RAI BIYU
CHAPTER 17
Bayan fitar Nawwara ya zauna kusa da gudan jininsa yana ta kallonsa, shi kansa yana jin rashin kyauta a abunda ya yi ma Nawwara sai dai ya yi hakan dan ya bata ta a gurin iyayen Bilal, kuma ya banbance wanda ta fi so tsakamin Bilal da Mustapha.
Hannunsa yasa aljihu ya dauko wayarsa ya kira wata nurse ta kawo masa wani file tare da sai ya cire wata kadarda ya rubuta ma Noor takardar sallama, sannan ya dauki dansa ya saba a kafada hakan yasa Noor farkawa sai ya soma jijjigashi kamar jariri.
“Shiiiiii cigaba da bachinka Daddynka ne”
Hakan yasa Noor tafewa a kafadar Jibril ya fito tare da shi harabar asibitin ya sakashi gaban mota sannan na zagayo ya shiga driver seat ya tashi motar sai kuma ya daga wayarsa ya kira wata number 1
“Ki shiga dakin da aka sallami Noor ki kwashe komai zan aiko da dareba ya dauka”
Yana fadar haka ya kashe wayar, ya tashi motar ya hau titi dake cikin asibitin kamin ya sadu da babban titi marafa dan baba da ke cikin birnin sokoto.
Duk bayan seconds ya kan kalli gefen da dansa yake sai idanuwansa su cika da kwalla, hamdalla yake yi ma Allah akan yau yana da gudan jinin wannan dalilin kadai ya isa yasa ya cigaba da tirsasa kansa gurin Nawwara, domin ita ce kadai macen da ta kawo masa wannan farinciki a rayuwa, bayan ya yanke tsammanin zuwansa.
‘I promise you Noor i will to my very own best na ga na zama uba na gari a gareka, i will make you and Nawwara proud of me’ 2
A kasan zuciyaraa yake wannan tunanin yana sauke ajiyar zuciya.
“Ba zan iya hakura da kw ba Nawwara, kema kina bukatar farinciki a rayuwarki, ni na bata komai dan haka ni ya kamata ace na gyara komai” 3
Wannan karon a fili ya yi furucin yana danna horn a bakin gate din gidansa, a hankali ya yi parking sannan ya dauko wayarsa ya yi ma Nawwara text akan cewar an sallami Noor saboda kar taje asibitin bata tarar da kowa ba, sannan ya fita motar ya zagaya ya bude ya dauko Noor da ke kokarin bude idanuwansa.
“Zan iya tafiya”
Ya fada saboda ya samu a sauke shi ya samu kallon gidan da kyau, kamar Jibril ya sani sai ya sauke shi ya rika hannunsa suna tafiya a hankali, rabon ido kawai Noor yake kamar zasu fado sabo kallon yadda kukasan wani tsohon bakauye, yana saka kafarsa cikin falon sai sayin tile din ya ratsashi ga sanyin ac da ya mamaye ko ina a cikin falon, suna shigowa Jibril ya sake shi ya nufi bedroom yana amsa waya, sai Noor ya daga kansa sama yana kallon pop falon da fankar kamin da dawo gurin kujerun falon da suka katsance farare sol kamar fentin falon da kuma center carpet din da ke falon, karasawa ya yi gurin kujeru sai ya zauna kasa ya kai hannu yana shafa manyan cushion din idanuwansa kuma suna kan katuwar plasma TV mai daukar ido gashi an kawata gurin da wallpaper fari mai daukar hankali, ga wasu manyan flowers da aka aje a gurin suma farar kamar labulayen falon. 1
“Noor Son tashi tashi zauna saman kujera ya zaka dauka kasa”
Jibril ya fada ganin dansa a kasa kamar wani almajiri.
“Momy ta ce idan mun shiga gidan mutane mu daina hawa musu kan kujera, kuma wasu mutane fada suke idan aka hau musu kujera” 2
Noor ya fada yana kallon Jibril da ya risino da kansa ya dauke ya dora saman kujerar ya rumgume ya lumshe ido, jikinsa ya yi sanyi sosai taya za a ce yana da irin wannan kudin amman ya kasa bawa dansa kulawa ta musamman da har wani abun na duniya zai burgeni ya kasa hawa? Shi ai iyayensa sun bashi kulawa taya ya kasa bawa dansa?
‘Lokaci be kure ba yanzu ma zaka iya he’s still a boy’
Wata zuciyar ta amsa masa wanda hakan yasa shi jin sauki, har ya bude ido ya kalli hoton Nawwara da Noor ke nuna masa.
STORY CONTINUES BELOW
“Laaaa ji Momy can”
“Kai ma za a maka naka ina son ka sosai Noor”
Noor ya dago ya kalleshi ganin ya yi masa abunda ba a saba masa ba, wato kiss shi dai yana ma Momysa amman ita bata masa jara ma Mama Habiba wani lokacin tana masa kiss idan ya yi abun kirki.
“Me kake so ka ci?”
“Bana jin yunwa a yanzu sai anjima, amman akan wacan abun zan ci”
Ya fada yana nuna dinning area da aka kawata da farin dinning table da aka kawata da farin cabinets mai kyau da kuma freezer da ke hade da cabinets din har baka iya banbancewa. Jibril ya shafa kansa yana murmushi.
“Idan ma a saman dakin nan kake son cin abinci Noor zan dora ka ka ci, ka saki jikinka nan gidanku ne”
“Da gaske?”
Ya gyada masa kai.
“Har da Momy nan zata zo mu zauna? Kuma da Inna?”
Ya sake gyada masa kai yana murmushi, sai Noor ya sauka saman kujerar yana kallon falon bakinsa har kunne hakuran nan a watse bakauye ya shigo gari.
“Can ina ne?”
Ya nuna Kitchen.
“Jeka ka gani”
Sai ya mika hannunaa ya riko hannun Daddynsa
“Aa zo muje tare dai”
“Idan na rigaka isa ba zan bari na shiga ciki ba idan kuma kai ka rigani isa ba zaka bari na shiga ciki ba, ka yarda?”
Ya daga kai yana dariya, sai suka fara yar tseren gudu shi da Jibril da yana lakkame da hannunsa mai ciwo, da gangan Jibril ya bari Noor ya riga shi isa sai duk suka rika dariya Noor har da tsalle, abunda ya dauki hankalin babansa sosai yana kallonsa kamar ya hadeyeshi saboda Kauna.
Suna fitowa daga kitchen din suka sake rigangan shiga bedroom haka suka bi suka zagaje gidan Jibril ya nuna masa ko ina har Swimming pool, a Garden sai da Jibril ya hau icen guava ya katso masa sannan aka sauna lafiya.
“Acan za a saka maka lilo”
Jibril ya fada yana nuna wani bangare na Garden din, sai Noor ya zaro ido.
“Da gaske”
“Eh har dakinka za a maka daban, a saka maka komai da komai har da tv ka da games”
Dadi ne yasa Noor ya rumgumeshi yana dariya, sai kuma ya dago kai ya kalleshi
“Sai gobe zamu je mu lallabata sai ta dawo nan mu zauna, mu a nan zamu kauna har gobe ko?”
Ya daga masa kai, sai Jibril yasa hannunsa ya daukosa suka nufo falo, saman kujera ya zaunar da shi ya yi masa hotuna kala kala har da video sannan ya kunna masa tv ya saka masa kids channel sai yazo ya dauke ya rumgume suna kallon tv tare.
NAWWARA POV.
Tsayawa na yi kallonta saboda na tantancewa idanuwa ita din ce ko kuwa wata ce mai kama da ita, idan har ita dince to gaskiya ta canja sosai fuskarta ta yi kala biyu fari da kuma wani farin na daban, ga wata uwar rama da ta yi fuskarta ta matse sosai.
“Na san zaki yi mamakin ganina Nawwara, kin yi kokari da baki manta fuskata ba duk tsawon wannan lokacin”
“Taya zan manta fuskar da ta kwace min yan ce a gidan aurena? Fuskar da mijina ya fifita sama da tawa”
“Ashe har yanzu a akwai soyayyar Jibril a cikin zuciyarki tun da har za ki iya kiransa da sunan mijinki”
“Miya kawo ki gidanmu? Taya kika zo me kike nema a gareni?”
STORY CONTINUES BELOW
“Wacce daga cikin ukun tambayar ki nan zan fara amsawa?” 1
“Duka zaki amsa min kuma ki tashi ki bar mana gida”
“Zan tafi Nawwara gidanku ya yi min yawa da zama, amman ina son ki bani lokacin ki ki saurari abunda zan fada miki ko kuma na ce zan rokeki”
Kamar ba zan zauna ba, sai kuma na zauna saman gadon Inna ina kallonta da jiran abunda zai fito bakinta.
“Na san za ki yi mamaki ganina a wannan lokacin kuma a cikin gidanku, abun da ya fi ko wanne mamaki ma taya aka yi yarinyar da ke Abuja ta zo har sokoto kuma ta gane gidanku ko”
“Ba abun mamaki ba ne Jibril zai iya fada miki”
Na fada mata kai tsaye, sai ta yi murmushin da ke nuna cewar maganar ta soketa.
“Mai zai sa Jibril ya fada min inda kike bayan ya gargade da cewar na fita daga rayuwarsa? Rabon da na saka Jibril a ido shekara biyu da rabi kuma saboda ke Nawwara”
“Ni kuma?”
Na tambaya da mamaki sai ta gyada min kai.
“Ke fa, sai bayan ya rabu da ke ya gane yaudarar kansa yake da cewar baya son ki, ni kaina a wacan lokacin na san yana sonki ko da kuwa baya son ki tau ya san kimarki domin baya taba bari wani ya fadi wata magana marar dadi gareki a gaban idanunki ko bayan idonkin ciki kuwa har da ni”
“Ban tambayeki labarin abunda ya wuce ko abunda zai zo gaba ba, dalilin zuwanki kawai nake son ji” 1
Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleni idanuwanta raurau ta ce.
“Yafiyarki na zo nema Nawwara”
“Ai ni baki min komai ba”
“Na yi komai Nawwara, na tozarta aure na yi amfani da dama ta na ci mutunci auren wata taya Allah ya zai bar ni na gina tawa rayuwar auren a cikin kwanciyar hankali? Bayan ban so yar’uwata abunda na so wa kaina ba?
Kaddarorin rayuwa sun yi ta faruwa da ni Nawwara wanda na ke sa ran saboda na ci mutuncin aurenki ne, a iya sanin da kika min ina budurwa har yau ina nan haka ban yi aure ba, a lokacin da muke soyayya da Jibril muna tsaka da maganar aure sai kawai babansa ya cilasta masa aurenki, a wacan lokacin Jibril sai yake ganin kamar idan ya rabu da ni be aureni ya ci amanata, da wannan damar na yi amfani na dauke masa hankali, ni da kaina na rika jan ra’ayinsa har muka fada kogin aikata alfasha wato zina, a tunani wayewa ce na yaudari kaina sosai da sakewa namiji jiki tun kamin ya aureni, ba ni da tufafin sakawa sai na tsiraici gyale ma irin wanda zai bayyana siffar jikina na ke sakawa saboda na dauki hankalinsa, haka duniya ta yi ta yaudarata har muka tsufa a kogin alfasha ban ankaro ba, bayan Jibril ya rabu da ke sai na bijirowa da Jibril maganar aurenmu abun mamaki sai ya ki amincewa, kin san dalili? Saboda ya riga ya san ni a ya mace tun kamin ya aureni, sai ya zamo baya ganin kimata kuma rashin yarda ta shiga tsakaninmu har ta kai shi da kansa yake cewa ko ya aureni ba zai samu natsuwa ba domin zuciyarsa tana raya masa bayan shi zan iya taraiya da wasu mazan, ina ji ina gani Jibril ya auri wasu matan ya bar a lokacin na ko sunana baya son a kira, ni kuma na gagara samun wani mijin aure na kirki saboda kowa kallon yar iska yake min, saboda na riga na gama zubar da mutunci na tun a yanayin suturata, duk wanda yanzo ba da aure zai neme ni ba sai dai da lalata ko kuma soyayya, wadanda suka zo neman aurena da gaske kuma sai a bi a zuge, a haka zama garin Abuja ya gagareni na koma gurin Yayata Kaduna, na natsu sosai a lokacin na zama ta kwarai fiye da yadda kike tsammani, amman mutuncin da na gagara tsarewa tun a wacan lokacin sai ya kasa bani damar na yi rayuwa yadda na ke so, a haka na fara shafa man nan na mai saka haske wai ko farina zai karu na kara burge maza amman a banza sai ma lalata fatata da na yi, ke ce kadai kika tsaya min a rai ina gani kamar hakkin ki ne yake bibiyata dan Allah dan girman Allah dan darajar Annabinsa ki dubi girman Allah ki yafe min Nawwara” 2
Kuka take sosai tana kokarin kama kafafuna, wanda hakan ke tabbatar min da cewar lallai Aysha ta yi nadama, sai dai me abunda bata sani ba, ba hakkina ne kawai yake binta ba, tabbas hakkin aure ba zai barta ba saboda ta tozarta da aure a lokacin da ta samu dama, amman an baro kyau tun ranar haihuwa, domin kuwa ta yi abun da yan mata yanzu suka dauka wayewa wato bayarda kai ga Namiji tun kamin ka aureshi da kuma shigar banza wacce Annabi Allah da kansa yake cewa masu wannan shigar tufafin ba zasu shiga aljannaba kuma ba za su ji kamshinta ba, taya namijin da ya sakin tun a gidanku zai yarda ya aureki? Ko da kuwa ya aureki ba zai taba ganin darajar ki ba kuma babu aminci na zaman aure a tsakaninku har a bada ga kuma azabar Allah tana jiranki matukar baki tuba ba, daman shi namiji duk abunda ya aikata ado ne, ko ina a qur’ane idan Allah zai ambata da da namiji yake farawa sannan mace amman da aka kai babin Zina sai Allah ya fara da macen kamin namiji saboda mace tafi shiga tarko kuma idan bata bada dama ba babu yadda za ayi ta namiji ya aikata. 2
Ajiyar zuciya na sauke zan yi magana sai ga text ya shigo a wayata na Jibril, wai an sallami Noor kuma ya tafi gida da shi sai gobe za su zo nan. Aje wayar na yi na kalleta zan yi magana sai ga Inna ta shigo cikin dakin tana tambayar lafiya jin shisshikar kukan Aysha.
____________________________________
Al-hamdulillah godiya ta tabbata ga Ubangijin da ke ba mu lafiya da rashinta, na samu sauki sosai na gode sosai da kukawarku da addu’o’inku Jazakallahu Khairan 😘 3
Let my advice be here, For those ladies da suke daukar mallaka kai ga saurayi ko da an muku engaged a matsayin wayewa ko soyayya Wallahi babu soyayya babu wayewa a cikin zina, kuma ko da mutun ya aureki baki da wata kima da mutunci a idanuwanshi, wani ma ba zai aureki ba kin ga kin ga kin zubar da mutunci a banza, kar kalaman banxa su yaudari zuciyarki kar karatun wasu littafan yasa ki rika daukar saka suturar banza a matsayin wayewa Wallahi ba duka writers ba ne include me suke rubuta dai dai ko rashinsa ba me some of our readers suna daukar dukan abunda aka rubuta ko abunda duniya take yayi a matsayin wayewa wanda sam ba haka ne kama mutunci da kimarki shi zai nunawa duniya ko wacece ke kuma mijinki da yayanki zasu yi alfahari da wannan, kar ki ga wata ta yi haka at the end ta auri a mijin kwarai a novels ne ko movies irin wannan abun yake faruwa, in reality 75% basa auren mutanen kirki matukar kika maida kanki karuwa babu namijin kwarai da zai so ki a matsayin matarsa, su ma mazajen na banza ai matan kwarai suke nema su aura, be wise, women with attitude na kwarai a lady with class class din kuma na kare mutunci ba na zubarwa, ko da ke ta kwarai a irin shigar da kike wani zai dauka ke yar iskace ko kuma marar tarbiya. 4
Some will say ya zata kawo mana wannan dogon sharhin nan ko? 😂 Wallahi abun yana ci damuna ne sosai kuma wannan ce kadai damar da na ke da ita wanjen yin wannan bayanin. Wanda na batawa rai ya yafe min Allah ya shirya mu gaba daya.Lafiya?”
Inna ta tambaya.
“Lafiya kalau magana ce kawai muke”
“Kin tabbata?”
“Ba komai Inna” 2
Ba dan ta yarda ta juya ta koma waje, ni kuma na gyara zamana na kalli Aysha na ce
“Ba ni kika cuta ba Aysha kan ki kika yi ma, daman duk mai cutar wani yana jin dadi kansa yake cuta domin alhaki zai dawo akansa wata rana, idan ma hakkina ne yake bibiyarki Wallahi na yafe miki daga yau ba zai sake binki ba” 2
Dagowa ta tu ta kalleni da idanuwanta da take faman kuka da su bakinta na rawa ta ce
“Wallahi Nawwara ke ta daban ce ban tsammaci zaki yafe min da wuri haka ba, na gode sosai Allah ya saka miki da Alheri”
“Amin, amman dan Allah ina son ki fada min taya aka yi kika gane gidanmu?”
Sai da ta share hawayenta ta koma saman kujerar ta zauna daidai sannan ta kalleni
“Siraj ne ya kwatanta min”
“Siraj kuma? Waye haka”
Na mata kamar ban san waye shi ba.
“Wani abokin Jibril ne, shi kadai ne wanda Jibril ya aminta da shi a yanzu, shine kadai mutumen da yake karfafa min guiwar cewar zai yi duk yadda zai yi wajen ganin Jibril ya aure ni” 4
“Yanzu kina nan akan bakarki cewar Jibril rai aureki duk bayan yaudarar da ya yi miki?”
“Bana jiransa shi kadai, idan wanda zai aureni da gaske ya zo zan aureshi, na dade da yafe masa abunda ya yi min saboda na san tun farko laifina ne ba nasa ba, kuma har gobe ina son Jibril”
Na sauke numfashi a hankali ina mamakin karfin hali irin nata son wanda baya son ka, ko da yake ya so ta da farko,amman ai ya cuce dan me zata wahalar da kanta gurin son sa. Kamar ta san abunda ke raina sai kawai ta ce
“Na san za ki yi mamakin jin har yanzu ina son Jibril, ke ma da ace kina son shi tun farko ko kuma rabo ya shiga tsakaninku da za ki kula shi, ko da yake Siraj ya fada min yanzu matsalar rashin haihuwa take damunsa shiyasa babu ruwansa da ko wace mace”
“Haka ya ce miki? Yaushe rabon da ki yi magana da shi?”
“Ko jiya mun yi waya da shi”
“Amman har yanzu be fada miki Jibril na da da ba?”
“Haka ya ce min Jibril ba shi da da kuma ya lalata rayuwarsa da shayeshaye hakan yasa mahaifinsa ya koreshi daga kamfanin da yake ya dora Siraj”
“Amman gaskiya Jibril be kyautawa rayuwarsa”
“Ni ma da na ji ban jidadi ba, amman Siraj ya ce zai yi iya kokarinsa wajen ganin ya dawo da shi hanya”
“Allah ya bashi iko”
“Amin”
Sai da ta shafe fuskarta ta gyara Hijabinta sannan ta dauki jakarta ta rayata ta mike tsaye.
“Na gode sosai Nawwara zan wuce”
Har bakin kofa na rakata sai zuciyata na ta tunani akan abokinsa Siraj, miyasa be fada mata cewar yana da da ba? Haka ma yasan lokacin da na fara aiki a kamfanin amman be sanar da Jibril bayan yasan Jibril yana neman ganina, amman kuma miye damuwata da shi ai abokinsa ne babu ruwana a ciki, maganganun Rabi ne suka fado min a rai kan na ankaro Inna ta jefo min wata tambayar.
“Wacece wannan yarinyar? Kamin nan miye shigo da ke kina kuka?”
Sai a lokacin na tuna da cewar na shigo ina kuka, sai wacan bacin rai ya dawo min na soma jin tsanar Jibril sosai a raina. Kusa da ita na zauna.
STORY CONTINUES BELOW
“Inna wannan Aysha wacce ta yi soyayya da Jibril ce lokacin da ya aureni, ita ce wacce ya ce yana so, shine yanzu take neman gafarata”
Haka na kwashe firarmu gaba daya na fada mata irin halin rayuwar da ta ce ta shiga bayan rabuwarsu da Jibril, sai kuma na dora mata da bayanin abunda Jibril ya yi min kamin ya fada mata cewar ya ansallami Noor daga asibiti.
“Jibril be kyauta ba, be da ce ya yi miki haka ba, ina tunanin ya yi haka ne saboda ya bata ki a gurin iyayen Bilal kuma suma ya saka musu fargabar wani abu zai iya faruwa da dansu matukar ya aureki”
“Ni Inna na tsane Jibril bakin mugu ne Wallahi ni ya dawo min da yarona ba zan barshi ya kwana a can ba”
Na fada ina shirin fashewa da kuka.
“Ai kara ki kyale Noor ya shaku da Ubansa tun wuri domin kin san dai Jibril ba zai ta ba bari ki je masa agolanci da dansa ba, ke ma kuma ba za ki ji dadin zaman auren ba matukar kika je da Noor domin Mahaifinsa zai rika amfani da wannan damar yana cin zarafinki da mijin da zaki aura, idan kuma mijin da kika aura ya nuna baya son zaman Noor ki ce baya son ki”
“Allah ka min mafita”
Na fada a fili a zuci kuma na ce Jibril din nan yabi ya tare min ko ina bana da wani sakewa. Muna nan zaune su Sakina suka dawo daga islamiya sai muka dauko wata firar har take fada mana wai malaminsu ya ce satin saman za a kawo kudin da zasu ba iyayensu domin su cigaba da daukar nauyin karatunsu.
“Wai Inna ba zamu koma sabon gidan nan ba?”
Ta tambaya, ni har na manta da maganar gida domin ban taba zuwa ma ganinsa ba.
“Ba zamu koma ba, ko kudin nan ba zamu karba ba duk Jibril ne yake shirya wannan abun, saboda ya siye mu da dukiyarsa”
“Ya fada miki shine?”
Inna ta tambaya.
“A a amman na san shi kadai zai iya wannan abun, idan ba shi ba ne waye ne”
“Nima na yi wannan tunani”
“Dan Allah Inna karku sake karba komai na sa idan ya baku, Wallahi mutumen ya raina mana hankali sosai ma saboda ya maida mu talakawa, ai da masu kudi ne mu be isa ya taka mu ba”
“Kin dai ce kin yafe masa, bana son wata rigima kuma bamu je muka rokeshi ya bamu ba bana son wata fitanar kuma”
“Ba zan yi komai ba ai, amman kawai abun yana ci na sosai Wallahi ya ci amanata sosai, kuma ya raina min da wayo da har zai ce ya wai yana neman ya sake aureni, Wallahi aurena da be so da Bilal sai an yi sai dai ya mutu azzalumi kawai”
Na fada cikin daga murya hawaye na zuba a ido, ji nake kamar ace Jibril yana kusa da ni yanzu na shakeshi ya mutu. Bayan mun yi sallah magariba na kira Bilal a waya sai ya dauka, na yi tsammanin zan ji shi a cikin wani yanayi marar dadi ko makamancin haka amman sai ya zo a kasin tunanina na jishi cikin farinciki da walwala
“Yar halak kin kirani daidai lokacin da zan kiraki na ce ki fito waje gani nan”
“Bilal kai ne”
“Ni ne mana, wani kika je kira ne kika kirani?”
“Aa kawai na ji na cikin farinciki”
Ya yi dariya
“Cikin bakinciki kike son jina”
“Aa kawai na dauka zaka ji haushi na ne kai da Abbah”
“Akan me zan ji haushinki Nawwara, abunda kika aikata be kara min komai ba sai kaunarki, yanzu dai fito gani nan kofar gida”
STORY CONTINUES BELOW
Daga haka ya kashe wayar ni kuma na lumshe ido cike da jindadi na sauke ajiyar zuciya, sannan na fadawa Inna na dauki Hijabi na saka na fito kofar gida, jingine da ginin gidan na sameshi kamar kullum yana jiran fitowa.
“Pearl”
Na kalleshi fuskarta da murmushi.
“Wallahi ban tsamaci haka ba ko kadan, na yi tsamanin Abbah zai maka fada ne”
“Nawancy kenan, ya yi min fada sosai amman akan rashin kunyar da na yi ma Hajiyar Mustapha ba wai akan abunda ya faru ba, kuma ko da yayi min fada akan ai ba zan dora laifin akanki ba, shine ma ya bani shawarar karna fadawa Mama cewar kin je station domin ya fahimci muna son junan kuma idan Mama ta ji zata yi fada”
“Na gode Allah da Abbah ya fahimta”
“Kuma ya ce na fada miki cewar Assabar din nan mai zuwa zai zo ya ga su Baba Sulaiman” 4
Na rufe idona da sauri saboda dadi da kunya da suka rufe ni lokaci daya.
“Da gaske?”
“Aa da karya”
Ya fada da fuskar zolaya, sai na sa dariya.
“Mama fa mi ta ce?”
“Me kike tsammanin zata ce?Addu’a kawai ta yi mana da fatar Allah ya sa alheri a ciki”
Na san yace haka ne kawai dan ya kareta amman ba zata so aurena da danta saboda tana ganin kamar kwaruwace xan yi ma danta bayan na yi aure biyu har da kuma yanzu na ce zan auri danta. Mun sha fira sosai a wannan daren sai da aka fara kiran sallah isha’i sannan muka yi sallama ba dan ran mu ya so ba ya tafi ni kuma na dawo cikin gida. Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindadinta akan maganar har ma ta yi mana addu’a, daga baya kuma ta tambaya abunda iyayensa suka ce kan abunda ya faru yau, ni kuma na labarta mata kamar yadda ya labarta min.
Bayan mun gama sallah isha’i wayata ta yi ringing ko da na duba sai na ga number Rabi na yi mamakin kiranta a wannan lokacin sai dai hakan be hanani dauka ba.
“Assalamu alaikum”
“Wa’alaikissalam Nawwara kina gida?”
“Ina gida lafiya dai?”
“Lafiya kalau akan maganar nan ne, bana son na yi shigowar rana wani ya gan ne, alhalin kuma ba Oga Jibril ba ne ya aiko ni”
“Yanzu zaki zo kenan”
“Idan zan samu dama ba”
“Allah ya kawo ki lafiya”
Daga haka na kashe wayar sai ga kiran Jibril ya shigo wayata, da gangan na ki dauka saboda ina tunanin wata maganar zai min ta daban, har sai da ya yi min kira fiye da uku sai kuma ya aiko min da sako karta kwana wato sms cewar Noor ne yake son magana da ni, da ya sake kira sai na dauka cikin rashin walwalah saboda tsanarsa da na ke ji cikin raina.
“Hello”
“Babe-Naj ga Noor zai yi magana ina fatar kina lafiya”
“Zan bashi but ki amsa min mana ko sanyi na ji”
“Zan kashe wayar idan baka ba shi ba”
“Allah ya huci zuciyarki, ya dorani akan ki Naj”
Yana fadar haka ya mikawa Noor wayar.
“Hello Momy ina wuni? Momy i miss you”
“I miss you too miyasa ka bi Daddynka ba ka zo nan ba?”
“Daddy ne ya zo da ni, kuma ya ce ke ma za ki zo gobe, Momy ki zo yanzu mu kwana nan dan Allah”
“Ba zan zo ba Noor, gobe ma ba zan zo ba har abada ba zan zo ba, idan kana son zama da ni ka ce ya dawo da kai gidanmu”
STORY CONTINUES BELOW
“Saboda me ba za ki zo ba?”
“Saboda nan ne gidanmu ni ba zan zauna ko ina ba sai gidanmu”
“Momy gidan yana da kyau fa, har ya fi na su Sadiq kyau dan Allah ki zo”
“Ba zan zo ba Noor, idan kana son zama tare da mu ka ce ya dawo da kai gida gurin mu”
“Momy zan yi kuka”
Ya fada cikin muryarsa mai nuna yana shirin yin kuka da gaske. Sai na ji muryar Jibril yana fadin
“No no don’t cry Noor tana maka wasa ne kawai zata zo”
Ni kuma na katse wayar na kalli Inna.
“Inna rabi zata zo yanzu, akwai maganar da zamuyi da ita”
“Wace magana ce?”
“Wallahi nima ban sani ba, amman dai ta ce tana da muhimmanci sosai”
“Da wa kike waya yanzu”
“Noor ne”
“Amman shine kike fada masa wannan maganar kamar wani babba? Kina son ki saka danki a damuwa ko? Ki raba masa hankali gida biyu”
“Amman Inna ai kara na fada masa gaskiya saboda yasan ba zan taba zama da mahaifinsa ba tun yanzu”
“Amman be kamata ki masa magana ta wannan hanyar ba, ki daina sauke masa haushin mahaifinsa akansa”
“Inshallah Inna ba zan kara ba” 1
“Allah ya kyauta gaba”
Sai da na amsa da Amin sannan na tashi na soma duba dakin inda be kintsu ba kimtsa saboda kar Rabi ta zo ta tarar da dakin ba a natse ba.
Tara saura kwata ta Rabi ta shigo gidanmu da lullubinta na katon gyale kai baka ma ce ita ba ce, duka muka hada baki gurin amsa mata sai na fita na shigo da ita cikin dakin ta gaisa da Inna sannan Inna da su Sakina da Jamila suka fita waje suka bar mu mu kadai.
“Ina tunanin babu wani gurin da ya kamata mu yi maganar nan sama da gidanku shiyasa na zabi na tarar da ke a gida, kuma idan da dare ba kowa zai gan ni ba balle har a tsammaci wani abu”
“Me kike so mu tattauna mai muhimmanci har haka?”
“Na fada miki akan ki da kuma dan ki da kuma Noor”
“Me muka yi?”
“Ba ku yi komai ba sai dai wanda ake shirin yi muku”
“Ban fahimta ba”
Ta sauke ajiyar zuciya.
“Nawwara ke kadai ce mace da zata iya tsamo Jibril daga tarkon Siraj a yanzu, ke kadaice zaki iya raba alakar da ke tsakaninsa da Siraj a yanzu” 1
“Miye nawa a ciki da har zan shiga na raba alakarsu? Babu komai fa tsanina da Jibril”
“Na san babu komai a tsakaninku a yanzu, amman ai akwai yaro tsakaninku, iya abunda na fahimta Oga Jibril yana son ki sosai, ke ce kadai zaki iya anrar da shi daga ramen da yake kokarin fadawa”
“Ni fa ban gane wannan bayanin na ke ba”
“Nawwara Siraj ba abokin kwarai ba ne, kokarin zamewa Oga jibril kafafu yake ya dilmiyar da shi, kokarin kwace duk wani abu da Jibril ya mallaka yake kokarin ganin ya zama na sa. 1
Sunana Rabi’at Abdulrazak, ni ba bahaushiya ba ce ni ibira ce asalina ni yar jihar kogi ce, ina zaman gurin Antyna ne a Abuja bayan na gama karatu na, daga baya na samu aiki a kamfanin One on One limitless company da ke Abuja, da sannu na fara aikina kwarewata da kuma jajircewa ta a akan aiki yasa mahaifin Jibril wato Alhaji Baahir yake yaba min sosai kuma ya dauki yarda ya bani, lokacin da zai turo Jibril aiki a nan sokoto sai ya sa muka zo tare akan na rika kula da duk wani abu da Jibril yake yi saboda yana ganin kamar Jibril ba zai iya kula da kamfanin yadda ya kamata ba, da muka dawo nan sai Jibril yasa aka yi ma Siraj transfer daga Abuja zuwa nan, ban san cewa Siraj abokin Jibril ba ne sai a wannan lokacin, ba zan iya fada miki dalilin alakarsu ba domin ni ma ban sani ba, amman da aka dawo da shi nan sai Jibril ya dauki yarda da amana ya mika masa, idan be samu zuwa meeting ba Siraj yake turawa, komai za ayi sai ya ce a a nemi Siraj”
Ta gyara zamanta kana ta yi dariya.
“Ba ina kishin Siraj ba ne Nawwara, sai dai akwai abubuwan da na lura da su akan Siraj, ina tunanin kamar shi ya koya masa shan cocaine saboda ua haukarta shi ko kuma ya juyar da hankalinsa zuwa wani gurin ba dan damuwar Jibril kawai ba, idan har dan damuwa ce shi Siraj baya da ita? Miyasa baya sha sai Jibril yake bawa? Abu na biyu ni yake sa na kira mahaifinsa na fada masa dukan abunda yake gudana a kamfanin marar kyau, Siraj ne yayi kokarin kashe Noor saboda yana tunanin idan har Jibril ya san yana da da zai sashi ya daina abunda yake kuma ya natsu, wanda ba haka Siraj ke so ba kuma yana ganin kamar idan Noor yana raye dole wata alakar zata sake kulluwa tsakaninki da Jibril wanda baya son haka shi be ki ma Jibril ya mutu ya mamaye dukiyarsa ba, da hadarin ya faru sai ya dorawa Bilal laifin ta hanyar sanar da Jibril cewar wani ya fada masa cewar Bilal ne ya yi kokarin kashe Noor saboda yana bakinciki Jibril, wannan yasa Jibril ya koreshi daga aiki har ma yayi kokarin kai kararsa kotu amman sai Siraj ya hana a cewar su wai basu da hujja su jira har sai an samu wani abun na daban wanda zasu rike su yi hujja da shi, ke kanki rayuwarki tana cikin hadari domin Siraj zai iya sawa a kasheki kuma a kashe Noor saboda Noor ya ga fuskarsa lokacin da ya yi kokarin kadeshi da mota, ya yi nadanar hakan kuma ya ji bakinciki sosai da Noor be mutuba, daga baya kuma sai ya wani tunanin ya zo masa cewar miyasa be sa wani ya aikata ba sai shi ya aikata? Wannan ya tabbatar da cewar nan gaba ba da kansa zai je kashe ki ko Noor ba wani ko wasu zai sa su yi, yana tunanin idan ya yi haka shikenan ya gama da rayuwar Jibril sai kuma ya yi amfani da cocaine ya karasa halaka shi.
Na san zaki yi mamakin jin haka ko kuma ki yi mamakin a ina na san duk wannan ko? Na sani ne saboda Siraj ya fada min, yana amfani da ni ne a matsayin wacce mahaifin Jibril ya yarda da ni, ya ce min zai aureni kuma duk abunda ya samu zai raba rabi ya bani rabi abunda yake kokarin yi yanzu ya mallaki nasa kamfanin ta karshin wannan kamfanin, a yanzu haka mahaifin Jibril ya sauke Jibril ya dorashi akan kamfanin kin ga ya fara samun dama kenan, ni kaina rayuwata tana cikin hadari domin mugun mutum baya yarda da kowa, ni kaina xai iya cutar da ni idan ya samu abunda yake so, saboda yana ganina kamar ba bahaushiya ba yasa yake son ya yi amfani da wannan damar ya cilla burinsa saboda yana ganin kamar muna da son kudi kuma idanuwana a bude suke, na masa na amince ne saboda na san idan har na ki amincewa zai iya kashe ko ya kulla min wani sheri saboda ya san na san sirrinsa, kuma a matsayin na wacce ke aiki karkashin Jibril ba zan iya fada masa wannan ba, bana da wata hanyar sai ta ki, ke kadai ce zaki iya hankaltar da shi domin ceton rayuwarki da ta danki da kuma ta Jibril har ma da tawa gaba daya, ki kuma tsirarta da Bilal daga sherin da yake kokarin laka masa, kin san idan wani abu ya samu Noor dole Jibril ya zargi Bilal kuma ba zai taba kyaleshi ba”
Hannu nasa na rufe bakina sai kuma na sauke ajiyar zuciya, kaina ya yi nauyi sosai kalamanta sun min hawa har na rasa wanne zan fara tunani balle na samu abunda zan ce mata, ji na yi ta dafani.
“Nasan yana da nauyi Nawwara, ki yi tunani akai, ban san abunda ya raba ki da Jibril ba, amman yana da kyau ki shiga rayuwarsa ko dan gaba ko kuma na ce ko dan danki, abu na karshe da zan fada miki shine Jibril yana son ki sosai da sosai, domin lokacin da Siraj ya sanar masa cewar kin mutu ya yi kamar na haukace, ba sai na gargadeki akan karki fadawa kowa wannan sirrin ba saboda ina ganin a mace mai tunani da hangen nesa na barki lafiya” 2
Da ido kawai na bita har ta fice, sannan na dawo duniyar mamaki da aljabi anya zan iya wannan aikin kuwa? Mi ma zai kai ni taimakon mutumen da ya nemi salwantar da tawa rayuwar? Abu na farko da ya zo min a rai shine Inna dole ne na fada mata komai ko dan neman shawararta, cikin hanzari na tashi na fita waje gurin Inna.Inna ta tsorata sosai da abunda na fada mata hankalinta duk sai ya tashi. +
“Taya zaki iya shiga cikin wannan lamarin Nawwara?ke fa mace ce ba namiji ba, kuma irin wadannan mutanen hatsarine rabarsu”
“Nima abunda na ke ta tunani kenan! Ona ganin aiki zan sa Jibril ya koma sai mu koma tare kin ga duk wani taimako zan iya bashi ta nan kuma ina lurar da shi akan wasu abubuwan”
“Gaskiya Nawwara ina jin tsoro, karki je ki janyo mana wani abun na daban kuma”
“Babu komai Inna ba zan fito kiri da muzu na fada masa abunda yake faruwa ba, ta dabara zan yi”
“Kina tunanin hakan ba zai haifar da wata matsala ba?”
“Inshallah ba zai haifar ba”
Ta kawar da kai ba dan ta yarda din ba, ni kuma ina ganin bana da wata mafita sai wannan. 2
JIBRIL POV.
Lokacin da Noor ya ji cewar Momynsa ba zata zo ba sai duk yanayinsa ya canja ya koma cikin jin bakinciki da damuwa, duk yadda Jibril ya so kar ya bata rai sai da Noor ya bata kuka ma sai da ya yi. A gado daya suka kwanta under one bedsheet, misalin biyu da rabi na dare Jibril ya farka ya shiga bedroom ya dauro alwala ya fito ya shinfida carpet ya soma sallah nafila da a yanzu ta soma zame masa jiki.
Kuka ya yi sosai yana neman yafiyar Allah akan abubuwan da ya gabatar marasa kyau sannan ya roko Allah bukatunsa tare da neman shiriyar Allah. Be san yadda zai karanta qur’ane ba but yasan yadda zai yi iistigifari da hailala da kuma tasbishi da kuma salatin Annabi. Yana zaune saman carpet din har aka yi asalati sannan ya tashi ya fita zuwa masallaci. 6
Misalin takwas da rabi Noor ya farka a lokacin Jibril na kitchen yana hada musu breakfast, ko da Jibril ya fito ya samu Noor tsaye bakin kofar bedroom yana ta kallon falon.
“Good morning Noor”
Sai kawai ya saka dariya kamar ba shine ya kwanta da fushi jiya ba, kuma ya rufe ido wai yaji kunya an gaishe shi. Jibril ya aje kayan da ke hannunshi saman dinning sannan ya nufo Noor ya duka daidai shi ya kama hannayensa ya rike.
“Ka tashi lafiya?”
“Lafiya kalau, Dady na manta ban tashi ba sai yanzu”
“Yeah ai kara ka yi bachi mai kyau ka samu ka huta ko?”
“Momy da wuri take tada ni na yi sallah” 3
“Yanzu ma ai lokaci be kure ba muje bedroom ka yi sallah”
Tare suka shiga bedroom din Jibril ya taimaka masa ya wanke bashinsa sannan yaa yi masa wanka ya yi alwalah sannan ya daura masa tawul suka fito yana dauke da shi. Ko da ya fito wayarsa na ringing da sauri ya dauka ya kara a kunne.
“Assalamu Alaikum Malam, okay gani nan fito”
Sai ya zaunar da Noor saman gado.
“Jira ni a nan ina zuwa”
Number Rabi ya nemo ya tura mata sakon daga bisani ya yi mata transfer na kudi i zuwa account dinta dan ta siyoma Noor tufafi, ko da ya fito Malamin na tsaye waje kusa achabansa yana jiran fitowarsa, cikin girmamawa Jibril ya mika masa hannu suka gaisa sannan ya dora masa da.
“Na san yau ya kamata ace mun fara but yau ina tare da yarona kuma yanzu idan mun gama karyawa zan kaishi gida, so ina baka hakuri zuwa gobe sai mu fara, kuma in fa hali ina son bayan mun yi da safe mu yi da yamma”
“Ba matsala, zamu iya farawa gobe din Allah ya kaimu amman kamar wane lokaci?”
“Irin takwas na safe haka, da dare kuma tara na dare nasan bayan wannan lokacin ina gida, sai salarinka nawa ake biyanka per month?”
STORY CONTINUES BELOW
“Aa ranka ya dade bana son sisinka, zan koya maka komai saboda da Allah”
“Kai amman ina godiya sosai Allah ya saka da alheri”
“Amin amin sai dai littafan da za a siyo”
“tau kamar nawa za a kashe?”
“Zamu siyo ahalari sai kuma husnul muslim da kuma dan goma mai hade da bakaken harufan arabi ta yadda zai maka sauki ganewa”
“Kana da account ne?”
“Eh akwai”
“Okay ina zuwa”
Wayarsa ya bude ya yi masa transfer 10k na siyen littafan, har Malamin na cewa kudin ya yi yawa sai ya ce ya dauki sauran abunda ya rage. Cikin dadin rai ya dawo parlour saboda yana jin ya fara taka wani mataki na gyara rayuwarsa, abunda yake ta kokarin yi shine ya zama uba na gari gurin Noor wanda zai yi alfahari da shi ko bayan ransa.
Da kansa ya yi feeding Noor sannan ya shiga wanka ko da ya fito Rabi tana parlour zaune ta kawo masa kayan Noor da ya bukaci taje ta siyo, ita yasa ta shirya Noor, shi kuma ya shiga ciki ya shirya kansa sannan suka fito tare harabar gidan ita ta wuce shi kuma ya kama hanyar gidansu Nawwara tare da Noor dake gaban Mota.
Jibril ne ya fara fitowa cikin motar sannan ya zagaya ya budewa Noor ya dauko ya dorashi kofar gidan.
“Shiga ciki ka ce da Mamanka ina waje”
Da gudu Noor ya shiga cikin gidan, bayan few seconds ya dawo ya ce
“Wai ta ce ka shigo”
Wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya dora kafarsa a kofar gidan ya shiga bakinsa kumshe da sallama.
“Wa’alaikaissalam”
Inna da amsa masa, sai ya zube a gurin yana kwasar gaisuwa kai baka ce ma shi ba ne, kansa a kasa yana mai jin kunyar Inna sosai kamar yau ya fara haduwa da ita.
“Tashi Jibril shigo ciki, ashe an sallami Noor”
“Eh an sallame shi jiya shine naje da shi gida”
“Allah ya kara lafiya”
“Amin ya rabb”
Daga haka ya mike tsaye.
“Bari na wuce daman wani gurin zanje na ce bari na fara kawoshi”
“To an gode”
Tashi ya yi ya juyo ba dan kuma yana da gurin zuwan ba, yace hakan ne kawai saboda ya kare kansa, yana son ya tambaya ina Nawwara kuma yana jin kunyar haka ga alheri yana son ya yi ma Inna kuma be san yadda zata kalleshi ba. Bayan na fito ya nufi motarsa sai yaji Muryar Nawwara ta kirashi.
“Jibril”
Ya juyo da sauri ya dawo zuwa inda take.
“Nawwara kina lafiya”
“Lafiya kalau”
“Am sorry about yesterday”
Ya fada yana kallon yanayinta sai kawai ya ga murmushi a fuskarta abunda ya bashi tsoro da kuma mamaki a lokaci daya, dan ya yi zaton wata bakar maganar zata fada sai kawai ya ji ta ce 1
“Never mind, ni har na manta da wannan ma, amman Jibril ka ce min zaka canja ko?”
Ya kara matsowa kusa da ita.
“Na canja Nawwara ba wai zan canja ba, Wallahi na canja”
“Idan har ka canja zaka zama uba na gari Jibril, kuma da na gari gurin Mahaifinka”
STORY CONTINUES BELOW
“Abunda na ke kokarin yi kenan ganin na zama uba na gari wa Noor”
“Miyasa zaka mikawa Siraj ragamar kamfanin mahaifinka?”
“Saboda na yarda da shi kuma mahaifina ya yarda da shi, kuma ba zan iya jan raganar kamfanin ba a yanzu”
“Saboda mai?”
“Saboda ke Nawwara tunanina da damuwata duka akanki suke”
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce
“Ya kamata ka yarda da kaddara Jibril, ka yarda abunda ya sameka da wanda zai sameka nan gaba duka daga Allah ne, ka daina saka tunani a cikin ranka saboda ni matar wani ce, idan har ka yarda da kaddara ina son ka cireni a cikin rayuwarka, Jibril ina son ka nuna min irin son gaskiyar da kake min ta hanyar maida hankalinka akan rayuwarka da kuma ta danka, ina son ka min alkawari Jibril cewar ba zaka sake shan cocaine ba, kuma zaka maida ragamar kamfanin mahaifinka a hannunka, ina son ka zama jarumi Jibril” 2
Kallonta yake yi ido cikin ido yake karantar gaskiyar kalaman dake zuciyarta, duka abunda ta rokeshi yayi zai iya yi matukar hakan zai faranta ranta.
“Na miki alkawari Nawwara zan yi duka abunda kika fada”
“And lastly ina son ka cireni cikin ranka Jibril, ka yi focusing akan rayuwarka ta nan gaba da kuma ta danka, ka sa a ranka ko babu Nawwara zaka iya rayuwa, domin can baya babu ni a duniyarka, a yanzu ma idan babu ni zaka iya, na tabbatar min da canjin da kake cewa ka yi Jibril ka zama namijin gaske”
Ya gyada mata kai yana murmushin da yafi kuka ciwo.
“I promise you Nawwara zan yi dukan abunda kike bukata”
“Zan maka addu’ah, kuma ina son na koma aikina tare da kai”
“Zamu koma yaushe kike so?”
“Allah ya kaimu, but Nawwara ina fatar ba za ki hanani kusanci da dana ba, kuma ba za ki hanani kyautatawa family ki ba”
“Na fi kowa son ka yi kusanci da Noor Jibril saboda na san ko nayi aure ba zaka bar ni naje da shi, so tun yanzu ina son Noor ya saba da kai sosai da sosai, matukar wannan canjin da na gani a yanzu a tare da kai ya tabbata zan fi kowa farinciki Jibril I’m ever ready to help you ko dan saboda Noor”
Matsowa ya yi kusa da ita kamar zai taba ta sai dai yasan babu wannan damar domin bata son ya tabata kuma shi ma kansa yana son sabawa kansa da wannan.
“Thank you so much Nawwara, Wallahi Ina son ki sosai ina son ki yarda da wannan”
“Na yarda Jibril”
“Ina jin kamar mafarki na ke Nawwara, you actually changed”
Ta yi murmushi tare da sanda kanta kasa abunda ya kara burge Jibril ya ji wani sonta na kara shigarsa, sai dai kalamanta na cewar ya fitar da ita daga ranshi be masa dadi ba, but shi kansa yasan yana bukarta cireta a ranshi ko dan ya samu sukuni a rayuwarsa.
MUSTAPHA POV.
Yau kwanansa biyu da dawowa daga asibiti, tun lokacin da Hajiyarsa ta yi ma Nawwara wannan furucin ransa ya sosu matuka yake jin rashin dacewa da kyautawa abunda Momynsa ta yi.
Dan haka ya yanke shawarar yau sai ya kaiwa Nawwara ziyara saboda ya bata hakuri kan abunda ya faru, dan haka yana fita sallah magariba be dawo ba ya wuce gidansu Nawwara, ya taki sa’a yana aikawa kiranta sai gata ta fito cikin Hijabi sai kamshin turare take, sallama ta fara masa sannan gaisuwa ta biyo baya, daga nan kuma sai dukaninsu suka yi shiru ita tana jiran abunda zai fada mata shi kuma yana tunanin ta ina zai fara, da ta fara gajiya da shirun ne yasa ta ce
“Ya jikinka? Sorry ban je na dubaka a asibiti ba”
Yayi mamakin jin furuncinta domin sam be tsammaci ma zata fito ba balle har ta kula shi haka har da tambayar jikinsa.
“Naji sauki sosai Nawwara, ina son na baki hakuri akan abunda Momy ta yi miki last time…”
Ta daga masa hannu.
“Mahaifiyarka tana da gaskiya Mustapha, na kaina uwa ce kuma uwa kadai tasan abunda wata uwar take ji game da danta, ni kaina ba zan yarda dana ya rasa rayuwarsa akan wacce bata san zafinsa ba, wacce na san ba zata taba aurensa ba.
Mustapha ya kamata ka yi tunani, ni da kai ba daya ba ne, ballanta wani abun ya shiga tsakanin ni da kai, yar uwata ka yi ma fyade taya kuma ni zan aureka? Zuciyarka ta daina yaudararka abunda ba zai taba tabbatuwa a gareka ba, ka daina hangen abunda ba naka ba, Ina tunanin mutuwar Habiba ta canja mana rayuwa dukanmu, ta zamo silar shiriyarka, shin miyasa ba zaka tsayardar tunaninka guri daya ba ka yi abunda zai fiddaka?
Duk yadda zaka so ni aikin banza ne, saboda komai ya riga ya lalace, a zan boye maka Mustapha soyayyarka ba zata taba samun gurbi a zuciyata ba ko da kadan ne, ka daina wahalar da rayuwarka akaina, ka yarda kaddara ce a haka sai kaga Allah ya kawo maka mafi alherinta”
“Thank you Nawwara na gode da kika fada min gaskiya, har gobe ina alfari kuma zan kasance a cikin alfari da son ki har abada, domin son ki ya canja min rayuwa, ya sa na zama kalar da ban taba tsammanin zama ba”
Ya fada idanuwansa na cika da kwalla.
“Ina maka fata ta gari Mustapha, domin ni Bilal zan aura kai ma ina maka fatar samun matar da zata so ka sosai kuma iyayenka su so ta tadda zaka ji dadin zama da ita”
“Thank you but ina son ki taya ni da addu’a domin abun ba sauki”
Ya fada yana murmushin karfin hali tare da share hawayen da suka zubo masa.
“Zan taya ka, ina maka fatar alheri”
Ya dade a tsaye yana kallonta yadda zai yi rayuwa babu ita yake hange, ya san gaskiya ta fada masa shi kanshi yana jin kamar ba zata aureshi ba, sai dai a ganinsa idan har bata aureshi ba ba zai taba gamsuwa cewar ta yafe masa ba, but kalaman da tayi masa a yanzu yasa shi canja tunaninsa kuma ya samu gansuwa a ransa cewar Nawwara ta yafe masa har zuciyarta, ya riga yasan matukar yana son ya shirya da iyayensa dole ya rabu da ita, duk da yana jin a yanzu ta zama wani bangare na jikinsa.
Kamar marar lafiya haka ya dawo gida nan da nan sai zazzabi ya rufe sai dai be bari mahaifiyarsa ta sani ba.