikemin in na fita? Dasauri ta mike tace wannan ne bincike? Maganinka naje maidawa nagani, amma wac…..katseta yai tare dacewa bansan tambaya, ya d’au makullin mota daya manta ya fita da album d’in. Ta bishi da kallo a fili tace wacece ☹? Tadade a zaune haka kawai take tunanin yarinyar, da alama hotunan bama na kasar nan bane, a ina ne? Ganin batada wanda zai bata amsar tambayoyinta yasa ta mike ta cigaba da gyaran d’akin, bayan ta gama tai wanka, ta fito tai breakfast. 1 Salman kam ya dade a mota rike da album din, idanshi ya kad’a yai ja a hankali ya bude album din ya kalli mahaifiyarsa, sannan ya bude ya kurama budurwar ido, yasa hannunshi akan fuskarta yana shafa, ya dade a haka kafin ya rufe, yaja motarsa. A falo salma ta zauna tasa kallo, hanne da wata na zaune a kasanta, salma tace hanne ko mu fita nan tsakar gida? Wajen garden d’incan? Hanne tace to ranki ya dade abinda kikeso shizamuyi, ta mike tare da yafa mayafinta suka fito, zamatai a garden tare da littafinta tana karatu. Ishaq ne yazo wucewa, dama kullum yazo wucewa sai ya leka bangarenta sai dai kullum ba kowa sai bayi, yau kam yayi sa’a yana lekawa yaga salma zaune akan kujera hankalinta gaba d’aya ya tattara akan littafin datake karantawa, kura mata ido yai jiyake kamar yaje ya rungumeta, fadawan dake bayansa ya kalla yace ku tsaya anan, shikuma ya shiga. Hanne ce ta d’ago jin motsin mutum, ishaq ya kalleta yamata alama da hannu su fita, cikin hanzari suka fita, ishaq ya karaso daf da ita yad’an sukunyo yace Amaryarmu karatu take? Cikin tsananin mamaki ta d’ago tare da saurin mikewa ta matsa baya, salma ta gaidashi, ya amsa tare da cewa Amarya kina lafiya? Yafad’a tare da matsawa, takara matsawa tare da cewa lafiya, amma yarima me kake anan? Ishaq ya tsaya tare da cewa laifine in nazo ganin matar kanina? Yafad’a cikin shagwaba, haushi ya kama salma amma tad’aure tace ayya nagode, zan shiga ciki naga kamar lokacin sallah ya kusa, bata jira mai zaiceba tai saurin wucewa ciki. Ishaq ya bita da kallo tare da cewa wow yarinyar nan tana kasheni gaskiya👌🏻… Salma na shiga ciki d’aki ta wuce ta hau kujera tace wannan kuma wani sabon salon fa? Meye namin shagwaba? Tsaki tai tare da cewa ni zaman d’akin ma yafimin😕. Haka taita zama har tai sallar isha’I, aranta tace wannan rayuwa haka zan d’ingayi? Da yaya kamal na aura nasan bazan kare a haka ba😞 bayan tayi isha’I tana zaune har bacci yafara d’aukanta. salman ya shigo ganinta a zaune akan kujera tana barci yasa ya karasa inda take ya kalleta, gaskiya tanada kyau, wata zuciyar tafad’amai haka, tuno yanda ta kuladashi jiya yai, tunda yake a duniya jiya shine rana ta farko da wani d’an adam yasan da cutarsa harya kula dashi, hannu yasa ganin kanta yad’an lankwashe garin bacci, salma kam jin kwanciyar ta mata dadi yasa ta cigaba da baccinta. murmushi yai ganin yanda take baccinta sannan ya kalli hannunsa da fuskarta take kai, wata zuciyar tace ahaka zaka zauna? A tsaye? Harsai ta tashi? Motsin daya d’anyi da hannunsa ne yasa salma ta bude ido da sauri ya zare hannunsa tare dayin gyaran murya, ta mike da sauri tace ka dawo? Ya juya baya yace ke kuma meye hakan?tace mekuma nai daga dawowa? Ya juya yai waje batare dayai magana ba, tace neman a d’auramin laifi da