ZUCIYA CHAPTER 18
Tun daga idanunsa take bi da kallo fuskarta sai murmushi ke bayyana, lalai soyayya da dadi amma batajin in har da wani ne zataji dadin soyayyar nan.+ Ashraf kam bacci ne ya daukeshi, jin yanda Nafi ke shafa masa kai. Bud’e kofar falon yasa ta kallo gun da sauri tana san ganin wanene ya bud’e kai tsaye. Ganin Anisa yasa ta zaro ido sai dai bataji zata iya d’aga Ashraf daga jikinta saboda Anisa. Itakam Anisa tun daga bakin kofa ta tsaya tana musu wani kallo, wani irin zazzafan kishi ne yake damunta, kitchen ta wuce direct ta debo ruwa cikin bokoti ta nufo Nafi. Itakam Nafi ganin tayi kitchen yasa ta saki numfashi na farin ciki, tare da kallan Ashraf, batai auni ba kawai sai ruwa sukaji akansu. A firgice Ashraf ya farka tare da mikewa tsaye, kallan mamaki ya shiga yima Anisa wacce ta shiga yin huccin masifa. Ya maida kallansa kan Nafi wacce dama kanta ba d’ankwali saboda dazu ya cire mata tun daga saman kanta har jikinta duk a jike yake jarab. Yaso yama Anisa magana amma ganin Nafi cikin wannan hali yasa ya wuce dakinsa da sauri ya d’auko towel sannan yazo ya rufa mata. D’aga ta yai ko kallan Anisa bai kuma yi ba ya wuce da ita cikin d’akinsa. Nafi kam tayi lamo har suka shiga ciki, ya kalleta yace ” kinji haushi ko?” Kai ta jinjina alamar eh, yai murmushi yace ” kinsan……” Ta katse shi da cewa ” haushi na d’aya kana bacci an tasheka.”5 Kallanta yai tare da murmushi ya jawota jikinsa, sannan ya kamo hannunta sukai toilet. Kallanta yai ya mika mata towel, ta amsa sannan tace ” ka fita to.” Baya ya juya sannan yace ” ki cire a haka dan ba inda zani, ai ba kallanki nake ba.” Ta ce ” taya zan yarda bazaka juyo ba?” Yai murmushi yace ” in ma na juyo ai abuna na kalla ba na wani ba.” Juyawa tai da sauri cikin kunya. Da kyar ta cire kayan ta d’aura towel din sannan ta sa kayan a bokiti, tace kazo ka cire naka sai in wanke mana.” Murmushi ya mata sannan ya sa wani takalmin ya shiga toilet din. Juyowa tai zata fita ya riko hannunta. Nan ta tsaya ba tare da ta juyo ba, yace ” ina zaki??” Kallansa tai da sauri tace “naam?” Yace ” ina zaki nake tambaya, dan nasan kinjini.” Tace ” waje zani in ka….” Hannunta yaja yai wajen sink da ita kallan sa kawai takeyi, gani tai ya d’auko man wanke kai da alama nashi ne ko na Anisa ne ni dai ban sani ba. Ya mata alama data sa kanta. Ta kalleshi tace ” yaya me…..” Hannu yasa a bakinsa alamar tai shiru sannan ya mata alama data sa kanta. Nan ta sa kanta tana tunanin me bawan Allahn nan yake shirin yi. Ribbon dinta ya zare sannan ya zuba man ya fara cud’awa a hankali, shiru tai tsantsar mamaki ne yake mata yawo a zuciya, dama haka Yaya yake??? Jitai yace ” kina mamaki ne?” Cikin rawar murya tace ” ni ban ce komai ba.” Ya sake murmushi sannan ya sunkuyo saitin kunnenta yace ” na dade ina sha’awar wanke kan nan tun kafin ki koma skul, sanda mukaje siyayya.” Tai kamar zata d’ago ya maida kanta kasa yace ” kina mamaki ne?” Tace ” na fahimci me yasa yaya nisa bazata iya rabuwa da mutumin nan ba.” a ranta tai maganar batasan a fili tai ba sai jitai yace ” da cewa akai zan rabu da ita? Ko kuwa abinda kike so kenan?” Idanu ta runtse kunya ta kamata, da sauri tace ” ni na isa? Na san irin san da kuke ma juna??” Murmushi yai a ransa yace ” bantaba san wani ba sai a kanki dan ban taba tunanin zan iya yima mace wadan nan abubuwan ba.” Anisa kam wacce tazo daukan kaya sam kasa dauka ma tai ta koma bangaren Umma tana zuba kuka kamar ranta zai fita. Umma ta taso da sauri zata mata magana, Anisa tace “kun cuceni wlh ni bada kudin ba bada mijin ba.” tai d’aki tana kukan takaici. Umma ta baza tagumi, a fili tace ” kai wannan yar bafilatanan anyi tsinanniya, anya kuwa haka ta barshi? Da alama zan fadama Uwarsa dan banaji ta barshi haka, dama ita inaaa sam bata yarda da ita ba. Bayan ya gama ne ya sa mata karamin towel ya sa mata akai sannan ya kalleta yace ” zaki fita in watsa ruwa ko zaki zo mu watsa……”+ Ai bata jira ya karasa bama tao waje da sauri, murmushi yai sannan ya tura kofar. Nafi kam kofar tabi da kallo tace “wato yaya sam bashida kunya ko?” Zama tai a bakin gado littafin nan na diary ta gani a hankali ta zaro shi ta bud’e shafin farko “To My dearest Son Ashraf.” Abinda ke rubuce kenan tai murmushi ganin wani d’an karamin hoto ba sai an tambaya bama Ashraf ne, passport ne da alama yana nursery aka d’auka tai murmushi sannan ta bud’e shafi na biyu. _Ashraf Allah baiyi zanga girmanka ba sai dai inaji ajikina ko bani zaka zama yaro na gari, mai san ‘yan uwansa da na kasa dashi._ Nafi ta sake murmushi tace “Abba ai d’an naka ne ba a gane cikinsa.” Tana bud’e d’ayan page rubutu ne sosai, tana kokarin karantawa taji motsin alama na bud’e kofa, da sauri ta maida littafin sannan ta mike. Ashraf ya kalleta sannan ya karaso inda take, yace “matsoraciya.” Kanta ta kawar gefe batace komai ba. Toilet ta wuce da sauri, yabi bayanta da kallo zuwa cinyoyinta da suke a waje, kansa ya shafa sannan ya zura riga doguwa ya fita falo. Nafi kam bayan ta watsa ruwa ta fito tare da tsayawa a d’akin to me ma zatasa? Ina kuma yayan yaje? Rigarsa ta gani t-shirt irin mai dogon hannun nan kawai ta zura sai ta sauke towel din kasa ta d’aurashi kamar zani. Tana d’aura kanta da ribbon Ashraf ya shigo, kallanta yai yadanyi dariya yace ” da har ina tunanin d’auko miki kayan yayarki?” Da sauri tace ” wacce yayar?” Ya d’an bata rai kadan yace “wace yayar kike da ita a gidan nan?” Baki ta tabe tace ” bansa kayanta bama an jikani ina kuma ga ta ganni da kayanta?ai inaji kanazir zata zubamin ta kyasta ashana.” Ashraf ya danne dariyarsa yace ” ke dai tsoronta kawai kikeji da alama, ko da yake baki da laifi Anisa ai akwai zuciya, ga kwarjini kuma bata da tsoro kamar o’o.” Nafi ta d’an harareshi kadan tace ” nima ai inada zuciyar kuma ba tsoro garen ba kawai dai raga mata nake nima.” Ashraf baisan sanda yasa dariya ba, sai dayai sosai sannan ya kalleta ta wani ci magani yace ” ayya bansan raga mata kike ba ai, ashe karamar matar tawa ba tsoro.” Nafi ta kara had’e rai tace ” ai in aka bi ta gaskiya ma nice babba dan nice uwargida.” Baki Ashraf ya bud’e sannan yai dariya yace “Uwar gida?” Ta turo baki tace” to wacce in ba ni ba?” Dariya yasa zai yi magana yaji ana knocking, nan yai waje yana dariya, lalai yarinyar nan, uwar gida??? Ha ha ha ni kaina sai da na sa dariya. Dan liti ne bayan ya shigo ne Ashraf ya kalleshi yace ” ya? Ina da ina yaje?” Nan Dam litti yashiga mai bayani, Ashraf yai shiru can yace ” shikenan sai zuwa gobe.” STORY CONTINUES BELOW Dan litti yamai sallama ya fita, Nafi bayan taji rufa kofa ne ta fito, a falo ta ganshi ya zauna tare da sa hannunsa duka biyu akan hancinsa zuwa bakinsa, Nafi ta zauna kusa dashi tace “Lafiya?” Kallanta yai tare da girgiza mata kai alamar ba komai, ya mata murmushi. Itama murmushin tai sannan tace ” nikam kun hadu da babansu Ferry ko?” Kallanta yai yace ” Inda kikai yaji?” Tai murmushi tace ” ka ganshi?” Kai ya d’aga alamar eh, sannan yace ” ya akai?” Tace ” baka sanshi ba ko?” Kai ya d’aga mata cikin rashin kulawa yace ” yeh.” Shiru tai hakan yasa yace “ya akai?ya kamata in sanshi ne?” Tai shiru kafin tace ” a company din Abba yai aiki da.” Kallan mamaki ya mata yace ” what?” Tace ” kuma da alama abokin Abba ne, dan bayan rasuwarshi ya ajiye aikinsa na company din.” Ashraf yace ” ko abokinsa ne mai zai sa ya ajiye aikinsa dan Abba ya rasu?” Shiru tai hakan yasa ya dafata yace “Nafisa!” Nafi tace ” wlh bansan dalili ba sai dai kamar yana zargin mutuwar Abba ne.” Shiru yai hakan yasa tace ” menene?” Ya kalleta yace ” sunansa Isma’il?” Kallan mamaki tamai tace kasan sunan ne?” Da sauri ya mike yace ” zan turo Little ta kawo miki kayanki.” Ta mike tace ” ina zaka?” Bai amsa mata ba sai makulli daya zara yai waje da sauri. Bayansa tabi da kallo, sannan ta kalli ledar daya bata d’azu, mam ta bud’e ganin kwalin waya yasa wani farin ciki ya kamata, irin wayar hannunsa ce har kalar sai dai ita bata kai waccen ba, wani murmushin farin ciki tai tace “Yaya na gode.” Nan ta bud’e wayar ta shiga ta tabata. ******** Ashraf direct a kofar gidan su Ferry yai parking, ya karasa suka kaisa da mai gadi sannan ya tambayeshi ko mai gidan na nan, mai gadi yace ” eh yana gida, wa za’ace mai?” Ashraf yace kace ” Dan marigayi Abbas ne.” Nan mai gadi yai cikin gida, baifi minti 3 ba sai gashi ya dawo wai ya shiga. Nan ya rakashi falon baki, Nabil na zaune kusa da mahaifinsa yana ganin Ashraf ya mike suka gaisa sannan cikin muryar rada yace ” rannan ya aka kare kai da budurwata Feena?” Ashraf ya makamai harara sannan shima cikin rada yace ” kai saurin gyara bakinka,wacce budurwar taka?” Yana kainan yai gaba, a gaban mahaifinsu Ferry ya zauna, tare da gaidashi cikin ladabi. Dad ya amsa sannan ya kalli Ashraf cikin tsoron abinda yazo dashi yace “Ashraf ya akai?” Ashraf ya d’ago yace ” Tun ranar da na fara zuqa gidan nan ka san ni ko?” Dad ya kalleshi bai amsa mai ba, Ashraf yai murmushi yace ” Na dade ina nemanka sai dai bansan ta inda zan soma cigiya ba, shiyasa nabarma kaina saninka.” Kallansa Dad yai yace ” nema na?” Ashraf yai murmushi yace “kasan lawyer din Abbana?Uncle Salim?” Dad yace ” Salim?” Ashraf ya d’aga kai yace ” ya sanar dani kai da amintar dake tsakaninka da mahaifina sai dai kowa na mamakin barinka company daga sanda Abba ya rasu.” Ashraf yad’an tsaya sannan ya cigaba, ” sai dai ni ina tunanin ba aminta bace tasa kabar company din sai dai cikin d’ayan biyu, ko dai kasan abinda ya faru da mahaifina? Ko kuma da kai akai abinda akai, sai dai a koda yaushe in zuciyata ta rayamin na biyun ina saurin neman sauki gun Allah daya sa hakan karya zama gaskiya.” Dad ya kalli Ashraf ga mamakin Ashraf sai jiyai yace ” Ya Mansir?” Ashraf yace ” kawu? Yana nan.” ya fada yana mai kallan mamaki. Dad yai murmushi yace ” me kake tunani gama da Mansir?” Ashraf ya d’an rage idanunsa yace “naam?” Dad ya sake murmushi yace ” u are smart, nasan kasan me nake nufi.” Ashraf ya kalli Dad yace ” nagane me kake san tambayata sai dai bansan meyasa nakeji a jikina ba Kawu bane kadai.” Dad yai murmushi yace ” As i expected nasan dan Abbas bazai bani kunya ba, u are right sai dai bazakaji komai a bakina ba, sai dai zan baka suna guda d’aya kaje kai amfani da wannan sunan ka gano shi da su waye suka had’u sukama Abbas haka.” Ashraf yai shiru yana kallan Dad, dad yace ” Auwal max.” Kaje kai tunani ka kuma yi amfani da wannan sunan mutumin ka gano su waye ragowar, in ka gano sai ka dawo ni zan sanar da kai abinda na sani saboda a lokacin ne zan gane lalai zaka iya komai.” Ashraf ya maimaita sunan “Auwal Max!” Sannan yai godiya ya mike ya fito, a wajen falon ya tsaya yana kallan kofar falon, lalai mutumin nan ya iya d’aure magana, ya maimaita sunan Auwal Max! Sannan ya fito daga gidan yayi sa’a bai ga Nabil ba da sauri ya fada mota yai gaba….. Ashraf yana fita daga gidan ya wuce gidan Uncle Salim, bayan sun gaisa ya kalli Uncle yace ” Uncle tambaya nazo da ita.”+ Uncle yace ” ina jinka, sai fatan Allah yasa na san amsarta.” Numfashi Ashraf yaja sannan yace ” Kasan Auwal Max?” Kallan mamaki Uncle yamai yace ” kwarai kuwa dan driver din mahaifinka ne koda yaushe suna tare.” Ashraf yai shiru hakan yasa Uncle yace ” menene?” Ashraf yad’an numfasa sannan yace ” Yana ina yanzu?” Kai Uncle ya girgiza yace ” Allahu a’alam, tun bayan hatsarin mahaifinka ban sake sashi a idona ba.” Ashraf ya kalli Uncle cikin mamaki sannan yace ” shima yana cikin motar sanda abin ya faru?” Uncle yace ” kwarai kuwa, a iya sanina tare suka fita sai dai bansan ya akai ba naga mahaifinka kadai a asibiti, sai dai inaji ko shi wani asibitin aka kaishi.” Ashraf yai shiru yana tunani kafin ya mike yace ” sai da safe na gode.” Bayan ya fito ya shiga mota ya jingina kansa da kujera, yana nazarin kalaman Uncle, mai zai sa Alhaji Isma’il ya fadamai sunan driver din mahaifinsa???? Ya dade yana tunani kafin yaja mota yai gaba. Nafi kam Little ta kawo mata kaya tare da mata kallan zargi, Nafi ta harareta tace ” me kike tunani?” Little tai dariya tace “ah to abin naku dai ba kunya da alama daga ke har yaya.” Nafi tai saurin fizgar kayanta tace ” me mukai?” Little ta girgiza kai tace “hmm ko sai nazo nayi gashi? Ko kuwa ba tun yau ba aka bud’e?”1 Idanu Nafi ta zaro sannan ta d’au kayanta ta dan bigama Little tace “lalai wannan kanwar batada kunya, to wlh mu ba ruwanmu salahaine.” Little ta rufe baki tace ” hmm da alama kam.” Nafi ta harareta sannan ta zura kaya suka fita tana kokarin kare kanta agun Little, ita kuma sai tunzurata takeyi. Ashraf yana dawowa gida yai sallah sannan ya kwanta akan kujera yana tunani, can wata idea ta fadomai hakan yasa yai bacci tare da tunani da fatan Allah ya taimakeshi gobe. Da safe ya shirya sun fita shida Dan litti, a hanyarsu ta office ya zaro wayar nan dake cikin jala ya saka number kawu sannan ya turamai sako kamar haka ” Yallabai ina bukatar taimakon ka, kudin hanuna sun yanke. daga Auwal Max.” Ya dade yana tunani kafin yai shahadar turamai, suna isa office ya kalli Dan Litti yace ” ka tabbatar kabi Kawu duk inda zaije, jikina yana ban zai fito yanzu ka bishi duk inda yai.” Dan Litti ya amsa da to, sannan Ashraf ya sauka, a hanyarsa ta shiga yaga kawu wanda yake kokarin saukowa daga beni, kallan mamaki yamai ganin yana cikin hanzari. Da sauri yasha gabansa, yace ” Kawu sai ina haka?” Kawu ya dan yi murmushin yake yace ” akwai aikin dazan je dubawa ne a construction site.” Ashraf yamai kallan zargi yace ” Hmm naga ne ka fito ba tare da Secretary dinka ba.” Kawu yad’an juya kai sannan yace ” yana mota yana jirana.” STORY CONTINUES BELOW Ashraf ya jinjina kai tare da cewa ” shekanan a dawo lafiya.” Nan yai gaba, kawu ya kalla yaga yana sauri, waya ya daga ya kira Dan Litti yace mai ya tabbatar yabi kawu gashinan ya fito. Ashraf office din kawu ya wuce yai knocking, kamar yanda yai zargi Secretary dinsa ne zaune yana rubuce rubuce, Ashraf yai murmushi sannan yace ” Cigaba da aiki dama gun Kawu nazo.” Ya mike tare da cemai, bayannan yanzu ya fita, Ashraf ya jinjina kai sannan yace ” amma ya akai ya fita shi kadai? Kana aikin ka kuwa?” Da sauri yai kasa dakai alamun ban hakuri yace ” wlh nace zan bishi yace in zauna ba dadewa zaiyi ba.” Ashraf ya juya ya fita batare da ya amsa ba. Ajiyar zuciya yai sannan yace ” ya ga sakon?” Kawu kam yana fita duk ya rikice ganin tun bayan faruwar abun nan bai kara ma tunawa da wani Auwal Max ba bare yasa ran haduwa dashi, menene nashi namai sako yanzu? Rashin kudi? Unguwar Nasarawa ya shigaz yai parking a wani tangamemen gida sannan ya fito da sauri yai cikin gidan yana waya, Dan litti na ganin haka ya kira Ashraf ya sanar dashi ya shiga wani gida. Ashraf yai murmushi tabbas gun wanda suka hada abun yaje daga ganin sako, yai murmushin ganin abun yazo mai da sauki yace ” zaka gane gidan?” Dan litti yace ” Yes Ma!” Ashraf yai dariya yace ” nine Ma?” Dan litti shima yai dariya yace ” ganinai tun da ka tashi yau bakai dariya ba shiyasa na saka.” A tare sukai dariya kafin Ashraf yace ” bayan La’asar kazo mu tafi.” ********** Nafi kam ganin Little ta fita skul, yasa taji gidan shiru, dan ma tanata latsa wayarta can ta mike da niyyar zuwa kitchen, a kofar falo suka had’u da Habib, mamaki ya kamata tace ” Ya Habib?” Ya sakar mata murmushi yace ” Gimbiya i really miss u.” Kallan mamaki tamai sannan tace ” ni?” Ya d’an hade rai, zai yi magana tai saurin cewa ” Little tana makaranta bakuyi waya bane.” Ya hade rai yace ” cewa nai gunta nazo?” Ta zaro ido tace ” inba gunta kazo ba,gunwa kazo to? nadai san ba guna kazo ba.” Ya kalletq yace ” taya kika san haka?” Tai murmushi tace ” haba ya Habib ina nakai wannan matsayin?” Yai ajiyar zuciya sannan ya mika mata leda yace ” tsarabarki ce ta Abuja.” Ta amshi kayan tana mai kallan mamaki, bata samu tai magana ba taga ya juya yai gaba, ta dan tabe baki tace ” Tsarabar Little dai.” D’aki ta maida kayan ba tare da ta bude ba sannan ta fita tai kitchen. ****** Ashraf sai yamma bayan sun tashi Dan litti ya wuce dashi gidan da kawu yaje, tun a kan hanya dayaga sun dau kwanar Nassarawa G.R.A yaji gabansa nafaduwa, addu’a kawai yake yi a ransa Allah yasa ba inda yake tunani zasu ba. Tsoronshi ya kara daduwa ne sanda yaga anyi kwanar gidan, idanu ya runtse cikin tsananin tsoro, Dan litti yai Parking sannan ya kalli Ashraf yace ” Mun Iso.” A hankali Ashraf ya bud’e idanunsa gabansa ne ya yanke ya fadi, da sauri ya fito daga mota yana girgiza kai alamar ba haka bane, ya kalli Dan litti yace ” ka tabbatar nan yazo?” Kai dan litti ya d’aga alamar haka ne, Ashraf ya dafa kansa cikin tsananin tsoro can wata zuciyar tace ” mayb baiga sakonka ba.” Jiyai ance ” Buddy.” Da sauri ya juya Habib ya gani ya fito daga gidan da saurinshi, yana karasowa ya rungumeshi yace ” Ayya Aminina da alama jikinka ne ya baka na dawo ko?” Ashraf ya d’an yi yake yace ” lalai kasha hanya.” Habib yace “sosai ma, dan ma naje naga gimbiya.” Kallan mamaki Ashraf yamai,Habib ya katseshi da cewa ” muje ciki ku gaisa da Dady kasan yace sam baka zuwa gunsa, gashi kullum sai ya tambayeni kai.” Ashraf yai murmushi sannan yace ” muje to.” Jikin Ashraf kamar wanda aka zubama ruwa haka yake tafiya, sunje shiga ya kalli Habib yace ” dama Dady da Kawu suna shiri??” Habib ya dafashi yace ” me kake fada, ka manta Dady baya shiri da Kawu har bayan auren Mumy.” Ashraf a ransa yace “then y??????” Jansa Habib yai suka shiga ciki. Dady na zaune yana karanta jarida yana ganin Ashraf ya mike cikin tsananin farin ciki yace ” wa nake gani kamar d’ana da baya nemana???” Ashraf yai murmushi ya karasa gunsa yace ” Dady na sameku lafiya?” Dady ya zauna tare da nuna ma Ashraf kusa dashi ya zauna, Ashraf ya girgiza kai sannan ya zauna a kasa wajen kafarsa yace ” Dady ina wuni?” Dady ya dafashi yace ” Ashraf nida d’ana amma ganinsa ya min wuya?” Ashraf yai murmushi sai dai a ransa yana kara kallan Dady da tunani kala kala dake yawo a ransa, can yace ” Dady kasan aikin namu ne sai a slow.” Dady yai murmushi yace ” to ya za’ayi dama komai sai hakuri.” Habib dake zaune yace ” wato Dady kaga Ashraf ka manta dani ko? Dama kullum tambayar ka ya Ashraf yake? Wani aiki yakeyi yanzu? Me yakeyi? Wa da wa ya hadu da d…….” Da sauri Dady ya katseshi da dariya yace ” kai kuwa ba dole inji halin da dana yake ciki ba?” Ashraf yai murmushi a ransa yace ” shiyasa kake barin Habib ke zuwa kwana akai akai saboda kasan me nakeyi???sai dai akan me? ” Nima nace lalai fa akan me kenan? Soyayyace ta ‘yan uwa ko akwai wani b’oyayyen al’amari a kasa???? Hmmmmmmm