RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 13 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 13 BY HALIMA K/MASHI

 

 

Ya rungume ta tare da fadin, “HaKika kin san……….

Yá mike,

“Bari in gwada wa Nafisa, Aliya ta yi ‘yar dariya tana sake bin hotunan da

kallo. Ya fita ya barta nan tsoron zuciyarta cike da

takaici. Tunda aka yi haihuwar ta lura Shatima ya zama

kamar wani soko.

Natisa kuwa da ta kalli hoton cewa ta yi, yaron

mai kyau abinshi. TA shafa cikinta tare da fadin, “Ni ma

Allah ya sauke ni lafiya”

Ya dora tafin hannunshi a kan nata,

“Ameen

Sweetyna. Amma da wa ki ka ga yaron yana kama?”Ta dan yatsina fuska,

“Da mamansa mana”

Ya ce,Kin duba da kyau?”

Ta yi zooming din hoton,

“Ga hancin nan irin

na Mamanshi”

Ya san kishin Nafisa don haka sai ya ce,

“Ni nafi ganin kamarshi da ke”

Ta kalle shi,

“Da ni kuma?”Ya ce,

“Eh mana kin san da ni ki ke kama”

Ta yi murmushi,Wai da gaske ina kama da

kai?»Ya ce,

“Sosai ma, in na cikinki ya fito kin ga

shi ke nan mun samu

“yan biyu, don na san da mu zai

yi kama”Ta sake kallon hoton,

“Guda daya ta tura maka?”

Yace

“Suna da yawa, bude ki gansu”

Tana kallon hotunan tana fadin,

“Ka tura min hotunan a wayana

Ya ce,To kin kirata kin mata barka?”

Ta ce, Ba ni da lambarta, kira min ita da

kanka Nafisa da Amna sun gaisa, inda Amna ta yi wa

Nafisa fatan sauka lafiya, bayan ta yi mata barka. Ran

Shatima ya yidadi, domin kullum yana addu’a Allah ya hada kan iyalansa.

Salma ba ta san da batun haihuwar ba, sai da taga Shatima da Aliya za su je Zaria wai za tayi wa su Hajiya barka. Ta tsinci zancen ne a bakin Aliyar

lokacin da ta zo daukar zanin gadonta da ta shanya a

kusa da motar da suka hau, tana fada ma Nafisa.Nafisa ta Ce,

“Ku gaida su, ni na kira ta a waya

ba iya zuwa zan yi ba

Salma ta kalli Shatima, sannan ta kalli Aliya ta

Ce,Anty wace ce ta haihu?”

Aliya ta kalli Shatima, ya daka mata tsawa,

Da Allah ni shiga mu je”

Ya yi baya da motar tamkar zai ture Salma,

tana jin lokacin da Aliya ke fadin,

“Ba ka fada mata

haihuwar Amna ba?”

Ba ta ji me ya ce ba suka wuce. Baki Salma ta

_tabe tare da fadin,

“Allah ya raya”. Har zuciyarta ta ji

dadin labarin. To sun dawo tana Zaria din ne ko ko?

Ba wanda zai ba ta amsa don haka a fili ta ce,

“Oho”A daki ta kira Badi’ atu ta ce,

“Ashe Amna ta

haihu?”Badi’atuta.ce,

*Kina nufin ba ki sani ba?” Salma ta ce, suna Zaria din ne?”Cikin mamaki Badi’atu ta ce,

Bakya gidan ne Kin yi tafiya?

Salma ta ce,

“Hmm, ina nan wallahi, amma

Yaya bai fada min ba”

Badi’atu ta cE

“Wai kun samu matsala da shi

ne na ga rannan da ya zo na tambaye shi ke sai na ga

ya hada rai, sannan ya ce kina gida. Da ko da kanshi yake min zancenki”

Salma tace

“Tun laifin da na ce miki na masa

da sallah shine har yanzu bai huce ba. Ko magana da kyar yake amsa min’

Badi’ atu ta Ce,

“Wai ba ki ba shi hakuri ba ne?”

Salma ta ce,Na ba shi har sau ba adadi, amma ya ki hakura

Badi’atu ta ce,

“Wai wane irin laifi ne haka mai

zafi?”

Salma ta yi shiru, Badi’atu ta ce, “Kina jina?”

Salma ta Ce,

“Ina jinki, sai dai in yi miki sako

ki karanta”Badi’ atu ta ce,

“To ki yi min sakon”

Ta rubuta mata sako kamar haka.

“Ya neme ni ne na kasa yarda, don ina jin tsoro

shine yake fushi

Badi”atu ta kira Salma ta ce,

*Ke ma kin san dole ya fusata”

Salma ta Ce,

«To ai daga baya na zo na ce na

yarda; kuma na bi duk wata hanya don in ba shi hakuri

amma yaqi, har ma na saba da yanda ya koma min yanzu”

Badi’ atu cikin tausayawa ta cE

“Sai dai in ba ki

hakuri in ce ki ci gaba da addu’a da kuma yi masa biyayya tunda ni ma ba wai na yi auran ba ne bare in

san ko akwai wata dabara. Hajiya kuwa bawai tana yinki ba ne bare in kai mata kara

Cikin sauri Salma ta ce,

“Don Allah ki taimaka

Karki fada, ke ma na fada miki ne don in ji sanyi a

raina, ba wai don ki ba ni mafita ba. Ina son in yi wa Hajiya barka ne”

Badi’atu ta ce,Bari in turo miki lambarta,

amma ai maijego England ta haihu sai ta dawo za a yi suna

Salma ta ce,

“Na ji tafiyar, na za ta ta haihu sun

dawo ne. to ki turo min lambar har da ta kaka

Badi’atu ta ce,To, ko kuma ki fada ma kaka

din tunda na ga ita tana yinki sosai, kin ga murna da na

kai mata sakonki na sallah? Ta ce, Shatima ke ce zai ci riba a cikin matanshi”

Salma ta ce,

“Allah sarki Kaka, Anty Badi’atu

ba zan kai mata Kara ba, kema amana na ba ki, insha

Allah ba zan taba kai Karan mijina ba har abada

Badi’atu tace

“To Allah ya ba ki ikon jurewa”

Nan suka yi bankwana. Ba a fi minti uku ba sai

ga sakon lambobi sun shigo. Ta kira Kaka ta yi mata

barka, Kaka ta yi ta saka mata albarka, sannan ta kira

Hajiya. Salma ba ta sha mamakin yanda Hajiya ta amsa

mata ba don ta zaci abin da ya fi haka ma.

An rada wa yaro

sunan

mahaifinshi

Muhammad Ja”afar, walima sosai Alhaji yayi a kofar

gidan, Shatima ma ya kasance a

abokansa. Dan sammako suka yi shi da Aliya.

Salma ta cire duk wata damuwa ta aje ta dage

da karatunta, yanzu burinta shine ta shiga islamiyya

Ta bari sai ranar da babu aiki ta same shi ko a

dakinsa yake. Tunda akwai islamiyya kusa da su, kuma

babu tsada in dai ya barta to za ta shiga ko a aljihunta

ne duk da ya rage abin da yake ba ta, ba ta fasa

adanawa ba.Gaban Salma yana faduwa ta nufi dakin Aliya.

Cikin sa’a sai ga shi ya fito sanye da jallabiya, da alamu ba fita zai yi ba don takalmin tsakar gida ne a

kafarshi. Ya kalle ta har zai wuce, ta yi sauri ta rusuna

ta sunkuyar da kai cikin tsananin faduwar gaba.

Ya katse mata tunani, ta ce,

“‘Amma da ma Yaya ina son in

roke ka ne ko za ka saka ni a islamiyya. Saboda duk na

manta da karatun da na iya

Shiru tayi, ta dago ta dube shi dan ta ga yanda

ya amshi maganar. Sai ta ga yana yi mata wani kallo mai cike da tsana, za ta fassara shi ko wulakanci, sai

kuma ta ga ya sa kai ya fita abinshi. Ta dan yi jim a

tsugunne, sannan ta mike ta nufi dakinta.

Sati daya tsakani ya zo ya aje mata wata leda akan kujera, ta fito kicin ta yi masa sannu da aiki ya

amsa, dan ta samu ma yau ya amsa mata tunda watarana ko kallo ba ta ishe shi ba.

Ya ce,Ga shi nan kayan islamiyya ne, ki

shirya anjima za ki soma zuwa

Cikin murna Salma ta ce

“Na gode, Allah ya

Kara budi

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *