NI DA PRINCE CHAPTER 8

NI DA PRINCE CHAPTER 8

Salman na fita a kujera ya zauna tare da furzar da wata iska, yace menai? Meyasa nazo nan? Ya mike tsaye tare da bude fridge yad’auko ruwan faro ya bude, ya kafa kai sai daya ahanye ruwan tas sannan ya saki numfashi. + Daki ya koma, salma ya kalla dake shimfid’a ya d’auke kai tare da hawa gado ya d’aure fuska yasa earphone a kunnansa, salma takalleshi aranta tace oh ni salma, jitai yace dani kike? Dasauri tace ba abu kakeji ba? Yace au in nasa earphone gulma ta kike kenan, ta juya baya tace nidai badakai nake ba, yace shine kika kira sunana🤔? Ta matsa kusa dashi kad’an tace ni? Yaushe? Yace kice baki kira sunana ba? Tace ni wlh sunana nakira, yai tsaki tare da kwanciya, ta harareshi tace oh 🤔 juyawa tai zata wuce, yasa hannu ya rikota, ta tsaya tare da juyowa😳, yace oh me?tace nifa badakai nake ba☹tafad’a cikin shagwaba, jawota yai ta fado kan gadon kusa dashi, ahankali tad’ago ta kalleshi. Yace oh me? Tace wai dakai nake? Yacs dakanki kike? Tai shiru, yace dazu natambayeki do u resent me kikace eh ko? Ta dan harareshi tace ba gaskiya kakeso nafad’a ba? Kaima kasan dole ne tunda kasa akaban suspension, sannan yanzu bana tunanin zan iya karasa karatuna😕. Salman yasa hannu ya jawota jikinshi, yazo saitin kunnenta cikin rad’a yace bake kikace ni kike so ba😏? Haushi ya isheta ta zare jikinta tare da mikewa tace Allah yatsaren😠, mikewa yai tare da riko hannunta ta baya da karfi ta juyo dan taji zafin rikon, fuskokinsu ne sukai daf da juna yanda kowa najin numfashin d’an uwansa, salman ya d’aure yace Allah ya sauwake? Ni ya kamata infad’I haka ko ke? Kasa tai da kanta tace hannuna😞 tafad’a cikin sanyin murya, salman ya kalli hannunsa ganin yanda yakama mata hannu yasa ya zare a hankali, ta rike hannunta tare da kallanshi🙄yace Allah ya isa ko? Tace yaushe nafad’a kuma☹? Ya juya ya koma gado.1 Ta dade tana kallanshi kafin itama ta kwanta sunyi shiru sai dai dukansu ba bacci suke ba, salma tace bacci? Cikin sanyin murya yace no, tace inada tambaya, yace tame? Tace yarinyar daxu wacece?salman yai shiru, takara cewa wacce? Jin bai amsaba yasa tace sry ina b’atama ra……jitai ya katseta dacewa *FARHA* tamaimata sunan tace wacce farha? Yace u don’t have to know, tai shiru duk da bataji dadin amsar ba amma bata kara magana ba, salman yasan bataji dadi ba amma shi kanshi baisan tunowa, dan yanzu maganar dasukai akan farha shikad’ai yasan me yake ji. 1 wajen 9 yagama shiri tana zaune tana kallansh, tace yau zanje gaisuwa gunsu fulani, yace to, tace aran waya in kira Abba plz kafin kafita, ya mika mata, ta amsa ta kira Abba sai dai an dade ba’a d’agaba harta katse, takara kira, jin muryar mutumin datake kewa yasa ta mike tsaye tare da cewa yaya kamal? Tafad’a tana kallan salman, ganin ya juya baya kamar hankalinshi ba’a kansu yakeba yasa tace yaya kamal ina kwana? Kamal kam duk ya rude jin muryar salma, yace salma Kinga Abba ba lafiya munanan ma asibitin aminu kano, dasauri cikin kid’ema tace what? Yace eh salma jiya da daddare muka kawoshi, dasauri ta kashe wayar,hawaye yafara zubo mata,kusa da salman ta karaso ta rike mai riga, salman ya juyo yana kallanta, ganin hawaye yasa ya rikece yace salma menene?tunda take yaune rana tafarko daya taba kiranta da sunanta, sai dai bata kula ba dan hankalinta nakan Abbanta. 1 Salman yakara cewa menene? Jikinshi tashige tasa kuka, shikanshi baisan sanda yasa hannu ya rungumota ba yace menene wai? Tace Abba na ba lafiya yana asibiti, prince yazanyi😰? D’agota yai yace meya sameshi? Tace bansani ba nima😪.1 Yace wuce kiyi wanka sai in kaiki, tace to nagode, dasauri tai toilet ya bita da kallo, cikin tausayi, salma kam wanka tai tad’auro towel sam ta manta salman na d’akin dan a kid’ime take, ta fito da d’aurin kirji, salman dake tsaye ya juyo ya kalleta, 😳 itama tana ganinshi tai saurin yin kara tare da komawa toilet din, yai murmushi tare da yin falo, sam ta manta yanannan kayan data cire ta maida ta fito, sai dai bakowa a d’akin tai saurin zura duguwar rigar atamfa tashafa mai da huda ta yafa mayafi, ta fito. Salman dake zaune a falo ya kalleta, tace dan Allah ba inda zan sami hijab? Yace ki zo mu tafi dan nima ina sauri ne, tace to tare da binshi. 2 Sun isa asibitin Aminu kano, ta kira number Abba a wayar salman, kamal ya d’auka tare da musu kwatance, nan suka isa gun, suna sauka a mota kamal ya taho da sauri ganin salma, ya kalleta wani abu na tasomai, itama kallanshi takeyi duk ya rame, salman dake tsaye yana kallansu.1 Salma ta daure tace yaya yanaga ka rame? Yace salma kema kinsan dole ne banajin zan iya rayuwa bake😞, idanta ya ciciko tace yaya ina Abba? Yace kuje ciki, ta juyo ta kalli salman dake tsaye ta inda ya fito daga cikin mota yana kallansu, tace muje cikin? Ya zagayo tare da cewa muje mana, kamal ya kalla wanda ya kuramaI ido, kana kallan kamal kasan kallan kiyaya yakema salman, salman ya d’auke ido tare da zagayowa ya kalli kamal yae d’an rakiya muje ko🤔? Kamal ya hade rai yace d’an rakiya? Salman yace wuce mana kana b’ata min tym😏.1 Kamal kam ji yake kamar ya shake salman sai daI kafin yai magana salma tace yaya muje mana makaranta zai wuce, tafiya yafara kamar mara lafiya salman ya kalleshi ya tabe baki. Sun isa gadon da akaba Abba, salman ya kalli d’akin kusan su bakwai ne a ciki, umma da goggo na zaune kusa dashi, salma da sauri ta karasa kusa da Abba, ta kuramai ido ganin yanda ya rame yasa hawaye kawai ya fara zubo mata. Salman kallanta kawai yakeyi jiyake hawayen da take har zuciyarshi yake tab’awa, juyawa yai ya kalli su umma da goggo ya tsugunna ya gaidasu da mai jiki, sannan ya mike, idanshi ne ya diri akan kamal dake kallan salma shima hawayen yake, wani mugun kallo yama kamal haka kawai yaji bayasan yaron. 3 Daurewa yai yakalli goggo yace meke damunshi wai? Tace hawan jininshi ne ya tasha yace ayya nan yace bari inga likita tace to, ya juya ya fita. Salma kam kuka takeyi, kamal ji yake kamar ya rungumeta ya lallasheta, juyowa tai tace umma meyasa ba’a fad’amin ba? Umma ta juya fuska, goggo tace Alhaji ne ya hana, salma tace su sa’a fa? Goggo tace yace kar afad’awa kowa kema kamal ne yafad’amiki dan baisan ya hana ba.1 Tai shiru tare da waigawa, ganin bataga salman ba yasa ta cigaba da lekawa, goggo kam ta fahimceta tace to mara kunya, yaje gun likita, dasauri tace kiji goggo ce miki akai shi nake nema? Kafin goggo tai magana sai ga salman da wani babban likita, ya gaidasu sannan yace zamu maidashi wani d’akin, goggo tace meyasa? Likitan ya kalli nurses din dake bayansa yace ku turo gadon, sukace to.1 Sannan salman yace goggo acan sai anfi kula dashi, tace to. Nan suka meke dukansu salma takalli salman tai murmushi Shima murmushin ya mata, kamal dake kallansu kishi duk ya isheshi. 1 Wani babban d’aki aka kai Abba, kana ganin d’akin kasan d’akine na mai matsayi, salma ta kalli salman tace d’akin nan yamana girma, salman ya harareta sannan ya kalli goggo da umma dakesan su fad’I abinda salma ta fad’a yace goggo karku damu ba wani abun bane, goggo tace angode d’an nan. 1 Salman yai murmushi sannan ya kalli salma ya mata alama da kaI ta biyoshi,sannan ya kalli su umma yace na wuce, dakyar umma cikin kunya tace angode, yai murmushi ya fita, salma ta kalli kamal wanda ya had’e rai sannan ta fita. 1 Kusa dashi taje tace makarantar zaka? Yace eh kinsan mai martaba yasa mai kula dani, in har banjeba da matsala, tai murmushi tace nikam shekarunka nawa? Salman ya had’e rai yace bangane ba😠 tai dariya tace bakafi 26 to 27 bako? Ya hade girar sama data kasa yace zaki fara ko? Tace sry gani nai ace har yanzu sai ana kula dakai🤔 ya juya yace ki biyoni mota, kallansa tai tare da sakin murmushi. 1 Kudi yad’auko mata mai kauri yace ki rike in case ko za’a bukaci wani abun,tace a’a nasan da kudi agun…..yace kinsan banasan musu ko? Hannu tasa ta amsa yace ko kefa? Natafi tace to zaka dawo ko in wuce? Yace da ke kad’ai kikazo dazakimin wannan tambayar? Tai kasa dakai, mota ya shiga yaja, har akasan ranta. 1 Juyawa tai, idanunta suka had’u dana kamal, ta karaso inda yake tace yaya, kamal ya juya cikin b’acin rai da sauri tasha gabanshi tace yaya meya faru? Kamal yasa hannu yaja hannunta ya fara tafiya tace yaya😳? ina zaka kaini? Kamal kam tafiya yake sai da sukai tafiya mai nisa, mutane nata kallansu, har sukaje gunda ba mutane sannan ya saketa.2 Tace yaya me kakeyi hakan? Kamal yace tambaya ta ma kike? Salma dama akwai ranar dazaki zauna da wani namijin cikin farin ciki bayan ni? Ta kalleshi da mamaki tace yaya ya kakeso inyi da rayuwata😰? cikin d’aga murya da fad’a yace salma tambaya ta kike? Duk son da kika nunamin dama na karyane? Ni zaki yaudara? Nad’auka yanda nake sanki haka kema kike sona ashe ba haka bane? Me zaki cemin? Itama cikin fad’a da kuka tace yaya ya kakeso inyi? So kake in kashe kaina? Duk jiran danamaka ka manta dani, kabarni da tsananin begenka, ba nema? Kamal ya dafa kafad’arta hawaye ya zubo mai yace salma ban barku ason raina ba y don’t u understand? Ta ture hannunshi tace fahimtar dani yanzu😠, kamal yai shiru tace bazaka iyaba? Dama nasan bakada abinda zakace, ta juya tafara tafiya. 1 Hawaye take harta isa d’akin, goggo ta kalleta tace daga rakiya shine kila dade? Batai maganaba ta zauna kusa da Abba ta kama hannunsa ta rike tana hawaye. Salman kam dama inya shiga class wayarsa yake d’auka yai ta d’annawa ba ruwanshi da abinda akeyi, yau kam yayi shiru tunanin salma kawai yakeyi, ko mahafin nata ya farka daga allurar baccin da akamai? Ko jikin ya kara tashi? In ya tashi ya salma zatai? Wannan dalilin yasa yai shiru, har malamin ya fita baimasan me akeyi ba.1 Najib ne yatab’ashi yace Prince ya akai? Amir yace hala tunanin Amarya ake, salman ya mike yace tunanin Amarya? Allah ya sauwaka, ya fita waje najib ya bishi yace ina zaka? Salman yace hm wani guri, sai gobe. 1 Dasauri ya fad’a mota yai hanyar asibiti. Salma na rike da hannun Abba taji yayi motsi, dasauri ta d’ago tace Abba😥? Yakalleta tare da lumshe ido tasa kuka tace Abba laganka kuwa? Murmushi ya kakkaro ta kalli umma tace umma me za’a bashi? Ta mike ta zubo mata faten tsaki wanda yasha manshanu da yakuwa, salma ta amsa tare da taimakawa Abba ya mike, nan ta shiga bashi,ahankali ya dinga amsa har ya shanye. Salman gudu yakeyi ya kai wajen titin gyad’I_ gyad’I mota tamai faci, haushi duk ya isheshi ga yamma tafarayi, waya yama driver dinsa yace ka kawomin prince 4 yanzu, yace to ganinan ranka ya dade. Salman nazaune a mota haushi duk ya isheshi ga salma bata da waya, sai wajen 5 ya iso. Dasauri ya amshi motar tare da barin driver din anan gun d’ayar motar. Salma ganin Abba ya koma bacci, ga goggo ta tafi gida, umma ce a ciki yasa ta fito waje ta zauna a dakalin gun, kamal ne yazo yazauna kusa da ita, ta d’ago ranta a had’e ganin kamal yasa ta mike, dasauri yasa hannu ya kamota yamaida ita inda take, tace yaya. Kamal yace salman jarabawa na fad’I sai dana zauna wata semester din tazagayo na sakeyI😞 kiyi hakuri dana barki ke kad’ai. Kallansa take tana hawaye tace yaya meyasa baka fad’aba ko ta waya? Yace banso kisan saurayinki rago ne gun karatu, ta runtse ido kwalla sai zubo mata take, yace muje ki rakani na siyoma umma lemo, nima inasan kati. Ta mike suka jero suna tafiya, salman da tun da ya iso yana kallan sanda kamal ya rikota duk yagansu duk da baisan me suka ce ba amma ranshi yagama dugunzuma. Ganin sun taho tare yasa ya kunna mota, cikin tsananin bakin ciki da bacin rai ya kunno motar da karfi, da gudu ya taho, saura kiris ya kadesu, dan sukam sun gama tsorata kamal ya kamo hannun salma yasata a bayansa da sauri, salman sai dayazo daf da kamal ya taka burki jikake kiiiiiiiiiiiiii… Kallan kallo suka fara, sai a lokacin kamal yaga ashe salman ne, salman kam hannun kamal daya rike salma ya kalla, daure wa yaI tare da fitowa daga motar, ya saki murmushi kamar ba komai ya matso kusa da kamal ya zare hannun salma sai alokacin tasan salman nema, ta kalleshi cikin tsoro, saidai ga mamakinta murmushi ya saki tare da kallan kamal yace ayya kamar baka gani? Ka dinga kula in kana tafiya karkaja a ragema farashi😉.1 Kamal kam mamaki ya hanashi magana, salman ya kalli salma yasa hannu yajawota yace kema kamar bakya gani? Tace hm hm bankula bane🙁 yaceina zaki? Without my permission? Ta kalleshi sannan ta kalli kamal tace dama….ya katseta yace muje muduba Abba mu wuce gidanmu, yafad’a tare da kallan kamal. Salman yafara tafiya itama ta bishi a baya, kamal kam ya kame yama kasa tafiya yana kallo har suka shiga ciki haushi ya isheshi yakaima motar naushi da kafa, sai dai maimakon yaji sauki sai zafin dayaji akafarsa😕 Sun isa d’akin, Abba na jingine sai dai ya rame sosai, salman ya karasa tare da gaidashi, ahankali Abba ya amsa tare dama salman godiya. + Salman ya kalli umma ya gaida ita, tai kasa dakai ta amsa, sun d’an yi shiru kafin Abba yace kuje gida dare yayi, salman ya kalli salma sannan ya musu sallama, itama salma ta musu sallama ta fita. A waje ya tsaya, yanakallan kamal ma tahowa gunsu yai murmushi tare da kallan salma yace muje ko? Ta kalleshi tace eh, ahankali ta matso suka jera suna tafiya, sai da sukazo daf da kamal sannan salma ta kalli kamal idanta taf da kwalla, salman ya kalleta ganin yanda take kallan kamal yasa ransa ya b’aci amma iya basarwa ta salman sai ya kalli kamal yace mr d’an rakiya dan zo ka shiga da ledojin nan tunda ciki zaka😉, kamal ya kalleshi sannan yace kai meyasa dazaka shiga baka wuce dashi ba? Salman yace karaso ka amsa, yafad’a tare da karasawa motar. Kamal ya kalli salma ranshi duk a b’ace tace yahkuri yaya ba….wani kallo da kamal ya mata yasa tai shiru, kamal ya tsaya kikam salma tafara tafiya ta juya tace yaya? Kamal ya d’aure ya karaso, salman yai murmushi tare da mikomai manyan ledoji guda biyu yace tnx d’an rakiya😊, kamal yace karka kara kirana da sunan nan😠. 1 Salman ya shiga mota tare da rufowa sannan salma ta shiga, ya zuge glass d’in mota ya kalli kamal yace ban san sunanka ba me kake so ince? Salma zatai magana ya juyo ya kalleta tai shiru tare da turo baki, ya kalli kamal yace nyt😏, yaja mota da gudu ya bud’ama kamal kura. 1 Kamal ya kalli motar yace wlh mutumincen sai na👊🏻. 2 Salma kam a mota suna hawa titi salma ta kalleshi tace plz ka dainacemai haka☹. Cikin zafin rai salman yai gefe ya taka burki da karfi, salma kam ta tsorata da sauri ta jiyo ta kalleshi, sai dai yanda taga idansa yasata tai shiru, ya kalleta tare da nunata da yatsa yace karki kuskura! *karki kuskura ki kara tarema wani a gaba* don’t u dare do that again😡. Salma kam jikinta rawa yake amma ta daure tace menai kuma? Ni meyasa kakemin haka? Tafad’a tare da zubo da hawaye, sai dai ganin tana hawaye yasa jikinsa yai sanyi ya juya tare da fara tafiya batare dayace komai ba. 1 Salma ta juya kai tana kallan window, wajen mai saida waya ya tsaya baice mata komai ba yafita, takalleshi tare dacewa kada Allah yasa kacemin kana zuwa😗. 1 Yad’an dade kad’an kafin ya fito, ya bude mota ya shiga, baice komai ba itama haka, har suka isa gida sun fito zasu nufi bangarensu wanI bafade yazo gun salman yace Ranka ya dade mai martaba na kiranka, ya kalli salma tare da mikamata karamar ledar yace wuce dashi ina zuwa tace to. Amsa tai ta wuce shima yai banaren mai martaba, salma na shiga bangarenta hanne ta taho da sauri tace ranki ya dade kun iso lafiya? Salma tace lafiya, hanne tace ina kukaje ranki ya dade🤕? Bakiga fad’an da fulani tai ba mai martaba ma sai da yai fad’a. Salma tace bangane ba😳? Hanne tace a ka’idar gidan ba’a fita sai mace tayi wata biyu amma ke kun fita ku biyu ba driver kuma ba wanda yasani😞. Salma tace bansani ba ai dana sanar😰, yanzu mai zai faru? Hanne tace kawai dai fad’a za’amai tunda ansan ke bakisani ba. Salma ta mike tai d’aki tare da zama dabas a kasa ta jingina kanta a gado, tasan salman bazai yi bayani ba saboda pride dinsa yanzu tasan anacan anamai fad’a. A hankali hawaye ya fara zubo mata tace because of me😪 kanta ta had’a da gwiwa, tayi wajen minti 30 a haka sannan salman ya turo kofa kallanta kawai yatsaya yanayi, meyasata kuka? Jin sheshekarta yasa ya kasa jurewa kofar ya rufe tare da karasowa inda take, ya tsugunna yasa hannu ya jawota jikinsa, ahankali tad’ago tace me akacema😰? Ran sarki ya b’aci ko? Sai a lokacin yasan dalilin kuka, hannu yasa ya fara shafo bayanta, ta kankameshi tace am sorry because of me…katseta yai yace ba saboda ke bane, meyasa kike da saurin kuka ne? Salma kam tai luf a jikin salman sai d’an shesheka datakeyi.1 Salman shiru yai yana tunanin fad’an da sarki yamai, shifa shiyasa bayasan zaman gidan nan, ace komai sai ka sanar?. Sun dade a haka kafin hankali salma ta zare jikinta, ta mike salman yasa hannu ya jawota ta zauna a inda take yace wa……..sai kuma yai shiru, azahiri so yake ya tambayeta meye tsakaninta da kamal? Amma jiyai bazai iya ba, kamar zata rainashi tai tunanin ya damu da itane, kallansa tai tace wa me? Hannunta yasaka tare da kikewa yai gyaran murya yace hm waya nake nufi wace kika shigo da ita, kiyi amfani dashi in kinaso, yana gama fad’ar haka yai toilet. Salma ta kalleshi tare da rangwad’ar dakai tana kallon ya shiga toilet tace kace kawai kasai min waya☹ ta mike da sauri ta bude wayar, 😳 kalan wayar tace inazan kai wayar nan? Iphone 6 taga ga an rubuta a jikin kwallin tace ahh wasa yakemin hala🤔 inani ina wannan wayar? Tanajin ya fito ta mike takalleshi ta karaso inda yake tace amma dak ba wannance wayar bako? Ya kalleta dariya takusa zuwa mai ganin yanda takeyi da ido, ya d’aure fuska yace bata miki bane? Tace ni😳ina na isa? Ai wai naga…..ya katseta yace in ta miki to ya isa 😒 ya fad’a tare da matsar mata da hannunta yai ciki, ta karaso da sauri batasan sanda ta rungumoshi ta baya ba tace thanks a lot😊. 1 Salman jinta a bayansa yasa yai murmushi, salma ta sakeshi tadawo tagabanshi tace nagode sosai prince ta saki wani sanssanyan murmushi tare da lumshe ido shima murmushin yai……. Nikaina murmushin nai😜

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *