SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 11

SILAR GIDAN AIKI




CHAPTER 11




Bayan Kwana Uku
Rana bata karya sedai uwar diya taji kunya, yau Saturday, za’a daura auren Mubeen da Haleema, +

Bangaren Nazeefa kuwa tun garin Allah ya waye hankalinta yai mugun tashin Dan tasan yau ba makawa za’a daura auren Mubeen, zazzabine ya rufeta sosai har dinshi dinshi take gani, tai kokarin ta boye abun dake ranta amma Ina seda aka gane! Dan jikinta yai zafi sosai, Asibiti aka kaita aka kwantar da ita akace Tana bugatan hutu sosai Dan jininta yayi kasa, anan ta sama daman Kuka yanda takeso koda an tambayeta se tace ita jikintane ya matsa Mata basusan Kukan rashin Mubeen bane…..

Haleema burinta ya cika, Mubeen kuwa KO a jikinshi inkun ganshi bazamu kuce ango bane, Dr Bashir ne da abokanshi suka matsamai ya shiga wanka Dan sunsan ana jiransu dan karfe 12:40 kuma 1:00pm ne daurin auren Mubeen ya Kalle Bashir yace” bazanjeba kuje kuce banda lafiya

Dr bashir ne yai kasa kasa da murya yace” nasan ba sonta kkeyiba Nazeefa kakeso but please ka daure ka shiga wankar Dan Kar a gane akwai wani abun please koma menene we talk later, Binshi da ido kawai yayi sannan ya shiga toilet, ya shiga ya kasayin Komai Dan ko kaya be cireba, kallon kanshi yayi a jikin mirror din dake bayin kawai ya fashe da kuka, Dan Zuciyarshi gaba daya ta kwadaito da son Nazeefa, A ranshi yace” Inama da Nazeefa za’a dauramun aure ai da tuni nayi wankana ya sake fashewa da kuka ya kusan 15mins a bayi yana tsaye yana kuka

Buga kofar toilet din yaji anayi yaji muryan Bashir yace” We’re waiting for you gentleman

Tsaki yayi yai sauri ya watsa ruwa ya dauro alwala ya fito fuskar nan a murtuke ba annuri, Abokanshi kuwa se ango Ango suke cewa

Shiryawa yayi cikin shadd gezna blue yasha ado sannan suka fito kayansu iri daya da Bashir direct motocin Eu suka shiga basu bata lokaci ba se wajen daurin auren

A daura auren Mubeen da Haleema, Mubeen na cikin mutane Haleema ta kirashi tace” angona na kaina, haushi ya isheshi yace plz Ina Cikin mutanene zamui magana later

nan take fuskarta ya sauya wai me yasa Mubeen yake Mata hakane, Wata zuciya kuma tace aikin banza an daura dai

Bayan daurin auren ne aka tafi dinner, shima nan seda abokanshi sukaiwa Mubeen fada sosai akan ya daure yaje, yace shi ba inda zaije, ansha gwagwar maya da shi sannan ya Kara kintsawa suka tafi amman fuskar nan ba annuri Sam, Dan shi gaba daya hankalin shi na wajen Nazeefa

Tun a wajen bikin yaga kalar kawayenta jikinshi yadanyi sanyi but bece Komai ba a cewarshi saboda bikin ne yan Mata sukai dressing haka

Nan MC ya umurce amarya da ango su fito sui rawa, Haleema ba jan aji, kan nan na rawa ta fito tsakiyar hall, kayan jikinta ya matseta, Mubeen shuru shuru be fitoba, MC yace ango ka fito Kar Kai mana fuck up ga amaryanka a tsakiyar hall, tsaki yayi, Haleema Kuwa dataga yana shirin bata kunya gaban kawayenta gogaggu, zuwa wajen inda yake tayi ta kamo hannunshi gaba daya hall din Yadau tafi raff raff raff duk rashin kunyarshi ranar seda yaji kunya

He has no option hakanan ya biyowata aka samu musu kida Haleema rawa tayi son ranta tamkar ba kowa a hall din, Mubeen kuwa se basarwa yakeyi yana mamakin rashin kamun kanta, Sundau kusan 15mins a haka masu musu vedio Masu hoto nayi, Sannan MC yace duk su matsa a bar amarya da ango a wajen, kowa komawa wajenshi yayi ya zauna

MC ne ya mik’a wa Haleema Speaker yace ta fadawa al’umman nan irin farin cikin da taji na yau ranar auranta…ta amsa tana murmushi tace” _I can’t express how happy I am, domin wani dadi nakeji na musamman, Sannan ta kalla Mubeen tace I love you my darling sannan inama kowa addu’an Allah yakaiku gida lafya mungode da soyayya_ Hall din yadau ihu sosai

MC yace” mungode Amarya, sannan ya mik’a wa Mubeen yace” Wani irin farin ciki kaji ayau?

Mubeen ya amsa yace” ina godewa Allah daya kawomu wannan rana me albarka, Allah ya kara cika mana burinmu na alheri!

Dr bashir yana jin maganar Mubeen ya gane inda ya dosa girgiza Kai yayi yace” Allah ya baka Nazeefa abokina

Anyi dinner Iya dinner Masha ALLAH, abun se Wanda yagani

Ankai amarya dakinta, komai Masha Allah, kawaye kuwa kowa se tsegumi akeyi dan part din da aka kaita yai bala’in haduwa

Haleema hankalinta kwance Dan burinta ya cika

Kawayen amarya ankwana an hantse, dare nayi abokan ango suka kawo angon dakinshi, nan dai suketa musu fada akan zauna lafiya

Da zasu tafine Mubeen ya rakosu, suka Dan kebe da Dr Bashir yai Mai fada sosai akan ya daure duk da ba choice dinshi ya aura ba yayi hakuri, Kar ya dinga nuna Mata kiyayya komai zaizo ya wuce da yardan Allah, Mubeen yace yaji ya gode sukai tafiyansu ango ya shiga dakin amaryanshi

Tunda Mubeen ya shiga dakin amaryarsa Ko kallon inda take beyiba hasalima Wayarshi ya dakko ya na Dan danne danne a wayarshi, mutumiyarku kuma Se iyaye takeyi ita adon dole amarya..haha

Yana zaune Yaga tinanin zemai yawa ya kalleta yace tashi muje muyi alwala mui sallah Mu godewa Allah, da sauri ta mik’e ta nufa toilet, shima toilet din dakinshi ya shige yai alwala sannan yazo dakint sukai sallah daganan be Kara ce mata komai ba ya koma gefen gado yai kwanciyarshi, da tinanin Nazeefa yai bacci

Haleema kuwa yau taga ikon.Allah, a ranta tace ji mutum kamar dutse AI KO hannunta ya taba a matsayin matarshi, Tsaki tayi itama ta kwanta tace munanan dakai Mubeen Bangaren Nazeefa Jikinta ya tsananta sosai dan taqi kwantar da hankalinta, balle idan ta tina yanzu fa mubeen ya aura Haleema se taji wani iri hakanan tai kokarin nutsar da kanta tana jera addu’o’i har ta sama natsuwa sosai, Kwananta uku aka sallameta amma idan kun ganta se kun tausaya mata, duk ta rame, bayan sundawo gidane Hassan da hussaini suna hira a farfarjiyar gidan, Hussaini yace” Twin bro kasan meye? wallahi yarinyar nan naban tausayi Sosai, Hassan yace ka rigani a fili na rigaka a zuci, Amma kasan meye duk yanda akai akwai abundake damun tane gaskiya Hussaini yace” to psychologist har ka gano kenan, Hassan yai dariya yace of course but nasan with time zamuji komai ne ma, Hussaini yai dariya yace uhmmm baridai nai shuru, Hassan yace seka fada, yace Zan fada amma ba yanzuba, dariya dukansu sukai saboda haka suke in suna tare sun dinga zolayar junansu kamar abokai
+

Suhaila da jamila Suna daki suka hango Hassan da Hussaini suna zaune suna dariya da ganin labarin da suke yana sasu nishadi, Jamila tace kingansu Chan maza kije ki trying luck dinki KO za’a dace tunda sunqi furta suna sanmu

Suhaila tace ki bari ni har na gaji ya zirga zirga a filin gidan nan, jamila ne tai dariya tace sorry dear ki tashi tunda abunda muke nemane ai bazamu gajiba, tace hakane fa

Tashi tayi cikin yanga da Dan siririn jikinta ta Fara tafiya a fargajiyar gidan har ta iso inda suke, Fara leke leke tayi kamar be duban wani abu, har tazo ta gabansu ba Wanda ya kula da ita don sun shiga cikin hiran Nazeefa sosai, Tazo daidai wajen taji Hassan nacewa Hussaini yama sunan yarinyar? Yace mum tace Sunanta Nazeefa har ka manta, gham taji gabanta yayi me suke nufi da hakan? Tan take ta bata ranta ta wuce Daki, tana shiga taga Nazeefa ta shugo dakin balla Mata harara tayi, Ta janyo hannun Jamila tace Mata zo kiji sukai waje

Chan bayan dakin suka nufa, jamila tace” ya akai ne? Suhaila tace wannan wawiyar yarinyar da aka kawo mana tanaso ta bata mana Plan, nan take ta sanar da ita hiran Nazeefa fa sukeyi da alamu daya na sonta Ko qilama duka suke sonta, Jamila tai Wani zagi da seda na saurara na Dan mintina

Sannan tace” ubanta yayi kadan wlhi setabar gidan nan batasan Mu Su waye ba kawai ta ganmu a rigane, rada Mata wata magana jamila tai a kunne sannan ta Kamo hannun suhaila tace Mu koma daki zatasan da mu takeyi

Daki suka wuce KO wanne da abun da yake sakawa a ranshi

******

Bangaren Amaree kuwa Hakanan sukai baccinsu ba Wanda ya kula kowa, Mubeen kam ko a jikinshi Dan ko digon sonta bayayi

Haleema kuwa kasa bacci tayi Dan se kusan asuba ta samo ta rintsa Dan takaici

Safiya nayi Mubeen najin yunwa, har 10:am ba’a tashi an daura Mai break fast ba

Kitchen ya nufa yaga wayam, Kwafa yayi ya wuce sasan mamanshi, Knocking yayi tazo ta bude Dan Alhaji benan Ana daura auran ya tafi Dubai, mamaki tayi dataganshi tace” lafiya kuwa? Marairaice fuska yayi yace mum lfy lau nazo ne in gaisheki

Tace ohh too Mu shiga ciki, falo suka zauna ya gaisheta yace” Mum ba abincine yunwa nakeji, Sake baki tayi tace” Ina amaryan naka bata girka muku bane? Daga Kai yayi yace eh Mum, Hmmm tace Faeeza zata dafa muku ta kawo, yace” OK Har ya tashi zai tafi mamanshi tace” yauwa inason magana dakai kasan kuwa jiya nai mafarkin Nazeefa wai na binmu zata kashemu

Zaro ido yayi yace” Nazeefa kuma? Tace eh sosai itafa, nifa Bari kaji tunda tabar gidan nan kullun cikin mafarkinta nake Dan a tsorace nake

Mubeen ne wasu zafafan hawaye suka zobomai kamar zaiyi magana kuma sai ya fasa, kallon mamnshi yayi ba tare da yace Mata komai ba ya mik’e ya fita a ranshi yana cewa irinkune masu jama yaya Su shiga wani hali, da tun farko kun amince AI da yanzu bake ba wannan mafarkan,

Mamanshi na zaune ta rike hannu tana mamakin Mubeen, lalle kam sunyi kuskure, wata bngaren kuma tace gwanda haka da yanzu SIRRINMU ya fito fili

Feeeza ce ta fito
Mum tace Mata maza maza ta daura ma gidan duka breakfast hardasu Mubeen, Faeeza tace lalle ma haleeman nan

Daki ya wuce ya kasa zama gaba daya, shi Sam bega abun so a jikin Haleema ba balle ma yai shaawar kasancewa tare da ita, yana Cikin tinanin ne Haleema ta fito kan nan ba Dan kwali daga ita se night gown, Wajenshi tazo ta zauna ya murtuke fuska yace meye haka? Itama ta hada rai tace bakomai ta wuce daki tana zumburar Baki wai kai da mijinka hmmmm

*****
Bangaren Mansur Turaki kuwa, kullun cikin Tinanin Aljanarshi yake, mafarkai kam sedai idan be kwantaba, yanzu kwata kwata ya cireta a sahon mutane ya dauke ta tamkar aljanar da take zuwa Mai a mafarki, mafarkinta ya za man Mai jiki,

Yanzu haka ma Mansur ya tafi yin wani course a China, Gaba daya ya cire rai ma zaiga Aljanarshi ya maida hankali a karatunshi,

Friend dinshi Abdallah kuma ansa bikinshi, Ya so Ace Mansur ya ga Aljanar shi cos shi yayi imani mutun ce ba aljana ba, yayi kokarin ya fahimar da Mansur but ina ya kasa fahimta

Mansur ya Kara dawowa so silent ba ruwanshi Sunna SAK😁Kusan one week ba abun daya shiga tsakanin Mubeen da Haleema na auratayya kowa harkar gabanshi yakeyi, tun Haleema tana damuwa har ta Dena cos sheke ayarta takeyi ta waya, kiran aminiyarta tayi ta sanar da ita ga abun dake faruwa, kawarta was surprised tace ya akai haka karkiban kunya mana duk gogewarki, wai nace ba auren soyayya kukai bane?

Haleema ta gyara murya tace” i to told you earlier Yar aikin gidansu fa yakeso so I don’t think yana sona nima fa kinsan bawai sonshi nakeba kawai Dan kudinshi nakesonshi, karaf a kunnan Mubeen lokacin yazo shiga dakin sai ya kasa kunne yaji, jin alamun tafiya taji da sauri ta kashe wayan Adaidai lokacin Mubeen ya shugo dakin

Wayartane yai ringing Mubeen ya kalleta yace, pick d call mana ba kiran wayarki akeyiba? Haleema cikin kwarewa na yan duniya tace” wai subar mutun yaci amarci bazasu bari ba sun dinga damun mutun da Kira kenan, A ran Mubeen yace saifa amarci kamar zaiyi dariya ya fuske ya dakko laptop dinshi yana Dan dube dube, Haleema kuwa text taima kawarta tace” I’ll call you later, BOO nanan, no need ki re reply ma, kawarta na gani tai murmushi…..

Bangaren Mansur Kuwa yanzu hankalinshi ya kwanta ya murje yayi kyau sosai yayi concentrating akan karatunshi, kana ganinshi kasan he gat no Prblm

Nazeefa Kuwa itama ta sake jikinta sosai ta saba da yan gidan sosai kwana biyun datai saboda tanacin abinci masu kyau, fatarta tayi kyau sosai ta murje, shape din jikinta ya Kara fitowa, Hassan da Hussaini kuwa dukansu ba Wanda be sonta dukda sunada wa enda zasu aura amma duk Wanda ka ganta dashi zaka aza saurayintane Dan sun dauketa tamkar irin Favorite cousin dinnan Dan jininsu ya mugun haduwa

Hankalinta kwance sedai tana Dan samun matsala da jamila da suhaila Dan suna Dan jejjefa Mata magana, nasan readers zasuso kuji shin wanene wa ennan yan Matan..

Suhailat Yar kanwar Hajiya bilkisune daga wani kauye aka Dakkota, farace sosai kasancewar buzayene, tun ta Fara girma akaga irin me dakko maganar nan ne a kauye cos tun bata tafasaba takeso ta kone sai hajiya bilkisu tace a kawota gidanta tasata makarantar primary tagama, kafin taje secondary school ne, lokacin yan gudun hijira aka kwasosu mota gudu, Sarki yaje ya gansu yaji jamila nata kuka akace Ina iyayanta akace batada kowa sai ita kadai ta rage sai sarki yace a bashi ita yazo da ita gidanshi

Cos lokacin sa’oin junane da suhailat sai ahaka hadasu waje daya, kasancewar itama ta gama primary se Sarki ya sakasu a secondary school me tsadan gaske, So komai tare sukeyi har suka gama zasuje Jami’ah sukace basason karatun aure sukeso a tinaninsu KO Sarki me tausayine zaice Bari ya hadasu da yayanshi aure sukaji shuru bama alamun wannan niyyar ga twins din sunqi Su furta suna sonsu Su kuma Su suhailat so sosai suke musu…wannan kenan

Jamila da Suhailat tunda suka fuskanci Nazeefa tazo gidan da farin jini suka tsaneta Dan abubuwa da dama suke Mata da yake Nazeefa tasha gwagwarmayar rayuwa duk abun da zasui mata baya damunta Dan wahala wanne ne bata ganiba so KO a jikinta hakanan take ta hakuri har tai wata daya tana shanye abubuwan da suke mata

Bangaren Mubeen kuwa har yau ba abun taya shiga tsakaninsu

Washe Gari Monday ta tashi da sassafe ya shirya ya tafi hospital abinshi Haleema na bacci tashi tayi taji kanshin tirarenshi, Shuru tayi tace wato harya fita! Kuka ta farayi tana zaman nan ya isheni ta lakubo wayarta Kiran kawarta tayi ta Sanar da ita komai tace na gaji wallahi I think I’ll let mummy knw halin da nake ciki

Kawartace me suna *Mamashow* tace haba meye aikinmu duk gogewarki ace kinsaka sanin yanda zaki ya kulaki wai ko beda lafiyane?

Haleema tace wani irin beda lafiya lafiyanshi kalau Kasai he doesn’t love me ne, Mamashow tace that aside Kina gidane ne tace” Ina zani? Tace alright ganinan zuwa kawo miki tiraren da nake amfani dashi Haleema tace OK tashi tayi tadan gyara dakin Tana jiran kawarta

***
Mubeeen kuwa Zaune yake a office yaje ward round ya dawo yana zaune yana Dan yin research,

Dr bashir shi ma yana office ya kalla agogo yaga12.00pm yace wa dayan abokin aikinshi yace bare naje na duba wani Frnd Dina OK yace Mai, motarshi ya dakko ya tafi Hospital din Su Mubeen, Samunshi yayi a zaune yayi shuru

Dr B.yace Ango Ango kanajin dadi fa, Mubeen yace wani irin dadi fita office da safe da Nazeefane yaushe Zan fito yanxu

Dr. B yace kullun bakinka Nazeefa yake furtawa ka rabu da ita mana Wani kallo ya wurga mai besan sanda yace sorry ba, Dr. b yace ya amarya?

Mubeen nan ya bashi labarin tunda fa tazo gidan KO hannunta be rike ba, DR B ya zare ido yace what? Bakada hankaline kasan hankinta na kanka ko to wallahi Bari kaji ka gaggauta bata hakuri Dan bakasan halin da take shiga ba

Mubeen ya kalleshi yace” Dan kawai bama……se yai shuru

Dr. Bashir yagane abun da yake son fada yace eh shi fa, gaskiya abokina ga gyara ba haka akeyiba kayi hakuri Komaifa zai wuce kasan Mata idan sunason Abu ba’ai musu ba se Su nema ta wata hanyar….Allah ya tsaremu Amen

Mubeen yace to inshaa Allah nan dai sukai hirarsu Dr.Bashir ya koma wajen aiki Mubeen kuwa ya shiga tinanin duniya🤣

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *