RABO AJALI CHAPTER 3

RABO AJALI





CHAPTER 3






Dai-dai lokacin da aka shafa fatihar D’AURIN AUREN NEEHAL DA NEELAH,
Najwah ta farka a firgice daga bacci had’i da kurma uban ihuuuu,
cikin tsantsar tashin hankali ta duro daga kan tamfatsetsen gadon da take kwance,
ta zube k’asa batare data kula da fad’uwar datayi ba ta mik’e zambur,
ta nufi k’ofar fita daga bedroom d’inta while tana cigaba da ihuuuun cike da tsoro jikinta nata kerrrrrma yana b’ari,
kacib’us sukayi da Mamah (mahaifiyarta) wacce ta nufo d’akin jikinta na rawa sakamakon jin ihuuuun Najwah!,
ganin Najwah bata kula da ita ba tana k’ok’arin fita yasata saurin rik’ota,
had’i da cewa ” ke lafiyarki kuwa….!?

Bakin Najwah na rawa ta fara k’ok’arin yin magana had’i da yin nuni da hannunta zuwa saman bed,
kallan gadon Mamah tayi taga bakomai kana ta mayar da kallanta ga Najwah,
ta kuma tambayarta a karo na biyu,
” lafiya! meke faruwa dake….!?

Cikin kerrrrrma Najwah tace ” Mamah Nee….Nee…. ha…l, tayi maganar a rarrabe,
ido Mamah ta zaro waje cikin rashin hankali tace ” meya same shi, wani abun ne ya same shi….!?

Ta jerawa Najwah tambayar a lokaci d’aya, cike da tsoro,
still kasa magana Najwah tayi, illa Neehal!…. Neehal…! datake ta faman fad’a,
gumi ya jik’ata sharkaf duk da sanyin AC dake d’akin,
ganin yanayin da Najwah ke ciki yasa gaban Mamah ya shiga fad’uwa yana dukan uku-uku,
dan a zatonta wani mugun abun ne ya samu Neehal,
cikin tsawa Mamah tace ” wai dan ubanki bazaki fad’a min abinda ya samu Neehal d’in ba…!?

Bakin Najwah na rawa tace ” ma.. far…. ki na… yi…,
tsoki Mamah taja had’i da cewa ” aikin banza kawai,
tayi maganar tana k’ok’arin fita da sauri Najwah ta rik’eta gami da sanya kuka,
tana cewa ” wallahi Mamah mummunan mafarki nayi akanshi,
kuma kinga tunda ya tafi fa bai kira ni ko sau d’aya ba, 
k’uluwa Mamah tayi sosai dan kwata-kwata ta tsani halayen Najwah, 
” dalla can ni gafara ki bani waje, mara kunya kawai, dan mijinki ya tafi kwana d’aya bai kira ki ba shine kike wannan abun…!?

“Banza sakarya mara wayo, kwana d’aya kawai da tafiyar miji, shine kike hauka….!?

Tayi maganar a zafafe,  jin abinda Mamah tace yasa Najwah k’ara marairaicewa tare da k’ara sautin kukanta sosai, 
ta kuma rik’e Mamah gam “please Mamah ki fahimce ni mana,  ba yadda za’ayi Neehal yana lafiya, 
ya tafi harya kwana wani daren ya k’ara yi batare daya kira ni koya kira wani ba, 
yadda Najwah tayi maganar yasa jikin Mamah yin sanyi ta d’an yi shiru tana tunani, 
Najwah ta cigaba da magana ” kuma haka nan naji gaba na na fad’uwa,  jiki na yana bani tabbacin wani mummunan abu yana shirin faruwa dani koma ya faru, 
jiki na yana bani kamar yana tare da wata mace, tayi maganar cikin sanyi tana kallan tails  while bata bar kukan ba, 
d’a da mahaifi sai Allah, take Mamah taji tausayin Najwah ya kamata, a hankali ta d’ora hannunta saman kafad’arta, 
kana ta soma magana cikin sanyi, 
” kiyi addu’a dan itace maganin komai da duk wata masifar dake tunkaro mutum, 
walau ya sani walau bai sani ba, ki kuma kasance mai kyautatawa mijinki zato a koda yaushe, 
Najwah zatayi magana Mamah tayi sauri cewa ” no! jeki yi alwala kiyi sallah ki sanar da mahaliccinki, majib’ancin lamuran mu, mai yaye mana k’unci da damuwarmu matsalarki, 
cikin sanyin jiki Najwah ta d’aga kai, Mamah ta shafa kanta had’i dayi mata murmushi tace ” good girl, kana ta fita, 
maimakon Najwah ta shiga bathroom tayi alwala kamar yadda mahaifiyarta ta sanya ta, 
sai ta koma saman bed ta zauna tana sharar hawaye had’i da sak’a da warwara.

STORY CONTINUES BELOW


******************

A b’angaren Neehal kuwa ana shafa fatihar d’auren auren shi da yarinyar da ko sunanta bai sani ba, 
saboda tsabar tashin hankali ko da aka ambaci sunnanta yayinda ake d’aura auren rud’ani bai barshi yaji sunan ba balle ya fahimta, 
a hankali ya lumshe idanshi hawaye na gangarowa daga idanshi, wanda shi kanshi bazai iya tantance dalilin zubarsu ba,
shin hawayen farin cikin ya tsira da rayuwarshi ne, 
kona bak’in cikin auren daya k’ara bayan yayiwa annurin ranshi alk’awarin bazai tab’a yi mata kishiya ba, yafi a irga, 
ko kuma hawayen tausayin Najwah ne ….!?

Ya tambayi kanshi cikin ranshi, 
Malam Liman  ya kalli Neehal  dake faman zubar hawaye kamar mace, 
cike da tausayin kanshi, dana tilon ‘yarshi dana kuma Neehal, 
wanda ya tabbatar auren dole akayi mishi, dan yasan idan da abinda Neehal yafi tsana a rayuwarshi bai wuce wannan auren ba, 
ya tabbatar ba k’aramin abu ne zai sanya namiji kamar Neehal mai kafaffiya zuciya da taurin kai kuka ba, 
duk da ya hango k’uruciya k’arara  cikin kwayar idonshi, 
ajiyar zuciya Malam Liman yayi a fili tare da d’ora hannunshi saman na Neehal, 
a hankali ya bud’e idanshi gami da d’ago kanshi ya kalli Malam Liman , 
Malam Liman yace ” tashi muje, ba musu Neehal ya mik’e suka bar wajen still hannunshi cikin na Malam Liman, 
har sunyi nesa Malam Liman ya kwalawa wasu matasan masari su uku kira, 
suna tafe samarin na bin su a baya babu wanda yace k’ala,  
har suka isa bakin bukkar da mai gari ya bawa Neehal kana ya kalli matasan yace ”  wannan bukkar tayi mishi k’ank’anta kasancewar yana da kaya da yawa, 
dan haka kuyi mishi wata babba mai fad’i sosai, 
cikin girmamawa suka amsa da to, 
bayan Malam Liman ya gama da samarin ya juya ya kalli Neehal, 
ya zuba mishi ido batare daya ce komai ba, ganin haka yasa Neehal cewa ” ina san shiga ban d’aki, 
cikin rashin fahimta Malam Liman yace ” meye kuma ban d’aki….!?

Shiru Neehal yayi batare daya san abinda zaice mishi ba, 
kana yace ” ina san zan d’an zaga ne, 
still Malam Liman bai fahimci Neehal ba, 
Neehal yace ” ina san na kewaye, ina nufin makewayi, inda zan tsuguna, 
” au! to! to! ai ban fahimta bane, kasan Hausar ba isar mu tayi ba, 
sunkuyar da kai Neehal yayi batare daya ce komai ba, d’aya daga cikin samarin Malam Liman ya kira, 
yace ” raka shi inda zai tsugunna,  “to! , saurayin yace kana ya kalli Neehal yace ” muje ko!, 
batare da yayi magana ba yabi bayan saurayin,  Malam Liman yabi bayan shi da kallo, 
zagayawa sukayi bayan bukka saurayin yace ” tsugunna nan, 
ko muyi gaba….!?

Filin Allah fetal Neehal ya kalla,  ya kalli saurayin yana zaro ido yace ” anan zan tsugunna!?

“Eh!, 
Neehal yace ” kaga fa fili ne cikin gonaki babu abinda zai tare ni koya kare ni, babu abin sakayawa a haka kake nufin na tsugunna!?

Saurayin yayi murmushi yace ” ai haka muke yi, idan mutum zayyi kashi ko fitsari cikin gona muke yi, 
idan kuma wanka ne sai mu tafi rafi, mu bamu da ban d’aki kamar ku birni mu ko’ina tsugunnawa muke yi mu biya buk’atar mu, 
a fili Neehal ya sauke numfashi gami da cewa ” gaskiya bazan iya ba, 
saurayin zayyi magana Neehal ya juya ya koma inda Malam Liman ke zaune, 
saurayin na biye dashi, Malam Liman yace ” kun dawo….!?

Neehal yayi shiru kanshi k’asa, saurayin yayiwa Malam Liman bayanin yadda sukayi da Neehal, 
d’an shiru Malam Liman yayi kana yace ” idan a matse kake kaje kayi kafin nasan abin yi, 
” a’a ba damuwa, Neehal yace, 
shiru Malam Liman ya kuma yi kafin ya kalli saurayin nan yace ” wacce bukkar dana ce muku tayi mishi k’ank’anta, 
ku bar mishi ita mazaunin makewayin, 
idan kun tashi yi mishi babbar sai kuyi mishi ita gaf da k’aramar, 
kusa da kusa yadda ko cikin dare yake da lalura zai iya shiga, 
da taimakon Malam Liman akayiwa Neehal bukka mai kyau wacce kota mai garin bata kaita kyauta ba, mai girma sosai da yalwa, 
cikin samarin wani ya koya musu yadda ake yin masan tsugunno akayi mishi,
cikin ban d’akin kana suka taya shi ya shinfid’a carpet ya sanka babbar katifarshi ciki,, 
suka shirya kayan tsaf bukkar tayi kyau sosai abin sha’awa,  
tayi kamar d’aki kasancewar akwai kome da kome, dayake bukkar nada girma sosai a cikinta daga gefe yayi kitchen, 
ya shirya kayan abinci dana girki a gefe d’aya, d’ayan gefen kuma ya shirya kayanshi, 
it look like bedroom & kitchen, sai da aka gama shirya komai kana ya kalli Malam Liman yace ” ina ake d’ebo ruwa ina san nayi wanka…!?

STORY CONTINUES BELOW


“A rafi muke wanka amma bari nasa aje gida a d’auko maka jarka sai a d’ebo maka ruwa ciki in yaso sai kayi wankan, 
Neehal yace ” ai ina da botiki bari na d’auko sai su raka ni na d’ebo ruwan, 
” a’a kabar botikinka sai ka rink’a zuba ruwan sha, jarkar kuma sai ka barta a ban d’akin, 
” nagode…!  Neehal yace a tak’aice, Malam Liman bai kula da godiyar da Neehal keyi mishi ba, 
ya mayar da hankalinshi ga samarin yana basu umarnin suje gidanshi su d’auki jarkoki biyu, 
suje rafi su ciko da ruwa kana su kawo, 
bayan samarin sun bar wajen Malam Liman ya mayar da hankalinshi ga Neehal,
yace ” ni zan koma gida saboda shirye-shiryen kawo maka matarka, 
kayi wankan sai ka huta zuwa dare za’a kawo maka matarka, 
” to nagode sosai, Neehal ya fad’a kanshi k’asa, batare da Malam Liman yayi magana ba yabar wajen, 
Neehal ya koma cikin bukkarshi ya zauna gefen katifa yana tunaninnika kala-kala, 
samarin basu jima ba suka dawo kowannen su d’auke da jarkar ruwa guda, 
cikin bukkar dake mazaunin ban d’aki suka aje kana suka sanar da Neehal sun kawo ruwan, 
cikin sanyin jiki da murya Neehal yayi musu godiya sosai, 
kana ya d’ibi kayan da zai saka ya shiga yayi wanka had’i da d’auro alwala, 
jallabiya da gajeren wando kawai ya zura ya gabatar da salla,  ya jima kan sallaya yana kuka tare da jera addu’a, 
kan auren da yayi da Najwah  yana kan sallayar ya fara jiyo gud’a tana nufo bukkarshi,
hakan ne ya tabbatar nishi da ‘yan kawo amarya ne suka iso, 
sosai gaban shi ya tsananta fad’uwa, cikin nutsuwa ya mik’e gami da ninke sallayar ya aje gefe, 
ya koma gefen shima daga k’asan carpet ya zauna, 
daga bakin k’ofa ya jiyo sallamar ‘yan kawo amarya wanda ya saka gabanshi gigitaccen fad’uwa, 
k’irjinshi yayi mahaukaciyar bugawa da tsananin k’arfin gaske, 
bakinshi na rawa ya amsa musu had’i da basu izinin shiga, 
matan da suka zo kawo Neelah bazasu wuce goma ba, dukkansu suka shiga cikin bukkar, 
dan ganewa idansu abinda matasan samarin nan suke fad’a, 
dan tuni suka kai labarin had’uwa da tsuruwar bukkar dan tunda suke basu tab’a ganin wasu abubuwan ba, 
sai a wajen Neehal, k’asan carpet suka zauna tare da zaunar da Neelah itama, 
matan suka shiga kalle-kalle suna al’ajabi, 
har suka manta da abinda ya kawo su, suka shiga magana k’asa-k’asa, 
baki ya tab’e yana binsu da kallo ganin yadda suka shagala suna kallan bukkar, 
da ganinsu ba sai ka tambaya ba kasan topical  k’auyewa ne na bugawa a jarida, 
ganin yadda suka cika mishi d’aki ga wani bashi-bashin wari na tashi, 
tunda ba turare suka sani ba, yasa shi yin gyaran murya cike da kyama yana binsu da kallo, 
tamkar yaga kashi,
gyaran muryar da yayi ne ya dawo da hankalin wasu daga cikin su gare shi, 
wata mace daga cikin matan tayi murmushin yak’e had’i da cewa ” ga yar mu nan mun baka ita amana, 
ka dubi Allah da manzonshi ka rik’e mana ita bisa gaskiya da amana dan Allah, 
kana ta juya ga Neelah dake tsugunne kanta rufe da mayafi, 
tace ” nasan halinki sarai Neelah da rashin ji da rashin kunya da fitsara, 
ki sani wannan ba namiji bane kamar kowa,  ba namiji bane kamar kowanne namiji ba, 
wannan namijin a hannunshi rayuwarki ta duniya da lahira take, 
dan haka kema ina rok’anki da kiji tsoran Allah kiyi mishi biyayya, 
kai Neelah ta d’aga batare da tayi magana ba, wata mata daga cikinsu kuma ta cafke ta d’ora daga inda d’ayar ta tsaya, 
sosai akayi musu nasiha duk da ba wani ilimin addini ne da mutanan k’auyen ba, 
d’an shiru kowa yayi d’akin yayi tsit kowa yayi jugum suna ta kalle-kalle, 
gyaran muryar Neehal ya kuma yi a karo na biyu dan ya fahimci basu da niyyar tafiya, 
da sauri suka mik’e had’i dayi musu sallama suka fita, 
suna fita yaja uban tsoki had’i da cewa ” useless villagers, 
kana ya juya da niyyar kwanciyya, daga bakin k’ofar ya kuma jin anyi sallama, 
jin muryar Malam Liman yasa shi saurin mik’ewa gami da amsa sallamar, 
an d’an jima kafin Malam Liman ya shigo hannunshi rik’e da tray,
Cikin nutsuwa Malam Liman ya zauna daga gefen Neelah a k’asan carpet, 
tare da tankwashe k’afafunshi, ya aje tray d’in a gefe, 
cikin girmamawa Neehal ya gaida Malam Liman, 
ya amsa a mutunce, d’an shiru ne ya biyo baya na wucin gadi, 
kafin Malam Liman yayi gyaran muryar cike da kamala ya soma magana, 
” bawan Allah kaji tsoran Allah, ka tuna akwai mutuwa, kwanciyar kabari da tsayyuwa gaban Allah, 
komai zakayi ka tuna akwai Allah akwai kuma hisabi, haka mutuwa gaskiya ce, 
batare dana sanka ba, kona san daga inda ka fito ba, batare dana san asalinka, 
tushenka da nasabarka ba, asali ma ban san waye kai ba, ban san daga inda ka fito ba, 
bani da sani akan ka, halaye da d’abi’unka, ban san k’abilarka da yarenka ba, 
ban san takamaiman daga inda ka fito ba, ban san su waye iyayenka,  danginka da ‘yan uwanka ba, 
babu abinda na sani daga gare ka ko naka, amma na d’auki auren tilon ‘yata wacce nafi so, 
fiye da komai da kowa na baka, bani da kowa a duniya face ita da mahaifiyarta, 
haka zalika suma basu da kowa face ni, ka tuna da alkhairi na, 
ka tuna da alkhairin danayi maka na ceton ranka da rayuwarka da nayi, 
ka tuna na ceci rayuwarka a sa’in da kake gaf da mutuwa, 
ka tuna dukkan mutanen garin nan kowa k’in baka ‘yarshi yayi, 
amma ni na d’auka na baka, dan haka ina had’aka da girman Allah, 
da girman wanda akayi duniya da lahira dominshi, ka dubi darajar mahaliccinka ka RIK’E MIN NEELAH AMANA, 
babu abinda nake nema ko buk’ata daga gare face ka rik’e min amanar NEELAH!!!, 
idan har ka rik’e min ita amana, ka biya ni, ka kula da ita da rayuwarta, ka bata kulawa dai-dai gwargwadon iyakar iyawarka, 
ka kula da addini da tarbiyyarta, ka bata ilimi dan girma Ubangijin sammai da k’assai, 
kayi min alk’awarin zaka kular min da Neelah, kayi min alk’awarin bazaka tab’a cutar da ita ba, 
tsit..! d’akin yayi babu wanda yace k’ala, idan Malam Liman kan Neehal ya kafe shi da ido yana karantar shi, 
ganin tsayin lokacin Neehal bece komai ba, bashi kuma da niyyar cewa koman, 
yasa Malam Liman sauke numfashi gami da cewa ” Allah ya sani ni dai alkhairi nayi maka, 
bana kuma tunanin zaka saka min da sharri dan da gani baka yi kama da mutanen dake saka sharri da alkhairi ba, 
ni bana buk’atar komai daga gare ka, bana san komai sai kayi min alk’awarin zaka kular min da Neelah, 
dan Allah kayi min wannan alk’awarin ko hankali da zuciya ta zasu kwanta,! 
nutsuwa ta ta dai-daita, 
a hankali Neehal ya sauke ajiyar zuciya gami da d’ago kanshi ya kalli Malam Liman, 
da sauri ya mayar da kanshi k’asa saboda had’a idon da sukayi da Malam Liman, 
yaga idanshi yayi jajir kamar gauta kwallar kuka ta cika mishi ido tana neman zubowa, 
cikin sanyin jiki gaban Neehal na fad’uwa yace ” in sha Allah zanyi iya bak’in k’ok’ari na akanta, 
murmushi Malam Liman yayi kwallar data cika masa ido ta gangaro zuwa kumatunshi, 
ya sanya hannu ya goge yana murmushi yace ” nagode! nagode sosai Muhammad Allah ya saka maka da alkhairi, 
kana ya juya ga Neelah dake zaune kanta k’asa, yace ” nasan halinki da tsiwa da rashin kunya Neelah,
wannan da kike gani ba mutum ne kamar kowa ba, shi daban yake a rayuwarki, 
yana da matuk’ar mahimmanci fiye da kowa, kada ki sake naji ance kinyi mishi tsiwa ko rashin kunya, 
duk abinda ya saki kiyi mishi babu musu, kada ki sake kiyi mishi gardama kinji ko!?

STORY CONTINUES BELOW


” To!, Neelah tace cikin sanyin murya, kallanshi ya mayar ga Neehal yace ” ga abinci nan na kawo muku da fura, 
Allah ya bamu alkhairi, Ubangiji ya tashe mu lafiya, 
” amin! Neehal yace yana mik’ewa da nufin ya raka Malam, 
” kayi zamanka karka damu kaji, bayyi magana ba sai da ya raka Malam bakin k’ofa suka k’ara yin sallama, 
kana ya dawo ya zube saman foam mattress yayi rigingine idanshi na kallan sama, 
a hankali ya lumshe idonshi ya shiga tunanin duniya da rayuwa, 
yana mamaki da al’ajabin yau wai shine cikin d’akin d’aya da mace, 
kuma a matsayin matarshi ta sunna wacce ba Najwah ba, 
kanshi girgiza gami da gyara kwanciyar shi yace ” lalle Allah shine ke tsarawa kowanne bawa rayuwarshi, 
babu wanda ya isa yasan gobe, balle jibi, 
babu wanda yasan k’addararshi ko abinda zai faru dashi, 
ya tuno haukan da Najwah keyi idan mace ta kalle shi kawai, 
ya tuno yadda yayi mata alk’awarin bazai tab’a yi mata kishiya ba sau da dama, 
ya tuno maganar da Nauman ya fad’a mishi, ya tuno irin shawarar da Mamynshi ke bawa Najwah, 
“Ikon Allah sai kallo, yace a fili yana fitar da numfashi, 
cikinshi daya karta k’irjinshi ya soma suya ne ya tuna mishi rabonshi da abinci tun kan ya shigo k’auyen Sunkhanni, 
a hankali ya bud’e idonshi yana tunanin abinda zaici, ya jima a haka kafin ya tuno da abincin da Malam Liman ya aje wanda ko kallan inda ya aje bayyi ba, 
kanshi ya d’ago ya kalli tray d’in,  a ranshi yace ” Allah dai yasa ba wannan shegen bak’in tuwon bane, 
kamar bazai tashi ba, sai kuma ya mik’e ya taka inda tray d’in yake, 
ya sanya hannu ya bud’e kwanikan, gasheshshan naman rago, 
da had’add’iyar damammiyar fura da nono ya gani, 
kama da wane bata wane, wani kayan sai amale, ganin yadda furar ta damu likui, 
taji nonon saniya ga man shanu nan kwance a sama,  yayinda gashashshen naman ragon ke tururi yasa yawon Neehal tsinkewa, 
amma saboda tsabar muskilanci da bak’in hali irin na Neehal yasa shi jan tsoki, 
had’i da komawa ya kwanta, 
wai shi karya bada kanshi. 

**********************

Tun daga k’ofar d’aki Malam Liman ya soma jiyo sautin kukan mahaifiyyar Neelah, 
da sauri ya k’arasa shiga d’akin, dan dama tun lokacin dayace ya bawa Neehal auren Neelah, 
ya lura ta shiga damuwa, ta danne damuwarta ne kawai gudun b’acin ranshi,
kasancewar ta mace mai tsananin biyayyar aure da matsanancin hak’uri kamar damo, 
dan duk duniya bata da abokin musu balle musiyar yawo ko fad’a, 
ta kasance mace mai tsananin hak’uri, kara da kawaici, tunda sukayi aure da Malam Liman, 
babu wanda zaice ya tab’a ganin ko musu tayi mishi, ko tangard’ar harshe bata tab’a yi mishi ba, 
bama shi ba haka take da gaba d’ayan mutanan k’auyen dan ta samu shaida wajen kowa, 
jin shigowar Malam yasata saurin goge hawayenta, had’i da mik’ewa tana yi mishi sannu da zuwa, 
” lafiya!  meke damunki….!?

Cikin sanyin murya tace ” bakomai, 
” a’a ina fa bakomai, bayan na shigo na ganki kina kuka,
” bakomai, ta kuma cewa tana k’ok’arin fita daga d’akin,  
” dan Allah kar muyi haka dake ki daure ki sanar dani damuwarki, 
sosai Malam ya rok’eta kafin tace ” Malam ni dai hankali na bai kwanta da auren Neelah da wannan bak’on ba,
kwata-kwata na kasa samun nutsuwa, zuciyata tak’i hutawa,  
” ashsha!  subhanallahi haba ya kike irin haka….!?

“Dan Allah karki k’ara furta irin haka, kamata yayi mu bisu da kyakkyawan fata da kuma addu’a, 
sosai Malam ya kwantar mata da hankali had’i da yi mata nasiha mai ratsa jiki. 

***********************

Jin yunwa na neman kashe shi yasa shi mik’ewa jikinshi na rawa da kerrrrrma, 
idonshi yana ganin bibbiyu ya isa gaban tray d’in yayi zaman dirshen, 
ya soma cin nama yana shan furar hannu baka hannu kwarya, 
Neelah na zaune inda aka ajiye ta, har zuwa lokacin bata motsa ba, 
bata kuma yi magana ba, har ya gama cin abincin ya k’oshi, 
a fili yayi hamdala gami da mik’ewa ya fita, ganin ya fita yasa Neelah bud’e rufin kanta, 
dan innarta (k’anwar mahaifiyarta) ta gargad’eta kan karta sake ta bud’e mayafinta, 
a hankali ta shiga bin bukkar da kallo tana mamaki dan bata tab’a ganin bukka irinta ba, 
kallanta takai ga fridge & generator k’atuwar da katifar dake aje, 
kana ta kuma kallan bargo da pillows da gidan sauro net, 
ta sanya hannunta tana shafa k’asan carpet tana mamaki bakinta bud’e, 
ta jima tana kallan bukkar tana mamaki kafin ta mik’e a hankali, 
ta nufi inda abincin yake ta zauna tana ci, 
kasancewar itama tana jin yunwar sosai, tana ci Neehal ya shigo, bai ko kalli inda take ba, 
ya wuce kan foam mattress ya kwanta, 
bayan ta gama cin abincin ta mik’e ta fita ta wanke hannunta, 
kana ta dawo ta taje gabanshi ta tsaya a hankali tace ” bacci nake ji! ina zan kwanta….!?

Jin muryarta ya sashi saurin d’ogowa a kid’ime ya kalle ta, 
ganinta da yayi yasa shi mik’ewa tsaye zumbur cikin tashin hankali, 
had’i da nuna ta da hannunshi yace ”  wannan halittar aka aura min…..!? 2

“Kina nufin kece matar da aka aura min……!?

Yayi maganar bakinshi na rawa…………!Bayanta ta juya ta kalla cikin rashin fahimtar abinda yake nufi, 
cikin k’araji Neehal yace ” wallahi bazan k’arbi wannan abun a matsayin matata ba, 
idonta kanshi batare da tsoron komai ba tace ” wanne abu kenan….!? +

Kallanta yake yi tamkar wani abun tsoro tun daga k’asa har sama, 
yaga ko irgan dangi bata fara ba, she’s so young, 
komawa yayi ya zauna saman foam jiki ba kwari, 
ya tallafe kanshi da hannayenshi yana tunani, ya dad’e a haka kafin yace ” shekararki nawa….!?

Yayi maganar yadda yake batare daya d’ago kanshi koya kalle ta ba, 
” *GOMA!* ta bashi amsa still idonta kanshi, 
a zabure ya d’ago kanshi ya kalle ta had’i da cewa ” what! goma..!?

“Meye goman, badai shekarunki goma ba….!?

“Eh! shekara ta goma mana, wani abun ne….!?

Jikinshi a sanyaye ya koma yayi zaman dirshen a k’asan carpet, 
gami da tallafe kumatunshi, take kanshi ya shiga sarawa gumi ya soma keto mishi ta ko’ina, 
duk da charge fan dake kad’awa a d’akin, idanuwanshi sukayi jajir kamar gauta, 
pure red eyes d’inshi ya d’ago ya zuba mata, yaga duka-dukanta bazata wuce jikin auta Suhaima ba, 
dayake ita a k’auye take, babu abinci mai kyau, ba tsaftaccan ruwan sha, 
balle ingantacciyar kulawa, shiyasa a jiki bazata wuce kamar Suhaima ba, 
a fili yace ” innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, 
Allahumma ajirni fi musibati wa’aklafli khairan min ha, 
ya dad’e nan tsugunne kafin ya rarrafa zuwa kan katifa ya kwanta saman katifa had’i da fad’awa duniyar tunani, 
a ranshi yace ” Astagfirullana wa atubhi alaik, Allah na tuba, wato idan nace Umaina cousin sister na, 
tayi mini kad’an da yarinta sai Allah ya nuna mani Umaima cousin sister Nauman, 
itama dana rainata sai Allah ya had’a ni da  Neesah, itama nace she’s younger, 
an now da Allah ya tashi maganinshi yanzu sai ya had’a shi da wacce ta fisu k’ank’anta, 
ta fisu rashin komai dayake magana,  k’auyenci, jahilci, k’idahumanci, wacce suka fita komaita, 
wacce bata kaisu komai ba, wacce ko’a aikatau dukkansu sunfi k’arfin su d’auke ta, 
yace ” bai auren Umaima da Umaina saboda basu da cikekken ilimin boko da wayewa, 
sannan bazasu iya d’aukarshi ba, har Neesah da tayi karatu a America, 
sai da ya kushi ta, da Allah ya tashi maganinshi sayya bashi illiterate, villager,
and she’s not wise at all, 
” zanyi bacci, ina zan kwanta…..!?

Yaji muryarta ta katse mishi tunaninshi, d’an kallanta yayi ya ganta tsaye tana ta faman soshe-soshe, 
a fili yace ” wannan rainanta zanyi ko tarbiyyarta zanyi kome…..!?

“Impact wannan rainonta kawai aka bani, RAINONTA ZANYI!, 
lalle _*RABO AJALI…!*_ duk duniya babu abinda yafi RABO k’arfi, 
dan haka ake cewa *RABO AJALI…!* kamar yadda babu wani mahaluk’i daya isa ya kaucewa ajalinshi, 
haka babu wanda ya isa ya kaucewa rabonshi, kamar yadda idan ajali ya zo ko ba ciwo ake zuwa ko babu ciwo, 
haka RABO keda k’arfi yake kuma kiran mutum zuwa gare shi duk inda yake, 
rabonka ko a bakin kura yake sayya fito ya dawo gareka, 
haka ko rabon taka waje ne dakai dole sai kaje ka taka, shiyasa idan kwanan mutum ya k’are, 
ganyen sunanshi ya fad’o k’asa, mala’ika azara’ilu sayya duba gabas da yamma, kudu da arewa, ya ga baka da sauran wani rabo a duniya dai-dai da kwayar zarra kafin a d’auki ranka, 
shiyasa Allah yace ” babu wata rai da zata d’and’ani mutuwa face ta gama cinye rabonta tas, 
” ni fa bacci nake ji! ta fad’a cikin shagwab’a da k’uruciya, 
a k’ufule Neehal yace ” a kaina zaki kwanta….!?

STORY CONTINUES BELOW


Baki ta turo mishi tana magana k’asa-k’asa,  ” yo!  ni ai bacci nake ji, tayi maganar cike da tsagwaron k’auyenci, 
“humm’un Neehal yace, kana yace ” zo ki kwanta a kaina, 
“to! , tace had’i da nufarshi dan bata san gatse yayi mata ba tunda Hausar ba isarta tayi ba,
” are you mad…!?

Yace da k’arfi yana ja baya daga zaunen da yake tamkar bala’i ke yunkaroshi, 
tsorata tayi dan haka tayi saurin ja baya, 
dan ubanki kina hauka ne….!?

” Ni dai karka k’ara zagin Baffa na, kuma badai uba na ba, 
ido Neehal ya zaro sosai jin abinda tace had’i da d’aure fuskarshi tamau, 
yace ” da wa kike…!?

Baki ta murgud’a mishi tare da kwanciya k’asan carpet daga can nesa dashi, 
tana cewa ” hikenan ni bacci na zanyi, 
kallanta yayi cike da mamakinta, ” ba dai uba na ba!  ya maimaita maganar cikin ranshi, 
” lalle zan gyara miki zama da tarbiyya dan na lura baki da tarbiyya yayi maganar yana kwanciya. 

******************

NEELAH  MUS’AB cikekkiyar bafulatana ce usul gaba da baya, 
dan kallo d’aya zaka yi mata ko batayi magana ba ka san bafulatana ce, 
‘ya d’aya tilo ga mahaifinta Mus’ab da mahaifiyarta ROOMAN, 
su irin fulanin dajin nan ne na asali tun kakanninsu, kafin daga baya su kafa d’an k’aramin k’auyensu mai suna Sunkhanni, 
dake k’aramar hukumar Hard’o-Koa’la jahar Taraba dake Nigeria, 
Neelah yarinya ce k’arama dan bazata wuce 10yrs ba, yarinya ce mai tsiwa, da rashin kunya, 
bakinta baya tab’a mutuwa wajen magana ko fad’a, duk da kasancewar iyayenta mutanen arziki masu kirki, 
da kyautatawa jama’a dan basu tab’a jurar suga an wulak’anta d’an Adam gaban idonsu, 
suna da matuk’ar hak’uri da kyautatawa al’umma, duk inda kake neman mutanen kirki masu dad’in zama, kara da kawaici idan ka samu iyayen Neelah ka gama, 
amma ita kam kamar zawo wajen rashin hak’uri, dan ko bata da lafiya magashiyan ka ka fad’awa Neelah magana saita d’ago ta baka amsa, 
gata da shegen surutu kamar tsada, magana kamar wacce ta k’one aka, 
babu abinda Neelah take so a rayuwarta kamar karatun boko dana addini, 
tana matuk’ar son tayi karatu, hakan yasa duk rashin jin Neelah ta mayar da hankalinta, 
ga primary school d’in dake k’auyensu, ta zage sosai tana karatu, 
dama gata da kwakwalwa dan duk abinda ka fad’a mata ya shiga kanta kenan har abada, 
irinsu ake kira da gifted intelligent, brilliant, dan hakan yasa duk coppers d’in da akawo suke mugun santa,
tana mayar da hankali sosai wajen karatu, shiyasa take nacewa coppers d’insu sosai, 
dan taji turanci, cikin hukuncin Allah yasa take fahimtar kad’an-kad’an, 
ta kuma iya karatu da rubuta duk da bata kware sosai ba, 
haka ma a fannin addini ta mayar da hankali sosai wajen mahaifinta, 
Malam Liman kuma Baffanta, dayake shi yayi makarantar allo yayi almajiranci, 
ya kuma yi ismiyya,  tuni ta iya bak’i,  ta kuma sauke uzu biyar cif-cif, yana kuma koya mata abubuwa da dama da suka shafi addini, 
dayake tana da yawan tambaya dan duk abinda ta gani matuk’ar bata gane shi ba, 
to saita tambaya anyi mata bayani akanshi, 
Neelah fara ce tas-tas kamar iyayenta, duk da ta kasance a k’auye inda ba wata kulawa, 
babu kayan gyaran jiki, babu sabulu mai kyau, da man shafawa mai kyau, 
amma duk da haka fara ce tas kamar zabiya, tana da yawalwar gashin kai dogo bak’i, 
mai cika wanda ya zubo mata har kusan d’uwawunta,  idanuwanta dara-dara farare kyal-kyal dasu, 
kamar madara, a lumshe kamar mai jin bacci, idanta kamar na mashaya, zara-zaran gashin idonta dana girarta, 
kam ba’a magana, don gasunan zaro-zaro, Allah yayi mata baiwar siririn dogon hanci mai kyau, 
sai d’an k’aramin tsukakken bakinta mai kamar gidan tsutsa, mai d’auke da hakwara da wushirya sama da k’asa, 
duk da kasancewar basa brush dan bama su sanshi ba, hakan baisa hak’oranta duhu farinsu ya dakushe ba, 
yadda take sirirya doguwa haka ma fuskarta doguwa ce, 
duk inda ake neman mace mai kyau, Neelah takai, dan Allah yayi mata baiwar kyau duk da ta kasance yarinya k’arama. 2

********************

Tunda Najwah tayi mafarki kan Neehal kwata-kwata hankalinya yak’i kwanciya, 
nutsuwa da hankalinta suka k’aurace mata,
musamman ma data ga har kwana biyu da yini d’aya, ba suyi waya kota ji daga gare shi ba,  sosai tsoro ya kamata, 
ta shiga matsananciyar damuws domin ta tabbatar matuk’ar yana cikin k’oshin lafiya, 
da kwanciyar hankali babu yadda za’ayi har ayi kwana biyu bai kira ta ba, 
amma saboda tsoran mahaifiyarta dole ta daure ta d’an kanne damuwarta,  deep down Allah kad’ai yasan me take ji, 
haka ma a b’angaren su Mamy da Daddy suma sun damu kwarai da rashin shi, 
Daddy ya danne damuwarshi,  bai bari ta fito ba saboda a tsammaninshi, 
bak’ar zuciyar Neehal ce ta motsa shiyasa tunda ya tafi bai kira su ba, 
duk da yasan da kamar wuya hakan.

STORY CONTINUES BELOW


***********************

Yadda Neehal yaga rana haka yaga dare ko gyangyad’i bayyi ba, 
balle bacci b’arawo ya samu damar sace shi, dan bai tab’a zaton jaririya, 
za’a bashi raino ba, duk bayan minti d’aya minti biyu sai ya juya ya kalle ta, 
had’i da jan uban tsoki, ji yake tamkar ya shak’e ta, 
gaba d’aya k’auyen haushin kowa da kowa yake ji, 
Baffa (Malam Liman) kad’ai ne baya jin haushin shi, 
baya kuma ganin laifinshi, asalima daddakon shi yake gani, 
duk da kasancewar Baffan ba wani tsoho bane, ya dai manyanta ne, 
sosai Neehal yake yabawa da hali, d’abi’u da karamcin Baffa, 
wani lokacin idan ya kalli Neelah ji yake kamar ya bankawa gaba d’aya k’auyen wuta kowa ya huta, 
shi babbar damuwarshi ma rashin service da network, yana san yayi waya da Mamy da Daddy, 
ya sanar dasu cewar ya iso lafiya, amma ba hali,  uwa uba kuma Najwah, 
wacce ya riga da yasan a halin yanzu ta shiga cikin mawuyacin hali, 
kan rashin jinshi da bata yi kwana biyu ba, yasan tana can cikin halin bak’in ciki da matsananciyar damuwa, 
tsoki ya kuma ja lokacin da idonshi ya sauka akan ‘yar Babyn robar da aka bashi *RAINO!!!*, 
yaga tayi d’ai-d’ai abinta irin kwanciyar ‘yan k’auye, tana ta baccinta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, 
sai sharar munshari take hankalinta kwance, zanin dake jikinta ya koma can gefe d’aya, 
haka ma d’an kwalinta,  k’afarta d’aya a kudu d’aya a arewa, 
pant ko ba’a maganarshi dan manyan su ma  basu sanshi ba balle kuma yara, 
wani k’ululun bak’in ciki ne ya tokarewa Neehal a wuya yaji kamar ya tashi ya shak’e ta ya murd’e mata wuya, 
take yaji duk duniya babu abinda yafi tsana da jin haushi tamkar mutanen k’auyen Sunkhanni, 
jin zuciyarshi na ayyana mishi munanan abubuwa da dama marasa kyau, ya sashi soma fad’ar ” لا حول ولا قوه الا بالله العلي العظيم انا لله وانا اليه راجعون, 
yayi ta maimaitawa cikin ranshi, a hankali nutsuwa ta soma saukar mishi, 
yaji wani irin sanyi na shiga zuciyarshi da k’irjinshi, batare daya sani ba bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi.

Bai farka ba har wajen k’arfe 8:00am na safe, cikin bacci Neehal yaji hayaniya da kwaramniya, 
a hankali ya bud’e idonshi sama-sama saboda baccin bai gama sakin shi ba, 
ganin yara sa’annin Neelah da wad’anda ma basu kaita ba, 
fal d’akin sun cika bukkar mak’il ya sashi saurin bud’e idonshi tar, 
don a zatonshi mafarki yake yi, ganinsu da yayi ne ya sashi mik’ewa zaune a zabure, 
had’i da cewa ” what…! in my room…! ?

Yadda yayi maganar ya tsorata sauran suka tsaya cak, 
suka bar abinda suke yi gami da zuba mishi ido, 
cikin fad’a yace ” uban wa ya kawo ku d’akin nan….!?

Gaba d’aya yaran suka nuna Neelah a tsorace saboda yadda Neehal keyi musu magana, 
cikin fad’a kamar zaici namansu d’anye, 
d’an tsukakken bakinta mai kama da gidan tsutsa Neelah ta turo, 
tare da cewa ” k’awaye na ne fa, kuma ai wasa muke yi, 
” nan d’akin uwar ki ne….?

Ya fad’a yana mik’ewa tsaye fuskarshi a d’aure tamau, baya taja a tsorace tana murgud’a mishi baki, 
irin na fitsararrun k’auye, juyawa yayi ga yaran ya daka musu gigitacciyar tsawa tare da cewa ” get! out! shegu masu kama da k’ok’una, 
kamar sunji abinda yace suka fice da gudu suna turereniya, 
wasu na take wasu, kuka ta saka tana buga k’afarta tace ” mun fa saba wasa dasu kullum, 
shine kawai zaka korar min k’awaye na, Allah sai na fad’awa Gwaggo, 
isa yayi gareta had’i da toshe hancinshi yace ” wallahi duk ranar da kika k’ara kawo min jakunan, 
yaran can masu kama da shantu sai naci uwarki, illiterate kawai, 
yayi maganar yana ficewa daga bukkar, bayanshi tabi da kallo tana murgud’a mishi biki, 
had’i da cewa ” kai dai ka sani, wasa ne dai bazan daina yi ba, 
ehe!  sai dai ka kahe ni! tayi maganar tana fari had’i da tafa hannu irin na k’auyawa, 
ban d’aki ya shiga yayi wanka da brush gami da d’auro alwala, 
ya dawo d’akin, ya shirya kana ya gabatar da sallah, yana kan sallaya yana azkar, 
matan inyamuran nan suka zo, kasancewar basu da tarbiyyar islama yasasu danna kai d’akin kai tsaye, 
had’i da kiran sunanshi ” Mr Lagosa!, 
bai amsa ba sai da ya gama azkar ya shafa kana ya juyo yana yi musu murmushi, 
yace ” morning! how is your day coppers….!?

STORY CONTINUES BELOW


“Fine ooo!  an you..!?

“Alhamdulillah!  ya basu amsa still yana murmushi, ido Neelah ta kafe shi dashi, take taji babu abinda take so sama da murmushin Neehal, 
sosai murmushin shi yayi bala’in burgeta duk da kasancewarta yarinya k’arama, 
ta kasa d’auke idonta daga kallanshi, d’aya daga cikin matan inyamuran, 
tace ” Mr Lagosa what is going on here, we are not understand oh!…!?

We seen you cry like a baby, an you run far far away, like lion want to catch you, all purples they follow you, an tie you, please help us to explain it, what’s wrong we beg you in the name of Jesus!, 
har ya bud’e baki da nufin yayi musu bayanin komai, daya faru, 
mummunar fad’uwar da gabanshi tayi ne ya hanashi furta koda kalma d’aya, 
d’an shiru yayi yana tunani, ya jima a haka kafin ya d’ago kanshi a hankali ya kalli Neelah dake tsaye, 
tana kallansu, idonta kanshi k’uri, a ranshi yace ” tayaya zan fad’a musu wannan abar matata ce….!?

“Tayaya zan fad’a musu wannan tatsitsiyar kwailar aka aura min….!?

“Kuma ina gudun abinda zaije ya dawo gaba, rufe baki na nayi shiru shi yafi min a’ala da alkhairi saboda tsoro da gudun abinda gaba zata haifar, 
yayi maganar cikin ranshi, “please Mr Lagosa tell us we’re so scared, please don’t hide us everything, we need to know if we’re in danger,
murmushi yayi wanda ya k’ara bayyanar da tsantsar kyau da k’uruciyarshi, 
a ranshi yace ” I must hide everything to you, because I want keep my secret, 
a fili kuma yace ” no! no! we’re not in danger, so don’t be scary, I just don’t want be here, 
so don’t be afraid we’re in safe an peaceful place, 
murmushi sukayi tare da cewa ” ah!  yesterday we’re not sleep ooo!  we think were in big trouble, 
yayi dariya yana k’ok’arin b’oye damuwarshi yace ” God for bod!  we never meet trouble by God grace, 
and w…..!  bai k’arasa ba yaji muryar Neelah na cewa ” lah ashe kaima kana da lob’awar kumatu irin nawa….!?

Gaba d’aya suka kalli wajen da suka ji maganar Neelah, kana suka mayar da kallansu ga Neehal, 
” who’s she….!?

“Oh!  I’m sorry for not introduce my house maid, so she’s my house keep an help, 
sukayi dariya gami da cewa ” how this young girl can know how to keep room clean…!?

“She’s so young,  don’t you see..!?

“Is better to change her!, she’s like baby, dariya yayi kamar ba komai yace ” she’s not bad, 
gudun kar su k’ara yin magana yasa shi saurin mik’ewa tsaye yana cewa ” let me sleep please!, 
“Okey!,  suka ce suna mik’ewa, bayan sun fita Neelah tazo gabanshi ta zauna, 
yayi saurin ha baya cike da kyankyami, yace ” ke! meye haka….!?

Batare data kula da yadda yayi mata ba, ta k’ara nufarshi, 
tsawa ya daka mata had’i da cewa ” karki kuskura ki k’ara takowa gare ni, 
kina neman sani amai, babu abinda ke tashi daga jikinki sai wari, d’oyi da hamami, 
ke baki jin warin jikin ki ne….!?

“Wari kuma..!?

Tayi maganar tana shinshina jikinta, 
tace ” ni banji komai ba, 
” ai dama gwano baya tab’a jin warin jikinshi, 
idan ke baki ji ba ni na ji, daga yau karki k’ara zuwa kusa dani, ko inda nake, 
shiru tayi tana kallan yadda tab’e baki, yana toshe hanci,  harya dasa aya, kana tace ” okey ba damuwa, idan ma warin nake, ai ba wani yayi maka dolen zama da ni ba, 
” ke!  ban d’aukar raini, most especially ma raini daga wajenki, 
wulak’antattu irinki, dan haka daga yau karki sake ina fad’a kina fad’a dan ubanki, 
shegiya ke in banda bak’ar k’addara kin isa ki taka koda inda na taka ne, 
balle zama guri d’aya da ni, ko masu aikin gidan mu sun fiki kyan gani, 
shegiya abar kyama da kyankyami, k’azama, yayi maganar yana zubar da yawo, 
sosai abin ya b’atawa Neelah rai musamman yadda Neehal ke zagin Baffa da Gwaggonta, 
baki ta murgud’a mishi cikin tsiwa tace ” karka k’ara zagar min iyaye na, 
a zafafe yadda kasan yana magana da babba yace ” idan an zaga me zakiyi dan ubanki? 2

“Oho dai, kanka da naka iyayen ka zaga ba nawa ba, “ke!  dani kike…!?

Yayi maganar yana tasowa had’i da nuna kanshi, 
” ido ta zuba mishi tana zunb’uro baki tare dayin magana ciki-ciki, 
ganin yana nufota yasata fita da gudu tana cewa ” eh! dakai d’in ake, wayace ka zagar min Baffa na, 
kallanta yayi cike da takaici yayi kwafa, kana ya shirya ya tafi primary d’in da zasu koyar acan, 
bai dawo ba sai bayan la’asar duk da k’arfe d’aya suke tashi, 
yayi zamanshi can ya gwammaci zaman can, makarantar ya tambayi wani inda zayyi waya, 
yake fad’a mishi nan babu services sai ya d’an fita daga garin ya hau wani dutse kafin ya samu yayi waya, 
ya bari da daddare ko gobe sayya rakashi, sosai Neehal yaji dad’i yayi mishi godiya, 
ya kuma tambayarshi yadda za’ayi ayi mishi wayarin generator d’inshi, 
saurayin yace ya iya ya bari gobe zayyi mishi,, 
daya dawo gida bai iske ta cikin bukkar ba, dan haka ranshi yayi kwal, 
biscuit da lemo yasha kawai ya kishingid’a, bai tashi ba sai da aka kira sallar magrib, 
yayi alwala ya tafi masallaci,  bai dawo ba sai da akayi sallar ishasha, 
zaune ya iske ta kan carpet bai kalle ta ba, ya cire kayanshi ya zura jallabiya ya  fita wanka, 
daya dawo ma bai kalle ta ba, ya shirya ya kuma cin biscuit da lemo ya kwanta, 
bai dad’e ba bacci yayi awon gaba dashi, cikin bacci ya juya yaji shi a takure, 
ya kuma juyawa yaji nauyi ya hana shi juyawa, a hankali ya mik’a hannunshi yana lalube, 
jin hannunshi saman mutum sayyayi tsammanin Najwah ce ya k’ara matse ta tsam a jikinshi, 
ya shigar da ita cikin k’irjinshi yana shafa ta, had’i da k’ok’arin had’e bakinsu yana fitar da numfashi gami da nishi………….!Jin hannunshi saman mutum yasa shi tsammanin Najwah ce ya k’ara matse ta tsam a jikinshi,
ya shigar da ita cikin k’irjinshi yana shafa ta, had’i da k’ok’arin had’e bakinsu yana fitar da numfashi gami da nishi,
cikin bacci Neelah taji bak’on yanayi yana bak’ontar duk ilahirin jikinta,
sama-sama taji kamar ana tura mata abu cikin bakinta, a d’an shagwab’e ta turo harshenta,
had’i da k’ok’arin zamewa gam ya rik’eta fuskarshi d’auke da murmushi,
muryarshi can k’asan mak’oshi yace ” ina zaki…..!?

Bai bari ta bashi amsa ba ya tura harshenshi cikin bakinta,
tare da soma sucking lips d’inta, jin abinda bata b’ata ji ba a iya tsayin rayuwar ta,
yasa ta saurin bud’e ido duk da nauyin bacci irin na Neelah,
a tsorace ta soma k’ok’arin kwace jikinta da bakinta daga gare shi amma ta kasa,
hakan yasata sakin gigitacciyar k’ara,
wacce tayi sanadiyyar dawowar Neehal cikin hayyacinshi,
wata irin muguwar hantsilawa had’i da katantanwa Neehal yayi a tsakiyar d’akin,
cikin matsanancin tashin hankali da firgici Neehal ya mik’e tsaye,
duk ilahirin jikinshi ya d’auki kerrrrma gami da tsuma, cikin d’imuwa ya nunata da yatsanshi,
yana jifanta da wani irin matsiyancin kallo batare daya iya furta koda kalma d’aya ba,
ya d’auki tsayin lokaci a haka yana k’ok’arin tuna ainahin abinda ya faru,
“no..! no…!! no…!!! yace yana dafe k’eyarshi lokacin daya tuno da abinda ya farun,
” impossible! ya fad’a dai-dai lokacin da idanshi suka sauka akan Neelah,
dake rab’e gefe tana furzar da yawo had’i da goge bakinta,
hakan daya gani ne ya k’ara tabbatarwa Neehal tabbacin kissing d’inta yayi,
tashin hankali wanda ba’a saka maka rana, cikin zallar tashin hankali Neehal yayi waje,
ya durk’ushe a k’asa cikin k’asa yana kakarin amai،  tare da zura yatsanshi cikin mak’ogwaronshi,
cikin k’ank’anin lokaci Neehal ya fita daga hayyacinshi, 
gaba d’aya ya rud’e, idonshi yayi mugun yin ja kamar gauta,
gumi ya jik’a mishi jiki sharkaf, amma yak’i daina kakarin aman,
gashi aman yak’i zuwa, babbar burin Neehal bai wuce yayi aman ba,
amma kwata-kwata babu ko alamar aman, yakai 1hr nan tsugunne yana k’ok’arin yin amai amma a banza,
Neelah na tsaye tana kallan duk abinda yake cike da mamaki,
dole ya yasa shi, tashi ya shiga ban d’aki, ya soma wanke bakinshi,
yakai 30 minutes yana wanke baki, sai da ya k’arar da toothpaste guda d’aya,
kana soma wanka cike da kyama, yake wanke jikinshi saboda k’ankyamin jikinshi daya tab’a nata,
sai da ya  d’auki tsayin lokaci yana wanke jikinshi kana ya fito ya shiga d’akin.

STORY CONTINUES BELOW


Ya barta nan tsaye tana binshi da kallo, a fili tace ” danya tab’a ni yake duk wannan abun….!?

Ta tambayi kanta, cikin d’akin ta koma itama ta zauna gefe,
Idonshi sunyi jajir kamar gauta ya zura jallabiya had’i da zama gefen katifa,
cike da zallar bak’in ciki da takaici, yayi shiru yana magana cikin ranshi,
” me nayi….!?

“Me yake shirin faruwa dani da rayuwa ta…..!?

“What’s come over me…!?

” Me nake shirin aikatawa…!?

“Anya kuwa nine, ni ne Neehal mijin Najwah….!?

Haka yayi ta zancen zuci yana yiwa kanshi tambayoyin da bashi da mai amsa mishi su,
kamar daga sama Neehal yaji Neelah tace ” dama kai d’an iska ne….!?

Pure red eyes d’inshi ya d’aga had’i da zuba mata su cike da tsantsar takaici……!
ya zuba mata ido yana kallan tatsitsiyar kwailar yarinyar dake kiranshi da D’AN ISKA….!,
ya soma k’are mata kallo tun daga sama har k’asa, kwata-kwata babu alamar halittar mace,
a tattare da ita, ko irgan dangi bata fara ba, k’irjinta a shafe kamar na babe, 
” ni dai karka sake tab’a ni, ni ba ‘yar iska bace, d’an shiru tayi kana tace ” dama ana shan baki….!?

Sosai bak’in cikin ya k’ara turnuk’e Neehal, yaji tamkar ya d’ora hannu aka ya fasa ihuuu,
ji yake kamar ya runtuma cikin daji da gudu yayi ta ihuuu saboda takaici,
cikin masifa Neehal yace ” shegiya! ke kin isa nasha bakinki dan ubanki…!?

“Kalle ki tatsitsiya kwaila dake har kike maganar kar a sake tab’a ki,
a tab’a ki a tab’i me, ko ince na tab’a me…!?

” Mace…!, ta bashi amsa tana murgud’a mishi baki,
” mace! ya maimaita cike da takaici, murmushi yayi yana kallanta cike da wulak’anci yace ” da alama kamar baki san me kalmar *MACE…!* take nufi ba,
dan inda kin san me kalmar take nufi da baki danganta kanki da ita ba,
ki kalle ki abu kamar KATAKO kice ke wai mace ce, amma a inda babu mata ko….!? 1

Ido ta zuba mishi tana kallanshi batare data ce komai ba,
” ai duk garin nan kaf ba mata dan banga mace ba, muciya dai da zani na gani, 
shegu gafallalu harda cewa mace with full confidence, murmushi tayi had’i da cewa ” rai dai wata rana kai da kanka zaka kira ni da mace,
wacce ta amsa sunanta mace in sha Allah…..!
” God forbid…! wallahi Allah har abada bazan tab’a kallanki a matsayin *’YA MACE* ba balle harna kira ki da mace,
shigiya figallliyar banza mai zubin mayun, 
ya k’arasa maganar yana zubar da wayun daya taru a bakin shi,
idanta kanshi tace ” ni ba mayya bace sai dai in kai ne mayen…!,
” dan uwarki ni ne maye….!?

” To ni meyasa kace min mayya,
tayi maganar tana tura mishi baki, kana k’asa-k’asa tace ” kuma badai uwata ba!,
” sai dai tawa….!?

“Tame zagi na…!, ” what…!?

yace a zabure! a tsorace ta mik’e tana ja baya tace ” naga ni ba zaginka nayi ba,
” useless! girl, ya fad’a yana kwantawa, daga ganin yadda yayi maganar tasan ba abu bane mai kyau dan haka tace ” hogijo mere!,
yadda ta fad’a k’asa-k’asa yasa shi fahimtar zaginshi tayi cikin harshen fullanci,
bai kuma magana ba yaja bargo ya rufa bayan ya tsartar da yawun dake tare a bakin shi,
baki ta kuma turawa kana ta koma gefe ta kwanta.

**********************************

A b’angaren Najwah kuwa ba’a magana domin al’amari yayi mugun tsananta gareta,
dan duk inda mutum yake tunanin zata shiga tsakanin damuwa,
da tsantsar tashin hankali ta shiga fiye da haka, bata cin komai bata sha komai,
bata ko bacci, duk ta rame ta fige ta k’ak’ashe ta koma kamar na Najwahn Neehal Lagosa ba,
tun mahaiyarta bata damuwa da halin da take ciki, tana shareta,
har abun itama ya fara damunta ya kuma soma bata tsoro,
danta tabbatar matuk’ar lafiyar Neehal lau babu yadda za’ayi ya d’auki wannan tsayin lokaci,
batare da ya kira gida ko sau d’aya ba, 
yauma kamar kullum Najwah na kwance a saman bed tana aikin rusgar kuka,
Mamah ta shigo tayi tsaye kanta batare data ce komai ba ta isa gareta,
ta zauna saman bed had’i da d’aukar kan Najwah ta d’ora saman cinyoyinta,
tare da shafa kanta tana bubbuga bayanta cikin sigar rarrashi,
sai da aka d’auki lokaci mai d’an tsayin kafin tace ” kiyi hak’uri Najwah ki daina kukan nan haka,
dan ba kuka ya kamata kiyi ba addu’a ya kamata kiyi, Allah yasa koma meye yazo mana da sauk’i,
addu’a itace maganin dukkan bala’i da masifun dake cikin duniya,
dan haka ita ce ta kamaceki adai-dai wannan lokacin dama kowanne lokaci,
cikin kuka Najwah tace ” getting to 1 months fa kenan har yanzu Neehal bai kira ni ba,
bai kuma kira kowa ba, ko gidansu Mamy bai kira ba, kin san kuwa matuk’ar yana lafiya zai neme mu dole,
ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka,
kanta Mamah ta cigaba da shafawa tana bubbuga bayanta kamar Baby,
tace ” ya isa haka Najwah, yanzu abinda nake so dake shiga bathroom kiyi wanka ki d’auro alwala kinji …..!?

STORY CONTINUES BELOW


Kai Najwah ta d’aga alamar taji batare data motsa ba, Mamah tace ” to ai ke kinga matsalarki,
ace mutum yana cikin matsala da damuwa amma bazai mik’a kukanshi ga Allah mai kowa da komai Ubangijin talik’ai majib’ancin lamuranmu ba…..!?

“Gaskiya matuk’ar kina so mu murya kiyi abinda nace kiyi yanzu,
dan kinfi kowa sanin bana san musu da gardama, bana kuma ban san na bayar da umarni ak’i bi,
jikin Najwah a sanyaye ta mik’e ta shiga bathroom, Mamah tace ki d’auro alwala karki manta,
tayi maganar tana fita, ta shiga kitchen ta had’o mata tea mai kauri,
had’i da paracetamol dan taji jikin Najwah da zafi sosai alaman zazzab’i,
a saman bed site ta aje mata tray d’in tana k’ok’arin fita taji k’arar bud’e k’ofar bathroom,
Mamah ta kalleta gami da cewa ” kinyi alwalar danace miki kiyi….!?

Jiki a sanyaye ta d’aga kanta alamar eh, yauwa good girl maza ki shirya kisha tea da paracetamol,
sai kiyi sallah da addu’a, ” to!  Najwah tace cikin sanyin murya,
kana Mamah ta fita tare da ja mata k’ofar.

********************************

Haka ma a fannin Mamy sosai ta shiga tashin hankali da matsananciyar damuwa،
ta matsawa Daddy sosai, kan maganar Neehal d’in، ” Alhaji ni fa gaskiya na gaji da shirun nan naka kan maganar Neehal,
Allah ya sani kullum kwanan duniya damuwa ta k’ara nunkuwa take yi,
gaskiya ya kamata kasan abinyi dan sanin kanka ne matuk’ar babu matsala,
babu yadda za’ayi Neehal yayi shiru har tsayin wannan lokacin bai nemi kowa ba,
ka fa san halin da k’asar nan take ciki na rashin tsaro, tsoro na ma d’aya kar aje kidnapping d’inshi akayi, suna can suna azabtar dashi mu muna nan muna kwana cikin ac,
ta k’arasa maganar hawaye na zoba mata,
sosai gaban Daddy yayi gigitacciyar fad’uwa matsanancin tsoro ya shige shi,
amma gudun karya k’ara d’agawa Mamy hankali yasa ya kanne halin dayake ciki,
yace ” haba Hajiya ki daina fad’ar haka mana, ai lafiya ita ke b’uya,
idan kika ji shiru to ana lafiya, kuma inda kidnapping d’inshi akayi da tuni sun kira waya,
sun buk’aci abinda suke da buk’atar, dan Allah ki taya shi da addu’a,
sosai Daddy ya kwantar mata da hankali had’i dayi mata alk’awarin zasu je har garin da weekend,
kana ta d’an kwantar da hankalinta ta kuma sanar da Najwah cewar da weekend zasu je,
amma duk da haka kwata-kwata hankalin Najwah yak’i kwanciya.

********************************

Washe gari around 8:30am Neehal ya farka, da sauri ya mik’e ganin lokaci yaja,
dan Allah Allah ya rink’a yi gari ya waye ya fita a raka shi inda service yake ya kira gida,
da Najwah dan yasan zuwa yanzu hankalinsu a mugun tashe yake kan rashin jinshi da basa yi,
a gaggauce yayi wanka ya shirya, ya fita cike da d’oki, dayaje makaranta ko signing bai tsaya yayi ba,
yayiwa wanda zai raka shi magana suka fita, sai da sukayi tafiya mai tsayi sosai,
wacce zata iya kaiwa ta 3 to 4km kafin suka k’arasa wajen da service d’in yake,
yaran yayi murmushi gami da cewa ” to mun zo waj…..!, 
bai k’arasa fad’a ba wayar Neehal ta soma k’arar notifications,
alamar shigowar sak’una, Facebook, Instagram, Snap, WhatsApp, Twitter etc, 
sukayi ta shigowa wayar kamar hauka, yayi murmushi yana sauke ajiyar zuciya a fili,
had’i da soma k’ok’arin latsa wayar amma tak’i latsuwa tayi hooking,
kasancewar yawan sak’unan dake shigowa, sai da sukayi a k’alla rabin awa kafin wayar ta saitu ta dawo normal,
hannunshi na kerrrrma yayi dialing number Mamy danya tabbatar tafi kowa shiga tashin hankali,
da matsananciyar damuwa kasancewar uwa daban take da kowa,
dai-dai lokacin da kiran ya shigo wayar Mamy tana zaune saman sallaya tana jera addu’o’in nemar mishi tsari,
had’i da mik’a kukanta ga Allah, 
wayar na soma ringing idonta ya sauka akan sunan my Apple of my eyes,
hannunta na rawa ta d’aga wayar cikin rawar baki kamar zata fashe da kuka tace ” Neehal….!?

Idonshi ya lumshe hawaye na gangarowa kan fuskarshi batare daya amsa ba,
“Neehal…! Mamy ta kuma kiran sunanshi a karo na biyu kuka na k’ok’arin kufce mata,
jin tana k’ok’arin yin kuka yasa shi saurin bud’e idonshi tare da danne duk wata damuwa da k’uncin dayake ciki,
yace ” my heartbeat I really misses you so much, 
” kana lafiya….!?

STORY CONTINUES BELOW


Mamy ta fad’a so calm, ” lafiya lau Alhamdulillah my heartbeat,
kuna lafiya kuma! ya Daddy….!?

“Duk muna lafiya, amma meyasa baka kira mu ba tun da ka tafi….!?

” Am so sorry Mamy garin ne babu service kwata-kwata,
” Neehal kasan mawuyacin halin da muka shiga sakamakon rashin jinka….!?

“Ka d’agawa kowa hankali dai-dai dasu Suhaima suna cikin damuwa,
haba Neehal meyasa kayi haka…!?

” Kiyi hak’uri Mamy wallahi Allah garin ne kwata-kwata babu service,
yanzu ma sai da na samu wani ya rako ni nan na samu service,
Allah duk yadda zan gaya miki yadda k’auyen yake Mamy bazaki tab’a zaton yakai hakan ba,
even imagination bazai iya imaging irin wannan mugun k’auyen ba,
yaron daya rako shi ya kalle shi jin kallamar saya fad’a, aiko suka had’a ido da Neehal,
sosai Neehal yaji kunya ta kamashi saboda irin kallan da yaro yayi mishi, 
na duk lalacewar garinmu ne dai, kuma muna alfahari dashi,
Neehal yayiwa yaron murmushin yak’e, yaron ya mayar mishi da martanin murmushin,
tare da kawar da kanshi gefe,
Neehal ya cigaba da magana ” sai da mukayi tafiyar 4km kafin muka samu service, 
” what…! 4 kilometers fa kace…!?

“Yes Mamy!, ” kuma a k’afa…!?

Mamy ta fad’a cikin tashin hankali,
” Allah kuwa Mamy, amma ki kwantar da hankalinki ina nan lafiya cikin kwanciyar hankali,
dan mutanen k’auyen akwaisu da kirki da karamci sosai,
ajiyar zuciya ta sauke kana tace ” Allah ya tsare min kai ya kuma kare min daga dukkan sharri,
Ubangiji yayi maka albarka ya haskaka rayuwarka, kayi hak’uri,
wata rana sai labari duk wanda kaga ya zama wani abu a rayuwa sai da yasha bak’ar wahala, 
idonshi ya lumshi cikin jin dad’i yaji wani sanyin dad’i na ratsa dukkan gab’ob’in jikinshi,
farin ciki ya lullub’e shi yaji gaba d’aya damuwa da bak’in cikin shi sun yaye,
cikin ranshi yace ” gaskiya mahaifiya daban ce,
a fili kuma yace ” amin ya Allah, Ubangiji na gode maka daka bani irin wannan mahaukaciyar,
uwa ta gari abin alkhairin kowanne d’a,
suna cikin magana Daddy ya shigo da sauri Mammy tace ” Alhaji Neehal ya kira,
basarwa yayi yace ” to madalla…!, amma cikin ranshi yaji dad’i tamkar an bashi aljanna,
ya tsinci kanshi cikin matsanancin farin cikin da rabon daya tsinci kanshi ciki harya manta,
Mamy tace ” Alhaji…! tana kallan shi, batare daya kalle ta ba, yace ” Hajiya!,
duk abinda suke yi Neehal na jinsu, yayi murmushi  had’i da cewa ” bani shi Mamy,
ba musu Mamy ta mik’awa Daddy wayar, kamar bayaso ya amshi wayarshi,
ya kara a kunnenshi had’i da cewa ” ina jinka…!, cikin shagwab’a Neehal yace ” kai! Daddy baka missing d’ina ne…!?

“Danka tambaye ni wannan maganar kace a bani wayar dama…!?

” I know you missed me so much Dad, yayi maganar yana dariya,
” akan me zanyi missing wanda bai damu da mu ba, ido Neehal ya zaro kamar yana gaban Daddy yace ” tab! lalle Daddy kaima kasan duk duniya babu abinda nafi damuwa dashi sama daku,
nasan kawai kana kishin na fara kiran Mamy ne ban kira ba,
Daddy yayi murmushi had’i da cewa ” Neehal!, 
Neehal yayi dariya yana cewa ” dama na sani ai, Daddy yace ” meyasa baka kira ba to….!?

Neehal yayi mishi bayanin daya yiwa Momy, yayi dariya tare da cewa ” kace ka motsa jikinka,
daka sani da tafiyar 7km kayi kaga daka fi jin k’arfin jikin naka ko….!?

A shagwab’e Neehal yace ” Daddy!, ” eh mana kai ba namiji bane, 
inda kazo lokacin da babu mota ko machine fa….!?

” Sai na hau jaki ko doki da rak’umi, Neehal ya amsawa Dady yana dariya,
dukkansu suka saka dariya,
kana Dady yayi mishi nasiha sosai, sukayi sallama da Daddy Momy ta amshi wayar,
harga Allah Daddy yayi bala’in tausayawa Neehal sosai, 
yana dai wagararwa ne kawai saboda yasan in Neehal yaga fuska bazai zauna yayi service d’in ba,
” Mamy zan rink’a zuwa nan kullum dan na rink’a magana dake kinji,
” a’a Neehal karka wahalar da kanka kan zuwa kullum ni dama babban buri na naji kana lafiya,
tunda kuma naji Alhamdulillah hankali na ya kwanta, dama shirun yayi yawa shine ba’a so,
amma duk sanda ka samu lokaci ka rink’a zuwa nan d’in muna gaisawa,
amma karka takura kanka kace lalle kullum sai ka zo munyi waya,
kasan yadda k’asar nan take babu tsaro kwata-kwata, kuma ba lalle ne koyaushe zaka rink’a samun wanda zai rako ba,
kaga ba tsaro ka rink’a bin dajin Allah kai kad’ai, kuma koba dan haka bama, lafiyarka ma abin dubawa ce tunda ba saba tafiyar k’afar kayi ba , idan yi zaka rink’a ciwon jiki dan haka ka bari duk sanda ka samu lokaci mayi wayar kaji Son,
ido ya lumshe yana saurarenta harta gama kana yace ” naji Mamy, itama tayi mishi nasiha sosai tare da addu’a, kana sukayi sallama.

STORY CONTINUES BELOW


Mamy na kashewa yayi dialing number Najwah duk ilahirin jikinshi na kerrrrma,
dan yasan tana cikin matsanancin halin bak’in ciki da muwa, gami da tashin hankali,
Najwan na kwance saman sofa a parlor idonta rufe amma ba bacci take ba,
wayarta ta soma ruri tana ji amma bata motsa ba, har kiran ya tsinke, 
hannun Neehal ya rawa ya sake dialing, kiran ya kuma shigowa amma Najwah bata motsa ba,
Mamah ta kalleta kamar zatayi magana sai kuma ta fasa,
har kiran ya kuma katsewa Neehal ya sake kira, kamar Mamah bazatayi magana ba,
sai kuma ta ce ” wai ni Najwah ba wayarki ake ta kira kina ji ba ne….!?

Batare data kalli Mamah  kota motsa ba, tace ” eh! itace, 
Mamah tayi shiru kamar bazatayi magana ba saboda yadda Najwah ta amsa mata,
sai ta kuma cewa ” to bazaki d’aga bane….!?

“Eh…! Najwah tace, Mamah tace ” meyasa….!?

Cike da k’osawa Najwah tace ” kawai!, Mamah bata sake magana ba,
ta mayar da kanta ga kallanta shirin gidan Badamasi da akeyi a Arewa24,
Neehal na k’ok’arin sake dialing number Najwah wayarshi ta mutu,
cikin tashin hankali ya sake kunna wayar amma tak’i kawowa,
sai lokacin ya tuna tunda yazo bai tab’a saka wayoyinshi a caji ba tunda yazo garin,
hannunshi na kerrrrma ya soma laluben d’aya wayar cikin aljihun shi,
koda ya d’auko ta gani yayi itama ta musu, cikin rawar jiki ya cewa yaron ” gaba d’aya wayoyi na sun mutu ba caji,
jiya kace min ka iya had’a generator ko…!?

Saurayin yace ” eh..! jikin Neehal na tsuma yace ” yauwa muje dan Allah ka had’a min,
ina da komai na siyo har fuel ina dashi, ba musu saurayin yace ” hikenan muje sai nayi maka,
ya fad’a cikin k’auyancin, sauri Neehal yake yi tamkar wanda zai tashi sama,
wanda yayi masifar bawa saurayin mamaki saboda da zasu zo Neehal bayyi tafiya haka ba,
d’an tsaki Najwah tayi had’i da mik’ewa ta d’auki wayarta  tayi bedroom,
ta aje wayar saman bed site kana ta nufi bathroom da niyyar shiga tana zancen zuci,
cak ta tsaya a dai-dai k’ofar shiga bathroom d’in lokacin data tuna ringing d’in wayar data ji d’azu,
take kwakwalwarta ta bata tabbacin abinda take tunanin tabbas d’azu sautin wak’ar Banke titli dil uda hai kahi door,
(Chennai express) yayi wanda shi ta sawa Neehal a ringing tone d’inshi,
wata razananniyar fad’uwa gabanta yayi cikin kid’ima da zallar tashin hankali,
ta juya da baya da gudu ta nufi inda wayar ke aje hannunta na rawa ta d’auki wayar,
ta soma dubawa sunan my Happiness, ta gani yayi mata har 5 missed call,
saboda  tsananin tashin hankali sai da wayar ta sub’uce daga hannunta,
jikinta na rawa ta durk’usa ta d’auki wayar had’i da dialing number shi, bugun farko taji switch up,
bata tabbatarwa kanta ba balle ta hak’ura duk ilahirin jikinta na b’ari kamar mazari,
ta sake dialing number still switch up, k’ara kira tayi a karo na uku still a kashe a haukace ta saki gigitacciyar k’ara had’i da buga wayar da bango tana kurma fitanannan ihuuu wanda yasa gaba d’aya gidan amsawa.

Cikin k’ank’anin lokaci Neehal da saurayin suka isa  rugar,
direct bukkarshi suka wuce tun daga nesa Neehal ya hango labulen d’akin a d’age,
amma saboda bai cikin nutsuwa yasa bai fahimci hakan ba,
suna d’an motsawa kad’an ya soma juyo kwaramniya sosai daga cikin bukkar,
amma bai damu ba, daga bakin k’ofar shiga bukkar Neehal ya fara ganin kayan sawarshi,
zube k’asa, da kwab’abb’iyar k’asa baki ya saki yana bin kayan da kallo kana ya shiga bukkar, 
tsaye yayi cak ganin yara turus dandazo guda cike da bukkar mak’il,
suna ta wasan k’asa wasu a saman katifarshi, wasu a saman carpet,
wasu saman kayanshi, sunyi caka-caka da d’akin tamkar bola,
sun wargaza komai, babu abinda yake a mahallinshi, Oga Neelah kuwa da boxer d’inshi tayi hula, tsaye kawai Neehal yayi yana kallansu,
bak’in ciki da zallar takaci suka hana shi koda motsa d’an yatsanshi,
idonshi yayi jajir bak’in cikinshi goma da gomiya kenan, abu yayi mishi biyu ya had’e mishi,
yaran suna ta hidimarsu babu wanda ya ganshi, hannunshi ya sanya ya dafe kanshi dake barazanar tarwatsewa,
lokaci d’aya gaba d’aya kamanninshi suka sauya ya zama tamkar devil monster, idonshi ya zama kamar garwashin wuta saboda ja,
zuciyarshi ta soma tafasa tana soya cikin zafin rai da tuk’uk’in zuciya Neehal yayi kansu…Zuciyarshi ta soma tafasa tana suya cikin zafin rai da tuk’uk’in zuciya Neehal yayi kansu,
d’aga idon da Neelah zatayi suka sauka akan Neehal dake dumfarosu,
a zabure kamar mayunwacin zaki, a matuk’ar razane Neelah ta kurma uban ihuuun,
had’i da yunk’urawa da niyyar guduwa, ihuun da tayi ne yasa gaba d’aya yaran suka nutsu,
Neehal da suka gani ne yasa su soma kuka suna ja baya suka had’e waje d’aya suna kuka,
” dalla ku min shuru dan banku, yayi maganar cike da hargawa, 
tsit sukayi suna zare idanuwa, Neelah yace ” uban wa yace ku shigo min d’aki….!? +

” Neelah…!, suka fad’a gaba d’ayansu,
” idan tace ku shiga wuta zaku shiga…!?

Ya kuma tambayarsu, gaba d’ayansu suka amsa da “a’a,
” ba nace karku k’ara shigo min d’aki ba….!?

“Dan Allah kayi hak’uri, suka fad’a cike da tsantsar tsoro ganin kwata-kwata,
babu alamar annuri a fuskar Neehal,
k’ara tsuke fuska yayi tamau yace ” wallahi daga yau duk ranar dana k’ara ganinku a d’aki na,
sai kun gane kuranku, dan sai na kusa kashe ku da azaba,
shegu ibilisai shaid’anu kawai, daga yau duk ranar data kuma cewa ku zo,
d’aki na kuyi wasa kuka kuma zuwa sai na yanka ku da wuk’a,
cike da tsoro yaran suka zazzaro ido, yace ” kun san yadda ake yanka kaza da saniya ko….!?

Babu wanda ya iya magana saboda tsoro, ya cigaba ” daga yau kuka k’ara shigo min d’aki yanka ku zanyi kamar yanda ake rago da kaza dan ubanku,
” ta kwarankwatsi bazamu k’ara higowa ba, aradun Allah kotace mu zo bamu zuwa,
suka fad’a cikin k’auyenci suna k’ara ruk’unk’ume junansu,
cikin tsawa yace ” get out…!, yayi maganar yana nuna k’ofar fita,
aiko kamar sunji abinda yace suka fara turereniyar fita, suna tattake junansu,
Neelah ta yunk’ura da sauri zata fice, cikin zafin nama Neehal yayi wuf ya rik’o ta gam,
tana jin ya rik’e ta ta soma kuka tana kiciyar kwacewa shiko yayi tsaye yana kallanta,
har yaran suka fita kaf kana yayi jefa da gefe ta buge kai k’um da bango,
taji buguwar sosai amma saboda tsoran da take yasa ta kanne,
ya isa inda take duk’e ya zuba mata kyawawan marika gudu biyu,
saboda tsananin azabar marin bata san sanda ta saki fitsari ba,
dan tunda Neelah take babu wanda ya tab’a ko dungurinta balle duka,
aiko ta gigice sosai tsoronshi ya kamata,
” kafin inje in dawo ki tabbatar kin gyara min d’akina tsaf kamar yadda yake,
wallahi idan kika sake na gama abinda nake baki gyara ba,
saina nad’a miki na jaki, nayi miki tsinannan dukan da sai kin kasa tashi,
kwala-kwalan idanuwanta ta zuba mishi tana kuka batare data ce komai,
” dan ubanki baki ji na…!?

STORY CONTINUES BELOW


Ya fad’a cikin zafi, da sauri tace ” ina ji, 
” yayi kyau, yace kana ya juya ya d’ebe kayan da za’a had’a generator shi ya fita,
Allah ya rufa mata asiri baiga fitsarin da tayi ba,
jikin Neelah na rawa ta soma gyaran d’akin while tana cigaba da kuka,
can nesa ya hango yaron da zayyi mishi aiki a matuk’ar tsorace kamar zaka ce mishi k’et ya ruga,
abinda yayi matuk’ar bawa Neehal mamaki kenan, amma sayya share kawai yace ” Bismillah zo ka had’a a tsorace yaran ya fara takowa,
ganin haka yasa Neehal yace ” lafiya……!?

Cikin k’auyenci yaron yace ” da gaske ana yanka mutane kamar rago….!?

Yadda yaron yayi magana yasa saura kad’an dariya kufce mishi,
amma ya dake yayi d’an guntun murmushi had’i da cewa ” kai haba ina ka tab’a jin ance ana yanka mutane…..!?

Cikin rawar baki yaron yace ” yanzu naji ka fad’awa yara, Neehal bai san sanda dariyar da yake dannewa ta kwace mishi ba,
a hankali Neelah ta d’aga labulan d’aki ta zuba mishi ido tana kallan yadda yake dariya,
yau ne karo na farko data tab’a ganinshi yana dariya, sosai ya burgeta,
dariyar ta k’awata mata shi, kyanshi da k’uruciyarshi suka fito sosai,
ta zuba mishi ido tana kallan shi ta kasa koda k’ifta idanuwanta,
a hankali taji wani abu ya tsarga mata tun dafa tafin k’afarta,
har zuwa tsakiyar kanta, taji wani abu yana ratsa k’irjinta had’i da huda zuciyarta,
ya caki k’ahon zuciyarta wanda yayi sanadiyyar saka gabanta mummunar fad’uwa,
k’irjinta yayi mahaukaciyar buguwa da tsananin gaske,
a zahirin gaskiya Neelah bata san so ba bata san me ake kira da so ba,
idanta na kanshi tana kallanshi fuskarta d’auke da yalwataccen murmushi,
hannunta saman k’irjinta ta dafe dai-dai satin zuciyarta,
sosai Neehal yayi dariya ta isheshi, kana yace ” kai ma sai kace yaron na fad’a musu ne fa kawai danna tsora ta su,
saboda gobe karsu k’ara, amma ba da gaske nake ba, ajiyar zuciya yaron ya sauke da k’arfi,
kana yace ” yauwa ni dai nace,, Neehal ya mik’a mishi kayan had’a generator, yaron ya sunkuya ya soma had’awa,
a jikinshi yaji ana kallanshi dan haka ya juya,
Neelah ya gani tsaye rik’e da tsinya a d’aya hannunta, while tana dafe da k’irjinta da d’aya hannun,
ta shagala sosai wajen kallanshi, ” ke dalla me kike yi anan..!?

Yayi maganar a tsawace, firgigit tayi had’i da had’iyar yawo k’ut ba shiri,
cikin tsoro ta fara cewa ” ammm….! hummmm…! dama…! dama….!,
” dama…! dama…! me!?

Ya fad’a idanshi cikin nata, duk da k’uruciyarta ji tayi bazata iya jure kallan cikin kwayar idanshi ba,
dan haka tayi k’asa da kanta batare data ce mishi komai ba,
” kin gama abinda na saka ki…..!?

“A’a tace cikin sanyi, wanda ita kanta bata san dalilin yin sanyin nata ba,
” baki gama ba amma kike tsaye kina kallona kamar tsohuwar mayya….!?

Still bata ce mishi komai ba, cikin fad’a yace ” wallahi karki bari nazo nan na iske ki,
cikin sanyi ta juya ta shige d’akin ta cigaba da aikin, har  Maghrib yaron bai gama had’awa ba,
” naji an kira sallah, muje muyi sallah inyaso ma k’arasa daga baya,
yaron bayyi mishi musu ba  ya bari, bai bi takan Neelah ba sukayi masallaci,
sai da Neelah tasha bak’ar wahala kafin ta gama gyara d’akin,
yayi tsaf komai ya koma muhallinsa ta fesa Air freshener kamar yadda taga yanayi,
gajiya da rashin sabo da wahala ya sanya ta zubewa k’asan carpet,
ta kwanta bata jima da kwanciya ba bacci yayi gaba da ita,
basu dawo daga masallaci ba sai da akayi sallahr ishaa dan dama Neehal ya saba,
idan yaje masallaci sallar Maghrib baya barin masallacin sai yayi sallahr ishaa,
bayan sun dawo basu d’auki lokaci mai tsayi ba yaron ya k’arasa had’a generator,
ya tayar haske ya haskake ko’ina, gaba da baya da cikin bukkar, har ban d’aki duk suka kawo haske,
kasancewar an saka globe, har d’akin inyamurai Neehal ya saka aka ja musu suma,
cikin k’ank’anin lokaci gaba d’aya ilahirin mutanen karkarar suka hallara,
gaban bukkokin su Neehal, suka cika mak’il harda me gari, maza da mata manya da yara,
wasu daga cikin su ma babu ko riga sai bante da d’aurin zani,
sororo Neehal yayi yana kallan ikon Allah, da zallar k’auyenci suna ta magana k’asa-k’asa,
da alama suna san sanin meye hasken lantarki ne, yaron daya had’a generator ne yayi musu bayani cikin harshen fullanci,
yayi musu bayani sosai yace musu itace hasken wutar lantarkin dayake basu labarin ya gani a burni,
aiko sukayi ta k’auyanci suna k’ok’arin tab’a globe d’in, 
shi dai Neehal shiru yayi cike da tsantsar mamaki da al’ajabi,
yaron ya juya ya kalli Neehal yace ” an gama maka komai babu abinda kake da buk’ata kuma….!?

STORY CONTINUES BELOW


Neehal yayi mishi murmushi had’i da cewa ” eh bana buk’atar komai,
nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, gobe mu had’u a makaranta sai na sallame ka,
yaron ya amsa cikin girmamawa tare tayi mishi sallama yabar wajen,
Neehal ya shige ban d’aki ya bar dandazon jama’a nan bakin bukkarshi, 
wanka yayi had’i dayin brush ya fito yadda ya barsu haka ya tarar dasu, 
bayyi musu magana ba yayi shigewarshi cikin bukka,
wasu duk sun zazzauna k’asa suka kallan wutar lantarki,
sosai yayi mamakin yadda Neelah ta gyara d’akin tsaf yayi need,
ga k’anshi yana tashi, baki ya tab’e gami da cewa ” shegiya ashe da samun waje ke saki yin iskanci da fitsara,
yayi maganar yana kallanta, sosai take bacci harda jan munshari kamar rago,
tayi d’ai-d’ai k’afarta d’aya ta kalli gudu d’aya ta kalli Arewa,
bak’in ciki da takaici suka k’ara turnuk’e shi, ganin wannan halittar wai matarshi ce,
” Allah ya isa an cuce ni wallahi,
yayi maganar had’i da yin kwafa, yana mik’ewa, daga shi sai towel ya kunna gas ya dafa Indomie,
ya ci kana ya mik’e yana niyyar saka kaya, a hankali a hankali Neelah ta soma bud’e idonta,
ba zato ba tsammani taga haske wal da sauri ta k’arasa ware idanta tar,
aiko idanta ya sauka akan globe d’in dake saman bukkar, sai taganshi kamar rana,
a zabure ta mik’e tana ihuun rana zata fad’o, ta nufeshi da gudu ta ruk’unk’ume shi,
ga jikinshi babu riga daga shi sai towel d’aure iya k’ugunshi,
cikin zafin rai ya soma k’ok’arin ture ta amma ina ta rik’eshi gam,
while tana cigaba da ihuuu tana tsalle, ” wayyo Allah na rana zata fad’o…..!,
tayi maganar tana yarfa hannu, cike da masifa ya bud’e bakinshi da niyyar yi mata masifa, 
cikin rashin sa’a hannunta da take yarfawa ya fad’a cikin bakinshi,
da k’arfi Neehal ya hankad’eta yayi waje da gudu, bata damu da fad’uwar da tayi ba,
ta mik’e ta bi bayanshi da gudu dan a tunaninta shima tsoran rana zata fad’o yake ji,
durk’usawa yayi k’asa yayita kelaya amai kamar wanda zai amayar da kayan cikinshi,
yadda kasan wanda ya ci kashe, tsaye tayi kanshi tana kallan yadda yake kakarin aman,
sosai taji babu dad’i a ranta da zuciyarta, taji tausayinshi sosai,
sai da ya amayar da gaba d’aya Indomie daya ci kana ya mik’e ya shiga ban d’aki,
sai lokacin Neelah ta kula da globe d’in dake waje da gefen bukkar,
da wanda ke cikin ban d’aki da bukkar inyamurai, ta kuma kula da generator dayake aiki,
sosai tayi mamakin abun, harta kai hannu zata tab’a sai tsoro ya hanata,
ta d’an jima tana kallan globe da injin kafin ta rufe aman da yayi da k’asa,
dan haka taga anayi a karkararsu, idan mutum yayi tsugunno ko hararwa sai a rufe da k’asa,
ta juya da niyyar shiga bukkar idanta ya sauka akan taron gaba d’aya jama’ar dake k’auyensu tsaye a k’ofar bukkar suna kallan generator,
da gudu Neelah ta juya ta isa gare su cike da murna fuskarta d’auke da fara’a,
tana niyyar zama Amminta ta korata cikin bukkar,
tana zumb’ura baki ta shiga bukkar ta zauna gefe, 
sai da ya sake wanka yayi brush kana ya fito, 
cikin ruwan bala’i yace ” uban wa yace ki saka min hannunki cikin baki na….!?

Kwata-kwata Neelah bata kula da abinda ya faru a lokacin ba,
san bama tasan hannunta ya shiga cikin bakinshi ba, ta bud’e baki zatayi magana, zai ta fasa ta d’anyi shiru,
tana tunani kafin tace ” dama saboda hannuna ya shiga bakinka kayi amai…..!?

” Haka fa ranar nan kayi ta kakarin amai harda wanka kayi, 
yauma gashi ka k’ara yi, cikin masifa yace ” wallahi daga yau kika k’ara gangancin tab’a ni,
ko kika yi gigin bari jikinki ya tab’a nawa, Allah sai kin gane kuranki sai kin gwammaci kid’a da karatu ,
stupid girl yayi maganar kamar zai dake ta,
baki ta murgud’a mishi had’i da cewa ” wande,
” me kika ce dan ubanki….!?

Tana turo baki tace ” kai ma me kace….!?

” Daga yau kar in k’ara yi miki magana da Hausa ki mayar min da Fulatanci,
ciki-ciki tace ” nima kada ka sake yi min yaran arna,
gadan-gadan ya nufo ta kamar zai yagi naman jikinta,
tayi saurin ja baya tana cewa ” kayi hak’uri..! karka k’ara duka na,
idiot yace yana juyawa, jallabiya ya zura had’i da zama kan katifa ya d’auki wayoyinshi,
yana ganin sak’unan sa suka shigo d’azu,
tana rakub’e gefe ta murgud’a baki tare da cewa ” suture, cike da tsiwa, yayi kamar bai jita ba, ya cigaba da abinda yake yi,
wajen k’arfe tara na dare ta fara gyangyad’i,
” ke wai dan ubanki baki da aiki sai bacci ne….!?

STORY CONTINUES BELOW


“To me zanyi maka…!?

” Ke…! baki wanka ne….!?

Ba tayi magana ba ta turo baki tana soshe-soshe,
” uhummm I know ai dama dole kiyi susa tunda daud’a ta samu mahallin zama,
tunda nake ban tab’a ganin kinyi wanka ko brush ba,
cikin tsiwa tace ” amma ai ina sallah ko….!?

Tayi maganar tana k’ok’arin kwanciya, ” tashi kije kiyi wanka,
k’azamar banza k’azamar wofi, babu abinda kike yi sai d’oyi,
baki ta murgud’a tare da cewa ” Allah bana wari, ” ke kin san Allah yau baki kwana d’akin nan idan baki yi wanka ba,
na gaji da shak’ar wari, d’oyi da hamami, “naga ina wanka a rafi, ina kuma wanke baki na da gawayi,
” nace ki tashi kije kiyi wanka ko….!?

Yayi maganar cikin hargowa, tsoro ne yasata mik’ewa da sauri,
jikinta yana rawa ta fita har tana neman fad’uwa, ya bi bayanta da kallo cike da kyama,
yana k’ok’arin kishingid’a ya tuna da sponge & brush d’inshi,
da sauri ya mik’e yabi ta, ya iske ta tsaye k’ofar bukka,
cikin b’acin rai ya daka mata gigitacciyar tsawa, ” bazaki shiga kiyi wankan ba dan ubanki…..!?

Jikinta na b’ari saboda tsoro ta shiga ban d’akin, ya bi bayanta,
tana k’ok’arin cire kaya ya shigo cak ta tsaya tare da cewa ” me zakayi……!?

Bayyi mata magana ba saboda tuk’uk’in bak’in cikin dayaji ya tokare mishi mak’ogwaro,
ya d’auki brush da toothpaste, sponge & soap ya bata yace ” daga yau dasu zaki rink’a amfani,
idanta kanshi ta amsa tare da cewa ” nagode, bai amsa ba ya fita, 
ta jima a ban d’akin kana ta fito, ta zazzage jakar kayanta k’asa ta zab’i kaya ta saka,
ya bud’e trolley d’inshi ya d’auko air freshener ya jefa mata,
yana kalleta a wulak’ance yace ” gaja kucaka….! d’auki ki rink’a fesawa, batayi mishi magana ba,
ta harta gama shiryawa, bata ko kalli inda ya jefo Air freshener ba,
balle ta d’auka, saboda zuciya, kasan Fulani da bak’in rai gami da gama, 
tsaye tayi kanshi batare da tayi mishi magana ba, sai da ya gaji da tsaya mishi da tayi aka,
yace ” wai ke baki da hankali ne zaki tsaya min aka ki kafe ni da ido, me zan baki….!?

“Bacci nake ji! ta bashi amsa cikin kasala tana hamma, yace ” to sai akayi yaya….!?

“Ina zan kwanta….!?

Kallanta yayi shek’ek’e kamar babba kana yace ” in da kika ga ya dace ki kwanta,
ya fad’a idanshi na kan waya yana latsawa,
tafiya tayi da niyyar hawa saman katifar yayi saurin mik’ewa zaune had’i da zuba mata uwar harara,
baki ta turo ba tare da ta daina tunkarar katifar ba,
” ke!  ina zaki kwanta….!?

“Nan tace tana nuna mishi saman katifar, ” you are mad! yace yana kallanta,
” to bana ce ka fad’a min inda zan kwanta kak’i ba,
” ke har kina tunanin ni zan had’a wajen kwanciya dake….!?

Shiru tayi had’i da tsare shi da kwakwalan idanuwanta, dan bata fahimci abinda yake nufi ba,
” Allah ya tsare ni da had’a wajen kwanciya dake, wallahi har abada bazan tab’a had’a wajen kwanciya dake ba,
koda zan mutu, ko da za’a k’ona ni da rai na bazan tab’a had’a shinfid’a dake ba,
yayi maganar yana zuba mata kallan banza,
” to ba Ammi tace min tare zamu rink’a kwana ba, tace tare zamu rink’a kwana shinfid’a d’aya,
tayi maganar a nutse, ” da wa d’in….!?

Ya fad’a kamar an fusgi maganar daga bakin shi, tace ” da kai mana!, ai Ammi tace munyi aure kai miji nane yanzu ni matarka ce,
” kam bura uba…! yace yana kallanta up an down shek’ek’e kamar kashi,
ji yayi tamkar ta watsa mishi wuta cikin ranshi saboda zafi da rad’ad’in daya ji,
” waye mijin naki….!?

Yace yana tsareta da shanyayyun idanuwanshi masu kama dana mashaya,
baki ta d’an zumb’uro kana tace ” kai mana,
” God forbid! ya Allah ya tsare ni da zama mijinki har abada,
Allah ya kiyashe ni tab’ewa, dan k’arshen tab’ewa da lalacewar da zanyi,
a rayuwa ta shine na amsa sunan MIJINKI…!,
ko na kira ki da sunan MATATA….!, ki saka a ranki har abada har a tashi duniya bazan tab’a kiranki da mace ba,
balle na kira ki MATATA….!, ki aje a ranki bazan tab’a amsa sunan MIJINKI…..! ba,
wallahi tallahi na rantse da girman Allah ko da za’ yagi naman jikina d’anye,
bazan tab’a sanki ko ba, bazan tab’a alak’anta kai na dake ba, dake da duk wani daya shafeki,
ko ya alak’antu dake har abada bana sanku bana k’aunar ku,
bazan tab’a san duk wani daya shafe ki koya alak’antu dake ba,
sai kije ki fad’awa ita Ammin taki data fad’a miki ni mijinki ne,
da har kike fiffika ke wai ga me miji, duk da kasancewar ta yarinya k’arama,
sai da taji zafin maganganun daya fad’a mata, musamman dayace baya santa,
bazai kuma tab’a santa ba, take jikinta yayi mugun yin sanyi, murmushi tayi batare data ce mishi komai ba,
ta kwanta nan k’asan carpet, har wajen k’arfe 12:00am na dare, Neelah batayi bacci ba,
tana juya maganganun Neehal cikin ranta, Allah Allah,
take yi gare ya waye taje ta tambayi Dadanta, while shima Allah Allah yake yi gari ya waye,
yaje yaji muryar sahibarshi.

STORY CONTINUES BELOW


*********************************

Mamah da Nabeelah suna zaune parlor suka jiyo ihuuun da Najwah,
cikin kid’ima suka nufi bedroom d’in da gudu, 
Mamah na shiga Najwah ta mik’e ta nufe ta tana ihunnn kuka tace ” Mamah shine ya kira ni,
” wah…!?

Mamah ce cikin kad’awa, “Neehal Najwah tace tana kuka,
sosai tsoro ya kama Mamah cikin rawar baki tace ” meya same shi…..!?

Saboda tunaninta ko mutuwa Neehal d’in yayi, cikin mahaukacin kuka Najwah tace ” Mamah d’azu shine ya kira ni ban d’aga ba,
tsoki Mamah taja had’i da watsa mata kallan banza tace ” yayi kyau ai….!,
tana fad’ar haka ta fita, Najwah ta d’ora hannu aka tana tuntuma uban ihuuu,
cikin nutsuwa k’anwarta Nabeelah (k’anwarta),
ta durk’usa gaban tana rarrashinta gami da bata hak’uri,
amma yadda kasan k’ara zuga Najwah take yi, 
” Nabeelah zaki bar d’akin nan ko sai na zo na same anan,
jiki a sanyaye Nabeelah ta mik’e ta fita, iske Mamah a parlor,
cikin girmamawa tace ” Mamah meyasa bazaki rarrashe ta ba…..!?

“Wa ni zan rarrashe bayan rashin mutuncin da tayi min kan nace ta d’aga wayar….!?

” Rashin mutunci kuma Mamah….!?

“Wallahi kuwa lokacin dayake kira danayi mata magana ta d’aga wayar har tsaki tayi min,
ko kallo na bata yi ba, kuma dan Allah ya nuna mata kuskuranta ya nuna mata mahimmancin uwa,
ni kuma sai naje ina rarrashin ta….!?

” Da tabi maganata, ta d’aga wayar a lokacin da bata shiga halin da take ciki yanzu ba,
” Allah ya kyauta! cewar Nabeelah cikin sanyi, Mamah ta amsa da ” Amin,
sosai Najwah tayi ta hauka tana ihuuun kuka, yadda kasan ranta zai fita,
tunda ta durk’ushe tana kuka bata bar wajen ba har garin Allah ya waye tangaran,
dan babu ma maganar bacci balle alamarsa.

********************************

Washe da wuri Neehal ya tashi ya shirya ya fita wajen da service yake,
ko neman abokin rakiya bayyi ba, cikin d’oki da zumud’i yayi dialing number Najwah,
Najwah na durk’ushe a inda take tana ta faman kuka taji wayarta ta soma ringing,
da har zata share sai kuma ta tuna da abinda ya faru, dan kwata-kwata bata cikin hankalinta,
bama ta lura da call ringing d’in shi ba, hannunta na rawa ta d’auki wayar,
aiko idanta ya sauka akan sunan shi, take jikinta ya d’auki rawa kamar maza, har wayar na sab’ucewa daga hannunta,
hannu biyu ta sanya ta d’auki wayar had’i da yin picking ta kara a kunnenta,
cikin rawar baki tace ” hello….!, ido ya lumshe had’i cusa hannunshi cikin kwantacciyar sumar kanshi,
fuskarshi d’auke da murmushi yace ” my everything…!,
wani sabon kukan ne ya kuma kufcewa Najwah saboda tsananin farin ciki,
take Neehal yaji bugun zuciyarshi ya tsananta, ta soma bugawa da sauri da sauri,
tana tsalle tamkar zata tsaga k’irjinshi ta fita, da sauri ya sanya hannu ya dafe k’irjinshi,
dake barazanar tarwatsewa, had’i da bud’e idanshi, cikin sassanyar murya yace ” yi hak’uri,
nasan nayi laifi I’m very sorry ban k’arawa, yayi maganar kamar me shirin yin kuka,
shiru Najwah tayi tana cigaba da kukanta, yace ” kin kasan dai kukanki yana d’aga min hankali ko….!?

Kai ta d’aga mishi kamar yana ganinta, yace ” to kin san haka meyasa kike kukan…!?

“Ko so kike ki d’aga min hankali….!?

Kukan dayaci k’arfinta ne ya hanata koda furta kalma d’aya,
” please say something mana,
kiyi min magana ko hankali ya kwanta, nutsuwa ta ta dawo jikina,
I really misses you my heart, shirun dai ta kuma yi, k’asa ya k’ara yi da murya cikin sigar rarrashi,
yace ” I beg you talk to me please, dan Allah ki taimaka kice wani abu,
kalmar data fara fituwa daga bakin ta, shine, ” kana tare da wata mace ko…..!?

Tayi maganar tamkar ranta zai fita,
da k’arfi gabanshi yayi muguwar fad’uwa, yaji k’afafuwanshi na neman kasa d’aukar shi,
ya kasa furta mata koda kalma d’aya, jin yayi shiru yasa Najwah fashewa da gigitaccen kuka,
tare sa kurma uban ihuuu tana cewa ” wayyo Allah na shiga uku na lalace,
rayuwa ta tazo k’arshe wallahi Allah Neehal mutuwa zanyi,
bazan tab’a iya sharing d’inka ba, bazan juri wata ‘ya mace ta kuma mallakarka ba,
ta k’arasa maganar numfashinta yana d’aukewa,
had’i da zubewa k’asa……….!Cikin zafin rai Neehal yace ” wannan itace kalma ta farko da zaki fara yi min magana da ita…..!?

” Baki tambaye ni ya nake ba, baki tambaye ni lafiya ta da inda nake ba…!,
sai wani zancen banza kika fara yi min, good yayi kyau!,
saboda nayi waya dake ko bacci kirki banyi ba, & saida nayi tafiyar 4km,
amma shine kika yi min wannan tarbar ko….!?

“Baki tambaye ni duk abinda ya shafi lafiya da rayuwa ta ba,
babu tambayar yanayi ko halin danake ciki, saboda lafiyata da rayuwa ta basu dame ki ba,
sai zancen mace bayan kin san matuk’ar lafiyar Allah babu yadda za’ayi na d’auki lokaci haka banyi waya dake ba,
to hell with you Najwah, dakyar Najwah tayi k’ok’arin saita nutsuwarta,
tace ” kayi hak’uri wallahi munanan mafarkai nake tayi ne,
” to da kike ta munayen mafarkai abinda ya kamata kiyi min yanzu kenan…..!?

“Ko ke a ganinki ta wannan hanyar ya kamata ace kin tarbeni….!?

” Ai da kike mugayen mafarkan ne ma ya kamata ki tambaye ni lafiya ta,
ya kuma kamata ki tsaya kiji abinda zance miki, amma dayake jahilin kishin ya gama rufe miki ido,
bama ki tsaya kin saurari halin danake ciki ba, balle ki tsaya kiji abinda zance miki,
imma a cikin wani yanayi ko mugun hali nake duk bai dame ki ba,
saboda rayuwata da lafiya duk basu shafe ki ba, basa kuma gabanki,
yayi maganar da d’an zafi, cikin matsanancin kuka har muryarta na shak’ewa,
tace ” mafarki nayi kana rayuwa da wata mace,
yadda kasan rugugin saukar aradu haka k’irjin Neehal yayi muguwar bugawa da tsananin k’arfin gaske,
cikin rawar murya da d’an fad’a yayi k’arfin halin cewa ” saboda ni fasik’i ne kuma  mazinaci ne ko….!?

“Saboda ni babu abinda ke gaba na sai mata……!
wai ni tsaya ma dan Allah Najwah me kike d’auka ni ne….!?

“Wanne irin kallo kike min…..!?

” A layin wad’anne irin mutune kika aje ni, mazinaci, ko fasik’i ko mutumin banza ko me……?

Ya k’arasa maganar muryarshi na cracking, cikin muryar kuka tace ” Allah ko d’aya bana yi maka kallan d’aya daga ciki,
kawai hankalina ne yak’i kwanciya, nutsuwata tak’i barina na samu salama,
tunane-tunane sunyiwa zuciyata yawa, kullum cikin tunani nake,
saboda jiki na yana bani abubuwa da dama,
ko nayi k’ok’arin k’aryata zuciyata da abinda jikina yake bani,
bana iyawa na rasa meyasa, but am sorry,
” saboda abinda kika sakawa ranki kenan, shiyasa kika k’i kyale kanki zama lafiya,
cikin lumana da kwanciyar hankali, ke kullum kina cikin yi min mummunan zato,
baki tab’a kyautata min zato na rasa dalili,
kuma abun yana matuk’ar damuna ace matata ta sunna itake yi min wani irin kallo,
itake zarginna, tak’i kyautata min zato, a zahirin gaskiya idan nace miki ban jin haushi nayi miki k’arya,
dan abun yana matuk’ar damu na, yana k’ona min rai na,
ke baki bar kanki kin samu nutsuwar ruhi da salama a zuciyarki ba,
nima baki barni ba, gaskiya ki canja, yayi maganar cikin k’arfin hali,
” to amma dai ai na baka hak’uri ko….!?

STORY CONTINUES BELOW


” Kuma na hak’ura ba, yayi maganar yana murmushi tamkar yana gabanta,
cikin k’asa da murya tace ” to meyasa baka kira ni ba…..!?

“Kin k’ara kenan…!, idan ance kibar wannan sai ki komawa wannan,
kuma kin san dai babu abinda zai hanani kiranki matuk’ar babu wani abun ko…..!?

Cikin shagwab’a tace ” me kuma nayi yanzu….!?

“Au bama kisan me kikayi ba kenan…?

” Eh! tace tana sakin murmushi, ” tom tunda baki sani ba shikenan,
” a’a please ni dai ka fad’a min, ta fad’a tana neman saka mishi kuka,
” yi shiru dear daina kukan, kin san me kikayi…..!?

“A’a! tace tana gyara kwanciyar ta saman carpet, yace ” ba yanzu na gama miki fad’an baki tambaye ni lafiyata ba,…..!?

“Eh…!, ta kuma bashi amsa, yace ”  yanzu instead of ki tambayi lafiyartawa,
sai kika kuma k’arawa kika tambaye ni dalilin dayasa ban kira ba,
cikin shagwab’a tace ” ayya sorry my heartbeat, ya kake…!?

” Ban so tunda sai da na rok’a, yayi maganar yana kyaikwayon muryarta,
tana dariya sosai tace ” au dama haka nake magana….!?

“Da baki sani ba….!?

” Ina kuwa zan sani tunda baka tab’a fad’a min ba, amma kaga ai na sani yanzu ko….!?

Sun dad’e suna waya cikin zallar so da k’aunar junansu, yadda kasan su fasa wayoyin su iske juna,
sun kai a k’alla 2hrs suna waya, kana Neehal yace ” tom lokacin shiga aji na ya kusa,
kuma kin san sai nayi doguwar tafiya a k’afa ta 4klms kafin koma gida,
” ayya sorry my Happiness, yanzu sai yaushe kuma….!?

” In sha Allah idan na samu dama zaki sake ji na dear,
” kamar ya sai ka samu lokaci…..!?

“Kamar yadda nake fad’a miki, tunda ke baki ganewa, kanki kawai kika sani….!,
baki ta turo kamar yana ganinta tace ” Allah ni dai a’a kawai kullum ka rink’a zuwa muna waya,
” tafiyar 8km kike so na rink’a yi kullum a k’afa….!?

“Eh! Allah ni dai ina san jin muryarka kullum,
” lalle uwa daban ce, lokacin dana ce zan rink’a kiran Mamy da Dady kullum cewa sukayi a’a,
saboda lafiyata da rashin tsoro, Allah yayi gaskiya daya fifita mahaifiya a saman kowa,
yayi maganar cikin ranshi, a zahiri kuma yace ” baki tausayi na Najwah….!?

“Baki damu da tsaran lafiyata ba, baki san komai ba sai kanki, 
koma me zai faru ke dai na kira ko…..!?

” A’a ba haka bane ina san jin muryarka ne, Allah I really misses you so much,
” I know you missed me, amma sai kice kullum nayi tafiyar 8km,
aiko cewa nayi zanzo kullum muyi waya ke me cewa a’a na bari ce,
” kayi hak’uri….! ta fad’a cikin sanyi, murmushi yayi had’i da cewa ” ai baki laifi ke kanki kin sani,
imma kinyi an yafe miki, tun kafin ma kiyi an yafe miki,
sai da suka k’ara yin wayar 1hr kana sukayi sallama dakyar suka rabu, 
bayan ta bashi Mamah da Nabeelah sun gaisa, zuciyar Neehal fess ya koma karkarar,
ji yake tamkar an bashi kyautar Aljannah saboda yadda yake jin zuciyarshi sakayau,
yana tafe yana murmushi kamar  mahaukaci sabon kamu.

********************************

Ko data ta tashi daga bacci bata ganshi ba bata wani damu ba, bakinta ta kuskure da sauri,
bata tsaya yin komai ba ta nufi gidan su wajen Abpa da Dadanta,
a gindin murhu ta iske Dadanta tana hura wuta da baki, cikin mutuwar jiki ta zauna k’asa,
kwata-kwata fuskarta babu walwala, d’an kallanta Dada tayi,
kana tace ” lafiya dai Bilgel….!?

Dada ta fad’a batare data daina hurar wutar ba, shiru Neelah tayi na d’an wucin gadi kafin tace ” Dada’am dama kowa mijinshi baya sanshi….!?

Dakatawa Dada tayi da hurar wutar had’i da d’agowa ta kalle ta,
kamar zatayi mata magana sai kuma ta fasa ta cigaba da hura wutar,
Neelah ta cigaba da ciwa ” meye aure, meye so me aure yake nufi, meye miji…..!?

STORY CONTINUES BELOW


D’agowa Dada tayi a karo na biyu ta kalleta sosai kana ta kauda idonta had’i da mik’ewa,
tana k’ok’arin barin wajen Neelah tace ” Dada idan mutum yace baya sanka bazai tab’a sanka ba me yake nufi….!?

” Aure hanya ce ta neman Aljanna, hanya ce dake sada mutum da rahamar Ubangiji,
abu ne dake k’unshe da dukkan farin ciki, da jin dad’in duniya,
haka hanya ce dake kai mutum wuta, ko sada mutu da fushin Ubangiji,
kuma abu ne mai k’unshe da bak’in ciki, b’acin rai da damuwa, 
dole sai anyi hak’uri, juriya, an kawar dakai sannan za’a cimma nasararshi,
cewar Abpa (Malam Liman) yana shigowa,, fuskarshi d’auke da murmushi,
” miji kuma shine shugaban mace duniya da lahira, shine hanyar tsirarta, 
shi wani ginshik’i ne na rayuwar d’iya mace, wanda ba’a had’ashi da komai,, 
ba’a zaginshi, ba’a yi mishi musu ko gardama, ba’a so yana fad’a kina fad’a,
miji mutum ne da ake bawa girma, dajara da k’ima, da marta ba a d’aukake shi fiye da kowa a duniya,
” so kuma wata halitta ce da Allah ya halitta tsakanin kowacce irin halitta,
wacce duk bayanin da zanyi miki bazaki gane yanzu ba, sai zuwa gaba,
kasak’e  Neelah tayi tana sauraron Abpa harya dasa aya,
kana tace ” to Abpa idan mutum yace ” baya sanya shikenan bazai tab’a sanka ba…..!?

“A’a Mamana, idan mutum yace baya saka yau me yiwa gobe ya dawo yace yana sanka,
haka idan yace yana sanka yau me yiwa gobe ya dawo yace baya sanka,
” to Abpa me akeyi aso mutum kuma me ake yi a daina san mutum….!?

” Ki zauna da suk wanda Allah ya had’a zama dashi lafiya,
ki zama mai kyakkyawar mu’amula tsakanin ki da mutane,
ki zama mai gaskiya, amana, tsoran Allah, tausayi da jin k’ai, 
mai ladabi da biyayya, ki kasance mai kyautatawa al’umma, 
ki guji duk abinda zai had’aki sab’ani da mutane, ki guji sab’awa mutane,
kiyi k’ok’ari duk wanda Allah ya had’aki zama dashi ku rabo lafiya,
ki gujiya zuciya da abin hannun mutane, kada ki kasance mai kwad’ayi, ko saka ido akan komai, ki tsarkake zuciyarki ki zauna da kowa lafiya, cikin aminci,
kada ki nufi kowa da sharri ko mugun nufi, 
” idan nayi haka zai so ni nima…!?

“Sosai ma kuwa tunda mijinki ne,
” miji na kuma Apba…!?

“Eh! mana Mamana mijiki ne,
” to ai shi yace ba miji na bane kuma bazai tab’a kira na da matarshi ba,
ajiyar zuciya Abpa yayi gami da satar kallan Dada, akayi sa’a itama shi take kallo,
basarwa Abpa yayi ya cigaba ” kul..! Mamana daga yau karki k’ara zuwa kice yayi miki wani abu,
kada ku k’ara yin magana ko abu naji kin sake kin k’ara fad’awa kowa a duniya,
duk abinda yayi miki koya fad’a kiyi hak’uri wata rana in sha Allah sai labari,
duk abinda zai faru tsakanin ku ki barshi tsakanin ku, kada ki kasance mai fallasa sirrin aure dana mijinta,
cikin sanyin jiki tace ” to Abpa meyasa yace ni ba matarshi bace……!?

Murmushi Abpa yayi irin na manya had’i da shafa kanta yace ” bai isa yace ke ba matarshi bace tunda Allah ya riga da k’addara hakan,
Allah ya riga ya d’ora mishi nauyi da hak’k’inki, ruwanshi ne yaji tsoran Allah,
amma ke matarshi halak malak, haka kuma  shima yake mijinki halak malak,
ke dai kiji tsoran Allah kiyi mishi biyayya, 
” Abpa zai so ni wata rana….!?

“In sha Allah zai so ki, ki dai kiyi mishi biyayya ki kuma ji tsoran Allah,
ki tsarkake zuciyarki ki zauna dashi bisa gaskiya da amana,
idan kika sake kika sab’a umarninshi ko kika cutar dashi, kika ha’ince shi,
Allah bazai tab’a kyale ki ba, sai ki d’and’ani azabatar Allah matuk’ar ba yafe miki yayi ba,
tana k’ok’arin yin magana Abpa ya mik’e had’i da cewa ” ya isa haka Mamana, 
yanzu yana ina….!?

“Nima dana tashi ban ganshi ba, ido Abpa ya zare gami da tsuke fuska yace ” bai sani ba kika taho….!?

“Eh mana! tace cike da k’uruciya, Abpa yace ” kina san Allah yayi fushi dake ya kuma k’ona ki a wuta…..!?

” A’a…! Abpa ta fad’a tana zaro ido,
Abpa yace ” to matuk’ar baki san Allah yayi fushi dake ya kuma k’ona ki a wuta,
kada ki k’ara fitowa ba tare da izinin mijinki ba, kada ki k’ara zuwa ko’ina har sai kin tambaye shi,
ya baki izini, idan bai barki ba ki hak’ura ko mutuwa zakiyi,
cikin sanyi tace ” to dole ne idan zan fita sai na tambaya…!?

STORY CONTINUES BELOW


” Shalele na yayinda yara mata suka kai munzali basa fita daga gida batare da izinin na gaba dasu ba, sab’anin hakan yakanzo da matsaloli ga rayuwarsu,
” to Abpa’am, ” yauwa Mamana maza tashi ki koma kinji, baki ta turo tare da cewa ” ban ci abinci ba yunwa nake ji,
sai lokacin Abpa yakai dubanshi ga Dada yace ” kin gama abincin ne….!?

“Na dai kusa..!, ” yauwa to idan kin gama ki samu yaro yakai musu,
kana ya mayar da kallanshi ga Neelah yace ” to kinji dai bata gama ba idan ta gama zata bayar akai miki,
shure-shuren k’afa Neelah ta soma cikin shagwab’a tana tab’e baki zatayi kuka tace ” Allah ni dai yunwa nake ji Abpa,
” yi shuru Mamana, zaki sha fura…!?

Baki ta washe had’i da cewa ” da zuma….!?

“Hummm sarkin kwad’ayi, akwai zuma, Abpa yayi maganar yana shiga bukkarshi,
ya d’auko kwaryar fura ya kawo mata, ” gashi maza kisha ki tashi ki koma,
batayi magana ba ta amsa tana murmushi, sai da tasha ta isheta sosai, kana ta mik’e zata tafi,
Abpa yace ” karfa ki sake ki biya ko’ina, ki koma bukkarku,
” to Abpa’am, ta fad’a tana fita daga bukkarsu.

******************************

A kishingid’a Neelah ta iske Neehal kanshi yana kallan sama,
fuskarshi d’auke da murmushi, kallo d’aya zakayi mishi kasan yana cikin matsanancin farin ciki,
batayi mishi magana ba ta koma can gefe ta zauna had’i da kafeshi da ido,
ta rasa dalilin dayasa duk lokacin data kalleshi, take jin sanyin dad’i na ratsa dukkan jikinta,
ta rink’a jin sassanyar iska mai cike da ni’ima tana kad’awa a sassan jikinta,
a hankali itama ta soma sakin murmushi had’i da rausaya kanta, saboda tsabar shauk’in so.

_Ni ko nace dukkanku kuna cikin wani yanayi kun shiga coci marar fasto, Allah ya taro ku, Neehal yana mararin shauk’in Najwah, Neehal ta fara d’and’anar zak’in so, son maso wani k’oshin wahala…..!!_

Muryarta k’asa-k’asa ta furta   ” Bodd’o..! (mai kyau ko kyakkyawa),
” ke wai mayya ce ….!?

Taji muryarshi ta bugi dodon kunnenta,, kanta ta kawar gefe batare datace komai ba,
” kallan uwar me kike yi min….!?

“Bakomai…!, ta bashi amsa cikin nutsuwa,
” shegiya mayya bak’ar daga, ko mayya ce sai kin ganni kin kyale ni,
hannu ta tafa had’i da cewa ” ahayyeee…! bira wand’e, tayi maganar cike da zallar k’auyanci,
” ke..! dan uwarki ni kike yiwa shewa da ihuuu aka…!, sa’anki ne…!?

“Eh..! tace tana kama k’ugu had’i da jijjige-jijjige da murgud’a mishi baki,
irin fitsararrun k’auye
kauuuuui! kauuuuuu Neelah taji saukar zafafan marika guda biyu a jere,
tsananin azaba da zafi ne ya sanya ta durk’ushewa k’asa ta fasa gigitaccen kuka,
tana shafa kunci a rud’e, ” ni sa’anki ubanki ne kona uwarki da zaki rink’a yi min iskanci kina yi min rashin kunya….!?

“Wallahi daga yau duk ranar da kika sake gigin yi min hauka da jakanta had’i da k’auyanci,
sai kin gane kuranki, cikin kuka tace ” a toyi am, halled’e ba kad’o b’aleja,
” wallahi kika sake kika zage ni sai na karyaki,
” Allah hitai cakam bema, bi shirel, tayi maganar tana cigaba da kuka,
” kika k’ara magana da fullaci sai na baki bak’ar wuya,
yayi maganar yana take mata k’afa da iya k’arfinshi, ihuuun azaba ta saka had’i da k’ok’arin kwace k’afarta,
cigaba yayi da murza yatsun k’afarta cike da mungunta, harda cije lips,
sosai take kuka kamar ranta zai fita saboda azaba, tana kuma k’ok’arin kwace k’afar, amma ta kasa,
sai da ya gaji dan kanshi kana ya d’aga mata k’afar yana cewa ” gobe ki k’ara dan ubanki,
da sauri ta sanya hannu ta damk’e yatsun k’afarta saboda rad’ad’in da suke yi mata,
kamar an saka wuk’a an datse su, sosai Neelah take kuka, ta had’a gumi sharkaf  hawaye ya had’e mata da majina,
” kiyi minshiru…!, ya fad’a batare daya d’ago kai ya kalle ta ba, 
ko motsi batayi ba ta cigaba da kuka abunta, ” ko kiyi min shiru ko yanzu na sab’a miki kamanni,
ya fad’a with care free, still bata yi mishi magana ba, ta cigaba da kukan,
tana rik’e da k’afarta, ” ok yace yana k’ok’arin mik’ewa, da gudu Neelah ta nufi k’ofa,
sai da takai bakin bukkar ta juyo ta kalle shi tace ” oho dai ni rayuwarka da zuciyarka na mara,
kuma sai dai bak’in ciki ya kahe ka, Allah lane,  wande kutiri,
ta k’arasa tana fita da gudu,  a fili Neehal ya maimaita ” ni rayuwarka da zuciyarka na mara,
lips ya cije yana murmushin mugunta yace ” you must pay, kema zan mari taki rayuwar da zuciyar,
Neelah bata dad’e da fita ba, yaro yayi sallama daga k’ofar bukkar,
Neehal yace ” waye….!?

STORY CONTINUES BELOW


“Bingel…! (Yaro)

” Meye….!?

Neehal ya fad’a cike da k’osawa,
Yaron yace ” daga gidan Liman aka aiko ni, ” shigo Neehal yace batare da fargaba ko tsoron Neelah ce takaishi k’ara ba,
yaron ya shigo d’auke da tray yace ” gashi inji Dadan Neelah tace a kawo maka,
” aje nan..!, yace a tak’aice, yaron bai kuma magana ba ya aje ya fita, ni’imtaccen k’amshi ne ya dagi hanci Neehal,
wanda yake matuk’ar bashi mamaki a duk sanda aka kawo mishi abinci daga gidansu Neelah,
k’amshin abincin ba k’aramin mamaki yake bashi ba, tunda yasan basu da kayan spices, 
basu kuma da kayan had’e-had’e na abinci, amma ya rasa yadda ake yi abincinta ke k’amshi da d’and’ano zakwaikwai,
sai lokacin Neehal ya tuna duk wayewar garin yau babu abinda yaci,
a hankali ya mik’e zaune daga kishingid’en da yake, ya jawo tray d’in gabanshi,
ya bud’a kwanukan, fura ya gani damammiya taji nono da madarar shanu,
had’i da zuma, sai dafaffen nama yasha daddawa da kayan k’amshi,
sosai ya ci naman da furar, kana ya d’an kwanta bai dad’e ba bacci yayi awon gaba dashi,
bai tashi ba sai da aka kira Sallah, ya tashi yayi alwala ya tafi masallaci,
bai dawo ba sai bayan sallar ishaa, yayi wanka ya kwanta batare daya damu da sanin halin da Neelah take ciki ba,
sai da ta tabbatar yayi bacci kana ta lallab’o ta dawo bukkar ta kwanta.

Washe gari da safe Neehal yana kan sallaya yana addu’a yaji sallamar su Mercy & Donyi,
cikin nutsuwa ya shafa addu’ar had’i da basu izinin shigowa,
“Mr Lagosa how you dare…!?

Suka fad’a suna zama k’asan carpet,
” broking English yace cikin ranshi, a fili kuma yayi murmushi had’i da cewa ” Alhamdulillah, an you…!?

“Not bad…! Mercy ta fad’a tana tab’e baki,
Donyi zatayi magana Neelah ta shigo, bata kalle su ba bare tayi musu magana,
ta rab’e ta wuce can cikin bukkar ta tada sallah, 
Donyi tace ” thanks to you Mr Lagosa,
since yesterday we’re looking for you, but we didn’t see you,
cikin rashin fahimta Neehal thanks for what, an why do you want see me…!?

” For the light sha, you’re so kind & good person with fresh heart,
thank you so much Mr Lagosa, tunda Neelah ta idar da Sallah ta zauna tana kallan d’an tsukakken bakinshi,
da yadda yake sarrafa shi wajen yin magana, sosai ta k’urawa bakinshi ido, 
bata ko blinking, sarai Neehal ya lura da irin kallan da Neelah keyi mishi, 
batare daya kalle ta ba ce “ki ci kanki mayya kawai,
da sauri ta mayar da idonta k’asa tare da cewa “fauru,
bayyi magana ba dan baya san su Mercy su fahimci wani abu tsakanin su,
sun d’an jima suna hira kafin  suka mik’e zasu fita, Donyi tana dariya ta d’ora hannunta,
kanshi had’i da cusa hannun cikin sumar kanshi tace ” thank you once again Lagosa,
take duk wani annurin fuskar Neelah ya d’auke cak, ta kafe Donyi da dara-daran fararen idanuwanta,
wanda kallo d’aya zakayi musu ka hango zallar kishi da b’acin rai cikinsu،
murmushin yak’e Neehal yayi yana k’ok’arin zamewa idanuwanshi suka sauka akan Neelah,
ba k’aramin mamaki da al’ajabi had’i da d’imuwa suka kama Neehal ba,
amma saboda k’arancin shekarunta sai yak’i yarda da abinda ya gani tattare da ita,
Neelah dake durk’ushe tana jin zafi a ranta da zuciyarta, tana jin tamkar an kunawa k’irjinta wuta,
which is ita bata san me hakan yake nufi ba, bama ta san takamaiman abinda ke faruwa da ita ba,
duk abinda take yi Neehal na lura da ita, amma yak’i gaskata abinda ya gani.

Bayan fitarsu Mercy a gaggauce yayi wanka ya dawo d’akin ya d’ora ruwan tea, ya soya kwai,
ya zauna k’asan carpet yana ci, ” zaka koya min turanci nima…!?

Tayi maganar cikin sanyi, banza yayi mata kamar baiji abinda tace ba,
” dan Allah ka koya min ina san in rink’a jin abinda kuke cewa idan kana magana da matan arna nan,
ina san na rink’a fahamar abinda suke ce maka, da abinda kake fad’a musu, dan bana san kana magana da wasu ni bana jin yaran,
tayi maganar a rarrabe kamar me koyan magana,
cak ya tsaya da abinda yake yi, yayi k’asak’e yana k’ok’arin k’in gastawa,
a hankali  ya juyo ya zuba mata ido na d’an lokaci yana san tabbatar da abin yake zato,
bayyi mata magana ba, ya cigaba da cin abincinshi ya gama ya fita.

After 2 months

Neehal kwance yana bacci yayinda Neelah ke durk’ushe gabanshi,
ta rafka tagumi hannu bibbiyu ta zuba mishi ido, tana kallanshi, 
tana jin farin ciki, nishad’i, annushuwa gami da tsantsar dad’i cikin ranta,
yayinda da sanyi had’i da ni’imtacciyar iska ke ratsa sassan jikinta,
daga b’angare d’aya tana jin wani abu yana tsargawa ta magunar jinninta, 
yana ratsa b’argo da jijiyoyin jikinta, yana bin magunar jininta tare da ratsa tsokar jikinta,
yana huda k’irjinta yana shiga cikin zuciyata, ta rasa dalilin dayasa duk lokacin data kasance tana kallanshi,
take ji wani irin yanayi marar misaltu a jikinta, 
tana jin abubuwa da dama idan tana kallan kyakkyawar fuskarshi,
takan tsinci kanta cikin farin ciki marar misaltu da iyaka idan tana tare dashi,
bazata iya misalta ko iyakance abubuwan da take ji idan tana kallanshi ba,
duk da Neelah bata san SO ba bata san me ake kira da SO ko SOYAYYA ba,
amma ta tabbatarwa kanta tabbas tana ji abu na daban kuma na musamman a kanshi,
wanda bata ji kan kowa, ba kuma ta tab’a ji kan kowa ba, bata da burin daya wuce taga tana kallanshi,
sosai take jin dad’in kallanshi, tana shagalta sosai idan tana kallanshi,
har takan manta kowa da komai da duniyar da take,
babban abinda yafi burgeta a fuskarshi bakinshi da hak’oranshi,
da kuma idonshi, abinda kuma yafi d’aukar hankalinta dariya ko murmushin shi,
abinda yafi jan hankalinta kuma maganarshi, da yadda yake yin maganar kamar baya so, sosai Neelah ke nishad’antuwa da kallan Neehal,
ta gama shagala da kallanshi, ta kafe shi da ido, wanda yasa hankalinta fita daga gangar jikinta,
harta mik’a hannu tana shafa fuskarshi batare data sani ba,
a hankali take shafa fuskartashi, batare data sani ba, which is ita harga Allah ba da wata manufa take yin hakan ba,
bama tasan takamaiman abinda take yi ba, kuma bata san abinda take ji ba saboda k’arancin shekarunta,
”  bodd’o gorko am, ta furta batare data sani ba,
cikin bacci Neehal yaji ana shafa fuskarshi, fuskar ya d’an yamuta, tare da kawar da fuskarshi gefe,
hannunta ta kuma zurawa tana cigaba da shafa fuskarshi,
dole tasa Neehal ya soma bud’e idanshi jin ba’a daina shafa mishi fuska ba,
saurin ware idonshi yayi tangaram ganin Neelah zaune ta k’ura mishi ido fuskarta d’auke da yalwataccen murmushi tana shafa mishi fuska,
” bodd’o gorko am….! sark’e mata maganar tayi a mak’ogwaro sakamakon idonta daya sark’e cikin na Neehal………….!!!!Da k’arfi Neehal ya sanya k’afa ya hankad’ata, ta fad’a baya ta mugu da k’asa,
batare daya damu da fad’uwar da tayi ba, yace ” uban me kike shafa min a fuska …!? +

Bata kalle shi ba, bare ta tanka mishi, ta tashi zaune tana kakke jikinta, had’i da murza inda ta buge,
” ba magana nake yi miki ba…! nace uban me kike tofa min….!?

Yayi maganar cikin zafin rai yana tunkaro ta, cikin tsoro da fargabar ganin yadda yake tunkaro ta tace ” babu komai,
” bazaki fad’a min abinda aka baki kike shafa min a fuskata ba….!?

Yayi maganar cikin masifa yana tsatstsare ta da ido, ” “Allah ba komai….!,
” idan babu komai uban me kike tofa min….!?

“Wani lak’anin aka baki kike shafa min danki mallake ni….!?

“To bari kiji imma wani suddabarun da surkullan kuke yi akai na wallahi na fi k’arfin ku, 
and you will never have me as husband, fool villager kawai,
ya fad’a yana huci kamar zaki, 
” Allah babu abinda nake tofa maka ko nake shafa maka,
” to uban me kike min….!?

Cikin yarinta tace ” kallanka kawai nake yi…!,
” kallan me kike yi min to…!?

Ya fad’a yana d’aukar step zuwa gareta, ” nima ban sani ba, kawai dai naji ina san kal….! kasa k’arasa maganar tayi ganin yadda ya tsare ta da ido,
” uhummm ina jinki, ” kawai naji ina san kallanka  ne….!, ta fad’a cikin fad’uwar gaba,
kasak’e Neehal yayi yana kallanta batare dayace komai ba,
” 10yrs in love…!?

Ya fad’a idanshi kanta , tare da komawa ya zauna saman foam, had’i da sauke ajiyar zuciya,
” you’re 10yrs an you’re in love with unknown person, yayi maganar yana murmushin gefen baki had’i da shafa k’asunbarshi cike da mugunta,
can k’asan mak’ogwaronshi yace ” SO…..!, yarinya kinyi mugun ganganci,
jin ya fad’i kalmar so yasa Neelah yin murmushi had’i da cewa ” dama Abpa yace wata rana zaka so ni, sai da akayi ‘yan sakanni kana Neehal ya fahimci maganarta,
aiko yadda kasan an tsira mishi allura ya zabura had’i da cewa ” what….!?

“Ni zan so kin ko wa….!?

” Eh! tace tana kallanshi! ” wonder shall never end, shi baban naki ne ya fad’a miki wata rana zan so ki….!?

“Eh! ta kuma bashi amsa, ” God forbid…! Allah ya tsare ni da sanki,
” wallahi Allah nayi muku alk’awari ke dashi, har abada har na mutu bazan tab’a sanki ba,
I said it now and I will say it for ever & ever bazan tab’a sanki ba,
ke koda gaba k’addara ta k’addara nace miki ina sanki, ko na zo miki da maganar soyayya k’arya nake,
idan har kika ga nace miki ina sanki akwai babban dalili, na zo ne kawai na cimma buri na akanki, amma bawai soyayya ce ta gaskiya ba,
dan haka ki aje wannan a ranki may be gaba yayi miki amfani,
bana sanki ba kuma zan so ki ba, dan k’arshen tab’ewar da zanyi a duniya da kuma walak’anta had’i  da kankanci shine na so ki,
babu wata bak’ar k’addara ko masifar da zata k’ara samu na a duniya kamar AURANKI,
babu wani iftala’in da zai kai min na AURANKI, bani da babbar jarabawa a duniya ta kamar ta AURANKI,
daga kan AURANKI bana jin zan k’ara ganin bala’i sama da wannan.

STORY CONTINUES BELOW


Cikin tsiwa Neelah tace ” nima k’addara ce tasa ka zama miji na,
“kam bura uba..! Neelah yace yana kallanta sama da k’asa kana ya d’ora,
da cewa ” it’s tragedy that brought us together not fate, look at you, it’s a shame that you be become my wife, idiot,
” yo dan kayi yaren arna ni birge ni kayi aka ce maka, dou b’erd’e wata ikka dubbe wati, ta fad’a tana murgud’a mishi baki,
” if you ever address me as such, I will severely deal with you nonsense,
yayi maganar yana huci tamkar wanda zayyi dambe da namiji sa’anshi,
an you will never become my wife as a I said, bak’ar jaka jahila kawai,
batayi mishi magana ba saboda tsoran ganin take-taken dukanta yake son yi,
dan yadda yake fuffukar nan  abu kad’an yake jira yakai hannunshi jikinta,
dan haka ta mik’e cikin sanyin jiki ta nufi kan katifa da niyyar kwanciya,
cikin tsawa yace mata ” what the hell are you doing….!?

Duk da bata ji abinda yace ba tayi bala’in tsorata da yadda yayi maganar,
tsaye tayi tana kallanshi tana kuma kallan katifar, ” tsayiwar uban me kike yi min aka…..!?

Muryarta na rawa tace ” am….am…..! da…..ma zan….! kwan…..ta ne…!,
tayi maganar a rarrabe kamar me koyan magana, cike da tsoro,
” uh hummm kwanta…..!, yace tare da jefa mata k’astaccen kallo,
cike da fargaba ta rab’a da niyyar kwanciyar saman katifar,
da k’afa ya hankad’ata ta kwaru da bango, yana huci yace ” ubanki ne yasai min katifar….!?

“Ko be san ana had’o mace da kaya gidan miji ba ya kawo ki sililinki….!?

Cikin kuka tace ” ni dai kayi min duk abinda zakayi min amma ka daina saka min Abpa da Dada,
” ank’i a daina saka su d’in kiyi duk abinda kike ganin zaki iya,
” halled’e ba kad’o b’aleja,  a toyi am, ta fad’a tana kuka, babban d’an yatsanshi ya d’ana mata a baki,
tare da kama lips d’inta ya rik’e da k’arfi yana murzawa cike da mugunta,
” ba na hana ki yi min magana da Fulatanci ba….!?

“Ka….yi hak’u….ri ba…n k’a…ra…wa, ta fad’a muryarta na cracking saboda tsananin azaba,
” wallahi idan baki daina ina fad’a kina fad’a ba ke zaki sha bak’ar wahala,
ya fad’a had’i da hankad’a baya ta fad’i tare da bugawa, ta hangame baki da niyyar yin kuka, yace ” had’iye shi, mai da wannan kukan, idan kika sake naji fim saina lahira yafiki jin dad’i,
dole tasa ta had’iye kukan dole, ta kama bakinta ta rufe  had’i da kwanciya,
cikin ranta tanayi mishi Allah ya isa.

********************************

Bayan watanni goma

Haka rayuwa tayi ta tafiya lokaci na shud’ewa, yayinda tsakanin Neehal da Neelah babu abinda ya ragu sai ma abinda ya k’aru,
dan babu ranar da baya gana mata bak’ar azaba, azaba kam Neelah tasha ta kala-kala a hannun Neehal,
dan ko sau d’aya bai tab’a d’aga mata k’afa ba,
kullum cikin dukanta da zaginta yake had’i da ci mata mutunci,
kuma ko sau d’aya Neelah bata tab’a kai k’ararshi gida ba, duk da kasancewar ta,
yarinya k’arama wacce ta shiga 11yrs bama ta gama cika shekaru gama sha d’ayan a duniya ba,
amma dayake tana da biyayya da hak’uri yasa tun kashedin da Abpa yayi mata,
kan karta sake ta kuma gayawa kowa tsakaninsu yasa bata tab’a sanar da kowa bak’ar azabar da yake gana mata ba,
while har lokacin bata fara irgan dangi da haila ba (menses, period),
kamar yadda Neehal yayi alk’awarin idan yazo service ko wuya zata kashe shi,
bazai tab’a komawa gida ba, har sayya gama hakance ta kasance,
dan tunda yazo ko sau d’aya baije gida ba, duk bak’in nacin da Najwah tayi-tayi mishi,
amma k’in zuwa yayi, duk abinda zatayi tayi amma Neehal baije ba,
tayi mishi hauka tuburan muraran, amma yayi burus da ita,
sai dai kullum suna manne a waya, kamar cingam, yayinda da tuni Neelah ta dad’e da kamuwa da mugun son Neehal,
kasancewar ta yarinya k’arama yasa ta kasa fahimtar hakan, 
yana zaune saman katifa yana duba texs yana kuma bada amsa,
dan haka yake yi, idan yaje wajen service ya huta, tana zaune can nesa ta tsare shi da ido,
bata ko k’iftawa, sarai ya lura da irin kallan da take yi mishi, 
dan haka ya tsuke fuska murtuk babu annuri,  bai san sanda ya tuntsure da dariya ba,
sakamakon texs d’in Najwah daya karanta, daga b’angaren Neelah ma sassanyan murmushi tayi sakamakon dariyar da yayi, ya danne WhatsApp record  yana cigaba da dariyar ya soma yi mata magana,
” kin bani dariya sosai, ke dai ki fito kai tsaye sak kice a hannu kike, kin matsu na dawo na d’an sosa miki,
karki damu na kusa dawowa gaba d’aya, daga wannan karon har abada bazan k’ara yin nesa dake ba,
ki sawa ranki Neehal naki ne ke kad’ai har abada, babu wata ‘ya mace dake gaba na bayan ke,
babu kuma wacce zanso bayanke, ke kad’aid’ai zan taso har k’arshen rayuwata, har rai da mutuwa zamu rayuwa mu biyu kawai,
daga mu sai rayanmu babu wani na uk………!,  tsayar da maganar yayi cak,
cike da tsantsar mamaki da al’ajabi, yau ya tabbatarwa kanshi da zargin da yake yi,
kan Neelah, tabbas ya tabbata Neelah sanshi take yi, dan lokaci d’aya yaga kamanninta sun sauya,
idanuwanta sun furfuto waje, gumi ya soma jik’a ta, while duk ilahirin jikinta na kerrrrma,
” love & jealous, in 11yrs, ya fad’a cikin ranshi, ” but bari na gwada ta na gani if she really loves me,
dan haka ya k’ara danna record ya soma magana idanshi kanta,
” Matata ta kaina, daga ke ba wata, babu k’ari, bake ba kishiya, ina sanki fiye da yadda nake son rayuwata, 
ina sanki fiye da kowa da komai dake cikin duniya, ke kad’ai ce macen danake so,
annurin rai na ke tawa ce ni nak……!,
kukan da Neelah ta sanya ne sanya shi tsaida maganarshi dole,
had’i da k’ura mata ido, ganin yadda take kuka tsakaninta da Allah yasa shi cewa,
” don’t…! don’t even try…! inba haka ba ke zaki sha bak’ar wuya,
lalle yarinya kin d’auko dala da gwauran dutse ba gammo, ni kike so….!?

STORY CONTINUES BELOW


” A kaina kike kuka…!?

“Lalle iska na wahalar dame kayan kara, ke yanzu in banda d’igimi dukan sauro da gatari,
ki kalle ni ki kalle ki kice ni zaki so, ni zaki haik’ewa….!?

” Kin san kwana nawa ya rage mu rabu har abada, rabuwa ta har abidin abidina….!?

“To idan baki sani ba ki sani yau saura kwana shida na barki har abada,
rana ita yau i yanzu baki tare dani, dan haka ina me baki shawarar da kada ma ki soma d’orawa kanki wahala,
dan neman soyayya ta tamkar a jefa tsokar nama cikin garken mayunwatan zakuna ne, 
haka neman so daga gare ni dai-dai yake da neman furfura a jikin tinkuya,
so na da kike neman d’orawa kanki idan bakiyi k’ok’arin yakice shi ba, 
shi zayyi ajalinki dan bana tunanin daga wad’annan kwanakin shidan da suka rage zaki k’ara gani na rayuwarki,
nema na kuma kamar neman fadama a cikin sahara ne,
dan haka kada ki sake ki bari zuciyarki ta kai ki ta baro ki,
karki bari yarinta da k’uruciya su kaiki ga hakala dan bazaki sake gani na ba balle soyayya ta,
dan haka ki daina kishi akaina, so a shawarce ki taimaki kanki, ki sauwak’awa rayuwarki,
kada kiyi k’ok’arin yanke d’an guntun farin cikin da kike ciki,
dan bazan tab’a sanki ba, kamar yadda bazaki tab’a zama cikekkiyar matata ba,
wait waima kin san da wa kike kishin…..!?

” Idan baki sani ba ki sani ita d’in MATATA CE ta sunna, wacce mukayi auren soyayya,
auren gata na so da k’auna tana so na ina santa, ba irin wannan wulak’antaccen auren naki ba,
ita kad’ai kuma nake so, haka akan santa da k’aunarta zan dauwama, 
ina fata ko a lahira Allah ya tashe ni a matsayin MIJIN NAJWAH……!,
mik’ewa Neelah tana kuka had’i da girgiza kanta tace ” gid’ad’o am, mi yidima anbo a yid’a am, 
ta fad’a had’i da fita waje da gudu tana kuka, bayanta yabi da uwar harara,
tare da tab’a baki yace ” banza k’idahuma jaka, ya k’arasa maganar yana kishingid’a,
a hankali ya lumshe idonshi ya shiga duniyar tunani,
” shin dama haka duka mata suke da kishi….!? 1

“To kodai haka Allah ya halicce su da kishi a jinin jikinsu….!?

” Najwah nada bak’in kishi, haka na hango irinshi a kwayar idon wannan yarinyar,
da haka bacci yayi awon gaba dashi bai farka ba sai da yaji an kira sallah, 
ya tashi yayi alwala ya fita, Neelah kuwa gindi bishiya ta samu tayi ta rusa kuka kamar ranta zai fita,
wanda ita kanta idan za’a kashe bata san dalilin yin kukan nata ba,
sai da taci uban kuka san ranta ta godewa Allah kana ta tashi ta nufi bukkarsu…..!,
a hankali ta kwanta k’asan carpet jin kanta yana sara mata,
har bacci ya soma d’aukar ta ta tuna da gargad’in da yayi mata kan wanka,
dan haka ta mik’e cikin mutuwar jiki ta fita daga bukkar ta shiga ban d’aki….!,
jikinta ba kwari saboda kanta dake sarawa ta cire kayan jikinta,
had’i da tsugunnawa tana k’ok’arin soma wankan,
ya shigo ban d’akin, cike da tsoro tayi saurin mik’ewa, had’i da sanya hannuwanta ta kare al’aurarta,
” m…..e…y…e…..!?

Tayi maganar cike da fargaba, bai kalleta ba ya nufi inda brush d’inshi yake,
” me zakayi…..!?

Ta kuma tambayar shi, still bayyi mata magana ba ya d’auki brush d’inshi ya matsa toothpaste,
” baka ganin wanka nake, ka bari idan na gama sai kayi…..!?

Tayi maganar while hannunta kare da gabanta, cikin b’acin rai yace ” wai dan Allah meyasa kika raina ni ne….!?

“Ko an fad’a miki ni sa’an ubanki ne…!?

Yayi maganar idanshi kanta, ganin yana kallanta yasata saurin maida hannunta d’aya kan shafaffen k’irjinta ta rufe,
” uban me kike karewa…..!?

” Kina wani rarrufewa kamar wani abun arziki…..!, shegiya k’irjin a shafe kamar faranti,
ni maccen arziki ma wayayya ‘yar boko kyakkyawa bata isheni kallo ba bare ke,
bak’ar jaka jahila wacce zata k’are a jahilci da k’auyanci, kuma ki gama rayuwarki batare da kin mori komai daga gareta ba,
sai bak’ar wahala, k’auyen ci, dabbanci, duhun kai da tarin jahilci,
sosai maganar shi tayi bala’in b’ata mata rai, ” bira wande, mi yid’ama ko sedd’a,
ta fad’a cikin tsiwa tana turo baki,
” illiterate….!, yace yana kallanta,
baki ta kuma zumb’urowa   had’i da cewa ” to ni dai ka daina kallo na,
k’olulun bak’in ciki da takaici  ne suka hana Neehal cewa komai,
ganin yarinya k’arama wacce  she’s not manure, ga k’irjinta a shafe kamar tangaran,
kwata-kwata babu wata alamar kasancewar ta mace amma tana cewa ya daina kallanta,
kwafa…! yayi cikin takaici batare daya kuma magana ba ya fita,
tabi bayanshi da kallo had’i da tofa mishi yawu tace ” hogije mere,
” me kika ce….!? 2

STORY CONTINUES BELOW


A tsorace ta d’ago kanta dan batayi zaton yana nan ba, balle har yaji,
” wani abu kaji nace….!?

Ta fad’a tana kallan shi, ” ubanki zaki ci duk ranar da kika sake na fahimci zagi ne kike da wannan shegen yaren naku,
yayi maganar yana huci, ” ni fa babu abinda nace, ban ce maka komai ba,
nunata yayi da yatsa kamar zayyi magana sai kuma ya fasa yayi kwafa kana ya fita, bata k’ara magana ba saboda tsoro, tayi wankan a gaggauce.

*******************************

Bayan kwana biyar…….!

Ana gobe Neehal zai tafi zai koma gida, da daddare bayan ya dawo sallar ishaa,
yana kwance saman katifa yana ta faman sak’a da warwara,
yayi nisa a duniyar tunani, kan abinda zayyiwa ‘yan k’auyen Sunkhanni ya huce takaicinshi,
da abinda zayyiwa NEELAH….! ya huce bak’in cikinshi,
kamar yadda tace ta mari rayuwa da duniyarshi, shima yana san ya mari tata rayuwar,
yana san yabar mata babban tabanshi cikin ranta da rayuwar ta,
wanda bazata tab’a mantawa ba har ta mutu, yana san yayi mata abinda harta mutu tana kukan bak’in ciki kanshi,
yana san kunnawa zuciyarta wutar bak’in cikin da shi zayyi sanadiyyar mutuwar ta,
yana san ya koyawa gaba d’aya mutanen karkarar hankali,
ta yadda gaba idan sunga bak’o wadda basu san daga inda ya fito ba,
bazasu k’ara gigin bashi auren ‘yarsu ba, yana san daga kanshi,
bazasu k’ara gangancin yiwa wani abinda sukayi mishi ba, a hankali ya gyara kwanciyar shi,
had’i da cewa ” me zanyi musu…..!?

“Ita kanta me zanyi mata wanda harta mutu bazata manta da ni ba….!?

” Wanne irin bak’in tabo zan barwa al’ummar wannan k’auyen….!?

“Me zanyi na koyar dasu hankali da darasi…..!?

” Me zanyi na gigita rayuwar ta, na mari duniya da farin cikinta…..!?

Haka yayita yiwa kanshi tambayoyin da bashi da amsarsu na tsayin lokaci,
ganin ya rasa mafita ya sashi mik’ewa ya soma zagaye bukkar hannunshi sak’ale a bayanshi,
” me zan musu na huce takaici da bak’in cikin da suka k’unsa min…..!?

“Me zanyi ne…..!?

” Ya Rabbi…..! yace yana cusa hannunshi cikin kwantacciyar suman kanshi,
had’i da sauke ajiyar zuciya da k’arfi, ” ko dai na tambayi Nauman ne…..!?

“Dan nasan zai iya taimaka min wajen samun mafita, to amma tambayar tashi bazata iya bani matsala ba kuwa….!?

” Ta ina tambayar shi zata baka matsala bayan Nauman bai san komai akan abinda ke faruwa ba….!?

Wata zuciyar ta amsa mishi, ganin bashi da mafita saita tambayar Nauman dan gaba d’aya kwakwalwarshi da tunaninshi sun gama rufewa,
yasa shi d’aukar wayarshi ya nufi wajen service, batare da tsoran komai, 
tunda yake bai tab’a zuwa yin waya koda da la’asar bane,
amma yanzu dayake ya saka mugun nufi da mugunta cikin ranshi ya tafi wajen,
yana tafe yana cigaba da sak’e-sake har ya isa, zama yayi a inda ya saba, had’i da dialing number Nauman,
harta fara ringing yayi saurin katsewa dan jin gabanshi na fad’uwa,
haka nan yaji matsanancin tsoro da fargaba sun shige shi, gabanshi ya shiga fad’uwa,
k’irjinshi ya soma dukan uku-uku, shiru yayi yana sauraren yadda zuciyarshi ke bugawa da tsananin k’arfi,
wayarshi data soma ruri ce ta dawo dashi cikin hayyacinshi,
tsaki yaja ganin sunan Nauman dan haka nan yaji zuciyarshi na gargad’inshi kan tambayar Nauman d’in,
murmushi yayi dan shawarar data fad’o mishi cikin ranshi,
a gaggauce yayi creating new Facebook account bada sunanshi ba tare da searching men problems & solution group,
yayi join da sauri ya rubuta tambaya kamar haka,
_” Slm dan Allah idan yarinya k’arama tana yi maka rashin kunya da fitsara tana yawan haik’e maka me zakayi mata ka huce haushinka….!?_

_Haka ma gaba d’aya ahalinta sunyi baka babban tabo dan Allah me zakayi musu ka rama…..!?_

Bai dad’e da turo sak’on ba wani ya turo da amsa kamar haka,
_Babban abinda zakayiwa mace ka wulak’anta ta, ka tozartata, ka kuma wulak’anta rayuwar ta, ka jefa iyayenta da ita cikin bak’in bak’in ciki da takaici marar iyaka shine kayi mata FYAD’E KA RABATA DA BUDURCINTA……!!!!_
_wani ma yace ” wallahi abinda nake da niyyar fad’a kenan ka riga ni_
_wani yace ” tabbas haka yake, wannan hakk’un ne…!_
a matuk’ar razane Neehal ya mik’e tsaye har wayar na sub’ucewa daga hannunshi,
cikin kid’ima yace  ” what…..!?

“Impossible….! yace yana shafa kanshi, ” ni NEEHAL BILAL LAGOSA…..! zan iya had’a jiki da wannan k’azamar yarinya…..!?

“Allah ya tsare ni, hummmm’umm, shi kad’ai yake ta sambatu cikin daji, kamar tab’abb’e,
yana ganin kiran Nauman dana Najwah nata shigowa wayarshi amma ya kasa picking,
ya dad’e nan zaune yana ta magana shi kad’ai kamar mahaukaci sabon kamu,
kana ya tashi ya koma bukka, har ya isa bukkar yana mita da babbami,
koda ya koma bukkar kasa zaune ko tsaye yayi,
yayi ta safa da marwa yana kai komo cikin bukkar, duk bayan minti d’aya zuwa biyu,
sai yayi kwafa had’i da sauke numfashi yace ” it’s impossible, abinda bazai tab’a faruwa ba kenan,
” tab….! ni Neehal zan had’a jiki na da wannan jaririyar, nayi sex da ita……!?

“God forbid…!, yana cikin haka ta shigo d’aure da d’aurin k’irji,
da alama daga wanka ta fito,  ta zauna daga gefe tana shafa mai,
ido ya kafe ta dashi yana kallanta sosai, ” tab wannan jaririyar zan farwa…! ni…..!?

Ganin yadda yake kallanta yasata cewa ” wai meye….!?

“Ubanki ne…! yace yana huci,  ” na fad’a maka duk abinda zakayi kayi iya kaina ka daina saka Dada da Abpa na,
” an saka su d’in dan uwarki….!, ” ni dai karka k’ara zagin iyayen na, ta fad’a cike da tsiwa tana tafa hannu,
cikin tsuran ruwan bala’i kamar yana magana da babba yace ” idan an zagi uwar ta ki kina da abin yi ne…..!?

“Ba dai uwata ba…!, tace tana murgud’a mishi baki, a zuciye Neehal ya d’auke ta da lafiyayyun maruka,
abinka dama dame zuciya a kusa, kana ya d’ora da cewa ” shegiya ‘yar k’auyen banza, jaka jahila dabba, me iyayen naki suka yi miki, inma banda cutarki da sukayi…..!?

“Inda suna sanki da sa d’auke ki su bayar ga wanda basu san usulunshi ba,
uban me suka tsinana miki in banda wargaza rayuwarki,
ke kanki rayuwarki bazata amfane ki ba balle ta amfani wani, 
shegiya wulak’antacciya mak’ask’anciya, mara galihu, ya fad’a kamar zai yagi neman jikinta,
  cikin kuka Neelah tace ” ni fuska ta kad’ai ka mara, ni kuwa farin cikinka da rayuwarka na mara,
ka fad’i duk abinda zaka fad’a , haka ka dake ni iya san ranka,
ka kuma kira ni da duk sunan da zaka kira ni, ka danganta da duk abinda kaga dama,
kamar yadda ban san gobe ba kai ma baka san gobe ba, baka san me gobe zata haifar ba,
rayuwar kowa a hannun Allah take, shi yake da ikon tsarawa kowa rayuwa,
haka kuma da kake cewa iyaye na basu tsinana min komai ba,
ai sun gama min komai tunda suka haife ni, kuma ‘yar halak ba shegiya ba,
suka koya min karamci da mutunta d’an Adam, suka koyar dani sanin daraja da k’imar mutum,
sannan da kace sun aurar dani ga wanda basu sani ba, kai suka taimaka kai suka yiwa rana,
kai suka rufawa asiri, dan badan ni ba da tuni kai kanka baka san inda kake ba,
kuma duk tsiya duk lalacewa ta dai matarka ce, tahirinka bazai tab’a cika batare daka saka ni ba,
kuma na riga da na shiga tahirin rayuwa da duniyarka, 
murmushin gefen baki Neehal yayi had’i da cewa ” haka ne, tarihi na bazai tab’a cika batare da na saka ki ba,
haka kuma gaskiyarki kin mari rayuwata da farin ciki na,
kamar yadda nima yanzu zan mari rayuwarki da farin cikinki,
zan illata duniyarki, zan tabbatar da tarihi na a cikin naki,
ta yadda ko kalmar tarihi kika ji sai kin tuna ni,
kinyi kuskure…!, kinyi babban kuskuran tilastani yin abinda banyi niyya ba, ya k’arasa maganar yana fisge zanin jikinta,
wanda tayi d’aurin k’irji dashi, ya wurga ta kan katifa,
yana cewa ” dama ban mori 50k d’in sadakin dana bayar ba, gwara na mori kud’i na ya fad’a yana danneta……………!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *