RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 14 BY HALIMA K/MASHI
Ya fita ba tare- daya saurareta ba. Ranar ta
soma zuwa islamiyya, har da hadda za ta dinga zuwa
sati da lahadi.
Maijego Amna sun dawo ranar Shatira da
Aliya da su Hajiya suka dira Kano. Sun samu gidan
tankam da mutane, har sun soma tunanin ko sunan ake
An yi musu tarba, kuma an amshi kayan barkan da
suka kawo. Shatima yana jin dadin zai ga kyakkyawan
danshi, Hajiya kuma tayi tam da ganin yanda aka aje
kayan barkan kamar a wulakance, domin ta zuba kudi
a kan wanda ta amsa a gurin Alhaji sannan sun z0 da
manyan raguna guda biyu wadanda Alhaji Musa
mahaifin Nafisa ya siya. Ita dai Hajiya suna zaune ita
da Aliya da maman Nafisa a dakin mahaifiyar Amna.
Sun gaisa da mahaifiyar da sauran bakin da ke dakin.
Anty Amarya ita ce ta gabatar da su da kuma kayan da
suka kawo. ‘yan dakin tareda Momy tunda sukace an
gode ba su sake bi ta kansu ba, kuma ba su samu damar
matsar da kayan daga inda suke ba.
Amna ta nufi dakin da aka sauki Shatima
saboda lokacin da suka iso sannan take wanka. Ba su
jima da tashi ba, Anty Amarya tace ta shiga dakin
Momy su gaisa da su Hajiya. Ta shiga ta rusuna tana
gaida su.
Hajiya cikin son nuna itace surukarta, ta fara fadin
“Sannu ‘yata, sannu da arziki. Allah ya raya mana
Muhammad Ja’afaru
je gurin Shatima
Amna dai ta mike, tare da fadin, “Momy bari inje gurin Shatima
Hajiya ta wage baki cikin murna, ta ce, “Ai ko
dai yana can dakin ko? To ina jaririn
Momy ta kalle ta, ta yi murmushi ganin
zumudin da Hajiyan ke yi, sannan tace
“yana tafe
Hajiya, za a kawo muku shi. Yanzu ake shirya shi”
Aliya tace “Ni ma shi na Kosa in gani”
Amna ta yi sallama ta shiga dakin da Shatima
yake, ya aje wayarshi cikin sauri da doki ya nufi Amna
suka rungume juna. Suka sumbaci bakin juna sannan
suka zauna kan cinyarsa ya dora ta.
“Ina yarona ne?”
Ta sa hannu ta tallafi fuskarsa, “Ana shirya shi
ne, ba mu dade da tashi ba ka san shigowar asubahi
muka yi, sai kawai muka ci gaba da bacci”
Ya sa hannu ya shafa cikinta,
“Baby ya fito
ko?”
Suka sa dariya, ya ce, “Kin kara kyau Amna”
Ta ce “Ko?”
Ya ce, “Sosai kuwa”.
Aka kwankwasa Kofa, Amna ta mike da sauri
don ta san Sumayya ce. Shatima shi ma ya mike tsam
ya tari Amna, ya amshi jaririn. A Kirji ya manna shi
tare da lumshe ido. Wata irin Kauna mai tsanani yake
ji, da tsantsar son yaron. Kamshin jaririn ya sa shi kara
jin wani shauki, ya dago cike da matsanancin farin ciki
ya kalli fuskarta.
‘Amna na gode,Allah ya saka miki
da mafificin
alkhairi, don kin gama min komai
a rayuwata
Cikin jin dadi da alfahari tace, “Allah ne ya
ba mu ba wayonmu ba ne”
Ya ce, “Duk da haka kin yi dawainiya da cikin,
kin ba ni dan fari mai kama da ni, kuma ki ka zaba
mishi sunana
Ya sa bakinsa a kunnen yaron ya yi masa kiran
sallah, ya jaddada masa huduba. Sun jima har aka
kawo abinci, tare suka ci cikin kulawa da Kaunar juna.
Hajiya dai ta kasa cin abinci saboda har lokacin ba taga jikanta ba.
Aliya ta ce, “Wai ni a raka ni inda yaron nan
yake don shi muka zo, amma har yanzu ba mu ganshi
ba”
Anty Amarya tace, “Au na manta, ina zuwa”.
Can ta dawo, “Suna gurin Babanshi”
Hajiya tace
“A karbo mana shi”
Aliya ta mike, “Nuna min inda yake in karbo
shi’
Suka fita da Anty, Aliya ta Kwankwasa kofar.
Shatima ya ce, “Shigo”. Don a zatonshi Sumayya ce.
Tana sako kai ta ga suna kicin-kicin ba shi
nono, Shatima ne ma ke rike da nonon. Aliya ta yi saurin sakin fara’a tare da danne wani Kululun takaici
da ya taso mata, ta ce, “Haba! Ashe kuna nan da dan
muna can muna jiran gain jariri?”
Shatima ya ce.
“Au ba ku ganshi ba? Yanzun
yana cin abinci”
Amna ta kalle ta, “Da ma har da ke aka zo?”
Cikin mamaki Aliya ta ce,
“Ai mun gaisa kuwa
lokacin da ki ka zo kuna gaisawa dasu jiya”
Amna ta kalli yaron, sanna ta ce. “Ban luraba
Yaron ya ja nono da karfi, amna ta lumshe ido
tare da fadin, “Wash!”
Ya ce,
“Sanno”. Ya sa hannunshi yana shafa
mata baya
Aliya ta tabe haki tare da kau da kai, Amna ta
kalle ta, “Zauna mana’
Ta ce Bari in je kun kawo shi, muna dakin
Hajiyarku
Amna tace Momy kenan?!”
Aliya ta fice cike da jin zafinsu, amma tana
zuwa dakin sai ta saki fara a, “Za ta kawo shi.
Maman su Nafisa ta ce, “To ke me ya sa baki
karbo shi ba?”
Maimakon ta ce nono yake sha tunda ita mata
gani, amma sai ta ce, “Ina, gani dai Qila yunwa yakeji”
Hajiya ta dan yi shiru, domin yanzu ta yarda
Zarginta wulakanci ne kawai. Ita da jikanta na fari sai an mata wulakanci zata ganshi, bayan ta fi su iko dashi ma? Gashi ita kanta uwar maijegon sai wani jin kai takeyi, taki ko da hira da su sai labarinsu suke da
“yan uwanta da kawayenta.
Aliya ta katse tunanin Hajiya da cewa,
“Dubi yanda aka bar kayan yaron can sai zama a kan
akwatunan ake yi. ko magana za a yi musu su bude su gani
Kan Hajiya ya sake sosuwa tace Kar wanda
yayi musu magana, in mun tafi su zubar da shi
Mama tace Kar ki dau fushi da sauri Majiya,
kin san manyan nan sai a hankali, da ma hulda dasu sai hakuri*
Hajiya tace “Uhum’! Tafiya ma zan yi”
Ta ciro wayarta a jaka, tana nemo lambar
Shatima yana dagawa, tace
“To ya kamata mu tafi
haka ko?”
Ya ce, “Da sauri haka Hajiya? Ki bari mana Sai
yamma?”
Ta ce, “Ni yanzun zan wuce, in kuma ba za ka
tafi ba to mu je mu hau ta haya
Ko ba a fada masa ba ya san Hajiya ranta ya
baci, ya yi tsaki cikin tunanin me ya faru? Amna ta
mike,
“Tunda ya gama bari a kai shi su Hajiyar su
ganshi ko?’
Yace Yauwa, kai shi”
Sai yanzun ya gane abin da ya sa Hajiya jin
zafi. Tana ta zumudin ganin yaron, amma har yanzun
ba ta ganshi ba.
Amna ta shiga ta mika yaron ga Aliya tare da
fadin, “Ga shi”
Hajiya cikin
*yar gajeriyar fara”a mai boye
damuwa tace
“Da kun barshi ma Allah ya raya
Amna wadda ba ta cika damuwa da damuwar
mutane ba bare ma ta gane wai haushi Hajiyan ta ji, ta
ce, “Badi’atu ba ta z0 ba ne?”
Hajiya ba ta tanka ba, sai Aliya ta ce,
Sai ranar suna
Amna ta fita ta koma gurin mijinta.
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe