RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 10 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
Shatima ya kalli agógonshi, sha dayan dare sam bai so ya kai wannan lokacin ba, alhali yana dakin Nafisa, domin shi ya san korafi ta da mita, har bai so ya mata wani kuskure, don baya son tun yanzun ya fara nuna fushinsa.
Kuma fita ce ta kama shi ta dole za su ga Gwamna. Daga can suka wuce bikin wani abokin aikinsu. Shatima ya mike tare da dafa na kusa da shi.
“Abubakar ba zan iya jira a gama wannan Dinner din ba. domin iyalaina suna zuba ido.” Shima ya mike, “To ai dole nima in tashi tun da
kai za ka sauke ni a kawo, ka manta motana tana can gurin aiki?” Shatima yayi fakin ya fito, duk da yayi ma
Nafisa sako ta waya cewa sun fito, amma haryanzun gaban shi yana faduwa.
Ya kwankwasa kofar, kusan sau hudu, sannan ya kira layin ta sau uku, amma bata daga ba, ya saka makullin mota yana kwankwasawa.
Ranshi ya soma ɓaci, domin yasan taji. Har ya fusata zai tafi mota ya shiga ya kwanta, don ba zai je dakin wata ba ya zama sabuwar matsala. Sai ya ji karar bude kofa. Ya waiwayo, ta bude ta leko fuskarta murtuk!
Ya ce, “Saboda wulakanci kina jina ina buga kofa
amma ki ka kasa zuwa ki bude min, na kira ki nanma ba ki daga ba?”
Juyawa tayi, shi kuma ya bi ta ranshi ɓace. Ya shiga dakinshi, ita kuma ta wuce nata. Ya gama al’amuran rayuwarshi da ya saba kafin ya kwanta. Sannan yayi kwanciyarshi.
Nafisa tayi tsammanin ya shigo ya roke ta, ko ya lallasheta. Sannan ya yi alkawarin ba zai sake yi mata irin haka ba, amma sai taji shiru. Ta tashi tayi ta kai-kawo.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Yayi rigingine idanunshi lumshe, yana nazari a kan halayan matansa din nan guda hudu. Bai ji shigowarta ba sai dai dan kukanta yaji, ranshi ya kara baci. Ya bude ido, sannan ya tashi zaune.
Itama ta zauna. Cikin kuka ta soma korafi, “Ni kullum in dai girkina ne sai ka nuna rashin kulawarka kaina, ni nasan kafi son su a kaina, nasan ni ke sonka amma kai ba ka sona.
Kana nuna min bambanci karara.” Ya daga mata hannu, cikin daga murya ya ce, “Wai ke ba ki da fahimta ne? ke kullum cikin korafi, bana turo miki message ba?
Ke in dai ina dakinki bani da kwanciyar hankali. Ban san me zan yi miki ki yarda ina sonki
ba.” Ta tsugunna ta hau kuka me karfi. Ya tashi ya
koma falo ya kwanta.
Nan ya kwana, da safe ya shiga dakin shi ya samu bata ciki, yayi wanka ya shirya. Bai ji motsinta ba ya leka kicin babu alamun zata hada mishi abin kari, don haka ya sabi jakarsa ya kai mota.
Ya nufi dakunan sauran kamar yanda yayi tsammani. Haka ya samu Amna tana bacci, a cikin kwana ukun da ba a dakinta yake ba, bai taba samun ta ido biyu ba.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya shafi kumatunta tare da sumbatar leбunanta. Ta bude ido. Ya ce, “Honey baccinki yayi yawa.” Ta yunkura ta tashi zaune. Nima ban san wane irin bacci nike yi ba honey ya zauna bakin gadon.
Ta ce, “Baccina ya karu, sai in kai karfe daya fa ban ji na gaji ba.” Ya rungumota zuwa jikinshi. “Ko an samo mana baby me hana bacci ne?” Tayi dariya “Haba dai, lokacin al’adana bai kai ba tukunna. Kuma naga Anty Amarya ta gidanmu tana rashin lafiya sosai, tayi ta amai.”
Ya kai hannu ya shafa damammen cikin ta, “Bani da ajiya ke nan?” Ta ce, “Babu, ina jin dai soyayyar da ka ke kashe ni da ita ne in kana gurina, sai in baka nan ta sani kasala.”
Ya mike tare da cire ta daga jikinshi. “Bari in tafi kada nayi latti, ki tashi ki dan karya sai ki koma bacci, abincin safe yana da muhimmanci a gurin dan Adam.” Ta ce, “To.” Suka yi sallama.
Yana shiga gurin Aliya ya same ta, kwance kan kujera tana kallo. Ya ce, “Kin yi abin kari kuwa don nan zan karya?” Ya fada tare da zama kusa da kafarta. Yasa hannunshi ya dafa kwafrinta. Ta kalle shi sannan ta mike zaune ta gaida shi.
Ya amsa tare da nanata zancen abin kari. Ta ce, “Na zaci wasa ne.” Ta mike da sauri ta dauko
Www.bankinhausanovels.com.ng
flaks na ruwan zafi tare da jera masa kayan tea a gabansa..
Cikin sauri taje kicin ta soyo masa kwai zuciyarta cike da son jin abin da yasa bai karya dakin Nafisa ba, har wani bangare na zuciyarta yana addu’ar Allah Yasa fada suka kwasa, zata dan bigi cikin shi taji.
Yana ci yana sa mata albarka, kuma a ranshi yana fadin Aliy matar rufin asiri ce.’ Ta ce, “Nafisa bata jin dadi ne?” Ya kalle ta, “Eh tun jiya jikinta ba dadi.”
Gabanta ya fadi, a ranta ta ce, “Kar dai ciki ne?” Tayi murmushi “Allah Sarki, zan je in dubata.” Ya ce, “A’a kada kije, kin san ba kowa ke son sannu ba a ciwo.”
Aliya ta ce, “Haka ne.” Nafisa tana daga cikin wadanda ba su son sannu. Ta ce, “Allah dai ya bata lafiya.” Sai da yayi tam! Sannan ya shiga gurin Salma. Tana zaune kan kujera, yau dai da kewar gida
ta tashi, tun da tazo bata kara jin labarin iyayenta ba, kuma babu wanda yazo dubata.
Bai zauna ba yana daga tsaye ta tsugunna ta gaida shi. Ya ce, “Yau kuma ya naga fuska babu
annuri?” Salma ta ce, “Dama ina son kazo in ce maka ni zan je Zariya yau.”
Ya ce, “Me ake yi a can?” Ta ce, “Ni dai ina son in ga su Inna ne gashi har an yi arba’in din Babanmu, kuma ban je ba.” hawayen da suka taru a ramin idonta suka zubo kan kumatunta.
Ya tako zuwa inda take, yasa hankici ya share mata kumatunta ta inda ruwan hawayen ya bata. Ya ce “Kin ga nayi latti.” Ya fada tare da kallon agogon hannunshi.
“Ki kwantar da hankalinki, in na dawo zamu yi maganar. Ni mun yi waya da Auwal jiya, duk suna
lafiya. Me za ki dafa min yau?”
Ta ce, “Duk abin da ka ce, bayan ko na dafa baka ci, sai ka ce ka koshi?” A ranshi ya ce, ashe tana sane. Ya ce, “Yau ba zan ci komai ba, zan ci naki ne amma ki min tuwo me kyau kar fa ya kone, bana son abu me kauri.”
Ta ce, “Miyar me za ayi?” Ya ce, “Kubewa danya.” Yasa hannu a aljihu, ya ciro dubu daya, “Gashi ki sai abin da ba ki da shi. Ke baki da fridge shi yasa ni ke baki kudin nama, su kin ga suna dashi, ki ba Baba Maigadi ya siyo miki.” Ta ce, “To.” Suka yi sallama ya tafi.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Nafisa ta tabbatar ita ce baya, don yana fita ta biyo bayanshi, taga shigarshi dakin Amna. Yau minti sha daya ma ya kwashe dakin ‘yar gwal dinshi kuma har minti sha uku.
Itama Salma yau ta samu minti tara, gashi har latti yayi saboda ya duba lafiyar wadanda yake so a rayuwarsa. Kila ma ya fada musu cewa sun samu matsala ne tunda ko’ina ya kara lokaci fiye da da.
Nan take taji zuciyarta tayi mata amanna da zargin ta. Don haka tasa sabon kuka ta shige uwar-daka.
Aliya ta gama karinta, dama tuni ta kammala gyaran dakinta. Tayi wanka, riga da siket ta saka na atamfa bata daura dankwali ba, ta yafa gyale ta nufi sashen Nafisa, don tana son sanin ciwon da Nafisa din ke yi, fatanta dai ya zama ba ciki ba ne.
Ta murda kofar ta shiga da sallama. Babu kowa a falon, sai da ta kare ma ko’ina kallo, a ranta ta ce, ‘Ashe itama an zuba Naira itam
a dai kujeru saiti biyu ne, sai dai na Amna sun fi tsada.
Ta kalli gurin Dining, ashe itama dai tana da su, ta taba baki, sannan tayi sallama. Can Kasa Nafisa ta jiyo sallamar, ta tashi ta fito. Ganin Aliya sai ta hade ranta tam!
Www.bankinhausanovels.com.ng
Aliyar ta ce, “Ina kwana, ya jiki?” Nafisa ta ce, “Wa ya ce bani da lafiya?” Aliya ta ce, “Mijinki da ya zo ya karya a gurina, ya ce baki jin dadi shi ne nazo in ga ko zan iya taimaka miki da taimakon farko.
Ran Nafisa yafi na da baci, ta ce “Fitar min a daki, kun ji dai da gulmarku ke da shi, kya fadi gaskiyar abin da ku ka tattauna, za ki zo kina wani wai kin zo duba ni, ja gulmarki ki fita.”
Aliya ta fito jiki babu kwari, sai dai da taje daki ta nutsu tana nazarin maganganun Nafisar, ana ta tunanin Nafisar tana da cikin tabbas, kila bata son ya fada ne take zargin ko ya fada. Kila shima ta fada masa bata son a ji ne shi
yasa ya ce kar taje ta gaida ta. Ran Aliya yayi
matukar baci, in zarginta ya tabbata lallai shirinta zai rushe.
Ta dauki wayarta ta shiga kiran Aisha. Ta daga tare da fadin, “Uwargidan Shatima, mai mulkin zuciyar Shatima da iyalanshi.” Aliya cikin sanyin jiki ta ce, “Hmm! Kawata ai wannan mukamin yana nema ya kufce min.”
Aisha ta ce, “Da aka yi me?” Ta ce, “Nafisa, wannan ‘yar uwar tashi ciki gare ta. Aisha ta ce, “Ke fa?” Aliya ta ce, “Shiru, kuma duk ranar da
Www.bankinhausanovels.com.ng
yake dakina sai mun yi mu’amala da shi.” Aisha ta ce, “Abin Allah ke nan, to yanzun ke ya za kiyi?” Ta ce, “Shi ne na kira ki in ji ko da wata shawara.” Ta ce, “Kin sha kwayoyin nan masu
daurayo mahaifa? Suna taimakawa kin sani.” Aliya ta ce, “Duk wata kwaya da na san zata taimaka min na siya nasha. Maigadi na rubuta na ba ya siyo min, don shima da ya gani sai dai na ce masa su ne ni ke sha.in cikina yana ciwo don nayi masa karyar ciwon ciki.”
Aisha ta ce, “To ki jira kila nan gaba kadan ke ma ki samu. Ki dai yi kokari ne ki ga cewa kimarki bata girgiza ba a gurinshi.”
Aliya cikin damuwa ta ce, “Ai na so ‘ya’yana su zama sune manya, dadin rike gida ke nan.” Aisha ta ce “Ba ki san in mace ta koma gurin miji yafi komai dadi ba, ko ‘ya’yanki ne kanana sai ki ga suna juya manyan don kaunarki ce zata shafe
su, kuma dole a zauna haka. Dubi gidan Hajiya Rayya mana Maman kawarmu Sa’ida, ita ce ta biyu, amma dubi yanda
take baza iko, ‘ya’yanta suna wadaka.” Aliya ta saki ranta har tayi ‘yar shewa, “Kuma fa haka ne. Su Sa’ida muna gama Secondary a ka
Www.bankinhausanovels.com.ng
kai su Umra, amma Tahir babban wansu an kasa biya masa kudin Makaranta.
Aisha ta ce, “To ai yanzun shagon saida waya da gyaran waya ya bude. Su ko su Sa’ida suna Ghana, şun jima suna hira kafin daga baya suka yi sallama da cewa tayi ta addu’a.
Nafisa tana kwance, tana jiyo sallar Azahar ana kira. Har zuwa yanzun bata karya ba, bakin ciki ta rasa inda zata saka kanta ace wai da miji ma ba ka da sirri, komai sai yaje ya fada ma kishiyoyi.
Sallama ta sake ji da bugun kofa, tsaki taja tareda fadin “Wace munafukar ce kuma oho!” Tayi banza da bugun. Sai da ta jiyo an shigo falon ana sallama. Ta dauki muryar Anty Maimuna kanwar Mamansu da ke aure a cikin Jaji (Barikin Sojoji), mijinta soja ne.
Cikin sauri ta fito da murna tana fadin, “Haba! Ni naji kamar muryar Anty, Anty sai yau?” Ta sauke ‘yar da ke hannunta, Nafisa ta dauke ta ta nufi cikin uwar daki tana fadin Anty shigo ciki kawai.
Kan gado ta sauke yarinyar tana kallonta tare da tambayar “Ina su Hisham?” Antyn ta ce, “Yana Makaranta, ko ba Makaranta ba zan zo da ita ba. Nasrin din ma don dai taki zama ne.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Nafisa ta ce “Gara ma da ki ka zo da ita na ganta.” Ta mike ta kawo mata ruwa da lemon roba. Ta ce, “Bari in dora abinci Anty, ina nan kwance ko karyawa ban yi ba.”
Anty Maimuna ta ce, “A kan me za ki zauna da yunwa ga fuskarki ma duk a kumbure sai ka ce kin ci kuka?” Nafisa tayi rau-rau tare da fadin “Hmm! Bari Anty Maimuna, wallahi ina cikin wani hali a gidannan. Sai da nayi ta yiwa Mama mita a kan wannan auren ta ce ba haka ba, gashi yanzun tun ba a je ko’ina ba bakin ciki zai kashe ni.”
Anty Maimuna ta zaro ido, “Fada min abin da ke faruwa don Allah, ke da mijin ko ke da kishiyoyi?” Nafisa ta soma kuka, “In su ne akwai wadda zan daga ma kafa ne? shi ne da kansa. kullum in dai yana dakina to fa sai sanda yaga dama zai dawo, in yi kwalliya in ta jiransa a banza.
Karfe shida fa yake dawowa, amma ni jiya sai sha dayan dare. Nayi magana ya shiga fada min maganganu, har da yin yaji yana kwana a falo.
Kuma gashi babu sirri, da safe yaje ya barbada ma matansa komai.” Ran Anty Maimuna ya baci, ta ce “To mene ne na zuwa ya fada musu don yaja miki raini?”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG